Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Wednesday, 21 August 2019

AMRAH NAKE SO COMPLETE (HAUSA NOVELS FACEBOOK)

adsense here
AMRAH NAKE SO COMPLETE (HAUSA NOVELS FACEBOOK)

[7/3, 8:40 AM] Princess Amrah???: *??MRAH NAKE SO!* ?(Labari mai ta?a zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi)

              Na Amrah A Msh
              _(Princess Amrah)_
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*

_Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (sickler)_


*Gabatarwa:-* Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah ma?aukakin sarki. Tsira da aminci su ?ara tabbata ga shugaban halitta, Annabi Muhammad (SAW) tare da AlayenSa.
   Kamar yanda na fara wannan littafin da IzininSa, ina fatan kammalashi da amincewarSa (Allah ma?aukakin sarki)

*GARGA?I:-* Wannan labarin ?ir?irrarre ne ba da gaske ba ne. Dan haka ban yarda wani ko wata su juya min labari ta ko wace siga ba. Duk wanda ya cire sunana ko ya ?ara wani abu ba da izinina ba *ALLAH YA ISA BAN YAFE BA.* Dan haka a kiyaye.*GODIYA:-* Bayan na mi?a godiya ga Allah ma?aukakin sarki, dole na mi?a godiyata ga ?ungiyar *NAGARTA WRITERS* saboda sun cancanci yabo da godiya. Allah Ya saka masu da alkhairi a kan namijin ?o?arinsu.

*JINJINA:-* Dole na mi?a sa?on jinjina ga ?awayen albarka *RAZ (Rabiatu sk msh and Zarah bb)* Allah ya bar zumunci ya ?ara mana ha?in kai.

*SA?ON GAISUWA:-* Ina gaishe da masoyana maza da mata, wanda na sani da wanda ban sani ba. Ku sani cewa Amrah mai ?aunar duk wani masoyanta ne wanda ta sani da wanda bata sani ba. Fatana a kullum shi ne Allah Ya ?ara mana son junanmu.

*ALBISHIRINKU:-* Ina mai maku albishir da cewa gani tafe da wannnan littafi mai ?unshe da soyayya da ban tausayi, kamar yanda masoyana suke yawan cewa bana masu littafin soyayya to yau gashi nan ina fatan zaku fa?akartu kuma zaku amfana da duk abin da zaku karanta a ciki.


                          0?1?


_Ranar talata, karfe 4:25 na yamma._Sanye take cikin zureriyar hijabi ruwan ?asa mai hannu. Hannunta wanda ta fiddo wajen hijabin ri?e yake da wata makimanciyar jaka, a ?ayan hannun kuma wayarta ce ?irar Samsung S7 edge.

 A hankali cike da natsuwa take taku har ta isa bakin gate ?in Islamiyar tasu.

?alibai ne ke shiga manya da yara, maza da mata.

?aga kanta ta yi a dai-dai saman gate ?in ta kalli rubutun da aka yi wanda fenti ne fari sai rubutun kalar tsanwa an rubuta *MADRASATUL-AMRAH BNT ABDALLAH.* Da larabci aka yi rubutun sai kuma daga ?asa aka rubuta da hausa.

Sunkuyar da kanta ta yi ?asa bayan ta gama karantawa ta gya?a kai hawaye na zirara daga idanuwanta.

Cikin makarantar ta nufa kai tsaye ta nufi ajinsu mai suna *FASLUL-KHAMIS (ALIYU BN ABI ?ALIB)*

Jiki a mace ta zauna kujerar gaba wadda ita ce kujerarsu. Saurin goge hawayenta ta yi jin Jidda na fa?in "To uwar hawaye. Wani abun ne hala?"

Murmushi ta ?ir?iro tare da fa?in "Babu komai Jidda. Me kika gani?"

"Fuskarki na gani kamar kin yi kuka. Kuma na san baya miki wahala dama." Jidda ta fa?a bayan ta dawo bisa kujerar ita ma ta zauna.

"Ko ka?an ban yi kuka ba. Iskan nan da ake ne ina hanya ?ura da ?asa suka bu?a?e ni har cikin ido. Shi yasa idona ya canza launi, kuma ga ra?a?i da yake yi min."

"Allah sarki! Ba laifi kam ana iska. Allah Ya kyauta. Yau kin makara, lafiya dai ko?"

Ajiyar zuciya ta sauke ta ce "Na yi lecture ne 2-4, ina dawowa a makare ko abinci ban tsaya na ci ba na taho Kuma gashi ma ashe malam bai shigo ba."

Kafin Jidda ta bata amsa sai ga wani malami ya shigo hannunshi ri?e da Umdatul-ahkam.

Bayan ya yi sallama sun amsa ne suka gaishe shi tare da fito da littattafansu suka bu?o dai-dai inda zasu tashi.

?aya bayan ?aya sai da kowa ta karanto inda aka masu baya sannan malamin mai suna Malam Yusuf ya yi masu ?ari kasantuwar ya ga mafi rinjaye sun fahimci darasin da ya gabata.

Yana fita Mallam mai Fiqhu ya shigo shima ya masu darasin sannan aka tashi daga makarantar.

Bayan sun fita sai da budurwar ta sake ?aga dara daran idanuwanta ta kalli sunan Islamiyyar cike da tausayi sannan ta sunkuyar da kanta ?asa ta tafi gida. A zuciyarta tana mai tsananin ?agara ranar jumu'a ta yi.

***

Da sallamarta ta shiga gidansu wanda yake ba wani babba sosai ba, sai dai daka ga gidan ka san suna da rufin asirinsu bakin gwargwado.

Wata matashiyar mata wadda ba zata wuce shekara talatin da biyar (35) ba ta amsa sallamar tana murmushi ta ce "Maryama an dawo?"

"Na dawo Mama. Aiki ake?" Ta tambaye ta bayan ta ?arisa shiga Kitchen ?in.

"Wallahi kuwa. Abbanki ne ya kirani wai yana son tuwon dare, shi ne fa na tashi da azama na ?ora masa. Har ma na gama tuwon miya ce ta rage." Maman tata ta fa?a tana zuba man-ja a tukunya.

"Kawo na ?arisa miki Mama." Maryama ta cire hijabinta ta rataye a kan ?ofar kitchen ?in ha?e da jingine jakarta jikin bangon kitchen.

"A'a Maryama. Ke da kika dawo daga makaranta? Na tabbata a gajiye kike, saboda ko abincin rana baki ci ba kina dawowa daga lecture kika yi shirin islamiya. Je ki cire Uniform ki zo kafin nan na zuba miki abinci."

"Wallahi Mama bana jin yunwa. Ki kawo na miki tun da dai ba wani aiki nake ba. Kullum ina makaranta ke ce kike yin komai. Dan Allah ki bari ni ma yau na samu wannan ladar."

Mama ta murmusa ta ce "Tun da dai kin matsa gashi nan ki ?arisa. Allah Ya miki albarka ke ma Ya ha?a ki da wanda zasu kyautata miki kamar yanda kike kyautata min."

"Amin Mama." Ta fa?a ha?e da kar?ar ludayin miyar ta kwashe jajjagen tarugu da albasa da daddawa dake cikin turmi.

Cike da natsuwa Maryama ta kammala miyar busasshiyar ku?ewa ta barta a bu?e dan kar ta rufe ta tsinke.

Hijabi da jikarta ta ?auka sannan ta nufi ?akinta domin gabatar da sallar magrib.

Bayan ta gama ta zauna ta yi adhkar har lokacin isha'i ya yi sannan ta fito sanye da dogon hijabi har kasa ta nufi ?akin Abbanta.

Zaune yake shi da Mamanta sai kuma ?aninta zaune a kasa.

Cikin ladabi ta gaishe da Abban nata sannan ta ce "Sannu da hutawa Mama." Ta zauna a ?asa kusa da Muhammad.

"Yauwa Maryama. Ai ke ke da sannu." Ta mata murmushi.

"Yaya Maryama sannu da aiki." Muhammad ?an kimanin shekara goma sha biyu ya fa?a.

"Yauwa ?an albarka. Ya tahfiz ?in?" Ta tambayeshi.

"Akwai wahala Yaya. Ko yau na sha zana duba bayana ki gani." Ya fa?a yana ?o?arin ?aga rigarshi ta baya.

"Ba sai ka ?aga min ba dan ba tausayinka zan ji ba. Ban san me ya sa ba Muhammad baka son karatu." Ta fa?a bayan ta ha?e fuskarta babu alamun wasa.

Cikin sigar a tausaya masa ya ce "Ina fa karatu Yaya. Malamin namu ne..." Ta yi saurin dakatar da shi,

"Kar ka ma malaminku sharri. Idan baka masa laifi ba ai ba zai dake ka ba. Ka ringa karatu sosai kuma ka guji aikata laifi ka ga idan akwai malamin da zai ta?a lafiyarka."

Shiru ya yi kafin ya yi dariya abinku ga ?aramin yaro ya ce "Kuma fa Yaya kin yi gaskiya. Kin ga Haneef shugaban ajinmu ba'a dukansa saboda kullum sai ya bayar da harda babu tangar?a. Kuma baya laifi ko ka?an."

"Ka gani ba. Kai ma sai ka yi koyi da shi ai, idan baka son duka." Ta fa?a tana masa murmushi.

"To Yaya. Bacci nake ji ma." Ya yi hamma.

"Bara na kawo mana tuwo sannan kaci ka yi bacci ko?" Ta mi?e tsaye.

Mama ta ce "Ai ni dai kawaici na yi dan na ga kuna fira da Muhammad. Yunwa nake ji  wallahi."

Abba ya ce "To ai gashi nan zata kawo yanzu"  Ya murmusa.

Ta nufi kitchen tana murmushi.

Misalin karfe tara suka kwanta kamar yanda suka saba da wuri suke kwanciya bacci gidan.*RANAR JUMU'AH 10th January 2015*
Pinky durling??
*RAZ 2????*
[7/3, 8:40 AM] Princess Amrah???: *??MRAH NAKE SO!* ?


(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi.)

            Na Amrah A Msh
           _(Princess Amrah)_
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


_Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (sickler)_


                          0?2?

A k'agare take ta iso gida domin tafiya Islamiya, amma wani Malaminsu mai Chemistry ya rik'e su har kusan k'arfe biyar na yamma. Yi take tana duba agogon wayarta, baki d'aya hankalinta ya koma ga ta tafi, har wasu hawaye take ji suna k'ok'arin fito mata.

Jin hak'urinta ya k'ure ya sa ta tattara ya-nata ya-nata ta mik'e tsaye, tun kafin ta fito daga row d'insu ta ji muryar malamin yana masu bankwana alamun ya gama lecture d'in ke nan.

Ajiyar zuciya ta sauke, had'e da godiya ga Allah sannan a hanzarce ta fita, ko k'awar tata ma bata tsaya jira ba.

Course mate d'insu Saifullahi ta gani bisa mashin d'inshi da alama yana jiran wani ne, amma Maryama sai da ta rok'e shi a kan ya taimaka ya tafi da ita sauri take.

Bai ko musa mata ba ya ce ta hau su tafi.

A maimakon ta kwatanta masa gidansu sai bata yi ba, islamiyyarsu kai tsaye ta sa ya kaita.

Cikin mamaki Saifullahi ya ce "Yau Friday ana Islamiyya ne Maryam?"

"Ba darasi zamu yi ba Saif, akwai abin da muke ne." Ta bashi amsa tana mai k'ok'arin sauka daga bisa mashin d'in. "Na gode k'warai Allah ya bar zumunci."

"Ameen Maryama. Allah ya bada sa'a. Sai anjima." Ya tada mashin d'in ya tafi.

A gaggauce ta isa bakin gate d'in, ta samu mai gadin zaune da radio rik'e a hannunsa.

"Sannu Baba. Mun yi da kai da an yi la'asar zan zo kuma sai gashi na kasa cika al-k'awari ko? Yi hak'uri, wallahi wani malaminmu na tsaya ya sallame mu."

Murmushi dattijon yayi ya ce "Babu komai ai. Kina lafiya ko?"

"Lafiya lau Baba. Mu tafi gidan nasu ko?" Ta tambaye shi.

D'aga mata kai ya yi tare da jawo 'yar k'aramar k'ofar da ke jikin gate ya rufe da kwad'o sannan ya soka makullin a al-jihunsa.

Mashin d'insa ya hau sannan ita ma ta hau daga baya  suka kama hanyar unguwar Gidan dawa da ke cikin Birnin Katsina.

Tafiya mai nisa ce ta sada su da gidan, kasantuwar akwai 'yar tazara daga Islamiyyar.

Bayan sun isa Malam Sallau ya kashe babur d'insa sannan ya ce "To Maryama mun iso, kin ga gidan nan."

K'ok'arin sauka ta yi a hankali bisa rashin sani har k'afarta ta d'an gogu a salansar mashin d'in, ta k'one kad'an.

"Subhanallahi!" Ta furta a hankali bayan ta k'arisa saukowa.

"Bi a hankali dai Maryama." Ya fad'a bayan ya gyara tsayuwar babur d'in.

"Mu shiga ko?" Ta fad'a cikin sanyin murya.

"Anya kuwa? Ki shiga dai, ki sanar da su idan sun bani izinin shiga sai in shigo."

Kallonshi ta yi kamar kar ta yi magana kuma dai ta daure ta ce "To Baba ai kuma basu san ni ba."

Da murmushi ya ce "Babu komai ai. Ki shaida masu cewa tare kike da Mallam Sallau, ba damuwa."

D'aga kai ta yi tare da shiga cikin gidan da sallama k'unshe a bakinta.

Gida ne ginin har k'asa irin na da, wanda kallo d'aya zaka masa ka tabbatar cewa gidan mabuk'ata ne.

Shiru ba'a amsa ba hakan ya bata damar sake yin wata sallamar nan ma dai shiru.

Sai a karo na uku sannan ta ji muryar dattijuwa ta amsa sallamar tana k'ok'arin fitowa daga cikin d'aki.

Ganin Maryama ya sa ta d'an saki murmushi irin ba wai dan ta santa ba, sai dan karamci kawai.

"Barka da zuwa. Iso daga ciki mana." Matar ta fad'a fara'a k'unshe a fuskarta.

Kai ta d'aga alamar to, sannan ta k'arisa ciki.

Tabarma matar ta shimfid'a mata sannan ta bata izinin zama ta zauna.

"Sannu Mama. Ina yini." Maryama ta furta cikin girmamawa.

"Lafiya k'alau 'yan mata. Sannu fa." Ta fad'a cikin rashin wayarta.

"Tare nake da Mallam Sallau, yana waje." Ta fad'a tana kallon Matar.

"Allah sarki! Yo to kuma ai da sai ya shigo ko? Shi dai Mallam Sallau kullum kamar bak'o. Dan Allah je ki k'ira sa da sauri. Mallam!" Ta k'walawa mai gidanta k'ira.

Tashi Maryama ta yi ta nufi waje tare da k'iran Mallam Sallau. Tana gaba yana biye da ita suka shigo ciki.

Matar ce zaune a bisa tabarmar sai mai gidanta a kusa da ita yana murmushi.

Mik'ewa ta yi da sauri ta ce "Mallam Sallau zauna daga nan. 'Yan mata zo mu shiga daga ciki ko?"

Da sauri Mallam Sallau ya ce "Ahh babu damuwa, ku zauna kawai, ai magana zamu yi."

Hannu ya mik'awa mutumin zaunen suka gaisa sannan ya zauna a kusa da shi.

Maryama kuma aka shimfid'a masu wata tabarmar suka zauna tare da matar.

Bayan sun gama gaggaisawa ne Mallam Sallau ya ce,

"Wannan yarinyar sunanta Maryama. D'aya daga cikin d'aliban Islamiyar *AMRAH BNT ABDALLAH.* Ta jima tana son sanin tarihin rayuwar *Amrah* tun daga lokacin da aka yi wani wa'azi; wanda Malamin ya d"auko zancen *Amrah* tun bai yi nisa ba kuma sai lokaci ya k'are. Tun daga lokacin take son sanin *Wacece Amrah?* ta same ni da maganar ya fi sau biyar, tun ina gudunta da maganar dai har na ce ranar wannan jumu'ar ta zo zan kawo ta domin ta ji daga gare ku. Ina fatan hakan ba zai zama takura ba."

Kallonsu suka mayar ga Maryama da ta d'an sunkiyar da kanta k'asa tana wasa da 'yan yatsun hannunta.

Matar ta ce "Allah Sarki!" Tare da share d'an siririn hawayen da ya fito mata.

Shi kuwa mutumin cikin k'arfin hali ya ce "Babu wata takura Mallam Sallau. Sai dai kuma gashi yamma ta yi yanzu magrib ta gabato."

Mallam Sallau zai yi magana Maryama ta yi saurin fad'in,

"Ehh wallahi. Babu damuwa ai ko gobe ma sai in zo ko da ni kad'ai ce. Tun da dai mun zo tare na ga gidan."

"Haka ne. Allah Ya kaimu to." Mutumin ya fad'a.

Cikin k'arfin hali Matar ta ce "Insha Allahu gobe zaki ji tarihin rayuwar *Amrah.* Zaki san ko wacece *Amrah Bnt Abdallah.* Ta sake share hawayen bisa kumatunta.

Sosai Maryama ke mamaki, lallai ta yarda cewa babu abin da ke cikin *Rayuwar Amrah* face tsabar tausayi, duk da yake bata san komai ba, abin da ta sani dai kawai ita Amrah d'in mace ce mai matuk'ar halin kirki, wacce ke da tarihi mai kyau kuma abin koyi.

Bankwana suka yi ta masu godiya sosai sannan suka fita waje ita da Mallam Sallau.

Har gida ya kai ta ta masa godiya sosai ta shiga ciki.

Tana shiga bata samu kowa a tsakar gida ba, kai tsaye ta zarce ciki.

Muhammad ne da gudu ya rungume ta yana fad'in "Yaya Maryama kin dad'e fa. Ina ta jiranki ki dawo ki koyan karatu, gashi gobe da sassafe zan bada harda kuma ban iya ba."

Da murmushi ta ce masa "Wallahi Muhammad na je wani wuri ne bayan na tashi daga makaranta. Amma gashi na dawo ai yanzu sai mu yi. Mama fa?"

"Tana cikin d'aki yanzu Baba ya dawo ne. Zaki koyan yanzu ko sai an yi sallah?" Ya tambaye ta.

"Bari a yi sallah tukuna. Ka ga fa ko abinci ban ci ba. Kar ka damu insha Allahu zan koya maka har sai ka iya sannan zamu daina." Ta sakar masa murmushi.

Shi ma murmushin ya sakar mata ya ce "Allah Ya yarda Yayata. Ki je yanzu ki yi wanka ki ci abinci ko?"

Kai ta d'aga masa sannan ta shige d'akinta.

Jakarta kawai ta ajje sannan ta yi wanka ta fito

Ta samu har Mama ta kawo mata abinci ta rufe da plate, ga kuma abin sha nan a jug da k'aramin cup


Murmushi ta yi mai cike da nuna jin-dad'i,

"Wayyo Mamana. Allah Ya saka miki da alkhairi." Ta fad'a sannan ta zauna ta fara ci. Zuciyarta cike da tsumayen gobe ta yi, duk da yake cewa akwai Islamiyya kuma bata son ta yi fashi amma fa bata jin zata iya hak'ura har a tashi. Ta k'udurta cewa da yardar Allah gobe k'arfe goma a gidan su Amrah zata mata.

Bayan ta gama ne ta koyar da Muhammad karatu har ya iya sosai sannan ta koma d'akinta.

Wayarta ta latso lambar Jiddah, babu jimawa kuwa ta d'auka.

Sallama ta yi bayan sun gaisa ne take shaida mata cewa idan ta je Islamiyya gobe ta fad'a ba zata samu damar zuwa ba, akwai inda take son zuwa ne.

Jidda ta ce "Kin manta gobe akwai rehearzal (Gwajin koyo) k'arfe tara? Da dai kin yi hak'uri Maryama, ko idan kika yi naki ne sai ki tafi."

Jinjina kai Maryama ta yi ta ce "Jiddah kin san fa ba lallai Mallam Ahmad ya bar ni tafiya ba duk iya k'wa-k'wata kuwa. Gashi kuma inda zan je yana da matuk'ar muhimmanci."

"To shi ke nan babu damuwa. Zan sanar ma Mallam Yusuf shi ne mai sauk'in kai. Allah Ya taimaka."

Murmushi Maryama ta yi ta ce "Yauwa na gode k'warai Jiddah. Sai da safe, ki gaishe da Mami."

"Zata ji." Ta tsinke wayar.

Jikin chaji ta jona wayar sannan ta koma ta kwanta. A zuciyarta tana nazarin wata magana wadda ita kad'ai ta saka ta fashewa da kuka.

Juye-juye kawai take yi bacci ya k'i d'aukarta, da k'yar ta samu ya d'auke ta a lokacin har sha biyun dare ta wuce.Pinky durling??
*RAZ 2????*
[7/3, 8:40 AM] Princess Amrah???: *??MRAH NAKE SO!* ?


(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi.)

            Na Amrah A Msh
            _(Princess Amrah)_
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


_Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (sickler)_


                          0?3?

Washe gari tun da safe ta tashi ta hau shiri, k'arfe bakwai da rabi Muhammad ya shigo da gudu yana fad'in,

"Yaya Maryama na shirya, wai ki fito in ji Baba."

Juyowa ta yi ta kalle shi ba tare da ta ce komai ba, sai dai kuma kallon da ta masa kawai ya isa ya tabbatar masa da laifinsa.

"Yi hak'uri Yaya Maryama." Ya fad'a a marairaice.

"Oya get out." Ta gwada masa k'ofa da hannu.

Kama kunnuwansa ya yi ya ce,

"Zan yi yanzu Yaya." Ya fita daga d'akin.

"Assalamu alaikum." Ya fad'a da k'arfi wanda har sai da dariya ta nemi k'wace ma Maryama.

Amsa sallamar ta yi ta ce "Ko kai fa. Ka tafi kawai Muhammad. Ka ce da Baba akwai inda zan biya ne kafin in tafi. Kar in tsaida ku kuma na san tahfiz d'inku babu wasa. Ka ga ko karyawa ma ban yi ba."

"To shi ke nan Yaya. Na tafi." Ya yi gaba.

Addu'a ta masa sannan ta ci gaba da shirinta cike da natsuwa, wanda dama halinta ke nan, komai nata a natse ne, slow d'in nata ma har ya yi yawa kamar wacce k'wai ya fashe mawa a ciki.

Misalin takwas da kwata ta gama shiri ta fito falo, Mama ta samu zaune da littafin hisnul-muslim a hannunta tana karantawa.

Ganin haka ya sa ta nufi kitchen, ruwan lipton ta zubo sannan ta zuba soyayyar doya a plate ta dawo falon.

A hankali take karyawa har ta gama sannan ta fitar da kayakin ta kai su kitchen. Ko da ta dawo har Mama ta gama adhkar d'in.

Gaishe ta ta yi sannan ta ce,

"Mama har an gama?"

Da fara'a Mama ta ce,

"Wallahi kuwa na gama Maryama. Ya aka yi yau kika makara? Na san halin malaman nan naku fa wani lokaci ba sani ba sabo ne."

"Ai da yake yau zamu fara rehearzal ne Mama. Duka d'aliban ma za'a ke fiddowa a fili muna yi a gabansu. Tun daga nan har lokacin walimar." Maryama ta bata amsa tana k'ok'arin zura hijabinta da ta ninke ta d'ora a bisa hannun kujera.

"Af! To masha Allahu! Allah Ya taimaka. Dawowa ba yanzu ba ke nan ko?"

"Gaskiya kam Mama. Wata k'ila ma ta-zarce zamu yi har shida na yamma sannan mu dawo." Maryama ta fad'a, ba kuma 'karya ta yi ba, haka tsarin abun yake, sai dai kuma ita kam ba can zata nufa ba, sai idan ta gama abin da take da wuri ne zata je ko da da yamma ne.

"Bara na tafi Mama." Ta fad'a tana k'ok'arin fiddo hannunta daga hannun hijabin.

"Allah Ya bada sa'a. Sai kin dawo."

"Ameen Mama." Ta fita daga d'akin.

Sai da ta koma d'akinta ta d'auko kud'i sannan ta fita.

A dai-daita sahu ta tsayar ta kwatanta masa unguwar.

K'arfe tara da minti ishirin ta mata a k'ofar gidan su Amrah. Bayan ta sallami mai adai-daita ta shiga gidan da sallamarta.

Amsawa matar gidan ta yi sannan Maryama ta shiga ciki da fara'a.

"Sannu da zuwa Maryama. Iso ciki." Ta fad'a cikin karramawa.

Shigowar kuwa ta yi har falo matar ta kai ta. Wasu irin tsofaffin kujeru ne irin wanda sun ji duniya d'in nan, katifar jiki duk ta gama lalacewa sai zallar katako wanda idan mutum bai kula ba ma tsaf zai iya jin ciwo.

Bayan ta zauna matar ta ce,

"Bara na kawo miki koko. Sai dai kuma  yanzun nan na ba almajiri k'osan, saboda kar ya sandare kuma ba cinsa zan yi ba, kokon ma a samus na zuba shi ne."

"Wallahi Mama ki bar shi na gode. Sai da na karya ma sannan na baro gida." Maryama ta fad'a.

"Eyyah! To shi ke nan ai. Ina zuwa." Ta fita daga falon.

Babu jimawa sai gata ta dawo, zama ta yi daga d'an nesa da Maryama san nan ta ce,

"Yanzu zan baki labarin Amrah, Maryama."

Gyara zama Maryama ta yi ta ce,

"To ina jin ki Mama."

"Sunanta ke nan na yanka Amratu. Amrah muke kiranta da shi ni da mahaifinta.

Amrah ita ce 'ya ta uku a gidan nan, sai dai kuma matsayin ita ce babba, kasantuwar duk yaran da muka haifa basa rayuwa.

Tun daga lokacin da muka haifi Amrah, mahaifinta ya d'auki soyayyar duniya ya d'ora a kanta, yake bata kulawa sosai fiye da sauran yaran da muke haifawa basa rayuwa.

Tun Amrah na da shekara d'aya a duniya take da wani laluri, na yawan k'ai-k'ayin tafin k'afa da kuma tafin hannu.

Abin mamamki, yarinyar da bata san wani abu ba a duniya, amma duk lokacin da tafin k'afarta ko hannunta ya dame ta da k'ai-k'ayi, da 'karfi zata kama hannuna ko na mahaifinta tana kai wa a inda yake mata k'ai-'kayin, da nufin a sosa mata.

Tun bamu fahimtar komai har ta kai ga mun fara fahimta, wato dai suna damunta da k'ai-'kayi ne.

A lokacin da ta cika shekara biyu a duniya ne kuma cututtuka suka fara nata yawa, wato yawan zazzab'i, sannan kuma da yawan ciwon gab'ob'i.

Yarinya k'arama 'yar shekara biyu, wacce ko maganar kirki bata iya ba, amma ta san ta ringa gwada duk inda ke mata ciwo tana fad'in,

"Hannu ciwo, cici ciwo, kai ciwo..." da dai sauransu.

Tun bana d'aukar abun serious har na fara damuwa, saboda har cikin dare idan abun ya tasar mata ko kad'an bama bacci, ita kuka ni kuka, mahaifinta ne kawai mai dakewa, yake k'arfafa min guiwa a ko da yaushe.

Ga ta da yawan yin zazzab'i, da zarar sauro ya cije ta sai zazzab'i, idan ta fara zazzab'in kuma shi ne sai wannan ciwon gab'ob'in wanda yake rikita mana lissafi.

Duk wannan abin da yake faruwa, ciwo da yake ta addabar Amrah, ko da wasa bamu tab'a gwada kai ta asibiti ba. Wani lokacin idan zazzab'in ya dame ta ne da kanshi Babanta yake zuwa chemist cewa 'yarsa na zazzab'i, sai a bashi maganin zazza'bin kawai ya zo a bata.

Wata rana, k'anwata ta zo daga Kaduna, ta zo ganin gida shi ne ta zo min wuni, ta samu Amrah bata da lafiya, na tasa ta a gaba ina mammatsa mata duk gab'ob'inta da take gwada min suna mata ciwo.

Cikin tausayi ta ce,

"Wai Yaya Murja me yake damun yarinyar nan ne? Abin tausayi har ta iya fad'in inda ke mata ciwo? Alamun ma ta saba ke nan."

Gyad'a kai na yi na ce,

"Zainabu ni kaina ban san me yake damun Amrah ba. Sai dai kawai na san zazza'bi ne idan ta yi shi yake sakar mata ciwon gab'ob'in nan. Tun da nake haifar yarana suna mutuwa ban tab'a had'uwa da mai irin ciwon da Amrah ke yi ba. Zainabu na fara tsorata sosai wallahi." Ta fashe da kuka tana kallon Amrah.

Ita kam Amrah baki ta wangale tana dariya, shi k'aramin yaro dama babu ruwanshi, yanzu zai gama kukan ciwo kuma yanzu zai kama dariya.

Zainabu ta numfasa sannan ta ce,

"Kuma ku baku tab'a kai ta asibiti ba?"

"Bamu tab'a ba Zainabu. Sai dai kawai Babanta da yake siyo mata magani. Yanzu haka tana da sauran panda yana nan bai k'are ba." Na bata amsa.

"Gaskiya Yaya Murja ku daure dai ku kai ta asibiti. Kar a je ana ciwo daban, magani daban. Likita bashi da halin bada waraka, sai dai kuma yana bada tashi gudunmawar. Ki daure dai a kai ta d'in."

Shiru na yi ina nazari a azuciyata. Na san tabbas gaskiya Zainabu ta fad'a min, sai dai kuma babu hali ne. Abincin da zamu ci ma wahala yake mana. Kuma ba wai zuwan ne nake ji ma ba, a'a, kud'in da za'a caje mu nake ma. Tun da dai komai na yanzu ya koma na kud'i.

"Kin yi shiru Yaya Murja. Gaskiya nake fad'a miki fa. Bai kamata ku zauna kuna ji kuna gani ciwo ya ringa cin yarinya ba. A ce wai yarinya da zarar ta yi zazzab'i sai k'asusuwanta su hau ciwo? Gaskiya akwai dai wata matsalar daban, ba wai zallar zazzab'i ba ne."

Cikin k'arfin hali na ce,

"Insha Allahu ranar litinin zan kai ta asibiti. Ni kaina abin yana damu na bani da yanda zan yi ne."

"To Allah Ya kai mu Yaya Murja. Allah kuma Ya bata lafiya." Ta mik'e.

Bankwana muka yi sannan ta tafi ta bar ni da tunanin kalamanta, hawaye na zirara daga idanuwana zuwa kumcina.Pinky durling??
*RAZ 2????*
[7/3, 8:40 AM] Princess Amrah???: *??MRAH NAKE SO!* ?


(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi.)

            Na Amrah A Msh
            _(Princess Amrah)_
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


_Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (sickler)_


                          0?4?

Sai dare sannan mahaifinta ya dawo, a gajiye lis yake, wanda kallo d'aya zaka masa ka tabbatar da baya tattare da walwala.

Duk da cikin halin da nake, na tausayin ciwon Amrah, bai hana ni tashi na tarbe sa ba.

"Sannu da dawowa Mallam. Zauna ka huta kafin na kawo maka abinci." Na fad'a ina mai k'ara dubar yanayinsa.

"To Murja." Ya fad'a jiki a sab'ule.

Kitchen na nufa na zubo masa dafadukar shinkafa da na ajje masa, na d'ibo ruwa daga tulu na kawo masa.

Sai da ya ci ya yi nat, na tabbatar ya samu natsuwa sannan na ce,

"Allah dai Ya sa an yi nasara."

Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce,

"Babu nasara Murja. Abin dai sai hamdala kawai." Ya kalle ni ya gyad'a kai, sannan ya ci gaba da fad'in,

"Duk yinin nan guda da muka sha, wai Alhajin ya fasa zuwa. Har fa lokacin da na ga magrib ta yi na ce ni dai zan tafi, wasu suka ce in dai k'ara ha'kuri, an tabbatar cewa yana gari wai zai zo. 'Yar d'ari biyun da nake da ita, da ita na ci abinci da rana, naira ta hamsin d'aka da waje yanzu haka. Ban san ya zan yi ba Murja. Talauci babbar cuta ce, wacce samun maganinta yake da matuk'ar wahala." Ya dafe kansa.

Cike da tausayi na ce,

"Sai hak'uri Mallam. Ta ko wace hanya Allah Yana jarrabtar bayinSa. Hakan kuma ba wai yana nunar da baYa sonmu ko kuma Ya manta da mu ba ne, a'a, na tabbatar cewa mun fi wasu, tun da mu da wuya mu rasa abin da zamu ci. Wasu kuwa babu, abin da zasu saka ma cikinsu ma wata wahala ne. Fatana dai kawai Allah Ya bamu ikon cinye wannan jarabawar."

"Ameen. Wai duk jiran nan da muka yi, sai bayan isha'in nan wani d'an korensa ya zo yana fad'in mu tafi, wai Alhaji ba zai samu zuwa ba, sai kuma wani lokacin. Dama kyauta ce ya yi niyya ba rok'arsa aka yi ba, kuma wani uzuri ya sha gabansa."

"Shi ke nan ai Mallam. Ka cire damuwa daga ranka. Allah Yana tare da mu..." tun ban rufe baki ba Amrah ta fasa kuka tare da tashi zaune, saboda dama tun d'azu ta yi bacci.

Da sauri na kama ta na d'ora a bisa cinya, ina rirrigarta a hankali had'e da tofa mata addu'o'i, dan a tunanina ko firgita ta yi ne. Abin mamaki sai d'ago min hannunta ta yi, cikin maganarta da bata gwanance ba ta ce,

"Umma hannu ciwo.." ta kuma fashewa da wani kukan.

Gyad'a kai na yi cike da tausayi, na kama hannun nata a hankali ina mammatsawa ina tofa mata addu'a har na samu ta yi shiru.

Bayan kamar mintuna biyar ta ce,

"Umma ya daina ciwon." Ta sakar min murmushi.

"To ki gode wa Allah kin ji 'ya ta? Allah Ya baki lafiya da duk kan 'yan uwa musulmai." Na fad'a ni ma ina mata murmushin.

Bakinta dama ya dad'e da sabawa da furta amin, hakan ya sa ta ce,

"Ameen Umma." Ta sauka daga jikina da sauri ta nufi mahaifinta, saboda sai a lokacin ma ta kula da shi.

Saurin kawar da damuwarsa ya yi ya d'auke ta,

"Amrah 'yata sannu kin ji? Insha Allahu zaki samu lafiya ke ma kamar kowa."

Bata ce komai ba sai lafewa da ta yi a jikinsa, take bacci ya d'auke ta.

Tabbatarwar da muka yi ta yi bacci ya sa a hankali ya nufi uwar d'aka da ita, ya kwantar sannan ya nufi yin sallah.

Bayan ya gama a lokacin nima na shigo d'akin har ma na kwanta a kusa da Amrah, ya hau gadon zai kwanta na yi saurin mik'ewa na ce,

"Ka gaji ko? Da alama kwanciya kake son ka yi. Gashi kuma ina son da mu yi wata magana."

Bayan ya hau gadon ya ce,

"Babu komai Murja. Ina saurarenki."

Saurin share k'wallata na yi sannan na ce,

"Dama gani na yi ya kamata mu kai yarinyar nan asibiti, sam bamu kyauta ba zaman da muke yi haka da ita, ba tare da sanin halin da take ciki ba. Mallam ban tab'a jin yaro mai irin lalurin Amrah ba, rayuwata tana matuk'ar dugunzuma a duk lokacin da ciwon yarinyar nan ya taso, tana matuk'ar bani tausayi. Tun bata san miye ciwo ba har ta kai ga ta sani yanzu. Yarinya 'yar shekara biyu da watanni amma har ta san ciwukanta."

Cike da tausayi Mallam ya ce,

"Haka ne Murja. Ni ma kaina na jima ina wannan tunanin, ina jin tausayinta sosai musamman yanda har cikin dare ba wani baccin kirki take samu ba. Ya kamata mu je asibiti, idan ma wani ciwon ne sai mu sani, mu bi dokokinsa ko ta samu sassauci."

Cikin kuka na ce,

"Haka ne Mallam."

Ajiyar zuciya ya yi sannan ya ce,

"Gashi kuma bani da kud'i Murja. Ban ajje ba ban ba wani ajiya ba. Na abin hawa ma kanshi babu bare kuma na sauran hidindimun asibiti. Wayyo ni Abdallah!" Sai ga hawaye suna zarya a bisa kumcinsa.

Duk da ni ma ina jin hawayen amma a haka na daure, shi ya koma macen ni kuma na koma namiji, na ci gaba da rarrasarsa har na samu ya yi shiru.

"Akwai 'yan samiruna da tasoshi tun na aure, suna wancan d'akin na ajiya tun-tuni. Insha Allahu da sassafe zan je gidan Rakiya Dillaliya, wata k'ila zata siya. Ko nawa ne ma dai ta bamu mu samu a kai ta asibitin. Ai ya fi mu je maula ana wulak'anta mu."

"To shi ke nan Murja. Allah Ya kai mu goben Ya sa a yi nasara." Ya furta a hankali.

"Ameen Mallam. Ka kwantar da hankalinka, Allah'n da Ya d'aura mata wannan cutar shi zai warkar da ita, insha Allahu zata warke, ta murmure kamar sauran yara."

Murmushi ya yi sannan ya ce,

"Ina fatan haka Murja. Na gode k'warai Allah Ya miki al-barka."

Da murmushi ni ma na ce,

"Ameen Mallam."

Daga haka bacci ya d'auke mu.

***

Washe gari kuwa tun da sassafe na fiddo 'yan tarkacen da zan siyar, sun yi k'ura sosai saboda sun kai kusan shekaru biyar a ajiye cikin d'akin ban fitar ba. Bashin omo na ci na wanke su tas, har shek'i suke yi sannan na kife suka bushe.

Buhu na nema mai tsafta na saka a ciki, sannan na nufi gidan Rakiya Dillaliya.

Da yake Allah ya duba zuciyarmu, kyakkyawar niyya ce a ciki, babu ko b'ata lokaci Rakiya ta siyi kwanonin, cas ta cake min naira dubu takwas da d'ari biyar.

Na matuk'ar jin-d'adi, da murna na nufo gida, zuciyata sayau, tamkar an ce min Amrah ta warke ne.

Sai da na fara biyawa na biya ku'din omo, sannan na siyo mana bredi da sauran kayan shayi, sai da dai na kaso dubu d'aya sannan na iso gida.

Ko da Mallam ya ga fuskata ya san akwai nasara, ga uwa uba leda a hannuna cike da karikitai.

"Mallam ta siya har dubu takwas da d'ari biyar." Na fad'a masa ina dariya.

Shi ma dariyar ya yi ya ce,

"Ahh lallai abu ya yi kyau. Ta kyauta sosai wallahi."

Halawartsinke na fiddo daga cikin ledar na mik'a wa Amrah, da sauri kuwa ta karb'a tana dariyar jin dad'i.

Kitchen na je na dafa mana ruwan zafi, na zuzzuba mana sannan na zuba kayan ha'di.

K'arfe goma da rabi muka gama, na ma Amrah wanka muka shirya sannan muka fito, Mallam ya rufe gidan muka nufi bakin titi.

Bamu jima ba muka samu keke napep, asibiti muka ce ya kai mu, ya tambaya,

"Mallam wace asibitin zan kai ku?"

Shiru muka yi mu duka dan bamu san inda zamu je ba, hakan ya sa ya sake maimaita mana.

"Wace asibiti ce ka sani wacce ake kula da k'ananan yara sosai?" Mallam ya tambayi matashin.

Shiru ya yi jim kad'an sannan ya ce,

"Ku je asibitin Turai, dama ta yara da masu ciki ce kawai ai." Ya fad'a yana kallon Mallam.

"In haka ne, ai ga Turai d'in can ma babu nisa sosai ko? A nawa zaka kai mu?"

"Ku kawo d'ari da hamsin." Ya fad'a.

Shiga ciki muka yi ya kai mu har cikin asibitin, dama kuwa babu nisa daga gidanmu, duk cikin unguwa d'aya ne sai dai kuma dole mutum ya hau abin hawa, idan ba haka ba kuma akwai gajiya.

Bayan mun shiga reception, muka tambaya abin da ya kamata mu yi, wata mata ta ce sai mun sai mata kati kafin komai.

Mallam ya je da kanshi ya sai mata katin aka cike, sannan aka d'ora a layin ganin paediatrician (likitan yara.)

Har bayan azahar layi bai zo kanmu ba, kusan k"arfe biyu aka kira sunanta.

Likita ce mace, sanye da lab court da medical glasses.

Kujerar dake fuskantarta ta bani izinin zama, bayan na zauna na gaishe ta da sakin fuska ta amsa.

"Me yake damunta ne?" Ta tambaye ni tare da mik'o hannu ta karb'i Amrah.

"Dr. Tak'amai-mai ban san me yake damunta ba, saboda wannan ne karo na farko da na kawo ta asibiti. Kawai dai na san ta jima tana fama da k'ai-k'ayin tafin k'afa da hannu, daga baya kuma sai abun ya canza, ta koma ciwon k'asusuwa, da zarar ta fara zazzab'i sai ko wace gab'a tata ta ringa mata ciwo, yanzu ko babu zazzab'in ma ciwo suke mata."

Zare glasses d'inta ta yi ta ajiye daga gefe sannan ta hau dudduba Amrah, ta cire mata kaya.

Tana cikin dubawar ba tare da ta d'ago kanta ba ta ce,

"Me nene genotype d'in ki? (Sinadarin jini)"Pinky durling??
*RAZ 2????*
[7/3, 8:40 AM] Princess Amrah???: *??MRAH NAKE SO!* ?


(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi.)

            Na Amrah A Msh
            _(Princess Amrah)_
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


_Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (sickler)_


                          0?5?

Cikin mamaki na kalle ta, ina k'ok'arin tuna a inda ma na san kalmar, saboda na yi boko bakin gwargwado, sai dai ban yi zurfi sosai a ciki ba, daga JS 3 na tsaya ban samu damar ci gaba ba. Mahaifinta kuma ya gama secondary ne bai wuce ta gaba ba.

"Me nene genotype d'in ki?" Ta sake tambaya ta bayan ta d'ago kanta ta kalle ni.

"Dr. Ban gane nufinki ba." Na fad'a idona a cikin nata.

"Sinadarin jini nake nufi. Wane iri gare ki?" Ta mayar da glasses d'inta.

"Uhm...ni ma ban sani ba Dr. Kamar dai zan iya tunawa, sanda zamu zana jarabawar aji uku an auna mana jini, blood O gare ni." Na fad'a ina tunani. "Tabbas ma kuwa O ne, O negative in ban manta ba."

Gyad'a kai likitar ta yi ta ce,

"Ba shi nake nufi ba Maman Amrah, wannan ai type ne na jini (blood group), genotype nake nufi. An tab'a yi miki awo?"

Sai a lokacin na gane manufarta. Na ce,

"Gaskiya ba'a tab'a yi min ba Dr."

"Subhanallahi!" Ta furta had'e da dafe kanta. "Ina mahaifinta yake?"

"Yana waje ne, bari in kira sa." Na mi'ke tsaye.

"Ku hanzarta please, daga ku ma na tashi aiki wani zai karb'e ni." Ta fad'a tana mai ci gaba da dudduba Amrah.

Babu jimawa muka shigo ni da Mallam. Da sallama na ce,

"Dr. Ga Mahaifin nata nan."

D'ayar kujera ta sa na jawo sannan muka zauna, mik'o min Amrah ta yi na karb'a ta ce,

"Mallam menene genotype d'in ka?"

"Tab! Na dai san ko menene genotype saboda na karance sa a Biology shekaru da dama da suka gabata. Sai dai kuma babu abin da zan iya tunawa game da shi Dr. Ban wani tab'a yin gwajinsa ba. Lafiya dai ko?"

Jinjina kai ta yi ta ce,

"Gaskiya dole ku yo wannan gwajin, sai kun yi shi sannan zan sake duba ta. Ita ma yarinyar a yi mata, gobe sai ku dawo." Ta rubuta mana awon a wata takarda ta bani. "Ku gwada wannan takardar. Dan Allah ku tabbatar kun yi shi daga nan zuwa gobe."

Mik'ewa muka yi sannan muka mata godiya muka fita.

Bamu bar asibitin ba sai da muka binciki inda ake awon genotype, duka d'ari biyar aka caje mu mu duka ukun, aka ce sai zuwa gobe mu karb'i sakamako.

A sa'bule muka nufi bakin asibitin, muna isa kuwa muka samu keke napep ta kawo wasu, babu b'ata lokaci ya d'auke mu sai gida.

Bayan mun isa, a k'ofar gida muka tarar da Annur zaune ya yi tagumi, ya k'urawa k'ofar gidan ido.

Sauka muka yi daga napep d'in muka sallame shi, sannan muka iso k'ofar gidan.

Da sauri Annur ya mik'e, take bak'in cikin da ke bisa fuskarsa ya kau, ya karb'i Amrah daga hannuna.

Murmushi na sakar masa na ce,

"Annur lafiya dai ko?"

Mallam ya yi saurin fad'in,

"Yo sai ma kin tambaya? Bai ga 'yar lelen tasa ba ne yau." Ya ci gaba da zura makulli a cikin kwad'o yana k'ok'arin bud'e k'ofar.

"Haka fa. Ai Annur ba nisa sosai muka yi ba. Mun je asibiti ne." Na fad'a ina masa murmushi had'e da shiga cikin gidan yana biye da mu.

"Ai Umma da har hankalina ya tashi, na zata ko wani wurin mai nisa kuka tafi babu ko bankwana."

"Ko kad'an Annur. Iyakacinmu asibitin Turai." Mallam ya fad'a.

Bayan ya sauke Amrah tsaye ya ce,

"Waye ne ba lafiya? Ko jikin Amran ne ya motsa?"

D'aga masa kai na yi sannan na ce,

"Amma kar ka damu, ta ji sau'ki sosai. An saka mu awon genotype ne, sai gobe zamu karb'i sakamakon mu kai ma likita."

Dafe kansa ya yi, cikin lokaci kad'an yanayinsa ya sauya, idonshi ya yi jajur kamar wanda zai yi kuka, yana son yin magana amma lab'b'anshi sai k'yarma suke kamar ba zai iya ba.

Ganin haka ya sa na 'kirk'iro murmushi na ce,

"Annur miye ne haka wai? Babu wata matsala mai girma fa. Idan ma akwai, wayo da dabararmu ai ba zasu tab'a magance mana komai ba, addu'a kawai zamu rik'a, domin ita ce makamin mumini. Insha Allahu zata samu lafiya."

Da k'yar ya iya furta,

"Umma ina matuk'ar tausayin Amrah, bana so wani abu ya same ta. Jikina yana bani in har wata babbar matsala ce tattare da ita, to tabbas ni ma zan iya kamuwa da wata cutar. Ummah wallahi tausayinta nake ji..." sai a wannan lokacin hawayen da yake b'oyo suka samu nasarar fitowa.

Ita kuwa Amrah kallonsa kawai take, ta dai san tabbas ba lafiya ba, ganin babban abokinta yana kuka..."

Maryama ce ta yi saurin dakatar da Ummah da fad'in,

"Kar dai na katse ki Ummah, baki fad'a min shi Annur d'in ko waye shi ba."

Jinjina kai ta yi ta ce,

"Haka ne Maryama.

Annur Ikra Hussain shi ne asalin sunanshi.

Mahaifin Annur babban mai kud'i ne, saboda a duk fad'in unguwarmu babu gida mai girman nasu, babanshi ya fi kowa kud'i, saboda tsohon pharmacist ne wanda ya jima da yin retire, yana da share a wasu daga cikin magungunan da ake yi, ciki kuwa har da kamfanin dana.

Annur shi ne d'a na biyar a gidansu, duka yayyenshi mata ne, sai shi d'in ne kawai namiji, sai kuma k'anwarsa mai bi masa, auta ke nan.

Yaro ne d'an kimanin shekaru sha uku a lokacin. Annur na da tarbiyya sosai, yana da son mutane, haka kuma akwai shi da girmama na gaba da shi.

Mun had'u da shi ne tun wata rana a k'ofar gidansu, ni kuma mun je cike wani form na tallafawa mata, wanda mahaifiyarsa take kula da shi, kasantuwarta ma'aikaciyar gwamnati ce ta b'angaren state government.

A lokacin Amrah na da wata biyar a duniya, shi kuma bai fi shekara goma sha d'aya ba. Tana ta tsala min kuka alamun ta gaji, shi kuma ya fito a inda muke jere a layi ya ji kukanta.

Da sauri ya iso inda nake, ya kalle ni ya ce,

"Me kika mata take kuka?" Har da nuna alamun shi ya ji haushi sosai.

Murmushi na masa na ce,

"Babu abin da na mata, rigima ce kawai. Ina ji ta gaji ne."

"To ki mata yanda take so ko kuma na kai k'ararki wurin Babana, in fad'a masa kina ba 'yar yarinya wahala."

Sosai ya bani mamaki, na d'aga kai na kalleshi, har a lokacin bai daina kallon Amrah ba. Na ce,

"To ko zaka karb'e ta ka taya ni rarrashinta ne?"

"Ehh kawo ta."

Na kuwa mik'a masa ita.

Duk irin kukan da yarinyar nan ke tsalawa, Annur na kar'barta ya ringa rirrigata ta yi shiru, k'arshe ma sanda ya dawo min da ita sai wangale baki take, kamar ba ita ce ta gama kuka ba.

"Gata nan ta yi shiru. Ya sunanta wai?" Ya tambaye ni bayan ya mik'o min ita.

"Sunanta Amrah." Na bashi amsa.

"Ta burge ni. Ina ne gidanku? Zan ringa zuwa ina d'aukarta kullum idan tana kuka."

"Gidan namu akwai 'yar tafiya yaro, ta can k'asa ne." Na gwada masa layin namu.

"Sunana fa Annur ba yaro ba. Zan jiraki idan kin tashi tafiya sai mu tafi tare. Ina son Amrah, kaman ki bani ita ta dawo gidanmu." Ya kama latsa mata kumatu sai wangale baki take.

Wannan shi ne silar had'uwarmu da Annur, tun daga wannan lokacin ya d'auki Amrah ya saka ta a ranshi, duk sanda bata lafiya haka zai wuni a gidan nan, idan tana kuka kuwa shi ma kukan zai yi, har sai sanda ta daina.

Amrah ta matuk'ar sabawa da Annur, kamar yanda shi ma ya saba da ita sosai.

Baya shigowa gidan nan ba tare da ya kawo mata wani abu ba, ta dalilin Annur har mahaifiyarsa ta zo nan gidan, ta kawo ma Amrah abun duniya iri iri, wai saboda yanda d'anta d'aya tal namiji ya nuna k'aunarsa ga yarinyar.

Tarihin Annur Ikra Hussain ke nan. Bari mu koma mu ci gaba daga inda muka tsaya."

Gyara zama Maryama ta sake yi tana mai sauraron Umma...


Pinky durling??
*RAZ 2????*
[7/3, 8:40 AM] Princess Amrah???: *??MRAH NAKE SO!* ?


(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi.)

            Na Amrah A Msh
            _(Princess Amrah)_
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


_Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (sickler)_


                          0?6?


Umma ta ci gaba,


"Ganin halin da Annur yake ciki, ya sa na ce,

"Annur akwai Islamiyya fa yau, ka tashi ka tafi kar ka makara. Kuma ka share hawayen nan bana so ka tafi gida da shi."

"Umma yau ba zan je Islamiyya ba, ko kin manta ke kika ce min daga asibiti kuke? Zan zauna har sai na tabbatar Amrah bata da wata damuwa daga nan zuwa dare, sannan zan tafi." Ya sake gyara zamansa.

Mallam ya ce,

"Ba za a yi haka ba Annur, gidanku ba zasu ji dad'i ka zauna a nan baka je makaranta ba. Mu ma kuma ba zamu so ta dalilinmu kana fashin makaranta ba. Ka tashi ka tafi ka ji? Gobe sai ka dawo ka duba ta, ka ga a lokacin ma an bata magani ta ji sauk'i ke nan." Ya sakar masa murmushi.

Shi ma murmushin ya yi ya ce,

"Kuma fa haka ne Abba. Bara in tafi to. Amrah.." ya kama mata hannu. "...zan tafi makaranta, zan fad'a wa Malaminmu a saka ki a addu'a, Allah Ya baki lafiya ko?"

Murmushi kawai Amrah ta masa, ta ce,

"Ameen."

Ta san dai idan an ambaci addu'a to amin ake cewa, ita ma shi yasa ta ce haka.

Sakar mata hannu ya yi, ya ce,

"To sai Allah ya kai mu."

"Allah Ya kai mu, Annur. Ka gaishe da Momy'nka." Na ce da shi.

"Zata ji." Kawai ya fad'a tare da barin gidan.

Na juyo ga Mallam na ce,

"Wato k'aunar da yaron can yake ma Amrah, abin har mamaki yake bani. Yaron da bai yi ko shekara sha hud'u ba, amma ya ta'allak'a rayuwarsa ga Amrah, ya sadaukar da baki d'aya lokacinsa ga Amrah."

Mallam ya jinjina kai ya ce,

"Ai k'aunar da Annur yake ma Amrah, a jininsa take. Ki tuna ranar da Amrah ke ta kukan nan bata da lafiya, sai gashi fa da gudu ya zo, wai jikinsa ne ya bashi cewa Amrah na kuka bata da lafiya, kuma sai gashi hakan ne. Haka zai zauna ya rizgi kukansa idan bata da lafiya, sai idan ta yi shiru ko shi ma zamu samu ya yi shiru. Haka ita ma yarinyar, duk iya rigimar da take sai idan bai d'auke ta ba, tun ma kafin ta kai haka. Da zarar ya d'auke ta sai ta yi shiru.

Ni tsorona d'aya ma, yanda iyayensa suke da kud'i, kar wata rana su wula'kanta mu saboda d'ansu, musamman yanda shi kad'ai gare su namiji, suna so su inganta rayuwarsa, amma wasu lokutan sai ya k'ek'ashe ya k'i tafiya makaranta saboda Amrah. Ina matu'kar tsoron ranar da abin zai cika su, zasu iya yin komai fa saboda Annur."

Ajiyar zuciya na sauke, na ce,

"Haka ne Mallam. Amma kuma fa son yaron nan da suke shi zai sa su masa duk abin da yake so. Ka tuna ranar da ya kawo Mamansa ta zo har nan ta duba Amrah? Alamun suna bayan buk'atarsa fa ke nan."

"Allah dai Ya mana jagora." Kawai Mallam ya fad'a. "Da kin nufi d'ora abinci ai ko dan yarinyar nan, kafin ta nema."

"Yanzu kuwa. Ai da yake mun yo cefane, d'orawa kawai zan yi." Na tashi na nufi d'ora girkin rana, a lokacin har la'asar ta kusa.

Washe gari,

Tun da sassafe muka gama shiri, takwas ma bata yi ba muka karya sai haramar komawa asibiti.

Tun ba mu fita ba sai ga Annur ya zo, sanye yake da Uniform na Gobarau Academy, school bag goye a bayansa.

Da fara'a ya ce,

"Umma na zo duba Amrah ne, ta ji sauk'i sosai ko?"

"Alhamdulillahi! Duk yau ko cikin dare ma bata yi ciwon komai ba. Ka ga shirin tafiya ma muke, asibitin zamu koma karb'an sakamako." Na bashi amsa ina tab'a kanshi.

"To tun da ta ji sauk'i bari in tafi. Dama na matsa wa Baba Amadu ne lallai sai ya biyo da ni na duba Amrah. Bara in tafi, idan mun tashi zan biyo ko kun dawo lokacin."

"To Annur, Allah Ya bada sa'a. Ka yi karatu sosai ka ji?"

Ya jinjina kai had'e da fita daga gidan, a dai-dai fitowar Mallam daga d'aki ya rufe.

"Kamar muryar Annur na ji ko?" Ya tambaye ni bayan ya datse d'akin.

"Shi ne fa da kan shi. Wai ya zo duba mutuniyarsa ne." Na bashi amsa had'e da saka ma Amrah takalmanta.

"Allah sarki!" Ya fad'a ya yi gaba na kama hannun Amrah, muka mara masa baya.

Bayan ya rufe gidan, muka nufi titi, babu jimawa muka samu napep aka nufi Turai da mu.

Ko da muka isa Turai child and maternity hospital, mun tarar da mutane sosai, kasantuwar akwai special doctor da yake zuwa a irin ranar ko wace talata, wanda musamman k'ananan yara yake dubawa.

Kai tsaye laboratory (d'akin gwaje gwaje) muka nufa, mutum uku ne kawai a gabanmu, su ma kuma ba wai result suka je karb'a ba, sun je a yi masu wani awon ne na daban.

Zama na yi bisa kujera na rungume Amrah, mallam kuma ya shiga ciki inda zai karb'o sakamakon.

Bai jima ba sai gashi ya fito, ya ce in tashi mu tafi.

Kusan minti arba'in muka d'auka kafin a bamu izinin shiga wurin likita, likitar jiya mai suna Dr. Xarah ce muka tarar, sai kuma wata d'aya likita zaune daga wata kujera, lab court ce a jikinta ta yi rolling d'in bular mayafi.

Da sallama muka shiga, bayan mun gaisa ta ce,

"Sannunku Maman Amrah. Ku zauna mana." Ta gwada mana kujeru guda biyun da ke fuskantarta.

Zama kuwa muka yi, waccan d'aya likitar ta ce,

"Dr. Xarah ni zan wuce, sai na gan ki."

Dr. Xarah ta ce,

"To shi ke nan Dr. Rabiatu. Insha Allahu zaki ji ni very soon. A gaishe min da yarana da Babansu."

Bankwana suka yi sannan ta juyo gare mu,

"Ina results d'in?" Ta fad'a bayan ta mayar da glasses a idonta.

Mallam ya mik'o mun sannan na isar da shi gare ta,

"Ga shi Dr." Na mik'a mata.

Ta jima tana dudduba takardun, shiru ya biyo baya na tsawon minti sha biyar ko ma fin haka, kafin ta zare glasses d'inta ta ce,

"Ya Salaam!"Ta dafe kanta.

Bamu ce mata komai ba, sai dai ambaton sunan Allah da ta yi ba kad'an d'in razana ni ya yi ba, take na ji hankalina ya tashi, zuciyata na dukan uku-uku.

Ajiyar zuciya nannauya ta sauke kafin ta ce,

"Ban san me ya sa ba, abu mai matuk'ar muhimmanci amma mutane sam! Basu yarda da shi ba.

Shekara da shekaru manyan likitoci sun sha fad'akarwa, cewa mu kasance masu awon genotype kafin mu yi aure.

Ba wai ku iyayen ake ji ba, su yaran da zaku haifa d'in ne abun ji.

Yaro k'arami, bai ji ba bai gani ba, bai san halin da duniya take ciki ba, amma tun yana k'arami a wargaza masa rayuwa, ta k'i yin inganci.

Me yasa ba'a kula ne? Me yasa soyayya take rufe wa mutane ido su gagara aikata abin da ya dace? Shin mutane basa tausayi ne? Basa duba future d'in su? Su dai soyayya kawai, kar a b'ata ran masoyi.

Yanzu fa wasu a tunaninsu da zarar na ce da wanda zan aura ya kamata mu yi awon genotype, zai iya daina so na ko? Zai iya ganin kaman ban yarda da shi ba ne? Zai ji a duniyarsa na raina masa hankali ko?

Me yasa zaki zab'i faranta ran wani namiji, ki cuci yaron da zaki haifa? Ko kin san cewa matuk'ar hakan ta kasance, mijinki zai iya dakatar da haihuwa da ke saboda gudun wahala? Ko kin san cewa zai iya zuwa ya nemi mai AA ya aura, wacce zata ci gaba da haifa masa lafiyayyun yara?

A rayuwar nan ta yanzu, wacce kud'i da lafiya suka yi k'aranci, kamata ya yi tun farko a gina rayuwa a kan abu mai kyau, a gina rayuwar yaro da tubalin mai kyau.

Wallahi auren soyayya ba tare da bincika sinadarin jini ba, babu abin da yake haifarwa face wahala. Ba wai ga yaron kawai ba, har ku iyayen da zaku yita jerangwama da shi, kuna cikin damuwa.

Yanzu ke baki sani ba, kin auri namiji wanda sinadarin jininsa AS ne, shi ma kuma ya aure ki, naki jinin AS ne, wane irin yara kike tsammanin zaku haifa?

Idan masu sinadarin jini AS suka yi aure su duka biyun, akwai yiuwar fa su haifi yaro mai amosanin jini (sickler)

Ba wai na ce lallai sai mai sickler zasu haifa ba, sai dai zasu iya samun sirkin mai sickler d'in.

Zasu iya samun mafi rinjaye AS a cikin yaransu.

Ita kanta AS d'in nan fa, akwai mai wahala, kafin ma a kai ga SS.

 Matuk'ar S d'in da ke cikin jininka ta rinjayi A d'in, to zaka iya zama mai laluri a ko da yaushe, tamkar yanda mai sickler zai yi, sai dai zaka iya samun sauk'i ba kaman na me SS d'in ba.

Yanzu ku bayin Allah, kun san abin da rashin awon genotype ya haifar maku?

Kun san cikin halin da kuka hefa 'yarku?

Yanzu kai, kana da AS, Ita ma mamanta tana da AS, What do you expect? Kuna zaton zaku ci gaba da haifar yara lafiyayyu ne? Idan ma duka yaran naku lafiyayyu ne, kun san wanda zaku haifa a gaba?

Ban ji dad'i ba ko kad'an, ku ne silar ciwon 'yarku, yarinyar da bata ji ba bata gani ba, jininta yana d'auke da amosani a cikinsa (sickle cell) a bisa sakaci da son zuciya irin naku.

Duk ciwukan da kuka ga tana yi, wasu daga cikin illolin sickler ne, cutar yarinyarku ke nan...." ta dakata daga nan ita kanta cike take da tausayi, idonta kamar zai kawo ruwa.

"...kuma duk irin wahalar da take tun tana da shekara d'aya, baku ta'ba tunanin kawo ta asibiti ba sai yanzu.

Any ways, da sauk'i ma tun da kun zo yanzu d'in ai.

Zan rubuta mata magunguna, sannan kuma akwai shawarwari da dama wanda in dai kuka bi su, insha Allahu cutar zata jima bata ringa tasar mata ba;

Babban abin da yake tasar da ita shi ne malaria, saboda haka sai kun kula, ko da wasa kar ku ringa bari sauro na cizonta. Duk yanda zaku yi, ku tabbatar baku barta inda sauro zai cije ta ba. Akwai gidan sauro ana bayar da shi kyauta a ko wace asibiti, ku nema, da zarar magrib ta yi ku tabbatar kun saka ta a ciki, kar kuma ku bari sauron ya shiga a ciki.

Abu na biyu, kar ku ringa barinta a cikin sanyi, saboda wannan sanyin zai iya saka mata zazzab'i, kuma zazzab'in masu sickler shi ne wanda ba a so. Saboda su basu iya zazzab'i ba, da zarar sun fara shi zai iya k'onar masu da baki d'aya jininsu, idan ma ba a hanzarta an saka masu wani ba, zasu iya rasa rayuwarsu.

Abu na uku, banda duka. K'ashinsu ba wani k'wari ne da shi ba, da zarar kun duke ta, zaku iya tab'o inda bai dace ba, kuma k'arshe wahalar ta dawo a kanku. Hakan kuma ba wai yana nufin kar ku tarbiyyantar da ita ba, a'a, sai dai ku kula. Ku san ta hanyar da zaku bi idan ta yi laifi. Ko School ta shiga nan gaba, ko da wasa kar ku bari ana dukanta.
Pinky durling??
*RAZ 2????*
[7/3, 8:40 AM] Princess Amrah???: *??MRAH NAKE SO!* ?


(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi.)

            Na Amrah A Msh
            _(Princess Amrah)_
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


_Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (sickler)_


                          0?7?

Abu na hud'u, ungo wannan." Ta jawo wata lakar gabanta, wani abu ta zaro sannan ta mik'o min,

"Thermometer ce wannan. Duk sanda zazzab'i ya kama ta, komai k'ank'antarsa ku ringa amfani da wannan, zaku saka a armpit d'inta, matuk'ar kuka ga ya kai 37.5degreeC, ko kuma idan a baki kuka saka mata, ya wuce 38degreeC, to lallai ku hanzarta ku kai ta asibiti mafi kusa da ku, saboda ya riga da ya haura, ya kai minzalin da zai iya k'one mata baki d'aya jininta.

Amma idan kuka kawo ta, sai a d'auki mataki tun da wuri kafin abun ya yi nisa.

Abu na biyar, shi ne folic acid. Ya zamana kullum kuna bata folic acid, ko kad'an kar ku ringa mantawa, zai bada taimako sosai da sosai.

Na shida, ta yawaita shan ruwa, ba kuma wai ruwan sanyi ba. Ruwa sosai zaku yawaita bata, saboda shi dama ruwa waraka ce ta cututtuka da dama, not only sickler.

Da zarar tana shan ruwa wadatacce, zaku ga tana fitsari akai akai, wannan fitsarin nata sauk'i ne sosai.

Da zarar kuwa bata fitsari sosai, to lallai akwai damuwa, dole zaku kawo ta asibiti a duba ta.

Wannan su ne abubuwan da ya kamata ku kula, ku tabbatar kun fita hak'k'inta, in har kuka aikata kaf abubuwan dana lissafa maku, lallai zata kasance mai cutar sickler amma sauk'ak'k'a.

Abu na k'arshe, ku ringa mata addu'a, saboda ita addu'a takobin mumini ce.

Sannan kuma kafin a saukar da cuta, sai da aka saukar da maganinta.

Allah maji kan bayinSa ne, mai karb'ar addu'ar bayinSa.

Ku ja yarinyarku a jiki, ku nuna mata soyayya, ku inganta abin da ya yi saura na rayuwarta, bakin gwargwadon iyawarku." Dr. Xarah ta yi shiru daga nan cike da tausayi.

Sosai kuka ya ci k'arfina, Mallam ne kawai mai d'an kuzari, shi d'in ma da zarar an ganshi an san damuwa na tattare da zuciyarsa.

Murmushi ta k'irk'iro ta ce,

"Maman Amrah sai hak'uri, Allah'n da Ya d'aura mata cutar shi zai bata sau'ki.

Ba kuma wai dan ba Ya sonta ba ne, a'a, jarrabta ce, kuma babu wanda ya fi k'arfin Allah Ya jarrabce sa.

Masha Allah, yarinyarku kyakkyawa da ita, gata b'ul-b'ul babu wanda zai kalle ta ya ce sickle cell ce.

Abin da ya rage, kawai ku yawaita bata abinci masu gina jiki, insha Allahu ba za a ta'ba ganewa ta jikinta ba.

A shawarce, saboda gaba, duk wanda zai nunar da yana sonta, ko ba dad'e ko ba jima, kar ku b'oye masa cutarta.

Saboda tun da wuri in ma bai san genotype d'insa ba sai ya nemi sani, idan har AS gare shi, duk irin son da yake mata dole ya hak'ura.

Idan kuma Allah Ya sa AA ne da shi, kun ga shi ke nan."

Nannauyar ajiyar zuciya na sauke, na ce,

"Mun gode k'warai Likita. Insha Allahu zamu bi shawarwarinki, Allah Ya saka miki da alkhairi.

Amma likita, hakan ko yana da nasaba da mutuwar da yaranmu suke yi idan mun haihu? Amrah ce yarinya ta uku da muka haifa, sauran biyun duk sun rasu."

Dr. Xarah ta ce,

"Tabbas ma kuwa, hakan zata iya kasancewa. Saboda wasu yaran idan nasu mai tsanani ne, ba a ma ganewa sai dai mutuwarsu kawai. It can be possible, mai tsananin ce tun wuri sai Allah Ya d'auke su."

Shiru na yi kad'an ina nazari kafin na ce,

"To shi ke nan. Fatanmu dai, Allah ya sau'kak'a wa duk musulmin Allah."

"Ameen. Idan kun fita sai ku nemi inda ake rijistar masu sickler, kyauta ake bayar da magungunansu a nan asibitin. Duk bayan sati biyu sai ku ringa zuwa kuna karb'ar mata."

Ta dafa kan Amrah,

"Amrah! Sannu kin ji? Allah Ya baki lafiya. Ki ringa yi wa kanki addu'a ko?" Ta sakar mata murmushi.

Murmushin na k'irk'iro na ce,

"Insha Allahu zan ringa saka ta tana ma kanta. Bari mu tafi. Mun gode k'warai." Muka mik'e.

Har a wannan lokacin Mallam bai ce komai ba, damuwa fal a fuskarsa.

Ba mu bar asibitin ba, sai da muka mata rijista, aka bata magungunan wannan satin, sannan muka tafi.

K'arfe sha biyun rana ta wuce sanda muka isa, ta yi bacci hakan ya sa na kwantar da ita, sannan na nufi d'ora girkin rana.

Bayan azahar, sai ga Annur ya zo, hannunshi rik'e da launch box d'insa, bayansa kuma goye da jikarsa.

Da fara'arsa ya k'ariso inda take zaune, zama ya yi shi ma ya ce,

"Amrah..." ya bud'e launch box d'in ta shi.

"...ga sauran abincina nan na kawo miki. Ban cinye ba saboda ke..."

Ya ajiye a gabanta, sannan ya bud'e jikarsa,

"...wannan kuma chocolate ce na siyo miki. Kar ki ba kowa." Ya fara bud'e mata ledar.

Daga inda nake na saki murmushi, sannan na iso inda suke.

"Wato dai Annur mu kake nufin kar ta ba ko? Ka yi dai-dai to."

Mallam da ke zaune ya murmusa ya ce,

"Ahh to, mu ma idan mun samu na mu sai mu hana su ai."

"Umma an karb'o result d'in nata kuwa?" Ya tambaye ni.

Zama na yi kusa da shi, na ce,

"An karb'o, Annur. Amrah sickler ce da ita." Na yi saurin share hawayen da ya fito min.

"Sickler Ummah? Irin wadda Saddam yake da ita? Gaskiya k'arya ne. Shi fa jikinshi babu girma, sai aukin k'ashi kawai. Babban kai kuma da shanyayyun k'afafuwa gare shi. Shi ne kuma za a ce wai Amrah ita gare ta? Ummah ko dai 'karya likitan yake maku?"

"Waye Saddam?" Na tambaye shi.

"Wani abokina ne. Sanda muna JS2 ma ya rasu." Ya bani amsa cike da damuwa.

"To ai ka ga shi da Amrah ba d'aya ba. Ita wannan cutar dama kowa da yanda take zo masa. Wani da sauk'i, wani kuma babu sauk'i.

Akwai wanda take canza ma halitta, kaman yanda ka ce ta Saddam d'in. Ita kuma Amrah, ka ga ta ta mai sauk'i ce, sai mu gode wa Allah ke nan, tun da abun ya zo da haka.

Kar ka damu Annur, insha Allahu babu wata damuwa, Allah Yana tare da mu, kuma shi zai bata lafiya.

Kai dai kawai abin da nake so da kai, ka ringa saka ta a addu'a, kar ka fasa. Zata samu sau'ki kaman kowa." Na sakar masa murmushi.

"To shi ke nan Umma. Zan ringa yi mata addu'a har ta samu sauk'i."

"Yauwa d'an al-barka, yanzu ka tashi ka tafi, ka huta kafin lokacin Islamiyya ya yi." Mallam ya fad'a bayan ya dafa masa kai.

D'aure fuska Annur ya yi, ya ce,

"Ni fa yau ba zan tafi ba, zan zauna a nan sai dare sannan. Har ma na sallami baba Amadu tun d'azu ya tafi."

Cike da mamaki na ce,

"Wace irin magana kake yi Annur? To me zaka zauna ka yi a nan? Na ce maka Anrah ta ji sauk'i fa. Ka tashi ka tafi kar Mommy ta maka fad'a."

Fir fir yaron nan ya ce ba zai tafi ba, shi fa yana nan zai yi jinyar Amrah ta yau.

Kumci na dafe, na ma rasa abin da zan yi.

Mallam cikin dabara ya ce,

"To ka tafi gida, ka ciro uniform d'inka sannan ka dawo, sai ka yi jinyar ta ta. Amma a haka, ai babu dad'i zama da uniform." Ya masa murmushi.

Fuska ya sake tsukewa, yana neman yin hawaye ya ce,

"Shi ke nan bara in tafi, tun da dai kora na kuke daga gidanku." Sai ga hawaye sun fara masa sintiri a kumatu.

D'aukar launch box d'insa ya yi, da jikarsa, yana kuka ya kama hanyar tafiya.

Baki d'aya na ji zuciyata ta yi sanyi, ba zan iya barinsa ya tafi a haka ba, hakan ya sa na jawo sa, na ce,

"Yi ha'kuri yarona. Tun da baka son tafiyar, zauna abunka ka ji?"

"Umma ba dai ni kuke kora daga gidanku ba? Shi ke nan ma, ba zan sake zuwa gidanku ba." Ya fizge hannunsa da na rik'e.

Da hanzari Mallam ya kamo shi, da fara'a ya ce,

"Zo nan abunka. Ka yi hak'uri ka zauna ka ji? Ko dan Amrah, ka ga har ta fara kuka."

Kallon Amrah ya yi, ganin da gaske kukan take ya sa ya dawo da sauri, ya hau bubbuga bayanta yana bata hak'uri har ta yi shiru.

Daga nan suka hau wasansu, yana ta bata labarin makaranta, ita kuwa murmushi kawai take, dan bata san abin da yake fad'a ba.

Ko da abinci ya dahu, tare na zubo masu shi da ita, yana bata a hankali a baki.

Sai da ya tabbatar ta k'oshi, sannan shi ya fara ci.

*K'ARFE HUD'U DA RABI NA YAMMA (4:30PM)*Pinky durling??
*RAZ 2????*
[7/3, 8:40 AM] Princess Amrah???: *??MRAH NAKE SO!* ?


(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi.)

            Na Amrah A Msh
            _(Princess Amrah)_
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


_Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (sickler)_


                          0?8?

Wata budurwa ce ta shigo, hannunta rik'e da wata yarinya, wadda kallo guda zaka mata ka tabbatar ta had'a jini da Annur.

Babu ko sallama suka shigo, biye da su wani matashi ne, sanye da matattun kaya, wanda na tabbatar cewa d'an koransu ne.

Tafe suke yana masu jinjina, had'e da kirari tamkar ya ga manyan Al-hazai.

Ko da ganinsu, tuni Annur ya mik'e tsaye, mamaki fal a fuskarsa ya ce,

"Aunty Saddiqa."

Tabbatarwar da na yi cewa danginsa ne, ya sa da fara'ata, duk da yanayinsu da na gani, cike suke da izza da gadara, na ce,

"Lale marhabun da ku. Ku iso ga tabarma ku zauna."

Kallon uku saura kwata Saddiqa ta bi ni da shi, bata ce min komai ba, sai dai ta kalli Annur cike da masifa ta ce,

"What's wrong with you, boy? What are you doing here?"

Ta sake bin gidan da kallo a k'ask'ance,

"Wai me kake tsinta a gidan nan ne? Lukkat the floor..." ta nuna k'asa da hannunta, alamun k'yama,

"...a haka kake zaune, har kuma kake iya had'iyar yawu? Taso maza mu tafi, tun ban mammare ka ba."

Iya 'kuluwa na k'ulu, bana son raini da wulak'anci, musamman ma yanda ta zo har inda muke ta same mu, kuma take neman wula'kanta mu.

"Ya Noor abeg let's go mana. Lukkat your uniforms, duk sun yi k'ura saboda floor d'in gidan, amma a haka kana zaune, ji k'azamar yarinyar da kake wasa da ita..." ta nuna Amrah.

Tun bata rufe bakinta ba, Annur ya hanzarta isa inda ta ke, ya mata wani mugun kallo, kafin ya ce,

"Islam, mind your tongue.  Da ki tab'a Amrah, gwara ni ki yi min. Wai me ma...?"

Bai gama maganarsa ba, ya ji sautin tsawar da Saddiqa ta masa,

"Shaarrup your mouth Noor! K'arya Islam ta yi ne? Kullum kana fama da zuwa gidan da bai kamace ka ba, kana k'ok'arin gurguntar da rayuwar iliminka, a maimakon ginuwar da iyayenka suke maka. Me yake damunka? Me ya sa ba zaka fita harkar mutanen da basu cancanta.."

"Ya ishe ki haka!" Na fad'a a fusace.

K'arisowa na yi inda take, cike da takaici. Iya k'ok'ari na yi shi, na so a ce na iya daurewa, na k'yale ta. Amma ina, sam! Na ji zuciyata ba zata iya d'auka ba, ba zan iya jurar cin fuskar da Saddiqa take min ba.

"Na kula, duk girmamawar da na miki, ko kad'an ke baki ga hakan ba. Na kula, sam! Baki cancanci darajta kin da na yi, saboda Annur ba.

A rayuwata, bana son cin zarafi, da kuma cin fuska.

An fad'a miki tsoro ne ya sa ni yin shiru, bayan duk cin fuskar da kike min?

Wa ya fad'a miki shiru-shiru tsoro ne?

Ko kuwa an ce miki talauci hauka ne? A tunaninki bamu da wata daraja ne, saboda muna talakawa?

Annur da kike gani, ban tab'a jawo shi na ce ya zo inda muke ba, ban tab'a kiransa da sunan ya zo gidan nan ba.

Dan Allah na ro'ke ki, ki tafi ki bar mana gida.

Duk iya talaucinmu, mun rik'e shi, bamu fita yawo kwararo kwararo muna maula ba.

Ki fita, tun ban tara miki mutanen anguwa da sunan kin zo har gida, kina tak'ulana da fitina ba.

Na rok'e ki, ki kama k'aninki, ki kuma shaida masa, ya tsaya inda Allah Ya ajje sa. Dan na ga alama, zuwansa inda muke, babu abin da zai jawo mana, face b'acin rai.

Ki tafi kawai!" Na nuna mata k'ofa, gabana sai dukan uku-uku yake.

Hankalina a tashe yake, ko kad'an bana son fitina, bana son ana fitina a inda nake.

Wata irin muguwar dariya ta fasa, tana tafa hannuwanta.

Wannan gardin wanda suka zo da shi, ya bud'e baki zai min masifa ta yi saurin dakatar da shi.

"Barta!" Ta juyo gare ni.

"Ki fad'i komai Madam, its your time." Ta had'a babbar yatsarta, da yatsar tsakiya, na hannun damanta ta murza su da k'arfi, har sau uku.

"Zaki san kin fad'a min bak'ak'en maganganu. Ba dai ni ba? Hmm!"

Islam cike da rashin kunya da fitsara ta ce,

"Matsiyata kawai. Ji yarinyar ma kayanta duk sun tsufa. Gashin kanta ko gyara babu. Lukkat everywhere..." ta hau yatsina tana kalle-kallen ko ina dake cikin gidan.

"Aunty Saddiqa mu yi mu tafi, dan kr wata cutar ta kama mu Please." Ta hau dod'e hancinta.

Tuni Annur ya d'auke ta da mari, sai faman huci ya ke, ya ce,

"Wallahi Islam idan na sake jin bakinki, sai na kakkarya ki."

"Ni kuma in b'ab'b'alla ka ba. Ai gaba da gabanta." Saddiqa ta fad'a.

"And ka zo mu tafi, tun ban maka da k'arfi da yaji ba."

Rai a b'ace, ya juyo ya kalle ni. Sosai hankalinshi ya tashi, ganin yanda damuwa ta dabai-baye duk ilahirin fuskata.

Ya duk'a daf da Amrah, murmushi ya k'irk'iro mata, ya ce,

"Zan tafi Babyna. Please don't cry. Gobe da sassafe kafin in tafi School zan biyo in sake duba ki. Yi min dariya ko?"

Dariyar kuwa ta yi, sai dai ganin ya mik'e tsaye alamun tafiya zai yi, ya sa ta fasa kuka mai k'arfin gaske.

Yana k'ok'arin komawa mazauninta, da 'karfi Saddiqa ta finciko sa, har sai da ya kusa buguwa da bango.

"Wallahi Annur, idan baka zo mun tafi ba sai na ci mutuncinka."

Babu yanda ya iya, a haka ya bi bayan yayarsa da kuma k'anwarsa, yana yi yana waigen Amrah, da har yanzu take kuka kamar ranta zai fita.

Sai da suka tafi, na ji wani irin kuka wanda ba zan iya tsayar da shi ba, zafafan hawaye ke fita daga k'wayar idanuwana, wanda zan iya kiransu, da hawayen takaici.

Wuri na nema na zauna, ina mai ci gaba da ruwan hawaye, ga Amrah ma bata yi shiru ba.

Muna cikin hakan, sai ga Mallam ya shigo, biye da shi, k'aninshi ne mai suna Marwana.

Da sallama suka shigo, na amsa ina mai k'ok'arin tsayar da hawayen da har yanzu suka kasa tsayawa, had'e da jawo hab'ar zanina ina share wanda suka gama wanke min fuska.

Duk da k'ok'arin da na yi dan ganin na b'oye damuwata, hakan bai hana su Mallam fahimtar halin da nake ciki ba.

Da azama Mallam ya iso inda nake, fuskarsa ta nuna damuwa k'warai da ainun.

"B'oye damuwa sam bata cancanta a bisa fuskar da ruwan hawaye ya gama wankewa da ita ba. Halin jarumta, sam! Bai cancance ki a dai-dai wannan lokacin ba.

Ko mutum bai sanki ba a baya, idan har ya kalle ki a wannan lokacin, sai ya tabbatar da lallai kina cikin damuwa.

Ki fad'a min Murjanatu, wane irin abu ne ya faru da ke, wanda har ya saka ki kuka?

Da alama dai ba ciwon Amrah ba ne, saboda ba haka zan same ta ba idan har shi d'in ne.

Yanayinku ke da ita, ya tabbatar min da cewa wani abu ne, wanda a tare ya b'ata maku rai." Ya dakata daga nan, yana mai k'ok'arin zama a kusa da ni.

Marwana kuma, ya d'auki Amrah yana ta rurrugarta, har ya samu nasara ta yi shiru, babu b'ata lokaci, cikin mintunan da basu fi biyar ba, bacci ya d'auke ta.

Nannauyar ajiyar zuciya na sauke, na kalli Mallam na ce,

"Mallam ashe talakan da yake zaune inda Allah Ya ajje sa, ya rik'e talaucinsa, zai iya zama mai laifi ga masu wadatar dukiya?

Ashe rashin shiga shirgin wasu, zai iya jaza mana wata matsala, ga wanda suke ganin sun fi mu d'aukaka?

'Yan uwan Annur ne suka zo..." na fad'a masa duk yanda muka yi da su har sanda suka tafi.

Cikin nuna halin ko in kula Mallam ya ce,

"To kuma shi ne ya zama abun damuwa da har kike asarar ruwan hawayenki?

Ni a ganina, ko kad'an wannan ba zai iya zama silar b'arnar hawayenki ba.

Ai da sauk'i, tun da ba gidansu kika je da nufin neman taimako ba. Har cikin gidanki suka same ki.

To sai me?"

Gyad'a kai na yi, na ce,

"Amma Mallam, baka ganin abin da suka min tamkar cin fuska ne a gare ni?

Duka a shekaru, Saddiqa ba zata wuce shekara goma sha tara zuwa ashirin ba.

Islam fa? Ko goma ban ce zata yi ba.

Amma a haka suka ringa cin zarafina, suna fad'a min magana, tamkar talauci hauka ne."

Hawaye ya sake cin k'arfina.

"Haba Murjatu! Yanzu ke, yarinyar da ba zata wuce shekara ashirin ba ce ta sa kika zauna kike kuka?"

Marwana ya kwantar da Amrah bisa tabarma, ya ce,

"Yaya Abdallah, dole Maman Bilal (Sunan da dangina da na  Mallam suke kirana da shi, tun sanda na haifi yarona na farko mai suna Bilal, kuma har ya rasu basu daina kirana da shi ba.) zata  yi kuka. Abin da kake ganin bai kai ya kawo ba, yarinyar da ta yi k'anwa ta biyar da ita, amma ta tsaya tana fad'a mata maganganu, tana mata rashin kunya.

Wallahi, Allah ne Ya kyauta. Da a ce na tarar da su, suke mata fitsara, da duk abin da zai faru sai dai ya faru. Dan wallahi marin yara zan yi, in yaso sai mahaifin nasu, Alhaji Iqra Al-Hussein ya sa a d'aure ni, a kashe ni."

Mallam ya ce,

"Sai hak'uri ai. Komai na duniyar nan, sai ana kai zuciya nesa. Wata rana sai labari."

"Haka ne." Na fad'a had'e da share hawayena.


Pinky durling??
*RAZ 2????*
[7/3, 8:40 AM] Princess Amrah???: *??MRAH NAKE SO!* ?


(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi.)

            Na Amrah A Msh
            _(Princess Amrah)_
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


_Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (sickler)_


                          0?9?

Jinjinar ban giram ga 'Yan *RAZ NOVELLA.* Fatan alkhairi a ko da yaushe. Na gode da k'warin guiwar da kuke bani. Keep it up dearies.?

***

Haka dai muka yi yammacin wannan rana, baki d'aya rayukanmu, sun yi bak'i k'irin. Hankulanmu sun dagule.

Ko da dare ya yi, na ke ma Mallam magana cewa,

"Ni ina ga kaman mu dakatar da Annur daga zuwa gidan nan, hakan ne kawai zai saka mu a cikin kwanciyar hankali.

Ba zata yiu a ce saboda shi ana cin zarafinmu ba, k'aramar k'anwata tana fad'a min magana son ranta."

Mallam ya nisa, ya ce,

"Hakan da kika fad'a sam! Ba shi ba ne mafita.

Idan Annur ya zo gidan nan, korarsa zamu yi?

Kina ga kamar mun masa adalci idan muka hana shi zuwa inda muke?

Annur yaro ne har yanzu, wanda bai mallaki hankalin kansa ba.

Ya kamata mu masa uzuri, tun da ba shi ya miki ba, hasali ma, shi kanshi bai ji dad'in lamarin ba.

A ganina, idan har ya zo muka dakatar da shi daga zuwa, ba mu kyauta masa ba.

Ki duba ki ga sha'kuwar da ke tsakaninsa da yarinyar nan, ki ga halin da yake shiga duk sanda bata da lafiya. Kina ganin mun masa adalci idan muka raba shi da ita a lokaci guda?"

Share hawayen da suka zame min abinci, a duk yammacin ranar na yi, na dube shi, na ce,

"Mallam wannan fa abu ne wanda ya shafi martaba da mutuncinmu.

Matuk'ar muka bar yaron nan yana ci gaba da zuwa, bamu san me gaba zata haifar ba.

Idan yanzu yayarsa d'aya da k'anwarsa ne suka zo, gobe bamu san wa zai zo ba.

Wata k'ila mahaifiyarsa da mahaifinsa ne zasu zo.

Amma idan muka hak'ura da shi, shi ma sai ya ha'kura da Amrah, tun da dama tun asali bai santa ba bata sanshi ba. Kowa sai ya zauna a inda Allah Ya ajje sa."

"Gaskiya kika fad'a Murjanatu. Sai dai kuma fa ni ba zan ta'ba iya korarsa idan ya zo ba.

Zan dai bar miki wannan aikin, sai ki san yanda zaki yi da shi."

Daga nan ya gyara kwanciyarsa, ya tofa addu'ar bacci.

Ni ma kwanciyar na yi, amma fir-fir bacci ya k'i d'auka ta.

Da zarar na runtse idona, sai in tuna abin da Saddiqa da Islam suka mana.

Da zarar na fara tunanin yanda zan hana Annur zuwa, sai wata zuciyar ta nusar da ni darajar hak'uri.

Baki d'aya sai in ji zuciyata ta yi sanyi, ba zan iya tsayar da shi ba.

Ko ba komai Annur ya gama min komai, ya nuna tsantsar soyayyarsa ga gudan jinina, ya d'aura damuwarsa a kanta, ya sadaukar da lokacinsa a kanta.

Na masa adalci idan na raba su? Ita kanta Amrah, na mata adalci idan na tsayar da farin cikinta daga zuwa inda take?

Kuka sosai nake, wanda na kasa tsayar da su, na kasa tantance ko na menene. Shin, na damuwar abin da ya faru ne? Ko kuwa na tausayin halin da Annur da Amrah zasu shiga idan suka daina ganin junansu ne?

Na sani sarai, ta Amrah mai sauk'i ce. Akwai yarinta a tattare da ita, ba zata jima ba zata iya mancewa da shi. Shekara d'aya ma idan ta d'auka bata ganinsa, zata manta da halittarsa a doron k'asa, matuk'ar ba maganarsa nake mata ba.

Shi kuma fa? Zai iya mantawa da ita? Ko kuwa zai iya cire k'aunarta daga zuciyarsa?

Kaina na dafe, had'e da had'iyar yawu da k'yar, na mi'ke tsaye.

Ko da na duba tsohuwar agogon da ke jikin bango, k'arfe sha biyu da rabi na dare ne.

Fitila na kunna, sannan na fita daga d'akin.

Ban-d'aki na nufa, na d"auro alwala sannan na dawo cikin d'aki, na hau jera sallolin da ko ni ban san adadinsu ba.

Ba ni ce da tashi ba sai kusan k'arfe ukun dare, sannan na hau gado, babu jimawa bacci ya d'aukeni.

Washe gari da safe, ina ta tsammanin zuwan Annur kamar yanda ya fad'a, amma sai bai zo ba, har goman safe ta wuce.

Ban yi mamaki ba, dan na san dama ba lallai ba ne ya zo, duk kuwa da yanda ya so zuwa d'in.

Abu wasa ba wasa ba, har aka yi sati biyu babu Annur babu alamunsa.

Tun abun baya damu na, har na fara damuwa.

Amrah kuwa, sunan da na koya mata take kiransa da shi, take yawan fad'i cike da damuwa,

"Hamma!" Take fad'i dare da rana. Wani lokacin tana kuka, wani lokacin kuwa har hijabina take d'aukowa tana bani, tana fad'in sunan Hamma, manufarta wai in kai ta inda yake.

Shi kanshi Mallam abin ya dame shi.

Ranar da Annur ya cika sati biyu bai zo inda muke ba, ya same ni da maganar, a tsakar fida da wani yammaci,

"Raina yana matuk'ar b'aci, zuciyata tana yamutsa, kaina yana dagulewa, a duk sanda na tuna da yaron nan.

Ban san me ya sa ba, ina jin rashinsa har cikin zuciyata.

Ina k'aunar Annur, ina tsannain kewar rashin zuwansa gidan nan.

To ni ma ke nan, ina ga Amrah? Ya take ji? A haka kuma dole ta bar abin a ranta, saboda yarintarta."

Baki d'aya jikina ya yi sanyi da kalamansa, ni kaina ina jin rashinsa har cikin raina, musamman ma idan Amrah na kuka, tana nemansa.

"Mallam ban san..." na dakata daga nan, saboda tozali da idanuwana suka yi da wanda muke kan maganarsa.

Da sauri Amrah ta ruga ta isa gare shi, ta rungume shi sosai kamar wani zai k'wace mata shi, tana fad'in,

"Hamma..." sai kuma ta yi shiru, ta sake kallonshi ta k'yalk'yale da dariyar da ke nunar da tsantsar farin cikinta.

A yanayinsa, dole mutum zai fahimci damuwar da yake cikinta.

"Sannu Annur." Na fad'a ina masa murmushi.

"K'ariso ka zauna mana Annur, zo ga tabarma nan." Mallam ya fad'a tare da gwada masa kusa da shi.

Zama ya yi yana d'auke da Amrah, ya gaishe mu.

"Kamar kana cikin damuwa, lafiya dai ko?"

Na tambaye shi.

"Umma akwai damuwa..." ya fashe da kuka mai tsuma zuciya, wanda har sai da ya karya min zuciya.

"Daddy'na ya ce zai mayar da ni Cyprus, inda Aunty Nadrah take aure.

Su Aunty Saddiqa ne suka kai masa zuga, wai bana karatu, kuma bana zuwa School, kullum wai ina nan gidan, wurinku.

Dady'na mutum ne mai son ilimi, yana son mu yi zurfi a karatu. Hakan ya sa ya yanke hukuncin tura ni can wurin yayata, wai in ci gaba da karatu a can, har lokacin da zan mallaki hankalin kaina.

Mamana kanta hakan bai mata dad'i ba, saboda yanda ta kula da bana so, ita kuwa tana son abin da nake so." Ya yi shiru daga nan, saboda kukan da ya ci k'arfinsa.

Da k'yar ya iya ci gaba da,

"Bana son rabuwa da Amrah, na so na kasance tare da ita, na kula da ita ko dan ciwon da take tattare da shi.

Na so a ce ta girma a gabana, in kula da ita, in k'aunace ta kamar yanda yayanta na jini zai mata.

Sai dai kuma kash! Hakan ba mai yiuwa ba ne, an b'ata min tsarina a kan yanda na so gina rayuwata."

Ya share hawayensa da hab'ar rigarsa, sannan ya ci gaba,

"Ina son Amrah, Ummah. Bana son abin da zai raba ni da ita. Ina so ku min wata alfarma guda d'aya, wacce in har kuka min ita, kun gama min komai."

Cikin kuka na ce,

"Ina jin ka Ann..nur.." na yi k'ok'arin shanye kukan da ke son hana ni magana.

"Kasantuwar Amrah yarinya ce, wacce babu wuya zata iya mantawa da ni.

Ina son ku yi bakin k'ok'arinku, na ganin bata manta da ni ba.

Na sani abu ne mai wahalar gaske, amma ina son ku min wannan alfarmar."

Cikin k'arfin hali da nuna jarumta Mallam ya ce,

"Na maka wannan al-k'awarin, Annur. Da yardar Allah Amrah ba zata tab'a mantawa da kai ba.

Zata sanka ko da ba a baki ba, a suna ma kawai.

Zamu ringa k'ok'arin sanar da ita irin halaccin da ka mata a yarintarta."

Sallama muka ji, muryar wani dattijo ne.

Mallam ya amsa sallamar had'e da mik'ewa yana shirin fita.

"Annur baku gama ba? Har Yallab'ai ya kira ni yanzu, na ce masa motarmu ce ta d'an tsaya." Mutumin ya fad'a da d'an k'arfi, yanda Annur zai ji.

"Ina zuwa Baba Amadu."

Ya kama hannuwan Amrah duka biyun, kuka sosai yake, kamar wanda aka duka.

Ita ma Amran kaman ta san abin da yake faruwa, ta dai gan ni ina kuka, ga kuma babban abokinta ma yana yi. Kukan take sosai kamar ranta zai fita.

"Ina k'aunarki Amrah. Ban so a raba mu ba a dai-dai wannan lokacin.

Na so na kasance tare da ke, na so na kula da lafiyarki, amma Allah bai nufa ba.

Dan Allah Amrah kar ki manta da ni, kar ki manta da Annur Iqra Al-Hussein a rayuwarki.

Ga wannan, kud'ina ne da abokin Dady'nmu ya tab'a bani sanda na je gidansa kwanakin baya, babu wanda ya san da su, ko Momy'nmu kuwa. Ina ta ajiyarsu ne, kamar na san abin da zai faru.

Naki ne halak malak, duk sanda wata buk'atarki ta taso, tun daga kan magani har sutura, a miki amfani da su." Ya zaro rafar dubu d'ari daga cikin wata bak'ar leda, ya damk'a ta ga Amrah.

"Na tafi. Sai wata rana.." kuka ya ci k'arfinsa.

Da gudu ya bar gidan, mallam na k'iransa amma ko waigowa bai yi ba.


_My fans, how was this chapter? Very touching ba? Soyayya ke nan. Comments d'inku yana 'kara min k'warin guiwa a ko wane lokaci. Amrah loves you irin over d'in nan.??_


Pinky durling??
*RAZ 2????*
[7/3, 8:40 AM] Princess Amrah???: *??MRAH NAKE SO!* ?


(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi.)

            Na Amrah A Msh
            _(Princess Amrah)_
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


_Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (sickler)_


                          1?0?

Wani irin kuka na fasa tamkar k'aramar yarinya, wanda duk jarumtar Mallam kasa bani hak'uri ya yi, shi kan shi kukan zuci yake, wanda a fuska kawai zaka iya fahimtar haka.

Jawo Amra da ke kuka kamar ranta zai fita na yi, na d'ora a cinya sai faman rurrugarta nake. Cikin kuka na ce,

"Ki yi ha'kuri Amrah. Duk da ba lallai kin san abin da yake faruwa ba, sai dai na san dole jikinki zai baki, rashin masoyinki na gaskiya.

Annur ya tafi ke nan, bana tunanin zai sake waiwayarki.

Ba wai ke kad'ai ba, ni kaina cike nake da zullumin kewar Annur da na tabbatar sai na yi ta.

Sati biu kawai da ya yi bai zo ba, ji na yi kamar in bi shi. Gashi yanzu zai yi tafiyar da ba lallai na sake ganinshi ba.

Tabbas Annur yaro ne d'an halak, wanda samun kamarsa zai yi matuk'ar wahala a dai-dai wannan lokacin.

Shekararsa goma sha uku, amma halayensa kamar sun fi na yawan mai shekarun nasa."

Na kuma fashewa da wani kukan, zuciyata sai tafarfasa take, ina jin kamar na kira Annur ya dawo gare mu, kamar na hana sa wannan tafiyar.

Sai dai kuma bani da yanda zan yi, domin kuwa k'addara ta rigayi fata.

Hukunci ne wanda mahaifinsa ya yanke, bani da yanda zan yi face hak'uri.

*BAYAN SHEKARA TAKWAS*

A dai-dai wanan lokacin ne Amrah ta cika shekara goma a duniya.

A iya tsawon wannan shekaru, wahala iya wahala tana yinta, saboda baki d'aya yanda muka d'auki sickler d'inta ba haka ba ne.

Wahala sosai take bata, ashe irin mai tsananin nan ce da ita.

Kullum cikin zarya asibiti muke, tun muna damuwa, har Allah Ya saka mana tawakalli a zukatanmu. Ita kanta yarinyar, ta saka ma ranta dangana.

Ranar wata laraba, da yammaci, misalin k'arfe shida na yamma,

Da gudu Amrah ta shigo, har tana cin tuntub'e.

"Umma.." ta fad'a cikin shesshekar gudu.

"Bi a hankali mana Amrah. Na sha fad'a miki cewa ki daina irin wannan gudun, wanda har zai sar'ke ki amma bakya ji. Me ya faru ne?"

"Umma wata mata ce, gata can sun faka motarsu a k'ofar gidanmu."

Dafe baki na yi, na ce,

"To fa! Wannan wace mata ce a cikin mota haka? Ko ta yi b'atan hanya ne? To Allah dai Ya sa lafiya."

Tun bamu kuma fad'in komai ba sai ga ta ta shigo ciki.

Mahaifiyar Annur ce, sanye cikin kaya na al-farma.

Fuskarta a sake ta yi sallama, sannan ta k'ariso daga ciki

"Marhabun da Hajiya Suhailah. Maraba maraba. Iso mana Hajiya."

Da fara'arta kuwa ta iso inda nake, ina k'ok'arin shimfid'a mata tabarma amma ta dakatar da ni,

"Ga kujera nan bari na zauna a kai kawai, babu damuwa ai." Ta sakar min murmushi.

Zama na yi a k'asa, na gaishe ta ta amsa da sakin fuska.

"Maman Amrah kin gane ni kuwa?" Ta fad'a tana kallo na.

"K'warai ma kuwa Hajiya. Ba mahaifiyar Annur ba ce?"

Jin na ambaci Annur ya sa da sauri Amrah ta iso gare ta, ta duka har k'asa ta gaishe ta.

"Lafiya k'alau Amrah. Lallai yarinya ta girma k'warai da ainun.

Ya k'arfin jikin naki?"

"Alhamdulillah! Jiki ya yi sau'ki sosai Mama. Ina fatan tare kuke da Ya Noor, saboda a ko da yaushe Ummah ce min take wai Ya Noor zai dawo gare ni, kuma gashi har yanzu bai dawo ba." Ta b'ata fuskarta alamun damuwa.

Dafa kanta Hajiya Suhailah ta yi, ta murmusa sannan ta ce,

"Annur zai dawo insha Allahu nan ba da jimawa ba. Ke dai abin da nake so a gare ki, kawai ki dage da addu'a. Allah ya shawo kan Dady'nsa, ya amince ya dawo gare mu.

Ni kaina ina cike da kewar yarona, ina son ya dawo ya ci gaba da rayuwa a gabana."

"Mama, har cikin zuciyata nake jin Ya Noor, nake mararin ganinsa.

Duk da ban sanshi ba, ba zan iya tuna komai game da shi ba, amma fa ina jin sa har cikin raina, kamar yanda na tabbatar shi ma ina ransa.

A yanda nake jin labarinsa a bakin Ummana da kuma Abbana, Ya Noor mutumin kirki ne, wanda ya nuna min zallar soyayya, ya kula da ni, sannan kuma ya bani lokacinsa.

Dan Allah Mama, ko a hoto ne ki gwada min shi, yau rana d'aya tal, in ga fuskar wannan bawan Allah, mai tarin halayen kirki.

Shekaru kusan hud'u ke nan ina fatan na ganshi ko da a mafarki ne, ko kuma a hoto, amma Allah bai karb'i du'a'ina ba, sai ga ki yau Allah ya kawo ki har inda muke."

Murmushi Hajiya Suhailah ta yi, ta ce,

"Abin da ya kawo ni ke nan Amrah.

Annur ya jima yana rok'ona a kan na zo gidanku, na had'a ku ko da a waya ne ku gaisa, amma ina guje wa maganarsa. Ba dan komai ba, sai dan sanin halin Dady'nsa da na yi. Matuk'ar ya fahimci wani abu to komai zai iya faruwa, saboda shi d'in bai had'a ilimin yaransa da komai ba.

Ganin halin damuwar da yake a ko da yaushe, ya sa yau na amince da buk'atarsa, zan kuma yi masa yanda yake so." Ta sake yin wani murmushin had'e da zaro wata leda mai d'an girma daga cikin jakarta.

Mik'o ta ta yi ga Amrah, ta ce,

"Waya ce wannan ya sa na siya miki, wai yana son ku ringa waya a kai a kai, kuna gaisawa, yana kuma jin halin da kike ciki.

A cikinta akwai hotunansa da dama ya turo, idan kin bud'e zaki gani."

Tsalle Amrah ta yi cike da murna ta karb'a wayan, a k'irjinta ta d'ora sai faman fara'a take, ta ma kasa furta komai tsabar murna.

"To ke baki iya godiya ba ne?" Na fad'a cike da mamakinta.

"A'a maman Amrah, bar ta ta yi murnanta. Shi d'in ma ya ji dad'i sosai sanda na amince masa." Ta fad'a had'e da mik'ewa.

"Ni zan wuce, sai kuma Allah ya sake dawo da ni. Sannan kuma ina neman wata al-farma a wurinku."

Da sauri na ce,

"Allah Ya sa zan iya, Hajiya."

"Dan Allah ki ringa turo min Amrah tana gaishe ni, lokaci zuwa lokaci.

Ina son yarinyar, ko dan soyayyar da Annur yake mata, ita ma kuma take masa.

Sannan kuma duk sanda kuke da wata matsala ko kuma damuwa, kar ki ji komai, dan Allah ki same ni da maganar, insha Allahu zan warware miki ita.

Amrah dai 'yata ce tamkar Annur, yanda nake jinsa haka ita ma nake jinta a raina, banbancinsu ba wani mai yawa ba ne.

Dalilai da dama ne suka hana ni waiwayarku, tun bayan tafiyar Annur.

Ciki kuwa har da rayuwar k'unci da na shiga, a lokacin da aka tafi min da yaro. Na ji a raina, bana son ganin duk wani abu da ya dangance shi, saboda tuno min da shi da yake.

Baki d'aya komai na shi na kyautar, saboda bana son gani.

Shi ya sa na ji ba zan iya zuwa wurinku ba, guje ma tada tabon da ke k'ok'arin warkewa.

Hatta da abokanansa na hana su zuwa inda nake, saboda gani nake idan har suka zo, zana ringa masu kallon kamar zan ga Annur a tare da su, bayan kuma ba haka ba ne.

Abu na biyu kuma, rabamu da ku da Dady'nsa ya yi, ya mana iyaka da ku ne saboda yaronsa, kuma na san halinsa sarai, matuk'ar ya ga wani abu yana shiga a tsakaninmu, to tabbas komai zai iya yi maku..."

Da sauri na dakatar da ita, jin ta yi wannan maganar ya sa na ce,

"To kuma Hajiya a haka ne kike so Amrah ta ringa kai miki ziyara?"

Murmushi ta yi,

"Ko za a tsare Dady'nsu a ce ya gwada Amrah bai santa ba. Bana ji ma ko sunanta ya rik'e har tsawon wannan lokacin.

Kuma shi 'din ba mazaunin gida ba ne, yana da manya manyan kamfanoni a Kaduna, da kuma Abuja, wanda suka danganci magani.

Kin ga kuwa ina ya ga wani lokacin zama gida, bare har ya kula da masu shiga da kuma masu fita? Har kuma ya iya tantance Amrah, a matsayin yarinyar da Annur ke so, har ya sadaukar da lokacin karatunsa a kanta?

Kar ki ji komai Maman Amrah, wannan mai sauk'i ne.

Ni dai kam ina son Amrah, kuma na miki al-k'awarin zuwanta inda nake ba zai tab'a saka ku da na sani ba, face shak'uwa da zata k'ara shiga tsakaninta da Annur, wanda nake fatan ya kai su ga yin aure duk sanda suka gama mallakar hankalin kansu."

Ajiyar zuciya na sauke, sannan na ce,

"To Hajiya, su kuma fa 'yan uwansa?

Ina nufin Saddiqa da Islam. A sanina dai su ma d'in basa k'aunar Amrah, saboda suna ganinta d'iyar marasa arzik'i.

Kina ganin kamar ba zasu ci zarafinta ba idan tana zuwa gidansu?"

Komawa ta yi ta zauna daga kujerar da ta tashi, ta ce,

"Maman Amrah ke nan. Ai Saddiqa ta dad'e da yin aure, kusan shekara bakwai ke nan, tana Bauchi a can take aure. Yanzu haka yaranta biyu fa.

Islam kuma tana India, a can take karatun medicine. Bata zuwa k'asar nan sai bayan shekara guda guda.

Dan haka dan Allah kar ki damu. Ina son Amrah ta shak'u sosai da ni, in bata gatan da ban ba ma yarona Annur ba."

Sai a lokacin na samu kwanciyar hankali, na murmusa,

"To insha Allahu kuwa Amrah zata ringa zuwa tana gaishe ki duk ranar jumu'a.

Sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba,

Kin san ita d'in yarinya ce mai yawan ciwo, saboda sikilar da ke gare ta

Da wuya ta cika sati d'aya da lafiya, ba tare da mun je asibiti ba.

Kin ga ke nan, ba ko yaushe ba ne zata samu damar zuwa, saboda yanayin jikin nata."

Hajiya Suhailah ta ce,

"Haka ne Maman Amrah. Ina mata fatan samun lafiya. Uban-giji ya bata lafiya, ya kawo mata k'arshen wannan wahala ta ta."

"Amin." Na fad'a sannan na mik'e, ganin ita ma d'in ta mik'e.

Hijabina na ciro daga bisa igiya, na saka.

"Amrah ba zaki mata bankwana ba?"

Na fad'a ina kallonta.

Kunya ta ji da gudunta ta shige dak'i, wai tun daga sanda Hajiya Suhaila ta ambaci aure a tsakaninta da Annur.

Har k'ofar gida na raka ta, wata irin b'arkekiyar mota ce aka kawo ta ciki, wadda daka ganta ka san lallai naira ta zauna masu.

Sai da ta shiga mota sannan muka sake yin bankwana na dawo gida, zuciyata cike da k'aunar matar, ta matuk'ar burgeni.

Yana da wuya a samu matar mai kud'i kamar Alhaji Iqra Al-Hussein, kuma tana son talakawa irinmu.


_A yi ha'kuri jiya ba a ji ni ba, mun samu matsalar wuta ne._


Pinky durling??
*RAZ 2????*
[7/3, 8:40 AM] Princess Amrah???: *??MRAH NAKE SO!* ?


(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi.)

            Na Amrah A Msh
            _(Princess Amrah)_
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


_Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (sickler)_


                          1?1?

Ko da Mallam ya dawo na shaida masa abin da ya faru, ba kad'an d'in murna ya yi ba.

Sosai ya nuna farin cikinsa a fili, dan a zahirin gaskiya, zan iya cewa Mallam ya fi ni damuwar rashin Annur.

"Amrah kawo wayar mu ga" ya fad'a yanda zata ji, saboda tun sanda Hajiya Suhailah ta tafi Amrah bata sake fitowa ba, sai yanzu da mallam ya shigo ake kiran sallar magrib.

Fitowar kuwa ta yi, hannunta rik'e da kwalin wayar.

"Ga ta Abbah.." ta mi'ko masa.

Kar'ba ya yi kuwa, nan ya saka sim card d'in da ke cikin pack d'insa, sannan ya saka batirin ya rufe da marfi.

Waya ce Nokia asha, kalar ja, mai matuk'ar kyau da d'aukar ido.

Kasantuwar Mallam ma yana da waya, ya san kanta, ya sa bai wani sha wahala ba wurin had'a komai yanda ya dace.

Ko da ya kunna, hoton Annur ne a saman walfefar wayar, ya yi wani irin k'ayataccen murmushi.

Kyakkyawar fuskarsa ta amsa wani irin k'asumba, irin wadda matasa ke tarawa take masu matuk'ar kyau.

Gashin kansa kwance yake luf luf, ya tara suma da alamun ya jima bai yi aski ba.

Baki d'aya halittarsa ta gama fitowa, tamkar yaron larabawa haka ya koma.

Da murna k'warai Mallam ya mi'ke tsaye, donshi har yana k'ok'arin kawo ruwa tsabar farin ciki.

"Annur haka ka koma? Allah sarki yarona!" Yana sake kallon hoton.

Da murna ni ma na ce,

"To ka bani nima na gani mana."

Mik'o min wayar ya yi,

"Yaro ya zama saurayi son kowa k'in wadda ta rasa.

Murjanatu taya ni kallo dan Allah."

Kamar wasu kid'mammu haka muka koma, farin ciki kuwa ko d'anmu ne na cikinmu iyakacin wanda zamu yi ke nan.

"Umma kawo ni ma na ga Yaa Noor d'in." Amrah ta fad'a, ita kanta da fara'a k'unshe a saman fuskarta.

Mik'a mata na yi, ta dube shi da kyau.

"Umma ai na san wannan..." ta fad'a cike da mamaki.

"Shi ne Yaa Noor d'in?"

Cike da mamaki na kalle ta, na ma rasa abin da zan fad'a.

"Wallahi Umma da gaske nake na san shi. Yanzu wai baki tab'a kula da shi ba a asibiti idan mun je wani lokacin?"

Mallam ne ya iya fad'in,

"Anya kuwa Amrah? Ko dai mai kama da shi ne kike gani? Annur fa baya k'asar nan."

Sake dubar hoton ta yi, cike da yak'ini ta ce,

"Wallahi Abbah na san shi. Kusan sau biyu ko sau uku ina ganinshi a asibiti.

Ranar farko ma a wurin ganin likita ne na ganshi,

Rana ta biyu kuma cikin keken guragu na ganshi. Na ukun ne dai ba zan iya tunawa ba, amma kam tabbas wannan ne nake gani."

Ganin bil-hak'ki take, ya sa na ce,

"Wai wace irin magana kike ne Amrah?

Kin san shekarar Annur nawa  rabonsa da k'asar nan?

Kusan fa shekara bakwai ko takwas ke nan.

Ba a kama ne a  duniya?

Wata k'il dai mai kama irin ta shi ce kika gani."

Mik'o min wayar ta yi, ta ce,

"Umma sake duba shi dai sosai. Na yi mamaki ki ce wai baki ta'ba ganinsa ba.

Wallahi Umma duk ganin da nake masa a tare da ke ne.

Har ma fa akwai ranar da ya gaishe ki, kin dai manta ne kawai."

Kallon mamaki kawai muke binta da shi, saboda yanda muke jin zancen nata kamar a wasa, ga ta ita kuma da gaske take, har tana dagewa rantsuwa.

"Umma ashe dama shi ne Ya Noor d'in. To ni dai gaskiya na yi fushi da shi.

Ashe yana ganina kuma baya min magana ko? Bayan kuma ya san ina cike da kewarsa, ina son ganinshi sosai." Ta b'ata fuskarta cike da damuwa.

Kamo ta na yi na zaunar a kusa da ni,

"Amrah! Ki cire tunanin Annur ne kike gani a asibiti.

Na fad'a miki cewa ba shi ba ne, Annur baya k'asar nan fa.

Kin san ana kamanni a duniya, ta yiu ke kamarsu ce kika gani, bare kuma wannan a hoto ne.

Dan haka ki daina wannan tunanin, ta ya Annur da yake mararin ganinki, kuma zai ganki ya share ki?

Wannan ba abu ne mai yiuwa ba."

Haka na ci gaba da k'ok'arin ganar da ita gaskiya, amma fa sam ta k'ek'ashe ta k'i yarda da maganata. A k'arshe dai ta nunar min da ta yarda, wanda a zahirin gaskiya ba yarda d'in ta yi ba kuma.

Haka dare ya yi na ringa juya maganganun Amrah, ban san dalili ba, haka kawai na saka ma kalaman nata alamar tambaya, ta yanda kallo d'aya ta ce ta san shi, kuma har take rantsuwa cewa wai ya tab'a gaishe ni.

Washe gari da safe ta yi shirin makaranta. Wata makaranta ce a can k'asan layinmu ta gwamnati take, yanzu haka tana primary 6 ke nan.

"Abba baka kira min Yaa Noor d'in ba fa, kuma kai ka ce yau da safe zaka kra min shi kafin na tafi makaranta."

Da murmushi Mallam ya ce,

"Ai kin ga yanzu fa makaranta zaki je Amra, insha Allahu na miki al-k'awari idan kin dawo zan kira miki shi, tun da akwai kati da kuma lambar wayarsa a nan ciki."

"Oya ki yi ki kammala shan kununki ko? K'osan ya ishe ki?" Na tambaye ta.

"Ehh, ya ishe ni Umma. Na gode."

Bayan ta gama ta zo na saka mata al-barka kamar ko yaushe, na ce,

"A yi karatu da kyau 'yata. Ina miki fatan alkhairi. Allah Ya miki al-barka."

"Amin Ummana. Bara in tafi."

Ta sab'i jakar makarantarta.

Bayan ta kusa isa zaure, ta juyo ta d'ago min hannu tana murmushi, wanda wannan d'ago hannun da ta yi, kawai sai na samu kaina da samun rashin kwanciyar hankali.

Take gabana ya hau dukan uku-uku. Na d'aga nawa hannun ni ma ina d'aga mata har ta fice.

Kallon Mallam da ke shan koko na yi, cikin wata murya mai nunar da fargaba ko kuma shakku, na ce,

"Mallam, kawai sai na samu kaina da rashin kwanciyar hankali a kan tafiyar yarinyar nan. Hankalina ya tashi ban san dalili ba."

Murmushi ya yi, ya ce,

"Murja ke nan. Ban san sai yaushe zaki cire ma ranki irin wannan tunane tunanen marassa ma'ana ba.

Ko kin manta addu'ar iyaye ce a kan Amrah?

Fita goma zata yi daga gidan nan sai kin saka mata al-barka, sannan kuma ki mata fatan al-khairi.

Kin ga kuwa, ai bai kamata ma ki saka wani tunani a ranki ba.

Kin san shi shaid'an ta ko wace hanya yana bi dan ganin ya dagula wa mutum lissafi.

Ki yi ta'awizi ki kore shaid'an, a duk lokacin da tunani irin wannan ya fad'o miki."

Kalaman Mallam suka sa na ji wani sanyi a zuciyata, na kuma samu kwanciyar hankali d'ari bisa d'ari.

"Maganarka gaskiya Mallam. Duk wanda al-barkar iyaye ke biye da shi, to tabbas baya tab'ewa.

Ko da a ce wani abu zai same shi, matuk'ar ya rik'e adhkar d'insa, sannan iyayensa na saka masa al-barka, ko ma me zai same shi, zai zo masa da sauk'i.

To bare kuma Amrah, yarinya 'yar shekara goma, wadda a kullum burinta shi ne ta ga ta faranta mana rai.

Ba wai dan Amrah tana tawa ba, amma wallahi zan iya cewa tun da nake a rayuwata, ban tab'a ganin k'aramar yarinya mai kyawawan halaye da d'abi'un kirki kamar ta ba.

Dama dukkan hani ga Allah baiwa ne, na gasgata wannan zancen.

Gata dai yarinya mara wadatacciyar lafiya, Allah Ya rage ta ta fannin lafiya, amma kuma sai ya wadatar da ita da halaye na gari.

Ina mata fatan d'orewa da wannan halaye nata, wanda nake fatan ko bayan babu ita a doron k'asa, zata zama abar koyi da kuma al-fahari ga al-ummah."

Daga nan wani irin kuka ya kufce min, wanda na rasa gane ko na me nene.

Ajiyar zuciya Mallam ya sauke,

"Haka ne Murja. Amrah kam sai dai mu dad'a godiya ga mahalicci.

Ga ta da k'walwa, tun daga b'angaren Islama har b'angaren boko d'in.

Ta zama yarinyar da duk wani abun da za a yi da ya danganci masu k'ok'ari, to ita ce farkon da za a saka a lissafi.

Idan wata gasa ce za a yi da ita a ciki,

Musab'aka har ta k'ananan hukumomi ta je, ta wakilci Katsina Local Government, sahun 'yan izib goma.

Duka wannan halaye nata sun ginu ne ta dalilinki Murja. Ke ce kika d'ora ta a bisa wannan tafarkin na kirki.

Tabbas! Samun uwa ta gari kamar ki sai an tona, ke jajirtacciyar mace ce, abar al-fahari kuma abar kwatance."

Du'kar da kaina na yi ina wasa da warwaron hannuna, ina k'ara jin tausayin Amrah a cikin zuciyata.

Ba dan komai ba sai dan kasa gafartawa kaina da na yi, saboda na san tabbas mu ne sila, ciwon Amrah tamkar mu ne silarsa.

Tun da inda a ce tashin farko mun yi abin da ya dace kafin aure, da duk hakan bata faru ba.

Sai dai kuma k'addara ta rigayi fata, kamar yanda Dr. Xarah ta fad'a mana.

Da wanann tunanin na mik'e, na tattaro kayana da na Amrah masu datti, zan wanke su.

Mallam ya ce,

"Na ji fa ta rok'e ki al-farmar kar ki yi wankin nan har sai ta dawo ku yi tare, shi ne kuma kika fiddo zaki yi?"

Ajje kayan na yi a k'asa sannan na ce,

"Wahalar da yarinyar nan ke yi ce nake ga kaman zata yi yawa Mallam.

Ka ga fa Dr. Xarah ta hane mu a kan saka ta aiki da yawa, musamman ma wanda k'asusuwanta zasu yawaita motsawa.

Shi ya sa ba zan sake barinta ta yi wanki ba. Girki da shara dai da ba wani wahala ne da su ba, sai in ringa taimaka mata wurin yinsu."

"Ehh to, haka ne kuma.

Ni bara in tashi in nufi wurin k'wadago. A yi min addu'a."

Kallonsa na yi da murmushi na ce,

"Allah Ya kare ka da kariyarSa mafificiya.

Allah Ya baka ikon ciyar da mu da halal.

Fatan al-khairi."

"Ameen." Ya fad'a had'e da tafiya.

Misalin k'arfe sha biyu na gama komai, har gyare-gyaren gida duka na yi.

Muroyoyin yara na ji ana hayaniya sosai, kuma abun na k'ara kusantowa a cikin gidanmu.

Saurin mik'ewa na yi jin sun shigo daga zauren gidan, wasu ma har sun iso daga ciki.

Ko da suka k'ariso na tambaye su, lafiya?

Wata yarinya 'yar za'kal d'insu ce ta yi caraf ta ce,

"Amrah Abdallah ce..." muryarta ta sark'e tsabar sauri da take ta fad'a min.

Cikin tashin hankali na ce,

"Fad'a min me ya faru da Amrata? Me ya samu yarinyata?"

"Wani malaminmu ne ya dake ta sume, har yanzu bata farfad'o...."

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" Na furta ban ko jira ta gama maganar ba.


_Duk wasu masu cutar sickler, tun daga manya har izuwa k'ananan yara, ina masu fatan samun sauk'i. Allah Ya sauk'ak'a masu, Ya kawo rahamarSa a gare su._

*Ku yi comment da AMEEN, Please??????.*


Pinky durling??
*RAZ 2????*
[7/3, 8:40 AM] Princess Amrah???: *??MRAH NAKE SO!* ?


(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi.)

            Na Amrah A Msh
            _(Princess Amrah)_
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


_Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (sickler)_


                          1?3?

Washe gari da sassafe sai ga Malaman makarantarsu sun zo, su kusan ashirin ko ma fin haka. Har d'akin ma bai iya d'auke yawansu ba.

A lokacin da suka zo Mallam baya nan, ya zo ya kawo mana abinci, ya wuce wurin aikinsa.

Har k'asa na du'ka muka gaisa, sannan na d'an bubbuga Amrah ta tashi.

Head master'nsu ne ya 'kariso dai-dai inda take,

"Sannu Amratu. Ya k'arfin jikin naki?"

Da fara'a k'unshe a fuskarta ta ce,

"Jiki da sau'ki sosai Mallam. Na gode."

Da haka malaman sukaita mata ya jiki, a k'arshe Mallam Mu'ammar cike da kunya ya dafe k'eyarsa, ya ce,

"Insha Allahu hakan ba zata sake faruwa ba. A yi hak'uri." Ya juyo gare ni, "Ban tsammanin abun zai kai har haka ba, da tun farko ban dake ta ba.

Insha Allahu ba zan kuma maimaitawa ba. Zan zama mutum mai tausayi, ba wai gare ta kawai ba, ga baki d'aya d'alibaina."

Ya juya ga sauran Malaman ya ce,

"Dan Allah ina mai neman afuwarku, daga yanzu duk wani d'alibi wanda za a kawo mai sickler, mu ringa kula da shi, mu san ta hanyar da zamu masa hukunci.

Sai mun kula sosai, mun basu kulawa tamkar 'ya'yanmu ko kuma k'annenmu na jini.

Ita rayuwar nan baka san wanda zai maka rana ba, sanann kuma kana naka Allah Na naSa."

Head master ya yi gyaran murya ya ce,

"Haka ne Mallam Mu'ammar. Na ji da'di k'warai da ka gane hakan, har kake bada taka shawarar.

Allah Ya tsayar nan, ita kuma Allah Ya bata lafiya."

"Ameen." Duka Malaman suka fad'a a tare.

Ku'di Head master ya zaro daga aljihunsa ya d'ora bisa gadon Amrah,

"Ga wannan a sai miki lemo. Allah Ya sauwak'a ko?"

Godiya na masa sannan suka fita, suka bar d'akin baki d'ayansu.

Bayan sun tafi na duba kud'in, dubu goma ne cif, hakan ba kad'an d'in dad'i ya min ba, saboda dama babu kud'in, abincin da Mallam ya siyo mana da safe ma da k'yar ya had'a ku'din ya siyo.

Kwananmu biyu aka bata sallama muka koma gida, ranar da muka koma sai ga Hajiya Suhaila ta zo, wai Annur ne ya fad'a mata Amrarsa bata jin da'di, da yake ya kira ta wayar Amrah'n Mallam ya d'auka yake shaida masa bata da lafiya, kuma baya asibiti a lokacin bare su yi waya.

Ta kawo ma Amrah sha tara ta arzik'i, a 'karshe ta mana fatan alkhairi sanann ta tafi.

Da yamma Mallam ya kira ma Amrah Annur. Sun jima suna waya, har take masa ta'din ganinsan da take yawan yi a Turai Hospital, amma ya shaida mata cewa ba shi ba ne, saboda shi tun da ya bar Nigeria bai sake dawowa ba. Wata k'ila dai mai kama da shi ne kawai take gani.

Rayuwa ta ci gaba da tafiya a haka, yau da lafiya gobe babu lafiya, a haka dai take rayuwarta cike da wahala.

Talauci kuma sosai muka rage shi, saboda babu abin da Hajiya Suhaila bata bamu, tun daga kan kayan abinci har sutura yi mana take, Amrah ma kuma ba laifi tana zuwa gidanta, abin dai sai sam barka.

A lokacin da Amrah ta yi JSS ne, take da shekara goma sha uku da watanni.

Ranar da suka gama zana jarabawarsu, Annur yake mata albishir da cewa mahaifinsa ya barshi ya dawo Nigeria  ya ci gaba da aikinsa, saboda ya da'de da zama Architecture babba, wanda yake da degree mataki na uku (ph. D) duk a 'bangaren zane-zane.

Sosai Amrah ta yi murna, dan zan iya cewa ko Hajiya Suhaila da ta haife sa, bata kai Amrah jin dad'i ba.

Ranar da suka yi waya cewa zai dawo gobe, kasa bacci Amrah ta yi, sai faman juye-juye take, ta ma rasa me ya kamata ta yi saboda murna.

Washe gari da sassafe ta fito tsakar gida ta hau shara, jin motsinta ya sa na fito a hanzarce na ce,

"Ya da shara tun da duku-dukun safiya, ba zaki yi shirin makaranta ba?"

Fuska a yamutse ta ce,

"Umma yau fa ba zan je ba. Kin manta Hammana zai dawo?"

Murmushi na yi na ce,

"Ya za a yi na manta da dawowar Annur? Ai ban ga zaman me zaki yi ba idan baki je ba? Ga ki kuma ke ce shugabar aji."

"Umma ai jiya Momy ta kira ni, wai yau da safe na je can mu yi shirye shiryen tarbarsa. Shi ya sa ma na tashi da wuri dan na kammala komai cikin lokaci."

"To ai shi ke nan. Amma ba kya gudun abin da Islam zata miki? Kin san fa ita ma yau tana iya k'in zuwa aiki saboda shi."

Tab'e baki Amrah ta yi ta ce,

"Duk abin da ta min ai sai in bata ha'kuri. Cike nake da murna yau bana jin masifarta da wulak'ancinta zasu yi tasiri a gare ni, har su hana ni tarbar Ya Noor."

Ajiyar zuciya na sauke,

"To ai shi ke nan. Amma sai kin daure, kin kai zuciyarki nesa."

"Insha Allahu kuwa Ummah. Ai kin san ni da wuya mutum ya b'ata min rai. Ina binsa da yanda yake so, sai dai ma a k'arshe shi d'in zai ji kunya."

"Na tabbatar da hakan kuwa 'yata.

Allah Ya miki albarka ya sa ki d'ore da wannan kyawawan halayen naki.

Wai har yanzu ba a saka ranar walimar saukar taku ba?"

"Basu saka ba Umma. Amma dai na san very soon za a yi ta. Shi ya sa ma suka ce kowa ya zama cikin shiri.

Har ma na gama tsara ma d'alibaina diramar (darama) da zasu yi ta larabci."

Murmushi na yi na ce,

"Ke d'in nan ce da d'alibai? Lallai ma."

"Umma kar dai ki ce baki san cewa ina da d'alibai ba? Tun bayan da muka yi sauka da tilawa aka raba mana azuzuwa.

Sauran "yan ajinmu ma aka fitar masu da aji...?"

"To bare kuma ke da kike Amira (Head girl)." Na k'arisa mata had'e da murmusawa.

"Ni dai ban fad'a ba Umma." Ta furta tana murmushi.

"Ai na san can kika dosa."

Ci gaba da sharar ta yi har sanda ta gama.

Zata yi wanke wanke na dakatar da ita,

"Je ki shirya kawai ki bar min wannna zan yi. Dan na ga a matse kike sosai."

"A'a Umma. Wallahi ki bari zan yi kawai. Wanke-wanken duka nawa yake?"

Ta ci gaba da ha'da ruwan kumfa.

"Sanin bashi da yawan ne ai ya sa na ce miki ki bari na yi. Kullum fa ke ke yi, yau rana d"aya dan baki yi ba ai ba damuwa."

Da 'kyar na samu ta bar wanke wanken na ci gaba. Ita kuwa ta nufi wanka.

K'arfe goma saura wayarta ta hau ruri, ganin Momy rubuce ya  sa ta hanzarta d'auka,

"Assalamu alaikum." Ta furta had"e da matse wayar da wuyanta, tana shafa kwalli.

"Ehh Momy saura k'iris na gama. Gani nan zuwa yanzu insha Allahu."

Ta d'an yi shiru daga nan,

"Da azahar? Ahh lallai to bara na hanzarta. Ashe ma isowar wuri zasu yi."

Ta tsinke wayar had'e da mik'ewa.

"Umma bara na tafi. Da azahar wai jirginsu zai sauka.

So nake Ya Noor ya fara cin girkina idan ya iso. Ni da kaina zan masa abin da yake so. Dama ya min text na favorite d'insa (abincin da ya fi so)"

"To shi ke nan Amrah. Allah Ya miki albarka ya sa a fita lafiya a dawo lafiya."

"Amin, Ummana." Ta furta had'e da fita tana murmushi.

Ko da ta isa ta samu Hajiya Suhaila sai ujila take, bata can bata can ana ta aikin tarbar bak'i.

Ashe wai har da Nadrah babbar yayarsu da yake gidanta zasu zo. Saddiqa ma tana kan hanya ita da yaranta, Islam kuma tana da theatre k'arfe sha biyu, hakan ya sa ta shirya ta bar gidan da wuri.

Haka sukaita aiki har sha biyu da rabi sannan Hajiya Suhaila ta ce ta bar sauran aikin ga mai aikinta Safina, zasu tafi Airpot ne dan ta san suna daf da isowa.

Wani wankan ta sake yi, sannan ta saka wata doguwar rigarta kalar baby pink, wadda aka k'awata da adon duwatsu hot pink.

Gyalen rigar ta yafe wanda shi ma kalarsa hot pink ce. Asalin rigar ma Hajiya Suhaila ce ta siyo mata ita daga Umra da ta je.

'Karfe d'aya da rabi ta masu a Airpot d'in Umaru musa Yaradua. Suna isa suka tarar da Saddiqa da yaranta uku sun isa, saboda dama a can suka yanke sahawarar had'uwa kawai.

A yanda Amrah ke bani labari; sun yi zama kamar na kusan mintina arba'in kafin k'arar jirgi ta dake dodon kunnuwansu.

Har da hawayen murna ta yi, a dai-dai lokacin da jirgin ya sauko k'asa.

Babban farin cikinta, shi ne yau zata ga farin cikin rayuwarta. Zata ga mutum ma fi soyuwa a zuciyarta, wanda ta ta'allak'a rayuwarta da shi. Bata san shi ba, bata tab'a ganinshi ba, tun bayan sanda ta yi wayo, amma a zuciyarta tamkar sun saba ne, wata irin shak'uwa take jin sun yi, a tsawon lokutan da suka d'auka suna waya.

"Mommy sun fara fitowa."

Muryar Saddiqa ce ta dawo da Amrah daga birnin tunanin da ta lula.

Murmushin yak'e ta yi, ganin ta kalli Saddiqa amma ta wurga mata wani matsiyacin kallo.

Bin bayansu ta yi, zuciyarta cike da tunane tunane, na yanda zata ga Hammanta Noor.

Amrah ba yarinya ba ce mai hanzari, komai nata cikin sanyi take yinsa, hakan ya sa suka mata nisa.

Da sauri Salmah ta dawo ta kama mata hannu,

"Aunty ki yi sauri mana. Kin ga har an miki nisa."

Murmushi ta k'irk'iro ha'de da 'kara saurin tafiyarta.

A lokacin da suka isa iyaka, wato daga inda ba za a barsu wucewa ba, har sai sanda matafiyan suka fito da kansu. Dakatawa suka yi, Salmah na k'ok'arin jan Amrah da hira, amma Mamanta Saddiqa ta daka mata tsawa, wanda dolenta ta yi shiru.

Tun daga nesa ta hangoshi, bayanshi goye da bak'ar jika, sai kuma wani babban trolly da ya jawo da hannunsa.

Biye da shi Nadrah ce, sai yaranta twins 'yan mata, wanda a girme sun girmi Amrah.

Kallonsa take tun daga nesa, bata gama gasgata tunaninta ba har sai sanda ya k'ariso inda suke. Fuskarsa yalwace take da annuri, idonshi k'yam a kanta.

"Shi ne..." ta furta a razane, tana nuna shi da yatsa.

"Ko shekaranjiya ba na ganka ba a asibiti? Yaushe ka warke? Yaushe ka daina hawan keken guragu?"

Har a lokacin bata ajje hannunta daga nuna san da take ba._Daga lokacin da yaro mai sickler ya haura ma shekara uku, za a iya ganin idanuwansa suna canzawa, suna rikid'ewa daga ainahin yanda suke. Wasu kuma hak'oransu jajaye ne. Duk iya k'ok'arin na brushing d'in da ake masu, ba zasu tab'a zama farare ba. Wannan duk cikin alamomin sickler ne. Da zarar kuka ga haka, hanzarta kai yaronku asibiti domin a masa awon genotype. Allah Ya kare mu da ahalinmu baki d'aya._


Pinky durling??
*RAZ 2????*
[7/3, 8:40 AM] Princess Amrah???: *??MRAH NAKE SO!* ?


(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi.)

            Na Amrah A Msh
            _(Princess Amrah)_
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


_Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (sickler)_


                          1?2?

Tafiya nake gudu-gudu, sauri-sauri. Baki d'aya hankalina a tashe yake, ban ma san inda nake dosa ba, sai dai kawai na san biye nake da yaran da suka zo fad'in sak'on.

A haka muka isa makarantar, kai tsaye muka nufi ofishin head master tare da yaran.

Amrata na gani kwance tamkar bata numfashi, malamai kusan guda biyar zagaye da ita, wani na tofa mata addu'o'i wasu kuma tagumi suka yi cike da tausayinta.

"Amrah!" Na fad'a a firgice.

"Ku fad'a min dan Allah me ya faru da 'Yata? Me aka mata?"

Na jawo ta na rungume tsam a jikina.

"Wallahi idan har yarinyata ta mutu ba zan tab'a yafe wa hukumar makarantar nan ba.

Tun lokacin da za a saka ta sai da muka zo nan tare da mahaifinta, ya maku bayanin lalurinta, gashi a k'arshe kun kasa kare min yarinya.

Wallahi matuk'ar ta mutu sai na yi shari'a da hukumar makarantar, in ya so sai ku fitar da ko ma wane malami ne ya mata wannan dukan."

Kuka sosai nake, ina sake dubar jikinta da aka farfasa da bulala, har a lokacin jini bai daina kwarara ba.

Wannan yarinyar 'yar zak'al ce ta ce,

"Kuma wallahi Mama ba fa ita ce ta yi laifin ba. Amrah babu ruwanta da kowa, bata fitina, ko fad'a ta ga ana yi a cikin ajinmu ma fita take.

Sai da ta rantse ma Mallam Mu'ammar cewa ba ita ce ya aika ba, amma ya ce wai ita ya aika ta d'auko masa red pen d'insa a staff room, gashi kuma bai ga sabon littafinsa ba, wai ita ce ta sace.

Duka 'yan ajin sai da muka bata shaida, amma bai yarda ba, sai da ya mata wannan wawan dukan."

Kai kawai na gya'da, hankalina a tashe na sab'e ta had'e da mik'ewa.

Ban san ma ya zan yi ba, kasantuwar ban fito da ko sisi ba tsabar tashin hankali.

Wani Malami wanda na tarar yana mata addu'a ne ya ce,

"Mu je na kai ku asibiti a mashin."

Ban musa masa ba, dan bani da wani zab'i da ya wuce na bi sa d'in.

Head master'n ne ya zaro dubu d'aya daga aljihunsa,

"Mallam Hafeez ga wannan, ko da za a buk'aci kud'i."

Ya juyo gare ni,

"Dan Allah Hajiya a yi hak'uri, an yi kuskure wanda k'addara ce kuma ta rigayi fata.

Insha Allahu hakan ba zata sake faruwa ba. Fatanmu dai yanzu ta farfad'o, sannan duk maganar da za a yi a yi."

Ko kallonsa ban yi ba kawai na fice, da sauri malamin da aka kira da Mallam Hafeez ya biyo bayana.

Bakin mashin d'insa ya isa, ya fiddo sannan na hau ina rungume da Amrah.

Tambayata ya yi asibitin da muke kaita na fad"a masa, hakan ya sa kai tsaye muka doshi can d'in.

Muna isa risafshan da sauri na k'arisa inda medical recoarder yake, tsabar yawan zuwa asibiti har ma na hardace lambar katinta, babu b'ata lokaci ya fiddo fayil d'inta.

Ganin tana unconcious ya sa ko tsayawa bin layi bamu yi ba, kai tsaye aka shigar da fayil d'in nata muka shiga wurin likita.

Dr. Rabi'atu ce yau muka tarar, ganinmu ya sa ta zare glasses d'inta cike da tausayi ta ce,

"Amrah jikin dai?"

Ta karb'e ta daga hannuna.

"Ehh..." kawai na fad'a ina son ci gaba da magana amma tashin hankali bai bar ni ba, sai faman kuka nake tamkar yau ne ta fara yin ciwon.

Da k'yar na iya jawo magana daga k'asan mak'oshina, na ce,

"Dr. Tun da yarinyar nan take ciwo bata tab'a irin wannan ba. Duk irin sumar da zata yi bata wuce minti biyar ko goma ta farfad'o.

Amma ki ga wannan, tun d'azu take a haka, ga jikinta ya yi zafi rau kamar garwashi."

Kuka ya sake cin k'arfina.

Ajiyar zuciya Dr. Rabiatu ta sauke,

"To yi hak'uri Maman Amrah, daina kukan mana. Insha Allahu zata samu sau'ki.

Amma me aka mata ne har haka?"

"K'awayenta ne suka zo har gida suka shaida min, wai wani malami ne ya dake ta." Na bata amsa ina mai k'ok'arin had'iyar sabon hawayen da ya fito min.

"Subhanallahi! Dama kuwa akwai irin wannan malaman, wanda basu da tausayi ko kad'an.

Banda abinshi, ina abun duka ga wannan 'yar halittar?

Idan ma dukan ne, ai sai ya san kalar wanda zai mata.

Amma ki ga fa, har yanzu jini bai tsaya ba."

Ta hau dudduba ta.

"Ina ga kaman dole sai ku kwanta fa, ko da kwana d'aya ne ta yi sannan. Tana da bu'katar kula sosai a nan kafin ku koma gida."

Mik'o min ita ta yi, sannan ta rubuta wata allura ta bani,

"Ki karb'o wannan allurar yanzu a famasi, sai na mata ita kafin komai."

Mik'ewa na yi a hanzarce, na nufi d'akin magani da takardar.

Su kansu sun san ni, sun san cewa a kyauta muke karb'ar duk wani maganinta ko kuma allura.

Bani allurar suka yi da sauri na koma wurinta.

Bayan ta karb'a, ta had'a ta sannan ta sa na kwantar da Amrah a bisa gadon da take duba marasa lafiya.

Allurar ta mata, wanda sai a lokacin na d'an samu kwanciyar hankali, ganin yanda ta d'an zabura a lokacin da allurar ta shiga cikin fatarta.

Bayan ta gama ta jefa allurar a cikin dustbin, sannan ta dawo mazauninta.

"Ki je nurses station ki kira min duk Sister d'in da kika had'u da ita." Ta ce da ni. "Daga nan ki kira min patient na gaba."

Fitar kuwa na yi, bayan na turo mata nurse ne ta umurce ta da a kaimu d'akin irin na mutum d'aya d'in nan (amenity) sannan ta dawo ta kar'bi sauran magungunan da ta rubuta ta karb'o a pharmacy, idan ta farfad'o sai a bata su.

Ina fita na ci karo da Mallam Hafeez, ya tambaye ni halin da ake ciki na shaida masa, sannan na bi bayan nurse d'in.

Bai tsaya ba shi ma d"in binmu ya yi a baya, kwantar da ita ta yi sannan ta tafi ta bar mu a wurin ni da Mallam Hafeez.

"Alfarma guda tal nake nema a wurinka Mallam Hafeez." Na furta ina mai dubansa.

"To Maman Amrah." Ya fad'a had'e da matsowa bakin gadon.

"Dan Allah wurin k'wadagon mahaifinta zan kwatanta maka, ka taimaka ka shaida masa halin da muke ciki."

Na kwatanta masa inda Mallam yake gyaran babur a k'ark"ashin wani bayerabe.

Dubu d'ayar da Head mastet ya bashi ce ya zaro ya bani, sanann ya tafi.

Bayan tafiyar Mallam Hafeez ba da jimawa sosai ba Amrah ta tashi, hawaye duk ya bushe a kumatunta.

Da hanzari na isa gare ta, bin ta nake da kallo har sanda na k'arisa dai-dai gadon da take kwance.

Ganina da ta yi cikin yanayin damuwa da kuma tausayinta ya sa ta sakar min murmushi,

"Ummah..." ta k'o'karta fad'i annuri bai kau daga fuskarta ba.

Duk da na san cewa 'karfin hali ne irin na Amrah, a rayuwarta ko kad'an bata so ta ganmu cikin damuwa, ba wai mu iyayenta kad'ai ba, kowa ma.

 A haka ni ma na sakar mata murmushin wanda iyakarsa bisa fuskaka kawai ina kallonta.

"Sannu Amrah." Na fad'a cike da tausayi.

"Yauwa...Ummah, k'ashin bayana ciwo kamar zai tsage." Ta fad'a tana k'ok'arin kai d'ayan hannun da ba a lik'a mata drip ba a bayan.

"Dama dole zai miki ciwo ai. Ki kwantar da hankalinki, zan kira Nurse yanzu zata baki kulawa sosai. Insha Allahu yanzu zai daina yi miki ciwon."

Na kama hanyar nurses station.

"Sister ta farka...ina nufin Amrah Abdallah, mai sickle cell."

Da hanzari ta tashi tsaye, wani kwando ne wanda already ta had'a medications d'in Amrah baki d"aya. Na yi gaba ta biyo ni a baya.

"Ki samo mata ruwa tukuna, wanda zata sha maganin da shi."

"To Sister." Na fad'a ha'de da nufar wajen asibitin.

Da kud'in da Mallam Hafeez ya bani na siyo mata ruwa da lemo, sai kuma biskit.

Bayan na iso, zaune na same ta, Sister kuma tana b'ab'ballo mata magnungunanta, tana d'orawa a wata container wacce suke saka magungunansu a ciki.

"Umma yanzu ya bar wurin nan..." ta fad'a cike da mamaki tana nuna k'ofa.

"Umma baki had'u da shi ba?"

Bayan na k'ariso ciki na tambaye ta,

"Wa ke nan?"

Had'e da d'ora robar ruwan sona a bisa teburin ajiye-ajiye.

"Umma, Ya Noor mana." Ta furta cike da yak'ini.

Gyad'a kai kawai na yi, dan a tunanina ko zafin ciwo ne kawai ya sa ta fad'in hakan.

"Umma wallahi da gaske nake. Sister dan Allah ba yanzu wani gurgu ya bar nan ba?"

Kai sister'n ta gyad'a alamar ehh.

"Na san ke ma kun had'u a dai-dai shigowarki sai dai ko baki ga fuskarsa ba ne.

Amma wallahi Umma shi ne nake gani. Na fad'a maku ke da Abba kun k'i yarda.

In dai wannan wanda kuka nuna min a hoto shi ne Annur, to tabbas shi ne yake kai da kawowa a cikin asibitin nan."

Kai na dafe cike da mamaki, tabbas na ha'du da wani a cikin keken guragu, sai dai kuma ban tsaya na kalli fuskarsa ba bare na tabbatar da gaske ne ko akasin haka.

Zama na yi ba tare da na sake furta komai ba, sai binta da kallo kawai da nake tana dafe da bayanta, amma hakan bai hana ta k'ok'arin tabbatar min da gaskiyarta ba.

"Maman Amrah, sai a kula sosai da magungunan nan. Sannan kuma a kula kar ta yawaita motsawa har sai sanda allurar nan ta sake ta sosai.

Ko fitsari zata yi gwara ki fita waje ki siyo mata fo, dan yawaita motsawar kanshi zai iya lalata mata treatment.

Sannan kuma sai kin yawaita tab'a jikinta, idan kika ji zazza'bin yana yawiata sauko mata sai ki kirani,

Ina jin dole za a mata awon jini dan tabbatar da ya k'one ko bai k'one ba?

Sannan a san madosa."

"To insha Allahu zan kula Sister. Na gode Allah Ya saka da alkhairi."

"Ameen maman Amrah. Allah Ya bata lafiya."

Daga nan ta fita ta bar mu.

Tana fita sai ga Mallam Hafeez a gaba, sai Mallam biye da shi, hankalinshi a tashe.

"Amrah 'yata me ya same ki?" Ya furta cike da damuwa, yana k'ok'arin isowa bakin gadon da take kwance.

"Sannu kin ji? Ashe ciwo ya tashi, Allah Ya kyauta ya tsare gaba."

"Ameen Ya Allahu." Mallam Hafeez ya furta.

Sai a lokacin ma na tuna da ba a mata treatment na raunin da aka mata wurin bulala ba.

Da hanzari na ce,

"Mallam ina zuwa." Na nufi wurin Sister.

Bayan na fad'a mata dalilin zuwana ta ce,

"Ehh ina sane da shi ai, small injury ne ba abun a damu sosai ba.

Gwara a bar mata shi a bud'e ya sha iska,

Dan kar a je a tab'a k'ila k'ashin wurin bashi da wani k'wari sosai. Wurin gyaran gira a rasa ido."

Na gamsu da maganarta sosai, hakan ya sa kawai na mata godiya had'e da tafiya._Yawan zazzab'i mai zafi wanda baya sauka, yana d'aya daga cikin alamomin sickler. Lura da kyau, mu zama masu kula da ciwukan da yaranmu ke yi, kar mu zama masu sake, har ciwo ya fara yi masu yawa. Allah Ya bada lafiya._


Pinky durling??
*RAZ 2????*
[7/3, 8:41 AM] Princess Amrah???: *??MRAH NAKE SO!* ?


(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi.)

            Na Amrah A Msh
            _(Princess Amrah)_
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


_Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (sickler)_


                          1?4?

_Sakon gaisuwa bad'e da jinjina ga *ANEESA ABUBAKAR RIMI (ANEELURV)* You are indeed a nice person to me, and to everyone. May Allah continue to bless you. Allah Ya barki da Oga._

***

Ba wai Annur kad'ai ba, ita kanta Hajia Suhaila sai da ta yi mamaki, mamakin kalaman  da ta ji suna fitowa daga bakin Amrah.

Kamar butum butumi Annur ya koma, bai d'auke kallonshi daga gare ta ba, bai daina mata kallon yaushe rabo ba, sai dai tabbas yana matu'kar al'ajabin furucin da ke fita a tsakanin lab'banta.

"Baki da hankali ne da zaki danganta Annur da wani gurgu?

To ta Allah ba taki ba! Bakinki ya sari d'anyen kashi.

Insha Allahu har abada Annur ba zai ta'ba zama gurgu ba.

Sai dai ki ga gurgunta a ta b'arahinki."

Hajiya Suhaila ce ta dakatar da ita da fad'in,

"Ya isa haka, Saddiqa! Wai sai yaushe ne zaki fara sanin darajar d'an Adam?

Sai yaushe ne zaki san irin darajar da Amrah take da shi a zuciyata?

Idan ma baki sani ba to yau ki sani, banbancinki da Amrah a zuciyata ba wani mai yawa ba ne.

Ina nata son da nake wa kaina irinsa.

Saboda haka, matuk'ar kina son farin cikina, to ya zama dole ki so abin da nake so. Ki so Amrah tamkar yanda zaki so Islam. Saboda wata rana ita ma ina sa ran zata dawo cikin zuri'armu."

Lokaci d'aya ya yi gaggawar sauke idanuwansa daga nata, ya fara k'ok'arin kawar da tunanin da yake.

"Barkanku da isowa." Hajiya Subaila ta furta, had'e da rungumar jikokinta 'yan biyu, masu kama iri d'aya.

Nadrah ce ta kalli Amrah had'e da sakar mata kakkausan murmushi ta ce,

"I guess, ke ce Amrah, right?"

Murmushin da Amrah ta yi ne ya tabbatar mata da hasashenta.

"Ai ko ba a fad'a min ba dama na san ke ce. Saboda yanda na karanci fuskarki da ta Noor a lokacin da muka k'ariso. Mu isa gida ko?"

Murmushi kawai Amrah ke yi ba tare da ta furta komai ba.

Duk irin mararin da take na ganin Hammanta, amma ta kasa yi masa magana. Kunyarsa take jin tana ratsa ko wace gab'a ta jikinta.

Kasantuwar dama da prado suka zo, hakan ya sa ta kwashe su su duka, in banda Saddiqa da suka tafi cikin motarsu ita da yaranta, banda Salmah da ta nace sai inda Amrah take zata bi.

Sai kusan la'asar sannan suka iso, take gida ya kaure da murna, yau dai family'n Iqra Al-Hussein sun yi had'uwar da suka jima basu yi irinta ba.

Sun samu har Islam ma ta dawo, a yamutse ta fito babban falon da aka k'awata da wasu manyan takardu da aka rubuta
*WELCOME BACK YAYA NOOR!* Wanda ba wata ta yi wannan aikin ba face Amrah, dama ta riga ta gama komai, sanda zasu fita ta bar ma Safina cewa ta bi ko ina ta lilli'ka mata takardun.

Haka aka yi zaman cin abinci, murna fal a fuskokinsu, sab'anin Islam da tun da ta ma Amrah kallo d'aya bata sake had'a ido da ita ba, tsabar tsananta da ta yi.

Haka yammacin ranar ta kasancewa wannan ahali, farin ciki sosai da nisha'di, wanda zan iya cewa Annur da Amrah sun fi kowa jin dad'in wannan yanayi.

Daf da magrib Amrah ta d'auko jikar kayanta cewa zata tafi gida, saboda wata tarbiyya da ta samu, a duk inda take, matu'kar magrib ta kunno kai to hankalinta na karkatowa zuwa gida.

"Momy ni zan tafi. Na gode 'kwarai." Ta furta a tsanake. Cikin magabarta dalla-dalla kamar 'yar koyo.

Salma ta taso da sauri ta rungume ta,

"Aunty dama ba a nan zaki kwana ba? Dan Allah mana ki kwana, wallahi zan miki fira mai dad'i."

Murmushi Amrah ta mata,

"Na baro Ummana da kewana ne. Insha Allahu gobe da na dawo daga School zan zo." Ta dafa kanta.

D'aya daga cikin 'yan biyun Nadrah mai suna Janan ce ta taso ita ma da murmushi a saman fuskarta ta ce,

"Aikam dai Amrah da kin tsaya kin kwana. Zan rakaki yanzu ki tambayo Maman taki pls. I need you by my side. Kina burge ni saboda son da Uncle Noor yake miki."

Ajiyar zuciya ta sauke, tana k'ok'arin yin magana ne ta ji 'yar uwarta mai suna Hanan ta ce,

"Abeg let her go, Janan. Ke shisshihinki ke had'a ni da ke."

"Ehh d'in miye ruwanki?"

"Ya isa haka ni dai. Ku barta ta tafi yamma na mata. Bata da wadatacciyar lafiya ne kuma ga sanyi sanyin yamma na saukowa.

Amrah sannu da k'ok'ari, mun gode k'warai. Ki gaishe da Umman taki."

"To zata ji k'warai Momy. Sai da safe."

Mik'ewa Annur ya yi ya ce,

"Momy bara na raka ta, daga nan ma sai mu gaisa da Umma."

Kallonsa Amrah ta yi da murmushi, mai cike da soyayya ta ce,

"Allah Yaa Noor da ma ka barshi, ka zauna ka huce gajiya kawai. Gobe ba sai ka je ba?"

"An k'i a bari d'in. Wato ke kad'ai zaki ganta ni ba zan ganta ba ko? Sai na je." Ya bi bayanta.

Su Islam tamkar zasu fashe tsabar takaici, su dai sun tsani Amrah babu dalili. Ko kuwa dai kasantuwarta 'yar talakawa ce ya sa suka tsane ta? Allah masani.

Dai-dai ana kiran magrib suka iso, a lokacin ina d'ibarwa mallam ruwan alwala, wanda dawowarsa gidan ke nan.

Baki sake, fuska d'auke da murmushi nake kallonshi, kallon yanda ya koma a zahirinsa, ya zama cikakken mutum, tamkar wanda ba d'an shekara ashirin da biyar ba.

Shi d'in ma murmushi k'unshe a saman fuskrsa ya k'ariso ciki, har k'asa ya du'ka ya gaishe ni.

"Sannu Umma. Ina wuni?"

"Lafiya k'alau Annur. An dawo lafiya ko?"

Na fa'da har a lokacin fuskata bata daina murmushi ba.

"Alhamdulillahi Umma. Mun same ku lafiya"

Ya furta had'e da tashi ya isa inda mallam yake zaune, shi kad'ai sai kallon Annur yake yana murmushi.

 "Lafiya lau fa."

Na bashi amsa.

Gaisawa suka yi da Mallam sannan ya mik'e.

"Bara na koma. A gajiye nake lis wallahi. Kuma akwai wani aiki da nake son yi a cikin daren nan."

A tare ni da Mallam muka furta "To Allah Ya hutar da gajiya."

Har k'ofar gida Amrah ta raka shi sannan ta dawo.

A ranar da suka cike kwana biyu da zuwa ne sai ga Annur da Janan sai kuma Salmah sun zo a cikin mota.

Jaye suke da wani babban akwati, wanda na rasa gane ko na menene.

Janan ce ta furta "Wannan tsarabar Amrah ce, daga Uncle Noor."

"To fa!" Na furta had'e da mayar da kallona ga Annur.

Tun ban fad'i komai ba ya gaggauta fita daga gidan.

"Wai duk Amrah kad'ai? Lallai a gaishe da Annur. Allah ya saka masa da alkhairi."

"Ameen Umma." Janan ta furta had'e da mik'ewa.

"Ban ga Aunty ba." Salmah ta fad'a tana wawware ido.

"Wai Amrah? Bata dawo daga makaranta ba." Na bata amsa.

"To idan ta zo a gaishe ta please."

Har k'ofar gida na raka su, na ma Annur godiya sosai sannan na dawo gida.

Bayan azahar ta dawo, a lokacin muka bud'e kayan muka hau duddubawa.

Kaya ne masu kyau, k'ananan kaya da kuma material irin na manyan yara. Takalma da jaka saiti biyu.

A take na sa ta ta kira Annur ta masa f
Godiya, na kuma shaida mata cewa ta fad'a masa, zamu zo har gida mu yi godiya.

Tun bayan dawowar Annur, rayuwa mai cike da k'aunar juna ta 'kara bun'kasa a zuciyoyinsu.

Soyayya suke mai cike da tsafta, wadda su kansu basu san cewa soyayya ba ce, sai dai kuma duk wanda ke tare da su, dole zai fahimci hakan.

Gashi dai k'aramin yaro, mai k'ananan shekaru, amma ya zama d'aya daga cikin manya manyan masu zane, wanda sunansu ya kewaye k'asar Nigeria.

Yau ta kasance ranar lahadi, wadda a yau ne za a gudanar da walimar saukar Al_Qu'ani mai girma ga su Amrah. Wanda suka samu nasarar haddace wa baki d'aya. Su biyar ne kuma kacal za a yi ma wa.

Wannan walimar babba ce sosai,  wadda tana d'aya daga cikin walimu manya da za a gudanar a jihar Katsina.

Akwai manya manyan ba'ki wanda zasu halarci wannan walima, ciki kuwa har da gwamnan jihar, da wasu daga cikin masu fad'a a ji dake jihar.

Bakin Amrah bud'e yake, saboda kusan in ce ta kai shekara d'aya tana shirin tarar walimar, ta jima tana shirye shiryen yanda walimar zata kasnace.

Cikin jerin mutanen, Annur ne zaune cikin wata farar shadda, d'inkin babbar riga wanda ya amsa sunansa.

Bakinsa a bud'e yake, yana mai bibiyar  duk wani motsi na Amrah, har a lokacin da aka fara gabatar da walimar.

_Kar mu yawaita dukan yaranmu masu sickler, saboda ita d'in cuta ce wacce take bin duk wasu k'asusuwa na jiki, take rage masu armashi, take neman dagula al'amurransu. Matuk'ar muka daki yaronmu, k'ashinsa zai iya samun matsala, wanda a k'arshe za a dawo ana regretting. Mu kula da kyau, sai mu san hanyar da zamu bi wurin horonsu._

A yi hakuri da ni, an mana ruwan sama ne wanda ya guyara mana wutarmu, abin dai sai hamdala.


Pinky durling??
*RAZ 2*
[7/3, 8:41 AM] Princess Amrah???: *??MRAH NAKE SO!* ?


(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi.)

            Na Amrah A Msh
            _(Princess Amrah)_
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


_Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (sickler)_


                          1?5?

Bayan gabatarwa da aka saurara daga shugaban makaranta, sai sauraran karatun littafi mai tsarki daga d'alibai.

Amrah ce ta k'arshe, inda ta karanto wasiyyoyi da Allah mad'aukakin sarki Ya lissafo a cikin suratul an-am.

K'ira'a ce mai matuk'ar da'di, tamkar d"iyar larabawa haka take rero karatunta.

Bayan ta gama ne ta koma mazauninta, inda aka tanadar domin zaman mutum biyar d'in da suka hardace littafi mai tsarki.

Daga nan sai da wasu d'alibai suka fito suka rero 'yan wa'kok'i irin na larabawan nan masu matuk'ar dad'i, sannan ne aka kira Amrah, in da zata kira d'alibanta domin gabatar sa dirmar da ta shirya masu.

Babban abin burgewa a cikin wannan dirama shi ne; yanda yaran suke k'ananan yara, duk cikinsu babu wacce zata haura ma shekara bakwai a duniya.

Bayan sun kammala da harshen larabci ne, Amrah ta kar'bi loud speaker domin yin bayanin abubuwan da dramar ta k'unsa da harshen hausa.

"Kamar yanda muka gani, yara ne biyu a matsayin ma'aikatan asibiti, sai kuma yarinya d'aya wacce ita ce matsayin marar lafiya, ga kuma mutum biyu a matsayin uwa da uba.

Mun ga yanda aka nunar da ciwo yake addabarta, har wani lolacin take fita daga hayyacinta.

Kwatsam wata rana ciwon ya tasar mata, aka kai ta asibiti domin bata taimakon gaugawa.

Likitar farko ta nunar ma iyayen yarinyar cewa ai wannan yarinyar su ma cire rai da ita kawai, domin kuwa tata ta zo k'arshe. Wannan ciwon nata ba na tashi ba ne. Su koma gida da ita kawai su jira lokacin mutuwarta.

A wurin gardama ta b'arke tsakanin iyayen nata, yayin da mahaifiyarta mace ta kafe a kan bata yarda da maganar likitan ba, domin kuwa babu wanda ya san gaibu sai Allah. Sannan kuma ita cuta ba mutuwa ba ce.

Mahaifinta kuma ya kafe cewa lallai sai dai su koma gida, saboda shi d'in dama ya gaji da kashe mata kud'i a banza kullum ciwo sai ta'azzara kawai yake.

Likitar ganin cece-kuce d'insu ya dame ta ya sa ta kore su daga ofishinta.

Gida suka wuce kai tsaye, har a lokacin mahaifiyar yarinyar bata cire tsammani ba.

Washe gari ta d'auke ta ta kai ta wata asibitin, inda suka tarar da d'ayar likitar can.

Ta mata bayanin lalurin yarinyar, take ta gamsu da bayaninta.

"Babu komai, ki kwantar da hankalinki, insha Allahu zata samu lafiya. ita cuta ai ba mutuwa ba ce, abin da nake so da ke dai kawai ki dage da yi ma 'yarki addu'a. Na miki alk'awarin kula da ita tamkar yanda zan kula da 'yata da na haifa da cikina."

Sosai mahaifiyar yarinyar ta ji da'di.

Haka wannan likitar ta ringa kula da yarinyar kamar yanda ta yi alk'awari. A k'arshe yarinyar ta tashi da k'afafuwanta, ta warke tas kamar bata tab'a yin ciwo ba.

Sai ga yarinyar da taimakon mahaifinta, ta zama rufin asirinsa, ta zama abar alfaharinsa a k'arshe.

Idan zamu auna wannan diramar, mu mata karatun ta natsu, zamu ga akwai tarin darussa a cikinta. Akwai abubuwan koyo da dama a cikinta.

Mun ga yanda likitar farko ta yanke k'auna daga rahamar mahalicci, bayan kuma Allah mad'aukakin sarki maji rok'on bayinSa ne.

Mun ga yanda likitar ta nuna masu tamkar ta san gaibu ne, bayan kuma La ya'lamul-gaibu illallah.

Daga cikin darussan wannan diramar, mun tabbatar cewa duk inda ake ba duka ake taruwa a zama d'aya ba.

Kamar yanda likitar farko ta kore su, sai gashi Allah ya had'a su da ta kirki. Ke nan dai kar mu zama masu yin jam'i ga komai, domin kuwa komai za a iya samun banbanci.

Mun 'karu da ilimin lallai cuta ba mutuwa ba ce, ganin mutum yana fama da ciwo, ba shi ba ne zai sa a yanke k'auna, domin kuwa Allah'n da Ya bashi ciwon, zai iya kawo masa sau'ki a ko wane lokaci. Sannan kuma kafin a saukar da cuta, sai da aka saukar da maganinta.

Duk irin ciwon da mutum yake fama da shi, kar ya zama mai gajen ha'kuri ga mahaliccinsa, ba wai rashin so ba ne ya sa ya d'ora masa cutar, a'a, yana neman ya k'ara kusanci gare Shi ne.

Yanzu idan muka d'auki wani misali; zamu ga so tari mutum yana fama da ciwo, a lokacin da yake ciwon, yana yawaita ambaton Allah, sallah a lokacinsa baya wuce sa. Ba dan komai ba, sai dan yana gudun kar mutuwarsa ta zo d'aukarsa bai gyara tsakaninsa da mahaliccinsa ba.

Amma idan zamu d'auko sanda baya ciwon, wata k'ila yana kwanaki bai yi zikiri ba, ita kanta sallar k'ila kullum sai lokacinta ya wuce yake yinta.

Ke nan wannan jarrabtar da Allah Ya d'ora masa na ciwo, ya k'ara kusanci a tsakaninsu.

Ina fatan wannan 'yar tak'aitacciyar dramar zata zama gyara a rayuwar mutane da dama wanda suka halarci wannan walima da ma wanda zasu kalla a gidajen talabijin.

Duk wanda suka zo wannan wuri, Allah Ya albarkaci rayuwarsa, Allah Ya biya masa duk kanin buk'atunsa na alkhairi.

Mun gode k'warai da gaske."

A lokacon da Amrah ta koma mazauninta, na ga da dama daga cikin mutane wasu na kuka sosai, wasu na share hawaye, wasu kuwa kallo guda zaka masu ka tabbatar lallai  jikinsu ya yi sanyi k'warai da ainun.

Babban abin da ya fi tab'a min zuciya a kan bayananta shi ne; nata lalurin, yanda take fama da nata cutar a ko wane lokaci, amma a hakan ta gode wa Allah, har take nunar wa mutane muhimmacin d'aukar k'addara.

A lokacin na k'ara tabbatar da rayuwar Amrah mai kyau ce, kuma abar a yi koyi da ita.

Bayan an gama bayar da kyaututtuka ne aka bu'kace ta da ta fito, gwamnan jihar ya bata kyautar kujerar Makka, sannan da tarin envelopes wanda manyan mutane da dama suka aiko mata da ita. A dalilinta, an ba makarantarsu kyautar naira miliyan d'aya.

Murna sosai ga mutane, Amrah wadda ke jin abun tamkar a mma farki ta kasa furta komai, da gudunta ta isa inda nake, ta min rungumar da ke k'ara shauk'i a tsakaninmu, ina jin yanda bugun zuciyarta ke tafiya dai-dai yanda ake sonshi, hawayen farin ciki basu daina sauka bisa kumatunta ba.

Jin an sake kiran sunanta ya sa ta saurin sakina had'e da mayar da kallonta ga inda loud speaker ke fitowa.

"Ta sake samun kyauta daga wani bawan Allah. Wanda shi ya san lalurinta, ya bada izinin duk sanda ciwon nata ya tashi, kai tsaye ta je asibitin kud'i ta Dr. Dara, ba tare da an caje ta ko sisi ba.

Bawan Allah'n ya buk'aci kar a fad'i sunansa."

Wani kyakkyawan hawaye ne ke sake fita daga k'wayar idonta, saurin isa matakalar ta yi, ta karb'i takardar da aka bata, wacce ita zata zama shaidarta a duk sanda zata je asibitin.

Shugaban makarantar da kanshi ya mik'a mata loud speaker, cewa ta yi kalaman godiya had'e da bankwana, kamar yanda dama can haka aka tsara, ita ce zata yi su.

Da larabci ta ringa zubo bayani, cikin k'warewa tamkar dama can harshenta ne larabcin, bayan ta gama ne kuma ta koma da harshen hausa.

"Kalamai ba zasu iya fad'in iya halin farin cikin da muke ciki ba yau.

Babban abin farin ciki a fa'din duniyar nan, shi ne yau mutum ya wayi garinsa da hardace littafi mai tsarki baki d'ayansa, sannan kuma yake amfani da shi.

Mai girma gwamnan wannan jiha, mai girma wakilin sarki Mukhtar, manyan mutanen da suka halarci wannan taron, iyayenmu, yayyenmu, k'annenmu, a madadin wannan makaranta da d'aliban da ke cikinta, ina mai amfani da wannan dama domin mik'a sak'on godiyarmu. Mun gode k'warai, Alllah Ya saka da alkhairi, Allah kuma ya mayar da kowa gidansa lafiya.

Mu kuma Allah ya bamu ikon amfanar da kanmu da kuma al'ummah abin da muka karanta.

Rabbi Ya sa mai amfani ne a gare mu. Ba wai mun koya, mun hardace kuma mu barshi ya tafi a haka nan ba.

Mu sani cewa, matuk'ar muka sake bamu karantawa, to tabbas zamu neme shi daga kanmu mu rasa.

Na gode."

Ta mik'a sifikar ga shugaban makarantar.

Kabbara aka d'auka da k'arfi, wasu na k'ok'arin tashi domin barin wurin, wasu kuma sun bari har sai an yi addu'a sannan.

Sai bayan an fara watsewa sannan Hajiya Suhaila ta zo, cikin rashin jin dad'i take shaida min abin da ya hana ta zuwa da wuri, Baban su Annur ne zai tafi Abuja, kuma bai tafi da wuri ba.

Tare muka rankaya muka koma gida, ni da ita da k'annena Zulaihat da Fatima a cikin motarta, sai Amrah, da wasu k'awayenta mutum hud'u suka bi motar Annur, wanda murna ta kasa b'oyuwa daga kyakkyawar fuskarsa, yana mai matuk'ar jin dad'in wannan lokacin.

Bayan mun koma gida ne mutane suka ringa zuwa yi mana murna, gida ya cika sosai kamar ana biki ko suna.

D'inkuna kala biyu Hajiya Suhaila ta yi ma Amrah, masu matuk'ar kyau da tsada.

Haka rabar ta kasance mana, farin ciki sosai da murna, shi kanshi Mallam abin ya k'i b'oyuwa, a k'ofar gida aka shimfid'a masa manyan tabarmi shi da 'yan uwa da abokansa.

Bayan wata d'aya.

A lokacin ne shugaban makarantar su Amrah ya zo har gida a kan maganar kujerar Makkarta, wai maganar ta taso, har ma an ce ta zo za a mata passport nan da kwana  biyu.

Sanda maganar ta riskemu a gida, sam! Amrah ta ce ita ba zata je ba. Wai sai dai ni ko mahaifinta wani ya karb'i kujerar, ba zai yiu ita ta je mu kuma bamu je ba.

Daga ni har mahaifinta sam muka k'i kar'bar wannan tayin nata, babu yanda bata yi ba amma muka kartake cewa dole sai ita d'in zata je.

Haka aka zo har gida aka tafi da ita da Mallam, aka yo mata passport na tafiya aikin Hajji. Saboda nan da sati bitu za a fara tafiya.


_Rayuwar nan cike take da k'alubale masu girman gaske. Mafi girman jarrabta shi ne a had'a ka da ciwo. Duk wani talauci mai sau'ki ne idan kana da lafiya. Cutar sickler na d'aya daga cikin manyan cutuka, sai dai kar mu d'auki hakan a matsayin iyakar rayuwarmu ke nan, sau da dama masu lafiyar suna mutuwa su bar masu fama da ciwon. Allah Ya 'kare mu da lafiya, Ya bamu ikon cinye jarabawoyinmu._


Pinky durling??
*RAZ 2*
[7/3, 9:54 PM] Princess Amrah???: *??MRAH NAKE SO!* ?


(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi.)

            Na Amrah A Msh
            _(Princess Amrah)_
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


_Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (sickler)_


                          1?6?

 Shirye-shiryen tafiyar su Amrah ya kankama sosai, har a makaranta ta yi bankwana.

Sai dai kuma abin da yake ci min tuwo a akushi, sanin lalurin Amrah da na yi, tana da buk'atar mataimaki a aikin Hajji da zata yi.

Yarinya mai yawan ciwo, bai kamata ta yi tafiyar d'in mako biyar ba tare da mai kula da ita ba.

Duk sanda zan mata maganar sai dai kawai ta yi murmushi, ta ce,

"Umma babu komai insha Allahu. kin ga ai na riga da na saba."

"Kayya, Amrah ai shi ciwo baya da sabo. Sai dai addu'a kawai."

Ranar da ya rage kwana biyar su tashi ne Hajiya Suhaila ta zo, take shaida min wai zata je aikin Hajji ita da Islam, sai dai su d'in ta Abuja zasu tashi, kyauta aka ba mai gidanta kujerar guda d'aya, yanayin aikinsa ya sa ya ce ba zai je ba. Shi ne ya had'a da Islam ita ya biya mata su yi tare.

Duk da ba ta gari d'aya zasu tashi da Amrah ba, si da na samu kaina da kwanciyar hankaali, na ji wani sanyi sanyi a zuciyata.

Shi kan shi Annur ya ji da'di sosai, a ranar ya zo mata bankwana saboda zai je Bauchi gobe, akwai wata University da ya zana, yake son zuwa don ganin yanda aikin ya kasance.

Har da kuka Amrah tayi sanda zasu rabu, ji take tamkar ba zasu sake had'uwa ba.

Canjin riyals ya mata na dubu hamsin, sanin ko ya bata ba zata karb'a ba ya sa ya bani cewa na ajiye mata.

Na masa godiya sosai tare da fatan alkhairi a tafiyarsa.

Haka lokacin tafiya ya yi muka raka ta har Hajj camp, daga can aka mana iyaka da ita, cewa za a fara kwasarsu a marcopolo zuwa Airport.

Tafiyar Amrah ta zame min wani gagarumin abu, kwata-kwata hankalina ya kasa kwanciya, duk da muna waya da ita akai akai, tun daga ranar da suka dira Jidda har yau da zasu bar Birnin Madina, zuwa garin Makka.

Bayan sun isa Makka ma sai da ta kira ni, a lokacin har harami ta je ta dawo.

"Umma yau sai ga ni ga abin da nake gani a kallo, ka'abah. Umma ashe k'atuwa ce ba k'arama ba, amma a kallo sai nake ganinta kamar k'arama."

 A yanayin da ta yi maganar kawai ya isa ya tabbatar da halin farin cikin da take ciki, sosai take nishad'i.

"To Amrah dama ina ta ga zama k'arama? Ki ce sai kika ga muk'ama Ibrahima."

 Na fa'da da fara'a sosai kamar tana a gabana.

"Umma na ga muk'ama Ibrahima, sai dai daga nesa ne ban matsa inda take ba saboda cinkoso. Insha Allahu nan ba da jimawa ba zan matsa har inda take in tab'a da hannuwana."

 Shiru na yi jim, kafin na ce,

"Amma ki kula sosai Amrah. Kin ga ke d'in ba wani girma ne da ke ba, kar a je a matse ki ki gagara numfashin kirki. Ina jin labarin yanda cunkoso yake kashe mutane fa."

 Murmushi ta yi mai sauti kafin ta ce,

"Insha Allahu Umma zan kula sosai. Da yake ma tare muke da Maman Abba, nan d'in ma d'akinmu d'aya da su."

"Allah sarki! Matar kirki ke nan. Na ji da'di sosai da Allah Ya had'a ku, dama tun a Hajj camp d'in nan na fahimci suna da kirki sosai.

To ya maganar su Hajiya suhaila? Kun had'u kuwa?"

"Bamu had'u ba umma. Jiya dai mun yi waya cewa sai gobe zasu zo nan Makka. Kin san su basu je Madina da wuri ba."

"Haka ne." Na furta ina canza salon maganar daga wasa  i zuwa ta kirki sosai,

"Dan Allah Amrah kar ki manta da abin da na saka ki. Ki ma kanki addu'a sosai, Allah Ya yaye miki cutar nan, da dukkan 'yan uwa musulmai."

Ajiyar zuciya ta sauke had'e da fad'in,

 "Insha Allahu zan yi sosai Umma. A Madina ma na yi ai."

Murmushi mai sauti na yi,

"Allah Ya karb'a to. Da duk wata addu'a da ta dace ba sai na fa'da miki ba. Ki gaishe da maman Abban, sai anjima." Na tsinke wayar.

Haka Amrah suka yi ibada sosai, kamar yanda nake ji daga Maman Abba a duk lokacin da muka gaisa da ita, tana yawaita fad'a min,

"Gaskiya Maman Amrah kin yi sa'ar 'ya, mai hankali, tarbiyya da kuma ilimin addini.

So tari idan wani abu ya shige min duhu, ita take tunasar da ni, da duk sauran 'yan d'akin ma.

Bata wasa da zuwa masallaci, duk irin laziness d'in da nake ji a kan zuwa masallaci, ita zata kwantar da kalamanta, ta sanyaya min jiki, wanda dole sai na je masallacin.

Baccinta k'alilan ne, tana raba darenta da nau'ukan ibadu, wanda ko a cikin manyan mata da suka gama mallakar ilahirin hankulansu, ba lallai a samu kamarta ba.

Na matuk'ar jin dad'in shigowarta duniyata, ta gyara min kurakuraina cikin hikima da fasaha, yanda ba zan tab'a jin haushinta ba. Ta tunatar da ni abubuwa da dama, wanda ba llallai ba ne na tuna su a duniyata.

Ina mai k'ara jaddada miki maman Amrah, ki k'ara gode wa Allah da kyautar Amrah da Ya baki."

 A dai-dai lokacin da ta kai aya a zancenta, na murmusa cike da jin dad'in kalamanta, had'e da furucin,

"Alhamdulillah." A tak'aice.

Jin Amrah ta karb'i wayar ya sa na ce,

"Sai anjima Amrata, a yi ibada sosai."

"Insha Allahu, Ummah. 'Yan jirgi na farko ma har an saka su yin d'awafin bankwana."

"To madallah. Sai anjima."

Cike da jin dad'in kalaman Maman Abba na ajiye wayar bisa kujera. Ni kad'ai ke sakar ma kaina murmushi. Ko da maman Abba bata fad'i ba, na sani, na san cewa na yi sa'ar 'ya, abar alfahari, wacce zata iya rayuwa a duk duniyar da zata tsinci kanta, ko da ni ko babu ni.

Murmushi bai fice daga fuskata ba na ji salllamar Annur, amsa masa na yi da murmushin da ban kawar da shi ba.

"Maraba da Annur."

Na furta had'e da mik'ewa na bashi wurin zama.

Bayan mun gaisa ne yake shaida min jiya ya dawo daga Abuja, maganar sabon ginin da zai ma kamfanin magani na dana, sabon reshen da zasu bud'e a garin Minna.

Fatan alkhairi na masa, sannan ya zaro kud'i naira dubu goma ya ajje min,

"Annur baka gajiya ne wai? Wasu lokutan har kunyarka nake ji, wasu lokutan na kan ji ina ma zaka duba zuciyata ka ga yanda nake ji a duk sanda zaka yi min kyauta? Na so dai a ce abin ya tsaya a tsakanin kai da Amrah kawai."

"Bana son jin haka daga bakinki Umma. Ko kin manta cewa ni ma d'anki ne kamar Amrah? A ganina, duk abin da zan iya yi ma Momy ba tare da haufin komai ba, haka zan miki shi ba tare da wani abu ba.

Please and please Umma, ki d'aukeni tamkar yanda na da'uke ki, ki bani matsayi kamar yanda na baki. Ki daina k'o'karin dakatar da ni daga kyautata miki."

Sai a sannan ya dakata da maganarsa, yana mai duk'ar da kansa k'asa.

Ajiyar zuciya na sauke,

"Haka ne Annur. Kar ka tab'a tunanin akwai wani banbanci a tsakaninka da  Amrah. Yanda take tawa haka kaima kake nawa. Allah ya maka albarka ya taimake ka a kan duk k'udururrukanka na alkhairi."

"Har na ji dad'i Umma. Bara in tashi. Su momy ma gobe muke tsammanin dawowarsu."

cikin Mamaki na ce,

"Tun da wuri haka? In ce ko su Amrah sun riga su tafiya?"

Bayan ya mik'e tsaye ya ce,

"Sun riga su kam. Kin san yanayin tafiyar tasu ba d'aya ba. Su ta can b'angaren tuni aka fara kwasar Alhazai, tun sallah da kwana hud'u."

Mi'kewar na yi ni ma na ce,

"Allah Ya dawo mana da su lafiya. Sai anjima."

Bayan kamar sati d'aya su Amrah suka dawo, sosai na yi mamakin yanda ta koma, ta yi b'ul-b'ul gwanin sha'awa kamar ba ita ba. Ta yi kyau matu'ka, ciwo kuma dama tun da ta je sau d'aya kawai ya taso mata, kuma Hajiya suhaila da Maman abba suka kai ta Saudi German, inda aka bata treatment mai kyau, suka kula da ita, suka killace ta har sai da suka ga ta murmure kamar ba ita ba.

Har da hak'orin Makka na zinari ta saka, wanda ya haskaka hak'oranta, ta sake cika sosai.

Sosai Annur ya yi farin cikin ganinta, wanda a ranar da ta dawo ya d'ora idanuwansa a nata, ya shiga wani irin hali mai wuyar fassara, duk irin dod'ad'diyar k'walwar mutum dole ya fahimci halin da suke ciki, dole a ga tsantsar kewar ganin fuskokin junansu da suka yi, na tsawon kwanaki talatin da takwas.

A cikin wannan rana ne Annur ya furta mata kalmar *"I LOVE YOU AMRAH."* Kalmar da bata tab'a shiga tsakaninsu ba tun da suke, saboda ita Amrah har a lokacin gani take kamar ba son soyayya take ma Annur ba, kamar sha'kuwa ce kawai a tsakaninsu. Sai dai kuma jin kalmar da ta fito a tsakanin lab'bansa, ya sa ta kasa gasgata kanta, take jin wani sabon yanayi a duniyarta.


*Sai yanzu, Annur? Duk iya zamanku da Amrah sai yanzu ka iya furta mata wannan gagarumar kalmar, wadda baka tab'a furta ta ga kowa ba?*

*Masha Allah! Hakan ya yi kyau ai.*

*Ina team Amranoor? Abin da kuka jima kuna tsumayi ko? To yau dai ta faru, sai kwasar rawa ke nan.*

*Wiyara wattpadians? Simply search PrincessAmrah. Vote and comment on each line, I'll be glad if you do so.*


Pinky durling??
*RAZ 2*
[7/4, 2:43 PM] Princess Amrah???: *??MRAH NAKE SO!* ?


(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi.)

            Na Amrah A Msh
            _(Princess Amrah)_
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


_Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (sickler)_


                          1?7?

Tun daga lokacin da soyayya mai 'karfi ta gama shiga tsakaninsu, zuciyata take ciki da farin ciki.

Sosai ciwonta ya yi sauk'i kuma, tun daga sanda suka dawo daga Saudiyya, har yanzu.

Yanzu haka Amrah ta shiga SS2 ne har ma sun kusa shiga 3, Annur kuma ya samu aiki a wani babban kamfanin k'ere-k'eren motoci da ke Birnin Abuja, yana masu aiki ta b'angaren zane-zane.

Hajiya Suhaila kuma ta samu Dady'n su Noor da maganarsa shi da Amrah, bai hana ba, saboda shi dama babban burinsa dai yaransa su ginu bisa tafarki mai kyau, su samu ingantaccen ilimi wanda zasu amfana da shi, kuma ya yi alfahari da su. Kuma Noor d'insa ya samu. Dan haka ba zai hana sa auren duk wacce ransa ke so ba.

A lokacin da ta shiga SS 3 ne aka fara maganar aure, har ma manya sun shiga maganar.

Har a tsawon wannan lokacin Amrah bata daina tunanin mutumin da ta yawaita gani a asibiti cikin keken guragu ba, bata daina mamakin mutumin ba, sau da dama ta kan same ni da maganar,

"Umma na rasa yanda zan yi na cire wancan mutumin daga zuciyata. A duk sanda zan zauna ni ka'dai, ya kan fad'o min a rai. Na rasa ko shi d'in waye, ban tab'a ganin kama irin tasu ba."

"Ba abun tunani ba ne wannan ba Amrah. Kin san a duniyar nan ana kama, akwai wanda kai kanka idan ka kalle shi zaka san kuna kama, kuma a zahirin gaskiya baka had'a komai da shi ba. Dan haka ki daina wannan tunanin. Annur d'inki dai shi ne kawai, kuma insha Allahu shi zaki aura."

 Da kunya ta duk'ar da kanta k'asa, tana wasa da yatsun hannunta.

Kud'in neman auren Amrah kansu dubu d'ari biyu aka kawo, a raina har ina jin kamar sun yi yawa.

Haka kayan saka rana da aka kawo, komai a wadace, katan katan d'in abubuwa haka aka ringa dire su a tsakar gidanmu.

Wata bakwai aka saka auren, wanda ya yi dai-dai da gama makarantarta.

Daga sanda aka kawo kayan saka rana, kafin a raba su sai da ta yi saukar Al-Qur'ani, tana fatan Allah Ya saka albarka a rayuwar da zata tsinci kanta, rayuwar da take yawan tunanin fad'amawa, take jin ina ma a ce a gidansu zata yita zama ko bayan auren. Ko kad'an bata son abin da zai raba ta da gida. Duk sanda zan yi wata tafiya zuwa garinmu, kafin in dawo sai ta yi ciwo, ba wai ciwon sikilarta ba, ciwon rashi na a kusa da ita kawai. Saudiya ma da ta je ashe daga farko sai da ta yi, daga baya ne ta koma dai-dai. To bare kuma yanzu da zata tafi ta bar ni, bari na har abada. Zata fad'a wata sabuwar rayuwar, mai cike da k'alubale.

Ba wai Amrah kad'ai ba, ni ma kaina da na haife ta dan dai aure ya zama dole ne. Har ji nake a raina 'Banda aure ibada ne, me zai sa ka haifi 'yarka, ka raine ta tun tana 'karama, ka so ta, ta so ka, amma rana d'aya wani ya raba ka da ita?'

Hawaye nake ni kad'ai a duk sanda na keb'e, nake irin wannan tunanin.

Ya zan yi da tunanin Amrah bayan barinta gida? Ya zan yi na cire tunaninta daga zuciyata? Wane hali zata ringa shiga a duk lokacin da ciwonta ya taso?

Sauk'in ma d'aya, bani da haufi ko kad'an a rayuwar da zata fad'a. Bana haufin wanda zata yi rayuwa a k'ark'ashinsa. Na tabbata zai kula da ita, tamkar yanda zan kula da ita. Zai nuna mata soyayya, fiye da yanda ni zan nuna mata. Zai bata ingantacciyar rayuwa, fiye da yanda ni zan bata.

Sallamar da Amrah ta yi ce ta dakatar da ni daga duniyar tunanin da na lula,

"Umma, ke kad'ai?" Ta furta had'e da zama kusa da ni.

Murmushi na k'irk'iro had'e da furta,

"Ni kad'ai fa. Ya makarantar?"

"Makaranta lafiya k'alau Umma. Yanzu ma Mallam yake fad'a min wata musabak'a da ta taso. Wai za a yi ta nan da wata biyar, ta k'asa ce. Kin san ni na wakilci jihar Katsina waccan shekarar, har na zo ta biyu. To yanzu a cikin mu ukun da muka zo farko ne aka d'auke mu, mu za a had'a da mutum uku da suke ko wace jiha, idan an had'a mu a nan ma wata gasar ce, wanda suka zo farko ciki za a fitar da wanda zasu wakilci Najeriya."

"To fa!" Na jinjina kai.

"Abun na yi ne ashe. Ba dai sai an k'ara k'unshe ku ba wannan karon ma ko?"

 Murmushi ta yi bayan ta mik'e tsaye, ta cire hijabin jikinta.

"Ba za a 'kunshe mu ba umma. Wancan ma dan muna da yawa ne sosai, akwai wanda suke da bu'katar gyara sosai a karatunsu. Amma wannan mu uku ne kawai, ni ce ma kawai fa daga islamiyarmu, sauran mutum biyun kowa da tasa makarantar."

"Yauwa to, yanzu na ji magana. Allah Ya taimaka Ya sa a yi a sa'a."

"Ameen Umma." Ta fura tare da shigewa cikin d'aki.

Babu jimawa kuma ta fito, fuskarta babu annuri ta ce,

"Umma, wai kuma yanzu Mallam Kamala ya kira ni, wai akwai wani wa'azin aure da aka gayyace shi ba zai samu damar zuwa ba, wai in taimaka in wakilce shi.

Umma wallahi ni ban shirya ma wa'azi ba yau, bare kuma na aure wanda dole sai an tsara komai." Ta dafe kanta had'e da zama.

Kad'a mata kai na yi, fuska d'auke da murmushi na ce,

"A'a 'yata. Bana son jin hakan daga gare ki. Malaminki fa ne ya buk'aci ki taimaka masa."

Ajiyar zuciya ta sauke,

"Ba wai bana son yi ba ne Umma, shirya masan ne dai ban yi ba. Kyau a ce tun jiya ya sanar da ni, ko kuma islamiyyar safe. Amma sai yanzu da azahar ta kusa ne zai fad'a min? Wai kuma da la'asar ake son in fara?"

Dafa mata kai na yi, cike da bata k'warin guiwa na ce,

"A hakan dai zaki daure ki yi. A cikin mutum nawa da ke makarantar, ya ware ki ke kad'ai ya ce ke zaki wak'ilce sa? A ganina ai wannan ma abin alfahari ne, ko?"

 Bata son jayayya da ni ko kad'an, a bata so d'in ta hak'ura, ta d'auko takarda da biro ta fara rubutu.

Ko da la'asar ta yi ta gama shirinta, dama ya turo mata inda yake son ta je d'in.

Hijabinta ta saka har k'asa, mai kalar ruwan toka. Mai hannu ce, hakan ya bata damar fiddo tafukan hannyenta a waje, ta rataye k'aramar jakarta, ta d'aura ni'kabinta, sannan ta min bankwana.

Fatan alkhairi na mata, sannan mahaifinta ma da ya dawo dai-dai lokacin ya mata, ta tafi.

Daf da magrib sai gata ta dawo a rikice, tamkar wacce bata cikin hayyacina.

Kallo d'aya zaka mata ka tabbatar bata cikin natsuwarta, kamar akwai wani abu na tashin hankali da ta gani.

Tambayarta nake me ke damunta? Me ya same ta? Amma ta kasa furta min komai, kallona kawai take tana zazzare ido.

Salati nake ina mai k'ara dubanta, duba ta tsanaki na ce,

"Zauna ga tabarma nan. Ki natsu sosai sannan ki min bayani."

Bata musa min ba, zaman kuwa ta yi, ta had'e kanta da guiwoyinta, ga jikarta a ma'kalk'ale da ita, sai nik'ab d'inta a d'ayan hannunta.

Dama na bata sosai ta samu natsuwa, har sanda aka kira sallah na zuba mata ruwa a buta, ta tashi ta gabatar da sallar.

A dai-dai gamawarta Mallam ya dawo, bayan ya zauna ne ta fara bamu labari.

"Umma, yau na had'u da tashin hankalin da tun da nake a rayuwata ban tab'a shiga irinsa ba.

Na ga abin mamaki, wanda tun da nake ban tab'a ganin irinsa ba.

Umma na kasa gasgatawa, shi ne, ko ba shi ba ne? Na kasa amincewa, shi d'in ne dai ko kuwa wani mutumin ne na daban?..." tana kaiwa nan ta yi shiru a zancenta, ta dafe kanta da ke barazanar fashewa, ta ci gaba da fad'in,

"A dai-dai sanda na gama wa'azi, k'arfe biyar da rabi na baro gidan, amaryar da k'awayenta suka rako ni har bakin titi, suka tsayar min da keke napep sannan suka bani dubu uku.

Keke nalep d'in to ba mai tuk'in bane kawai zaune, su biyu ne har da wani a gefensa.

Duk da na yi addu'a sanda zan bar gida, na yi addu'a bayan fitowata daga gidan da na yi wa'azin, sannan kuma na yi addu'a a dai-dai sanda zan hau napep d'in. Na samu kaina da rashin natsuwa, gabana sai fad'uwa yake ban san dalili ba.

A titin ring road da ya kamata mu yi gabas daga shi, sai na ga sun zarce da ni.

Ganin haka ya sa na ce,

"Mallam, Gidan dawa fa na ce ku kai ni."

Daga mai tuk'in har na kusa da shi babu wanda ya furta min komai, babu wanda ko da kallona ya yi. Sai ma k'ara wutar napep d'insu da suka yi.

Salati nake ina ambaton sunan Allah, hankalina baki d'aya ya gama tashi, sai faman kalle-kalle nake.

Wata kwana na ga sun shiga da ni, daga nan suka ringa shiga lungu da sa'ko, har muka b'ulla wani k'asurgumin daji, wanda tun da nake a rayuwata ban tab'a sanin akwai irin wannan dajin a Katsina ba.

A dai-dai bakin wata gidan gona suka dakata, wanda ba shi ne ke tu'kin ba ya fara sauka, sannan wanda yake tuk'in ma ya sauka.

"Wai bayin Allah ina ne nan kuka kawo ni? Dan Allah ku rufa min asiri, ku taimaka ku fitar da ni daga wannan dajin."

Dariya suka k'yalk'yale da ita su duka biyun, kafin suka finciko ni da k'arfin tsiya daga napep d'in, suka isar da ni cikin gidan gonar.

A wani babban falo suka dire ni, ina kuka sosai, kuma har a lokacin ban manta da sunan Allah ba,  ban daina neman taimako daga mahaliccina ba.

Cikin wani d'aki suka shiga, sai ga d'ayan ya dawo, d'ayan kuma bai fito ba.

Wanda ya fito d'in ne na ji yana waya, wayar da ta tayar min da hankali, ta sa gabana ya ringa duka da sauri-sauri.

"Oga mun zo kuma baka nan sai Yax kawai muka samu. An samu wata d'anya shakaf. Uztaziya ce sosai, dan fuskarta ma a nad'e take da nik'ab, ina jin a jikina zata maka sosai. Ehh zata maka sosai ma kuwa." Ya k'arasa wayar da dariya a fuskarsa.

Bayan wasu da'kik'u wanda ba zasu wuce goma ba, sai ga Ogan nasu ya iso, fuskata na kallon wata k'ofa ta inda wancan d'ayan ya shiga, har ya iso daf da ni ban sani ba.

Hakalina bai gama tashi ba, ban daina jin fargaba ba, sai a lokacin da idanuwana suka fad'a a saman fuskarsa.

Shi d'in kanshi da mamaki yake kallona,

"Ke ce?" Ya furta had'e da zaro ido.

Mik'ewa na yi ina gwada sa da yatsa, ido da bakina duk a bud'e suke,

"Kai....kai ne Ogan nasu dama?"


*To fa! Me ke faruwa ne haka? Wanene wannan Ogan wanda suke satar 'yan mata? Me yasa yake mamaki dan ya ganta, hakan na nufin ya santa ke nan? Ita d'in ma da alama ta sanshi fa. What is happening? What do you think, readers?*

*Duka zaku samu wannan amsoshin a next page insha Allahu.*


_kar mu manta da ambatar sunan Allah a duk halin da zamu tsinci kanmu. Mu daure mu kira sunan mahaliccinmu, saboda shi ne kad'ai zai iya bamu kariya, zai kub'utar da mu daga halin da muka tsinci kanmu._


*Wattpadians, don't forget to comment on each line, and then vote after reading every page. Ina kallonku, masu karantawa basa voting, Ghosts ke nan. PrincessAmrah zaku yi searching don samun many books of mine. Thanks always*


Pinky durling??
*RAZ 2*
[7/4, 11:31 PM] Princess Amrah???: *??MRAH NAKE SO!* ?


(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi.)

            Na Amrah A Msh
            _(Princess Amrah)_
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


_Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (sickler)_


                          1?8?

Sunkuyar da kansa ya yi  k'asa yana mai murtsuka gashin kansa da duka yatsunshi.

Jin k'afafuwana kamar suna neman gagarar d'aukar gangar jikina yasa na gaggauta zama da k'arfi, idanuwana suna masu kawo ruwa.

"Esien!" Ya k'wala ma d'aya daga cikin yaran nasa kira.

Da hanzari sai ga d'aya daga cikin wanda suka sato ni ya wanzu a gabanshi, cikin wata murya ya ce,

"A mayar da ita, ta kwatanta maku gidansu ku kai ta, bana so ku mata wani abu kuma."

"An gama Oga." Ya furta had'e da komawa 'daki ya kira d'ayan abokin nasa.

"Kar'bi wannan takardar, daga nan ku tsaya chemist ku siyo min wannan maganin, har yanzu ina jin ciwo a k'afafuwan nan nawa, ina sauri ne ban tsaya na siyo ba."

 Kar'ba ya yi sannan ya juyo da kallonsa gare ni, da alama cike yake da mamakin yanda Ogan nasu ya bijirewa tayinsu, shi d'in da a kullum yake jin dad'i idan ya ga yarinya budurwa, musamman kamilallu, wanda a ganinshi su ne zai samu zumarsu yanda yake so, ya lashe zumar cike da jin da'di, a 'karshe ya b'atar da su ba tare da sun san inda kansu yake ba.

"Mu je." Muryarsa ta dirar min a kunne, bayan tsawon lokacin da na lula a birnin tunani.

Bin bayansu na yi kai tsaye muka doshi waje, a daidai k'ofar fita ya dakatar da ni,

"Kar maganar nan ta fita matuk'ar kina son numfashinki."

Kai kawai na jinjina masa, har a lokacin ban daina ruwan hawaye ba.

Napep d'in na shiga, bakina bai daina addu'a ba, tunani da k'wak'walwata basu daina tababa a kan abin da na gani ba.

A cikin napep d'in ne abokan suke fira, duk da halin da nake ciki, duk da rabin hankalina baya tattare da ni, hakan bai hana ni mayar da hankalina gare su ba.

"Baabaa amma fa na yi mamakin Oga. Gashi dai abin da ya fi so, amma bai yi tsiyar ba."

Dariya wancan di'n ya k'yalk'yale da ita,

"Ina ganin dai ciwon k'afar nasa ne ya motsa. Baka ji har da magani ya ce mu siyo masa ba? Da alama shi ya sa ya sallame ta."

D'ayan ya ce,

"Zan iya yarda da hakan kam. Duk soyayyarsa da son falle sababbi dal a leda, amma ya bar garab'asa. Gaskiya Oga Sans akwai damuwa a tattare da shi."

 Baki na bud'e ina mamakin sunan da suka k'ira sa da shi, ina mai jinjina sunan 'Sans' a bakina.

To waye shi? Wannan wane mutumi ne wanda kamanninsa iri d'aya da Yaa Noor d'ina? Duk ta k'are shi ne wanda na yawaita gani a asibiti. Shi ne wannan gurgun da nake gani a keken guragu tsawon shekaru da dama da suka gabata.

Amma kuma ta ya zan gasgata cewa ba Yaa Noor d,ina ba ne bayan kamar tasu babu banbanci?

 'Ta d'abiu da sa'banin halaye.' Wani sashe na zuciyata ya bani wannan amsar.

"Ke mun zo Gidan dawa. Ta ina zamu bi?"

Muryar gardawan ta dawo da ni daga duniyar da bani na kai kaina ba, duniyar da tunane-tunane ce kawai ta jefa ni.

"Kwanar gaban shagon can zaku shiga."

Na fad'a da disasshiyar murya, wacce kuka ya gama dishasarwa.

Har gaban gida suka kawo ni, suka kuma k'ara bige min warning a kan kar maganar ta fita, kar na bari hukuma ta shiga, saboda komai zai iya faruwa da ni."

 Amrah na kai wa wannan gab'ar ta dakata, tana shesshe'kar kuka sosai, jikinta sai faman rawa yake.

Cike da tashin hankali na jawo ta a jikina, ni d'in ma kukan nake sosai.

"Ya isa haka to. Ai gashi babu abin da ya same ki ko? K'arfin addu'a ke nan."

Ni d'in ma ban daina kuka ba.

"Gaskiya ba za a bar maganar nan ba. Ya zama dole hukuma ta shiga wannan maganar, ko dan gaba."

Mallam ya furta yana mai jinjina lamarin.

"Dan Allah Abba kar a shigar, wallahi ina tsoro."

 Ta fa'da cike da muryar kuka.


"To ke ya kike ganin gaskiyar lamarin? Ni dai na tabbata ba Annur ba ne, na san Annur yaro ne mai hankali, yaro ne mai sanin ya kamata, wanda na yi imani da Allah ba zai kasance mai irin wancan halin ba.

Ga kuma babbar hujja, wancan d'in ma da kike fad'i gurgu ne, kuma ga wannan ma maganar ta kusa zuwa d'aya. Da alama dai kama ce mai tsanani suka yi. Kin san ana samun irin haka."

Cike da gamsuwa Amrah ta jinjina kanta,

"Na yarda da wannan bayanin Umma. Tabbas na san ba Ya Noor d'ina ba ne. Kuma dan ya nunar da alamun mamaki a lolacin da ya gan ni bai zama hujja a ce shi ba ne, tun da shi d'in ma na san shi a asibiti, shi ma ya san ni, mun sha had'uwa da shi, har gaishe ki ma yana yi. Da alama dalilin da ya sa ya sallame ni ba tare da ya min komai ba ke nan. Wallahi na yarda ba Hammana ba ne, wancan mutumin banzan dai ne. Fasi'ki, mazinaci, azzalumi!" Ta k'arisa da share hawayenta.

"Mallam tun da dai abun haka ne, kuma shi d'in bai mata komai ba, kawai mu hak'ura, mu barsu, akwai ranar da zasu ha'du da dai-dai ya su."

"Haka ne. Allah Ya tsayar nan to. Allah kuma Ya k'ara karewa."

"Ameen ya Rabb. Kuma sai fa da ta nunar da bata son tafiyar, kamar ta san abin da zai faru. Ni na tilasta mata tafiyar, ashe abin da zai faru ke nan."

Wani kukan ya sake kufce min.

"Ya kamata ku yi shiru haka nan. Babu abin da addu'a ta bari. Kuma na yarda cewa addu'ar da ta yi ne ya sa abin ya tsaya nan, har zuciyarsa ta sanyaya, ya iya tuna ma ya ta'ba ganinta.

Kin san mafi yawancin mutanen banza irin wa'innan, sun fi d'aukar mummunan hukunci a kanka ma sanda ka nunar da ka sansu. Amma hikima irin ta Allah, da taimakonSa sai suka sallame ta.

Lallai babu k'arfi babu dabara face a wurin Allah ma'daukakin sarki! Shi ya halicce mu, shi muke bautamawa, kuma shi ne maji k'anmu. Shi ne mai taimakonmu a duk lokacin da Ya ga dama. Shi ke kare mu a duk sanda muka nemi kariyarSa.

Babu babban butulci sama da neman taimako ko kuma agaji ga wanin Allah. Sau da dama wasu sukan butulce, su nema taimako ga d'agutu, wanda shi d'in kanshi sai Allah ya bashi iko.

Me zai hana duk sanda muka samu kanmu a cikin tashin hankali, mu ambaci "INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN!"? Ita ce kalma mafi girma, wacce ya kamata mu ambata a duk sanda wani tashin hankali ya riske mu.

Kin kyauta sosai y'ata, kin buk'aci taimako ga Allah kuma Ya taimake ki. Ina alfahari da ke, ina alfahari da baki d'aya halayenki, ina alfahari da iyalina."

Ya 'karashe maganar da murmushi shimfi'de a saman fuskarsa.

Take muka manta da duk wani tashin hankali, muka ci gaba da rayuwarmu kamar kullum, tana min labarin yanda wa'azin auren ya kasance.

Tun daga wannan tashin hankalin da muka shiga, bamu sake samun kanmu da shiga wata damuwa ko matsala ba, Annur kuma dama na fad'a ma Amrah ko da wasa kar ta masa tad'in. Tun da dai mun tabbatar cewa ba shi ba ne, kawai dai mai kama da shi ne. Na tabbatar idan muka fa'da masa ba zai ji dad'i ba, kuma zai yi bincike sosai har a gano mutanen, bayan kuma mun saki maganar, gwara dai mu barsu da duniya, saboda ta fi bagaruwa iya jima.

Haka kwanaki suka ci gama da gudanya, har su Amrah suka fara zana jarabawar WAEC.

Ranar da suka fara ne ta dawo cikin yanayin zazzab'i, irin mai zafin jikin nan sosai, wanda ko rintse idonta cikin wani hali take yinsa.

Mallam Mu'ammar ne da kanshi ma ya dawo da ita bisa mashin d'insa, bayan sun fito daga exams.

A yanayin da na ganta, sai da hankalina ya tash, gabana ya ringa fad'uwa.

"Me ya faru da ke?"

Na gaggauta tambayarta.

Tab'a fatar jikinta da na yi ne ya bani amsar tambayar da na mata, tun kafin ita d'in ta amsa min.

"Subhanallahi! Lafiya lau fa kika fita Amrah. Ko kin shiga ruwan saman nan da aka yi ne"

A daburce na sako zancen, ina mai sake tab'a jikinta.

"Umma an caccanza mana hall ne har sau uku, daga farko aka kai mu Class, sai aka sake canza wani, a 'karshe kuma aka kai mu exam hall. Kuma duk a cikin ruwa muka yi yawon. Tun daga sannan ne na ji jikina ya mutu, zazzab'i mai zafi yana sauko min, da k'yar ma na rubuta jarabawar."

Ta k'arisa maganar tana mai yin hamma, irin mai nuna yanayin zazzab'in nan.

"Aikam tashi zaki mu tafi asibiti, tun da wuri ma.." ban rufe baki ba muka ji sallamar Annur.

Sanye yake da suites ba'ka'ke, sai light blue riga mai dogon hannu daga k'asa, neck tie di'nsa bak'i mai di'go di'gon light blue d'in.

Amsa sallamar tasa na yi, ina mai k'oka'rin k'irk'iro masa murmushi.

Bayan mun gaisa da shi, Amrah ma ta gaishe shi ne yake tambayar lafiya? Dan ya kula da yanayin namu.

"Ehh to, ta dawo exam ne ka ga ko uniform ma bata cire ba. To kuma zazza'bi take sosai, ga hawaye nan sai fita suke da kansu. Yanzu haka shawarar kai ta asibiti ma nake."

Kallonshi ya miyar ga Amrah, cike da soyayya, kallo mai nuna zallar tausayi, k'auna da kuma irin kewarta da ya yi.

Kalar idanuwan nasa ne suka sauya, daga farare tas da suke, zuwa jajaye. Haka yake, a duk sanda zai tarar Amrah bata da lafiya, kuka ne kawai baya fasawa.

Cikin wata irin murya ya ce,

"Ta shirya zan kai ta Umma."

Maganar da ya yi ce ta sa na tuno zancen da nake so mu yi da shi, wanda na jima ina yi masa amma ya yi kunnen uwar shegu da ni.

"Yauwa, Annur ba dai zan gaji da rok'onka ba, dan Allah..."

Saurin dakatar da ni ya yi,

"Wallahi Umma bana jin zan iya yin awon genotype. Ina ji a jikina ni ba AS ba ne, AA ne da ni. Ban san ya zan yi ba idan na yi wannan awon aka ce ina da AS, ban san wane hali zan shiga ba. Bana jin kasantuwar Amrah SS zai sa na hak'ura da aurenta."

Gya'da kai na yi ina kallonshi. Cikin k'wayar idonshi na kalla, na karanci yanda soyayya ta makantar da shi, ta sa baya ganin komai sai Amrah. Soyayya ta kurumtar da shi, ta sa baya jin maganar da nake masa a kan wannan awon. Sosai na fahimci yanda soyayya ta jirkitar da tunaninsa, ta sa ya kasa gane muhimmancin wannan awon.

"Amma Annur, baka tunanin halin da yaranku zasu shiga nan gaba? Me kake tunani idan yaran da kuka haifa suka shiga cikin hali irin na Amrah, ko kuma ma wanda ya fi nata?"

"Wannan ba abun damuwa ba ne Umma. Zamu iya tsaida haihuwar ma baki d'ayanta. *AMRAH NAKE SO* ba wai abin da zata haifa min ba.

Wallahi ko AS nake da shi ba zan iya hak'ura da ita ba. Bana jin zan yi rayuwa mai kyau ba tare da Amrah ba. Bana jin zan ta'ba yin aure matu'kar ba Amrah na aura ba. Saboda haka, Umma, awon genotype bashi da wani tasiri a gare ni. Dan Allah yau dai a tsayar da maganar nan. Tun kafin a saka ranar aure muke yinta, Umma ta gagara k'arewa, har gashi yanzu bai fi mana watanni uku a d'aura aure ba."

Jin ya dakata daga nan, ya sa na dafe kaina, baki da'ya jikina ya yi sanyi.

"Ai shi ke nan. Amrah tashi mu tafi. Bara na d'auko makullin gidan a d'aki. Amma ki fara kiran Abbanki ki sanar masa."_Addu'a na sauk'ak'a masifu da bala'iku sosai. A duk halin da zamu tsinci kanmu, na ciwo ne ko kuma wata damuwa, kar mu manta da INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN!_Pinky durling??
*RAZ 2*
[7/5, 2:42 PM] Princess Amrah???: *??MRAH NAKE SO!* ?


(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi.)

            Na Amrah A Msh
            _(Princess Amrah)_
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


_Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (sickler)_


                          1?9?

Bayan mun isa asibitin ne muka buk'aci a had'a mu da Dr. Xarah ko kuma Dr. Rabiatu, amma aka shaida mana Rabiatu bata nan, dole sai dai Dr. Xarah.

Bayan mun shiga Ofishin nata, kallo d'aya ta ma Amrah ta tabbatar da bata jin dad'i.

"Sannu Amrah." Ta furta cike da tausayi.

"Jikin dai kuma" ta jinjina kanta.

"Wallahi kuwa Dr. Daga makaranta ta dawo min haka. Wai ruwa aka saka suka shiga wurin canjin hall, har ruwa ya mata duka."

"Subhanallahi! To Allah Ya kyauta gaba."

Ta zaro lokar dake gaban teburinta.

"Ungo thermometer, ki saka a armpit d'inki."

Karb'a ta yi kuwa ta saka, ta d'an jima kafin ta nemi ta fiddo ta.

"Subhanallahi! Temperature d'inta har ya haura ma 47. Lallai zazza'bi ya shige ta sosai. Bara na rubuta mata magani. Ku tsaya ku karb'a sannan a mata awon jini, idan ya sauka dole a tarbi abun, a mata k'arin jini."

Ta hau rubutu.

Bayan ta gama ne ta mik'o min takardar, tare da yi mana fatan alkhairi.

Har zan fita ta dakatar da ni,

"Maman Amrah wai yaushe ne ma aurenta?"

Murmushi na yi na ce

"Wata biyu ne da 'yan makwanni suka rage. Insha Allahu idan ya matso zan zo na sanar miki."

"To Allah Ya kaimu. Ina fatan dai an san genotype d'in angon nata." Ta furta a hankali.

Kallona na mayar ga Annur, ina k'ok'arin magana ne ya yi caraf ya ce

"Ehh, an yi Dr. AA ne da shi"

"To masha Allahu. Haka ake so ai." Ta fad'a.

Bankwana muka mata sannan muka fita.

D'akin magani muka fara zuwa aka bata, sannan muka nufi laboratory domin awon jini.

Bayan an gama auna mata mun fito, Annur ya ce,

"Umma bari dai na je a min wannan awon, ba dan komai ba sai dan na tabbatar, idan AS gare ni tun wuri sai na san hanyar bi domin tsayar da haihuwa, duk da dai jikina baya bani hakan."

Ajiyar zuciya na sauke,

"Haka Nake so Annur. Bari mu jiraka a can har ka dawo."

Ya tafi, mu kuma muka zauna jiransa.

Kusan awa d'aya ya da'uka sannan ya dawo, fuskarsa k'unshe da murmushi, farin ciki ya gagare b'oye kansa. Hannunshi d'aya rik'e da takarda, d'ayar kuma a cikin kansa yana wasa  da sumar kansa.

Tun daga nesa yake furta,

"Umma kin gani ba, dama na fad'a miki."

Bayan mun mik'e taye na ce,

"AA gare ka ke nan?" Ni d'in kaina ina murmushi.

"AA gare ni Umma, kar'bi takardar ki gani."

Bayan na duba ne na tabbatar da maganarsa. Da gaske abin da ya fad'a. Wani irin dad'i na ji ya kewaye ilahirin zuciyata, na kalli Amrah da ita kanta da'din ne ya mamaye ta.

Da farin ciki muka isa gida, wanda sai da muka biya ta Crispy ya mana take away na abinci da lemo kafin muka isa.

***
Rayuwa ta ci gaba da tafiya, kwanaki na gudanya, muna 'kara kusanta ga Allah, har Amrah suka gama jarabawarsu duka, WAEC DA NECO d'in. Wata da'ya kacal ya rage aurenta.

A iya wannan lokacin har lefenta an kawo, akwati saiti biyu, da kaya na ji da fad'a, zan iya cewa tun da nake a rayuwata, ban ta'ba ganin kayan lefe kamar na Amrah ba.

Sadakinta naira dubu d'ari aka kawo, komai dai sai hamdala. Fatana a ko da yaushe, shi ne Allah Ya kawo farin ciki a rayuwar auren Amrah. Yanda Hajiya Suhaila ke nuna mata gata da soyayya, ina fatan d'orewar hakan har gaban abada.

Saitin kayan d'akinta da Mallam ya siya mata masu kyau, ba wasu na 'karya ba ne sosai, iya k'arfinsa ya yi, kuma a hakan ya samu rufin asiri. Komai ya yi kyau sosai.

A makuna hud'un da ya yi saura na auren Amrah, babu abin da bamu gama ha'dawa ba. Hatta da kayan abincin da za a ci lokacin aure mun gama had'awa. Kayan kitchen d'inta bakin gwargwado mun had'a mata. Dama 'yan uwana sun had'a min gudunmawa tun watan da ya gabata sun bani, da su na 'kara na mata siyayyar kayan kitchen d'in, kayan 'yan gayu, wanda na san mai rayuwar Abuja zata iya buk'ata. Dama kuma sun ce kayan kitchen ne kawai za a tafi Abuja da su, kayan d'akinta a nan Katsina zata barsu, gidansu wanda zasu ringa sauka idan sun zo. Abujan babu abin da basu zuba mata ba.

Da murna ta shigo cikin gida, bayan ta cire hijabinta ta zauna kusa da ni.

"Fuskarki ta bayyanar da farin cikin da kike ciki. Da alama an faranta miki rai."

Da murmushi ta ce,

Umma, sati mai zuwa zamu tafi Sudan, kin san na fad'a miki a can za a yi musabak'ar k'asa da za a yi. Umma ni na haye a duk fad'in ka'sar nan, ni da wani namiji da'ya ne kawai zamu wakilci Najeriya, shi zai zama na b'angaren maza, ni kuma a b'angaren mata. Shi d'in d'an jihar Gombe ne."

Cike da farin ciki na ce,

"Alhamdulillahi Ya Allah! Kai amma wannan labari ya min da'di sosai wallahi. Har na ma rasa me zan yi dan murna. Allah ubangiji Ya taimaka Ya bada sa'a. Allah Ya baku ikon d'auko ma K'asarmu lamba ta farko a wannan gasa.

Oh ni Murja! Wallahi jin abun nake tamkar a mafarki, wai 'yata da na haifa da cikina zata tafi wata K'asa gasar Al-Qur'ani mai girma, kuma wai 'Kasa baki d'aya zata wakilta.

Ke alheri ce Amrah! Ke abar alfahari ce, wacce ko wace uwa zata so samun irinta. Ke abar koyi ce Amrah, wacce ko wace macen kirki zata so zama irinki.

Allah Yana tare da ke Amrah, insha Allahu zai taimaka miki, zai baki nasara. Kuma na yi alk'awarin zan hana idanuwana bacci in kwana ina miki addu'ar samun nasara."

"Ameen Umma. A lokacin da zancen nan ya tabbata, har da hawayen farin ciki na yi. D'alibaina kansu sun taya ni farin ciki. Daga masu kukan murna sai masu hawayen farin ciki. Matan auren da nake koya ma har da wacce ta rungume ni, wai ina ma iyayena zasu bata kyaur Malama Amrah, wallahi da ta gwada min k'auna fiye da yaran da ta haifa da cikinta."

Ni d'in ma rungumarta na yi, idanuwana na kawo ruwa, ban sake ta ba, haka kuma a tsaye muke bamu zauna ba.

A haka mallam ya tarar da mu, tun bai nemi bayanin dalilin halin da muke ciki ba, na hau zayyane masa komai, ina yi ina hawaye mai had'e da dariya.

"Abin da ya dawo da ni gida ke nan, Murja. Ina wurin aiki na ji wani abokina yana saurarar radio, kamar an ce na d'aura kunnuwana a bisa bayanan, caraf kunnuwana suka jiye min sunan 'yata, a matsayin wacce zata wa'kilci K'asa baki d'aya, a musabak'ar da za a gudanar ta K'asa, a 'Kasar Sudan.

Na kasa gasgata hakan, sai da na ji muryar Malaminsu da kanshi, yana mai nuna irin farin cikinsa. A k'arshe na ji muryar jakadan musaba'ka na jiha, yana nuna tashi murnar, da d'aya daga cikin d'aliban jiharsa ce zata wakilci 'Kasa ta b'angaren mata.

Abun nan ya min dad'i kwarai da gaske. Na sake jinjina wa kaina, ke, da kuma 'yata. Tabbas samun 'ya kamar Amrah babbar sa'ar rayuwa ce.

Amrah 'yata, ba zan ta'ba gajiyawa da shi miki albarka ba. Ba zan ta'ba daina miki fatan alkhairi ba."

A haka wannan rana ta zame mana ranar farin ciki, farin cikin da na jima ban yi irinsa ba.

Shi yasa ake so ka gode wa Allah a duk halin da kake ciki. Ka karb'i duk irin yanayin da mahaliccinka Ya yi ka. Kar ka butulce maSa saboda wata jarrabta da Ya yi maka, ko ba komai ka fi wani. Idan baka da lafiya, ka gode maSa, idan ka gode maSa, sai Ya baka ta wani fannin.

Gashi dai duk wahalar da kika sha tsawon shekaru goma sha shida da watannin da na haife ki kike fama da ciwo, ciwo kuma mai matu'kar wahala, wanda babu wuya mutum zai iya kauce ma sharia, ya ji kamar shi ne aka fi tsana duk duniya. A haka muka jure, muka dage da addu'a, muka tsayanta Allah d'aya ne. A hakan da wahalar da kike, muka tarbiyyantar da ke, muka d'ora ki a bisa tafarkin kirki.

A k'arshe mun ga ribar hakan, kin zama abar alfahari gare mu, malamanki, makarantarki, jiharki, da ma 'Kasarki baki d'aya."

Annur kanshi sanda ya ji wannan labarin ya matuk'ar jin dad'i. Shi a gidajen talabijin ma ya ga sanarwar, kuma daga 'kasa aka mak'ala sunanta.

Cikin lokaci k'ank'ane magana ta gama kewaye 'Kasa. Sunan Amrah ya shiga wurare da dama wanda bata ta'ba mafarkin zata je ba, sai ga sunanta ya je. Mutane da dama suke son ganinta, suke san sanin wai wacece wannan yarinyar mai tarin baiwa, wacce ta k'etare mutane da yawa, ta zama wa'kiliyar 'Kasarta?

Ranar da zasu tafi, har Kano muka rakasu, ita da Malaminta.

A iya inda zamu rabu, na kama hannuwanta duka biyun, na kalle ta cikin ido, na ce

"Ina miki fatan alkhairi 'yata. Ba zan tab'a daina yi miki addu'a ba. Insha Allahu nasara tana tattare da ke. Allah Ya taimaka, Ya bada sa'a. Ki kula da kanki, Amrah."

Wasu irin zafafan hawaye suka ringa kwarara daga idanuwana.

Cikin kuka take wasa da hannuwana, cikin kuka take k'irk'iro murmushi, cikin kuka take fad'in,

"Zan kula da kaina insha Allahu, Umma. Ki yafe min duk wani abu da na miki, b'oyayye da kuma bayyananne."

Zare hannu guda na yi daga cikin nata, da shi na share hawayen da ina share sa ina dambe da wani, wanda ke shirin sake fitowa.

"Baki ta'ba yi min komai ba Amrah. Banda alkhairi babu wani abu a tsakanina da ke. Idan ma akwaishi, na yafe miki."

Na sakar mata murmushi.

"Allah Ya 'kaddara saduwarmu, Umma." Ta fad'a had'e da zare hannuwanta daga nawa, ta rik'e na mahaifinta.

Tun bata furta komai ba ya ce,

"Baki ta'ba yi min komai ba 'yata. Idan ma akwai to na yafe miki. Ina mai neman gafararki, a bisa halin da muka jefa rayuwarki a ciki. Har yanzu na kasa yafe wa kaina. Har yanzu gani nake mu ne sila, mu muka jefa ki cikin wannan cutar. Ki yafe..."

Bai rufe bakinsa ba ta saka tafukan hannunta ta dafe masa bakin nasa,

"Bana son jin haka daga gare ka, Abbana. Komai na duniyar nan da zai samu mutum, to k'addararsa ce. Na sani, na kuma yarda cewa tawa k'addarar ke nan. Babu mai k'in d'aukar k'addara face butulu. Kar ka damu Abbana. Na yafe maka duniya da lahira. Na yafe maku kai da Ummana."

Cikin hawaye take murmushi.

Gaban Annur ta koma, wanda tun d'azu idonsa yake cikin nata.

Murmushi ya 'kirk'iro mata, ba tare da ya furta komai ba.

"Zan tafi Hammana. Ka yi min addu'ar samun nasara."

"Nasara na tare da ke insha Allahu, Amrah. Allah Ya taimaka, Ya bada sa'ar abin da aka je yi."

Lumshe idanuwanta ta yi, sannan ta sake bud'e su a kanshi.

"Kar ka manta da ni, Hammana. Duk rintsi duk wuya, kar ka manta da Amrah. Ni ma ba zan tab'a mantawa da kai ba."

Gyad'a mata kai ya yi, idanuwanshi cike da shauk'in soyayya,

"Idan har zan iya mantawa da ke, to tabbas zan iya mantawa da kaina. Ke ce rayuwata, Amrah. Ke ce duk wani tunanina. Na so a ce tare zamu yi tafiyar nan, sai dai kuma Allah bai nufa ba. Ni ma tafiya ta taso min, zuwa K'asar Malaysia, ina tunanin sai kamar ana gobe zaku fara zan dawo. Amma duk da haka, rayuwata tana tare da ke, zuciyata tana tare da taki. Motsinki da komai naki yana tare da nawa. Ina matu'kar k'aunarki."

Juyowa ta yi ta kalle mu, cikin jin kunya ta sunkuyar da kanta k'asa.

Saurin d'auke kallonmu muka yi daga gare su.

"Na gode k'warai Hammana. Na gode da sadaukar da rayuwarka da ka yi a kaina. Na gode da k'aunar da ka nuna min. Na gode da komai ma."

Ta fashe da kuka sosai.

"Ya isa haka to, please. Kin sani sarai, kin san yanda hawayenki yake da zafi a gare ni. Kin san yanda na tsani ganin zubar hawayenki. Kin san yanda rayuwata ta tsani ganin kin yi asarar hawayenki. Ki tafi, ga malaminki can yana ta jiranki."

"To Hammana. Allah Ya k'addara saduwarmu." Ta tafi.

Har ta isa iyakarmu da su bata daina waiwayenmu ba, bata daina hawaye ba.

Baki d'aya jikina ya yi sanyi, na rasa dalili. Duk da ina son tafiyar tata, na san ci gaba ne a gare mu baki d'aya, amma a hakan ji nake kamar ta fasa tafiyar, kamar ta dawo gare mu.

A haka muka kama hanyar parking lot. Muka shiga motar Annur, muka kama hanyar dawowa Katsina.

_Tabbas soyayya gaskiya ce, wacce Allah ne yake d'aura ma mutum ita, ba tare da zuciyarsa ta shawarce shi ba. Abu mafi dad'i a soyayya, shi ne ka had'u da mai sonka tsakani da Allah. Ka had'u da mai k'aunarka, wanda zai sadaukar maka da rayuwarsa. Ina rok'on Allah Ya had'a mu da masoyanmu na gaske. Allah Ya aurar da mu ga masoyanmu na gaske._


pinky durling??
*RAZ 2*
[7/6, 9:25 PM] Princess Amrah???: *??MRAH NAKE SO!* ?

(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi.)

            Na Amrah A Msh
            _(Princess Amrah)_
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*

_Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (sickler)_

                          2?0?

_Sa'kon gaisuwa ga tarin masoyan *AMRAH NAKE SO!* Kuna da yawa sosai, lissafo ku ba abu ne mai sau'ki ba. Sai dai duk inda kuke, ku sani cewa ana tare, ina yinku irin sosai d'in nan.??_


***
Tun da muka shiga mota nake kuka, na rasa dalilin da yasa hankalina ya gaza kwanciya, damuwa da k'unci fal a cikin zuciyata.

Mallam ne yake rarrashina, amma duk da haka na gagara yin shiru, ruwan hawaye basu daina kwaranya daga idanuwana ba.

Bayan mun isa Hajiya Suhaila ta kira Annur a waya, har ya shaida mata cewa daga Kano muke, mun raka Amrah ne zasu tafi Sudan.

Wayar tasa ya bani, ta nunar min da rashin jin da'dinta sosai, a bisa rashin yi mata bankwana da Amrah ta yi. Sam! Bata ji da'din hakan ba. Kuma ko kad'an tafiyar bata zata nan kusa ba ne, bata zata cikin satin ma zasu yi tafiyar ba.

Ha'kuri kawai na bata sannan muka yi bankwana. Annur d'in ma ya bar gidan, wanda shi kanshi idan ka kalle shi zaka tabbatar yana cike da damuwa.

Ko da dare ya yi haka bacci ya gagara d'aukata, na ringa juyi, damuwa ta gama mamaye kaf ilahirin zuciyata. Yau d'in nan Amrah ta tafi, amma ji nake kamar ta yi sati bata nan.

Rayuwarta nake tausayi, mafi rinjaye a k'aunar da nake mata, ta ta'allak'a ne da tausayinta da nake, tausayin rayuwarta, tausayin yawan ciwukanta.

Tuno bankwanan da muka yi da ita kawai nake, ina tuna murmushin da take yi mai had'e da ruwan hawaye, da kuma yanda ta ringa wasa da hannuwa.

Wasa ba wasa ba, yanda na ga rana haka na ga dare. Jin kiraye kirayen sallar asuba na yi, wanda ko kad'an ban zata daren har ya kai haka ba.

Bayan gari ya waye ne Mallam ya duba wayarsa, ya ci karo da text da ta masa cewa sun sauka lafiya, yanzu haka suna masaukinsu.

Hamdala na yi a lokacin da ya bani labari. Ban san sanda na saki wani murmushi ba. Baki d'aya zuciyata na ji ta wanke, duk k'uncin da nake ciki babu shi.

"To Alhamdulillah! Sauka lafiyan dama ake buri. Zan kira ta anjima insha Allahu, gudun kar na shiga lokacinta yanzu."

Mallam ya furta shi d'in kanshi farin ciki lullub'e da fuskarsa.

A kai a kai muka ringa gaisawa da ita a waya, duk sanda zamu yi waya kuwa zan shi mata albarka, zan mata fatan alkhairi. Haka ma mahaifinta.

Ana gobe zasu fara musabak'ar Annur ya dawo, ya zo gaishe mu ne nake masa tad'inta, ta ce min za a nuna musaba'kar a tashoshi da dama, ciki kuwa har da sunnah tv, ni kuma gashi bamu da kayan kallo.

"Zan zo har nan mu kalla a waya' insha Allahu. Ai ina nan sai ranar Sunday zan tafi. Na san zasu saka live a internet."

Annur ya fad'a yana min murmushi.

Cike da jin dad'i na ce,

"Yauwa to, aiko da na ji dad'i sosai. Allah Ya nuna mana goben lafiya."

"Ameen, Umma. Bari na tafi. Idan Abba ya dawo a gaishe shi."

"Zai ji 'kwarai. A gaishe da Hajiya Suhailar. Ka mata albishir, ta tara gobe ta kalli 'yar tata."

"Zan fad'a mata, Umma."

Ya tafi.

Washe gari kuwa kusan k'arfe goma sai gashi ya zo. Malam dama ya ce ba zai fita aiki ba har sai sanda muka gama kallon musabak'ar, ko kwana nawa za a d'auka ana yinta kuwa.

Ko da ya kunna mana muna kallo, da 'Kasar Egypt aka fara. Namijin ya fara sannan macen ma ta yi.

A haka aka ringa yi, ba laifi karatu ya yi sosai, sai dai abin da ba za a rasa ba.

Har aka gama ta ranar ba a kira Najeriya ba. Haka yasa Annur ya ce zai tafi, gobe insha Allahu kafin a fara zai dawo, sai mu ci gaba da kallo.

Hakan ce kuwa ta kasance. Abun mamaki har a ranar ma ba a kira K'asarmu ba.

Sai ranar k'arshe, wacce kuma ita ce Annur zai tafi, amma a haka ya kashe tafiyar ranar, ya mayar da ita ranar litinin, dan kawai ya faranta mana rai.

Najeriya ce ta k'arshe, sai da namijin ya yi, kafin aka kira Amrah don ta yi.

Ban san sanda na mik'e ba, ganin 'yata ta doso mazaunin masu musabak'ar, cike da natsuwarta.

Wani kwali ne mai kyau aka mik'o mata, wanda a cikinsa ne ta d'auko takarda guda d'aya, ta mik'a ta ga wani wanda aka tanadar domin mik'awar kawai, shi kuma ya isar da ita ga alk'alan musabak'a.

Jan farko aka fara yi mata, a cikin suratul Bak'arah. Haka ta ringa zayyano karatunta babu kuskure, ko jar danja d'aya ba a mata ba har aka haska mata tsanwar danja, wadda ke nunar da zata dakata daga nan.

Wani jan aka mata, cikin suratul Yunus, nan ma dai haka ta ringa karatu babu kuskure ko kad'an. Daga nan sai suratul Noor. Murmushi ta saki a sanda aka jawo mata ayar farko, tana jin da'din surar, tana matuk'ar son surar, gata kuma sunan sahibinta ne.

Tun asali ta sha wahalar surar ne, sanda take hardarta har kuka ta ringa yi, saboda matuk'ar wahalar ayoyin cikinta. Amma daga sanda ta iya, sai k'aunarta da take yi.

Kamar mai bada labari haka ta ringa karatu, babu kuskure bare tangard'a a karatunta.

Cikin ja na hud'u ne aka ja mata suratul-Yaseen.

A nan kam ta dad'e tana karatun, saboda wannan shi ne ja na k'arshe da za a mata, kuma dama a kan jima kafin a dakatar da mutum. To gashi kuma dama ita ce mutum ta k'arshe a musaba'kar baki d'aya.

A daidai "kun fa yakun." Ta dire, tun bata fad'i ayar k'arshen ba ta kwanta a saman bencin, saboda irin kujerun nan ne masu had'e da teburinsu, amma na k'arshe, masu k'irar gidan sarauta.

 Tana duk'ewa kuma da alama dama ta kai k'arshe, tsanwar danja aka haska mata, wacce ke nunar da ta gama karatunta ke nan.

Tun da ta duk'e bata taso ba, da dama an yi tunanin ko dan karatun da ta yi ne, saboda da  wasu idan suna karatu kuka suke yi. Mu d'in ma kanmu haka muka yi zato.

Sai dai kuma abun mamaki, ta fi k'arfin minti goma a haka, ko motsi kanshi ya gagare ta.

Cike da mamaki aka nuno yanda alk'alan suke kallon kallo wa junansu, suna neman sanin dalilin duk'iyar tata.

Umurni suka yi ga d'aya daga cikin mata securities da suke gadin b'angaren da mata suke, kan ta zo ta ga ko kuka ya ci k'arfinta ne ya sa ta kasa ta shi.

Isowar kuwa ta yi inda take, kuma har a lokacin ba a daina d'aukar video ba. Muna kallon komai da yake faruwa a kan idanuwanmu. Sai dai mun gagara furta komai a tsakanin mu duka ukun.

Tashin hankali, wanda ba a saka masa rana. Matar na d'an jijjiga Amrah kad'an, sai ta rikito daga bisa kujerar ta fad'o k'asa.

Take Annur ya sake wayar tasa k'asa a rikice,  har sai da ta yi rugu rugu. Ya dafe gefen da zuciyarsa take, idanuwansa suka kawo ruwa, jikinshi ya hau rawa baki d'aya.

A yanda muka ji labarin faruwar abun, wai daga sanda suka ga ta fad'o d'in, hankalin mutane da dama dake wurin ya tashi, take aka yi waya aka kawo ambulance, domin a kai ta asibiti.

Babu jimawa kuwa sai ga motar ta iso, tun wanda suka d'auke ta d'in, suka tabbatar cewa gawa ce, bata raye. Amma gudun akasin haka, yasa suka yi shiru, tare da malaminta, da sauran jakadan Najeriya suka tafi asibiti.

Sai dai suna zuwa, likita ya tabbatar masu cewa bata raye, ta rasu.

Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!

Mun shiga tsananin tashin hankali Maryama. Ba zan ta'ba iya kwatanta miki adadin tashin hankalin da muka shiga ba.

Amrah ta rasu, Amrah bata raye, Amrah ta mutu ta bar mu. Shi ke nan mun rasa ta, shi ke nan mun rasa Amrah, ba zata tab'a dawowa gare mu ba.

Malaminta aka sa ya kira ya sanar mana, shi d'in kanshi cikin kuka muke waya da shi, cikin kuka yake sanar da mu abin da ya faru.

A can aka binne gawarta, gudun kar a d'auki dogon lokaci kafin a iso da ita Najeriya. Har da hoton gawar aka d'auka aka gwada a gidajen talabijin da dama, ana sanar da rasuwar baiwar Allah'r da sai da ta gama musaba'karta, a bisa teburin Allah Ya kar'bi rayuwarta.

Duk wani mai imani sai da ya girgiza da wannan al'amari mai matuk'ar d'aure kai. Wadda dubban al'umma sun kalli komai da ya faru. Sun saurari daddad'an karatunta. Sun ga yanda ta rikito 'kasa, har lokacin da aka d'auke ta.

A yadda sanarwar ta zo, Amrah ce ta zo d'aya a wannan musabak'ar, ita ce wacce ta fi kowa maki, ba wai a mata kad'ai ba, har ma da mazan baki d'aya.

Duk wata kyauta tata zasu damk'a ta ga malaminta, da kuma jakadan Najeriya, su isar da ita ga magadanta.

Ko da Malamin nata ya sanar mana a waya, cike da tashin hankali Mallam ya ce masa kar ma ya karb'o, a mata sada'katul jariya kawai da su. Mu kam mun yafe. Kujerar Makkar da aka bata ma, mun sadaukar da ita ga malaminta, ya je ya yi aiki, ya mata addu'a.  Saboda a halin tashin hankalin da muke ciki, bana jin zan iya amfani da duk wani abu wanda ya shafe ta.

Annur kuwa dama tun daga lokacin da labarin rasuwarta ya riskemu ya sume, bai sake farfad'owa ba, har sai da ya yi kwana biyar a haka.

Ko da ya farfad'o da sunan Amrah ya tashi, yana fad'in,

"Dan Allah ku ce min mafarki nake, ku tasar da ni daga wannan mummunan mafarkin da nake yi. Wallahi ba zan iya rayuwa ba tare da ita ba. Amrah ce wani 'bare na zuciyata, ita ce tunanina baki d'aya."

Kuka yake sosai, wanda dole duk na kusa da shi sai ya tausaya masa.

Rasuwar Amrah na d'aya daga cikin rasuwar da ta girgiza al'ummar Najeriya. Ta shiga record na Najeriya.

Wai ashe bankwana muka yi da Amrah a lokacin da zata tafi. Ashe ganin 'karshe na mata. Ashe ba zan sake ganin y'ata ba. Ashe mutuwa zata mana yankan k'auna.

Ranar da Annur ya farfa'do ne ya tilasta ma Hajiya Suhaila cewa zai zo inda muke, akwai maganar da yake son yi da mu.

Duk da halin da yake ciki, a haka suka zo, su duka jikinsu sanyaye.

Kallo d'aya na ma Annur hankalina ya tashi, na sake tuno da y'ata, nake ganin kamar tafiya ce ta yi, zata dawo gare ni.

Shi kanshi Annur d'in abun tausayi ne. Cikin lokaci 'kank'ani ya gama zubewa, ya koma kamar zautacce.

Cikin kuka na masu iso, Hajiya Suhaila ce ta zauna bisa tabarmar, Annur kuwa k'asa ya rashe, yana wani irin kuka mai tsuma zuciya. Yana gyad'a kanshi, da alama magana yake son yi amma ta gagara fitowa.

"Sannunku da zuwa Hajiya."

Na furta cike da k'arfin hali, muryata da ta gama disashewa da k'yar ta fito, har ake jin abun da na fad'a.

"Ya kamata ku daina kukan nan haka nan. Bai kamata ku ma Amrah kuka ba, sai dai kukan sabo kawai.

Amma irin mutuwar da Amrah ta yi, mutuwa ce wadda kowa zai yi fatan ya yi irinta.

Amrah ta yi kyakkyawan k'arshe, kuma dama an ce mutum zai tashi a kan abin da ya mutu yana aikatawa, ke nan Amrah zata tashi tana karatun littafi mai tsarki.

Ga Annur nan, shi ya takura lallai sai ya zo, akwai maganar da yake son ya yi da ku."

Ta k'arisa maganar tana mai gya'da kanta.

"Umma..." ya fad'a cikin rawar murya, yana mai k'ok'arin had'iyar k'wallarsa.

"Umma shi ke nan...shi ke nan na rasa ta. Na rasa Amrah har abada, ta tafi ta barni, bayan kuma alk'awarin da muka ma junanmu na rayuwa tare. Amrah ta tafi ta barni..."

 Ya sake fashewa da wani kukan.

Ni ma kukan nake sosai, na du'kar da kaina ka'sa, ina k'ara tuna rayuwar Amrah, rayuwa mai cike da abubuwan koyi, rayuwa mai tsananin ban mamaki.

"Umma...bana jin zan ci gaba da rayuwa a doron k'asar nan. Bana jin rayuwata zata yi kyau matuk'ar babu Amrah a cikinta."

Kuka riris yake, kamar jinjirin da ya jima bai ci abinci ba. Shesshek'a yake sosai, idanuwanshi na nunar da tsantsar damuwar da yake cikinta.
_Dan mutum yana fama da wata cuta, ba lallai ba ne a ce ita zata zama silar mutuwarsa. Kar dan kana ciwo, ka ringa tunanin lallai lokacin tafiyarka ya kusa. Ita cuta ba mutuwa ba ce. So da yawa mai lafiyar ma yana mutuwa ya bar wanda yake ciwo. Kamar yanda muka gani a rayuwar Amrah. Mun ga yanda ta kasance mai ciwo, tun tana 'yar shekara d'aya a duniya, har ta gama mallakar hankalinta kullum cikin ciwo take. Mun ga yanda cutar sickler bata zama ajalin Amrah ba. Mun ga yanda ta mutu babu ciwo, sai dai gawarta kawai. Ikon Allah ke nan._

_Ya Allah! Ka sa mu yi kyakkyawan 'karshe. Allah ka sa mu cika da imani. Allah Ya ji k'an magabantanmu. Wanda suka rasa iyaye, Alllah Ya ji k'ansu da rahama. Wanda suka rasa makusanta, ko kuma wasu malamansu, Allah Ya had'a mu a darussalam.


_*I was crying when I was typing this chapter. Ba wai kukan littafin ba, a'a, kukan rayuwa kawai, kukan mutuwa, wacce dole zata zo mana komin daren dad'ewa. Ni, ke, kai, ku dole wata rana zata d'auke mu. Me muka tanadar mata? Idan yanzu Allah Ya zare ranmu, me muka shirya na had'uwa da Mahaliccinmu?*_


wattpadians, comment on each line. Ko da ban samu damar baku amsa ba, kuna raina.

Thanks.

Pinky durling??
RAZ 2
adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *