Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Friday, 14 June 2019

Omar ko farooq complete Novel

adsense here
Omar ko farooq complete Novel

Omar ko farooq complete Novel


[8/30, 10:05 PM] ‪+234 706 897 1326‬: ® *OMAR* *KO*  *FAROOQ* ❓ 

          1_5 


  "Omar ko farooq samari kenan masu ji da kai, hade da bugun abujaa. 'Yan biyu ne wajen Alhaji Basheer da mummy'n su Hajia zainab. "Sun taso cikin gata da soyayyar mahaifan su, babu abinda suka nema suka rasa, saidai a kwaisu da rashin mutunci wulakan ta dan Adam a wajen su ba karamin Abu bane. "Tabbas wannan hali nasu yana damun mummy idan tayi magana daddyn su zaice ai yarane a barsu, a haka har suka sangarce, "idan akace batun kamanni mutun duk kwakwar sa bazai iya banbance su ba, wannan su ake kira da identical twins. Shiyasa idan daya yyi laifi toh da wuya a kama su, saidai duk a hadasu ayi maganin su wannan kuma abu ne me wahala sbd daddyn su ya tsaya mu,  idan an tambayi daya zaice bashi bane haka nan dayan baka d wani shaida d zaka tabbatar da hakan. 
     "Idan muka koma bangaren kyau, tofah saidai ace masha Allah dogaye ne masu fadin qirji da fuskar su a kewaye Wanda yyi daidai da dara-daran idanun su masu matukar kyau tamkar masu jin bacci, hancin su kuwa dogo ne yyinda kasan sa akwai kewayeyyen pink lips. Sumar Kansu kuwa akwance take har wani sheki take habawa taji gyara. Omar shine babba yyinda farooq shine karami ma'ana hasan da hussaini. 
     Idan akace 'yan mata ba'a mgn toh tanan zaka iya banbantasu domin farooq akwai son 'yan mata yana chilling life dinsa, yyinda omar baima da lkcin ko wacce kucaka. Dariya bata damesu ba, dukda farooq yana kula 'yan mata bawai ko wacce jik and jak yake kulawa ba aa sai me class sanna su suke biyoshi bawai shike binsu ba. 
    "Yau kwana daya kenan da dawowar su daga india bayan kammala karatun su da sukayi, inda omar ya kanci harkar likitanci fannin operation, yyinda farooq ya dauki fannin duba matsalar data shafi mata (Gynecologist).
     "Sai wajajen 11 suka shigo side din iyayen nasu, dake jiransu danyin breakfast. "Bayan sun gaisa daddy ya kallesu cike da murmushi. Mummy ma haka ganin twins dinta sun gama kr2. "Bayan sun kammala cin abincin daddy yyi gyaran murya kowa yyi shiru yana sauraren abinda zai ce....
Nuceey luv😘
[8/30, 10:06 PM] ‪+234 706 897 1326‬: ® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓ 

          6-10


 "Daddy yace toh Alhamdulillah tunda Allah ya kawo mu wannan lkcn da muka dade muna jira. "Abu na farko shine na Gina muku hospital naku me suna *OMAR* *FAROOQ* *SPECIALIST* *HOSPITAL* a tare twins din sukayi murmushi hakan ya tabbatar wa iyayen nasu sunji dadi kenan. "Daddy yace bayan nan kowa na Gina masa gida nan ma murmushin sukayi, "abu na karshe shine kowa inaso ya fito da Matar da zai aura, Amman Ku sani a tsarina banason Ku kwaso 'ya'yan talakawa hop kun gane....mummy tayi saurin kallon daddy bude baki tayi tace haba alhji talaka da me kudi duka mutum daya yyi su ai, kuma...daddy ya daga mata hannu enough plss, mummy na ganin haka taja bakin ta tayi shiru dan batason ja in ja da alhji gaban yaransu dan a ganin ta be dace ka dinga CeCe kuce a gaban yara ba.
     "Daddy ya kalli twins yace hop kun gane, gaba1 suka gyada Kansu. "Ana suka tashi dan komawa side dinsu. "A hanya farooq yyi 'Yar dariya hakan yasa omar ya kalle shi yace lpy? "Farooq yace wai daddy ke zancen aure, omar yaja tsaki yace ai ko beyi ba kaikam kana bukatar aure, "farooq ya zaro ido yace haba bro. Nayi karami dayawa. "Omar ya tabe baki yace shi yasa kuma kke chilling da enmata koh, farooq ya Sosa qeya batare d yace komai ba, nan kowa ya shige dakinsa.
     "Omar kwance kan gado yana tunanin abinda daddy yace shidai mgnr gsky be shirya aure yanxu ba, hasalima mata basa gaban sa shi a nasa tunanin bega abin burgewa a aure ba, dukda yanada enmatan dake nuna so gare hakan be tabajin a zuciyar sa mace ta birge shi ba, wasu ma zaton su ko farooq ne Amman d sunga ba fuska zasu gane omar ne, ajiyar zuciya ya saki yyinda ya tuno cewa daddy yace bayason su auri 'yan talaka wato kwarya tabi kwarya, murmushin yake yayi toh shi ko zaiyi aure ya rasa wacce zaiso sai masu warin kodaddan kaya?,god forbid masu kudin ma sai a slow, shi yasa Sam baya son dawowa naija sbd wannan mgnr auren yasan dole sai sunyi musu. Da wannan tunanin bacci ya sace shi.
Nuceey luv😘
[8/30, 10:18 PM] ‪+234 706 897 1326‬: ® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓ 

        11_15 "Da yamma duk sunci kwalliyar su, anan falo suka tarad da mummy tana kallon News. "Gud evening mummy, a tare suka furta, mummy da murmushi ta kallesu tace aa my twins har kun fito. "Eh mummy suka bata amsa bayan sun zauna. "Mummy tace gud. "Sannan ta kallesu tace twins, gaba1 sukace na'am. Mummy tace bawai nace kuyi watsi da mgnr mahaifin Ku bane, Amman inaso Ku fahimci Abu daya ita rayuwa da mai kudi da talaka duk Allah ne ya halicce su, shin meye ribarku idan kun kyamaci talaka? Nidai burina Ku samo mata na gari masu cikar kamala da sanin ya kamata. "Gaba1 shiru sukayi suna sauraron ta saidai kash yanda ya shiga haka ya fita a kunnen su, a fili kuwa nuna mata sukayi ah ba komai mummy zamu kiyaye insha Allah. "Sosai mummy taji dadi ta kuma sa musu albarka.
    "Kasancewar yau Monday da wuri suka shira, sosai sukayi kyau tamkar a sace su, bayan sun gama breakfast, suka dunguma zuwa mota don tafiya hospital cox yau ake bikin bude shi, dan haka anyi gayyata sosai dan taya twins din daddy murna.
    "Sosai aka taru bayan addu'o'i da akayi tare da fatan dorewa har abada, da kuma Allah ya sanya Alkhairi cikin harkar, nan daddy yace xa'a fara diban ma'aikata ranar laraba domin tantance kwararrun likitici. "Bangaren mata kuwa abin ba'ace komai sosai kowacce mace me aji taci burin kasancewa mata daya daga cikin su.
    

   **************
"Tafe take cike da nutsuwa hijab dinta har kasa yyinda take rungume da qur'ani a hannun ta, "Assalamu Alaykum, sallama tayi cikin wani madaidaicin gida, Wanda yake ginin kasa ne da Alama gidan ya dade dan har katan gar taso ta rushe, qara maimaita sallama tayi nan taji shiru anan ta qara sauri bayan tana kokarin cire hijab dinta, ta nufi d'an dakin su dake kwaya d'aya JAL a cikin gidan. "Bude labulen tayi, ganin Umman ta tayi kwance tana nishi kadan2 da sauri ta afka dakin nan ta shiga kiranta ummaaa, umma,  meya sameki? Wacce aka kira da umma tace da kyar ba komai Imaan zanji sauki insha Allah, buh umma meke damun ki? "Umma tace cikina ke ciwo inaga ramar da naci jiya take son 6atamin ciki karki damu zanji sauki insha Allah... Ta karasa mgnr tana nishi. "Imaan badan ta yadda ba ta kyaleta kurum dan ta lura a 'yan kwanakin nan umma batajin dadi dauriyace kurum irin tata. "Mikewa imaan tayi ta canja kayan jikin ta sannan ta fita dan dafawa umma ganyen darbejiya kamar yanda ta bukata dan tasha.

*******
"Kwararrun ma'aikata maza da mata aka diba a wannan hospital din bayan tantance su da akayi, aka tatse, aka yashe, kafin aka bar me rabo acewar  _Omar_ da _farooq_ basa son malalatan doctors Wanda basu San kan aikin su ba, shiyasa dayawa Wanda suka shiga musamman matan suke jinsu on top. " bayan gama tantancewa suka sa date akan Monday zasu fara aiki a hospital din bayan sanar wa d sukayi.
Nuceey luv😘
[8/30, 10:19 PM] ‪+234 706 897 1326‬: ® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓ 

          16_20


 "Masha Allah Monday nayi kowa ya fada bakin aiki, sosai ma'aikatan suke da kwazo kuma marasa lpy sunzo Wanda suke Neman sauki, "Wanda suke buqatar operation kuwa sai hamdala suke domin Dr Omar yasan aikinsa yyi komai successfully, yyinda Dr farooq shima yasan nasa aikin dan sosai mata masu matsaloli suka halarci ganin kwararran likita. "Aiki ya kankama ba iya Kano ba hatta makotan jahohi da dama sun samu lbrin asibitin *OMAR* *FAROOQ* *SPECIALIST* *HOSPITAL* Me tarin kwararrun ma'aikata.

    *****

"Wanke wanke take tana 'yan wakokin ta, ji tayi nishin umma ya tsanan ta, da dauri ta ajiye komai ta fada dakin, ummaa, ta kira sunan ta sau uku Amman da kyar umma ta iya amsa mata, "ba shiri ta bankada kasan tabar mar dake dakin su nan ta tarad da 500 a kasan wajen, ita kadai CE kawai arzikin su a duk fadin gidan, "cike da tausayin Kansu ta kalli umma, tace umma tashi mu tafi asibiti, umma ta girgiza kai dan tasan koda sunje basuda kudin magani. "Imaan ta canja kayan jikin ta zuwa Riga da skirt da dogon hijab dinda na islamiyya. "Nan ta daukowa umma nata hijab din, umma ba yanda ta iya dan ita kanta tanajin jiki ta rasa meke damun cikin ta. "Dakyar ta mike sannan ta tashi da kyar, "imaan ta sakala hannun ta a kafadar umma, vayan sun fito tayi dabarar rufe dakin na su, sannan suka fito waje. "Mai napep ne yaxo wucewa nan imaan tayi saurin tare shi. "Me napep yace INA zaku? "Imaan tace general hospital, me napep yace kudin Ku 600, "zaro ido imaan tayi tace dan Allah malam ka sassauta mana, me napep yace toh kawo Dari biyar. "Imaan tace haba dan Allah ka tausaya mana mahaifiyata bata da lpy wai baka ga halin da take ciki bane? "Me napep yace malama iya ragewa na miki, nima ya kamata ki tausaya min a wannan zamanin na 'Yar buhariyya kinsan komai yyi tsada dala ta tashi. "Imaan ranta bace tace komai da an tabo mutane dala ya tashi wani Sam be San me ake nufi da dalar ba Amman sbd Dora lefi da rashin rungumar kaddara a kowanne hali da muka tsinci kanmu sai Ku dorawa shugaba alhalin shi ba _kunfayaqun_ bane. "Ah lalle toh idan wa'azi zakimin kinga tafiya ta Sana'a na fito nema ba wa'azi ba. 
    "Imaan ta kalli umma duk ta canja kamanni da gani tanajin jiki, da sauri ta tsaida me napep din dake shirin tafiya, tace dan Allah babu wani hospital nan kusa? "Me napep yace shigo muje akwai sbd da aka bude satin daya wuce, "da sauri imaan tace nawa ne kudin daga nan? Me napep yace 250, "imaan tace toh muje, haka da kyar umma ta shiga napep din sannan imaan itama ta shiga. 
    "Basu wani dade ba sai gasu a wannan hospital din, gaban imaan ne ya bada rass yanda ta ga tsaruwar hospital din shiya tabbatar mata da private ne, to yanxu INA zata samu kudin magani? "Kallon me napep tayi tace wannan ai private ne malam babu wani me saukin kudin? Me napep yace ke yarinyar nan kin cika mita wallahi ni Ku fita inada abun yi. "Imaan ta kalli umma, umma ta daga mata kai alamar su fita, haka suka fito bayan ta biyashi kudin sa.  "Sannu a hankali suka shiga cikin asibitin imaan ta rikice da kallon tsaruwar wajen kamar ba hospital ba, ta rasa INA zasu bi dan ganin doctor, "wata matace tazo wucewa da Alama ta rako marar lapiya ne., am baiwar Allah imaan ta tsaida ta. "Matar tace na'am lpy? Imaan tace dan Allah INA xanbi dan ganin doctor? Matar tayi mata kwatance sannan ta tafi. "Basu yi wani tafiya me nisa ba suka isa wajen nan suka zauna, nan imaan ta tambayi wata INA ake yankar kati. "Nuna mata wajen akayi nan taji ance ta kawo 200, ba yanda ta iya haka ta biya.

   "Sannu a hankali har aka zo kan sunan umma, nan suka mike suka shiga office din doctor, tunda suka shigo yake rubuce2 saida ya gama ya dago kai yace meke damunta? Imaan tayi masa bayanin komai. "Dr yace sai anyi mata scanning kafin musam meke cikin ta.. Imaan tace a INA akeyi? Dr ya daga waya ya kira wata nurse bayan 4mins saiga ta. "Nurse din tace Dr islma'il wats going on? "Dr ya kalli su imaan yace tafi dasu ayi mata scanning, nurse tace ohk.
   "Wani daki suka shiga nurse din tace zaku biya kudi, take cikin imaan ya bada kululu.. Karfin hali tayi tace nawa ne kudin? Nurse din tace 5000, imaan ta zaro ido sannan tace am toh dan Allah kiyi mata zanje na ranto kudin. Nurse ta kalli imaan kallon raini tace Amman bakida hankali ko, imaan tace kamar ya? Nurse din tace an taba aiki ba kudi ne? Imaan tace dan Allah nace ai, take nurse din tace oya tattare mamarki kubar hospital din nan tun kafin Dr Omar [truncated by WhatsApp]
[8/30, 10:21 PM] ‪+234 706 897 1326‬: ® *OMAR* *KO* *FAROOQ*  

        21_25 "Imaan tace waye shi? Nurse din tace ke dallah ban sani ba, imaan tace dan Allah gayamin waye shi, nurse din ta mike a kan kujera tace tashi kubar dakin nan, haka ta koro su waje, daidai lkcn Dr Omar yazo wucewa, da sauri nurse din ta dan sunkuyi Alamar girma tace morning sir, Dr Omar batare d ya kalleta ba ya daga mata hannu kawai, Imaan na ganin haka tace oh da Alama wannan shine Dr Omar kamar yanda taji Matar ta fada da farko. "Da sauri ta sha gaban sa, ba nurse din ba hatta shi kansa Dr Omar din saida yyi mamakin abin da imaan tayi, imaan kanta tsaye tace dan Allah idan Kaine Dr Omar ka taimaka kace a dubamin lpyr umma tana cikin wani hali wallahi, "Dr Omar ransa a 6ace ya daga murya yace wacece ke? Waya baki right na ki shigemin gaba? Imaan take kwalla ta ciko mata dan yanda taga umma na juyi a kasa tace ka taimakamin Dan Allah, Dr Omar cikin zafin rai yace da xaki shigo hospital, kinga An rubuta *TAIMAKO* *SPECIALIST*  *HOSPITAL* ❓. "Imaan ta girgiza kai dan ita ko sunan hospital din bata daga kai ta gani ba. "Anan Dr Omar yaja wani dogon tsaki sannan ya kwalla kiran cleaners dake hospital din, "da dauri suka fito dan kowa tsoron shi suke. " cike da izza yace Ku fitar min da wa'annan garbage ( datti) din. Atake sukace ohk sir. Imaan kuwa ranta yyi kololuwar baci, garbage? Ta maimata, ganin ya fara tafiya ta daga murya tace mungode da wulakanci, saidai ka sani dan Adam ko ya yake akwai tasa ranar. "Dr Omar yanajin ta Amman be waiwayo ba dan tsari da irin wannan masu warin kodaddan kayan 6ata lkci ne. "Cleaners din mata suka kama umma da nufin fitar da ita, Amman ga mamakin su suka jita sharab kaman kayan wanki hakan ya tabbatar musu da rai yyi halin sa. "Take kowa ya matsa, imaan ta kallesu tace umma ta suma Ku taimakamin mufitar d ita dan Allah, wata mata tace yarinyar saifa hakuri dan Allah ya amshi abarsa... What? Karya kuke wallahi umma nada rai tacemin very soon zata samu lpy, wayyo umma ki tashi ki qaryata mutanen nan. Haka imaan tayi ta surutai, kamar wata zararra, "bayan minti 20 aka kai umma gidan ta na gsky. "Imaan kuwa fita tayi tana hada hanya tana kuka kowa daya kalleta saita basa tausayi, saidai fah kowa ya wuce dan wannan zamanin tsoro gareshi mutane sun 6ata sunan wasu, ma'ana idan mutum yyi niyyar taimakon ka sai kaga Wanda aka taimaka ya kai Wanda ya jawo shi cikin inuwa zuwa rana. "Haka imaan tayi ta galallawar ta kan hanya, ga yunwa ga tashin hankali, A kasan wata bishiya ta dan rakube dukda akwai samari dake zama ta wajen hakan be hanata zama ba sbd gajiya da tayi. 

   "Da dare kowa na harkokin gaban sa, imaan tana kasan bishiyar nan, bata koma gida ba kasncewar 'yar 50 din data rage mata ta fadi, babu kuma Wanda zai taimaka mata ta koma gida, cikin ta ne yake juyawa sakamakon rashin abinci tun jiya d rana da taci, "a hankali take jin hirar wasu samari kala2 suna cewa ah baba da ganin ta ai zatayi mai, tun rana take kasan bishiyar nan, kaga mu afka mata kawai. Imaan najin haka ta mike ganin su tayi sun nufo ta. "A take tasa gudu dan ta lura basuda imani, ai suna gaanin tasa gudu suma suka Mara mata baya, sosai hankalin imaan ya tashi ganin ita suke be dgske.

  "Tafiya yake yana driving hankali kwance, sai jin music yake, yana cikin tafiya yaji ya bugu Abu, ai da sauri ya fito a motar, "ganin mace yyi kwance da alama taxo tsallakawa ne, duba kanta yyi yaga jini Na zuba kamar an bude famfo, dan karamin tsaki yaja danshi bazai je hospital ba at dis tym around, kusan 12 fah kenan, daukar ta yyi yasa bayan mota da nufin tafiya da ita gida. 
    Sosai yake gudu, dan yaga jinin d gske yake fita. Tafiyar 15mins ne ta kaishi tangamemen gidan nasu, "da gudu ya dauko ta a bayan mota sannan ya shiga da ita gidan, "mummy ya kira sunan ta, mummy dake shirin tashi dan komawa daki tayi bcci ta juyo ganin sa  riqe da yarinyar mummy tace _subhanallahi_ me name gani farooq? Farooq yace wlhy mummy kade ta nayi a mota tazo tsallakawa, mummy tace toh me kke jira ji yanda jini me zuba oya yi sauri ka dauko _first_ _aid_ _box_ farooq ya kwantar da ita yace ohk. "Side dinsu ya wuce a gurguje yaxo sannan ya fara kokarin tsaida jinin, bayan ya gama sannan ya gwada jinin Yarinyar yaga group O positive, ya kalli mummy, mummy tace meya faru? Farooq yace tana bukatar jini ne, mummy tace toh sa mata naka. Farooq yace ba daya bane, coz nawa  O negative ne, mummy tace toh yanxu ya za'ayi? "Farooq ya kalli Omar da tun shigowar shi yana kan wani kujera yasa system a gaba da alama akwai abinda yake, gefe guda coffee ne ya gefe Yana sha a hankali, "yace uhum ko bro zai bada nashi. "Mummy tace ban gane ba, bakuda bambanci ta kowanne waje taya jinin Ku baze zo da[truncated by WhatsApp]
[8/30, 10:23 PM] ‪+234 706 897 1326‬: ® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓ 


          26_30   
 "Farooq yace yes mummy we ar identical twins, buh it can't nevar be dsame, mummy mutane dayawa basa iya banbantamu Amman ke kina iyawa, kinga dole akwai hanyar da kike ganemu koh. "Mummy tayi murmushi tace yeah, yanzu dai a samu mafita. "Farooq yace ki dan fadawa bro ko zai bata, mummy ta kira sunan.Omar tace zo a Debi jinin ka a bawa wannan baiwar Allah'n. "Omar dukda yasan positive gareshi Amman ya hade girar sama data kasa yace ni mummy jini na negative ne, mummy ta saki baki tace tohhh yaushe ka faramin karya omar? Sunan da ya Dade beji mummy ta kirashi kai tsaye ba. Gashi Sam bayason bacin ranta, dan haka yace ma farooq zo ka diba, ya fada yana kumbura fuska, farooq kuwa dariya ce taso kwace masa ganin yanda bro dinsa ya wani bo ne face. "Yana sa allura jikin sa, omar yace auchhhh... "Farooq yyi murmushi a zuciyar sa yace ji mutumin d yake fede mutane Amman ji yanda yake wani noke jiki.. Omar ne ya katse shi da fadin kayi abinda ke gabanka ba tunani ba ka wani barmin allura cikin jiki tana zuke min jini. "Dariyar d farooq yake boye ta subuce, yace sorry bro nan ya cire allurar, Omar kuwa yahau jijjiga hannu ransa a bace.
     "Mummy tace kaita dakina saika daura mata jinin tunda dare yyi ai ba'a barta a falo ba, farooq yace toh mummy, nan yace bari naje side dinmu na dawo 2mins pls, mummy tace no prob. "Kallon omar tayi daya ci gaba da latsa system kamar bashi ne dazu yake karar ciwo ba, daidai zai kai coffe bakinsa mummy tace kai son tashi ka dauki yarinyar muje daki kafin ya dawo, Atake omar ya fara tari dan coffee daya sha be wuce ba, mummy tace sannu, ganin tarin yake d gske ta bude fridge dake dakin ta dauko masa ruwa, karba yyi yasha, bayan ya lafa.. Mummy tace toh tashi ka... Bata karasa ba ya sake wani tarin wannan karan na karya ne danshi harga Allah beji zai iya daukar ta ba dukda tunda aka shigo d yarinyar be kalleta ba, wayasani koh kazama ce ya fada a ransa yana me ci gaba d tarin karya dukdan kar mummy ta matsa masa d zancen. "Mummy kam ta dauka tarin gaske ne sai sannu take masa, ahaka farooq ya qaraso da sauri sannan ya dauki yarinyar ya kaita dakin mummy, omar na ganin haka ya daina tarin.  "Kan dan karamin gadon mummy ya ajiyeta sannan ya daura mata karin jinin.

   "Mummy ta shigo, farooq ya dago bayan ya gama yace gata nan mummy gud nyt. Mummy tace ohk nyt.
  "Dasafe around 11 duk sun hallara kan dining danyin breakfast, mummy ta kalli farooq bayan duk sun gaishe ta, tace yarinyar nan bata farfado ba fah har yanzu. "Farooq yace ba damuwa mummy nan da 5hrs zata tashi insha Allah. "Mummy tace Toh Allah yasa, farooq yace ameen, omar kam sai cin abincin sa yake cike da kwanciyar hankali,
    "Farooq yace wai mummy yaushe daddy zai dawo? Mummy tace sai jibi. Farooq ya gyada kai yace toh Allah ya kaimu tace ameen.
Nuceey luv😘
[8/30, 10:24 PM] ‪+234 706 897 1326‬: ® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓

       31_35
 "Bayan 5hrs yarinyar ta fara motsi da hannun ta, can ta fara motsi da kafar ta, "daidai lkcin mummy ta shigo dakin, ganin tana motsi tayi saurin isa gaban ta sai hamdala take, fuskar ta tashafa tace sannu koh, a hankali yarinyar ta bude idanun ta, tass ta sauke su kan mummy, a razane tayi kokarin tashi, mummy ta tayata mikewa, yarinyar tsayawa tayi tana kallon dakin daya yi mugun haduwa, tunda take arayuwa bata taba shigar daki irin wannnan ba, shin kodai gidan yankan kai ne? Take zuciyar ta ta bada dammm, kallon ta tadawo kan mummy da itama kallon ta take, "muryar ta na rawa tace baiwar Allah dan Allah a INA nake? "Mummy tayi murmushi tace kwantar da hankalin ki, yanxu dai sakko daga gadon nan kiyi wanka tun jiya kike bacci, "zaro ido tayi balo-balo tace bcci tun jiya? Kallon Agogon dake manne a dakin tayi Wanda yyi mugun haduwa 4:05 ta gani, a rikece tace meya kawoni nan dan Allah... Bata karasa ba taji cikin ta ya murda kanta ya Sara  ahhhh tace, mummy ta riko ta tace tashi ga bayi shiga kiyi wanka daga baya saimu yi mgn, ba musu ta mike, sannan ta fada toilet bayan mummy ta taimaka Mata.
   "Sanda ta shiga toilet din kallon kauyanci takeyi, tayi kusan 5mins tana tsaye ta rasa inda zata taba,  fitowa tayi, mummy da mamaki tace harkin gam...., bakin tane ya katse ganin ko alamar wankan batayi ba, "yarinyar tace a hankali bansan ya zanyi ba. Mummy ta mike ohk, follow me, nan tabi bayan ta, cike da nutsuwa mummy ta nuna mata komai sannan ta fito. Nan itama tayi komai kamar yanda mummy tace.

   "Fitowar ta, ta iske mummy bata dakin, nan tayi gaban mirror, anan ta shafa mai me kamshi kansancwar ta 'Yar son kamshi hakan be mata wahalar gane wasu abun ba. "Bayan ta gama ta juyo dan maimaita kayan ta. "Harta cira zata saka mummy ta shigo rike da tray na abinci, "da sauri mummy tace aa ga kaya nan na fiddo miki dasu dauki ki saka, wata doguwar riga CE me kyau gaban kirjin anyi mata kwalliyar duwatsu masu hasken kyau. "A kunyace ta dauki rigar ta saka tana mamakin wannan Matar daga haduwa bata santa ba tahau yi mata hidima.
   "Bayan ta gama mummy ta miko mata tea me kauri, girgiza kai tayi tace ta koshi. "Mummy tace ki saki jikin ki bazan cutar dake ba, jin haka ta karbi tea din, daman cikin ta sai murdawa yake ga kanta sai zafi yake mata tamkar zai tsage. "Bayan ta kammala mummy ta miko mata plate na dankali da kwai, nan ma saida taci kusan rabin plate sannan ta aje, bayan gama mummy ta bata magani tasha.
    "Saida ta huta na 5mins, sannan mummy tace ya sunan ki? Yarinyar tace *FATIMA* Amman amfi kirana da _IMAAN_, mummy tace wow wat a nice name, ta fada tana murmushi, Imaan itama murmushi tayi dukda ta qagu taji dalilin ta na zuwa gidan nan, "gane hakan yasa mummy ta fara bata lbrin abinda ya sameta da yanda aka kawota gidan, sai alkcin imaan ta tuna ashefa wa'annan samarin da suka bita da gudu shi yyi sanadin ta na tsallaka titi har abun yazo da tsautsayi. "Mummy tace so ki fadamin inane gidanku sannan meye dalilin ki na fitowa daga gida A wannan tsohon Daren????
 Nuceey luv😘
[8/30, 10:24 PM] ‪+234 706 897 1326‬: ® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓ 

        36_40 "Imaan tace, sunana Fatima abubakar, INA zaune a nan kano unguwar rijiyar lemo, mahaifina malam abubakar da umma ta Sadiya sunyi auren so da kauna asalin su 'yan Maiduguri ne wannan tashe tashen bom din yasa sukayi hijira suka dawo garin Kano da zama, inda mahaifina ya sai dan madaidaicin gida da sauran kudin dake gareshi, daga nan ya fara sana'ar saida kaji, da wannnan muke cikin rufin asiri, tun INA shekara 5 a duniya Allah yyi masa rasuwa, sosai ummata ta shiga wani hali na tashin hankali kasancewar ba kowa suke dashi a garin kano ba, haka dai ta fara sana'ar wankau makota su kawo mata ta wanke a haka take ci damu, nayi makaranta ta INA js3 yanxu haka kasancewar halin yau dukda ta gwamnati CE dole za'a bukaci wasu kudi a wajen mu dan zana takar dar j.s.c.e. "tun lkcin muke ta fafutuka Allah be bamu ikon hada kudin ba, bangaren islamiyya kam Alhamdulillah na kammala sauka ta, sai hadda da wasu littafai da nake yanxu... "Labarina na karshe shine mafi muni da rashin dadin ji, nan taja numfashi tare da matse hawayen da suka cika mata ido tun dazu. "Sannan tace, jiya INA wanke wanke..... Tass ta zayyane wa mummy abinda ya faru da ita jiya, da rashin mahaifiyar ta da tayi.

   "Allah sarki mummy tace cike da tausayin imaan, tace gsky na tausaya miki sosai dukda mummy ta fahimci a hospital na yaranta abun ya faru, saidai taja bakinta tayi shiru. "Ta kalleta tace Imaan, imaan tace na'am. Mummy tace kin amince na maye miki gurbin Wanda kika rasa? Imaan ta zaro ido waje dan Abin mamaki ya bata tace ni kuma?, mummy tace eh, Imaan tayi kasa d kanta tana wasa d 'yan yatsun ta. "Mummy tayi murmushi tace tun lkcn Dana ganki sai naji hankali na ya kwanta d ke, tunda nake yarana biyu, gashi inason 'ya mace a rayuwa wa. Koda ace akwai iyayen ki a Raye daman zan nemi alfarmarsu su bani ke, Amman cikin ikon Allah saiga yarinya tazo har gida na. "Imaan tayi murmushi kawai. "Mummy tace daga yau mummy zaki dinga kirana ba baiwar Allah ba.. Ta karasa fada tana murmushi. "Imaan itama murmushin tayi kasan zuciyar ta cike da farinciki dan koda ta koma gida bata fa kowa, gashi batasan ma inane hanyar Maiduguri ba. "Kallon mummy tayi da murmushi tace banda bakin da zan gode miki mummy saidai nace Allah ya saka da Alkhairi. "Mummy tace ameen. Tashi kiyi sallolin da ake binki, imaan tace toh.

   "Bayan ta idar ta koma jikin mirror nan ta sake fesa turare da simple make up, sannan ta fito waje kamar yanda mummy tace mata. "A falo ta tarad da mummy zaune tana kallo. Itama zama tayi a kasa. Mummy tace haba imaan tashi daga nan ki dawo nan. "Imaan ta mike ta koma inda mummy ta nuna mata kusa da ita. Ahaka suna hira jefi-jefi, can sukaji An bude kofar falon tare da sallama.
    "Mummy ta kalle sa da murmushi tace tofah yau Kaine ka dawo da wuri haka? Farooq yyi murmushi yace kinsan nabar patient a gida ya kamata na duba ta. Mummy tace hakane, imaan na jinsu saidai hankalin ta na kan film din da take kallo. "Nan farooq yace mummy INA take? Mummy tayi masa nuni da ita, oh abinda ya fada kenan danshi tunda ya shigo hankalin sa be kai gareta ba. "Matso yyi kusa da ita,.. Yaga hankalin ta na kan Kallo yadan buga kujeran yana kallon ta. "Da sauri ta jiyo gareshi. "Tana ganin sa ta hade girar sama data kasa dan har abada bazata manta fuskar nan ba, fuskar da tayi sanadin mutuwar umman ta. "Take ta maida kallon ta wajen Mummy, mummy tana ganin haka ta kauda kai, tasan za a rina, haka ta fada a zuciyar ta.
   "Imaan zata sunkuyar da kanta kenan sai sukaji an sake bude kofa,  daga kanta tayi, tasss ta sauke manyan idanun ta cikin nasa bala-balan idon, a razane ta maida kallon ta ga farooq Wanda shima ya hade rai kamar yanda omar yyi sbd yaga yyi mata mgn tayi banza dashi shine ransa ya fara baci. "Ido imaan ta zaro ganin fuskoki  masu kama daya, Wanda duk kwakwarta ta kasa tantance waye omar daga cikin su. "A zuciyar ta tace *OMAR* *KO* *FAROOQ*??? Wanne ne a cikin su yyi mata rashin mutunci???
Nuceey luv😘
[8/30, 10:25 PM] ‪+234 706 897 1326‬: [8/17, 5:34 PM] Nuceey luv😘: ® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓


         41_45


 "Omar kam mamakin ganin ta yyi, dan bazai manta yarinyar data sha gaban sa a hospital ba abinda yasan tabbas kowa shakkar sa yake shiyasa tayi matukar bata masa rai., wata xuciyar tace kodai itace yarinyar da ka bawa jini? Ai da sauri ya sake kallon ta lkcn imaan ta sunkuyar d kai. "Take ran omar ya sake baci shidai gsky idan wannan kazamar aka bawa jinin sa gsky an gama dashi. Mwtss Yaja tsaki qasa2 batare da kowa ya jisa ba. "bece uffan ba illa wucewa da yyi, "mummy na ganin hakan tayi kokarin kawar wa imaan tunanin da take, a hankali ta furta omar lpyr ka yau ko mgn babu? Jin hakan yasa imaan tayi saurin kallon mummy dan ganewa idon ta wanne direction mummy ke kallo. Anan ta tabbatar wa zuciyar ta Wanda y shigo yanxu shine omar. "Omar batare d ya kalli mummy ba yace yau a gajiye nake mummy, mummy tace oh toh sannu., "imaan tajuyo kallon ta ga farooq daidai lkcn shima ya dawo da kallon sa ga imaan din dan shi harya maida hankalin sa ga kallo. "Yanxun ma fuskar sa a daure ya sake maimaita mgnr dazu, cikin muryar ta me sanyi cike da nutsuwa tace masa da sauki. "Farooq yadan ware ido dan yanda take sarrafa bakin ta yyi matukar birge shi., besan lkcn daya dan saki fuskar sa ba. Shima a hankali yace toh INA ne yake miki ciwo yanxu? "Imaan ta sunkuyar da kanta ganin ya tsareta da ido, tace ba komai, yace kinsha mgni? Nan kuma kai ta gyda masa. Farooq ya mike yana fadin gud. Sannan ya tashi yyiwa mummy sallama ya shige side dinsu.
    "Yana tafiya mummy ta kalli imaan tace sai kinyi hakuri da sabbin yayun ki, a hankali komai zai tafi normal, imaan kuwa ta kwakulo murmushi kawai dan bataso ta nunawa mummy irin tsantsar tsanar dake tattare a zuciyar ta da takeyiwa omar.
   "Omar kuwa tana komawa daki bayan yyi wanka ya canja kayan sa zuwa na shan iska. "Ji yyi duk ransa a bace yake, dan haka ya mike da sauri ya nufi dakin farooq, q falon sa ya tarad dashi yana kallo. "Farooq yace lpy bro na ganka haka? Omar ya watso masa kallo bayan ya iso gareshi yace uban wa ya baka izini kasa wa wannnan kazamar jinin jiki na? "Farooq cike da rashin damuwa yace wannan kuma daga baya kenan ai da kasan bazaka bayar ba meyasa ka bata tun farko? Omar yace ba wannan na tambayeka ba ya katse shi zuciyar sa na zafi. "Farooq yace so ka tmbyi mummy, "omar yyi kwafa batare da yace komai ba yabar wajen. "Farooq kuwa tsaki kurum  yaja.
 " Da dare dukka sun hallara kan dining table, Amman banda imaan tana dakin mummy tayi zaman ta dan batason sake haduwa d wannan omar din. "Mummy najin shiru bata fito ba, dan haka ta mike ta koma dakin. "Mummy tace imaan taso mana muci abinci. Imaan tace na koshi mummy, mummy tace banason gardama oya taso. "Ba yanda imaan ta iya haka ta biyo bayan mummy. "Suna zuwa wajen taja mata kujera dan ta zauna. "Omar harya dauko spoon zai kai bakinsa yana ganin ta take yaji shu kansa abincin ya fita ransa dan wani irin kyama imaan din ke bashi Ahe spoon din yyi dukda wata irin yunwar da yakeji haka ya tashi yabar wajen. "Mummy na hankalce dashi saidai batace uffan ba. "Farooq kam tabe baki kurum yyi yaci gaba dacin abincin sa. "Imaan kuwa duk sai taji itama ranta ya sake baci. ganin irin kallon rainin da omar ya bita dashi saikace yaga kashi kafin yabar wajen. "Mummy CE ta katse ta d fadin zauna mana imaan, dolen ta, ta zauna sannan mummy ta turo mata plate gaban ta don ta Debi abinci.Nuceey luv😘
[8/17, 6:38 PM] Nuceey luv😘: ® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓ 


        46_50


 "Ahaka ta tura abincin bada dadewa ba farooq ya yabar wajen shima. "Haka itama tana gamawa ta tashi, kallo ta zauna ta fara yi.
   *******
"Saida aka kai ruwa rana kafin daddy ya amince da zaman imaan a gidan dan a ganin sa tamkar an dauko wani datti ne an ra6a musu, kasancewar yau ya dowo., sosai mummy taji dadi na amincewar Daddy da yyi. Dan Haka ta fara tunanin kai imaan makaranta dan inganta rayuwar ta.
   "Da safe bayan sun kammala a dining danyin breakfast, yauma sai daga baya imaan ta iso wajen. "Kanta a kasa ta shiga gaishe da daddy, daddy ya amsa mata ba yabo ba fallasa dan Har yanxu da dan sauran kin da yake mata. "Nan ta gaishe da mummy, mummy ta amsa mata ba yabo ba fallasa. "Kallon ta takoma ga twins duk hankalin su nakan abinci har omar kasancewar mummy ta bishi daki jiya ta nuna masa rashin dadin ta na kyamar imaan da yake nunawa a fili, nan ma muryar ta na rawa ta gaishe su. Kamar bazasu amsa ba can daga baya farooq ya amsa mata. Mummy tace xauna kici abinci, imaan ta zauna daidai kujerar da mummy ta nuna mata wacce  take fuskantar omar. "Gurin yyi shiru kowa abinci yake aikawa cikin sa. "Imaan tayi nisa cikin tunani dan haka take zuciyar ta tabata shawarar tunda kowa hankalin sa nakan abinci bari ta dago da kanta dan tantance omar da farooq, dan idan suka hade rai bata gane waye omar, dan har muryar su iri daya CE. "A hankali ta dago kanta, daidai lkcn omar ya dago kansa dan ya gama cin abincin kenan, ai carab suka hada ido., atake omar ya watso mata kallo na cike da tsana. "Itama dukda ta tsorata hakan be hanata watsa masa hararaba. "Abinda ya bawa omar mamaki kenan, take ya boye mamakin ya sake hade gira. "Mikewa yyi zai bar wajen. "Mummy tace har ka gama? Yace eh mummy, "mummy tace da akwai zancen da nakeson maka. "Omar yace OK, sai mummy tace but jeka shirya sai kazo ka sameni, omar yace toh.
   "Kowa ya gama sannan aka bar wajen. "Imaan CE ta tashi ta shiga tattare plate din dake wajen. "Saida ta gama mummy tace dauko hijab dinki. "Imaan tace toh. "Nan ta koma daki ta dauko sannan ta dawo falo. "Shima omar shirin tafiya office yyi sannan ya tarad d mummy a falo. "Bayan ya zauna. "Mummy tace yauwa son, so nake ka wuce da imaan wannan skul din danyi mata interview sannan kayi duk abinda suka bukata. "Gaban imaan ne ya bada rass itafa Sam batason kasancewa kan wannan marar imanin.  "omar kam tsabar takaici kasa cewa komai yyi taya mummy zatace ya dauki wannnan dattin yasa a motar sa? "d Sauri yace am mummy inada emergency fah., mummy tace son kenan ai idan kanada emergency ranar koh breakfast bakayi ai, omar kamar zaiyi kuka yace toh mummy ga farooq nan sai ya kaita. Mummy ranta a bace tace idan bazakayi abinda nace ba ka fadamin basai kanamin kwana2 ba. "Omar ya sunkuyar da kansa zuciyar sa sai tafasa take shi tunda yarinyar nan tazo gidan nan mummy take masa fada kuma duk a dalilin ta abinda yafi komai tsana kenan ayi masa fada. "Dolen sa ya mike murya can ciki yace shikenan. Sannan ya kama hanyar fita.
  "Mummy ta kalli imaan tace tashi ki bisa, itama ba musu ta mike, dan ta lura Sam mummy bataso ayi mata gardama.
   "A mota ta samesa, "ya kifa kansa a sitiyari ransa na masa quna. "Imaan tayi kusan 5 sec kafin ta murda kofan baya da nufin shiga. "Omar najin alamun an bude ya dago kansa tare da watso mata wani mugun kallo. "A take imaan ta sunkuyar da kanta. "Wata irin tsuka yaja sannan yaja motar da qarfi Wanda yyi sanadiyar girgiza 'yanmatan hanjin imaan dan ta tsorata da lamarin sa a zuciyar ta tace kodai aljanu gareshi? Haka yake ta gudu kamar zai tashi sama. "Can kuma ya rage gudun daga baya kuma, ya tsaida motar. "Yana tsayawa yyi shiru bece komai ba. "Imaan ma shirun tayi tana kallon ikon Allah. "Can omar ya jiyo cikin tsawa yace jira kike na fitar dake ko me? "Imaan ta zaro ido yyinda take kokarin fita daga motar, a zuciyar tace toh taya zan San fita kkeso nayi bayan ni ba Allan musuru bace, "tana sauka Omar ya Watso mata wasu kudade masu yawa, batare daya yi mata bayanin komai ba ya fisgi motar sa ya barta a wajen. "Baki bude imaan ta saki ta bishi da kallo kamar wata wawiya tama rasa abin cewa dan takaici, a fili tace me kuma yake nufi da wannan kudaden???
Nuceey luv😘
[8/30, 10:26 PM] ‪+234 706 897 1326‬: ® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓


     51_55


 "Mamaki ne ya isheta, tayi kusan 10mins a tsaye ta Tara abin yi, "driving yake harya wuce sai ya ganta, hakan yasa yyi riverse, 'imaan na tsaye kamar soja sai ganin mota tayi ta tsaya gaban ta, da sauri ta matsa tare d kawar d kanta dan batasan ko waye ba. "Farooq yana daga ciki ya fito, imaan na dago kanta ta fahimci farooq ne kasancewar kayansu ya banbata bayan haka har motar su iri dayace. "Farooq ya matso kusa da ita sanna. Yace imaan me kike anan wajen? "Imaan kamar zatayi kuka, tace ya omar ne ya ajeni a nan kuma mummy tace ya kaini skul ayi duk abinda ya dace, "farooq y jijjiga kai yasan bro dinsa ba'a taboshi ba yana wulakanci bare kuma aka tabo shi. "Nan yace shiga mota muje. "Imaan tace toh. "Har zata shiga baya yace dawo gaba, haka tabi abinda yace. "Ga mamakin ta nan suka sake gangarawa inda omar y sauke ta, basuyi tafiyar 5mins suka isa makeken gate din Queen Amina secondary school, a sai yanzu ta fahimci dalilin kudin da ya omar ya bata wato taje tayi komai da kanta kenan?, yo ita idan mutum ya sani ba taya zaisan akwai skul ta wajen? "Ahaka suka karasa bayan sun shiga cikin skul din. "Nan farooq yyi mata komai yanda ya kamata har akayi mata interview yana wajen yana mamakin yanda imaan ke ja, komai aka tabo ta sani. For d first tym yaji tadan birgeshi Kadan dan yanason yaro me hazaka. "Bayan an gama PC skul din tace zuwa Monday ta fara zuwa skul. Farooq yyi mata godiya sannan suka fito. "Bayan sun fito imaan tace am ya farooq, farooq ya kalle ta batare d yace komai ba. "Kudin hannun ta d omar ya watsa mata take mika masa tace gashi, farooq ya yatsina fuska yace mezan dasu? Imaan tace kudin skul din kenan ai. "Farooq yace mtwss shige muje. "Imaan taja bakinta tayi shiru batare d tace komai ba, sannan suka bar makarantar. "Imaan na jiran ya maida ta gida sai gani tayi yabi wata hanyar, "imaan bata ida tunanin ta ba, taga ya shiga da ita hospital dinsu. "Har yyi parking imaan ta kalleshi zatayi magana farooq yasa yatsan sa a baki alamar tayi shiru, haka taja 'yan matan bakinta tayi shiru. Sanan ya fito, itama fitowar tayi, wata hanyar yabi dasu, dan haka itama ta fara binshi kamar jela, duk Wanda suka hadu saisun gaishe shi, ammn yi yake kamar besan d zaman su ba. "Ahaka su shiga can su fita can har suka kai office dinsa, imaan dai mamakin girma da lungu2 hospital din takeyi. "Bayan sun shiga ya nuna mata waje ta zauna. "Shikuma yasa rigar likitoci yafara gudanar d aikin sa. Imaan kam ta sunkuyar da kanta tana cike da kunya yanda mata ke fadar matsalolin su ga ya farooq, a yanda ta lura shi ko a kwalar rigar shi dan ko aikinsa yake batare d wata matsala ba. "Kusan azahar imaan na zaune harta fara gajiya, "ga yunwa data addabe ta, tana wannan zaman aka kawo mata abinci lkcn farooq ya fice dan yin salla. "Imaan tace waye ya turo ka? Yace oga. Sannan Wanda aka turo din ya fice. "Imaan kuwa yunwa takeji sosai dan haka ta fara aikawa cikinta abinci, har ta gama farooq be dawo ba, dan haka ta mike tayo alwala tayi salla. "A wajen yin addu'a ta bingire tana bacci. "Lkcn da farooq ya dawo tabe baki kurum yyi.
   "Mummy na gida taga har azahar ba imaan babu labarin ta, dan haka tahau kiran omar Amman taji wayar a kashe, hankali tashe ta kira farooq tace dubamin omar ko lpy ya kashe wayar sa? Farooq yyi murmushi yasan imaan zata tambaya dan haka yace eh dazu munyi salla dashi a masallaci, saidai yacemin akwai emergency a gaban sa, maybe dan hakan ya kashe wayar sa. "Mummy ta sauke ajiyar hrt, har zata tambayr shi imaan sai kuma ta fasa. Nan suka katse wayar.
    "Omar kuwa yana office hankali kwance yana gudanar da aikin sa, tun jiya wata number take damunsa, kuma duk layinsa dsme number ake kira, ana turo masa messages na kauna. Dalilin hakan yasa ya rufe gaba1 wayoyin sa dan bayason takura. 

   "Da yamma masu tafiya nayi, masu aikin dare na zuwa, omar ne ya fito a office bayan ya kammala abinda zaiyi, ya wuce inda motar sa take, anan ya shige yyi hanyar gida hankali kwance.
   "Farooq kuwa sai magrib sannan yace imaan ta taso su tafi dan sosai hankalin imaan ya tashi duk taji zaman hospital din ya dameta, "lkcn da suka bar hospital din wata hanyar taga yabi da ita, da sauri ta kalleshi, "wannan karon ma hannu yasa mata alamar tayi shiru. "Wayar shice tayi kara bayan ya kara a kunne yace hello, oh yeah gani nan hanyar zuwa club din, ohk bye. "Imaan hankali tashe ta zaro manyan idanun ta batasan lkcn da ta furta club????? Da karfi ba, Wanda taso tsorata farooq, tsaki yaja yace yes, imaan tace dan Allah ka maidani wajen mummy, farooq yace cinyeki akace za'ayi? Imaan tayi shiru, farooq yace so karna sakejin bakin ki.. A zuciyar sa kuwa yasan dalilin sa nakin maida imaan gida da wuri, take yyi saurin kashe wayoyin sa ma gaba1.
  "Omar kuwa bayan yyi parking a gida. Tsaye ya tarad d mummy a falo, yanayin sallama, mummy batare d ta amsa sa ba tace INA *imaan*??? darararammm take qirijin omar ya fara dukan Tara Tara danshi gaba1 ya manta da zancen wata imaan, shi sai yanxu ya tuna inda ya barta,a zuciyar sa yace so bata dawo gida ba kenan?, eh lalle yau mummy zatayi farfesun sa.... Bai ida zancen ba mummy ta katse shi da fadin bakaji me nace bane? 
Nuceey luv😘
[8/30, 10:27 PM] ‪+234 706 897 1326‬: [8/18, 7:35 PM] Nuceey luv😘: ® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓


      56_57"Murya na rawa yace am.. Daman.. Na turo ta gida bayan an gama komai na skul, "mummy ranta a bace tace abinda zakamin kenan omar? Ni nasan ko kamshin gsky babu a zancen nan naka, "omar y dafe kai, yace sorry mummy wlhy.. Common rufemin baki, abinda nakeso dakai shine duk inda kasan ka jefar min da yarinya kaje ka nemo min ita na baka 2hrs matukar baka dawo da imaan gidan nan ba sai ranka yyi matukar baci. "Omar yyi shiru ya juya zuciyar sa sai tafasa take, yanzu a duniya ba wacce ya tsana kamar imaan tunda har tayi sanadin da mummy take masa fada mwtsss yaja tsaki daidai lkcn daya bar gidan, yana fitowa kuwa rasa abun yi yyi, dole ya koma wajen daya ajiye imaan dazu. 
   "Farooq kuwa a mota yace imaan ta jirashi, sannan ya fice abinsa. "Yana wajen club har wajen 11:30 sai alkcn ya tuna da yabar imaan a mota, da saurin sa yabar wajen, sannan ya koma mota. Tana kwance har tayi kuka ta gode Allah bcci yyi awun gaba d ita. "Kiran sunan ta yyi, yaji bata amsa ba, dan haka ya dan buga hannun ta, a firgice ta tashi tana kallon sa sannan ta fashe da kuka tace dan Allah ka tausayamin ka kaini wajen mummy, farooq yace shiii, sannan ya furta kinason na maidaki wajen mummy? Imaan ta gyada kai, ohk toh idan mun koma kada kice na zo dake wajen club kinji abinda nace? Imaan ta girgiza kai alamar eh. "Farooq yace gud. Sannan yq tada motar sa suka bar wajen. "Sunyi tafiya me tsawo kafin suka iso unguwar tasu. "Farooq ya hango motar omar a kofar gida, hakan yasa shi yin murmushin mugunta, guddd ya furta a fili yasan wannan kadan daga cikin aikin mummy kenan, "omar kuwa yana mota ya kifa kansa tunanin duniya ya ishe shi, ya kira farooq yafi a kirga Amman shiru kkeji, dolen sa y tsaya zubawa sarautar Allah ido, ya kasa shiga gidan dan besan me zai cewa mummy ba gashi saura 5mins ya cika a lkcn data diba masa. Mwtsss yaja tsaki tare da furzar da wata iska me zafi. 
   "Lkcn da farooq ya shige gida, a tsaye suka tarad d mummy sai safa da marwa take, "mummy na ganin imaan tazo da sauri ta riketa tana tmbyr ta meya faru da ita? "Imaan ta kalli kofa daidai lkcn farooq shima ya shigo, mummy tace wai tare kuke? Farooq yace eh mummy, mummy tace garin yaya kukayi dare haka? "Farooq ya shafa kai sannan yace aiki ne ya rikeni mummy daga nan na biya ta wajen frnds dina can muka Dade, mummy tayi tsaki shirmen banza shirmen wofi wannan ai shashanci ne farooq, taya zaka dauketa maimakon ka dawo da ita gida sai ka wuce d ita gantalin ka? Faroiq Kansa a kasa yace sorry mummy, mummy taja tsaki tace wannan ya zama na karshe. Farooq yace toh sannan yabar wajen., shi badan komai yai hakan ba saidan omar yanda ranar yazo yana masa masifa akan deban jinin sa d yyi, shi yasa y rama ta wannan hanyar, da haka ya wuce dining table dan yunwa yakeji, mummy tace oya bishi kema kici abincin imaan tace toh.
  "Tym na cika omar ya shigo gidan duk jikinsa a sabule, saidai yyi mamakin ganin motar farooq shi Sam bai lura da zuwan su ba. "Sallama yyi mummy ta amsa masa bayan ta jefe shi da harara, karasowa yyi ya sunkuta gaban mummy yace wallahi mummy bada gangan ta 6ace a hannu na ba, saida na gama mata komai na skul sannan na sata a napep kasancewar an kirani emergency, "mummy tace wai imaan hakane? Take gaban omar ya bada rasss cike da tsoron kada imaan ta tona masa asiri na wulakancin d yyi mata, hade d mamakin ganin ta d yyi. "Imaan har zatace aa sai farooq yyi mata alamar tace eh dan ya fara tausayawa twins dinsa, "imaan tace duk abinda ya fada hakane, take omar ya saki ajiyar zucuyar d be shirya ba. "Mummy ta tabe baki tace next tym karka karayin haka, omar ya CE toh, sannan ya tashi, yunwa yakeji Amman ya gwammace ya wuce side dinsu, daidai zai wuce ya wurgowa imaan wata muguwar harara, imaan ta saki baki tana ganin ikon Allah, a zuciyar ta tace zakasan ka harareni wallahi. Nuceey luv😘
[8/18, 8:14 PM] Nuceey luv😘: ® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓ 


     58_59


"Bayan kwana biyu, yau ta kasance Saturday, babu aiki kenan, "burin imaan naya zata kuntatawa omar take dan yanzu ba laifi suna dan taba hira da ya farooq Amman ba sosai ba, "omar kuwa har abada bazata manta abinda yyi mata ba, "bangaren omar kuwa Sam Allah be hada jinin sa Dana imaan ba, ko kadan bayason ganin ta, shu hakanan yake daukar ta a kazama. "Imaan CE gaban dining tana jera abinci, mummy ta karaso wajen ta tace je ki kira yayunki muci abinci. "Imaan tace toh. "Side din su ta nufa. "Wajen farooq ta fara zuwa kasancewar ta taba zuwa sau daya, a daki ta sameshi yana kwance be tashi ba. "Daga bakin kofa tahau Kiran sunan shi, ya farooq Amman shiru, dan haka imaan ta hau kan gadon sannan taja kunnen sa kamar yanda yake Jan kunnen ta muddin ya tarar ta tana bcci, kamar a mafarki yaji an fisgi kunnen sa, ai da sauri ya mike yana karkade kunnen sa, imaan ta kyalkyalce da dariya, bayan ta sauka kan gadon. "Farooq yaja tsaki yace wallahi na kamaki saikin gayawa 'yan garinku imaan ta murguda masa baki tace ehdin, saukowa yyi zai kamata ta kwashe a guje tana fadin Nima mummy CE ta aikoni wai kazo muyi break. "Farooq ya girgiza kai kawai sannan ya shige toilet.
   "Sashen omar ta nufa anan ta tura kofar a hankali kamar wata munafuka, bayan tayi sallama taji shiru, har kusan sau uku ba'a amsa ba. "Har zata tafi wata zuciyar tace bude dakinsa mana, aikuwa hakan tayi. Bude dakin tayi Amman taga baya nan sai mamakin tsaftar dakin take tamkar na mace, haryafi na wata macen ma. "Jin alamun zubar ruwa hakan ya tabbatar mata a toilet yake, dan haka ta tabe baki a zuciyar ta tace idan yaso karma yaci abincin. "Haka ta juya abunta. "Daidai zata fita ta hango ayaba kan fridge da Alama anason sata ciki ne, imaan har zata wuce wani tunanin yazo mata. "Anan ta koma jikin fridge din, sannan ta balli kwaya daya, tass ta cinye, sannan ta dauko bawon ta dawo dakin omar, a hankali ta tura kofar, wata irin hamdala tayi ganin har yanxu be fito ba, dan haka ta la6a6a daidai bakin kofar ta jera bawon ayabar. "Tana gamawa ta fito a hankali tare d jawo kofar kamar yanda ta gani. "Sannan ta fice daga side din zuciyar ta fal cike d murmushi.  
   "Lkcn da ta koma bangaren mummy har farooq ya isa wajen. "Imaan tace laah harka fito? Farooq yyi banza da ita, sai alkcn ta tuna lefin da tayi, a take ta canja fuska itama tace kuma kuma ma ai Kaine ka faramin nima na rama... Bata karasa ba farooq yace kikace me? Imaan tayi shiru, ganin mummy tabar wajen tasan sarai zai iya murde mata baki, dan haka taja 'yan matan bakin ta tayi shiru... Gane hakan yasa farooq ya matso ya jawo kumatun ta yace maimaita abinda kikace? Imaan tsabar zafin rikon d yyi mata batasan lkcn data saki kukan shagwaba ba, mummy ta fito da sauri tana fadin lpy? Farooq yace rashin kunya tayi mummy, mummy tace mwtss Allah ya kyauta, sannan ta koma inda ta fito. "Farooq kuwa yyi murmushi yana me kallon imaan.
   "Toh 6angaren oga omar fah 🤔...Nuceey luv😘
[8/30, 10:29 PM] ‪+234 706 897 1326‬: [8/19, 6:00 PM] Nuceey luv😘: ® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓ 

       60_61


"Imaan ta 6ata rai sannan suka fara cin abinci. 
   "Omar yana wanka bayan ya gama ya fito, yana sa kafar sa a waje sai ji yyi suuuu ya zame, auchhh... Ya furta sosai ya bugu a qugu, rarrafa yyi bakin gado, cike da wuyar faduwar d yyi, duba wajen d ya zame yyi, ga mamakin sa sai yaga 6awon ayaba, sosai y shiga tunanin ta yanda akayi 6awon ayaba yazo har dakinsa. Shidai yasan ko cin ayaba baiyi ba, can ya shiga duniyar tunani, duk iya tunanin sa ya rasa ya akai 6awon ayaba yazo dakinsa, tunanin sa ya fara ga 'yan gidan duk Wanda ya tunano yasan bazai aikata ba, tunda yasan ko kusa farooq bazai sa masa ba toh aknme zai sa masa? Nan ya koma kan imaan, mwtss yaja tsaki har yaushe ya sakar mata fuska da zata shigo dakinsa? Harma tayi tunanin sa masa ayaba? Anan ya mike da kyar ya isa gaban mirror dake dakin sai kace mace sannan ya fara shiryawa har lkcn bai daina tunani ba ga azaba da qugun sa yake, shidai yasan ko mage basuda ita a gidan. Haka ya fito zuwa falon sa, mamaki ne ya isheshi ganin falon a bude ba kamar yanda ya barshi ba, tunanin sa ya tsaya cakk ko shakka babu lkcn da yake wanka yaji sallamar imaan, kenan itace tasa maka 6awon? Wata zuciyar ta tambaye shi a fili ya furta yesss yana me furzar da iska cike da 6acin rai tamkar yana magana d wani. Zuciyar sa CE ta fara zafi dan haka ya fice a falon ya isa side din mummy.
    "Imaan ya tarad a dining tana tattare plate harsun gama cin abinci, tana ganin sa tayi saurin sunkuyar d kanta alamun rashin gsky ya tattara a wajen ta. "Hakan ya tabbatar wa omar abunda yake zargi. "Imaan baki na rawa tunda ta kalleshi sau daya ta tabbatar wa kanta tarkon ta ya danu. Tace good morning ya omar, ya omar yace mrng. A takaice., sannan yace ki kawo min abinci na falona, imaan tayi saurin dago kanta ta zaro ido a xuciyar ta tace kaddai ya gane nice nasa masa? Oh ya rabbi help me 🙄., omar yana ganin yanda kamannun ta suka canja yyi murmushin gefen baki Wanda d alama na mugunta ne, a zuciyar sa yace ashedai karamar marar kunya CE ke., batare d yace mata komai ba ya juya wajen mummy dake kallo ya gaishe ta a tsaitsaye suka gaisa d farooq a tsaitsaye sannan ya koma side dinsu.
  "Imaan jiki ba kwari ta tattari abinda ya kamata ta jerasu cikin faranti sannan ta wuce side din omar. "A falo ta tarad shi yana kallon kwallo. "Tana shigowa omar ya mike ya sawa kofar key. Sannan ya dawo ya zauna duk abinda yake fuskar sa a tamke babu alamar wasa. "Imaan qirjinta ya bada damm, jiki na rawa tace gashi, bece mata kala ba, ganin haka ta mike da zummar tafiya, dagowa yyi ya watso mata wani kallo, take cikin imaan ya bada kulululuuuu ai batasan lkcn data zube a kasa ba. "Cikin dakilewar murya kamar bayason magana, yace ki zuba ruwan zafi a jug sannan kisa Lipton guda goma a ciki, imaan tace toh. "Bayan ta gama abinda yace, omar yace tashi kiyi kneel down. "Imaan ta zaro ido tace ya omar menayi kuma? "Omar yace tambaya ta kike? Tace eh menayi? Omar ya mike yace ohk bari kiga me kikayi, kunnen ta ya kama ya murda sosaiii har Sanda tayi kara Amman baiyi kokarin saki ba, imaan cikin kuka tace yi hakuri zanyi yanda kace, omar yyi murmushin mugunta sannan ya sake mata kanta. "Imaan tashi tayi sannan tayi kneeling, "bayan like 15mins suna zaman kurma, can omar yace dauko min wancan ruwan Lipton din, imaan ta mike da kyar dan kafafun ta sun fara tsami sannan ta dauko, omar yace toh shanye, "imaan a kidime tace yah omar kallifa babu sugar ga Lipton har goma ai yyi daci. "Omar ya sake hade rai batare d ya kalleta ba yace zakyi abinda nace ko saina tashi? "Imaan ta kafa bakinta kur6a daya tayi saurin cire kanta, tsabar daci ta kasa hadiyewa, tashi tayi da nufin zubar wa omar batare d ya kalleta ba yace zauna, imaan ta zauna, sannan yace hadiye abinda ke bakin ki. Imaan kamar tayi kuka ta runtse idon ta tafara hadiyewa, omar duk yana kallon ta ta gefen ido sai murmushin mugunta yake, "da kadan kadan saida yasa imaan ta shanye tasss cikin ta kamar zai fashe haka takeji. "Sai nishi take, omar yace tashi ki sakeyin kneeling, imaan na hawaye tayi abinda yace. Can yace ki daga hannun ki sama ki rufe idon ki, sannan ki bude bakin ki. Imaan tace dan Allah ya omar kayi hakuri. Omar yace hakuri? Ai bakiga komai ba tukun tunda ke Allah y yi ki muguwa, wannan duk mijin daya aureki ya auri azzaluma. Gaki karama dake Amman kinsan takan mugunta. "Imaan tace nidai dan Allah kayi hakuri bazan sake ba. "Omar yace kina bukatar wani ruwan Lipton din kenan. "Imaan ta jijjiga kai.  "Omar yace toh kiyi abinda nace banason bata lkci. "Imaan na kuka tayi abinda omar ya sata.
  "Omar tashi yyi daga inda yake zaune sannan shima ya 6allo ayaba daya ya cinye, sannan yasa a daidai bakin kofar fita. Dawowa yyi ya zauna abinsa ziciyar sa fari kall sa6anin da da yake a 6ace. "Saida imaan tayi kusan 20mins a haka sannan yace tashi. "Bayan ta tashi d kyar yace fice kiban waje. Dadi ya cika imaan ganin ya barta zata tafi harda cewa thank you. "Omar ya girgiza kai yana me cike da murmushin mugunta. "Imaan kuwa garin sauri taje bakin kofa kenan sai jinta tayi suuuuuuu.....
Nuceey luv😘
[8/19, 6:48 PM] Nuceey luv😘: ® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓ 

       62_63


"Ta fadi a wajen, innalillahi wa'inna ilahin raji'un abinda imaan tace kenan hade da zubar da hawaye tsabar azaba ma ta kasa ihu. "Omar kuwa duk yana jinta Amman ko kallon ta baiyi ba, imaan kam sai kuka take a zuciyar ta kuwa ta jawa omar Allah ya isa yafi a qirga. "Wayar omar ce ta fara ringing ganin mummy kan screen din yasa ya daga da Sauri, mummy daga dayan 6angaren tace ka turo min imaan yanxun nan. Tana fadar haka ta kashe wayar, "omar yyi saurin kallon imaan yaga ko alamar tashi batayi dan ta bugu sosai, "cikin tsawa yace tashi ki fice mummy na Neman ki. Imaan hawaye nabin kumatun ta Amman ta kasa tashi. "Dole tasa Omar ya tashi daga inda yake , sannan ya dauki imaan tamkar jaririya sai mamakin rashin nauyinta yake, yanayin step daya, wani 6awon ayaban ya jawo take suka zube a wajen saiga imaan kan qirjin omar, shikuma buguwa yyi daidai inda ya fadi dazu tsabar azabar ciwo baisan lkcn daya sake matse imaan a qirjin sa ba. "Kusan 5sec yyi ta maza sannan ya daddafa jikin bango ya sake tallafo imaan, sannan ya zagaya gefe ya bude kofar falon. "Imaan dai na ganin ikon Allah saidai itama qugunta ciwo yake ga kafafun ta dake tsami bayan haka ai d tayi dariya, a zuciyar ta tace ashema rago ne ya omar dinnan Amman daya hada rai saikace namijin zaki.
   "Yana rungume da ita ya isa side din mummy da kyar. "Mummy ta tashi da sauri tace omar lpy? Meya samu imaan din? Kuma tun dazu meta tsayayi bata dawo ba? "Omar yace wlhy mummy kallo muke ayaba Dana kai side dina jiya taci, toh ta manta ta barshi a kasa, lkcn d kikace tazo tym din data tashi sai tsautsayi yasa ta taka ta zame. "Imaan na kwance qirjin yah omar har yanxu tayi lamo tana sauraron qaryar da yake xurarawa, a zuciyar ta tace ya omar badai qarya ba wallahi. "Mummy tace oh kwantar ta anan, sannu kinji ai daman tsifa nakeson miki kinga kanki ya tsufa. Imaan dai shiru tayi. Mummy tadan ta6a kafar ai take ta callara kara mummy tace ya salam bari na dafa ruwan zafi kada wajen ya kumbura. "Sannan tabar wajen. "Tana Barin wajen imaan ta kalli omar tace mutum har mutum Amman zalunci da karya ya cika masa zuciya tayi mgnr kasa2, omar ya daure fuska yazo da nufin murde mata kunne tuni ta saki kara tace mummmmyyyy....
  "Mummy ta fito a guje daga kitchen ai da sauri omar yadan matsa. "Mummy tace meya faru? Imaan ta kalli omar a fakaice ta watsa masa harara, sannan tace fitsari nakeji mummy, mummy tace toh bari omar ya kaiku bakin toilet. "Kai maza dauke ta, ta fada tana kallon omar. Omar baice komai ba sai yin abinda mummy tace, yana kissima abinda zai mata da zarar ya kaita dakin mummy, da sauri kuwa imaan tace kaini bakin toilet din falo. Yyi kamar baiji ta ba, dan haka tace mummy a kaini na falo. "Mummy tace kaita na falo son. Omar yace toh mummy, sannan ya kaita. "Dakyar ta dingisa ta kama kofar toilet din, sannan ta kalli omar daya hade rai tace look omar ya dago kansa, sannan tayi masa gwaloo tahowa yyi d nufin kamata dan mummy ta koma kitchen, imaan tayi saurin rufe toilet tana dariyar mugunta. Koba komai tadan rama kadan.
  "Koda ta fito shiya maida ta kujera kamar yanda mummy tace, sannan yabar wajen cike dajin haushin daukar  imaan d yyi. "Mummy kuwa tsumma ta samu mekyau tahau daddan na mata. "Ihu imaan tahau yi, a haka farooq yyi sallama bayan ya shigo, yake tamabayr abinda ya faru, mummy ta sanar masa yanda omar yace mata. Sosai ya tausayawa imaan sannan ya karbi tsumman yace mummy kawo na  tayaki, mummy tace toh. 
 Kar6a yyi yahau yi mata a hankali, imaan tun tana ihu har ta daina, qarshe ma bacci yyi awun gaba da ita.
Nuceey luv😘
[8/30, 10:29 PM] ‪+234 706 897 1326‬: [8/20, 1:54 PM] Nuceey luv😘: ® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓


       64_65


"Omar yana komawa side dinsa ya fara tunanin abinda suka faru shida imaan, tsaki yyi a fili yace komeyasa na dauke ta ma? Mtwss haka yyi tayi abunda.
   "Bayan kwana biyu yau ta kasance monday, sosai tayi kyau cikin uniform dinta, a gurguje taci abinci, mummy tace farooq tashi maza ka kaita. "Farooq yace toh. "A mota sai hira suke abinsu, har ya kaita skul, kafin ta fita farooq yace kiyi kr2 d kyau kinji koh. Imaan ta gyada kai, murmushi yyi mata sannan ya daga mata hannu, har ta shige cikin class sannan ya tada mota yabar wajen. "Koda aka tashi farooq yana office Amman hankalin sa nakan agogo dan mummy tace ya dauko ta, hakan kuwa akayi tun karfe daya tayi masa a skul din. "Imaan ya tarad bakin gate, fitowa yyi a mota, imaan na ganin sa ta taho da gudu tayi hugging dinsa. "Farooq ya shafa kanta yace imaan ya skul? Imaan tadan ta6e baki tace lpy. "Farooq yace toh muje gida nasan mummy nacan na jiranki, imaan tayi murmushi sannan ta shige gaba. Shima zagayawa yyi ya kunna motar suka bar wajen. "Kullum farooq shike kaita ya dauko ta hakan yyi wa omar dadi dan tun Monday ya kirkiri cewar yanada emergency, dan kar mummy tace shi zai kai imaan skul. Yanxu kuwa ya lura mummy ko kadan batayi masa zancen imaan saima maida farooq d tayi driver'n karfi d yaji. 
  "Yau data kasance weekend ne, duk suna gida, yanxu haka suna falo har daddy hira suke sosai hankalin su kwance, daddy yyi gyaran murya hakan ya tabbatar musu da yanada magana kenan dan haka sukayi shiru suna sauraron sa. "Daddy ya kira sunan omar d farooq gaba1 suka amsa a tare, "daddy yace na lura Ku Sam babu zancem aure a gaban Ku, nayi muku magana kunyi biris d ita koh? Dukkansu suka sunkuyar d Kansu kasa, "daddy yace idan bazaku fitar d mata ba ni zan kawo muku matan aure, omar yyi saurin kallon dadday da kyar ya iya furta No daddy pls, daddy yace toh zaman me kuke da vazakuyi aure ba? Kalle Ku fah dukkan Ku zaku kai 29, da zarar kunje 30 kun fara tsufa. Shekarun ka yana jaa, "Omar kansa a kasa yace kayi hakuri daddy zamu kawo maka mata, Amman a bamu nan d wani lkci. "Daddy yace kamar yaushe kenan? Karfa Ku jaju6omin 'Yar talaka, sai alkcn mummy tayi saurin dago kanta ko kadan batason Kalmar da daddy yake furtawa yaransu, imaan dake wajen kuwa sunkuyar d kanta qasa ta sakeyi tana me jinjina lamari irin na daddy. "Daddy kuwa sarai yasan mummy batason Kalmar Amman y kauda kansa kawai yana meci gaba da mgn. "Sai alkcn farooq yace daddy duk yanda kace ai hakan zamuyi insha Allah. "Daddy ya gyada kai yace wannan shine karo na farko, karku bari na sake magana ta qarshe dan saidai Kuji an daura muku aure da wasu. "Gaba1 suka gyada kai.
  "Da yamma imaan taci kwalliya ta kalli mummy dake kan gado tace na shirya mummy, mummy tace toh jeki ki kiramin Omar, imaan tace toh. "Side dinsa ta nufa. Tayi sallama saidai taji shiru, shiga tayi taga baya falo, dan haka ta karasa dakinsa. "Kwance ta ganshi yyi shiru d alama y tafi duniyar tunani dan haka ta buga kafansa da sauri ya mike yana Binta d kallo, duk Wanda ya kallesa yasan ransa a bace yake, tasowa yyi imaan ta matsa da sauri, matsowa ya sakeyi ta sake matsawa ganin yanda yake binga da kallo dukta tsorata da shi. "Omar kuwa bai bar matsawa gareta ba har saida ya hadata da jikin bango har numfashin su na haduwa.Nuceey luv😘
[8/20, 3:24 PM] Nuceey luv😘: ® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓ 


       66_67


"Qarshe imaan rufe idon ta tayi tana sauraron abunda zai biyo baya. "Omar kuwa kunnen ta ya kama auchhh ta furta, da daya hannun y buge mata baki, sannan yace uban waye ya baki izinin shigomin room? Imaan tayi raurau bayan ta bude idon ta dan azaba, tace Mummy CE ta aikoni, omar yace shine ke baki iya sallama ba? Imaan tace Allah nayi kusan 3tyms. "Omar ya jijjiga kai bayan ya sake mata kunne yace daga yau idan bakiji na amsa ba ki koma kice bcci nake, imaan ta zaro ido waje tace ya omar qarya ba kyau...bata qarasa ba ta kama kumatun ta yace nine me karyar? Imaan ta jijjiga kai. Omar yace toh kiyi abinda nace, imaan tace toh duk hawaye ya cika mata ido. "Omar yace matukar naga hawayen nan sun sauka kasa sainayi maganin ki. "Imaan tayi shiru tana maida hawayen ta. "Omar yace toh ficemin a daki, ai be karasa mgnr ba ta bara dakin da sauri har tana tuntube, "tana fita daidai lkcn farooq ya fito a nasa side dan haka ta kece da kuka. "D sauri farooq ya qaraso wajen ta yana tmbr ta meya faru? "Imaan cikin kuka tace yah omar ne ya mintsine ni ya kuma mareni, "farooq ya dauko hanki a aljihun sa sannan ya fara goge mata hawayen yace sorry zan rama miki rabu d shi, oya muje wajen mummy, "suna zuwa shima omar ya shigo dakin. Mummy ta kalli omar tace maza kaita kayi mata shopping, omar ya kalli imaan, sannan y kalli mummy yace akwai abunda nakeyi a daki fah mummy tunda ga farooq sai ya kaita... Mummy ta katse shi d fadin ka sanni sarai banason musu ai naga farooq din ko ka fini ido ne? Omar ya sunkuyar da Kansa sannan yace shikenan mummy, "juyawa yyi d nufin ficewa, imaan kuwa taso ace farooq ne ya kaita dan tafi sakewa d shi. Mummy tace tashi ki bisa ki dauki duk abinda kike buqata imaan tace toh mummy, farooq ta d'agawa hannu, shima y daga mata yana murmushi dan shima yaso ace shi ya kaita., saidai y lura ran mummy yadan 6aci gwara yaja bakinsa yyi shiru.
   "A mota ta tarad d shi, har zata bude kofar baya omar ya daka mata tsawa yace ni driver dinki ne da zaki shige baya? Imaan tayi saurin rufe kofar, sannan ta bude ta gaba, ko daidaita zama batayi ba ya fisgi motar a guje, imaan dai cikin sai kadawa yake tsabar tsoro. "A wani katafaren store sukayi parking, bayan yyi omar yace jeki na baki 10mins kiyi sauri. "Imaan ta kalleshi d sauri tace toh kaxo mu tafi mana. "Omar ya watso mata wani mugun kallo, ai batasan lkcn data fice a motar ba. "Shiga tayi sannan ta fara daukar kayan kwalliya a gurguje d turaruka, saida tayi kusan 15mins a ciki sannan ta fito, kasancewar omar ya shigo ya bada ATM dinsa akan duk abinda ta dauka, a ciri kudin. "Lkcn da imaan ta kusan zuwa jikin motar, mamaki ne yasa ta tsaya cakkk, wata siririyar mata ta gani tare d ya omar, suna gaisawa sai murmushi yake mata abunda bata taba gani ba kenan. "Dan a zaton ta baya kula kowacce mace. "Ta dayan 6angaren tabi ta sanya kayan ciki sannan ta shige mota zaman jiran sa. "Omar kuwa sai alkcn ya lura d zuwan imaan, lekowa yyi yace ke fito, imaan tace na gama ai. Omar yace ki fito nace, imaan ta fito sannan ta zagayo inda yake, wannan matar tace woow omar wannnan sister dinka CE? "Omar yace yes, da murmushi a fuskar ta tace no wonder naga kuna kama kaii ta fika kyauma ta karasa mgnr tana dariya. "Omar kuwa dariyar da yake dazu ta tsaya tsakk ji yyi tamkar ta watsa masa garwashin wuta, kai a duniya ma ba'a ta6a ya6a masa mgn ba irin ta yau taya zata hadashi d imaan? Sannan harda qarin ta fishi kyau??? Kai Amman ta cuceshi wallahi. "Imaan kuwa dadi taji har cikin ranta taji ance ta fishi kyau, take ta dago ido ai tsarab suka hada ido dashi dan haka tayi masa gwalo sanna ta sunkuyar d kanta kasa, ran omar ne ya sake 6aci wannan Matar ta katse shi d fadin yadai Omar? Naji kayi shiru. "Omar yyi murmushin yake yace am.. Muna sauri ne Meenat.sai mun hadu next time. Meenat tace oh sorry, buh kadan bani number ka, so dat mu dinga gaisawa. "Omar yace ohk a gurguje ya bata sannan ya tisa keyar imaan suka bar wajen. "Meenat course mate dinsa ce.a inda sukayi makaranta a america.
   "Koda suka shiga mota ba me cewa kowa ci kanka. "Saida suka isa gida, bayan yyi parking, sannan ya riko kunnen imaan, imaan ta kalleshi a tsorace, omar yace uban wa kikema gwalo dazu? "Imaan tayi shiru. "Omar yace karkiyi zaton abinda tace gsky ne, dan babu inda kika baro a kamannin gwaggwon biri, imaan ta zaro ido. "Omar ya gyada kai yace yes kamar ki sakkk data gwaggwon Biri. 
 "Imaan ta ture hannun ta sannan ta bude kofar da Sauri ta fita tana goge hawaye, a daidai bakin kofa sukaci karo da farooq, farooq yace mekuma ya faru? Imaan ta bare baki ta fara kuka dan takaici ta kasa cewa komai. "A haka ya jata falo. "Mummy ta kalleta d sauri tana tmbyr ta abinda ya faru, imaan kuwa ta sake barke baki, mummy tace yimin mgn mana, imaan cikin muryar kuka ta sanarwa mummy abinda omar yace mata. "Atake mummy tahau salati sai alkcn omar shima ya shigo. "Mummy tace wai omar yaushe ka baci da shirme ne? 
Nuceey luv😘
[8/30, 10:30 PM] ‪+234 706 897 1326‬: [8/21, 3:38 PM] Nuceey luv😘: ® *OMAR* *KO* *FAROOQ*  ❓

      68_69

 "Omar yace sorry mummy, mummy tayi kwafa sannan ta lallashi imaan.
  "Yau d ta kasance Monday bayan imaan ta shirya, mummy tace jeki kiramin omar. "Imaan ta zaro ido tace mummy shi zai kaini? Mummy ta gyada kai. "Imaan idonta yyi raurau batare d tace komai ba sannan ta tafi kiran omar. "Omar yana daki ko tashi a bcci beyi ba kasancewar sai 9 zai fita, duk ta sakankance yanata bcci, "imaan tayi sallama kusan 3tyms bataji an amsa ba. "A hankali ta tura kofar dakin ta hango shi ya lullu6e cikin blanket yanata kwasar bcci hankali kwance, har zata shiga ta tuna d warning din d yyi mata jiya, dan haka ta ja baya, sannan ta fice a dakin. "Wajen mummy taje ta sanar mata yana bcci, mummy tace toh ki taso sa mana, imaan tace mummy yace idan yana bcci karna tashe shi, mummy taja tsaki tace zakije ko saikin makara bakije skul b? Imaan ta juya da sauri dan ta tuna idan biology teacher dinsu ya shiga baya bari a Shiga, gashi shine me first period ko kusa batason tayi missing, d wannan tunanin ta koma side din omar, yanda ta barshi dazu haka ta sameshi. "Shiru tayi ta rasa abin yi, take abinda yyi mata jiya ya dawo mata, a fili ta furta wai nice me kama da gorilla ta nuna kanta., lkci guda ranta ya soma 6aci tunanin yanda zata rama takeyi,  tunanin ta ne ya tsaya kan fridge, d sauri ta isa wajen ta budeshi sannan ta dauko ruwa a faro, sannnan ta dawo dakinsa. "Bakin gadon sa ta nufa kallon sa ta tsaya yi yanda yake baccin sa bilhakki da gsky, murmushin mugunta tayi sannan, ta bude gorar, tultultultullll ta kware ruwan jikin omar bayan ta yye blanket din. "A razane ya tashi daga daddadan bccin d yakeyi cike da firgice yake kallon jikin sa ranshi ne yyi matukar baci lkcn da ya hango imaan na shirin fita a dakin, cikin zafin nama ya tashi ya damko ta. "Imaan tanaji an damko ta tafara zirarar hawaye tasan yau babu me kwatar ta sai Allah. "Omar kuwa tsabar takaici ya rasa ma abinda zaiyi, karshe tashi yyi ya koma falo da imaan, ya rasa meyasa imaan ta raina sa haka, wannan wacce irin wawiyar yarinaya CE? Ya tmbyi zuciyar sa. "Bai zarce da imaan ko INA ba sai gaban fridge din, sannan ya kwaye hijab din jikinta, kokarin cire rigar ta yake, sai alkcn bakin imaan ya budi cike da tsoto tace yah omar dan Allah kayi hakuri, wani wawan mari ya sakar mata dan a ganin sa idan tana bashi hakuri wani rainin take masa, ai take bakinta ya fashe,  
   "Imaan ta kece da kuka, omar kuwa yaci gaba d kwaye rigar jikin ta, saida ya cire rigar nan duk kokarin imaan na karya cire Amman kasawa tayi karshe ma murde mata hannu yyi, ya barta daga ita sai bra da vest da skirt na makaranta, "ruwa me matukar sanyi ya dauko a fridge, take y soma tsiyaye shi jikin imaan. "Tsabar sanyi imaan batasan lkcn data riko omar ba sosai tayi hugging dinsa wani irin shock Omar yaji kamar yanda yaji ranar da suka fadi sanadin 6awon ayaba. "Omar yyi kokarin cireta daga qirjin shi, Amman imaan taki saima kara kankame shi da tayi, cikin muryar kuka tace dan Allah ya omar kayi hakuri wlhy bazan sake ba. "Omar cikin tsawa yace kisake mana, imaan tace aa, omar ya turata d iya qarfin sa yace duk lkcn da kika sake samin qazamin jikin ki a nawa saina 6allaki. Wai ma kin manta warning dina na jiya koh?Nuceey luv😘
[8/21, 4:17 PM] Nuceey luv😘: ® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓ 


      70_71


"Imaan tayi shiru, omar yace so saina yanke wannan kazamin kunnen naki sannan zaki daina abinda kike, imaan tace nima mummy CE ta aiko ni, omar yyi kwafa sannan ya cillo mata rigar ta, oya saka ki barmin falo. Da sauri imaan ta karba ta sanyi hijab sai rawar sanyi take, "tana zuwa falo shima be dade ba ya shigo, mummy tace ya kaita skul. Ba ason ransa ba ya kaita. Koda suka shiga mota ba me cewa kowa komai. "Sanda suka je bakin skul din sannan ya ajiyeta ba kamar farooq ba d saiya kaita har ciki. "Juyawa yyi ya tafi abinsa batre d yace komai ba. "Ko da rana ma, umarnin mummy ya dawo dashi skul din, saidai shi office ya wuce da ita. 'Lkcn da suka shiga hospital din kowa kallon su yake, dan sunsan waye omar Sam baya shiga sabgar mutane. "Daidai inda umman imaan ta rasu sukabi ta wajen, take mutuwar mamanta ta dawo mata sabuwa fal. "Take imaan ta hade girar sama data kasa wani irin tsanar omr ta dawo mata sabuwa falll, har suka shiga office din omar be lura d yanayin ta ba. "Waje y nuna mata ta zauna. "Sai alkcn y kalleta yaga ta hade rai, tabe baki yyi yasan be wuce dan ya yaki maida ta gida bane. A ransa kuwa yace kyayi kya gama. "Haka yaci gaba da lura d marasa lpy, "fuskar imaan kuwa a murtuke kamar an aiko mata d sakon mutuwa, "karshe ma fashewa d kuka tayi, omar yanajin haka y waigo yana me kallon ta d mamaki. "Saidai kuma ya tabe baki kawai bece mata komai ba. "Aikawa yyi a kawo mata abinci, a zaton shi ko yunwa ta fara ji. "Koda aka kawo mata abincin ma ko kallon sa batayi ba. "Saima kara tsanar shi da takeji a xuciyar ta, "omar cikin tsawa yace malama kina cikamin kunne, idan kuka zakimin ki ficemin a office, imaan najin haka ta tashi, tayi hanyar fita. "Omar ya kalleta da mamaki saidai bece uffab ba dan yasan ba inda ta sani a hospital din.
   "Imaan kuwa tana fita 6angaren farooq ta nufa. "Tana bude kofar ta fada kanshi d sauri tana kuka, farooq dake zaune hankali tashe yake kallon ta yace lpy imaan waya kawoki nan?  Mwtssss akayi tsaki a gefen su, wata budurwa dake zaune a wajen tayi, imaan tayi saurin dagowa tana kallon ta, farooq ma kallonta yake da mamaki, katse shirun tayi da fadin, ashedai mgnr mutane gsky ce, yau na gani da idanuna haba farooq akan wannan yarinyar dama tuntuni kakemin wulakanci? No wonder idan na kiraraka baka dagawa sai kayi niyya, mutane dayawa sun sanar dani har office kana zuwa d ita shiyasa naxo yau domin na tabbatar wa kaina. Kasani duk son d nake maka bazan iya hada kishiya da 'yar ficiciyar yarinyar nan ba... Tana kaiwa nan ta fici cike d kunan rai. "Imaan ta kalli farooq taga ransa a bace, a sanyaye tace ya farooq wannan din wacece? Farooq kuwa ransa ne yake ta tafasa ya rasa wacce irin kasa muke ciki ta Nigeria fisabilillahi dan yana xuwa d imaan office dinsa shine suke soyayya? Mwtss yaja tsaki, "imaan ta sauka kan tainyar sa tana shirin fita, farooq ya riqo hannun ta yace, INA zaki? Imaan kanta a kasa tace naga kaman ranka a bace ne shiyasa zan tafi, farooq ya kwakwulo murmushi yace no ai bakece kika 6atamin ba. "Imaan tace toh yah farooq wannan din wacece? Farooq yace suhailat, imaan ta zaro ido tace wacce kuke waya? Farooq ya gyada kai. "Imaan tace Amman ji fah yanda take ta fada harda nunani d yatsa. "Farooq yace shareta. "Imaan tayi shiru can tace toh ya farooq d gske ta fasa auren ka? Farooq yace eh, Amman ai kinsan bazan rasa wasu ba. "Imaan tace ehmana, toh yanzu wa zaka aura? Farooq yace ikon god yarinyar nan ko 'Yar jarida zaki zama? Imaan tayi murmushi tace aa  yace toh tambayoyin ya isa haka. "Imaan tace toh bari nayi maka ta qarshe, farooq yace inajin ki, "imaan tace toh tunda suhailat ta fasa aurenka ai ni saika aureni mu cusa mata takaici koh.? Nuceey luv😘
[8/30, 10:30 PM] ‪+234 706 897 1326‬: ® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓


         72_73


"Farooq ya zaro ido waje cike da mamaki yace, imaan shekarun ki nawa? Imaan tace 16yrs, farooq ya girgiza kai yace kina wannan shekarun harkin fara tunanin aure? Imaan tace naga dai zamu cusawa suhailat haushi ne kaga idan ta qika akwai me sonka. "Farooq yyi murmushi yace na gode Amman nikam baxan aureki ba. "Imaan ta zaro ido tace bakaso na nima kenan. "Farooq yace ah Nina isa? Inason ki mana imaan, "am tukunnan ma meya kawoki nan kina kuka? ( yyi tmbyr dan kawar d wancan zancen.) "Imaan ta tabe baki ta Shiga sanar masa abinda ya faru. "Farooq ya girgiza kai yana mamakin rashin jituwa irinta imaan d dan uwansa ya rasa me imaan ta tarewa omar, "can yace kinci abinci? Imaan tace aa, fatooq yace ohk. Anan yasa aka kawo mata abinci tanaci suna hira abinsu.

    "Omar kuwa jin shiru bata dawo ba sai ya fito waje dan dubata. Iya duban sa ya rasa inda imaan ta shige kwatakwata besan imaan tasan wajen zaman farooq ba shiyasa be kawo zataje wajen ba, sosai hankalin sa y tashi lkcn daya tuno fadan dazai fuskanta wajen mummy matukar be samu imaan ba, haka yyi ta zagaye yana duban ta Amman be sameta ba, "har lkcn tashi yyi baiga imaan ba. Jiki sa6ule ya koma gida yana tunanin abinda zai tarad. "Farooq kuwa lkcn tashi nayi ya kama hannun imaan suka dawo gida. Koda mummy ta tmbyesu yace mata shi ya dauko ta sakamakon aiki d  yyiwa omar yawa be samu tym ba. "Omar kuwa yana bakin gate ya kasa shigowa gidan, can d tsayiwar ta ishesa yyi ta maza ya shiga gidan. "Yana shiga ya tarad da mummy a falo, d murmushi ta amsa sallamar sa, omar dai mamaki ne ya isheshi kodai imaan din ta dawo d kanta ne? Ya tmbyi kansa, ai koda ta dawo ma saita hadashi d mummy, hakadai yyi ta tunani har mummy ta katse shi da fadin lpyr ka kuwa yau? Omar yyi murmushin yake, yanason tmbyr ta imaan Amman yana tsoron yanda tmbyr zataje ta dawo dan haka yaja bakinsa yyi shiru. "Na gaji ne, ya bawa mummy amsa. Mummy tace eyya jeka huta mana. Ai kamar jira yake ya mike d sauri yabar wajen. A hanyar sa ta komawa side dinsa can ya hango farooq d  imaan sai buga kwallo suke suna dariya mamaki ne kurum ya isheshi na yadda imaan ta dawo gida.

 "Farooq ya dauki ball da niyyar cirata sama, imaan tace Allah ya farooq nice d bugawa, farooq yahau dariya, aiko ba zato ba tsammani yaji tayi tsalle ta makale a qirjinshi tana kokarin kwace ball.... Ai baisan lkcn data fadi kasa ba, omar kuwa yana kallon su ya tabe baki da qarfi ya furta girma dai ya fadi. Sai alkcn suka lura dashi, farooq yyi murmushi, imaan kuwa harara ta wurga masa. "Omar ya zaro ido yace ni kike harara? Imaan ta murguda baki, tahowa yyi d niyyar dukanta, d karfi tace Allah ka tabani saina fadawa mummy yauma yaddani kayi, omar ya tsaya cakk dan bayason fadan mummy, dan haka yyi kwafa ya nufi 6angaren sa. "Su kuwa sukaci gaba da wasan su.
  "Farooq ne kwance kan gadon sa sai juyi yake tunanin sa cak ya tsaya kan imaan, tun mgnr da tayi masa a office yake ta juyasa, a zuciyar shi yace na amince da zancen imaan ko na barshi?Nuceey luv😘
[8/31, 10:33 AM] ‪+234 706 897 1326‬: [8/27, 12:50 PM] Nuceey luv😘: ® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓         82_83 Zanyi amfani da wannan dama wajen bawa masoyana hakuri bisa jina da kukayi kwana biyu banyi posting ba, ba komai yaja ba sai lectures da mukeyi sosai ga exam da muke shirin yi, abin dai sai du'a'i, Amman dai insha Allahu yanxu komai normal. Ku kasance tare da mai kaunarku a koda yaushe _*Nuceey*_ _*luv*_.

  **************


"A rikice yace nima shi nake nema mummy, mummy tayi kwafa sannan ta juya batare da tace masa komai ba.shima farooq sake ficewa yyi a gidan dan Neman inda Omar ya shiga.

  ***
Tunda ya fito a taron yake ta falfala Gudu kamar zai tashi sama idon nan nasa sun qanqance sakamakon 6acin rai da yake ciki zuciyar nan kuwa sai tafasa take tamkar ruwan da aka Dora kan gas. "Ikon Allah ne kawai ya kawo omar gidan shi, Wanda daddy ya Gina masa idan yyi aure saiya tare aciki, dake gidan babu gateman dolen sa ya sauko a motar, sannan ya bude gate, unguwar shiru kamar ba mutane saidai daka ga ginin gidajen wajen zaka tabbatar wa kanka ba qananan mutane ne suke rayuwa aciki ba. "Bayan yyi parking motar sa sai ya wuce falon sa direct, abunda yyi matukar bashi mamaki shine bai wuce ganin yanda aka gyara main falon ba, dake gidan me hawa biyu ne, yanda aka sa colours din komai red& ash shiya tabbatar masa da lalle wannan auren fa dgske ake masa, saidai ba laifi ya yaba da tsarin colours din, qarshe kuma ya ta6e baki ya haura sama da sauri, dakin shi ya wuce batare dya duba dayan dakin dake wajen ba, "yana shiga ya cire duk kayan jikin sa sannan ya fada toilet ya sakar ma kansa ruwan sanyi, kusan 15mins ya dauka sannan ya fito, kamar dai tsarin dakinsa na gida, saidai wannan yafi kyau sosai, ran nan nasa saikace ana qara masa fetir a ciki sai tafasa yake, farin idon nan ya koma red, "duk yanda yyi ya mance sunan yarinyar da aka daura masa aure abin ya faskara,tunawa da sunan ta kuwa shike qara tunzura 6acin ransa, a fili yace kai anya daddy yasan waya aura masa? _Fateema_ fah? Mtwss gaskya an gama dashi wallahi, an cuceni toh ma me zaiyi da wannan tatsitsiyar yarinyar? Dayaga dai tunanin sa zai sake birkitashi yasa ya mike kan gado rai a 6ace da wannan tunanin bacci yyi gaba dashi.


  "Farooq duk inda yasan omar zai shiga yaje Amman babu labari, kwata2 be kawo gidan omar a ransa ba. "Haka ya koma gida, mummy kam ranta yyi mugun 6aci bata ta6a zaton omar zai watsa mata qasa a ido ba gaban dubban jama'a, Amman koda ta shiga cikin mutane sai tayi kokarin 6oye fushin ta.
  "Koda farooq ya dawo, mummy yaja gefe zuwa side dinsa sannan ya sanar mata shifa began omar ba, cikin 6acin rai mummy tace toh shi yaro ne? Yaje duk inda zaije karka qara Neman sa, tana kaiwa nan ta tashi da nufin tafiya, farooq yyi qasa da murya sannan ya shiga lallashin mummy dan ya lura tana cike da 6acin rai sosai, "dakyar ya iya calming nata, sannan tabar side dinsa, a zuciyar ta tace dadin yara dayawa kenan idan wani ya bakantaa maka sai wani ya faranta maka. "Haka biki ya watse batare da omar ba, 'yan gulma sunyi abunsu har sun gama, amarya ameera ta tare gidan angon ta farooq, "koda akace za'a dau amaryar omar, mummy hanawa tayi tace a kyaleta a wajen ta. "Amarya _Imaan_ kuwa hankalin ta kwance batasan wainar da ake toyawa ba, dukda basa shiri da omar Amman kwana biyun da bata ganshi ba ta danyi kewar sa, farooq ta tmby, farooq yace yyi wata 'Yar tafiya ne, imaan ta tabe baki tace shine ko salllama babu, farooq ya kalleta da mamaki tunda yasan bata shiri da omar ai ba yanda za'ayi ta damu, kasa shiru yyi yace a'a kodai kin fara son bro dina? Ya fada yana murmushi, imaan tace cabdin Allah ya sauwake me zanyi da tsoho, farooq ya zaro ido yace Ashe nima kallon tshoho kikemin, imaan tayi dariya, tace lah ya farooq Allah banda kai, farooq yace toh yanzu akace ki auri omar zaki auresa? Imaan ta zaro ido tace dan Allah ya farooq ka rufamin asiri ko maza sun qare bazan auresa ba. "A razane yace what? Imaan tace umhu ai kaima kasan Kaine mijina, farooq ya girgiza kai yana tunanin hadin gambizar da su mummy sukayi, *OMAR* bayaso *FATEEMA* Tace tsoho, _daddy_ da _mummy_ kuma sun ```hada```.

Nuceey luv😘
[8/27, 2:23 PM] Nuceey luv😘: ® *OMAR* *KO* *FAROOQ*  ❓          84_85 "Haka omar yake rayuwar sa cikin wannan gida shi kadai, saikace maye, farooq kuwa yana gidan shi anacin amarci dukda yana cikin tunanin dan uwansa, kamar daga sama ya tuna da gidan omar, ai ko minti daya be qara ba yabar gidan shi, direct gidan omar ya nufa, "a tura kofar gate din yyi ga mamakin sa yajita a bude, hakan ya tabbatar masa da akwai mutum a ciki, yana shiga kuwa yaga motar omar aciki, hamadala yyi, sannan ya kutsa kanshi cikin falon, sallama yyi yaji shiru, dan haka ya haura sama, dakin omar ya gwada budewa yaji ta budu, dan haka ya tura, bayan yyi sallama, nan ma shiru, mamaki ne ya kasheshi ganin omar sai baccin sa yake hankali kwance, saidai da mutum ya lura zai tabbatar wa kansa ya danyi rama. "Matsawa yyi yadan bubbuga kafar sa, omar dake bcci yaji ana bugun sa a razane ya tashi yana kallon farooq da mamaki, "farooq ma mamakin yake dukda yadan daure fuska, atake baccin omar ya washe sannan yace malam lpy? Farooq ya nemi bakin gadon ya zauna, sannan ya kalli omar yace haba bro abinda kayiwa su mummy kayi adalci kenan? Yanzu kusan 4days baka je inda suke ba just bcoz sunyi maka gata? Haba bro. "Omar ya tabe baki yace kaga malam gidana kazo ba dandalin wa'azi ba idan shi kkeson yi kaje ka masallaci ko inda akeyi kayi inaga zakafi samun lada. "Da mamaki farooq yace bro ni kke fadawa haka? Akan an baka imaan? "Cikin tsawa yace ni nace inason ta? Cewa nayi a auramin ita? Bana sonta, bana qaunar ta har abada baxan ta6a sonta ba. "Farooq yace bekai ga haka ba ai, abinda nake jiye maka shine ranar da zakayi nadaman wannan kalaman da kake furtawa.. Omar yace ya isheka haka farooq tun muna shaida juna ka daina min mgnr jaririyar, farooq ya cije baki cike da takaici yasan hakane ai da tun farko ya sanarwa mummy zai auri imaan da duk hakan bata kasance ba, a fili yyi murmushi sannan ya fara mgn a nutse, yace sorry bro, Amman inaso ka gane fushin iyaye kan 'ya'yan su ba karamar masifa yake jawowa ba, duk abinda iyaye zasuyi wa yaransu bazasu taba yin abinda zai cutar da su ba, abinda iyaye sukayi mana bazamu ta6a biyansu ba biyayya itace tamu duk abinda sukace muyi zamuyi matukar be kauce addini ba, koda bama son Abu yakamata mu tausasa zuciyar mu muyi na'am da za6in su sai kaga qarshe mune dacin moriyar abun, INA rokon kayi kr2n ta nutsu kaje ka bawa su mummy hakuri dan Allah. "Omar yyi shiru shi kansa yasan be kyautawa su mummy ba, Amman harga Allah beji zai iya aminta da imaan a matsayin Matar sa ba. "Tabe baki yyi sannan yace sai nayi tunani. "Farooq yyi murmushi sannan yace ohk no prob, ahankali abinka da tsakanin twins, ba wani bata lkci farooq yyi ta Jan omar da hira har saida ya tabbatar ya ware daga bacin ransa sannan yabar gidan zuciyar sa wasai.


"Tunda yabar gidan omar yake ta tunani qarshe dai ya yanke shawarar komawa gida dan bawa mummy hakuri.  "Cikin shirin  sa ya fito na T shirt da wando, kwalliyar tayi matukar amsar jikin sa, yyi kyau sosai. "Motar sa ya shiga sannan ya kama hanyar gida, a hankali yake tuki harya isa gidansu. "Ya Dade cikin mota sai yanxu ma yakejin tsoron haduwar sa da mummy, dole dai ya fito a motar qirjinsa na bugawa dafdaf yasan mummy idan ta fara masa fada sai ikon god, gefe guda kuma tsanar imaan tana masa yawo a kwanya. 

  "Ahankali ya tura kofar falon hade d sallama, jin shiru ya tabbatar masa d ba kowa a falon. Qarasawa falon yyi Da nufin sake yin wata sallamar tarrrr idanun sa suka sauka kan wani photo dayayi bala'in yi masa kyau dake maqale jikin bango, idan bazai manta ba wannan shine hoton da akayi masa shida imaan lkcn data rungume shi, sosai ya shagaltu da kallon hoton, dan ba qaramin kyau sukayi ba. Mwtsssss yaji anja tsaki, juyawar da zaiyi yaga mummy ce data fito a dakin ta, da sauri ya sunkuyar da kansa, mummy kam juyawa tayi dan komawa dakin ta. "Ganin haka yabi bayanta da sauri, har dakin ya bita batare da tace masa komai ba tayi zaman ta tana duba wata jarida. "Mummy, omar ya kira sunan ta, mummy tayi banza dashi, kusan sau uku ya kira Amman ta share shi. "Omar yace dan Allah mummy kuyi hakuri akan abinda nayi muku sharrin zuciyane ya debe ni har na aikata abinda nayi, tsaki mummy ta sake ja cikin kunan rai tace ka tashi kabar min daki inada abinyi, omar ya rike kafar ta yace mummy dan Allah kiyi hakuri bazan sake ba insha Allah. "Mummy tace ka bani mamaki omar, ko a mafarki ban zaci akwai ranar da zamuyi maka kyautar Abu kayi watsi dashi ba, bama a iya gaban mu ba aa a gaban duniya ka nunawa duniya iyayen ka basu isa da kai ba, omar ya sadda kansa qasa ko kusa baison bacin ran iyayen sa, da kyar da sidin goshi ya lallaba mummy harta yadda, "qarshe mummy tace naji abunda nakeso kasa aranka shine auren ka d imaan babu saki, a rikice ya kalleta saidai ya kasa cewa komai dan bayason ya qarawa kansa wani lefin dakyar ya iya gyada kansa a matsayin ya yadda, mummy tace duk lkcn daka musgunawa imaan ta sanar min ko na gani da idona sai nayi mummunar sa6a maka, nan qirjinsa ne ya bada darararam, a fili kuwa yace insha Allah mummy zanyi yanda kikace, mummy tace gud, next week zaka dau Matar Ka. Omar yace Allah ya kaimu. Yana fadin haka yabar dakin sannan ya nufi side dinsa. "Mummy kuwa addu'a tayi Allah ya hada kan omar da imaan. Allah kuma ya sanyawa auren Albarka da daurewa har abada, nima dai nace ameen.

Nuceey luv😘
[8/31, 10:34 AM] ‪+234 706 897 1326‬: ® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓        86_87"Imaan CE ta shigo gidan a gajiye sai kwala sallama take ta dawo daga skul, dake kwana 2 mummy ke kaita skul, lkcn tashi kuma farooq ya kawo ta kafin ya wuce nasa gidan tunda basu koma aiki ba sakamakon hutun amarci da suka dauka. "Dakin mummy ta wuce tayi sallama, tana shiga ta tarad d mummy tana salla, "ajiye skul bag dinta tayi sannan ta fada toilet, wanka tayi, sannan ta fito, "lkcn mummy harta idar da sallah, imaan tace mummy sannu da gida, mummy tayi murmushi tace ya skul. Imaan tace uhum sai du'a'i, can kuma tadan 6ata fuska. "Mummy tace mekuma ya faru? Imaan tace mummy kinga fah kullum naje skul, sai a dinga nunani anacewa wai ga amaryar DR omar. "Mummy tace ke share su, imaan tayi narai2 da ido tace dan Allah mummy wai dgske ne? Mummy tayi shiru itama ta gaji da 6oyewa imaan batun auren ta, "can tace eh ba qarya bace, a rikice imaan tace whattttt??? Mummy ta girgiza kai alamar confirm, "imaan ta durqushe a wajen tana rusa kuka kamar wacce akayi mata rasuwa, "mummy tashi tayi ta isa gareta duk ta rikice da kukan imaan, lallashin ta tafara yi, Amman kamar ana angiza kukan imaan. "Mummy ta rasa abin yi, imaan kuwa bata daina kukan ba, mummy tace kinga imaan bakyason omar din  ne? Idan bakyaso sai a raba auren karki cuci kanki ki sanar min, dan banaso naci amanar ki, cakk kukan imaan ya tsaya tayi shiru tana tunanin maganganun mummy, idan akwai abinda zata sakawa mummy tasata farinciki shine ta amince da auren yaranta, rashin amincewar kuwa kamar tayi mata butulci ne, "karki takurawa kanki wajen amincewar abinda bakyaso ke dasu farooq duk daya na dauke Ku cewar mummy, imaan ta dago kanta tana goge hawayen ta tace aa mummy ba nufi na ba kenan, duk abinda kika zabamin wallahi INA maraba dashi Allah yasa hakan shine mafi alkhairi, da farinciki mummy ta rumgume imaan tana fadin ameen 'yata na gode na gode Allah yyi miki albarka, Imaan ta kwakwulo murmushi tace ameen, mummy tace toh Amman meya saki kuka dazu? Imaan tayi shiru dalilan kukan ta ai sunada yawa barkatai, abinda yafi daga mata hankali be wuce wai da omar aka daura mata aure ba, mutumin data fara tsana a rayuwar ta kenan, kuma itama tana da tabbacin ba wacce ya tsana kamar ita toh taya zaman su zai kasance da wannan hadin gambizar?....mummy ta katse mata tunani da fadin kinyi shiru. "Imaan tayi murmushi sannan ta sunkuyar da kanta kasa dan wasu hawayen ne ke Neman zubowa kan kumatun ta, a hankali tace sbd ya farooq, mummy tace farooq kuma? Imaan ta gyada kai, mummy tace meya miki? Imaan ta sanarwa mummy alkawarin auren ta da farooq yace zaiyi. "Mummy tayi shiru a zuciyar tace itama kanta taso hakan Amman data ga baice komai ba shiyasa taja bakinta tayi shiru, a fili kuwa ta furta tace don't worry, shi daman haka Allah yake ikon sa, kana naka ne shima yana nasa, Amman idan akabi nasa sai aga daidai. Imaan ta gyada kai cike da gamsuwa. "Mummy tashi tayi tabar dakin, imaan kuwa na ganin ta fita ta kifa kanta a jikin gado tana rera kuka yyinda zuciyar ta take ci gaba da tafasa, d wannan kukan bacci ya kwashe ta, kasancewar ba sallah take ba. "Sai da mummy ta shigo dakin sannan ta gyara mata kwanciyar ta.*******
Tun daga wannan ranar mummy take gyara diyar ta, omar kuwa ko kadan bayason ma ya hadu da imaan, haka zalika itama bata kaunar su hada hanya duk mummy na lura dasu saidai kawai ta basar taci gaba da bawa imaan abubuwan daya kamata, tsumi na musamman mummy tasa aka kawo wa imaan, imaan kuwa sai sha take abunta dan taji shi da zaqi, hadin kankana kuwa ba'ace komai, imaan bata ta6a kawo komai a ranta ba dan haka take shansu hankali kwance. "Imaan tayi bulbul abinta sai qara kyau take tamkar ba itace jaririyar da omar yake ambata ba.

****""
Yau data kasance Friday sati biyu da auren omar da imaan kenan, yau kuma mummy take son damkawa omar Matar shi a hannun sa.
Nuceey luv😘
[8/31, 10:34 AM] ‪+234 706 897 1326‬: ® *OMAR* *KO*  *FAROOQ* ❓          88_89 "Imaan CE durkushe gaban mummy, a dakinta sai  wa'azi take mata na zamantakewar aure, "mummy tace yi nayi, bari na bari imaan shine ribar aure, banban abun kuma shine hakuri, duk yanda masoya suka kai da soyayyar su, har sukayi aure toh INA tabbatar miki abinda zai biyo bayan zaman nasu shine hakuri., dukda na sanki ba baya bace wajen kwalliya da tsabta, toh inaso ki kara zage damtsen ki domin ita mace 'Yar kwalliya CE,... Wa'azi sosai mummy tayi mata, imaan kuwa ba abinda take sai kuka. "Mummy tashi tayi ta kaita falo, alkcn daddy ya fito shima, mummy ta danna kiran omar be Dade ba shima sai gashi, a wannan wajen daddy shi yaja musu kunne sosai a karshe yyi musu fatan Alkhairi, imaan dai kuka take kamar an bude famfo a idon ta, "mummy CE ta rike hannun ta lkcn har omar ya fice a falo, "yana cikin mota mummy ta iso da imaan wajen sa. "Da kyar mummy ta iya cire imaan jikin ta dan wani irin kuka da takeyi kamar anyi mata mutuwa Sam batason rabuwa da mummy. "Haka ta ajiyeta gaban mota, mummy ta leko tana kallon omar daya juya kansa gefe ransa sai tafasa yake dan jin kukan imaan da yake tamkar qara masa guguwar tsanar tane, "mummy ta kira sunan sa, da murmushin yake ya juyo yana kallon mummy, na'am ya amsa, mummy tace ga fateema nan na damka maka amanar ta, Ka kulamin da yarinya ta karka soma cutar da ita. "Omar yace insha Allah mummy zan kiyaye, ohk batun skul, ka dunga kiyaye lkcn tafiyar ta da kuma dawowar ta, omar ya gyada kai alamar ya amsa. "Mummy ta shafi kumatun imaan dake kuka sannan tabar wajen. "Tana barin wajen omar ya fisgi motar a guje Wanda har yasa imaan ta dago tana kallon sa a razane,  ganin fuskar sa tayi a murtuke kamar an aiko masa da sakon mutuwa, sunkuyar da kanta tayi a sanyaye a zuciyar tace ni daman nasan za'a Rina Allah kadai yasan irin zaman da zasuyi, take kuma ta kece da wani irin kuka, da sauri omar ya daka mata tsawa yace ya isheki kukan kuma haka, be qarasa bama imaan tayi saurin kama bakin ta wani mugun tsoron sa ya dirar mata lkci guda.

  "Gudu yake tamkar zai tashi sama, har ya iso unguwar su, yana zuwa gate, aka bude masa dake ya samo me gadi tun jiya. "Gate man sai daga hannu yake yana yalla6ai sannu da zuwa, inaa ai omar ko kallon sa beyi ba, wani wawan parking yyi, bayan ya tsaya sai yyi shiru, imaan dai kanta a qasa batasan ma a'ina suke ba. "Omar cikin daga murya yace jirana kike na fitar dake ko me? Imaan najin haka tayi saurin bode motar batare da ta kalleshi ba. "Tana fita omar ya sake fisgar motar a guje, kadan ya rage ya buge imaan dam ma ta matsa da sauri, baki galala ta tsaya kallon sa hanyar waje ya nufa, har ya fice a.gidan gaba1 bata daina kallon sa ba. "Wasu zafafan hawaye ne suka sake zubo mata, yana nufin anan zanyi ta tsayuwa kome? Wai wannan wanne irin aure ne? Imaan ta tambayi kanta. "Jikin wata fulawa ta matsa sannan ta samu wani waje tayi zaman agun, tana zaman jiran tsammani.

Nuceey luv😘
[8/31, 10:35 AM] ‪+234 706 897 1326‬: ® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓ 


       90_91"Tun yamma imaan ke zaune a wajen, sai bayan isha, sannan omar ya dawo, bayan yyi parking ya fito har zai wuce sai yaga imaan kwance ta shimfida dankwalin kanta ta kwanta bcci, "mamaki ne ya isheshi dan zaton sa lkcn daya barta zata shiga ciki da kanta, wata uwar tsuka yaja sannan ya buga qafar ta, a firgice ta tashi sbd tsoro har wani zare ido take har zatayi ihu cin karo da fuskar omar a murtike yasa ta rufe bakin ta, cikin tsawa yace uban me kike anan? "Imaan tayi shiru lkcn data maimaita tmbyr da yyi mata a zuciyar ta, renin hankali ma kenan...katse mata tunanin yyi da fadin ba mgn nake miki ba? Imaan me makon ta bashi amsa tsabar takaici ma sai ta kece da kuka, mwtss yaja tsaki sannan yace oya muje, imaan tayi tsaye ko motsawa taki yi, omar ya samu keyar ta ya hankada ta, dolen ta tafara tafiya tana share hawaye. "Har falo suka isa daga nan ya haura sama ya barta a wajen, kusan 10mins imaan na tsaye ko zama batayi ba, jin shirun yyi yawa yasa tabi bayan sa dan tagaji da tsayuwar, qirjinta na bugawa ta haura sama, daga nan taga daki guda biyu tunanin be wuce wanne omar din ya shiga ba, "kofar dake kusa da ita ta tura a hankali hade da sallama, gani tayi ba kowa saidai da alama yana toilet dan taji qarar ruwa, juyawa tayi ta fita a dakin, duba dayan dakin tayi, tsayawa tayi tana kallon tsaruwar dakin yanda taga gaban mirror cike da kayan kwalliya hakan ya tabbatar mata nata ne, dan haka ta shiga ciki ba wani bata lkci, "toilet ta fada tayi wanka tayo alwala sannan ta fito, bayan ta idar da sallar da ake Binta ta tashi tabi lpyr gado, saidai me? Wata mahaukaciyar yunwa ke damun ta, dan rabon ta abinci tun safe, na rana kuwa kasa ci tayi dan yanda tasha kuka, "juyi take sosai, ganin babu sarki sai mahalicci yasata mikewa dan nemawa kanta abinci, "hijab dinta ta sanya sannan ta fito zuwa qasa, ga mamakin ta taga omar yana zaune kan kujera yana kallo yana shan coffee hankali kwance, "kauda kanta tayi sannan ta wuce kitchen, tunda ta shiga nan ta shagaltu da tsaruwar kitchen din, babu abinda babu a kitchen din, indomie ta dauko ta dafa tare da kwai 5mins ya isheta ta gama komai sannan ta juye a plate, "falo ta fito rike da indomie'n sannan ta nufi wajen fridge, omar na falon yi yayi tamkar besan da mutum a wajen ba, "budewa tayi dan daukar ruwa, ganin lemo a ciki yasa ta dauko, zaunawa tayi kan daya daga jerin kujerin dining table din da shima ya tsaru dan kyau, saida ta gama ci sannan ta maida plate din kitchen bayan ta wanke shi ta fito, yanxu kam garau takejin ta sabanin da datake jinta sai a slow. 


   "Zata haura sama kenan taji ance ke zonan, ba musu ta juyo dan tasan waye me kiran, gaban sa ta tsugunna tace gani ya omar, omar dake kallo yyi banza da ita, kusan 15mins tana tsugunne a wajen, sannan yace karkiyi zaton dan an makala min ke ki zata zan daukeki a matsayin Matar aure NO, har abada bazan ta6a son kiba imaan, kin shigo rayuwar gidanmu hakan be isheki ba sai da kikayi yanda kikayi aka cusamin ke cikin rayuwata kinyi sanadin rushewar fariciki na duk wani plan dina kin rusa, banda niyyar aure Amman ta sanadin ki an qaqaba min ke, toh bari kiji kada ki zata dan mummy tamin mgn a gida ki dauka nayi na'am d zaman lpyr ki a'a saidan inaso ki gane kin rasa farincikin ki kenan imaan, kisa a ranki kina cikin _rayuwa_ da _mutuwa_ kisa a ranki kinyi bankwana da farinciki na har abada matukar bakije wajen mummy kince ke bakyason auren nan ba, koda yake is too late, kin zabi zaman kunci saidai nace miki welcome to black house. "Imaan banda hawaye babu abinda ke ambaliya a fuskar ta, magana ma kasawa tayi yo me zatace? Ai ita kanta shaida CE omar bazai taba sonta a rayuwa ba kamar yanda baza ta taba sonshi ba toh Wanda yyi silar mutuwar mahaifiyar ta har akwai wani sauran so da zatai masa?... Omar ya katse mata tunanin da take bayan yyi murmushin mugunta yace da kin Adana wannan hawayen naki inaga zuwa nan gaba zasufi maki amfani, tunani kuwa yanzu ma kika fara, so get out of my side ya fada a tsawace. "Jikinta a sanyaye ta mike dakyar ta iya daga kafafun ta sannan ta haura sama hawaye na zarya a kan kumatun ta. "A zuciyar ta tace shin dama haka ya omar yake? Wai wanne irin aure akayi mata? Yanzu me ya omar yake nufi da kalamansa?????


Nuceey luv😘
[8/31, 11:38 AM] ‪+234 706 897 1326‬: [8/23, 6:49 PM] Nuceey luv😘: ® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓

       74_75"Duk wani tunanin sa yarasa menene mafita.  Qarshe tashi yyi daga kwanciyar side din omar ya nufa. "A falo ya tarad dashi. "Omar yana zaune kan kujera yana kallo. "Farooq ya qarasa da sallama sannan shima ya zauna yana kallo suna hirar su jefi2, can farooq yace bro wata shawara nakeson ka bani, omar ya tattara nutsuwar sa ga farooq yace INA jinka. "Faroiq yace kasan daddy ya matsa mana da zancen auren nan ko? Omar yace eh, farooq yace hala ka samu matar da zaka aura? Omar ya tabe baki yace kyale dadday ni ban shirya yanxu ba, farooq ya zaro ido yace sai yaushe kenan? Omar yace sai lkcn da nayi niyya. "Farooq ya girgiza kai yace kasan halin daddy fah kada ya kawo mana wasu matan Wanda ra'ayin mu baya wajen su. "Omar yace kaga malam idan auren nan zakayi kaje kayi danni ban shirya ba., bayan haka kaida kacemin na baka shawara meya kawo wannan zancen auren? Farooq yyi murmushi yace kwantar da hankalin ka, kasan shawarar da zaka bani? Omar yace saika fada. Yyi mgnr a takaice dan ya kosa yaji abinda zaice. "Farooq yace inason na auri _Imaan_ shin meka gani a kai? Whatttt.....ido wuru wuru omar ya zaro yana me kallon dan uwansa, can kuma ya kwashe da dariya yana nunashi da yatsa yace ah lallema bro, shin INA dukkannin 'yan matan ka suke? Masu ji da class? Manya dasu? Ka rasa wacce tunanin ka zai qare sai kan wannan tatsitsiyar yarinyar? Yaushe aka gama tsigeta daga shan nono?.... Farooq ya katse shi d fadin haba bro shawara nace ka bani bawai ka tsaya muzanta imaaa ba, omar da kyar ya tsaida dariyar d yake yace, kasan Allah wallahi ka cire zancen imaan a ranka dan Sam yarinyar nan ba class dinka bace, haba karka bamu kunya mana, kuma kasanme? Daddy bazai aminta da auren Ku ba kwatakwata sbd asalinsu bamasu hali bane, kaifa da kanka kke bani lbrin da kyar daddy ya amince da zaman yarinyar nan a gidan nan fah? Wallahi tun da sauran mutuncin ka wajen daddy ka janye wannan zancen inaga shawarar da zan baka kenan. "Farooq yyi shiru d alama zancen omar na ratsa kwanyar sa. "Can ya nisa yace shikenan na gode da shawarar ka. Omar yyi murmushi yace u r wlcm. "Anan sukaci gaba da hirar su.
  
****""
Bayan sati biyu, farooq ne ya samu daddy har dakinsa ya sanar masa zancen auren sa, daddy da murna yace wacece? Farooq yace amira 'Yar alhji mukhtar. Daddy yyi murmushi yace good naji dadi sosai, ai namiji idan yyi aure yafi martaba. Farooq dai ya sunkuyar da kansa, mummy dake gefe itama tayi murna tasa albarka. "Daddy yace toh dan uwan naka fah shi be fitar da matar bane? Farooq ya Sosa kai, yace be sanar dani ba daddy, daddy yace turomin shi. Farooq yace toh. "Bayan minti biyar yyi omar a falon daddy, daddy yace kai kuma fa ya mgnr naka auren? Omar ya Sosa kai yace emm daddy har yanxu ban samu wacce ta dace dani ba. "Daddy yace haka kace? Omar ya girgiza kai. Daddy yace ohk zaka iya tafiya. Omar ya tashi cike da farinciki ganin daddy be dau abun da zafi ba. "Bayan fitar sa, daddy ya kalli mummy yace yaronki yana wasa da mgn ta. Mummy itama da damuwa ta kalli daddy dan ta kosa ta fara ganin jikokin ta, tace toh Amman baka CE masa komai ba ya tafi, daddy yace shi yarone? Akanme zanyi ta maimaita mgn? Ga dan uwansa nan ya samawa kansa lpy ai. "Mummy tace yanxu wanne hukunci ka yanke next? Daddy yace akwai mata dayawa d suka nuna suna sonsa acikin su zan sama masa wata saidai yaji anyi masa aure, mummy ta nisa sannan tace Allah ya zabar da abinda yafi alkhairi daddy yace ameen.
Nuceey luv😘
[8/23, 8:24 PM] Nuceey luv😘: ® *OMAR* *KO* *FAROO* ❓      76_77


"Omar kuwa yana fitowa a dakin daddy ya samu imaan a main falo tana kallon wani Indian film. Omar har zai wuce sai kuma ya dawo da baya ya rankwashi kan imaan, "imaan ba zato ba tsammani taji rankwashin har tsakiyar kanta. A razane ta juya tana kallon sa idon sa duk ya ciko d kwallah, "yah omar menayi maka dan Allah? Omar yace ban hanaki kallon Indian film ba? Imaan tace toh dannan kalla meye aciki? Omar ya zaro ido oh wato tmbyta kike miye aciki koh? Imaan tayi shiru,  omar yace shikenan zan fadawa mummy kina koyon yanda kiss dan kiyi wa gateman, imaan ta zaro ido tace na shiga uku ya omar yaushe nace maka haka?  Omar ya daga gira yana murmushi burinsa ya cika tunda ya sata kuka. "Imaan kuwa tashi tayi daga zaman da take ta kama rigar shi  tace dan Allah ya omar karka Sanar wa mummy ni wlhy ban taba yima kowa kiss ba. "Omar yace kinaso na yadda? Imaan ta gyada kai, omar yace ohk biyoni, imaan tace toh. Haka tabishi kamar jela, side dinsa suka nufa, bayan sun shiga falon sa, yace jeki dakina ki gyara ki wanke toilet sannan kizo kiyi mopping, imaan ta kwalalo ido tace haba ya omar banyi maka komai ba fa, kawai ma shrrin k...da sauri omar ya kalleta yace sharri na miki. Tayi saurin girgiza kai, omar ya daka mata tsawa oya je kiyi abinda nace or na je na sanar mata, jiki a sabule ta tafi dakinsa tana mgn ciki2 Allah wannan yah omar din mugune, omar yace kikace me? Da sauri imaan ta qara saurin tafiyar ta fatan ta Allah yasa beji abinda tace ba. Shikuwa omar kallo ya kunna yana ganin news,  "saida tasha wuya sosai kafin ta iya gyara gadon omar dan ma Allah ya sota, mummy tana koya mata badan haka ba ai da wuyar saitafi haka. "Saidai ta gama sannan ta komai toilet dinsa, komai tsaf2 yake a zuciyar ta tace mutum har mutum Amman sai mugunta data cika masa kwanya fisabilillahi meye abin gyara anan? Haka imaan ta cika kunfa a katon boket, sannan ta kwara duka toilet din, sannan ta Debi wani ruwan ta kwara haka tayi tayi har kumfan ya tafi, ganin haka ta lall6a ta fito a toilet din kadan ma ya rage santsi ya kwashe ta. "Falo ta tana haki, omar ta samu ya fara bcci, hamdala tayi sannan ta la6a6a tabar falon, tana fitowa ta tafi side din mummy a guje.
  

*****
Daddy ne ya tara su a falo yake sanar musu sun gama mgn d Abban amira zuwa nan d 2weeks za'a daura aure, mummy tace da wurwuri haka? Daddy yace toh me za'a jira ai idan akwai kudi sai ayi komai akan lkci basai an ja ba. Mummy tace Allah ya sanya Alkhairi daddy yace haka nakeson ji, "farooq dai yyi murna abinsa, shi kansa omar ya taya dan uwansa murna. Haka sukaci gaba da hirar su har farooq ya mike da nufin tafiya side dinsa dan kiran mutuniyar sa, Imaan CE ta tashi tabi bayansa, omar ma tashin yyi. "Lkcn da duk suka fita, mummy ta kalli daddy, tace alhji yanxu ya mgnr da mukayi ranar? Daddy ya hade girar sama data qasa yace zainab abinda ya Dade be kira ba kenan, yace tun muna shaida juna kada ki sake min wannan mgnr Sam banji zan iya ba, mummy ta sunkuyar da kanta tace Allah ya huci xuciyar ka banyi hakan dan 6ata maka raiba, Amman INA rokon ka da kasake tunani akai dan Allah, daddy ya 6ata rai batare d yace komai ba.
  "Imaan har falon farooq ta nufa, saida suka zauna farooq yace my sisi yadai? Imaan ta 6ata rai tayi shiru. "Farooq da damuwa yace imaan yimin mgn mana. "Imaan ta fashe da kuka a rikice yace ya salam wani Abu aka miki? Imaan ta daga kai. Farooq yace waye? A hankali tace kaine ya farooq. "Farooq ya zaro ido yace ya salam menamiki? Imaan tace yah farooq ka daina sona gashi nan daddy yana mgnr auren ka da wata Amman bakace dani zakayi ba. "Dariya, mamaki, tausayi sukayi masa durar makiyiya a lkci daya,  kwantar da murya yyi yace sorry my sis ba nufina haka ba, kinga yanzu kina Ss1 going to ss2 yaushe kika gama skul kikayi university kafin muyi aure? Ai kinada lbrin yanda daddy yace dole mu kawo mata a yanxu ko. "Imaan ta girgiza kai. "Farooq yace toh kiyi hakuri idan kika gama skul, a shekarar zamuyi aure, d gske? Ta tmbyeshi farooq yace yes, imaan sai alkcn ta saki ranta tana murmushi. "Shima farooq mutmushin yyi yana me mamakin wautar imaan, shi abin nata da wasa ya daukeshi Amman ga dukkan Alamu ita da gske take, wata zuciyar tace Allah ya kaimu lkcn saika aureta as second wife. Da wannan tunanin ya ajiye a zuciyar sa. Sannan sukaci gaba da hirar su yama manta da kiran wata Ameera.


*****
Shirin biki sosai akeyi yyinda aka shiga sanarwa a gidajen radio da talabijin, mutane sai mamaki suke wai duk yanda suke twins Amman wai daya ne zaiyi aure, haka dai masu surutu nayi, 'yan mata kuwa sai haushi sukeji duk Wanda sukayi dating da farooq zataso ace itace Matar sa, sai sukaga duk cikin su sun kasa gano wacece wannan amirar? 
 Toh nimadai nace wacece amira?
 "Aisha ( ameera) kenan ya ga alhji mukhtar yarinya CE ajin farko, ga kamun kai da hankali, babanta yana daya  daga cikin Wanda za'a jerasu a masu kudi, sun hadu da farooq ne lkcn data je hospital tana me ciwon Mara period dinta zaizo kenan, Amman yana wahalar da ita, koda taje a kunyace ta iya yiwa farooq bayani, shikuma farooq tunda ya kyalla ya ganta, yaji ta kwanta masa a rai, har ya kasa hakuri da dabara ya samo asalin inda take, cikin ikon Allah kuwa ya samu soyayyar ta, takaitaccen bayanin ta kenan.

Nuceey luv😘
[8/31, 11:39 AM] ‪+234 706 897 1326‬: [8/24, 5:56 PM] Nuceey luv😘: ® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓


       78_79"Shirye_shirye ake, both gidansu ameera da farooq, farooq har gida ya kawo ameera suka gaisa d mummy, sosai mummy tayi farinciki dan ta lura yarinyar tanada hankali da nutsuwa, imaan kam ta saba da Anty ameera kamar sun dade, har gidan su tana zuwa tayiwa farooq rakiya, dake imaan sun sami Hutu sai bikin yazo mata a daidai, yawo sosai suke zuwa ita da farooq da ameera, itakam burge ta suke yanda suke tafiyar da soyayyar su. "Akwana a tashi babu wuya a wajen Allah, yauta ta kasance Friday inda dubban jama'a suka taru domin daurin auren farooq, 6angaren omar ma sosai yake taya dan uwansa murna, kowa sai mamakin sa ake shine babba Amman beyi aureba. "Shadda wacce tasha dinku ubansu, na hango taurarin sun fito daga side dinsu, duk yanda kaso ka banbanta omar da farooq, bazaka iyaba sbd tsantsar kyaun da sukayi, dinkin sosai ya amshi jikin su, abunka da basu saba sa babbar Riga ba, sai abin ya zama gwanin sha'awa son kowa kin Wanda ya rasa, cikin takun kasaita suka fito a side dinsu fuskarsu dauke da murmushi, "daidai lkcn imaan ta fito a dakin mummy, kwalliya sosai mummy tasa akayi mata, ba karamin kyawu tayi ba, make up dinnan yahau, ga daurin da akayi mata ya matukar karbar ta, saikace itace amaryar, fitowar kenan isowar su omar da farooq me camera na gefen su, masu kirari nayi, imaan na ganin su tayi sauri da nufin hugging din farooq, saidai ta kasa banbanta su, haka ta qarasa wajensu inda zuciyar ta ya bata, ba zato ba tsammani omar yaji imaan tayi hugging dinsa, dagowa tayi tana dariya tace kagani nayi kyau? Omar shime besan lkcn da yyi dariyar ba ai kamar jiran sa ake sai ganin hasken camera suka gani, dukkansu suka juya da sauri dan ganin Wanda ya daukesu camera man suka gani da farooq da shima yake riqe da waya yana, daukar su pic, juyowar su shiyayi daidai da qara musu pic din, raf-raf-raf aka hau tafi, wasu sai fadi suke ko sune amaren? Dan sun rasa waye farooq din. Hotunan da akayi musu ba qaramin kyau sukayi ba. Omar dai yyi murmushi batare da yace komai ba ya kama hannun imaan da take ta washe baki jin ance sunyi kyau duk azaton ta da farooq akayi mata photo. "Har dakin mummy ya kaita still ta sake cewa ya farooq bakace nayi kyau ba? Omar yyi mata shiru, sannan ya fara tafiya, imaan tayi saurin tashi kamar zatayi kuka tace nayi kyau? Kai ya daga mata da murmushi sannan ya wuce da sauri, imaan a zuciyar ta tace haladai yau axumin mgn kke. "Shikuwa omar yaso ya disga ta da niyyar sa ya tureta, Amman yana tsoron fadan mummy dan a falon ta abin ya faru, shiyasa ya samawa kansa salama bayan haka sosai ransa ya 6aci haddai ma hotunan da akayi musu saikace sune amaren, mwts yaja tsaki, mota guda suka shiga shida farooq dan zuwa daurin aure, abokansu suka hau wata motar, wasu kuma suka hau tasu omar, ma'ana daya yyi driving daya ya zauna a kujera me zaman banza. "Koda suka shiga be tankawa kowa ba sa6anin da dayake murmushi, farooq yana lura dashi saidai shima ya basar yana hira da abokan su. "Wanda yake driving din babban abokin farooq kenan, yace kai Amman fa omar kunyi bala'in kyau d wannan yarinyar fah, omar yanajin sa ya share shi, farooq yace kaifa dan iskane wannan sister mu ce, da sauri yace kai dan Allah? Farooq yace dgske, abokin ya kalli wanda me kujerar me zaman banza yace Yusuf d alama na samu mata a gidan su farooq fah. Sai alkcn omar yaja tsaki yace malam kayi abinda ke gaban ka bawai surutu ba ka wani cika mutane da surutu akan wannan yarinyar, wanda yake driving din yace aa kace rowar sister Ku zakumin, farooq yace ah karka damu idan imaan CE zamu baka, omar ya sake Jan tsaki a karo na biyu, shi haushin sa daya yarasa me suke gani jikin imaan da kowa zaice yana sonta, baya manta lkcn daya kai imaan skul, bayan ya ajiyeta har zai tada mota wani dake cikin mota ya fito da sauri yana masa alamar ya tsaya, "lkcn daya tsaya mutumin ya tmbyeshi imaan ko sister sa CE? Yace eh, bawani 6ata lkci ya fada masa tunda take zuwa Skul din yaji yana sonta kuma da aure, ya yaba da hankalin ta da nutsuwar ta da kuma kokarin ta. "Sosai omar yyita mamakin wannan mutumin, qarshe yace yyi hakuri kr2 zatayi, mutumin yace shi zai jira ko shekara nawa zatayi, cikin tsawar d be shirya yinta ba yace malam anyi mata miji, ai d sauri mutumin ya bashi hakuri ganin yanda ransa ya 6aci sannan yabar wajen., da wannan tunanin kala2 suka isa babban masallaci na Kano inda za'a daura auren farooq da amaryar sa ameera.


  
Nuceey luv😘
[8/24, 6:41 PM] Nuceey luv😘: ® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓             80_81 
"Tunda suka isa taron ake busa saikace 'yan'yan sarakuna kai duk wanda ya halarci bikin zai tabbatar was kansa lalle wannan auren bana wasa bane, manyan mutane harda shugaban kasar america ya hallaci wannan hamshakin daurin auren, makada da mawaka kam ai sai abinda yyi gaba, dan sun sami sun baje kolin su, "ba'a dau wani lkci ba aka fara sanarwa kamar yadda al'ada ta tanadar a musulunci, kowa ya shaida daurin auren _FAROOQ_ _DA_ _AMARYAR_ _SA_ _A'ISHA_ akan sadaki me inganci, habawa nan aka fara tafi da Sam barka abindai ba'a cewa komai. "Bayan minti biyar dakyar aka yi sanrwa a lasifiqa akan a saurara, "abinka da dubban mutane baka gane abinda ake cewa,
   "Sanarwa aka sake yi, bayan haka mutane da shaidu sun shaida an daura auren farooq da a'isha haka mukeson su shaida an daura auren omar da amryar sa.... Arazane omar ya mike da sauri ya matsa kusa da daddy dake suna kusa, ya rike hannun sa cike da tashin hankali, bakinsa na rawa yace dan Allah daddy, kayi hakuri dan Allah karkamin haka daddy, daddy yyi murmushin sa irin na manya, sannan ya kalli me sanarwar yace ci gaba da abinda kke, farooq yana gefe shi kansa ya tausayawa bro dinsa dukda dai basusan dawa daddy zai hada auren ba. "Me sanarwa yabi umarnin dadi, ya cika aikinsa. "A firgice omar yake kallon daddy da matukar mamaki, anya yasan wacce ya aura masa kuwa? "Ba'a iya tantance yawan tashin hankalin da suka bayyana kan fuskar omar, mikewa yyi yabi cikin mutane fuskar nan babu alamar annuri, haka yyi ta keta mutane har yaje inda sukayi parking, toh Allah yaso shi akwai extra key a hannun sa, hakan ya bashi damar tuka motar a guje, "mutanen dake wajen kuwa sai mamaki suke, sundai ga an sanar frooq za'a daurawa aure Amman sai sukaga sa6anin haka, haka taro ya watse, farooq dai yaken dole yakeyi burinsa yaje ya duba inda omar ya tafi, yasan sa da zuciya idan yyi zuciya abun ba kyau, har zai tashi ya bishi daddy yace ya tsaya karya soma binsa. Haka ya hakura, mutane kuwa sai tayasu murna suke, haka taron ya watse.
  "Dakyar farooq ya samu ya sulale yabar wajen, shima wata motar ya shiga sannan ya karbi key gun wasu abokansu, ba inda ya nufa sai gida. "Tun abakin gate yyi parking sannan ya wuce side dinsu direct, dakin omar ya nufa ya Ganshi a bude, alamar be ma dawo gidan ba kenan. Zai fito kenan suka hadu da mummy fuskar nan tata a tamke 6acin rai qarara a fuskar ta, abinda ya sake hargitsa tunanin farooq kenan, cikin tsawa tace ina omar din yake?
Nuceey luv😘

adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *