Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Friday, 7 December 2018

Barrister Salmah complete hausa novel document

adsense here
Barrister Salmah complete hausa novel document
[11/14, 11:41 AM] Salmah QueenπŸ’πŸ’…πŸ½: πŸ‘©πŸ»‍πŸŽ“ *Barrister Salmah* πŸ‘©πŸ»‍πŸŽ“


_*Written by Salmah Queen*_πŸ’πŸ’…πŸ½πŸ‡³πŸ‡¬ _God bless Nigeria_πŸ‡³πŸ‡¬
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*


_Ι―Ι› Ι–Ζ‘Ε‹Ε§ ʝųŞŧ Ι›Ε‹Ε§Ι›Ε™Ε§Δ…Δ±Ε‹ Ε‹Ι– Ι›Ι–Ε³Δ†Δ…Ε§Ι›, αƒͺΕ³Ε§ Ι―Ι› Δ…Ω³ΕžΖ‘ Ε§Ζ‘Ε³Δ†Ι§ Ι– Ι§Ι›Δ…Ε™Ε§ Ζ‘Κ„ Ε™Ι›Δ…Ι–Ι›Ε™Εž_


# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
_*Bismillahir rah manirrahim da sunan Allah me rahma mai jin kai zan fara rubuta wannan littafin Wanda yake cike da fad'akarwa da gami da ilman tarwa Allah ubangiji ya ban ikon kammala shi ameen*_Page 1-5Yau take talata da misalin 9:am a garin abuja cikin eagle square hall cike yake da mutane maza da mata kowanne ka ganshi fuskar sa d'auke take cike da farin ciki,
Hall din ne yayi shiru sakamakon tahowar shugaban baristocin nigeria ya k'araso sakamakon kiran da akai masa domin yin jawabi tare da rantsar da d'aliban

Tafi jama'ar wajen suka d'auka jikake raf raf raf d'aga hannun sa yayi alamun jinjina da nuna farin cikin,
Shiru ne ya jiyar ci hall d'in fara jawabin sa yayi ,sai da ya dau lokaci yana jawabi tare da nasiha ga d'aliban

Kiran d'aliban akai domin su fito a rantsar da su

Jere suke ciki kayan su na baristoci sun ja dogon layi su hamisin da tak'was abin gwanin sha'awa hannun su d'auke su ke da award,

Bazan iya misalta irin farin cikin dake d'auke akan fuskokin su ba

Gaba d'aya naji muryoyin su sun had'a baki suna magana nan take na maida hankalina wajen su,

"Munyi alkawari zamu kasance masu gaskiya da amana a cikin ayyukan mu ba son kai ko rashin adalci"

Gaba d'aya hall din ya dau tafi jikake raf! raf!! raf!!! Haka suka cigaba da yiwa k'asa alkawarurruka sannan nan suka fara sakkowa daga kan steps din zuwa wajen 'yan uwan su cike da farin ciki kasancewar su baristoci.

Wata matashiyar budurwa nagano tafe take cikin nutsuwa har ta k'araso wajen wasu da ke zaune cikin farin ciki ta rungume su

Cikin kuka take magana "Umma yau Allah ya cikan burina nagode ma Allah" cikin jin dadi wadda aka kira da Umma da dago ta tana share mata hawaye "ba abinda zamu cewa Allah sai godiya kiyi amfani da abun da kika fad'a ki kasance mai gaskiya da amana da adalci karki kasance mai karb'ar cin hanci domin tauyewa wasu haqqin su" Umma ta fad'a cike da farin ciki
"To Umma in shaa Allah zan kiyaye"

Ido suka had'a da Abban ta hannun sa ta rike sannan ta mika masa award din karb'a yayi sannan ya had'a da hannun nata ya rike "duk abinda zan fad'a miki Umman ki ta fad'a sai dai na k'ara jaddada miki  cewa kikasance mai gaskiya a cikin aikin ki koda koda kuwa aikin ya biyo ta kaina Allah yayi miki albarka ya kare ki daga mahassada" gaba d'aya muka amsa da "ameen"

"Wai waya ga wata akan kujeran barrister nida 'yar shila" ya Salim ne yai magana zumb'uro baki nai had'e da Kai masa duka caraf ya rike hannun
 "tuba nake ranki shi dad'e ina taya ki murna Allah ya taya riko ya baki ikon aiki da gaskiya"
 Ya fad'a tare da rissinawa "amin" nace cikin jin dadi hade da mitsinin sa a kumatu
"Irin wannan mitsini haka kamar 'Yar bare-bari kin ci bashi"

Rungumar da akai mata har sai da suka kusa zubewa k'asa "bestie yau Allah ya cika mana burin mu ko batai magana ba nasan maryam ce ko k'amshin turaren ya isa ya sanar da ni hakan.

Kuka suka fara " hmmm sufa mata haka suke komai kuka farin ciki Kuka bakin ciki Kuka ko Abu ne ya fiye burge su yanzu sayi masa kuka" ya Salim ya fad'a

Wasu dattawa ne suka k'araso wajen nan mazan sukai musabaha matan suka gaisa cikin girmamawa daman can sun San junan su har k'asa na durk'usa nagaida iyayen maryam nan suka kuma yimana nasiha gaba d'ayan mu

Nan kowa ya fara hawa mota dan komawa garin su  nan muma muka hau tamu motar nida Umma muna baya sai ya Salim a matsayin driver sai kuma Abba a gefen sa nan muka hau hanyar *kano ta dabo tumbin giwa*sai kusan biyu da rabi sannan muka Iso

A gajiye muka shiga gidan nan 'yan gida suka taso cike da farin ciki aka soma murna kamar ranar suka fara ganina

Shiri sosai school of law bagwada dake kano take domin dumin gudanar da partyn da ta shiryama d'aliban nata da sukai grad a the efficient inda kowane d'alibi aka bashi damar gayyatar 'yan uwa da abokan arzik'i.........πŸ–ŠUrs Salmah queenπŸ’πŸ’…πŸ½
[11/17, 11:47 AM] Salmah QueenπŸ’πŸ’…πŸ½: πŸ‘©πŸ»‍πŸŽ“ *Barrister Salmah* πŸ‘©πŸ»‍πŸŽ“


_*Written by Salmah Queen*_πŸ’πŸ’…πŸ½πŸ‡³πŸ‡¬ _God bless Nigeria_πŸ‡³πŸ‡¬
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*


_Ι―Ι› Ι–Ζ‘Ε‹Ε§ ʝųŞŧ Ι›Ε‹Ε§Ι›Ε™Ε§Δ…Δ±Ε‹ Ε‹Ι– Ι›Ι–Ε³Δ†Δ…Ε§Ι›, αƒͺΕ³Ε§ Ι―Ι› Δ…Ω³ΕžΖ‘ Ε§Ζ‘Ε³Δ†Ι§ Ι– Ι§Ι›Δ…Ε™Ε§ Ζ‘Κ„ Ε™Ι›Δ…Ι–Ι›Ε™Εž_


# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.comcomPage 6-10
_Albarka da nasara sun tabbata ga wanda yake kyautatama mahaifan sa kasance mai biyayya sai kasami cigaba a rayuwa,Ka kasance mai yiwa iyayenka biyayya domin watarana kaima mahaifi ne nashiha ce Allah ya sakawa iyayen mu da aljannna ameen_ πŸ‘ŒπŸ»
Salmah kenan tun safe k'awayen ta ke kiran ta domin shirin partyn nasu kwance take a d'akin ta shiru kamar ba kowa wayar ta dake jone jikin charge ta fara ringin bestie maryam ne ya fito kan screen d'in saura kad'an kiran ya tsinke sannan ta d'auka "wallahi kedai kin fiye Jan aji da yawa Allah da ya katse kiran bazan kuma kiran ki ba" maryam ta fad'a "haba bestie na to ai in baki kira ba ni sai na kira balle ma baza ki iya jure rashin kira na ba"

"Kira nawa nai miki baki picking ba"

"Ayya sowie ban gani bane kin San bazan k'i d'aukan kiran ki ba ynx na fito daga wanka ne pls"

"Tom naji sai shegen dad'in baki ko shima wajen k'walliayar baza ki ba"

"Ni gaskiya baza'ae min ba sai dai na rakaku"

"Kut ke kin ma isa ae wllh ko kina so ko baki so sai anyi ki zama cikin shiri yanzu zamu k'araso" kit ta kashe wayar

Kayan da muka k'arbo daga wajen tela nagama gogewa jaka na da takalmi na d'aukko naji muryan su maryam da Aysha a tsakar gida suna gaishawa da Umma

Da sauri Aysha ta shigo d'akin "to tunku sai ki taso mu tafi kin San k'awalliya da cin lokaci" maryam kuwa kayana dake gefen gado da zuba a jaka nan suka jani muka fita sai da naima umma sallama sannan muka tafi wajen make-up d'in

Sai da akai musu sannan akai min light make-up dan ko jam bakin arzik'i ba'a sa mata ba amma hakan besa ta kasa yin kyau ba duk da ba fara bace amma tana da kyaun fata nan muka sa ankon grad din nan me kwalliya ta fara d'aukan mu photo.

"Idan nayi editing pictures d'in  zan turo muku"
 "OK tom shikke nan"
"to sai kun dawo"

Nan suka tafi basu zame ko ina Ba sai the efficient inda tuni jama'a sun halarta kowa kagani cike da farin ciki
nan aka hau yin pictures da friends

Waje na samu na zauna daga can gefe ina iya gano Aysha da saurayin ta ita kuwa maryam ta shige cikin jama'a kamar k'amshin dahuwa lol

Waya na na ciro na fara aikin selfie gaskiya ni kai na nasan nayi kyau nan nan fara juya ido tubarkallah daman akwai shi, k'aran shigowar message naji life partner nagani fuska d'auke da murmushi na bud'e

Take annurin fuska na ya d'auke
 "please my future kiyi haquri bazan sami damar zuwa ba yanxu muka shiga meeting ne kuma ba lallai mu fito da wuri ba kiyi haquri amma zan san yadda za'ae na..."

Ban k'arasa karanta wa ba na fita daga ciki kamar nai Kuka haka fuska ta tayi maryam ce ta k'araso da sauri "tun d'azu nake neman ki" shiru nai mata ban magana ba
Dan Kuka zai iya zuwa idan nayi magana
"Lafiya me ya faru haka ran ki ya b'aci"?

Mika mata phone d'in nayi nan ta karanta " mtsww wllh kina da matsala akan haka zaki Kuka kawai share kinga da ba wani babban uzirin ba abinda zai hana shi zuwa just forget taso muje ku gaisa da sweet hrt d'ina"

Hannun na tafara ja "cika ni ba inda zani ae dole kice na basar kin san naki swtyn yazo"

Hakuri ta fara bani da k'yar na tashi muka tafi

A bakin motar su muka ganshi shi da abokin sa gaisawar mutunci mukai sannan na tafi wajen 'yan  gidan mu

"Kai sa'eed wannan fine gal d'in fa amma dai maryam k'awar ki ce ko uhmm gaskiya ina ciki"

"Kai ko gajiya da magana baka yi" sa'eed ya fad'a

"To ae irin wannan ba'a sanya da su"

"Ae kuwa kama fita dan wannan da kake gani amarya ce" maryam ta fad'a

Wata irin zabura yayi "haba dan Allah da gaske kike ko kuwa dai baki son bani itace" ya fad'a yana kallon abokin sa sa'eed

"Allah da gaske nake"
"Oh my gosh!"

Ita kuwa har b'acin ran ta ya tafi tuni ta shige cikin jama'a kamar ba ita ba............πŸ–ŠUrs Salmah queenπŸ’πŸ’…πŸ½
[11/20, 10:05 AM] Salmah QueenπŸ’πŸ’…πŸ½: πŸ‘©πŸ»‍πŸŽ“ *Barrister Salmah* πŸ‘©πŸ»‍πŸŽ“


_*Written by Salmah Queen*_πŸ’πŸ’…πŸ½πŸ‡³πŸ‡¬ _God bless Nigeria_πŸ‡³πŸ‡¬
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*


_Ι―Ι› Ι–Ζ‘Ε‹Ε§ ʝųŞŧ Ι›Ε‹Ε§Ι›Ε™Ε§Δ…Δ±Ε‹ Ε‹Ι– Ι›Ι–Ε³Δ†Δ…Ε§Ι›, αƒͺΕ³Ε§ Ι―Ι› Δ…Ω³ΕžΖ‘ Ε§Ζ‘Ε³Δ†Ι§ Ι– Ι§Ι›Δ…Ε™Ε§ Ζ‘Κ„ Ε™Ι›Δ…Ι–Ι›Ε™Εž_


# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.comcomPage 11-15

_*Ka kasance mai yin sallah akan lokaci dan watarana itace zata tayaka kwanciyar kabari,Ka kasance mai yawan istigfari don samun kusancin ubangijinka,Ka yawaita yin hailala koda yaushe domin shine mafi soyiwar kalami a gurin Allah*_


Daga wajen taron sukai sallama da k'awayen ta nan suka taho gida ita da 'yan uwan ta,

Da sauri na fad'a toilet dan yi alwala har anyi magariba ana ta kiran sallar isha'i

Na idar da sallah ke nan ina azakar dan ban samu nayi da yamma ba waya na ya soma ringing life partner tsaki nayi sannan nayi banza da kiran wani kiran ne ya kuma shigo nan ma ban d'auka ba sai a na uku dan nagaji dajin ringin sannan na d'auka murya k'asa-k'asa sallama yayi kamar yarda ya saba  a k'aaan mak'oshi na amsa

"Tun d'azu nake kira baki picking ba lafiya"? Shiru nai masa " tab yau na tab'o 'yar rigima ayi min afuwa a fito ina waje"
"Ni ni ni gaskiya" be jira na gama magana ba ya kashe wayar

Kamar nai Kuka haka na fita da hijjab d'in da nai idar da sallah a  falo na tarar da su  Umma "Umma Ahmad yana kira na" "karki dad'e" haka kawai ta fad'a

Yana tsaye tun daga soro nake jin k'amshin turaren Wanda yaso mantar dani laifin sa bakina na kuma zumburowa

Shi kuwa wani lafiyayyen murmushi ya saki tun kan na k'ara so ya tsugunna a k'asa "am on my kneels gimbiya ta kaina bisa wuya na, nazo a hukuntani akan laifin da na yi"

Allah sarki tausayin sa ne ya kamani amma ban nuna masa ba" to ka tashi ni ban son naga kana min irin haka"

"Sai kin hakura zan tashi"
"Allah in ba zaka ta shi ba zan koma gida" na fad'a ina k'ok'arin juyawa da sauri ya tashi

"Haba tawan d'an saki ran naki mana ko ma samu ruwan sama ya zubo" yana magana yana kallon sama har 'Yar dariya yaso ban amma na dake "ni ban son wannan ae salon sab'o ne"

"To ya gajiya ina taya ki murna Allah ya bada sa'a yayi jagora amin" muka amsa gaba d'aya

Dai dai saitin kunne na yazo ya rad'an wata magana ban San lokacin da nasaki dariya ba har da d'an rissinawa

"Ni yau banyi niyar dariya ba ka sani"
 "Ya ma za'ae nazo na tafi ban saki dariya ba so kike na kasa suku ni"

Nan suka shiga ba da tsare-tsaren su daga nan yayi mata sallama ya tafi ita kuma ta shiga gida kamar ba wadda ta fito da fushi ba falon Umma ta shiga nan ita ma ta zauna tana cin abinci suna shirin su ko wane shiri suke yi ku dai ku biyo ni4:45am na asuba alarm din wayar ta ya soma cikin bacci ta sa hannu ta kashe 5:00 am wayar ta kuma yin k'ara sai dai wannan ba alarm bane kira ne cikin bacci ta d'auka ba tare da ta duba  ba "nasan baki tashi ba an yi kira kije tashi kiyi alwala haba yanzu fa na kwanta har asuban yayi" "eh ki tashi mana oya oya kinje fili kinyi rawa dole Kika sa tashi sallah maza tashi"

"Ni ba rawar da nayi to tashi ni zan tafi massalaci karki koma sai kiyi azkar" be jira amsa ba ga kashe

"Da k'yar ta tashi idon ta da k'yar take bud'e shi sabida bacci ta shiga toilet sanyi ruwan me yasa tayi da wuri ta fito amma da sai ta cigaba da bacci a toilet

Tana idar da sallah tana shirin komawa ya kira " kinyi azkar d'in ne"? "A'a sai anjima zan yi"

"Yanzu me kike jifa da bazaki ba ban son wasa fa da addini" kashewa nayi dan ya fara ta kura min
Sarai yasan taji haushi amma ya share ta koda idar bata bi ta kasan ba ta koma baccin ta,

Magana sa'adah k'anwar tace ta she ta "ke kuma mene kin ishi mutane da magana sai kin samin ciwon kai" "Umma ce tace nai miki magana ki tashi ki wanka ki fito ki breakfast" "to naji fita"
Har ta fita ta dawo
"Oh ya ilahi me kika dawo yi"?
" na manta ban gaishe ki ba good morning aunty "
Fuska na saki nace "morning ya kike ya gajiya" sai alokacin na kalli agogo 7:6 cikin sauri na kammala komai na fito a gurguje na karya dan duk inda su maryam suke suna hanya............πŸ–Š


Urs Salmah queenπŸ’πŸ’…πŸ½πŸ‘©πŸ»‍πŸŽ“ *Barrister Salmah* πŸ‘©πŸ»‍πŸŽ“


_*Written by Salmah Queen*_πŸ’πŸ’…πŸ½πŸ‡³πŸ‡¬ _God bless Nigeria_πŸ‡³πŸ‡¬
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*


_Ι―Ι› Ι–Ζ‘Ε‹Ε§ ʝųŞŧ Ι›Ε‹Ε§Ι›Ε™Ε§Δ…Δ±Ε‹ Ε‹Ι– Ι›Ι–Ε³Δ†Δ…Ε§Ι›, αƒͺΕ³Ε§ Ι―Ι› Δ…Ω³ΕžΖ‘ Ε§Ζ‘Ε³Δ†Ι§ Ι– Ι§Ι›Δ…Ε™Ε§ Ζ‘Κ„ Ε™Ι›Δ…Ι–Ι›Ε™Εž_


# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.comcomPage 16-20*Idan xakayi taimako karkayi saboda wata manufa kayi saboda Allah ladan ka yanaga Allah,idan mutum yayi maka abu Mara kyau katuna da maikyau dayayi maka saboda kowani mutum yanada hali maikyau yana mummuna,karka bari bacin rai yadinga ziyartar zuciyarka saboda duk lokacin da ranka yabaci shaidan ne acikin jinin jikinka da ruruhinka nasiha ce*πŸ‘Œ
Na fara sharar tsakar gida ke nan naji sallamar su "har kun iso sannun ku" nan suka shiga d'akin Umma ni kuma na k'arasa sharan a d'akin na tarda su suna karyawa zama nai suna ci ina hira "ke wllh da k'yar na tashi sabida gajiya" maryam ta fad'a tana tura dankali a baki "ke dai maza ci mu tashi mu tafi kar lokaci ya kure wai umma ice dak ba wannan ce tai girkin nan ba naji yayi dad'i da yawa" aysh ta fad'a tana kallon Salmah "ke da halla can an fad'a miki ban ita girki bane ke dai ci karki k'ware"

Haka suka gama ci Abin sha'awa k'awaye kamar 'yan uwa kan su a hade "to ni dai nace Allah ya bar zumunci"

A gurguje sukai ma Umma sallama sannan suka fita Aysha ce ke Jan motar basu zame a ko ina ba sai gidan kunshi bakowa sai wasu 'yam mata su biyu

An gama yiwa d'aya nan suka zauna ana hira har aka gama yiwa 'yam matan
"To da wa xan fara" mai kunshin ta fad'a tana murmushi maryam da Aysha har suna had'a baki "da wannan" suka nuna Salmah dan itace amarya

Nan mai Kunshi ta ran gad'a masu baki da ja masha Allah sunyi kyau ba irin na Salmah domin ya hau fatar ta sosai sabida gyaran jiki da ta sha

Yinin ranar Sam basu zauna ba

A gidan d'an hausa sokkoto road dake kano da yamma gidan ya fara cika da mutane ga wajen da aka tanada dan amarya ya sha traditional ducration masu kid'an k'warya kuwa sai kid'a ake inda nago fili cike da manyan mata ana ta rawa

"Haba wai baza ku k'araso bane tuni an fara cika ko so kike ayi Abu da magariba " aunty ga munan fa muna state road kad'an ya rage mu k'araso"

Kashe wayar nai na mik'awa Aysha idona ya kawo k'wallah "haba mene haka karki b'ata kwalliyar mana" maryam ta fad'a "ni wllh duk na gaji a d'aga anki dame xan ji ko'ina na jiki na ciwo yake"

"Ke dai k'ya fad'i gaskiya kawai kice yau baki ga swt kalbin ki ba shima duk inda yake yana can yana tunanin ki" duka na kai mata dai-dai nan muka k'araso wajen kamun.

Wow masha Allah abinda naji jama'ar wajen suna fad'a da sauri na k'arasa dan ganewa idanuna kai gaskiya duk hassadar me hassada bazai samu hanyar da zai kushe ta ba dan ko ta ina ta had'u

Tsawon ta baya bukatar takalmi mai tsawo baka ce chocolate colour,ga idon nan masha Allah fari tas sai kayi tunanin yasa eyelashes siririya ce bata da jiki amma hakan be hana ganin shape d'in ta ba tubarkallah komai yaji.

Maryam da Aysha ne suka sata a tsakiya sauran kuma suka rufa musu baya nan suka rankaya har gurin zaman amarya

A nutse take tafi kamar yadda ta saba
Nan ma fara ganin hasken flash ko ta ina da k'yar aka samu aka dakatar da masu d'aukan photo akai ma  amarya kamu irin na al'adar hausawa duk nakosa a gama dan wata irin gajiya ce take lullube ni idona kuwa har yaji yake

Nan aka fara watse wa kowa ya tafi cike da fari ciki,

Haka sauran rana ku kowacce da event d'in da aka shira duka ango yaje in banda kamu Wanda shi ka d'aine be je ba...........πŸ–ŠUrs Salmah queenπŸ’πŸ’…πŸ½πŸ‘©πŸ»‍πŸŽ“ *Barrister Salmah* πŸ‘©πŸ»‍πŸŽ“


_*Written by Salmah Queen*_πŸ’πŸ’…πŸ½πŸ‡³πŸ‡¬ _God bless Nigeria_πŸ‡³πŸ‡¬
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*


_Ι―Ι› Ι–Ζ‘Ε‹Ε§ ʝųŞŧ Ι›Ε‹Ε§Ι›Ε™Ε§Δ…Δ±Ε‹ Ε‹Ι– Ι›Ι–Ε³Δ†Δ…Ε§Ι›, αƒͺΕ³Ε§ Ι―Ι› Δ…Ω³ΕžΖ‘ Ε§Ζ‘Ε³Δ†Ι§ Ι– Ι§Ι›Δ…Ε™Ε§ Ζ‘Κ„ Ε™Ι›Δ…Ι–Ι›Ε™Εž_


# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.comcomPage 21-25


*Haba 'yar uwa ki sani kefa uwace wata ran ke zaki bada tarbiya kuma duk irin halin da shi 'yar ki zata tashi,mene amfanin beyewa samarin zamani ana d'aukan ki ana shan minti ke kuma sabida k'awadayin abinda za'ae miki ba Wanda duka-duka bazai wuce wani abun ba mene amfanin ki bari jikin ki mai daraja ya zama kamar kasuwa kowa ne kato yazo ya kai hannu dan kawai kar aga bakya rike babbar waya bakya wanka irin na waccan, kisan shifa namiji duk abinda yayi ado kefa rayuwar gajeriya duk dadewar ki wata ran gidan miji za'a kai ki, ki rike mutuncin ki domin mutunci madara ne nasiha ce*πŸ‘ŒπŸ»

Yau ta kasance ranar lahadi da musalin 11:00 jama'a suka shaida d'aurin auren Dr.Ahmad idris me k'wabo da sis da Brr.Salmah Muhd

Kowa yana San barka inda marok'a suke ta fama aikin su

K'arfe hud'u tuni gidan su amarya sun fara shirin raka amarya gidan ta nan aka kai ta gidan ta gwanin sha'awa kamar kar na fito komai a tsare yake nan mutane suka watse aka bar maryam Aysha sai aunties d'in ta nan suka hau gyaran gidan suka bi kowane sako suka sa turare kan kace me tuni gida ya d'au k'amshi nan sukai mata sallama

Dan bazan ce rakiyar ango dan wannan al'adar bata yarda da ita ba haka ango ya shigo gidan tun daga haraba k'amshi ya fara yimasa Barka da zuwa haka ya shiga cikin gidan cike da farin ciki da annashuwa

Sallama yayi sannan ya shiga d'akin a hankali ta amsa sallamar basu b'ata lokaci ba sukai alwala sannan sukai sallah raka'a biyu kamar yanda addinin mu ya tanadar

Kajin da ya siyo ya d'aukko ya zuba a plate wayyo tuni k'amshi ya maimaye d'akin sannan d'aukko fresh milk masu sanyi gaske

Tuni yawu na ya fara gudana ganin ba samu zan ba basu San ma da ni ba yasa na tashi na bar d'akin ina had'iyar yawu

To ayi bacci lafiya ango da amarya.

Anyi kwanan nan farin ciki kiran sallah asuba ne ya farkar da shi a hankali Ya tashi sai da yai wanka sannan yayi alwala bakin gadon ya zauna yana kallon fuskar ta cike da so da k'auna "Allah nagode ma daka bani mata ta gari" abinda naji ya fad'a ke nan

A hankali ya fara shafar gefen fuskar ta kamar a mafarki taji anan hura mata iska a kunne  a hankali ta bud'e idon ta cike da bacci ganin sa yasa tai sauri rufe fuskarta da hannun ta

"Asuba tayi amarya ta" nai kamar banji shi ba k'ok'arin Jan bargon yake da k'arfi na rike

D'aga ta yake k'ok'arin yin "a'a ni kabarshi zan tashi da kai na" "ki bari na taimaka miki"
  "Nop ka tashi ka tafi masallaci kaji zasu tayar karka rasa jam'i" *madallah da samun mace ta gari da watace Sam yau bazai sami damar tashi asubar ba bare yaje masallaci*
Da sauri ya tashi "ki kular min da kanki" ya fad'a yana fita

Sai da ta tabbatar ya fita sannan ta tashi da k'yar jiki duk yayi tsami a haka ta shiga toilet nan ta tarda ruwan zafi a abun wanka  shiga tai sai da ta tabbatar ko ina na jikin ta ya gasu sannan ta fito

 *point of correctioga amare idan mace aka kaita gidan miji lokacin da zaki wanka karki zuba detol kamar yadda kukaji anan fad'a hakan yana da illa domin shi detol anyi shi ne domin kashe k'ayoyin cututtuka nan kuma jikin akwai k'wayoyi masu amfani in kika zuba detol tofa har su zai kashe dan haka a ruwan zafin gishiri kawai zaki zuba*

Wanka tayi sannan tai alwala a hankali ta fito duguwar riga kawai ta jira sannan ta tayar da sallah,tana cikin sallah ya shigo zama yayi yana kallonta wani irin son ta yana k'ara shigar sa

Alamun ta idar dan kunya irin tata ta hana  ta ko  d'aga kan ta,tsugnnawa yayi gabanta ya riko hanun ta
"barka da asuba zaujatee tunda ba zaki gaishe ni ba" a hankali ta bud'e baki tace "good morning"shima alamar motsawar bakin kawai ya gani ya gane  " morning dear ya gajiya"shiru tai ba amsa "fatan ba inda yake miki ciwo ko"? nan ma shiru " oh ya salam kiyi magana mana"
Murmushi yayi Wanda har sai da tajiyo sautin sa
Kan ta Ankara tuni ya d'auke ta caraf sai kan gado.................πŸ–Š[11/23, 8:19 PM] Salmah QueenπŸ’πŸ’…πŸ½: πŸ‘©πŸ»‍πŸŽ“ *Barrister Salmah* πŸ‘©πŸ»‍πŸŽ“


_*Written by Salmah Queen*_πŸ’πŸ’…πŸ½πŸ‡³πŸ‡¬ _God bless Nigeria_πŸ‡³πŸ‡¬
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*


_Ι―Ι› Ι–Ζ‘Ε‹Ε§ ʝųŞŧ Ι›Ε‹Ε§Ι›Ε™Ε§Δ…Δ±Ε‹ Ε‹Ι– Ι›Ι–Ε³Δ†Δ…Ε§Ι›, αƒͺΕ³Ε§ Ι―Ι› Δ…Ω³ΕžΖ‘ Ε§Ζ‘Ε³Δ†Ι§ Ι– Ι§Ι›Δ…Ε™Ε§ Ζ‘Κ„ Ε™Ι›Δ…Ι–Ι›Ε™Εž_


# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.comcomPage 26-30
*ki zama mace mai aji kamun kai da nutsuwa yawan tara samari beda amfani karki bari ki zama kamar motar haya sai dai kowa ya tare ya hau nasiha ce*πŸ‘ŒπŸ»


"Pls dan Allah ka yi haquri"

"Au daman kina jina kika min shiru" to bakai ne ba"  sai kuma tayi shiru tuni ido ya kawo ruwa

Nan ya fara lallashin ta "ni ka k'yaleni bacci nake ji" ta fad'a a shagwabe

"Ni bazan k'yale ki ba sai kin kalle ni" ya fad'a yana k'waik'wayon ta

K'ok'arin had'a ido yake da ita amma duk yanda yaso had'a ido abun ya ci tura dan wata irin kunyar sa take ji 
Haka ya haqura ya k'yale ta cikin mintuna kad'an bacci yayi awon gaba da ita abun ka ga wadda ta gaji

Shima bayan ta yaje ya rungume ta kamar wani zai sace ta haka ya rike ta cike da tunani iri iri har shima bacci yayi gaba da shi .


K'aran phone d'in shine dake kan bed side drawer ya tashe shi sai da ya nutsu sannan Ya d'auka hajiyar sa ce

"Cikin girmamawa ya gaishe ta" ta amsa da kulawa "ya Yar tawa" kallon ta yayi tana baccin ta hankali kwace gefen fuskar ta ya sha a ranshi yace sleeping beauty
 "bacci take Hajiya"

"to ka gaishe ta,daman abinci driver ya kawo ya kuma tarar baku bud'e gidan ba sai kaje ka bud'e" kan yace wani abun ta kashe wayar

Nan ya tashi yaje ya bud'e sannan driver ya gaishe shi cikin girmamawa a dining ya ajiye sannan ya fad'a toilet har ya fito bata farka sai da ya gama shirin sa cikin shadda sky blue kai masha Allah ku zo kuga inda kyau yake Ahmad dogone yana da d'an kauri kadan baki ne me kyau ga sajen sa ya kwanta gefen fuskar sa abun sha'awa da ka kalle shi kaga cikakken namiji me hankali da kamala

K'amshi turaren da yake fesawa ne ya tashe ta daga bacci ta cike mudubin ya gano ta

"Kai madam irin wannan kallo haka kamar yau kika soma gani na" ya fad'a cikin tsokana

Har ta saba zumb'uro baki nan taturo shi gaba sannan ta juya kamar me bacci "kina wannan bakin da kike turowa gaba uhmmm"yayi murmushi tare karasowa inda take ido ta rufe ruf kamar me baccin

" kin gama kalle ni kuma kin wani juya irin bacci nan kike ko" wasa ya fara mata nan take ta tashi amma idon ta a rufe yake

"Kai wannan kunya taki tayi yawa ko Wanda suka zo daga rugar ku baza au nuna miki kunya ba,tashi in miki wanka ni yunwa nake ji" da sauri ta tashi "a'a ni dai"
Cikin ya shafa kamar bakomai a cikin haka yake lafe a jikin ta nasan yunwa kike ji"
Hannun ta cire sannan ta tashi ta shiga toilet.

Sai da tai wanka tsaf sannan ta fito lekowa ta fara ganin ya fita yasa ta fito ta fara shirin nata ae zama nayi na saki baki ina kallon ynada ake bin ko wane sako da lungu na jiki ana sa tutare har wani man kitso nagani kamar turare ta d'aukko ta fesa akan nata tab

Wannan shirin bana k'are bane shi kuwa Ahmad falo ya fito ya zauna yana kallo amma hankalin sa yana wajen Salmah

K'amshi turaren ta ne ya dawo da shi daga duniyar tunanin wata atamfa ce a jikin ta exclusive super holland me adon blue nan tasa yari blue da abin hannu sai takalmi shima blue

Ae tun da ta fito ya saki baki yana kallon har ta k'araso ta zauna a d'aya daga cikin kujerun falon

"Barka da hutawa" ta fad'a kan ta akasa komawa yayi kusa da ita nan ya d'aukko waya ya fara yimusu pictures wow perfect match abun sai Wanda ya gani

"Ka tashi muje kaci abinci kace kana jin yunwa" ba musu ya tashi suka nufi dining............πŸ–Š_ku fa yi haquri readers har yanzu ban iso gundarin labarin ba ina bin hanyar da zaku gane ne ku cigaba da biyo ni ina tare da ku masoyana love you all ina muku kallon luv_😍😍😍


Urs Salmah queenπŸ’πŸ’…πŸ½
[11/25, 11:56 AM] Salmah QueenπŸ’πŸ’…πŸ½: πŸ‘©πŸ»‍πŸŽ“ *Barrister Salmah* πŸ‘©πŸ»‍πŸŽ“


_*Written by Salmah Queen*_πŸ’πŸ’…πŸ½πŸ‡³πŸ‡¬ _God bless Nigeria_πŸ‡³πŸ‡¬
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*


_Ι―Ι› Ι–Ζ‘Ε‹Ε§ ʝųŞŧ Ι›Ε‹Ε§Ι›Ε™Ε§Δ…Δ±Ε‹ Ε‹Ι– Ι›Ι–Ε³Δ†Δ…Ε§Ι›, αƒͺΕ³Ε§ Ι―Ι› Δ…Ω³ΕžΖ‘ Ε§Ζ‘Ε³Δ†Ι§ Ι– Ι§Ι›Δ…Ε™Ε§ Ζ‘Κ„ Ε™Ι›Δ…Ι–Ι›Ε™Εž_


# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.comcomPage 31-35
*Duk zuciyar da take  mai yafiya, to mai ita zai rayu cikin hutu da nutsuwa,Duk rai da ta yarda da kaddara, za ta rayu cikin sa'aada (dadin rayuwa) da farin ciki,Duk mai,yawan maimaita"alhamdu lillah" farin ciki da jin dadi,Duk harshen da yake  istigfari kowane lokaci,zai samu budi kuma za a arzuta shi ta inda bai tsammani ba nasiha ce*πŸ‘ŒπŸ‘Œ

*S*aving din su tayi suka fara cin abinci tunda suka fara ci idon sa ke kanta sam ya hana ta sakewa sai juya cokalin take tana tunanin barkatai

"Madam wai abincin ne be miki dadi bane ko mai sai juyawa kike kin k'i ciki in wani kike so sai na tashi na girka miki"ya fad'a yana k'ok'arin tashi ban San lokacin da na rike masa hannu ba
"A'ah ka barshi kawai dai na k'oshi ne"
"Tab me kika ci kika k'oshi haba ni da nake so a satin nan naga kin yi k'iba ki zama kamar ki sau biyar "
 "Wai rufan asiri sai kacce wadda ta zo duniya dan ci"
Haka yai ta Jan ta da magana har ya samu taci abincin

Sai da suka d'an tab'a hira kad'an duk da ba sakin jiki tai da shi ba tashi tsaye Yayi "to swty bari naje na gaida su Hajiya daga nan zan wuce wajen su Umma na gaishe su suma"
Fuska ta cike da murmushi "tom sai ka dawo Allah ya kiyaye a gaishe su"

"Au daga nan ba irin 'Yar rakiyar nan tab"

Kai na sunkuye na tashi muka jera har bakin motar sa da sauri na k'arasa na bud'e masa ya shiga ina d'aga masa hannu har ya fita.

Sannan na koma cikin gida zuciya ta cike da son mijina

Waya ta na d'auka na kira Umma muka gaisa "Umma wai ba Wanda zasu zo ne " to kowa ya gaji yanzu ma suke tashi daga bacci"

"Umma dan Allah su zo wllh gidan shiru ba dad'i wllh" "to zan fad'a musu"
"Su zo fa da wuri"

Bayan mun gama waya da Umma Maryam da Aysha na kira sai da had'a mana conference call nayi muka sha hira nai musu bangajiya da godiya "wai dan Allah yaushe xaku zo ne "?
" ke ni wllh nagaji da fita amma ki kwantar da hankali zamu zo "Maryam ta fad'a nan mukai sallama anan kan kujerar bacci ya kwashe ni

Cikin baccin naji kamar waya ta na ringing ina bud'e ido naji kira na ake yi sis zainab nagani da sauri na d'auka " hello" ki fito ki bud'e mana mun zo tun d'azu" ko kan nayi magana ta kashe wayar

Da sauri naje na bud'e nan aka zauna akayi hira suka kuma gyara gidan basu tashi tafiya ba sai wajen 5:00pm

Wayyo da zasu tafi kamar na bi su.

Dawowa nai sai a lokacin na tuna da waya ta 5 missed call partner life Allah sarki ina k'ok'arin kiran sa ya kira

"Baby na kina ina na kira baki picking ba ko bacci kike"?

" A'ah su sis zainab ne suka zo shiyasa ban ji k'aran wayar ba"

"Oh shine ko a Neman ni Ina na Ina ta missing naki"

Hmm murmushi nayi kawai "ba sai kinyi girki ba ki zauna ki huta yanzu zan taho"

"To sai ka dawo Allah ya kiyaye min kai" "ameen mother of my kids"
Kiss ya watso min sannan ya kashe wayar

Wanka na shiga na b'ata lokaci wajen wanka sannan na fito na hau shiri

Light make-up nayi na feshe jiki na da turaruka sannan nai sallah magrib

Ina zaune na kunna kallo ke nan ko 5 minutes ban ba najiyo motar shi wata kunyar sa ce ta rufe ni tun kan ya shigo da sauri na fad'a toilet na fara had'a masa ruwan wanka

Tun daga falo yake ranga d'an kira amma ban amsa ba sai da na gama
 A bkin toilet d'in na ganshi "kina jina ina magana kikai shiru"

"Ina toilet ne kuma kasan ba'a magana a ciki"
 "Kefa baki tab'a bari aka ma ki da laifi ba sai kin kare kan ki"

"Hmm ga ruwan wanka nan kashiga kai wanka nasan a gajiye kake " duk Wannan magana kana a k'asa yake "

Riko hanun ta Yayi " zo ki taya ni wankan mana"da sauri na k'ace hannun na gudu falo ina ji dariyar sa ya shiga cikin minti kad'an ya fito cikin wata jallabiya Yayi kyau sosai.............πŸ–ŠUrs Salmah queenπŸ’πŸ’…πŸ½
[11/26, 10:22 PM] Salmah QueenπŸ’πŸ’…πŸ½: πŸ‘©πŸ»‍πŸŽ“ *Barrister Salmah* πŸ‘©πŸ»‍πŸŽ“


_*Written by Salmah Queen*_πŸ’πŸ’…πŸ½πŸ‡³πŸ‡¬ _God bless Nigeria_πŸ‡³πŸ‡¬
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*


_Ι―Ι› Ι–Ζ‘Ε‹Ε§ ʝųŞŧ Ι›Ε‹Ε§Ι›Ε™Ε§Δ…Δ±Ε‹ Ε‹Ι– Ι›Ι–Ε³Δ†Δ…Ε§Ι›, αƒͺΕ³Ε§ Ι―Ι› Δ…Ω³ΕžΖ‘ Ε§Ζ‘Ε³Δ†Ι§ Ι– Ι§Ι›Δ…Ε™Ε§ Ζ‘Κ„ Ε™Ι›Δ…Ι–Ι›Ε™Εž_


# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.comcom


Page 36-40

*Don't always think about how people treat you,because it will make you have a bad feelings to others,never  forget that everyone shall be rewarded according to their deed.*πŸ‘ŒπŸ‘Œ


Abinci ya taho musu daga gidan su nan suka ci
 "Af na manta ban d'aukko miki photo album na biki ba"
"Wai har an gama aikin sa"?
" to mene wahal sa inda da kud'i" "babu" na fad'a

Tashi Yayi ya fita sai gashi ya dawo da su a hannun sa zube su yayi guda uku ne
"Kai yaushe akai wanna pictures din da yawa haka"?
Ta fad'a tana k'ok'arin d'auka

Bud'e wa nayi na fara kalla kai na d'aurin aure ne munyi kyau a Wanda akai a gidan mu

Ina kalla yana ban labari

Dai dai nan nazo kan wani photo gaba d'aya maza ne kallon su nake mafi yawan su duk suna kama idona ne ya kai kan wani suna kama da Ahmad sai dai shi fari ne k'ur na kafe shi da ido
Ina tuna inda na san shi amma na kasa

" madam ya akai" ya katse tunanin da nake "amh wannan kamar na San shi"? Ta nuna shi

" a ina"? Ya tambaya ye ta "na manta may be ma me kamar sa na tab'a gani"

"Mukhtar ne cousin d'ina ne ya fita waje karatu ne ana hidimar bikin mu ya dawo shi yasa baki san shi " "yayi kyau"

Kallon na cigaba nan bacci ya kawo min ziyara hamma na fara ido na ya fara kankancewa

"Ya madam"? Ahmad ya fad'a dan ko motsin da be gamshe shi nai ba yanzu zan fara tambaya
" bacci nake ji" tattare kayan yayi ya ajiye ni kuma tuni na tashi na yi cikin bedroom

Ae a kwanakin nan banda aiki sai kalla photo album ina son tuna in da nasan mukhtar Wanda suke kira da dady sabida sunan kakan su Ahmad ne

Ina zaune da yamma nayi nisa cikin tunani

            ************

"Dan Allah ki taso muje" maryam ta fad'a tana Jan hannun ta "ni wllh ban son fita in yamma tayi titi duk ya cika kowa yana sauri ya koma gida"
"To mu ina ruwan mu dasu" maryam ta fada "ke wallhi in kina son Abu  sai kinyi kamar me"
"Lallai ma salman nan har ke zaki cewa wani haka ke fa in kika kafe akan Abu sai dai mutun ya haqura"

"Au haka ma kika ce to na fasa " ta fad'a tana ajiye mayafin doguwar rigar ta "sorry habibty girman kujerar ki pls" haka maryam tai ta dadin   baki Salmah ta tashi suka fita shop rite siyayya,

Haka suka shiga suna siyayyar su gwanin sha'awa

"Kai wllh nayi mantuwa" da gudu-gudu Salmah ya koma cikin "me kika manta"? Maryam ta tambaye ta " chocolates kin San ba yadda za'ae nazo nan ban sai chocolates ba" "Allah ya shirye ki nan suka siya suka fito
A d'aya daga cikin kujerun da suke wajen ta zauna " ya salam me kuma zamuyi anan "? Maryam ta fad'a " sha zan yi "dan Allah ki taso mu tafi kinga an kusa magariba kar ae mana fad'a a gida"
"K'aramin tsaki Salmah ta ja sannan ta tashi bud'ewa tayi ta fara sha tun a haraban wajen " wayyo ni 'Yar nan Salmah wai yaushe zaki girma" da sauri tace "gobe" "kalli  tafiya kike kina shan chocolate kamar wata baby "
Kokawa suka fara dai dai k'ara min titin bayan shop rite Wanda xai dawo da kai gandu maryam ce taci nasarar k'wace ledar chocolate d'in ae batai wata-wata ba kawai tai jifa da ita

"Kut ree wllh sai kin biya ni a bata " wata razananniyar tsawa aka daka musu sai lokacin suka lura da abun da sukai wasu samari ne su uku tsaye ledar da maryam ta jefar ta chocolate ta b'ata d'aya daga cikin su abun yaso ya bawa Salmah dariya ganin farar suit d'in sa ya b'aci amma sai ta basar

"Sowie" suka had'a baki suka fad'a "ke wace irin dabba ce xaki b'ata mutane kina gani" "kasan  dai ina sane bazan b'ata ka ba ko kayi haquri in zaka haqura" maryam ta fad'a tana Jan hannun  Salmah "in kuma ban haqura ba fa"? Ya fad'a a zuciye "sai ka rama" Salmah ta fad'a tare da watsa masa kallon raini

Kan su an k'ara ji kake tassssssss ya wanke fuskar maryam da mari

"Kut mele ci..................πŸ–ŠUrs Salmah queenπŸ’πŸ’…πŸ½πŸ‘©πŸ»‍πŸŽ“πŸ‘©πŸ»‍πŸŽ“ *Barrister Salmah*πŸ‘©πŸ»‍πŸŽ“πŸ‘©πŸ»‍πŸŽ“


_*Written by Salmah Queen*_πŸ’πŸ’…πŸ½πŸ‡³πŸ‡¬ _God bless Nigeria_πŸ‡³πŸ‡¬
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*


_Ι―Ι› Ι–Ζ‘Ε‹Ε§ ʝųŞŧ Ι›Ε‹Ε§Ι›Ε™Ε§Δ…Δ±Ε‹ Ε‹Ι– Ι›Ι–Ε³Δ†Δ…Ε§Ι›, αƒͺΕ³Ε§ Ι―Ι› Δ…Ω³ΕžΖ‘ Ε§Ζ‘Ε³Δ†Ι§ Ι– Ι§Ι›Δ…Ε™Ε§ Ζ‘Κ„ Ε™Ι›Δ…Ι–Ι›Ε™Εž_


# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.comcom
Page 41-50
*Haba 'Yar uwa me zasa ki banzatar da jikin ki,ki maida shi wata hanya ta samun kud'i, ya zaki saki jiki ga namiji bayan be zama mijin ki ba daga kawo kudin aure sai ki sakar masa jikin ki ki bashi damar taba ki yanda yaso ganin ya kawo kud'i wllh ki hankalta wani yana kawo kudi har da sa rana amma da ya samu abinda yake so shikke nan sai ya gudu ya barki kudin auren da kayan ki samarwa kan ki mafita shikke nan ya barki da kuka da nadama dan Allah mata mu dinga tunani nasiha ce*πŸ‘Œ

*K*ut mele si" salmah ta fad'a inda Maryam ke dafe da kuncin ta

Ae kan ya ankara tuni Salmah ta sharara masa wani k'yak'kyawan mari zata kai na biyu abokin sa ya rike mata hannu

"Kan bala'i" abinda mukky ya fad'a ke nan wata irin zabura yayi yayo kan su tuni sauran abokan suka rike shi

Fusge hannun ta tayi "ku barshi naga abinda zai min ashe kai d'an akuya ne ae kaine dabban tunda zaka d'aga hannu ka mari mace"

K'ok'ari yake su sake shi amma sun ki wani ne daga cikin abokan yai magana
"haba me kwabo da sisi ba girman ka bane ka tsaya kana fad'a da mace ba,please calm down bata san kai wane ba"

"Wane shi in ba dabba jaki mara hankali Wanda be San darajar mace ba,kai wannan da ganin sa besan darajar uwar sa ba" Salmah ta hakikance tana ta masifa

Ae tuni yai wani kukan kura yayo kan ta wasu maza ne suka shiga tsakanin su da gudu,

"Ae da kun barshi ba abinda zai iya"

Maryam ce take Jan hannun ta tana kuka please sis dan Allah ki taho mu tafi, "ke da Allah k'yale ni naga abinda zai min k'aramin d'an iska kawai" dan Allah Hajiya ki tafi be kamata ace mace mai daraja ta tsaya tana fad'a da maza ba" wani daga cikin mazan da suka shiga tsakani ya fad'a tare da tsayar musu da adai-daita sahu

Sai da ya tabbatar sun shiga sannan ya juyo inda su mukky suke "kai kuma kai hattara in haka halin ka yake to tun huri ka daina kaga k'aramar yarinya taima rashin kunya" "to ba gwanda ma rashin kunya ba akan ina namiji mace ta d'ga hannu ta maren ai daga wannan ranar na gama da duk wata tak'ama da izza" d'yan ya fad'a "to Allah ya kiyaye gaba aboki na ae hattara" suka tafi suka bar su tsaye

D'aya abokin nasa ne jibson yayi k'ok'arin Jan shi cikin mota

Cikin murya wadda take d'auke da tsan-tsan bakin ciki da bacin rai mukky ke magana "wllh tallahi sai nai maganin wannan yarinyar ko 'Yar uban wace ita kamar ni zata d'aga hannu ta mara abinda ko d'an uwana namiji beba bare mace"

"Kai ma da mukky duk wannan maganar k'ara haddasa ma bacin rai zatai kawai ka basar nan da gobe ma baka k'asar" mubaraq ya fad'a

Wata tsawa ya daka masa wadda ni kai na sai da na tsorata shi kuwa jibson dake driving wani wawan burki ya ja "ae wallahi ko lahira naje na dawo sai na rama indai ni nai mukky me kwabo da sisi....."

"Ah badai lahira ba mukky ka sassauta wannan ba irin matan da ka kai takawa ba ce"

"In magana zaka fad'an pls bud'e min na fita jibson

Su Salmah da maryam kuwa ba wadda taiwa wata magana haka suka cigaba da tafiyar kurame ana zuwa unguwar su Salmah ta fita " kayan ki" Maryam ta fad'a har ta fara tafiya ta dawo ta kab'a rai a b'ace kamar ita tai mata laifin

Tana shiga gida ko sallama babu tai hanyar d'akin ta "Salmah zo nan" k'arasowa tai ta zauna "baki iya sallama ba kuma kin shigo kamar wadda aka koro"
"Umma fitsari nake ji ne" "to koma mene kidinga sallama" daga haka bata k'ara magana ba ita kuma Salmah ta tashi tai d'akin ta gado ta fad'a ta tsunduma duniyar tunani
"Wllh ba namijin da zai taka ni na barshi ko dan uban wane bare ma harka d'aga hannu kai mari tab ashe da Maryam ce kad'ai zai iya dukan ta da sannun zanyi magani ko wane dan iskan namiji Wanda besan darajar mace ba indai na sami abinda nake so ba d'an me kwabo da sisi ba ko d'an biyar da goma ne" da sauri ta tashi tai toilet tayo alwala.........πŸ–Š*To fa ana wata ga wata,Ko shin wane mukky,zai zasu sake had'uwa da Salmah har ya rama marin sa uhmmm ku dai readers ku biyo ni*Urs Salmah queenπŸ’πŸ’…πŸ½[2/12, 10:30 PM] Salmah QueenπŸ’…πŸ½πŸ’: πŸ‘©πŸ»‍πŸŽ“πŸ‘©πŸ»‍πŸŽ“ *Barrister Salmah*πŸ‘©πŸ»‍πŸŽ“πŸ‘©πŸ»‍πŸŽ“


_*Written by Salmah Queen*_πŸ’πŸ’…πŸ½πŸ‡³πŸ‡¬ _God bless Nigeria_πŸ‡³πŸ‡¬
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*


_Ι―Ι› Ι–Ζ‘Ε‹Ε§ ʝųŞŧ Ι›Ε‹Ε§Ι›Ε™Ε§Δ…Δ±Ε‹ Ε‹Ι– Ι›Ι–Ε³Δ†Δ…Ε§Ι›, αƒͺΕ³Ε§ Ι―Ι› Δ…Ω³ΕžΖ‘ Ε§Ζ‘Ε³Δ†Ι§ Ι– Ι§Ι›Δ…Ε™Ε§ Ζ‘Κ„ Ε™Ι›Δ…Ι–Ι›Ε™Εž_


# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.comcom
Page 51-55

*Assalamu alaikum yan uwa na kuyi haquri na rashin cigaba da yin wannan novel din hakan ya faru sakamakon exam din da mukayi to da muka gama sai na nemi na huta na wani lokacin kun San jiki da jini ga kuma harkar karatun naija sai addu'a shiyasa amma in shaa Allah yanzu zan cigaba da yi muku shi a taikace har lokacin da Allah zai bani ikon kammala shi fatan za ku biyo ni cin kis cin kis, sannan ina godiya ga duk Wanda suke kira na suna min fatan alkhairi da Wanda masoya na nagode da nunan soyayyar ku gare ni,nima ina tare da ku a duk inda kuke nagode Allah ya bar zumunci*

Girgiza ta yayi a firgece ta kalle shi tare da murmushin yake "darling ka dawo ko waya baka kira ni ba" ta fada tana kallon sa hmm sai da yayi ajiyar zuciya sannan ya kalle ta cike da nutsuwa "baby wai meke damun ki haka kika fad'a cikin kogin tunani haka"?

" bakomai ba abinda nake shine yasa kawai kuma ma ae tunanin ka nake yi"
"Ah haba Wannan da ganin sa ba tunani na kike ba da nawa kike zan ga fuskar ki d'auke da murmushi amma kuma sab'anin haka ina tab'a ki kika firgita"
"To fa zaman gidan ne shiru ba kowa"
"kawai haka zaki fad'a baki tsaya b'oyen ba"

"To yanzu tashi muje toilet na had'a ma ruwa sai kaci abinci" cikin k'waik'wayon muryar ta yace "tom baby na" hakan da yayi y bata kunya had'e da dariya ta rufe fuskar ta "Allah sarki my queen ina son ki ga hankali g kunya" "nima ina son ka my king"

Haka ta had'a masa ruwan wanka da wayo ta fito daga toilet d'in ta nufi dining ta kuma shirya abinci nan ya iske ta da waya a hannu tana buga game "barka da fitowa darling dee" ta fad'a tare d mikewa ta soma zuba masa abinci kur ya kafe t da ido har ta gama "cokalin t mik'a masa y k'arb'a " oya muci mana" a shagwabe tace masa na koshi "be kuma mata magana ba ya fara cin abincin sa Wanda ya k'agauta ya ci sabida k'amshin sa har ya gama b Wanda yayi magana jefi-jefi yake kallon ta ita kuwa hankalin ta yana kan wayar ta Wanda ynz kuma da alama ba game take ba Abu ne mai muhimmanaci dan gaba d'aya ta tattara hankalin ta wajen
Gefen fuskar ta ya shafa " hada ido sukai yi nan suka sa kar ma junan su murmushi a tare suka had'a baki suka ce

 *Allahumma barik lana fihi wazidna min hu*

Hugging nata ta yayi a hankali ta zame sannan ta riko hannun sa kuje d'aya suka zauna cikin salo irin na masoya yake wasa da gashin kanta ita kuwa wani lumshe ido take yi a hankali yayi mata magana kamar me rad'a "baby na d'azu munyi magana da abban ki akan aikin ki cikin watan nan ake sa ran fitowar opper d'in ku ta fara aiki murya can k'asa tace " Allah ya nufa" dan ita tuni hankalin t yayi gaba barin wajen nayi dan kar naga abinda zai hanani bacci.
Wajen 9:00 na dare suna zaune kallo suke  ita kuwa wayar tace a hannun ta gyaran murya yayi kallon sa tayi tare d fad'in "sorry oga just one minute" hmmm nidai matsala ta dake "Wannan wayar" "Abu nake dubawa" to y shari'a?" "Hmm may be m a week d'in nan za'a yanke masu hukunci" "to Allah yayi jagora" amin

Kallon sa tayi cike da nutsuwa "darling wai yaushe zaka kai ni na gaida su Hajiya ne?"  "Kinga ko d'azu da naje sai da Hajiya aunty taimin maganar wai in bazan kawo ki ba to su zasu zo" kishiyar hajiyar su ke nan "tom zuwa yaushe ke nan?" "Da gobe in ka dawo daga office sai muje ko? " "eh tom shikke nan Allah yai nuna mana goben Lafiya" amin


Washe gari tun bayar fitar sa office take aiki tana gama gyara gidan naga ta nufi kitchen had'a cake naga tayi nan ta fara aikin sa kamin wani dogon lokacin ta kamalla nan ta soma donuts haka tai ta aiki kmr me shirin yi walima

K'arfe 3:00 yana gidan wata k'walliya naga tafi cikin atamfarta me ruwan gayen da ratsi fari mayafi d takalmi ma fari sai jakar hannu itama fara Masha Allah tayi kyau duk d ba gwanar lambata k'walliya ce ba,
Wajen hamper (abar jera flasks)
naga ta nufa d'auka tayi sannan tace masa "na shirya" agogon hannun sa ya kalla "keda kin matsu ki ganki a waje sai kace wadda gidan ke cizo" tuni ta kai mota "ka same ni a waje" da sauri ya bi bayan ta ya karbi hamper d'in "to ina zaki da Wannan kuma"? " su Hajiya zan kai ma" dai dai na suka k'araso wajen motar shiga tayi shi kuma yasa a baya sannan ya shiga suka tafi suna hira gwanin sha'awa a haka har suka isa gidan

K'annen sa ne a parlorn 'ya'yan Hajiya aunty suna ganin ta suka taso suka rungumai ta sannu da zuwa aunty........Urs Salmah queenπŸ’πŸ’…πŸ½
[2/16, 8:38 PM] Salmah QueenπŸ’…πŸ½πŸ’: πŸ‘©πŸ»‍πŸŽ“πŸ‘©πŸ»‍πŸŽ“ *Barrister Salmah*πŸ‘©πŸ»‍πŸŽ“πŸ‘©πŸ»‍πŸŽ“


_*Written by Salmah Queen*_πŸ’πŸ’…πŸ½πŸ‡³πŸ‡¬ _God bless Nigeria_πŸ‡³πŸ‡¬
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*


_Ι―Ι› Ι–Ζ‘Ε‹Ε§ ʝųŞŧ Ι›Ε‹Ε§Ι›Ε™Ε§Δ…Δ±Ε‹ Ε‹Ι– Ι›Ι–Ε³Δ†Δ…Ε§Ι›, αƒͺΕ³Ε§ Ι―Ι› Δ…Ω³ΕžΖ‘ Ε§Ζ‘Ε³Δ†Ι§ Ι– Ι§Ι›Δ…Ε™Ε§ Ζ‘Κ„ Ε™Ι›Δ…Ι–Ι›Ε™Εž_


# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.comcom
Page 56-60


'Yar uwa kin san cewa rayuwar aure zo mu zaune ce kuma zo mu b'ata, yau in an sha zuwa gobe sai a sha mad'aci,zaman aure Ibada ne, Ibada kuma tana tare da baraxanar samu cikas daga shaidan,zaman aure dole sai an sa hak'uri da juriya Abokin zamanki yana da halaye biyu, mai kyau da marar kyau, idan yayi miki marar kyau din toh ki hango abinda yayi miki me kyau sai hakan ya faranta miki kuma ya rage miki ganin laifin sa,
Tabbas rayuwar aure tana buk'atar hak'uri, juriya da yiwa juna afuwa,zaman lafiyar rayuwar aurenki tana buqatar agaji daga wajen Allah, saboda haka ki ringa saka shi acikin addu'o'inki,komai ya faru gare ki kai kukan ki wajen Allah hak'ik'a yana tare da ke kuma yana jin ki,ki zamo me sirri tsakanin ki da mijin ki, saboda haka ki taqaita bayyana matsalolin gidanki ko da ga waliyyenki ne,bare wasu k'awayen,sabida acikin makusan tan ki baza'a rasa mak'iyan 6oye ba, da masu miki hassada, saboda haka bayyana matsalolin gidanki na iya faranta musu, sai kiyi hattara da masu baki shawara,iya girki kwalliya tsafta,uwa uba biyayya na kuma kara soyayya Daga wajen mijin ki,duk kyaun ki in ba wad'an nan abubuwa to kuwa sunan ki sorry,Wannan nasiha ce baga matan auren kawai ba har yammatan dan suma wata ran zasu kasance matan aure.


                   ***


"Kai mene haka sai ku yarda min da ita kun wani kan k'ame ta kamar..."
"Toh ikon Allah Ahmad yaushe ka koyi rashin kunya" Hajiya Aunty ce ta katse masa maganar sa sum-sum ya shige d'akin Hajiyan sa yana sosa k'eya "hmm daman na fad'a miki ba'a yabon d'an kuturu sai ya shekara da yatsaya gaba d'aya yaran nan basu da kunya a fad'a kice banda shi yau gashi yayi a gaban ki" Hajiyar sa ta fad'a "kin ga be ma kula da ni ba ya tafi yana wani  sosa k'eya"

"Hajiya mun tsaya magana ko gaisawa bamuyi da 'yar tamu ba" kaina k'asa su Hamida,Jasmin sun sani tsakiya
kusan sa'anni na ne sai ma Afnan itace ma k'arama hira suke min amma kunya tasa na kasa magana sai Sai smilings da nake yi
Da sauri na durk'usa har k'asa na gaishe su cikin fara'a suka amsa

"Wai ina yake ne na wanke shi tas yanzu aka kawo min labarin yazo shi da matar sa" matar wansa ce Khadija da suke burmawa "gani wani abin zaki min" ya fad'a yana fitowa "me kuwa zan ma sai dai kawai nace kar ka sake ka koya ma k'anwa ta rashin kunya irin taka"
Dariya gaba d'aya parlon suka k'washe da ita

Gaisawa mukai da ita cike da kulawa kinga ni yanzu unguwa zani amma in shaa Allah zan zo na yini mu sha hira na baki labarin k'uruciyar mijin na ki" tafita tana dariya

Nan ta fita muka cigaba da hira sama-sama da su Hajiyan

"Ai kullum ya zo sai munce yaushe zai kawo ki sai yace be komawa gida da wuri sai da yaji mun ce zamu zo shine yau ya kawo ki yara ma suna son zuwa yace a barki ki huta sa zo" Aunty sa ce ta fad'a
 "wllh nima in son zuwa sai yace wai na bari a kwana biyu ma zo"

"To yanzu dai magana ta k'are tunda na kawo ki, af kinga na manta" hermper d'in ya d'aukko "Hajiya ga girkin amarya"
"Hajiya aunty ce ta k'arba kai masha Allah harda wahala" bud'ewa ta shiga yi "kinga kamar tason Alhaji yace ai masa chickenpepper" Nan kowa ya d'auka har kusan magrib ana tare ana hira, nan suka tashi suka bar mu da su Jasmin da Hamida

"Allah aunty in mun gama exam zamu zo mu taya ki kwana" Jasmin ta fad'a "kai amma da naji dad'i kuwa dan gidan shiru wata ran har tsoro nake ji" "aunty.." Da sauri na katse ta pls dan Allah kudaina cemin Aunty kunga duk age mate d'ina ne ni har kunyar amsawa nake" "tab ai gwanda ma ki koyi amsawa dan duk family d'in nan haka ake cewa matan yayye koda ka girme su" Hamida ta fad'a "OK naji amma ku dinga ce min Sister salma ba sai kunce Aunty ba" "tom shikke nan Aunty au Sis Hajiya Aunty tace kije daga nan sai kiyi sallah " tom nace tare da shi har d'akin suka raka ni, "to wai ku duk inda take kuna biye da ita ko hira kun k'i bari muyi ku fita ku bani waje" ta Kore su Haba Aunty muma ba sai ayi hiran da mu ba" Hamida k'yale ta su gana ai barin ta zaiyi ta kwana" jasmine ce ta fad'a tana kok'arin fita "lallai da yake kowa sha-sha-sha ne irin ku ba sai ya bar ta ta kwana Kinga shiga toilet kiyi alwala ki fito kiyi sallah"

"Hajiya Aunty ina Amaryar tamu yanzu ake cewa ta zo shine na shigo mu gaisa" "ai kuwa baza ka ganta ba tunda baka iya zuwa can ba"

"Haba zani mana kin San kullum cikin hidima muke da yau zani ni da friends d'ina sai kuma naji tazo"
"Daman lawyer ka karanta da sai yafi dacewa da ka iya shirya zance" Jasmin ta fad'a wallih ya mukky ka daina abinda kake yi"

Dariya suka yi Jan kunnen ta yayi ya fita "bari naje wajen amaryar ta ta nunan pictures din ta kamin naje har gida mu gaisa"

"Mukky Mukky na kuma maimaitawa a raina..............πŸ–‹Urs Salmah queenπŸ’πŸ’…πŸ½
[2/18, 2:11 PM] Salmah QueenπŸ’…πŸ½πŸ’: πŸ‘©πŸ»‍πŸŽ“πŸ‘©πŸ»‍πŸŽ“ *Barrister Salmah*πŸ‘©πŸ»‍πŸŽ“πŸ‘©πŸ»‍πŸŽ“*Story and written*
            *By*
*Salmah Queen*πŸ’πŸ’…πŸ½

πŸ‡³πŸ‡¬ _God bless Nigeria_πŸ‡³πŸ‡¬


® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_Ι―Ι› Ι–Ζ‘Ε‹Ε§ ʝųŞŧ Ι›Ε‹Ε§Ι›Ε™Ε§Δ…Δ±Ε‹ Ε‹Ι– Ι›Ι–Ε³Δ†Δ…Ε§Ι›, αƒͺΕ³Ε§ Ι―Ι› Δ…Ω³ΕžΖ‘ Ε§Ζ‘Ε³Δ†Ι§ Ι– Ι§Ι›Δ…Ε™Ε§ Ζ‘Κ„ Ε™Ι›Δ…Ι–Ι›Ε™Εž_


# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https:/bio/www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com


Page 61-65
*A gaskiya ina jin dad'i masoya ma da irin k'aunar da kuke nuna min naji dadi ina alfahari da ku nagode masu kira na da masu yimin magana ta WhatsApp ne ko Facebook haka ma Wanda suke turo min da sak'on test messages ina godiya Allah ya bar zumunci nagode*😍😍

just follow me on Instagram @aleeyusalmah

*M* ukky! Mukky!! na kuma maimaita a raina nayi nisa cikin duniyar tunani muryar Hajiya Aunty ta katse ni "in kin idar taso muje wajen Alhaji ku gaisa" "tom" nace tare da tashi zaman mayafi na na kuma gyarawa muka fita tana gaba ina biye da ita

" Allah ya Mukky Aunty Salmah me kyau ce ka gatan kuwa" pictures d'in bikin ta fara k'oka'arin nuna masa "kalli ka gani har tafi kyau a fili"

Daman k'irjin sa ya buga ta maza yayi ya b'oye razanar sa ya k'are mata kallo lallai Wannan kamar Wannan Mara kunyar ko da yake ba lallai ta zama ita ba naga Wannan ba tai kalar rashin kunya ba duk cikin ransa yake fad'a ita kuwa Jasmine bata lura da tunanin da yake ba sai surutu take zuba masa

"Ke ni karbi wayar ki, kin tsaida ni kin  cika ni da magana sauri nake zamu unguwa k'yacewa Hamida na zo ina sauri ne amma zan dawo" "Tom amma nasan baza ka dawo ba kawai ka fad'a ne" nan ya fice yana  tuntun-tuni

Cikin girmama muka gaisa da Alhajin su Ahmad kai amma Wannan gidan anyi mutanen kirki muna zaune Ahmad ya shigo nan yayi mana nasiha gaba d'aya muka fito
D'akin Hajiyan sa muka tafi nan itama tai mana nasiha a haka su Jasmin da Hamida suka shigo "Sis zo muje d'akin mu muyi tamu hiran"

"To aku uwar magana tafiya zamu yi weekend k'wa zo kuyi hirar ki shirya nan da 5munites ki samen a mota" yayi ma Hajiya sallama ya fita

"Yawwa to zo muje d'akin mu kiyi kwalliya" Hamida ta kama hannu na kallon Hajiya nayi "to tashi kuje amma kar ku Dade tunda jiran ki yake yi"

D'akin muka je kallon d'akin nayi amma yayi kyau irin na 'Yammatan  zamani masu ji da aji da gayu komai a tsare gaban dressing mirror suka kai ni zama nayi ina kallon kayan k'walliya kamar gidan make-up

"Sis bari nayi miki kin San   ina zuwa wajen training make-up ita kuma Hamida wajen training din cake take zuwa"
"A'a nagode ban son make-up da yawa" "ai nima kad'an zan miki" "ki bari in kin zo k'ya yimin" nan na kashe maganar powder kawai na sa sai lipstick amma duk da haka nayi kyau ta mudubi muka had'a ido da su dariya mukayi gaba d'aya dan sun kwantan a raina na,number d'ina suka karb'a sannan muka fito, a kofa muka ga Aunty tana k'ok'arin shigowa "yawwa muje" ta fad'a har mota suka rakani ledoji naga Afnan tasa a gidan baya suka rufe motar har muka bar gate d'in suna tsaye suna d'aga mana hannu.

Shi kuwa Mukky be zame ko ina ba sai gidan su Jibson "ah abokina yanaga ka shigo kamar Wanda aka koro"?
" ai dole ka ganni haka me kama da Wannan yarinyar nagani" "wacce fa" Mubaraq ya watso masa tambayr "ni wallahi har ban son ma na tunata wadda mukai fad'a" "OK wadda ta mare ka zaka ce" Jibson ya fad'a wata uwar harara ya watsa masa "nifa ban son iskancin nan ban fad'a dan kai min rashin mutuncin ba" "oh sorry my friend a ina ka ganta"?
" a wayar Jasmin wai ita ce matar Ahmad " "ah haba dai kana da pictures din mu gani" ya fad'a yana matsawa kusa da shi "a'a sai dai na duba IG din Jasmin d'in" "kai abokina ni wallahi ma d'auka ka manta haba sai kace ba namiji ba kawaika share" mubaraq ya furta Wannan maganar "hmm dan dai ba kai aka Mara ba ne ni nunan muga ko ita ce Kasan har yanzu ina gano sanda ta filla ma mari jikake tasss!" jibson ya fad'a da tare da tuntsirewa da dariya ba Mukky ba har Mubaraq sun ji haushi "to wakilin shaid'an daman duk abinda Mukky yake kai ke zuga shi" Mubaraq ya fad'a "to wai shin ma in ita ce me zakai mata ma Abu sama da shekaru da yin sa" Mubaraq ya tambaye shi murmushin takaici yayi tare da cije lebe kamar a lkcn akai masa "daukar fansa zan yi sai ta San ta mari namiji wallahi" "wallahi Mukky kabi a hankali kar ka biyewa Wannan wawan" Mubaraq ya fad'a tare da gyara kwanciyar sa "yawwa ka ganta" nuna masa yayi da sauri jibson ya k'arb'a "wow so cute irin matar da ake so"  nan ya fara zance ya manta akan me suke magana "kaga Mayan mata ba yayi abinda ya dace ya tsaya kallon matar aure" Mubaraq ya fusge wayar kallon ta yayi "ba lallai ta zamo ita ba ai an kwana biyu kawai ka basar" ya mik'a masa wayar "kai baka San zafin abin ba" to ai daman duk tsun-tsun da yaja ruwa shi ruwa ke doka da bakai musu ba da bata mare ka ba,wai da ita ka Mara kila Zane ka zata yi"wata dariya suka kwashe ta ita Mukky kuwa kamar yayi kuka nan ya fita yana cin alwashin sai ya rama ya bawa abokan sa mamaki.cikin hanzari Mubaraq ya tashi ya bishi tsaya ni mana ka tafi kabarni wajen Wannan d'an iskan" da gudu jibson ya bisu "to ai nima k'afar ku k'afata duk inda zaku sai na biku my guys ina ji da ku"

A mota kuwa hira yake mata amma sam hankalin ta baya kan sa yana wayar ta da take chatting da su Jasmin ko waccen su hira take mata tama rasa wadda zata saurara dan hiran tayi dad'i fusge wayar yayi "haba dan Allah ka ban wayana mana" mtsww yayi tsaki wace irin hira kike haka har mun zo ina miki magana baki Sani ba" kalla tayi sun ma shiga gidan dariya tayi "ni da su Jasmin ne sisters d'in ka sun min ina ma a gidan nan suke" "to ai sai ki dawo da su, muje ni na gaji" kwanciya tayi ta lumshe ido darling ni na fika gajiya ko tafiya k'iwar yi nake yi " fitowa yayi ya zagayo inda take "oya fito" yi tayi kamar bata ji shi ba ai kuwa batai aune ba sai ji tayi ya d'auke ta kamar baby dariya ta soma "ka ajiye ni mana" ai baki son tafiyar shine na hutar da ke" cakulkuli ta soma yimasa dariya ya fara abin abin sha'awa ai kuwa be dire ta ko ina ba sai kan gado nan suka zube gaba d'aya suna dariya.................πŸ–‹


Urs Salmah queenπŸ’πŸ’…πŸ½πŸ‘©πŸ»‍πŸŽ“πŸ‘©πŸ»‍πŸŽ“ *Barrister Salmah*πŸ‘©πŸ»‍πŸŽ“πŸ‘©πŸ»‍πŸŽ“*Story and written by*
    _*Salmah Queen*_πŸ’πŸ’…πŸ½
πŸ‡³πŸ‡¬ *God bless Nigeria* πŸ‡³πŸ‡¬
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_Ι―Ι› Ι–Ζ‘Ε‹Ε§ ʝųŞŧ Ι›Ε‹Ε§Ι›Ε™Ε§Δ…Δ±Ε‹ Ε‹Ι– Ι›Ι–Ε³Δ†Δ…Ε§Ι›, αƒͺΕ³Ε§ Ι―Ι› Δ…Ω³ΕžΖ‘ Ε§Ζ‘Ε³Δ†Ι§ Ι– Ι§Ι›Δ…Ε™Ε§ Ζ‘Κ„ Ε™Ι›Δ…Ι–Ι›Ε™Εž_


# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
*follow me on Instagram* @aleeyusalmahPage 66-70*fans kuyi haquri na rashin typing na kwana biyu da ban ba kusan jiki da jin yana bukatar Hutu nagode da kulawar ku ina tare da ku a duk inda kuke*😍😍Previous page:-  A mota kuwa chatting suke ta yi da su Jasmin ta rasa wadda zatai ma reply dan kowaccen su magana take mata har suka iso bata sani ba kallon ta yayi gaba daya hankalin ta yana kan wayar gun tun tsaki yayi ya fusge wayar "haba malama wannan wane irin chat ne haka har mun iso baki sani ba" wllh ni da su Hamida ne sisters d'in ka sun min wllh dama anan gidan suke" "to ae Sai I dawo da su, muje ni na gaji" kwanciya tayi Kamar bata ji shi ba "darling na fika gajiya ni kiwar tafiyar ma nake yi"
Zagayowa yayi saitin kofar "oya fito" yi tai Kamar bata ji shi ba ae kan tayi wani Abu ya d'auke ta kamar wata baby dariya take "ka ajiye ni mana" "ae baki son tafiyar shine na hutar da ke" cakul-kuli ta fara yi masa nan suka fara dariya be ajiye ta ba sai akan gado.....


D'agowa yayi yana kallon ta ita ma kallon sa take yi "dia ni na rasa wane irin so nake miki kullum k'aruwa yake yi pls mene sirrin"?

" kawo kunnen ka kaji" da sauri ya mika kunne ae kuwa tana gani ta kama kamar zatayi magana sai kawai ta cije kunne wata k'ara ya saki ai kuwa da gudu tayi toilet tana dariya

Bin bayan ta yayi "ai bashi kika ci sai na rama nan ya fara zuba mata ruwa tana ramawa abun sha'awa
 Haka Salmah da Ahmad suke gudanar da rayuwar su cikin jin dad'in

Sai da ta cika two months a gidan sannan ya kai ta gidan su ta wuni kamar baza ta dawo ba dan idan ya fita gidan fad'i yake mata

Sai da yamma sannan Abban ta ya dawo shi da ya Muhd

Cikin farin cikin ta gaishe shi " Abban wllh I miss you so much " "to my salmaty yaza'ai haka rayuwar aure take, sanda aka kawo Umman ki har kuka take in zan fita" gaba d'aya suka sa dariya banda umma da tayi kicin-kicin "to kije ki shirya kamin me gidan naki ya zo" "tom Abba"

Tana fita yazaro wata paper daga brief case d'in sa umma ya mik'awa "tame ce Alhaji" "to ki karanta mana "

Tun daga yanayin da umma ta shiga kana gani kasan tana cikin farin ciki "kai Alhamdulillah masha Allah naji dad'i"

"D'azu ina office Alhaji Hassan yace yana son gani na ina zuwa ya mik'o min, Yanzu in zasu tafi sai ma bata kinga system d'in da d'an uwan ta ya saya mata"da sauri umma ta d'auka ta kamfanin apple farin ciki wajen umma bazai k'watan tu ba

Suna zaune Salmah ta shigo "Abba ga Ahmad ya zo zamu tafi" " to ce masa ya shigo" a ladaf ce ya gaida su nan Abba ya bashi takardar "to ga wannan opper d'in Salmah ce ta samu aiki a federal high Court" ai Salmah wani irin tsalle da ihu tasaki "wayyo Allah na Allah nagode ma" rugume Abba tayi tana murna shi kuwa yana ta murmushi irin nasu na manya "to Abba angode Allah ya k'ara girma da lafiya"


 sai da umma tayi mata tsawa sannan ta nutsu suka tafi suna ta murna


"Darling ina taya ki murna Allah yataya rik'o amin sweet heart wllh na rasa wane irin farin ciki zan yi"


"In mun koma gida sai ki sallah ki godewa Allah"


"Cikin nasara Salmah ta fara zuwa aiki a sabuwar motar ta da Ahmad ya siya mata, Salmah ke nan buri ya cika

Suna ganin cases iri-iri abun tana ganin sa kamar ba wuya Ashe abun bana wasa bane

Kullum tana cikin bincike amma in ta dawo gida a jiye komai take ta kula da mijin ta................πŸ–Š


Urs Salmah queenπŸ’πŸ’…πŸ½

adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *