Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Friday, 14 June 2019

SHI KADAI NAKE SO Complete hausa romantic novels

adsense here
SHI KADAI NAKE SO Complete hausa romantic novels

SHI KADAI NAKE SO Complete hausa romantic novels

SHI KADAI NAKE SO cmplt[1/9, 10:27 PM] Beelybadaru😍: 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
*SHI KADAI NAKE SO*
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
           ✨✨✨
              ✨✨
                 ✨

✨By Beelybadaru😍✨

_Bismillahir-rahmanir-rahim_

*Wannan littafin nawa qagaggen labari ne banyi don cin xarafin wani ko wata ba, idan yayi dai dai da labarin rayuwarka ka gafarceni, kuma kar wanda ya juya min labarina ta wata siga, wanda yayi hkn na barsa da Allah...*


            ✨1 to 5✨

_I dedicated this page 2 u Ayusher Moh'd, Rabi'at sk msh, Asy khaleel, Wally, Aneelurv(Sweet dota), First lady, Mufeeda Mu'axu, HummyB(Melody), Afma, Yarruma(Sweet momma)._


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

```Kallon juna suke cike da so da qauna, kai da ka gansu xaka tabbatar da cewa su masoyan juna ne na ainihi. Ita ta soma sauke idonta daga kallon da suke ma junansu, sannan ta dago tare da cewa "*Habeeby* ina sonka fiye da yanda nake son kaina, bana tunanin xan iya rayuwa ba tare da kai ba, kaine majinginin rayuwata idan ka matsa rayuwata gaba daya rugujewa xatayi". 

Dagowa yayi shima ya kalleta cikin so da qaunarta da suke yawo cikin jinin jikinsa sannan yace "*Habeebty* sonki a cikin jinin jikina yake, soyayyarki wani bangarene mai mahimmanci a rayuwata, cireshi a cikin xuciyata abu ne mai wahalar gaske, ta yaya kike tunanin xan iya rayuwa babu jini a jikina? Ta yaya kike tunanin xan iya rayuwa babu xuciya a jikina? Cire sonki a raina ba abune mai yuwuwa ba, don kuwa idan har aka ce xa'a cireshi ai dai a debe duka jinin jikina domin kuwa sonki a cikin jinin jikina yake yawo". 

Lumshe ido ta tayi cike da jin dadin kalamansa, haqiqa sunyi nisa a soyayyar junansu, rabasu abune mai wahalar gaske. 

Bude baki tayi da nufin yin magana sai ji tayi an fincikota ta baya, waigawa tayi da sauri don ganin ko waye, gabanta ya fadi ganin Abbanta da tayi tsaye a gabanta fuskarsa daure kamar wanda aka aikoma da saqon mutuwa. 

Jikinta ne ya dauki kyarma, durqushewa tayi a gabansa hawaye har sun soma xarya a kumatunta, shima durqushewar yayi cike da jin tsoron abinda Abba xaiyi masu. 

Wani wawan mari Abba ya watsa mata, a gigice ta dafe kuncinta don har wasu taurari ta gani shima da hanxari ya dafe kuncinshi don ji yayi kamar shi aka mara don yaji xafin marin har cikin xuciyarshi. 

Cikin bacin rai Abba yace "*KHADEEJAH* ni xaki maida qaramin mutum? Ni xaki kunyata? Ke har kin isa in yanke magana a kanki ki bijiremin? To bari kiji in fada maki ko xaki mutu baxaki auri wannan yaron ba auren xumunci xakiyi kamar yanda kowane dan'uwanki yake yi". 

Ya waiga ya kalli saurayin da har lokacin bai sauke hannunshi  daga dafe kuncin da yayi ba, yace " Kai kuma ban gargadeka ba akan kar na sake ganinka da diyata ba? Karka kuskura na sake ganinka da ita idan ka bari hakan ta faru......" Yayi kwafa, sannan ya juya ya fara tafiya can ya waigo kuma ya kallesu sannan yace "Ki tabbatar da kin shigo gida cikin secon biyu".

 Da sauri ta miqe ta qarasa gabanshi ta durqusa tare da hade hannayenta biyu guri guda sannan cikin muryar kuka tace " Abbana na roqeka da Allah kayi hkr kayi min rai karka rabani da *AHMAD* wllh shine rayuwata baxan iya auren kowa b in bashi ba, *SHI KADAI NAKE SO* zuciyata tarwatsewa xatayi Abba idan har ka rabani dashi". 

Wani dogon tsaki yaja ya tare da yin ball da ita yace "Ah lallai dole xakizo ki tasani ki ri qa gayamin magana n ranki, to bari kiji in gaya miki dolenki ki amshi auren xumunci kamar ynd yan uwanki suka amsa, daga rana irin ta yau bake ba Ahmad kinji na fada miki". 

Jin hakan yasa Ahmad yayi saurin qarasowa wajen Abban shima ya durqusa gabanshi tare da cewa " Abba don Allah karka rabani da Khadeejah wllh *ITA KADAI NAKE SO* Abba meyasa kake neman ruguxa mana rayuwarmu, Abba don Allah kayi hkr ka barmu  mu auri junanmu". 

Banxan kallo ya watsa mashi sannan ya shige cikin gida. Ahmad har ya fara xubar da hawaye, da sauri Khadeejah tace "Ka daina xubar da Hawayenka Habeeby, xuciyata quna take a duk sanda naga hawayenka na xuba". 

Shima kallonta yayi sannan yace " Habeebty kema ki daina xubar da naki hawayen ko kadan bana son ganin hawayenki na xuba". Tabbas *HAWAYEN MASOYA* akwaisu da xafi, don kuwa a ynx ji suke kamar xuciyarsu xata fashe ganin hawayen junansu. 

Kamar an tsikareta ta miqe tare da cewa "Habeeby xan shiga ciki". Kafin yayi magana tayi saurin shigewa cikin gidan. Tashi yayi kamar wani mara lpy, da qyar ya qarasa wajen motarshi yana hada hanya kamar wani dan qwaya, haka ya shiga motar yajata a tsiyace ya bar qofar gidan. 

Khadeejah kuwa tana shiga  ta tadda Qanwarta mai suna *AYUSHER* xaune a falo tana kallo, kallo daya tayi mata ta wuce sama dakinta, yayinda Ayusher ta bita da kallon tausayi don kuwa tasan duk abinda ke faruwa, sosai take tausayin er uwar tata don dai bata da yanda xatayi ne, Tashi tayi ta bita dakin. 


    ✨TUNA BAYA✨


   _Beelybadaru😍_```
[1/10, 1:17 PM] Beelybadaru😍: 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
*SHI KADAI NAKE SO*
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
           ✨✨✨
              ✨✨
                 ✨

✨By Beelybadaru😍✨

         ✨6 to 10✨

_This page is 4 u Sis Ayshert, Sys Nabeelah, Sys Khadeeybadaru, Sis Hawwybadaru, Nana Zeey, Zee-rabs, Sayyida Dz._

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

        ✨TUNA BAYA✨

```Alh Auwal Bafu shine sunan mahaifin Abban Khadeejah, Alh Auwal mutumin kirkine matarshi daya Hjy Hauwa'u, itama mutuniyar kirki ce, suna da Ya ya uku, Alh Abdul-wahab shine babbansu wanda aka fi sani da Daddy yana da ya ya ukku, sai Alh Ibrahim wato mahifinsu Khadeejah wanda aka fi sani da Abba, sai kuma autarsu Hjy Zainab wadda aka fi sani da Umma, tana da Ya ya biyu mace da namiji ya rasu shekara 8 data wuce. 

Alh Ibrahim Auwal y kasance mutumin kirki kuma y iya xama da jama'a, kasuwanci yake yi, kuma shi maxaunin Kaduna ne a unguwar G R A, Yana da mata biyu Hajiya Waliyyah da Hajiya Hafsat. 

Hjy Hafsat mace mai mutunci da kamala, itace matarshi t farko, amma sun jima Allah bai basu haihuwa ba, dangi suka uxura mashi har saida y qara aure ya auri er dangi, lokacin da ya auri Hjy Waliyya suna xaman lpy sosai da Hjy Hafsat. 

Watan Hjy Waliyya Hudu Allah y bata ciki, nan fa dangi aka fara yima Hjy Hafsat habaice2, hqr ta dinga yi har Allah y sauki hjy Waliyya lpy, ta haifi danta namiji mai kyau yaci sunan mahaifinsu wato Ibrahim suna kiranshi da Mu'azzam, shekararsa biyu ta sake haihuwar mace taci suna *Rabi'atu* tun daga nab bata kuma haihuwa ba kuma hr lokcin bata chanja ma Hjy Hafsat ba. 

Allah maji roqon bawa, Hjy Hafsat ta tashi da matsanancin ciwon ciki suna xuwa asibiti aka tabbatar masu da cewa cikine da ita, sosai Alh yayi murna kamar itace haihuwarsa ta farko, Hjy Waliyyah ma tayi murna sosai don tsakani da Allah suke xaune da Hjy Hafsat. 

Bayan watanni ta haifi erta santaleliya mai kama da ita ranar suna yarinya taci suna KHADEEJAH bayan shekara biyu ta sake haihuwar erta mace taci suna *Ayusher*, bayan wasu shekarun biyu ta sake samun ciki wanda ya kasance yana bata wahala sosai tunda ta sameshi har xuwa lokacin haihuwar. 

Lokacin haihuwa ta haifi yaranta duk maxa guda biyu, ko ganinsu batayi ba Allah ya amshi rayuwarta, Allah sarki Abba yaji mutuwar sosai shi da Hjy Waliyya, ita ta dauki yaran tace xata rainesu tamkar ya'yan data haifa,  suna yara sukaci suna *Aliyu da Haydar*. 

*BAFU FAMILY* shine sunan family din su Khadeejah, Family'n ya shahara sosai don duk qasar nan babu wanda bai sanshi ba, family ne na hadin kai sam baka jin kansu, kuma suna da tarin yawa, don akwai qannen Alh Auwal Bafu da dama kuma suma suna da nasu ya'yan da jikoki sannan suna da tarin dukiya kuma suna taimakon junansu, kuma tunda suka taso auren xumunci ake yi, maman su Khadeejah ce kawai ta kasancxe bare a cikinsu shiyasa sam bata jin dadinsu. Wannan kenan..... 

✨FARKON HADUWARSU DA AHMAD✨

A shopping mall suka hadu lokacin sunje siyayya ita da Ayusher da kuma su Aliyu, bayan sun gama siyayyar suka biya kudi sannan suka fita, sai da sukaje wajen mota sannan tayi saurin tsayawa tare da cewa "Oh na manta purse dita a ciki". 

Aliyu yace " kai big sis kiyi sauri plx ki dauko Allah n qosa na koma gida". Hararanshi tayi sannan ta juya da dan hnxari ta koma ciki. Waige2 t farayi can ta hango purse din tata da sauri tayi wajenta da niyyar daukowa, sai ganin wani hannu tayi xai dauka, a hankali ta dago kanta don ganin ko waye, idanunta ne suka sauka a kan fuskar wani kyakyyawan saurayi, sam baiyi kama da hausawa ba, sai ka rantse irin larabawan nan ne, kallon kallo suka tsaya yi can ta sauke idonta qasa sannan ta dauki purse din ta dago tare da hararansa tace "Da daukarmin xakayi?". 

Murmushi yayi da ya qara fiddo da kyawunshi yace " Nayi laifi idan na dauka na kawo miki?". Qara hararanshi tayi sannan ta juya xata wuce, yayi saurin tsayar da ita ta hanyar cewa "Excuse me". Waigowa tayi ta aleshi da jiran jin mai xaice, murmushin ya kuma yi sannan ya saita wayarshi saitinta sannan yace " Kinyi min kyau can i take a picture of u?". 

Kafin tayi magana sai jin qarar daukar photo tayi, ta watsa mashi harara xatayi magana sai ga Ayusher ta shigo tana cewa "Sis kin barmu una ta jiranki, waigawa tayi ta kalleta an ta waiga ta kalli Saurayin ta juya ta fice, shi kuma yayi tsaye yana kallonta da murmushi a fuskarsa.........    _Beelybadaru😍_```
[1/12, 6:35 AM] Beelybadaru😍: 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
*SHI KADAI NAKE SO*
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
           ✨✨✨
              ✨✨
                 ✨

✨By Beelybadaru😍✨

       ✨11 to 15✨

_This page is 4 u Abdul-mr, smilesπŸ˜ƒ, Raheem jEga, Ililee._

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

```Suna isa gida suka iske Aunty Rabi'atu taxo gidan ita da mijinta Uncle Mus'ab, dan Daddy ne (Yayan Abbansu Khadey). Da diyarsu qwara daya mai suna Hayfah, yarinyar farin jini gareta sosai suke shiri da Khadeejah. 

Suna shiga falon Hayfah ta taso da gudu ta maqalqale Khadeejah, dagata sama tayi tana dariya tana mai cewa "Babyna yaushe kukaxo?". Dariya itama tayi tare da cewa "Aunty yau mukaxo kuma naxo miki da tsayaba". Khadeejah tayi murmushi suka qaraso falon ta xauna kan kujerah sannan tace " Aikuwa naji dadi sosai nima na taho miki da chocolate ". 

Tsallen murna ta hau yi, nan suka gaisa dasu Aunty Rabi'atu sannan suka bige da hira, basu suka daina firar ba sai da sukaji kiran sallar la'asar sannan duk suka miqe don gabatar da sallah. 

2 days later

Suna xaune a falo ita da Aliyu da Haydar, suna kallon wani indian film mai suna DILWALE, Aliyu ya dan kauda kai daga kallon sannan yace "Ni banga abin kallo ga indian film ba, duk films dinsu basu burgeni". 

Khadeejah ta watsa mashi harara don ita gwana ce wajen iya harara, ita har ta saba da ita ma, tace " Basu burgeka amma ka gyara xama kana kallonshi?". Haydar yace "Hmmm ai bruh Aliey kinibibinshi yayi masa yawa". 

Aliyu ya miqe tare da cewa " Ni bari ma in tashi na tafi daki, gwara ko barci ne nayi". Ya juya ya shige daki, ba'a fi minti biyu ba sai gashi ya dawo ya xauna ya cigaba da kallon, binshi sukayi da kallo, can Khadey tace "A aha kai da kace baka son kallon miyasa ka dawo kuma?". Kallonta yayi sannan yace " Taimaka masu kawai xanyi na kalla ba don halinsu ba. 

Gaba daya suka kwashe da dariya barin ma Haydar da dariyar mugunta, Haushi ya kama Aliyu yayi kan Haydar da nufin bugunshi, Haydar yayi saurin miqewa yayi hanyar waje da gudu, a bakin qofa sukayi karo da Ayusher, duqewa tayi tana riqe da goshi cikin jin xafin buguwar da sukayi da Haydar tace "Dallah can miye haka? Ji ynd  ka bigemin kai". 

Haydar ya watsa mata harara tare da cewa " To Aunty Masifatu, ina sane ai baxan bigeki ba". Tsaki tayi ta miqe ta wuce cikin  ta xauna gefen Khadey tace "Aunty kije ana sallama dake". 

Da mamaki Khadeey tace " ana sallama dani kuma? Waye?". Ayusher tace "Wannan da na ganku tare dashi a Super market". Mamaki ya cikata to mi ya kawoshi gidansu? Yama akayi yasan gidansu?.

Tashi tayi ta koma dakinsu sannan ta dauki hijab dinta sannan ta fito ta wuce su Aliyu dake xaune a falon duk suka bita da kallo. Tana fita Haydar da son jin gulma ya matso kusa da Ayusher cikin rada yace " Sis waye shi?". Hararabshi tayi tare da cewa "Bansani ba ynx fa ka gama yimin rashin kunya". Tabe baki yayi ya koma inda yake ya xauna. 

Aliyu kuwa mai xaiyi inba dariya ba? Cikin dariyar yake cewa " Waih Haydar ka bonsu, irin wannan kankana haka?. Cike da jin Haushi Haydar ya miqe ya fara binshi da niyyar huce haushinshi a kanshi, nan suka fara xagayen falon, Ayusha kau ba abinda take inba dariya ba. 

Khadeejah kuwa tana fita ta hangoshi jingine a jikin motarsa yau wankan qananan kaya yayi  black nd white yayi masifar kyau gashin kanshi yasha gyara har wani nannadewa yake saboda silbi. Dago da kanshi yayi ya kalleta, wani sanyayyan murmushi ya sakar mata, sai taji yayi mata kwarjini sosai don a nufinta tun daga nesa xata fara balbaleshi amma sai taji ta kasa aiwatar da hakan. 

Har ta iso inda yake bai daina kallonta ba, hararanshi tayi tare da cewa "Kallon fa?". Lumshe idanuwanshi yayi sannan ya bude yayi murmushi yace " Laifi ne idan na kalli sarauniyar kyawawan matan duniya?". Dan xaro ido tayi waje sannan tace "Ni din? A ina na xama kyakkyawa har haka?". 

Murmushin ya kuma yi sannan yace "Ai kin wuce hakan ma". Hararan ta kuma watsa mashi sannan tace " To ynx dai mai ya kawoka gidanmu?". Ya gyara tsayuwarshi sannan yace "Naxo ganinki ne saboda na kasa samun sukuni a cikin xuciyata". 

Cikin rashin fahimta tace " Ban fahimceka ba?". Murmushin ya kuma yi sannan ya kuma gyara tsayuwarsa yace "Zuciyata ce ta axaxxala min akan lallai sai naxo ta ganki taji sanyi". Hararanshi ta kuma yi sannan tace " Tunda baxaka fada ba ni xan shiga gida". 

Da sauri yace "A a karki tafi plx ki tsaya xan fada miki". Tsayawar tayi ba tare da tace kmai ba, yace "Am Khadeejah ni dai sunana AHMAD ABDULLAH, tunda na ganki xuciyata ta kasa samun sukuni, na rasa meke damuna cikin en kwanakin da muka hadu dake, sai daga baya xuciyata ta tabbatar min da sonki nake so na haqiqa".... 
   _Beelybadaru😍_```
[1/13, 7:37 AM] Beelybadaru😍: 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
*SHI KADAI NAKE SO*
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
           ✨✨✨
              ✨✨
                 ✨

✨By Beelybadaru😍✨

        ✨21 to 25✨

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

```Sharewa tayi ta cigaba da abinda take don batajin xata iya fita, idan ya matsu ko waye ya qara kira ya sanar da ita ko waye shi sannan ta fita, bayan minti biyu sai jin qarar shigowar text tayi a wayarta, daukowa tayi ta duba, nmbr ce dai da aka kirata taga an rubuta:-

      *Deejah Ahmad ne, don Allah ki fito ko ganinki kadai nayi*

Murmushi ta saki lokaci guda taji wani farin ciki ya lullubeta, tashi tayi ta shiga dakinsu, kallon kanta tayi a mirror, bata jima da yin wanka ba, doguwar riga ce ta atamfa a jikinta, sai taga sam batayi mata ba, hakan yasa ta bude wdrp dninta ta fiddo wani material riga tda sket pink da ratsin milk a jiki ta sanya, sannan ta dauko milk din gyale ta yafa. 

Tsintar kanta tayi da shafa powder har da lipstick, tana gamawa ta dan fesa turare kadan sannan ta fito ta nufi hanyar fita, har takai bakin qofa Umma ta fito daga daki, kallonta tayi da mamaki tace "Khadeeja ina xuwa haka?"

Ji tayi duk kunya ta kamata ta sadda kanta qasa tare da cewa "Umma xanje garden ne". Dan murmushi Umma tayi tace " Kodai kinyi baqo ne xaki ce garden xaki da wannan kwalliyar?". Rufe fuskarta tayi da mayafin jikinta tana murmushi. 

Umma tayi dariya tace "Kije, amma fa a dai kiyaye". Ta amsa da "Toh Umma". Sannan ta fice daga falon xuwa inda Ahmad yake. 

Ahmad kuwa har ya gaji da tsayuwa y koma mota ya xauna, shi yayi tunaninma baxata fito ba ga mamakinsa sai hangota yayi tana fitowa, sosai yayi farin cikin ganinta, yayi saurin fitowa daga motar yana kallonta da murmushinsa mai sanyi cikin wani shauqin sonta da qaunarta. 

Ji tayi duk ta daburce, kallon da yake mata duk y rikita ta, sadda kanta tayi qasa ta cigaba da tafiyar har ta qaraso inda yake sannan ta dago kanta ta kalleshi sannan ta watsa mashi harara tare da cewa "So kake na fadi kenan?". 

Da sauri yace " Kai haba ni naso ki fadi? Kawai dai ina kallonki ne saboda nasan hkn shi ne samun sukunin xuciyata". Kallonshi tayi ta rasa inda yake zaro kalamai hk. 

Kauda kai tayi sannan tace "Tohm ka kirani gani naxo". Dan shiru yayi na dan lokaci sannan ya dan tako xuwa gabanta ya tsaya yana kallon kyakkyawar fuskarta. 

A hnkali cikin muryarsa mai dadi ya fara magana yace " Deejah baki amince da soyayyata ba har ynx? Deejah soyayyarki nema take ta zautani, ban taba son wata 'ya  mace kamar ynd nake sonki ba, kin xame min jini da fata, kece kadai muradin xuciyata, ke xuciyata take mararin xama da ita a matsayin abokiyar rayuwata ta har abada, na plx don Allah ki amince da soyayyata ko xuciyata ta samu sassauci akan radadin da take."

Sosai kalamansa suke ratsa dukkanin jijiyoyin jikinta, runtse idonta tayi a hnkl sannan ta bude ta kalli Ahmad daya tsareta da oily eyes dinshi, ji tayi duk yayi mata kwarjini, bata san lokacin da bakinta ya ffurta "Ahmad bawai sonka ne banayi ba kawai ina tunanin ko na fara sonka dole xamu hkr da juna". 

Da sauri Ahmad yace " Saboda me kika fadi hakan?". Khadeejah tace "A family dinmu auren xumunci ake yi mana, ko na fara sonka nasan dole xamu rabu". Shiru ya danyi na wani lokaci xuciyarsa na masa xafi, shi kam sam baxai iya rayuwa ba Khadeejah ba domin kuwa sonta ya mamaye dukkanin xuciyarsa. 

Kallonta yayi sannan yace " Deejah ke kinason Auren xumunci?". Girgixa kai tayi tare da cewa "Wllh ban taba sha'awar auren xumunci ba".  Ahmad yace " To miyasa ake son yi maki shi bayan sunsan aure anayinshi ne don a samu kwanciyar hnkl meyasa ke xa'a sanyaki cikin tashin hnkl?".

Shiru tayi don maganar Ahmad gsky ne, idan har akayi mata auren xumunci to tamkar rabata da farin cikinta akayi, to amma ya xasuyi? Don ita kanta ta tabbatar ma xuciyarta ta fara son Ahmad....     _Beelybadaru😍_```
[1/13, 8:03 AM] Beelybadaru😍: 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
*SHI KADAI NAKE SO*
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
           ✨✨✨
              ✨✨
                 ✨

✨By Beelybadaru😍✨

       ✨16 to 20✨

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

```Da sauri ta dago kai ta kalleshi sai dai sam ta kasa yi mashi magana, ganin hakan yasa ya cigaba da cewa "Khadeejah soyayyarki ta shiga xuciyata ba tare da ta nemi ixinina ko ixininki ba, cikin kwana biyu sanki yayi xurfi a cikin xuciyata, ta yadda bana tunanin xan kasance cikin farin ciki idan na rasa ki". 

Ganin bata da abinda xata fada hakan yasa ta juya ta fara tafiya da niyyar shiga gida, cikin wata murya ya kira sunanta da " DEEJAH". har cikin xuciyarta taji kiran, a hankali ta waigo ta kalleshi, murmushi ya sakar mata, bata san lokacin da itama ta mayar masa ba, sannan ta jya tayi cikin gida, hakanan ta tsinci kanta cikin farin ciki. 

Binta yayi da kallo har ta shige ciki sannan ya danyi murmushi ya shiga motarshi yaja ya bar gidan da niyyar wataran xai dawo har ya shawo kanta. 

✨WAYE AHMAD ABDULLAH✨

Mahaifinsa maxaunin Kaduna ne shima, kasuwanci ne sana'arsa yana da kudi sosai kuma yana taimakon al'umma, matarshi daya mai suna Hjy Zainab, su uku ne a gurin iyayensu, Ahmad shi ne da na fark wajen iyayenshi, a nan qasar yayi karatunshi na secondary ya tafi qasar Jordan yayi karatunsa na degree da masters shima duk a a fannin kasuwanci, a halin ynx yana da shekara 29 a duniya kuma kyakkyawa ne shi sosai, sai kuma qaninsa mai suna Farouq, da kuma autarsu Asiya, wadda suke kira da Asy. 

Wannan kenan. 

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Khadeejah tana shiga dakinsu ta xarce ba tare da tasan da xamansu Ayusher a falon ba, tana shiga ta kullo qofar tare da jingina jikinta ta lumshe idonta a hankali ta bude, ga mamakinta sai ganin Ahmad tayi a gabanta yana mata wannan murmushi nasa mai rikitata, da sauri ta rintse idonta ta sake budewa sai dai bata ganshi ba, dafe kanta tayi tare da cewa "Ahmad me kayi min ne da nake tunaninka?". 

Ranar dai haka ta wuni sukuku duk tunanin Ahmad ya cika mata xuciya ta rasa meke damunta. 

_Washe gari_
             Tana xaune a dakinsu sai ga Ayusha ta shigo, har ta xauna gefenta bata san ta shigo ba don tayi nisa cikin tunanin Ahmad. Dafata tayi, a firgice ta dago kanta don bata san da xuwanta ba ganin Ayusha ce yasa ta sauke ajiyar xuciya.  

Ayusha tace " Sis wai me yake damunki? Tun jiya naga duk kin chanja". A hnk ta kalleta sannan tace "Babu komai sis". Ayusha tace " Banyarda ba gsky, ynx dama akwai abinda xaki iya boyemin sis? Karki mnt fa nice abokiyar shwararki kanar ynd nima kike abokiyar shawarata". 

Khadeejah ta dago ta kalleta bata da xabin daya wuce ta sanar da ita damuwarta, nan ta fada mata tun farkon haduwarsu da md har xuwa jiya da yaxo gidan. Ayusher ta danyi shiru can tace "To amma sis kina ganin xa'a barki ki auri bare? Bayan kinsan auren xumunci akeyi a family dinmu". Khadeejah ta dan mararaice fuska sannan tace " Nima abinda nake tunani kenan, shiyasa bana so na fara son Ahmad". 

Ayusha tace "Ai ki yarda kawai kin fara son Ahmda, duk da ban taba soyayya ba amma nasan kin fara sonshi". Da sauri tace  " Kai haba ni ban fara sonshi ba". Ayusher ta miqe tare da cewa "To ynx dai kixo Qawarki Ummu taxo". Da sauri ta miqe tana cewa " Allah sarki My Ummu nayi missing dinta, nan ta miqe suka fito falon tare da Ayusha. 

Tana fitowa Ummu ta miqe da sauri sujayi hugging juna cike da farin ciki don sun dan jina vasu hadu va saboda tafiyar da Ummu tayi na sati biyu. (Ummu qawar Khadeejah ce tun suna primary har xuwa secondary, haka kuma islamiyarsu daya, a unguwa daya suke xaune.)

Suka sake juna sannan suka xauna Khadeejah na cewa "Besty nayi missing dinki, yaushe kuka dawo?". Ummu tace " Wllh nima nayi missing dinki bestyna, jiya muka dawo ban kuma samu kiranki ba shiyasa naxo yau". 

Nan suka bige da hira Ayusha ta kawo mata abinci da drinks, suna cikin firar Hjy Waliyyah ta fito, nan Ummu ta gaisheta cikin ladabi, ta amsa da  fara'a a fuskarta tace "Lpylow Ummu ya maman taki take?". Ummu tace " Lpylow take tace a gaisheki ma". Umma tace "Ina amsawa sosai". Nan ta wuce dakin Abba don gyarawa saboda yau xai dawo daga tafiyar da yayi ta sati biyu.

2 days later

Tana xaune a falo kamar kullum su Ayusher suna schl don ranar Thursday ne ita ta gama tun last year, Ayusha ce take Ss3 ynx, wayarta da je gefe taji tana ruri, dubawa tayi taga new nmbr, sai data kusan katsewa sannan ta daga, ji tayi ance " Plx i fito waje ina qofar gidanku". Kafin tayi magana aka kashe wayan. Mamaki ya cikata wanene wannan da xaiyi mata wannan kiran? Sai dai kuma taji muryar kamar ta santa, to muryar waye?. 

(Ni kam nace ki tambayi kanki ko kije ki gani, wata harara ta watsomin ba shiri na bar gurinπŸ˜„)
    _Beelybadaru😍_```
[1/14, 8:13 AM] Beelybadaru😍: 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
*SHI KADAI NAKE SO*
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
           ✨✨✨
              ✨✨
                 ✨

✨By Beelybadaru😍✨

     ✨26 to 30✨

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

```Ahmad ya cigaba da cewa "Plx Khadeejah ki sanar dasu cewa kina da masoyin da xai iya mutuwa idan ya rasaki, ki sanar dasu kina da masoyin da xai iya aikata komai saboda sonki, ki sanar dasu kina da masoyin da yake maki so na haqiqa, Deejah in na rasaki bansan ya rayuwata xata kasance ba". 

Dagowa tayi ta kalleshi abinda ya bata mamaki shine ganin hawaye kwance a fuskarsa, sosai jikinta yayi sanyi wani irin sonsa na qara shiga xuciyarta, ya xatayi da aqidar famiy'n su? Ita kam gsky tana son Ahmad amma bata san ya xata fuskanci iyayenta da wannan maganar ba. 

Ahmad ya kalleta sannan ya cigaba da cewa " Deejah idan suna tunanin bare xai cucesu ne yasa basa aurar da ya yansu ga bare, plx ki fada masu wllh ni bani da niyyar cutar dake ko kadan, sonki nake tsakani ga Allah". 

Khadeejah ta dago ta kalleshi da raunannun idanunta da suke niyyar xubar da qwalla tace "Ahmad nima ina sonka amma bansan yaxan in fuskanci iyayena da wannan maganar ba". Sanyi yaji a ranshi jin tace tana sonsa, a hnkl yace " Kin tabbata kina sona?". Gyada masa kyai kawai tayi alamar "Eh".  Zaiyi magana kenan sukaji an kwala ma Khadeejah kira. 

Da sauri ta waiga don ganin ko waye. Yah Mu'azzam ta gani tsaye jikin motarshi, yaushe ya dawo daga tafiyar tasa? Tambayar da xuciyarta ke mata kenan. Kallon Ahmad tayi tace " Ahmad yayana ya dawo munyi waya". Tana kai nan bata jira jin amsarsa ba ta wuce da sauri xuwa wajen Yah Mu'azzam don tasan hali. 

Tana xuwa ta tsaya dan nesa dashi tana cewa "Lah Yah ashe ka dawo?". Watsa mata banxan kallo yayi sannan yace " Da ban dawo ba kin ganni?". Tabe baki tayi a ranta tace "Ai fa ka dawo kenan ynx xaka takura ma mutane". 

Kafin ta sake yin wata magana sai ga gani tayi wani kyakkyawan saurayi ya fito daga motar, suna dan yanayi da Yah Mu'azzam hakan ya bata tabbacin shima dan uwa ne, don ita ba sanin su tayi ba sosai don ko anxo family meeting ba tsayawa take kallon mutanen ciki ba. 

Ji tayi Yah Mu'azzam na cewa " Baki ganin yayanki baxaki gaishe shi ba?". Qara kallonshi tayi taga sai wani shan qamshi yake ta dan tabe baki kadan sannan tace "Ina wuni Yah". Sai da ya jima sannan ya amsa da " Lafiya". 

Wucewa tayi cikin gidan ba tare da ta sake cewa komai ba, suma suka shiga cikin gidan. Ahmad kuwa yana nan tsaye har lokacin yana kallonsu, ji yayi ranshi ya baci ganin ynd ake ma Deejanshi kallon wulaqanci duk da bai san ko suwaye ba, amma kamanninsu ya tabbatar mashi da cewa en uwanta ne, take yaji ranshi ya dagule da ya tuna da auren xumunci ake yi masu, jiki a sanyaye ya shiga mota ya ja , gate man ya bude masa gate ya fice daga gidan. 

Suna shiga ciki Umma dake xaune a kan kujera tana kallo a kallesu, fadada fara'arta tayi tana cewa "Wa nake gani haka kamar SAIFULLAHI?". Dan murmuahi yayi ya gaishe da ita bayan ya xauna kan daya  cikin kujerun da suke falon. Amsawa tayi da fara'a sannan tace " Yaushe ka dawo qasar wannan xuwan baxata haka?". Saif yace "Wllh jiya na dawo shi ne yau nace bari naxi na gaishe da Auntyna". Umma tace "Aikam naji dadi sosai". Ta waiga ta kalli Khadeejah da ke niyyar shiga daki tace "Khadeejah xoki kawo ma yayanki drink mana". 

Juyowa tayi ba don taso ba ta wuce kichen ta bude fridge da dauko lemo ta dora a faranti da cups guda biyu sannan ta kawo masu ta ajiye a saman qaramin dining din dake tsakiyar falon ta tsiyaya masu a cup ta miqa masu, Saif ne kadai yayi mata godiya, juyawa tayi ta  dakinsu, Saif ya bita da idanuwa har ta shige sannan ya sauke idanuwanshi daga kallonta. 

   _Beelybadaru😍_```
[1/16, 5:18 PM] Beelybadaru😍: 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
*SHI KADAI NAKE SO*
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
           ✨✨✨
              ✨✨
                 ✨

✨By Beelybadaru😍✨

      ✨31 to 35✨

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

```Tana shiga daki ta turo qofar ta rufe sannan ta xauna gefen gado, nan take tunanin Ahmad ya fado mata a rai, wayarta ta jawo ta duba nmbr dinshi da ya kirata daxu, murmushi tayi sannan ta shiga don yin saving, tunanin sunan da xata sanya mashi ta shiga yi, a ranta tace "My honey, girgixa kai tayi no My reality, ta kuma cewa A a Habeeby.

Dan murmushi tayi tayi saving da Habeeby sannan ta daga kamar xata kirashi sai kuma ta fasa, data daga xata kira sai kuma ta fasa, a na hudun ne xata kira kenan sai gashi ya kirata, murmushi ta saki sai da ta kusan tsinkewa sannan ta daga, sauke ajiyar xuciya yayi sannan yace " Deejah basu yi miki komai ba ko?". Cikin rashin fahimta tace "Suwaye? Me xasu yimin?". 

Ahmad yace " Yayyanki mana naga kamar suna miki wani kallo". Murmushi tayi tace "Basuyi min komai ba Yaya, duk yayyena ne su". Ajiyar xuciya y sauke tare da cewa " Deejah bamu gama magana ba kika tafi, ya xa'ayi?". 

Dan jim tayi sannan tace "Yau Abba xai dawo sai dai wani satin". Da sauri yace " What? Har wani satin Deejah? Kinsan fa baxan iya jurar rashin ganinki ba". Ajiyar xuciya itama ta sauke ita kanta baxata iya jurar rashin ganinahi ba har na sati sannan tace "Tohm shikenan kaxo gobe in Allah ya kaimu ama karka shigo cikin gidan ka tsaya daga waje sai naxo". 

Murmushi yayi sannan yace " Yawwa Allah ya kaimu lpy". Ta amsa da "Ameen". Sun jima suna fira daga bisani suka katse wayan ba don sunso ba, bata jima da gama wayan ba sai gasu Ayusher sun dawo. 

Dakin ta shigo ta jefar da jikkarta kan gado da qaramin hijabinta itama ta fada kan gadon tana "wash Allah na gaji sosai". Harararta Khadeejah tayi sannan tace " Ke kullum gajiya, sai kace a qafa kuke dawowa". Miqewa tayi daga kwanciyar tace "Allah big sis baki ji ynd na gaji ba, ga yunwa inaji". 

Khadeejah tace " Ai sai kiyi kiyi wanka sai kiyi sallah kici abincin". Tashin tayi ta dauki towel ta cire uniform din sannan t fada toilet don yin wanka. 

Washe gari wajen 11 Abba ya tafi wajen aiki, Su Ayusha kuwa suna makaranta, ya rage daga Umma sai Khadeejah, sai kuma su Yah Mu'azzam da suje can bangarensu. Wayarta ce ta hau ruri tana dubawa taga Ahmad ne, murmuahi tayi sannan tayi pckng, sallama tayi bayan ya amsa yace "Gani a qofar gidanku Deejah". A hnkl tace " Toh ganinan xuwa". Katse wayan tayi ta miqe ta gyara fuskarta ta sanya hijab dinta sosai tayi kyau. Fitowa tayi tana leqe taga ko ba kowa a falon, taci sa'a kuwa babu kowa. 

Har ta kai bakin qofa taji kamar motsin Umma da sauri ta waiga tana cigaba da tafiyar, ji tayi gab tayi karo da wabi abu, da sauri ta durqushe tare dafe goshinta cike da jin xafi, da sauri shima ya duqa a gurin tare da dagota, juyowa tayi ta kalli ko waye, Saif ta gani a gabanta shima yana dafe da goshinsa. 

Ji tayi ranta ya baci tayi saurin miqewa tana dan goge jikinta duk da tiles ne a gurin, kallonta yayi ya wulaqance sannan yace "Bayan tafiyana kin samu ciwon ido ne da har yasa baki ganin hanya baki ganin mai tahowa?". 

Tuni ranta ta qara baci ta dago ta watsa mashi harara sannan tace " Ashe bakaji labari. Ba? Na dauka ka sani ai, ince karatun dr kayi don kaxo kayi min magani". Sosai kalamanta sukayi mashi xafi, kamarshi ita yari ya qarama xata a baqar magana? Lallai dole yayi maganinta, amma yasan me xaiyi. Dan murmushin mugunta ya saki sannan ta raba ta gefenta ya shige cikin gidan. 

Binshi tayi da harara sannan taja dogon tsaki ta nufi hanyar fita. Can gefen gidan ta hangoshi jingine jikin motarshi, murmushi mai sanyi ya sakar mata lokci daya taji duk bacin ranta ya kau, itama murmushin ta sakar masa, har ta iso bai daina kallonta ba, sai da ta  ta dan harareshi tace "Why u looking me like dat?". 

Dan murmushi yayi tare da cewa " Nayi laifi ne?". Hararar ta kuma yi masa ba tare da tace komai ba, murmushi yayi yace "Ai banyi laifi ba don na kalleki ko ba haka ba MAI KYAU? (Mr smilesπŸ˜ƒ)". Kallonshi tayi ganin ynda bai gajiya d murmushi tace " Wai meyasa kai baka gajiya damurmushi?"murmushin y kumayi sannan yace "Kema meyasa bakya gajiya da harara?"  Hararar tashi  kumayi xatayi mgn kenan sai ganin motar Abbansu tayi y nnkaro inda suke....... 
    _Beelybadaru😍_```
[1/17, 8:04 PM] Beelybadaru😍: 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
*SHI KADAI NAKE SO*
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
           ✨✨✨
              ✨✨
                 ✨

✨By Beelybadaru😍✨

        ✨36 to 40✨

_I dedicated this page 2 u Muhtasyn._

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

```Zaro ido tayi tana kallon motar jikinta har wani kyarma yake, Ahmad da mamaki yake kallonta sannan ya maida kallonshi ga inda take kallo. Wani mutum ya gani sunyi kama da ita hkn ya tabbatar masa da cewa Abbanta ne ko kuma wani babba nata.

Fitowa Abba yayi daga cikin motar ya nufo inda suke fuskarshi a daure, Cikin kidima Khadeejah ta fara ja da baya cike da tsoro take fadar "Na shiga ukku Ahmad Abba ne". Cikin muryar kuka take fadar hakan, sosai yake jin kukan nata na taba xuciyarshi amma bashi da yadda xaiyi ne. 

Abba ya qaraso gurin ya kallesu da bacin rai ya kira sunan Khadeejah, a tsorace ta daho kanta tana kallon Abban nata, cikin tsawa yace " Wuce ki shiga gida". Ai kafin ya rufe bakinsa ma tuni ta wuce cikin gidan da gudu. Ya waiga ya kalli Ahmad da ke tsaye shi kanshi sai da gabanshi ya fadi da Abba yayi ma Khadeejah tsawa, Abba ya sassauta murya sannan yace "Amma dai kai baqo ne a garin nan ko?". 

Ahmad ya dan sadda kai yace " Abba cikin garin nan iyayena suke amma ban jima da dawowa qasar ba". Abba ya jinjina kai sannan yace "Miye tsakaninka da Khadeejah?". Cikin jin kunya ya sunjuyar da kansa qasa sannan yace " Abba.... Sai kuma ya kasa fada, Abba yace "Tambayarka nake". Daurewa yayi yace "Abba sonta nake". 

Abba ya kalleshi sannan yace " Amma bata fada maka qa'idar family dinmu ba?". Yace "Abba ta fada min, amma Abba....... ".  "Look," Abba ya dashi sannan yace "To kuma mi ya tsayar da kai bayan kasan ta fada maka yadda tsarin family dinmu yake?".

Dago da kanshi yayi idonshi har ya kada yace " Abba don Allah ka tausaya min wallahi ban iya rayuwa babu Khadeejah". Wani kallo Abba yayi masa sannan yace "Da ba rayuwa kayi ba kenan?". Shiru Ahmad yayi xuciyarshi na mashi xafi, a hnkl yace " Abba ba tun ynx nake son Khadeejah ba na dade ina dakn sonta a cikin xuciyata shekaru da dama da suka wuce, Abba......" 

Daga masa hannu Abba yayi tare da cewa "Bana son dogon xance, ina so in sanar da kai wani abu, Khadeejah na riga nayi mata mijin aure don hk kar na sake ganinka a qofar gidan nan". 

Yana kai nan ya juya ya wucewarsa Ahmad wasu hawaye suka xbo masa masu xafi dafe saitin xuciyarsa yayi jin xafin da take masa, a hnkl y bude motarshi ya shiga, sai da ya jima a ciki da yaji ya dan samu relief sannan ya tada mota yabar qofar gidan.

Khadeejah kuwa tana shiga gidan da gudu ta nufi dakinsu, har ta wuce Saif dake xaune a falo bata sani ba, tabe baki yayi ya cigaba da kallonsa. Tana shiga ta fada kan gado kuka mai qarfi ya kucce mata, meyasa Abba xaiyi mata haka? Meyasa baxai barta ta auri wanda take so ba? Ita kam gsky ba xata auri kowa ba sai Ahmad domin shi xuciyarta ke so. 

Abba kam yana shigowa bai bi ta kan Khadeejah ba, ganin Saif da yayi ya manta da abinda xaiyi ma Khadeejah, fadada fara'arshi yayi tare da cewa " Saifullahi yaushe ka dawo?". Murmushi Saif yayi yace "Abba tun shekaran jiya na dawo, jiya kuma naxo baka nan". Abba yace " Ayya jiya nayi tafiya ne shiyasa". Nan Saif ya gaishe da Abba, Abba yana tambayarshi mutan gida yace duk suna lpy. 

Abba ya miqe xai shiga daki ya waiga ya kalli Saif yace "Am kai kadai kake xaune ina khadeejah ne? Ba sai ta taya ka fira ba?". Saif yace "Ynx naga ta shigo ta shiga dakinsu". Abba ya daure fuska sannan ya hau qwala ma Khadeejah kira. 

Tana daga daji taji kiran Abba, gabanta ya shiga faduwa ta tashi da sauri ta sauko qasa tana amsa kiran, abinda tayi tunani bashi Abba yace ba, ji tayi yace " Ya xaki bar yayanki shi kadai baxaki xauna ki taya sa xama ba?". Kallon Saif tayi da yake ta faman murmushin da shi kadai yasan manufarsa, ranta ya baci sosai shi baxai iya xama shi kadai ba?. Muryar Abba ta tsinkaya yana cewa "Oya maxa xauna ki taya sa fira" xaman tayi ba don taso ba shi kuma Abba ya wuce dakinsa. 
  _Beelybadaru😍_```
[1/19, 10:28 AM] Beelybadaru😍: 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
*SHI KADAI NAKE SO*
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
           ✨✨✨
              ✨✨
                 ✨

✨By Beelybadaru😍✨

      ✨41 to 45✨

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

```Ahmad kuwa Allah ne kadai ya kaisa gida lpy don driving din kawai yake baya cikin hayyacinsa, yana xuwa ko gyara parking bai yi ba ya fito daga motar ya nufi cikin gidan yana dafe da saitin xuciyarshi, a falonya tarar da  Mummynshi xaune tana kallo sai Asy dake gefenta tana charting, binshi sukayi da kallon mamaki. 

Shi sam bai ma lura dasu ba ya kama hanyar shiga dakin Mummynshi don bai ma nufi part dinshi ba, da sauri Mummy ta taroshi tare da riqo hannunsa tana mai cewa "Ahmad me yake damunka haka?". Kasa yi mata magana yayi sai dai ya kuma nufar hanyar shiga cikin dakin, taimaka masa tayi har xuwa cikin dakin ya kwanta kan gado yana maida numfashi sama2 don ji yake kamar xuciyarshi xata faso, lokaci guda kuma xaxxabi mai xafi ya sauka a jikinsa. 

Sosai Mummy ta rikice ganin dan nata cikin wannan halin, Asy ma ta kasa xaune ta kasa tsaye hankalinta duk ya tashi, Mummy ta kira Daddy a waya ta sanar dashi halin da Ahmad yake ciki, nan take yace mata gashi nan xuwa da Dr. Ba'a jima ba sai gasu sun iso, nan Dr ya shiga duba Ahmad. 

Bayan ya gama en dube dubensa yayi masa Allurar barci nan take bacci ya kwasheshi sannan ya kalli su Daddy yace " A gsky y kamata ku ringa kula da abinda danku yake so, ya xama dole ku bashi abinda yake so domin kuwa xuciyarshi tana gab da kamuwa da ciwo". 

Cike da tashin hnkl Daddy ya kalli Mummy yace "Hajiya akwai abinda Ahmad ya nema ya rasa ne?". Girgixa kai tayi tare da cewa " Gsky babu sai dai ko can waje yake son wani abun". Daddy ya jinjina kai, ya kalli dan nasa da yake barci sannan ya fita shi da Dr yana bashi shawarwari akan a kula da Ahmad a dinga bashi duk abinda yake so sannan kuma ya daina sa damuwa a ranshi ya kuma rage tunani. 

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

_2 days later_

Abba ya kira Khadeejah da Saifullahi da sauran en gida baki daya ya sanar da ita cewa yayi mata miji, sosai ta firgita da kalaman Abbanta cikin rawar murya tace "Abba waye mijin daka xaba min?". Abba yace " Saifullahi ne domin kuwa shi da bakinsa ya fada min cewa kun sasanta tsakaninku". 

A firgice ta miqe tana girgixa kai hawaye ha sun fara xubo mata, cikin muryar kuka tace "Abba wallahi bana son Yah Saif, kuma shima sam baya sona ko kadan, Abba Ahmad shi ne rayuwata wllh *SHI KADAI NAKE SO* Abba ka taimaki rayuwata ka barni na auri wanda nake so". 

Wani wawan mari Abba ya dauketa dashi wanda har si data duqe a gurin tana kuka Ayusha tayi saurin riqota itama tana hawayen, Abba ya nunata da yatsa yace " Baki isa ki chanja tsarin family din nan ba , dolenki kibi umarnina kamar ynd kowace 'ya take bi, qarshen watan nan xan kira Daddy in sanar dashi komai, sannan xan kira Abba na Kaduna(Mahaifin Saifullahi) na sanar dashi komai axo a sanya rana". 

Wani kukan ne ya qara xuwar mata, ta miqe da gudu ta bar falon ta wuce dakinsu kai tsaye ta fada kan gado tana wani irin kuka mai ban tausayi a ranta tana cewa "Allah sarki Ummana nasan da ace kina raye da baxaki bari ayi min auren dole ba". Nan ta cigaba da kukanta soyayyar Ahmad na qara shiga xuciyarta, sai ynx take jin baxata iya rayuwa babu Ahmad ba. 

Bangaren su Abba kuwa, Khadeejah na fita Umma ta kalli Abba tqce " Alh kabi yarinyar nan a hankali mana, ba haka ya kamata kayi mata ba". Daga mata hannu yayi tare da cewa "Kinga Waliyyah kiyi min shiru, ita qaramar yarinya ce da kullum sai anyi mata bayani? Dolenta ta amince da auren nan". Yana kai nan ya fice ransa a bace. 

Saifullahi kuwa lokaci guda yaji son Khadeejah ya dirar masa a xuciya wanda baya jin xai iya haqura da ita. Ayusha ta miqe ta watsa ma Saifullahi harara ta wuce xuwa wajen er uwarta, suma su Aliyu banxan kallo sukayi masa sanna suka fice daga falon cike da jin haushinsa. Shi kuwa tabe baki yayi a ransa yace "koma dai me xakuyi kuyi tayi ni dai kam baxan iya haqura da Khadeejah ba..... "
   _Beelybadaru😍_```
[1/20, 3:23 PM] Beelybadaru😍: 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
*SHI KADAI NAKE SO*
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
           ✨✨✨
              ✨✨
                 ✨

✨By Beelybadaru😍✨

      ✨46 to 50✨

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

```Sosai Khadeejah ta shiga damuwa da hukuncin da Abba ya yanke a gareta, tsanar Saifullahi qaruwa take cikin xuciyarta, yayinda soyayyar Ahmad ke qara xurfafa cikin xuciyarta. 

Wayarta ta jawo ta shiga gallery, pixs din Ahmad ta gani wanda ya turo mata da suna chatting, sun kai kusan 20, nan ta shiga kallonsu tana share hawayen dake kwaranya a idanunta, Umma ce tayi sallama ta shigo dakin, xama tayi gefen gadon da Khadeejah ke kwance, ta kalli Khadeejah da bata san da shigowarta dakin ba, dafata tayi a firgice ta dago tna kallon Umma, sauke ajiyar xuciya tayi ta shiga share hawayen dake fuskarta. 

Umma tace "Haba Khadeejah miye na wannan kukan? Meyasa kika fara soyayya da ani bare bayan kinsa auren xumunci akeyi a family din nan?". Kallon Umma tayi da raunannun idanuwanta tace " Umma ya xanyi? Nima bansan ya akayi na fara sonshi ba, Umma meyasa Abba xaiyi min haka? Meyasa baxai barni na auri wanda nake so ba?". Kuka sosai ta fara yi, Umma ta jawota ta rungumeta tana rarrashinta kamar diyar data haifa. 

(Tabdi a ynx kuwa xa'a samu kishiyar da xatayi ma 'ya'yan kishiyarta haka? Gsky ko xa'a samu kadan ne)

Bayan kwana biyu

In kaga Khadeejah sai ka rantse da Allah ba ita bace, duk ta rame ta daina walwala, abinci ma sai Umma ta takura mata sannan take ci, sosai en uwanta ke tausayinta, kullum bata da aiki sai na kuka don kuwa Abba ya kwace mata waya balle tasamu ta ringa waya da Ahmad. 

*AHMAD*

Yasha ciwo sosai duk ya rame, Ahmad mai yawan murmushi ynx sam babu shi, duk ya koma kalar tausayi, maimakon yaji ya rage son Khadeejah sai ma ji yayi snta na qaruwa cikin xuciyarsa, bashi da aiki a kullm sai na kallon Hotunan Khadeejah da kuma kiran wayarta sai dai sam baya samunta, duknya shiga damuwa, kuma a matse yake da sin ganinta, kullum sai yayi hawaye Mummynshi har mamakin irin son da yake ma Khadeejah take. 

*KHADEEJAH*

Ji tayi in bataji muryar Ahmad ba xata iya rayuwa ba hakan yasa ta nufi dakin Umma ta isketa xaune gefen gado,  itama xuwa tayi ta xauna tare da cewa "Umma don Allah ki aramin wayarki xan kira Ummu mun dade bamu hadu ba". Ba musu Umma ta dauko wayar ta miqa mata, godiya tayi sannan ta fita daga dakin ta nufi dakinsu ta kulle ta shiga toilet shima ta kulle sannan ta sanya nmbr Ahmad ta fara kira, sai da tayi masa  wajen 4missed call bai daga ba, ji tayi kamar ta fasa  ihu don bakin ciki, amma ta daure ta qara kiranshi. 

Bangaren Ahmad kuwa yana ganin kiran yaqi dagawa ganin new nmbr ce, ko kadan bayaso a dameshi idan yana tunanin Khadeejah, ganin kiran ya qara shigowa yasa ya dauki wayan rai a bace ba tare da yi mgn ba. 

Tana jin ya dauka tace " Habeeby". Ai kamar wanda aka mintsina ya miqe da sauri cike da farin cikin jin muryar Khadeejah shima yace "Habeebty". Lumshe idonta tayi jin muryar Ahmad da tayi sannan ta bude tace " Habeeby na shiga damuwa sosai dalilin rashin ganinka da nayi na kwanakin nan, Habeeby xuciyata nema take ta tarwatse a dalilin sonka". 

Lumshe idonshi yayi hawaye har sun fara xubo masa sannan ya bude yace "Habeebty kinsan kuwa halin dana shiga lokacin da Abba yace min yayi maki miji?, Habeebty TA DALILIN SO(Waliyyah 'Wally')nki xuciyata na neman kamuwa da cuta, soyayyarki ta mamaye dukkanin xuciyata, tinaninki shine abincina, bani da sukuni ko kadan, ta yaya xan ganki Khadeejah?". 

Shiru ta danyi na wani lokaci sannan tace " Abba ya qwace wayana sannan ya hanani fita, ya xanyi Habeeby?". Cikin muryar kuka take maganar. Ahmad yace "Plx Deejah don Allah xanxo wajen gidanku plx ko leqowa ne kiyi na ganki". Gyada kai kawai tayi tare da cewa " Shikenan xansan yanda xanyi", yace "Yawwa ABLA sai nazo". 

Yana fadar haka ya smkashe wayar, bin wayar tayi da kallon mamaki, ABLA?  a ina yasan wannan sunan? Ita dai ta tabbata mutum daya ne ya santa da wannan sunan kuma shi ya sanya mata sunan tun suna primary schl ita kuma tana kiranshi da ABUL, amma ya akayi Ahmad yasan sunan? Ya xama dole ta tambayeshi inda yasan sunan.... 
   _Beelybadaru😍_```
[1/21, 8:48 AM] Beelybadaru😍: 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
*SHI KADAI NAKE SO*
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
           ✨✨✨
              ✨✨
                 ✨

✨By Beelybadaru😍✨

      ✨51 to 55✨

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

```Tashi tayi ta fada toilet tayi sabon wanka sannan ta fito ta shirya cikin riga da sket na atamfa ta sanya hijab, tayi kyau sosai, tana gama shirin wayar Umma tayi qara nan tayi saurin dubawa ta dauka, kafin tayi magana Ahmad yace "Ina nan qofar gidan plx ki fito". Ta amsa mashi da "to". 

Duba wayan tayi ta goge nmbr Ahmad sannan ta kira Ummu gudun kada Umma ta ganeta, sun danyi hira kadan sannan ta yanke wayar. Ta miqe ta fito daga dakin cikin sanda, bata tarar da kowa ba a falo hakan yasa ta fita da sauri tana waige dama Ayusher bata nan tana gidan Hajiya mama(Kakarsu) su Aliyu kuwa suna yawonsu. 

Tana fita ta iske mai gadi baya wajen gate din hakan yasa ta sauke ajiyar xuciya ta bude da sauri ta fita, tun daga nesa ta hangoshi tsaye jikin a, tun kafin ta qarasa yake ta faman murmushin farin ciki, sosai yake jin Khadeejah cikin xuciyrshi. 

Tana qrasowa ta bude motar ta shiga shima shigar yayi, ta kalleshi cike da shauqin so da kuma kewarsa, shima ita yake kallo, duk sun rame kamar wadanda sukayi ciwon shekara, kallonta yayi da raunannun idanunsa sannan yace " Abla nayi missing dinki sosai, Deejah bana tunanin xan iya rayuwa ba tare da ke ba". 

Sosai ta kalleshi sannan tace "Habeeby a ina kasan wannan sunan?". Dan murmushi yayi ya jawo wani dan kwali ya bude ya dauko wasu hotuna guda biyu ya  mata. Amsa tayi tana dubawa ta dan waro ido waje, (Ganin hakan yasa nima na hangame kai ina son ano ma idona hotunan, wasu kyawawan yara na gani mace da namiji, macen baxata wuce 6yrs ba, shi kuma namijin baxai wuce 10yrs ba, kamarsu daya sa da Ahmad da Khadeejah, hakan ya tabbatar min da sune suna yara). 

Dagowa tayi tana kallonshi cikin rawar murya tace " ABUL kaine dama?". Gyada mata kai yayi yana murmushi, sai a lokacin ta tuna da yawan murmushin Abul lokacin da suna yara. Sosai wani sonshi ke qara shiga xuciyarta, lokaci guda ta fara tuno rayuwar da sukayi da suna yara a primary school. 

Ahmad da Khadeejah makaranta daya sukayi a nan garin Kaduna, a lokacin Khadeejah na aji 4 shi kuma yana aji 6, sosai suka shaqu da junansu, da an fito break xaki gansu tare, babu abinda ke raba su, duk makarantar babu wanda bai sansu ba wasa ma tare sukeyi, duk sanda xasu tafi gida sai sunji kamar suyi kuka. 

Daga baya ma ganin sunansu baiyi iri daya ba yasa suka sanya ma kansu suna ABUL DA ABLA tun daga lokacin suke kiran kansu da wannan sunan. Lokacin da Abul ya kammala primary dinshi, ranar sunyi kuka kamar wadanda aka aikowa da saqon mutuwa, iyayen Abul daqyar suka rabasu, jan Abul suka farayi yana tirjewa yana kallon Abla dake ta faman kuka. 

Fixgewa yayi ya ruga wajen Abla ya rungumeta cikin uryar kuka yana cewa "Abla kixo mu tafi gida tare, ni baxan sake xuwa schl ba". Itama cikin kukan tace " Abul Abbana buguna xaiyi in na bika, kullum sai yayi tamin fada wai ina yawan maganarka a gida". Abul ya dago kanshi ya kalleta sannan ya dago hannunshi yace "Abla promise me baxaki manta dani ba". Ta dora hannunta akan nasa tace " I promise u baxan manta da kai ba, kaima kayi min". Yace "Nima nayi maki". 

Dan qaramin robbon din dake kanta ta ciro ta miqa mashi tare da cewa " Ga wannan ka riqa tunawa dani". Amsa yayi shima ya ciro wani dan qaramin xoben axurfar dake hannunshi ya miqa mata yace "Nima ga wannan ki riqa tunawa dani". Amsa tayi ta sanya a hannunta, murmushi yayi mata itama ta mayar masa.

Juyawa yayi ya kalli iyayensa dake tsaye suna kallonsu da mamakin irin shaquwar da sukayi, ya kalli Abla sannan ya juya suka nufi wajen motarsu yana waigen Abla da take hawaye, shima hawayen yake yana daga mata hannu ar suka shiga mota, tafiya sukafarayi Abla ta ruga da gudu tana bin motar tana kuka shima ya fiddo kansa waje yana kallonta yana kukan, ganin sunyi mata nisa yasa ta durqushe a wajen tana kuka. 

Tun daga lokacin bata qara ganin Abul ba, haka shima don asar waje aka maidashi karatu wajen Uncle dinshi. Sai ynx da suka girma sannan suka hadu, (Nace lallai soyayyar yarinta dole xakuji xafin rabuwa da junanku.)       
    _Beelybadaru😍_```
[1/22, 12:04 PM] Beelybadaru😍: 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
*SHI KADAI NAKE SO*
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
           ✨✨✨
              ✨✨
                 ✨

✨By Beelybadaru😍✨

     ✨56 to 60✨

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

```Khadeejah ta daga kai ta kalleshi sannan tace "Abul ashe kaine? Meyasa baka qara nemana ba?, kullum da tunaninka nake barci". Dan murmuahi yayi yace " Jordan aka kaini karatu, ranar da na fara haduwa dake a super market din nan ban dade da dawowa ba". Gyada kai tayi, nan ya dauko ribbon din da ta bashi ya nuna mata, sosai take jin farin ciki, da da halin da xata shiga gida da ta dauko mashi xoben shima ya gani, don tunda yayi mata kadan ta cireshi ta boye har ynx yana nan. 

Kallonshi tayi cikin fuskar tausayi tace "Habeeby Abba ya fitar min da mijin aure kuma ni wllh bana sonshi kai nake so". A firgice ya kalleta yace " What? Meyasa Abba xaiyi mana haka? Meyasa yake neman ya ruguxa mana rayuwarmu?". 

Tuni hawaye sun wanke mata fuska tace "Bansan meyasa yayi mana hakan ba Habeeby, ya kamata Abba ya tausaya mana ya barmu mu auri junanmu, wllh sam bana son Yah Saif". Cikin tashin hnkl Ahmad yace " Miye mafita Deejah? Wllh ban iya rayuwa babu ke, mutuwa xanyi idan na rasaki". 

Da sauri tace "Ka daina fadar haka Ahmad wllh nima xan iya mutuwa saboda son da nake maka, amma ya kamata mu fawwala wa Allah dukkanin lamuranmu mu roqeshi alkhairin da ke cikin wannan abun". 

Daga hannunshi yayi sama tare da cewa " Ya Allah ka sadamu da Alkhairin da ke cikin wannan tarayyar tamu, Ya Allah ka xaba mana abinda yafi xama Alkhairi a rayuwarmu". Amsawa tayi da "Ameen ya rabbi". 

Kamar an mintsileta tayi sauri ta bude motar xata fita, hannunta ya riqo da sauri, cak ta tsaya ba tare da ta juya ta kalleshi ba, cikin wata irin murya yace " Ina xaki tafi ki barni Habeebty?". A hankali ta juyo ta kalleshi sannan ta sadda kai qasa tace "Gida xani Habeeby Abba ya kusan dawowa kuma kasan in ya dawo mun kade dagani har kai". 


Ba don yaso ba ya saki hannunta ta fita daga motar ta nufi cikin gida, sai da ta shige sannan ya sauke kanshi daga kallon da ya bita dashi, ya sauke ajiyar xuciya, yana matuqar son Khadeejah, son da baya tunanin xai iya rayuwa ba tare da ita ba, cikin sanyin jiji ya tada motar ya bar qofar gidan.


A haka kullum suke haduwa da junansu a boye a boye, sai rannan da Abba ya gansu, sunsha fada sosai wajenshi, Saif kuwa kullum qara shige mata yake shi ala dole sonta yake, tayi roqon duniya akan ya rabu da ita amma ya qiya yace lallai sonta yake da gsk baxai iya rabuwa da ita ba. 

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Tana shiga daki ta rufo qofar sannan ta jingina da qofar tare da rintse idonta hawaye masu xafi suka fara bin fuskarta, xuciyarta xafi take mata sosai, meyasa Abba yake qoqarin tarwatsa mata rayuwa? Ita kam bata jin xata iya auren kowa face Ahmad domin *SHI KADAI TAKE SO* kuma bata tunanin xata iya hada soyayyarshi data wani. Dafe saitin xuciyarta tayi tana maida numfashi da qyar don ji take kamar xuciyarta xata tarwatse. 


Ahmad kuwa yana isa gida ko gyara parking din motar baiyi ba ya fito daga motar ya shiga cikin gidan, Asy ya fara karo da ita tana niyyar fitowa, wani dishi dishi ya fara gani a falon, nan ya fara tafiya yana hada hanya,  tayi saurin riqoshi cikin tashin hnkl tace "Yaya mai ya sameka?". 

Bai iya bata amsa ba illa kallo daya bita dashi hawaye na xuba a idonsa, sosai take tausayin Yayanta don tasan duk akan soyayyar Khadeejah ne yasa ya shiga wannan halin, ta taimaka mashi har xuwa wajen kujera ya xauna yana maida numfashi da qyar. 

Mummy da Daddy suka fito daga daki cikin tashin hnkl suka isa wajen Ahmad, sosai suke tausayin dan nasu, Dadfy ya ynk shawarar xaije ya  Abbansu Khadeejah. 


Washe gari kuwa, yaje gidansu Khadeejah yayi sa'a kuwa ya samu Abba, bayan sun gaisa yake masa bayanin koshi waye da abinda ke tafe dashi na nema ma Ahmed Auren Khadeejah, ran Abba ya baci, yace dashi yayi hkr ya riga yayi mata miji. 

Duk ynd Daddy yaso ya shawo kan Abba abin yaci tura Abba sam ya toshe hhi yace bai yrd ba yayi ma Khadeejah miji, cikin sanyin jiki Daddy ya koma gida, ya fada ma Mummy ynd sukayi.    _Beelybadaru😍_```
[1/23, 12:06 PM] Beelybadaru😍: 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
*SHI KADAI NAKE SO*
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
           ✨✨✨
              ✨✨
                 ✨

✨By Beelybadaru😍✨

       ✨61 to 65✨

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Mummy ta jinjina mae2 lamarin, tausayin danta ya qara shiga xuciyarta don ta tabbata baxai iya jurar rashin Kahdeejah ba don ya riga yayi nisa a sonta nisan da sam baya jin kira. 

_Bayan kwana 2_

Abba ya sanya an hadu Family meeting, kowa ya hallara manyan Family din, anci ansha kamar  ynd aka saba, nan Abba yake fada masu abinda ya yanke, sunyi farin ciki sosai don dama suna shirin yin wannan hadin, sai dai Baban kano(Qannin Alhj Auwal Bafu)  ne yace "Ashe ka rigani da ina cewa xanyi ma jikana kamu na wajen Gwaggwansu". Abba yayi murmushi tare da cewa " Ai ynxn ma bata baci ba tunda akwai qanwarta sai ayi da ita". Duk akayi dariya. 


Nan Aka tsayar da ranar biki nan da wata biyu xa'a yi shi, Daddy ne ya bada kudin sadaki dubu hamsin(50,000) Abba na Kaduna ya bada dubu dari (100,000) na amarya idan tana buqatar wani abu da kudin jin magana, lefe kuma akace shi Saif din xaiyi abinsa, Kawu Kabiru(Dan Abba na kaduna) yace shi xaiyi ma Khadeejah kayan daki, Umma tace ita xatayi mata kayan kichen, haka dai kowa ya dinga fadar gudummuwarsa, nan kowa yayi farin ciki. 

Su Family din haka suke duk abinda xa'ayi na auren bare suma sunayinsa. Haka aka sha fira sannan kowa ya watse masu kwana suka tafi makwancinsu masu tafiya suka tafi, Umma dai cewa tayi kwana xatayi saboda yamma tayi sosai kuma bata son tafiyar dare. 


Bayan an watse da daddare suka hadu a babban falo gaba dayansu harda Umma, nan Abba yake sanar da su Khadeejah duk abinda ya faru da kuma lokacin da suka yanke na aurensu. A firgice Khadeejah ta dago ta kalli Abba cikin tashin hnkl tace "Abba don Allah....." Abba ya dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu yace "Ya isa bana son jin komai mun riga mun gama magana kuma baki isa ki chanja mana tsarin Family ba". 


Kuka mai qarfi ya kucce mata ta sadda kanta qasa tana ta faman yi, Ayusha ma tuni ta fara hawaye tana tausayin er uwarta, su Haydar ma idonsu har ya kada, Hjy Waliyyah ma tana tausayin Khadeejah sosai. 

Umma da mamaki take kallon Khadeejah dake ta faman kuka sannan ta kalli Abba tace " Wai meyake faruwa Abba, bata son Saifullahin ne kome?". Cikin bacin rai Abba yace "Tsabar wulaqanci irin nata ba, wai sai wani can bare take so". 

Umma ma ranta ya baci tace " Ji wani shashancin banxa, kinsan tsarin Family din nan amma shine  kika fara soyayya da wani bare can?". Cikin kuka Khadeey ta dago ta kalli Umma sannan tace "Umma bansan ya xanyi bane, Umma da a ynx na fara sonshi da xanyi qoqarin daina sonshi, amma Umma kinsan soyayyar yarinta wahalar fita xuciya gareta, Umma don Allah ki tausaya min kiyi ma Abba bayani ynd xai fahimce....." Wani kallo da Umma ta watsa mata ne ya sanya tayi shiru. 

Umma tace "Haka AFMA(Diyarta) ta dinga yi lokacin da xa'a hada ta aure da Abdur-Raheem, amma gashi nan ynx suna xaman lafiyarsu, don haka kema nasan xaki dawo hny ki fara son Saifullahi". Da sauri ta girgixa mata kai tace " A a Umma, bana tunanin xan iya son wani bayan Ahmad, Ahmad shi kadai ne cikin xuciyata *SHI KADAI NAKE SO*". 

Sake baki Umma tayi tana kallon Khadeejah tace "Yayi maras kunya, ke ko kunya baki ji kike fada min haka? To da kyau, aure kuma ba fashi dole ayi shi". Hajiya Waliyyah tace " Umma bai kamata ku tarar mata ba ku dinga tursasata, kamata yayi a dinga lallashi ta har ta yarda". 


Watsa mata harara tayi tace "Ita din yarinya ce da xa'ayi ta maimaita mata abu daya? Mun riga mun gama magana dole ne ta auri Saifullahi. Qara sautin kukanta tayi, nan Ayusha ta riqota tana taya ta kukan. Umma tace " To mai er uwa ku tashi ku bamu guri, baxaku xo ku tasa mu kuyi tayi mana kuka ba". 

Tashi tayi tana ganin dishi dishi, Ayusha ma ta miqe ta riqa hannunta, basuyi nisa da fara tafiya ba Khadeejah taji wani jiri ya debeta, tayi qasa luuu ta fadi, Ayusha na in tarbota ta kasa, a firgice duk suka nufo inda take kwance kamar bata numfashi, Yah Mu'azzam yace a fito da ita xuwa wajen mota, Hjy Waliyyah da Ayusha suka riqata har xuwa wajen mota aka shiga da ita nan suka xarce gaba dansu xuwa asibiti...... 
```Beelybadaru😍```
[1/25, 2:22 PM] Beelybadaru😍: 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
*SHI KADAI NAKE SO*
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
           ✨✨✨
              ✨✨
                 ✨

✨By Beelybadaru😍✨

      ✨66 to 70✨

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Suna isa aka amsheta aka wuce da ita emargency likitoci suka duqufa a kanta don ceto rayuwarta, Ayusha, Aliyu, Haydar, Hjy Waliyyah ba abinda suke illa safa da marwa, duk hankalinsu a tashe yake, can na hango Saif xaune ya dafe kanshi, Umma da Abba ma suna xaune duk sun shiga damuwa, Yah Mu'azzam ma yana daga gefe a tsaye. 

Sai da aka dau wajen 30mnts da shiga da ita sannan sai ga Dr ya fito, da sauri suka tare shi, Hjy Waliyyah tace "Dr ya jikin nata?". Dr Usman y goge fufar dake fuskarsa da Handkachief sannan ya cire safar dake hannunsa ya kallesu yace "Jiki Alhmdulilah ta samu barci ynx sai dai ina so na tambayeku". Abba yace " Muna saurarenka". Dr yace "Akwai wani abu da ta nema ta rasa ne?". Kallon juna sukayi Abba yayi karaf yace " A a Dr babu abinda ta nema ta rasa".

Dr yace "Tohm gsky ya kamata ku tambayi erku ta fada maku abinda take buqata kuyi mata shi don ta cire damuwar dake cikin ranta, don kuwa tana gab da kamuwa da ciwon xuciya". A dan firgice suka kalleshi ya gyada masu kai yana mai qara tabbatar masu da maganarshi, yana kainan ya wuce xuwa office dinshi. 

Hjy Waliyyah ta kalli Abba tace "Alh don Allah ka sama ma yarinyar nan farin ciki ka barta ta auri wanda take so". Wani kallo Abba yayi mata yace " Karki qara kawo min wannan maganar, aurenta da Saifullahi babu fashi dole ayi shi". Shiru tayi bata kuma cewa wani abu ba don tasan halin Abba, Ayusha kau tuni har ta fara hawaye saboda tausayin er uwarta. 

Bayan minti goma Dr ya basu ixinin shiga suka shiga, cikin dan qanqanin lokacin nan har ta rame tayi wani fari, har lokacin barci take bata farka ba, Ayusha ta amshi wayar Ummah(Hjy Waliyyah) ta fita daga dakin, can wani lungu ta samu ta duba nmbr Ahmad da yake tayi saving dinta nan ta kirashi bugu daya ya dauka don ya gane nmbr. 

Yana dauka yace "Habeebty hankalina ya kasa kwanciya so nake kawai na ganki". Ayusha tace " Yah Ahmad ba ita bace". Ahmad ya gane muryar hakan yasa yace "Ayusha ina Khadeejah'n?". Ayusha tace " Yah Ahmad muna nan asibiti Sis bata lpy". Cikin tashin hnkali ya miqe daga xaunen da yake yana tambayarta wane asibiti ne, nan ta fada masa har da nmbr dakin da aka kwantar da ita, kamar wani xautacce ya fito daga dakinshi ya nufi wajen motarshi duk da rashin lpyr da yake yi. 

Yana shiga ya tada ta a tsiyace, gate man yayi saurin bude masa gate ya fice da gudu, Allah kadai ya kaishi Asibitin lpy don gudu yayi ba kadan ba.


Yana isowa ko gyara parking baiyi ba ya nufi cikin asibintin duba nmbr dakin yayi, bude qofar kawai yayi ya fada, idanunsa basu sauka ko'ina sai kan gadon da Khadeejah ke kwance tana barci har lokacin. 

Bai ma lura da mutanen dake xaune a dakin ba ya nufi wajen gadon jiki a sanyaye ganin ynd Deejanshi ta koma cikin qanqanin lokacin da bai wuce 1hr ba. Duqawa yayi qasan gadon saitin fuskarta yana kallon kyakkyawar fuskarta da tayi wani fayau da ita, tuni hawaye suka fara xubo mashi a hankali ya furta "Habeebty ki tashi don Allah karki tafi ki barni". Shiru yaji ko motsa hannunta batayi, kuka ne ya kucce mashi ya riqo hannunta tare da cewa " Deejah na roqeki ki tashi karki tafi ki barni don Allah".

A hankali ta fara bude idonta  ta saukesu akan kyakkyawar fuskar Ahmad dake sharkaf da hawaye, itama hawayen ne suka fara zubo mata suka sauka akan dayan hannun Ahmad dake kusa da fuskarta , da sauri ya dago kanshi ya kalleta, wani farin ciki ya lullubeshi, murmushi ya  sakar mata itama tayi murmushin. 

Maganar Dr yaji yana cewa "Ya jikin patien din?" Waigawa yayi ya kalli Dr din sai a lokacin ya lura da mutanen dake cikin dakin, Umma Abba Yah Mu'azzam Yah Saif duk sun daure fuska, baya ma Abba da Saif da sukejin kamar su shaqo Ahmad din. 

Sakin hannunta yayi ya sadda kanshi cike da jin kunya, Abba ya daka mashi wata tsawa tare da cewa "Me ya kawoka nan? Bana rabaka da ita ba? Xo ka fice tun kafin in sassaba maka". Dr yace " Haba Alhj ka manta Patien garemu? Don Allah kuje waje kuyi maganar da xakuyi". Nan duk suka kama hanyar fita, Ahmad kuwa yana nan durqushe inda yake bai motsa ba, Dr bai damu dashi ba ya cigaba da duba Khadeejah.    
     ```Beelybadaru😍```
[1/27, 7:20 PM] Beelybadaru😍: 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
*SHI KADAI NAKE SO*
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
           ✨✨✨
              ✨✨
                 ✨

✨By Beelybadaru😍✨

      ✨71 to 75✨

_This page is 4 u Dr, Ruqayyat Umar😘_

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Kwanansu biyu a asibitin aka sallemesu ganin jikin nata yayi sauqi, Ahmad kuwa cikin kwanaki biyun nan a asibitin yake wuni duk ynd Abba yaso hanashi xuwa amma ya qiya dole ya haqura ya kyaleshi. 

Suna komawa gida ta cigaba da jinya bayan ta watsake aka fara shirye shiryen bikinta, sosai ta qara shiga damuwa, ita gani takeyi ynx Abba kwata kwata baya sonta tunda har ya xabi ruguxa rayuwarta akan farin cikin family dinsa. 

_Bayan wata daya_

Idan kaga Ahmad baxaka taba cewa shi ne ba, yayi wata muguwar rama duk ya koma wani iri yau lafiya gobe ba lafiya, su Mummy duk sun shiga damuwa, Daddy ba xuwan da magiyar da baiyi ma Abba a akan yabar Ahmad ya auri Khadeejah amma yaqi daga qarshe ma yayi xuciya ya bar maganar. 

Khadeejah ma ta rame sosai ga ciwo da take fama dashi wanda bata fada ma kowa ba don tasan ko ta fada ma a banxa tunda ba tausaya mata Abba xaiyi ba ya barta ta auri wanda take so, kullum sai tasha kuka sauqin ma suna dan waya da Ahmad da wayar Umma.

 Saif ma ynx tausayin Khadeejah yake don yana lura da halin da take ciki, sai dai yasan ko me xaiyi su Abba baxasu fasa auren nan ba, hakan yasa yayi shiru da bakinsa. 

********

Tana kwance a kan gadonta kamar kullum tana share hawaye Ayusha na gefenta tana faman lallashi itama tana matsar qwallan nata  don har ta saba. Khadeejah ta kalli Ayusha tace "Sis baxan iya rayuwa ba in ban auri Ahmad ba, Sis meyasa Abba baya sona?". 

Ayusha ta share hawayenta sannan tace "Kiyi hkr sis ki daina fadar haka, insha Allahu xaki mallaki Yah Ahmad". Wani sanyi ya ratsa xuciyata amma data tuna bai wuci sauran weeks bikinta da Saif sai taji wani bakin ciki a ranta. Ta runtse idonta sannan tace " Sis wallahi baxan iya xama da Yah Saif a matsayin miji ba, wllh ban taba jin ina sonsa ba, Ahmad *SHI KADAI NAKE SO*". 

Ayusha ta jinjina kai tare da cewa "Na sani Sis, amma ya kamata ki rage damuwa a ranki don Allah sis". Shiru kawai tayi ba tare da tace komai ba. 

🌟🌟🌟🌟🌟

Yau saura kwana biyu bikin Khadeejah da Saif, sosai hankalinta ya qara tashi ganin da gaske ake, don en uwa duk sunxo gidan ya cika maqil tun kafin ranar daurin auren, Ahmad kuwa yana can kwance ba lafiya, don ya riga ya sadaqar yasan tunda aka kawo i yanxu ya rasa Khadeejah. 

Ranar daurin aure ma kowa  yaxo sai faman hada hadar daurin aure ake, wasu en uwan su Khadeejah ne suka hau gyaranta, ita kam bama tasan sunayi ba, don kuwa tayi nisa cikin tunanin Ahmad dinta, ynx shikenan an rabata dashi? Gsky ba'ayi mata adalici ba, kwalliya ake mata amma sam ta kasa tsayar da hawayen da suke xubo mata, duk mamaki ya kama en uwan nata to bata son auren ne ko me?. 

Ganin kwalliyar baxata yuwu ba yasa suka fice daga dakin suka kira Ummah, ba'a jima ba Hajy Waliyyah ta shigo dakin da sallamarta ciki ciki ta amsa  sallamar don bata jin xata iya yin magana a wannan lokacin. 
     Ua ta xauna gefen gadon ta dafa kafadar ta tace " Khadeejah har ynx baxaki bar yawan tunanin nan ba?". 

Fashe mata tayi da kuka tace "Ummqh ya xanyi? Ynx Abba ya daina sona, Umma ki maka min ko ganin qarshe nayi ma Abul". Da mamaki take kallonta tana tuna inda ta taba jin sunan, da sauri ta kalleta tace " Kina nufin Ahmad shine Abul? Abokin yarintarki?". Gyada mata kai kawai tayi, Umma ta tausaya mata sosai ta bata tabbacin insha Allah xata dan ynd xatayi su hadu da Ahmad, sosai tayi farin ciki. 

Bangaren Ahmad kuwa yana nan kwance duk damuwa ta ishe shi burinshi a ynx bai wuce yaga Khadeejah ba, Farouk dake gefenshi wayarshi tayi  qara, nan ya dauka yaga abokinshi ne, nan ya daga, da sauri ce "What daurin quren Khadeejah kuma?.. Gaban Ahmad ya fadi don yasan Khadeejah shi ake nufi,asu xafafan hawaue suka xubo masa. 

Farouq na gama wayar cikin tausayawa ya kalli Ahmad yace "Yaya sai dai kayi hkr don ynx hk Abokina y kirani yace yn nan gidan su Khadeejah ana haramar daurin aurenta." A kidime ya kalleshi sai dai bai iya firta komai ba, ya miqe xai fita daga dakin, jiri ya kewasheshi nan ya xube a sume, cikin tashin hnkl Farouk ya fita ya a mutan gidansu nan aka daukeshi aka wuce dashi asibiti. 

Gidan su Khadeejah guda kawai ke tashi, don har an daura auren, Khadeejah dake daki jigum burinta kawai taji ance an fasa auren sai ji tayi ana guda ana cewa "An daura aure". Kanta taji ya juya lokaci guda ta fara ganin dishi dishi nan ta fadi sumamma, itama cikin tashin hnkl aka kwasheta aka nufi asibiti da ita. 

😭😭😭 Wayyo Ahmad wa Khadeejah


 
```Beelybadaru😍```
[1/31, 10:42 PM] Beelybadaru😍: 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
*SHI KADAI NAKE SO*
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
           ✨✨✨
              ✨✨
                 ✨

✨By Beelybadaru😍✨

       ✨76 to 80✨

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Asibiti guda aka kaisu, dakin Ahmad yana kusa dana Khadeejah, kowannensu bai san inda kanshi yake ba, familyn biyu duk sun shiga damuwa, likitoci sun iya bakin qoqarinsu amman basu farfado ba, Dr ya kira Abba office sukaje, ya sanya Nurse ta kira mashi Daddy, nan fa suka hadu a office din. 

Abba ya kalli Daddy da mamaki yace "Alh kaima ka kawo mara lpy ne?". Daddy duk haushin Abba yake ji don komai ya faru da dansa shine sila. Abba ya danyi yaqe yace " Alh nasan fuahi kake dani Amma don Allah kayi hkr ka daina nima ba'a san raina hakan ya faru ba". 

Cikin bacin rai Daddy yace "To me kuma xaka fadamin bayan kana neman illatamin yaro, kana ganin abinda kayi ma yaran nan shi ne xai qara danqon xumuntarku?"...  Ya danyi murmushi ya cigaba da cewa " Toh ku daina wannan tunanin don kuwa ba abinda xai qara maku face tarwatewar xumunci, amma ynx banga amfanin sanar dakai wannan ba don ba wani amfani xai yi maka ba tunda an riga an daura aure."

Abba duk jikinshi yayi sanyi xaiyi magana Dr yace ya tari numfashinshi da cewa "ynx dai ba abinda mukaxo yi ba kenan munxo neman maslaha ne akan ciwon ya'yanku". Duk suka maida hankalinsu gareshi, Abba yace " Dr me yake damunsu?" Dr Usman yace "Dama na fada maku ai, idan baku yi bawa ya yanku abinda suke so ba xasu shiga wani hali, ynx hk Ahmad ya kamu da ciwon xuciya, ita kuma Khadeejah jininta ya hau sosai". 


Duk hnklnsu ya tashi, barin ma Abba da yasan shine silar faruwar komai, nan Dr yayi en rubuce 2 a takarda sannan ya basu shawarwarin da suka dace, jiki a sanyaye suka fito daga office din, Daddy ya kalli Abba da mugun kallo yace " Kaga irin abinda ka jawo ma dana ko? Ynx gashinan kasa ya kamu da ciwon xuciya". 

Abba duk yayi nadama yace "Kayi hkr Alh bansan abin xai kai haka ba, amma insha Allah xan dai daita komai". Daddy yace " Me xaka daidaita? Bayan ka riga ka daura mata aure? ". Abba yace " Tabbas kuwa na daura wa Khadeejah Aure a yau kuma insha Allah xan gyara komai". 

Tsaki kawai Daddy yayi ya wuce xuwa dakin da Ahmad yake, har lokacin bai farka ba, yayi wani fayau dashi sosai yake tausayin dan nasa, Mummy ta tarbeshi da tambayar me Dr yace, ba bata lokaci yayi masu bayanin komai, Asy da Farouq ba abinda suke sai hawaye, Mummy ma tayi nata hawayen. 

Bangaren Abba kuwa shima ya wuce dakin har lokacin itama bata farka ba, nan shima aka shiga tambayarshi me Dr yace, suma ya fada masu duk  sukayi da likita, sun tausaya ma Khadeejah sosai, Yah Saif har da hawayenshi sosai Yake jin tausayin Khadeejah. 

*15mnts later*

A hankali ta soma bude idonta wanda da qyar take budeshi, tun tana ganin dishi2 har ta koma gani lpy, kallo tabi mutanen dake dakin, a hnkl abubuwan da suka faru suka shiga dawo mata, runtse idon tayi hawaye na qara xubowa a idonta, jin ana tayi mata sannu yasa ta bude idon, kai kawai take daga masu ba tare da tace komai ba. 

Kallon Yah Saif tayi dake jingine jikin bango, dauke kanta tayi ta maida dubanta kan Abba da sauri ta kawar da kanta, ta kalli su Ayusha da su Haydar dakre ta faman yi mata sannu, murmushi kawai ta musu ta kalli Ummah, marairaice fuska tayi tace "Umma ki taimaka min ko dau daya ne naga Ahmad, don Allah". 

Tausayinta taji sosai ta kalli Abba, Abba ganin hakan yasa ya miqe daga xaunen da yake yace " Ki taimaka mata muje dakin da aka kwantar dashi". Cikin farin ciki Khadeejah ta fara qoqarin tashi amma ta kasa, Abba ya kira Dr ya fada masa, nan yaxo ya ire mata drip din dake hannunta, Ummah da Ayusha su suka riqata, Abba na gaba suna biye dashi, gaba daya aka dungumo xuwa dakin da Aka kwantar da Ahmad. 

Cikin sakin fuska suka gaidasu bayan sun gaisa Abba ya sanar dasu abinda ya kawosu, Mummy ta waiga don gani Khadeejah sai hangota tayi durqushe qasan gadon tana xubar da hawaye, sam tama kasa yin kasa magana, ta wantar da kanta saitin hannunshi, wasu hawaye suka xuba tasuka sauka kan hannun Ahmad. 

A hankali ya fara motsa hannun nasa ganin hakan cikin murna ta waiga ta i mutanen dajun tana cewa "Ya tashi Umma"......... 
   ```Beelybadaru😍```
[2/8, 7:29 PM] Beelybadaru😍: 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
*SHI KADAI NAKE SO*
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
           ✨✨✨
              ✨✨
                 ✨

✨By Beelybadaru😍✨

        ✨86 to 90✨

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Sun samu sauqi sosai a ranar aka sallamesu kowa ya xarce gidajensu, Daddy ya bada kudin sadaki da duk wani abu da ake buqata na neman aure, sai bayan sati daya xa'a kai amarya gidan mijinta, kuma a cikin satin aka kawo lefe. 

Dama can ansa amarya lalle, ynx shirye shiryen biki kawai akeyi, Kamu akayi ranar Alhamis, amarya da ango sunsha kyau kamar ka sace ka gudu, ranar juma'a akayi walima, Asabat aka sha hidimar biki da yamma aka dauki amarya aka kaita gidan mijinta, sannan kowa ya watse aka bar amarya Khadeejah da Ayusha da kuma Ummu sai kuma Ruqayyah diyar qanin Abban kaduna wacce xa'ayi aurensu da Yah Mu'axxam nan bada jimawa ba. 

Suna nan xaune ango ya shigo da abokanshi cikinsu har da Yah Saif, nan suka gama barkwancinsu, Yah Saif ya kada qeyarsu suka fice daga gidan aka bar amarya da angonta. 

Bayan ya dawo daga rakiyarsu, ya xauna gefen Khadeejah, wani farin ciki yake ji wai yau shi ne da abar sonshi Khadeejah, a hnkl y dage mayafin dake kan fuskarta, fuskar nan tasha make up sai dai hawayen dake xuba a idonta, sosai yaji wani iri. 

A hnkl y shiga share mata hawayen sannan ya jawota jikinsa ya rungume yana lallashinta tare da kalamai masu sanyaya xuciya, lamo tayi a jikinsa tana shaqar daddadan qamshin jikinsa, sai da ya tabbatar tayi shiru sannan ya dagota yana kallon kyakkyawar fukarta. 

Murmushi mai sanyi ya saki sannan ya miqe ya cire babban rigarshi, ya soma rage kayan jikinsa, ganin hkn yasa Khadeejah saurin sadda kanta qasa, murmushi yayi bayan ya rage kayan y janyo towel ya daura sannan ya shiga toilet din dake dakin. 

Wanka yayi sannan ya dauro alwalah ya fito, har lokacin tana nan inda take, qarasawa yayi inda take yace "Habeebty in xakiyi wanka ki tashi kiyi daga nan kiyo alwallah". Miqewa kawai tayi ba tare da tace wani abu ba ta nufi hnyr toilet, yayi saurin cewa " Baxaki rage kayan jikinki ba?". Waigawa tayi ta harareshi cikin wasa sannan ta shige toilet din, dariya ya danyi sannan ya shafe jiki shi da lotion sannan ya xura jallabiya ya xauna xaman jiranta. 

Khadeejah kuwa tana gama wankan ta dauro alwalar kamar ynd yace sannan ta duba, taga towel a linke, hkn yasa ta daukoshi ta daura, sai dai ko gwuiwa bai kai mata ba, gyalenta ta jawo ta lullube duk da wajen qafafunta ba wani rufuwa yayi ba, a hnkl ta bude qofar kamar wata mara gsky ta leqo kanta a hnkl tana duban dakin tana addu'ar Allah yasa baya nan. 

Karaf suka hada ido dashi da sauri ta koma cikin toilet din, dan murmushi yayi ya miqe ya nufi wajen toilet din, turawa yayi xai bude tayi saurin rufe qofar, dan murmushi yayi sannan yace "Toh ki fito mana". Maqe kafada tayi kamar yana ganinta tace " Ni dai a'a sai dai ka miqo min kayana". 

Dariya ya danyi sannan ya koma ya dauko mata rigar baccin ya dawo tare da cewa "Toh gashi". Bude qofar tayi a hnkl ta miqa hannu murmushi yayi maimakon ya bata rigar sai ya riqe hannun nata, tura qofar yayi ya jawota ta fada jikinsa, qara qanqameshi tayi don bata so ya ganta a hkn. 

Qoqarin dagota yayi ta qara qanqameshi, duk jikinsa yayi  wani iri, cikin wata murya yace " Deejah dago mana". Kamar xatayi kuka tace "Umm umm ni ban iya dagowa a hk". Dan murmushi yayi sannan yace "Toh a hk xamu tsaya? Ki dago ki amshi kayan ki sanya". Dan dago da kanta tayi ta turo baki cikin shagwaba tace " Toh ba kai bane ka jawoni kuma kasan ban sanya kaya ba?". 

Dariya yayi sannan yace "Toh miye don na ganki ba kaya?". Qara turo bakin tayi tana harararsa ta qwace kayan daga hannunsa sannan ta fito daga jikinsa da sauri ta juya xata shige bayin yayi saurin riqo gyalen data lillibe dashi, xamewa yayi daga jikinta ganin hkn yasa tayi saurin shigewa. 

Wani irin yanayi ya tsinci kansa a ciki, yayi dan murmushi sannan ya koma ya xauna, Khadeejah kuwa tana shiga bayin ta kulle ta jingina jikin qofar tana maida numfashi kamar wacce ayi gudun fanfalaqi, murmushi ta saki sannan ta bude rigar xata sanya. 

Waro ido tayi ganin ynd rigar take shara shara, gashi ba damar qara fita, hkn yasa ta sanya rigar, komai na jikinta ana gani kasa fita a hkn tayi hkn yasa ta janyo towel din ta rufe jikinta sannan ta fita.

Murmushi kawai yayi ya miqa mata hijab ta sanya dama ya shimfida kafet, nan ya jasu sukayi sallah raka'a biyu sannan suka miqa godiyarsu ga Allah da ya mallaka masu junasu, bayan sun idar suka ci kaxa, itama da qyar ya tilastata taci kadan. 

Ji tayi idonta na lumshewa saboda barcin da take ji, ganin hkn yasa yace ta kwanta ta huta, kwanciyar tayi da hijabin a jikinta, bata fi minti biyu ba bacci ya kwasheta, miqewa yayi shima ya kauda kayan abincin sannan ya hau gadon, a hnkl y jawota jikinsa ya cire mata hijabin, wani yarr yaji lokacin da yaga Deejah a hk, a hnkl y soma shafata yana sumbatarta, nan ya shiga sarrafata ynd yaso. 

Cikin barci taji kamar ana tattabata hkn yasa ta bude idonta, ganin abinda Ahmad yake mata yasa jikinta ya dau kyarma, ta soma tureshi tana cewa ita bata so, amma shi sam bai san ma tana yi ba, kukan da takeyi ne ya dakatar dashi daga abinda yakeyi, y koma gefenta yana maida numfashi..... ```Beelybadaru😍```
[2/10, 7:26 AM] Beelybadaru😍: 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
*SHI KADAI NAKE SO*
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
               ✨✨✨
                  ✨✨
                     ✨

✨By Beelybadaru😍✨

        ✨91 to 95✨

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Da qyar ya samu ya lallasheta tayi shiru sannan barci ya daukesu baki daya. Washe gari asubar fari ta miqe ta fada toilet tayi wanka tayo alwallah sannan ta fito, nafila ta fara yi sannan tayi raka'atanul fajr, sannan ta miqe taje saitin fuskarshi ta tsaya tana tunanin ynd xata fara tadashi. 

Hannunta ta kai saman sumar kanshi, a hnkl ta fara shafa sumar kan nashi, a hnkl ya fara bude idon nashi ya saukesu akan Fuskar Khadeejah, murmushi ya sakar mata, itama murmushin tayi, duk sai kuma taji kunya, miqewa tayi da niyyar barin wajen, yayi saurin riqo hannunta ya jawota ta fada jikinsa. 

Runtse idonta tayi da sauri, yayi murmushi sannan ya dago fuskarta yace "Sallah ko?". Gyada masa kai kawai tayi ba tare da tace komai ba, miqewa tayi daga jikinsa ta gyara xaman hijabinta sannan ta nufi wajen carpet din da tayi sallah a kai. 

Miqewa shima yayi ya nufi toilet yayo Alwallah sannan ya fito, shima yayi raka'atanul fajr sannan ya jasu jam'i sukayi sallar Asuba, bayan sun idar sukayi addu'o'i sannan ya miqe ya kalleta tare da cewa " Muje mu koma barci ko?". Maqe kafada tayi tace "Ni bana jin barci ynx". Dan murmushi kawai yayi sannan ya nufi kan gadon ya kwanta ya runtse idonshi amma sam ba barci yake ji ba. 

Khadeejah kuwa wani irin barci take ji, tana nan xaune ta fara gyandad'i tun tana yin kamar xata fadi har barcin ya kwasheta ta kwanta nan saman carpet din, barci mai nauyi ya kwasheta. 

Ahmad kuwa miqewa yayi ya leqa yana kallon Khadeejah, dariya taso ta bashi ganin ynd ta qudundune cikin hijabinta kamar wata er mage tana barci, ya sauko daga kan gadon ya qaraso inda take ya tsugunna. 

Kallon fuskarta ya tsaya yi ya kalli kyawawan idanuwanta masu dauke da dogayen eye lashes, da dan dogon hancinta w d yayi dai dai da fuskar ta ta, ga danqaramin bakinta mai dauke da pink lips, murmushi kawai yayi ya miqe ya dauketa cak bai direta ko'ina ba sai a kan gado, cire mata hijabin yayi sannan ya rufa mata bargo yayi sannan shima ya kwanta ya lullube da bargon, a hnkl ya jawota jikinsa nan da nan barci mai nauyi ya kwasheshi. 

_Washe gari_

Sai wurin qarfe 10 Khadeejah ta farka, mamaki ne duk ya cikata ganinta da tayi a jikin Ahmad kuma a kan gado, a hnkl ta xare jikinta daga nashi ta sauka, fita tayi xuwa falo, kallon falon kawai takeyi ganin ynd yayi kyau sosai, dakuna kusan hudu ne a cikinsa duk da nata, shiga kowanne tayi taga kowanne da toilet dinshi da kuma kaya a cikinsa, na kusa da dakinta ta shiga, yayi kyau sosai duk kayan da ke ciki irin nata ne sai dai banbancin ita nata pink nd white ne, shi kuma nashi blue nd white ne. 

Gyare2 ta hau yi, ta gyare ko'ina ta sanya turaren qamshi ko'ina ya bude da qamshi sannan ta koma cikin dakin, har lokacin bar i yake hakan yasa ta fada toilet tayi wanka ta fito, ta shirya cikin wata doguwar riga ta shadda, ta kashe dauri ta feshe jikinta da turaruka bayan tayi simple make up. 

Gadon ta nufa a hnkl ta xauna a saman side drower wajen saitin fuskarshi, a hnkl ta shiga qarema kyakkyawar fuskarshi kallo, idanuwansa ta kalla wadnda suke manya da dogayen ey lashes, ga dogon hancinshi da dan qaramin bakinshi mai dauke da Pich lips, ga sajenshi da ya kwanta luff a fuskarshi. 

A hnkl ta kai hannunta kan fuskar tashi tana shafa sajenshi, juyi yayi da idanuwanshi sai kuma ya budesu yana mata wani kallo na shauqi, sadda kanta tayi qasa tana wasa da yatsun hannunta, murmushi yayi sannan ya riqo hannun nata yana murxawa a hnkl, ji tayi duk wani iri, taso ta kwace hannun nata amma ta kasa, can dai ta dake cikin sanyin murya tace "Habeeby ka tashi kayi wanka". Miqewa yayi ba tare da yace komai ba, ya saki hannun nata sannan ya cire jallabiyarsa ya daura towel, ita dai Khadeejah kanta na qasa har lokacin. 

Kallonta yayi cikin tsokana yace " Habeebty bana iya yin wankan kixo kiyi mani plx". Dagowa tayi ta kalleshi, waro ido tayi don batayi tunanin xata ganshi hk ba, tayi saurin maida kanta qasa ba tare da tayi magana ba. 

Er dariya yayi ya nufo inda take sai da yayaxo saitinta sannan ya durqusa ya dago fuskarta suka hada ido, tayi saurin runtse idon, girgixa kai kawai yayi yana dan murmushi sannan ya miqe ya fada toilet don yin wanka.
   ```Beelybadaru😍```
[2/12, 7:31 AM] Beelybadaru😍: 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
*SHI KADAI NAKE SO*
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
               ✨✨✨
                  ✨✨
                     ✨

✨By Beelybadaru😍✨

       ✨96 to 100✨

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Tana nan xaune taji ana knocking hkn yasa ta miqe ta fita xuwa falo don bude qofar, Asy ta gani tsaye da kulolin abinci a hannunta, murmushi Khadeejah tayi mata sannan tace "Sannu da xuwa Asy". Murmushi Asy tayi sannan ta shiga cikin falon ta ajiye kulolin tana mai cewa " Aunty Deejah ina kwana?". Cikin sakin fuska ta amsa da "Lpylow Asy ya su Mummy?". Asy ta amsa da " Suna lpy tace a gaisheki". Tace "Ina amsawa, ki xauna mana". 

Girgixa kai Asy tayi tace " A a wucewa xanyi Aunty, Mummy tace kar na dade". Khadee ta bata fuska tace "Tohm ki tsaya muyi breakfast din mana". Er dariya tayi tace "Idan naje gida xanyi". Xatayi magana kenan sai ga Ahmad ya fito da jallabiya a jikinsa, Asy da sauri tace " Yaya ina kwana?". Sai da ya qaraso cikin falon ya xauna kan kujera sannan ya amsa da "Lpylow Qanwa kun tashi lpy?". Ta amsa da " Lpylow Yah, dama abinci na kawo maku inji Mummy". 

Murmushi yayi tare da cewa "Ayyah mungode ki gaishe da Mummy din sai na shigo da anjima". Cikin xolaya Asy tace " Yah ai baka fara fita ba". Tasowa yayi yayi kanta xai maketa yana cewa "Ke bakyaji ko?". Dariya tayi da gudu ta fice daga falon tana cewa " Allah Aunty karki barshi ya fito sai yayi wata biyar". Tana kai nan ta fice, Khadeejah tayi dariya, shima dariyar yayi tare da cewa "Asy bata ji Allah". 

Juyawa tayi xata koma cikin daki taji ya rungumota ta baya, lumshe idonta tayi a hnkl, ya kwantar da kansa saman kafadunta sannan cikin wata murya yace " Habeebty yunwa nakeji muje ki bani abinci, ko ke bakyaji?". Ya qarashe maganar yana shafa cikinta, riqe hannun nasa tayi sannan ta juya tana fuskantarsa, sai kuma ta sadda kanta qasa cike da jin kunyarsa. 

Er dariya yayi sannan ya riqo hannuwanta yace "Wannan kunyar sai nayi yaqi da ita". Dagowa tayi ta kalleshi sannan tace " Yaqi kuma name?". Yace "Ynx dai muje muci abinci yunwa nake ji". Ba musu suka wuce saman dining inda Asy ta ajiye kulolin, xama sukayi, har a lokacin Ahmad na riqe da hannun Khadeejah, kallonshi tayi tace " Habeeby ka sakar min hannun naje na dauko plates". Miqewa yayi tare da cewa "Sai dai mu tafi tare". 

Dariya tayi suka wuce xuwa kitchen din, suka dauko suka dawo, a tare suka abincin, nan ya fara bata tace ita sai ya fara ci tunda shi kejin yunwa, shi kuma yace baxai ci da kanshi ba sai dai ta bashi. Ba yadda ta iya dole tayi feeding dinsa, sannan shima ya bata. 

Kwashe kwanukan sukayi suka kai kitchen suka wanke sannan suka dawo falo. Xama sukayi a kujera, Ahmad ya rungumota yana sinsinar ta, ji tayi mararta ta fara ciwo, da sauri ta riqe cikinta tana cije lebe, cikin rudu Ahmad yace " Lpy Deejah? Me ya faru?". 

Kasa magana tayi saboda tsananin ciwon da mararta ke mata, kuma tasan ba komai bane face period, don duk sanda xatayi sai tayi ciwon ciki. Ahmad duk ya rude sai faman tambayarta yake, da qyar ta daure tace ya taimaka mata xuwa daki, miqewa yayi ya dauketa cak sai daki, har xai ajeta kan gado tace Toilet xai kaita. 

Ba musu ya kaita yayi tsaye a gurin yana mata sannu, cewa tayi ya fita, yace babu inda xashi ya barta cikin wannan halin, da qyar ta samu ya fita ta tura qofar, a hnkl ciwon ya lafa, ta miqe ta gyara jikinta sannan ta dauki always din dake toilet din ta sanya, ta fito daga toilet din. 

Karo taci da Ahmad a qofar toilet din, nan yayi saurin riqota yana mata sannu, murmushi kawai tayi masa sannan tace "Habeeby na samu sauqi". Ajiyar xuciya ya sauke sannan yace " Habeebty wannan wane irin ciwo ne? Ko kema kina ciwon ciki idan xakiyi period?". Duk kunya taji ta kamata, ta sadda kanta qasa, yace "Fadamin mana, period kike?". Ganin ya dameta da tambaya yasa ta gyada mashi kai kawai sannan ta wuce ta fice daga dakin don kunyarshi ma takeji.

Ji yayi duk ba dadi, amma ba yadda xaiyi dole xai haqura har xuwa sanda xatayi wanka, shima fitar yayi daga dakin xuwa wajen Deejah. ```Beelybadaru😍```
[2/12, 2:01 PM] Beelybadaru😍: 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
*SHI KADAI NAKE SO*
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
               ✨✨✨
                  ✨✨
                     ✨

✨By Beelybadaru😍✨

     ✨101 to 105✨

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

_5 days later_

Deejah tana xaune a falonta cikin shigar wata doguwar riga ta material, ta caba ado sai qamshi take, tana xaune xaman jiran Ahmad da yaje gaida su Umma dasu Mummy. 

Knocking taji anayi, da sauri ta miqe ta gyara kallabinta don duk a tunaninta Ahmad ne, xuwa tayi a hnkl ta leqa don ganin ko waye sai ganin Ayusha tayi, ai da sauri ta bude qofar, suna hada ido suka rungume juna suna farin ciki, a hk suka shiga cikin falon, waigawa tayi don rufe qofa sai ganin su Haydar tayi sai kumbura suke, ganin bata kulasu ba sai Ayusha. 
Ai da sauri ta koma wajensu ta riqo hannuwansu tana farin ciki tace "My brodas nayi missing dinku alot". Dan sakin fuska sukayi sannan Haydar yace " Same 2 u big sis, don muma muna cike da kewarki". 

Aliyu yace "Allah tun bayan da kika tafi sai gidan yayi wani iri". Dariya tayi sannan taja hannuwansu kamar wasu qananan yara suka qarasa cikin falon wajen kujeru suka xauna, nan ta shiga tambayarsu ya su Umma da Abba, suka amsa da duk suna lpy suna gaisheta. 

A nan ne su Aliyu suke fada mata an sanya ma Ayusha da Yah Saif rana nan da wata uku biki. Farin ciki sosai tayi, nan ta tashi ta kawo musu abinci da abinsha, don tuni ta fara girki, suka ci suka yi nat, sai labari suke kamar kar su daina. 

Wayar Khadeejah dake wajen TV tayi ringing hkn yasa ta miqe ta qarasa wajen wayar, ganin mai kiran yasa ta saki murmushi, dagawa tayi tare da yin sallama, maimakon taji muryar Ahmad sai jin wata muryae tayi ana cewa " Don Allah kuxo babban asibitin garin nan mai waΓ±nan wayar ya samu accident. 

Dumm taji gabanta ya fadi, ta duba wayar har an tsinke, har ynx kunnuwanta sun kasa gaskata mata abinda suka ji, ji tayi kanta ya sara mata, gaba daya jikinta duk ya mutu, cikin rawar murya ta fara "Inna lillahi wa inna ilaihir raji'un....." Tana kai nan ta sulale ta xube qasa sumamma. 

Da sauri su Ayusha sukayo kanta, Ayusha ta riqota cikin firgita har ta soma hawaye ta shiha jijjigata tana kiran sunanta amma shiru, Aliyu ya dauko ruwa ya kawo ma Ayusha, nan suka yayyafa mata ruwan, a raxane ta miqe tana waige waige cikin muryar kuka take cewa "Ina Habeeby? Plx karku cemin da gaske yayi accident?.... Kuka sosai takeyi, su Ayusha duk sun shiga rudu, wayar ta qara ringing Aliyu dake kusa da ita ya dauka, mutumin daxu ne ya kuma cewa "Kuyi gaggawar xuwa yana cikin wani hali". Cikin qarfin hali Aliyu yace " Wane asibiti ne?". Nan ya fada masa ya katse kiran. 

Tashi yayi cikin sanyin jiki yace "Ya kamata muje asibitin ynx". Miqewa Ayusha tayi ta miqar da Khadeejah dake ta faman rusa kuka, Haydar ya riqeta ita kuma Ayusha ta shiga dakinta ta dauko mata hijab ta sanya mata suka fice daga falon, driver daya kawo su Ayusha shi ya tafidasu xuwa asibitin, a kan hny Aliyu ya kira su Abba da Daddy ya sanar dasu, duk hnklinsu ya tashi. 

Suna isa ba da jimawa ba sai gasu Abba Umma Daddy Mummy Yah Saif Yah Mu'azzam Asy da Farouq sun iso cikin tashin hnkl, duk ynd Khadeejah taso ganin Ahmad aka hanata don likita na ciki yana dubasa, duk ta fita hayyacinta lokaci guda. 

Ba'a jima ba sai ga likita ya fito yana share xufa, cikin axama duk suka tunkareshi suna tambayar ya mai jikin, cikin sanyin jiki ya kallesu sannan yace " Alhj ku sameni a Office". Yana fadar hk y wuce, su kuma suka mara masa baya Abba da Daddy, Khadeejah ganin hkn yasa ta kubce daga riqon da Uma tayi mata ta qarasa jikin window dakin da Ahmad ke ciki, ta hangoshi kwance kamar mara rai kanshi daure da bandage an dan rufe mashi fuska sai dai ba duka ba. 

Ta ja baya cikin tashin hnkl, da gudu ta nufi office din Dr, su Mummy na kiranta amma bata sauraresu ba, burki taja a lkacin da ta isa qofar office din ta jiyo maganar Dr yana cewa "Alhj a gsky munyi iya bakin qoqarin mu don ganin mun ceto rayuwarsa amma mun kasa, sai dai kuma kuyi hkr don Allah ya karbi abinsa....."

Iya abinda ta iya ji kenan, don gaba daya lokaci guda jinta da ganinta suka dauke na wasu mintina, sai kuma a hnkl suka fara dawowa kalaman Dr suna mata yawo a kai, miqewa tayi da gudu ta koma dakin da aka kwantar da Alhmad....... 
```Beelybadaru😍```
[2/14, 1:03 PM] Beelybadaru😍: 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
*SHI KADAI NAKE SO*
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
               ✨✨✨
                  ✨✨
                     ✨

✨By Beelybadaru😍✨

     ✨106 to 110✨

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Shiga tayi dakin tana tafiya kamar wacce kwai ya fashewa a ciki, hawaye kawai suke xuba a idonta, bakinta ya rufe gum ta kasa furta koda kalma daya. 

Tana isa bakin gadon a hnkl ta yaye lullubin da akayi mashi, kallon fuskarshi take cikin wani yanayi, ta durqushe a gurin tare da shafa fuskar tashi hawaye na xuba a idonta, kukan xuci kawai take yi, a hnkl ta kwantar da kanta saman kirjinshi tare da saqala hannunta daya cikin nasa daya kuma yana a kan fuskarsa. 

Sai a lokacin kuka yaxo mata, kuka sosai ta shiga yi, a lokacin ta samu bakin magana cikin rawar murya ta fara cewa "Habeeby..... Meyasa xakayi min hk?.... Meyasa xaka tafi ka barni a lokacin da nake buqatarka a rayuwata?...... Why Abul..... Why!!!?". 

Ta qara qanqameshi tana kuka mai tsuma xuciya, su Umma ma ba abinda suke face hawaye, suma su Daddy sun shigi dakin duk suma hawayen sukeyi. Ayusha ce tayi qarfin halin qarasawa wajen Khadeejah ta durqusa gabanta tana hawaye ta dago kanta tana mai cewa " Aunty kiyi hkr don Allah, dukkan mai rai mamaci ne...." 

Khadeejah tayi saurin katseta ta hanyar cewa "No Ayusha ni nasan Habeebynah bai mutu ba... " ta daga kai ta kalli su Abba cikin muryar kuka tace "Abba ka fada ma Dr qarya yake Abul dina bai mutu ba". Shi kanshi Dr sai da hawaye suka xubo masa, sosai yaji tausayin Khadeejah wannan wane irin so ne haka?. 

Kuka sosai sukeyi ita da Ayusha dasu Asy, Ayusha ta jawota jikinta ta rungume tana matsar qwalla. Khadeejah har wani shidewa takeyi don kuka, ga xuciyarta na wani irin duka har Ayusha sai da ta tsorata. 

Dagowa tayi da sauri ta maida kallonta ga Ahmad tace " Habeeby ka tashi ka tabbatar musu da baka mutu ba, Habeeby ni ina ji a jikina baka mutu ba, plx wake up Habeeby."

Hannunsa dake cikin nata taji ya motsa, da sauri ta kai dubi hannun taga yana motsi, ta maida kallonta kan fuskar shi taga hawaye na fita daga idonshi amma bai bude idon ba. 

Ta rasa me xatayi ma don farin ciki, dariya mai hade da kuka tayi ta waiga ta kalli du Daddy tace "Abba dama nace maku bai mutu ba gashi nan ya tashi". Da sauri duk suka qarasa bakin gadon nashi, Dr ya shiga dubashi, sannan ya dago ya kalli du Daddy fuska dauke da murmushi yace " Alhmdulilah ya farfado saura fatan samun qarfin jiki". Kowa ba abinda yake sai hamdala. Wanda ya taimaki Ahmad yaxo ya kawo masu makullin arshi da wayarshi, nan sukayi mashi godiya suka bashi kudi yace sam baxai amsa ba, ba yadda basuyi ba akan ya amsa ya qiya dole suka qyaleshi. 

Satin Ahmad daya a asibitin yana samun kulawa sosai, ya warke ynx sai dai abinda ba'a rasa ba, Khadeejah ta sha tsokana wajen su Ayusha akan halin da ta shiga lokacin da akace Ahmad ya rasu, shi kam ji yayi wani sonta na qara shiga xuciyarsa, an sallamesu suka koma gida cike da farin ciki. 

Ta hada mashi ruwan wanka yayi ta bashi kayan shan iska ya sanya ta fesheshi da turare, shi kam kallonta kawai yake cike da so da qauna, itama shiryawar tayi cikin doguwar riga ta English wears, tayi kyau sosa suka fito falo, dama sun dawo da abinci hkn yasa suka xauna suka ci sannan suka koma falo suka xauna suna kallo da fira. 

Ranar dai haka sukayita cikin farin ciki da annashuwa. 

*_Bayan wata Uku(3months later)_*

Shirye2 bikin Ayusha da Yah Mu'azzam kawai sukeyi, en uwa duk sunxo, Ummu itama an sanya ranar bikinta da wani saurayinta mai suna  Lamido, kowa ka gani murna yake yi, yau  ranar kamu ce. 

"Haba Habeeby ka tashi ka shirya mu tafi kada a fara bamu nan". Dagowa yayi ya kalleta yace "Nifa bana so kina wahalar min da babyna, nasan idan kikaje kin dinga xirga2 kenan duk ki gajiyar min dashi". 

Hararar wasa ta watsa mashi sannan tace " Au ta babynka kadai kake bakajin ta Mummyn nasa?". Er dariya yayi sannan yace "A a nufina fa ku duka". Riqo hannunshi tayi ta jashi da nufin dagashi ta kasa, dariya yayi yace " An gaya miki ni qarami ne?". Ta shagwabe fuska tace "Haba mana Habeeby ni dai ka tashi kayi wankan". 

Miqewa yayi tare da cewa " Ai indai kika sanya ma ranki abu sai kin san ynd kikayi kika sameshi, ynx dai indai kina so muje sai dai muje ki taya ni wankan?". Kallon jikinta tayi ta shirya cikin material doguwar riga na ankon kamun, ta waro ido tare da cewa "In bata kayana da ruwa". 

Ya koma ya xauna tare da cewa " shikenan ba xuwa kenan". Da sauri ta riqoshi tana lallashi, da qyar ta samu ya miqe ya shiga wankan, bayan ya shirya suka nufi gidansu a motarshi. 
```Beelybadaru😍```
[2/17, 12:26 PM] Beelybadaru😍: 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
*SHI KADAI NAKE SO*
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
               ✨✨✨
                  ✨✨
                     ✨

✨By Beelybadaru😍✨

      ✨ 111 to 115✨

*Note:- Kuyi hkr na rashin jina da kukayi kwana biyu, luv u oll my fans😘😘*

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Suna isa lokacin har su Afma sunje, nan fa aka hadu ana ta shafta, Ahmad kuma suka fita shi da Abdur-raheem(Mijin Afma). Sai faman make up ake ma amare Ayusha da Ruqayya sun fito ras da dasu abokan wasa su Afma sai tsokanarsu suke wai basuyi kyau ba, Ruqayya dai murmushi kawai take ita kam Ayusha harara kawai take xabga musu don tasan tayi kyau dinπŸ˜‰

Anyi kamu lpy, angwaye da amare sunsha kyau kamar ka sace ka gudu, su Asy ma duk sunxo da Farouq, kai har su Mummy ma sai da suka xo, ansha pictures da videos. 

A nan ne qanin Yah Saif mai suna Usman ya ga Asy yaji ta kwanta mishi a rai, tunanin aqidar family dinsu yayi don yasan baxa'a barshi ya auri bare ba, amma tunawa da Khadeejah yasa hnklnshi ya dan kwanta, nan yaje kai tsaye ya samu Asy ya fada mata abinda ke ranshi. 

Itama tunawa da ynd akayi auren Yah Ahmad da Khadeejah ne yasa tace A a, da qyar ya shawo kanta a cewar komai xai daidaita. Anyi biki lpy an kai amarya gidan mijinta. 

Bayan komai ya lafa Usman ya samu Abban su Khadeejah ya sanar dashi abinda ke ranshi, murmushi kawai Abba yayi yace xai samu sauran yayi masu bayani, yayi mashi godiya ya tafi. 

Su Khadeejah sai da aka kai amarya dasu, bayan sun kaita ne sukayi bankwana don Ahmad yace gida xasu tafi kafin ango ya shigo. Ayusha ansha kuka ganin Khadeejah xata tafi, da qyar ta lallasheta suka tafi. 

A mota ta iskeshi xaune yana jiranta, tana xuwa tayi murmushi don jan fada take sonyi, maimakon ta bude front sit ta  shiga sai ta bude back sit ta shige ta hakimce. Sakin baki Ahmad yayi yana kallonta ta mirror, sai kuma ya juya ya kalleta. Dariya taso ta kucce mata tayi saurin tufe fuskarta da gyale tana dariyar qasa qasa. 

Ji tayi shiru kamar ba kowa a cikin motar hkn yasa ta bude fuskarta taga wayam baya nan, da sauri ta waiga wajen bata ganshi ba, waigawar da xatayi gefenta sai ganinshi tayi xaune a gefenta ya kishingida tare da lumshe ido. Kallonshi ta tsaya yi, gsky Ahmad kyakkyawa ne na qarshe, abinda take fada cikin xuciyarta kenan, hura mata iska yayi a fuskarta, tayi saurin lunshe ido ta bude, murmushi ya sakar mata tare da cewa "Baby wannan kallon fa?". 

Ji tayi duk kunya ta kamata, ta sadda kanta qasa tana wasa da fingers dinta riqo hannun nata yayi yana murxawa yace " Habeebty yau waxaiyi driving dinmu?" Kallanshi tayi da mamaki sai kuma tayi murmushi tace "Ni xanyi". Dariya yayi yace " Toh jeki ki tada motar nidai ina nan barci xanyi". 

Fita tayi kamar gaske ta koma driver sit ta shiga da yake makullin na jiki hkn yasa ta murda ta kunna motar, shikuwa kallonta ya tsayayi don shi du ya dauka wasa take, gani yayi tana neman fara tafiya da motar hkn yasa yayi saurin miqewa daga kishingiden da yake yana cewa "ke wai da gsk kike driving dinmu xakiyi?" Dariya tayi tace "Au da ka dauka da wasa nake ai na.....Maganar tata ce ta tsaya sakamakon jin motar ta fara tafiya, ai da sauri Ahmad ya riqe burki, ita kuwa runtse ido tayi cike da jin tsoro don ita har ta sadaqas, Allah yaso gabansu ba wata mota ko wani abun fili ne, sai motarsu Saif da take qoqarin shigowa suna ganin hkn sukayi parking suna salati.

Da qyar ya samu motar ta tsaya sannan ya kwanto da kujerar motar ya koma gaba yana kallon Khadeejah da har lokacin bata bude idonta ba har hawaye sun fara xubo mata. Murmushi ya saki sannan ya jawota a jikinshi ya rungume yana shafa bayanta, a hnkl yace " ki bude idonki mun iso ai". 

A hnkl ta bude idon nata tana kallon gabnsu taga motar a tsaya ta sauke ajiyar xuciya, Ahmad ya qara yin murmushi yace "Gsky kin iya driving cikin qanqanin lokaci muka isa gida". A shagwabe ta kai mashi duka tana cewa " Allah ni dai ka bari". Dariya yayi tare da bude motar ya fito a cewa "Ai dama ban take burkin ba". Itama fitowar tayi xatayi magana su Saif suka qaraso wajen suna tambayar lpy? 

Dariya Almad yayi yace " Ka ganta nan cewa tayi xatayi driving dinmu shine na Bata ta kusa antaya mu barxahu". Saif yayi dariya yace " Ai ni nayi xaton kwace maka motar tayi, Toh Allah ya kyauta gaba". Ya amsa da "Ameen" n sukayi ashi sai da safe suka wuce gida. 

🌟🌟🌟🌟🌟

Komai ya daidaita don har an sanya ranar ranar bikin Asy da Usman, Yah Farouq ma yaga wata diyar qanin Abban Kaduna mai suna Asma'u har sun sasanta tsakaninsu magana taje wajen manya an gama komai har an sanya rana suma. 

Bayan wasu watanni Khadeejah ta Haifi erta kyakkyawa murna wajen Ahmad bata misaltuwa. Ranar suna yarinya taci sunan Ummansu Khadeejah  Hafsat suna kiranta da Seemah. 

*Bayan shekara uku*

Zaune suke ita da Ahmad suna kallo, kwanto da kanshi yayi kan kafadar Khadeejah yace "Habeebty ina sonki da yawa". Murmushi tayi ta shafi gefen fuskarsa tare da cewa " Nima ina sonka da yawa Habeeby". Seemah ce ta shigo dakin, in ka ganta sai ka dauka tayi shekara hudu, don tayi girma, xuwa tayi ta xauna kan cinyar Ahmad tana ta turo baki, shafa kanta yayi da yasha gyara yace "Babyna waya taba min ke?" cikin muryar shagwaba da qwaranci "Abee ba frnd dita bace take cewa kullum sai sunyi wasa da aninta tana cewa ni bani dashi, Abee nima ina son ani". 

Murmushi yayi yace " Tohm ga Amminki nan ki fada mata". Kallon Khadeejah tayi tace "Ammi xaki siyomin ani ko?". Dariya Khadeejah tayi tace " Ba ga qaninki can ba Adeel gidan Aunty Ayusha?". Turo baki tayi tace "Umm umm nidai anan gida nake so". 

Ahmad yace " Tohm karki damu kinji insha Allah nan ba da jimawa ba xaki samu qani". Runguneshi tayi cike da farinciki tace "Yeh Abee thank u so much I love u". Peck ya bata a goshi yace " I luv u too dear". Tashi tayi ta fice daga falon ta koma dakinta. 
```Beelybadaru😍```
[2/19, 7:37 AM] Beelybadaru😍: 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
*SHI KADAI NAKE SO*
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
               ✨✨✨
                  ✨✨
                     ✨

✨By Beelybadaru😍✨

     ✨116 to 120✨

        *_THE END_*
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

*Bayan wata biyar*

Ranar tashi tayi da wani irin ciwon ciki, ga barci da take yawan yi, Ahmad kuwa koda ya dawo daga office ya ganta a wannan halin ya kwasheta xuwa asibiti, a nan ake sanar dashi tana da juna biyu, ranar yayi farin ciki kamar shi ne farkon samun haihuwarshi, itama Khadeejah tayi murna sosai sai dai bata nuna ba. 

Kuma a lokacin ake bikin Asy da Usman, sai Farouq da Asma'u, shina dai sunyi shagali sosai kamar ba gobe.

*7yrs later*

Hjy Khadeejah an xama manyan mata, Alh Ahmad ma an xama manyan mutane, don ynx hk shekararsu biyu kenan da xuwa aikin hajji, bayan ya biya ma su Daddy dasu Abba. 

Ynx hk Khadeejah tana da 'ya'ya hudu, Seemah er shekara goma ynx tayi girma kamar wata er shekara sha, sai sai mai sunan Mummy wacce suke kira da Adeela, sai kuma Ni'imatu sai auta Shuraim. 

Ayusha kam 'ya 'yanta ukku Adeel shi ne babba, sai Husnah, sannan Jalal, ynx hk tana dauke da cikin na na uku. 

Su Aliyu da Haydar an xama manyan samari, ynx hk sun gama degree dinsu, masters xasu wuce don sunce sai sunga  qarshen biro da takardaπŸ˜„

Rayuwa tayi masu dadi, dukkanin gidajen suna xaune cikin farin ciki da kwanciyar hnkl. Asy ma 'ya yanta uku. 

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Khadeejah ce ta fito daga dakinta cikin shigar alfarma, kai inka ganta sai ka dauka wata er 20yrs ce, jikinta sam baya nuna yawan shekaru, sai faman zuba qamshi take. 

Ahmad dake xaune ya taso yana sakar mata wani kalan murmushi, tun kafin ta qaraso ya rigata qarasawa, hugging dinta yayi tare da kwantar da kanshi saman kafadunta ya lumshe ido tare da cewa "Habeebty wai ke bakya tsufa ne? Kullum qara kyau kike". 

Murmushi tayi sannan ta dago da kanshi ta shafa gefen fuskarshi tace " Habeeby kaima hkn ne ai". Riqo hannayenta yayi tare da cewa "Lah kina ganina da gemu xaki ce ban tsufa ba?". 

Hararanshi tayi cikin wasa tace " Ina gemun yake a nan? Sajen ne gemu?". Murmushi yayi sannan yace "Tohm naji ynx muje muyi lunch cox i'm feeling hungry". Itama murmushin tayi sannan tace " Tohm Bari na kira su Seemah suxo muci". Da sauri yace "A a ni xan kitasu, bana so kina wahalar min da kanki da yawa." Murmushi kawai tayi ta girgixa kai ta bishi da kallo. 

Ba'a jina ba sai gasu riii sun fito, don harda Husnah da Jalal din Ayusha sunxo masu yawo, nan suka hadu a centre table aka fara cin abinci ana raha, abin gwanin ban sha'awa. 

Nima dai Beely gefe guda na koma ina hadiyar yawu don qanshin abincin ya cika min hanci, ganin basu da niyyar bani yasa nayi sanda na shige ktichen nayi kalar tukunya😜😜

    *ALHAMDULILLAH*

Laifin dadi qarewa, hausawa dama sunce komai yayi farko xaiyi qarshe, a nan na kawo qarshen wannan littafi nawa nai taken *SHI KADAI NAKE SO* Ba Khadeejah kadai ba ni kaina Habeebynah *SHI KADAI NAKE SO*😍

Kura kuran dake ciki Allah ya yafe mana, Allah kuma ya bamu ikon amfani da darussan daje cikin sa. 

*JINJINA GA:-*

BEELYBADARU😍 NOVELS
O H W
EXCELLENT WRITERS
CLEVER WRITERS
PERPECT WRITERS
ANEELURV NOVELS
ASY KHALEEL NVLS WORLD
PHERTY B~B NVLS
RAZ NOVELLA 1&2
THE QUEEN BEE
AFMA'S NVLS GRP
WALLYNOVELS
     Waih lissafosu wani jan aikine sauran da ban lissafo ba ina miqa jinjinata a gareku. 

*KUNA RAINA*
AYUSHA MOH'D(my Ayusha)
FIRST LADY (Dear nah)
AFMAH (Besty)
ASY KHALEEL(My Asy)
RABI'AT SK MSH (Sistona)
WALIYYAH WALLY(My Wally)

*FATAN ALKHAIRI A GAREKU*
Aneelurv
Amrah 
Zarah b~b
Classic Feedo
Mufeeda Mu'axu
Humairah melody
Ramalurv
Dr Ruqayyat
Ummieeja'afar
Mjay
Faty azland
Jameelah k/msh
Abdul-mr, smiles
Raheem jEga
Abdul AAJ
Ililee. 
    Wadanda ban fada ba kuna raina kuma. 

*SADAUKARWA*
Na sadaukar da wannan littafin nawa ga daukacin iyalan *BAFU FAMILY*, Allah ya qara hada kanmu. 

*IYAYENA ABUN ALFAHARINA*
Kun kasance komai nawa, Alh Hassan Badaru, Allah ya gafarta maka yasa Aljannah ta xamo makoma a gareka😭😭
Mahaifiyata mai share hawayena Allah ya barmin ke Allah ya qara naki lapiya. 


_TAKU CE HAR KULLUM_
    
      ```BEELYBADARU😍```
[2/19, 8:23 AM] Beelybadaru😍: 🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
*SHI KADAI NAKE SO*
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
           ✨✨✨
              ✨✨
                 ✨

✨By Beelybadaru😍✨

       ✨81 to 85✨

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Gaba daya dakin suka maida kallonsu gareshi, lokacin har ya fara bude ido shi ya saukesu kan fuskar Khadeejah da hawaye suke ta sintiri akan fuskarta, dan murmushi ya sakar mata, Wanda daka ganshi xaka tabbatar da yana jin jiki sosai. 

Itama murmushin tayi tare da riqo hannunsa cikin shauqin so tama kasa yin magana, kallon juna suka shiga yi na tsawon lokaci, Muryar Daddy ce ta katse masu kallon da suke ma juna, duk suka waiga suka kalleshi, ita sai a lokacin ma ta lura da mutanen dake dakin, wata irin kunya ce ta rufeta. 

Ta sadda kanta qasa tare da qoqarin xare hannunta dake cikin nasa, gam ya riqe hannun yaqi saki don ji yake idan ya saki hannun xata tafi ta barsa ne. Daddy yace "Ahmad miye hakan kukeyi? Ka manta ita matar aurece? Ka sakar mata hannu su tafi". 

Sai a lokacin ya tuna da yau aka daura ma Khadeejah aure, wani xafi yaji a xuciyarsa, a hnkl ya fara sakin hannun nata hawaye na xuba a idanunsa, ya juyar da kanshi tare da runtse idonshi ba tare da yace komai ba, shi kadai yasan mai yake ji a xuciyarsa. Da sauri Khadeejah ta dago kanta ta kalli Ahmad dake xubar da hawaye, cikin sanyin jiki da qunar rai ta miqe tana girgiza kai hawaye na xuba a fuskarta ta nufi hnyr fita da dan saurinta. 

Saif dake bakin qofa yayi saurin tare ta, dago kanta tayi ta kalleshi cikin muryar kuka tace " Yah Saif ka bani guri na wuce,  baxan iya jurar ganin Abul cikin wannan halin ba". Daddy da Mummy duk suka kalleta da mamaki, ke an dama ita ce Abla, masoyiyar Ahmad ta yarinta?. 

Riqo hannunta Saif yayi ya jata xuwa gaban Abba sannan ya kalleshi yace "Abba miye kake boyewa haka? Ka fada masu gsky mn". Kallon Abban suka tsaya yi don jin wace gsky xai fada. Abba ya jawo hannun Khadeejah ya nufi gadon da Ahmad ke kwance har lokacin bai bude idonsa ba, jawo hannunsa yayi ya hada dana Khadeejahn, hkn ys Ahmad bude idonshi sannan ya waigo yana kallonshi. 

Cike da mamaki suke kallon Abba, me yake yi hk? Dadfy ne yayi qarfin halin cewa " Alh me hkn yake nufi?". Murmushi Abba ya danyi sannan yace "Sai mara imani ne xai iya raba wannan soyayyar da aka gina ta tun yarinta, Alh tun lokacin da na gane Tsantsar soyayyar dake tsakanin Ahmad da Khadeejah jikina yayi sanyi sosai, na xauna nayi naxari akan lamarin, ina son diyata sosai kuma ko kadan bana son ganin quncinta, hakan yasa naje har gida na samu manyan family dinmu nayi masu bayani nd xasu fahimceni, cikin ikon Allahk suka fahimceni din, nan aka kira Saifullahi aka yi mashi bayani shima ya gamsu sosai sai dai ya nemi alfarmar da a hada shi dako Ayusha ce mun amince mashi don ina da yaqinin Ayusha bata fara soyayya ba amma dik da hakan nace xan tambayeta in komai ya lafa. 

     Mun juya sa ranar xuwa ga Ahmad nace kar a fada masu har sai bayan an daura masu auren sannan su sani, to a yau ne aka daura auren Ahmad da Khadeejah". 

Kowa ya sake baki yana kallon Abba cike da mamakinshi, Daddy yayi qarfin halin cewa "Amma Alh ka shammace mu da yawa". Murmushi kawai Abba yayi. Daddy yace " Muje waje muyi magana". Ba musu kuwa Abba ya bishi suka fita daga dakin, Mummy ta kalli hj Waliyyah tace "mungode sosai Hjy". 

Umma tayi murmushi tace " Ba damuwa bari naje dakin can n hada kayayyakin mu don nasan sallama yau ne tunda an samui maganin ciwon". Duk sukayi dariya, mummy ta miqe tare da cewa "Ai lallai kam, muje na taya ki". A tare suka fita, Khadeejah ta kalli Yah Saif tace " Yah Saif nagode sosai". Dan murmushi yayi yace "Ki daina godemin Qanwata". Yah Mu'azzam ma murmushi yayi ya fita daga dakin. 

Yah Saif ya kalli Ayusha yace " Wifey muje ki tayani fira plx". Hararanshi tayi cikin wasa, kafin tayi magana yace "Wow wannandajin kallon fa?". Da sauri ta juyar da kanta tana dan murmushi, duk sukayi dariya, Saif yaja hannunta da tsiya suka fice daga dakin. Aliyu da Haydar suka miqe, Haydar yace " Uhm kunga bari muba big sia nd big bro guri su dan taba hirarsu", Khadeejah ta watsa mashi harara, dariya sukayi suka fice, Ahmad kau murmushi kawai yake yi. Farouq da Asy suka miqe suma suna dariya suka fice. 

A hnkl ta maida kallonta ga Ahmad da ta kafeta da Oily eyes dinshi a murmushi kwance a fuskarshi, itama murmushin tayi sannan ta dan harareshi tare da cewa "To ai saika miqe ko?". Dan maqe kafada yayi tare da cewa " Ni bana iya miqewa sai dai ki miqar dani". 

Dan waro ido tayi sannan tace "Ina xan iya tadaka?". Dariya yayi tare da cewa " Ashe amaryar tawa raguwa ce". Turo baki yi cikin shagwaba tace "Ni Allah A a xan iya". 

Tana fadar nan ta fara qoqarin janshi da nufin ta miqar dashi, dariya yayi sosai sannan ya jawota ta fada jikinshi, a hnkl ta dago tana kallonshi tana maida  numfashi a hnkl, kallon a sukeyi na tsawon lokaci cikin wata murya Ahmad yace " I love you soo much Khadeejah, I cant live without U, U r d only one in my heart". 

Dauke idonta tayi daga kallon da take mashi sannan cikin muryarta mai sanyi tace "I love u 2 Ahmad, its Ur luv dat made my life see the light beyoung my darkness". 

(Ni kam nace Hmmm)
 ```Beelybadaru😍```adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *