[5/2, 10:39 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
*JEEDDERH LAWALS*
🐾°•01•°🐾
GARIN KANO
Tafe take cikin natsuwa mai tattare da kwantaccen nishadi a kawatacciyar fuskarta. Budurwace mai kimanin shekaru ashirin da uku zuwa da hudu, ba zaka gane yanayin kalar fatar ta ba, ita ba fara ba, ba kuma baka ba, haka ba zaka kirata da chocolate color ba, a takaice dai tana da wata irin kala ce ta daban. Wani babban gida mai wargajejen gate irin mahadi-ka-ture dinnan ruwan gold take dosa, sai data tsaya suka gaisa da wasu maza biyu dake zaune a can gefen gidan a karkashin bishiyar umbrella a zaune suna hira sannan ta shiga gidan, nan ma sai da ta tsaya suka gaisa da maigadi gidan cikin girmamawa kafin ta bi wata siririyar hanya mai shimfide da grass carpet wadda zata sadaka da ainihin main parlour na gidan.
Cikin siririyar murya tayi sallama falon ta shiga a nutse, kamilalliyar dattijuwa dake zaune a cikin falon tana kallon tashar Saudi 1 idanunta saye da farin medicated glass na kara karfin gani, ta dago ta dubi inda mai sallamar take shigowa bakinta ya motsa a hankali wajen amsa sallamar, fuskarta ta dan washe da fara'ah lokacin da tabi budurwar da kallo yayin da take zama a kan carpet din gefen kafar dattijuwar. Hajiya Karima ta kalleta a nutse tace "Rayyanatu, har kin dawo kenan?" ta gyada kai a nutse kuma cikin girmamawa tace "ehh Ummie, Hajiya Tabari tace tana gaishe ki sosai" fuskarta ta kara washewa da fara'a sosai tace ina amsawa kuwa.... Yara sun kusa dawowa, yakamata ki hanzarta ki dora abinci kafin su dawo koh? Ta amsa da toh Ummie. Har ta mike taji Hajiyar na cewa.., "Modibbo yace yau sakwara yake son ci, don haka sai a cire shi cikin namu abincin ki mishi nashi, kin dai san irin yadda yake son sakwarar shi tayi" ta koma ta kara rusunawa tace "Ehhh Ummie, za ayi in shaa Allahu" Ummie tace to madallah.
Dakin da aka ware mata ta fara shiga ta cire kayan jikinta ta sanya wasu sannan ta shiga kitchen din, ta duba time table na abinci ta ga jallof rice ne da farfesun kayan ciki ne abincin daren yau, don haka ta hau shirye-shiryen komi. Ta fereye doya ta dora bisa wuta, sannan ta fito da kayan ciki daga cikin freezer ta wanke su tas ta dora akan wuta bayan ta zuba wadatacciyar albasa da citta, ta kuma dora shinkafa. Doyar na dahuwa ta sauke ta ta dauko turmi ta fara aikin kirbi, kafin kace me! ta hada zufa sharkaf. Ta dan dakata tayi tsaki a fili tace "haka kawai a dinga saka mutum yin wahalar banza, yanzu haka duk wahalar dakan wannan da nasha nasan a banza zata tashi tunda ba wani ci za ayi ba, don dai kawai halin mugunta da son a wahalar da mutum, an san ba za aci abu ba amma sai a saka shi girka abu mai wahala..." Ta kara jan wani tsakin da yafi na dazu tsawo..., "aichhh! I cnt really understand wat's in dix guy's head, he's a total jerk... Very selfish...!" daga kan wannan da za tayi sai idanunta biyu cikin nashi... Tsaye yake a kofar kicin din ya harde hannayenshi biyu a kirji sanye da shadda bugaggiya dinkin Abacha sai dai kanshi babu hula, akwai alamun ya dan jima a wajen babu mamaki duk zagin da ta dinga auna mishi sun shiga kunnuwanshi. Gabanta ya bada sautin dararasss!! kamar fadowar gini, ta zaro wasu dara-daran fararen idanuwa tass kamar madara, ta shiga motsa dan karamin bakinta amma sautin maganar taki fitowa......
🐾💕💕💕🐾
[5/2, 10:39 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•02•°🐾
Wani irin murdadden mutum ne mai wani irin murdadden hali da fahimtar inda ya saka gaba ke matukar ba mutane wahala, hatta da iyayenshi kuwa. Miskili ne na gaban kwatance.
Ya karasa shigowa cikin kicin din a hankali kuma cike da ginshira, ba zaka taba fadin ga yanayin da zuciyar shi da fuskar shi ke ciki ba, sai ma wani guntun murmushi daya saki wanda siraran fatar lebbanshi ne kadai suka nuna yayi. Ya bude fridge ya dauko ruwan faro ya bude ya daddaka, bai kara kallon inda take ba ya doshi hanyar barin kicin din hannunshi rike da sauran ruwan a cikin robar. Ta bishi da kallo tana marmara idanuwa kamar ta saki ihu har ya gama fita daga kicin din kafin ta sauke idanunta cikin saddakarwa ta maida su kan sakwarar ta dan rankwashi kanta "ohhh! Wat did I jst do? Oh my....!" "....idan kin gama a ajiye min a karamin dinning..." kamar daga sama ta tsinkayi muryar tashi, ta zabura ta mike tsaye, sai kuma ta kara komawa ta zauna dabas. Cikin rawar murya tace "uhhh??.. Toh... Toh..." ya dan saki guntun murmushi ya juya. Ta dafe kai tace waiyoo!! Yau na bani ni kam. Cikin sanyi da rawar jiki ta gama aiyukanta na ranar.
Tana cikin yin wanke-wanke taji hayaniyar yara suna shigowa cikin falon, ta danyi murmushi tace yara an dawo kenan! Ba'a jima ba taji an rungumota ta baya, an kuma rufe mata idanu a lokaci guda, tayi dariya tace Hauwa.... Adam.... A tare suka saki dariya kafin Adam daya rufe mata ido ya saki ya zagayo ta gabanta ya rungumeta yana cigaba da dariyar da yake yi. Ta hadesu gaba daya ta rungume a jikinta na tsawon lokaci kafin ta sake su ta shafa kawunan kowannen su tace "oyaa, magriba ta gabato maza aje a cire kaya ayi sallah, yau sai bayan Isha'i zamu yi lesson ok??" Hauwa tace "toh Anti, amma ai ke zaki ja mu sallahr koh?" tayi murmushi tana shafar kanta "a'ah, aiki nake yi sosai yau, kuje wajen Ummie" a tare suka amsa da toh, suka fita daga kicin din da dan gudunsu ita kuma ta mike ta cigaba da wanke-wankenta.
Bayan sallahr isha'i suka yi lesson kamar yadda ta musu alkawari, a dakin ta baro su suna tilawar Al-qur'ani ta fita falo ta tattara kwanukan da aka yi amfani dasu zata wanke. Kamar yadda tayi tsammani, ba a wani ci sakwarar data kirba da yawa ba. Ta ja wani dan guntun tsaki tana tattara kayan, tace Allah ya isa na wahalar da aka bani. Fita tayi da sauran ta mikawa mai gadi ita kuma ta koma ciki ta kimtsa komi, ta duba agogo lokacin karfe tara na dare. Hijabi ta saka ta fita, a harabar gidan taci karo dashi yana ta kai kawo hannunshi daya saye cikin aljihu da alamun waya yake yi, da yake farfajiyar gidan akwai wadataccen haske sakamako bulbs da aka saka, yadda ya mata kallo daya ya kawar da kai itama sau dayan ta kalleshi ta watsar, kanta mike ta bude gate ta fita.
Makotansu ta shiga wanda tazarar gidaje uku ne a tsakaninsu. Shima babban gida ne mai kyau, masu manya-manyan motoci ne jibge a harabar ajiye motoci, wasu an rufe su ma da tamfol saboda ba kasafai ake hawansu ba. Ta danna kararrawar dake manne da kofar falon aka mata izinin shiga, ta tura kofar a hankali ta shiga falon. Yana ganinta yayi fara'a sosai, itama dan guntun murmushi ta saki ta nemi waje ta zauna suka gaisa a dan tsaitsaye, ta lalubo first aid box a karkashin karamin teburin da yake a tsakiyar falon ta isa gefenshi ta zauna. Hannunshi ya mika mata, ta fara warware bandeji dake a babban dan yatsanshi ta wanke raunin har ya fara kafewa ta manna mishi plaster, nan yayi mata godiya sosai, ta hada kan kayan ta mayar inda suke, daga nan suka yi sallama ya rakata har bakin kofa bakinshi dauke da godiya, murmushi kawai take yi har ta bar falon. A tsakiyar dakinta ta same su sun bararraje suna ta shakar barci, ta ciccibe su daya bayan daya ta kaisu dakinsu ta kwantar dasu bayan ta shafe su da addu'o'in tsari sannan ta koma nata dakin, bandaki ta fara shiga ta rage mararta ta dauro alwala ta dawo ta canza kayan jikinta zuwa doguwar riga mai rangwamen nauyi ta barci, ta rufo dakinta tare da kashe wutar dakin ta nufi dan karamin gadon dake gefen dake shimfide da tattausan zanin gado ta kwanta, idanuwanta ta lumshe tana bude su a hankali, wani dan tattausan guntun murmushi ya subucewa fatar bakinta, addu'ar kwanciya barci tayi ta janyo filo ta kankameshi kam a kirjinta kamar mai tsoron a kwace mata shi, a haka barci yayi awon gaba da ita.
••••••••••••
Da sassafe ta fito ta fara gyaran falo kamar yadda ta saba dama tuni ta kammala shirya karin safe, ta shiryawa su Adam lunch box nasu, ta shiga dakin yaran ta tashe su ta musu wanka suka yi sallah sannan ta shirya su cikin kayan makarantarsu suka fito falon, iyayen na kan dinning suna karyawa, Rayyah ta duka ta gaishe su cikin girmamawa, suka amsa mata. Kicin ta koma don ta ida sauran ayyuka kafin su gama karin. Suna gamawa ta raka su Adam har gaban motar da direba ke jiransu zai kaisu makaranta, ta bude bayan motar ta ajiye musu jakunkunansu da hade da lunch box, ta shafa kawunansu tace bye! Suka hada baki suka ce take care! Tayi murmushi yayin da direba yaja motar suka tafi ita kuma ta koma ciki. A dan corridor mai shimfide da grass carpet suka ci karo da ita, ta ci ado kamar wadda zata je modeling sai tashin kamshi take kamar a kamfanin turaruka sai wani yatsina take yi, ta mika mata keys din dakinta ta amsa, bata furta uffan ba ta wuce sai itace ta bita da Allah ya kiyaye hanya. Safeenah Biebie kenan!!
Jeedderh🐾
5/2, 10:39 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•03•°🐾
Wata irin dariya ce ta kubce mata lokacin data shiga dakin Biebie, ta tsaya tana karewa dakin kallo kamar ba dakin mutum ba, ko ina kaya ne a zube da littafai dasu takardu duk a watse babu ko wajen saka kafa, kai kawai ta gyada ta fita daga dakin ta koma nata, drawer ta bude ta ciro wata sullubebiyar wayar Samsung edge silver tayi latse latse na en mintuna, kafin ta mayar da ita inda take ta rufe drawer din ta fita falo. Kai tsaye dinning ta nufa da niyar tattara kayan da akayi kari dasu, bata taba tsammani da mutum a wajen ba sai data mika hannu da niyar fara hada plates sai kawai ta ga mutum a zaune yana karyawa, ta ja baya cikin razana da ganinshi da kuma mamaki, ta shiga bashi hakuri kamar zata fashe da kuka, hannu kawai ya daga mata alamun ta tafi, cikin sauri ta juya ta fada dakin yara cikin hardewar kafa. Ta rasa dalilin da yasa duk lokacin da er magana ta shiga tsakaninta da Modibbo take tsintar kanta cikin rawar jiki. Daga bangarenshi shima kallo ya bita dashi, yana ji a jikinsa yasan wannan halittar, not the face, but the personality. His mind kept telling him that yasan ta amma a ina? Duk lokacin da zai ganta sai gabanshi ya fadi, faduwar gaban da take tuno mishi da wata wadda a dalilinta ne har yau ya kasa ganin ko wace diya mace da gashi, to him kowace mace yana kallonta ne kamar namiji dan uwansa. Wannan dayar dai daya rasa tana ina yanzu cikin duniyar nan? Ko wane hali take ciki yanzu?? Take idanuwanshi suka canza kala, zuciyarshi tayi bakikkirin, abincin da bai kammala ci ba kenan ya warci briefcase dinshi ya fita. Kamar wanda zai tashi sama haka ya warci motar cikin matsiyacin gudu ya bar gidan. Sai data ji fitar shi ta iya fitowa daga dakin ta gyara falon, sai a lokacin ta samu ta karya. Wanka ta shiga, kafin ta fito tayi shirye-shiryen da zata yi karfe sha daya da rabi ta wuce, don haka ta dora girkin rana kawai.
°°°°°°°°°°°°
Ranar Laraba da yamma a harabar gidan, Rayyah ce da makocinsu Samuel zaune akan fararen kujerun roba suna hira. Gidan babu kowa, kowa ya tafi wajen aikinshi wasu kuma sun tafi wajen karatu. Maigidan Alhaji Abbas dan garin Yola ne amma aiki ya kawo shi Kano har yayi aure anan, don haka Kano ta zamo mishi gida yanzu, babban controller ne kuma dan kasuwar Electronics daga Japan zuwa Nigeria don haka bai cika zama a gidan ba saboda tafiye-tafiyen shi, matar gidan kuma Hajiya Karimah er asali garin Takai ce ta jihar Kano tana aikine da ma'aikatar lafiya ta jihar Kano. Yayin da babban dansu Abdul-Ra'ouf da suke yiwa lakabi da Modibbo saboda sunan Baban Alhj Abbas ne yaci, babban likitan fata ne a asibitin Aminu Kano, sai Safeenah da take bi mishi suna mata lakabi da Biebie tana kazantar Elect. & comm. Engineer a ECE, sannan en biyu Hauwa da Adam dake primary 5 a makarantar Nurul-Huda Islamic school ce, kullum sai yamma suke dawowa. Don haka idan gari ya waye kowa ya kama harkar gabanshi, Rayyah kadai ake bari a gidan wadda ta kasance mai aikinsu watanni biyu da suka wuce, amma sabon da suka yi da mutanen gidan musamman yaran kai kace ta shekara dasu sai dai fa banda mai karkataccen hali Modibbo, don shi ba a ma zancen shi.
Sau tari idan ta gama ayyukan gidan, kadaici ya kan dame ta, gashi ita ba gwanar kallace-kallace bace. Sai ta fara fita tana dan zagaya anguwar, a haka ne suka hadu da Samuel, tun dai suna gaisawa a tsaitsaye har ya fara lekawa gidan suna er hira, watarana ma tare da abokanshi Michael da Simon yake zuwa, su basu cika zama a cikin Kanon ba. Hakane ya sabbaba musu wata shakuwa da xumunci na musamman a tsakaninsu.
Kwanaki uku da suka wuce yazo suna hira kamar yadda suka saba, ta kawo mishi fruits na dan motsa baki. Tana kokarin yanka tuffa shi kuma ya kawo hannu da niyar daukar kankana, ba tare data kula ba ta danna mishi kaikaifar wukar hannunta a babban yatsanshi, nan kuwa jini ya bata wajen. Ta garzaya cikin gida ta dauko first aid box tazo ta mishi dressing wajen. Daga ranar ne kuma take zuwa har gidanshi tana mishi dressing din raunin wanda dama bata taba taka kafarta a gidan ba sai bayan aukuwar lamarin.
Yanzun ma da yazo sai data sake duba mishi raunin, ta dube shi tana dan murmushi, tace "kila zuwa gobe ka ga raunin ya kafe ma gabadaya, da alamun kana da power mai sa rauninka yana saurin warkewa" dariya yayi sosai yace ni din?? Tace Ehh mana. Kallonsu ya koma kan karamar mota corolla kalar sararin samaniya data silalo farfajiyar gidan a hankali tayi parking a inda aka tanada domin ajiye motoci. A hankali murfin gaba ya bude, ta ziro kafafunta ta fito. Sanye take cikin riga da wando na Pakistan rigar yellow wandon kuma purple sai ta yane kanta da siririn shara-sharan gyale multi color na purple da yellow, duk da cewa tana da er kiba ba laifi hakan bai hanata hawa kan heels ba, ta rataya jakar Vincci yellow a kafadarta. Cike da isa da takama take takunta dai-daya kai a dage, kai daga ganinta kaga woman of high class da take jin yes! ita macece da zata amsa sunan cikakkiyar mace a ko'ina ne cikin duniyar nan. Yadda kasan bata san da mutane a wajen ba haka ta wuce ta gabansu ko kallo basu ishe ta ba, hakan ya faru ba sau daya ba sau biyu ba, don haka yau ma kamar kullum ido kawai suka bita dashi har ta shige cikin gida...
Jeedderh🐾
[5/2, 10:39 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•04•°🐾
Samuel ya saki ajiyar zuciya ya maido dubanshi ga kallon Rayyah da har lokacin idanunta na kan kofar da budurwar ta shiga tana murmushi, yace "wai wacece waccan dinnan?" tana murmushi tace "Safeenah kenan! Itace diya ta biyu a gidan nan, tana ji da kanta kamar diyar shugaban kasa, tana amfani da kyawun da Allah yai mata da kuma dukiyar da Allah ya horewa iyayenta tana taka wanda taso. Sai dai tana da kirki da kyautatawa amma fa ga wanda taso tayiwa kirkin" ya dan tabe baki "I see! Kenan mu bata so ta kyautata mana din bane shi yasa take wulakanta mutane? Gaba dayan unguwar nan ban taba jin wani ya yabi halinta ita da dan iskan yayan nan nata na, wat a bi***es!!" ya karasa cikin kwafa. Tayi dariya tace rashin fahimta ne da wuyar sabo ke gare su. Ko ni nan farkon zuwana gidan nan wane irin rashin mutunci ne Biebie bata shuka mun ba? Tun wani assignment da na taba yin karambanin gyara mata na sha la'adar mari daga baya kuma ta zo taga ashe daidai ne, tun daga nan muka shirya, gashi nan yanzu mun zamo kamar wasu en uwa. Ni kaina sai daga baya ne nazo na fahimci kirkinta.
Ta mike da dan saurinta tace "Sam bari na shiga daga ciki sai anjima" shima ya mike yana dan murmushi tace ba damuwa, c u then. Tayi murmushi ta juya yayin daya bita da kallo cikin wani irin murmushi mai wuyar fassara har ta shige sannan ya juya ya fita. Tana shiga dakin Biebie ta taro ta da mitar, "Na rasa me wannan arnen Samuel din yake yi anan wajen ki, kusan kullum sai na ganshi anan" Rayyah ta dan rausayar da kanta, "kawai haduwar jini ne ba wani abu ba, amma kin san Samuel ai ba ma tsaran hira ta bane ko kadan" ta kalleta tana zama akan gadonta tayi jifa da jakarta tana cewa ni wallahi gayen tsoro yake bani, fuska bakikkirin da ita kamar na gwaggon biri, idanuwa jawur, haba! Rayyah ta kwashe da dariya tace amma Biebie kin zagi bawan Allahn nan sosai pa. Itama dariyar tayi tace to ba gaskiya ne na fada ba??!.
**** ****
Wani yammaci Safeenah ta dawo daga makaranta, lokacin Rayyah na kishingide akan kujera a cikin falon, tuni ta kammala komi na gyaran gida har ma da girkin dare abinta, ko'ina kamshi ne mai sanyi yake tashi a gidan. Sautin wakar Eternal Love na Michael L.R ne ke tashi a tausashe a cikin falon. Tayi tsaye a kanta tana kallon yadda take bin wakar a nutse kamar ita ta rera ta, idanunta a lumshe, fuskarta cike da walwala kai daga gani babu tambaya kasan tana cikin farinciki idan kayi la'akari da yadda take gyada kai fuskarta na fitar da wani irin annuri. Itama sai kawai ta tsinci kanta da murmusawar, ta nemi gefenta ta zauna tana kallonta, can kuma ta nisa tace "da alamun babu abinda ke damunki pa yarinyar nan, waka ma kike ji hankalinki kwance koh?" ta bude idanunta a hankali tana kallonta da sauran murmushin da har yanzu bai bace a fuskar ta ba, tace "wane irin jin dadi? Kadaici ne kawai ya dameni nake dan shakatawa kawai" ta dan saci kallonta tana rage sautin TV tace "Tohh.... Shi fa Samuel din naki ina ya shiga ne? Kwana biyu bana ma ganinshi ma anan" fuskarta ta nuna jimami tace "eyyah! Ai Samuel yaje kauyensu. Mahaifiyar sa ce wai bata da lafiya" ta girgiza kai, Allah sarki, Allah ya bata lafiya. Bata amsa ba ta maida dubanta ga takardu da ta shigo dasu, tace "kar dai har kin gama aikin project din?" ta danyi tsaki, "ina fa ba gama. Ai ke kam kinji dadi ma da karatun ki iyaka secondary ya tsaya kawai, amma wahalar dake cikin karatun gaba da sakandire tana da yawa sosai. Kafin ka fara sai ka sha wahala, idan zaka kare din ma dai wata wahalar ce!" Rayyah tayi murmushi tace to amma duka me ya rage miki ne? Duka pa bai fi wata daya da en kwanaki ba wahalar taki ta zama romo, Biebie tace da haka kuma. Suka mayar da hankulansu tashar BB for u (Body Building), suna gudanar da shirinsu akan yadda ake hada sinadaran da suke rage kiba da teba, hankalin Biebie ya karkata wajen kasancewarta er lukuta duk da cewa bata da teba, kuma yanayin yadda take maintaining jikinta ma yasa kibar tayi mata kyau, kuma tabi jikinta ta zauna das amma cewa take bata son kiba, ita tafi son irin yanayin jikin Rayyah er siririya da ita. Daga karshe ma jotter da biro da dauka tana rubuta muhimman tips, Rayyah ta shiga tsokanarta suna dariya.
Washegari da safe duk suna falo wajen karfe goma sha daya na safiyar ranar da yake weekend ne babu aiki, Rayyah na kan kujera tana yiwa kan Hauwa ado da beats da ribbons masu kyau irin na yara. Hankalinsu duk yana kan television suna sauraron labarai, wai jiya barayi sun shiga gidan kwamishinan ilimi na jihar Kano sun saci makudan kudi da gwala-gwalan matanshi da motoci sun kuma yiwa babbar diyar shi fyade, jikin kowa na falon yayi sanyi sosai. Ummie ta girgiza kai cikin jimami tace "satar da ake yi a Kano ta fara yawa a kwanakinnan, Allah dai ya tona asirin masu yi" gabadayansu suka amsa da ameeen.
Rayyah ta bi mai karanta labaran da kallo., wani irin hargitsattsen murmushi ya bayyana a fatar bakinta.....
Jeedderh🐾
[5/2, 10:40 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•05•°🐾
Da dare tana kicin tana fereye kabewa wadda zata yi taushen funkason safe da ita taji an shigo kicin din, sau daya ya kalleta ya watsar, itama da taga shine sai ta juyar da kanta wajen cigaba da gudanar da abinda take yi. Fridge ya bude ya dauko limes manya guda uku ya koma gefe yana kokarin barewa amma ya kasa, bata san dalili ba. Kabewar hannunta ta ajiye ta matsa kusa dashi ta mika mishi hannu alamun ya kawo ta taimaka mishi, "can i??" wani lalataccen kallo daya watsa mata ba shiri ta matsa tana yiwa kanta Allah ya kara, shegen karambani irin nata ya ja mata. Bata kara ko tari ba har ya bare limes din yasa su a juicer ta markade su ya tace ya juye ruwan a dogon cup, ice cube ya zuba a ciki ya bar kicin din yana kallonta kasa-kasa, itama a kaikaice take jifanshi da harara har ya fita a kicin din. Tana gamawa da taushen ta bude fridge ta dauko tukudi da Biebie ta saka ta dama mata, yayi sanyi sosai kamar yadda take so kuwa. Ta nufi dakin nata rike da kofin a hannu. A bakin gado ta same ta a zaune ta dafe kai, ta ajiye kofin a gefenta tana tambayarta lafiya? Yanayin data ganta data dago kanta sai data firgita, fuskarta tayi jaa sosai da yake Biebie fara ce tass don ta biyo farar fatar mahaifinsu ne sabanin Modibbo daya dauko bakar fatar mahaifiyarsu. Ta zauna a gefenta cikin tashin hankali tare da dafa kafadarta, "Biebie lafiya? Me ya same ki?" ta dauko wata shesshekar kuka mai tsawo ta dire, "kin san Allah gobe sai na targada en biyu, sai dai Ummie nima ta karya ni!" Rayyah tace "calm down, cool.... Me suka miki??" ta janyo wani frame a kasa ta mikawa Rayyahr. Zane ne aka yi na wani lambu mai kyawu sosai, sai dai zanen ya riga ya baci saboda ruwa da aka watsa mishi alhalin bai gama bushewa ba. Ta kalle ta, "wanna pa?" tace "gifts din da zamu ba Dean din mune pa ranar convocation dinmu, wallahi baki san wahala da kudin da muka kashe ba kafin ayi zanen..., amma a dare daya en iskan yaran nan suka shigo har dakina suka watsa mishi ruwa ya lalace, ni kuma Allah...!" Rayyah tayi saurin dafe mata baki, "kinga idan wannan ce matsalar to baki da damuwa. Dauko min sauran kalolin zanen" Safeenah ta saki baki sauran kaloli?? Kin iya zane ne? Tayi murmushi "ke dai ki dauko mana" ta mike ta bude drawer ta ciro wani madaidaicin box da kayan zanen suke ciki. Rayyah ta bude ta dauki kala guda daya ta duba, ta dan girgiza kai "hava no wonder! Da ace da kalolin vimpyte da kuma takardar sacvytes aka yi amfani wajen zanen to ko da an watsa ruwa babu abinda zasu yi, sai dai suna da tsada ne Ina jin shiyasa ba a siye su ba.." Rayyah take yi mata bayanin yayin da take dora painting frame din akan karamin teburi dake gefen gado. Ta bude kalolin, ta dauki brush din zane ta sa cikin wani abu mai kama da farin ruwa, tana gogawa zanen ya fara gogewa kamar ba a taba zane akan farar takardar ba. Sai data goge duk wajen da yayi dameji tsab, ta fara maida zanen yadda yake. Safeenah kam baki da hanci ta ware tana kallon yadda Rayyah take zanen kamar wata expert, har ta gama Biebie bata samu bakin magana ba. Idan ba sani kayi ba ba zaka taba sanin shine bataccen zanen dazu ba. Ta mika hannu ta dauki frame din ta kara dubawa sosai kamar wadda take tantamar wani abu. "Rayyah... How...?" ta fada tana kare mata kallo cike da zargi, tayi er dariya tana maida sauran kalolin cikin akwatin, "kar ki damu. I was once an art student, kuma painter, so kinga ba abun mamaki bane ba koh?" ta tattara kayan ta mayar dasu inda ta ga Safeenah ta dauko su, ta dawo inda take har lokacin zanen na hannunta tana jujjuya shi cikin mamaki. Tace "ga tukudin ki nan nasan ma yanzu babu sanyin ma, sai da safe" ta juya zata fita, har ta kai bakin kofa Safeenah ta tsayar da ita ta hanyar kiran sunanta, ta juya ta kalleta. Murmushi ta sakar mata tace Thank u Rayyah!! Ta dan sakar mata murmushin itama ta karasa fita daga dakin tare da ja mata kofa.
~~~••••~~~
Tun da safe ya shigo sashen nasu da yake sashen shi daban yake a cikin gidan. Ita kadai ya samu a falon tsaye a gaban dinning tana kokarin hada abin kari. Bai san lokacin da yaja wani siririn tsaki ba, bai san dalili ba, shi dai kawai yasan ya tsani ganin yarinyar. Duk lokacin da zai ganta sai wani lamari daya jima da binnewa a zuciyarsa ya tonu, shi kuma ya tsani tonuwar abinnan fiye da yanda ya tsani mutuwarsa. Sai kawai ya juya ya fita ba tare daya karasa ciki ba, dama yazo ne ya gaida su Abbu saboda da wuri zai fita wajen aiki yau.
Jeedderh🐾
[5/2, 10:40 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•06•°🐾
Gabadaya daya gidan yau sun tashi da shirye-shiryen taryar kanin Ummie dake zaune a Mumbai shi da matarshi ne. Don haka tun safe suna kicin har da Ummie din data dauki hutu wajen aikinta musamman saboda kanin nata, a soya wannan, a dafa wancan, a girka wancan, gida dai ya hade da hargitsattsen kamshin girki har ka rasa wanda zaka shaka.
Biebie ta shigo kicin din a sukwane tana kwalawa Rayyah kira da gyalenta a hannu. Duk suka juya a firgice suna kallonta. Ummie tayi tsaki tace "ke kam ban san irin ki ba Safeenah, wannan uban kira haka kamar wadda taci miki bashi?" ta ja birki a gaban Rayyah tana er shessheka, tace Rayyah kin ga abun mamaki? Rayyahr tace na me? Tace wae ashe en fashin da suka shiga gidan kwamishina suka yi sata ranar nan ashe su... su.... Samuel ne da abokanshi!!"
Rayyah bata san sanda ludayin hannunta ya fadi kasa ba, Ummie ta fara sallallami cikin tu'ajjibi. Rayyah ta dafa kirji ta zaro idanu cikin kaduwa "me??? Da gaske kike Safeenah?" tace "wallahi kuwa, yanzu haka en sanda na can gidan su suna bincike. An fito da makudan kudade masu yawa da makamai. Wai jiya suka shiga gidan wani hamshakin mai kudi shi da abokanshi, anan en sanda suka yi awon gaba dasu bayan sun yi artabu dasu har suka harbi en sanda biyu!" jikin Rayyah ya shiga rawa sosai, ta hau salati da sallallami da tasbihi har sai data ji natsuwa ta saukar mata. Jiki a sanyaye ta duka ta dauki ludayin ta daya fadi ta cigaba da aikinta amma gabadaya ba a cikin natsuwarta take komi ba. Ummie da Biebie ne suka dinga tattaunawa akan lamarin amma ta kasa tsoma musu baki.
*****
Karfe bakwai na daren ranar baki suka sauka. Hajiya ta dinga ina-taka-saka-ina-taka-aje dasu. Da kyar ta samu ta yakice Hauwa da Adam daga jikinsu ta raka su sashen da aka gyara musu tace su yi wanka su dan huta sai su zo su ci abinci.
Bayan sun gama kintsawa sunyi sallar Isha'i, suka tafi bangaren su Ummie din, aka baza musu babbar ledar cin abinci a tsakiyar falon. Gabadaya mutanen gidan suka zauna suna cin abinci banda Modibbo da shi baya ma garin. Abincin su suke ci a nutse ba tare da wata hayaniya ba, baka jin komi a tsakiyar falon sai karan cokula, sai kuwa er hirar da Ummie take jan kanin nata da ita jefi-jefi.
Rayyah ta bullo daga dakinta da er sassafarta zata gaida baki. Lokacin da suka iso tana sallah, bayan ta gama kuma sun tafi su kimtsa, don haka ta tsaya har sai data sallaci isha'i kafin ta fito don yi musu sannu da zuwa. Taku daya biyu da tayi ta ja tayi turus ana ukun cikin faduwar gaba sakamakon ganin mace da namijin da tayi a gabanta un expected, ba kuma tare da ta shiryawa hakan ba, mamaki da al'ajabin dake ranta sun gaza boyuwa a fuskarta. Su dinma kallon mamaki da tsoro suke jifanta dashi, amma a cikinsu ba wanda ya iya ko motsi. Da kyar ta iya daga kafarta cikin sassarfa ta juya zuwa dakin da aka bata matsayin nata, Jameelah matar Mukhtar kanin Ummie ta mike da saurinta ta bita a baya tana kwala mata kira. Ga mamakin daukacin jama'ar gidan, maimakon RAYYAH, sai suka ji tana kiran AMEENAH!!! Abin ya matukar daurewa jama'ar wajen kai ba kadan ba. Mukhtar shima ya fara kokarin mikewa zai bi bayan matarshi. Ummie tayi saurin riko hannunshi ya koma ya zauna idanunshi na kan kofar dakin da suka shiga, cikin daurewar kai da lamarinsu tace me ke faruwa ne anan Mukhtar? Ni fa kaina ya kulle. Kun santa ne? Kai yake gyada mata kamar karamin yaro kafin ya sauke wata irin ajiyar zuciya yace "kwarai kuwa, na santa farin sani ma kuwa, Itace dalilin zuwanmu Najeriya ma karewa. Ameenah ce, diyar Alhaji Sani Wakili, yarinyar da nake riko!"
Suka kwalalo mai idanuwa su duka cike da mamaki, Ummie tayi karfin halin cewa mai zai kawo ta nan? Kuma ma aikatau?? Ya girgiza kai "wallahi ban sani ba, na san dai wani dan hargitsi da suka yi da iyalan gidansu watanni biyu baya, daga nan ne aka neme ta aka rasa. Ashe tana nan" ya karisa fada yana danna wayar hannunshi, ya mike tsaye ya tunkari dakin da suka shiga dazu yana kara wayar hannunshi a kunne, "hello Faruq, gamu nan ga Ameenah yanxun nan muka ganta.... Idan da hali gobe kayo sammako kazo Kano....!" abinda yace kenan ya katse wayar ba tare daya jira amsar wanda ya kira ba.
Su Ummie suka juya suka bishi da ido suna jijjiga kawuna kamar wasu kadangaru har ya shige dakin. Fiye da awa guda kenan suna sandare a gun babu mai kwakkwaran motsi a cikinsu. Sai da Alhaji ya mike ya wuce dakinsa sannan fa suma suka samu kuzarin mikewa kowa ya nufi dakinshi zuciyoyinsu fal da tambayoyin da suka san babu mai amsa musu sai su Mukhtar kadai.
*Toh pha!!!*
Jeedderh🐾
[5/2, 10:40 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•07•°🐾
*☆☆☆☆☆☆☆☆☆*
Karfe shida na safiyar washegari aka doka musu kofar falo, Safeenah data fito daukar ruwa a fridge ta tafi ta bude kofar cikin tunanin waye da safiyar nan? Wani kyakkyawan saurayi ya bayyana a bakin kofar, cikin murmushinsa mai kyau yace mata hiii! Taji wani yarrr har tsakiyar kanta, abinda bata taba ji ga kowane da namiji ba. Cikin rawar murya ta amsa fuskarta na nuna alamun rashin sanayya. Ya fahimci hakan, sai ya kara gyara tsayuwar da yayi yace "m Faruq. Jiya da dare Mukhtar ya kira ni yace yaga kanwata data bata anan gidan" sai lokacin ta dan saki fuskarta "ohh! Sorry. Shigo plsss" ta kauce daga bakin kofar. Daidai lokacin Mukhtar ya fito daga dakin Ameenah, gabadayansu a dakin suka kwana basu samu sun runtsa ko na sakan daya ba suna ta hirar yaushe gamo. Ya karaso da saurinshi ya rungume Faruq suka gaisa, a matukar kagauce yake daya saka er kanwar tashi a idon shi. Tare da Mukhtar suka koma dakin, lokacin har sun kwanta ita da Jameelah. A gefe guda kuma kayanta ne a hattame cikin trolleys suka hada yau da asuba don sun ce ayau zasu tafi da ita Gombe.
Jin maganar Faruq a dakin suna gaisawa da Anti yasa ta tashi a sukwane ta fada jikinshi tana dariya, ya dan janye ta daga jikinshi shima yana dariyar, yace "bar taba ni maras kunya kawai, shine kika wani tafi without even letting me knows koh? How dare u??" ya gama fada yana dan rankwashin kanta a hankali. Ta kara afkawa jikinshi ta rike shi tsam tace am sorry Yaya, ba zan kara ba. Ya zagaye hannayenshi a bayanta yana dan murmushi, a hankali yaji ta sakar mishi nauyin jikinta, yana dagota yaga ashe barci take yi. Dariya ya dan yi tare da ciccibarta a hankali ya dora ta kan gado ya gyara mata kwanciyar ta. Cikin mamaki yake kallon fuskarta, ya juya ga Mukhtar daya rabbe hannu a kirji ya jingina da kofa yana kallonsu cikin murmushi, yace mishi cikin nuna damuwa "wat happened to ha face?!" Anti Jameelah tayi dariya "nima kaina nayi mamaki dana ganta a haka, wai fa badda kama ce tayi!" su duka suka kwashe da dariya, Faruq yace amma me yasa? Uncle Mukhtar yace shine abinda bamu sani ba muma. Ya maida dubanshi gareta yana dariyar yadda ta maida kanta bakar karfi da yaji, sai lokacin ya juya suka gaisa da Anti Jamila, itama gadon ta hau ta kwanta, babu jimawa barci yayi awon gaba da ita, yayin da Mukhtar ya ja Faruq sashen shi don suma su samu su runtsa tunda Faruq yace mishi a hanya ya kwana yasan shima bai yi barci ba jiya kenan.
Sai bayan azuhur suka tashi, masallaci suka tafi sai da suka dawo ne suka shiga cikin gidan. Duk suna falon su duka suna hirar duniya banda Rayyah-Ameenah, Safeenah na gefen Anti Jameelah dake cin abin tana ta jefa mata tambayoyi game da Ameenah amma Antin taki amsa mata ko daya, cikin haka su Faruq suka danno kai falon. Jin sansanyar muryar Faruq a gefenta yana gaishe da Ummie ya saukar mata da wata irin kasala da sanyin jiki, ta matsa jikin Anty ta rabe kamar wata munafuka tana tambayar kanta me ke faruwa ne da ita haka?
Uncle Mukhtar ya dubi Anti Jameelah yace "Ameenah fa?" tace "wanka ta shiga, muma yanzun nan muka tashi daga barci" ya gyada kai, Ummie ta shirya musu abinci a gabansu, ba bata lokaci suka fara cin abincin. Safeenah ta samu kanta da satar kallon Faruq duk bayan wucewar sakanni, gani take a iya tsayin rayuwarta bata taba ganin kyakkyawan namiji wanda ya dauki hankalinta cikin lokaci kankani kamar Faruq ba. To ai ya cancanta yaja hankalin kowace macen ne, don kuwa Faruq kyakkyawa ne na gaban kwatance mai suffa da kira ta mazajen kwarai! Amma abin haushin a gareta shine yadda ko da wasa bata ga alamun ta dauki hankalin Faruq din ba.
Kofa aka yi knocking, Ummie ta umarci Safeenah data je ta bude. Ta tashi cikin sanyin jiki ta tunkari kofar, sai lokacin idanun Faruq ya sauka akanta, ya bita da kallo cikin birgewar da shigar jikinta ta mishi. Sai gata sun shigo tare da Hajiya Tabari aminiyar Ummie. Da sauri Ummin ta taro ta suka zauna aka gaisa, yayin da Biebie ta kawo mata abin jika makoshi. Ummie ta dubi kyakkyawan babyn dake hannunta tace Hajiya ina kika samo kyakkyawan yaro haka? Haj. Tabari tayi murmushi tana kallon yadda yaron ya lafe a jikinta kamar wanda yake tsoron a kwace shi tace "Al-Ameen??". Mukhtar, Faruq da Jameelah suka kalli babyn suna mishi dan murmushin nuna sanayya.
Suna nan zaune ana er hira kadan-kadan, Ameenah ta bayyana a bakin kofar......
©Jeedderh🐾
[5/2, 10:40 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•08•°🐾
Ba wadanda basu santa ba, wadanda suka santa din ma idanu suka zuba mata suna kallonta kamar wata wadda ta diro daga wata duniya ta daban da wadda suke ciki, a can kasan zuciyoyinsu kuwa tasbihi suke ga Ubangiji mai Girmah, makerin wannan halitta...
A mike take gabadayanta, doguwa ce amma tsayin nata madaidaici ne. Bayan dara-daran idanunta masu tattausan kallo, wani siririn hanci ne daya zauna das a doguwa kuma zagayayyar fuskar ta. Dan madaidaicin faffadan baki dauke da siraran lebba jajaye wadanda suka kawata fuskar tata sosai, haka siririyar kakkaurar girar idonta da gashin idanu masu sheki. Duk da cewa dankwali ne a kanta, amma yanayin yadda wasu tausasan gassu suka yi luf a goshinta suna barazanar tabo girarta kadai ya isa ya tabbatar maka da cewa tana da wadataccen gashin kai. Kalar fatar jikinta kuwa fara ce amma ba kar ba, ja ce, jawur.
A nutse kuma a hankali ta tako kanta a kasa har kujerar kusa da Yaya Faruq ta zauna, yayin da suka cigaba da kallonta kowa da abinda yake kissimawa a cikin ranshi. Baby Al-Ameen yana kyalla ido ya ganta, ya sauka daga jikin Haj. Tabari ya nufe ta da tafiyar shi ta en koyo mai hade da dan gudu yana cewa Mam-mmahh!!! har yana faduwa, ta mike da saurinta ta dauke shi ta cilla shi sama ta cafe tana dariya, ta fara mannawa kumatu da bakinshi kisses yana ta kyalkyala mata dariya. Ta koma kan kujerar data tashi ta zauna rungume dashi a jikinta, ya nanike ta sosai kamar wanda yake so ya koma cikinta. Su Ummie sai suka kama haba cike da al'ajabi da daurewar kai game da al'amuran Rayyah data rikide ta dawo Ameenah jiya, Who really is she? They were curious, (n so I was!).
Mukhtar ne yayi gyaran murya, wanda hakan yasa suka maida hankulansu kanshi, yace yana mai duban Abbu, "nasan cewa zuwa yanzu zuciyoyinku cike suke taf da sake-sake da tambayoyi akan Ameenah, qila ma har damu. Kamar dai yadda na fada muku ne tun jiya, wannan Itace Ameenah da muke riko. Watannin baya ne ta dawo nan Nigeria, kuma sai suka samu wata er matsala a can gida, daga nan aka neme ta sama da kasa aka rasa. Wannan satin nace yakamata dai mu zo mu bincika da kanmu tunda har yanzu babu wani labarinta, nace mu fara biyowa ta nan mu muku ko da kwana biyu ne tunda mun jima sosai bamu zo nan ba in yaso daga can Gombe sai mu koma. To kuma cikin hikima ta Ubangiji sai gashi muna zuwa muka ci karo da ita anan, duk da cewa bamu san dalilinta na yin hakan ba, nasan dai she must have a big reason". Yayi shiru yana sauke kallonshi a kanta.
Falon ma ya dauki shiru, kowa ma ita yake kallo. Kowa so yake yaji wai meye dalilinta na badda kamar da tayi, kuma a matsayin yar aiki! Yayin data sadda kanta kasa kamar mai tsoron yin magana, can kuma ta dago tana duban su Abbu tace,
"Da farko dai ina mai baku hakuri akan irin zuwan da nai muku na kuma boye muku asali na, ba wai nayi hakan da wata manufa bane ko munafunci, illa nayi ne a dalilin aiki. Det. Ameenah Sani Wakili, Ina aiki da kungiyar yan sanda ta fararen kaya na kasa wato SSS!" tayi shiru ta sadda kanta kasa, gabadayansu kallonta suke yi cikin tsananin mamaki, har su Uncle da Ta Faruq kuwa don dai sam basu san da wannan zancen ba. Ta cigaba, "ba tare da sanin kowa na gidanmu ba ba nemi aikin, ranar da aka sanar dani na samu aikin na dawo gida ne da niyar nayi surprising nasu, unfortunately sai na tarar ana wata hatsaniya ta dalilinmu ni da Al-Ameen wanda wannan ya danganci personal life dina ne. A wancan lokacin nayi niyar barin nahiyar ne gabadaya, nayi niyar in bar kasar in nufi wata can mai nisa inyi rayuwata ni da dana Al-Ameen kawai ba tare da takurawar kowa ba. To kuma sai wani umarni yazo min daga headquarter na SSS cewa ana bukatar na gudanar da binciken sirri akan wasu barayi da suka addabi nahiyar Kano, da kidnappers da suka addabi garin Ikko, aka bani zabin inda naga ya dace naje ni kuma na zabi Kano, saboda haka ne nayi badda kama domin nasan duk inda na shiga a fadin duniya sai dangina sun zakulo ni wanda ni kuma ban shiryawa hakan ba a yanzu. Na shirya na taho Kano kan cewa nan da watanni biyu zan kai cikakkun bayanai game da barayin nan don ana bukatar a cafke su cikin gaggawa.
Babban dan Hajiya Tabari Faisal, shi ya kasance abokin aikina. Bayan na iso Kano na sauka a gidansu muka fara shawarar ta yadda zamu gudanar da aikinmu ba tare da an samu wata tangarda ba, daga baya da muka samu bayanin inda suke zaune ne muka yanke shawarar zuwana unguwar a matsayin er aiki, tare da taimakon Hajiya Tabari. Anan na bar Al-Ameen a hannunta don bana son zargi ya dasu a zuciyoyin wadanda zan zauna dasu. Nayi kokari nayi creating zumunci a tsakanina da Samuel da abokanshi, ta haka nake samun guntattakin bayanan da muke turawa ofishin en sanda, duk da cewa ba yadda nake so ba bayanan suke zo mana. Ranar nan da kaina Ina sane na yanke shi da wuka, nayi amfani da bandage da plaster na musamman na nade mishi yatsa, dalilin su muke daukar duk wata hira da suke yi shi da abokan satar shi, na kuma yi kokari nayi planting bugs a cikin motar da yake hawa da cikin gidansu, inda kuma cikin Ikon Allah ta haka ne muka san zasu shiga gidan babban dan kasuwa Alhj. Tanimu su yi sata, kuma suna da plans na idan sun gama da can su fado nan gidan su yi sata, su mana fyade ni da Biebie.... " ta saki wani dan guntun murmushi mai kama dana mugunta kafin ta cigaba, "....sai muka yi amfani da wannan damar aka kamasu red handed, yanzu haka dai suna hannun en sanda ana cigaba da bincike akan su.... Da ace Uncle bai zo ba, da ina tunanin barin kasar nan da sati daya ne kwata-kwata, sai kuma muka ci karo dasu anan ashe kanin ki ne ban sani ba. Wannan shine takaitaccen dalilin daya kawo ni nan gidan....!". Falon ya dan dauki er guntuwar hayaniya da kus-kus game da labarin Ameenar, kafin kuma suka ci gaba da en hirarraki. 'Yan biyu da mamakin canzawar nannynsu a dare daya yaki sakin su har yanzu, suka matsa suna shafa fatar jikinta suna tambayar wai fatar tace? Sai da suka ba kowa na falon dariya. Sai bayan La'asar Faisal dan gidan Hajiya Tabari yazo daukanta, Ameenah tayi musu rakiya har inda yayi parking motarshi suna kara tattaunawa game da aikinsu, daga karshe dai suka yi sallama ta koma cikin gida.
Daki suka kule ita da Biebie da Anti Jamila suna ta hirarrakinsu yayin da Uncle da Faruq suka tafi xagaya gari, yara kuma suna falo suna ta wasansu da Al-Ameen.
©Jeedderh🐾
[5/2, 10:41 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•09•°🐾
Karfe goma na safe Ameenah ta fito daga dakinta janye da trolley Anti Jameelah na biye da ita. Sanye take da doguwar rigar material yellow mai tashi ta yafa dan siririn bakin gyale a kanta. 'Danta Al-Ameen ma yana cikin shiga mai kyau yana rike a hannun Uncle Mukhtar.
Ameenah ta durkusa a gaban su Ummie tayi musu sallama, suka rungume juna ita da Biebie cikin jimamin rabuwa da juna da zasu yi, haka twins suka rungumeta suna kukan sai sun bita, da kyar ta samu suka saketa akan Alkawarin zata zo ta gansu. Gabadaya suka musu rakiya har bakin motarsu suna musu adduar a sauka lafiya. Faruq da yake zaune a seat din direba ya juyo ya kalli Biebie suka hada idanu dashi, kallon juna suka yi ido cikin ido na en wasu sakanni, ya sakar mata wani tattausan murmushi mai isar da wasu sakonni zuwa gareta na musamman, ya kanne mata idonshi guda daya tare da jan motar suka tafi fuskar shi na dauke da murmushin da yake kan fuskarshi still. Biebie tayi tsaye tana kallon motar har suka fita daga gate din cikin wani irin sanyin jiki, zuciyar ta na kara jaddada mata cewa ta kamu da soyayyar wanda bai san tana yi ba, sai dai murmushin da yai mata yanzu fa? Ita dai tasan ba irin murmushin data saba gani a tare da sauran mutane bane....!
Suna fita daga cikin layin suka yi clashing da motar shi shi kuma yana kokarin zai shigo layin. Coincidentally idanuwanshi suka sauka a bayan motar, yayi sa'ar yin tozali da budurwar, tana yiwa wani kyakkyawan babe wasa. Hakoran ta farare tass masu kyau da tsari suka kara haska fuskarta. Bai san lokacin daya take birki ba zuciyarshi na racing, idanuwanshi sun rufe, bai ga kowa a cikin motar ba sai ita. Da gaske ita din ce? Ko kuwa dai mafarki ne yake yi?? Ko kuwa son ta har ya kai minzalin da zata dinga mishi gizo??
Wani wawan u-turn yayi da motar ya zabure ta cikin wani matsiyacin gudu ya bi bayansu sai dai ko kalar motar bai gani ba, ya dinga zagaye titin yana raba idanu amma inaa! babu su babu alamun su. Gefen hanya ya samu yayi parking yana shessheka kamar wanda yayi tseren kilometers dari, gabadaya kwalwanshi ta rikice, ta dauke daga aiki ya rasa tunanin me ya kamata yayi a lokacin. Shi dai yasan cewa babu tantama ita ce ya gani, amma yana cikin rudanin itan ce ko kuma wata mai kama da ita ce ya gani ko kuma aljana ce?
Ba tun yau ya sadakar kan cewa ya fada tarkon son jinnu ba, saboda yadda yarinyar da ko sunanta bai sani ba take shiga cikin rayuwar shi kuma ta bace bat bata barin ko kurar ta ya gani. Ya shiga gyada kanshi cikin yarda da abinda zuciyarshi ke rada mishi a kanta, ya furta a fili "yes! She must not be a human, yes of course!! Ba mamaki aljanar ce". Da haka ya ja motar cike da kwarin gwiwa ya nufi gida, sai ganin shi suka yi kwatsam kamar wanda ya diro daga sama don bai sanar dasu dawowar shi ba, nan suka shiga maraba dashi.
*****
Tafiya suke yi kan shararren titin da zai kaisu Gombe, Ya Faruq ya kure malejin motar kamar wanda yake so ya tashi sama. Hira suke yi cikin nuna kauna da fahimtar juna wanda har sun manta yaushe rabon da su yi irinta. Karfe biyu a cikin garin Gombe ta musu. Gidansu wani babban flat house ne dake cikin Wakili's Estate, babban gida ne wanda gabadaya cikin estate din babu mai girman shi. Estate din gari guda ne mai dauke da parts parts wanda manyan 'ya'yan marigayi Sani Wakili da kannensa suke zaune a ciki, tsakanin kowane gida akwai tazara mai dan yawa, hakane yasa idan mutum yaso zai iya share sati guda curr ba tare da yaga wani ba.
©Jeedderh🐾
[5/2, 10:41 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•10•°🐾
Isarsu gidan ke da wuya, gida ya hargitse da murnar dawowar Auta-Ameenah, babu babba babu yaro. Da kyar ta samu ta yakice su ta isa ga Amminta dake zaune akan wata kujerar alfarma a tsakiyar falon su. Ta duka a gefenta ta kwantar da kanta akan cinyarta ta lumshe idanu a hankali tana shakar daddadan kamshin dake fita daga jikin mahaifiyar tata yayin da kewarta ke kara taso mata. Cikin kwantar da kai da kasalallen sauti tace "Ammie ki yafe min please, nasan cewa ban kyauta miki ba. M sorry, na saka ki cikin damuwa saboda son kai irin nawa, kiyi hakuri ba zan sake maimaita abinda nayi ba". Dattijuwar taji zuciyarta tayi sanyi sosai, taji dan fadan da tayi niyyar yi mata ma ya bace bat. Bata ce komi ba sai hannuwanta data dora akan autar tata tana shafawa a hankali. Cikin haka yayunta maza da mata suka shigo falon, ta tafi da murnarta ta dinga rungume su daya bayan daya tana gaishe su, sai da suka gama murnar suka zaunar da ita a tsakiyar falon suka rufu a kanta kowa da kalar fadan da yake mata akan tafiyar da tayi babu sanarwa ta barsu cikin zullumi da tashin hankali. Tun tana iya basu hakuri har tayi shiru, daga karshe kuma sai ta fashe musu da kuka, hakan sai kuma ya sanyayar musu da jiki suka sassauta da fadan suka koma lallashi da nasiha. Yara kanana da matasan dake cikin estate din suka fara shigi da ficin zuwa mata sannu da zuwa, abinci kuwa har sai da suka rasa inda zasu ajiye shi.
Bayan sallar La'asar ta shirya ita da danta, ta shiga cikin estate din, sassa-sassa ta dinga shiga tana gaisawa da danginta, sai bayan magriba ta dire a gidan babban Yayansu Al-Mustapha tayi sallah taci abinci acan, a takaice dai sai wajen karfe goma na dare ta samu ta koma part dinsu.
Kwanansu Uncle Mukhtar biyu suka koma Mumbai cike da kewar Ameenah da babyn ta. Itama cike da jin kewar tasu suka rabu, sai dai tana so ta zauna cikin danginta ne yanzun don haka bata samu damar amsawa Uncle tambayarshi a gareta na cewa yaushe zata koma musu ba.
Kimanin satinsu biyu kenan a Gombe, sunyi fresh ita da babynta sun kara kyau, kowa tattalinsu yake yi, ta samu kwanciyar hankali irin wadda ta jima bata samu irin ta ba. Yau data tashi ko barcin asubahi bata koma ba, baby Al-Ameen ya hanata barci da kiriniyarshi da alamun yunwa yake ji. Da kanta ta shiga kicin ta hada mishi custard ta zuba wadatacciyar madara a ciki ta zauna tana bashi, yana gama sha kuwa barci ya dauke shi. Ta kura mishi idanu tana kallonshi fuskarta na cike da annuri tana jin kaunar yaron a cikin zuciyarta har ma da jinin jikinta. A hankali ta zame shi daga jikinta ta mike, hijabi ta zura ta tafi sassan kanin mahaifinsu Kawu Hamza domin ta gaida shi.
A babban falon shi ta same shi a zaune ya harde kafafu akan kujera yana sauraren labaran safe. Kawu Hamza mutum ne mai tsananin taurin kai da fada, kaifi daya ne shi wanda idan yayi magana to ta zama fakat! Don kuwa baya canzata kome za ayi, sai dai yana da tausasawa da taushi ta wani fannin. Ba kannenshi ba, har yayyen shima suna shakkarshi don kuwa bashi da sauki, shi yasa gabadayan yaran gidan suke matukar jin tsoron shi. Cikin dari-dari tayi sallama ta shiga falon ya amsa mata babu yabo babu fallasa. Ta durkusa a can nesa dashi ta gaishe shi ya amsa, tayi shiru a zaune kamar wadda take jiran yace wani abu, amma har ta share kimanin mintuna takwas a durkushe bai sake kallon inda take ba ma. Don haka ta tashi ta juya zata tafi cike da kwarin gwiwa, sai data kai bakin kofa ta jiyo sautin muryarshi a kaurare, "dan zo mana Ameenatu...!" gabanta yayi wani mummunan faduwa, taji kamar ta ruga da gudu ta ga hakan ma wata damuwar ce, bata da zabi daya wuce ta juya, ta fara tafiya a hankali kamar wadda take kan kaya tana hardewa, bata karasa kusa dashi ba ta zube akan gwiwoyinta kamar mai neman gafara. Kallonta yake yana sakace hakoranshi yana jifanta da wani irin murmushi, yayin da cikinta ya shiga kadawa......
©Jeedderh🐾
[5/2, 10:41 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•11•°🐾
Ta jima sosai a gabanshi ba tare daya kara ko kallonta ba har sai data gaji da durkuson, can dai ya mula ya mulmule yace "har kin gaji da gudun kin dawo ne?" ta dukar da kanta kasa bata ce komi ba, ya sake cewa "to ya zancen mu dake? Kin dai san ba wai canza maganar zanyi ba saboda wannan dan gudun watanni biyun da kika yi ba koh?" gabanta ya kara faduwa ta dago tana kallonshi, "Kawu....!!" ya zaburo mata dama cike yake da ita, "kawun me? iye?" ta girgiza kai idanunta cike da kwalla tace kayi hakuri don Allah Kawu ka janye zancen yin aure yanzu, wallahi ba zan iya ba!...
Kallonta yake kamar wata sabuwar mahaukaciya har sai data dasa aya, yace Ameenatu? Ta amsa. Yace "to bari kiji....., kin ga kwana talatin cis? To shi na baki ki fitar da miji, zan hada aurenku da Rukayyah, Faruq da Maimunah duk a rana guda in auras. Ina sanar miki ko bayan bangon duniya zaki gudu wannan karon ba zai dameni ba. Sai dai zaki je ne ki dawo ki tarar da igiyar aure a kanki, don haka zabi ya rage naki. Aure ne nan da wata daya ba fashi, idan kuma baki fitar da miji ba zuwa lokacin to ni zan samar miki. Tashi kije na gama magana!".
Tayi kamar ba da ita yake ba, sai daya sake fada a dan tsawace kafin ta mike ta fita kafafunta na hardewa, da kyar ta iya kai kanta sashensu.
Da yake ranar assabar ce babu aiki, kafatanin Yayyenta maza suna sashen sun zo gaida Ammie kamar yadda suka saba. Suna dakinta suna hirarraki game da al'amuran da suka dabaibaye rayuwarsu da kuma hirar duniya. Tana zuwa tsakiyar falo ta dora hannu a ka ta dage ta tsala ihu, a guje Ammie da sauran yayyenta suka fito daga daki suka rufu a kanta suna tambayar lafiya? Bata samu damar magana ba sai kuka data fashe da, da kyar Ya Faruq ya lallasota ta magantu "Kawu ne...!".
Ammie ta dubeta, me kawun yayi? Taja shesshekar kuka ta dire, "ni bansan me nayi wa Kawu ba baya so na... Wai aure zai min bayan ban shirya yi yanzu ba. Ni idan ya gaji da gani na ne ya fada min mana, Ina da wajajen da zanje in zauna shekara da shekaru ba tare da sun gaji da ni ba...!" Yaya Mustapha ya mata dakuwa da hannunshi, "gidanku Auta! Kawun ne kike cewa ya gaji dake don rashin ta ido? Haka kike so a zauna a zuba miki idanu kina yawo tsakanin wannan gida da wancan, wannan garin da wancan kamar wata marassa galihu??" jin haka sai ta dargwaje da kuka sosai, Yaya Bashir ya matsa ya dafa kafadarta, cikin muryar lallashi yace haba Auta! Shi fa auren nan da Kawu yake cewa sai kinyi kin dai san ba wai don baya sonki bane ko kuma ya gaji da ganinki ba, it's for ur own benefit Auta. Kin san duk wata kima da martaba ta diya mace na gidan aurenta, bayan wannan ma Auta it's high time. Shekara nawa da mutuwar Marwan? Almost 2 and half fa, kuma ki ce ba zaki yi aure ba yanzu alhalin you have the chance to? Kin fi so ne mu zuba miki ido kina yawace yawace barkatai da wani aiki marar fasali balle amfani wai aikin en sanda?"
Ganin alamun cewa babu wanda zai goya mata baya cikin yayyen nata yasa ta kara rushewa da kuka sosai, kuka mai karya zuciya. Yaya Faruq yayi saurin matsawa kusa da ita ya janyo ta jikinshi yana dan bubbuga bayanta alamun ban hakuri, ya dubi sauran en uwanshi yace "haba! Ku dinga tausaya mata mana! Ko gama farfadowa daga ciwon rasuwar mijinta bata yi ba sai ku dame ta da zancen aure? Ita dai bata ce ba zata yi ba, cewa tayi ku dan bata lokaci har zuwa lokacin da danta zai yi kwari koh? Kuma ni ban ga aibu a aikin da take yi ba ko kadan...!" Anti Rukky ta dan kalleshi, "ai kai dama kullum kana goyon bayan Ameenah ne no matter what, kai kake kara shagwaba ta kana sawa tana raina mutane pa!" Ammie tayi saurin tare Faruq daga yin magana don tasan yanzu zasu iya hawa sama, ta amshi Ameenah daga hannun Faruq ta kalleta cikin lallashi, "it's okay Auta na daina kukan haka nan kinji? Kyale yayun nan naki da basa son ki muje daki ki ji..." ta ja hannunta suka tafi Anti Rukky ta rufa mata baya... Yayin da mazan suka samu waje suka zauna suna tattaunawa game da matsalar Ameenah.
A can daki kuwa da kyar Ammie da Anti Rukky suka shawo kan Ameenah tayi shiru ta daina kuka, bayan Ammie tace zata samu Kawu da kanta tace mishi ya kara mata lokaci, sai lokacin fa ta danji sanyi a ranta har ta dan murmusa. Aikuwa kwananta biyu ta tattara kayanta ta tsere gidan Yayarsu Anti Fati da ke aure a Ghana don a cewarta ganinta da Kawu yake yi ne a gidan yake sawa yaji ya gaji da ganinta.....
©Jeedderh🐾
[5/2, 10:41 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•12•°🐾
Ta samu tarba mai kyau daga gareta da 'ya'yanta, tarba fiye ma da wadda tayi tsammani. Daki guda aka ware mata ita da babynta wanda daga gani saboda zuwanta ne aka yi tsarin, komi wanda karamin yaro kamar Al-Ameen zai bukata an ware shi daban a cikin dakin. Gaskiya en uwanta suna matukar ji da ita kuma suna kaunarta, abinda ta dinga fada a cikin ranta kenan lokacin data shiga dakin, hakan ne ya kara saukar mata da natsuwa da farin ciki sosai. Wanka ta fara yi, ta yiwa babynta ma ta nado shi cikin towel tana yi mishi wasa yana ta bingira mata dariya, a lokacin jinta take yi kamar wata wadda bata da kowace irin damuwa a cikin duniyar.
Shirya shi tayi tsaf itama ta shirya suka fita falo, Anti Fati da yaranta suna jiranta akan dinning table. Ta zauna suka yi serving dinta lafiyayyun kalolin abinci, ta kuwa bude cikinta sosai ta ci abincin nan. Suna gamawa Anti ta hada su da direba da securities biyu suka shiga gari sai yamma likis suka dawo a gajiye tulis.
Wannan rayuwar farinciki data tarar yasa ta manta da wani zancen Kawu Hamza da batun aure, auren data tsana ta ki jini. Suna can abinsu taci biyar ta tsoma goma, babu aikin da take yi sai dai yawace yawacen wajajen shakatawa da parks.
Satin su uku a can matar Yayar su Abdul-Hadi ta haihu. Suka yi shiri har ma da Anti Fati suka taho Najeriya wajen suna, sunyi bul-bul dasu ita da babynta gwanin ban sha'awa, ba zaka taba musu kallo daya ka kawar da kai ba, ko kai waye ka gansu a lokacin sai sun tafi da imaninka.
Abin mamaki a can ta samu Safeenah tazo wajen suna, suka tari junansu cike da farinciki da nuna kewar juna. Sai da suka nutsu ne Ammie take fada mata ai ita Faruq ya tsayar a matsayin wadda zai aura. Ameenah ta hangame baki cikin mamaki, kafin tayi dariya kawai ta girgiza kanta, dama tasan za a rina yadda taga suna satar kallon juna lokacin da Faruq yaje Kanon. Ko bayan dawowarsu haka ya amshi lambar Biebie din a wajenta a cewar shi yana so ne su gaisa da ita, daga nan ta sha kama shi suna waya da ita, ta kuma sha tsintar hotunanta birjik a wayar Faruq din. Nan kuwa ta shiga tsokanarta, matar Yaya sama matar Yaya kasa sai da Ammie ta tsawatar mata don kuwa ta hanata sukuni a gidan wai ita kunya, tayi dariya da taji abinda Ammie tace, tace Ammie ba wani kunya wallahi tsegumi ne kawai ba wani abu ba, wannan matar har wani kunya ta sani? Ammie ta dauki filon kujera zata maka mata tayi waje da gudu, a bakin kofa suka yi karo da Ya Faruq. Ta kalleshi tana dariyar tsokana, "A'ah! Ka ga mijin kawata!" ai kuwa ya bita da gudu suka kwasa, nan suka shiga zagaye falon suna dariya. Ammie kam kai kawai ta iya girgizawa tare da furta "Allah ya shirya!" don kuwa tasan idan suka fara guje-gujen nan ba wanda yake hana su har sai sun gaji don kansu.
A daren ranar tana dakinta a tsakiyar gadonta tana kokarin shirya baby Al-Ameen cikin kayan barci lokacin da Biebie tayi sallama ta shigo dakin na Ameenah, tsayawa tayi tana kara kallon dakin kamar yau ne ta taba ganin hadadden daki irin wannan. Babban daki ne mai kyau wanda yaji saitin wani madaidaicin royal bed brown, haka daga wardrobe zuwa su dressing mirror da lockers din dakin duka browns ne. Labulayen dakin kuwa orange-red ne, gaskiya dakin nata ya burgeta sosai. A tsakiyar dakin an shimfida wani tattausan brown circled carpet, daga can gefen gadon ta dan karamin gadon yara ne da kayan wasan baby Al-Ameen. A jikin bangon dakin kuma babban frame ne na hoton duka family dinsu, sai dai daga gani drawing ne ba photograph bane, kai yawancin hotuna da frames din da suka manatee kowace gaba ta bangon dakin zane ne ba snapped photos ba.
Ta karasa gefen gadon ta zauna tana kallon Ameenah, tace waye yayi drawings dincan Ameenah? Bata dago ta kalleta ba ta amsa ni ce!! Ta kalleta cike da mamaki, ke kuma? Yaushe kika iya drawing?? Dai-dai lokacin ta gama daurawa baby Al-Ameen robe din jikin rigar shi, ta dago shi tana dan jijjigawa tana murmushi tace ba dai na iya ba zaki ce, cewa zaki yi yaushe na koya? Kwalin degree nake dashi akan zane!! Safeenah ta kama haba cikin mamaki tace da gaske?? Tayi dariya sosai da yadda tayi, tace Kina mamaki ne? Tace not even wondering, but doubting as well. Ta kalleta tana daga gira, kallo irin na 'au Allah?' kamar taji tambayar da tayi mata tace kwarai! How did u manage to train for police and at d same time studying arts&drawing? It's somehow difficult u know, u even confuse me wallahi.....
Ameenah ta danyi wani irin murmushi mai ciwo da tasowar wani abu mai kama da makaki da tokare makoshi, tace "umhhh... !" kawai. Biebie taso ta kara cewa wani abu, sai dai canjin yanayin data gani a fuskar kawar ta ta yasa ta mannawa bakinta kwado ba don taso ba. Sai ta dauko wata hirar ta daban ta fara jan ta da ita, sai dai ta kula da kyar Ameenah take iya daurewa tana amsa mata, don haka tayi excusing kanta ta tafi zuwa dakin da aka mata masauki.
A gabadayan ranar barci ya kauracewa idanun Ameenah, ta mike zaune dangargar a tsakiyar gadon, sosai take jin zuciyarta na suya. Safeenah ta taso mata da wani miki a cikin ranta wanda ya fasa mata wani tsohon kurji daya fara warkewa a zuciyarta gashi yanzu ya dawo mata sabo fil ya fashe, mugunyarsa ya fara azabtar da ruhinta.
Ta jingina kanta da allon gadon ta kurawa wani zane ido wanda aka zana shi da kala da takarda mafi tsada a duniya.
Kyakkyawa ne fari tass, duk da cewa ba duka ake ganin fuskarshi ba ma'ana dai ta gefe aka zana shi. Yanayinsa da kalar fatar shi tafi kama data mutanen Libya ko kuma India. Yayi dariya yayin da gefen kumatunshi suka lotsa sosai irin double dimples dinnan, ya saki wasu fararen tantabaru guda biyu daga hannunsa sannan kuma ya bisu da kallo, wasu kyawawan butterflies suna shawagi a saman kansa. Wato zanen ya zanu sosai, kai daga gani kasan kwararre ne sosai yayi zanen. Daga shi har tantabarun jiki sun fito sosai a cikin zanen yadda kasan ka kirasu su amsa... Wani irin murmushi ne ya subuce a bakinta, very cute and soft, yle feeling very bitter deeply inside ha heart.
A hankali rayuwarta ta baya ta fara yi mata yawo a idanu kamar a lokacin take faruwa.....
*......AMEENAH SANI WAKILI.....!*
©Jeedderh🐾
[5/2, 10:41 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•13•°🐾
*....AMEENAH SANI WAKILI....!*
Mahaifina Alhaji Sani Muhammad Wakili da mahaifiyata Hajiya Zakiyyah, en asali garin Gombe ne kuma dukkaninsu a cikin Gomben suke Da zama. Auren hadi ne aka daura musu ba tare da kowannensu ya sani ba, sai dai dukansu sunyi biyayya ga zabin iyayensu kuma sun ga falalar biyayya ga iyaye, da kuma samun budi cikin al'amuransu.
Allah ya albarkace su da haihuwar 'ya'ya takwas., Yaya Al-Mustapha shine da na farko a wajensu yanzu haka shi babban matukin jirgin sama ne, sai Yaya Fati tana aure a Ghana, Yaya Hadiza tana auren wani kusa a Gwamnati suna zaune a Abuja ita da iyalanta, Yaya Bashir kuma lecturer ne a FUG, Yaya Abdul-Hadi likitan ido ne dake aiki da asivitin Saudi-Nigeria, Yaya Faruq kuma yana aiki da matatar man fetur ta Najeriya dake rassan Gombe, Anti Rukky wannan shekarar ne ta gama karantunta na medical doctor a jami'ar KL, sai ni Auta Ameenah. Gabadayanmu mun taso karkashin kulawar jajurtattun iyaye, sun tsaya mana tsayin daka wajen ganin mun hada kawunan mu mun zama tsintsiya madaurinki daya, kuma Alhamdulillah mun taso ne cike da kaunar juna, sam bama son bacin ran junanmu.
Mahaifinmu ya rike kujerar Gwamnan Gombe a lokacin ko haihuwa na ma ba ayi ba, bayan ya sauka mutane sun so ya sake fitowa sai dai ya ki. Sai ya fara kasuwanci wanda cikin dan kankanin lokaci sunansa da kasuwancinsa yayi tambari a ciki da wajen Gombe, Allah yayi mishi nasibi a cikin al'amuransa. Mahaifina mutum ne mai son taimakon mutane, son zumunci, kaunar en uwanshi, wanda kuma abin hannunshi bai rufe mishi ido ba ko kadan. Yasan manyan mutane da manyan Gwamnati iri-iri, da wannan damar ya dinga amfani yana samawa matasa da diyan 'yan uwa da abokai yana sama musu aiki da gurbin karatu a wajaje da dama, haka ne tasa mutane ke girmama shi kwarai.
A kokarinsa na son hada kawunan en uwanshi waje guda saboda iyayensu sun jima da rasuwa, su hudu kawai suka bari duka maza, Kawu Tijjani shine babba, sai babanmu, Kawu Hamza sannan Kawu Shazali. Mahaifinmu ya sayi wani makeken katon fili ya fara gininshi da gidaje arba'in, clinic da katon store. Yayi niyar zai tattaro en uwanshi da iyalansu domin su zauna under one roof, an dai kammala ginin lafiya lau sai dai Allah bai nufa za a tare dashi ba, Allah ya amshi ransa a wani daren juma'ah a lokacin ina da shekaru takwas a duniya. Hakika munyi kukan rashi sosai, kukan rashin wani majingini muhimmi a cikin rayuwar mu.
Wata daya da rasuwarsa Kawu Hamza ya tattara mu muka koma estate din da zama. Babban Yayanmu Al-Mustapha shi ya amsa kason mu bayan an raba mana gado ni da Anti Rukky, Ya Faruq dana Ammie ya hada da nashi ya cigaba da juya mana.
Kawu Hamza ya cigaba da tallafarmu ya kuma rike gidan kasancewarsa mutum ne mai zafin nema da kuma fada yasa kowa ke shakkarsa a gidan. Da yawan wadanda Abbanmu ya samarwa aiki sun ci gaba da waiwayar rayuwarmu duk da cewa ba ma cikin rashin komi, ciki har da Uncle Mukhtar wanda Abbanmu ya sama mishi aiki a Jordan bayan ya gama degree dinshi akan engineering, ita kuma matar shi Jameelah ya samar mata gurbin karatu. Allah ya hada jini na da couple dinnan tun asali, shekarunsu uku da aure amma har lokacin Allah bai basu haihuwa ba. Lokaci zuwa lokaci idan mun samu hutu a school uncle Mukhtar ya kanzo da kanshi ya daukeni inje in musu hutu a Jordan, haka idan suka tashi zuwa Najeriya to akwatun tsarabata daban ne, na saba dasu sosai fiye ma da wasu en uwana da muke zaune dasu a cikin estate din saboda yadda suke tattalina.
Duka-duka watanni shida ne da rasuwar Abbanmu lokacin da Uncle Mukhtar ya diro Najeriya da burinsa na son a basu rikona. Ganin yadda muka shaku dasu sosai yasa bai samu matsala daga wajen su Ammie ba sai wajen Yaya Faruq daya kasance duk cikin yayyena ba wanda muka yi sabo dashi kuma yake ji dani kamar shi. Yayi tsalle ya dire kan cewa bai yarda in tafi in barsu ba, aka yi lallashin duniya amma ya ki yarda sai da Kawu Hamza ya mishi jan ido kafin ya amince ba don ranshi yaso ba. Cikin kwanaki uku kacal abubuwa suka kammala, muka daga kasar Jordan.
A Jordan na tarar da wata irin sabuwar rayuwa mai tsananin ni'ima da gardi, gata, tattali, da kulawa. Kasancewar ni kadai ce a gabansu yasa babu irin so da ban ga kalarsa ba a wajen wadannan bayin Allahn. Bana kewar gida ko kadan saboda kullum muna cikin waya dasu, kuma sukan ziyarce ni lokaci zuwa lokaci musamman Yaya Al-Mustapha idan harkokinsa suka kawo shi Jordan, haka kuma nima Uncle yana kaini hutu wajensu, a haka rayuwata take tafiya. Lokacin da na cika shekaru goma na kammala elementary school. Lokacin Uncle ya samu karin matsayi a wajen aikinsa an kuma canza masa wajen aikin zuwa Mumbai sai dai lokacin saura shekara daya kacal ta gama karantunta saboda haka shi ya tafi ya barmu a Jordan. Na jira Anti Jameelah ta gama karantunta yayin da nake zuwa makarantar hadda cikin dan lokacin, kafin kuwa shekara guda din ta zagayo tuni na sauke Al-Qur'ani mai girma har ma na fara nisa a haddar shi har Anti Jameelah ta kammala karantunta muka koma Mumbai da zama.
Tun tasowa na, kai tun ma ina yarinya Allah ya hore min baiwar iya zane, ko a makaranta a inda nafi maida hankali kenan, don haka Uncle ya sama min makaranta wanda su base teaching dinsu akan arts & painting ne, a can na kara samun experience sosai.
Wannan kenan....!!!
©Jeedderh🐾
[5/2, 10:41 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•14•°🐾
Ana cikin haka ne Anti ta samu ciki, farin cikin da muka yi ni da Uncle abin bai faduwa. Dadi na daya za a haifa min en kanne ina wasa dasu, in goya su, muje park tare. Idan ina gayawa Anti ko Uncle haka sai dai su yi ta dariya. Hidimar gida sai ta dawo hannu na, muddin ina gida to bana barin ta daukar ko tsinke, fannin girki ne kawai take dan kama min don zuwa lokacin ba iya shi nayi ba tunda dama can ni bana shiga kicin. A haka cikin ta yayi ta girma har ya shiga watan haihuwarshi, Anti ta haife twins dinta mace da namiji Uncle ya musu huduba da Salmah da Asleem. Duk da cewa muna nesa da gida amma dangi sun halarci taron suna sosai. Yayar Uncle Hajiya Karima taje tayi kwana daya ta koma, sai dai cikin Ikon Allah har ta tafi bamu hadu da ita ba, dalilin da yasa sam ban gane ta ba lokacin da naje Kano.
Wata kanwar mahaifin Anti Jameelah ce aka bari zata yiwa Antin wankan jego, zaman Iya Hari a rayuwarmu shi ya kawo tabarbarewar zaman lafiya da kwanciyar hankalin dake gidanmu. Tunda matar ta zo na kula cewa bata yi maraba dani ba sam, idan na gaishe ta bata amsawa sai dai harara ta biyo baya, don haka na fara yin baya-baya da ita.
Watarana da safe na shiga dakin Anti daure da tawul iyaka gwiwa ta, maclean din toilet dina ne ya kare don haka naje zanyi amfani da nata. A bakin kofar dakin muka ci karo da Inna Hari, na dan durkusa na gaishe ta, bata amsa ba sai bina da tayi da kallo har na kule uwar dakin Anti ta sameta a zaune bakin gado tana shayar da Asleem. Muka gaisa sama-sama na sanar da ita bani da maclean ne, nan ta kawo guda daya ta bani. Ina juyowa muka kara cin karo da Inna Hari ta shigo dakin, ta sake bina da wani irin kallo wanda ya fadar min da gaba sosai, har na baro dakin ina jin idanuwanta a jikina. Jiki a sanyaye na gama shirin makaranta na fito, dakin Anti na koma zan amshi kudin makaranta na da yake a wajen ta Uncle yake bari. A bakin kofar na jiyo muryar Inna Hari kamar cikin fada tana magana, ".....kada ki yarda Jameelah! Wannan yarinya da danyen jiki irin wannan kike bari tana yawo a tsakar gidanki har ki barta da mijinki a waje guda?! To wallahi ki kiyayi zamani da yaran zamani, idan baki tashi tsaye ba wallahi sai dai kiji gari ya waye ana buda ta zama kishiyar ki...!!".
Gabana ne yayi wani mummunan bugawa, kafafuna suka shiga rawa sosai, da kyar na samu na iya saisaita kaina nayi sallama na danna kaina dakin. Gani na a shirye tsaf cikin kayan makaranta, Anti ta bude jaka ta miko min kudi na amsa cikin rawar hannu. Ban iya furta ko uffan ba na juya na fita, Inna Hari ta sake bi na da wani kallon, zan iya cewa a tarihin rayuwata ban taba cin karo da irin wannan kallon ba sai yau. Sai dai dadin da naji shine ko da na dawo daga makaranta ban ga wani canji daga Anti ba, hakan sai ya sanyayar min da rai.
Kwanaki suka cigaba da tafiya, ni dai ban san ya aka yi ba, amma as time goes on sai naga sakin fuskar da Anti take yi mun ya ragu, haka ta daina yawan ja na a jiki da take yi. Bata cika son ina rabar jikin Uncle ba hakan ni kuma hakan ya riga ya zame min sabo... Kai ko waya taga ina yi dashi sai ta hau ni da fadan me yasa zan kira shi? Kai kafin dai Inna Hari ta koma Najeriya sai da ta wargaza mana zaman lafiyar gidan mu tas.
Kamar dai watarana bayan tafiyar Inna Hari, Uncle yayi wata tafiya ta sati biyu ya dawo. Dama na matsu da dawowar tashi saboda a matukar takure nake da sabon yanayin da Anti ta tsiro dashi. Ina jiyo sallamarshi na mike da hanzari na tare da jefa laptop din da nake game dashi akan kujera na saki ihu, na tafi da murnata na dale jikinshi ina mishi oyoyo. Nan ya daga ni sama yayi juyi dani a falon yana dariya kamar yadda ya saba, sam baya jin nauyin jikina haka zai daga ni sama yayi ta juyi dani kamar wata baby, ya dire ni kasa ya durkuso da kanshi saitin kumatu na da niyar bani peck a kunci ko goshi....
Wata irin gigitacciyar tsawa da aka ba shiri nayi baya a razane., Anti ce tsaye a kanmu tana huci kamar wata macijiya, banyi mamaki ba don kwanan nan irin wannan side din nata ne nake gani. Uncle kam baki ya saki cikin mamaki yana kallonta. Ta iso fusace ta janye ni daga wajen tayi wurgi dani gefe, Allah ya taimake ni na fada kan kujera. Uncle ya cika da mamakinta sosai, yace Jameelah meye kike yi ne haka? Aikuwa ta zabura ta hau masifa da jidali, ta inda take shiga ba tanan take fita ba, wai akan me zai kama ni ya rungume ya hada da jikinsa har da kokarin yi mun kiss, akan me? Ita dai ya kiyaye ta don ba zata laminta ba..... Ta wuce dakinta fuuuu a fusace kamar kububuwa tana maganganu da sam ban fahimci ko kalma daya daga cikin su ba. Ya bita da ido yana kallo cike da tsananin mamaki, can kuma ya dawo kaina ya fara lallashi na don kuwa kuka nake sosai saboda tsoron da Anti ta bani, sai da yaga na ware sosai sannan ya tashi ya bi bayan matarshi. Bai jima ba ya fito fuskarshi dauke da alamun damuwa, gani na zaune a falo yasa ya dan saki fuskar tashi. Yazo ya kama hannuna muka tafi dakina, a can ya tambaye ni ko naci abincin rana? Na girgiza kaina a sanyaye don ko karyawa ma banyi ba, wani guntun sauran cookies dana siya a makaranta ne na samu naci yau da safe. Ya girgiza kai cikin tausayi kafin ya tashi ya fita, can ya dawo da leda mai dauke da tambarin wani suya spot. Ya zauna a gefena ya bude ledar ya fiddo gashin kaza yayi jazur yana ta kamshi, da kanshi ya yanko min kazar ya miko min, hannu na rawa na amsa na fara ci hannu baka hannu kwarya, rabon da inci nama har na manta, kai ba nama kadai ba, sauran abubuwan makulashe ma, da har sai naci na ture amma yanzu babu su. Uncle kam bina yake da kallo cikin tausayi, sai dana kusa gama cinye kazar nan kuwa, Uncle yace kin koshi ne? Na gyada mishi kaina. Ya bude robar yoghurt ya tsiyaya ya mika min, na amsa. Sai daya tabbatar da na koshi sannan ya Kyale ni ya tafi dakinshi. Ganin yanayin gidan yau babu dadi yasa da yamma na shirya na tafi gidansu wata kawata da muke aji daya a makaranta a can bayan gidanmu, Hanan. A can na jima sosai muna hirarrakin duniya, sai bayan magriba ta raka ni na koma gida.
A hankali na fara fahimtar inda Anti ta dosa, sam bata kaunar ta ga na rabu da jikin Uncle har shi kanshi din ko kadan. Da na gane hakan sai nima na kame kaina na daina kusantar shi, mu'amalar mu dashi sai ta fara yin baya, idan ka ga hirarmu dashi sai dai a waya idan baya gari, shima sai dai in kule a uwar daki na.
Tafi-tafiya na fara wata irin rayuwa ta cikakken 'yanci, babu kwaba idan nayi ba dai-dai ba, babu tambayar ina zaki je idan zan fita, haka idan zan fita in kwana a waje Anti ba zata tambaye ni ina naje na kwana ba, babu tashi kiyi sallah ko wani abu makamancin haka, tsakani na da Anti sai dai kyara da tsangwama. Aikuwa sai na fara rama nan da nan saboda damuwar da nake sa wa raina, ban taba kwana in tashi da yunwa ba sai a wannan tsakanin, saboda na saba a kodayaushe sai dai in ga abinci a shirye kan table, wani lokacin ma sai an hada da lallashi kafin in ci abincin. Yanzun kuwa sai aka daina shirya abincin kan table sai dai a barshi a kicin, ni kuma lokacin ji na nake kamar wata bakuwa a gidan. Sai idan naga yunwa tana nema ta kashe ni ne zan tafi kicin in dauki abinci, to watarana ma sai dai in tarar ba a ajiye mun ba sai dai in dora tukunya in dafa.
Ana cikin haka aka tura Uncle kasar New Zealand zai yi wani course na watanni goma, saboda karatuna Uncle yace ba sai mun bishi ba, mu zauna a gida zai dinga zuwa mana weekend duk bayan sati biyu. Anti taji haushin haka sosai don har sai data kasa boyewa tayi magana wai saboda nine zai tafi ya barsu anan? Ya dai samu ya lallashe ta ya tafi yana mai kara jaddada amanata a hannunta don ya kula da rikon sakainar kashin da take yi mun. Ashe hakan ba karamin kara bata mata rai yayi ba, bayan tafiyar Uncle babu irin tsirfa da rashin mutuncin da ban gani ba daga gareta ba, dan abincin da nake dafawa ma kiri-kiri ta hana ni kunna gas wai kada in tada mata gobara a gida, dole dai na hakura na koma siyen abinci da kudina, watarana kuma in dauki abincin a haka inje gidan su Hanan in dafa.
Duk wannan bidirin da ake yi babu wanda yasan halin da nake ciki a gida, Allah ya halicce ni wata irin mutum mai dan banzan zurfin ciki, kafin kaji damuwata aiki ne babba. Ko da can da ina gida Ya Faruq ne kawai mai jin cikina, yanzun kuwa da bana kusa dashi idan mun yi waya ko ya tambaye ni akwai damuwa? Sai dai in girgiza kaina ince babu..... Babu wanda na sanarwa irin sabuwar rayuwar da na shiga.
©Jeedderh🐾
[5/2, 10:42 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•15•°🐾
Ana cikin haka aka tura Uncle kasar New Zealand zai yi wani course na watanni goma, saboda karatuna Uncle yace ba sai mun bishi ba, mu zauna a gida zai dinga zuwa mana weekend duk bayan sati biyu. Anti taji haushin haka sosai don har sai data kasa boyewa tayi magana wai saboda nine zai tafi ya barsu anan? Ya dai samu ya lallashe ta ya tafi yana mai kara jaddada amanata a hannunta don ya kula da rikon sakainar kashin da take yi mun. Ashe hakan ba karamin kara bata mata rai yayi ba, bayan tafiyar Uncle babu irin tsirfa da rashin mutuncin da ban gani ba daga gareta ba, dan abincin da nake dafawa ma kiri-kiri ta hana ni kunna gas wai kada in tada mata gobara a gida, dole dai na hakura na koma siyen abinci da kudina, watarana kuma in dauki abincin a haka inje gidan su Hanan in dafa.
Duk wannan bidirin da ake yi babu wanda yasan halin da nake ciki a gida, Allah ya halicce ni wata irin mutum mai dan banzan zurfin ciki, kafin kaji damuwata aiki ne babba. Ko da can da ina gida Ya Faruq ne kawai mai jin cikina, yanzun kuwa da bana kusa dashi idan mun yi waya ko ya tambaye ni akwai damuwa? Sai dai in girgiza kaina ince babu..... Babu wanda na sanarwa irin sabuwar rayuwar da na shiga.
Ranar wata Alhamis ina dakina da safe, kadaici duk ya dame ni. Zane nake yi a cikin art pad dina lokacin da kiran Hanan ya shigo waya ta. Hanan kawa tace sosai, makarantar mu daya da ita kuma ajin mu daya, kaf fadin makarantar mu ita kadai ce kawata. Haifaffiyar garin Rajashtan ce, aiki ne ya kawo babanta Hashim Mumbai.
Da zumudi na na daga wayar muka gaisa da ita, tace in shirya anjima da misalin karfe goma zata biyo ni muje babban Stadium, yau babban dan wasan kwaikwayo na kasar India superstar Marwanuddeen Muhammad Khan zai yi shooting part din wani film dinshi da zai fita wata mai zuwa. Nayi tsallen murna na dire cike da farin ciki, Marwan is my hero. Ina matukar kaunar acting din mutumin sosai don bana jin dadin shirin ko wane dan wasa irin yadda nake jin dadin fina-finan sa. Na tambayeta zancen ticket tace tuni ta siya mana, don haka muka yi sallama da ita akan zamu hadu a gidansu.
Lokacin da muka isa stadium din ya cika makil da mutane duk da cewa ba a fara shirin ba, muka nemi waje muka zauna muna hira muna hadawa da cin pop corn har aka fara daukar shirin. Wasan shine ending part a sabon film dinshi 'Real Footballer' da zai fita wanda shi Marwan din ya fito male leading star actor, usually ban cika son kallon ball ba, amma yau da naga yadda jarumin yake mulmula kwallon da kafarsa kamar wani Ronaldo sai naji ta bani matukar sha'awa kuma jarumin ya kara burge ni. Bayan an gama daukan shirin jarumin ya shiga gaisawa da masoyanshi, sannan ya sanar damu ranar da film din nashi zai shiga kasuwa. Sai da nayi yadda nayi na kutsa ta cikin mutane na dauki hoton mutumin nan sannan muka tafi, a hanyar mu ta komawa baki na yaki rufuwa saboda tsabar murnar da nake ciki. Hanan ta bani e-mail address dinshi, tace wannan personal address dinshi ne wanda yake dashi mainly for shakikanshi da manyan fans dinshi, itama a wajen PA dinshi ta amsa da yake abokin yayanta ne, saboda yadda ta ga ina son actor dinne yasa ta amsar min. Na kuwa yi mata godiya sosai. Aikuwa ina komawa gida na janyo wayana na tura mishi sakon ban gajiya da yadda nake dokin film dinshi ya shiga kasuwa, har zanen da na mishi lokacin da yake buga kwallo sai dana tura mishi. Nayi mamakin tsintar hoton a shafin sa na twitter washegari, bayan kwana biyu kuma na tsinci sakon godiya daga gareshi, yana cewa zanen ya burge shi sosai, kwarai rashin girman kanshi ya burge ni.
*☆☆☆☆☆☆*
Marwanuddeen Muhammad Khan wanda aka fi yiwa lakabi da superstar Marwan, shahararren dan wasan kasar India ne na Bollywood wanda tauraruwar sa ke matukar haskawa a wannan zamanin, yana da masoya bila adadin a kowane sassa na wannan duniyar. Darajarsa a Bollywood industry zata kai kimanin crores ashirin da dori, wanda canjin sa a kudin Najeriya zai kai kimanin miliyan dari bakwai da arba'in kenan.
Fahimtar shi da nayi a wani irin mutum mara girman kai yasa jifa-jifa musamman idan na kalli films dinshi. Wajen daya burge ni ina tura mishi comment, inda ya bani dariya kuwa zama nake yi in zana wajen inyi comment din tsokana in tura mishi, wajen daya bani haushi kuma ko bai burge ni ba kai tsaye nake fada mishi wajen bai yi kyau ba babu wani kwane-kwane.
A hankali wani irin sabo ya fara shiga tsakaninmu dashi, duk da cewa bamu taba jin muryar juna ba ko haduwa face to face, ya kance bai taba haduwa da mutum iri na ba, mutum straight forward wanda baya damuwa da halin da wani zai shiga muddin zai fadi gaskiyar sa ne, gani kuma ina da ban dariya. Idan ya fadi haka ni kuwa sai inji kaina ya fasu don murna. To ni kaina halin Marwan yana burge ni ba kadan ba, mutum ne mara girman kai wanda bai dauki rayuwar shi da nisa ba kamar yadda wasu celebrities din suka dauki tasu rayuwar ba. A takaice dai sai ya zamana babu abinda ke debe min kewa irin fina-finan Marwan dashi karan kansa Marwan din, kasancewar sa mutum mai yawan barkwanci.
©Jeedderh🐾
[5/2, 10:49 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•16•°🐾
A gefe guda matsalar Anti ta fara yawa. Gabadaya yanzu na tashi daga er riko na dawo er aiki. Ni ce gyaran gida, girki wanda zanyi amma kwayar abincin wannan ba zata shiga ciki na ba, nice rainon twins duk da cewa suna da nanny dinsu. Rayuwa ta dai a gidan ta dawo abin tausayi, irin ta yara marassa galihu, gashi na kasa sanarwa da kowa halin da nake ciki har shi uncle din kuwa, idan yazo mana weekend yayi ta tambayana meke damuna saboda yadda nake ramewa ina karewa a tsaye, sai dai kawai ince mishi babu komi ko kuma ince karatu ne.
Cikin watanni hudu kacal da tafiyar Uncle sai gani warwas a gadon asibiti. Ulcer tayi min mugun kamu, sai da aka kai ga rage min hanji saboda ya fara lalacewa. Aikuwa Anti ta ga tashin hankali a wajen uncle, rufe idonshi yayi ya zazzaga mata rashin mutunci, ya kuma tabbatar mata muddin tana son ganin zaman lafiyar ta dashi to lallai ta canza wannan sabon halin nata.
Ganin haka sai ta zubar da wadancan makaman yakin ta dauki wasu, duk ayyukan da take saka ni sai ta daina haka bata hana ni dora abinci da kaina, amma sai ta daina bani kudin break wanda uncle yake bar min a wajenta idan zai yi tafiya, ni kuma bana son fadan da suke yi ta dalili na. Don haka na binciko ATM card dina, daga gida duk karshen wata Yaya Faruq yana turo min kudi yace in dinga hidima dasu, da bana bi ta kansu saboda bani da matsalar komi, amma yanzu dasu nake en kananun hidindimu. Idan suka kare sai in kira wani a cikin yayyena ya turo min. Duk da cewa su basu nuna wani abu idan na tambayesu, amma ni kullum na musu wayar sai in dinga ji na wani banbarakwai, ko kadan bana jin dadin hakan saboda roko ba dabi'ata bace, amma kiri-kiri sai da anti tasa na koya.
Ranar litinin na tashi da sassafe na shirya a gaggauce saboda ina da jarabawar Visual art a ranar. Jiya ban samu na runtsa ba ko kadan ina ta karatu a sakamakon ban samu damar yin tests din course din ba saboda rashin lafiyar da nayi, so nake in samu inyi kokari a exams dinshi yadda idan aka hada da assignments dina in samu ko maki 60 ne cikin dari, in dai samu in wuce aji na gaba.
Na samu Anti a daki tana zaune na gaishe ta, ta amsa fuska a hade. Cikin dari-dari na mata maganar cikon kudin school fees dina ba a gama biya ba, kuma uncle yace min zai turo mata da kudin sai dai banji tayi maganar ba har yanzu gashi kuma makaranta sun bani deadline, muddin ban biya kudin yau ba to ba zan yi jarabawa ba.
Kai tsaye tace tuni Uncle ya turo min da kudin tun satin daya wuce, sai dai tuni tayi sha'anin gabanta dasu don haka inje in san yadda zanyi tun wuri. Wata irin kwalla mai tsananin yaji da radadi naji ta ciko idanuna tana son silalo min, na ciji bakina ina kokarin hana hawayen su zubo min. Ban furta uffan ba don nasan idan nayi magana kuka ne zai kwace min, na juya na koma daki na. Atm card dina na fara nema nasan kila kudin ciki su ishe ni, sai dai sama ko kasa na rasa katin nan, na hargitsa daki na yayi kaca-kaca amma babu alamun ATM. Sai kawai na zube a tsakiyar daki na rushe da kuka cike da bakin ciki, ban taba dana sanin zuwa gidan Uncle ba irin ranar. Ina da iyaye da en uwa masu sona amma gani nazo inda bani da dangin iya bare na baba ana treating dina kamar wata mara galihu. Nan na kudurce a raina idan na gama wannan shekarar zan koma Najeriya abina na cigaba da karatu na a gaban Ammie na da Ya Faruq masu so na.
Da dai naga bani da mafita, dole na mike tsaye. Na duba agogo na ga bakwai da rabi, kawai nace bari inje makarantar ko Allah zai sa su kyale ni. Abin haushi da takaici naje bus stop na tarar bus din da nake hawa har ta tafi. Na fara trekking zuwa babban titi don nasan acan zan samu tunda kudin hannu na ba zasu kai inyi shatar taxi ba.
Ina tafe akan titi ina rangajin gajiya, ga yunwa, barci, gefen kaina sai sara min yake yi da karfi (migraine) ga ciki na dake cakudawa yana min ruri, haka na hau titin nan kwalam ina tafe ina sharar kwalla. Ban san cewa na hau tsakiyar titi ba sai da naji wani irin kuuuuu!! karar take burkin mota a baya na. Razanar da nayi ne yasa na tafi luuu na zube a gaban motar kafin daga bisani na silale kasa, na zube warwas bisa kwalta. Nayi nayi in tashi amma na kasa, wani irin zogi nake ji a hannuna mai gigita kwalwa. Ji nayi an bude murfin motar an fito, sautin Innalillahi....! Naji yana tashi cikin wata tattausar murya mai laushi cike da ginshira. Duf! Kamar daukewar ruwan sama haka naji na nemi ciwon nan na rasa, cike da tsananin mamaki na waro ido ina kara kallonshi cikin tantama, shine ko ba shine ba......?????????!
*Happy Birthday To U my dearest ANTI ZEE....*
©Jeedderh🐾
[5/2, 10:51 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•17•°🐾
I couldn't really believe what I saw! Marwanuddeen ne tsaye a gabana, ya hade cikin jeans da T-shirt din formies, takalminshi baki sau ciki shima dai na formies din ne, sai jar hula pick up ruwan shirt dinshi wadda nake zaton saboda badda kama ya saka ta saboda shi kadai ne yake jan motar ba tare da security ba. Bai yi wata-wata ba ya kamani na tashi zaune, ya saka ni cikin motar yana jero min sannu har ya zagaya daya gefen yaja motar. Tuki yake a hankali kuma a nutse cikin kwarewa ba tare daya nuna tsarguwa ko damuwa da kallon kurilla da nake jifanshi dashi. Tafiya mai dan nisa muka yi yaja tunga a bakin wani karamin clinic. Ya fito daga motar bayan ya maka bakin gilashi a fuskarsa, zuwa lokacin kafata ta saki don haka da kafafuna na taka har cikin clinic din, aka min dressing a hannu don anan kawai naji ciwon. Likitan yaso in zauna in samu hutu ko da na awa daya ne amma fir naki amincewa nace mishi ina da jarawabawa yau n I can't lose it, sai ya bani magunguna. Muka tafi yana jaddada min lallai in samu wani abu inci saboda ulcer ta tana gab da tashi.
Cikin motar muka koma ya tashe ta muka bar asibitin, a motar nayi luf akan kujera cike da tunanika barkatai a raina har zuwa lokacin bayan sannu babu maganar data kara hada mu dashi. A bakin wani shago da aka rubuta Ice Land yayi parking ya fita ya shiga wajen, bai jima ba ya dawo hannunshi rike da leda mai dauke da tambarin wajen, ya shigo motar ya miko min ledar. Ba musu na amsa ina godiya, biscuit ne da meat pie da fresh milk. Yawuna ya tsinke sosai, tsohuwar yunwa ta ta taso, na mike kafa na fara turawa cikina meat pie da biscuit ba kakkautawa ina yi ina korawa da fresh milk din nan, sai dana musu tass, nayi gyatsa na godewa Allah. Sai lokacin da hankali na ya dawo jikina na lura da irin kallon da yake jifa na cike da mamakin yadda na cinye abubuwan, murmushi na danyi cikin jin kunyar shi na kauda kaina gefe.
Sai da muka hau kan babban titi ya dan kalle ni, cikin turanci ya tambaye ni a wace makaranta nake? Nima cikin turancin na mayar mishi da 'Empirical College of Arts'. Ya kada kan motar shi zuwa titin makarantar, har kofar gate din makarantar mu ya ajiye ni, na mishi godiya sosai na fita daga cikin motar.
Cikin faduwar gaba na dumfari gate bakina dauke da addu'ar Allah yasa Computer dake dauke da sunayen wadanda basu biya school fees ba a kashe take. Sai dai cikin rashin sa'a ina gama shigar da sunana cikin computer matsayin attendance taki shigar da sunan nawa, securities suka hana ni shiga. Har kasa na durkusa ina rokon su taimake ni su Barbi in shiga in zana jarabawa, jibi kawuna zai dawo daga tafiyar da yayi yazo ya biya min amma fir suka ki sai ma kora ta da suka shiga yi. Idanuna suka yi luhu-luhu cike da tashin hankali, idan na rasa jarabawar nan nasan nayi asarar wannan shekarar kenan dole sai na maimaita wata.
Ji nayi wasu tausasan hannuwa sun dafa ni, nayi hanzarin dagowa na kalli wanda ya dafa ni. Mamaki ya kama ni ganin ashe har yanzu bai tafi ba, ya tashe ni tsaye ya tambaye ni meke faruwa? Cikin harshen turanci. Na sadda kaina kasa ina cizon lebba na na kasa na kasa magana, ina jin nauyin fada masa, sai kuma naga cewa shine last hope dina a yanzu dai, idan na bari ta tafi zan cuci kaina ne kawai, zan rasa jarabawa na har abada! Ban san lokacin dana bude baki na fada mishi cikon kudin makarantana na wannan term din ne ban gama biya ba, gashi Uncle dina da zai biya min kudin baya nan yana Australia kuma na rasa contact dinshi ban san ya zanyi ba.... Na gama fada ina matse kwallar ido na. Ya matsa ga securities ya tambaye su nawa ne kudin? Suka latsa computer take ta nuno musu adadin kudin da ake bina, rupee dari biyu da hamsin kimanin Naira Dubu Saba'in da biyar. Ya zaro master card daga cikin wallet dinsa ya mika musu, suka zira shi cikin wata na'ura suka yi en danne-danne a jiki nan ya zari abinda zai zara ya fito da wata takarda tare da card din, suka mika mishi ya rike card din ya miko min takardar.
Na rasa irin godiyar da zanyi wa bawan Allahn nan, sai kawai na zube a kasa bisa gwiwoyina ina hawaye, shima ya fahimci na kasa yi mishi godiya ne. Sai yayi murmushi wanda yasa kuncinsa na dama ya lotsa sosai, naji wata irin faduwar gaba ta ziyarce ni saboda wani irin kyawu da naga ya kara yi a idanu na, ya dafa kaina yace kar ki damu, je ki kiyi jarabawar ki Allah ya baku sa'ah! Ya wuce ya shige motar shi yaja yayi gaba, sai dana hangen motar sannan na tashi na karkade jikina na shiga makaranta.
Kai tsaye library na wuce, a can na samu Hanan tana karatu. Nima na samu waje na zauna na fara kararun kafin lokacin shiga jarabawar yayi.
Gidansu Hanan muka wuce daga makaranta, nayi wanka nayi sallah naci abinci ta bani kayanta na saka. Muna falonsu ni ina kwance akan kujera take tambayana abinda ya same ni a hannu na, na bata labarin duk abinda ya faru sai dai ban fada mata Marwan ne ya biya kudin ba, ta tausaya min sosai. Tace waye wanda ya taimaka miki? Ban san lokacin da wani murmushi ya subuce min ba, na lumshe idanuna, a hankali kamanninsa da duk wasu wasu moves nashi ayau suka shiga dawo min a cikin idanuna, na bude idanuna fess cikin na Hanan na sakar mata wani kayataccen murmushin, cikin wata irin soft murya mai cike da wasu irin feelings nace mata "Wani neh.....!!!!"
©Jeedderh🐾
[5/2, 10:50 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•18•°🐾
Ban koma gida ba sai da Magriba, nannyn su Asleem kawai na tarar a gidan, Chandni sunanta tana zuwa da safe tayi rainon su Asleem da hidimomin su zuwa dare sai ta tafi. Na dauki yaran na dan musu wasa sannan na wuce daki na.
Sai dana kammala komi nayi shirin kwanciya barci sannan na haye gado na. Na janyo waya ta na bude e-mail dina na turawa Marwan sakon jinjina da godiyar irin taimakon da yayi min yau. Ba a dauki wani dogon lokaci ba sai ga amsar shi yana tambaya na cike da mamaki, wai ashe nice yarinyar dazu? Yace no wonder! Ashe dalilin da yasa ya dinga ji a jikinsa kamar ya sanni kenan? Haka kawai yaji ina bashi dariya musamman idan ya tuno da yadda na dinga cin abinci hannu baka hannu kwarya dazun. Na dinga dariya kuwa ni kadai a daki. A wannan ranar na kara mishi wani matsayi a zuciyata. Muna hira dashi barci ya dauke ni cike da wani irin nishadi da rabon inji kamarsa har na manta.
Washegari ina tashi da safe na fada toilet nayi wanka, ina cikin shafa na janyo wayata na bude. Kai tsaye sashen sada zumuntar Marwan na face book na shiga, wani post daya yi a jiya da dare misalin karfe sha daya na daren ne ya dauki hankali na., cikin yaren Hindi yayi posting din 'Today for the very first time in my life, I met an amazing woman. Usually I don't like seeing females eating roughly in front of me, but wen I saw ha eating like that, I wanted to just........! 😘😎' bai karasa ba ya dora alamun emoticons. Aikuwa comments sun fi dubu ashirin kowa na tambayar shi wace ce yarinyar nan?? Naji ni wani sakayau, feeling very empty kamar bani ba, kar dai dani yake?? Naso in tambaye shi nima inji ko dani din yake, sai dai tsoron kada yace ba dani yake ba yasa na basar da zancen duk da cewa abin yana cikin raina.
✿✿ *♡LOVE♡*✿✿
Mun samu hutu na tsayin sati biyar, duk da cewa wannan karon position dina na 8 ne sabanin na hudu ko na uku, amma nayi murna da na wuce zuwa aji na gaba. Da kyar na samu na shawo kan Uncle ya yarda ya barni inje Najeriya inyi musu hutun sati biyu, nan na hau shirin komawata gida Najeriya ba tare da na sanarwa da kowa kudiri na ba saboda gudun kada a sagar min da gwiwa.
Ranar asabar lokacin saura kwana biyar in tafi gida, uncle yazo mana weekend. Ya kwashe mu duka gidan muka je wani babban amusement park har da Hanan. Mun zagaya wajen sosai mun sha wasanninmu da daukar hotuna, muka yi sayen kayan makulashe masu yawa. Mun jima sosai a wajen kafin muka yi haramar komawa gida. A bakin gate aka tsayar damu ana checking bayan booth din masu shiga da fita don tabbatar da tsaro, ana cikin duba na gabanmu kafin azo kanmu, na juya ina kallon motocin dake kokarin shigowa. Daidai ana sauke bakaken gilasan bayan wata hadaddiyar bakar matrix, nayi ido hudu da kyakkyawan matashi Marwan. Wani tattausan murmushi ne shimfide akan kyawawan kumatunsa, bakin shi ya motsa da kalmar, "aap kaise hain??" (how are u doing?), nima murmushin na saki sosai cike da farin cikin ganinsa, ban san me ya kawo sa wajen ba amma nafi kyautata zaton ko harkar fina-finan shi ce ta kawo shi. Na motsa lebbana nima a hankali na mayar masa da amsa, "mein theek ho! Aur aap??" (am fine.... And you??) ya sake murmusawa yace mein too! (me too!). Ya min alamun bye, direban dake tuka shi yaja mota suka tafi har lokacin da murmushi a saman fuskar shi.
Na bi motar da kallo nima ina murmushi cikin wani yanayi har suka bace min. Uncle ya ja mota muka fita muma. A hankali na saukar da ajiyar zuciya tare da kwantar da kaina akan kujera ina tunano Marwan, ban san me yasa ba, a barci nake ne ko a farke, aiki nake ko karatu, a kwance nake ko a zaune, tunanin mutumin nan shi kadai ransa yana like dani kamar wani magnet. Ya mamaye kaso mai girma a duniyar tunanina, ko ina na juya shi kadai ke min yawo a fuska na wanda ni a karan kaina bansan dalilin da yasa hakan ke faruwa dani ba!.
[Mamielow., na ga sakon ki akan littafin Bayan Rai. Nima nagode sosai da irin yabon ki da kuma shawarwarinki,nima kuma Ina kaunar ki dama Masoyan littafin Bayan Rai baki daya......!]
©Jeedderh🐾
[5/2, 10:51 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•19•°🐾
Ranar Alhamis jirgi ya daga dani, mun jima da Uncle akan waya a filin jirgin kafin mu tashi kamar ba zamu rabu ba, yace min shima next week zai dawo gida gabadaya, ni kam ina tunanin hirar karshe ce muke yi dashi a garin India don na gamawa kudurcewa a raina cewa na bar gidan Uncle har abada.
A Najeriya na tadda cincirindon en uwana sun zo tarba na a filin jirgi, na rasa ina zan sa kaina? Yau gani a gaban Ammie na da Ya Faruq da en uwana masu so na. Nan dai muka rankaya gida, a can ma wata tarbar na tarar ta abinci iri-iri. Musamman Ammie ta shiga kicin da kanta ta shirya min kaloli na nau'in abincin da nake so. Daren ranar bamu runtsa ba, muna dakin Ammie muna shan hira har dare ya tsala, sauran yayyena suka tafi suka barmu da Ya Faruq da Ammien. Muna jan ta da hira muna ta kwasar dariya, akwai fahimtar juna tsakanin mu da mahaifiyarmu, tana jan mu a jikinta sosai shi yasa bama jin nauyin bayyana mata duk damuwar mu. Sometimes idan ka ga yadda muke hira da ita muna tsokanarta sai kayi tsammanin cewa kakarmu ce. Shima Ya Faruq daya gaji da hirar nan ya barni ya mana sallama ya tafi dakinshi. Ni kam ranar a gefen Ammie na na kwana.
Sati na biyu cif a Gombe, nayi kiba abi na nayi fresh dani saboda bana tare da wata damuwa. Uncle ya bugo waya in koma, na kuwa ce babu inda zan koma ni na dawo gida, aka kuma yi yin duniya naki fadar abinda su Uncle din suka min, kawai dai nace ni yanzu nafi son zama cikin en uwana ne. Ammie tace bani da hujja kenan, Ina kuka riris haka suka raka ni filin jirgi muka rabu cike da kewar juna.
Kai tsaye Abuja jirgin ya wuce damu, ya ajiye fasinjoji ya dauki wasu, ni dai ina zaune cikin tafasar zuciya cike da takaicin komawa ta gidan Uncle, na baro inda ake so na ana nan-nan dani zan komawa lonely and scattered life dana fara mantawa da ita. Na dauki jaridar Vanguard ina dubawa kafin jirgi ya gama lodi a tashi, ni kam ji nake dama ace jirgin ba zai tashi na, da nafi kowa murna da farinciki.
Mutane suka gama shigowa jirgi ya fara haramar tashi, cikin siririyar murya naji anyi sallama a gefena an zauna a kujerar kusa dani, na amsa ina waiwayo wa. Kamar hadin baki shima ya waigo, sai kuwa muka hada ido. Cikin mamaki na zaro idanuna ina kara kallonshi, shima ya zare sun glass din idanunshi cike da mamaki. Mamakina daya me ya kawo Marwan Nigeria? Ko dai yana da alaka da nan ne? A lokaci guda muka furta "how comes??" ni dashi, muka saurara muna sauraron jin amsa daga bakin dayan mu, muka kara cewa "what brought you here??" a lokaci daya again. Kawai sai muka kyalkyale da dariya, muka yi tayi har dan tari ya sarke ni, ya fara dan bubbuga min bayana a hankali har na samu na nutsu. Ya dube ni a tausashe yace "go ahead and ask me..." na gyara zamana na kalle shi nace "me ya kawo ka Najeriya? Kana da alaka da nan ne ko kuma kazo yin wani abu ne?" yayi wata tattausar dariya da tasa gefen kumatunshi na dama da cleft dinshi suka lotsa, yace "mahaifina haifaffen garin Kano ne, iyaye, kakanni, yayye, da kannenshi duk suna nan Kano" na gyada kaina cikin mamaki, "ban taba sanin hakan ba, asali ma ni ban taba tsammanin hakan ba don ko kama baka yi mun da dan 9ja" ya sake wani murmushin, "ba lallai kowa ya tsammani hakan ba don a India na taso nayi karatu da komai nawa, sai dana girma ne sosai na fara zuwa wajen dangin mahaifina..... Amma ke dama kina da dangi ne a 9ja ko wani abu kika zo yi ??". Nace ni anan aka haife ni, kawai dai ina zaune ne wajen Uncle dina dake aiki a can Mumbai din. Ya gyada kai, "Kema ai ba kya kama da en Nigeria, wallahi kin fi mun kama da irin larabawan nan half cast na Libya da Moscow!" na kama baki ina jijjiga kai cikin dariya nace ni din?? Yace da gaske pa!! Na jingina da kujera ina kallonshi ina cigaba da dariya.....
Muka cigaba da hirarmu a nutse, musamman daya fara kwabo min hausarshi kamar ta en koyo wai shi a dole ya iya hausa, ni kam me zanyi ba dariya ba? Nan nayi ta kyakyatawa kamar bani da wata damuwa a raina. Har jirgi yayi landing a Mrs. Jick airport dake birnin Mumbai din, muka fito muna cigaba da hirarmu. Da Uncle na fara tozali, sai Anti dauke da Asleem Hanan kuma na rike da Tasleem. Tuni na manta da wanda ke gefe na wanda shima escort dinshi da dangi suka lullube shi amma hankalinshi na kaina. Da er sassarfa ta na karasa wajen su Anti, madadin in rungume Uncle kamar ko yaushe, sai na kai gwiwoyina har kasa na gaida shi ya dafa kaina yana murmushi ya amsa, na juya ga Anti na gaishe ta, ba laifi ta amsa da dan alamun afuwa a fuskarta. Nan na rungume Hanan, na amshi en biyu ina ta murnar ganinsu, daga nan muka fada mota Uncle yaja mu sai gida.
Ban tashi tunawa da Marwan ba sai da ina duba mails dina naga sakon shi, cikin hausar da bai kware ba wai "kun keuta! She ne kika tafi ba sai anjime ko?? 😠?" nan kuwa na kwashe da dariya sosai kafin na mayar mishi da amsar ban hakuri. A hankali a hankali rayuwa tana tafiya, wani matsananciyar shakuwa ta ginu tsakani na da Marwan, ta kai matakin da idan daya bai ji muryar daya ba a wuni to babu kwanciyar hankali. Yanayin zaman mu da Anti ya dan sauya, yanzun muna zama mu ci abinci tare, ina gaishe ta ta amsa faram-faram, ni dai nafi kyautata zaton ko don taga Uncle ya dawo gida ne yasa ta canza hali. A haka muka zana jarabawar fita daga makaranta muka zauna zaman jiran sakamako.
A daren ranar muna falo mu duka cikin outfit na party, Uncle ya hada min er kwarya-kwaryar liyafa na taya ni murnar gama jarabawa lafiya. Aka kada door bell, na tashi da sauri na naje na bude. Wanda na gani ne a tsaye rike da bouquet yasa na zaro idanu na cike da mamaki. Ya kanne min ido daya, "Hii there.... Kina mamakin gani na ne? Ko ba ayi maraba dani ba in koma??" na sadda kaina kasa jikina a sanyaye, duk bidirin da muke ni da Marwan ko da wasa babu wanda yasan abinda ke tsakaninmu dashi. Muryar Uncle na jiyo yana kwala min kira, na kauce na bashi hanya ya shigo falon na maida kofar na rufe. Tare muka jera dashi muka koma falon ina ta sunke-sunken kai. Uncle ya taso da saurin shi ya ba Marwan hannu suka gaisa tare da nuna mishi wajen zama, na koma gefen Uncle na zauna kaina a kasa. Ina jin Marwan ya gabatar da kanshi wajen su Uncle, ni kam na kasa ko kwakkwaran motsi. Uncle ya sadda kanshi saitin kunnena yana min rada, "en matan Uncle yaushe aka yi saurayi Uncle bai sani ba??" na dukunkune fuskata a jikinshi, cikin shagwaba nace ni pa ba saurayi na bane! Yace da gaske?? To waye shi?? Na kasa magana sai turo baki, dariya yayi muka cigaba da gudanar da liyafar mu. Sai wajen karfe goma Marwan yayi haramar tafiya, Ni da Uncle muka raka shi har inda yayi parking motarshi, suka yi musabiha da Uncle ya juya ya tafi ya barni dashi a tsaye.
Ya maido da dubanshi gareni yana dan murmushi, "Ni pa da niyya biyu nazo gidan nan!" nace "niyya biyu? Ta me kenan??" ya daga kafadarshi, "well! Na farko in taya ki murna, na biyu kuma inyi confessing soyayya tah......!!".
©Jeedderh🐾
[5/2, 10:51 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•20•°🐾
Na hangame baki idanuwa kamar zasu fado kasa har da kara karkade kunne wai ko banji daidai bane, "Ehhh?????!!" ya sake daga kafada, "it's not as if baki ji me nace ba.... Cewa nayi Ina Son Ki! Wat about u? Do u love me...???!" Wayyooo kasa tsage in shige mana! Na rufe fuskata da hannuwa ina wani irin murmushi, ina jin sautin murmushin daya saki. "I take that as yes! Je ki kwanta, sai da safe kinji??" ban iya motsi ba har ya shige motar shi yaja ya tafi. Na jima sosai a wajen nan a tsaye, da kyar na samu na iya komawa cikin gida. Anti da Uncle suna falo suna hirar su, suka bini da kallo har na shige daki. Naji dadi sosai da basu min magana ba don bani da kuzarin amsa musu. Ina shiga dakin nayi tsalle na dire kasa, "yesss!! I got him!!!" nayi tsalle na fada kan gado na dinga birgima ina shilla kafa sama, murna kamar inyi me? Na rungume filo kam-kam ina jin yadda zuciya ta ke racing. Ranar da kyar barci ya dauke ni.
Daga nan sai me?? Soyayyah mai karfi ta shiga tsakaninmu da Marwan, muka fara yin ta gadan-gadan. Gidanmu babu wanda bai san da zaman Marwan ba, haka idan yazo har cikin falo zai shiga su gaisa da Uncle da Anti. A dalilin haka zaman mu da Anti ya dawo normal, duk da haka ban gama sakin jiki da ita ba. Sai dai labarin soyayyar tamu bai shiga duniya ba saboda mutane.
Makarantar mu suka samu matsala wajen fitar da sakamako, don haka ne suka bada sanarwar mu yi hakuri sakamakon jarabawar mu ba zai fita yanzu ba sai nan da watanni takwas. Dalibai suka shiga zanga-zanga suna cewa basu yarda ba, sai dai babu wani cigaba dole dai suka hakura. Ganin zamana a gida baya min dadi, Uncle ya nemi shawarata akan zai samar min Diploma school ko ta koyon girki ko computer ko kuma koyon sana'o'in hannu, tunda su diplomar su wata bakwai ne, nace ya cike duk wadda yaga tayi mishi.
Bayan kwana biyu da yin haka Marwan yazo gidan mu, mun jima dashi a farfajiyar gidan inda muka saba hira dashi har dare yayi ya tashi zai tafi, anan ne ya miko min wata takarda, na amsa na duba. Police training centre naga an saka a sama har ya cike min, naji mamaki, me zai yi hadi na da police ni kam? Yace it's just 9 months pa! Nasan zuwa lokacin sakamakon jarabawar ku ya fito. Wallahi ina sha'awar ganin mace na aikin en sanda, I know it'll suit you. Ban ce kiyi aikin dan sanda ba fa! Kawai kiyi training din ko yaya ne, kuma ma kinga zaki koyi yadda zaki dinga kare kanki idan bukatar hakan ta taso". Nace to zan nunawa Uncle, yadda yace zan fada maka. Daga nan muka yi sallama dashi ya tafi.
Uncle kam cewa yayi hakan ma yana da kyau, inje kawai. Nan na fara zuwa training din, amma fa ba karamar wahala muke sha ba a wajen amma haka na jajirce ko don in farantawa Marwan rai. Muna cikin wata na takwas jarabawar mu ta fito, sakamakon mu kuma yayi kyau sosai. Uncle da Marwan suka fara fafutukar nema min gurbin karatu a jami'a. Lokacin training dinmu ya dauki zafi sosai saura wata daya mu gama.
Muka gama training dinmu na fito da 3rd class position saboda na nuna kwazo sosai.
Ranar da za a yaye mu har Yaya Faruq sai da yazo wajen taron, ni ce kira ta uku cikin jerin sunayen mutanen da za a ba Kyauta. Na tafi cikin fareti da kayan junior police a jikina har na isa gaban shugaban makarantar, Marwan ya bini da flashes har kan step. Ban suka rataya min sarkar ban girma ta uku mai dauke da sisin gwal. Haka aka cigaba da gudanar da taron yaye mu cikin tsari inda daga karshe muka rufe taron da fareti kowa ya watse. Ranar kam bakin Marwan yaki rufuwa sai fara'ah yake tayi, a cewar shi bai taba ganin wanda kakin dan sanda yayi wa kyau ba kamar ni. Nima farin cikin ne ya lullube ni, domin buri na kenan, fatana ne hakan in dinga ganin shi cikin farin ciki.
©Jeedderh🐾
[5/2, 10:52 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•21•°🐾
Ba ayi sati biyu ba admission dina ya fita a babbar university ta Kelvin University of Arts, sun bani painting and drawing kamar yadda nayi applying. Na fara shirye-shiryen fara zuwa karatu, Hanan sun koma New Delhi ita da iyayenta acan zata cigaba da karatunta.
Kwatsam sai ga Kawu Hamza ya diro Mumbai, muka tarye shi cikin murna sosai musamman ni dana jima ban ganshi ba. Bayan ya huta mun gyara mishi mazaunin da zai kwanta, aka kai mishi abinci yaci. Ya tara mu mu duka a falo ya sanar damu dalilin zuwanshi takanas babu sanarwa. Yace bai yarda in tafi jami'a ba har sai ya aurar dani, domin haka mahaifinmu yake yi tun kafin rasuwar shi. Duka yayyena mata suna gama sakandare yake aurar dasu, wadda mijinta ya yarda ta cigaba da karatun a gidanta sai taci gaba, wadda kuma bai yarda ba shikenan. Anti Rukky har an saka nata ranar auren, watannin baya mijinta yayi hadari ya rasu, shi yasa Kawu ya kyaleta ta tafi KL kafin Allah ya kawo mata miji.
Uncle yayi iyakar kokarinshi yayi wa Kawu bayani yadda zai fahimta, cewa nayi kankanta da aure yanzu, ya daure ya bari koda nan da shekaru biyu ne sai ayi amma Kawu ya kekashe kasa yace ba dashi za ayi wannan abun ba, ga yadda al'adar gidanmu take shi kam ba zai ruguza ta ba saboda wani dalilin Uncle maras kai da kafafu. Cewa ma yayi idan bani da mijin aure a hannu yanzu to ya riga da ya min a Najeriya, zai turo shi mu gana. Ganin cewa Kawu ya dage ne da gaske yasa Uncle ya kira Marwan a waya ya mishi bayanin halin da ake ciki, duk da cewa baya gari amma haka ya ture duk abubuwan dake gabanshi ya dira a Mumbai washegari. Suka tattauna da Kawu sosai ya mishi bayanin komi da dalilinsa na yin hakan, yace to a bashi zuwa nan da jibi zai je yaji ta bakin mahaifiyar shi. Kawu yace babu damuwa, zai zauna zuwa jibin, idan ya dawo sai ya koma. Ko hirar kirki bamu yi ba dashi ya kada kai ya tafi Shimla inda anan ne mahaifiyarsa take zaune.
Bamu hadu a waya ba sai da dare, ya kira ni lokacin ma har na kwanta. Na daga kiran da sansanyar murnata, ya amsa a kasalance, muryar shi na bayyana halin damuwar da yake ciki. Gabana ya fadi, abu na farko daya fado min a rai shine cewa mahaifiyar shi baya yi na'am da zancen auren mu ba kila. Cikin sauri da sarkewar murya na tambaye shi lafiya? Yace babu komi Meenah, mura ce ke damu na. Ban yarda da hakan ba, amma sai na kyale shi kawai. Muka fara hira yana tambaya na game da makaranta da yake last week na fara attending classes, ni kuma Ina bashi labaran ban dariya. Nan da nan ya wartsake yana ta kyakyatawa, naji sanyi sosai a raina. Dare ya tsala sosai lokacin da ya min sallama yace zai kwanta, nayi kan-kan da muryata tayi kasa sosai na kira shi da sunan da yake tsananin faranta mishi rai idan yaji na fade shi.., nace "Mera Dil Khushi.... (Farin cikin zuciyata!)" ya dan ajiye numfashi tare da yin murmushin jin dadin da sunan ya mishi yace menene Meenah darling?? Na kara sanyaya muryata yadda zai jita har cikin ransa nace "meke damun ka ne? Ka taimake ni ka fada min damuwar ka ko na samu nayi barci mai dadi, kasan cewa raina ba zai taba mun dadi ba matukar kana cikin damuwa..." yayi shiru na dan lokaci kafin yayi faking wata dariya wadda kana jinta ma kasan cewa kakalo ta yayi don dole kawai don ya kwantar min da hankali, yace m fine fa darling, me kika gani ne har ya saka ki zargi cewa ina cikin damuwa? Na girgiza kaina, haba dai! Kaima kasan cewa ba haka na saba jin muryar ka ba, duk da cewa bana ganinka amma nasan cewa kana cikin damuwa. Plssss ka fada min mana ko na samu sanyi a cikin raina, kaji?? Yayi shiru na dan lokaci har sai dana sake cewa huhhh??? Dan Allah!!
Ya ja ajiyar zuciya mai nauyi kafin yace "Meenah ina tsoron hukuncin da Mahaifiyata zata yanke min akan aurenmu dake ne, wallahi jikina ya bani ba zata amince min nayi auren nan ba!!" a sanyaye kuma cikin matsanancin faduwar gaba nace Me yasa kace haka?? Ya sake jan wata ajiyar zuciyar, yace "saboda..... Ermmm.... Saboda ex wife dina!!!" na zabura na tashi zaune dangargar daga kwanciyar da nayi a sukwane, nace "what!??? Ur ex-wife????!!"
©Jeedderh🐾
[5/2, 10:52 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•22•°🐾
A sanyaye yace "kiyi hakuri, ban sanar dake akan lokaci ba. Sunanta Hindu, diyar kawar Mamanmu ce ta kut da kut, Maah ta hada mu auren zumunci da ita bayan na kammala degree na wai da niyar kara dankon zumunci a tsakaninsu. A New Delhi muka zauna da ita lokacin ina karamin star ne a harkar fina-finai na ban yi waya shaharar azo a gani ba. A iya tsawon zaman da muka yi da ita na shekaru biyu na fahimce ta a wata irin mace mara tarbiya, wadda bata san darajar mijinta da auren da yake kanta ba. Wallahi tunda na aure ta jin dadi da natsuwa suka yi kaura daga cikin rayuwa ta, na nemi walwala da kuzari na na rasa. Magana ta gaskiya na auri Hindu ne don yiwa mahaifiyata biyayya ba wai don ina sonta ba, ta fannin Hindu ne dai nasan cewa I was her crush since college, ban san zuwa lokacin ko tana sona ba still. Hindu macece mara son zama lafiya da dan banzan korafi, dan kankanin laifi zan mata sai ta kai kara ta wajen mahaifiyata, sai tafi sati tana nanata magana guda babu gajiyawa. Akwai wani kamfanin mahaifinmu da muka ci gadonsa ni da kani na Kabeer yana nan Mumbai, da na fara shirye-shiryen dawo dashi New Delhi ne, amma saboda Hindu yasa na canza shawara kan zan barshi a Mumbai kawai. Hankalina sai ya koma kan tado da kamfanin da da a rufe yake, sai harkokin film dina da zamana a gida duk suka ja baya. Ina so ne in yi saurin tayar da kamfanin yadda idan Kabeer ya dawo daga makaranta yana karantar business administration zai cigaba da kula da kamfanin, ni kuma in cigaba da gudanar da harkokin film dina a nutse.
Sau biyu ina kama Hindu tana zubar min da ciki, raina ya baci sosai da abinda take yi, na mata kashedi na karshe akan cewa kada ta kara zubar min da gudan jini na. Sai dai bata dauki gargadina a wani abu ba, ba a kwashe watanni biyar cikakku ba sai gata a gadon asibiti ta zubar da wani cikin. Raina yayi mummunan baci har na rasa abinda zan ce mata, da naje asibitin da aka kwantar da ita tana kwance ta wartsake daga azabar da tasha, idanunta fess babu alamun komi ta kalloni wai tana tambaya ta ya aka yi nasan cewa tana nan? Kawai ce mata nayi daga nan ta wuce gidan su, zan neme ta idan na yanke shawarar yadda zanyi da ita.
A ranar ban kwana a New Delhi ba na wuce Goa zanyi shooting film dina da zai fita, washegari tun da safe kiran mahaifiyata ya riske ni, tace lallai tana son gani na in ajiye komi nake inje. Haka na tafi Shimla bayan na dauki duk wasu takardu shaidar zubar min da ciki da Hindu tayi. A can na sameta a gidan mahaifiyata fuskarta tayi jawur da shacin hannu wai ni na mare ta. Maah tayi ta fada kamar zata dukeni, sai dana bari ta gama fadace-fadacen ta sannan na zube mata takardun na kuma yi mata bayanin halin da muke ciki ni da Hindu, duk da cewa ban fadi wasu abubuwan bama amma ran Maah sai daya baci sosai. Nan ta shiga yi mata fada kan cewa abubuwan da take yi bata kyautawa, menene abun zubar da ciki kuma?? Wallahi budar bakin yarinyar nan sai cewa tayi, ita bata shirya haihuwa dani yanzu ba, idan ita Maah din ta damu da in samu dan cikina mai zai hana ita ta haihu dani?? (Wa'iyazubillah!!). Ai a take na tashi na watsa mata yatsu na biyar a kuncinta har sau hudu, na kuma furta mata kalmar saki biyu. Nan ta fita tana masifa ta bar Maah na kuka da sallallami. Da kyar na samu na shawo kanta ta daina damuwa, sai dana ga ta dawo cikin natsuwarta sannan na mata sallama na koma wajen aikina.
Yanzu shekarunmu biyu da rabuwa da Hindu, ban san ya aka yi suka shawo kan Maah ba ita da mahaifiyarta, ni dai naga sun shirya har ta fara matsa min da maganar in dawo da Hindu. Yanzu dai a inda muke da ita kenan, to kuma bansan ya zamu kare da ita akan zancen aurenmu dake ba."
Na saki ajiyar zuciya yayin da wata zufa ta lullube ni. Nayi shiru da tunanika barkatai a raina har na rasa da wanne zanyi dealing. Ranar dai haka muka yi sallama dashi ran kowa a jagule, jiki a sanyaye babu kwari balle mu samu tausar junanmu.
©Jeedderh🐾
[5/2, 10:52 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•23•°🐾
Washegari tun safe har dare babu labarin Marwan, nayi duk iya kokari na to reached him even at phone amma ban samu damar yin hakan ba. Jikina yayi sanyi sosai, na kasa hadiya ko ruwa a cikina, jikina ya gama bani cewa mahaifiyar Marwan bata yarda da auren mu ba, idan hakan ne kenan Marwan zai kyale ni? Idan ya kyale ni ya zanyi da rayuwata?? Kawai ji na nayi na kece da kuka mai karfi, na dukunkune akan gado nayi tayi ba kakkautawa. Anti ce ta shigo ta same ni a wannan halin, cikin sauri tazo ta tashe ni daga kwanciyar da nayi hankali a tashe tana tambayata me ya faru?? Duk yadda naso in boye mata maganar kasawa nayi, at least yakamata ace wani yaji ko don a bani shawara. Na bayyana mata komi babu abinda na boye mata, na kula itama nata jikin yayi sanyi sai dai ta boye min. Ta rungume ni tana dan dukan bayana cikin alamun rarrashi tace min kada in damu, in Allah ya nufa Marwan mijina ne to babu makawa dole sai na zama matarshi no matter what. Zuciyata ta danyi sanyi, sai dai duk yadda taso akan in samu in dan ci wani abu kasawa nayi, da kyar ta samu ta dura min robar yoghurt. Ranar dai haka raina ya kwana a jagule.
Washegari wajen karfe tara na safe sai ga Marwan a gidanmu, wayyoo dadi! Kasa jira a fada min abinda ke faruwa nayi, na tafi bakin kofar dakin Kawu ina labe. Marwan ya ba kawu hakuri akan rashin dawowa jiya da bai yi ba yace bai iso garin da wuri bane sai wajen karfe sha biyun dare, ya kuma kara da cewa mahaifiyar shi ta amince da zancen aurenmu, Yayan mahaifinsa dake Kano zasu je neman aure na a wajensu Kawu idan ya koma gida. Kawu Hamza yayi hamdala ga Allah kafin ya saka mana albarka, a ranar ya juya gida. Murna a waje na kamar inyi me! Na ruga daki na da gudu nayi sujjada ta godiya ga Allah. Anti ta shigo da fara'ar ta zata bani labari, ganin halin da nake ciki yasa ta gane cewa labari yazo min tuni don haka ta juya. Wayata na janyo na kira Marwan ina bayyana masa farincikin da nake ciki, "akwai pa matsala Meenah!!" cewar shi a sanyaye. Gabana ya dan fadi, murnar da nake ciki tayi kasa, nace matsalar me kuma? Ya nisa, yace Maah ta amince da aurenmu ne akan sharadin zan maida Hindu dakinta, ni kuma na amsa mata da zan maida ta ba tare da na nemi shawarar ki ba. Duk da dukan da zuciyata tayi bai sa na kasa kakalo murmushin dole ba, "to sai me don zaka mayar da tsohuwar matarka? Ni in dai akan wannan ne kake damuwa to ka daina, na amince dari bisa dari akan ka maida ta" yace da gaske kike? Sai na saki murmushi very soft, nace "anything for ur happiness dear...!!" sai yayi dariya, yace nagode my angel, Allah ya kawo ranar aurenmu. Nace Ameen.
*******
Sati uku kacal aka saka a matsayin ranar biki, ni kam kafin lokacin na cigaba da zuwa makaranta abi na. Saura sati biyu a fara bikin muka tafi Nigeria don mu uku za ayi wa bikin, akwai Jamila diyar Kawu Jazuli sai Lawisa diyar Kawu Hamza, don haka shirye-shirye ake yi bana wasa ba. Duk da hakan na fita ta daban a cikin amaren, domin tun a India Anti take ta faman gyaran jikina, gashi mun dawo nan Ammie ma ta dora da nata. Nayi wani irin fresh na ban mamaki yadda kasan cewa an canza min kamanni ne, ga wani popularity da nayi cikin dangina da abokaina, ko ina nayi sai dai kaga ana nuna ni, ala dole zan auri celebrity. Ana saura sati daya daurin aure yayyena mata suka fara dira, su kam irin nasu shirin ba a yin magana. A cewarsu bikin Auta Ameenah ne da Marwan, dole ne duniya tasan cewa ni pa er gata ce.
Ban san ta yaya zan bayyana tsaruwar bikin mu ba, illa iyaka ince ban taba ganin bikin daya burge ni irin bikin mu ba. Garin Gombe ya kwashi baki kala-kala da celebrities dangin mawaka ne da en wasan kwaikwayo iri-iri musamman daga India, bikin da mutane da dama suka ce basu taba ganin taron da yayi jama'a irin bikin mu ba. A daren ranar aka mika ko wace amarya gidanta, nima a daren ranar jirginmu ya daga zuwa India. Fadin irin kukan da nayi a lokacin ma bata baki ne, duk da cewa ba yau na saba barin su Ammie na ba, amma sai naji kamar idan na tafi shikenan, a haka dai muka rabu da en uwana ina kuka suna taya ni.
(Sauka lafiya Amaryah Meenah-Auta!)
©Jeedderh🐾
[5/2, 10:53 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•24•°🐾
Garin Shimla muka sauka, gida guda aka ware mana ni da en rakiya ta. Mun samu tarba ta mutunci da karramawa daga hannun en uwan Marwan, muka yi wanka muka biya bashin sallah data same mu cikin jirgi muka ci abinci, daga nan muka kwanta sai barci. Wayan da Marwan ya bugo min ce ta tashe ni daga barcin da nake, na daga wayar cikin magagin barci muka gaisa ya min barka da zuwa don ba dashi aka je taro mu ba. Muna ta hirarmu yace da dare zai turo azo a tafi dani wajen dinner da abokanshi suka shirya ta taya mu murnar aure, na amsa da Allah ya kaimu daren lafiya. Daga nan muka yi sallama. Da dare sai ga wasu mata su biyu sun zo wai zasu shirya ni don zuwa dinner, nace toh. Nan suka hada wani irin ruwa da wasu furanni suka min wanka sosai da wasu irin sabulai masu kamshi, suka wanke min gashi tass, daga nan suka min gashin jiki da gashi da wani irin turare mai kamshi. Awanni biyu curr suka dauka suna shirya ni, sai gani na fito tsab cikin saree mai tsada na en asali kasar India, suka saka min sarkar gwal a hannu, kunne, kafa, yatsun hannu har a hanci na. Gashina suka shirya shi ya kwanto har gadon baya na, suka bi suka manna wasu stones a jikin gashin sai sheki yake da tashin kamshi. Lokacin dana fito su Anti suka ganni sai suka kama baki tsabar mamaki, don kuwa na koma sak kamar wata cikakkiyar ba'indiya. Suka saka ni a tsakiya har gaban motar da zata dauke ni zuwa wajen dinar, tasha adon roses masu kyau, na shiga ciki su kuma suka shiga dayar. A cikin motar na samu angon shima cikin saree na maza kalar nawa wato golden ash, ya saki baki yana kallona kamar ranar ya fara gani na. "kin yi kyau pa!" nace kaima haka. Yasa hannu ya sarkafo nawa yana matsawa a hankali har muka isa wajen dinar. An kawata wajen da kayan decorations sosai, kafin mu fita daga motar ya dauki gyalen saree din da suka dora min a kafadata ya dora min shi a saman kaina. Mutane muka samu dankam a wajen suna jiran isowar mu, muna fita daga motar en jaridu, gidajen tv da mutane suka biyo mu da ruwan flashes har zuwa mazauninmu. Nan aka fara gabatar da dinner ba bata lokaci, muka yanka cake, muka yi rawa, muka amshi gifts. Da aka tashi muka shiga gaisawa da jama'a suna taya mu murna. Kai wannan ranar nayi marking dinta as a very precious day to me, ganin yau gani gaban manya-manyan en wasan India tun daga Bollywood, tollywood, kollywood, da sauransu suna zuwa suna taya mu murna mazan su da matansu muna ta gaisawa, masu hotuna kuma nata aikin dauka. Bamu muka bar wajen ba sai karfe ukun dare, a gajiye kwarai muka bar wajen.
A cikin mota Marwan ya janyo ni jikinsa ya fara danna gabban jikina a hankali, na fara jin wani yarr a jikina. Abu ne da bai taba faruwa a tsakaninmu ba tunda muke dashi. Na fara kokarin janye jikina daga nashi, ya kara janyoni jikinsa na koma kan cinyarsa dangargar, a kunnena yake rada min relax mana! M just massaging your body, na ga kin gaji da yawa.... Ba yadda na iya haka na kara kwanciya a jikinsa ya cigaba da matsar sassan jikina. Kafin mu isa gida dai gabadayanmu mun fita a yanayinmu. Direban daya dauko mu yayi parking a kofar gidan da aka mana masauki, na zame jikina daga na Marwan na bude motar zan fita, hannu yasa ya janyo ni da karfi na koma cikin jikinsa, ya saka duka hannuwansa biyu ya tallabo fuska ta na kalleshi ido cikin ido. Gabana ya fadi sosai, kallon dake cikin kwayar idanun Marwan ban taba ganin irinsa a cikin idanunsa ba, kallonsa kallo ne mai tsabta amma na yau, it was full of lust. Na janye nawa idanun don ba zan iya jurewa kallon nashi ba. Ya fara matso da fuskata gab da tashi har sai da hancinsa ya fara gugar nawa, ya kawo bakinshi saitin nawa zai yi kissing dina, zuciyata ta fara daka tsalle kamar zata fado daga kirjina, na lumshe idanuna cikin yanayin dana kasa fassara irinshi. Komi ya tuna? Ji nayi ya dan saurara kafin ya sake ni ya koma ya jingina da jikin kujera yana sauke numfashi, tsawon mintuna biyu ya bude idanunshi ya kalleni idanunshi sun sauya launi, muryarshi ta zama rough cikin dan lokaci, yace je ki kwanta Meenah, sai da safe!, Kai kawai na iya gyada mishi na fita daga cikin motar. Ban bari tunanin komi ya shiga raina ba, na fada kan gado ko kayan jikina ban cire ba na hau barci.
Washegari aka kara zuwa aka shirya ni cikin wata shigar ta Saree ruwan gwaiduwar kwai, a cewar Marwan gidansu mahaifiyarshi za a kaini. Zamu yi sati guda a can ni da Hindu wai suna kula da yanayin zamanmu da tarbiyarmu, idan kuma satin ya cika zasu raka mu asali gidanmu dake Mumbai. A ranar muka yi sallama da dangina da suka rako ni, wasu sun koma Najeriya, Anti ta koma Mumbai yayinda Anti Rukky ta koma KL inda take karatunta. Motoci uku suka zo daukata, Kareemah kanwar Marwan wadda take zaune a Kano amma yanzu tana aure a Zamfara, ta kamo hannuna ta kaini har cikin mota ta zaunar dani. Ni kadai suka bari a cikin motar, ita ta juya ta shiga wata, direba ya ja motar muka bar gidan.
©Jeedderh🐾
[5/2, 10:53 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•25•°🐾
Mahaifiyar Marwan da abokanan ta suka fito suka tarye mu da kansu, gidansu babban gida ne da dakuna manya manya, ga daki na ga na Hindu haka suka mana bayani. Ban taba haduwa da mahaifiyar Marwan da Hindu ba sai a ranar, dama dama mahaifiyar Marwan na gaisheta ta amsa babu yabo babu fallasa duk da cewa na fahimci fara'ar data dinga min ta yake ce saboda idon mutane, Hindu kuwa kallo daya dana mata ban sake marmarin maimaitawa ba saboda wata irin harara data dinga watsa min. Daya bayan daya suka dinga nuna mana gidan da yadda al'adu da dokokin gidan suke, suka ce daga ranar ni da Hindu zamu dinga girki da gyaran gida, suka raba mana girki ni da ita, idan nayi na rana sai tayi na dare, na safe kuma tare zamu dinga haduwa muna yi da ita, babu mu babu haduwa da mijinmu sai dai a waya, ba a yarda mu fita ko nan da kofar gida ba, dokoki dai kala-kala, muka amsa da zamu kiyaye da dokokin, daga nan suka hadamu suka mana nasiha akan mu zauna lafiya mu kuma bi mijinmu. Da suka gama abinda zasu yi aka watse aka bar ni da surukata da kishiya ta, gani na tsuru ni kadai a zaune, Hindu da Maah sun hade kansu a gefe suna ta yara yaren Malayalam yasa na silale daki na jiki na a sanyaye, na san cewa ba zamu yi zaman dadi da surukata da kishiyata ba.
Washegari tunda nayi sallar asubahi ban koma barci ba, kicin na tashi na shiga. Sai da nayi en share-share da goge-goge saboda kicin din ya danyi kura, na hau dube-dube har Allah yasa na gano food time table dinsu naga abinda za a girka na fara girki, thanks to Hanan, idan bangaren girki ne babu wanda ban iya yi ba na kabilu da yarukan kasar India daban-daban. Sai dana kusa gamawa Hindu ta shigo kicin din, na juya na kalleta da er fara'ata na gaishe ta cikin harshen turanci, ta juyar da kanta gefe, ganin haka sai na koma yaren Hindi, nan ma ta janye kanta, sai na tabe baki na juya ga girki na. Tana tsaye na kammala girkin na shirya komi a tsakiyar falo, na kimtsa kicin din na koma dakina na watsa ruwa na kimtsa jiki na na fita falon. Maah tana zaune Hindu na gefenta suna karyawa, na durkusa na gaisheta, ta dube ni ta watsar ta amsa da kyar, dan murmushi kawai nayi na koma gefen Hindu na zauna na janyo plate na zuba abinci nima na fara ci. Da rana ma haka nayi girki, na gyara falo da dakin Maah Hindu na zaune na kallona kamar wata er aikinta. Da dare kuwa da tayi nata girkin, cokalin farko dana kai bakina da kyar na iya hadiye shi saboda wani masifaffen yaji dana ji, haka na daure na dinga tsakura ina kaiwa bakina, ranar da matsanancin ciwon kirji na kwana.
Kullum Hindu zata yi girki to yajin da zaka ji cikin girkin sai ya wuce tunaninka, daga baya ne na fahimci cewa ni kadai ce nawa abincin yake yaji, babu mamaki da gayya ake saka min shi cikin abinci. Haka na daure na cigaba da jurewa har muka yi sati guda cif, a kuma ranar Marwan ya dira a gidan don tunda aka kawo mu bai zo ba sai dai muyi waya dashi. Maah ta hada mu mu duka ukun ta mana nasiha akan mu zauna da junanmu lafiya kuma tsakani da Allah, mu kuma kiyaye hakkokin aure dake kanmu don a ranar zamu bi jirgi zuwa Mumbai. Muka kimtsa kayanmu muka fito, da zamu tafi na ga ta ja Hindu gefe suna magana kasa-kasa, duk sai naji na tsargu musamman da yake suna maganar ne suna kallo inda nake. A haka dai muka yi sallama da ita muka tafi.
Gidan da aka min jere a Mumbai din nan muka dira tunda ita har zuwa lokacin bai samu inda zai ajiye ta ba, to zata zauna damu kafin a sama mata wajen zama. Ya nunawa kowa dakin da zata zauna, duk muka shiga muka yi wanka gami da dauro alwala muka fito falo kamar yadda ya umarce mu, nan yaja mu sallar magriba da isha'i. Bayan mun gama muka zauna muka ci abincin da yayo mana oda, muna gamawa na hada kan kayan na kai kicin na wanke su tass na mayar da su ma'ajiyar su. Falo na koma, Hindu na zaune a gefenshi kan kujerar da yake da yake 3-seater ce, nima naje na zauna a daya gefen.....
©Jeedderh🐾
[5/2, 10:53 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•26•°🐾
Ya sake zaunar damu ya mana nasiha akan zaman tare, ya kuma kafa mana wasu dokoki game da zaman mu sannan ya raba mana girki, kowa zata dinga yin kwana biyu ranar girkin ta. Ya dinga kokarin hada mu muyi hira amma fir Hindu taki, sai ma ta juyar da kanta ga TV tana kallo. Karfe goma tana yi ya umarce mu da mu tashi muje mu kwanta, ya kama hannuna yaja ni zuwa dakina...
Kawai tsintar ta muka yi a gabanmu kerere ta kama kugu tana jijjiga jiki. Marwan ya dubeta, lafiya ke kuwa? Ta kalleni sama da kasa, lafiyar kenan. Naga kana neman shigewa da ita daki ne shine naga ya kamata in tunatar da kai kan cewa ba kwanan ta bane, nawa ne!! Shima ya kalleta sama da kasa, yace amma baki da hankali koh? Tace da hankali na rass... Ai koda ace ban girme ta ba, ni uwargidan ta ce bai kamata ka dauki kwana na ka kai mata ba. Yace look Hindu! Kina sane da cewa da Meenah aka fara daura min aure kafin ke, kenan a shari'ance a dakinta zan kwana yau, a al'adance kuma ta zamo uwargidanki, ke ba uwargida bace yanzu!" ta dura wata ashar, "wallahi ba ka isa ba Marwan! Nace daga kai har ita baku isa ba, babu shegiyar data isa ta lalata min daren amarci na wallahi....!" ya girgiza kai cikin gundura da zancenta ya kara janyo hannuna, dama ina gefe ina kallonsu ina mamakin karfin hali irin na Hindu. To karfin hali mana tunda ga gaskiya nan kiri-kiri amma tana takewa. Yaja ni muka shiga dakina ya barta anan tana zazzaga masifa.
Kan kujera ya zaunar dani, bai zauna ba ya kalleni, "1 sec" na gyada kai ina mishi murmushi, ya fita daga dakin. Minti daya ya dawo hannunshi dauke da kwalin tatacciyar madara mai kamshin inibi, ya ajiye akan center table ya tsiyaya a cikin dogon cup, ya zauna a kusa dani. Kafin ince wani abu sai jina nayi akan cinyar shi, ya saka hannunshi daya ya zagaye ruwan cikina dashi, ya dauko cup dinnan da daya hannun ya dora min akan bakina, kai na hau girgiza mai alamun na koshi. Ya dan harare ni cikin wasa, yace "come on baby, amshi ki sha mana. Ina kallonki fa tun dazu babu abinda kika ci bayan kuma nasan kina jin yunwa, oya haaaa bakin...!!" nayi murmushi ganin yadda ya hade rai, na bude bakin babu musu ya fara shayar dani madarar mai tsananin gardi da sanyi, aikuwa tass na shanye ta, ya kara tsiyayar wata yana bani....
Wayarshi ta fara kida cikin tattausan sauti, na mika hannu na dauka don tafi kusa dani na mika mishi ya amsa bayan ya ajiye kofin., 'Maah...' dana ji ya ambata ne ya tabbatar min da kiran mahaifiyar sa ne. Ban san me take fada mishi ba, na ga dai yanayin shi ya sauya, annurin fuskarshi ya bace. A can kasan makoshin sa naji yana amsa "to.... to...., naji..." daga haka ya yarfar da wayar kan kujera ya dafe kanshi yana furzar da hucin bacin rai. Na juya ina fuskantar shi, nasa hannu a hankali na dafa kumatunshi ya dago yana dubana da idanunshi da suka sauya launi, nace "Wat's up darling??" yace kin gani koh? Waccan shegiyar yarinyar har ta fara hada ni da mahaifiyata? Yanzu har ta mata waya ta shirya mata karya da gaskiya, gashi yanzu tace dole sai naje na kwana a wajenta!!".
Gabana ya fadi, raina ya baci sosai. Wannan wane irin rashin adalci ne? Ya za ayi a raba ni da mijina wanda naci burin kasancewa dashi a wannan dare mai dumbin tarihi? Mai yasa za a dauki kwana na a kaiwa wadda bata san daraja da dumbin muhimmancin da wannan dare yake a garemu ba?? Ya za ayi ga gaskiya a zane baro-baro amma a dinga take ta da gangan kawai don son zuciya irin na mutane???
_"ki taya mijinki yiwa iyayensa biyayya ko da ace ranki ko nashi basa so, ki bishi da 'Toh' a duk wani umarni da shi ko iyayensa zasu baki matukar bai kaucewa umarnin Allah da manzon sa ba. Auta, kada ki kuskura ki nuna bacin rai ko wani abu makamancin haka idan mahaifiyar sa ta saka shi yin abu wanda bai miki dadi ba, koda kuwa za a take hakkin ki ne!... Ki musu biyayya, ki dinga addu'ah, in shaa Allah zasu gane basa kyauta miki watarana, da sannu zaki ji dadin hakan., kuma zaki ga mijinki yana martaba ki kuma yana girmama ki.... Allah ya albarkaci rayuwar aurenki Ameenah!!"_
Nasihar da Ammie ta min ranar da zamu taho India ta fado min a rai. Take na tattaro duk wata natsuwa da dauriya na aza a zuciyata, na dora hannuwana akan kafadunsa na sanyaya murya nace "to menene a ciki mine?? Kaje kawai, kwana uku kamar yau ne, after all ma zan dinga ganinka kullum, dama shine abinda nake fata a rayuwata, na kasance da kai a kowane lokaci!" ya dora hannunsa bisa gwiwoyina yana kallona idanunsa cike da bacin rai, na dan murmusa. Yace "amma kinsan Maah bata mana adalci ba koh?" nayi saurin rufe mishi baki da hannuna, nace "ka daina fadin haka plss! Ita babbar mu ce kuma ta fimu hangen nesa da sanin abinda kaje yazo.., ka bi umarninta kaji? Kasan cewa ba zata ji dadi ba idan kaki bin umarninta, kuma ka fini sanin fushin da Allah yake yi da wadanda suka bata ran iyayensu..!".
Wani irin lallausan murmushi ya saki a sanyaye, kyawun daya kara yi a lokacin was just unimaginable, naji wani sonsa ya kara mamaye ni, wasu irin feelings da ban taba ji a rayuwata ba suka fara min yawo a jiki.... Hannuna ya kama ya dan sumbata kafin yace "thanks for the reminder.... Allah ya miki albarka" naji wani sanyin dadi a raina, Ammie tayi gaskiya. Na murmusa sosai nace nagode dia.... Taho muje kada ka bata lokaci, ya kalleni "r u sure babu damuwa idan na tafi??" nayi leaning bakina a saitin kunnenshi na rada mishi, "u r mine now.... I wouldn't have any worries with me, as long as u will continue to stay by my side....!" ya rungumeni a jikinsa yana er dariya, "baki da matsala game da haka Meenah ta, m urs, n I'll always be!! I promise...". Ya mike na take masa baya har zuwa bakin kofa, har ya fita ina shirin rufe kofar naga ya juyo, na dan dakata ina kallonsa. Ya tallabo kumatuna da duka hannuwansa yana kallon tsakiyar idanuna, "r u sure u gonna be okay?" na gyada mishi kaina, yace OK! Sleep tight, with me in your mind n soul, promise?? Na jinjina kaina cikin wani irin yanayi, ban aune ba naji tausasan lebbansa akan nawa, naji wani yarr tun daga tsakiyar kaina har tafin kafata. Ya dago a sannu ya sake ni, ya fara tafiya da baya-baya yana murmushi yana min waving da yatsun shi uku, na maida masa martanin murmushin na maida kofata na rufe.... Sai dana shanye sauran madarar daya ajiye sannan nayi changing dress zuwa kayan barci, nayi dimming din wutar dakin na bi lafiyar gado na kwanta. Ban bari tunanika sun addabeni ba, daddadan barci nayi mai cike da mafarkai dadada. Sai da asubahi ya shigo da kansa ya tashe ni, nayi alwala na fita falo ya jamu sallah.
©Jeedderh🐾
[5/2, 10:56 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•27•°🐾
Kwanaki uku suka zo suka wuce girki ya dawo hannuna, a tsawon wannan lokacin ko gaisuwa bata shiga tsakanina da Hindu ba, tsakanina da ita sai dai harara da tsaki. Wani irin bakin kishi gareta wanda ban taba gani ko jin kwatankwacinsa ba, duk da haka ina mata fatan Allah ya yaye mata shi. A daren bayan mun kammala dinner muka zauna muna kallon labarai, ni dai kamar kodayaushe karfe tara na bugawa na mike na musu sai da safe na shige dakina, ta bini da harara tana maganganu kasa kasa da ban gane abinda take fada ba. Toilet na fada na watsa ruwa sannan na dauro alwala zanyi shafa'i da wutiri. Ina fitowa na same shi zaune akan kujera, yana ganin na fito ta mike yace da fatan kina da alwala? Nace ehh, ya gyada kai, "good! Jira ni in fito mu yi sallah" shima ya fada bandakin. Kafin ya fito har na shirya na zura doguwar riga da hijabi a jikina na hau kan abin sallah.
Ya jamu muka yi nafila rakaa takwas muka rufe da shafa'i da wutiri. Ya jima sosai yana mana addu'a game da neman albarka a zaman aurenmu yayin da nake amsa mishi da Ameeen, daga karshe muka shafa addu'ar a tare. Ya mike ya fita, can ya dawo hannunsa dauke da gorar fresh milk da kofuna, na kula hakan yana daga cikin al'adun rayuwarsa shan tatacciyar madara a duk dare kafin ya kwanta. Ya zauna a gefena ya tsiyaya a cups ya miko min na amsa na fara kurba a hankali. Muna gama sha na dauke kayan na kaisu inda ya dace na ajiye na ajje. Kafin na dawo har ya mike akan gado, sai a lokacin ne naji wani irin nervousness ya lullubeni, wannan shine lokaci na farko da zanyi spending dare na tare da wani da namiji, da namijin ma Marwan, mijina!. A sanyaye na nufi gadon na haura ta can karshen gado na kwanta gabana yana dan faduwa, ya kalleni sosai "amma dai ba da wannan katuwar doguwar rigar zaki kwanta ba koh?" na kalli rigar kafin na maida kallona gareshi nace to menene aibunta? Ya girgiza kai, "nooo, ban yarda ba Meenah. Ba zaki sake a cikinta ba, tashi ki canza kaya" bana jin zan iya yin musu dashi a lokacin, dole na dira daga kan gadon naje gaban wardrobe na bude na lalubo wasu riga da wando na barci, na cire doguwar rigar jikina ya rage daga ni sai karamin siket ash color wanda tsawonsa ya tsaya min a gwiwa, sai half vest itama dai ash ce. Na fara kici-kicin saka kayan dana ciro, daga can kan gadon yace "kinga..." na juya na kalleshi, yace "ba sai kin saka su ba, wadannan ma sun ishe ki barci taho ki kwanta" ba musu na ajiye su na koma can karshen gadon inda na fara kwanciya na kwanta gabana yana dan bugawa, yasa hannu yayi dimming wutar dakin, fitila mara haske ta kunnu.
A hankali naji ya gangaro ta inda nake ya rungumoni ta baya, gabana ya buga rasss! Ina jin shi kanshi yaji yanda zuciyata ta dinga racing da sauri. Ya juyo dani muna fuskantar juna, wani irin fitinannen kamshi mai sanyaya rai yake fita daga jikinshi, ya min rada a kunne., "relax mana kid! U r still a child, babu abinda zan miki er shila na.... Rainon ki zanyi har sai kin zamo kaza kin gane? So feel free with me...." ya karashe yana shafar gashin kaina da tattausan hannunshi. Ban san sanda na kara nutsa kaina ba a faffadan kirjinshi, ya saka hannuwa ya zagaye bayana dasu yana shafawa a hankali. Wani daddadan barci ya sace mu don sai da muka makara sallar asubahi ranar. Tare muka fita falon ni dashi, akan sallaya muka samu Hindu a zaune daram idanunta kyamm akan kofar dakina. Mamaki ya kama mu, matar da kwanaki uku da suka wuce da kyar take fitowa sallah Itace da dako wannan uban sammakon? Lallai su kishi manya!!
Muna gamawa sallah muka koma barci. Kwananshi bakwai a tare dani ya koma ga Hindu. Mun kara samun fahimtar juna a tsakaninmu, soyayya da shakuwa ta kara habaka a tsakaninmu. A haka rayuwarmu ta cigaba da tafiya, ina zuwa school abuna, Shima Marwan ya koma wajen harkar film dinsa. Yanzu ya zama busy sosai saboda yana ta kokarin ganin ya tada kamfaninsu da yake a rufe, don haka yanzu bai cika zama a gida ba, daga baya ma tsayar da harkar fina-finan shi yayi har zuwa lokacin da farfado da kamfanin zai kammalu.
A iya tsawon zaman da nayi da Hindu a gidana na tsayin wata uku, babu wani abun arziki da yake hada ni da ita sai zallar rashin mutunci da izaya kala-kala. Ita kadai muke bari a gidan idan muka fita, sai ya zamana duk ranar girkina idan na tafi makaranta to zan dawo in tarar da gidan da kicin kaca-kaca an bata su kamar gidan mahaukata, ko dai ayi girki a ki gyara kicin din, ko kuma ayi ciye-ciye na hauka a falo a barshi a haka, ni har mamakin yadda take bata gidan nake yi. Na dai yi imanin cewa ba ita kadai take wannan aikin ba. Abubuwa iri-iri dai wadanda babu dadin ji, haka nake fuskantar matsala daga en uwan Hindun, idan suka zo gidan nan har bana son in fita, habaici, zunde, bakaken maganganu babu kalar wanda bana gani. Wannan duk basa bata min rai akan irin yadda surukata take min, Maah ta sha daukar waya ta kira ni ta zage ni tass tace wai na hana Hindu zaman lafiya ita da mijinta, bayan kuma ita da munanan halayenta ne suke janyo mata. Sai dai ina iyaka kokari na wajen danne duk abubuwan da suke min, ba zaman su nake yi ba, wanda nake zama dominshi yana sona, yana tattalina, kuma yana girmamani, don haka duk abubuwan da suke min bana taba daga kai in kalle su. As long as wanda nake zaune dashi yana farin cikin kasancewa dani, to m fine!! Babu abinda zai dame ni da abinda zasu dinga fada!!!!.
©Jeedderh🐾
[5/2, 10:56 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•28•°🐾
Bana manta wata ranar talata na dawo daga makaranta da yammaci likis a matukar gajiye don ranar sai karfe biyar na gama lectures kuma kafin in dawo yamma ta riga tayi gashi ni nake da girki ranar. A gurguje na shiga kicin na dora sassaukan girki, Allah ya taimake ni yau Hindu bata 6ata gidan ba. Farar taliya na dafa don ina da miya, nayi warming din wayar na saka kifin gwangwani a ciki, tana dahuwa na hada komi na kai kan dinning na ajiye. Na koma kicin na dauko lemuka da ruwa, a bakin kofa muka ci karo da ita, tana kokarin fitowa ni kuma zan fita, muka hada goshi da goshi ni da ita ji kake garammm! Muka ja baya a guje muna sosa wajen out of pain, ban gama warwarewa daga wannan ciwon ba naga wasu taurari masu haske suna gilmawa ta idona kafin duhu ya mamaye su sakamakon wani bahagon mari data kifa min a kunci na. Na dago a gigice na kalleta, ta nuno ni da yatsa cikin balbalin masifa, "ke dabbar ina ce da zaki kawo min karo kamar wata tunkiya? Banza, munafuka mai shiga tsakanin mata da miji.... Wallahi idan baki fita a harkata data mijina ba ina gab da nakasta ki anan gidan...! Ke wallahi zan iya na kashe ki har lahira ko na samu na huta daga bakin cikin da kike kunsa min...!!!".
Abin yayi yawa! Bayan rashin mutunci yau kuma har da mari?? I can't take it anymore! Banyi wata-wata ba na mayar mata da nartanin marin ta, nace "mind ur tongue Hindu ki kuma san wadda kike kira banza don kema baki da banbanci da banzayen...!!" tunkuda ni gefe tayi ta fita daga kicin din, nayi taga-taga sulbin tiles ya kwashe ni ya maka da kasa na fadi akan hannuna na dama. Na saki wata karar wahala sakamakon wata azaba data ratsa ni har tsakiyar kwalwa na, na kasa koda motsa yatsar hannu na ne. Hindu bata juyo ta kalleni ba ta wuce daki abinda. Nayi-nayi in tashi amma na kasa, hannun ma jin shi nake kamar ba a jikina yake ba. Wasu hawayen radadi da azaba suka shiga zarya akan kumatu na. Na kwashi tsawon mintuna biyar a haka, sai ga Marwan ya fado falon kamar wanda aka jefo. Nayi ajiyar zuciya ta ganin mala'ikan taimako. Cikin dakusasshiyar murya data data rine da kukan azaba na kwala mishi kira daga cikin kicin, "Marwannn...!!" ya shigo da saurinsa yana kiran sunana, gani na da yayi a kwance ya karaso wajena da sauri ya fara kokarin tada ni zaune, nan yaga yadda hannuna ya kumbura sosai, a rikice ya kwantar dani a jikinsa ya shafo saman wajen, "Meenah! Wat's wrong with you? Hu did diz to u??" na kara narkewa a jikinshi ina wani irin kuka na asalin shagwababbun yara, nan kuwa na kara gigitashi.
Ciccibana yayi cimak ya kaini cikin mota yaja muka tafi asibiti. Ashe tsagewar kashi ce, nan suka min allurar kashe zafi suka gyara min wajen amma duk da haka sai da naji zafi ba kadan ba. Yana gefena ana gyaran na nutsa kaina a jikinsa ina kuka, har muka dawo gida kuka nake shi kuma yana ta aikin lallashi na. A hanya muka tsaya ya jidar min kayan makulashe da gasasshen nama kafin muka karisa gida.
Ina rungume a barinsa na dama ya riko kayan da muka siya da daya hannunsa muka shiga falon, tana zaune a falon tana kallo, kallo daya ta mana ta dauke kai taja wani mummunan tsaki, muna wucewa ta gefenta naji tace wahalallen banza kawai, mijin tace!! Wuce ta muka yi ba tare da mun tanka ta ba, idan da sabo ai ya ci ace mun saba da irin wadannan kananun maganganun.
Komi dana saba yi a ranar shi ya min, ya min wanka ya shirya ni tsaf, ya kuma ciyar dani kazar da muka siyo da fresh milk wadda nima yanzu ta zamo daya daga cikin al'adun rayuwata. Ya kalmashe ni cikin jikinsa muka sha barcinmu mai cike da natsuwa. Washegari ko daya tambayeni ce masa nayi zanewa kawai nayi shine na fadi, kallona yayi kawai yayi murmushi kafin yace to Allah ya sauwake, ba wai don ya yarda da abinda nace ba, saboda yana smelling something fishy, ranshi yana gaya mishi kamar Hindu tana da alhaki game da ciwo na don yasan halinta sarai.
Tsawon sati biyu yana jinyata har na warke garas, ko su Anti da suka zo duba ni ban fada musu gaskiyar abinda ya faru dani ba, bayan duk zaman jinyar nan dana yi Hindu koda wasa bata taba yi mun sannu ba.
Ana cikin haka kwatsam bayan kamar kwana biyar yace mata ta hada kayanta yau zata yi parking zuwa gidan daya samar mata, gaskiya nayi farinciki sosai don a hakikanin gaskiya na tsorata da lamarin Hindu kwarai da gaske. Gareta kam kamar bata ji dadin hakan ba, saboda har ta gama kintsawa muka tafi raka ta tana ta kumbure-kumbure. Gidanta hawa daya ne wanda aka yi shi da zallar duwatsun siminti. Ire-iren gininnikan da nake ganin kamfanin Duala-Herab na tsarawa da ginawa ne. Maganar gaskiya gidan nata ya burge ni sosai. Na kama mata muka yi en gyare-gyare duk da gidan ba wata kura yayi ba, sai wajen karfe goman dare na musu sallama na taho, Marwan ya dawo dani gida ya koma can da yake ranar girkinta ne. Ranar kam hadadden barci nayi mai suna barci, na rabu da masifar Hindu!!
©Jeedderh🐾
[5/2, 10:58 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•29•°🐾
Bayan watanni biyu muka samu hutu sati biyu na karshen zangon karatu na farko, a cikin dan tsukin kuma kamfanin Marwan ya mike har sun zuba ma'aikata an fara kera jewelries da takalma har da jakunkuna, kaninsa Muhammad Kabeer da yake shekararsa na karshe a jami'ar Cambridge shi zai dinga kula musu da kamfanin idan ya dawo amma ya samu wanda zai kula da kamfanin for the time being kafin Kabeer din ya dawo saboda shi ayyukanshi ba zasu bari ba.
Ranar wata assabar ina kicin ina girkin rana ya shigo gidan a gaggauce ya same ni, yace in hada mishi kayanshi yanzu karfe hudu zai bi jirgi zai je New Delhi amma ranar litinin zai dawo. Nace me zaka yi acan? Yace gobe ne Holi Festival, akwai film da nake kan yi kuma festival din is part of d film. Nace menene kuma Holi Festival? Yana balle maballan rigarsa yace Holi festival bikine da mutanen kasar India, Asia da makotansu ke gudanarwa a duk ranar karshen watan Phalgun (February) ko ranar farkon watan Purnima (March). It's a Spring Festival also known as the festival of love or colors. A bikin zaki ga ana wasa da kaloli iri daban-daban ana raye-raye da kide-kide, wannan shine Holi Festival. Nace Woahh! Wallahi ina matukar son in ga hakan a zahiri, don Allah in biyo ka? Yace naaa.., ai na fada miki ba jimawa zan yi ba, kiyi zamanki a gida kinji?? Daga haka ya fada toilet. Yana fitowa na tare shi da magiya kamar zanyi kuka har dai ya amince, nayi tsallen murna na dale jikinshi ina murna. Na janyo akwati na shirya mana duk abinda nasan zamu bukata acan. Karfe shida da rabi jirginmu ya sauka a New Delhi, tuni ya mana booking din daki a Nas-Vegas hotel don haka muna isa mota tazo daga hotel din ta kwashe mu zuwa cikin hotel din. Wanka muka yi yaja mu jam'in sallar magriba da isha'i, muka ci abinci daga nan ya fita wajen director din film dinsa zasu kara tattaunawa game da shirin. Sai da nayi barci ya dawo dakin, kayan barci kawai ya saka ya hau gadon ya rungumo ni tsam har barci ya dauke shi shima.
Washegari wajen karfe goma na safe muka fita zuwa wajen Shooting din, na shirya cikin riga da wando en Pakistan wandon ruwan gwaiduwar kwai rigar kuma peach sai gyalen su multiple color na peach da yellow, yayinda na rataya peach din jaka nasa yellow din takalmi. A kasar hotel din muka tsaya na sayi er karamar camera sannan muka tafi.
A wata babbar majami'a suka yi shooting din, ina zaune daga gefe rike da camera ta ina ta daukar motsin Marwan. Suna gamawa yaja ni muka shiga wurare iri-iri har da kananun kauyuka da suke near Delhi, duk mun shiga mun ga yanayin yadda suke gudanar da nasu bikin. Bamu koma masaukinmu ba sai yamma likis, acan bakin hotel dinma mutane muka samu babu masaka tsinke ana ta kide-kide ana watsi da kaloli, kafin ma mu karasa bakin hotel din jikinmu ya baci da colors. Na tsaya ina daukar hotuna, ban ankara ba naji nayi karo da mutum, kafin in dago in bashi hakuri Marwan ya matso ya janyo hannuna muka kutsa ta cikin mutane muka shige hotel din ba tare dana kula da camera ta data fadi ba. Sai da muka isa daki har mun gama shirin kwanciya na tuna da camera ta, na Benet neman duniya amma tace daukeni inda kika ajiyeni. Ai kuwa ranar Marwan ya ga daru, tasa shi nayi a gaba ina kuka kamar karamar yarinya. A cewata shine yasa na rasa ta. Ranar banyi barcin kirki ba ina ta mita, shima kuwa haka na hana shi yayi barcin, motsi kadan sai ince mishi sai ya biya ni hotunan camera ta. Tun dai yana lallashi na har dai ya gaji ya koma gefe yana dariyar mita ta, daga baya ya janyo ni jikinsa ya rungume kam-kam yana shafa bayana a hankali, a haka ya samo kaina nayi shiru har barci ya daukeni.
Washegari da kyar ya lallasheni na yarda na shirya muka fita zagaya gari, amma sai da muka tsaya a shagon dana sayi camera muka kara siyan wata sannan muka tafi. Mun zagaya New Delhi sosai, mune malls, parks, gidajen tarihi, mun dai sha yawo don a gajiye tulis muka koma masaukinmu. Washegari litinin da safe muka juya Mumbai gida.
*♡BAYAN SHEKARU BIYU...!!!♡*
©Jeedderh🐾
[5/2, 10:59 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•30•°🐾
*♡BAYAN SHEKARU BIYU...!!♡*
Zaune akan three-seater dake girke a tsakiyar falon, ni kuma ina kwance akan akan kujerar nayi matashin kai da cinyarsa yana shafar gashin kaina a hankali. Sanye muke da couples attire wando 3-quarter da er shirt iri daya banbanci kawai nashi na maza ne nawa kuma na mata. Lallashina yake akan in daure in dan ci ko da tuffa ne daga cikin jerin fruits din daya zube min cikin wani dan kwando, ya bani magani in sha ni kuma naki. Muna cikin haka muka jiyo knocking din kofa, ba tare daya motsa daga zaunen da yake ba ya bada izinin shigowa. Hindu tare da wata mata da zata yi sa'arta suka danno kai cikin falon babu ko sallama, ta danyi turus da ganin yanayinmu kafin ta dake ta karaso tsakiyar falon suka nemi kujera suka zauna. Na yunkura zan tashi zaune jiri ya kwashe ni ya mayar kan cinyar Marwan, dole na kara kwantar da kaina a jikinshi. Na dube su na gaishe su cikin er fara'ata cikin fargabar abinda ya kawo ta gidana, zamanmu da ita har yau babu abinda ya ragu sai ma karuwa da yayi, suka amsa a yatsine suna kara kare min kallo, kamar wadda aka tursasa haka ta bude baki da kyar tace ya jiki? Na amsa mata da jiki Alhamdulillah! Daga haka tayi shiru tana kallonmu kasa-kasa tana turo cikinta dan kimanin watanni shida da en kwanaki. Marwan ya mata murmushi yace Maman baby, ya darling dina? Da fatan dai bata takura miki koh? Ta tabe baki tana girgiza kai a yatsine ba tare da tayi magana ba. Wani irin kallon tuhuma take min tunda suka shigo falon, ina ga ta kasa hadiyewa ne har sai data amayar da abinda ke cikin ranta, "naga kin dashe da yawa, ko dai cikine dake??" na sunkuyar da kaina kasa ina dan murmushi, shi kuma ya kalloni yana dan murmushi shima amma ba wanda ya bata amsa. Ganin haka yasa ta fahimci cewa hasashenta ya zama gaskiya kenan. Wani irin mahaukacin kishi ya turnuke mata zuciya, babu shiri ta mike tsaye kawarta ta rufa mata baya suka mana sallama, na samu na mike zaune da kyar na jingina da kujera saboda jiri, nace tun yanzu? Ko ruwa pa baku sha ba! Ban samu albarkacin ko kallo daga garesu ba suka sa kai suka wuce Marwan ya musu rakiya har inda suka ajiye motarsu, sai daya ga fitarsu daga gidan sannan ya dawo ciki.
Suna hawa kan titi Hindu ta gangara gefen titi tayi parking tana numfashi cikin bacin rai da fusata kafin ta fashe da kuka bakin ciki, abokiyar ta wadda take makociyarta ce matar wani dan wasan kwaikwayon India shima ta shiga bata baki tana kara kitsa mata mugun abu.... "Ki daina kuka Hindu nasan abinda kike gudu, kuma na goyi bayanki dari bisa dari. Ba zai yiyu ki jera haihuwar 'ya'ya da ita ba wallahi, har abada hakan ba zai faru matukar ina raye! Ki kwantar da hankalinki kawata ni nasan abinda zamu yi, wallahi wannan cikin karya yake yazo duniya... Da wanne zaki ji? Da shariyar miji baya sonki ko kuwa da tulin 'ya'yan kishiya??" Hindu ta tsagaita da kukan da take yi tace me zamu yi yanzu er uwa? Ki taimakeni don Allah! Tayi dariya tace kada ki damu, nice pa! Ki bari muje gida zan fada miki. Hindu tayi murmushi tace I believe you kawata, nasan matsalata zata warware yanzu, suka yi dariya ta ja motar suka wuce.
Cikin kwanaki biyu na warware daga zazzabin daya min mummunar damka fiye da sati biyu ina jinya a gida, amma kwana biyun nan na samu sauki har na komawa lectures dina. Ranar laraba wajen karfe goma na safe ina cikin bayi ina wanka zanje makaranta na dinga jiyo karan intercom. Mamaki ya kama ni, wanene a wannan lokacin? Marwan dai baya gari yau da asubahi suka tafi Pretoria harkokin film dinsa sai yayi sati biyu ma sannan zai dawo. Na dauraye jikina na daura babban towel na fito, hijabi babba na saka a jikina wadda ta rufe har duduniyar kafata sannan na fita wajen kofa. Zuwa lokacin an daina buga kofar amma kuma da alamun akwai mutane a bakin kofar, na kama handle din kofa kenan zan bude naji kamar muryar Hindu tana magana, na dakata da bude kofar na kasa kunne a jikin kofar, tabbas kuwa ita dince., "mu tafi kawai tunda ba a bude ba nasan bata nan, kila makaranta taje" naji wata muryar daban tace "...muje kawai, amma banji dadin rashin samunta ba wallahi" wata murya kamar ta matar da suka zo da Hindu ranar nan tace "amma yarinyar nan ta auna arziki sosai. Da mun sameta Allah sai mun lakada mata na jaki, sai mun mata dukan da zai barar da wannan cikin Allah wallahi!" duk cikin yaren Hindu suke yin maganganun, Hindu tace kada ku damu, next time zamu gauraya da ita ne, ai ba karaya zamu yi ba, nice kadai wadda zata dinga haifewa Marwan yara a gidansa, babu wata 'ya mace da zata samu wannan ikon!!!
Ina jinsu suka juya suka tafi suna maganganu, na leka ta kofar makulli ina lekensu, su hudu ne biyun cikinsu ma kamar sun girmi Hindun. Sai dana tabbatar da cewa sun bar kofar gidan sannan na koma cikin falo, na lalubi kujera na zauna ina ajiye numfashi kai kace har sun min dukan ne. Da kyar na samu na kaurara jikina na tafi lectures ko wankan ban karasa ba haka na fita. Ranar kam ban fahimci komi na lectures din da muka yi ba saboda tunanika da suka cunkushe min a zuciyata. Daga makaranta gidan Uncle na wuce direct. Anti kadai na samu a gidan yara suna makaranta, Uncle yana wajen aiki, itama Antin dawowarta daga wajen aikin kenan da yake ta fara aiki. Sai da muka yi sallah muka ci abinci sannan na zayyanewa Anti duk abubuwan da suke faruwa tsakanina da Hindu, da abinda suka zo suka yi yau da safe. Anti ta kama baki cikin jimami tana jinjina lamarin, tace wannan Wace irin masifa ce mata baki sha mata ba baki ci mata ba amma ta dinga neman raba ki da cikin ki? Wannan ai hauka ne da rashin tunani!! Na rausayar da kaina gefe guda, nace to ai ko da ace sun min dukan, to dukan banza zamu min tunda ni dai bani da wani ciki da zasu zubar. Anti tace kika sani? Nayi murmushi kawai na kauda kaina gefe. Anti tace for now kiyi shiru da bakin ki kada ki fadawa kowa, amma idan suka sake dawowa to in fadawa Marwan yasan matakin da zai dauka saboda she can be a threat to my life, ta kuma ce in dage in dinga addu'a akan Allah ya kare ni daga sharrinsu. Na mata godiya da shawarwarin data bani. Ina nan a gidan har su Aslim suka dawo daga makaranta, suka zagayeni muna hirarraki da wasanni har na taya su yin assignment. Sai bayan magriba su Anti suka rakani gida har Uncle dasu Aslim, acan ma sai data kara yi mun nasiha ta bani shawarwari sannan suka koma gida. Bayan na gama duk abinda yakamata inyi a daren, na rufe duk kofofin gidan da windows, na kashe wuta, sai na janyo wayata na fada kan gado na kwanta na dannawa Marwan kira, nan muka raba dare dashi muna hira.
_Plsss ku dinga yi mun uzuri kwana biyun nan bana yin posting akan lokaci kuma bana yin mai yawa, akwai wasu abubuwa da nake ta fama dasu ne wallahi. Ina fata masoya littafin Bayan Rai zasu saka ni cikin addu'a tare dani da sauran en uwa musulmai akan Allah Mai Girma ya warware mana duk matsalolin mu... Ina kuma godiya ga mabiya littafin akan irin comment dinku da yadda kuke karfafa min gwiwa wajen correction, nagode sosai Allah ya bar kauna!_
©Jeedderh🐾
[5/2, 11:00 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•31•°🐾
Cikin Ikon Allah har aka yi sati biyu Marwan ya dawo ban sake jin duriyarsu ba. Suna sauka a filin jirgi ya kira ni ya sanar dani dawowarsu yace in shirya masa lunch a gidana zai sauka duk da cewa ba nice da girki ba ranar. Na fada kicin na hada mishi kalolin abinci musamman na arewacin Najeriya don yana son irinsu sosai, nayi wanka na tsala kwalliya mai kyau amma ba mai daukar hankali ba don nasan ba girki na bane kada in shiga hakkin abokiyar zama na. Ina sallame sallar isha'i na jiyo knock din kofa, na tafi da sassarfa ta na bude kofar. Yana tsaye a bakin kofar muka hada ido dashi, nayi tsalle na dale jikinsa ya rungume ni tsamm a jikinsa yana dariya. Ina jikinshi muka shiga cikin falon ya maida kofar ya rufe, a tsakiyar falon ya daga ni cakk yayi juyi dani muka zube akan kujera muna shesshekar dariya. Na kura masa ido ina kallon yadda ya kara kyau da fari, ga wata tattausar gargasa da saje da suka yi luf a gefen kumatunsa. Ya kanne ido gami da dage gira yana murmushi, "me yasa kike kallona like this?? Na canza miki ne baby???" na dan yi ajiyar zuciya, nasa hannu na shafa gefen kumatunsa, "kayi mun kyau sosai Khushi, I missed you!!" yayi er dariya yaja kumatuna, "silly girl! Ai kin fini yin kyau ma, amma nayi kewarki fiye da yadda kika yi kewa na baby.... Oya taho ki bani abinci yunwa nake ji".
Na mike a nutse na doshi hanyar kicin cikin takun daukar hankali, ya bini da wani irin kallo lustfully yana kissima wasu abubuwa a cikin ransa, komawa yayi cikin kujerar ya kwanta restlessness ya lumshe idanunsa. Sai dana gama shirya dishes din a gabanshi sannan ya sauko daga kan kujerar, ya zauna a tsakiyar falon inda na shimfida mishi ledar cin abinci, ya tankwashe kafafu kamar yadda ya saba cin abinci. Ni kuma na zauna a gefenshi ina zuba mishi abincin a nutse, ya kuwa ci abincin sosai. Daya gama na kwashe kayan na kai kicin, na dawo na zauna muka dasa hirar yaushe gamo har karfe goman dare ya wuce bamu ankara ba, sai da Hindu ta kira shi a waya sannan ya min sallama, na tashi na raka shi har bakin mota. Anan ma kamar kada mu rabu, da kyar muka yi sallama ya tafi ya barni cike da kewarsa, naso ace yau din ranar girki na ce, in kwanta a faffadan kirjin mijina mai sanya ni natsuwa. Na lumshe idanuna a hankali cike da tunanin Marwan.
☆☆☆☆☆☆
*TWO WEEKS LATER*
Tsaye nake a jikin dogon yaro ina tufke gashin kaina bayan na gama kwalliya cikin wasu English wears riga baka da farin siket, rigar doguwa ce har gwiwa sai dai a gefen cinyoyin rigar anyi wasu tsaga tun daga kwankwaso har kasa, tana da dogayen hannuwa ta kuma kama ni tsam wanda hakan ya taimaka kwarai wajen fito da zahirin tsarin diri da kirar da Allah yayi a kirjina, siket din kuma single ne ya tafi gabadaya babu wani kwalliya ko style. Na kurawa kaina ido ta cikin madubin ina kallon halittar jikina, a yau da nake tsaye a hakan ina cikin shekaruna na ashirin da biyu ne cif da dorin watanni. Nayi aure ina da shekaru sha tara da dori, na samu tsawon shekaru biyu da watanni shida a gidan aurena, amma har yau da nake tsaye haka ni din budurwa ce, ban san dadin aure ba, ban san me ake ji a cikin gamayyar aure ba. Tun bana damuwa da hakan har na fara damuwa, lokaci tafiya yake yi, kuma ni mutum ce lafiyayyiya, ina bukatar abokin rayuwa a gefena to fulfill my desires, amma ban ga alamun daga Marwan ba, he's still seing me as an underage girl wadda bata kai ta fara daukar lalurar aure ba, a cewar shi har sai na shekara ashirin da biyar, lokacin......
Agogo ya buga karfe bakwai da rabi, hakan ya farfado dani daga duniyar tunani dana tafi ya kuma tuna min cewa Marwan yana falo yana jirana zamu yi sallar isha'i. A gaggauce na dauki hijabi na saka na fita falon, yana kan sallaya yana jan carbi, na zauna daga bayansa nima ina jan carbi har aka kira sallah, yaja mu muka yi isha'i muka hada da shafa'i da wutiri, sannan muka ci abinci muka zauna kallon labaran dare.
Da misalin karfe goma da rabi nayi sallama a dakinshi hannuna dauke da tray wanda na dora goran madara mai sanyi da kuma kofuna. Yana zaune a gaban computer yana latse-latse, na matsa gareshi na ajiye tray din na zauna a kusa dashi, na tsiyaya a kofunan na dauki daya na mika mishi guda, murmushi yayi ya amsa ya min murmuring din thanks cikin murmushi, ya kafa kai ya shanye tas ya miko min kofin, daga nan ya rufe computer. Ya tashi ya shiga toilet yayi brush ya fito ya saka kayan barci, nima na tashi na shiga na wanke bakina da mouth rinse mai kamshin inibi. Marwan na kaunar duk wani abu da aka sarrafa da inibi, hatta da yawancin turarukan da yake amfani dasu masu kamshin inibi ne, shi yasa nima na lazimci amfani da Ire-iren su domin faranta ran mijina.
Lokacin dana fito daga bayi har ya riga ya kwanta ya rage wutar dakin zuwa mai matsakaicin haske, na cire kayan jikina ya rage daga ni sai brazier da dan karamin siket, ire-iren wadannan kayan su duka zame min kayan barci shekaru biyu da suka wuce, wani lokacin ko na saka kayan barci masu nauyi bana feeling comfortable a cikinsu. Na fesa body spray a jikina da humra masu sanyin kamshi, nima na hau gadon na kwanta. Sai naji ya kashe fitilar gami da jawo ni jikinsa yasa bargo ya lullubemu, nayi whispering 'good night!' a cikin kannensa na kara shigewa cikin jikinsa, dumin jikinsa da kamshin da jikinsa ke fitarwa suka suka sanyani cikin wani yanayi wanda ban san sanda na kara lafewa a jikinsa gami da kara kwantar da kaina akan kirjinsa......
©Jeedderh🐾
[5/2, 11:00 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•32•°🐾
Ya nutsa kansa a wuyana yana fitar da wani zazzafan numfashi, hannunsa kuma na karade gabadayan bayana, wuya, da gefen cikina cikin wata irin shafa mai tada tsigar jiki.
Ba haka ya saba min a sauran daruruwan kwananmu da suka shude ba, don haka ne jikina ya fara wata irin kakkarwa amma na kasa tabuka komi. A hankali kuma da kyar na samu na iya furta Marwannn...!! Sakamakon hannunsa da naji yana kokarin balle min maballan brazier, ya dago fuskana ba tare daya bari na kara furta uffan ba naji ya manna bakinsa kan lebbana, ya kamo harshena ya fara tsotsa passionately, naji numfashi na yayi yajin aiki na wucin gadi, kafin in dawo hayyacina daga shock din abinda ke faruwa da lebba na Marwan ya zare min rigar mama yayi jifa da ita. Ya maido ni kan kirjinsa yana matsa da shafar breast dina cikin rawar hannu. Wani irin yuuu na dinga ji a cikin kaina, gabadaya na rasa inda kaina yake. Ina jin sanda hannunsa ya dinga shafar fatar cikina, yatsunsa suna circling din cibiyata, ina so in hana shi abinda yake yi mun amma na kasa. I can't lie, I was enjoying what he was doing to me. Cikin yanayin fita hayyaci na rike hannunsa daya saka yatsansa a center na, na fara kokarin zare jikina amma saboda irin rikon daya min na kasa ko motsi. Muka dinga hada wani irin numfashi mai tsananin nauyi da wahalar fitarwa, ni dai na rasa a duniyar da nake na kuma rasa inda zan sa kaina ko abinda nake ji yana yawo a magudanar jini na zai daina yawo. Na samu na cire bakina daga nashi, bai yi wata wata ba ya maida bakinshi kan nipples dina.....
A karon farko a tarihin rayuwar aurenmu, muka raba dare cikin nuna tsananin kaunar da son da muke yiwa junanmu ta hanyar romance. Washegari sai na kasa hada idanu da Marwan, haka kawai wata irin kunyarsa take lullubeni a duk lokacin dana kalleshi. Tun baya ganewa, har dai ya kula yau dai kunyarsa nake ji, gashi kuma ya kasa ya tsare yaki ya fita daga gidan.
Yana kwance akan lallausan carpet din tsakiyar falon yayi matashin kai da filon kujera, ni kuma ina ta kokarin shirya mana lunch akan dinning, ya saka hannu ya janyo ni na fada kan kirjinsa. Nayi saurin kulle idona gamm kamar wadda ta ga dodo, dariya ya saki a tausashe, "wai Meenah na zama surikin kine kike ta wani sunke fuska tun dazu?" shiru ba magana kamar mai magana da dutse, sai ma kara nutsa kaina da nayi a faffadan kirjinsa, "ok.... Tunda haka ne ba zaki yi magana ba to bari in dora daga inda na tsaya jiya....." ai a sukwane na dago kaina tare da sauke idanuna fess akan fuskar shi, cikin shagwaba nace "kai don Allah!" me zaiyi kuwa in ba dariya ba? Da kyar ya sake ni bayan na mishi alkawarin zan daina dari-dari dashi.
Muna gama sallar La'asar yace inje in shirya mu shiga gari yawo, naje na tsalo wankana da sabulai masu kamshi. A daddafe na gama wankan saboda yadda nipples dina suke min wani zogi. Yana zaune akan gado a shiryansa tsab, ganin fitowa na ya mike ya taroni ya zaunar dani akan stool, mai ya dauka wai zai shafa min. Yana fara shafar ya dora daga inda ya tsaya kamar yadda yace dazu, na kasa daurewa azabar da nake ji musamman kan nipples dina wadanda yafi takurawa da tsotsa, kuka na sakar masa a saitin kunnenshi a shagwabe, sai dai bai saurara min ba kamar yadda nayi tsammani. Sai da yaji ya gaji don kansa sannan ya kyale ni, ya gama shirya ni muka fita.
A sati uku da suka biyo baya, rayuwar aurenmu ta canza akala zuwa wata nahiya ta daban, wannan canjin rayuwar ya saukar mun da wata irin natsuwa da jin dadi wadanda basa misaltuwa. A bangaren Marwan kam abun was quite different, en wasannin da yake yi dani basu kare shi da komi ba sai ma kara mishi wahala da matsananciyar sha'awa ta, gashi shi tsakaninshi da Allah gani yake nayi kankanta da irin wadannan abubuwan, gani yake ba zan iya daukar lalurar shi ba....
Wannan Kenan!!!
•{Kuyi hakuri da wannan zuwa anjima plsss....}•
©Jeedderh🐾
[5/2, 11:01 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•33•°🐾
Rayuwa taci gaba da juya mana a haka. To me, Marwan yasa naji a raina cewa yes, ni mace ce! Cikakkiyar mace., ya kuma nuna min cewa shi cikakken namiji ne, gwarzo. Wannan dan takaitaccen lokaci da muka yi a tare, nayi treasuring dinshi fiye da sauran lokutan da suka wuce mana a baya.
Cikin haka muka riski daren wata juma'ah, daren da muka kira FARIN DARE! (Zulfa Aliyu), daren da muka yi ittifakin bamu taba riskar daddadan dare mai tattare da alkhairi irin sa ba, daren da Ni da Marwan muka zamo daya, ya zama ni na zama shi, ya zamo babu wata hijabi da tayi saura a tsakaninmu....
Muna cikin gudanar da wasanninmu kamar kowanne dare, sai dai na fahimci cewa yau wasannin na Marwan sun fi zafi ya kuma fi kowane dare rikicewa da fita a hayyacinsa. Hankalina ya dauke cikin wasannin da yake yi min, kamar daga sama na tsinci muryar sa a tsakiyar dodon kunnena, "Meeenahh.... Ki lazimce, ki yarda a wannan daren in karya alkawarin dana daukar miki don Allah! Wallahi-Tallahi bana jin zan iya tsallake daren yau ba tare da nasan ke din, wanka ce ce ba, plsss kinji???".
Ni kaina zan so hakan ta faru, ina son mijina kuma bana kaunar abinda zai saka shi cikin rudani, don haka nasa hannuwana na kara rungume shi tsamm a cikin jikina. Duk da cewa banyi magana ba, ya fahimci cewa na bashi hadin kaina. Cikin wani irin rawar jiki ya juya ni kasan sa, ya lalubo bakina yana tsotsa cikin wani irin salo.....
A wannan dare Marwan ya kawar da budurci na, ya mayar dani cikakkiyar 'ya mace cikin lallashi da so da qaunar juna marar misali, sai dai na sha azaba bata kadan ba saboda yanayin zuwan daya min. Amma duk da hakan banyi nadamar mallaka masa kaina ba.
Shi ya taimaka min na samu na kimtsa jikina, da asubahi ya jamu sallah da muka gama muka koma muka kwanta barcin gajiya. Lokacin dana farka karfe goma sha biyu da kwata na rana, jikina yayi wasai ba ciwo sai dai ba karfi. Marwan baya dakin, nayi wanka na shirya cikin doguwar riga mara nauyi don jin jikina nake yayi min nauyi sosai, ina fita falo na tarar har ya hada mana abinci, ya zaunar dani muka ci abincin ina jikinsa yana tattalina. Yinin ranar a gida yayi shi bai leka ko nan da can ba.
Cikin watanni biyu kacal, idan ka ganmu ni da ango na ba zaka yi fatan dauke idanu daga garemu ba. Munyi wani irin kyau da fresh, a yanzu ne muke cikakkun amarya da ango. Son Marwan ya bi jinin jikina, babu inda so da qaunar shi basu kewaya a jikina ba, zuwa extent din da nake ganin idan har babu shi ba zan iya rayuwa ba.
Ranar nan na dawo daga makaranta da yake wasu lokutan ni nake kai kaina, na samu dogon go slow a hanya don haka na canza hanya, sai gani a unguwar su Hindu nace bari in biya mu gaisa. Suna tare da wannan abokiyar tata na same su a falo suna hira, cikinta ya fito haihuwa yau ko gobe. Cikin mamakin yadda na bude cikin dan lokaci na kara yin kyau suke kallona, rabon data ganni tun ranar da suka je min dubiya. A tsaitsaye muka gaisa dasu suna ta wani yatsina suna jifa na da wani irin kallo wanda na kasa fahimtar ko na meye, ganin haka na mike tare dayi musu sallama don banga fuskar zama ba.
Ina bada baya, Manjunath kawar Hindu ta fara kitsa mata muguwar shawara, ita kuma ta hau kai ta zauna.....
Ina isa gida kiran Marwan ya shigo wayana da yake yaje Najeriya kwanansa biyu acan, kanwarsa Iklimah ta haihu yaje barka. Nan yake gaya min cewa washegari zai dawo, dariya kawai nayi na mishi fatan a dawo lafiya muka yi sallama. Washegari kuwa tun dana tashi da safe ban koma barci ba, gabadaya tsarin parlour na canza har da bedrooms. Ban samu kaina ba sai gab da La'asar, nayi sallah sannan na shiga kicin na dora girki. Ina gamawa na fada wanka na cude jikina da sabulai masu kyau da inganci da ruwan dumi, na shirya cikin material ash riga da siket da suka min cif a jiki, na bi duk wasu gabobin jikina na shafa humra mai sanyin kamshi sannan na zira hijabi na sallaci magriba.
Sai karfe tara ya shigo gidan, na tare shi da murnata na taimaka mishi yayi wanka ya shirya cikin jallabiya. Sai wani bina yake da kallo kamar zai cinye ni. Muka fita falo nayi serving dinshi duk abubuwan dana dafa mishi. A dokance yake dani sosai don haka ko hirar da muka saba yi bai bari munyi ba ya ciccibeni sai kan gado.... Wayar shi data fara kara ne ta katse mana hanzari, ya saki tsaki tare da daukar wayar., Hindu ce!!
©Jeedderh
[5/2, 11:01 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•34•°🐾
"Kana gari??" abinda ta tambaya kenan, ya danyi jim kafin yace "A'ah, menene?" Tace "ok, dama ina son ganin ka ne, amma shikenan sai da safe!" ya amsa da Allah ya tashe mu lafiya, suka kashe wayar.
Ya sake janyo ni jikinsa na janye, nace "me yasa zaka ce mata haka? Ka sani ko haihuwa ce ta taso mata ko kuma wata matsalar?" ya danyi tsaki, "ki kyale rigimar Hindu kawai ai ke kin san halinta, abinda bai kai ya kawo ba zai sa ta katse min jin dadi na. Kin san idan nace mata ina gari kuma ba zan je inda take ba rigima ce zan daukowa kaina. Don haka malama matso maza naji dumin nan naki mai gusar da hankali ko na samu natsuwar dana jima ban ji ta a raina ba...." murmushi nayi cikin jin dadin kalamanshi na matsa na ra6u da jikinsa.....
Ba mu muka samu muka rabu da juna ba sai da dare ya tsala, na tursasa mishi sai da muka yi wanka sannan muka koma barci. Garin yayi shiru kamar babu wani mai rai a duniyar, ya kara janyo ni jikinsa, yanda naji yana goga jikinsa da nawa ya tabbatar min da cewa shi fa bai gaji ba. Na janye jikina daga nashi a shagwabe ina cewa ni dai don Allah ka bari mu runtsa mana, dare yayi sosai pa. Yace to ni ina ruwana da daren? Nace wai kai baka gajiya ne? Yayi shiru, na matsa na kwanta a jikinshi ina shafa kirjinshi nace kayi hakuri har zuwa gobe don Allah, kasan a gajiye nake kuma ya kamata in tashi da wuri gobe kaji?? Ya kwantar da kaina akan kirjinsa yana shafa tattausar sumar kaina a hankali, "it's okay Meenah, sleep tight!!" nayi chuckling kadan na kara shigewa cikin jikinsa, barci mai dadi ya dauke mu.
Cikin tsakiyar kaina na dinga ji ana buga kofa, na bude idanuna cike da barci da mamakin waye wannan da tsakiyar dare haka? Barci yaci karfina sosai, na sake komawa ban san lokacin da Marwan ya fita ba.
Bayan kamar minti biyar da fitar shi sai na dinga jiyo alamun kamar ana rotse a falo, a sukwane na diro daga kan gado na duba babu Marwan a dakin. Na duba agogo ya nuna min karfe uku da kwata ne na dare lokacin, na fita falo ina kiran sunan Marwan amma ban ji ya amsa ba sai wani kakari dana dinga ji kaman nashi. A gigice na kunna wutar dakin, nan naci karo dasu cikin mummunar shigar bakaken kaya suna ta dukan Marwan har sun kaishi kasa yayi jina-jina, na kwala ihu na nufe su da gudu na kankame mijina ina kuka na dinga tambayar me ya musu? Basu kula ni ba. Wani daga cikinsu ya kama ni ya watsar gefe, kaina ya bugi wata makings, ina dagowa naga ashe intercom ce ta security din unguwar da suka makala a kowane gida saboda emergencies irin wannan..... A haukace na shiga danna makunnar ganin irin mummunan bugun da suke mishi, na kasa daurewa na kara komawa inda suke, cikin kuka da tashin hankali na rukunkume shi ina rokon su kyale shi zamu basu duk abinda suke so. Daya daga cikinsu yasa kafa yayi jifa dani gefe har sai da bakina ya fashe, ban san sanda na zuciya ba na wawuri kwalbar mayonnaise na bugawa daya a kai da karfina, take nan ya sulale kasa sumamme.....
Dai-dai nan sai ga jiniyar security, suka yi duru-duru cikin tunanin abin yi kafin suka arce suka bar dan uwansu anan, ai kuwa na take musu baya sai dai tuni suka kama katanga suka dira, daidai lokacin en sanda suka shigo gidan nan wasu suka bi bayansu, wasu kuma suka matso suna tambayana abinda ya faru. Ina kuka na zayyana musu duk abubuwan da suka faru, muka juya cikin gidan tare dasu. Marwan da wanda nawa rotse suna kwance shame-shame a kasa cikin halin kaka-ni-kayi, nan aka ciccibe su zuwa cikin mota. Kamar wanda ya diro daga sama, muka ci karo da Muhammad Kabeer kanin Marwan a kofar gidan. Saukar shi kenan daga states yayo gidanmu ashe da rabon zai ga tashin hankali, tare dashi muka dunguma zuwa asibiti.
©Jeedderh🐾
[5/2, 11:01 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•35•°🐾
Babu wani bata lokaci aka amshe mu a asibitin kasancewar akwai en sanda, aka wuce dashi emergency suka barmu tare da en sanda suna kara min tambayoyi. Muna nan har aka kira sallar asubahi, sam na kasa zaune na kasa tsaye sai kai da kawowa nake yi, sai ga Hindu ta iso hankalinta a tashe ban san waya fada mata ba amma nasan kila Kabeer ne, ni kam tashin hankali bai barni nayi tunanin kiran kowa ba. Sai lokacin na kira uncle na fada musu abinda ya faru da kuma asibitin da muke, ba a jima ba kuwa sai gasu hankali a matukar tashe. Sai karfe goma na safiya sannan aka fito dashi, jikinshi yasha nadin plaster da bandeji kamar wanda yayi hatsarin mota. Muka bisu har zuwa wani daki aka kwantar dashi, daga nan likita ya nemi ganinmu muka bi shi zuwa ofis dinsa.
"Magana ta gaskiya wannan patient da muka gama akan shi yana cikin mawuyacin hali da rayuwar kila wa kala a sakamakon irin mugun duka da aka mishi na keta, bayan haka anyi amfani da takalmi mai nauyi sosai an bugi kirjinsa musamman saitin zuciyarsa, don haka ina bakin cikin sanar daku cewa zuciyarshi ta kumbura sannan yanayin fitar numfashin sa ya canza don haka muka mishi allurar hutu ta tsayin kwana uku domin mu ga yadda jikin nashi zai kasance. His chance of living is very low, but i promise you that things will not go out of hands In shaa Allah.....!!"
Bayanin da likitan ya mana kenan, kafin ya gama rufe baki Hindu ta durkushe kasa dafe da kugunta tana kuka, nan da nan nurses suka dora ta akan gado suka yi labor room da ita. Muna fitowa muka ci karo da mahaifiyar Marwan, jin abinda kenan sai ta zube kasa sumammiya aka kwashe ta zuwa wani dakin, kai ranar na ga tashin hankali irin wanda ban taba gani ba a rayuwa ta.
Awanni biyu curr, sannan aka fito da Hindu daga labor room ita da kyakkyawan babynta a nade cikin wani lallausan towel sai tashin kamshi suke yi. Zo kaga rige-rigen daukar baby ko ta kan uwar bamu bi wadda take ta shaqar barci. Jikina har rawa yake lokacin da Maah ta miko min babyn, na kura mishi ido ina kallo hawaye ya ciko min ido, gashi nan dai kamar Marwan yayi kaki ya tofar, babu abinda ya dauko na Hindu. Cikin dauriyar da nake ciki tun dazu na kira sallah sannan na tada ikama a kunnuwansa, sannan na tofa mishi addu'o'i na tsare kai daga zina a al'aurar sa. Na rungume jaririn a jikina wata irin tsabtacciyar kaunar yaron ta dinga tsirga jikina, kawai na fashe da kuka. Imagining if Marwan was fine irin murnar da zai nuna na dinga yi. Daidai nan en sandan nan suka zo suka mana sallama suka ce zasu je su dawo don har zuwa lokacin wanda na yiwa rotse aka bai farfado daga suman da yayi ba, muka musu godiya suka tafi. Uncle ya kawo zamzam da dabino na tauna dabinon na zuba ruwan dabinon a bakin baby na kuma shayar dashi ruwan zamzam. Yana tashi nurse ta amshe shi ta kaishi wajen mahaifiyar shi, amma sun hana mu ganinta. Muna asibitin nan har karfe bakwai na dare, daga Marwan din har Hindu babu wanda muka samu damar gani. Karfe bakwai suka ce mu wuce gida don basa barin en jinya, haka muka juya gida jiki a sanyaye babu kwari. A duk yinin ranar ba zance ga abincin kirki daya shiga cikina ba, gidana muka dunguma gabadayanmu har su Anti, sai dai basu shiga gidan ba suka mana sallama suka tafi gida, ni da Maah da Kabeer muka shiga cikin gida.
A gurguje na dafa sassaukan abinci nayi serving dinsu, yadda kasan wadanda aka takurawa haka muka dinga tsakurar abincin nan muna turawa a cikin mu. Na kaisu inda zasu kwana na musu sai da safe na tafi dakina, alwala na dauro na dukufa sallah ina nemawa Marwan sauki a wajen Allah.
Kwanaki uku suka zo suka wuce babu wani cigaba, na rame na fita a hayyacina kamar mai jinya koda yake bani da maraba da mai jinyar ma. Hindu ta warware an sallameta, ita kam har taso ta fini damuwa da halin da Marwan yake ciki. Gidana ta koma da zama gabadaya, don haka en zuwa dubiya da barka dangin shi ne ko na Hindu duk a gidana suke tarewa. Tare muke kwana da Iklimah kanwar Marwan, ita take tausa ta da kalamai masu dadi da kwantar da hankali.
A cikon kwana na biyar, mun je asibitin tun da safe kamar yadda muka saba zuwa, yanzu suna bari a shiga inda yake sai dai basa barin ayi hayaniya. Idanunshi a bude tarwai muka same shi a kwance, da alamun ya jima da tashi. Farin ciki ya mamaye mu, na rasa me zanyi a lokacin? Kawai na rushe da kuka, na ruga da gudu na fada jikinshi na rungume shi ina ci gaba da kukan, yasa hannu yana dan bubbuga baya na a hankali alamun rarrashi. Su Maah suka zagaye gadon da yake kwance kowa na furta kamar Alhamdulillah! Na koma gefenshi na zauna akan stool din dake gefen gado hannuna sarke cikin nashi kamar wadda take tsoron a kwace shi. Likita ya shigo ya duba jikin shi, Yanayin fuskar sa ya nuna alamun gamsuwa da yanayin jikin Marwan, don haka ne muka kara jin zuciyoyin mu sunyi wasai. Bayan fitar likitan na taimakawa Marwan yayi wanka da ruwa mai dumi kamar yadda likitan yayi umarni, ya sha madara marar sanyi ya biya bashin sallah da aka biyo shi.
Bayan ya gama ya zauna, aka kawo mishi danshi, ya amshe shi ya rungume shi a jikinsa, ya mishi huduba da Muhammad Al'Ameen. Ranar mun wanzu cikin farin ciki a asibitin nan, da yamma kamar kada mu tafi haka muka dinga ji.
Washegari da muka zo jikin nashi har yafi warwarewa, yana zaune a gefen gado da dan karamin qur'ani a hannunsa yana karantawa. Ganin cewa ba kowa a dakin lokacin na duka a gabanshi na bashi kyakkyawan sumba a kumatu, na gaishe shi sannan na taimaka mishi yayi wanka ya karya da abu mai dan ruwa wanda na dafa. Daga nan hira muka zauna muna yi, baby Al-Ameen yana hannuna yayin da nake zaune a gefen Maah da mahaifiyar Hindu, Hindu na zaune a gefen Marwan akan gado. Muhammad Kabeer kuma yana kan stool daga can bakin kofa. Kawai ji muka yi an turo kofar dakin an shigo, dan sandan nan ne da yake kula da case din wanda na yiwa rotse, ni na ma manta dasu ko don kwana biyu ban gansu bane? Muka gaisa dashi a mutunce ya duba jikin Marwan, ya dube mu daya bayan daya yace wacece Hindu anan? Dama na kula tun daya shigo ta tsure da ganin shi, a razane ta mike hannunta a kirji tace gani, lafiya? Ya kare mata kallo kafin yace haka nake fata, amma muna da case dake don haka akwai yiwuwar zaki biyo mu zuwa can police station don amsa wasu tambayoyi! Ta zaro ido muryar ta na rawa tace "memm.... me nayi...???" Ya girgiza kai, "idan mun je can zaki ji".
Mahaifiyar Hindu ta mike a dan zafafe, "Malam ban gane ba! ta yaya zaka zo ka dinga neman rainawa mutane wayo? Me tayi da zaku tafi station da ita??" a sanyaye Marwan ya dubi dan sandan yace Malam, idan da akwai matsala ne ka mana bayani kawai, ba wai ka zauna kana kwana-kwana ba. Kasan ba zai yiwa ina zaune ka tafi min da mata zuwa station ba tare da ka bani kwakkwarar hujja ba" dan sanda ya gyada kai yace "ban so zan fada ba, amma tunda Kun matsa shikenan.... Dama wanda muke tsaro ne cikin wadanda suka suka dira gidan Marwan ya farfado daga dogon suman da yayi, ya mana bayanin wanda ya tura su gidan bayan yasha dan karen duka, yace Hindu ce ta tura su su kashe Marwan!!"
"What???!" kusan duka dakin muka fada a razane tare da mikewa tsaye, ita kuwa Hindu zubewa tayi akan gwiwoyinta tana kuka hade da fyace majina.......
©Jeedderh🐾
[5/2, 11:02 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•36•°🐾
"Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!!" muka dinga maimaitawa, kafin mu ankara sai ganin Maah muka yi rike da wuyan rigar Hindu tana jijjigata cikin karaji da rishin kuka, tace "me muka miki Hindu? Me dana ya miki daya cancanci wannan muguwar sakayyar Hindu? Ashe duk soyayyar da kike ikirarin kina mishi ta karya ce? Na tauye farin cikin dana na aura masa ke duk da cewa baya so, amma haka ya zauna dake, Hindu duk baki ga wannan ba kike so ki kashe min shi???" kuka take yi sosai tana magana, itama Hindun kukan take yi kamar zata hadiye zuciyar ta. Mohammad Kabeer ya tashi jiki a sanyaye ya janye Maah daga jikin Hindu yana fadin relax Maah! Just relax.... Ta hayayyako masa sosai kamar zata duke shi, ba zanyi relaxing ba Kabeer, dana pa take nema ta kashe min? Wallahi ba zan yarda ba sam!! Da kyar ya samu tayi shiru ta zauna, amma fa sai kwafa take yi tana girgiza kafa. Marwan dai bin kowa yake yi da kallo ba tare da yayi ko tari ba, Allah kadai yasan halin da yake ciki a wannan lokacin.
Kabeer ya kalli Hindu tana ta faman kuka, fuskarta tayi jawur abinka da farin mutum. A nutse kuma a tausashe yace "Hindu, ki mana bayanin abinda ya faru tsakaninki da Allah, na miki alqawarin komi munin abinda kika aikata zan tsaya a bayanki!" Maah tana neman yin magana yayi saurin katseta, "plsss Maah....!" yana mai daga mata hannu alamun tayi shiru.
"wallahi ni ban tura a kashe Marwan ba na rantse da Allah!!" abinda ta fara fadi kenan cikin shesshekar kuka, yace naji, to wa kika tura a kashe? Ta girgiza kai, ban ce a kashe kowa na, kawai..... Sai kuma tayi shiru tana goge hawayenta. Ganin tayi shiru bata sake magana ba yasa yace a dan tunzure da yanayinta na kamar tana son rainawa mutane wayo, "muna sauraronki.... Idan kuma ba zaki iya bayani anan ba zan hada ki da dan sandan nan idan kunje station sai kiyi bayanin acan ko?" ta girgiza kai a hankali, ta bude baki da kyar ta fara...
"Tun wata dubiya da muka je wajen Ameenah, na ga kamar tana da ciki. Tun daga wannan lokacin naji Hankalina ya tashi, a wautata bai kamata ace mun jera haihuwa da ita ba a matsayina na babba. Kawata kuma makociyata matar Raj Mooby...." ta dago tana dubanmu daya bayan daya tace nasan ai kun san ko waye Raj?? Na daga Kai a hankali ina tunanin kwanakin baya da dadewa sun taba yin takun saka da Marwan akan wani film da aka saka Raj yace ba zai yi ba shine aka maida Marwan har aka kara mishi kudi kan wanda aka ba Raj, hakan ya jawo sanadiyar batawar su. Ba a jima ba da aka sake maimaita haka, aka cire Raj a film saboda halayen daya dinga nunawa aka maye da Marwan tare da ninkawa Marwan din crores da aka taya Raj dasu ya raina, shine yaji haushin abin har yaci kwalar rigar Marwan a lokacin yana ikirarin zai yi maganin shi a cikin industry. Bayan an raba fadan da kyar, daga baya kuma suka shirya har suka yi wani film su biyun.... Hindu ta cigaba da magana.... "...itace ta dinga zuga ni da mugayen shawarwari akan lallai in san yadda zanyi kada Ameenah ta haifi wannan cikin. Ni kuma na hau na zauna, a washegarin ranar ta raka ni gidan Ameenar ita da wata kawarta da niyar mu mata dukan da zai sa cikin ya zube sai kuma muka yi rashin saa bamu same ta ba. Nace mu Kyaleta kawai tunda koda ace zata haihu dai ni zan riga ya, itama ta nuna hakan yayi. Bata kara tayar min da zancen ba sai a satika biyu da suka wuce, ta dinga zuga ni da maganganu iri-iri, shaidan da kishi suka tunzura ni muka yanke shawarar cewa zamu yo hayar yan banga su je su yiwa Aneenah duka na fitar hankali sai su hada da satar mata golds dinta yanda babu wanda zai zargi wani abu sai dai kawai ace yan fashi ne.... Ashe ni ban sani ba amfani suke yi dani ita da mijinta.. Bayan na samu labarin abinda ya faru na tafi gidanta da kukana zan gaya mata, kawai na tadda ta ita da mijinta da sauran en bangar nan suna hira da dariya, suna fada musu cewa irin bugun da suka wa Marwan da kyar ya tashi su kuma suna ta kwasar dariya..... Don Allah ku yafe min, nasan cewa na aikata babban kuskure....!!"
Ta kifa kai cikin tafukan hannuwanta tana rusar kuka sosai. Maah ta mike tana kuka kashirban lullubin saree dinta yana warwarewa, fadi take tana karawa wallahi idan danta ya mutu ta rantse da Allah ba Raj da matarshi ba, ita kanta Hindu din a gidan yari zata kare rayuwarta. Muka mike muna lallashinta ko ta daina ihun da take yi, kawai sai ganin Marwan muka yi ya zube warwass akan gadon......
©Jeedderh🐾
[5/2, 11:02 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•37•°🐾
Na kwalla kara na nufe shi da gudu ina kuka ina jijjiga shi, likitoci suka shigo a sukwane suka kora mu waje, ba da son ranmu ba muka fita muna kuka kamar ance mana ya mutu. Ina fita naci karo da Ya Faruq da Uncle Mukhtar, na fada jikin Ya Faruq ina kuka ina ce mishi Marwan zai mutu... Wallahi idan ya mutu qila nima mutuwar zanyi....!! Hawaye suka ciko idanunshi yayi ta maza ya hana su zuba, a hankali yake dan bubbuga bayana gami da shafa kaina a hankali, "ba zai mutu ba Auta, In shaa Allah tare zaku rayu dashi har abada!".
Fiye da mintuna talatin muna tsaye a wajen cike da taraddadi, kofar dakin da muke tsaye ta bude, gabadayanmu muka juya muna kallon likitan daya leko fuskarshi babu walwala, yace "majinyacin yana son ganin ku" muka fada dakin gabadayanmu cikin rawar jiki....
Likitoci biyu ne a kanshi da nurse, muka zagaye gadon da yake kwance muna kuka sosai. Ya kai dubanshi ga Maah dake tsaye a saitin kanshi, cikin shakakkiyar murya yace "Maah ki yafe min idan na taba saba miki...." kuka ya kufce mata, tace chufff Marwan, baka taba saba min ba, ba zaka mutu ka barni ba, ina zan sa raina??? Shima hawaye ne ke ta kwaranya daga cikin idanunshi, ya kalli Hindu yace "na yafe miki Hindu, Allah ya yafe miki kurakuranki na yanzu dana baya...." Ya danyi tari, "ku zama shaidata ko a wajen Allah, ko a bayan raina na ba Ameenah kyautar Al-Ameen har mutuwarshi...." ya kalleni, "na baki amanar dana Ameenah, ki rike amana.., ki bashi tarbiya mai kyau da nagarta wadda kika taso da ita...." wani tari mai karfi ya sake sarke shi. Cikin azama da dukan zuciya mai karfi na riko hannunshi na rike tamau, nace "kada ka min haka Marwan... Alkawari kamin cewa tare zamu mutu. Ka taimake ni ka tashi mu tafi gida mu cigaba da rayuwar mu da muka fara shimfidawa... Idan ka tafi ka barni nima mutuwa zanyi, ba zan iya jure rashin ka ba....!" na kifa kaina akan kirjinsa ina kukan daya karyar da zuciyar mutanen dake dakin suka fara sharbe. Iklimah ta matsa gaban gadon tace Yaya.... Ya juya ya dubeta da idanunshi da suka fito kuru-kuru suka yi jawur, ta fashe da kuka tace kai ka zame mana uba bayan rasuwar namu mahaifin, idan ka tafi ka barmu mun tabbata cikakkun marayu kenan, don Allah ka tashi!!.
Ya daga baki da niyar yin magana amma tarin daya sarke shi ya hana shi. Wani irin tari ya dinga yi babu kakkautawa, daga baya kuma ya fara kakari. Jikina ya fara rawa, zuciyata ta dinga bugawa da sauri, jikina ya bani lokacin rabuwa na da Marwan yayi. Ban san daga ina karfin zuciya yazo min ba, kawai ji nayi ina lakanta mishi kalmar shahada. Sai dana maimaita sau hudu kafin naji ya amsa, ya kara damke hannuna sosai.
Daga nan jikinsa ya saki, hannunshi dake rike da hannuna ya saki ya koma ragwaf ya zube akan gadon, kyawawan fararen idanunsa da suka washe suna kaina, har yau sun ki gogewa a memory na, haka kyakkyawar fuskarshi ma'abociyar haiba da kamala ta kunshe da wani irin murmushi.....
Ga alamu nan a baiyane cewa Marwan dina ya koma ga mahaliccinsa amma da gangan zuciyata taki aminta da hakan, duk da cewa na ga mahaifiyarshi da sauran mutanen dakin suna kuka da salati amma ban yarda cewa ya mutu ba....
A gigice na dinga jijjiga shi ina kiran sunanshi da karfi kamar wata zararriya, ji nayi an janye ni daga jikin nashi, a haukace na juyo nayi tozali da Ya Faruq, sai kawai na dinga nuna mishi Marwan da yatsa na amma bakina ya gaza furta komi. Muhammad Kabeer yayi karfin halin yaja bargo ya rufe gabadayan jikin Marwan tare da rufe idanunshi kwallar fuskar shi na diga a kasa....
Nayi sak, yayin dana dinga jin kaina kamar ba a jikina yake ba, kai gabadaya ma ji na nayi kamar bani ba ce ba.......
********
©Jeedderh🐾
[5/2, 11:03 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•38•°🐾
*********
Har aka gama shirya gawar Marwan aka fita da ita daga cikin gidana ban san ina kaina yake ba, gani nan ni dai idanu na biyu ras a bude amma na kasa tabuka komi... Na bi makarar da aka saka shi a ciki da kallo, tun ina mata kallon sosai har ya zamo na fara ganinta dusu-dusu, mutane suka fara dawo min biyu-biyu, zuwa uku, daga nan kuma sai naji komi na duniyar ya bace min, ban kara sanin inda kaina yake ba.....
•••••••••
A hankali na dinga bude idanu na da suka min nauyi, fanka na fara gani tana wulwulawa, ban iya tuna komi ba amma kokarin tunawa nake yi sanda naji an kira sunana a tausashe, "AMEENAH??!" na kalli inda sautin ya fito, Ammie, Anti Rukky, Uncle, Anty, Ya Faruq da Muhammad Kabeer suna tsaye a gefena na dama fuskokin su dauke da damuwa. A take komi ya fara dawo min cikin memory na, na lumshe idanuna cikin jin wani matsanancin zafi a zuciyata. Ya salam!! I wished idan na bude idanuna at that time zan ga cewa mafarki nake, mummunan mafarki wanda ba zan kara marmarin in rufe idanu na ba saboda kada in sake maimaita shi, sai dai ko da na sake bude idanuna ina kan gadon asibitin nan a kwance, mutanen nan na tsaye a gefe na, da gaske dai Marwan ya tafi ya barni. Na dafe saitin kirjina nace "Inna lillahi wa Inna Ilaihi raji'un... Allahumma ajirni fi musibatun wa akhlifniy khairan min ha...!!"
Wasu hawaye masu tsananin zafi da yaji suka fara xubowa kan kumatu na, Ammie ta kamo ni ta rungume sosai tana shafa kaina a hankali, sai lokacin na samu na fashe da kuka mai karyar da zuciya, duk jikinsu yayi sanyi su ma suka fara sharar kwalla.
Sai a washegarin ranar aka sallame ni daga asibiti, ashe kwana na biyu a kwance ban san inda nake ba. Gidana aka wuce dani don acan ake zaman makoki, ina ganin dumbin jama'a a cikin gidan zuciyata ta karye, da kyar muka samu muka shiga cikin gidan saboda en jaridu da suka baibaye me suna neman bayani. A cikin gida ina dora idanuna akan Al-Ameen wani sabon kuka ya tashi, muka hadu da Hindu da Maah muka yi tayi kamar ba zamu daina ba, da kyar muka samu muka lallashi kan mu. Tun daga ranar Al-Ameen ya dawo hannuna, abinda ke kaishi wajen Hindu to shan nono ne, yana gamawa zata miko min shi, in goye shi tsam a bayana ina jin shi kamar Marwan. Sati biyu mutane na nesa dana kusa sun koma gida, aka barni ni da Hindu da wata er uwar su Maah a gida muna takaba. Wannan zaman kam zama ne na girmama juna da ganin kimar juna muke yi, muna zaune lafiya lau kamar ba mu ba. Zamu hadu da Hindu mu sha hirar mu akan zaman mu na baya, wani lokacin muyi dariya wani lokaci kuma mu sha kuka.
To dama ita rayuwa ba wata aba bace ga wanda ya hankalta, Allah yasa mu dace!
Tuni en sanda suka cafke Raj Mooby da matarshi ana ta bincike, da yake abu ne na manyan mutane domin kuwa daraktocin Marwan sun yi ruwa sun yi tsaki akan lamarin don haka abin bai zo wa su Raj da sauki kamar yadda suka yi zato ba.
Mun gama takaba da sati biyu muka hallara a wata babban kotun shari'ar musulunci anan cikin Mumbai, kotu tayi rabon gado inda Al-Ameen ya tashi da shares din Marwan dake kamfanin su Marwan din shi da Kabeer da wasu filaye da gidaje da kuma kudade, ni da Hindu kuma kowa gidan da take zaune, Hindu aka bata wani indomie joint ni kuma gidan yin ice cream duk anan cikin Mumbai da kuma zunzurutun kudi. Mahaifiyar shi da sauran kannenshi duk sun samu nasu rabon, hakika Marwan ya tara dukiya kafin ya tafi, sai dai Alhamdulillah! Duk yawan dukiyar nan tashi bata dame shi, yana taimakawa gajiyayyu da ita, yana taimakawa addinin Allah da ita, yana kuma kashe dukiyar ta hanyar data dace. Don haka sai dai ince Alherin Allah ya kai masa har cikin kabarinsa.
Bayan anyi rabon gado, aka fara shari'ar su Raj. Saboda kwararan hujjoji da aka samu a take kotu ta yanke musu hukuncin daurin gidan yari na shekaru biyar tare da biyan tara, Hindu zata yi waya takwas a gidan yari da aiki mai tsanani don hakan ya zama darasi ga yan baya. Ana gamawa kotu ta tashi, na kama hannun Hindu na rike kam da kyar en sanda suka janye ta muna kuka, Maah ta zo ta rungume ni tana kuka take rokon in yafe mata, ta min kaza, ta min kaza saboda Hindu, gashi dan nata da take yin hakan saboda dashi ya tafi ya barta, wadda tayi don ita kuma taci amanar ta... Kai maganganu barkatai kamar wadda kwalwarta ta juye. Ji nayi kafafuna sun kasa daukata, na tafi na zube a tsakiyar kotun jikina a sanyaye, na rasa abinda zan yi a lokacin. Na jima sosai a haka kafin na tashi da niyar tafiya, taku daya, biyu, ana uku sai na zube anan.....
*>To all BAYAN RAI readers, ina ta samun korafin ku na cewa bai kamata Marwan ya mutu ba, sai dai idan Marwan bai mutu ba abubuwa da dama ba zasu faru ba, sannan shi kan shi littafin ba zai amsa sunan Bayan Rai ba kenan..... Kowane rai yana da kaddarar sa, kuma ko wane rai zai dandana zafin mutuwa..... Ina fata makaranta sun fahimta. Ku cigaba da bibiyar labarin don jin yadda zata kasance! Love Yah!<*
©Jeedderh🐾
[5/2, 11:03 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•39•°🐾
Sai bude idona nayi na tsinci kaina a gadon asibiti, sati na biyu cikin coma wadda shock ya haddasa min. Ammie na fara ganin kafin Kabeer da Ya Faruq, suna ganin farkawa ta suka shiga hamdala. Ya Faruq ya fita da kanshi ya kira Dacta, wata kyakkyawar farar mata ta shigo da fara'ar ta ta duba ni, komi ya nuna normal. Ta fara cire na'u'rorin da suka manna min a jiki tana tambaya na fatan babu inda yake min ciwo? Nace babu. Ammie ta kama ni muka je bayi ta taimaka min na wanke jikina tas da ruwan dumi, na fito na zura wando da riga marassa nauyi wanda asibitin ya tanada saboda patients. Na zauna a gefen gado bayan Ammie ta saka min filo a bayana. Ina shirin tambayar ina baby Al-Ameen su Uncle suka yi sallama shi da Anti Jameelah suka shigo, Tasleem da Asleem na biye dasu yayin da Al-Ameen yake a hannun Anti. Fuskokin su ya nuna jin dadi sosai da gani na a zaune, su Asleem suka baibayeni suna watsa min surutan makaranta. Na dan ji sanyi sosai a cikin raina, Uncle ya kalle ni ya min murmushi na dan sadda kaina kasa ina dan murmushi, Anti Jameelah ta miko min Al-Ameen na amshe shi. Yayi bul dashi alamun yana samun kula sosai, naji kwalla ta ciko idona. Na rungume shi a jikina ina dan jijjiga shi, na kalli Anti nace "Anti nagode for taking care of him" ta zauna a gefena ta shafo kumatu na, "stop embarrassing me girl, Al-Ameen da na ne nima. I prepared a very delicious and yummy potato porridge for you, Asleem miko min box din abincin can...." nayi saurin tare ta, "nooo Anti, ba yanzu ba, bana jin yunwa" Ya Faruq yayi saurin kallo na, me kika ci da ba kya jin yunwa? Na danyi murmushi, "cikina ne a cike Ya Faruq, zan ci anjima in shaa Allah..." ya gyada kai kawai muka cigaba da hira.
Da dare muna zaune daga ni sai Ammie a dakin, sauran duk sun tafi gida. Lallashina take yi in daure in ci abinci, tunda na tashi babu abinda ya shiga ciki na. Shiru kawai na mata na sadda kaina kasa, tunanin yadda zan saka wani abu a cikin baki na nake saboda ji na nake full bana bukatar komi a wannan duniyar da Marwan ya tafi ya barni in rayu ni kadai a cikinta, i was depressed and i lost any other hope. Fatana daya a lokacin nima in bi bayanshi, bani da wani buri ko sha'awar koyawa zuciyata rayuwa a duniyar da babu Marwan, Marwan becomes a part of my being wanda yake tattare da bugun zuciyata, ina mamakin ta yadda mutum zai rayu a duniya without heart beat...! Sai na fara sharar kwalla a hankali. Ammie ta fusata, ta dankwafar da bowl din hannunta ta tashi daga kusa dani, tace "sai kije kiyi tayi Ameenah, maza kiyi starving din kanki ki mutu ki bi bayan Marwan ko ba haka kike so ba? Wallahi da haka ake so da bamu yi shi ba, ba son Marwan kike yi ba tunda har kin kasa yarda da kaddarar da Allah ya dora miki. Kin rasa mahaifin ki ma balle miji? Kina nema ki bata musuluncin ki saboda wata banzar soyayya??!...." sosai ranta ya baci dani, ta dinga fada ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba. Kawai sai na ida rushe mata da kuka, da wanne take so inji ne? Yaya take so inyi da rayuwa ta? Son Marwan a jinina yake, ban san ta yanda zan yi in cire shi ba ko kuma in koya wa zuciya ta hakurin rashin sa ba, sai dai idan jinin jikina za a zuke a tittila min wani....
Likitar nan ta dazu ta turo kofa ta shigo, sanye take da doguwar rigar castrada anyi wa wuyan rigar da hannunta surfani mai kyau irin na mutanen yammaci Asia, tayi rolling da grey gyale na rigar, fuskarta saye da farin madaidaicin medicated glass. Ta tako a nutse ta nufo inda nake zaune fuskarta dauke da murmushi, haibarta da kamalarta suka cika min ido. Her charismatic feature is one in world, ban taba ganin mutum mai tarin baiwarwaki irinta ba. Kamshin turarenta kadai ya sanyayar min da zuciya, murmushinta kawai ya tsayar da kukana, irin wadannan mutane daidaiku ne a doron kasa. Ta zauna a gefe na a nutse har zuwa lokacin tana murmushi, ta dafa kafadana ta fara magana cikin turanci, tace "haba Ameenatu autar mata? Waye ya fada miki don ka rasa miji shine rayuwar ka ta kare? Ina tawakkalinki? Kin manta da cewa yarda da kaddara yana daya daga cikin ginshikan imani? Ko kuwa kin manta cewa duk wani mai rai mamaci ne? Kuma ita mutuwa tana kan kowa? Ko daina yiwa Marwan kuka don baya bukatar shi daga gare ki, addu'arki yake bukata, yana bukatar karfin zuciyar ki da kika karya, yana bukatar ki kula da dansa amma kin kwanta kin ki ki kaurara jikinki balle ki kula dashi din... Kina ina yara suke rasa iyayensu, iyaye su rasa yayansu, yayye su rasa kannensu, kuma su yi hakuri su yarda da kaddara and move on with their lives??..."
Na sadda kaina kasa, zuciyata ta fara rage suyar da take min, naji wata natsuwa da tsoron Allah na shiga ta, kalaman likitar nan suka dinga huda jikina suna ratsa ni. Abin kamar wani magic, naji wani karfi ya mamaye raunin da zuciyata tayi, wani kuzari ya dinga shiga ta yana kara min karfin jiki dana zuciya. Likitar ta kara cewa,
"Ameenah, ita rayuwar nan da kike gani, mutane na yin ta ne kawai ba wai don suna jin dadinta ba, sai don yin bautar da aka halitto mu domin yin ta. Bari in fada miki wani sirri game da sarewar rayuwa, the more you lose hope, the more your heart will break, the more your dreams will fall. A hankali duk wani burinka zai fadi, ya ki cika, mafarkin ka ya zama ba gaskiya ba, y?? Bcoz kai a karan kanka baka da assurance na zamowar wannan mafarkan naka gaskiya, tell me, ta yaya mafarkin ki zai zamo gaskiya idan kina karya ta shi?" na girgiza mata kai a hankali alamun babu, tayi murmushi tace "then cheer up Ameenah! Ki tashi ki fuskanci rayuwar ki ta gaba, past is past, Marwan has gone to where he belongs to, ki gina rayuwar ki data danki cikin kwarin gwiwa. You can do it, ki sanyawa ranki hakan. See possibility in every impossibility sai ki ga komi yana zo miki da sauqi duk wahalarsa. In shaa Allah rayuwar ku zata haskaka, Allah kadai yasan dalilin da yasa ya dauke Marwan daga gare ku wanda ni na tabbatar da cewa hakan alkhairi ne. Don haka ki sake bude idanunki cikin wannan sabuwar rayuwar... Allah yana tare da ku, n we will always be...!!".
Zuciyata ta nutsu da kalamanta da ita kanta ma, she was right. Nasan cewa komi ta fada gaskiya ne, kawai zuciya ce idan ta karaya ta yanke buri to komi naka ma sai ya yanke. Cikin kwarin gwiwa na dauki bowl din da Ammie ta ajiye min, farfesun kayan ciki ne da yasha veggies, na fara ci a nutse. Ban san ya aka yi cikina ya bude ba, sai a lokacin nasan ashe ina jin yunwa, taste dina ya dawo. Na cinye na ajiye kwanon a gefe, Likitar nan ta tsiyaya ruwa a cup mara sanyi ta bani nasha tare da magunguna na. Sai lokacin ta mike ta mana sallama, Ammie ta raka ta har bakin kofa tana mata godiya. Ta maida kofar ta rufe ta dawo gare ni ta zauna a gefena ta cigaba da kwaurara min gwiwa da nasihun ta. Na tashi na shiga toilet na dauro cikakkiyar alwala, na zira doguwar riga da hijabi na fuskanci alkibla na fara jero dogayen nafilfili har sai dana ji kafafuna na niyar sagewa, na sallame sallar na daga hannuwana sama ina yiwa Allah kirari ina hawaye, ina rokawa Marwan gafarar Ubangijin Talikai, nima kuma na roki dauriya da jurewa rashin shi a kusa dani.
_[Sadaukarwar wannan shafin ga duk wata matar aure data rasa mijinta, mijin daya rasa matarsa, uwa data rasa 'ya'yanta, yara da suka rasa iyayensu, dama sauran 'yan uwa musulmai da suka riga mu gidan gaskiya. Allah ya bamu hakurin jure rashin wadanda muka rasa, Allah yasa mu cika da kyau da kuma cikakken imani, Ameen!!]_
©Jeedderh🐾
[5/2, 11:03 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•40•°🐾
Washegari ras na tashi ina jina cikin wani nishadi da jin dadi. Ina kan gado muna hira da Ammie su Uncle suka shigo dakin, sun ji dadin gani na a haka. Na tashi da murnata na karbi Al-Ameen daga hannun Anti, yaro dan kimanin wata biyar da kwanaki. Yayi bul dashi Masha Allah, alamun girman jiki da wayo sun bayyana a tare dashi. Ina daukar shi ya bingile da dariya, sai nima naji na sanya dariyar na rungume shi. Likitar nan ta jiya suka shigo tare da wani likita, ta duba ni tana tsokanata ana ta dariya har suka fita bayan sun tabbatar min da nan da en kwanaki za ayi discharging dina. Kwana biyu na kara a asibitin aka sallame ni, Nigeria muka yi haramar wucewa daga nan asibitin. Ammie ke aikin hada mana kaya tace ni in zauna in yiwa Al-Ameen wasa kamar tasan aikin da nafi so inyi kenan, don haka na koma gefe ni da dana. Likitar nan mai suna Rachna ta turo kofar dakin ta shigo, cikin dan lokaci mun yi sabo da matar sosai kasancewar ta mace mai kazar-kazar da faram-faram da jama'a. Ta shigo tana tsokanata wai yau dai gida ko? Na kalleta kawai ina dariya. Tayi rubuce-rubuce a jikin wani fayel ta ballo takardar sallama ta mikawa Ammie. Ta bani hannu muka yi musabiha da ita, ta juya zata fita na bita da kallo. Haka kawai nake jin matar a cikin jikina, naji bana son rabuwa da ita. Nace doctor! Daidai tana kokarin kama handle din kofa, ta tsaya cak kafin ta juyo tana kallona fuskarta dauke da murmushi, na taka a nutse na isa gareta muka rungume juna, na kara mata godiya game da irin taimakon data min, muka yi musayar lambar waya da ita sannan muka yi sallama ta fita. Ba ayi minti goma ba Ya Faruq ya turo kanshi dakin, na mike rungume da Al-Ameen na yafa gyalen riga da siket din dake jikina, Ammie da Ya Faruq suka kwashi tarkacen mu muka fita. A motar asibitin muka isa airport, muna zuwa babu bata lokaci aka yi aune-aune da checkings muka fada jirgi, mutane suka gama shigowa aka rufe jirgin, muka tasamma barin kasar India....
🇳🇬PROUDLY 9JA....!🇳🇬
Saukarmu a babban filin jirgin sama dake jihar Gombe da misalin karfe biyar da rabi ne a agogo gida Najeriya, na wulkita idanuwa na gefe inda cincirindon en uwana suka ja tunga, a cikin yayyena Yaya Abdul-Hadi da Anti Fati ne kawai ban gani ba, ga kuma sauran relatives dina. Na rasa irin kaunar da en uwana suke keyi mun, a kowane abu da za ayi cikin dangi nawa sai ya banbanta, suna girmama komi nawa, suna nuna son da suke min a fili karara, a zahiri. Kafin kace meye wannan? Sun yanyame ni kamar wasu kudaje, kowa so yake ya rungume ni. Al-Ameen kam tuni aka shiga wasa-re-re dashi daga hannun wannan zuwa wancan, a haka dai muka shiga mota muka tafi gida.
As always and expected, can gidan ma wata tara ta musamman na taras daga matan yayyena har ma da iyaye maza da mata, suka yi ta shigowa suna yi mun ta'aziya har dare ban samu na huta ba.
Sai washegari da muka yi wanka, muka karya tare dasu Ammie. Na dauki baby na muka shiga cikin estate din gaishe-gaishe. Rayuwarmu a Gombe gwanin dadi, tattalinmu ake yi sosai kamar wasu kwai. Lokaci zuwa lokaci Yaya Faruq ya kan fita yawo damu, watarana har wajen aiki yana zuwa dani. Duk dai abinda zai dauke mun kewa da tunanika Ya Faruq yana min su, haka idan muka fita ya dinga jidowa baby Al-Ameen kayan wasa dana makulashe kamar me. Ni da baby na munyi bul, gashi har ya fara koyon zama lokacin. Yayi wayo sosai don babu muryar wanda bai sani ba a sasan mu, kullum kamanninsa da Marwan kara fitowa suke yi, dalilin da yake kara min son yaron a raina kenan.
BAYAN WATA DAYA...!
Hankalina ya kwanta sosai, ni da Marwan a yanzu sai addu'ah. Duk da hakan, sau tari idan na tuno shi baya hana in shige daki in shaki kuka na sosai, har zuwa lokacin ina jin Marwan a raina, ina jin mutuwarsa kamar a lokacin aka yi ta. Na tattara nawa-i-nawa muka koma Mumbai saboda makaranta, Ammie tayi-tayi dani akan in bar mata Al-Ameen amma na ki, saboda yanzun shi kadai ne sanyin idaniyata, kallonshi ya kan dauke min kewar Marwan a yawancin lokuta. A Mumbai dana shiga tsohon dakina na gidan Uncle wani kuka na fashe dashi, mutuwar Marwan ta dawo min sabuwa dal kamar a lokacin aka yi ta. Ranar da zan bar dakin kallon karshe na dinga mishi, ina ganin kamar idan na tafi kenan, har abada. Sai gani na sake dawowa cikin shi din da zama cikin wata hikima ta Ubangiji.
Washegari na shiga makaranta, Allah ya taimake ni kararun semester bai yi nisa ba amma duk da haka an yi min nisa kwarai, akwai alamun sai na dage sosai don kada a barni a baya. Daga makaranta central jail na mata na wuce wajen Hindu, na tsaya a hanya na mata sayayyar kayan bukata masu yawa. Tana ganin Al-Ameen a hannuna ta fashe da kuka, kukan daya karyar min da zuciya nima na shiga taya ta muka yi ta rerawa, muka yi muka gaji muka yi shiru. Daga nan muka shiga hirar duniya da rayuwarmu har lokacin da aka debar mana ya cika. Muka rabu da juna muna sharar hawaye. Daga ranar nan duk karshen sati na kan kai mata ziyara, muje mu yini a wajenta ni da Al-Ameen. Makaranta kuwa karatu nake yi babu kama hannun yaro, tare nake zuwa makaranta da Al-Ameen saboda gidan babu kowa. Wata tsohuwar ma'aikaciya na samu Ummu-Hani tana kula min dashi idan zan shiga class, na yarda da amanar matar da tsabar ta, gata kuma musulma. Duk karshen wata nake sallamarta.
Watannin Al-Ameen tara ya fara magana, ranar daya bude baki yayi magana ranar na fito ne daga toilet daure da towel bayan na mishi wanka, yayi rigingine yana ta en wasanninshi na yara. Ina tsaye a gaban mirror Ina goge danshin jikina, sai na jiyo er siririyar murya daga inda yake zaune ance "Mahm.....mieee" na juyo da sauri ina kallonshi kamar mai tantama, nace cike da kidima da murna "baby me kace?" ya sake cewa "Mahm....mieee!!"
Na saki karamin towel din hannuna na nufe shi da gudu na sure shi ina ihun murna, na janyo waya na shiga dannawa mutane kira ina musu albishir din baby na ya fara magana har gidan yari na kira aka hada ni da Hindu na fada mata, da dare kuwa sai ga Kabeer yazo gidan, muka hadu dasu Uncle dasu Asleem muka hada kwaryar liyafa ta murnar fara maganar Al-Ameen. Ban yi kasa a gwiwa ba na fara koya mishi sunayen Allah tsarkaka, dama tun kafin ya fara magana idan muna zaune haka kawai na kan kunna mishi irin wanda ake yi da er waka saboda yara. Da alamun zai yi surutu sosai, haka zai zauna yayi ta gwalantun hira ni kuwa in saka shi a gaba inyi ta tikar dariya....
©Jeedderh🐾
[5/2, 11:03 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•41•°🐾
Ina cikin browsing akan wani assignment da aka bamu naci karo da wata makaranta da ake koyar da training akan binciken sirri. Ban san me yasa ba, haka kawai na shiga bincike game da makarantar, tsarinta, yadda zanyi registration, da sauran su. Ba tare da nayi shawara da kowa na naje mkrntr nayi register dasu. Marwan kawai na dinga tunawa a lokacin da nake registration din, lokacin da yace yana sha'awar ganin mace na aikin en sanda, duk da cewa ba irin wanda yake so bane amma shima ai aikin en sanda ne, kuma ma idan ta kama zan saka kaki, hakan ne ya bani kwarin gwiwar kai kaina makarantar. Na kai musu da takarduna na training din da nayi na watanni tara, suka ce bana bukatar wani dogon training saboda ina da experience a harkar, watanni shida kawai zanyi su bani takardar gama karatu, kuma da yake karatu da training din part time ne, ba bata lokaci na rattaba hannun amincewa. Dama sauran watanni bakwai na gama degree dina, abin was not easy ko kadan, gashi muna yawan halartar manyan cases da criminals da dama a ciki da wajen Mumbai, amma duk da hakan ban karaya ba, ban kuma sanyawa raina zan karayar ba, ina son cikawa Marwan wani buri daya daga cikin burirrikansa kafin rasuwar sa. Su Uncle kansu sun lura da yadda na zama busy a dan takin, kullum na fita da safe bana dawowa sai yamma likis ko kuma dare, suka yi juyin duniya akan in fada musu inda nake zuwa amma naki fada musu, kullum amsata daya ce; aikin project dina nake a makaranta.
Haka mintuna suka dinga wanzuwa suna shudewa su zama awanni da kwanaki zuwa sati sannan watanni. An sallami Hindu daga gidan yari da sati biyu muka kammala training dinmu, da takardun shaidar zamu iya samun aiki a koina, kuma zamu iya fadada karatun mu. Hankalina ya kwanta ta wani fannin. Sai na tattara duk wata natsuwata na mayar kan jarabawa dake tunkaro mu. Bayan wata biyu na gama kararun degree dina, sati na biyu ina warware gajiyar karatu da kujiba-kujibar projects, sannan na fara shirin tafiya Najeriya.
Kafin in tafi sai da naje Shimla wajen Maah na kai mata Al-Ameen. Dama lokaci zuwa lokaci ta kan zo ta ganshi ita da Kabeer, ni ce dai ban taba zuwa ba. Na samu tarbar karramawa daga gareta, sosai taji dadin ganin jikanta. Anan Hindu da mahaifiyarta suka zo suka same mu, suka ga yadda yaro na yayi girma na ban mamaki, gudu da yawo babu inda baya zuwa ga surutu caii a bakinshi kamar aku. Kwananmu biyu a can na sanar dasu kudirina na son komawa gida, anan kuwa na ga abin mamaki. Mahaifiyar Hindu tsalle tayi ta dire tace ba zai yiwu in tafi mata da jika ba, rikon da na mishi ma sun gode in basu jikinsu haka. Gabadayanmu ta bamu mamaki tunda a gabanta Marigayi Marwan ya furta ya bani Al-Ameen duniya da lahira, duk wani lallami da bayani daga bakinmu zuwa gareta a banza ya tashi. Sai da Kabeer ya shiga zancen sannan ta kyale mu. Aikuwa ban kara ko yini daya a India ba, ranar dana dira Mumbai da dare washegari da safe muka bi jirgi sai Najeriya.
Zaman mu a Gombe babu yabo babu fallasa, na samu makarantar kananun yara na kai Al-Ameen, ni kuma Ina zaune a gida babu abinda nake yi. Muna waya dasu Uncle suna fada min yadda Maman Hindu ta dame su da zarya akan su fito mata da jikanta ko kuma ta kaisu kotu, ni mamakin karfin halinta kawai nake yi, nace su barta ta kaimu kotu din bai dame ni ba tunda akan gaskiyata nake rike da Al-Ameen.
Zama hakanan ya ishe ni bana jin dadi, rabin kudin gadona na dauka na ba Yaya Al-Mustapha aka fara gina masallatai da bore holes a kauyuka, gyaran tituna da sauran sadakoki da niyar Allah ya kai ladar kabarin Marwan. Ban yi shawara da kowa ba na samu wani malamin training dinmu ta internet, da taimakonshi na samu aiki da kungiyar binciken sirri ta kasa anan rassan Gombe. A ranar da nayi niyar kai takarduna ranar Kawu Hamza ya kira ni har falonsa yace yana so a cikin manema na in cire miji inyi aure, maganar shi ta kidima ni kwarai. Haka na tafi headquarter zuciyana cike da sake-sake, abinda na sani kawai shine cewa ni bazawara ce yanzu wadda take da damar da zata zabi mijin aurenta da kanta, don haka Kawu bai isa yayi min auren dole ba. Ban shirya yin aure yanzu ba, ba kuma zanyi ba don ban ga wanda zai maye wawakeken gurbin da Marwan ya bari a cikin zuciyata ba.
A can headquarter dana kai takarduna, a ranar suka kaini ofis din da zan zauna har da dauko files aka jibge a gabana. Abin sai yazo min a wani iri, nayi murmushi yayin da nake daga files din cike da farin ciki, nasan a duk inda Marwan yake a yanzu yana cikin farin ciki kuma yana alfahari dani. Karfe hudu ne lokacin tashi na, na rufe files din gabana na dauki jakata nayiwa abokan aikina hudu dake cikin ofis din sallama na tafi. Da murnata na isa gida zan sanar musu da labarin wajen aikina, abinda ya bani mamaki bai wuce ganin Maman Hindu da tarin kawayenta a gidanmu ba, an taru a kofar sasan mu ana ta cece-kuce suna ta masifa da yaruka kala-kala su lallai sai an basu Al-Ameen sun tafi dashi ko kuma su sanarwa da hukuma. Ganin shigowata duk sai suka maida hankalinsu kaina, rigima ta dawo sabuwa. Ran yayyena ya baci sosai da wannan rashin mutuncin nasu, Ya Al-Mustapha yazo a fusace ya amshi Al-Ameen dake hannuna ya mika musu yana cewa in dai akan wannan abin ne kuke tashin hankalin wannan to gashi nan, kuma dauke shi ku tafi!! Na tafi da guduna na warce shi daga hannunshi gabannin ya mika mata shi, nace cikin daga murya, "ba zai yiwu ba ya'ya, Al-Ameen dana ne halak-malak, a gabansu aka bani shi don haka ban ga wanda ya isa ya raba ni dashi ba!!" aikuwa suka kara hayayyako min, ni kuma na rufe idona nace wallahi ba zan basu Al-Ameen su tafi dashi ba. Yaya Al-Mustapha ya zuciya, bai san sanda ya min barin makauniya da bayan hannunsa na hagu a fuskata ba, wuta ta dauke min na wucin gadi, na zuba mishi ido cike da mamaki ina kallonshi.. Abune da bai taba faruwa dani ba tun yarintata, daya daga cikin yayyena yasa hannu ya dake ni. A guje na nufi cikin gida ina kuka, ba a jima ba na dawo hannuna dauke da takardun shares din Al-Ameen na jefawa su Maman Hindu, nace "nasan saboda wannan ne kuke so Al'Ameen ya dawo hannunku, to ga dukiyar nan ku jikata ku shanye.... Zan kula da Al-Ameen da hannuna da kuma karfin aljihuna. Sauran bayani ku nemi Muhammad Kabeer domin har yau ban ga ko sisi daga cikin kudin gadon Al-Ameen ba, takardu ne kawai a hannuna...."
Sai suka fara borin kunya suna nade tabarmar kunya da hauka, wai su ina ruwansu da wata dukiya? Jikansu kawai suke so, ban kula su ba na koma cikin gida na shige dakina na kulle ina shakar kukan bakin cikin wannan al'amari. Daga karshe dai suka kwashi takardun suka tafi suna zage-zage....
©Jeedderh🐾
[5/2, 11:04 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•42•°🐾
Kwana biyu muna rigima da en gidanmu, sun dage lallai sai na mayar musu da Al-Ameen alhalin su wadanda suka tado rigimar ma tun washegarin ranar da suka zo suka koma India, dama abinda ya kawo su kenan. Ni kuma na musu tsaurin ido nace idan har ba zasu taya ni rike amanar da aka bani ba to lallai zan bar musu gidansu, in tafi wata duniya can in rayu da dana. Duk a zatonsu burga ce kawai nake yi, ina tauna tsakuwa don aya taji tsoro basu san cewa da gaske nake ba, wen it comes to Marwan and Al'Ameen, i can do anything!, no matter what difficulties. Da naga sun takura min da zancen sai nayi niyar bar musu gidan for good, kai tsaye naje ofis nace ina neman alfarmar a sanya ni cikin wadanda za a tura Kano domin bincike akan kidnappers din nan, dama neman wanda zai je ake yi don haka babu musu suka bani bayanai.
Ban bi jirgi ba, mota na bi. Wannan shine karo na farko dana fara zuwa Kano, kuma wannan shine aiki na farko da zan fara gudanarwa. Duk da cewa ko acan akwai kananun bincike da muke yi da sunan assignments, don haka ban ji komi ba. Burina kawai shine in bar Gombe kuma kada in bar barakar da zata a gano inda nake da wuri. Faisal ne yazo ya dauke ni daga tasha, shine abokin aikina. Sai dana ganshi naga ashe ma dan uwan su Marwan ne amma alakar tasu ta nesa ce amma nasan shi don saboda yana yawan kai mana ziyara idan yaje can. Gidansu ya kaini a madadin hotel. Kwana biyu muna bincike har muka gano mafakar en fashin, muka yanke shawarar zanyi badda kama inje unguwar a matsayin er aiki. Saboda zuwana a haka kuma da da zai iya disa zargi a zuciyar mutanen da zan zauna dasu, don haka ne na maida kaina bakar karfi da yaji, na bar Al-Ameen a wajen Hajiya Tabari, dangin sa suna zuwa suna ganshi a can da yake da muka zo Kano sai dana kaishi family house din su Marwan din. A gareni kam tsuntsu biyu ne zan jefa da dutse daya... Wannan shine dalilin daya kaini gidan Hajiya Karima aikatau, kuma shine dalilin da yasa na bar gida na kuma canza kamanni na...!"
Ta ja ajiyar zuciya bayan ta dawo daga dogon tunanin data tafi, idanunta sun yi jazur saboda kuka, ga roll din used tissue kusan guda uku a gefenta wadda ta fyace majina da goge hawaye da ita.
*_Wannan shine cikakken tarihin Ameenah Wakili da d'anta Al-Ameen..._*
*☆☆☆☆☆☆☆☆*
Sai karfe goma sha daya na washegarin ranar Ameenah ta fito daga dakinta, tuni babynta ya kai kanshi ga Ammie tun da safe, ganin Ameenah tana barci yasa tayi duk wata hidimar shi. Yanayin da suka ganta a ciki bai basu mamaki ba, amma ya fadar musu da gaba. Idanunta sunyi luhu-luhu, fuskarta tayi jawur! Akwai alamun kuka da rashin barci a tattare da ita, ko basu tambaya ba sun san amsar daya ce; ta tuno Marwan. Don haka babu wanda ya tambayeta abinda yake damunta, suka shiga nan-nan da ita, Ammie take tausar ta da nasihu a siyasance. Da yammaci Ya Faruq ya saka amaryarshi a gaban mota Ameenah da Al-Ameen na baya suka shiga gari yawo wajajen shakatawa da manyan malls, sai bayan magriba suka koma gida.
Kwana biyu Biebie ta koma Kano cike da kewar daukacin jama'ar Wakili's estate, hakika su din mutane ne masu karimci ababen girmamawa, becoming one of them will b a great pleasure!
Ameenah kam dari-dari take yi da Kawu Hamza, jira take yi kwanakin daya dibar mata su cika taga yadda zasu kare dashi don dai ita babu wani aure data shirya yi yanzu.
Har kwanakin suka cika bata ji ya tayar mata da zancen ba, haka ne yasa ta shiga murna da tunanin kila ya daga mata kafa ne. Don haka ta tattara ta koma Mumbai, a cewarta ganinta da Kawu Hamza yake yi ne yasa ya tado zancen auren, amma idan ya daina ganinta a gidan halan ya sakar mata mara tayi fitsari.
Ranar da Ameenah ta tafi, a ranar Kawu Hamza, Kawu Jazuli da babban dan Kawu Hamza Idris da kuma Yaya Al-Mustapha suka tafi Kano don nemawa Faruq auren Safeenah. Sun samu tarba ta karimci daga garesu, suna falon Alhj.. Abbas wanda ya tanada musamman saboda manyan baki, bayan an gama cin abinci da raha, sai suka shiga gudanar da abinda ya kawo su, Alhaji Abbas yace idan dai Safeenah ce ya basu. Anan take suka fidda ranar aure, nan da wata guda. Daga nan sai hira ta barke, hira irin ta manya mai cike da fahimtar juna.
Alhaji Abbas yayi gyaran murya alamun akwai magana mai muhimmanci Da yake son yayi, duk sai suka yi shiru suka maida hankulansu gare shi. Yace "wato Alhaji Hamza, ko da ace baku zo ba nima dama ina da niyar zuwa. To amma tunda kun zo yanzu ina ga bari ayi komi a yanzu kawai. Maganar gaskiya na yaba kwarai da tarbiyar er ku Ameenah wadda ta zauna damu watannin baya, idan har baku yi mata miji ba ina rokon iri daga gare ku, na yiwa d'a na AbdulRasheed-Modibbo sha'awar ta., ina fatan bamu makara ba??!"
Shiru suka yi kowa yana saka abu a ranshi, ya kallesu lafiya Alhaji? Kawu Jazuli yayi gyaran murya yace "wannan kudiri ne mai kyau, sai dai ita Ameenah wadda muke magana a kanta yanzu BAZAWARA ce, ta taba yin aure har da D'a duk da cewa dan ba nata bane, zaku iya aurenta a haka? Kuma kuna ganin babu kwara a cikin lamarin duba da cewa Modibbo saurayi ne wanda bai taba yin aure ba??"
Alhaji Abbas yayi irin tasu ta manya yace "haba Alhaji! Banyi tunanin jin hakan daga gare ka ba. Dama don budurci kadai ake yin aure? Ina tunanin tarbiya, nasaba ma suna daga cikin manyan ginshikan aure? Idan dai don wannan ne to ba abun damuwa bane, Modibbo zai so zabin dana mishi koda wadda ta girme shi ce balle wadda ya girma. Ni dai ina bara....!" sai duk suka yi dariya suka ce "an baka!!"
Da wannan sai alkiblar auren ta canza daga daya zuwa biyu, sun bayar an basu! Exchange Marriage kenan! :)
Daga nan Yaya Al-Mustapha ya rufe taron da addu'ahr Allah Ya ba ma'auratan zaman lafiya, a ranar suka juya Gombe da niyar fara shirin bukukuwan da za ayi nan da wata daya!...
*** *♡♡♡* ***
©Jeedderh🐾
[5/2, 11:04 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•43•°🐾
*** *♡♡♡****
Kamar saukar guduma haka yaji maganar mahaifin nasa, ya dago a razane, tuni idanunshi suka canza kala cike da firgici da tashin hankali kala-kala, ya sauke su akan mahaifin nashi dake zaune fuskarshi cike da annuri, cikin doubting din abinda kunnuwanshi suka jiyo yace "Abbu, aure kuma??" ya kara fadada fara'ar shi yace kwarai aure, da Ameenatu yarinyar data zauna tare damu anan, kanwar Faruq ce! Na maka sha'awar ta zama matar ka, yarinya ce mai hankali da hangen nesa, though ta taba aure!!". Sai ya shiga kallon mahaifin nashi a gigice kamar wanda yayi gamo.....
Duk sauran bayanai da Abbun yayi Modibbo bai tsinci ko kalma daya a cikinsu ba, bai fahimci komi ba. Yayi nisa a nannauyar duniyar tunani wadda ta mayar dashi kamar statue. Abinda yaji kawai shine cewar da Abbu yayi, "zaka iya tafiya...." ba musu ya mike ya bar falon. Part dinshi dake can nesa da part din su Ummie duk a cikin gidan ya nufa yana hada hanya kamar bugagge, da kyar ya iya kai kanshi falo. Ya maida kofar ya rufe barammm da kafafunshi ya bita da makulli, kan kujera yaje ya zauna ya nutsa yatsun hannunshi duka goman a cikin tattausar sumar kanshi sai hada zufa yake yi duk kuwa da karfin split din dake falon. Ya 6ata wasu hadaddun mintuna talatin a wajen kafin ya tashi, da kyar yake daga kafafunshi har zuwa cikin bedroom dinshi. Ya janyo drawer dake gefen gado ya ciro kwalin cigarette din wrolp ya tsigo daya ya kunna lighter, kyakkyawan xuka ya mata ya fara fesar da hayakin cike da gwaninta. Nan da nan ya tada hayaki a wajen kamar wata er karamar gobara, sha yake ba sauki yana fesar da hayakin cikin kunar zuciya, idanunshi sun canza kala, "wa ce ce? Wace mai karar kwanan ce ake shirin aura mishi??"
Zuciyar shi ta kasa yardan mishi cewa wai wannan bakar yarinyar, wannan yarinyar daya tsana ce za a aura mishi ba, kai no way! It must not be her. But if, unfortunately happens to be ita dince, hmmm!! Ya ajiye numfashi yana girgiza kai. Yana tausayawa yarinyar kuwa, don kuwa ya tabbata gidan mutuwarta ne za a kaita, sai dai idan su wadanda suka kulla auren sun gaji da ganin halin da zai saka ta su zo su raba auren kamar yadda suka hada. Don dai shi ba zai taba daga baki yace da iyayensa bai yarda da hakan ba, iyayensu basu dora su akan wannan turbar ta musu dasu ba.... Ko ba wanna ba, lokaci tafiya yake yi, yanzu yana cikin shekarar sa ne na talatin da uku. Ya cancanci ace ya nemi wadda zasu gina rayuwa ta aure, rayuwa wadda addinin musulunci yace ayi, tun lokaci bai kure mishi ba, tun bai kai ga karya tubalin daya ginawa kansa ba, tun bai fara kai hannunsa ga 'yammatan dake kawo kansu gare shi ba, tun kafin hakuri da dauriyar sa su kare, tun kafin ya kai ga dorawa matan banza kirjin shi..... Da ace iyayen shi sun dan kara mishi lokaci basu mishi wannan shigar saurin ba, da ace basu zaba mishi waccan bakar yarinyar ba. Da da kanshi zai nemo yarinya wadda zata dace da yanayin matar da yake so a matsayin Uwar 'Ya'Yansa ya aura koda ace baya sonta. Zai iya rufe idon shi ya aure ta don kare kai daga Zinah, da kuma neman albarkar aure, zai daure yayi tarayya da ko wace mace koda kuwa baya sonta, amma banda wannan bakar yarinya, he can't even imagine how to live with her a karkashin inuwar aure....
Haka dai Abdul-Rasheed-Modibbo ya cinye tsawon daren shi cikin saka da warwarar yadda zai warware kullin wannan aure kafin a daura shi, ba kuma tare da sunan shi ya fita ba!
~~••••**••••~~
Amaryah Ameenah tana can Mumbai bata san kalar wainar da ake toyawa a Nigeria ba, hasalima ita neman aiki take yi acan tunda dai babu wanda ya bata goyon bayan ta cigaba da aikin 'yar sanda! Iyayenta da yayyenta sun ce basu yarda ba, wannan ai ba mutuncin su bane. Ya Faruq ne kawai ya goya mata baya, to dama shi Ya Faruq bashi da wani katabus in dai akan Ameenah ne, yana danne farin cikinsa akan nata, yana goya mata baya a duk wani decision data yanke, komi Ameenah zata yi to him, daidai ne. Kauna ce mai tsananin tsabta Allah ya sanya a tsakaninsu, Yaya Faruq shi ya zame mata Yaya, ya maye mata gurbin kawa, ya kuma maye mata gurbin kanwa, sannan ya zame mata abokin shawara. Saboda haka kaf cikin yayyenta daga mazan har matan bata da kamar FAROUQ, he's the least, but the best!!
Amma ai ance sarkin yawa yafi sarkin karfi, everyone is against it, su biyun ne kawai dai, don haka ta sanyawa zuciyarta salama ta mika resignation letter dinta, ko bata yi aikin ba tayi kararun dai, kuma tasan wanda tayi dominshi yasan tayi, har yau tana mishi addu'ar dauwama a gidan aljannar Firdaus. Wajen aikinta sun yi mamaki sun kuma ji babu dadi, ita din ma taji ba dadin to amma ya zata yi? She has no other option.
Ta fara aiki da wani art gallery studio dake acan Mumbai din, Uncle daya san halin da ake ciki game da zancen aurenta yayi kokari akan ganin ya hanata neman aiki amma bashi da wani kwakkwaran dalili da zai fada mata don baya so maganar auren ta fasu da wuri, yafi so ace koda zata sani sai auren ya matso sosai so that she wouldn't try to stop the marriage. Shi da so samu ne ma to ya zamana sai bayan auren zata sani... Don haka daga shi har matarsa Jameelah ido suka zuba mata, suna mata fatan samun sassautawar zuciya akan maganar aure.
©Jeedderh🐾
[5/2, 11:04 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•44•°🐾
Dawowar ta daga Dumpeen Art Gallery kenan a matukar gajiye, rungume take da Al-Ameen wanda ta biya ta makarantar yara da take kaishi ta dauko shi. Har yanzu babu maganar aiki, ta rasa dalili ko ina taje sai sunce ta dawo nan da kwanaki kadan idan kuma ta koma sai dai su ce tayi hakuri basu da wajen ajiye sabbin ma'aikata, bata kawo komi a ranta duk da cewa abin yafi karfin ace coincidence ne saboda taje neman aikin yafi waje biyar Anna kullum maganarsu daya ce; babu space. Amma tana kyautata zaton zata samu da Dumpeen Art tunda su sabon guri ne budewar last week tasan karya ne su ce suna da cikakkun ma'aikata. Tana fitowa daga cikin art gallery din ta nufi inda tayi parking din motar ta, a bayan motar ta taga motar kamfanin su Uncle, ta dan tsaya jimm tana tunani can kuma sai ta girgiza kai, no way! Me zai kawo Uncle nan?? Ta shiga motar taja ta tafi.
A galabaice kwarai ta isa gida saboda yunwa, a falo ta samu Anti tana amsa waya da alamun daga Najeriya ne, ta kwantar da Al-Ameen akan kujera saboda yayi barci, ta maida dubanta ga Anti data kashe wayarta tace da kyar, "Anti yunwa!.... Akwai abinci?" Anti tace "yana kicin, yanzu na sauke" da sauri ta shiga kicin din ta fito hannunta dauke da kula, plate, fork, cokali, bowl da goran ruwa da cup a cikin wani babban tray, ta ajiye su akan karamin table taja shi har kusa da kujerar da Anti take zaune. Wani hadadden kamshin farfesu ya daki hancinta lokacin data bude kular, ba shiri ta hadiye yawu ji kake mukut!! Ta figi cinyar kaza data dahu luguf ta fara ci tana lumshe idanu kunnuwanta har motsi suke kan dadi, taci iya cinta ta sha romon kazar sosai tayi gyatsa ta ture kwanon gefe, anti tace har kinyi me? Tace koshi mana of course. Anti tace Aikuwa sai kin cinye kazar nan tass! Ajiye ta zanyi anjima na miki warming dinta, Ameenah murmushi kawai tayi, ta bude plate din da aka rufe da wani kyakkyawan kyalle, wainar kwai ce aka yi sharbebiya ta sha veggies kala-kala, tana kaiwa bakinta tauna daya tayi ta dakata tana son tuno inda tasan taste din wainar kwan, ganin anti bata nuna komi a fuskarta ba yasa ta basar kawai. Hatta da ruwan data sha lokacin sai data ji ya canza taste.
Washegari da safe bayan ta kai Al-Ameen makaranta ta dawo, anti ta kai mata breakfast dinta har daki, farfesun kifi ragon ruwa da yasha ganyen spinach da Irish potatoes a ciki, sai kuwa wainar kwai irin ta jiya. Ta kalli Antin da mamaki, "amma ya abincina ya banbanta da naku? Na ga tea da fried Irish kuka karya dashi yau?" anti tace "ahhh, yayi kadan ne shi yasa na miki naki daban" ta dan gyada kai cikin doubting, ta janyo abincin ta fara ci yayin da anti ta fita ta bar mata dakin. Da dare kuma ba sai ta kai mata gashin nama ba? Ya sha tumatiri da farar albasa yayi ruwa-ruwa yana ta tashin kamshin spices. Ta kasa hadiye mamakinta tace "wai ko dai kun cire ni daga girkin kune Anti? Naga ba abnd kuka ci ba kenan yau da dare!" Anti ta danyi dariyar yake tace kusan haka, tace me?? Antin ta basar, "ke kici abincin ki kada ya huce..., bari in dauko Al-Ameen yayi barci a dakin su Asleem" tasa kai ta fita daga dakin.
Kwana biyu abubuwa suka cigaba da tafiya a haka, tana tunanin abin zai ragu amma inaa! Karuwa ma yayi. Yanzu hatta da ruwan wankanta sai Anti ta zuba wasu ganyayyaki da wani abu mai dan banzan kamshi. Haka duk bayan kwana biyu sai tayi tsuguno, Anti tace wai maganin sanyi ne. Kai daidai da ruwan shanta ya zama na daban, jin shi take zaki cauu kamar zuma. Ta tuna lokacin da zata auri Marwan irin wannan abubuwan Anti ta dinga bata sai dai bai yi yawa irin haka ba, zuciyarta ta kasa natsuwa da wannan abun nasu Anti, bata fahimce su ba. Sai dai bata son zarginta ya tabbata, shi yasa a duk lokacin data bude baki da niyar tambayar su tsoron irin amsar da za a bata take yi. Shi yasa tayi shiru kawai ta zuba musu ido.
Har ta kwanta amma bata yi barci ba idanunta a bude suke tangaras tana kallon ceiling zuciyarta na mata sake-sake, Anti Jameelah tayi sallama ta shigo dakin hannunta dauke da mug, Ameenah ta zuba mata ido yayin da bakinta kadai ya motsa wajen amsa sallamar. Ta mika mata mug din, Ameenah ta amsa. Tatacciyar madarar shanu ce sabuwar tatsa kila ma ta yanzu ce, ta kai bakinta da niyar sha sai kuma ta fasa, tace "Anti in tambaye ki mana don Allah!" anti ta dan sha jinin jikinta, tace ehh, ina jinki. Tace me yasa kike bani kayan karin ni'ima ne? Ko dai kina da wata masaniya akan cewa Kawu zai min aure??" ta fada cikin faduwar gaba da tsoron irin amsar da Antin zata bata, ta gaji da nuku-nukun da ake mata, idan ma auren ne za ayi kawai a fito fili a fada mata sai ayi ta ta kare.
©Jeedderh🐾
[5/2, 11:04 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•45&46•°🐾
Aunty ta kalleta da mamaki, "ya aka yi kika sani??" a tsorace kuma a diririce ta kalli Antin cikin zaro ido, duk da cewa tayi tsammanin jin hakan amma kuma da taji sai taji abin yazo mata a bazata, unexpected as if Antin ta watsa mata dalma a kunne haka taji saukar maganar a kunnuwanta. Cikin kyarmar murya tace "kenan.... kenan.... Hakan yana nufin.... Da gaske aure za a min??" tausayinta ya cika Anti kamar zata fashe da kuka, tace kiyi hakuri Ameenah, muma waya kawai aka mana aka sanar damu zancen auren, kiyi hakuri ki rungumi zancen auren nan hannu biyu kuma da zuciya daya. Idan kika yi hakan zaki ga ribar biyayya ga magabata. Ki sanyawa zuciyarki salama Ameenah kin san halin Kawu Hamza sarai, ko ba tsoron abinda zai biyo baya idan kika ki amincewa da auren ba, kina ganin ya dace ki sa kimarsa da mutuncinsa su zube a idanun mutane??" taji jikinta ya danyi sanyi, gabadaya Anti ta daure ta da jijiyoyin jikinta. Ta sadda kai kasa tana kwararar da hawaye, bata damu wai tasa hannu ta share ba haka ta barsu suka yi ta zuba. Anti ta dafa kafadarta ta cigaba da mata magana cikin kwantar da murya, "kada kiyi fushi da zabin Kawunki Ameenah, Allah kadai yasan alherin dake ciki. Marwan is no more! You have to face the reality and move on with your life, nasan cewa ba zaki taba mantawa da Marwan ba. Amma Ameenah, ita 'ya mace kimarta da mutuncinta suna gidan aurenta, har zuwa yaushe ne zaki zauna a haka without a life partner? Shi auren nan yana da benefits da dama a gareki da Al-Ameen, ko babu komi zai bude ido ya ganku ku biyu and call you his parents! Zaki ji dadi ya bude baki da ido watarana yace miki Maah, wher is dad? Will u b fresh in it??" Ameenah tayi saurin girgiza kai, anti tace to ko don wannan, Ameenah na roke ki kada ki watsa mana kasa a ido, m begging youhh....!!
Sai kawai ta kece da kuka ta fada jikin Antin, kuka take ba kakkautawa. Anti ta dinga tapping bayanta a hankali cikin sigar lallashi, a ranta kuwa fadi take, "Ya Allah! Yaa Ladeef!! Rayuwar baiwar nan taka taga kaddarori iri'iri, ka tallafi rayuwarta data marayan d'anta kayi mata zabin miji nagari, Ya Allah ka albarkaci rayuwar aurensu Ameeen!" ta lumshe ido hawayen tausayin Ameenah na kwararo mata.
Anti ta cigaba da rarrashinta har sai data ga ta nutsu ta daina kukan da take yi sai dai shessheka. Ta tashi jiki a sanyaye ta mata sai da safe ta fita. Madarar da Ameenah bata sha ba kenan ta koma ta kwanta. Ta rasa yanayin da zuciyarta ke ciki, ita dai tasan cewa bata na'am da zancen auren nan. To amma kuma wani sashe na zuciyarta yayi na'am da hakan. Da taci gaba da tarawa da debewa sai taga ai kashi sittin na sassan gudanar da tunani na jikinta sun fi kawo dalilan ya kamata ta amince da auren. Ta tashi zaune dangargar a tsakiyar gadonta tana sake-sake, me yafi dacewa tayi yanzu? 'Neman zabin Allah!!" Wani sashe na zuciyarta ya rada mata hakan. Tsam ta tashi kamar wadda aka tsikara ta je ta dauro alwala tazo ta fara nafilah.
Daya daga cikin manyan kyawawan halayen Ameenah kenan, sam bata barin zuciya tayi ruling dinta. Ta kan nemi zabin Allah a duk wasu al'amura da suka cunkushe mata. Bata samu ta runtsa ba sai data sallaci asubahi.
๛♥๛♥๛♥๛♥
Lambu ne mai tsananin kyau, yana ta tashin kamshin kyawawan nau'ikan furanni da aka shuka a wajen ga bishiyoyin fruits dangin su peach, strawberries, mangoes, guava, berries, dama wasunsu da dama sun nuna sosai. Hadari ne ya gangamo sosai aka fara walkiya mai karfi da rugugin tsawa, kafin kace me! An kece da ruwan sama kaman da bakin kwarya.....
Cikin sauri ta tashi daga kan kujerar da take ta ruga da gudu tana neman mafaka. Daga can nesa ta hango wani kyakkyawan farin mutum tsaye cikin furanni yana shafa su da kyawawan fararen hannayensa yana murmushi mai kayatarwa, inda yake sam babu ko dishin ruwa. Sai ta kara karfin gudunta har ta cimma shi...., cike da murna, tsantsar mamaki da tsananin farin ciki take kallon mutumin daya rikide ya dawo MARWAN!! Yayi fari sosai, yayi wani irin haske mai ban mamaki, gassu tausasa shimfide a kyakkyawar fuskarsa da kuma hannayensa, fuskarshi na fitar da wani irin sheki mai tattare da annuri... Sai ta fashe da kukan murna ta afka jikinshi gabadaya, yayi saurin kaucewa rungumar data kawo mishi yana girgiza mata kai a hankali, yace "A'ah Ameenah!! M not ur Muharram, m no more ur husband kin manta ne??" sai ta tsaya ta ta kura mishi ido a nutse, tace Marwannn....! Ya saki kyakkyawan murmushin nan nasa yace "nazo ne na miki godiya akan irin rikon da kike yiwa gudan jinina Al-Ameen, ki sani duk addu'o'in da kike yi mun suna zuwa gare ni kuma Ina jin dadin hakan. Sai dai ki sani bana farin ciki ko kadan da gudun aure da kike yi, me yasa kike yin haka Ameenah??" sai ta zube bisa gwiwarta tana kuka a hankali mai tsuma zuciya, tace "ina jin tsoron in sake yin wani auren in rasa damar sake haduwa da kai a gidanmu na gaskiya a matsayin ma'aurata!!" ya sake yin wani murmushin yace "Ameenah!! Kowane dan Adam da kike gani yana da kaddararsa, tamu kaddarar kenan muma don haka dole mu rungumeta da hannu biyu, kiyi hakuri ki daina kuka. Kin ga mata na sun zo, zan koma tare dasu..." ta daga kanta a hankali ta dubi wadanda Marwan ya kira da MATAN SHI! Duk iya kwatancen ta da lissafinta ta kasa kwatanta siffofin MATAN MARWAN! Abinda ta sani kawai shine matane masu wani irin haske marar misali wanda bata taba ganin kwatankwacinsa ba. Suka matso gare shi kowace ta kama hannunshi ya dubeta fuskarshi na dauke da murmushi yace "bye Ameenah, sai watarana.... Kin ga mijinki can, wanda zai kula dake fiye dani yana jiranki, Allah ya albarkaci rayuwar aurenku!!" Ameenah ta shiga girgiza kai tana kuka tana rokon shi akan kada ya tafi, wata sansanyar iska mai ni'ima ta fara hura ta, ta lumshe idanunta kadan. Budewar nan da zata yi sai wayam! Babu Marwan babu Matan shi!! Ta tashi da sauri tana waige-waige tana kwala mishi kira, ruwa ya fara jigata amma bata yi yunkurin neman mafaka ba.
Tana cikin waige-waige ta hango wani giant mutum ya juya mata baya hannunshi rike da bazara, a gefenshi wasu kyawawan yara ne suna ta wasanninsu cikin nishadi. Kamar wadda maganadisu yake ja haka ta ji ta tunkari mutumin kamar ba kafafunta take takawa ba. Tun kafin ta karasa gare shi ya juyo fuskarshi cike da annuri. A tsaye yake sosai, mutum ne wanda ilimi da baiwarwaki suke baiyane akan kyakkyawar fuskarsa mai cike da kwarjini, kalar fatarshi kuwa za a iya kiranta baka. Bayan wannan babu abinda zata iya karaswa game dashi...
Mutumin ya tare ta da wata runguma mai laushi, suma yaran nan sai suka rugo da gudu suka rungumeta suna kiranta da MUMMY!! Mutumin ya dauki daya daga cikin yaran ya sumbaci goshinta, ya mikawa Ameenah yace "karbeta ta Ameenatu.... Hasken idaniyar mu ce, gudan jininmu!" sai ta samu kanta da sakin murmushi, yayin da taji kaunar yarinyar ta mamaye mata zuciya. Ba musu tasa hannu ta amshi yarinyar ta rungumeta, mutumin ya kamo hannunta suka juya suna tafiya a nutse, wani kyakkyawan kerarran gida suka nufa dake cikin lambun, sauran yaran suka rufa musu baya.....!!
*******
A hankali ta fara bude idanunta, maimakon cikin lambu, sai ta ganta a dakinta, kwance akan gado! Tayi-tayi ta tuno fuskar mutumin nan amma ta kasa amma jikinta na gaya mata cewa tasan shi. Anti data jima a tsaye akanta tun dazu tayi gyaran murya tace Ameenah lafiya? Tayi firgigit ta kalli wajen da taji sautin ya fita, ita din ce dai. Ta bude baki a hankali idanunta cike da kwalla tace "mafarkin Marwan nayi Anti" ta zauna a gefen gadon ta kamo hannuwanta duka biyun ta damke cikin nata tace Marwan kika ce? Ta gyada kai kafin ta bata labarin duk abinda ta gani a cikin mafarkin.... Anti tayi shiru tana kallonta cikin nazari, can kuma ta nisa a hankali ta dubeta tace "me kika fahimta game da wannan mafarki? Ta runtse idanu a hankali tace "na fahimci kara yin aure na yana daya daga cikin dalilan da yasa Marwan ya tafi ya barni! Kuma shi kanshi Marwan din yana farin ciki da kuma na'am wa auren da zan sake!" Anti tace bayan wannan da?! Ta girgiza kanta a tausashe alamun babu. Anti tace tabbas auren nan yana nufin abubuwa da dama ciki har da mutuwar Marwan. Rabo! Rabo ajali!! (Aysha Kurah) ,kuma wani baya haihuwar dan wani. Don haka ki kara hakuri Ameenah kina jina? Ta gyada kai a sanyaye, jikinta yayi laushi tubus tun daga mafarkin da tayi. Anti ta shafa kanta tana murmushi tace to tashi kiyi wanka, it's past eleven already. Sai lokacin hankalinta ya dawo jikinta, tayi saurin kallon gefenta, wayam! Babu Al-Ameen, ta kalli Anti zata yi magana ta tare ta ta hanyar cewa "Uncle ya kaishi makaranta tun dazu" sai ta dan saki murmushi kawai ta tashi ta fada toilet. Yanzu ma haka ta tarar da bath tub cike da ruwa, an zuba wasu irin furanni a ciki yana ta tashin kamshi mai sanyi. Ta dan ja wani siririn tsaki don tasan aikin Anti ne, rariya ta bude ruwan yabi ta ciki ya fita ta sake hada wani ruwan ta matso kumfa ta shiga ciki. Kwanciya tayi a cikin ruwan ta lumshe idanunta, bata san iya adadin lokutan data bata ba sai da taji Anti ta kwankwasa mata kofa sannan ta bude rariya ruwan ya fita, ta dauraye jikinta ta fita. Ko mai bata tsaya shafawa ba ta saka jallabiya ta fito falo. Anti ce kawai a falon, ta karbi hutun karshen shekara ne a wajen aikinta. Kai tsaye dinning ta wuce ta hau daga kuloli, tsaki kawai take yi don kuwa gashin kifi ne da yasha magungunan data tsana, da wani irin kunun alkama da yasha hadin data rasa ko na menene, haka nan dai ta zauna ta dan tsakura ta tashi ta koma dakinta. Gyale ta yafa ta saka wani flat sandal na roba ta fita, unguwan ta shiga zagayawa da kafa saboda damuwa da kadaici da suka dameta. Anti Rukky ta kira ta suka sha hirarsu amma bata yi mata zancen daya danganci aurensu ba, itama sai bata tada maganar ba. Sai data je makarantar su Al-Ameen ta dauko shi sannan ta koma gidan. Da dare duk suna falo tana koyawa su Asleem assignment, Al-Ameen na gefe ta tura mishi puzzle piece na haruffan larabci yana ta bugawa. Uncle da Anti suka fito daga dakin Uncle din, Anti Jameelah ta wuce kicin zata hada mishi dinner shi kuma ya zauna akan kujera yana kallon Ameenah fuskarshi dauke da murmushin tsokana, yace "Amarya... Amaryah....!!" nan da nan annurin fuskarta ya bace bat kamar daukewar ruwan sama. Ta wani cune dan bakinta gaba kamar gidan tsutsa tana kunkuni, Uncle ya fashe da dariya. Anti ta fito daga kicin da tray a hannunta ta zauna a gefen Uncle ta fara serving dinshi, jefi-jefi suna hirar bikin Ameenah. Haushi ya cikata yazo mata wuya, sai kawai ta tashi ta sungumi danta ba tare data kara kallon su Uncle din ba ta nufi dakinta. Uncle ya kira sunanta, "Ameenah!" yana kokarin danne dariyar data kamo shi. ta dakata ba tare data juya na, yace "ki fara shiri nan da kwana uku zamu tafi Nigeria saboda kwanaki shida suka rage daurin aurenku" ta juya tana kallonsu kamar zata yi magana, sai kuma ta fasa kawai ta gyada kai ta tura kofar dakinta da sauri ta fada, suka bi bayanta da kallo cike da alhini. Bayan kofar tabi ta sulale a hankali, tasa duka tafukan hannayenta a fuskarta ta fashe da wani irin matsanancin kuka zuciyarta na mata zogi, sai da tayi ya ishe ta kafin ta lallashi zuciyarta ta tashi daga bayan kofar. Ta shimfide Al-Ameen akan gado, ta zauna a tsakiyar gadon ta kura mishi ido tana kallonshi cikin tunanika daban-daban, iri-iri, kala-kala.....!!.
©Jeedderh🐾
[5/2, 11:05 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•47•°🐾
Ana washegarin zasu tafi Nigeria, komi na tafiyarsu ya kammala. Duk wasu kaya na sakawa a gida tun daga kan furnitures, kitchen wares, kai hatta da cokali daga India aka saye shi, tuni Uncle ya auna su zuwa Kano. Anti kuma ta dage da kimtsa ta abinda ya danganci gyaran jiki ciki da waje, jiya ma a Dulhania Saloon suka yini, wata shahararriyar mai gyaran jiki Xehrah Mahendi ta yaryarawa Ameenah kunshi sannan ta mata gyaran jiki dana gashi. Ta fito sak a amarya kuwa. Yanzu ma tana zaune ne kawai tana karewa lallen hannunta kallo, ya zanu ya matukar yin kyau. Anti ta shigo dakin hannunta rike da silver bowl karama data dama tukudi a ciki yasha kwakwa da dabino, zuma har dasu cikwi. Ta mikawa Ameenah, maimakon ta amsa sai ta cuno baki, tace kina yiwa Allah Anti ki daina dura min kayan nan haka, baki san irin wahalar da nake sha ta dalilinsu bane. Anti tayi dariya tace ashe dai suna aiki, daidai kenan. Ke kin fi so ne kije masa salam ba taste kamar ruwa? Ina so ne in sa surikin nawa ya gigice, ya kasa tantance wai Budurwa ce ne ko kuwa Bazawara??!
Ameenah ta kara turo baki tana wani hura hanci, tunda taji cewa Abdul-Rasheed Modibbo ne angon ta sanya ranta a inuwa akan abinda take kulafucin kada wani ya dandana bayan Marwan. Tace Anti kina yin abu kamar baki san halin Modibbo ba? Anti tace sanin halin nasa ne yasa nake so na rikita shi da fatar jikin ki ma kawai kafin akai can ciki.... Ai ke dai Allah ya nuna mana ranar auren nan lafiya mu sha bidiri. Maza ki shanye tun kafin ya sha iska. Ta amsa tana yamutsa fuska kamar wadda ta amshi kashi, Anti tace eyh, koma me zaki yi dai sai kin shanye shi tass kin bani kwanon nan Ina tsaye a kanki!! Ita karfin halin Antin ma sai ya dawo bata dariya, dole ta murmusa ba don ta shiryawa hakan ba, Anti tace to ko ke fa, Amaryar mu??!.
*GOMBE....*
kwance yake akan irin wooden couches dinnan na hutu da aka tanada a gefen swimming pool din dake cikin Vomella Hotel dake cikin Gombe, Modibbo ne yake sana'ar tashi (tada hayaki). Da yammar nan ya iso Gombe bisa aikowar mahaifanshi, sun ce yazo su kara fahimtar juna shi da amaryar tashi su kuma tsara yadda bikin nasu zai kasance. Wannan wata babbar dama ce a gare shi ta wargaza zancen bikin cikin ruwan sanyi ba tare da sunan shi ya fita ba, don haka koda ya karaso Gombe bai tunkari gidan su amaryar ba ya nemi babban hotel ya kama. Ya bari sai gobe ido na ganin ido zai je ayi ta ta kare, ya huta da wannan makalallen auren, in yaso daga baya sai ya nemo mace wadda yake ganin ta dace dashi, karfaffa ba irin wannan er shalau din ba kamar igiya, wadda yake ganin duk ranar da tsautsayi yasa ya rutsa da ita ya dora mata nauyin kirjinshi, sai dai wata amma ba ita ba, don kuwa raga-raga zai yi da ita. Don haka Allah-Allah yake gari ya waye yaje su hadu, shi kadai yasan kudirin dake ranshi.
*****
Ta 6angarenta ma jiran zuwan shi kawai take yi, tana tunanin cewa tana da wata dama ta karshe da zata kashe zancen auren nan ya mutu murus, tana jin cewa zata iya zaman aure da kowa amma banda mai baudadden hali irin Modibbo!
Koda sakon zuwanshi yaje mata a washegarin ranar, bata ji ko dar ba ta zari gyalenta ta tafi har wani harbin iska take yi, zuciyarta na gaya mata wannan shine 'The End' na zancen aurenta. Tasan cewa Modibbo baya daukan raini ko kadan, kuma baya son wulakanci, to abinda tayi niyar yi mishi kenan, tasan cewa idan tayi haka to babu yadda zai ci gaba da auren nan tunda tasan cewa shima ba son auren yake yi ba. Anti ta bita da kallo cike da faduwar gaba, Ameenah must be up to something, tasan ruwa baya tsami banza. Farin cikin dake shimfide akan fuskarta abin tambaya ne, sai ta shiga addu'ar Allah yasa ba ruwa zata ballo musu ba don tasan halin su biyun kamar yunwar cikinta.
Yana cikin motar da yazo a cikinta Discussion Continues sanye da suits na wani cotton mai tsananin taushi maroon color, yasa bakin tie da bakin cover shoe, rigar ta sama ya ajiye akan kujerar mai zaman banza ya bar er ciki fara kawai, fuskar nan tasha wani makeken sun glass na Prada wanda ya mamaye rabin fuskar. Kafarsa daya na cikin motar daya na waje, idanunshi nakan kofar sashen su yana jiran fitowarta.
Can sai gata ta bullo tana takun nan nata mai daukar hankali, cike da natsuwa.....
Bai gasgata abinda idanuwansa ke hango masa ba har sai daya kai ga zare gilashin idonsa ya runtse ido na dan lokaci, ya sake budewa, but still, ita din dai yake gani tana tunkaro shi. Yarinyar nan fara... mai zubi da kira mai kyau... Aljanar shi... Wacce gani biyu ya taba mata a rayuwar shi amma ta cigaba da zuwar mishi cikin mafarkinshi!! Kar dai??... Ko dai....???! Ya shiga girgiza kansa cikin wani irin yanayi, sam ya gaza tantance halin da zuciyar sa ke ciki, farin ciki ko akasinsa??
Gare ta kam, tunda ta tunkaro shi taji gabanta na bugawa sosai, wani irin kwarjini ya mata marar misali. Sai dai ta kasa tantance ma'anar kallon da yake jifanta dashi wanda tafi kyautata zaton shine ya haifar mata da faduwar gaban. Har ta matso kusa dashi idanunshi na kanta cikin wani mayataccen kallo kamar wanda ke son gano wani abu a fuskarta, ba zato ba tsammani taga yaja murfin motar ya rufe garammm! Kamar tashin duniya, ya kuma warci motar a dari da tamanin ya bar gidan. Sai tayi turus tabi motar da kallo bakinta a bude, da salon rashin mutuncin da yazo dashi kenan? Ai kuwa daidai kai ka samu. Tana daga idonta ta hango Kawu Hamza a tsaye daga can kofar sashen shi, babu mamaki ya ga duk abinda ya faru a tsakanin su, bata nuna alamun ta ganshi ba ta hau matse hawayen karya zuciyarta fal farin ciki, tasan Kawu Hamza will not stand it.
Kawu Hamza kam iya shaka ya shaka sosai, wannan wane irin wulakanci ne surikin nasu yazo dashi? A fusace ya koma cikin gida ya lalubi waya ya dannawa Mukhtar kira, yace lallai-lallai ya nemo Modibbo duk inda yake a garin Gombe yana nemanshi, bai kara ko a ba ya kashe wayar ya bar Mukhtar cikin faduwar gaba da tambayar kanshi lafiya???
©Jeedderh🐾
[5/2, 11:05 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•48•°🐾
Modibbo kuwa Allah ne kadai ya kaishi masaukin sa lafiya, ya shige dakinsa ya kulle da makulli ya hau kan gado ya kwanta ruf da ciki idanunsa a runtse gam. He still couldn't believe what he'd seen, did he really saw ha? Was it not illusion?? Kai ko dai mafarki yake yi ne? Nan ya tashi zaune ya fara mintsinin tattausar fatar hannunshi, da alamun dai da gaske ne hakan ya faru.
Yana cikin wannan halin kiran Uncle Mukhtar ya shiga wayarshi, a kasalance ya daga, ya tambaye shi yana ina? Sai ya rasa abinda zai ce, babu mamaki yayi witnessing rashin mutuncin daya zabgawa Ameenah ne yanzu, da kyar ya lalubo abin fada, yace "ina nan asibitin fata na Gombe, dama akwai wasu ayyuka da zanyi acan din to kuma yanzu har na shigo gida zan ga Ameenah sai aka min emergency kira, shine na tafi tun gabanin mu gaisa., yanzu haka ina shirin shiga tiyata ne ka kira ni!" Uncle yace to Allah ya kyauta, dama Kawu Hamza ne yace a kira ka yana nemanka, bari in sanar dashi. Suka kashe wayar a lokaci daya. Modibbo ya sake wata kakkarfar ajiyar zuciya fuskarshi dauke da murmushi, so it's her! Yarinyar data hargitsa mishi tunani ta mayar dashi wani gaula! Ashe bakar yarinyar nan ce, ita ce Ameenah. Farin ciki ya cika shi ya rasa me ma zaiyi? Ba zato ya kwala wani kakkarfan ihu, ya fara birgima akan gadon yana ihu kamar wani sintacce, daga karshe ya diro daga gadon dalilin kiran sallah da aka yi, ya shiga toilet ya dauro alwala ya fita zuwa Masjeed. A can ma bayan an gama sallah mikewa yayi ya fara jero nafilfili yana mai godewa Allah bisa wannan kyauta daya mishi, da ace ya 6ata auren nan tuntuni da hakika ya kasance cikin dana sani mara amfani for the rest of his life, and he wouldn't be able to forgive himself idan yayi hakan!!
Da misalin karfe biyar na yammacin ranar, tsaye yake a gaban dressing mirror. Wata shadda ce getzner ruwan makuba da aka mata dinkin Abacha a jikinshi, ta mishi kyau sosai yadda kasan bashi ba, ya dora karin hula ta zauna mishi das, turarukan daya fesawa jikinshi kuwa basu da adadi. Kanshi yake karewa kallo yana son ganin ta ina zai ga wata makusa? Amma bai gano komi ba, ya saki kayataccen murmushi tare da daukar makullin motar shi ya fita. A nutse yake tukin zuciyar shi na azalzalarshi da son sake ganin Ameenah. Tunanin ta sigar da zai je mata yake yi, matsayin masoyi? Ko kuwa wanda zai aureta kawai? Da wadannan tunanikan ya tura kai falon Kawu Hamza bakin shi dauke da sallama, Uncle Mukhtar ya biyo shi a baya.
Tana sashen Yaya Abdul-Hadi ana ta shirye-shiryen walimah da za ayi gobe da safe anan farfajiyar gidan. Tana zaune ne kawai, amma sam tunaninta baya tare dasu, ta cilla wata duniya ta daban. Imran dan gidan Ya Abdul-Hadi ya shigo inda suke da gudu yana kwala mata kira, ta dube shi tana dan murmushi tace ya aka yi ne Imu na?? Yace Kawu Hamza yana kiran ki. Gabanta kam ya fadi sosai, ta tambayi kanta me ya faru? Haka nan dai ta mike ta tafi cike da taraddadi.
A falon na Kawu durkushe take a gabanshi cikin dar-dar kamar ace mata at! ta fece da gudu, ta dan saci kallon Modibbo daya nutsu sosai a gaban Kawun kamar wani kamilin gaske, shima ita din yake kallo. Tayi saurin kau da kanta gefe bayan ta auna mishi harara. Kawu yayi gyaran murya ya dubesu yace "dalilin tara ku anan wajen ba wani dalili bane sai don na kara tambayarku game da ra'ayin juna musamman ke Ameenah, bana so daga baya wani abu yazo ya faru a kuma zo ana kuka gani. Don haka Ameenah menene ra'ayin ki game da wannan aure? Kina da matsala dashi ko kuwa??" ta ciza tattausan lebenta na kasa cike da wani irin murmushi, babu mamaki Allah ne ya dubi halin da zata shiga ya kawo mata wannan kyakkyawar damar. Babu jin ko dar game da hukuncin data yanke tace "zan amince Kawu, a bisa sharadi daya; idan har ya amince da zaman Al-Ameen tare dani, ba kuma zaman agolanci ba to babu damuwa daga bangare na, na amince!" Kawu ya maida kallonshi ga Modibbo da zufa ta yanko mishi, yace to kai kaji abinda Amaryar taka tace, shin ka amince??
Ya saci kallon inda take zaune, kanta na kasa amma yana hango wani kwantaccen murmushin mugunta a bisa fatar bakinta, nan ya kamo bakin zaren. Ya dage gira sama, wato abinda ta kulla kenan? Tana tunanin idan tayi hakan zai ki amincewa ne? Ai kuwa idan hakane u're wrong Ameenah! Ba wai da daya na, idan ma duka duniyar ne zaki tare da ita a gidana I will accept u, as a wife and they, my children.., ganinki kawai tare dani babban makami ne na kare kaina daga bacin rai.
Sai yayi murmushi ya kalli Kawu daya zuba mishi ido yana jiran amsar shi, yace Kawu na amince, na kuma yi alkawarin rike shi amana tamkar dan dana haifa a cikina!.
Fuskar Kawu ta washe da farinciki sosai, yace Masha Allah! To ke Ameenah kin dai ji abinda yace. Allah ya gani na fita hakkin ki, don haka aure babu fashi. Jibi war haka an daura In shaa Allah!! Ku tashi kuje na sallame ku, Allah ya muku albarka. Yadda kasan wadda aka bugewa kafafu haka Ameenah ta mike da kyar, jiki a sanyaye ta fita. Ya kara dukawa yawa Kawun sallama ya rufa mata baya da sauri. Kawai ganin mutum tayi ya tari gabanta, taja ta tsaya ta kama kugu tana kallon shi fuskar nan kamar wadda taga mala'ikan mutuwa. Tace malam lafiya? Ya daga kafada, ita ta kawo haka malama! Naga Kina shirin wucewa ne ba tare da kin tsaya mun tattauna yadda zamu tsara bikin mu ba. Ta kara tamke fuska tace "Malam ni babu wani biki da zanyi, idan kai kaga zaka iya sai kayi amma fa ba dani ba" yace "ahhhh! Sai Yanzu kika tuna min. Ashe fa matar tawa ZAWARA ce! Su kuma Zawarawa ba ayi musu biki irin na 'YAN MATA..... Well, ki godewa Allah ma zaki samu albarkacin 'yanmatan da za a hada ku tare dasu ayi shagalin biki mana, don haka dole zaki je duk bukukuwan da za a gudanar" tace dalili?? Zuciyarta cike da takaicin kalmar Zawara daya kira ta da ita. Yace "dalili? Saboda nima zan je, idan har zan je ya zamar miki tilas kema kije!" taja tsuka, "to ba zan je din ba, sai dai idan gawana za a cicciba akai wajen bikin". Ta bi ta gefenshi zata wuce, ya janyo hannunta da karfi ta dawo gabanshi suna fuskantar juna, ya maida fuskar shi ya dinke tsaf daga sassauta din da yayi. Yace watch your mouth Ameenah, don ina shirin zama mijinki ba wai yana nufin zan zauna ne ina fadar magana kina mayar min gatsar babu respect ba kin gane? Yasa hannu a aljihun shi ya ciro bundles na dubu ya kamo hannunta ya dora mata su, "ga wannan kiyi hidimar biki dasu ke da kawayen ki, ni yau zan koma Kano in shaa Allah gobe zan juyo tare da abokai na, Jibi a daura aure in dauki er Bazawarar Amarya ta mu tafi Kano....!" Haushi ya kawo ta wuya, anya yasan irin dafin dake tattare da kalmar nan tashi ta zawarci? Ba zata iya jura ba..., da gudu tabi ta gefenshi tayi part din Yaya Abdul-Hadi. Ya bita da kallo yana jin kamar ya bita ya kamota ya rungumeta ya lallashe ta don yasan ya bata mata rai sosai, sai dai idan yayi hakan ya bada kanshi da wuri, ya kula yarinyar sai an biyo da ita ta bayan gida kafin a daidaice da ita, ya kada kanshi ya fada mota ya mata key ya dauki hanyar Kano, to sauka lafiya!
Can kuryar dakin Anti Nadiya ta shige tana huci kamar wata tsohuwar zakanya. Anti Jameela ta biyo bayanta don ganin yadda ta shigo a gigice, ita kuma daidai lokacin tayi jifa da kudin, Anti ta cafe su ta waro ido a kansu tace "yauwa! Angon nan naki yasan yayi abu at d ryt time, kamar dama yasan tunanin inda zan lalubo kudin da za a sayo kulolin da zaa raba a wajen walimah nake don na hannunmu sun kare tun a cikin gida, kin ga sai a karo da wannan!" ta juya ta fita tana kwalawa Sadi kira. Ameenah ta bita da kallo cike da takaici, tana jin kamar taje ta kwace kudin ta yayyaga su gutsi-gutsi.
☆**☆**☆**☆
©Jeedderh🐾
[5/2, 11:05 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•49•°🐾
Karfe takwas da rabi na daren ranar a cikin farfajiyar gidansu ta mishi, ya kashe motar ya fito cikin wani nutsattsen taku fuskar shi na dauke da kayataccen murmushi, jinshi yake kamar wanda aka yiwa albishir da gidan Aljannah. Yayi sallama a kofar falon tare da tura kofa ya shiga a lokaci guda, Ummie da Safeenah ne kawai a falon da alamun suna sirrantawa ne, baki en biki wadanda suka zo suna sashen baki har sun kwanta. Ya zauna akan kujera kusa da Ummie yana wasa da makullin motarshi, farin ciki da dokin dake fuskar shi sun kasa boyuwa. Cike da mamaki suke binsa da kallo, kamar kuma suna doubting anya Modibbo ne kuwa? Yanayine da basu taba ganin irinsa a tattare dashi ba, hatta da mahaifiyarshi kuwa a iya tsawon rayuwar ta. Safeenah tace Yaya wat happened? U look so happy, jubilated...me ya faru ne hmm?? Ya kara sakin wani tattausan murmushi triumphantly, feeling so high. Sai Biebie ta kara sake baki tana kallonshi cike da mamaki marar misaltuwa, bata taba ganin Yayan ya murmusa haka ba. Mutumin da sam ganin murmushi a fuskarsa na en sakanni ne amma ji yadda yake ta murmushi tunda ya shigo, kana iya hango tsabar Farin ciki da murna shimfide a kwayar idanunsa, gashi nan kuma zane baro-baro a fuskarsa. Ta tabbata koma meye ya faru ba karamin al'amari bane. Yace babu komi Safeenah Amarya, kawai ina cikin muuudu mai kyau ne kawai. Ummie tace ya aka yi ka dawo yanzu? Yace gobe in shaa Allah zan koma tare da abokaina. Tace to Allah ya kaimu ya amsa da ameen Ummie, bari in je in kwanta, m extremely tired wallahi, very tired!! Ummie tace gashi Mukhtar yace a tambayeka a inda za a kai kayan Ameenah, gobe zasu iso daga India. Yace a kaisu gidana na Lamido crescent, acan zamu zauna. Ummie ta gyada kai, "amma da kake cewa ba zaka zauna acan ba?" dariya kawai yayi ya tashi ya musu sai da safe, Safeenah tace Yaya Ango!! Cike da tsokana, tasan cewa harara ce zata biyo baya don kuwa baya son sunan ko kadan. Amma ga mamakinta sai ya watso mata fararen hakorannan nashi tas-tas dasu har wani reflecting suke, yace haka yake amaryar mu Safeenah...! Ya fita daga falon yana en wake-wake cikin nishadi. Suka bishi da kallo suna tattaunawa game da canjin da suka gani tare da Modibbo kamar bashi ba.
Yana shiga daki ruwa ya fara watsawa, bayan ya fito daga wanka ya zura kayan barci ya dauki waya ya samu gefen gado ya kwanta ya shiga kiran abokanshi yana fada musu daurin auren shi Jibi ne, duk sun sha mamaki suka yi ta mishi korafin kin sanar musu da wuri da yayi, hakuri kawai yake basu yana cewa daurin auren ne yazo kai tsaye shi yasa. Wasu sun ce a goben zasu bishi, wasu kuma suka ce sai ranar daurin auren zasu je, wasu kuma suka ce idan amarya tazo zasu je su gaisa. Dariya yayi yace ko basu zo ba ya gode da fatan alkhairin da suka mishi.....
Farfajiyar gidan ta Wakili's estate cike take da manyan canopies marassa adadi, babban guri ne da aka tanada musamman saboda shagulgula irin wannan. Amaren guda uku sun sha adon riga da siket na wani tattausan yadin silk sky-blue, Anti Jameelah ce tayo musu shi daga can India, sai aka dora musu alkyabba baka a jikinsu. Suna zaune akan wasu kujeru na alfarma sun fuskanci dubban jama'ar da halarci taron walimar auren su zazzaune akan fararen kujerun roba a karkashin canopies din. En jaridu da masu daukar hoto na gefe suna daukar hotuna, Wakili's Family babban family ne daya tara manyan en kasuwa, en siyasa, ta bangaren army ma ya tabo manya, family ne wanda ciki da wajen Gombe babu wanda bai san da zaman su ba, daidai gwargwado mutane suna girmama su. Muryar Malama Atika Abubukar ta karade wajen da sautin Wa'azinta ta hanyar lasifika, tayi magana akan hakkin miji akan matarsa da hakkin mata akan mijinta da kuma hakkokin da suka rataya akansu su duka, ta tabo mafi yawan matsaloli da ma'aurata suke fuskanta a wannan zamanin da kuma hanyoyin da take gani yakamata abi domin a magance su. Da yawan matan dake wajen jikinsu yayi sanyi sosai da wa'azin malamar, suma amaren jikinsu a matukar sanyaye yake saboda tunawar da suka yi cewa gobe war haka fa wani nauyi ne zai hau kansu wanda shi zai yi sanadin zuwansu Alanna idan sun sauke shi ta hanyar data dace, kuma dai wannan nauyi zai iya kaisu zuwa wuta idan har basu kiyaye dokokins sa ba. Ameenah kuka take yi sosai, tana rokon Allah akan yasa ta yiwa mijinta biyayya irin wadda Malama Atika tace mace na yiwa mijinta, tana tsoro! Tana tsoron zuciyarta, tana tsoron zuciya ta hana ta bin mijinta Allah ya jefata cikin azabarsa.
Daga karshe Malamar ta rufe taron da addu'a da fatan alkhairi ga Amaren, aka watse daga taron bayan an bi duk wanda yazo wajen da jaka irin ta biki mai dauke da sunayen duka amaren da angunansu, akwai kula a cikin jakar itama da sunayen couples din, kowa ya tafi yana musu fatan zaman lafiya mai dorewa.
Aka bar Ameenah a zaune har zuwa lokacin tana kwararar da hawaye cike da alhinin irin sabuwar rayuwar da zata shiga gobe. Sauran amaren kuwa tuni sun shige cikin kawayensu suna gaisawa dasu don haka babu wanda ya kula da halin data shiga. Ta mike a hankali take tafiya, kanta na masifar sara mata sam bata da karsashi. Can kuryar dakin Anti Nadiya ta shige ta kulle kofa ta kwanta ba don tana jin barci ba, Al-Ameen yana wajen Ya Faruq don haka bata damu data nemi inda yake ba. Har zuwa lokacin da nata angon ya iso tare da zugar abokanshi cike da dokin sake dora ido akan kyakkyawar fuskar ta, yau kawai da bai ganta ba zuciyarshi a matukar galabaice take. Amma neman duniya aka rasa Ameenah a cikin gidannan, an kuma kira wayarta aka ji a kashe. Sai jikin shi yayi wani irin sanyi, duk yadda yaso ya boye damuwar ranshi game da ita abin yaci tura, bai san me yasa ba yarinyar na da wani irin tasiri a ranshi wanda yasa sam bashi da wani katabus muddin akanta ne. Abokanshi sun lura da halin daya shiga a take, very disappointed, missing his bride very badly. Sai suka shiga mishi tsiya, wai ya daure mana, yau ne kawai ya rage, gobe war haka suna tare ta zama tashi. Hakora kawai ya dinga watsa musu cikin yake, don kuwa can kasan zuciyar shi is aching him, ita kawai yake son gani. Kawai sai suka shiga cikin sauran angwayen ana ta hirarraki da en matan amare, Sai bayan magariba suka bar gidan.
©Jeedderh🐾
[5/2, 11:05 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
*A LOVE STORY SEALED WITH CHALLENGES.....*
🐾°•50•°🐾
Ameenah bata fito daga dakin ba sai da tara na dare ta gota, tun lokacin tana kwance babu abinda take yi sai kuka da tunanika, idan an kira sallah zata tashi tayi tunda akwai toilet a cikin dakin. Dama dai ba a zancen abinci, rabon data saka wani abu a bakinta tun wani tukudi da Anti Nadiya ta takura mata tasha da safiyar ranar, bayan shi bata ci komi ba, kuma bata sha'awar cin komi.
Su Anti Jamila na falon suna hira lokacin data fito daga dakin, idanunnan nata sun kada sosai. Cike da mamaki suke bin ta da kallo, sam basu yi tunanin tana dakin ba, ko kadan ma hankalinsu bai kawo zata je wajen ba tunda ba a cika ta'ammali da dakin ba. Anti Jamila ta kalleta tace baki da lafiya ne Ameenah? Ta girgiza kanta a sanyaye amma bata ce komi ba, Anti Nadiya tace tun dazu Ammie da Faruq ke neman ki, Al-Ameen yayi ta kuka da bai ganki ba. Sai lokacin tayi magana cikin shakakkiyar murya kamar wadda mura ta kama, tace can zan je yanzu. Ta juya a sanyaye zata fita, Anti Jamila tace kin kuwa ci abinci Ameenah? Ta juyo tana kallonta fuskarta dauke da dan murmushi duk don ta kore damuwar data hango zane baro-baro akan fuskokinsu, tace manta da abimcin nan Anti, a koshe nake. Sai da safen ku.... Ta karasa fita da saurinta.
tun daga nesa ya hango ta tana tafe a hankali kamar wadda kwai ya fashewa a jiki, ya saki wata irin doguwar ajiyar zuciya wacce bai ma san yayi ta ba. Tun komawarsu hotel din da yayi masauki shi da abokansa, gabadaya zuciyarshi ta rasa sukuni. Iya dauriya yayi amma abin ina, kasa daurewa yayi wai har sai gobe ne zai ganta, gani yake yi idan ya wayi garin gobe ba tare daya saka Ameenah a kwayar idanunsa ba, babu mamaki a tarar da gawarsa a daki. Ya rasa irin mayataccen son da yake yi mata, da dai abin bai kai haka ba amma tunda ya sake ganinta for the third time, ya sake rasa sukunin shi, daidai da sakan daya tunanin Ameenah yaki ya kyale shi, komi yake yi tare da tunaninta yake yin sa. Ba shiri ya dauki makullin mota ya taho gidan don Anti ta tabbatar masa cewa lallai Ameenah na cikin gidan.
Ba zato taji an ja hannunta anyi gefe da ita, baki ta kware da niyar kwala ihu taji ansa hannu an rufe mata baki, a lokaci guda kuma aka ce "shhhh!!!" manyan idanunta da suka canza kala ta daga a hankali ta kalleshi, inda suke babu wadataccen haske. Duk da cewa bata ga fuskarshi ba, amma ta dauki muryar shi. Cikin sauri ta ture hannunshi daga bakinta ta fita fili wajen haske, ya biyo bayanta ya tsaya a gabanta suka fuskanci juna. Ya matsa daf da ita kamar wanda ke son shigewa jikinta, yace ina kika shiga tun dazu muke ta nemanki? Ta dan matsa baya kadan, cikin tamkewar fuska tace bana tunanin abu ne wanda ya shafe ka sanin inda naje din!. Ya daure fuska, "ban gane ba? Kin kuwa san irin kunyar da kika bani dazu? Nazo da tarin abokaina suna son ku gaisa amma aka neme ki aka rasa, kin san irin muzancin dana shiga lokacin?" tace Wannan ba damuwa ta bace Modibbo! Plss idan baka da wani abin cewa excuse mee... Kaina yana sara min. Ya bude manyan idanunshi akanta, hakan ya janyo mata jin wani irin kasala a jikinta. Yace me yasa ne baki da kunya ko kadan Ameenah? Me yasa sam baki san inda ya dace da wajen da bai dace kiyi rashin kunya ba??" baki ta murguda tace ina ga ai kai ka tari rashin kunyar, Kai ka shiga harkata da rayuwata don haka indai rashin kunya ne to yanzu kuwa ka fara gani!. Ya dage gira sama, "Allah da gaske? To Dan Allah sake yi mun rashin kunyar yanzu mana ki gani, zanyi maganinki anan take wallahi, don't try me Ameenah I don't tolerate sh**t da kike gani na nan!!". Kashedin ya shige ta sosai ya kuma fadar mata da gaba, amma hakan bai hanata bude baki cike da jarumtaka ba tace anyi maka rashin kunya din, kayi duk abinda zaka yi....!!" babban yatsan hannunshi na hagu ya hada da yatsan tsakiya ya sakar mata su a baki, ba shiri ta sanyawa bakinta kwado, tasa hannu ta dafe wajen Saboda tsananin zugin da yake mata. Kan kace meye wannan? Hawaye sun fara zarya akan kumatunta kamar an bude famfo, dariya ce ta kusa kamoshi, lallai yarinyar nan a shagwabe take. Murya irin ta wanda ke son fashewa da kuka tace "Allah ya isa na mugu! Kuma ma auren an fasa tunda kai mugu ne!!".
Ya saki murmushi sosai yace "very good! Da kin kyauta min sosai kuwa, kuma Ke zaki yiwa kanki babun badinahu. Kin dai san ko yanzu kika fasa aure na to a goben ko mata hudu nace zan aura ba zan rasa ba, saboda ni saurayi ne sabon jini, fresh guy babe! Sabanin second hand. Ke kanki kinsan bacin kaddara babu abinda zai yi hadin saurayi da Bazawara!!". Sai ta damke bakinta da hannu ta falfala cikin gida da gudu don kuwa ta tabbata idan ta bude bakin to kuka zata fashe dashi, abinda kuma bata so kenan; ya gano weak point dinta.
Shi kam binta yayi da kallo har ta shige cikin gidan, ya shafa sumar kanshi yana murmushi cike da nishadi marar misaltuwa, yace "yarinya ki gama duk kewaye-kewayen ki da rashin kunyar ki, gobe war haka nasan tuni na kashe bakin tsanyar" ya fada motarshi ya fita daga gidan a nishadance.
Sai data tsaya a bakin kofar falonsu ta share fuskarta sannan ta shiga ciki, ba kowa a falon don haka ta shiga dakin Ammie. Tare ta same ta da wasu daga cikin en uwansu da suka zo bikin, ta gaishe su suna ta tsokanarta. Alfarmar ta musu yaken murmushin data saba ma yau basu samu Ba. Ammie ta dinga bin ta da kallo har ta iso wajenta, tace Auta nah kin kuwa ci abinci? Karya ta mata tace Ehh. Ta gyada kai tace to Maza kije ji kwanta dare yayi, da ganin ki kuma kina bukatar hutu. Sai da safe ta musu ta juya ta tafi dakinta, akan gado ta samu Al-Ameen a kwance yana barci, tayi murmushi ta shafa sumar kanshi tare da sumbatar goshin sa. A hankali ta haura kan gadon ta kwanta tare da rungumoshi zuwa jikinta, fatan ta daya Allah yasa kada Ammie ta hanata tafiya da Al-Ameen idan zasu tafi Kano gobe, ta lumshe idanunta har barci ya dauketa.
*_Washegari...._*
Qarfe goma sha daya na safe aka daura auren Amaren hudu, da yake gabadaya aka hada auren aka daura har na Safeenah saboda Alhaji Abbas yace kada a wahalar da mutane kawai a daura anan, Ana daura auren maza suka zarce da reception a Vomella Hotel, yayin da aka dauko Amarya Safeenah daga Kano aka taho Gombe da ita saboda ta samu ta halarci dina da za ayi da dare.
©Jeedderh🐾
[5/2, 11:06 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•51•°🐾
Tunda taji an daura aure jikinta yayi wani irin sanyi marar misaltuwa, gado ta haye saboda zafi da jikinta ya dauka ta dukunkune a cikin bargo tana rawar sanyi. Anti Jameela ta shigo dakin ta same ta a halin da take ciki, tayi salati tana tafa hannu ta nufeta da sauri, ta tsorata da halin data ganta. Tace Ameenah kan ki kike so ki kashe ne?? Ta fita da sauri sai gata ta dawo da kwano da magani, ta taimakawa Ameenah ta tashi zaune, da kanta ta dinga bata abincin tana lallashinta cikin tausasa murya. Ya Faruq ya shigo dakin sanye da bugaggiyar bakar shadda, ta daga ido a hankali tana kallon Yayan. Wani irin haske da annuri ne kawai ke fita a fuskarshi, lallai shekin angonci daban yake. Ya zauna a gefen gadon ya dan dafa goshin Ameenah yana tambayar Anti ya jikin nata? Tace mishi zazzabin ya dan sauka yanzu. Ya amshi magani a hannun Anti ya durawa Ameenah a baki Anti tabi da ruwa, suka shiga bata kalamai masu taushi sai gata tana murmushi. Shi da Anti suka yi dariya a lokaci guda, Faruq yace toh ko ke pha Auta?? Maza tashi ki wa baby wanka a shirya min shi, mu je mu taro amarya ta dashi tana kan hanya. Ameenah tayi dariya ta sungumi Al-Ameen dake barci a gefenta ta shige toilet, su Anti suka fita suka ja mata kofar dakin.
Ta wanke Al-Ameen tas wanda sanyin ruwa ya farkar dashi ya bude ido tangararas yana kallonta yana mata wasanni wadanda suka saba idan tana mishi wanka. Ta biye mishi itama, baka jin komi a lokacin sai sautin dariyar su. Ta nade shi cikin towel suka fito, daidai lokacin Anti Hadiza yayarta ta fado dakin, tace yauwa Anti ga dana ki shirya min shi, bari inyi wanka" ta koma bandakin Anti kuma ta dauki Al-Ameen ta fara shirya shi.
Lokacin data fito har Anti ta gama shirya shi cikin tattausar farar shadda irin ta jikin Faruq, sai tashin kamshi yake. Ameenah ta rungume yaron tana jin kaunar shi sosai a jikinta. Ta dago shi daga jikinta tace kayi kyau yaro na! Yayi dariyar shi mai kyau dimples dinshi suka lotsa sosai, yace Ke ma mommy. Dariya tayi ta nutsa yatsar ta a kumatun shi inda ya lotsa tace Love yah baby. Gaban mirror ta koma ta shafa mai, ta zira rigar sallah a jikinta ta sallaci azuhur. Sannan ta dawo gaban mirror ta zauna ta fara shafe-shafen hoda, duk da ba wata kwalliyar azo a gani tayi ba amma kyawunta ya fito sosai. Tana cikin zira gown din atamfa da Anti Hadiza ta fitar mata na ankon su, Antin ta sake shigowa da plate a hannunta, tace baby Al-Ameen Faruq yana jiranka a falo. Ya fita da gudunsa yana wa Ameenah bye.
Ta mikawa Ameenah plate din tace "amshi ki cinye yazo Auta" ta kalli plate din farfesun kaza ne yana ta kamshin daddawa da tafarnuwa mai dadi, ta cuno baki kamar zata yi kuka tace "wai farfesun ne again?? Ni pha na gaji da cin abubuwan nan!" Anti Hadiza tace ba zaki gane irin gatan da muke kokarin yi miki bane yanzun har sai kinje gidanki Auta, wannan shine martabar ko wace 'ya mace. In dai kina son kiyi gashi a idon wannan mijin naki to ina tabbatar miki wadannan sune manyan makamai daya kamata ki yake shi dasu musamman da ba a budurwa zai aure ki ba" tace to wai ni dama nace miki ina son yaso ni ne? Anti tayi murmushi tace baki ce ba, yi hakuri kici wannan ne na karshe kinji? Tana kumbure-kumbure da gunaguni haka ta amsa ta cinye kazar ta shanye romon. Anti ta dauki kayan kwalliya ta kara gyara mata kwalliyar ta, ta dauki dankwalin atamfar ta mata wani irin nadi a kai sai ta fito kamar wata African queen. Anti Hadiza tayi murmushi tace Masha Allah!! Kin yi kyau sosai kanwata. Bata san lokacin da murmushi ya subuce mata ba, Ameenah mutum ce mai tsananin son compliment. Anti tace yauwa, just continue smiling like this for the whole day, promise?? Ameenah ta gyada kanta da sauran murmushi a fuskarta. Anti tace good! Muje ku gaisa da baki. Ba musu ta bi bayan Antin. Falon nasu a cike yake da mutane, tana fitowa sai kowa yayi caaa a kanta, masu guda nayi, masu tsokana nayi, da kyar ta samu ta fita daga sashen ta tafi na Ya Almu inda a can sauran amaren da kawayensu suke. Tana shiga hasken flashes na camera ya dallare mata ido, tayi saurin saka hannu tana karewa. Muhibba daya daga cikin cousins dinsu ta riko hannunta suka shiga daukar hotuna kamar ba gobe, suna yi suna shakiyancin su kamar dai yadda kawayen amarya suka saba yi, Ameenah sai dai tayi murmushi kawai idan suka tabo ta.
Sai karfe hudu na yamma amaryah Safeenah da tawagarta suka iso, Ya Faruq ya kamo hannun matarshi dake lullube cikin lafaya ya jata har sashen ta inda zata zauna, bai kuma saki hannun ba sai daya kaita har kan gadonta ya zaunar da ita, mutane suka bi bayansu masu shewa nayi masu daukar hoto nayi. Abokan wasa suka mishi caaa akai dole ya bar gidan. Nan sashen amaren suka koma aka cigaba da gashi.
Da misalin karfe takwas na daren ranar, amaren na zazzaune a gaban mirror sanye da dinner gown, masu kwalliya na tsaye a kansu kowacce na gwada basirar da Allah yayi mata ta wannan fannin. Kada ku so ku ga amaren a wannan lokacin, yadda kasan a sace su a gudu saboda tsananin kyawun da suka yi kamar wasu masu modeling. Doguwar riga ce har kasa a jikinsu ta wani silk yadi, sai dai kowannensu kalar shi ta banbanta, wani net aka yi amfani dashi aka yi tattara a bayan rigar inda sauran ya zuba har yana jan kasa. Da yake dukansu suna da gashi Masha Allah, sai suka kitsa gashin jela daya bayan sun bar wani style a gaban goshin su, suka nade jelar gashin ya bada wani style na daban kamar nadin fure, suka yi amfani da pin suka nade karshen, sai suka dauki siririn gyalen kayan suka dan zizaro shi daga sama sauran gyalen ya sauka a gadon bayansu. Kamshi suke fitarwa mai sansanyan kamshi. Kafin a gama shirya su tuni Abokan anguna sun kwashe kawayen amarya, saura angunan kawai da amaren.
Kowacce wadda ta shiryata ta kama hannunta suka fita, motoci ne bakake har guda hudu anyi parking dinsu a kofar falon, angunan na tsaye cikin shiga ta yadi mai taushi wadda ta hau da kayan dake jikin amaren. Kowane Ango ya tafi ya taro amaryar shi cike da tattali ya bude mata kofar mota ta shiga ta zauna, amma shi Modibbo tsayawa yayi cak kawai ya kurawa amaryar tashi ido cike da maita. Ji yake kamar ya hadiyeta ko ya samu ya huta da wannan azababben son da yake mata, kanta a kasa haka suke tafiya amma tana jin idanuwansa akanta, don haka koda wasa bata yi kuskuren daga idanuwanta ba, sai da suka isa daf dashi kafin ya samu kuzarin dauke idonshi daga kallonta, yayi azamar sa hannu ya bude murfin motar na baya, matar ta taimaka mata ta shiga, ya maida murfin ya rufe. Daya gefen ya zagaya ya shiga ya zauna a gefenta, direba yaja motar a hankali suka bar farfajiyar gidan.
©Jeedderh🐾
[5/2, 11:06 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•52•°🐾
A cikin motar babu wanda yace da dan uwansa ci kanka, ita gefe guda ta juyar da kanta tana kallon hanya tana tunano wani lokaci da aka mata kwalliya cikin saree zata je dinar auren su ita da Marwan, irin tattalin daya dinga mata da kulawarshi a gareta, farincikin daya shiga a wancan lokacin...., sai zuciyarta tayi saurin ce mata kul! Yanzun ke matar aure ce, matar wani... Tayi saurin lumshe idanunta tana jan a'uziyyah tana istigfar. Yayin da Modibbo ya jingina bayanshi da seats din motar ya dafe kanshi, a zahiri idan ka ganshi zaka yi tunanin stress da gajiya ne suka tarar mai, though yes akwai gajiya wadda kusancinshi da Ameenah ya saukar mishi yanzun nan. A kaikaice kuma hanci ya ware yana shakar daddada kuma tattausan kamshin da Ameenahr keyi wanda yake jin kamar duk shaka daya da zai yi yana kara mishi tsabar son ta da sha'awar kasancewa da ita, hakan ya saukar mishi da wata irin kasala marar misali. Jikinshi lakwas haka suka isa Vomella Hotel inda za ayi dinar. Wajen ya kawatu sosai, haske tarr yadda kasan rana ce ba dare ba, mutane dankam suka tarar a bakin shiga wajen suna jiran isowarsu. Da isar su kuwa en jaridu da masu hotuna suka taro su da ruwan flashes har kan mazauninsu sannan kowa ya nemi waje ya zauna, babu bata lokaci aka fara gudanar da events na dinar. Muhseen babban abokin ango Modibbo shi ya bada tarihin ango na karshe (Modibbo), bayan ya gama bada tarihin ya kara da cewa shi bai taba ganin taro ko biki wanda ya kayatar dashi irin wannan ba, ya kuma ce bai taba ganin ango da amarya da suka dace da junansu irin wadannan ba. Ya kara da cewa akwai yiwuwar shima zai zagayo ya lallabo cikin Wakili's Family ya nemi wadda zai yi plan B da ita don ya kula duk kyawawan 'yanmata ne masu cike da zati a cikin familyn. Duk sai aka kwashe da dariya a wajen sosai, yayin da enmatan wajen suka ji kansu ya fashe sosai. Sai wajen karfe goma sha biyu aka tashi, daga nan aka wuce da amare Rukky da Maimunah gidajensu don dama tuni sun yi sallama da iyayen su, suka rungume Ameenah su ukun suna kukan rabuwa da kyar aka samu aka janye su.
Wannan karon ma Modibbo ne ya bude mata motar ta shiga, direba yaja motar suka tafi. Har suka bar wajen idanunta basu daina zubar da hawaye ba, akai-akai ta kam sa yatsa ta dauke hawayen. Ido ya zuba mata jikinshi a sanyaye, zuciyarshi na tsikarin shi wai ya rungumota ya lallashe ta, amma sam yaki ba kanshi damar yin hakan. Baya so yarinyar ta samu damar raina shi tun yanzu, yanzun ma har suka isa gida bata kalli inda yake ba, direba yana gama gyara fakin ya musu sallama ya fita daga cikin motar.
Cike da wata irin takama ya bude motar ya zagaya ya bude gefen da take, ta zuro kafarta ta fito a hankali, ya maida murfin ya rufe. Yaki matsawa ya bata hanya ta wuce, taku biyu ya kara ya isa dab da ita har suna jin numfashin juna don itama Ameenah ba baya bace wajen tsawo, ta dan ja baya a hankali, ya kara matsawa shima, haka suka yi tayi har sai daya dangana ta jikin motar. Ya kai bakinshi saitin kunnenta kamar mai rada yace "so, ina kike shirin tafiya ba ko sai da safe? Me yasa ba kya respecting dina ne Ameenah?? Dazu fa ko gaishe ni baki yi ba.... Kin kyauta kenan??" dan karamin bakinta ta tabe tace zancen kyautawa da rashin kyautawa bana zaton akwai shi a tsakaninmu... Gaisuwa kuma ban ga dalilin da zai sa na gaishe da kai bane. Yayi kasa da muryarshi yace ko albarkacin ina mijinki ba zan ci ba kenan?
Ta daga idanunta tana kallon tsakiyar idanunshi tana murmushin da yafi dangana shi dana takaici, tace da ka ambaci kalmar miji sai naji ka bani dariya, ko ka manta cewa kai da bakinka Ka fada min cewa aurena kawai zaka yi don ya zamar maka dole ba don kana sona ko kuma kana maraba da auren ba? Ina ganin kamar idan ka kira ni matar ka baka yiwa kanka adalci ba don ban cancanci na zama matar ka ba.... Shima murmushin ya saki sosai cikin kara kaurara idanunsa cikin nata, kallo mai ma'anoni da dama, sai ta rusunar da nata kwayar idanun don ba zata iya jure kallon kwayar idanunsa ba yanzun. Yace to yanzu ya za ayi kenan? Gashi kuma ina so ki zama matar tawa! Ta dago ido da sauri ta kalli fuskarshi, kafin ta kawar da nata fuskar zuwa kallon wani sashen daban tace babu abinda za ayi, saboda ni bana so ka zama mijina... U're lacking so many things as a husband! Yace like what??... Tayi shiru bata amsa ba. Hannu ya saka ya juyo da fuskarta zuwa gare shi, cikin zafin nama ta buge hannun nashi tace "don't u dare touch me again Modibbo! Plss don't!!" ya kalleta da mamaki yace bana tunanin na aikata wani sabo don na taba fuskar matata! Cikin daga murya tace "sau nawa kake so na fada maka cewa yadda maka dauke ni a mata ba nima ban dauke ka a matsayin miji ba? Stop putting all dat shows and get lost!! Nasan you r just pretending, but baka sona kuma baka so ka aure ni ba!!" ya gyada kanshi, you r ryt! Bana sonki, sai dai abinda ya faru ya riga daya faru, aure dai an riga an daura bamu da yadda zamu yi haka ne? Don haka na yanke shawarar zama dake a matsayin mata duk da cewa bana sonki!" ta ja tsaki, "matsalar kace ka soni ko kada ka soni bai dameni ba ka gane? Abinda kawai na sani shine ni dai ba zan so ka ba! I've already given my heart to someone who deserves it!..."
Idanunshi cike da bacin rai yake kallonta, "me kike nufi kenan?" ta murguda baki, "abinda kaji shi nake nufi!!". Hannu yasa ya shafo tattausar sumar kanshi tun daga goshi har keya, bata ankare ba sai jin saukar lebensa tayi akan nata.....
Ta zaro ido cikin tsabar shock din da hakan ya haifar mata, jikinta yayi wani irin sanyi lakwas ta rasa duk kuzarin ta. Gare shi kam jin sa yayi kamar wanda yake ziyartar duniyar Neptune saboda wani irin feeling mai dadi da yaji yana ratsa shi har tsakiyar kansa, feeling wanda bai taba experiencing irinsa a duniyar sa ba. Tsananin taushin lebunanta da wani kamshi mai sanyi da suke fitarwa, ya taimaka kwarai wajen fitar da AbdulRasheed-Modibbo a hayyacinsa, wani irin hadamammen kiss ya dinga mata mai zurfi, gabadaya ta rasa kuzarin ture shi daga gareta. Shi da kansa yayi tunanin nan ba muhallinsa bane, a hankali ya fara janye bakinsa daga nata amma bai janye daga jikinta ba. Ya bude idanunsa dake lumshe ya sauke su a kanta, idanunta a bude suke rass cikin shock din da bata fita daga cikinsa ba. Sai lokacin wani karfi yazo mata, tasa duka hannuwanta biyu ta tura shi baya da karfinta. Yayi taga-taga kamar zai fadi don sam babu kuzari a tattare dashi, Allah ya takaita ya tsaya cak.
Ya nunata da yatsa yana magana a wahalce don har zuwa lokacin numfashinsa bai daidaita ba, yace "next time, try and mention anoda man in front of me again, ko kuma ki murguda min baki, I promise you that ba tsotsar bakin zanyi ba, cinye shi zanyi duka in ga karyar rashin kunya!!".
Ta daga baki kamar mai son tace wani abu amma maganar taki fita, sai ta hutar da kanta ta juya ta bar wajen cikin sassarfa. Ya bi bayanta da kallo idanunsa na lumshewa, ji yake kamar ya kara kamota ya cigaba da kissing lebunanta don bai gaji da tsotsar su ba. Ya jima sosai a wajen kafin ya shiga mota ya tafi masaukinsa.
Lokacin daya isa karfe dayan dare ta wuce, abokansa dake tare dashi har sun yi barci. Wanka ya fara yi yayi shirin barci ya kwanta, amma barci yace bai san idanunsa ba. Yayi-yayi abin ya gagara, juyi kawai yake a gadon, Ameenah kadai yake bukata a lokacin, ita kadai. Sai dai baya tunanin ko an kaita gidanshi zai iya yin wata mu'amalar aure da ita, zai jure ko wace wahala ce ya kauda kai daga gareta har sai ya tabbatar daya saka mata zazzafan son shi a zuciyarta.
Ta bangaren Ameenah ma bata samu barci ba, da taga tunanika sun addabeta sai ta daura alwala ta kalli alkiblah. Tana kan sallaya tana karatun Al-Qur'ani mai girma aka kira sallah, ta mike tayi raka'atanil fijr ta sallaci asubahi. Sai lokacin taji wani irin mayen barci ya mamaye mata idanu, tana gama sallar ko abin sallar bata dauke ba ta koma kan gado ta kwanta, ta janyo Al-Ameen ta rungume tsam a jikinta kamar wadda take tsoron a kwace mata shi, a haka barci ya dauketa.
©Jeedderh🐾
[5/2, 11:07 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•53•°🐾
Karfe goma daidai na safiyar ranar Ameenah na gaban motar da zasu tafi Kano, cikin rakiyar duka yayyenta da wasu da yawa daga cikin jama'ar gidan, tuni en rakiyarta zuwa Kano sun nabba'a a cikin mota har da Anti Fati wadda a daren ranar zata bi jirgi ta koma Ghana. Sauran yayyenta mata duk a ranar zasu koma gidajensu. Ameenah kuka take yi sosai kamar wadda za a kaita kabari ba gidan aure ba, Ammie na kara yi mata nasiha akan wadda Kawun nan ta suka yi mata. Ya Faruq da kanshi ya bude murfin motar ya saka ta ciki, ya leka kanshi ta cikin murfin motar yace a sanyaye Auta menene abun kuka kuma? Kar ki jawo wa kanki ciwon kai fa... Ta daga baki cikin kuka tace Yaya, Al-Ameen.... Yace kada ki damu, zamu kula dashi in shaa Allah, kina yin wata guda acan zan kawo miki shi da kaina I promise you. Oyaa maza ki goge hawayenki, it's hurting me. Tayi murmushi tana goge hawayen, amma tana share su wasu suna kara gangarowa. Daidai lokacin angon nata ya bude bayan motar ya shigo, Safeenah ta leko ta tagar motar tana musu fatan a sauka lafiya. Muhseen abokin shi ya shigo ya tashi motar, daukacin jama'ar wajen suka daga musu hannuwa suna musu fatan a sauka lafiya. Ameenah ta kara bin farfajiyar gidan su da kallo idanuwnta cike da kwalla, karo na biyu kenan data bar gidansu zuwa gidan aurenta, wancan karon tana so kuma tana muradi da dokin kasancewa da wancan mijin, yayin da wannan karon kwatakwata bata son kasancewa da wannan mijin, bata kuma kaunarsa. Zuciyarta kuma na cike da tsoron kalar zaman da zasu yi da Modibbo, a yadda take ganin take-taken sa namijin duniya ne na gaske, tasan ba zai bata damar suyi zaman doya da manja irin yadda take so suyi ba. Tafi-tafiya ta daina kukan da take yi sai dai lokaci zuwa lokaci tana share hawaye dake zarya a kumatun ta. Modibbo kanshi na ga wayar hannunsa yana latsawa amma hankalinsa kacokam yana gareta, wani irin kuna zuciyarsa keyi saboda kukan da take yi babu sassauci, zuciyarsa na gaya mishi saboda bata son shi ne take yin wannan uban kukan. Anya a duniya akwai abinda yafi son maso wani kuna da kuma ciwo kuwa? Sai yaji kamar shima ya fashe da kukan, ya daure zuciyarshi ya cigaba da latsa wayar shi cikin kunan rai, idanunshi suka kada jawur. Muhseen ya lura kamar couple din basu cikin annashuwa irin ta sabbin ma'aurata, he was curious. Sai dai kasancewar sa wayayyen mutum wanda bai cika son shiga cikin harkar da babu ruwansa ba, sai ya juya ga Amaryar ya fara tsokanarta, wae ko bata son zuwa Kanon ne su juya ya maida ta Gombe yanzun nan? Tun dai tana mishi dan yake har ta ware tana tikar dariyar tsokanar Muhseen, yana da barkwanci sosai. Zuciyar Modibbo ta fara rage zugin da take ganin yadda Ameenah ta saki jiki sosai suna hirar kasar India ita da Muhseen da yake dukansu a can suka yi karatu shi da Modibbo. Bai saka musu baki cikin hirar tasu ba, ya kan dan murmusa dai kawai idan Muhseen ya tabo shi. A hankali ta fara jero hamma, barci sosai ya cika mata idanu ta dan kwantar da kanta akan Kujera barci yana fizgarta kadan-kadan, cikin dan kankanin lokaci ya kwasheta.
Ya dan saci kallon inda take, ta dan takure alamun iskar dake shigowa ta cikin tagar motar yayi mata waya, yanayin yadda kwanciyar da tayi ma kanta ba comfortable bace ba mamaki ta tashi da ciwon wuya. Sai ya mika hannu cikin tsanaki ya jawo ta ya saka cikin jikinsa, ya maida gilasan motar ya rufe, ganin haka sai Muhseen ya kunna musu AC yana dan murmushi.
Tsabar farincikin da Modibbo ya shiga a wannan lokacin baya misaltuwa, yau Ameenahr shi ce kwance a cikin jikinsa me ya kai wannan farin ciki da alfahari a garesa? Lallen hannunta yake kallo, ya fito sosai a farar fatar hannunta kamar a lokacin aka zana shi babu alamun disashewa, ya kamo duka hannuwan nata ya kai bakinsa ya sumbata cike da wani irin shauki. Muhseen yayi gyaran murya, harara ya jefa mishi, "Malam bi a hankali kada ka tasar min mata daga barci da wannan katuwar muryar taka" yayi er dariyar tsokana yace ahh, ni kawai ina tuna maka cewa ba ku kadai ne a motar ba don naga kana kokarin wuce gona da iri. Ya maida kallonshi gareta data dan motsa, yace ai ni ba dan iska bane irinka!! Muhseen ya kyalkyale da dariya yana dukan sitiyari yace banza je ka dai, na kyale ka ne kawai saboda kai farin shiga ne a harkar, so zan yi maka uzuri..." Modibbo ya gyada kai kawai yana dan murmushi ba tare daya tanka shi ba, tun asali shi mutum ne mara son magana sosai, shima Muhseen din yana cin darajar shakuwar su ne, abokansa ne tun yarinta. Ga Muhseen da dan banzan surutu da son tsokana, amma a haka ake abotar. Sanin hali sai shima Muhseen din yayi shiru ya maida hankalinsa ga tuki yana bin sautin wakar dake tashi a hankali daga cikin radion motar.
*KANO TA DABO.....*
Karfe daya na rana a cikin kwaryar garin Kano ta musu, Ameenah na dukunkune a jikin Modibbo tana barcinta cike da natsuwa har zuwa lokacin. Kai tsaye Lamido Crescent gidan amaryar suka wuce, hadadden gida ne hawa daya mallakin Modibbo. A wani zamani da aka tura shi Pondicherry yin wani course, ya ci karo da irin gidan a can, gidan yayi matukar birgeshi. Ya ga dacewar ya gina shi a matsayin gidan da zai rayu da masoyiyar shi a ciki, don haka ya dauko zanen gidan gabadayansa ya kawo aka fara gina mishi, lokacin da aka gama ginin ya ma cire rai da samun ta a rayuwarshi kwatakwata, don haka ya rufe gidan da kudirin ko da ace zai yi wani auren sai dai ya nemi wani gidan su zauna da matar amma ba dai wannan ba. To da yake shi mutum baya taba rasa abinda yake rabon sa ne sai gashi wadda aka gina gidan domin ta da kuma sunan ta ne zata shiga gidan, Allah Kenan!!
Tsayuwar da motar tayi a cikin gidan ne ya farkar da Ameenah daga barcinta. Tayi shiru tana so ta tantance a inda take kwance, ta dago a hankali ta kalleshi ba tare data janye daga jikinshi ba. Idanunshi fes a kanta ya ja fuska kamar bashi ba, kunya da takaici suka dirar mata sosai, kenan tunda ta fara barci a jikinsa take duk wannan tsawon lokacin? A hankali ta janye jikinta daga nashi ta gyara zaman gyalenta ta bude murfin motar ta fita, ya bita da kallo amma bai yi yunkurin fita ba. Muhseen dake kokarin fita ya dubeshi yace malam a cikin motar zan barka koh? Ya doka mishi harara yace idan kai kafiri ne toh ni musulmi ne, masallaci zan wuce. Ya dan dafe bakinshi yace awwwh! Na manta ashe anyi azuhur. Cikin motar ya koma ya tasheta yabi ayarin sauran abokansu da suke fita daga gidan bayan sun sauke en rakiya.
©Jeedderh🐾
[5/2, 11:07 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•54•°🐾
Wasu cousins din Modibbo su biyu suka fito daga can wata siririyar hanya suka tari amaryar da en rakiyarta, suka musu jagora har cikin gidan. Ameenah ta saka kafarta ta dama a falon bakinta na dauke da bismillah da addu'ar da Ammie tace ta dinga yi. Babban falo ne wanda ya sha saitin wasu genuine Italian leather seats manya, kofofi biyu ne kacal a falon kasa sai babban dinning table orange color da kujerunsa. Falon babu wani tarkace, daga katuwar plasma, sai wani katon flower vase baki da aka dora bisa dan karamin center table din dake tsakiyar falon. Gabadaya falon lullube yake da wasu mahaukatan marbles masu sheki sama da kasa, komi na falon a bisa tsari yake irin dai na cikakkun en boko da suka san ma'anar bokon. Fuskar amarya na lullube a cikin gyalenta babu abinda ta gani a falon ta dai ji suna ta zuzuta tsaruwar falon. Suka taka steps din bene suka hau sama, dan karamin falo ne a saman da dakuna guda shida reras. 'Yanmatan nan suka kai baki inda aka tanadar musu don su huta su kuma ci abinci, Anti Fati da amarya suka shiga dakin amaryar. Suna shiga ciki kafafunsu suka nutse cikin wani tattausan carpet bugun hannu, dakin babba ne sosai. Daga can gefen kudu na dakin katon gado ne wanda ke barazanar lashe mutane biyar ba tare da sun matsi juna ba, kafin ka kai ga gadon sai ka taka matakalar hudu, an lailaye gadon da wani lallausan bedsheet beig color, gadon rufe yake ruf da wani shara-sharan material mai kama da net shima beig. Sai toilet, dressing mirror, da wardrobe. Komi na dakin beig ne yana ta fitar da kamshi mai dadi.
Anti ta umarci Ameenah data shiga toilet ta dauro alwala, sai lokacin ta yaye rufar da tayi tana karewa dakin kallo a nutse. Zuciyarta ta karye sosai, wace irin kauna su Uncle suke yi mata a duniyar nan? Duk wata kauna da da yake bukatar samu daga wajen iyaye to ta samu fiye da irinta a wajensu. Da kyar ta iya daga kafa ta shiga toilet din, nan ma wani sabon babin kallo ne ta bude baki a hangame. Duk shige-shigen ta da yawace-yawacenta bata taba ganin toilet daya tsaru irin wannan ba, fadar abubuwan cikinsa ma bata baki ne kawai dai tasan ya hadu sosai. Alwala tayi ta fito, har Anti ta shimfida mata abin sallah. Ta tada kabbarar sallah ta fara da nafilah kafin ta sallaci azuhur. Kafin ta gama aka shigo musu da abinci mai rai da lafiya, Ameenah dai bata samu ta ci ba, gabadaya a koshe take jinta. Da kyar Anti ta samo kanta ta dan tsakuri abincin. Da suka gama suka fita har amarya din suka zagaya gidan, ashe basu ga komi ba dazu, yanzu ne suke ganin asalin gidan; kicin dinta kawai da kayan dake cikin kicin din sun isa su sa mutum ya sare da lamarin mutanen nan. Sai da suka zagaya ko ina na gidan har da su lambu a bayan gidan da wajen hutawa, gida dai yayi dari bisa dari sai fatan Allah ya ba maxauna gidan zaman lafiya mai dorewa, addu'ar da suka dinga yi musu kenan.
Anti Fati ta ja Ameenah suka kule a daki ta dinga mata nasiha tana kara nusar da ita game da falalar dake cikin aure da amfanin aurenta a garesu, tace "ki duba irin gatan da Mukhtar ya miki Ameenah, kina zaton akwai abinda zaki yi a duniya ki rama irin halaccin da yayi miki?" Ta girgiza kai, Antin tace "to wannan dama ce kika samu ta rama halaccinsa a gare ki, don Allah Ameenah kada ki rama alkhairi da sharri. Nasan duk wahala jinin Uncle Mukhtar yafi karfin kallon banza daga gareki, kada ki manta Abdul-Rasheed dan gidan yayar Mukhtar ne uwa daya uba daya, ko don darajar Uncle don Allah ki zauna lafiya dashi ko da ba kya son shi, kada ki saba umarnin shi, kada ki guje shi a shimfida don Allah da mala'ikun sa na fushi da masu aikata haka, ki daure ki ba mara da kunya kinji Auta?? Yadda na sanki a yarinya mai biyayya da jin maganar na gaba da ita don Allah kar ki sauya daga haka, Yanzu Abdul-Rasheed shi zai zama komi naki, sai kinyi masa biyayya ne zaki shiga aljannah kin fahimce ni?" ta girgiza mata kai tana hawaye. Anti ta fara janta da hira data taimaka wajen sanyaya mata rai har zuwa lokacin da direban da zai kaita airport ya iso, Ameenah ta rike Antin tana kuka riris har tana hadawa da ihu, da kyar ta saki Antin ta fita itama tana matse kwallar kewar Autar tasu.
Ana kiran magriba wata motar tazo ta kwashe en rakiyarta zuwa gidan Ummie, umarnin Ummien ne wai saboda kada su takurawa amarya da angon, gobe tun da safe zasu juya Gombe kenan ba lallai su sake haduwa da amaryar ba a goben, don haka suka mata bankwana suka tafi bakinsu dauke da addu'ar fatan sake saduwa da junansu cikin Alkhairin Allah, aka bar Amarya-Ameenah cikin tangamemen gidan AbdulRasheed-Modibbo ita kadai kwal kamar mayya. Har ta sallaci ishai da misalin karfe takwas na dare amma bata ji duriyar angon ba. Sai ta koma can karshen gado ta takure kanta a jikin bango, tana cike da kewar Ammie da Al-Ameen, amma tsoron kasancewarta ita kadai a cikin gidan ya danne kaso tamanin na kewar dake cin ranta, a tsorace take sosai.
Sai wajen karfe tara taji alamun bude gate, mota ta shigo an rufe, bata motsa daga inda take zaune ba amma jikinta ya bata kila ko Modibbo ne da abokansa. Ba a dauki wasu lokuta masu tsawo ba taji an turo kofar dakinta an shigo. Har zuwa lokacin kayan dazu ne a jikinsa wato babbar riga da er ciki kalar teku, kowa dai yasan yadda kalar sea ocean ke fitar da kyawun baki, ga bakin nashi ya hadu da shekin angonci don haka yayi kyau sosai ba kadan ba. Fuskarsa dauke da wata irin fara'ah ya shiga dakin yana mai zabga mata kirari, "amaryah... Amaryah ta buda sha kallo.... Amarya ba kya laifi sai kin kashe dan masu gida!!!" tayi gaggawar kawar da kanta can gefe guda zuciyarta na tambayarta dalilin daya hana ta kulle kofarta tun dazu cike da da-na-sani.
Ya ajiye ledar daya shigo da ita bisa dan karamin teburi dake tsakiyar dakin, ya janyo resting chair kusa da teburin ya zauna akai tare da mike kafa daya akan daya ya kalleta, "taso ki ci kazar amarcin kafin ta huce, kin san da zafi tafi dadi" ba ta tashi ba, hasalima kwanciya tayi ta juya mishi baya. Hular kanshi ya cire ya ajiye akan kujerar ya tashi ya nufeta cikin wani irin taku na cikakkun maza!.... Kafin ya isa inda take ya zare babbar rigarsa ya saura er ciki kawai, ya dora rigar akan gadon. Hannu yasa ya juyo ta suna fuskantar juna, yace ba dai jan aji ne zaki yi ba? Ina jan aji bai kamace ki ba tunda wannan ba shine karon ki na farko ba, ni nine farin shiga, in kika ja min aji ba ki min adalci ba. Da kyar ta bude baki tace sanin cewa kai farin shiga ne ya sanya naki jerawa da kai don kwatanta adalci, Farin shiga ai sai farin shiga ba tsohon hannu ba. Ya fadada murmushin dake fuskarsa sosai yace yeah! U're ryt! Buh kada ki damu, farin shigar ma na nan zuwa, but for now zanyi maneji da tsohon hannun.... Ya juya zai tafi, "....ki taso ki ci abinci fa ina fada miki" komawa tayi ta sake kwanciya, sai daya kai tsakiyar dakin ya juyo ya ganta a kwance. Komawa ya sake yi ya tsaya a gefen gadon, "Ameenah ki tashi ki ci abinci ko in ciccibe ki Allah-Wallahi...." Kara lafewa ma tayi akan gadon, yayi kwafa yana balle links din hannun rigar shi ya nannade hannun, ba tare da zaton ta ko tsammani ba taji an daga ta sama cimak kamar wata er tsako......!
©Jeedderh🐾
[5/2, 11:07 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•55•°🐾
Duk zille-zillenta ko a jikin Modibbo, sai daya kaita har kan kujera ya zaunar shima ya zauna a gefenta. Ba tare daya nuna ya damu da irin kallon takaici mai cike da tsana da take jifansa dashi ba ya janyo ledar daya ajiye yana kokarin juye abinda ya shigo dashi a cikin plate, duk da cewa a can kasan zuciyar shi kallon yana mintsinin ranshi. Gashin peacock ya juye a cikin plate din tangaran, yaji albasa da tumatiri da dan attaruhu gashi ya danyi ruwa har tiriri yake yi alamun ba a jima da sauke shi daga kan wuta Ba. Yayi amfani da fork da wuka ya yanko naman ya nufi bakinta dashi, tayi saurin janyewa. Ya kura mata ido cike da tuhuma yace me nufinki kenan? Kai tsaye tace ba zan ci ba! Yace wasa kike yi koh? Me kika ci ne? Ya fada yana kokarin taba cikinta, ta ja baya da sauri tana watsa mishi harara. A fusace tace idan ma ban ci abincin ba ina ruwanka, cikin ka ko nawa? Yayi kasa da murya cikin sigar lallashi wanda bai ma san ya aka yi yayi hakan ba, abinda ya sani kawai shine yana so ta saka wani abu a cikinta don ya tabbata babu wani abin kirki data ci, hakan kuma ya dame shi zai yi komi kuma don ganin ta ci abincin ciki har da lallashinta. Yace da ruwana Ameenah, saboda kula da cin ki da shan ki duk yana karkashin iko na ne yanzu, ba zan so Allah ya tambayeni dalilin barin ki da yunwa ba.
Ta tashi tsaye daga kan kujerar, tsakaninta da Allah tace in dai wannan hakkin ne na yafe maka duniya da lahira, kai har dama duk wasu sauran hakkoki nawa dake kanka kaje na yafe... Hannu yasa ya dawo da ita ya zaunar inda ta tashi, ya kara dauko naman ya nufi bakinta dashi yace "naji nagode, amma ni ban yafe miki nawa hakkin dake kanki ba, umarni nake baki yanzun.... Karbi kici tun kafin na miki dura kin dai san zan iya!". Kwalla ta ciko idanunta kamar ta kece da kuka haka take ji, da wannan damar ta hakki zai yi amfani yana kwararta. Abinda ta dinga fada a cikin ranta kenan, ta bude bakin a hankali ya saka mata naman, shima ruwane ya tasattsafo a nashi idanun, yayi saurin maida su. Ya dinga bata naman zuciyarsa cike da alhini, ga dai Ameenah macen daya jima yana mafarkin kasancewarta matarsa a gabanshi yau, kuma a matsayin matar tashi, sai dai ita bata dauke shi a matsayin mijin ba. Wai har sai yaushe ne shima zai dandana zakin so kamar sauran mutane?
Bai kyale ta ba sai daya tabbatar data koshi, sannan ya fara cin naman shima jiki a sanyaye. Bayan ya gama ya shayar da ita tatacciyar madara shima ya sha, da kansa ya hada kayan da suka yi amfani dasu ya fita ya kai kicin, ya sake dawowa dakin. Tana zaune inda ya barta a zaune zuciyarta na luguden daka cike da tsoron abinda zai biyo baya. Rigar shi dake kan gadonta ya dauka tare da hularshi ya tsaya a kanta, ya jima yana kallonta ba tare da yayi magana ba ita kuma bata daga kanta ba. Ya saki ajiyar zuciya a sanyaye cike da tausayin kansa da zuciyarsa, muryarsa a shake yace ki je kiyi brush ki kwanta Ameenah, sai da safe! Ya juya cikin sauri ya bar dakin babu ko waiwaye, sai da taji ya maida kofar ya rufe sannan ta saki wata nannauyar ajiyar zuciya ta samun relief tayi hamdala, a nutse babu fargabar komi ta fada toilet da niyar watsawa jikinta ruwa don yanayin garin akwai zafi.
Dakinshi ya shiga ya lalubi gefen gado ya zauna ya dafe kanshi, ya fada nannauyan tunani na neman mafita game da zamansu da Ameenah. Ya kula sosai zasu sha dabi da yarinyar wanda baya jin zai iya aminta da hakan. Yadda zuciyarsa take bukatar soyayyar ta, haka gangar jikinsa ke bukatar nata jikin. Ya dade sosai cikin zuzzurfan tunani na neman mafita, me ya kamata yayi yanzu? Soyayyar zai fara nema ko kuma gangar jikinta? Ko kuwa duka a lokaci guda?? Daga karshe dai ya lalubo mafitar da yake ganin itace mafi a'ala a gareshi. Bai san lokacin da wani tattausan murmushi ya subuce masa ba, ya mike da kuzarin shi cike da kwarin gwiwa ya fada wanka.
Barci har ya fara daukarta lokacin da taji an turo kofar dakin an shigo tare da kunna hasken dakin, cikin sauri ta kalli kofar, Modibbo ne a tsaye jikin kofar ya harde hannu a kirji yana kallonta. Cikin wani irin rawar jiki da sauri ta yayimo bargo ta rufa akan dan karamin wandon jikinta wanda da kadan ya kai mata cinya da wata half vest mai hannu daya. Yayi fuska kamar bai ga komi ba duk da cewa gabadaya babu inda baya rawa a jikinsa saboda kyakkyawar kirar Coca-Cola bottle daya gani ta Ameenah. Ya karasa shiga cikin dakin ba tare daya kara kallon sashen da take ba yace idan kina da alwala taso muyi sallah. Ta bishi da kallo cikin alamun tambaya, har ya dauko abin sallah ya shimfida bata samu ta motsa ba. Ya juya ya kalleta, murya a dan kaurare yace ke fa nake jira. Tace ban gane sallar da kake nufi bane. Ya ja fuska sosai yace "kuma so kike yi ki san ko wace iri ce koh??".......
©Jeedderh🐾
[5/2, 11:07 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•56•°🐾
Ta kula tambayar ta dan bata mishi rai, sai ta bame bakinta bam da kwado ta sadda kanta kasa. Rashin kunya da tsiwa sam basa cikin tsarin rayuwar Ameenah, a har kullum ita mai girmama na gaba da ita ne da bin maganarsu, amma ta rasa dalilin da yasa daga shigowar Modibbo cikin rayuwarta gabadaya ya canzata daga yarinya mai shiru-shiru zuwa tsiwatacciya duk da dai shi kadai ne take yiwa rashin kunyar, amma bata jin dadin hakan, musamman a yanzun da take karkashinsa a matsayin mata. Sa'insa dashi bata kamace ta ba, idan zata tuna nasihun dasu Ammie da kawunnan ta suka mata jiya da yau duk akan ta bi umarnin Modibbo ne, sun ce tsakaninta dashi to ne kawai a duk maganarsa umarninsa hakan bai sabawa addini ba.
Sai ta mika hannu gefen gado cikin sanyin jiki ta janyo hijabinta wanda ya rufe mata har tafin kafa ta saka, ta zuro kafafunta kasa ta sauka daga kan gadon ta nufi inda yake cikin nutsattsen taku. Ta bi bayanshi ya ja su sallar nafilah har raka'ah hudu, dogayen surori ya dinga janyowa yana rerawa cikin wata daddadar kira'ah kai kace Sheik Muhammad Minshawi ne yake rera karatun, har shagaltar da ita ya dinga yi wajen sauraron hadaddiyar kira'ar tasa. Bata so ya sallame sallar ba, taso ace ya ci gaba da karatun har gari ya waye, zata saurara ba tare da gajiyawa ba, hakan zai fiye mata daya zauna yana mata surutan rainin wayon nan nashi. Ya dafa kanta ya janyo addu'o'i sosai ya tofe ta dasu, daga nan ya tambaye ta game da addini da hukunce-hukuncensa, kamar yadda yayi zato bata gaza amsa tambayarsa ko daya ba. Daya gama ya umarceta akan taje ta kwanta, ba musu ta mike da hijabin nata ta nufi gado. A bakin gadon taji an riko mata hijabi, ta juyo da sauri cikin faduwar gaba, shi din ne a tsaye rike da hijabin. Ko kafin ta samu damar tambayar ba'asi ya fara kokarin cire mata hijabin, ta rike hijabin gam da iya karfinta, ta karfin tuwo ya cire hijabin nata yayi wurgi da ita can gefe, ta saka hannuwanta duka biyun ta kare kirjinta, tace cikin dauriya da salon rashin kunya mai tattare da in-ina, "Mmalamm.... Meye haka kake yi??" dariya taso kama shi ganin yadda ta diririce kamar ba Ameenahr wannan mai tsiwa da zafin kai ba.
Hannunta ya janye daga kirjinta ya maye su da nashi kirjin ya rungumeta tsam kamar zai tsaga kirjinsa ya saka ta ciki, wani irin al'amari mai wuyar fassarawa ya ziyarcesu su duka. Idanunsa a lumshe ya kai bakinsa bisa dogon wuyanta dake fitar da sansanyan kamshin gel na turaren nabeel ya fara watsa mata ruwan sumba. Zuciyar Ameenah ta dauko rawa kamar ta daka tsalle ta fito daga kirjinta ta duro kasa, iyakar karfinta ta saka ta tunkude shi don taga alamun dan kuzarin nan ma babu shi tattare da Modibbo. Ya sake mika hannu ya kamota tayi saurin bige hannun taja da baya, "Mm... Malammmmm, bana son iskanci... Mey haka?" yace murya a shake, "mijinki kike kira da dan iska pa Meenahh!!" gabanta ya fadi sosai, ta shiga wani yanayi mai kama da bacin rai, duk duniya mutum daya yake kiranta da wannan sunan, tun daya bar duniya kuma babu wanda ya sake kiranta dashi sai yau. Tace kada ka sake kiran sunana da Meenahh don ba dashi aka min huduba ba, idan ba zaka kira ni da Ameenah ba to kayi shiru, ni zai fi min ma ka kira ni da ke ba Meenahh ba.... Yadda ta runtse ido tana mishi kashedi ba karamin burgeshi yayi ba, ya zuba mata ido cike da birgewa yana kallo yana doka murmushi, she is cute! Bata san ya aka yi ya isa gabanta ba, kawai tsintar bakinta tayi a cikin nashi. Duk yadda taso ta yakice shi wannan karon dai bata ci nasara ba, sai da yayi ra'ayin kansa sannan ya dan sassauta rikon daya mata, "Ameenah! Meye haka kike yi wai?" cikin kunan rai tace bana son abinda kake yi min, ka kyale ni! Ya girgiza kai a nutse yana dubanta cikin lumshe idanu, "a'ah Ameenah, sunna ce fa? Meye aibuna don ina kokarin yin koyi da da fiyayyen halitta? A cikin koyarwarsa ne yace idan kayi sabuwar amarya ka shayar da ita madara ko ka ciyar da ita nama, ku sallaci nafilah bakin iyawarka, ka roki Allah game da dukkan alkhairan ta ka kuma nemi tsari da dukkan sharrinta, ka kuma roki Ubamgiji samun zuriya dayyiba daga gareta, daga nan kuma sai kayi abinda zai samar da 'ya'yan... Abinda nake yi kenan ai". Hannuwanta duka biyun ta saka ta rufe kunnuwanta, cikin karaji take nuna masa kofa, "Modibbo kana yiwa girman Allah ka bar min daki tun kafin kalamanka su tarwatsa min zuciya, please Modibbo ka fita!!" ta bashi tausayi sosai, sai dai baya jin zai iya canza kudirinshi, ya girgiza mata kai, "but I don't want to......" ya matsa gareta a hankali, tayi stepping back kawai sai taji ta rigingine akan gado, ta zaro ido a firgice tana kallonshi. A yunwace yayi pouncing kanta kamar mayunwacin zaki, ya shiga aika mata da sakonni masu nauyi a jikinta, a hankali wata jijiya mai tura sakwanni zuwa kwakwalwa a jikinta ta shiga turawa kwalwar Ameenah sakon cewa itama fa tana muradin abin, yayin da kwalwar ta turawa gangar jikinta tsananin bukatuwa da kuma gamsuwa da zakakan kisses din Modibbo suka samar mata, nan aka shiga dambe tsakanin gangar jiki da zuciyar Ameenah, gangar jikin na so, amma zuciyar ta kafe akan bata so, yayin da gangar jikin itama ta kafe tana fadada zuciyar itama fa Ameenahr lafiyayyar mace ce tana bukatar namiji kamar sauran lafiyayyun mutane. Daga karshe dai gangar jikin ta samu nasara. Cikin yanayin fita hayyaci Ameenah tasa hannu ta rungume Modibbo gam a jikinta, ta shiga maida mishi nartanin kisa-kisan da yake watsa mata.
The moment Modibbo take control, she regretted it. Ta fara ture shi daga jikinta sai dai inaa! Modibbo tuni ya bace daga duniyar lafiyayyun mutane masu hankali zuwa ta kuntattu. Duk yadda yaso yayi controlling kansa abin yaci tura, Ameenah irin matan nan ne masu padlock, yanayin halittar ta da gyaran data sha sun taimaka kwarai wajen fitar da Modibbo-AbdulRasheed daga dan guntun hayyacin daya rage masa, ya shiga zaro maganganu da surutai wanda Ameenah bata yi nasarar tsintar komi a cikinsu ba don itama ba a cikin hayyacinta take ba, tana cikin shock na tsananin azabar da Modibbo yake gana mata, a ganinta tsantsar mugunta kawai yake gwada mata. Tun tana kuka da hawaye har hawayen suka daina zuba sai dai kukan kurame kawai, daga baya ma kukan kuramen sai ya gagara sai shessheka da ajiyar zuciya kawai, azabar da take ji tayi imanin ko a daren farkonta bata dandani kamar ta ba.
Ya rungumeta sosai a jikinsa kamar zai maida ta ciki, yana rada mata nauyayan maganganu na tsantsar so da godiya wadanda ko a daren farkonta bata ji su ba. Bata dauke su a bakin komi ba face sambatun shauki da fita hayyaci. Ba jimawa barci mai nauyi yayi awon gaba dashi, ta ture shi daga jikinta ta juya mishi baya cikin kwararowar hawaye.......
©Jeedderh🐾
[5/2, 11:07 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•56•°🐾
Ta kula tambayar ta dan bata mishi rai, sai ta bame bakinta bam da kwado ta sadda kanta kasa. Rashin kunya da tsiwa sam basa cikin tsarin rayuwar Ameenah, a har kullum ita mai girmama na gaba da ita ne da bin maganarsu, amma ta rasa dalilin da yasa daga shigowar Modibbo cikin rayuwarta gabadaya ya canzata daga yarinya mai shiru-shiru zuwa tsiwatacciya duk da dai shi kadai ne take yiwa rashin kunyar, amma bata jin dadin hakan, musamman a yanzun da take karkashinsa a matsayin mata. Sa'insa dashi bata kamace ta ba, idan zata tuna nasihun dasu Ammie da kawunnan ta suka mata jiya da yau duk akan ta bi umarnin Modibbo ne, sun ce tsakaninta dashi to ne kawai a duk maganarsa umarninsa hakan bai sabawa addini ba.
Sai ta mika hannu gefen gado cikin sanyin jiki ta janyo hijabinta wanda ya rufe mata har tafin kafa ta saka, ta zuro kafafunta kasa ta sauka daga kan gadon ta nufi inda yake cikin nutsattsen taku. Ta bi bayanshi ya ja su sallar nafilah har raka'ah hudu, dogayen surori ya dinga janyowa yana rerawa cikin wata daddadar kira'ah kai kace Sheik Muhammad Minshawi ne yake rera karatun, har shagaltar da ita ya dinga yi wajen sauraron hadaddiyar kira'ar tasa. Bata so ya sallame sallar ba, taso ace ya ci gaba da karatun har gari ya waye, zata saurara ba tare da gajiyawa ba, hakan zai fiye mata daya zauna yana mata surutan rainin wayon nan nashi. Ya dafa kanta ya janyo addu'o'i sosai ya tofe ta dasu, daga nan ya tambaye ta game da addini da hukunce-hukuncensa, kamar yadda yayi zato bata gaza amsa tambayarsa ko daya ba. Daya gama ya umarceta akan taje ta kwanta, ba musu ta mike da hijabin nata ta nufi gado. A bakin gadon taji an riko mata hijabi, ta juyo da sauri cikin faduwar gaba, shi din ne a tsaye rike da hijabin. Ko kafin ta samu damar tambayar ba'asi ya fara kokarin cire mata hijabin, ta rike hijabin gam da iya karfinta, ta karfin tuwo ya cire hijabin nata yayi wurgi da ita can gefe, ta saka hannuwanta duka biyun ta kare kirjinta, tace cikin dauriya da salon rashin kunya mai tattare da in-ina, "Mmalamm.... Meye haka kake yi??" dariya taso kama shi ganin yadda ta diririce kamar ba Ameenahr wannan mai tsiwa da zafin kai ba.
Hannunta ya janye daga kirjinta ya maye su da nashi kirjin ya rungumeta tsam kamar zai tsaga kirjinsa ya saka ta ciki, wani irin al'amari mai wuyar fassarawa ya ziyarcesu su duka. Idanunsa a lumshe ya kai bakinsa bisa dogon wuyanta dake fitar da sansanyan kamshin gel na turaren nabeel ya fara watsa mata ruwan sumba. Zuciyar Ameenah ta dauko rawa kamar ta daka tsalle ta fito daga kirjinta ta duro kasa, iyakar karfinta ta saka ta tunkude shi don taga alamun dan kuzarin nan ma babu shi tattare da Modibbo. Ya sake mika hannu ya kamota tayi saurin bige hannun taja da baya, "Mm... Malammmmm, bana son iskanci... Mey haka?" yace murya a shake, "mijinki kike kira da dan iska pa Meenahh!!" gabanta ya fadi sosai, ta shiga wani yanayi mai kama da bacin rai, duk duniya mutum daya yake kiranta da wannan sunan, tun daya bar duniya kuma babu wanda ya sake kiranta dashi sai yau. Tace kada ka sake kiran sunana da Meenahh don ba dashi aka min huduba ba, idan ba zaka kira ni da Ameenah ba to kayi shiru, ni zai fi min ma ka kira ni da ke ba Meenahh ba.... Yadda ta runtse ido tana mishi kashedi ba karamin burgeshi yayi ba, ya zuba mata ido cike da birgewa yana kallo yana doka murmushi, she is cute! Bata san ya aka yi ya isa gabanta ba, kawai tsintar bakinta tayi a cikin nashi. Duk yadda taso ta yakice shi wannan karon dai bata ci nasara ba, sai da yayi ra'ayin kansa sannan ya dan sassauta rikon daya mata, "Ameenah! Meye haka kike yi wai?" cikin kunan rai tace bana son abinda kake yi min, ka kyale ni! Ya girgiza kai a nutse yana dubanta cikin lumshe idanu, "a'ah Ameenah, sunna ce fa? Meye aibuna don ina kokarin yin koyi da da fiyayyen halitta? A cikin koyarwarsa ne yace idan kayi sabuwar amarya ka shayar da ita madara ko ka ciyar da ita nama, ku sallaci nafilah bakin iyawarka, ka roki Allah game da dukkan alkhairan ta ka kuma nemi tsari da dukkan sharrinta, ka kuma roki Ubamgiji samun zuriya dayyiba daga gareta, daga nan kuma sai kayi abinda zai samar da 'ya'yan... Abinda nake yi kenan ai". Hannuwanta duka biyun ta saka ta rufe kunnuwanta, cikin karaji take nuna masa kofa, "Modibbo kana yiwa girman Allah ka bar min daki tun kafin kalamanka su tarwatsa min zuciya, please Modibbo ka fita!!" ta bashi tausayi sosai, sai dai baya jin zai iya canza kudirinshi, ya girgiza mata kai, "but I don't want to......" ya matsa gareta a hankali, tayi stepping back kawai sai taji ta rigingine akan gado, ta zaro ido a firgice tana kallonshi. A yunwace yayi pouncing kanta kamar mayunwacin zaki, ya shiga aika mata da sakonni masu nauyi a jikinta, a hankali wata jijiya mai tura sakwanni zuwa kwakwalwa a jikinta ta shiga turawa kwalwar Ameenah sakon cewa itama fa tana muradin abin, yayin da kwalwar ta turawa gangar jikinta tsananin bukatuwa da kuma gamsuwa da zakakan kisses din Modibbo suka samar mata, nan aka shiga dambe tsakanin gangar jiki da zuciyar Ameenah, gangar jikin na so, amma zuciyar ta kafe akan bata so, yayin da gangar jikin itama ta kafe tana fadada zuciyar itama fa Ameenahr lafiyayyar mace ce tana bukatar namiji kamar sauran lafiyayyun mutane. Daga karshe dai gangar jikin ta samu nasara. Cikin yanayin fita hayyaci Ameenah tasa hannu ta rungume Modibbo gam a jikinta, ta shiga maida mishi nartanin kisa-kisan da yake watsa mata.
The moment Modibbo take control, she regretted it. Ta fara ture shi daga jikinta sai dai inaa! Modibbo tuni ya bace daga duniyar lafiyayyun mutane masu hankali zuwa ta kuntattu. Duk yadda yaso yayi controlling kansa abin yaci tura, Ameenah irin matan nan ne masu padlock, yanayin halittar ta da gyaran data sha sun taimaka kwarai wajen fitar da Modibbo-AbdulRasheed daga dan guntun hayyacin daya rage masa, ya shiga zaro maganganu da surutai wanda Ameenah bata yi nasarar tsintar komi a cikinsu ba don itama ba a cikin hayyacinta take ba, tana cikin shock na tsananin azabar da Modibbo yake gana mata, a ganinta tsantsar mugunta kawai yake gwada mata. Tun tana kuka da hawaye har hawayen suka daina zuba sai dai kukan kurame kawai, daga baya ma kukan kuramen sai ya gagara sai shessheka da ajiyar zuciya kawai, azabar da take ji tayi imanin ko a daren farkonta bata dandani kamar ta ba.
Ya rungumeta sosai a jikinsa kamar zai maida ta ciki, yana rada mata nauyayan maganganu na tsantsar so da godiya wadanda ko a daren farkonta bata ji su ba. Bata dauke su a bakin komi ba face sambatun shauki da fita hayyaci. Ba jimawa barci mai nauyi yayi awon gaba dashi, ta ture shi daga jikinta ta juya mishi baya cikin kwararowar hawaye.......
©Jeedderh🐾
[5/2, 11:07 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•57•°🐾
Wannan dare bata taba riskar irin shi ba, daren data kira Bakin Dare! Dare mafi muni da kunci a rayuwarta. Tana sake-sake barci ya kwashe ta itama.
Da asubahi ya rigata tashi, tana dukunkune a jikin sa tana barcinta a nutse, abu ne wanda ta riga ta saba dashi, duk lokacin da suka yi making love da Marwan to ya kan saka ta cikin jikinsa su koma barci. To a jiyan ma bayan ta gama koke-kokenta kasa daurewa tayi sai data dangana jikinta da jikinshi. Yayi shiru yana sauraron fitar numfashinta akan kirjinsa a hankali, jin shi ya dinga yi kamar wanda aka wa bushara da aljannah. Cikin tsanaki ya zame jikinshi a hankali gudun kada ya tashe ta, sai daya jera mata pillows sannan ya bar dakin. Yana fita ta bude idanunta, tun tashin sa itama ta farka kin nuna masa alamun ta tashi tayi. Tayi kokarin ta tashi zaune wata azaba ta ratsa ta ba shiri ta dan saki kara, sosai take jin radadi. Da cije baki da runtse ido ta samu ta sauka daga kan gado, da bin bango ta shiga toilet ta tara ruwa a bahon wanka mai madaidaicin zafi ta shiga ta zauna har ruwan ya huce, ta tara wani ta sake zama. Daya huce sai tayi wanka ta dauro alwala ta fito ta tayar da sallah.
Modibbo kam ana gama sallah ya dan zauna yayi azkar har gari yayi haske, cikin sauri ya shigo gidan wai ya tasheta daga barci kar ta makara sallah, amma ga mamakinsa sai ya sameta a zaune akan abin sallah tana karatun al-qur'ani mai girma. Yayi tsaye a jikin kofar yana kare mata kallo, daga bisani ya juya ya sauka kasa. Bayan kamar minti ashirin ya dawo dauke da tray a hannunsa ya dire a gabanta, ba tare data kalleshi ba ta rufe Qur'anin ta tashi ta koma kan gado ta kwanta, bai yi fushi ba ya sake binta har kan gadon, ya tsiyaya tatacciyar madara mara sanyi a cikin mug, hannu yasa ya tashe ta zaune ya mika mata kofin, sai a lokacin ya mata magana, yace karbi ki sha Ameenah in baki magani. Kwalla ta ciko idanunta tayi saurin maidata, ta girgiza masa kai. Ya lankwasa murya cikin sigar lallashi yace pleaseee.. Ba don ni ba... Yanayin yadda yayi maganar yasa ta kasa masa musu, ta amshi kofin ta kai bakinta ko rabin madarar bata sha ba ta ajiye. Ya balle murfin goran ragolis ya balli magani ya mika mata, ta afa su a baki ta kora da ruwa. Ya taimaka mata ta koma ta kwanta, yasa bargo ya rufe ta dashi ya bar mata shi a saitin ruwan cikinta. Ya tattara kayan yayi waje dasu bayan ya rufe mata kofar, ta lumshe idanunta a hankali tana sake-sake cikin ranta har barci ya dauketa.
Shima dakinshi ya koma ya kwanta, duk da yau Monday ce amma ya dauki hutun angonci na sati guda. Sai wajen karfe goma ya tashi, shima dalilin waya ne da Ummie ta mishi tace direba yana jiransa a kofar gida ya kawo musu breakfast, ya tashi ya sauka yaje ya amso kayan. Kan dinning table ya ajiye kwandon, sai daya leka Ameenah yaga har zuwa lokacin barci take shaka. Dakinsa ya koma ya fada wanka, ya fito ya shirya cikin wani voyl maroon mai cizawa, bai dora hula ba sai dai ya taje sumar kanshi ya shafa mai. Fita yayi ya karya ya kwashi makullan motarshi ya fita.
Ita kam sai gab da azuhur ta farka, lokacin data duba agogo tayi mamakin lokutan data dauka tana barci. Tayi mika tana salati ta diro daga gadon ta fada bayi, wannan karon ma sai data shiga ruwan zafi duk da cewa babu radadin amma ta kara jin karfi a jikinta sosai. Ta fito ta shirya cikin wata doguwar rigar atamfa dinkin buba, bata shafa komi ba sai mai da hoda amma fa tayi kyau sosai, fuskarta tayi wasai sai er rama kadan wadda idanunta ne kadai suka dan shige ciki.
Data gama sallar azuhur kan kujera ta koma ta nade tana canza channels, ko takan abinci bata bi ba don bata jin yunwa ko kadan. Ta janyo waya ta kira Ammie suka gaisa, aka bata Al-Ameen ya fara mata shirmen hirarsa tana ta kwasar dariya ran nan nata kal kamar farar takarda, sun jima sosai akan waya daga bisani suka yi sallama. Ko ajiye wayar bata yi ba kiran Anti Jamila ya shiga wayar ta, ta daga tace tazo ta bude musu kofa suna jiranta a waje. Ta tashi ta sauka kasa, ta jima sosai tsaye a tsakiyar falon tana jinjina irin tsaruwar falon, gaskiya babu abinda zata ce da Anti Jameelah da maigidanta sai dai fatan alkhairi kawai. Sai data kosar da idanunta sosai sannan ta je ta bude musu gate, su Anti ne har da relatives din su Marwan don suna mutunci dasu sosai. Sai zuwan su ne ma Anti Jamila tasa ta dan tsakuri abincin da suka kawo daga gidan Ummie, nan suka yini a gidan sai da yamma suka tafi. Anti tace gobe da yamma zata koma don dama Uncle tun a ranar daurin aure ya bar 9ja, zuwa lokacin zazzabine sosai ya rufe Ameenah ruf da kyar ta samu ta raka su kasa, ta dawo ta libge akan gado kamar kayan wanki, da kyar ta sallaci magriba a daddafe ta kara komawa ta nade a cikin bargo.
Maodibbo bai shigo gidan ba sai da karfe tara ta gota, yana can tare dasu Muhseen suna ta hira bai kula da lokaci ya kure ba sai da daya daga cikin abokan nasu ya nuna mishi agogo yana tambayar wai ko dai ya manta da amaryah ne?? Ya wawuri makulli ya fita a sukwane babu ko waiwaye balle ya tankawa shakiyancin da suke mishi. Sai daya tsaya a wani suya joint ya sayi suyar kaji da tarkacen yogurts da fresh milk don yace wa Ummie a daina kai musu abinci ya hutar dasu. Sai daya canza shiga zuwa ta kayan barci sannan ya tafi dakin Ameenah.....
©Jeedderh🐾
[5/2, 11:08 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•58•°🐾
Tana can tsakiyar gadon ta nade cikin bargonta mai damisa irin mai rubi biyu dinnan, amma still rawar sanyi take yi. Ya ajiye ledar hannunshi da sauri ya nufe ta a rikice, Ameenah lafiya?? Abinda yake nanatawa kenan har ya hau kan gadon ya janye bargon data rufa dashi, rawar sanyin data ke yi ta karu har hakoranta na hadewa da juna, ta kasa ko bude ido, hucin zafin jikinta ya bugo shi kamar wuta, ya dafe kai Ohhh God! Ya maida mata bargon da sauri ya fita, dakinshi yaje ya dauko first aid box yazo ya fara bincikar ta. Allura ya hada ya zurkuda mata, duk da halin da take ciki sai data yi dan kara, ya shiga lailaya mata wajen yana ambaton sorry!! Cikin ledar yaje ya dauko mata yoghurt, ya tsiyaya a cup ya mika mata, tayi saurin girgiza kai don ko karnin shi bata son ji, ya narkar da murya yace daure ki sha Ameenah magani zan baki, kinji? Karbi don Allah..... Ya shiga bata da kanshi, ko rabi bata sha ba ta amayo mishi yoghurt dinnan tas a jikinshi da dan sauran abinda taci da rana. Yana rungume da ita kamar zai rushe da kuka dan tausayi har ta gama, ya dauketa ya dora akan couch shi kuma yaje ya gyara wajen, ya kawo air freshener ya fesa a gun, shima ya koma daki ya canza kayan jikinshi ya dawo dakin cikin shiga fiye data dazu yana ta kwarara kamshi mai dadi. Ya kara ciccibarta ya maida kan gadon, da lallashi ya samu ta dan kurbi yoghurt din ya bata magunguna. Yaje ya tattara sauran kayan ya kai kicin, ya dawo ya taimaka mata ta kwanta. Ya dan rufa mata bargo duk da zazzabin ya sauka, shi kuma ya koma kan couch ya kwanta bayan ya kashe musu wuta.
Washegari data tashi babu zazzabin a jikinta sai dai rashin kwarin jiki, ya taimaka mata ta dauro alwala suka dawo ya shimfida mata abin sallah, shi ya tafi masallaci ita kuma ta sallaci tata a daki. Da gari ya danyi haske ya dawo ko sama bai hau ba ya fada kicin ya shirya mata sassaukan abinci da yake Abdul-Rasheed ba daga nan ba in dai akan girki ne, ya kware sosai kamar wani chef. Kafin takwas tayi ya gama komi, ya cicciba ya kai mata ta dan ci ya bata magunguna ta koma ta kwanta, sai daya ga barci ya dauketa sannan ya tafi dakinshi ya kwanta. Ranar bai fita ba sai can da yamma bayan ya tabbatar da ta wartsake sosai, sai bayan isha'i ya dawo. Kofar dakinta ya tura amma sai yaji kofar a rufe, mamaki ya kama shi, ya bubbuga yaji shiru. Sai ya leka ta kofar makulli ya hangota a zaune tana ta faman latsa remote da plate din yankakkun fruits a gabanta, yayi ajiyar numfashi, da alamun ta warke kenan tunda har ta iya sauka kasa. Sai ya koma kasa ya adana kajin da fresh milk din daya shigo dasu. Can wajen karfe goma yana kwance yaji karan bude kofar dakinta, cikin sauri yazo bakin kofar shi yana hangota, ita din ce ta zura dogon hijabi har kasa, yaji wata faduwar gaba ta ziyarce shi. Ina zata je da wannan daren? Ko dai guduwa zata yi?? Yayi kokarin bin bayanta sai ya tuna makullin gidan ai yana hannunshi, sai dai in doguwar katangar gidan zata kama ta dira. Yana nan yana saka da warwara yaga ta dawo hannunta dauke da kwalin fresh milk mai sanyi wadda ya shigo da ita ta shige daki ta kulle, ya jingina kanshi da kofar dakin yana karewa ceiling din dakin kallo.
Wasa gaske Ameenah ta daina yarda su hadu da Modibbo, kullum tana daki bata yarda ta fito sai idan ya bar gidan ta fito tayi en gyare-gyare da abinda zata yi kafin ya dawo ta koma.
Bai damu da hakan ba ko kadan, a ganin shi indai tana lafiya to Falillahilhamdu, sai dai a yawancin lokuta ya kan yi kewarta sosai, yana so ya sake kadaicewa da ita sosai, zumar daya dandana daga gareta zuma ce da ba dai a dandanata a barta ba, sai dai asha ta kuma ayi ta son nata har abada, sai dai ya kan lallami zuciyarsa ya nuna mata lokacin hakan bai yi ba, ya sha alwashin wani abu ba zai kara shiga tsakaninsu da ita ba har sai ya koya mata son sa, ba zai so haifar 'ya'ya da macen da bata son shi ba gudun kada kiyayyarshi ta shafi yaran. Cikin haka ya koma bakin aikinshi, idan ya fita tun kafin takwas sai karfe hudu ko biyar yake dawowa. Ya fahimci tana son shan fresh milk don haka yake kwaso mata ita yayi ta jibge mata su a fridge. A haka suka shanye wata guda cur, haduwarsu da Modibbo sai dai by mistake, kila ta fito daga daki shima ya fito su danyi starring din juna su kauda kai, watarana ya tambayeta tana da matsala? Sai dai kawai ta girgiza kai ta koma dakinta. Wannan rayuwar kadaicin data kirkirarwa kanta bata yi mishi dadi ko kadan, to amma ya zai yi???
Ta takura su Ammie sosai akan a kawo mata Al-Ameen dinta, Ammie tace ta fara tambayar izinin mijinta. Ta turo baki kamar tana gaban Ammien tace to ai tun farko sai da muka yi yarjejeniya dashi, ya yarda da zaman Al-Ameen a tare dani, menene kuma na sake fada mishi?? Ammie tace ke dai tunda nace ki tambaya to ki tambaye shi din.... Ta katse wayar. Tsaki ta ja tayi jifa da wayar.
Ya dawo daga aiki ya ganta coge a jikin kofar dakinta ta harde hannu a kirji kanta a kasa, kasa-kasa yake kallonta yana so yayi magana amma yana tsoron ta shige dakinta, sai kawai ya hau kokarin bude dakinta. Muryarta ya tsinkaya daga bayanshi, "Ammie tace a tambaye ka za a kawo Al-Ameen..." ya dan juyo yana kallonta, fatar jikinta tayi wani fess da gani babu tambaya kasan tana shan hutu, to bata zuwa koina, kullum sai dai taci ta kwanta ko hasken rana sai dai ta hango shi ta window. Yayi saurin janye idonshi daga kanta saboda wani abu da yaji yana taso mai game da ita, yayi kokarin saisaita muryar shi data fara tangadi, yace Allah ya kawo shi lafiya.... Kafin ya gama rufe baki ta fada dakinta ta rufo, yabi kofar dakin da kallo yana gyada kai cikin kunan rai.
Bayan kwana biyu Ya Faruq ya kawo mata shi da kansa kamar yanda yayi alkawari, tare suka zo da Safeenah. Ta kara habakewa ta zama lukuta ta gaske, sunyi kyau sosai daga ita har Faruq din. Al-Ameen ma ya kara girma sosai, ya kwaso da gudu yana Mommy.....!! Ta daga shi sama ta cilla shi ta cafe tana dariya, tana jin kamar ta maida shi ciki. Ta dinga ina taka saka ina taka tsare da bakinta, babynta na jikinta. Suna nan Modibbo ya dawo daga wajen aiki. Bayan anyi isha'i gabadaya suka rankaya gidan su Ummie, wannan shine karo na farko da Ameenah taje gidan tun da aka kawo ta, Ummie dai tazo kuma ana kawo mata su Hauwa akai-akai suna mata yini. Ummie tayi murna da zuwansu sosai, suna nan suna hira har sai da sha daya ta wuce sannan suka musu sallama suka tafi, Faruq masauki ya kama, anyi-anyi dashi yaki kwana a gidan su Ummie. Washegari ya koma, Safeenah ta kara kwana biyu itama ta bi bayan shi.
Dawowar shi daga wajen aiki kenan, yana kokarin bude dakinshi ya jiyo muryar Ameenah sama-sama, "ya za ayi baby? Ba a sako maka underwears da kayan shan iska ba..." ya danyi murmushi ya shige dakinshi, wanka ya fara yi ya canza shiga ya dauki makullin mota ya fita. Sai gashi niki-niki da ledoji a hannu, ya tsaya bakin kofarta ya bubbuga. Ta taso ta bude cikin mamaki don bai taba mata haka ba, a kofar ya coge yana mata wani kwantaccen murmushi tace lafiya?? Ledar hannunshi ya mika mata, ta amsa. Tana shirin maida kofa ta rufe Al-Ameen ya leko kai ta kofar, yace mommy! Modibbo ya sakar mishi murmushi ya durkusa a gabanshi yace "hello baby, ya kake?" ya kalli mommyn ya sake kallonshi, ya turo baki yana kallon Ameenah. Bata bari yace wani abu ba ta janye Al-Ameen ta maida kofar ta rufe shima ya juya abinshi. Al-Ameen ya dame ta da tambayar wai wanene wancan?? Tace sunan shi Uncle, yace Uncle Wa? Tace kace mishi Uncle kawai. Zai sake watso mata wata tambayar tace mishi shhhh! Ya kuwa yi tsit.
Ga mamakinta koda ta bude ledar kayan shan iska ne da underwears na yara daidai Al-Ameen, har da su turaruka da takalma, sayayya dai rankataf! Ta dan yi murmushi kadan, "well thanks for this, yau dai ya dan birge!" ta fada a ranta.
©Jeedderh🐾
[5/2, 11:08 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•59•°🐾
Ranar assabar da safe ya ci kwalliyar shi cikin kananan kaya sai kamshi yake yi, yayi knocking a kofarta. Ta taso ta bude kofar ta coge a bakin kofar tana kallonshi, cikin murmushinsa da baya bacewa a fuskarsa in dai yana tare da ita yace morning! Ta dan ji kunyar kin gaishe shi da bata yi ba, ta kauda kai gefe ita bata amsa gaisuwar shi ba ita kuma bata gaida shi ba. Yace a bani aron Al-Ameen zai raka ni unguwa... Ta dan tsaya tana kallonshi, sai kuma ta juya ta kwalawa Al-Ameen kira, yazo gun a guje yace mommy gani. Ta dan kalli Modibbo tace kazo ka raka Uncle unguwa. Ya kuwa koma dakin da gudunshi ya kwaso takalman shi ya dawo, ta duka ta sanya mishi takalman, Modibbo ya kama hannuwanshi suka tafi yana mata bye.
Bayan fitarsu wankin kananan kayansu ta musu da yake akwai wanda yake musu wanki da guga, mai aikin da yake zuwa kullum yana share farfajiyar gidan da ban ruwan fulawowi shi yake musu wanki da guga. Ta gama tayi wanka tayi lunch, ta zauna jiran dawowarsu duk kadaici ya cika ta amma har aka kira yi sallar la'asar shiru sai da yamma likis tana falon kasa a cikin kicin taji Al-Ameen ya shigo da gudu yana kiran sunanta, ta tare shi tana mishi oyoyo. Bakinshi kamar zai tsage yake bata labarin Daddy ya saka shi a makaranta, tace wane daddy?? Yace daddy na nan gidan mana, yace sunan shi daddy ba Uncle ba. Ta kama haba, "kaji wani karfin hali., ko yaushe ya zama danshi??" ta shafa kanshi tace kace makaranta ya kaika? Ya gyada kai da sauri, "Ehh mommy. Ranar litinin zan fara zuwa" tayi mamaki, kuma tayi farin ciki sosai don dama abinda take tunani kenan, sai dai bata san ta inda zata fara bane. Ya coge a bakin kofar kicin din yana kallonsu ita da dan nata suna ta bashi sha'awa. A jikinta taji ana kallonta, don haka ta waiga a nutse ta kalli bakin kofar, ya soke hannuwa a aljihun jeans dinsa, idanunnan nashi farare tass suna kanta, ko data waigo ma har idanu suka hada amma sai ita ce ta janye nata, yace "makaranta na kai shi, ranar litinin zai fara zuwa. Ai kinsan Nurul-Huda to can ne, nasan kin san tsarin su tunda su Adamu ma a can suke" ta gyada kai kanta a kasa tana kokarin kaucewa hada idanu dashi don suna jefa ta ne a cikin wani yanayi da kasala mai yawa, tace an gode, amma da ka bari nima da ina shirin zan kai shi. Yace tunda na riga ki kaishi ai an wuce wajen koh? Ta sake gyada kai, "an gode!" ya dan saki murmushi mai sauti, "naaa don't mind! Al-Ameen kamar da ne a gareni.... Uniform din sa na dakin ki" ya juya ya tafi, ta bishi da ido zuciyarta na kwarzanta mata kirki irin na Modibbo, amma tana hana bakinta fada, musamman kalmarsa ta kusan karshe a gareta, ".... 'da ne gareni.....!" zuciyarta ta jima tana nanata maganar a cikin ranta, daga karshe ta watsar da komi ta cigaba da girkinta dan ta na mata surutun wajajen da suka je. Tana gama girkin ta warewa Modibbo nashi, ta kwashi sauran suka kule a daki ita da babynta.
Ranar litinin tunda asubahi bata koma barci ba, ta je ta hada breakfast ta kuma hadawa Al-Ameen lunch box wanda zai rike mai ciki sosai tasan idan ya tafi sai biyar zai dawo na yamma. Ta koma daki ta tashe shi yayi wanka, ta shirya shi tsaf cikin uniform din makaranta. Dogon wando ne trouser blue mai cizawa sosai, sai shirt grey, neck tie kalar wandon, bakin belt da takalmi sau ciki shima baki. Ta taje mishi tattausar sumar kanshi wadda ta kwanta lambam a wuyanshi, yayi kyau Masha Allah kamar ka sace shi ka gudu. Ta dube shi tun daga sama har kasa, komi ya hau perfectly, ta kara gyara mishi zaman name tag din shi a aljihun shirt dinshi, an rubuta Al-Ameen Muhammad Marwan.... Tayi murmushi tace u look muah baby! Dariya kawai ya mata. Ta zaunar dashi akan cinyarta tana bashi abinci a baki.
Karfe bakwai da rabi Modibbo ya bayyana a bakin kofar da yake yau bata rufe kofarta ba, hannunsa rike da brief case alamun yayi shirin tafiya ofis, yace "baby zo in sauke ka a school kafin a samo maka direban da zai dinga hidimar makarantar ka" ya warci school bag dinsa ya tafi yana cewa mommy sai na dawo! Ta mike tana dariyar dokin da yake tace gandoki kenan! Muje in maka rakiya toh!! Ta kamo hannunshi suka bi bayan Modibbo suna er hirarsu. Modibbo jin sa ya dinga yi kamar ya dora hannu aka yayi ta kwarara ihu saboda tsabar farin cikin daya cika mishi ciki, yau shine zai je wajen aiki cikin rakiyar Ameenah? Duk da cewa dai rakiyar was not meant for him, amma shi wannan abin alfahari ne a gare shi ba karami ba kuwa, don haka har ya shige mota ya tasheta annurin dake shimfide a fuskarsa ya gaza boyuwa sam. Ta bude gidan gaba Al-Ameen ya shiga, ta dora mishi jakarshi da lunch box akan cinya ta duka ta sumbaci goshinsa tace Allah ya tsare baby nah!, ayi karatu sosai fa, kuma ka ci abinci kaji good boy? Ya gyada mata kai yana mata murmushi, da hannuwanta biyu ta dinga musu bye-bye har suka tafi.
☆☆☆☆☆☆☆
Hausawa suka ce 'mai da wawa!' da wannan karin maganar Modibbo yayi amfani a matsayin makamin yakin yakar zuciyar Ameenah, tsawon sati biyu yana hidimar kai da dauko Al-Ameen daga makaranta har dai aka samar masa da direba, bai taba fita ya dawo hannunsa babu leda ko wani abu da zai ba Al-Ameen ba, haka a kowane dare su kan zauna a falo shi yake koyawa yaron duk wasu homeworks dinshi ya kuma wayar mishi da kai akan abinda bai gane ba. Idan kaji yanda yake maida kansa yaro yana biyewa Al-Ameen suna wasa abin sai ya matukar baka mamaki, cikin kankanin lokaci yaron yayi matukar sabawa da Modibbon kamar wanda suka shekara a tare. A hankali sai Ameenah ta fara cire shi daga layin mutane masu girman kai da baudadden hali data saka shi, ta maido shi layin mutanen kirki masu girman kai. A cewarta duk rashin fahimtar halin shi ne ya kawo haka, amma yanzu data fara fahimtar shi ta fara gane irin halayen shi.
Saboda shi Ameenah ta daina rufe kofa, don ko ta rufe sai Al-Ameen ya dameta akan ta bude shi dai hira zai je wajen daddyn shi, watarana ma idan ya tafi a can yake kwana. Tun dai tana mishi fada har ta gaji ta daina tunda ba ji yake yi ba, ta kawo na mujiya ta zuba musu.
*********
Yau ranar talata, yawancin ma'aikata da dalibai duk suna gida ne a dalilin public holiday da ake yi. Tun data shirya breakfast suka koma kan gado suka nade, bata farka ba sai wajen karfe goma na safe. Al-Ameen na zaune dangargar akan gadon da puzzle game a hannunsa yana kokarin hadawa. Ta ciccibe shi yana zillon ta sauke shi ya gama game din shi tayi kunnen uwar shegu dashi, wanka ta mishi ta nado shi a babban tawul ta dire shi akan gado sannan itama ta shiga wankan. Ba wani jimawa ta fito daure da tawul pink mai matsakaicin tsayi tunda bai sauka har gwiwarta ba, ta janyo jakar kwalliyar Al-Ameen ta nufo shi, hankalinsa na kan game dinshi, ta zauna a gefen gadon tana kokarin tsiyaya mai a tafin hannunta, tace come on baby, zo a shafa mai. Ya kallota cikin shagwabe fuska, "mommy don Allah ni dai ki bari in gama game dina, please kinji??" tace to ai ban hana ka game ba ko? Cewa nayi kawai kazo in shirya ka. Ta fada tana kokarin janyo shi, kafin ta ankare ya dira ta daya gefen rike da game din ya nufi kofa da gudu, ta dafe kai "da alamun shiririta ce akan Al-Ameen yau" ta fada a hankali. Tashi tayi tabi bayanshi da dan gudunta tana kwala mishi kira, dakin Modibbo ya fada, bata yi wata wata ba ta rufa mishi baya itama.
Yana tsaye a gaban mirror daure da towel, shima fitowarsa daga wanka kenan ya tsaya yana karewa kansa kallo ta cikin dogon yaro, ya dan fada kadan. Yana ta sake-saken yadda zai bullowa lamarinsa da Ameenah don a gaskiya hakurinsa ya kusa karewa, a matukar takure yake. A daren jiya kaf bai samu yayi barci mai kyau ba, yana ta kokarin nemawa kansa mafitar data dace dashi don zaman nan da suke yi da Ameenah baya jin zai iya jurewa su ci gaba da yin irin shi.
Yana cikin wannan halin yaji an banko kofar dakinshi an shigo da gudu ana kiran daddy!! Cikin sauri ya juya, Al-Ameen ne, ya labe a bayansa ya cukuikuye shi, sai gata itama ta shigo da dan gudunta, idanunta a rufe ta nufe shi tana magana, "ka zo in shirya ka Al-Ameen sai ka hau guje-guje? Ni nace zan hana ka yin game din ka ne...???"
Modibbo kam mutuwar tsaye yayi ya kura mata ido, rabin gashinta data jika ya zubar mata a kirji da gadon baya yana digar da ruwa, ga santala-santalan kafafunta masu tafiyar da hankali da suke lullube da wasu bakaken gassu suma har yanzu da sauran lema a jikinsu, ya sauke kallonsa akan jajayen tausasan lebbanta tana wa Al-Ameen magana, ya kai harshe ya laso siraran bakaken lebbansa yana jin wani irin yanayi yana ratsa shi, "tsuntsu daga sama gasasshe!!" ya fadi hakan a can kasar zuciyarsa.
©Jeedderh🐾
[5/2, 11:08 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•60•°🐾
Dariyar Al-Ameen ce ta dawo dashi hayyacinsa, ya maida dubansa gare su. Yaron ya mayar da abin wasa, idan Ameenah ta biyo shi nan sai yayi can, daga karshe dai ya mata wayo ya sille ya bar dakin ta daga kafa zata bishi, Modibbo ya saka mata kafa, ta tafi lauu zata fadi.... Cikin saddakarwa ta runtse idanunta tana sakin er kara kadan, sai ji tayi caraf! Hannu ya ratsa ta tsakanin kirjinta an rike mata towel, ta tsaya cikk!! Ita bata kai kasa ba, kuma ba a tsaye take ba. Wani electric shock ya dinga ratsa ta a daidai shacin kirjinta inda yatsun shi uku suka ratsa, ya zuba mata mayatattun idanunshi masu cike da tarin sonta da sha'awarta matsananciya. Sakonnin dake fitowa daga karkashin zuciyar shi suna biyowa ta cikin idanunsa suna ratsawa ta nata idanun masu girma ne, nauyinsu yafi karfin er juriyar data rage a cikin zuciyarta, kafafunta ne suka shiga rawa cikin nuna gajiyawa da yanayin tsayuwar data yi, ta fara tafiya luuuu cikin sagewar kafafu, yayi azamar janyo ta da karfi ta fada cikin faffadan kirjinsa, yasa hannuwanshi duka biyun ya rungumeta tsantsam, ya nutsa kanshi cikin gashinta daya ratso ta gefen wuyanta yana shakar daddadan kamshin shampoo data yi amfani dashi ta wanke gashin. Zazzafan hucin nasa ya dinga ratsawa ta cikin gashinta yana riskar fatar wuyanta, yana huda duk wasu hudoji da kofofin jikinta yana aikawa gangar jikinta da kwakwalwarta wasu irin sakonni masu wuyar kwatantawa. Ta fara zame jikinta daga nashi a hankali idanunta a lumshe, hakan yasa ya dan sassauta rikon daya mata ta dago fuskarta yana kare mata kallo, tsawon wasu mintuna ya kira sunanta cikin wata murya data saka ta doubting Anya Abdul-Rasheed ne kuwa?? Ta bude idanunta a hankali ta sauke su a fuskar shi amma ba cikin idanunshi ba, yace "you are beautiful Ameenah! Komi naki mai kyau ne.., idanunki... Hancinki.... Girarki... Kuncin ki... Bakin ki...." yana yi yana sumbatar duk inda ya fada, ya kalli tsakiyar idanunta ya kara narkar da muryar shi yace "n I fancy your mouth most..." ya kai mata wani deep kiss a bakin wanda ya kusa shidar da ita, cikin yanayi na fita hayyaci ta kankame hannayenta da zuciyarta ke azalzalarsu dasu rungume Modibbon yadda zai ji dadin sumbatar ta da kyau. Ya fara manna fatar bakinsa a wuya, kafada, zuwa saman kirjinta idanunsa a lumshe. Yayin da aka fara maida bayanai tsakanin gangar jiki da zuciyoyin Ameenah, gangar jikin na matukar son abinda Modibbon yake mata, zuciyar tana so sai dai wata zuciyar ce dai take kushe hakan, take hana mata jin dadin abubuwan da yake mata, tana ce mata wai "wanin Marwan ne fa!" daya zuciyar tace "ko ma Uban Marwan ne, desire have no boundaries, idan ka samu dama kawai ka kawar da ita at the immediate moment...." sai suka saka Ameenah cikin rudani da canki-cankar wanne zata bi, wanne zata kyale??
Hannunshi yasa yana kokarin balle dan tawul din nata, ta saka hannunta tayi saurin dafe nashi. Ya dago idanunshi da suka canza launi daga farare tas-tas zuwa reddish brown, ya saka idanun cikin nata yana watsa mata wani hargitsattsen kallo, sai ta maida nata idanun ta kulle gam saboda ta fahimci ma'anar kallon; he needs ha, very badly.
Cikin murya mai kama data mashayan da suka gama buguwa yace "Ameenah! Don't you need me??" ta dan dago da saurinta tana kallonshi, idanunsa na kanta har zuwa lokacin, sai tayi azamar dauke nata. Yace "idan ke baki yi ni ina yi Ameenah, baki ga kokarina ba? Watanni fiye da uku na zuba miki ido kawai ina kallo, kin san irin wuyar da nake sha kuwa wajen kokarin dauke kaina daga gare ki?? Naji baki so na..., amma don Allah kar ki hana ni morar kadan daga cikin baiwarwakin da Allah ya miki, ni fa mutum ne ba dutse ba Ameenah...." bai bata damar magana ba ya kamo lebbanta da bakinshi yana tsotsa, a lokaci guda kuma ya saki towel dinta yayi kasa, ya hada ta da faffadan kirjinshi wanda gashi yayi wa kawanya sauran damshin jikinsu ya hadu ya haifar musu da wani irin tashin tsigar jiki, wato wata irin salo yake caressing fatar bayanta. Akwai wani magic dake tattare da hannunshi dama shafar da yake mata gabadaya, ko waye tayi imanin baka isa kayi resisting tarkon shafar nan mai batar da hankali ba, don haka ba tare da kara wata shawara ba gangar jikin Ameenah ta sallamawa Modibbo kanta, tabi bayanshi suka lula duniyar Sama-Jannati.......
Sai da suka gama samarwa kansu nutsuwa reality strucks Ameenah, wani bakin takaici marar misali ya ziyarci Ameenah, ta rushe da kuka wanda ke bayyana zallan bakin cikin da take ciki. Yana kwance a gefenta idanunshi a lumshe, har zuwa lokacin bai gama regaining consciousness nasa ba, sai daya ji an kira sallar azuhur sannan ya mika hannu kasan gado ya lalubi towel din shi da yayi fatali dashi dazu ya daura, ya kai dubanshi ga Ameenah, ta gaji da kukan har barci ya dauketa, bargo ya ja ya rufa mata. Toilet ya fada ya kimtsa jikinshi ya fito, a dakin yayi sallah don tuni masallaci an sallame, ya fito ya leka dakinta Al-Ameen na kwance shima yana ta kwasar barci, sai ya sauka kasa. Abincin kari data hada na kan dinning a bude, ba mamaki Al-Ameen ya ci kuma bai rufe ba, ya tattara komi ya kai kicin ya hada sassaukan abinci wanda zai mata dadi a baki, ya gama ya hada komi a kan babban tray ya hau sama. Tashinta daga barci kenan tana tsaye gaban gado daure da dan tawul dinta, idanunta sun dan tasa kuma sun danyi ja saboda kukan da tasha kafin tayi barci. Ya maida kofar dakin ya kulle ya saka keys din cikin aljihun rigar sa, bandaki ya shiga bayan ya ajiye tray din hannunsa ya hada mata ruwan wanka, ya fito ya kamo hannunta ya kaita har cikin bandakin sannan ya fita, dakinta ya koma ya dauko mata jallabiya ta mata baka da hijabi da underwears ya kawo mata, lokacin ta fito wanka ta amsa ta saka ba tare data kalleshi ba ta tada sallah. Ya sake komawa dakinta ya dauko hand dryer dasu mayukan gashi ya dawo dakin. Tana gamawa yaja hannunta ya zaunar da ita akan stool, ya jona dryer a socket ya fara kafar mata da gashin yana yi yana tajewa yana shafa mai, daya gama ya dauko mayuka ya shafe mata kai yasa comb ya taje ya kawo tafkeken band ya tamke mata gashin, mamakinsa kawai daya cika ta sai ta kasa magana, tana dai tambayar kanta a inda ya koyi gyaran gashi haka.
Daya gama wannan sai yaje ya dauko abincin daya hada ya kawo mata har gabanta ya ajiye, yace ci abinci Ameenah nasan babu abinda ya shiga cikin ki yau" wannan kulawa da yake nuna mata sai ta saka jikinta yayi sanyi, ta tsinci kanta cikin wani irin bakon yanayi data kasa tantance ko meye ne, da kansa ya dinga bata abincin a baki har ta koshi, sannan ne fa shima ya fara cin abincin cikin nuna rashin sassauci alamun yunwa yake ji sosai. Wani irin tausayin sa ne yayi mata kawanya a zuciya, bata tantance Ba sai gata tana xubda hawaye, hankali tashe ya dakata da cin abincin da yake yi yace Ameenah lafiya? Cikin murya irin ta wanda ke son rushewa da kuka tace ni dai ka bude ni in fita.... Yace matsalar kenan? Ta gyada kai, yace it's okay daina kukan. Ya mika mata keys din ta amsa da sauri ta tashi ta bude kofar ta fita.
©Jeedderh🐾
[5/2, 11:09 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•61•°🐾
Kan gado taje ta kwanta a bayan Al-Ameen dake barci, ba wai don tana jin barcin ba sai don tana so tayi refreshing din kwalwarta ta kuma bata damar yin naxari. Ta lumshe idanunta tana tuno moments din dazu, idan ba kunnenta ne ya jiyo mata ba daidai ba kamar taji Modibbo yana ce mata yana son ta, yana kuma rokonta akan itama ta so shi, ta kasa gaskanta maganar, tafi dangana hakan da sambatu kawai. Sai dai me yasa ta kasa tunanin maganganun Modibbo a gareta? Haka ta cigaba da tunanika har babynta ya tashi, ta mike da niyar samo mishi abinci.
Yinin ranar da tunanin maganganun Modibbo ta yini, are the words genuine? Ko kuwa dai kawai sambatun ne kamar yanda take zargi?? Ranar har a cikin barcinta mafarkin Modibbo da maganganunsa ta dinga yi, wannan lamari ya matukar daure mata kai. Da safe ta gama shirya Al-Ameen, tana zaune akan resting chair dake cikin bedroom dinta shi kuma dan nata na gefenta yana bitar karatunshi, ta zabga uban tagumi da hannuwa bibbiyu cikin yanayin rashin cikakken sukuni, da taji alamun taba kofa sai tayi saurin kai dubanta ga kofar. Cikin wannan halin ne ya bayyana tsaye a bakin kofar, cikin shiga ta wata danyar shadda ruwan jinin kare, ya dora hular nan kamar don shi aka yi ta yanda ta zauna mishi das a goshi. Ameenah ta tsinci kanta cikin faduwar gaba, ta kuma samu kanta da kura mishi idanu kurr kamar mai son gano wani abu a jikinsa. Al-Ameen ya tafi da gudu ya rungume shi yana gaida shi, shi kuma ya dauke shi ya rike a hannu yana mishi en wasanni, wannan so da yake nunawa Al-Ameen shi yake kara tsuma zuciyar Ameenah. Ya kalleta yana dan murmushi, tayi saurin sadda kanta kasa, yace madam ina kwana?? Ba yau Modibbo ya fara gaida ta ba, amma irin kunyar da taji yau bata kadan bace, cikin rawar murya tace "eyhh?? Ina kwan....na..!" ya dubeta da dan mamaki, sai kuma yayi dan murmushi suka fita daga dakin shi da Al-Ameen. Tayi kokari ta dauki jakar Al-Ameen da lunch box dinshi tabi bayansu har gaban mota, bayan sun gama sallama da danta ya shiga mota da yake direban shi bashi da lafiya, sai ta duka tace "Allah ya kiyaye hanya!" Ba da Al-Ameen tayi maganar ba yau, dashi take. Yayi sararo yana binta da kallon mamaki mai kama dana tsoro, tambayar kanshi yake anya Ameenah ce kuwa? To abu ne wanda bai taba kuskuren fita daga cikin bakinta ba a tarihin zamansu. Yayi ta maza ya amsa da "Allah yasa" yaja motar suka tafi. Tana nan har suka fita tana kallonsu, ita kam ba karamin jin haushin kanta tayi ba da wannan katobarar da tayi, me ke damunta ne? Zuciyarta ta fara kawo mata abubuwa da dalilai iri-iri, ta dinga girgiza kai, "no Ameenah! Not so soon, please u can't fall in love again....!".
Duk yadda taso ta kaucewa tunanin Modibbo a wannan yinin abin yaci tura, komi take yi yana nan makale a zuciyarta, hotunan different events dinsu dashi ya dinga dawowa a idanunta. Ameenah fa ta susuce, kafin lokacin dawowarshi yayi ta gama galabaita, shi kadai take son gani. Lokacin data ji karan motarshi na shigowa gidan sai ganinta tayi a bakin windon ta tana lekensu kawai, suka fito daga motar, hannunshi na cikin na Al-Ameen dayan kuma ya riko jakar Al-Ameen din suka shigo falo suna ta hirarsu. Murmushinsa ya saukarwa jikinta wata irin kasala, ta koma bakin gado ta zauna dabas cikin rashin kwarin jiki. Yau ko fita tarar Al-Ameen din bata yi ba don bata da kuzarin tashi sam. Dare yayi suka kwanta barci amma atafau barci yace bai taba sanin idanun Ameenah ba, ta dinga birgima akan gadon tana juyi, abin mamaki fuskar Modibbo kawai take mata gizo a dakin, murmushin sa, dariyarsa, kirkinsa, kai komi nashi taji yana burgeta.....
Ga dai sheda a bayyane mai nuna cewa ta fada tarkon so, amma da gangan taki yardan ma ranta hakan, a ganinta babu space a zuciyarta na wannan abun yanzu.
Kwanaki suka cigaba da turzawa Ameenah ta cigaba da nutsewa cikin kogon son Abdul-Rasheed, a wadannan lokutan shi kansa ya lura da canzawar da tayi sai dai bai taba kawowa ransa wai so bane don ya riga ya gama fidda kanshi daga cikin masu wannan sa'ar.
Yau da dare har ta kwanta barci ta tuna Al-Ameen baya dakin, ta diro daga gadon ta dauki dogon hijabi ta zura ta tafi dakin Modibbo tasan yana can, sai tayi amfani da wannan damar taga wannan kamilalliyar muryar ta Modibbon, wadda ta hana ta samun lokacin kanta a yinin yau. Tun yau bata saka shi cikin kwayar idanunta ba, don haka a matukar dokance ta tura kai dakin zuciyarta cike da burin dora ido akan fuskar tashi.
Al-Ameen na kwance akan gadon shi yana barci kamar yadda ta zata, shi kuma yana tsaye ya juyawa kofa baya yana tsane sumar kanshi da dan karamin towel daga shi sai dan karamin towel a kugun shi. Ta daga idanunta a nutse tana kara kallon Surah da Suffa irin ta manyan maza masu kirar sadaukai. Bayan shi take karewa kallo cikin tsananin dukan zuciya, bayan kyawun hali da kyawun fuska na Modibbo ashe akwai wani boyayyen kyawun a tattare dashi wanda bata sani ba sai a yau dinnan da take kallonshi in his real Image?! Komi ake nema a wajen cikakkun maza da suka amsa sunan Isassun Mazaje to Modibbo ya tara fiye da nasu ya kuma zarta su, irin halittar su halitta ce mai wuyar samu, irin halittar da kowacce 'ya mace da tasan ciwon kanta za tayi fatan samu, ta kuma ji matukar haushi idan ta rasa irinsu. A yau ta daina karyata kanta akan son Modibbo, tana dai kokarin kare kanta ne game da yadda aka yi ta fada tarkon sonsa. Abdul-Rasheed namiji ne mai kyawun halaye da kyawun suffa, ta kowace fuska bashi da wata nakasa, bugu da kari yana sonta, tana hango matsanancin sonta a kwayar idanunsa duk da bai fada mata ba. Halayensa abin so ne, kuma ko kaki Allah ba zaka kushe shi ba don bashi da abin kushewar, ta kowanne fanni dai ya hadu dari bisa dari. Ita zuciya an halicce ta ne da son mai kyautata mata, Modibbo yana kyautata mata matuka, tunda tazo gidan bata ga rashin kyautawa daga gare shi ba daidai da kwayar zarra, kenan bata da laifi, kuma bata yi laifi ba idan taso MODIBBO-ABDULRASHEED a BAYAN RAN MARWAN????!.......
Sai ta samu kanta da juyawa ba tare data dauki Al-Ameen ba, ba kuma tare da tayi magana ba. Ta koma daki ta kwanta akan gado, ta yarda son Modibbo take, amma ta yaya zata sanar dashi halin da zuciyarta ke ciki game dashi a matsayinta na 'ya Mace? Me zata yi da zai karkato da hankalin Modibbo gareta???!
*Ameenah fa ta shiga cikin cakudaddiyar kura, tana bukatar shawarar ku. Lol.... Godiya da jinjinar ban girma ga masu kokarin bibiyar littafin ba gajiya, ina alfahari daku a duk inda kuke, ina kuma godiya bisa dimbin kaunar da kuke nuna mun... I love you all* 😍😘
©Jeedderh🐾
[4/27, 6:58 AM] +234 703 480 5764: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•62•°🐾
Kwana daya, biyu suka wuce cikin nazari da tursasawa zuciya son neman mafita. Cikin wannan halin ya tafi wata seminar Abuja ta kwana biyar, daga sama kawai yaji maganar don sai a ranar tafiyar da safe aka bugo waya aka gaya mishi, ba tare da wani bata lokaci ba ya shiga shirin tafiya, ko babu komi yana son yin nesa da Ameenah na dan lokaci, yana so ya gaskata abinda ya fara hangowa a cikin kwayar idanunta, idan hakan ya zama gaskiya ya tabbata zai zama bashi da sauran wata damuwa a cikin ransa.
Ameenah sai tashi tayi daga barci da safe taci karo da takardar daya rubuta mata cewa yayi tafiyar sati daya zuwa Abuja. Modibbo daya san a ranar Ameenah tayi shirin confessing soyayyarta gareshi na tabbata da ba zai tafi ko nan da can ba. Da bakin ciki ya tokareta a makoshi ta rasa yadda zata yi, sai kawai ta dukunkune takardar ta jefa a baki ta taune, ta zauna dabas akan kujerar dinning inda anan ne ta samu takardar, ta nutsa duka hannayenta a cikin gashinta, yanayinta na nuna nan da kowane lokaci zata iya kwalla ihu mai karfi. Ta share wasu kyawawan mintuna ashirin a wajen, da kyar ta iya jan kafafunta ta isa ga fridge ta bude ta dauko gorar Mountain Dew ta bude ta kurba, sanyin lemun da dan gas da tsamin shi suka ratsa makoshinta zuwa cikinta, ta lumshe idanu a hankali tare da furta "Mashaa Allah!" sai data tashi lemun tas tayi jifa da goran, ta haura sama ta fara aikace-aikace zuciyarta na gaya mata ba zata zama sakara, kuma sukuku ta dalilin Abdul-Rasheed ba, sai dai duk kuri ne kawai take yi don kuwa komi take yi tunaninsa na nan makale da ita, duk yadda tayi don ta yakice shi abin yaci tura.
Data ga kadaici yana neman ya dameta sai ta dauki wayarta ta kunna data connection, rabonta da social medias har ta manta sai yau. Messages suka yi ta shigowa ta e-mail dinta da facebook daga mutane da dama wadanda ta sani suna taya ta murnar auren data yi, sai ta samu kanta da binsu tana karantawa daya bayan daya tana murmushi, tana jin farin ciki marar misaltuwa yana ratsa mata har cikin kokon kanta. Anan ta yini akan waya tana ta shiririta, ta shiga nan site din ta fita ta koma wancan har babynta ya dawo daga makaranta, shima yayi ta mata mitar ina daddyn shi ya tafi yayi kewar shi ta dai samu ta taushe shi kan cewa zai dawo kwanan nan, amma duk da haka da an dan jima sai yace Mummy ina daddy ya tafi? Mummy yaushe zai dawo? Mommy ki kira min shi a waya mu gaisa... Tun tana iya amsa shi har ta gaji ta daina.
Kwana biyu suka zo suka wuce mata cikin tsananin kewar Modibbo, kewa irin wadda bata taba jin kwatankwacinta ga kowace irin halitta ba. Har mamakin kanta take yi, bata taba zaton cewa zata so wani mutum ba, so irin wanda take yiwa Modibbo a bayan ran Marwan. Ba zata ce bata dandani irin sa ba a soyayyarta ta baya ba, amma zata iya cewa bata dandani rabin azabar da take dandana a yanzu ba.
Da yamma ta gama hada musu abinci sai ta hau sama dashi, tun kafin ta karasa take jiyo muryar Al-Ameen yana hira sama-sama, ta danyi murmushi tana girgiza kai. Ta land-line din dake falon yake amsa wayar, ya dago ya kalleta yace "Mummy daddy ne ya kira ni, yace he misses me alot" ta dan tsaya tana kallonshi, sai kuma tayi murmushi tace da gaske? Ta fada tana wucewa kan karamin dinning ta ajiye kayan hannunta. Ta bangaren sa kuwa gabadaya ji yayi yana shirin dauke numfashi saboda muryarta daya jiyo ta cikin wayar, ya lumshe idanunsa cike da wani irin shauki yana sauke ajiyar zuciya da sauri, gani yake babu wanda zai iya yin namijin kokarin da yayi. Kwana biyun nan da yayi jinsu yake kamar shekaru biyune, yana son Ameenah, yana kuma kewarta, sai dai yana son ya koyawa Ameenah son shi ne ta karfi da yaji, so yake ta zama tashi har abada, don haka zai jure komi don ganin burinsa ya cika....
Muryar Al-Ameen ta ratsa dodon kunnenshi, yayi saurin dawowa hayyacinsa ya amsa a hankali "yes baby... Let's hang up now, zan kira ka gobe da yamma war haka in shaa Allah kaji?" ya katse wayar ba tare da yaji ta bakinshi ba, Al-Ameen ya kalli telephone din yana tabe baki, tace yah dai baby? Ya kara tabe baki daddy ne ya katse wayar bamu yi sallama ba. Ta matso ta zauna gefenshi, tace yi hakuri kaji? Kila yana da abun da yake so yayi ne urgently kaji baby na? Ya gyada kai, "ai yace zai kira ni gobe wai" tayi saurin cewa da yaushe? Yace wai cewa yayi kamar yanzu. Tayi murmushi ta rungumoshi jikinta ta nutsa hannunta a tattausar sumar kanshi tana shafawa, tace it's okay baby, ka daina frowning fuskan ka kaji? Zai kira ka OK?? Ya gyada kai, ta kara murmusawa "good boy, zo muje muyi alwala an kusa kiran sallah" suka mike a tare suka tafi daki don dauro alwala.
©Jeedderh🐾
[4/27, 6:58 AM] +234 703 480 5764: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•63•°🐾
Ranar kuwa tun da yamma tayi ta kasa ta kasa ta tsare a falon taki matsawa ko nan da can, tana daidaitar lokacin daya kira jiya ta samu tayi dabara ta tura Al-Ameen bayan gida yayi wasa, shi tuni ma ya manta da zancen daddy yace zai kira shi. Bai jima da fita ba kuwa land-line ya shiga kara, ta zabura ta isa ga wayar a sukwane jikinta har wani mazari yake, sai data daidaita sautin muryarta kafin ta daga wayar a nutse ba tare data yi magana ba, "Hello baby Al-Ameen" ya fada cikin tsararriyar muryarsa mai cike da ginshira wadda take fita tar-tar tamkar ansa abin tace murya an tace ta. Ta kasa magana saboda yadda muryarsa ta ratsa ta tana kassara mata gabbai, shirun yaji yayi yawa ya sake cewa "Al-Ameen?? R u there?" duk yadda taso ta daure abin ya gagara, hakan nan ta samu kanta cikin rawar murya, "ba... ba Al-Ameen din ban.... ne....!!" ya runtse idanu da karfi yana jin wasu irin particles na mishi yawo a cikin jinin jiki, ya samu ya cije ya aro dauriya ya yafa a birnin zuciyarsa, sai dai sautin muryarshi ya canza zuwa muryar wani da matsananciyar kewa da so ke azabtar dashi sosai, yace "ohhh, ina Al-Ameen din yake?" yanayin yadda ya canza muryarshi ya saukar mata da natsuwa a cikin zuciyarta, tace yana bayan gida yana wasa. Yace "OK, idan ya dawo kya gaishe shi, m hanging up!" tayi saurin cewa ba ce... Ya dakata da kokarin kashe wayar da yake yi yace ina sauraronki. Sai data turza ta cije har da su runtsa idanu ta samu ta warto maganar da kyar ta furta, tace "yaushe zaka dawo ne??" cikin nuna halin ko in kula da kalaman nata, amma fa a can kasan zuciyar shi kamar farar takarda don a ganinshi ta fara damuwa dashi ne, zargin da yake yi kan cewa kila tana son shi zai tabbata, yace kin damu da in dawo ne?? Tayi saurin dawowa cikin hayyacinta, ta dauko in-ina tana son gyara katobarar da tayi, tace "a... a'ah... ko kadan... Akan me ma zanyi kewar ka.., kawai.. Kawai dama ina son zan fita ne... kuma baka nan". Ya saki murmushi mai sauti yace "it's okay Ameenah, na fahimce ki. In shaa Allahu zan dawo very soon, a gaida Al-Ameen!" ya kashe wayar yana murmushi. Tayi tsaye a gaban desk da wayar a hannunta tana jujjuyawa zuciyarta cike da takaicin maganar da tayi da maganganun daya gaya mata.
Washegari take ji a bakin Al-Ameen wai yace gobe zai dawo, da gaske ta tsinci kanta cikin farin ciki marar misaltuwa. Washegari data kama juma'ah tana dawowa daga raka Al-Ameen ta shiga gyaran falo tun daga sama har kasa, har tsarin falon ta canza. Ta shiga dakin shi zata gyara, sai taga kamar wuce gona da irin zai yi yawa, sai kawai ta basar ta sauka kasa ta shiga kicin. Abincin gabashin en kasar India ta fara preparing sai dai kayan kawai ta tanada ta ajiye da niyar sai ya dawo zata dafa yanda zai ci shi da dumin sa.
Tunda taga an kira sallar la'asar bai karaso ba tace kila shigowar dare zai yi ko kuma ta yamma, tayi wanka ta fito tayi shafe-shafe a jikinta sosai na mayuka iri-iri da body sprays har da humra duk inda ta gitta sai ta bar kamshi, amma fuskar ba komi sai hoda data murtsika ta shafa lip gloss mai kyalli don bata son ta zake da yawa ne. Ta tsaya a gaban wardrobe tana karewa clothes dinta kallo, idanunta ya sauka akan wata atampa mai kama da Kampala orange mai ratsin purple dinkin bubu, ta janyo ta saka. Sosai rigar ta fito da shape dinta ta fito kamar wata er tsana, dan kwalin yafa shi tayi kawai don bata cika shiri da dankwali ba. Ta koma falon sama ta kame tana latsa waya sai baza kamshi take yi kamar wata first lady. Al-Ameen ya dawo daga school da yake karfe hudu suke dawowa ranar juma'ah, ta tare shi kamar yadda ta saba tana mishi oyoyo, ta mishi wanka yaci abinci suka zauna tana mishi bitar karatun da take koya mishi a gida.
Karfe biyar da en mintuna suka ji karar horn din mota, Al-Ameen ya tafi bakin taga yana leke. Tsalle yayi ya saka ihu, ko ta kanta bai bi ba ya sauka kasa da gudu yana ihun ga daddy! Ameenah taji ta wani irin tsamo-tsamo kamar wadda aka jefa cikin ruwa, taji kamar ta falla da gudu itama taje ta tare shi, sai dai ba zata iya hakan ba, sai taje bakin window tana lekensu, ya durkusa rungume da Al-Ameen suna dariya cike da dokin ganin juna. A jikinshi yaji kamar ana kallonshi, cikin dabara ya dago kanshi sama inda take aikuwa suka hada idanu, cikin wani irin zafin nama ta maida bayanta ta jingina da bargon dakin jikinta na rawa, zuciyarta na addu'ar Allah yasa bai ganta ba. Murmushi ya saki a tausashe yaja hannun Al-Ameen suka shiga falon yayin da maigadi ya biyo shi da kaya. Tun daga tsarin falon da yadda yake fitar da kamshi mai dadi ya gamsu da yadda ake dokin dawowar shi, zuciyar shi ta kara wankewa tayi tass, hai yake ya kalli kwayar idanunta yaga shin meye gaskiyar abinda yaji a muryarta ranar nan, shin da gaske itama tana kewar shi??
Tana zaune akan kujerar falon suka shigo shi da dan nashi, tun shigowar su taji gabanta na mugun faduwa, ta kasa daga ido ta kalli inda yake duk da cewa abinda zuciyarta ke muradi kenan, gani take kamar idan yaga fuskarta ma kawai ba idanunta ba zai iya hango matsananciyar kewar shi take dankare a cikin zuciyarta, ta kuma kasa boyuwa akan kyakkyawar fuskar ta. Har ya zauna akan kujerar dake fuskantar ta Al-Ameen ya dare kan cinyarshi yana mishi surutai amma hankali da idanun shi na kanta. Yafi minti biyar a zaune a gun amma bashi da alamun yi mata magana, da kyar ta iya daurewa ta dago ta kalleshi a kaikaice, tace "sannu da zuwa!"
©Jeedderh🐾
[4/27, 6:58 AM] +234 703 480 5764: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
*_I Dedicated this page to my one and only Sisi, Anti Zee!! Love ya_*
🐾°•64•°🐾
Ba karamar dauriya yayi ba wajen danne zuciyarshi dake azalzalarshi daya tashi tsaye ya kwarara ihun farin ciki ba, yaja fuska sosai ya amsa da mun same ku lafiya? Taji wani dummm a tsakiyar kanta, me ke faruwa da expression din fuskar shine?? Bai ji dadin tarbar data mishi bane ko kuma bai yi kewar ta bane? Kunya ta kamata kamar ta nutse a kasa, bai san ta yaya ta lalubo courage din data mishi magana dashi bane hala?? Sai ta tashi ta sauka kasa, ya bita da kallo yana murmushi har ta sauka. Shima tashi yayi ya fada dakinsa, ba wata kura da yayi don haka ya ajiye brief case dinshi akan gado ya fada bayi don watsa ruwa. Ba a fi mintuna ashirin ba yaji gidan ya kaure da masifaffen kamshin girki, ya dinga doka murmushi yana jin kansa kamar wanda ke yawo a sararin samaniya don farin ciki, ashe dai ana murna da dawowar shi? Kafin ya gama abinda zai yi har ta shirya komi akan dinning, Al-Ameen ta tura ya kira shi. Dama yunwa tun dazu take nanikarshi, ya kama hannun Al-Ameen suka sauka kasan. Tana zaune akan kujera ya wuce ta ya hau kan dining, ta taso taje da kanta tayi serving dinshi. Ya lumshe idanunshi ya jingina kanshi da kujerar dinning din kamshin da take fitarwa yana kara tsuma mishi zuciya, sai data gama itama taja kujera ta zauna, sannan ya bude idanunshi da suka canza launi yaja plate din gabanshi ya fara cin abinci. Dadin abincin ya ratsa shi har kunnuwanshi na motsi, sai dai ya basar ya dinga tura abincin kamar wanda ake tursasawa, yayin data zuba mishi ido tana jiran comment dinshi kamar yanda ya saba a kwanakin baya, yana kai lomar farko zai lumshe idanu yace Umhhh.. Yummy. Wani lokacin har thumb up yake mata da hannu. Sai dai yau ko tari bata ji yayi ba, ta dauki cokali ta dandana abincin wai taji ko bai yi dadi bane, taji kamar ma bata taba yin abinci mai dadin wannan ba a rayuwarta, sai jikinta ya kara yin sanyi, ita kam ta shiga ukunta, kar dai Modibbo ya daina sonta?. Haka tayi ta tunane-tunane ta kasa cin abincin har ya gama ya tashi ya haura sama ya barta anan. Da dare tana kwance a dandaryar kafet din dakinta tana latsa waya Al-Ameen ya shigo dakin da gudu hannuwanshi rankatakaf da kayan makulashe dana wasa tsaraba inji dadyn shi, ta tashi zaune tana duba kayan ranta kal, ko banza Modibbo yana son Al-Ameen sosai, tana da tabbacin hakan ne yake kara mata ganin kimar shi a idanunta sosai.
Washegari ma haka ta tashi tun da asubahi ta shirya mishi hadadden abin kari, ya share waje kamar jiya yaci iya cin sa ya mike babu godi bare na gode, da zai fita yace Al-Ameen yazo ya ajiye shi a makaranta tunda direban shi bai zo ba, ta dauki jakar Al-Ameen din ta raka su har bakin mota, bakinta dauke da addu'ar Allah ya kiyaye hanya, amma bawan Allahn nan haka ya tayar da motar ya tafi ko kallonta bai yi ba, Ameenah fa ta tsorace, jiki a matukar sanyaye ta koma cikin gida. Da yake ranar asabar ce tana da tabbacin ba zai jima ba zai dawo, tayi kwalliya mai daukar hankali wadda take zaton zata dauki hankalinshi ta zauna zaman jiran shi, sai dai har aka kira azuhur bai shigo gidan ba, Allah ya taimaka ma bata 6ata lokacinta wajen shirya mishi abinci ba. Bata gaji ba ta sake cancada wata kwalliyar cikin Pakistan riga da wando, rigar mai karamin hannu ce kuma ta kama ta tsam kirjinnan kamar zai tsaga rigar, wandon Kanshi ya matse mata kafafu, gashin kanta ta taje shi ya kwanta lambam har gadon bayanta, ta zauna a falon kasa tana canza channels sai tashin wani hargitsattsen kamshi take. Bai shigo gidan ba sai wajen karfe hudu na yamma, tana falon dai ta kasa ta tsare tana jiran dawowarshi, idanunta na kan TV a tashar Zee Music suna hasko wakar Bezubaan, ya jima sosai tsaye a kanta yana kallonta, tayi nisa kwarai da kallon da take yi ko motsin sa bata ji ba. Tayi mishi kyau sosai kamar ya lashe ta don kyau. Dago idanun nan nata da zata yi taci karo da nashi idanun a kanta, ta saki wani kayataccen murmushi tana kokarin kara nutsa idanunta cikin nashi yayin da yake ta kokarin kawar da nashi daga gare ta, cikin sanyin murya data gama narkewa cikin kissa tace sannu da zuwa!! Ta mike ta iso gabanshi ta karbi ledojin daya shigo dasu ta nufi kicin cikin taku mai daukar hankali, ya bita da kallo wani irin yanayi na ratsa shi. Kifi ne ya kawo Titus sai fruits. Ta wanke kifin tas ta dora a wuta zata yi farfesu, fruits din kuma ta wanke ta hada fruit salad ta dauki plate din data dora su ta haura sama, a dakinshi ta same shi yayi rub da ciki akan gado idanunshi a lumshe, ta danyi knocking, ya daga idanunshi wadanda suke cike da gajiya ya sauke su a kanta, ta danyi murmushi tana jan karamin table ta aje plate din hannunta tace gajiya ko?? In hada maka ruwan wanka ne? Ya girgiza kai a hankali, ta dan gimtse fuskar gwasaleta din da yayi, tace "toh ga fruits na hada maka, ka tashi kaci".
Ya dan yatsina fuska, "Anya? M very tired wallahi bana jin zan iya cin komi yanzu, kema I'll like it if u can excuse me plss, I want to have a rest!" ta zuba mishi idanu cikin mamaki, firgici, da tsoro. Yau ita da kanta Modibbo ke kora daga dakinshi? Me tayi mishi ne da zafi haka?? Ta mike babu gardama jiki a matukar sanyaye ta fita, ya bita da ido yana dan murmushi, "haka zanyi ta jurewa Ameenah, har zuwa lokacin da zaki sauke girman kanki da miskilancin ki bude baki ki furta kina sona yanzu!!" ya sauka daga kan gadon ya dira akan fruits din ya fara cin yana lumshe idanu. Ita kam takaici ne ya makureta sosai, wulakancin da Modibbo yake mata ya fara isarta, ko laifi ta mishi ai bai kamata ya dinga punishing dinta ta wannan hanyar ba, sai dai koma meye ne ta daura aniyar sai taga abinda ya turewa buzu nadi. Hakan da yake mata ba zai dameta ba, mijinta take so ba wani abu ba, zata jure komi don ganin ta dawo da sonta dake kokarin fita daga birnin zuciyarshi.
******
Kwana biyu ta dauka mishi kafa don ta kara samun lokacin lalubo mafita, bata daina mishi girki ba kuma bata daina mishi rakiya ba don yanzu har gyaran dakinshi tana yi, ta dai daina shige mishi ne kamar yanda ta fara da. Su Al-Ameen sun samu hutun farkon zangon karatunsu, don haka yana gida tare da momynsa.
Yau ranar alhamis, tare suka shiga kicin suka yi abincin rana dashi, tana girki shi kuma yana zaune akan kujera yana mata hira tana kwasar dariya har ta gama suka fito suka zauna a falo, ta dora shi akan cinyarta suna ciyar da juna. Da suka gama ta dauke shi suka hau sama, underwears dinshi ta dauka da nata ta shiga toilet ta wanke su tas ta shanya, tana fitowa taga Al-Ameen na kwance akan gado yana wasa da wayarta, ta nufe shi tana murmushi tace baby bana hana ka yi mun game da waya ta ba? Oya bani nan. Yace mommy dan tsaya kadan in kashe boss. Ta tsaya tana kallonshi har ya kashe boss din ya shiga gida na gaba, ta hau kan gadon ta kamo shi tace wayo ko baby? To na gano ka bani waya ta, ni bansan yaushe ka koyi game dinnan ba wallahi duk ka hana caji ya dinga zama a wayata kwanan nan. Ya kyalkyale da dariya yace to dan tsaya in baki, ta sassauta rikon data mishi tana mika mishi hannu alamar ya bata, sauka yayi daga kan gadon ya fita daga dakin da gudu, ta diro itama ta bishi da er sassarfa tana masifar Al-Ameen yana nema ya maidata abokiyar wasan shi, sai dai sama da kasa Al-Ameen baya falon. Ta bude dakin daddyn shi ta shiga a karo na biyu don tasan lallai anan zai buya, tayi iya dubanta babu shi. Tunanin bayan gida inda yake wasa ya fado mata, ta bude kofar kenan zata fita idanunta suka sauka akan wardrobe data dan bude alamun an bude ta, tayi murmushi ta nufi wajen kai tsaye. Nan ma Al-Ameen baya nan, ta dan ja tsaki ta maida wardrobe din zata rufe, sai kuma ta dakata sakamakon wani abu data gani, cikin mamaki da tu'ajjibi ta kai hannu ta dauko abin tana jujjuyawa, ganin abun take kamar a mafarki.......
©Jeedderh🐾
[4/27, 6:58 AM] +234 703 480 5764: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•65•°🐾
Idanu a zare ta daga camera sama tana jujjuyata, tana da tabbacin ko da ace mutuwa zata yi ta farfado to ba zata taba mantawa da cameran nan ba. Tana nan a sabuwar ta yadda ta rasa ta kamar yau ne aka saye ta, ta kunna ta tana kallon hotunan ciki daya bayan daya, da videos tana playing dinsu. Zuciyarta cike take da mamaki mai tattare da rudani, tambayar kanta take a Ina Modibbo ya samu camerar nan? For how long yake tare da cameran?? Ta kula akwai wasu hotunan ta wanda ba ita da kanta ne ta dauke su ba, idan dai zata iya tunawa to kayan dake jikinta a cikin hoton kayan data saka ne a ranar da zasu koma Mumbai ita da Marwan a New Delhi, washegarin ranar data rasa camerar ta, to kuma gata a cikin dakin Modibbo, me ya kawo ta nan?? Cikin rawar jiki ta shiga bincikar kayan sawar shi tana fatali dasu, can hannunta ya lalubo wata er karamar na'ura mai kama da laptop, tayi saurin janyota ta bude, da kyar ta samu ta iya lalubo makunna ta latsa haske ya kawo, list kawai ta gani na kwanakin wata, cikin daurewar kai ta dinga scrolling down, idanunta suka tsaya cak akan kwanan watan 28 February na shekarar dubu biyu da daya, ta latsa ya kawo mata dogon layin rubutu ko paragraph babu;
"New Delhi, India.
A lokacin ina karatu a India, wani abokina Ramarao yayi suggesting akan in bishi garinsu New Delhi wajen gudanar da bikin Holi da suka saba yi a kowace shekara at first na nuna kin amincewa, daga baya yayi convincing dina na bishi. Tafiyar awowi ashirin da biyu ne daga Kolkatta inda nake karatu zuwa New Delhi a jirgin kasa, don haka ba karamar galabaita nayi ba kafin mu isa. Hakan yasa sai a washegari muka samu muka fita, muka zagaya gari sosai da wajajen tarihinsu duk da cewa ba a son raina muka yi yawon ba, bayan mun gama yawon Ramarao ya raka ni inda ya min masauki ya min sallama ya tafi, sai daya tafi ne na kula da makullin motar Abbanshi akan kujera, da sauri na sauka kasa ina nemanshi. A kasan hotel din mutane ne dankam suna ta kade-kade da raye-raye ana ta watsi da kaloli, kwata-kwata na rasa hanyar da zata fitar dani zuwa bakin titi inda yayi parking din motar shi. Ina cikin kutsawa cikin mutanen naji saukar wani abu akan kafafuna, a lokaci guda kuma naji munyi karo da wani. Wallahi a take naji wani mahaukacin sanyi na ratsa kasusuwa na, zuciyata ta dinga bugawa da sauri kamar zata tsaga kirjina ta fito wanda bansan dalilin hakan ba. Na dago da sauri da niyar ba wanda muka yi karon hakuri, kyakkyawar yarinyar data dauki hankalina a take itama ta bude bakin zata yi magana, sai kawai naga wani ya janye ta suna ta kutsawa ta cikin mutane yayin da budurwar tayi ta waige na, har suka bace bat ban kifta ido ba balle in motsa daga inda nake, daga can kuma sai na tuna abinda naji ya bugi kafana dazu, na duka na dauko camera. Koda na duba hotunan yarinyar ne birjik dana wani kyakkyawan ba'indiye, a idanuna sai naga sun yi mun kama sosai sai nayi zaton ko yayanta ne. Cikin sanyin jiki na samu na fita daga cikin Que din, sai ma muka ci karo da Ramarao ya dawo, ban samu na iya furta ko kalma daya ba kawai keys din na mika mishi na koma daki na nayi daidai akan gado ina jin yadda wasu irin zafafan abubuwa suke ratsa ko wata kofa ta jikina wadda jini ke bi a guje suna shigar min zuciya da karfi.
Abinda ban taba yarda dashi ba a rayuwata shine Love At First Sight, kai bama shi ba, ita kanta soyayyar a karan kanta ban bata wani muhimmanci ba duk da cewa I dated so many girls kafin in fara karatu, amma a lokacin dai bani da ko budurwa don sam babu tsarin soyayya a cikin raina, karatun zama cikakken likitan fata shine kadai a zuciya da kwalwa na. Don haka na dinga karyata kaina dake fada min cewa yau na fada a tarkon so, na dinga kokarin na cire tunanin yarinyar daga cikin raina sai dai hakan bai yiwu ba. A karo na farko a tarihin rayuwata dana kwana cikin wani irin shauki na wata azababbiyar soyayya da nake ta karyata kaina da cewa ba ita bace, wannan dare yazo min da wasu irin sauyuka a rayuwata wadanda ban taba zaton faruwar su a shekarun rayuwata da nake ciki ba a lokacin. Idanuna biyu ras aka kira sallar asubahi, bayan na gama sallar ne ma na samu wani wahalallen barci ya kwashe ni mai cike da mafarkan yarinyar. Wajen karfe goma sha daya na safe na fito daga dakin hotel din a shirye na tsab, sai dai fa babu wani kuzari ko karsashi a tare dani. Na tsaya ina kallon gari daga saman benen da nake, iska mai sanyi yana kwararowa yana ratsa jikina, na lumshe idanuna for some seconds kafin na bude, nayi gam da katar idanuna suka sauka akan abinda na kwana na wuni ina tunani da mafarkin shi, cikin sauri na koma daki na dauko camerar ta da niyar in mayar mata na fito na sauka kasa. Lokacin dana sauka tana kofar wani shagon electronics tana wasa da furanni dake kofar shagon, sai na samu kaina da labewa ina daukarta hoto da cameran nata, daidai lokacin da nayi niyar zuwa wajenta, lokacin ne naga the same gayen nan na jiya ya nufo ta, ta juya tana kallonshi tana murmushi, sai na tsaya don in ga abinda zai faru. Ya iso ya rungumeta tsam a jikinshi yana rada mata abu a kunne, ita kuma ta nutsa kanta a kirjinshi tana sakin wata sansanyar dariya. Yanayinsu a lokacin yafi kama dana masoya ba wai 'wa' da 'kanwa' kamar yanda nayi zato jiya ba. Sai naji na kasa ko daga kafana bare in karasa inda suke, ta gabana suka bi suka wuce ni, daga baya na naji sun hadu da wasu en mata da nike zaton ko kawayen budurwar, suka gaisa suna tambayarta ashe da gaske Super star Marwan Khan shine wanda ta aura?? Ita kuma ta amsa musu da ehh. Suka masu fatan alkhairi suka yi musayar lambar waya suka rabu. Ban san iya adadi lokutan dana dauka a tsaye a wajen ba, da kyar na samu na lallashi zuciya ta na koma daki, zuciyata na gaya min cewa na manta da ita tunda matar aure ce. Sai dai me? Har na wayi gari tunanin yarinyar yaki fita daga raina sai ma karuwa da yayi. Daga nan nayi concluding din cewa I've fallen in love with a married woman!, for the very first time dana fara dora idona a kanta. Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!! Wace irin masifa ce take bibiyata haka?? A ranar na azalzali Ramarao sai da muka koma Kolkatta don a tunanina ko zamana anan din ne ke kara hura min wutar dake ruruwa a cikin raina sai dai me? Masifar sai tafi ta'azzara acan, sakan daya bai taba wucewa ba tare da yarinyar ta fado min a rai ba. Sai na fara tsoron kaina, ko dai aljana ce kawai take son bude min ido? Wannan tunani shi ya danyi encouraging dina na fara manta ta, sai dai lokaci zuwa lokaci takan fado min a rai. A haka dai muka gama service dinmu na dawo gida Kano inda ba tare da bata lokaci ba na fara aiki da asibitin Malam Aminu Kano. Saboda yarinyar nan ne na daina ganin ko wace ya mace da gashi, ya zama ko wace Mace ina kallonta ne a namiji kamar ni sai basa birge ni basa bani sha'awa ,bana muradin kasancewa dasu ko kadan, yarinyar nan dai ita daya, ita nake sha'awa da so. Na cinye shekaru uku curr a cikin wannan hali, da kaina na hakura da ita don kuwa na tabbata zuwa lokacin ba zan same ta ba. Kwatsam na tsinci labarin mutuwar dan wasan kwaikwayo Marwan Khan a medias, takanas na dauki kafa har India wajen ganin matar shi, sai dai a cikin matan sa biyu da aka nuna min babu mai kama da yarinyar nan, na dawo Kano jiki a sanyaye. Ba a dai jima ba aka kawo mana wata er aiki wadda ta dinga min yanayi da yarinyar nan, shi yasa na tsani ko da ganinta ne don kuwa tana tuno min da yarinyar nan. Ashe without my knowing, she is the same girl. Ranar da naji ashe itace wadda zan aura, nayi farin ciki marar misaltuwa. Sai dai Ameenah bata so na, amma nayi alkawarin zan koya mata yadda zata so no. Kai koda ba zata so ni ba, zan zauna da ita a hakan cikin kiyayyar da take min, I wouldn't mind because I soooo much love her, bhohhot!!".
Ai kafin ta gama hawaye sun jika mata gaban riga, kuka take yi sosai da karfinta, ta dinga bin sakonnin da yake fayyace son da yake mata da wasu incidents da dama da suka faru a tsakaninsu, daga karshe dai sai ta rungume er na'urar a kirjinta tana kuka mai tsuma zuciya, kuka mai nuna tsananin kauna ga Modibbo da tarin nadamar irin abubuwan data dinga mishi. Dama so irin wannan ya kanyi existing a wannan duniyar? Wacece ita? Wacece ita to deserve such love and emotions?? Tasan Modibbo yana sonta, amma ko kadan bata taba kawowa ranta cewa son da yake yi mata has gone to that extent so far ba. Idanunta suka lalubo wani album a can kasan wardrobe din, ta dauko shi da sauri ta bude. Wani katon hoton ta ne ya bayyana wanda ya dauke shi a washegarin ranar da suka hadu, tana tsaye ta harde hannu a kirji tana murmushi, hoton yayi matukar yin kyau, a can kasan hoton anyi rubutu da manyan kananan alphabets boldly;
*'Since I first set my eyes on you, I felt 1000 Walts of power electrifying me, I felt like I come to earth just because of u. I loved you by then, and I still love u now.... Ameenah! My Life!!'*
Bata san lokacin da dariya ta kubuce mata ba, ji tayi kamar shine da bakinsa yake fada mata maganar. Yayin da a gefe guda tsaftacciyar soyayyar Abdul-Rasheed ke kara ratsa ko wacce gaba ta jikinta, tana jin kamar ta janyo lokacin dawowarsa daga aiki yayi ta fada masa itama tana son sa, ta fada masa abinda yake jiran ji daga bakinta. Haka ta wanzu a dakin for a very long time tana ta kallon hotunanta da karanta siririn zuciyar AbdulRasheed-Modibbo, sai data ga lokaci ya ja sosai sannan ta tashi ta mayar da komi inda yake ta fita daga dakin ta koma nata. Akan carpet ta tadda Al-Ameen yana barci, tayi murmushi tare da daukarshi ta aza akan gado ta bashi sumba a goshi, ta dago tana kallonshi, can kuma ta shafa lallausar sumar kanshi ta furta kalmar 'Thanks Al-Ameen!' cikin murya kamar wadda take yin rada.
*********
©Jeedderh🐾
[4/27, 6:59 AM] +234 703 480 5764: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•66•°🐾
Karfe biyar na yamma ya dawo daga wajen aiki, lab coat dinshi rataye a kafadarshi yayin da ya rike briefcase dinshi a daya hannun. Gidan shiru babu motsin Al-Ameen bare na Ameenah, ya tsaya a saitin kofar dakinta kamar zai shiga sai kuma ya fasa, ya bude kofar dakinshi ya shiga. Kokarin cire kaya ya fara yi, yana so yayi wanka ya kai Al-Ameen gida wajen su Hauwa ya musu hutu don sun dame shi daya kai musu shi ko kuma ya kawo su gidan shi, shi kuma yafi so ya dauke Al-Ameen din daga gidan saboda yana so su zama daga shi sai Ameenah a gidan ayi ta ta kare a tsakaninsu, ya kula bata da niyar sauke girman kanta ta fada mishi tana son shi while shi kuma ya gaji da zaman jiran gawon shanu, shi yasa tun a yau ya dauko hutun shekarar shi don yayi alkawarin dole a cikin satin nan sai sun shirya da Ameenatu.
Yana kokarin 6alle botiran shirts dinshi bayan ya fito daga wanka, yaji wasu tausasan hannuwa sun ratsa fatar kirjinshi an rungumoshi ta baya, wani sansanyan kamshi mai matukar tausasa zuciya ya dinga sirarowa yana shigar mishi ta hanci, cikin wani irin salo ta fara shafar ilahirin fatar kirjinshi tana dan matsawa a hankali, take tsigar jikinshi ta fara tashi sosai, hankalin shi yayi mugun tashi. Da karfi kuma cikin sauri ya lumshe idanuwanshi yana sakin wani irin wahalallen numfashi.
Ta kai bakinta wuyanshi tana mishi magana cikin muryar rada wanda hakan ya assasa mishi wani irin rawar jiki na babu gaira babu dalili., "So.... For all this long time u were just pretending, showing dat u didn't love me koh??"
Ya daga baki da niyar yin magana sai dai maganar ta gagara fitowa, ta kara nutsa yatsunta a ramin cibiyar shi tace "hmmm? Say it, u don't like me ryt??" sakon da take isar mishi a sassan jikinshi sako ne mai girma wanda ya fara kokarin fitar dashi daga cikin hayyacinsa. Ya dauko wata in-ina da kyar "ah... I don't... I mean kema ai baki sona!" tace shi yasa kaima ka dinga nunawa kamar baka sona? Ya gyada kai, sai kuma ya girgiza da sauri yace nima ai ba sonki nake yi ba Ameenah! Ta saki wata er sassanyar darinya, "ohh really??" ya daure ya gyada kai da kyar. Ta nuno mishi cameran hannunta, "idan baka sona then..., me ya kawo wannan abin cikin kayanka?? A iya sani na tawa ce!!" ya zaro idanu sosai yana kallon cameran, how on earth?? Tace shhh!! Ta sake shi ta zagaya ta gaban shi suna fuskantar juna, kwalla ta ciko idanunta sosai, tace cikin rawar murya irin ta mai son kecewa da kuka, "ka so ni so irin wanda ban taba jin an yiwa wani mahaluki irin sa a duniya ba, ka so ni a lokacin dana nuna bani da wani makiyi sai kai a duniyar nan, na nuna maka kiyayya, na ci mutuncin ka, na tozarta ka, na fada maka bakaken maganganu but still.... Ka cigaba da sona a hakan, me yasa? Me yasa kake sona da yawa har haka??" hawayen idanunta suka fara gangarowa akan kumatunta, yayi saurin sa yatsa ya yana goge mata kwallar, amma shima nashi idanun kwalla ce ta taru tana shirin zubowa. Ba zato yaji ta afka kirjinshi ta rungume shi, runguma mai karfi. Yayi kasake idanu a zare yana son ya gaskata abin da yaji, kuka ta fashe dashi sosai, da kyar ya iya tattaro nutsuwar shi yayin da kwallar idanunshi ta gangaro akan kumatun shi, ya fara shafa gashin kanta a hankali cikin sigar lallashi. "shhh, it's okay Ameenah.... It's okay....!!" shi yake fada mata a kunne cikin sigar lallashi, ta shiga girgiza kanta, "ka yafe min Modibbo... Ban yiwa soyayyar ka adalci ba...." yayi saurin toshe mata baki da hannunshi, "Ameenah! Ki daina fadin haka, you didn't do anything wrong, kai koda ma ace kinyi ni ban dauke shi a bakin komi ba, wallahi ban ji haushi ba. I'm glad that kin fahimci irin son da nake miki Ameenah, wannan farin ciki ya wanke duk wata damuwa dake cikin raina wallahi. Nagode sosai Ameenah.... Nagode!".
Ta kara kankame shi sosai tana sakin wani kukan, "kai wane irin mutum ne Modibbo? Wane irin so kake yi min?" ya girgiza kai, "ban sani ba Ameenah, ni dai kawai nasan ina yi miki tsananin so wanda bansan iyakacinsa ba Ameenah. I soo much love you, kece dai ban sani ba??" ta boye fuskarta a kirjinshi tana murmushin jin dadin maganganun shi, yace ba zaki yi magana ba iye? Say something?! Ta dago daga gare shi ta dan ja baya tana kallon tsakiyar idanunshi, tace "Ina Sonka Modibbo, Ina Sonka, Ina Qaunar ka, Ina Son....!!!" bai bari ta karasa ba ya janyota da sauri ya hade bakinshi da nata, suka yi wani kiss na dan lokaci kafin ya maidata kirjinshi ya rungumeta kamm kamar zai karya mata kasusuwa, sai daya ji ta fara fitar da numfashi da kyar tukuna ya sarara mata ya dan sassauta rikon. "At last! At last!! Finally..... Alhamdulillah!!!!" abinda yayi ta nanatawa kenan ya kasa magana kwakkwara......
Kuyi hakuri da wannan zuwa gobe please, m kinda busy ne kwana biyun nan shi yasa.
*UMMU MUHSEENAT masoyiyar Bayan Rai!!, Ameenah tace a gaishe ki sosai!*
©Jeedderh🐾
[4/27, 6:59 AM] +234 703 480 5764: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•67•°🐾
Ya saketa ya dagota yana kare mata kallo, murmushi tayi ta sumbaci tsakanin kirjinshi, ta kamo tafin hannayen shi ta sumbata duka, ta shige cikin jikinshi sosai suka ba juna wata tsattsaurar runguma mai nuna tsantsar so, kauna, da yarda da juna. Sun jima a haka sosai kafin suka saki juna, yace "Ina Al-Ameen?" tace yana daki. Yace "kije ki shirya shi ki hada mishi kaya zan kaishi hutu wajen su Adam, sai mu ci amarcinmu a nutse koh?" ta jefa mishi hararar wasa ta juya cikin sauri da wani hadadden taku ta fita, har ta kai bakin kofa ta juyo suka hada ido, ta kanne mishi ido daya ta fita da sauri. Ajiyar zuciya ya saki yana dan murmushi, a can kasan ranshi yana godiya ga Ubangiji madaukakin Sarki.
Suna fita shi da Al-Ameen ta fada kicin ta hada mishi lafiyayyiyar dinner, tana gamawa ta dauko turaren kamshi ta turara gidan da dakunan barcinsu, nan da nan gidan ya rikice da daddadan kamshi. Ta shiga toilet ta silla wanka mai sunan wanka ta fito, sai data yi sallar isha'i kafin ta zauna a gaban mirror ta fara kakale jikinta da mayuka masu kamshi. Yau kam kwalliya ta zauna tayi sosai, duk da ba mai yawa bace amma mai daukar hankali ce sosai. Ta gama ta koma jikin wardrobe tana laluben kayan da zata saka, nan ma ta jima kafin ta zakulo wasu riga da wani na Pakistan. Wandon ya matseta sosai, daga kasa anyi wata tattara da kwalliya mai kyau yayin da rigar take doguwa wadda ta kawo mata har gwiwa amma anyi tsagu a gefen cinyoyin rigar, haka hannuwa da wuyan rigar kamar net suke don ana iya hango brazier data saka, kayan sun mata kyau sosai. Ta gyara gashin kanta ya zubo mata har gadon baya, sai ta dauki yanki kadan ya dauko har saman kirjinta, ko Ina ta gitta kamshin turare kawai yake tashi.
Sai wajen karfe takwas da rabi na dare taji karan shigowar motar shi. Kafin tayi wani yunkuri ta jiyo knocking, ta mike cikin wata irin tafiya mai daukan hankali, ko ina na jikinta yana girgiza, ta bude kofar suka yi tozali da juna. Tsayawa yayi yana kallonta tana doka mishi wani hadadden tsadadden murmushi, da kyar ya iya lumshe idanunshi ya sake bude su a kanta fes, fadar irin kyawun data yi a idanunshi bata baki ne, abinda kawai ya sani shine tayi kyau yau fiye da ko yaushe, fiye da kowace 'ya mace a duniya nan!.
Ta mika hannu ta riko hannuwanshi duka biyun ta janyo shi cikin falon ta maida kofar ta rufe, matsawa tayi jikinshi har yana iya shakar numfashinta tace "welcome my jaan!!" yayi murmushi tare da lalubo hannayenta ya manna mata sumba a tafin hannu yace "Thanks Piyaa, kinyi kyau sosai". Tayi juyi a gabanshi tana fari da idanu tace da gaske? Ya gyada mata kai. Hannuwanshi ta kama ta fara ja, tace "dinner is ready Jaan, zo kaci abinci nasan kana jin yunwa koh?" yace sosai ma kuwa. Tayi fuskan tausayi tace ohh sorry, zo muje.... Suka jera har falon sama inda ta kawata dinning da dishes kala-kala. Wani karin abin birgewa da ban sha'awa shine wasu kyawawan roses data kawata table din dasu sai kuwa candles a kunne. Wajen ya rikice da kamshin turaruka daban-daban na daki. Ta janyo mishi kujera ya zauna itama ta zauna a gefenshi, ta janyo plates ta zuba duk wani nau'in abinci data tanada, da kanta ta dinga bashi kamar wani jariri sai da yayi nak sannan shima ya fara ciyar da ita. A lokacin idan ka gansu zaka tabbatar da cewa basu da wata damuwa ko kadan a zukatan su, sai tsantsar kaunar juna.
Tare suka tattara kayan ya taya ta suka wanke komi suka gyara kicin din, daga nan kowa ya fada dakinshi suka shiga wanka. A matukar kagare yake da isowarta gareshi, ko wane lokaci ya dan rufe idonshi yanayin da yake hangowa zasu shiga anjima kawai yake hangowa a kwayar idanunshi, tsigar jikinshi har wani tashi take yi. Ya gama duk wani shirin taryarta zuwa dakinshi da yakamata yayi, sai dai har sha daya ta nemi ta wuce amma babu Ameenah babu duriyarta. A kagare yaja shirt ya dora akan singiletin dake jikinshi ya fita zuwa dakinta. Tsaye ya sameta a tsakiyar dakin tana kara duba shigar data yi na wata karamar riga ko cinyoyi bata gama rufe mata ba, da yake irin V-neck dinnan ce gabadaya bayanta a bude yake, ta kuma bi jikinta ta lafe kasantuwarta cotton silk. Tana jin an turo kofa ta juya a dan firgice ta kalli kofar, suka hada idanu dashi. Tsayawa yayi cak a inda yake ya kasa motsi, yayin data juya mishi baya a kunyace tasa hannu ta rufe fuskarta.
Ya daga kafa a hankali ya karasa zuwa gareta yasa hannu ya juyota suna fuskantar juna idanunshi na karade sassan jikinta da kallo, sai daya kalleta ya more son ranshi, yasa hannu ya banbare hannayenta daga fuskarta. Kasa daga ido ta dube shi tayi, ya danyi murmushi a hankali yace yau kuma surukinki na zama Ameenah?? Ta kara sunne kai kasa, ya girgiza kanshi, "no Ameenah, please kar muyi haka dake. Look at me.... Plsss!!" ta dago da kyar kamar mai tsoron hada ido dashi ta kalli tsakiyar idanunshi, suka kalli juna na tsayin minti daya, ya lumshe idanunshi ya bude su a hankali akan fuskarta, "woww!! Masha Allah! Subhanallah!! I can't believe kece Ameenah, u look different. Ohh God I soo much love you my angel....!!!" cikin sauri ta fada kirjinshi ta rungume shi sosai, idanunta a rufe take furta "I love you too Modibbo...!!" ji tayi ya daga ta cakk sai cikin dakinshi, wani irin sanyi mai dadi da kuma kamshi ya bugi fata da hancin Ameenah, ta kara nutsa kanta a wuyanshi tana shakar kamshin jikinshi dana dakinshi. Just like how Modibbo is unique, haka ma komi nashi yake classic, unique and 1daful. Hatta da gadon kwanciyar shi a gyare yake tsaf, ga wasu jajayen furanni da suka sake kayata gadon, ya dire ta akan gadon, ya koma ya latsa makunnar wutsa hasken dakin ya dawo dim, ya dawo kan gadon ya saki net ya haye kan gadon ya jawota jikinshi, sai a lokacin ta bude idanunta tun shigowar su dakin. Tana hango kyallin kwayar idanun shi da take cike da sonta ta dan hasken daya rage a dakin.
Ya lalubo kunnenta ya fara yi mata rada a hankali cikin tattausar murya, "....this night... This moment... Even the day, I promise to never forget 'em in ma whole life, even if I will die and come back, I'll hold into the taste of this night... I promise you this Ameenah...!!" ya lalubi bakinta da nashi ya fara tsotsa a hankali, ta saki jikinta sosai tana caressing bayanshi da tattausan hannunta.
Daya-bayan-daya ya dinga zare kayan jikinsu yana jifa dasu, yayin da harshen shi ke bin fatar jikinta licking, sucking kamar wani tsohon maye. Kalar soyayyar tasu ta yau daban ce, wani passionate romance da suke wa juna abin yafi karfin biro na, don haka nayi layar zana a dakin.....
*☆☆☆☆☆*
©Jeedderh🐾
[4/27, 6:59 AM] +234 703 480 5764: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•68•°🐾
Rayuwar farin ciki da salama, aminci da yardar juna da tsantsar soyayya suke shimfidawa, kowa ya shiga gidansu ya fita to zai bada 100% shaida akan yadda suke tattalin junansu.
Wani yammaci tana balcony a zaune bayan ta gama gyara gidanta da jikinta, maigidan ya tafi wajen aiki Al-Ameen kuma na makaranta. Sanye take da Saree wanda akasarin en matan India ke sawa a wannan zamanin, rigar a iya cibinta ta tsaya skirt din kuma ya kai mata har kasa. Gyalen kayan maimakon ta yafa sai ta rataya shi a wuyanta kawai.
Zaune take a gaban painting board da drawing materials cike a wani madaidaicin akwati mai kyau tana faman sana'ar Zane, ji tayi an rufe mata idanu, ta tsaya cak da aikin da take yi, murmushi tayi a tausashe tace "welcome my jaan..." ya zagayo ta gabanta suka kurawa juna ido suna murmushi na zallan so, ya dubi shigar data yi ta dauki hankalinshi sosai yace kinyi kyau my baby! Fari tayi da Idanu fuskarta kamar gonar auduga, ya dubi zanen da take yi ya danyi murmushi yace "nyc 1 babe, wato mai zane ce take zana kanta koh?" tayi murmushi itama tana kallon zanen, itace a zaune cikin shigar data yi yau tana zana Al-Ameen da yake wasa, ta fara tattara kayan zanen tana cewa "ai zane ya tashi tunda mai gida ya dawo..., amma mai yasa ka dawo da wuri yau?" ya fara kokarin cire coat din jikinshi, ta amshe shi tana taimaka mishi, yace well, I was just missing you, shine na tarkatawa Dr. Tukur sauran ayyukan na tsero gida. Tace good job! Oya, wanka ko abinci?? Ya dan rausayar da kai gefe, "hmmm..... Food?!" tayi dariyar yadda yayi sosai, taja karan hancin shi, "acici! Come, let's go and cook simple food for you" suka sauka kasa bayan ta kai mishi coat da brief case dinshi daki.
Cikin mintuna talatin ta gama hada mishi abincin, ta shirya su akan dinning. Yau rigima ce sosai akan Modibbon nata, kamar wani baby haka ta zaunar dashi tana ciyar dashi abincin da hannayenta, suka gama ta tattara kayan ta kwashe su zuwa kicin ta fara wankewa. Nan ma bai kyaleta ba, bin ta yayi duk inda tasa kafa nan zai maida tashi, da yarda dan tsaya kuma sai ya rungumeta ta baya yayi leaning kanshi a kafadarta, a jima kadan kuma sai ya sumbaceta. A takaice dai kafin ta gama sai daya jigatar da ita sosai. Suna cikin wannan yanayin suka jiyo karan door bell, ta juya tana kallonshi tana dan murmushi, tace baby is back! Plss let him in. Ya kanne mata ido daya yana murmushi ya juya ya fita daga cikin kicin din, "I'll be back soon...." kai kawai ta girgiza ta juya ta cigaba da shirya plates a ma'ajiyar su. Shiru bata ji Al-Ameen ya fado kicin din da gudu yana kwala mata kira ba, ta gaji da jira ta janyo kitchen rag ta goge hannunta ta fita daga kicin din da niyar taje taga abinda ya tsayar dasu. A bakin kofa suka ci karo, bai bari tayi magana ba ya yafa mata gyalen wuyanta yaja hannunta har tsakiyar falon, ga mamakinta me zata gani?? Hindu ce a zaune akan two seater tare da Mohammed Kabeer a gefenta sun zubo mata idanu, da mamaki da farin ciki suka tarar mata a rai sai kawai ta tsaya cak tana kare musu kallo, su kam murmushi suke jifanta dashi mai cike da nuna kewa. It has been good two years kenan rabon dasu hadu da juna. Hindu ta tashi taje ta kama Ameenah, suka bawa juna wata kyakkyawar runguma very warm ta tsawon lokaci, kafin suka saki juna suka samu waje suka zauna hannuwansu na sarke dana juna, bakin Ameenah ya kasa rufuwa. Nan fa falon ya dawo na mutanen gabacin Asia, Hindi kawai kake ji yana tashi. Sai da suka gama gaisawan yaushe gamo da Hindu sannan ta maida hankalinta ga Kabeer tana gaishe shi, ya harareta cikin wasa yace ai ni nayi fushi, sai da kika gama dokin ta ne sannan zaki kalloni? Tayi dariya sosai tace afwan! Gwiwa na a kasa. Duk suka saka dariya banda Modibbo daya zuba musu ido. Kafin kace meye wannan?? Ta cika gabansu da drinks da snacks kala-kala, aka bude dandalin hirar yaushe gamo wannan karon cikin turanci don suna saka Modibbo cikin hirar tasu. Anan take jin ashe next month ne auren Hindu da Kabeer din, sun zo wajen dangin su Marwan ne sai suka ce a rako su su gaishe ta. Ta nuna murnarta a fili ta kuma ji dadin haka har cikin zuciyarta. Kabeer ne ke tambayanta Ina baby Al-Ameen?? Ta dan kalli agogo tace I wonder ko me ya tsayar dashi yau, suna dawowa before this time....". Suka cigaba da taba hira game da alamuran da suka shafi rayuwarsu. Ba a fi minti biyar ba kuwa sai ga Al-Ameen ya fado falon da gudu yana mai kwala mata kira, "Mommy!! Hi Mum m back...!". Gabadayansu ido suka zuba mishi har ya karaso ya fada jikin Ameenah, ta rungume shi suna dariya. Sai da suka natsa ta janye shi daga jikinta tana mishi nuni da inda Hindu take zaune, cewa tayi cikin turanci, baby ka gane waccan kuwa?? Ya zuba mata ido sosai yana murmushi, yace "Mommy ce, Mommy na ce ta India!" gabadaya suka saki dariya, Hindu ta bude mishi hannayenta ya kuwa tafi da gudu ya fada jikinta. Hindu ta makalkale yaron a jikinta hawaye na zarya akan kumatunta, Ameenah bata san lokacin da kwalla ta ciko idanunta ba, kaunar data gani ta Uwa da d'a a tare dasu ya tuno mata da Marwan, idan da ace yana raye ko ya zai ji idan yaga yadda danshi ya girma har haka??
Abinda Hindu ta fada kenan lokacin data saki Al-Ameen ta dora shi akan cinyarta, tace Ashe ka sanni sosai son?? Ya gyada kai yace Mommy tana nuna min hoton ki kullum tace sunanki Momi na a India kike, kuma tace zata kaimu in ganki idan muka yi long holiday. Tayi dariya sosai tace lallai Son ka iya surutu Ashe!! Ya ciro mata littafan makarantar shi yana nuna musu abinda aka musu yau yana basu labarin abubuwa, sai da aka kira sallar magriba sannan ne fa suka fita masallaci matan kuma suka yi sallah a daki.
Anan suka kwana tare dasu don duk yadda suka so da suje su nemi masauki Ameenah ki tayi, dole sai a dakinta Hindu ta kwana Kabeer kuma ya kwana a wani dakin. Wajen kwanciyar ma Hindu tayi-tayi da ita akan taje ga mijinta amma taki tafiya, haka suka saka Al-Ameen a tsakiyar su suna ta lailayar yaron. Sai a lokacin Ameenah tasan ashe har lokacin Kabeer ne ke cigaba da juya dukiyar Al-Ameen dake hannunsa, tace yanzu haka yana shirin bude wani kamfanin ne a cikin Bangkok. Ameenah ta taya su murna sosai, Hindu tace Kabeer din yana zancen wai bai dace ya cigaba da rike dukiyar Al-Ameen din ba, yana ganin it's better ace tana hannun su Ameenar tunda duka dawainiyar Al-Ameen din a hannunsu take. Ameenah ta girgiza kanta tace noo, Plss ku daina tayar da zancen nan Hindu, da safe zamu yi maganar dashi. Zan ci gaba da kula da Al-Ameen da gumi na, ya cigaba da kula mishi da dukiyar shi kawai, idan ya girma lokacin na aurar dashi sai ya damka mishi abinshi ya kula da iyalin shi dasu....." suka yi dariya gabadaya.
Sai da dare a washegarin ranar suka raka su airport, suka daga India da alkawarin su Ameenah zasu xiyarci bikinsu. A cikin mota suna tafiya zasu koma gida, hannunshi na sarke cikin nata guda suna hirar su jefi-jefi yayin da yake driving da daya hannun, yace "u know sweetheart??" tace mene? Yace m preparing a very great giant surprise for u.... Ta kalleshi cikin doki tace da gaske? Menene?? Ya girgiza kai, "Nooo, ba zan fada ba sai an bani goron albishir" ta dan turo baki a shagwabance, "kai don Allah!" yace shikenan tunda baki so. Ta kara matse hannunshi tace Ina so mana, so tell me, me kake so?? Yace "a baby!!" tace ai Allah ne xai bani ba nice zan ba kaina ba. Ya dan hade fuska, "to idan ya baki din sai nima na baki...!!" kanta ta mayar ta jinginar da Kujera bata yi magana ba ita ala dole tayi fushi, suka yi tafiya mai dan nisa ya juya ya kalleta yace "zamu biya ta wajen su Ummie??" ta gyada kai da sauri kuma cike da doki, "yauwa Plsss muje, Allah yasa yau ma Dashishin nan nata mai dan banzan dadi!" ya dan ja bakinta yana dariya wannan dan guntun bakin ya iya kwadayi! Ta ture hannun gefe tana turo bakin, ya cigaba da tsokanarta yana dariya, tun bata biye mishi har dai ta biye mishi suka yi tayi har suka isa gidan su Hajiya.
*After a Year & a half (18 Months...)*
©Jeedderh🐾
[5/2, 11:10 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•69•°🐾
★★★★★★★★
*AFTER 18 MONTHS.....!!*
"Masha Allah! Fatabarakallahu Ahsana Khaaliqeen!.... Gaskiya matar babban Yaya kin iya haihuwa, wannan zukekiyar baby har haka!!" Fadin Saleemat kenan yayin da take rungume da babyn da Ameenah ta sauke a jiya da yamma, kyakkyawar bouncing baby girl, kowa ya dauke ta sai ya furta Masha Allah, lafiyayyiyar jaririya ce kyakkyawa mai tafiya da imanin duk wanda yayi setting din idanunshi a kanta, fara jajir da ita kamar Ameenah, a kamanni kuwa babu abinda ta bari na Modibbo, don haka kamar ta da Saleemat har ta baci, bakin Saleemat dai yaki rufo tana ta baro bayanai, Ameenah kam na gefen gado rungume da Bomboy (Sani) dan gidan Ya Faruq da Saleemat a jikinta mai kimanin watanni hudu.
Gidan cike yake da en uwa da abokai ana ta amsar barka, amma haka Modibbo ya dinga ratsa mutanen nan wasu ayi gaisuwar mutunci a tsokani juna har dai ya dangana da uwar dakin Ameenah hannunshi rike da wata leda. Su uku ne a dakin lokacin, yana shiga Saleemat da Bintu suka mike suka tasamma kofa. Suka yi musayar murmushi shi da maijegon, ya zauna a gefen gado bayan ya manna mata peck a goshi, yace Maman Baby ya hidima?? Ta rangwadar da kanta gefe, "Alhamdulillah!" Ya janyo ledar daya shigo da ita ya fito da fresh fruits masu kyau yace ga sakon ki, tasa hannu ta amsa tace thanks! Ta kai inibi guda bakinta ta tauna tare da lumshe idanunta, guda ta cira ta nufi bakinshi dashi, ba musu ya daga bakin ta saka mishi a baki. Suka cigaba da ciyar da junansu fruits din ba tare da sun furta ko a ba, can ya kalleta yace ni kam ina babban Yaya Al-Ameen ne, ban ji duriyar shi tunda na shigo?! Ta dan girgiza kai, "manta da yaron nan, yana can wai yana hadawa kanwar shi jirgin wasa" ya dara sosai yace ohh Al-Ameen! Da alamun dai automobilist zai zama, naga suna shiri da karafa sosai. Tace ai shiyasa kullum hannunsa baya rabuwa da rauni. Yace amma kuma ai yana fitar da sakamako mai kyau, don idan ya sarrafa miki wani karfen sai kice wani babban mai fasaha ne a fannin kere-kere. Tace da wannan dai..... Daidai lokacin baby ta farka, ya riga Ameenahn daukanta yana shillata sama yana mata en wakoki, sai ta koma gefe tana bangala musu dariya ita da babyn. Sai daya gaji ya mika mata babyn, "ga in-law na nan a bata abinci!" Ta dan harare shi ya daga gira, "ah toh! Ai ban fadi ba daidai ba, ke dai kika ce danki kika haifawa mata, kinga kenan sai mu fara kiranta da surukarmu tun yanzu Koh??" Sai kawai ta kai mishi dukan wasa a gefen cinya tana girgiza kai cikin murmushi, zuciyarta na cike da farin cikin yadda mijinta yake sonta yake kuma goya mata baya a duk wasu decisions nata, be it yana so ko akasin haka, as long as tana so, to it doesn't matter to him anymore, zai taya ta su so abin ne kawai.
Ya dauki kafarta yana ja mata yatsu har ta gama shayar da jaririyar, ta kwantar da ita a gefenta. Hankalinta kacokam ta mayar kanshi yana kokarin fito da wasu keys ya mika mata, cikin daurewar kai ta amsa tana binshi da kallon tambaya, bai yi magana ba ya sake zaro takardu ya mika mata, ta amsa ta karanta title din dake rubuce a sama, *"UMM-AMEEN PAINT HOUSE?!"* Ta fada, "me kenan" ya mata rada a kunne "a thank u gift, for giving me such a wonderful baby, I love you!" Tace "me too! But plss ka min bayanin meke cikin takardun nan" yace "well, it's just a small painting joint da na bude miki na kuma zuba miki ma'aikata experts a wannan fannin. Akwai bangaren Zane, akwai painting, akwai bangaren kera irin flower vases da sauran tukwane na kasa, akwai kuma bangaren sculpturing duk an zuba ma'aikata. Kina da babban ofishinki a can as the CEO, but zuwanki wajen da yin aiki a wajen will b under ur wish, idan kina so kiyi aikin zaki yi, idan kula da wajen zaki yi toh, idan ma wani zai kular miki da wajen wannan duk yana hannunki, ni dai nayi aikin da zanyi ga takardu nan da komi na wajen na damka ga mamallakiyar wajen...."
Jikinshi ta fada tana ihun murna da godiya, farincikin dake dankare a ranta a wannan lokacin bai faduwa. Daga karshe ta lalubi bakinshi ta kamo lebenshi na kasa ta sumbata, sumbata mai bayyana irin unexpressed farincikin dake ranta. A wannan lokacin bai iya daurewa ba, rike ta yayi sosai ya fara mayar mata da martani, sai da yaji yana shirin shiga wani yanayi sannan ya saketa ya rungume tsam a faffadan kirjinsa.
Kafin kace me wannan?! Magana ta bazu tsakanin dangi, kowa sai son barka yake yiwa Ameenah. Ranar suna jaririya taci sunan Yahanatu sunan Ummie, suna mata inkiya da Muhaaseen. Alhamdulillah! Taro yayi kyau ya kuma yi albarka, aka watse aka bar Maijego, maigidanta, da baby da yayanta suna cigaba da wankansu.
(Sai mu ce Allah ya raya Muhaaseen!)
*★◉18 Years Later!!◉★*
©Jeedderh🐾
[5/2, 11:10 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•70•°🐾
★◉18 Years Later!◉★
*Ireland...., U.S.A*
"Muhaaseen!! Wallahi idan baki taho ba nan da minti daya zamu tafi mu barki, tun dazu kin zaunar damu a mota muna jiranki kamar wasu sa'anninki??" Budurwar ta jiyo ta kalleta, "haba Mommy!! Kin fa san yau ranace mai muhimmanci, I have to look good don nasan za a dauki hotunan mu a watsa a duniya, kin ga bai kamata ace nayi looking some how ba kin gane ai!!" Ta gyada kai, "to zauna ki cigaba da kwalliyar kada Allah yasa ki fito nan da minti daya, zaki zauna ki mana jiran gida kuwa!!" Ta juya ta fita. Ta ajiye eye pencil din hannunta ta suri jakarta ta tashi da sauri, sai data kara duba kanta a madubi taga ta fito yadda take so sannan tabi bayan mommyn da dan saurin gudu saboda heals data saka. A mota ta janyo wayarta ta lalubo sunan 'Nourr!' ta kira, wayar ta gama kara ta gama ba a dauka ba, taja dan siririn tsaki ta jefa wayar cikin jaka tana ciza dan tattausan lebenta na kasa...
*U.A.E.I Concert\Hall*
Mutane ne bila adadin a makeken hall din mai kama da seward stadium din Amsterdam, both fararen fata da bakake, duk da cewa dai masu jajayen kunnuwan sun fi yawa a filin. Babu abinda kake gani sai hasken flashes kawai, en jaridu da masu aikin talbijin da radio daga sassa daban-daban na duniyar nan ke ta shawagi a filin. Maganar da M.C ke yi ce ta saka hall din yayi tsit, hakan ya ba muryar shi damar amsa kuwwa a ciki da wajen hall din.
"Oh yes, young ladies and gentlemen, here m presenting to u ur precious engine creator, the young but humble AL-AMEEN MUH'D MARWAN!!" ji kake kyas! Kyas-kyas! Kyass!! Karan flashes din en jaridu dana sauran mutane da suka juya suna daukar wanda ya fito daga cikin wani hadadden bango like daga can kan stage din daya sha adon balloons da roses. Oh My God!! Na rasa ta yaya zan fayyace muku haduwar saurayin nan, yau dai duk kwarewa ta a faiyace sura aradun Allah na kasa, ba zancen kyau da cikar sura ba ma, kwarjinin kawai.
Shigar da yayi kawai na wasu gray Spanish suits malam 100% natural cotton suits, wandon da suits din da tie gray ne yayin da yasa black shirt da black cover shoe. Takalmin da yasa a kafarshi kuwa da agogon dake daure a tsintsiyar lallausar fatar hannunshi kadai sun isa sayan wani karamin flat house. Yana da suka mai yawa aka da kuma tsayi, anyi mishi irin two-step style din nan. Matashin a tsaye yake mikakke ziyam da wani dan doron tsawo da yayi wanda sai ka lura sosai sannan zaka kula dashi. Daga ganinsa kaga tsayayyen matashi in his 25th-27th, fari ne tass babu dishin baki ko yaya a fuskar nan tashi, jikinshi yana da kira irin ta maza mai tattare da wasu irin baiwarwaki da ba kowa ne Allah ya ba irin su ba a cikin bayinsa sai daidaiku.
Ya tako yana tafiya cike da ginshira da kasaita kamar wani dawisu,filin ya kaure da tafi da sowa yayin da MC ya dage yana zuba bayani....
"Ladies and gentlemen, please welcome our giant, gentle, smart, genius, handsome Al-Ameen. Shine mutum na farko daya fara daga tutar Nigeria ta fannin kere-kere da sarrafa karafuna inda ya kera jirgi a karo na farko a tarihin Nigeria.... Now m introducing him to him and his co-workers Macker, Zhu Cheng and Israel, plss give them a big hand!!" Wajen kuwa ya kaure da tafi da sowa, yayin da suka jera tare da co-workers din nashi suna tafiya cike da jin kai kamar masu tafiya akan gajimare har suka zauna a wajen da aka tanadar musu. Daya bayan daya aka dinga kiransu suna fita suna bayanin irin gudummuwar da suka bayar wajen kera jirgin..
Kamar yadda ko wannensu yake fara fada, M. Al-Ameen shi ya jagorance su wajen kirar, kuma shine wanda ya fara bada shawarar a kera jirgin, "wanda a yanzu haka yau ya kwashi mutane dubu da hamsin zuwa kasar China, tafiyar awa goma sha hudu da mintuna talatin ya kuma sauke su lafiya ya kwaso wasu ya maido su nan ba tare da anci karo da wata matsala ba. Yes I know, mu uku muka yi aikin wanda at first was a challenge from our mentor but M. Al-Ameen ya taka rawar gani sosai far far than us, we are very proud of him!" Cewar Zhu Cheng lokacin daya bayar da bayanin shi.
Kada ku so kuga yadda hankalin miliyoyin mutanen dake hall din ya koma kan matashin daya mike, akwai alamun hankalinshi baya jikinshi lokacin daya tashi, dara-daran fararen manyan idanunshi hall din suke bi suna karade shi da kallo a nutse, akwai yiwuwar yana neman wani ne. Idanunshi suka tsaya cak a kanta, tana daga jerin mutanen da suka zauna a seats din gaba na hall din. Sanye take da wata silk gown ruwan zuma mai siririn hannu, ta dora bakar blazer mai yashi kaman bayan lemon, tayi rolling da dan siririn bakin gyale. Doguwar zagayayyiyar farar fuskar matashiyar na saye da wani makeken bakin gilashin Prada irin no respect dinnan wanda ya mamaye rabin fuskar tata, baka ganin komi a fuskar sai dan faffadan dogon hancinta da siraran lebba da suka sha jan baki pink suna ta sheki.
Har yaje gaban table din ya tsaya idanunsa na kanta, Allah kadai yasan inda budurwar take kallo saboda ta boye idanunta a cikin gilashi. Da kyar ya samu ya daidaita kansa ya tunkari dumbin jama'ar da suka tattara hankulansu gare shi, ya daga en madaidaitan jajayen lebbanshi ya fara magana a tausashe kuma a nutse kai idan ka ganshi sai ka rantse ba shine yake fitar da haruffan ba. Sautin muryarshi kawai ya isa ya narkar da zuciyar ko wace diya macen dake saurarenshi saboda tsananin dadin muryar tashi kamar busar sarewa, yace.... "A certain interviewer once asked me, dat who is behind my success?? I didn't answered him by that time, but I want to answer that question today, I mean right now!!. She plays an important role in my life, she is the reason why I stand before all of you today, the reason I am who I am today. She made me into somebody while I was nobody, she loves and cares for me more than every body. That woman, loves me as her biological son even though m not, the woman who in my everything made an exception. That special person in my life is my mother, my in-law, my mentor, my....., my....., my everything!!" Raf! Raf!! Kake jin tafi, emotionalist din wajen har sun fara share hawaye jin irin tsantsar soyayya dake cikin sautin muryar Al-Ameen. Sai daya dauke er siririyar kwallar data sauko a kuncinsa sannan ya dauki remote ya saita projector ya latsa, take hasken wajen ya dauke duhu ya bayyana. Haske ya bayyana a katon farin board, Al-Ameen ya fara tsara bayani daki-daki na yanda suka kera jirgin yana nuna musu wasu abubuwan da irin challenges da wahalhalun da suka fuskanta da kuma irin nasarar da suka samu don kuwa babban kamfanin zirga-zirgar jiragen sama KEA AIRLINES ne suka sayi jirgin, kuma kowa yasan yadda girman kamfanin nan yake ba sai an fada ba. Bayan nan sun dauke shi tsawon mintuna talatin, ya gama ya koma ya zauna. Idanunshi ya mayar kan budurwar nan da babu alamun ko er sanayya a tsakaninsu data nuna, lamarin yarinyar ya daure mishi kai ya kuma saka shi cikin shakka da wasi-wasi, daya kalli mominshi kuwa bai so ya dauke fuskarshi daga gareta ba, irin farinciki da alfaharin daya gani shimfide akan fuskarta ba zai misaltu ba, ta mishi thumb up da hannunta har da dan sarawa, yayi wani irin murmushi tare da kanne mata ido daya, (da alamun Al-Ameen dan du.... ne. Lolx!). Har aka gama event din taro ya tashi matashi Al-Ameen bai san me ake yi ba.
Ana fara watsewa ya mike cikin sauri, en jaridu suka rufa mishi baya kowa yana so yaji ta bakinshi, "Sorry! I don't have much to say....!" Abinda yake fada musu kenan har ya samu ya sauka daga kan stage din da kyar. Duk da haka basu daina binshi ba sai da yayi dabarar hada su da abokan aikinshi shi kuma ya zame.
©Jeedderh🐾
[5/2, 11:10 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•71•°🐾
Babu inda bai zagaya ba a cikin hall din amma sama ko kasa babu labarinta, ya ciro handkerchief yana goge zufar data tsattsafo a saman goshin shi. Daga bayanshi yaji an dafa shi, "heyy!! Me kake yi anan?" Cikin sauri ya juya yayi tozali dasu, iyayen shine gabadayansu. Cikin sakannin da basu fi biyar ba ya kare musu kallo amma bai ga abinda ya fito nema ba. Yayi saurin dukawa ya dafa kafar mahaifiyar shi Hindu, kafin ya kai tayi saurin riko kafadunshi tace "May Allah bless you my child!" Ya kara dukawa zai dafa kanin mahaifinshi wanda yake a matsayin mahaifi a gare shi, shima yayi saurin rike shi ya rungumeshi yana dan dukan bayanshi, yace "am proud of you son!". Ya juya ga mahaifiyar shi Haj. Ameenah, tana tsaye a gefensu hannunta rike tsam cikin na maigidanta suna ta jefo mishi murmushi, ya durkusa har kasa ya gaishe su. Ameenah ta nutsa yatsanta a cikin sumar kanshi ta shafa tace "bravo baby! You make us proud today" yayi murmushi yace nagode mami nah! Alhaji AbdulRasheed ya kamo hannunshi yace wato ni dai kullum ba za a daina nuna min wariyar launin fata ba koh? Al-Ameen ya dan sosa kanshi yace sorry daddy! Kasan a komi pa uwa ce ke fara zuwa first. Ya dage gira sama yana kallonshi, "ohh haka ne? I c. Amma a danyi kokari a dinga ganinmu kafin ita, tun kafin in murda kambuna, ka gane ai!" Ya dan saki murmushi yana dan sosa wuyanshi, "it's okay daddy.. kar ka damu, next time...." Ya fada yana kallon Ameenah data zuba musu ido tana murmushi, harara ta jefa musu cikin wasa tace "biye mishi ya dinga zuga ka baby, ai kasan sauran!" Alhj. AbdulRasheed yaja hannunshi, "zo muje mu kyale matar nan in law, naga alamun tana so ne ta hure maka kunne don taga ina shirin kwace mata fada" suka tafi suka bar su Hindu na musu dariya.
A can wajen da aka tanada don ajiye baki a cikin mkarantar nan Al-Ameen ya samar musu waje suka zauna, ya yafito kaninshi Masood dan gidan Hindu da Mohd Kabeer da hannu, yaron ya tashi yaje gareshi, suka danyi kus-kus dinsu na en muntuna. Ya matsa kusa da maminshi, cikin muryar rada yake tambayarta "Mamie, yanzu zaku wuce gida ne?" Itama a hankali tace aah, akwai wasu mutane daddynku yake son gani yanzun. Ya mike tsaye yana dan sassauta neck tie dinshi yayin da suka bishi da kallo, yace ni zanyi gaba sai kun iso. Bai jira amsar kowa ba ya kara gaba.
Cikin motarshi Landana-Vanquish, ruwan toka, tafiya yake yana murza sitiyari a nutse kuma cikin kwarewa. Iskar garin Ireland na ratsa kasusuwan jikinshi da yake motar convertible ce. Bai ja birki a ko ina ba sai a kofar dan karamin flat dinshi, ya janyo remote ya latsa gate ya bude. Ya silalo motar a hankali har cikin gareji yayi parking ya fito.
A tsakiyar falon shi, kayan zane ne a baje kala-kala, an shirya komi tsaf amma ba a fara zanen ba. Wani soft smile ya subuce a fatar bakinshi, "Cherry.... Cherry!" Ya shiga kwalla kira ba kakkautawa, kofar daki a bayanshi ta bude, "yeah!, what?" Ya juya bayanshi cikin sauri yana kallonta, ta turbune fuska tana turo dan siririn bakinta gaba, yasan laifinshi. Ya hada hannuwanshi biyu waje guda alamun roko yace am so sorry dear, please forgive me ba zan kara ba. Ta zobaro baki gaba, "amma kaima kasan baka kyauta ba koh? Missed calls nawa ka gani nawa a wayanka between jiya da yau?" Yace "nasan nayi laifi, shiyasa nake baki hakuri. Ba zan kara ba" ta kauda kai gefe, "kullum haka kake cewa amma kullum sai ka sake again" yace I promise u diz d last, idan na sake ki min duk abinda zaki yi. Tace promise?? Ya gyada Mata kai, promise. Ta danyi murmushi tare da mika mishi hannunta na dama, "by the way, congratulations!" Yayi murmushi shima ya mika mata nashi hannun suka yi shaking hands, "thanks dear..... So wat's wit d drawing apparatus?" Bata bashi amsa ba taja hannunshi har kan kujerar dake gaban drawing board din dake cikin falon ta zaunar dashi tare da fadin don't move okay? Ya gyada kai. Ta janyo pencil, har ta dora akan takarda ta sake juyowa gare shi, "don't spoil my drawing like u did last time, idan kayi koh?" Tayi gritting lebenta da hakoranta, "Allah zamu 6ata". Yayi saluting dinta, "yes ma'am!" Tayi murmushi ta juya, ta kunna mp3 dake gefe wakar Ankit Tiwari da Palak Mucchal ta Sanam Teri Kasam ta fara playing. Ta fara zanen tana yi tana kallonshi......
*9ja...*
Durkushe suke a kan tattausan carpet din daya zagaye kasan falon yayinda iyayen ke zaune akan kujera. Alhaji AbdulRasheed ya dube su su biyun yace "yanzu kai kana nufin gabadaya UK zaka koma da zama?" Ya gyada kai, ehh daddy. Kamfani na yana can babu yanda za ayi inyi relocating dinshi zuwa nan ne, kaga dole dai sai ina can din". Ya maida dubanshi ga Ameenah, "uwargida kinji fa wata sabuwa" ta gyada kai, well, it's not a bad idea after all, amma bari muji ta bakin maduga uwar tafiyar.... Duk suka maida hankulansu gareta.
Muhaaseen, matashiyar budurwa mai jini a jika er kimanin shekaru sha takwas. Shekarar data gabata ne ta gama karatunta na sakandire yanzun tana jiran admission ne a jami'ar Bayero inda take son karantar fannin hakori wato dental, duk da cewa she has talent a fannin Zane da painting amma tace bata son karatun, Wanda ta iya ma ya isa.
Ganin duk ita suke kallo yasa ta sadda kai kasa, ta motsa bakinta a hankali kamar mai tsoron magana tace "am sorry Mom, Dad, ba zan iya auren Yaya Al-Ameen ba!!" Bai san ya aka yi ba sai ganin shi yayi a tsaye kan kafafunshi yana nuna Muhaaseen da hannu bakinshi na rawa amma ya kasa magana. Abin ya daurewa iyayen kai matuka, a iya sanin su dai yaran na matukar son junansu, meke faruwa ne haka???
©Jeedderh🐾
[5/2, 11:10 PM] +234 816 492 9724: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕
🐾°•72•°🐾
_I want to use this opportunity to thank you all by staying with me, being here for me, following me tirelessly.... I really appreciate having you by my side, I mean you, my FANS! I love you sosai and I really like the moments that we've spent togedha. May Almighty Allah bless us all abundantly, and may we all meet like this again, in Allah's mercy.... Thank u all!!_
*★★LAST PAGE★★*
Alhaji AbdulRasheed ne ya daure yayi magana don Ameenah babu baki a lokacin, yayi gyaran murya yace "meke faruwa ne Uwata? I mean wani abu ya faru ne a tsakanin ku da yayan naki?" Ta girgiza kai, "babu komi daddy, kawai na yanke shawarar ba zan iya auren shi!"
Zufa ta shiga yankowa Al-Ameen ta ko'ina, da kyar ya iya daga bakinshi cikin rawar murya, "but...buh Cherryyyy.... Why???" Ameenah data fara hura hanci a fusace ganin yadda dan nata ya rikice a lokaci guda ta daga baki da niyar magana, AbdulRasheed yayi saurin dakatar da ita, "it's okay.... Uwata?" Ta amsa a hankali, na'am daddy? Yace "idan ma wani abu ne ya faru a tsakaninku, go ahead and solve it by yourselves. Kin san cewa tun farko da bakin ki kika fada mana kin amince da Al-Ameen a matsayin mijinki, kowa a dangi yasan da wannan maganar don haka ba zaki maida mu mutanen banza a idon duniya kin gane? Tashi kuje!" Ta mike a hankali tana turo baki ta doshi kofa, Al-Ameen ya bi bayanta kamar wanda kwai ya fashewa a jiki.
Abbakar kanin Muhaaseen yaro dan shekaru 11 ya dubi kanwarshi Badar ya mata rada a hankali "anyi dumping Yaya Al-Ameen, I wonder how he's feeling ryt now..." Badar ta kyalkyale da dariya tace "amma banso haka ta faru ba, nasan yau kowa sai ranshi ya baci a gidannan tunda aka 6atawa BOSS rai" Ameenah ta harare su, 'gulman me kuke yi anan?" Abbakar yayi saurin kawar da kai, Momi ba komi. Kunnenshi ta kama ta dan ja, "r u trying to fool me? Tashi ka bani waje stupid boy..." Ai a sukwane ya mike Badar tabi bayanshi. Musah dan shekara bakwai dake zaune a gefen daddynsu ya kyalkyale da dariya, tana kalloshi yayi tsit kamar bashi bane mai dariyar.
A bakin kofar fita Muhaaseen taja birki, ta mika mishi hannu tace "giv me ma 50k!" Ya kalleta cikin mamaki, 50k? What for? Tace "ka manta? Our bet??!" Ya danyi jim na en mintuna yana so ya tuna, idanu ya zaro sosai lokacin daya tuno abinda ya faru. Cimak ya daga ta sama ya shiga juyi da ita yana ihun dariya, iyayen suka taso cikin mamaki suka iso garesu, "lafiya? Meke faruwa anan?" Inji Ameenah. Ya direta kasa yana shesshekar dariya, "Mamie... Mamie, Allah yarinyar nan ta raina ni da yawa...."
Muhaaseen ta rufe baki da hannayenta tana dariya. Ameenah ta harareta, "zaki fada min abinda ya faru ne wai ko sai na hanbare ki??" Muhaaseen tace"Mamie, shine fa ya fara kawo maganar, ranar nan yace ba zan taba iya rejecting dinshi a gabanku ba, ni kuma nace zan iya. Shine yace to mu saka 50k idan nayi rejecting dinsa zai bani 50k idan kuma na kasa ni zan bashi.... To yanxu nayi, don Allah ba sai ya bani kudina ba?"
Ameenah ta daga hannu kamar zata daketa, tayi saurin kaucewa ta fada jikin daddynta ya rungumeta suna dariya. Ya dago kanta ya kalleta yace "yanzu dai akwai zancen aure a kasa kenan??" Ta nutsa kanta a kirjinshi cike da jin kunya tana murmushi, ya dubi Al-Ameen dake share zufa, teasingly yace "to suriki na sai a fara shiri koh? A zo a kira mutane su zo daurin auren yayanmu, zan bada a buga invitation card da wuri don next week in shaa Allah nake so ayi a daura auren. Na kula wannan matar taka juya ka zata dinga yi ya waina a tanda, kamar dae wata er ware....!" Ameenah tayi saurin kai dubanta gareshi "da wa kake?" Yace ahh! Kuji ni da mata, nace ne dake nake? Ta yatsina fuska "to kowa dae yayi zagi a kasuwa yasan da wanda yake...!" Al-Ameen ya kamo hannun Abbakar don yasan idan suka tsaya haka zasu yi tayi kamar wasu kananan yara, yanayin relationship din iyayen nasu na matukar burge shi ba kadan ba, zamantakewar su da soyayyarsu da yadda suke girmama juna yana burge shi sosai, yana kuma fatan shima zai yi irin wannan zaman da matarshi har tsufan su. Yace "heyy guys! Let's go on a date, ayi celebrating murnar auren da zanyi" aikuwa suka kwashi ihu suka yi waje da gudu, Abbakar yaja ya tsaya, "amma ina za mu je?" Badar tace"let's order everything sai muje sculpture garden na UMM-AMBAM Art Gallery mu shakata abin mu ko ya kuka ce??" Muhaaseen ta mata thumbs up, "good idea Bee, let's go, hurry!" Suka dunguma gabadayansu suka fita suna wa iyayen bye-bye , su kuma suka bisu da kallo cikin murmushi har suka 6ace musu.
Suka maida dubansu ga juna suka sake yin wani murmushin, ya kamo kugunta ya matso da ita kusa dashi "so wat's next? Anyi solving wannan matsalar" ta kalleshi, "zancen his excellency H.B..." Ya dafe kai, "God! Manta da mutumin can kawai, na fada mishi ba zan iya amsar ministan lafiya ba, nauyin yayi mun yawa" ta tabe baki, "but wat r u going to do? Yanzu haka an gama appointing dinka as the new minister of health!" Ya zaro idanu "What?!" Ta danyi murmushi "sorry! But u know dat u deserve it koh? Ko kana mana black stomach ne kan zamu koma Abuja da zama?" Yayi rolling idanu "darling...." Ta katse shi shhhh! It's okay..., I know dat u can do it. Ya gyada kai "yeah! I know. Amma tunda bada sanina aka yanke shawarar ba, u must pay for what you did". Ta daga kafada, "yes, I'll. Me kake so?" Yaja hannunta har master bedroom dinshi, ya jefata kan gado shima yabi bayanta. Ya rungumota a jikinshi bakinshi a saitin kunnenta, "5 rounds... 1 for celebrating kin cika alqawarin da kike fatar cikarshi shekara da shekaru, 2....." Ya fada yana zuge zip din rigarta, "..... Na murnar na zama minista..... 3....." Tayi saurin katse shi ta hanyar hade bakinshi da nata, ya lumshe idanunshi cikin sauri, yaja bargo ya rufe su dashi ruf.....
Da dare gabadayansu suna falo akan dinning, daddy ya ajiye cokalin hannunshi ya dubi yaran yace "next week idan kun samu hutu zamu je Gombe, a can daura auren yayyenku su wuce UK daga can!" Suka kwashi ihun murnar zasu je su ga tsohuwa Ammie....
Daya bayan daya Ameenah ta dinga binsu da kallo har ta sauke idanunta akan Al-Ameen, ya duka yana yiwa Muhaaseen rada a kunne, ita kuma tana murmushi cike da nuna so. Ameenah ta lumshe idanunta a hankali ta sake bude su akan su, "Marwann!!" Tayi whispering a cikin zuciyarta, "r u watching? Ur son has become a giant, handsome, responsible son. Har kullum ina godiyar kyautan shi da kayi mun, Alhamdulillah. Ko yanzu zan mutu I'll have no regret, nasan cewa ko bayan raina jinin gudan jinina dana gudan jinin Marwan zasu taka doron kasa....!" "....balle ma sai kin goya su a gadon bayanki in shaa Allah!!" Ta jiyo sassanyar muryar ta ratsa kasusuwan kunnenta a hankali, ta kalleshi a nutse fuskar shi na dauke da kyakkyawan murmushi. Ya kanne mata ido, ta saki murmushi very soft, ta dora kanta akan kafadarshi, yasa hannunshi a bayanta yana shafawa a hankali ya rada mata kalmar"love you" a kunnenta, ta kara lumshe idanunta tana kara nutsa kanta a kafadarshi. Yaran sai suka fara er dariya suna jimke baki suna kus-kus, tana musu kallo daya kowa ya dawo sense dinshi, babu wanda ya kara ko tari. Tayi murmushi ta maida kanta ta kwantar a kafadar gudan ranta, yayin daya kara rungumeta warmly a jikinshi...... ALHAMDULILLAHH!!
*THE END!!*
Gaisuwa ta musamman zuwa ga:
*Khaleesat haiydar Facebook hausa novel group*
*Jeedderhs world Hausa novel whatsapp group*
*Deejah Abdul novel WhatsApp group*
Dama sauran novel groups da ba zasu rubutu ba, nagode sosai da kaunar da kuka nuna min during all this time, Allah ya bar kauna.
Kamar kullum, kofofin korafi, gyara, comments, da sauransu a bude suke a wajena, kuma Ina maraba dasu a koda yaushe.
Littafin *BAYAN RAI!* kirkirarren labarine dana jima ina kirkirar shi, idan suna, halayya, yanayi, ko wani abu yazo daya da rayuwar ka/ki, wannna coincidence ne, banyi la'akari da rayuwar kowa wajen rubuta labarin ba.
Littafin Bayan Rai tukuici ne gare ki, Leemoh my friend, Ina miki fatan Alkhairi a duk inda kike.
I dedicated this whole book to my one and only blodd, *ANTI ZEE*.
FANS 💗💗💗💗 sai mun sake haduwa a sabon littafi na mai zuwa in shaa Allah.
©Jeedderh🐾💕