[10/11, 5:27 PM] +234 814 288 0264: 🍒🍒🍒
🍒🍒
🍒
*YARINYAR*
*BABA*
🍒🍒🍒
🍒🍒
🍒
_*Written & Edited*_
_*By Zee Mmn Khady*_
*```Just a short story```* 👌🏻
*Page* 1-10
🖍 "Gaskiya ni Momy bazani school d'innan ba, kawai sai mutum yaje wannan banzan malamin yari'ka yimashi kallon banza, kamar wata tsiya yafika, Ilham tafad'a tana shagwa6a.
Matar data kira da Momy tace "ke ilham banison shashancin banza da wofi, ki maza ki tashi kitafi tun kafin ranki yayi mugun 6aci cikin gidannan.
Wasu 'kyawawan yara su biyu mace da namiji 👫 'yan kimanin shekaru bakwai, suka fito sanye cikin uniform d'insu, gwanin ban sha'awa sukace "momy mun shirya, sannan suka maida dubansu ga ilham wacce keta zo6ara baki ita a dole bazata school ba, sukace "aunty ilham dan Allah ki shirya mutafi kinsan idan muka makara uncle zemana duka.....
Cikin masifa ta kallesu ta daka masu uwar tsawa 😁 "bazaniba nace ku wuce Ku bani wuri idan ba so kuke in 6ata maku rai ba, dan uwarku ni sa'arkuce dazakuce sai kunjera dani kuntafi school.....
Saukar wani lafiyyayen mari taji 👋🏻wanda momynta ta shimfid'a mata a kunci, wasu star's 💫✨ tagani suna zagaya mata kai saboda bala'in zafin marin saida ta fasa 'kara.
Hakan yayi dai-dai da fitowar dadynsu daga d'akinsa,
Ganinsa yasa ilham fad'uwa 'kasa kan kafet d'in dake shimfid'e tsakiyar falon tana kuka "wayyo Allah nashiga ukku dady ka taimakeni....
Da sauri yazo yakamata ya d'agota sannan ya rungumeta jikinsa yana tambayarta "lafiya ilham waye yata6a min ke,?
Cikin muryar kuka da shagwa6a take magana 😩 "momy ce wai dole sai naje school nikuma nace bazaniba.
Haba ilhama danme bazaki school ba ga 'kannenki sun shirya suna jiranki,
'Kara shagwa6ewa tayi tare da 'Kara narkewa jikin dad d'inta tace "ni bazaniba.
Cike daso da 'kauna dady ke rarrashinta yace "shikenan tunda baki zuwa je d'akinki ki kwanta ki huta, kukuma Hassan da hussaina kuje driver ya kaiku.
Yaran sukace "dady meyasa yau bazaka kaimu da kanka ba? Yace "saboda yayarku bazataba, dama saboda ita nake kaiku....
Yaran suka tafi suna turo baki, ☹ duk da suna yara basu son abinda dady yake masu, 'kiri-'kiri yake nuna yafison yayarsu akansu.
Cikin takaici Momy ta kalli dady tace "wallahi karage tsananin son da kake nunama ilham, saboda duniyar nan batada tabbas, kaso naka duniya ta 'kishi, ka'ki naka duniya tasoshi,...
Cike da jin haushin momy dady yafita yabar gidan, dan bayason jin maganar yarage nuna soyayya ga ilham, kullum fatanshi Allah 'kara ninka mashi son dayake mata a cikin zuciyarshi.💘
Cike da takaici momy ta nufi d'akinta, a zuciyarta tana cewa *Hmm yau naci sa'a ba'a rufeni da fad'a ba*
Dan some time duk randa tayima ilham fad'a itama ranar sai ranta ya 6aci...
💃🏻💃🏻💃🏻 love u all
📝 Zee Elkaseem
[10/11, 5:27 PM] +234 814 288 0264: 🍒🍒🍒
🍒🍒
🍒
*YARINYAR*
*BABA*
🍒🍒🍒
🍒🍒
🍒
_*Written & Edited*_
_*By Zee Mmn Khady*_
*```Just a short story```* 👌🏻
*Page* 11-20
🖍 Ilham kuwa tana shiga d'akinta kan gado ta fad'a ta jawo wayarta 'kirar iPhone6 tashiga danne-danne, kusan kullum haka take batada wani ayki daga karatun novel's sai games a waya, kuma a haka dadynta ya d'aure mata gindi yahana Momy ta tsawata mata, acewarshi Momy tabarta ta huta tunda itama Momyn ba wanda yahanata ta huta, tunda gidansu cike yake damasu yimasu hidima kome yaimasu ake hatta da sharar d'akin dasuke kwana akwai meyi.
Haka ilham tayita game a waya data gaji ta ajiye ta d'auko wani English novel tacigaba da karantawa, kusan awa biyu tana karatu, saida taji idanunta na zafi sannan ta tashi ta kashe fankar daketa faman juyawa tana ba d'akin iska, Ac ta kunna lokaci guda d'akin yad'au sanyi takoma tabi lafiyar gado, bacci me dad'i yayi awon gaba da ita.
Kusan awa ukku tana bacci, ba sallah ba salati, wannnan shine baccin asara, sai bayan sallar la'asar sannan ta tashi mi'ka tayi tare dayin wata uwar hamma, sannan ta fita falo, zama tayi kan dining sannan ta 'kwalama Ameeno kira, "Ameenoo.... Da gudu tazo har tana tuntu6e kad'an yarage yafad'i tace gani, cike da isa da gadara ilham take magana, "maza ki kawomin abincina, da sauri Ameeno ta amsa da "to ,sannan tanufi kitchen jiki na 'kyarma, Ameeno itace yarinyar dakema ilham hidima, wacce da kad'an ilham d'in ta girmemata, dan yanzu lham bata wuce shekara sha tara ba yayinda Ameeno takeda shekaru sha shida zuwa sha bakwai,.
Haka Ameeno takawo abincin tajera gaban ilham sannan tanufi pridge ta d'auko mata lemu da ruwa, saida ta tabbatar tagama had'ama ilham duk wani abu dazata bu'kata sannan takoma d'akinsu na 'yan aiki, saratu meyima su Hassan da hussaina hidima ta kalleta tace "hmm 'yar mulkin taki tatashi kenan, naga sai hidima kike tun d'azu, Ameeno tace kedai bari wallahi bacin Albashin da ake bani yanada tsoka da tuni nayi ritaya da aikin waccan 'yar izgilin.
Inna jummai dake zaune tana jin duk firarsu wacce itakuma itace me aikin Momy, a gidan dady ne kawai beda me aiki dan momy tahana tace itace zatari'ka yimashi kome, hatta da girki indai name gidanne ita ke Shig kitchen tayi dakanta.
Inna jummai tace "Hmm aini narasa halin wannan yarinya, wallahi Albasa batayi halin ruwaba, iyayenta mutanen kirki basuda wula'kanci, amma ita sai ahankali.
Haka 'yan aikin suka ri'ka tattauna matsalolinsu, da kokawa akan yanda ilham ke wulakantasu, hatta inna jummai wacce a girme ta girmi uwarta amma bata ganinta da gashin arzi'ki...
Love u all💃🏻💃🏻💃🏻
📝 Zee Elkaseem
[10/11, 8:09 PM] +234 814 288 0264: 🍒🍒🍒
🍒🍒
🍒
*YARINYAR*
*BABA*
🍒🍒🍒
🍒🍒
🍒
_*Written & Edited*_
_*By Zee Mmn Khady*_
*```Just a short story```* 👌🏻
*Page* 31-40
🖍"Hellow Leena kin isone, a d'ayan 6anagaren Leena tace "kefa nake jira ina a mota bakin get d'in gidanku kinsan su big boy basu san westing time, ilham tace "na dad'e da sanin haka gani nan fitowa yanzu, tafad'a tana niyyar ficewa daga falon.
Jitayi an shaqota an d'auketa da wani lafiyayyen mari wanda saida taga wani duhu ya gifta mata,
Momy ce ke cika tana batsewa tace "wallahi ilham bazaki fita a hakaba, kodai ki canja shiga kokuma ba inda zaki, ko ubanki daya d'aure maki gindi kina abinda kikaga dama nasan baze barki kifita a hakaba, kamar ba jinin musulmi ba.
Ilham kuwa dafe kunci tayi tana zubar da wasu zafafan hawaye, da gudu tanufi d'akinta kan gado tafad'a tana sharar hawaye, hankalinta be 'kara tashiba saida taduba madubi taga sawun yatsun Momy guda biyar kwance a kumatunta.
Gashi tariga ta 'kwallafa rai ga zuwa birthday d'in class mate d'insu akeyi kuma itace best friend d'insa tare ma zasu yanka cake, to idan batayi wannan shigar ba wace shiga momy keso tayi, sotake tasaka atamfa ko less idan taje a d'auketa bush girl, wasu zafafan hawaye suka 'kara zubowa a fuskarta tasa hannu ta goge.
Wayarta tashiga 'kara alamar 'kira na shigowa, kobata dubaba tasan Leena ce dan tasan tana Bakin get tana jiran fitowarta su wuce.
Bata ko kalli inda wayar takeba har tayi ringing ta tsinke, kira ya 'kara shigowa karo na biyu, sannan tasa hannu ta d'auka ta danna 'ok' sannan takara a kunne cikin muryar kuka take Sanar da Leena abinda Momy tayimata, wani irin haushin momy yakama Leena, shiyasama koda tazo bata shiga gidanba dan tasan data ganta da ahigar dake jikinta yanzu tafara yimata wata nasiha marar kai, wacce idan zata shekara tanayi bazatayi amfani da itaba.
Leena tace "kiyi ha'kuri kitashi ki saka wasu kayan saiki sako wannan a jaka idan mukaje can saiki canja,
Haka kuwa akayi wata jallabiya me adon duwatsu ilham ta saka sannan tayi rolling da gyalen jallabiyar wancan kayan kuma ta zubasu a site bag d'inta, sannan ta d'an gyara face d'inta tafito, bata ko kalli inda Momy takeba tasa kai tafice, cike da takaici Momy tace "Allah dai ya shirya.
Dan duk abinda ilham keyi dadyntane yake bata go a head, yanzuma wannan abin datayima ilham d'in dayana gidan da sai rayuka sun 6aci, dan Momy tarasa wane irin so yakema ilham, momy ta girgiza kai tace addu'a kawai zan dage dan Al'amarin ilham da dadynta sai du'a'i......
Love u all 💃🏻💃🏻💃🏻
📝 Zee Elkaseem
[10/11, 8:14 PM] +234 814 288 0264: 🍒🍒🍒
🍒🍒
🍒
*YARINYAR*
*BABA*
🍒🍒🍒
🍒🍒
🍒
_*Written & Edited*_
_*By Zee Mmn Khady*_
*```Just a short story```* 👌🏻
*Page* 21-30
🖍Ilham na kammala abinda take d'akinta tanufa toilet tafd'a kai tsaye ta she'ka uban wanka, tana fitowa taje gaban dressing mirror tafara d'and'asa kwalliya saida tagama sannnan tanufi wadrope d'inta wacce ke sha'ke da kaya ta tsaya tana tunanin wane zata Sanya, zuwa can ta hango wasu riga da wando English wear's shi ta d'auko haka ta sanya wando wanda yayi masifar d'ameta domin irin pencil d'innanne , sannan ta d'auko wata riga wacce zamu iya kiranta akwai ya babu, dan rigar purple colour ce tanada kwalliyar fari agabanta sai akayi ado da purple d'in duwastu aka rubuta *TOUCH ME* haka tasa rigar wacce ko hannuwan kirki batadasu gashinnan na kanta yasha gara ta d'aureshi ya zubu har kan kafad'unta.
Ba 'karamin kyau ilham tayiba kamar wata baturiya, dan kusanma tafi turawan kyau dan ilham kya'kkyawace ajin farko, farace me madai-daicin tsayi, tanada shafe me kyau, ga dogon hanci manyan idanuwa sai d'an 'karamin baki.
Bayan tagama shiri saida ta kalli kanta a madubi ko ita tasan tayi masifar kyau, sannan tajawo takalminta kalar purple me matsakaicin tudu ta Sanya, wani d'an yalolon gyale ta yafa a kanta wanda zamu iya kira akwai ya babu, dan kusan beda wani qmfani.
Haka tafito daga d'akinta tana taku ahnkali kamar wacce ke tausayin 'kasa.
Falo ta iske momynta, kallonta kawai tayi sannan tanufi 'Kofa tace Momy zanje Unguwa, Momy bata tanka mataba saida takai bakin 'kofa zata fita taji muryar momy tana magana cikin d'aga murya...
"Ilham kada ki kuskura kibar gidannan, cak ta tsaya dan duk abinta tana shakkar momynta, shiyasa tafison idan zatayi abu yakasance dadynta nanan, dan idan yana kusa momy bata Isa ta taka mata burkiba.
Muryar momyce ta dawo da ita Daga duniyar tunanin data Lula,
"Wallahi bazaki fita a hakaba kamar d'iyar kafirai, wai ilham kinada hankali kuwa?.....
Tsaye tayi bakin 'kofar batada niyyar motsawa, ringing d'in wayarta yasa ta motsa ta fiddo wayar Daga side bag d'inta, tana dubawa sunan 'kawarta tagani Leena, saboda haka da sauri ta danna OK dan tasan tare suka tsara tafiyar, sannan ta kara a kunnenta........
Love u all 💃🏻💃🏻💃🏻
📝 Zee Elkaseem
[10/11, 8:21 PM] +234 814 288 0264: 🍒🍒🍒
🍒🍒
🍒
*YARINYAR*
*BABA*
🍒🍒🍒
🍒🍒
🍒
_*Written & Edited*_
_*By Zee Mmn Khady*_
*```Just a short story```* 👌🏻
*Page*41-50
🖍 suna Isa gidan da za'ayi birthday d'in sukayi parking motor d'insu sannan suka fito, shigar da Leena tayi bazaka ta6a cewa tanajin yaren Hausa ba.
tun 'kofar gida sukejiyo sautin kid'a na tashi jikin ilham har tsuma yake dajin tashin kid'an,
A cikin gidan kuwa duk wanda yakamata ya halacci birthday din ya halarta mutum biyu kawai ake jira ilham da leena, in ran Hakeem yayi dubu ya 6aci sai cika yake yana batsewa gashi sai kiran wayarta yakeyi taki d'agawa, Hakeem ya kalli big boy yace "gskiya ilham bata kyautamin ba, ace duk taron nan ita kawai ake jira......
Big boy yace "nima inata try no Leena ya'ki Shiga......
Kafin yarufe baki yaga shigowarsu da sauri yataso ranshi 6ace yace haba ilham tun d'azu ake jiranki amma sai yanzu kikazo, kuma ji.....ji dan Allah wata shiga da kikayi miye wannan? Yafad'a yana nuna kayan jikinta.
Tace sorry my wlh Momy ce tayi west time d'inmu ka duba kaga face dina, yakai dubanshi ga fuskarta yaga sawun yatsu biyar kwance akumatunta take yaji tausayinta yakamashi yace sorry my dear, Yakama hannunta suka nufi wani d'aki a can ta canja kayan jikinta zuwa Wanda ta taho dasu a jaka, Hakeem yashiga rarrashinta har yasamu ta saki ranta, yayi murmushi yace yauwa my dear ga wannan ki saka a bakinki sweet ya mi'ka mata ba musu ta kar6a ta 6are ta jefa a bakinta, shima wani ya 6are yasa a baki.
Ilham kuwa tunda tasha wannan sweet d'in da hakeem yabata sai taji duk wani 'kunci da damuwa da 6acin ran da Momy tasata duk sun gushe.
Sun shiga gun birthday d'in mutane na zazzaune, suma sun samu guri zun zauna sannan aka fara gabatar da shagalin, ga kida sai tashi yake, ilham da Hakeem suka yanka cake mutanen gurin suka d'auki tafi, Hakeem ya yanko yasmata a baki, itama haka tayimashi,
Bayan wannan aka shiga shagali anata ciye-ciye da lashe-lashe, bayan angama kowa yakama harkar gabanshi wasu sun shiga fagen rawa wasu kuma sun kama friend d'insu sunata fira,
A da duk inda ilham taje magrib nayi idan hankalinta yayi dubu tashi yake, kuma kome take saita koma gida, amma yau sai taji duk wannan tsoron yafita daga zuciyarta, soyayya sosai sukasha a ranar itada Hakeem, Leena kuma itada big boy,
kada kuyi mamaki idan nacemaku duka gurin birthday d'in ba wanda ya haurama shekara ishirin, dan duk class mate d'insu ilham d'inne.
Haka sukayita bad'ala tsakanin mata da mazan gurin, sune basu tashi birthday d'inba sai karfe sha biyu da Minti ashirin da biyar na dare.
Hankalin ilham yayi matu'kar tashi lokacin data lura da daren datayi bata koma gidaba, cikin rud'ewa tafara magana "dan Allah Hakeem ka maidani gida wallahi nasan yau sai Momy ta 6atamun rai, Hakeem yayi murmushi yace kada ki damu babyna nina gayamaki yau Momy bazata maki fad'aba, dama nasan bakida matsala da dady, itadai hankalinta tashe yake tace nidai mutafi, yace "to muje, ilham ta kalli Leena wacce ke kwance kan cinyar big boy, yanata latsata bako kunya, tace "Leena nizan wuce kedai nasan ba yanzuba, Leena ta d'ago da rikitattun idanunta wad'anda suka canja launi saboda tsabar jaraba tace "ni gaskiya ba yanzuba sai naga abinda yaturema buzu nad'i.
Cikin minti sha biyar Hakeem ya sauke ilham 'kofar gida, kwankwasawa tayi megadi ya bud'e mata ta wuce, zaune ta taradda Momy da dady a falo da Alama dawowarta suke jira,
Ganinsu zaune yasa gabanta yayi mummunar fad'uwa sai yanzu ta tuna da kayan jikinta Wanda Momy tahanata fita dasune......
Love u all 💃🏻💃🏻💃🏻
📝 Zee Elkaseem
[10/11, 8:28 PM] +234 814 288 0264: 🍒🍒🍒
🍒🍒
🍒
*YARINYAR*
*BABA*
🍒🍒🍒
🍒🍒
🍒
_*Written & Edited*_
_*By Zee Mmn Khady*_
*```Just a short story```* 👌🏻
*Page* 61-70
🖍 Wani 'katon fili aka jiyeta tskiyar wasu mutane wanda ganinsuma abin tsoro ne, su duka sanye suke da jajjayen kaya sunyi d'amara da wani ba'kin kyalle sannan sun d'aura wani a kawunansu, fuskokinsu anyi wani zane a goshinsu da farin Abu, sannan bakunansu ba'kikkirin kamar sun shafa ba'kin tukunya.
Wata mace ce zaune kan wata katafariyar kujera wacce akayima kwalliya da zanen kwarangwal d'in kan mutum, matar tana ri'ke da wata farar yazga a hannunta, koda ganin matar basai ka tambayaba kasan itace shugabar wannan mutane.
Ilham na durkushe tsakiyarsu takasa d'ago da fuskarta barantana ta kalli mutanen dake gurin, saida wannan matar ta taso tazo gaban ilham ta nunata da wata sanda take wani haske yafito daga jikin sandar yashiga jikin ilham, lokacin ilham taji duk wani tsoro ya kawar daga cikin zuciyarta ta d'ago da manyan idanuwanta tari'ka bin mutanen dake gurin da kallo, abinda yabata mamaki shine mutum na farko data fara tozali dashi shine Hakeem best friend d'inta sannan big boy sai kuma Leena sai sauran class mate d'insu sunkai su goma sai sauran mutanen dabata saniba.
Wannan matar wacce itace shugaba ta kalli ilaham tace barka da shigowa wannan 'kungiya tajin dad'in rayuwa, my name is Abigael, nice shugabar wannan 'kunhiya tajin dad'in rayuwa yawanci duk wanda kikagani a nan suna cikin wannan 'kungiyar ne kuma sun shigetane dan sunason jin dad'in rayuwarsu batare da sun samu takurawa daga gurin iyayensu ko waniba.
Nasan jiya zakiyi mamakin yanda Momy takasa aiwatar da kome a kanki lokacin dakikayo dare gurin birthday d'in Hakeem to wannan 'kad'an kenan daga cikin aikin wannan 'kungiya tajin dad'in rayuwa idan zaki lura cikin wannan 'kungiya duk yarane yan kimanin shekaru sha takwas sha bakwai zuwa ishirin, zakiga a zahiri suna aikata abinda sukaga dama ba tare da iyayensu sun takurasuba duk da wasu daga cikinsu basuda iyayen kuma hakan besa sun shiga cikin gararin rayuwaba, to daga yau kema kinzama member ta wannan 'kungiya.
Sannan Abigael takoma kan kujerarta ta zauna bayan tagama ma ilham wannan bayani, ilham kuwa zuciyarta tagama dakewa da 'kungiyar lokacin tagama amicewa da zama yar 'kungiyar.
Abigael ta d'aga sandar tsafinta sama take wani haske ya mamaye gurin duka yan 'kungiyar suka had'a baki sukace
*AJI DA'DIN RAYUWA*
Abigael ta kalli ilham tace gobe munason jinin momynki koya yake kiyi kokari yazuba 'kasa.
Ba'a jira jin abinda zata fad'aba Abigael ta sallami taro Kowa Yakama gabansa.
Love u all 💃🏻💃🏻💃🏻
📝 Zee Elkaseem
[10/11, 10:28 PM] +234 814 288 0264: 🍒🍒🍒
🍒🍒
🍒
*YARINYAR*
*BABA*
🍒🍒🍒
🍒🍒
🍒
_*Written & Edited*_
_*By Zee Mmn Khady*_
*```Just a short story```* 👌🏻
*Page* 51-60
🖍 ilham tayi matu'kar mamaki yanda momynta ta tarbeta da fara'a ta taso tana cewa "ilham sai yanzu kika dawo kinsa munata jiranki dadynkima yakasa runtsawa saboda rashin ganinki, jiki na 'kyarma ilham tace "wallahi Momy abubuwane sukayi yawa a gun birthday kuma kinsan nice best friend d'in Hakeem dole kome dani za'ayishi yanzuma tahowa nayi badan angamaba kawai saboda ina tunanin kada kiyimin fad'a.
Sai lokacin dady yasa baki yace "ba damuwa ilham _*YARINYAR BABA*_ sunanda yake kiranta dashikenan "jeki ki kwanta ki huta, cike da mamaki ilham tanufi d'akinta a zuciyarta tana cewa _{yau meya faru da Momy hartakemun magana me taushi haka, Wanda nasan duk lokacin danayi ba dai-daiba ba wanda ya Isa yahana tayimin fad'a idanma duka yakama ta dokeni}_
Momy kuwa binta tayi da kallo tanason yimata fad'a amma data kalleta sai taji wani Abu ya dakar mata zuciya bakinta yayi nauyi takasa furta mata wata kalma me zafi.
Tana shiga d'akinta ta cire kayan jikinta ta d'aura wani d'an 'karamin towel tafad'a toilet ta ahe'ka wanka sannan tafito tashafe jikinta da wani lafiyayyen lotion me dad'in 'kamshi, sannan tasaka kayan bacci tabi lafiyar gado ba sallah ba salati, barantana tayi addu'a yayin kwanciya bacci.
Kullum idan ilham zata kwanta sai momynta tashigo d'akinta ta tambayeta tayi sallah idan batayiba nan zata tasata gaba tayi sannan tasata tayi addu'oi ta kwanta, amma yau Momy tana tunkaro d'akin ilham sai taji kamar ana ri'ke mata 'kafa ana maida ita baya, sai taji bata son zuwa d'akin ilham d'in komawa tayi d'akinta ta kwanta wani irin bacci me nauyin gaske yayi awon gaba da ita.
Ilham kuwa koda ta kwanta sai taji kanta yayimata wani irin nauyi, sai juyi take kan gado zuwa can sai taga d'akin na juyamata, lokaci guda wani irin haya'ki ya turnu'ke d'akin wanda idan da mutum ze shiga ciki baze iya ganin abinda ke gabanshiba, ganin haka yasa ilham rud'ewa wani matsanancin tsoro yashiga cikin zuciyarta duk illahirin jikinta 'kyarma yake,
Kusan mintuna sha biyar d'akin na juyamata sannan kome ya lafa yakoma yanda yake jitayi anyi sama da ita, tafiya akacigaba dayi da ita cikin sararin samaniya batare dataga Wanda ke tafiya da itaba.......
Love u all 💃🏻💃🏻💃🏻
📝 Zee Elkaseem
[10/11, 10:31 PM] +234 814 288 0264: 🍒🍒🍒
🍒🍒
🍒
*YARINYAR*
*BABA*
🍒🍒🍒
🍒🍒
🍒
_*Written & Edited*_
_*By Zee Mmn Khady*_
*```Just a short story```* 👌🏻
*Page* 81-90
🖍 Ke Ilham kada ki kuskura ki d'auki kudinnan.....
Ke yanzu dan kina hauka zaki d'auki dubu ishirin ki kaima wata dan zatayi birthday dan bakisan ciwon kankiba, ke shikenan kullum aikinki kenan daga biki sai birthday fatty, haba ilham kiyima kanki fad'a mana,
Sannan Momy ta juya gurin daddy tace "haba dadyn ilham bekamata ace ka d'auki kud'i kamar hakaba kaba ilhan takaima wata 'kawarta dan zatayi birthday fatty, ga mutane nan masu Neman taimako da yawa kaje ka basu mana Allah zebaka lada.
Daddy ya fusata da maganar Momy yace "banison abinda kikemun kibarni inyima 'yata duk abinda takeso idan banyimataba waye zanyimawa, ilham itace farin cikina kuma itace nafara sawa a idanuna amatsayin 'yarda na haifa, saboda haka kada ki kuma yimin haka.
Momy ta 6ata rai tace "to wallahi Alhj yau duk abinda ze faru saidai yafaru Amma wallahi ilham bata isa ta d'auko 20k takaima wata banzar 'kawaba wacce batada tarbiya, ni wallahi wannan makarantarma ko kad'an yanzu bani 'kaunarta.
Dady ya kalli ilham yace "jeki d'auko ninace ki d'auka kuma kud'inane bana momynkiba, ilham ta matsa da niyyar shiga d'akin Momy ta daka mata tsawa "kada ki d'auko....
Dady yace jeki d'auko.....
Ilham tawuce tasa kai d'akin Momy na kada tayi amma bata sauretaba ta kutsa kai cikin d'akin aiko a fusace Momy tabita d'akin ta ficikota ta falla mata wani lafiyayyen mari, tace wuce dan ubanki.
Ilham ta dafe kunci tafasa 'Kara saboda tsananin zafin marin da momy tayimata, jin haka yasa dady shigowa d'akin yana tambayarta abinda yafaru.
Su Hassan da Hussaina kuwa sungaji da jira saboda haka sukaje driver ya kaisu school, dan dama kullum shine ke kaisu idan kaji dady yace ze kaisu to tare da ilham za'ayi tafiyar to itakuma ba kullum take zuwa school d'inba.
Ranar dai hatsaniya akayi sosai tsakanin Momy da daddy, Momy kuma ta dage akan baza'a d'auki kud'inba 'karshema kulle d'akin tayi ta tafi d'akinta da key d'in.
Cikin 6acin rai daddy Yakama hannun ilham suka nufi mota, suna tafiya yana rarraahinta itakuma sai kuka take, har cikin ransa yakejin kukan nata,
Bank suka biya yasaka ATM 🏧 yaciro kud'i yabata 30thausand sannan ya wuce.
Haka ilham tashiga school d'in ranta 6ace.
A class ne bayan anyimasu break fast duk Kowa yafita amma ilham batada niyyar fita saboda har yanzu zuciyarta zafi take, tunda tashigo Hakeem ya kula da halin datake ciki saboda haka shima kasa fita yayi ya tsaya yana tambayar ilham dalilin 6acin ranta.
Nan ta kwashe kome tagayamshi, cike da damuwa yace "ilham bakiyi abinda Abigael tace kiyiba da kinyi da Momy bata Isa ta 6atamaki raiba, ilham ta share hawayenta tace kada ka damu Hakeem yau Dana koma zan aiwatar da kome, Hakeem yayi murmushi yace yauwa babyna saikin daure bekamata ace babbar yarinya kamarki kullum kina cikin 6acin raiba......
Aranar dai haka Hakeem ya rinka 'karfafama ilham gwiwa tare dayimata kalamai masu dad'i harta saki ranta.
Love u all 💃🏻💃🏻💃🏻
📝 Zee Elkaseem
[10/11, 11:21 PM] +234 814 288 0264: 🍒🍒🍒
🍒🍒
🍒
*YARINYAR*
*BABA*
🍒🍒🍒
🍒🍒
🍒
_*Written & Edited*_
_*By Zee Mmn Khady*_
*```Just a short story```* 👌🏻
*Page* 71-80
🖍Washe gari ilham ta tashi jikinta ba kwari ko kad'an, ba abinda take tunawa sai abinda yafaru da ita daren jiya, a zuciyaryta tace _(Ashe dama shiyasa su Hakeem da Leena da big boy basuda wata matsala a rayuwa kullum zaka gansu cikin farin ciki, basuda wata damuwa a rayuwa abinda sukeso shi sukeyi,)_
Ta numfasa tace _"to ay nima banida matsala kan kome tunda duk abunda nakeso dady yanayimin kuma bayason 6acin raina, matsalata dai Momy, kuma itama yanzu tazama labari tunda Abigael ta tabbatar min bazata 'kara yimin fad'aba zanyi duk abinda nakeso_.
Cike da 'karfin gwiwa ta tashi tafad'a toilet tayi wanka sannan takira Ameeno ta kawomata break fast, bayan ta gama shirin tsaf cikin kayan makarantarta, sannan tayi kalaci tagama ta tsallake ta wuce, bayan fitarta Ameeno tazo ta d'auke kayan ta maida kitchen...
d'akin su hassan da husaina ta wuce ta iske me aikinsu tagama shiryasu takamo hannunsu suka fito, falo suka iske Momy da daddy sun kammala nasu kalacin, dady cikin shigar manyan kaya yana shirin fita gurin aiki, ganin fitowar su ilham yasashi washe baki yana dariya yace "Ilham *_YARINYAR BABA_* yau zakije school d'in, cikin sanyin jiki tace "eh dady zanje, cikin fara'a yace to kuzo muje in saukeku, ilham tace "to amma dan Allah dady inaso kabani 10k zanba wata friend d'ina gudummuwa zatayi birthday, dady yace "ba damuwa kije d'akina ki bud'e loka ki d'auko 20thausand ay dubu goma me zasuyimaku a gun birthday, wani irin farin ciki yakamata tace 'thanks my dear dad, tanufi d'akin cikin rawar jiki a zuciyarta tanata godema dadynta da yanda yake biya mata duk wata bukata data kawomashi.
Harta kai bakin 'kofar d'akin, Momy ta daka mata tsawa
Ke Ilham dakata.....
Jiki na 'kyarma ilham ta tsaya cak inda take bata ko 'kara taku d'ayaba.
Momy tace kada ki kuskura ki d'auki kud'innan......
Love u all 💃🏻💃🏻💃🏻
📝 Zee Elkaseem
[10/12, 2:44 PM] +234 814 288 0264: 🍒🍒🍒
🍒🍒
🍒
*YARINYAR*
*BABA*
🍒🍒🍒
🍒🍒
🍒
_*Written & Edited*_
_*By Zee Mmn Khady*_
*```Just a short story```* 👌🏻
*Page* 91-100
🖍 Da misalin 'karfe d'aya aka tashi su Hassan da hussaina driver yazo d'aukarsu ilham naganin haka ta tattara yanata-yanata tayima 'kawayenta sallama, duk da ba wannan lolacin bane na tashinsu tunda yanzu ilham tana ss 3 ne sai 'karfe biyu ake tashinsu, yan biyu kuma suna primary 2 ne ana tashinsu 'karfe d'aya, abinda yasa zata bisu shine tanaso tayi amfani da wannan damar taba 'kungiuarsu jinin momynta, dan bakin iya 6acin rai yau momy ta 6atamata, amma daga yau angama.
Saboda haka 'yan biyu na isa gurin motar itama tana isowa, sun Shiga itama shiga kawai tayi ta zauna batare datacema kowa 'kala ba, husaina ce ta kalleta tace aunty ba'afa tashekuba kuma naga kin shigo mota,.....
Ilham ta daka mata tsawa na shigo d'in dan ubanki kinfini sanin ba'a tashemuba d'in, ainasani yanzu nakeson tafiya.
Hassan yace "mudai ki sauka kibari daddy yazo ya d'aukeki tunda dama kullum shine ke kawoki kuma yana d'aukok.......
Kafin ya ida fad'a tasa hannu ta dokemar baki, cikin masifa tace tunda bansan da hakaba Kaine zaka gayamani shashasha...ta buga uban tsaki mtswww...
Sannan ta kalli driver Wanda yake zaune shi betafiba kuma bece uffan ba, cikin d'aga murya tace dallah Malam mutafi kana 6atamin lokaci.
Jiki na 'kyarma driver yaja mota suka d'au hanya, dan yasan akan ilham ze iya rasa d'an Albashin dayake samu, kuma gashi dashi ya dogara.
Montocin da basu wuce sha biyuba suka sadasu da gida, sukayi horn megadi ya bud'emasu get suka shige.
Bayan ya ajiye motar inda aka tanada domin ajiye motoci, ilham ce tafara bud'ewa tafita, d'akinta ta wuce kai tsaye tafad'a toilet tayi wanka sannan ta canja 'kaya, ta kwalama Ameeno kira, saida gaban Ameeno yayi mugun fad'uwa danjin ilham a gida yanzu, kuma tasan indai taje school ba yanzu bane lokacin dawowarta, jiki na 'kyarma ta isa ta dur'kusa tace gani, ilham tace jeki kawomin lemu da cake yauba saikin yimin girkiba, cike da farin ciki Ameeno tabar d'akin zuwa kitchen dan kowoma *_YARINYAR BABA_* abinda ta bu'kata.
Saida ta kammala sannan tafita zuwa d'akin momynta, bata isketa d'akiba sai motsi dataji a kitchen saboda haka nan tanufa dan tasan yanzune lokacin da Momy ke shiga kitchen domin had'ama daddy abinci.
Ranta yayi fari dan ganin Momy zaune kan kujera a kitchen tana yanka d'anyar ku6ewa, domin yau abinda zata had'ama megidan kenan tuwom semo da miyar d'anyar 'ku6ewa.
Love u all 💃🏻💃🏻💃🏻
📝 Zee Elkaseem
[10/12, 3:02 PM] +234 814 288 0264: 🍒🍒🍒
🍒🍒
🍒
*YARINYAR*
*BABA*
🍒🍒🍒
🍒🍒
🍒
_*Written & Edited*_
_*By Zee Mmn Khady*_
*```Just a short story```* 👌🏻
*Page* 111-120
🖍 A yau 'kungiyar *Aji dad'in rayuwa* tayi bikin karrama ilham akan namijin 'ko'karin datayi gurin kawo jinin momynta, hakan ba 'karamin cigaba yakawoma 'kungiyarsuba, dan tsafi ya nuna cewa shigowar Ilham wannan 'kungiya babban cigabane agresu.
Saboda haka Abigael ta tabbatarma ilham daga 'yau batada sauran 6acin rai danagane da wani d'an Adam adoron 'kasar nan, kuma daga yau zata fara jin dad'in rayuwarta batare da momynta ta takurataba, dama batada matsala da daddy, Hakeem kuwa sai Kallon ilham yake yanamata murmushi, itama murmushin take tare dajin dad'i acikin ranta.
💤💤💤💤💤💤💤💤💤
Tun daga wannan lokacin ilham tari'ka yin abinda taga dama fita kuwa idan zatayi Momy bata isa tahanataba, kaya sai wanda taga dama take sanyawa, mini siket da body hug, da wando pencil sune kayan fitar ilham zuwa unguwa daddy kuwa yana gani beta6a hanataba, saima duk abinda take bu'kata ya sakarmata mukullin ma'ajiyar kud'insa kullum ta eba yanda takeso bedamuba domin kud'in akwaisu.
Mota ilham ta gayama daddynta tanaso yasiyamata, gaban momy suka ajiye magana ta fad'amashi irin wacce takeso yayimata Al'kawarin zuwan motar cikin wannan satin,
Momy kuwa data yun'kura zatayi magana tanaso tahana amma bakinta sai yakasa furta kome kamar ansa kwad'o da makulli an rufemata baki.
Saida suka gama maganarsu daddy yacema ilham taje ta shirya ze kaita shopping, aiko cike da murna tanufi d'akinta shima nashi d'akin yawuce.
Sunfito cikin shiri daddyn ilham sanye cikin jaket masu ruwan 'kasa ilham kuma wani matsiyacin wando tasanya wanda yafito da duk wani shape na jikinta, sai wata riga wacce batada maraba da bes, kanta bako d'an kwali tayi parking d'in gashinta, sannan suka wuce momy tana zaune tana kallonsu tanason magana amma takasa.
Sai bayan fitarsu wani kululun ba'kin ciki yatokaremata a wuya, da sauri tashige d'aki tafad'a gado tafashe da kukan ba'kin ciki.
Kuka tayi sosai sannan tatashi jikinta duk ba kwari tafad'a toilet tayo Alwala ta kabbara sallar nafila, bayan tagama ta dad'e zaune tana addu'oi sannan taji sau'kin ba'kin cikin dake damunta.
Cikin satin motar ilham ta 'karaso had'ad'iyar mota 'kirar camry dunkulalliyar kalar ja me duhu, ilham tayi farin ciki sosai, tun daga lokacin ta'karo wulakanci tacigaba da baza tsiyarta.
Momy kuwa ta du'kufa da addu'a kullum ba dare ba rana, saboda tayi imanin addu'a itace takobin 🗡 mumuni.
Love u all 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
📝 Zee Elkaseem
[10/12, 3:08 PM] +234 814 288 0264: 🍒🍒🍒
🍒🍒
🍒
*YARINYAR*
*BABA*
🍒🍒🍒
🍒🍒
🍒
_*Written & Edited*_
_*By Zee Mmn Khady*_
*```Just a short story```* 👌🏻
*Page* 131-140
🖍 lham lafiya mike damunki, tundaga d'akina nake jiyo ihunki kina fad'in impossible, meye baze yiyuba?
Cikin tsananin rud'ewa jikinta na 'kyarma tace "ba kome kawai nayi wani mafarkine wanda ya tsoratani,
Cike da damuwa momy tace ilham dole kiri'ka muyagun mafarkai ilham baki damu da addininkiba, baki damu da sallah ba barantana addu'a
Nidai sai dai ince Allah kyauta.
Haka momy tabar d'akin ilham zuciyarta cike da tunani barkatai, al'amarin ilham yana matu'kar tsoratata, gashi ko kad'an bata iya tsawatar mata.
A ranar haka ilham ta wuni sukuku ba 'karfi jikinta ko kad'an tana tunanin yanda zata tseratar da daddynta daga sharrin Abigael,
Bakin iya tunani tayi amma batasamu wata mafitaba.
Washe gari kuka ilham tayini tanayi ta kulle kanta cikin d'aki, dan jiya 'kungiya ta tabbatar mata da kada ta kuskura tawuce kwana biyu bata bada jinin daddyntaba.
Haka tayi kuka tagode Allah batare da wani yasaniba, har kanta yafara ciwo.
_*BAYAN KWANA BIYU*_
Yaune kungiya ta ibarma ilham kada ta wuce bata kawo jinin mahaifintaba,
_*Misalin 'karfe 3:00am na dare*_
Taron 'kungiyane kamar yanda suka saba, saidai yau tsai-tsaye suke yayinda Abigael ke zaune kan katafariyar kujerarta, ilham kuma tana dur'kushe gabanta tana sharar hawaye,
Cikin tsananin 6acin rai Abigael ta kalli ilham tafara magana tare da mi'kewa tsaye tana nunata da sandar dake hannunta
"Kisani ilham baki isa kisha jinin iyayen wasu ba kuma kiyi arzi'ki da kud'in kiji dad'in rayuwa kekuma kice baza'aji dad'i da jinin iyayenkiba.
Tunda kika shigo cikin 'kungiyarnan yau tsawon shekara bakwai bamu nemi wani kwa'kkwaran Abu daga garekiba sai yau, saboda haka dole kibi umarni ko kinso, ko kin 'ki.
Sannan kisani guri na'kara kure mana kinaso ki kawo mana cikas, tokisani gobe da daddynki yashiga toilet da niyyar yin wanka baze fito da raiba, dole ne musha jininsa yanda akasha jinin iyayen Kowa cikin wannan 'kungiya.
Abigael nagama fad'in haka taro yatashi, ilham na dur'kushe inda take takasa ko motsin 'kirki sai wasu hawaye masu yaji ke zuba daga idanunta.
'Dago kan dazatayine taga wayam ba Kowa gurin ba Alamr mutane sun zauna, hakan ya tabbatar mata duk sun tafi,
Wata uwar 'kara tayi sannan tafd'i gurin tana birgima,
Jitayi andafata Hakeem tagani, cike da tausayawa yake rarrashinta, har a zuciyarshi yakejin ilham besan 6acin ranta amma yazasuyi dokar 'kungiyace dole tabi, haka Kowa yayi.
Sai gab da dallar asuba sannan ilham da Hakeem sukabar gurin.
Love u all 💃🏻💃🏻💃🏻
📝 Zee Elkaseem
[10/12, 3:33 PM] +234 814 288 0264: 🍒🍒🍒
🍒🍒
🍒
*YARINYAR*
*BABA*
🍒🍒🍒
🍒🍒
🍒
_*Written & Edited*_
_*By Zee Mmn Khady*_
*```Just a short story```* 👌🏻
*Page* 141-150
🖍 washe gari da misalin 'karfe tara na safe,
Zaune suke kan dining suna breakfast
Kowa naci hankalinsa kwance
Amma banda ilham wacce taketa juya spoon d'in cikin cup d'in tea ba abunda ke zuciyarta sai tunanin yanda zata ku6utar da daddy daga hannun shugabar 'kungiyarsu Abigael.
Duk abinda ilham keyi daddy na kula da halin datake ciki
Saboda haka shima duk sai yaji yashiga damuwa lokaci guda
Ya maida dubansa ga ilham yace _*"YARINYAR BABA*_ meke damunki?
Da sauri takai dubanta ga daddy sannan tasaki fuskarta ta 'ka'karo wani busashshen murmushi Wanda zamu iya kira da ya'ke Wanda yafi kuka ciwo tace
"Ba kome, cikin damuwa daddy Yakama hannunta ya had'e danashi cikin sigar rarrashi yake magana
"Haba ilham ashe akwai wata damuwa dazata sameki ki 6oyemin.
Ilham ta wasance tace wallahi daddy ba kome, kawai hakanan naji jikina ba dad'i amma yanzu ma naji kome ya wuce.
Duk abinnan Momy na zaune tana kallonsu, bata sanyamasu bakiba, illah wani irin 6acin rai dake addabar zuciyarta
Ganin yanda daddy kullum yake 'kara shagwa6a ilham
Gashi itakuma yanzu bata iya hana kome.
Cikin jin dad'i dady yace "yauwa ilham d'ita kinsan banison 6acin ranki ko kad'an, wani murmushi ilham tasaki wanda bekai cikiba.
Dady yace "yanzu dai ki shirya mufita shan ice cream, ko kin washe dan banison kina shiga damuwa,
'Kila idan muka fita muka d'an zaga gari kin warware.
Su Hassan da hussaina dake zaune sunajin duk yanda daddy ke rarrashin ilham kamar wata 'karamar yarinya,
Wanda kosu beyima haka, suda suke 'kannenta wacce tabasu kusan 9 Year's, sukace "daddy muma muna zuwa....
Kafin su ida fad'a ya tari numfashinsu tare da d'aga masu hannu yace "kubari anjima driver ya kaiku banison 6ata lokaci....
Sunajin haka suka nufi d'akinsu suna turo baki dan sun dad'e da sanin yanda daddy ke nuna banbanci tsakaninsu da 'yar'uwarsu.
Bayan sun wuce ne daddy ya kalli ilham yace bari inshiga toilet inyi wanka,
Kema kije ki shirya, bejira jin amsar dazatabashiba yanufi toilet d'in
Ilham tayi saurin binshi takamo hannunshi idanunta na zubar da hawaye tace dan Allah daddy kada kayi wankannan......
Dady yace dan me?
Ilham tarasa amsar dazata bashi sai hawaye dake zuba daga idonta.
Ganin batada niyyar yimashi magana yasa ya zare hannunshi daga nata tare da saka 'kafarshi toilet d'in.
Love u all 💃🏻💃🏻💃🏻
📝 Zee Elkaseem
[10/12, 3:35 PM] +234 814 288 0264: 🍒🍒🍒
🍒🍒
🍒
*YARINYAR*
*BABA*
🍒🍒🍒
🍒🍒
🍒
_*Written & Edited*_
_*By Zee Mmn Khady*_
*```Just a short story```* 👌🏻
*Page* 151-160
🖍 saka 'kafar daddy keda wuya cikin toilet d'in ya dorata akan wani jan abu me kama da bawon ayaba, wanda keda tsananin tsantsi sai kuma ya had'u da santsin tiles d'in dake toilet d'in 'kafarsa tayi gaba yayinda yakasa d'aga ta bayan, kawai sai jinsa yayi 'kasa tare da sakin wata razananniyar 'kara
Da gudu Momy tayo kansa tana salati, amma kafin ta 'karaso inda yake har rai yayi halinsa.
Wata irin razananniyar 'kara ilham tasaki lokacin da aka tabbatar mata da mutuwar daddynta, tashiga rera wani irin kuka na fitar hayyaci,
Koke koke akayi sosai 'yan'uwan daddy Dana momy duk sunzo akayima daddy sutura aka kaishi makwancinsa.
*su daddy an kwanta dama, oh,oh duniya kenan*
💤💤💤💤💤💤💤💤💤
Yau kwanan daddy bakwai da rasuwa ilham bataje meeting d'in 'kungiyaba, saboda haka 'kungiya tayi matsanancin fushi da ita,
Yau da misalin 'karfe biyu da rabi na dare duk 'yan 'kungiyar sun halarta hada ilham, gurin yayi tsit Kowa yana jiran jin irin hukuncin da Abigael zatayima ilham dan ba wanda besan yanda Abigael take jiran zuwan ilham ba,
Saboda tsarin 'kungiyarsu ba'a fashin zuwa meeting saboda hakan ba 'karamin cibaya yake kawomasuba rashin zuwan d'aya daga cikinsu.
Cikin bala'i da matsanancin 6acin rai Abigael ke magana "ilham kina nema kikawo mamu na'kasu cikin wannan 'kungiyar tamu, a tarihin wannan 'kungiya yau tsawon shekaru goma sha biyu kenan da kafuwarta amma babu wanda yata6ayin fashin kwana biyu be halarci taroba, amma ke yau tsawon kwana bakwai bakizoba, sabida haka yanzu zamuyimaki hukunci dai-dai da laifinki.
Sannan ta kalli sauran 'yan 'kungiyar tace kunsan duk wanda yayi fashin kwana d'aya bulala goma ce, saboda haka zamu had'a goma sau bakwai zamuyima ilham hukunci kamar yanda akema kowane d'an 'kungiya.
Hakeem najin haka hankalinsa yayi matu'kar tashi dan yasan da'kyar idan akayima ilham bulala saba'in ta rayu saboda yasan azabar bulalar ana bugunka kamar ana zubama wuta ajiki.
Saboda haka cikin tsananin tausayin ilham yafito ya dur'kusa gaban Abigael sannan ya had'e hannuwansa alamar Neman alfarma yace "ina neman alfarma daga gareki shugaba da a rangwantama ilham sakamakon jikinta baze iya d'aukar bulalar 'kungiya d'ai-d'ai har saba'in ba.
Hakeem yanada 'kima a idon Abigael baze iya naman wani Abu tahanshiba, saboda haka aka sassautama ilham zuwa bulala hamsin.
Ilham na dur'kushe gaban Abigael,
Abigael ta nunata da hannu take wata igiya ta d'ad'd'aureta ta yanda ko motsin kirki bata iyawa, sannan tanunata da sandar tsafinta bulalace taji tanata sauka ajikinta me tsananin azaba batare dataga Wanda ke dukantaba.
Haka akayimata bulala hamsin tanata ihu, bayan an gama ne, Abigael tace "sannan kuma hukuncin na 'karshe agareki muna bu'katar jinin momynki daga yau zuwa gobe, bamu buk'katar 6ata lokaci.....
Love u all 💃🏻💃🏻💃🏻
📝 Zee Elkaseem
[10/12, 3:41 PM] +234 814 288 0264: 🍒🍒🍒
🍒🍒
🍒
*YARINYAR*
*BABA*
🍒🍒🍒
🍒🍒
🍒
_*Written & Edited*_
_*By Zee Mmn Khady*_
*```Just a short story```* 👌🏻
*Page* 161-170
🖍 washe gari haka ilham ta tashi cikin tsananin tashin hankali, dan yanzu tariga tasan Momy kad'ai taragemata idan taba 'kyngiya jininta wane hali zasu shiga itada 'kannenta,
Wani irin kuka tafashe dashi, kukan yinsa take kamar na fitar rai har batasan shigowar momy d'akin ba.
Momy takai kimanin minti goma tsaye tanama ilham magana amma ilham batasan da zuwantaba, saboda haka zama tayi gefen gadon tare da dafa ilham d'in tace "ilham meke damunki,? Meyasa kike kuka haka,?
Wani irin rud'u ilham tashiga dan batasan da zuwan momy d'akinba.
Saboda haka batada amsar dazataba momy kawai sai tafad'a jikin Momy tacigaba da wani irin kuka me tsuma zuciya,
Momy kuwa ganin ilham na kuka batasan lokacin da itama wasu zafafan hawaye suka zubo daga idanuntaba, tashiga rarrashin ilham dan a tunaninta ilham tana kukan rashin mahaifinta ne.....
Haka sukayita kuka bame rarrashinsu, ilham dai tana kukan yanda Abigael takeson takawo jinin momy, itakuma momy tana kukan tausayin 'yarta dan tasan irin sha'kuwar dasukayi da mahaifinta.
Ranar haka ilham tawuni baci ba sha, duk tabi tafita hayyacinta, momy tayi rarrashin harta gaji, tasamata ido.
_*3:00am*_ na dare, duk yan 'kungiya sun halarta, yayinda ilham take dur'kushe gaban Abigael tanata kuka tana ro'konta akan tabarmata momynta kada takasheta, wata irin mahaukciyar dariya Abigael ta 6a66ake da ita, sannan ta d'ad'd'aure kamar bata ta6a koda fara'aba tace ilham kina wasa da 'karfin tsafin wannan 'kumgiyar amma yanzu zakiga abin mamaki.
Momy na kwance kan katafaren gadonta tana bacci marar dad'i, duk tahad'a uban gumi sakamakon mafarkin datakeyi meban tsoro daban mamaki.....
Abigael dake zaune kan katafariyar kujerar tsafinta tayi nuna wani iccen bedi dake nesa kad'an da gurin dasuke, saiga momy ta bayyana d'ad'd'aure jikin iccen anyimata mugun d'auri yanda ko motsin kirki bata iyawa.
Abigael tayi nuni da momy tare da cewa ilham kalli can,
Cikin sanyin jiki ilham takai dabanta ga inda Abigael ta nunamata
Wani irin matsancin tashin hanakali tashiga sakamakon ganin momynta daure jikin iccen bedi gakuma wani 'katon mutum ya tunkareta da wata shar6e6eyar wu'ka da niyyar soka mata ita aciki.
Ilham naganin haka batasaan lokacin datafasa wata uwar 'karaba tanufi gurin da gudun tsiya wanda ita kanta batasan tanadashiba, yayinda shima wanda ze kashe Momyn ya zura a guje yanufi momy da wu'ka tsirara a hannunsa.
Amma kafin yakai ga momy ilham ta isa ta shige gaban momyn takareta, shikuma idanunshi sun rufe besan lokacin daya caka wukar da niyyar cakata a cikin momy, amma sai ya cakata a cikin ilham
Lokacin tasaki wata mahaukaciyar 'kara wacce duk illahirin dajin saida ya amsa, tafad'i nan ba alamar numfashi tattare da ita.
Lokacin momy tafarka daga mawuyacin baccin datake duk tahad'a uban gumi kamar an she'kamata ruwa,
Lokacin kuma mugun mafarkin datayi da ilham yashiga dawomata a kwalwa.
Cikin tsananin firgici tatashi ba abunda bakinta keyi sai addu'oi tanufi d'akin ilham dan ganin halin datake ciki.
Love u all 💃🏻💃🏻💃🏻
📝 Zee Elkaseem
[10/12, 3:47 PM] +234 814 288 0264: 🍒🍒🍒
🍒🍒
🍒
*YARINYAR*
*BABA*
🍒🍒🍒
🍒🍒
🍒
_*Written & Edited*_
_*By Zee Mmn Khady*_
*```Just a short story```* 👌🏻
*Page* 171-180
🖍 Da hanzari momy ta Isa d'akin cikin tashin hankali dan ganin ilham kwance 'kasa tayi wata irin kwanciya wacce daganin wanda yayita kasan be cikin lafiyarsa koma ace babu rai tattare dashi,
Ilham......ilham....ilham...momy tashiga jijjigata tana kiran sunanta, amma ba Alamar numfashi tattare da ita, cikin tsananin tashin hankali momy takira Ameeno me aikin ilham takama mata ilham suka kaita mota driver yaja suka nufi asibiti.
Suna zuwa aka nufi emergency da ita wani likitane ya tabbatar masu da mutuwar ilham.
Nan momy ta aza hannu aka tafashe da wani irin matsanancin kuka me ban tausayi, haka aka d'auko gawar ilham aka koma da ita gida,
Bayan sunkoma ne momy tashiga kiran 'yan'uwanta dana daddyn ilham tana sanar dasu, cikin 'kan'kanin lokaci gidan yacika da jama'a haka akayima ilham sutura aka kaita kushewa.
🤔 _*Oh ilham anshafe babinta tazama labari,*_
_*Ya Allah ka tsare mana 'ya'yanmu a duk inda suke, Allah karesu daga duk wani sharri na duniya Allah kabamu ikon tarbiyantar dasu tarbiya tagari*_.
A gurin 'kungiya kuwa tun lokacin da 'yan 'kungiya sukaga yanda akyima ilham kisan wula'kanci duk sai hankalinsu yatashi dan basu ta6a manta ranar da aka kafa 'kungiya saida Abigael ta tabbatar masu babu cuta ba cutarwa ga 'yan 'kungiya, amma gashi yau an kashe 'yar'kungiyar kenan suma watarana za'a iya kashesu.
Aiko nan suka shiga magan-ganu 'kasa-'kasa take suka yanke shawara tsakaninsu, aiko kamar had'a baki sukayo kan abigel suna fad'in bazamu ta6a yarda da kisan 'yar'uwarmuba, suka rufar mata da duka, kafin ta farga sunyimata laga-laga, saida suka tabbatar dabata numfashi sannan suka barta, amma meze faru suduka suka kasa matsawa daga inda suke, yayinda wani ba'kin haya'ki ya turni'ke gurin suduka suka shiga wani irin mawuyacin hali wanda ko nufashi basu iya maidawa.......
Hakeem kuwa yana gefe ba abinda yake sai zubar da hawayen ba'kin cikin kisan da'akayima ilham d'insa.
Yana kallon yanda 'yan kungiyar keta wahala cikin wannan ba'kin haya'kin me tsananin yaji.
Love u all 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
📝 Zee Elkaseem
[10/12, 3:54 PM] +234 814 288 0264: 🍒🍒🍒
🍒🍒
🍒
*YARINYAR*
*BABA*
🍒🍒🍒
🍒🍒
🍒
_*Written & Edited*_
_*By Zee Mmn Khady*_
*```Just a short story```* 👌🏻
*Page* 181-200
🖍 haka sukacigaba da sha'kar azababben hayaki me d'aci da yaji cikin 'kan'kanin lokaci numfashinsu yafara d'aukewa, kafin kace me wasu dayawa daga ciki sun rasa rayuwarsu,
Haka Abigael tacigaba da sarrafa tsafinta saida ta tabbatar da duk 'yan 'kungiyar sun mutu bame sauran numfashi sannan ta 6a66ake da wata mahaukaciyar dariya.
A hankali Hakeem ya bud'e idanunshi wad'anda ko gani baya iyayi sosai, yacigaba da jan ciki yana matsawa daga inda yake, har ya isa inda wukar da aka kashe ilham take yade yasa hannu ya d'auko.
Abigael kuwa tajuya bayanta, tanata zuba wata uwar mahaukaciyar dariya, dan ganin tayi nasarar kashe mutanen dasukayi niyyar kasheta, har Hakeem yazo gaf da ita batasan yazoba saboda tsananin sautin dariyar datake gagga6awa, dan yanzu burinta idan kome ya lafa zata sake sabbin yan kungi.
Hakeem kuwa iya 'karfinsa ya da6ama Abigael wannan wu'kar gefen cikinta, wata matsananciyar 'kara tasaki tare da d'aga sandar tsafinta ta bugama hakeem a ka, shima wata uwar 'kara yasaki lokaci guda sukayi mutuwar kasko.
_*Wannan shine 'karshen 'kungiyar aji dad'in rayuwa tare da 'yan 'kungiyar baki d'aya*_.
Bayan kwana bakwai da rasuwar ilham, momy ta aiki Ameeno me aikin ilham kasuwa tasiyo mata cefane, kan hanyarta ta dawowa gida taga an dadda6e wani me siyar da jarida anata siye matsawa tayi itama dan ganema idonta, ganin hotunan su ilham 6aro-6aro cikin shigar yan mafiya yasa hankalinta yayi masifar tashi, kud'i tami'ka itama ta siyo sannan ta wuto gida.
Bayan taba Hajiya cefanen tawuce d'akinsu can ta iske jummai me aiki dame aikin 'yan biyu, bata tsaya wata-wataba ta tattara yanata-yanata tace tom sai anjimanku ni aikina daga yau yakare gidannan, su jummai suka tambayeta dalili bata tsaya wani dogon bayaniba tami'ka masu jarida tafice ko bankwana batayima momyba tabar gidan.
Su inna jummai ma koda suka fahimci abinda jaridar ta kunsa tattara yanasu-yanasu sukayi sukabar gidan tare da bawa momy jaridar.
Koda momy ta karanta tayi kukan ba'kin ciki, 'karshe kuma tagodema Allah dayasa ilham ta mutu kafin ta kashesu, amma dukda haka tanamata addu'ar neman gafara gurin ubangiji itada mahaifinta.
_*Alhmdulillahi Anan nakawo 'karshen wannan takaitaccen littafin nawa, ina fatan masu karatu sun ilmantu kuma sun nishand'antu sun kuma d'auki darussan dake ciki*_
Litatafan marubuciyar.
1)Siyasa ko soyayya
2)Duniya juyi
3)Halin girma
4)Gidan Asali
5)Autar Hajiya
6)Alhini
7Yarinyar baba.
💗 *ZANEN ZUCIYA*💗
*Coming* 🔜
```Kyakkyawar gaisuwa ga group members *Ciwon ya mace* *Zee Mmn khady fans nd novel*```
*Sai kunjini a sabon littafina bye*
Love u all 💃🏻💃🏻💃🏻
📝 Zee Elkaseem