Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Saturday, 24 August 2019

AZUMIN ILU COMPLETE (hausa romantic novels)

adsense here
AZUMIN ILU COMPLETE (hausa romantic novels)

COMPILED BY

Asha karatu lpa duk wanda ya/ta karanta baiyi dariya ba dan allah yasanar dani nikuma xanyi masa kyauta wadda zai sha mamaki wlh.


*B.W.A*

πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚
*AZUMIN ILU*
πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚

Page 1&2

     *MAMAN MAMY ce nace Ku huta*✍

*sadaukarwa gareki aminiyata Kawar Alkhairi ga nawa goron azumi tunda ban sayi sugar da gero ba*πŸ˜†A guje ya shigo gidan har yana karo da tumakan dake tsakar gidan...shigar jikin shi kawai zaka kallah kasan cewa ILU ko a kauyen su babba ne wurin shirme da shiririta.. Wani zabgegen wando ne jikin shi mai irin felar nan na mutanan da ....ga wata bajejejiyar Riga wadda ake kira da Yar shara yasha wani kafcecen glass da ido dayane kawai ke gani ........kai fans ILU fa babba ne a kauye an su ..cikin nan nasa kato dashi kamar shi kadai ake cidawa gidan ......

Haba ILU baka gani ne zaka shigo mana haka ...ko dai biyoka akayi ne.... Wata Yar tsohuwa ta fara masa fada .....kai dai ba ranar da zakayi hankali ILU...... Kinga iya niba wani dogon zance na tambaye ki ba ....wai jita jita naji agari cewar gobe ne zaa tashi da azumi acan santar na kyallu na jiyo.....

Yar dariya iya tayi ...kai ILU amma bakada dama ...yanzu murnar zuwan azumince ta da ka shigo haka.... Eh da gaske ne in Allah ya amince gobe ne zaa tashi dashi sai kazama cikin shiri .....

Wayyo Allah wayyo na shiga ukku na lalace shi kenan lokacin mutuwa ta yazo na shiga ukku ni ILU ...ya fada tare da dukewa kasa yana matso kwalla......

Kai ILU lafiyarka kuwa ....yanzu AZUMIN ne kakema wannan ihun ...oh ni salame Allah na gode maka......

Haba iya ba dole inyi kuka ba... Kina gani da safe Kofi gudu nake sha na koko inci dumamen tuwo kwano guda ....da rana ta daga zani rumfar shehu inci awara ta nera Dari... Da rana in kwashi kwano guda na abinci ...kafina mangaruba inbi na sauran yaran gidannan in cinye in malam ya dawo yaci ya rage ya bani... Da daddare bayan naci tuwo kwano agida saina fita na ni almajirai bara inkara cika cikina.... Yanzu sai ace nida abinci sai anyi sallar magrib ai lokacin na mutu kawai.....

Malam ne ya babba ke da dariya dama tun sadda ya shigo ILU ke bayani... Itama iya dariyar takeyi .....ato shiyasa Nike maka fadan cin abinci amma bakaji... Kome na noma a gidannan Kaine ke cinye shi ...nikam nayi murna da zuwan WATAN RAMDAN wata mai falala da rahama kai yanzu ILU duk bazaka tuna da niimomin da zasu sauko ba sai ta abinci kake ......malam ya fada dariya cike da cikinsa......

Cikin kuka ILU ke fadin wllh malam nayi murna da zuwan shi ...ni yauma zan fara nawa ...amma can cikin zuciyar ILU ba haka abin yake ba tunanin yunwa kawai yakeyi .....uhm kai dai kasani azumi ba fashi sai kayi talatin cif ko zaka mutu kaji dai abinda nace maka ...suma mutanen kauyen sun huta da fitinarka na Dan wani lokaci.... Malam ya fada tare da shige wa cikin dakinsa yana dariya....

Iya CE ta dubeshi.. Ni kaga da wannan kukan da tashi kayi ka amso min nikan tuwo shagon talle daya fiye maka ...insamu inmana abincin sahur.....

Jiki ba kwari ILU ya mike yayi waje yana baje fantalon wandonsa....

Duk inda yaga gungun mutane sai ya tsaya yace... Ato WATAN RAMADAN gobe sai Ku shirya don yunwa badai Kanwar Babar mutum bace bare ta raga masa

Sai mutane suyi dariya suce ..ILU da kanka kake ...mai cikin Zane sai akwashe da dariya shikau gogan ko ajikinsa .....

Maman MAMY CE nace Ku huta don AllahπŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜†πŸ˜†

*B.W.A*

πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚
*AZUMIN ILU*
πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚

        *peg 2*

*MAMAN MAMY CE*✍

*karfa acika ILU da dariya saboda bashi kadai bane akwai masu tsoron yunwa*πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚

*gaisuwa ga yan BRRILIANT*⚜hantsi leka gidan kowa

Ahaka yaje ya dakko nikan ya dawo sai shela yake gobe azumi kamar maigari ya sashi πŸ˜‚

Yana dawowa sallar magriba ya tule kasa kusa da Kanwar shi asabe .....dubanta yayi wai iya bata gama sanwar bane .....dubanshi tayi kai ILU kayi mata hakuri yanzu zata gama aci ci ...ko kallon inda take bai kara yi ba yacigaba da kallon inna na tuka tuwo .....

Loma yake kamar ya kwana bai Ciba ....in kaga tuwon da aka jibgomasa saika rantse da Allah na mutum ukku ne ........

Iyah...Allah dai yasa kin yi tuwon nan da yawa saboda sahur ...kinsan sai naci Wanda ya linka wannan saboda kar inji yunwa sosai ....kinga salon way on nawa ko asabe ya kalleta tare da afka wafceciyar loma bakinsa yana side miyar da ta biyo ta bayan hannunsa .....

Dariya asabe tayi ba wani wayo ILU ....duk wannan tumbin da kake fama dashi saiya sabe.. Ta ida maganar tana kumshe dariya ....shidai baice komai ba yaci gaba da saka lomar tuwonsa baki... Aishi komai dai dai yakeji.....

Kade kaden da yaranmu suka saba lokacin azumi domin tada sahur.... To haka abin ya kasance a kauyen Ku suma.....malam ne ya hau tashin ILU dake kwasar bacci ......

Jamaa kuzo kuga uban dumamen tuwon da ILU ya kwashe su malam kallonsa kawai suke ....asabe kam kagara tayi gari ya waye taga yadda ILU zai kasance......

Washegari yana dawowa sallar asuba ya koma ya kwanta ...cike da tunanin yau ba batun shan koko ....

Misalin 10 na rana ya tashi ...cikinsa ya fara kiran ciroma ...gashi yana tashi yaje yayi uban tulin kashi kunga kenan ba maganaπŸ˜†

Ragwaf ya dawo ya zauna karka shin bishiyar bedi dake tsabar gidan yana kallon yadda tinkiya ke kwasar dusa abinta..... Iya ya kalla dake shara...

Wai iya meyasa su tumakai basu yin azumi ne yanzu jibi yadda shegiya r tunkiyar nan ke cin dusa kamar da gayya takeyi saita wani kalle ni saita cika baki don inji haushi .....ya fada yana Harar tunkiyar da batasan Allah ma ya aje shi ba ....

Dariya iya tayi sosai ....ILU kenan kai dai ka tashi kayi wanka ka fita can wajen abokanka Ku cigaba da salatin annabi ...kar yunwa tasa ka mazgar min tunkiya nasan halin ka ......

Mikewa yayi tare da sakin tsaki ......yunwa nata kwalkwalar sa ....jibarta da kunnuwa fala fala... Wai da tunkiyar yake

Ita dai iya batace komai ba saboda tasan abinda ke damunsa...

Afujajan ya fito wankan ya samu wata Yar jallabiya ya sagala da wata doguwar cafzaha yayi waje .....saura kadan ya bige asabe da sauri ta matsa tana dariya .....

Santar na kyallu ya nufa inda abokansa ke zama.... Tun daga nesa suka hau yimasa dariya suna cewa....
Yayi ILU n iya mai cikin Zane yunwa dai ba Kanwar  babarsu mutum bace bare ta raga masa.....

Wani wahalal Len yake yayi ...ya nemi wuri ya zauna ya fara Jan cazbaha yana kallonsu baice masu kanzil ba .....dariya basiru yayi aaa ikon Allah mutumenfa da gaske n gaske ibada yake Ku kalla salati yakeyi ILU ILU ILU na malam .....gaba daya suka babba ke da dariya....

Kudai zauna nan ...ILU ya fada a wahalce yana zare idanu .....

Anata fira ILU kam anyi tsit sai salati akeyi... Can su kaga ILU ya hau lumshe idanuwa... Aa ILU bacci zakayi basiru ya tambaya....

Aa basiru babacci zanyi ba bari dai agama min hisabi cikin cikina da alama hanjina basu da kwari .......

   πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚


[5/14, 10:50 AM] ابو Ψ΅Ω„: *B.W.A*


πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚
*AZUMIN ILU*
πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚

         *peg 3*
*MAMAN MAMY CE*✍


*Allah ka sada mu da alkhairan dake cikin wannan wata mai albarka Allah ka bamu ikon yin duk wasu ayyuka masu lada acikin wannan wata na RAMADAN*πŸ™πŸ™πŸ™πŸ™


Dariya suka sa masa gaba daya ....sannan sukaci gaba da hirarsu akan abinda ya shafi watan na RAMADAN .....ahaka har aka kira sallar azahar ..ILU kam na jinsu amma ko kallonsu baiyi bare yasa baki .....


Basiru ne ya dubeshi mutumen ankira sallar azahar ka tashi muje muyi sallah sai ka wuce gida kadan huta .....duk cikin dariya yake maganar....


Kamani basiru wllh ashirin ashirin Nike ganinku ...ILU ya fada yana kyafta idanu... Dariya sukasa gaba daya ...ahaka suka kamashi suka nufi masallacin mai gari ....kamar Wanda bai lafiya ...duk Wanda yace lafiya ILU sai yace ...yunwa Ai ba Kanwar babata bace bare ta ragamin sai mutane suyi dariya ..suce da sauran ka ILU tunda bakin bai mutu ba......
Sallah akeyi amma liman sai jawo dogayen surori yake ....kafafuwan ILU rawa kawai suke ...saura kadan ya sallame sallar yayi tasa shi kadai ...hawaye kam wani nabin wani ga wata rana mai zafi da akeyi garin....


Ana kammalawa yayi kwance yana lumshe idanu... Wllh basiru liman mugu ne dayake ya lura da yanayi shine yake Jan dogayen surori ...Wanda ya kara bin sallar shi ..πŸ˜‚


Da kyar basiru ya gimtse dariya ya samu yayi addua ...sannan ya dubi ILU kayi addua kuwa mutumen kake gulma ...kuma ba kyau gulma ana azumi kai ko baa azumi gulma ba kyau .....


Nayi addua mana basiru nace Allah ya nuna min asha ruwa ..wllh yau abincin da zanci ba karami bane ....kuma ni ba gulma Nike ba gaskiya ce ....


Ahaka dai suka rakoshi gida sai ruwan balai yake ma liman kamar shi yasa shi yin azumin ...su kau ba Wanda ya kula shi saboda kowa yasan Matsalar shi ......


To ILU sai anjima mun biyo maka zuwa waazi n da malam zaiyi kafin faduwa r rana..... Kar Wanda ya biyo min kuje kawai ni naje idan ranar ta fadi Ai inaga duk dayane ko... Ya fada yana hararar su ....aa yi hakuri malam ILU abin bana zafi bane...

Na zafin ne ...shin malam din ba ubana bane innaga dama sai ince ya yimin waazin cikin gida ba shikenan ba... Ya shige cikin gida yanata ruwan balai... Abokan kuma suka juya suna masa dariya .....
Yana shiga sukaci karo da asabe zata fita.... Wani wawan bugu ya kai mata cikin zafin nama ta kauce tana dariya ....waike bakida hankali ne baki ganin mutane ...yi hakuri ILU ba gani ba ta fada tana gimtse dariya.....


Wata uwar harara ya gallara mata yayi gaba yana kallon iya dake sama dabbobi abinci... Ga matsayatan da suka fi kowa cin abinci ....amma sai ace ILU ya cika cin abinci ...ga sunan yini kike basu abinci ....iya CE ta dago tana murmushi....


Haba ILU ya zaka hada kanka dasu ...sufa dabbobine kai kuma mutum ne .....eh naji ni mutum ne amma Ai yunwa duk iri daya CE kuma duk abinci abinci ne... Haka kawai sai adameni da su dabbobi ne ...ya wuce dakin shi yana tijara..... Malam ne ya dubeta dake can gefe yana lazimi...


Ki daina biye masa azumi ne dai sai yayi talatin cif koda yunwar zata kashe ka ...katon banza bai aje komai ba sai katon ciki......
Ana kiran sallar laasar ne malam ya leka dakin shi ....ILU tashi kayi alwalla mu tafi masallaci ....malam ka yafeman mutuwa zanyi ILU ya fada yana yan kwalla ....eh Ai dama kullu nafsin zaikatul maut dukkan mai rai mamaci ne ....kazo kayi sallar sai ka dawo ka mutun tunda lokaci yayi ......


Mikewa ILU yayi yana fadin ...eh dama Ai ka kagara in mutu tunda kace ina cinye maka hatsin daka ke nomawa ...to ka daina murna saina ci abinci sosai a duniya zan mutu ...oh ni ILU Ashe anyi Sukuti aga na mutu ahau murna to ina nan ......


Shidai malam murmushi kawai yayi ya wuce gaba ...inka gama shawara da mutuwar ka fito mu tafi masallaci saura ka batamin lokaci .......


*muje zuwa*
             *labarin ILU*
[5/14, 10:50 AM] ابو Ψ΅Ω„: *B.W.A*

πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚
*AZUMIN ILU*
πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚

       *peg 4*


*MAMAN MAMY CE*.....✍


*hhhhhh ILU na wuta ina binshi da gas*🀣🀣🀣🀣🀣🀣🀣
Ahaka ya gama surutansa ya  tashi jiri na dibar shi ya yi alwalla idanuwansa har wani lumshewa sukeyi saboda tsabar yunwa .......

Ahaka suka tafi masallacin sai rangaji ya keyi shi kau malam murmushi kawai yake yi ....wani bangaren kuma tausayin ILU yakeji sosai saboda yadda yayi sabo da abinci kamar jakiπŸ˜‚


Ana kammala sallah ILU ya baje yana ta maida numfashi ...Nan take jamaa suka baibayeshi suna sallalami ....da yawansu dariya suke masa saboda sun San abinda ke damunsa
..malam ne ya iso da sauri


Sannu ILU bakada lafiya ne... Daga kai kawai ILU yayi ya kasa cewa komai... Maigari ne ya dubi malam... Gaskiya malam ILU ya aje AZUMIN nan tunda bazai iya kaishi ba shiga addinin Allah saukine dashi ko ba yanzu ba sai ya rama tunda lalura CE... Shiru malam yayi yana kallon ILU dake wani kara fitar da numfashi shidai yasan halin abinsa da anbi ta tashi da an kyale ILU yakai AZUMIN nan .....mutane ne suka dinga magana akan abar ILU ya aje AZUMIN ...ba da son ran malam ba ya amince ya koma gefe ya yi zaman shi ganin yadda zaa kaya da ILU n malam ...
Maigari ne ya Ciro naira Dari ya mikawa basiru ....ungo nan jeka siyo mashi fura ta talatin nonon ashirin sai ka dawo mashi ruwan sanyi na goma ka kawo min arbain ......

Da sauri akaga ILU ya mike ...alkuran furar talatin bazata isheni ba ...ka bari kawai ya siyo min ta duka nayi maleji... Kuma ka siyo min ruwa masu sanyi gaske inba sanyi sai ka mai dashi ....kuma duk cikin ku ba Wanda yayi kwantan abinci gidansa ya hadomin dashi ...fisabilillah wa ILU jamaa...... Shiru akayi nadan lokaci sannan jamaa suka hau dariyar ILU shi kanshi basiru tsaye yayi ya kasa tafiya saboda dariya....
Shi kanshi maigari saida ya dara bare kuma mal dake can gefe dama yasan zaayi hakan.....

Am basiru bani nerata Dari ...jamaa kar Wanda yaba ILU abinci Ku kyaleshi ya kaishi tunda shi raggon banza ne baida jumurin yunwa
......

Komawa kasa ILU yayi ya kwanta yana fadin....to Ai shikenan Ku bari in mutu kowa ya huta dama yan kauyen nan duk kun tsane ni kowa ILU kowa ilun malam....
Ahaka kowa ya watse ya barshi nan kwance kamar matacciyar sanuwa sai katon ciki da yayo sama kamar tulin kayan wanki .....Sai misalin 5 na yamma ya lallaba ya mike ya nufi gida... Jamaa nata masa sannu suna dariya kasa kasa saboda kowa AZUMIN na gwalar sa amma ba kamar ILU ba .....


Iya ya iske zaune tana gyara waken kosai .....yanzu tsakani da Allah iya sai yanzu zaafara aikin shan ruwan ...jibi fa saura kadan rana ta fadi to wllh aka kira sallah Baku gama ba zaa kwashi yan kallo a gidan nan....

Itadai iya batace komai ba itama yunwar ta isheta ....


Asabe ya kalla dake tace kullu... Waike meyasa baki aiki da sauri ne dubi yadda kike aiki kamar wadda kwai ya fashewa aciki .....

Shin ILU zo kayi in sauki ne abun ....afusace ya nufeta.....

*Allah ya kawo mana watan RAHAMA lfy*
[5/14, 10:50 AM] ابو Ψ΅Ω„: *B.W.A*

πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚
 *AZUMIN ILU*
πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚
     
      *peg 5*

*MAMAN MAMY CE*.....✍
Nace Ku huta fans😍


*wannan peg nakune masoyan ILU acici mai cikin Zane*🀣🀣🀣🀣

Hakuri ta hau bashi ....na tuba ILU bazan sake ba... Ganin yadda ta tsorata yasa ya wuce abinsa yana masifa kamar shi kadai ke azumi kauyen ......


Misalin 6 na yamma ya fito sai dukewa kasa yake yana dafe cikin shi idanuwa sunyi jajir dasu ....malam ya hango ya Debi uban kosai aroba zai fita rabawa almajirai...

Da gudu ILU ya isa gaban shi ya riko robar kosan yana maida numfashi .....

Haba malam ya mu bamu koshi ba zaa kaiwa na waje kosan ya kalla ya kuma kalli sauran Wanda iya ke toyawa ....koni kadai zan iya cinye wannan kosan ban koshi ba shine kuma sai ahau rarraba dashi.....


Murmushi malam yayi ...haba ilun malam Wanda ka bada shine naka... Wanda kaci Masai zaije.... Yanzu kai anaka haukan ko barinka mukayi da kosan nan duka zaka iya cinye shi?????


Wllh tsab zan cinye shi har in nemi kari ...kuma da kace Wanda naci Masai zaya Ai nan ma wata sadakar nayi ma tsutsotsin dake cikin Masan tunda su zasu cinye kashin da nayi ...don Allah malam kayi hakuri kabar mana kosan mu in zan bar kosai guda yayi kwantai Allah ya tsine man ......


Dariya malam yayi ka fahimceni ILU ita sadaka ba lallai sai ka wadatu ba zaka bayar ....a musulunce anfi so ka bayar da abinda kafiso to Allah zai Baka lada sosai ....ka bada kadan Allah ya baka Wanda ya fishi ..sadaka maganin talauci duk mai sadaka Allah bazai taba barin shi cikin talauci ba zakaga da ya bayar Allah zai mayar masa da Wanda ya fishi sannan ga lada.. Bare cikin wannan watan mai RAHAMA .....ILU ka bari abada sadakar nan ni zan hada maka da nawa kason saika cinye ni nasha koko...


Sakin robar ILU yayi yana turo baki.... Abasu amma Allah da kasonka zan hada inaji ina gani bazaa kware niba .....murmushi malam yayi ya Ciro nera hamsin aljihunsa karbi wannan maza tashar alu ga kankara can ankawo ka siyo mana mu jika musha....A wahalce ILU ya karbi kudin ya fita yana rangaji ..malam yabi bayansa da robar kosan da zai rabama yara ....saida ya tsaya ya gama Harar almajiran sannan ya wuce tare da fadin munafukan banza ......
Tun daga nesa ya hango Layin da ke akwai can ya hango basiru da mudi abokan sa nata bin layi ...dariyar mugunta yayi duk da uwar yunwar dake kwalkwalarsa .....Can ya zagaya bayan mai sayar da kankara ya fara rada masa ....sannu da aiki bawan Allah dama maigarine ya aiko ni abashi kankara ....dubanshi mai saida kankara yayi ....yaga ILU yaci magani kamar bashi ba ....ba musu ya karbi kudin ya bashi kankara ukku harda kyautar daya gudu kenan....ILU na dariya ya daga ma su basiru hannu yayi tafiyar shi .....

Lokacin daya isah har sun gama komai suna zaune sunata laximi ...mika masu yayi yai kwance kasa yana fadin... Astagafirrillah da karfin gaske.. Malam ne ya dubeshi ILU kayi cikin zuciya mana...


Aa malam bari inyi afili kunfi sanin halin da Nike ciki na yunwa....
[5/14, 10:50 AM] ابو Ψ΅Ω„: *B.W.A*
????????????
*AZUMIN ILU*
????????????

       *peg 6*
*MAMAN MAMY*.....✍

*sadaqa cikin azumi Allah shine zai baka lada.. Taimaka wa Wanda bai dashi baka fadi ba Allah yasa mudace*


Uhm ILU kenan ...yanzu tashi kayi alwalla mu tafi masallaci ankusa kiran sallah .....

Ba musu ya mike yayo alwalla ya Debi kosai guda goma ya zuba cikin aljihu ya dubi iya da tayi Sukuti tana kallon ikon Allah.....sannan ya kalli asabe dake harararsa ...saura asa guda goman nan cikin lissafi nasan halinki asabe kina iya cewa cikin kaso na.. To dandano ne ....Ku saiku dauki guda biyu biyu tunda tsakani da Allah Baku kaini shan wuya ba ...koma ba haka ba Ai dama kasona yafi na kowa cikin gidannan ........sudai ba wadda tace masa ci kankaMalam ne yace muje ..kai kasani ...har sun fita ya dawo... Iya karfa amanta kason malam nawa ne ..ehhe kar ace min an mance ....ya kuma juya ya fita ba tare daya jira amsar su ba .....Masallaci suka nufa ...daukacin mazan garin na can domin yin sallah sai sadakar dabino da ruwa masu sanyi akeyi ...don hasana saida ILU ya karbi ruwa ukku ya rukunkume jikin shi malam na kallon shi baice mashi kanzil ba .....Saura yan mintina liman ya tashi ya fara gyaran murya yana Dan zagayawa lokaci ya karasa.... ILU ne ta dubi basiru ...uhm dubi liman wllh abin shi harda gayya lokaci yayi ya kira sallah amma ya kiya ....murmushi basiru yayi kai ILU bakada dama ...lokaci baiyi ba da da yayi daya kira ..
.


Har ILU zaiyi magana yaji liman ya fara addua cikin lasifika ...da sauri yakai ledar ruwa bakinsa da niyyar da yace allahu! Ya datsa ma ledar pure water hakora ko tunanin addua baiyi saita abinda zaisa ma cikin shi .....basiru ne ya rike hannun ...mutumen a taimaka ayi addua tukun ...An kwala kiran sallah ...da sauri ILU ya hau addua bai gama wata wata ke zuwa ....ya Riga kowa FASA ruwa zuka biyu yayi ma ledar ya shanye... Ajiyar zuciya ya saki sannan ya dakko wata ledar zai FASA... Basiru ya katse sa...Kai ILU saika cika cikin da ruwa ka rasa inda zakasa abinci ...ina ba dai cikin ILU ba
..Ai nan da kake gani basiru komai da isashen wurinsa a cikin nan nawa ....

Basiru bai kara cemasa komai ba ya kyaleshi ya shanye ruwan kafin sannan ya tamne kosan daya dakko guda goma Dan ball I ya na basiru ......Ana kammala sallah ILU ne na farkon mikewa yana fadin... Nidai malam nayi gaba saika taho kunsan Allah ma yace a gaggauta buda baki ....shiru malam yayi tunda aka dauki AZUMIN baiji ILU yace Allah yace ba sai yanzu da yake maganar ci CE is... Girgiza kai kawai yayi yaci gaba da adduar sa .... Mutane kam dariya suka hauyi kasa kasa cike da kaunar ILU....


Yana fita ya sheka da gudu yana fadin ....iya gani nan azubamin koko cikin kwanon shan ruwa ....iya gani nan ....
Asukwane ya isa gidan saura kadan yayi kwllo da bokitin kokon ....azabure iya ta dubeshi ..lfy ILU waya biyoka ...

Yunwa ta biyo ni kinsan tun dazu take bina ....ya fada tare da nufar kayan da yaga an shirya masa gefe... Dama jikin iya har rawa yakeyi ta sallameshi kafin ya iso....
Zaunawa yayi tare da bude kwanon kosai ganin shi yayi himili dariya yayi yasan cewa da kason malam aka hada masa ...kai iya Allah ya biyaki da ana samun tsaffi irinki da bayin Allah irinmu sun more ...,

Itadai iya batace komai ba tasan anjima kadan zaa amshe yabon.... Bibbiyu yake tura kosan yana hadawa da koko ana haka malam ya shigo da kwano a hannu.,..


*muje zuwa*
πŸ˜‚πŸ€£πŸ€£πŸ˜‚πŸ€£πŸ˜‚πŸ€£
[5/14, 10:50 AM] ابو Ψ΅Ω„: *B.W.A*


πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚
*AZUMIN ILU*
πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚

       *peg 7*
*MAMAN MAMY CE*.....✍

Nace Ku huta πŸ˜†


Saida malam ya gara zama ...sannan Iya tayi mashi barka da shan ruwa asabe ma tayi mashi banda ILU ko kala baice ma malam ba sai zubawa uwar hanji yakeyi ......


ILU barka da shan ruwa ...malam ya fada cike da zolaya dai dai lokacin daya kai kofin koko bakin shi .....a haba malam duka yaushe nasha ruwan bare afarayiman barka tukunna dai...ILU ya fada yana kara dagwalo yaji ga kosai.....Wasa wasa ILU ya kasa cinye Rabin kosan nan... Duk hadamarshi saiga ila na zare idanu gashi daya motsa sai cikin ya bada kululu alamar ruwa ya cika cikin...bare kunsan azumi Nada haka sai kaga kamar zaka Iya cinye Abu amma sai ka kasaMalam yana kallon shi yanaso yayi dariya amma yaki yarda ta fito ....
Wai Iya kodai AZUMIN nan da nayi an rage min fadin cikina ne ...duka dubi Dan kosan da naci da koko n da nasha amma naji cikina ba sauran wuri gashi banci abinci ba ......


Dariya Iya tayi ...wa zai rage maka fadin ciki ILU... Kawai daga yin azumi sai ciki ya ragu ...uhm dama haka azumi yake sai kaita hadama amma abinda zakaci ba wani bane .....

Ikon Allah ILU ya fada yana satar kallon malam dake tamnar naman kaji Ashe sune a kwano ....


Tuni miyan ILU ya tsinke ..dubarace ta fado masa da sauri ya dauki kwanon kosan ya isa gaban malam ya dukar da kai kasa ...


Barka da xshan ruwa Babana.... Kasan soyayya ta da da uba bazan Iya cinye kosan nan da kason ka ba dama wasa Nike ma Iya ...Itakuma ta hada min da naka ..INA wane ni ...tuba Nike dattijo mai ran karfe .....


Wllh malam karka kulashi ..wayo ne dashi karya yake.. Ka tsare shi ya cinye shi tunda shi yace yaji ya gani ....asabe ta fada tana ma ILU dariya kasa kasa....


Kai kai wai asabe meyasa ke Yar bakin cikina CE duk gidannan kin tsani kiga INA warwasawa ...yinin yau INA lura dake kina min dariya to wllh ki shiga hankalinki dani .......

Ya isa haka malam ya dakatar dashi... Naji ni yanzu na koshi da kosai kaje ka ajiye anjima kaci naci guda biyu wurin salame ya isheni... Amma daka hana abada sadaqa da duk ina zaka kaishi ...malam ya fada tare da yagar naman kaza....


Kuttt! ILU ya hade miyau ...kai dai bari malam Ai gobe in zaka bada sadakar aba harda kaji ..ILU ya fada yana kallon naman kaza yana  murmushin dole ....

Malam baisan sadda dariya ta kubuce masa ba... Duk yagama dago ILU... Kara cirar naman yayi ya mika masa kwanon ...ungo anshi ka diba ka basu sauran.....Jiki na rawa ILU ya karba ya mike tsaye tare da fadin godiya muke ya malam... Saida ya yagi kafcececiyar  tsoka sannan ya dubi asabe.....Wllh asabe yau sai da naga kana nan malaikun mutuwa da manyan nagani da tuni na mutu.... Uhm ni ina ruwana koma waka gani ...nidai ka bamu kason mu sai kaci gaba da bamu labarin ......


Kash! Asabe kin cika kwadayi ki rage wllh ....wata tsokar ya kara yagowa ...asabe! Ya fada da karfi . .yau anyi rana yau naji ki shirya kamar ma banda makogwaro naji.... Oh! Ni salame.. Iya ta fada tana kallon ILU ...


Ai yi hakuri Iya karbi kason ki.. Kafafuwa ya miko mata ...taki karba tacigaba da hara rarsa ..ungo mana Iya abinda yasa na baki saboda na taba mafarki ...ance in tsaffi mata nacin kafar kaza to kafafuwansu za suyi kwari sosai ...kinsan ita kaza akwai kwarin kafa ...bare ke dazu da kina aiki kina dingisa su ji nayi kamar insa hama in bigesu kowa ya huta.....


Ai da kasa hammar ka dai daita minsu Iya ta fada tana dariya tare da amsar kafafun tasan karamin aikinsa ne ya hanasu duka.....


Ke kuma asabe ungo kai.. Ya mika mata kan kazar ...saboda na lura irin kanku daya da kaza ...kinga kin kara hankali ma ...wani dogon tsaki asabe taja wllh banci ...Alhamdulillah ....shiyasa kike birgeni asabe biya ...komawa yayi zauna yaci gaba daci... Asukwane asabe ta warci irin bayan nan ta ruga daki ta turo kofa ....


Dariya ILU yayi haba yarinya bashi kikaci ...Iya kau da malam sai dariya suke tsokar dake hannun malam yaba Iya ta kara...


Kiran sallar ishai aka hau kira... Malam ne ya dubi ILU tashi kayi alwalla mu tafi masallaci.....*Maman MAMY CE*
[5/14, 10:50 AM] ابو Ψ΅Ω„: *B.W.A*

πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚
*AZUMIN ILU*
πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚
   
      *peg 8*
*MAMAN MAMY*.....✍
To malam ILU ya fada tare da yin wata mika ta mussamman... Iya ga kosai na nan a ajemin saura ki badashi sadaqa nasanki da tausayin Dan almajiri ....wa ni na isa in taba abinci ILU ...iya ta fada tana murmushi ....

Ahayye sama duniya tayi dadi!!! Haba ina amfanin yunwa da zan ganta ido da ido ...saina kashe ta ..koni ko ita wllh iya....

Har malam zaiyi magana sukaji ankwada sallama kofar gida... ILU fito mu tafi massalaci ..muryar basiru yaji daga kofar gida...

To basirun inna mai yan kunnuwa gani nan.... Lol! Wai ILU yaushe zaka daina radawa mutane suna ne ...iya ta fada..

Uhm kyaleshi yayi Ai ansha ruwa da dazu ne ko bakin shi bakiji sai idanu.... Aa malam wllh bani kadai nasha wahalar azumi ba ..tsaya kaji..sai kuma ya fara dariya ..ina ganin maigari dazu zai shiga gida saura kadan ya bige kai da alama bai ganin kofar gidan saboda yunwa πŸ˜†πŸ˜†

Dif wutarsu ta dauke mussaman malam da dariya ke cinsa ..ILU ba karamin sha kiyi bane... Saida ya gama kwasar dariyar sa sannan yace ....shi kuma liman dazu ana sallar azahar sau biyu karanta bisimilla ...nan ma wata dariya r ya saki .....

Ita kuma iya ...wani Dan karamin icce malam ya fizgo ya kaimashi bugu ya kauce ..yayi waje yana fadin muje basiru tun kafin tsohon nan ya kaini kasa....

Aida ka tsaya Dana koya maka hankali ...Ai dama nasan da yagama shsrrance yan waje zai dawo kanmu ...yana gamawa dake zai dawo kaina tunda shi jairine ....Ai ni garama ayita AZUMIN mun samu saukin ka ....

Yar dariya iya tayi ..uhm Allah dai ya kimtsa ILU v..kullum shirmensa gaba yake yi ....

Alwalla malam yayi yabi bayansu zuwa masallaci.  .....

ILU fa ya mike duk ya ishi mutanan kauyen da tsokana ba Wanda yake ragamawa ba babba...koda aka gama sallah lulawa sukayi cikin kauyen daukar magana shida abokan sa ..bai dawo gidan ba sai wurin goma na dare ...


Sanda ta hauyi yadda kar malam yaji sadda ya dawo ....iya CE ta fito fi tsari saboda har sunyi bacci ..inwa tagani tsaye cikin razsna tasaki butar tare da fadin auzubillahi waye nan....

Da sauri ILU ya fito karta tona masa asiri ..nine iya ..kai kudai mata Allah yayi maku tsoro wllh kin kuma san ko barawo ne ko kallon arzuki baki Ashe shi ba....

Haka ya ratsata ya wuce yana mita saura inji zancen wurin malam wllh saina ballswa tunkiyarki kafa... Aa bazai ji ba ni na isa iya ta fada da karfi... Saboda tasan in ILU yace zaiyi Abu to sai ya aikata shi ....

Saida ya cinye sauran kosan da tuwo mai yawan gaske sannan ya kors da koko ya kwanta ....

Tun da suka tashi sahur asabe ke faman tada ILU amma yaki tashi saima gyara kwanciya yake ....

Malam ne yace ..kyaleshi asabe jekiyi sahur dinki.. Ai gobe ya sani yayi csahur din ma ya aka kare bare baiyi ba ...


Asabe kam komawa tayi taci gaba da sahur dinta ...iyace ta mike Umm bari inkara tada shi ni kadai nasan balain da zai mana gobe ....

Ki kyaleshi ya Dade baiyi ba laifin wa ..malam ya dakatar da ita.. Mikewa tayi aa malam nasan fitinar ILU kamar yunwar cikina bari dai in gwada .....


Iya ta tada ILU ta tadashi amma ILU yayi kunnen uwar shegu da iya haka ta hakura ta dawo taci gaba dacin abincin ta kafin lokaci ya kure .....
Haka dai suka gama suka kwanta ba tare da ILU ya tashi sahur ba..
*muje zuwa dai fans.. Kunsan akwai bidiri ILU zai tashi da dorere*πŸ˜†
[5/14, 10:50 AM] ابو Ψ΅Ω„: *B.W.A*

πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚
*AZUMIN ILU*
πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚

     *peg 9*
*MAMAN MAMY*..✍
      Nace Ku hutaπŸ‘πŸ»*wannan peg nakine zuzun Alkhairi ...Allah ya raya mana hafeez da hanan*🌹🌹
A firgice ILU ya tashi ji yayi kamar ana kiran sallah.... Da gudu ya nufi dakin Iya yana kwalamata kira... Iya Ku tashi wllh lokaci ya kusayi Ku tashi muyi sahur.. Gani yayi zuwama dakin Iya bata lokacine sai kawai ya wuce kicin da makekiyar rigarsa yana fadin....


Nidai duk Wanda bai tashi ba Matsalar shi CE ..nidai innayi sahur kowa ma ya gane sai ayita tadaku kunaji kuyi banza da mutane ...

Yana fitowa da kwanon abinci malam na fitowa dama sallah yake yanajin duk abinda ILU ke fadi.... Kardai ka kuskura ka ci abincin nan saboda lokaci yayi ...


Sakin kwanon ILU yayi woyyo Allah na shiga ukku ni ILU yanzu shine zaaki tadani wayyo Allah... Saiga ILU na ruwan hawaye ....
Iya CE ta fito da hijab jikinta ...haba ILU sai kace ba namiji ba don bakayi sahur ba sai ka ishemu da ihu sai kace Wanda ya rasa iyayensa ...

Kyaleshi yayi salame wane irin tadine ba a yi masa ba yaki tashi ...kuma dorere ba fashi akan shi tunda ba kanshi farau ba....

Aa malam ba kowane tadi aka yimin ba naki tashi.. Tsakani da Allah an watsa min ruwa anga ban tashi ba ko anturamin lomar abinci anga ban tashi ba... ILU ya fada cikin muryar kuka ...ni banma ga alamun anwani tadani naki tashi ba... Kawai dai kunaso yunwa ta kashe nine shiyasa ...


Eh yunwar ta kashe ka .....Ai wurin
[5/14, 10:50 AM] ابو Ψ΅Ω„: *B.W.A*

πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚
*AZUMIN ILU*
πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚
       *peg 10*

*MAMAN MAMY*..✍

*fans Ku yafeni ganin peg 9 kadan wllh bisa kuskure ya tsaya haka plsss ayi hakuri*
Ai wurin ibada ka mutu... Kaga maza kaje kayi alwalla mu tafi massalaci kar mu rasa sallah ...wucewa ILU yayi yana fadin shikenan dai an cuceni wllh ancuce ni sai Allah ya sakamin ...

Salame dake gefe ..dariya tahauyi kasa kasa .....ahaka yayi alwallar suka tafi massalaci sai gunguni yake shidai malam bai kara CE mashi kanzil ba dama yasan zaa Rina ansaci zanen mahaukaciya ....

Bayan an fito salla h ne aka tsaya ana gaggaisawa liman ne ya lura da yanayin ILU ....aa mutumen lafiya na ganka haka... Daure fuska ILU yayi tare da dauke kai can sama baida alamar ba liman amsa... Malam ne yayi murmushi ..Ai liman yau mutumen ka baiyi sahur ba shine yake wannan tubukurin .. Saiga liman da maigari na dariya harda dukewa jin cewa yau ILU baiyi sahur ba sunsan cewa akwai bidiri kenan ...

ILU kau kara daure fuska yayi basu San cewa dariyar nan ta bata masa rai ba....liman ne ya dafashi haba namijin duniya ka nuna mana kai jarumi ne ba raggo ba ...duk da dai gaskiya bantaba yin dorere ba kusan shekara biyu kenan rabon da inyi dorere bansan wahalar shi ba amma nasan namijin kwarai lfy Lau zaiyi shi ba irinka ba ILU ..yana magana suna dariya da maigari malam ma murmushi kawai yakeyi ...

Wani Dan guntun murmushin mugunta ILU yayi harya hango ta inda zai rama dariyar da liman da maigari keyi masa ....

Tare suka jero da basiru ya baro malam can suna tattaunawa da mai gari ...wllh basiru inna yadda nayi dorere nan mutum hudu  sai sunyi shi sunji yadda naji ...zaro idanuwa basiru yayi dawa dawa ILU...

Da salame da Iya suda suka ki tadani inyi sahur sai liman da mai gari da sukemin dariya bare liman har wani fadi yake rabon da yayi dorere anyi shekara biyu to wannan shekarar zaiyi shi ...abinda yasa bansa malam ba saboda shi dama wani lokacin ko ya tashi sahur din ba abinci yake ci ba sai dai yasha ruwa yacigaba da sallah ...

Kai ILU tayaya zaka hanasu tashi sahur.. Dariya ILU yayi tana kara gyara bajejejiyr rigarsa da tasha faci kala kala... Kai dai sa ido kayi kallo basirun inna... A haka sukayi bankwana kowa ya nufi gida shikam basiru baiyi mamaki ba yasan duk abinda ILU yace zaiyi tofa sai ya aikata shi ....Misalin 8 na safe ya tashi yaufa ILU ba kanta ..tun lokacin ya fara jin yunwa ...fitowa yayi tsakar gida yayi tsaye gidan shiru kowa sai baccin shi yake hankali kwance ....wani takaici ne ya tokare ILU haushin baccin da yan gidan keyi ya keji shi kuma ya kasa yi ....


Ai wllh yadda banyi baccin nan ba bamai yinshi gidannan ..Ai yau an tokalo tsuliyar dodo.. ILU ya fada tare da nufar tumakan dake tsakar gidan ..ya hau kwance su  ..maza kuyi xwaje ...

Saida ya korasu tsaf sannan ya leka dakin Iya ya hau buga masu kyaure ...Ku tashi sai bacci kuke ga tumakai can sun fice daji... A azabure Iya ta mike tare da fizgo wani yagaggen Zane ta rufa tayo waje harda bige ILU.. Ina sukayi ILU yau naga ta kaina ni salame ...da gudu Iya ta fita waje harda tuntube... Dariya ILU ya hauyi dama yasan haka zata faru yadda Iya keji da tumakanta shiyasa bata barin su fita koda yaushe suna cikin gida .....

Asabe CE ta fito da hijab ..haba ILU muje mana mu koro su sai kabar Iya ta fita Ita kadai ...hhhh hhhh kedai jeki asabe biya  ina nan kuje Ku kuro su badai kunyi sahur ba yaci gaba da dariya ...hararshi asabe tayi haba nidai nayi mamaki ace gaba daya tumakai sun kwance kuma lokaci guda ..uhm wllh ILU kaji tsoron Allah yanzu don bakayi sahur ba sai kaita wahalar damu alhalin mun tadaka kaki tashi....


Malam ne ya nufosu da kara... Da gudu ILU yayi gefe yana dariya yi hakuri ya malam ...jeka Ku tafi akorosu dakai  jairi maza Ku tafi tare kaima ka shawo wahalar da zasu sha wurin korosu ....

Da gudu ILU ya fita yana dariya ..lafiya lau malam aini dama yau rayuwata a wahala zata kare ....mutumen da baiyi sahur ba har an tambayeshi wahala ....
Asabe CE tabi bayan shi tana dariya taji dadin yadda malam yayi masa..

Girgiza kai kawai malam yayi ya koma daki ..dama yasan yau abinda ILU zaiyi ba karami bane ...

Saida suka wahala sannan suka samu suka hado kan tumakan ..zanen da Iya ta yafa saida ya dawo bisa kai saboda wahala kafafuwannan sunyi futu futu kamar basu taba ganin ruwa ba... Asabe CE ke fada mata ILU ne ya sake su..

Uhm Ai dama nasan wannan akininshi ne to Ai shima ya wahala tunda dashi aka korosu...

Dariya ILU yayi ...ba komai Iya don na wahala ni dama baccine banso kuyi gaba daya yadda yunwa ta hanani baccin safe to gara kowama ya tashi...


Asabe CE ta kalli Iya itama Iya asaben take kallo .....

*hhhhhh Maman MAMY ce duk Wanda ya karanta novel di nan baiyi dariya ba plss plss ya aiko min da sako zai iso gareni ..ni kuma zan bashi amsa ngd*🀣🀣🀣
*B.W.A*


πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚
*AZUMIN ILU*
πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚

      *peg 12*
*MAMAN MAMY*......✍


*wannan peg na sadaukar dashi dungurigum gareki kawata Lubabatu Umar malumfashi tabbas ki wuce haka awurina kin kuma cancanci yabo ....ngd sosai Allah yabarmu tare*πŸ€πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹Amma wllh ILU bakada kirki yanzu saboda Allah abinda kayi ka kyauta... Mudi ya fada yana share uwar zufar dake keto masa .....


Yo Ai kai mudi ba Wanda ya kaini kyautawa saboda da na jawoku aguje bakin masallaci na ajiye Ku ...kunga da an kira sallah alwallah kawai zamuyi mu shige masallaci muyi sallah .....

Ai kuwa hakane ilun malam ..basiru ya fada yana dariya sai kawai suka babba ke da dariya su duka kamar sabbin kamu ...

Wata Yar bishiya suka zauna suna jiran lokacin sallah ya ida suyi kowa ya tafi gida saboda kwatsetsiyar ranar da akeyi ....

Can suka hango liman buzun buzun da babbar Riga sai zabga sauri yake ya kira sallah ...ya kama kan nan nashi ya nade da rawani da katuwar cazbaha a hannunsa ....ILU ne ya fara magana ....dubeshi kamar Wanda zaya janaiza wllh da liman zai gane daya bar Nada rawanin can ...shidai ba sarki ba ba dogari ba amma sai ya kama kai ya nanndae kam kamar kan rago .....

Gaba daya suka fashe da dariya... Kai ILU amma bakada kirki wllh yanzu liman kake ma wannan sharrin kasan kau duk balain ka bazaka sa ya cire rawanin can ba koda yaushe yana kansa kai har bacci dashi yakeyi....


Uhm yanzu kam zansa ya kwance shi ..bari Ku gani ....mikewa ILU yayi tare da nufar liman a firgice ....

Wayyo liman kunama kunama ...da sauri liman ya hau dire dire yana fadin a ina ilun malam kasan ni kunama batamin da kyau ....Wani ihun ILU ya kara saki gata can bisa kanka ya malam ...a azabure liman ya sauke rawanin kasa ya hau shafa kai cike da furfura yana fadin subhanallah subhannala .....mutane ne zagaye dasu ILU kowa na mamakin tsoron kunama irin na liman ....saida ya gama dire dirensa sannan ya tsaya tare da duban ILU da yayi kasake yana kumshe dariya...

ILU malam ina kunamar ban ganta ba.... Yar dariya ILU yayi nima sai yanzu na lura liman wai Ashe wani Dan kwaro ne ba kunama ba kasan me yin dorere bai gani sosai ....
Aiko mai mutane zasuyi ba dariya ba abokan ILU su basiru harda dukewa kasa  ...shikau liman kunyace ta lillbshi dukawa yayi ya dauki rawaninshi ya Dora bisa kai ya wuce buguzun buguzun yana fadin irinku agari annobane ILU n malam ....Ana gama sallah ...ILU yunwa ta fara cin karfinsa ....da kyar ya Iya fitowa bakin masallacin yayi kwance ...kowa yazo wucewa sai yace sannu ILU malam Ai yunwa dai ba Kanwar Babar mutum bace bareta raga masa ba ...ILU dai ba bakin magana sai idanu....


Liman ne ya dubeshi ...dariya yayi jairi Ai yunwa ita kadai ke maganinka ILU baccin yunwa da wahalarka da zamu sha taka cikin AZUMIN nan ba karama bace ....Ba yadda su basiru basuyi da ILU ba akan ya tashi su tafi gida amma yaki tashi saima ya fara kuka yana kiran malam! Wayyo malam ...da sukaga haka sai suka kyaleshi sukayi tafiyar su saboda malam na cikin masallacin yana jinshi.....


 ILU! Malam ya fada rike da bulalar bugun almajirai ...zaka tashi mu tafi koko sai jikinka ya gayama ka yaufa jairin Yaro raggo ....

Da sauri ILU ya mike yasan karamin aikin malam ne ya zuzzura masa ita ....haba ya malam tama zaayi in kasa tashi Ai dole nane ma in tashi in ina son ganin rahamar Allah ......

Dan murmushi kawai malam yayi ..to muje... Haka malam ya tusa ILU gaba sai fadi yake Allah dai ya tsinewa yunwa yunwa batai ba arayuwa ....


Suna shiga malam ya wuce daki abin shi yabar ILU zaune in war dasu Iya keshan iska.....

Asabe CE ta kalli Iya wai Iya yau me zamuyi ne na budabaki..... Wllh asabe bansani ba amma da ILU zai daure daya auno mana filawa shagon dahiru da sai muyi fanke ....eh wllh don Allah ILU ka taimaka ka auno mana ..asabe ta fada kasa kasa cike da tsoron abinda zai biyo bayan maganar tata ....Asabe! Naam ILU da mai kamfanin da ake filawar da wanda yayi asalin kawota kauyen nan da mai shagon da filawar take dake kanki dake rokona in auno maki Allah yasa Ku rika jin yunwar da nikeji ...ke Allah ma ya tsinema matar data kirkiri fanke a duniya ....

Dariya asabe tasanya itama Iya dariyar take hatta dai malam dake cikin daki saida yayi murmushi ....

Haba ILU daga tace ka auno filawa ayi fanke sai cibi ya zama kari  ...in kuma munyi fanken nan bamu kadai zamuci ba harda kai kilama saika fimu ci .....Iya ta fada cikin sigar rarrashi .....


Uhm iya asabe ta rainani in baccin rain I ita bata Iya zuwa sai ta aikeni niba wanta bane ...kuma da ake maganar hardani zaaci to a hanani mana ga gidaje da yawa a kauye ....wllh Ku kyaleni inba haka ba yanzu nan zan saki tumakai...Aa yi hakuri ILU anbar zance iya ta fada da sauri tasan halin ILU...

*hhhhhh muje zuwa labarin ILU*
[6/21, 4:20 PM] ابو Ψ΅Ω„: *B.W.A*

πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚
*AZUMIN ILU*
πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚

      *peg 13*

*MAMAN MAMY*...✍

```ayi hakuri fans najina shiru kwana biyu labarin ilu na nan don yanzu akazo wurin saboda yanzu muke dai dai da ilu yanzu be duk mai hali irin na ilu zai San yayi aboki```πŸ˜†πŸ˜†πŸ˜†🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
*RAMADAN MUKRAAM*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
*wata mai rahama Allah ka sadamu da alkhairan dake ciki Allah rahamar dake ciki Allah ya sada mu da ita ba don ibadun mu ba ba don halayenmu ba ya Allah*πŸ™πŸ»πŸ™πŸ»πŸ™πŸ»

Itama asabe bata kara cewa komai ba saboda tasan karamin aikin ILU me ya jawo masu aikin dayafi wannan ....bats kara cemasa komai ba ta mike ta ziri hijab tayi waje sayen filawar .....ILU kam kara gyara kwanciya yayi yaci gaba da hamma .....

Koda asabe ta dawo nan ta sameshi kwance sai zare idanu yake kamar tsohon dodo ....asabebiya ya fada cikin rawar murya... Naam ILU yaya ko bazaka kai labari bane ....asabe ta fada tana murmushi ...uhm asabe kenan ai indai ILU bai kai labari ba to ba Wanda zai kai a kauyen nan... Nidai yanzu ki taimaka ki kaimin ruwa inyi wanka shine kawai abinda zan rokeki ....ILU ya fada awahalce ...kamar tace baza tai ba sai kuma ta tuno halin ILU ...zumbura baki tayi ta dauki bokiti ta kwalhi ruwa ta kai mashi ...

Dawowa tayi bisa kanshi ...ILU nakai maka ...yawwah year kanwata Allah dai ya baki miji na gari dazai rika saki dafamin abinci kala ukku duk ranar da naje gidanki ziyara harma inna tashi tahowa yasa ki juyemin sauran aleda ya matsamin sai na taho dashi gida.... Ya kuma bani naira Dari yace insha ruwa ahanya ....

Ba asabe da iya dake tsakar gida ba hatta malam dake cikin daki dariya yake hard a dukewa ......said a ILU ya bari sun gama babbaka dariyar sannan ya mike tare da fadin kamani ki kaini yar kanwata ya fada yana lumshe idanuwa shi kadai yasan azabar dayake sha ....

Dan matsawa asabe tayi ...aa ILU no bazan iya kamaka ba ...bari dai iya ta karaso kila ta iya kamaka amma ba no ba.....

Murmushi ILU yayi ..uhm asabe kenan ai indai sai iya ta kamani zan tashi ai kila saina shekara ban matsa daganan ba ...ai ita waccan tsohuwar ki barta kawai da aukin kula da tumakai wannan fa in akuya daya zata yini kwancewa ta fita tofa iya zata yini itama tana kamota no na rasa gane wannan soyayyar dake tsakaninsu ba.... Dariya asabe ta hauyi hadda tafa hannuwa...

Da ka kalli iya zakasan ran tsaffi ya baci da sauri ta karaso gaban ILU ta fizgi hannunsa guda saiga ILU ya ida mikewa .....wllh ILU ka kiyayi tsufa na wato kai nan gani kake ka fini karfi ko to ba zaa taba had a tsohon kashi da sabo ba .....

Dariya ILU yayi spsai... To ai dama no wasa Nike maki yanzu da cewa nayi iya zoki taimaka ki kamani in tashi da langabewa zakiyi kice kafafuwanki ciwo suke amma yanzu cikin ruwan sanyi kin kamani na mike ....kai asabe wllh tsohuwar nan Nada karfi ...ya fada tare da kyalkyalewa da dariya... Malam me yaji dramar tayi mass dad I sai ya fito waje ya shimfida tabarma ya zauna yana kallon ikon Allah...

Asabe in banda dariya ba abinda take ...iya kam sukuti tayi tana yar dariya ...nufoshi tayi da niyyar kai mashi bugu ...cikin zafin nama ya nufi bayi da Dan gudunsa yana dariya wahala...

Uhm tunda Nike ban taba ganin jairi irin ILU ba kaini ko ada baa tabayin jairi irin wannan yaron ba ...iya ta fada tana dariya tare da kallon malam...

Shima dariyar yayi ...salame kenan ai ILU sai addua CE kawai zata iyayin tasiri akanshi ...Allah ne kuma kadai zai iya shirya shi saboda haka mu cigaba da tayashi addua acikin wannan wata mai alfarma kunsan cewa wannan watan rahama ne ana gaggauta amsar rokon bawa ...to Allah yasa dai mu dace ...ameeen suka fada gaba daya ....

Can saiga ILU ya fito daga wanka gefen wuyanshi da gefen fuskarshi duk kumfa wai nan anyo wanka.... Malam ya fara wucewa ...shikam malam baice komai ba girgiza kai kawai yayi tare da yar dariya yaci gaba da duba quranin dake gabanshi ...yazo ya wuce iya itama batace komai ba sai dariya ...asabe CE ta kalleshi tare da babbakewa da dariya.....

*muje zuwa labarin ILU*
[6/21, 4:25 PM] ابو Ψ΅Ω„: *B.W.A*

πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚
*AZUMIN ILU*
πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚

       *peg 14*
*MAMAN MAMY*....✍

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
*RAMADAN KAREEM*
*Allah ka karbi ibadunmu ka yafemana zunubanmu ka sadamu da alkharain dake cikin wannan wata mai cike da falala*πŸ™πŸ»
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

```tofa jamaa yaufa kawar ILU ba kanta ummuherny πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚bare kuma asmeenat zeyyan ni kaina jagoran labarin ILU n yau nagane kurena```to Allah yasa mudaceπŸ˜‚
        Ameeen maryamu karki mana dariya...✍

Tsaye yayi yana kallon asabe dake ta dariya... Aa lafiyarki kuwa asabe kodai kwalwar ta tabu ne ...hhhhhhh haba ILU jibi jikinka duk kumfa sai kace wani kara min yaro
..

Wani Dan guntun tsaki yayi sannan ya nufi dakinsa ...ke asabe wani lokacin baki ganewa ...ai shi kumfa magani ne baki taba jin ance kumfa nasa arziki ba ina sane na barshi ...ki acigaba da dariya duk ranar da nayi arzikin sai kin rains kanki sile bazakici ciki ba dagani sai iya sai ya malam .....yayi gaba yana zare idanu yabar asabe na dariya....

Ranar fa malam sai dai kyale ILU yayi da batun zuwa massalaci salar laasar ..saboda yakai makurar gajiya ko magana ma baiyi sai idanu kamar gyada....

Misalin 6 na yamma su iya na tsakar gida aiki ...sai ganin ILU sukayi ya fito yana fadin Allah! Allah ...yana dafe ciki tare da kakarin amai ...

Da sauri iya ta nufoshi tana fadin yau na shiga ukku ni salame ILU mutuwa zakayi ....girgiza kai ILU yayi a wahalce ..aa iya ba yanzu zan mutu ba kawai dai ina hangen mutuwa ne ....ashha ILU sannu iya ta fada tare da kamashi ya zauna ...

Zaman yaji bazai iya ba yayi kwance lame lame yana bada wassiyya shi ala dole mutuwa zaiyi ....kowa yayi banza dashi sukaci gaba da aikinsu malam ma addua yayi tayi masa saboda abin na ILU ta wuce misali shi kanshi bazai so abarshi ya kara yin dorere ba ....

Ana kiran sallah  ..asabe ta Debi ruwa ta watsa mashi ...sai lokacin ne ya mike ya fizgi ruwan sanyi dake hannun asabe said a ya kwankwada son ranshi sannan ya dire kofin yana maids numfashi ....sannu ILU iya ta fada dake tsaye gabanshi ....yawwah ILU ya fada yana hararsu aranshi fadi yake duk zsku ji yadda naji.
..

Bai mayi sallah ba sai da yaci ya koshi yayi gyatsa sannan yayi alwallah ya kabbara sallah.... ILU fa ansha ruwa har wani karatu akeyi da karfi ana gyara tsayuwa kamar bashine ke kiran zai mutu ba ....

Kusa da malam ya zauna yana fadin ....sannu da shan ruwa ya malam don Allah inka rage kabani ...fanken nan ba abinda zaimin...murmushi malam yayi to ILU zan rage maka ...

Bawanda bai rage ma ILU  ba ya kuma cinye sannan ya yi wata mahaukaciyar gyatsa yayi alwalla ya nufi hanyar fits yana fadin nidai nayi gaba ya malam .....

Tofa ILU Kaine kayi alwallah zaka massalaci da wuri lallai ansamu acigaba cikin azumin nan Allah mungode maka ....iya ta fada tana murmushi...

Malam ne ya girgiza kai.. Uhm lallai salame Ashe har yanzu baki ida gane halin ILU ba... Ni nasan akwai abinda zai fitar dashi da wuri badai yaci ya koshi ba zakice na gayamaki ....sukuti iya tayi to Allah dai ya shieyamana ILU.... To ameeen inji malam....

Ta bakin malam kuwa saboda ILU na fita shagon sayar da magani ya nufa yana yan wake wakenshi .....halliru barka da shan ruwa da Allah maganin bacci mai karfi zaka bani ....cike da mamaki halliru ya kalleshi ....ILU me zakayi da maganin bacci ana azumi ...uhm bari kaidai ...ni dama in INA bacci ban azumi ban iya bacci shine nace bari in nemi magani....

Wayyo Allah sarki ILU... To gasunan kala biyu ne  gadai Wanda kesa bacci sosai nan amma bazan bakashi ba.... Aa halliru bani shi kai dai ba magana r kudi bace nawa yake.... Nera Dari ..to gashi.. Yana halliru kudi ya karbi magani ya saka aljihu ya wuce yana yan wakokinsa cike dajin dadi..

Saura kadan ya isa massalaci suka hade da basiru.. Said a suka gaisa sannan suka jero ILU na fadin.... Da yardar Allah gobe liman da mai gari dore re zasuyi ...cike da mamaki basiru ya kalleshi ta yaya ILU n malam ...

Yar dariya ILU yayi kadai da ido kayi kallo...

*to fans kuma kusa I do kuyi kallo doreren mai gari da liman*

        Muje zuwa labarin ILU dani ataskar kungiya msi albarka brrilaint writer's assciaton hantsi leka gidan kowa.......⚜
[6/21, 4:26 PM] ابو Ψ΅Ω„: *B.W.A*

πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚
*AZUMIN ILU*
πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚

      *peg 15*

*MAMAN MAMY*....✍

         *nace Ku huta*😁

Shiru basiru yayi cike da tunanin abinda ILU zaiyi yau....

Ana gama sallah ...ILU yaja basiru suka nufi wani shago inda ake sayar da lemu kwalba mai sanyin gaske ya say I guda biyu ...suka taho shidai basiru nata kallon ikon Allah... Sun danyi nisa kadanne suka zauna  bisa wani Dan dakali....

Lemun ILU ya balle ya jefa magani daya daya aciki ya mayar ya rufe ya dubi basiru ya kwashe da dariya... Wllh basiru har na hango yadda liman zai fara rangaji da wannan rawanin nashi ...shi kuma mai gari nasan sai ya rasa gane hanyar gida...

Zaro idanu basiru yayi kai ILU ko tausayi babu.... Hhhhhhh basiru kenan ai kanka kasan waye ilun malam duk Wanda yaci tuwo dani miya yasha kai dai ka kama bakin ka

Wa ni basiru ya fada... Ai inkaganni lahira kaini akayi... Yawwah basirun inna mai yan kunnuwa.... Tare suka nufi gidan liman...

Kofar gida suka sameshi zaune yana Jan cazbaha ga sauran kayan buds baki gabanshi ...

Sallama sukayi mashi ..suka nemi gefe suka zauna tare da gaidashi day I mashi barka da shan ruwa....

Cike da mamaki liman ke amsawa tare da fadin wa Nike gani kamar ilun malam Allah dai yasa lfy ...murmushi ILU yayi tare da dukar da kanshi kasa irin na ladabin nan ..kai ILU ba karamin jairi bane ...
Aa lfy lau ya liman kawai yau nace dai bari inzo inmaka barka da shan ruwa ....sai kawai liman yahau washe baki yana fadin Allah dai yayi maku albarka yarannan ...basiru kam sai kumshe dariya yake....

Ameeen ya liman ILU ya fada tare da dakko lemu guda ya mika mashi... Ga wannan kadan sha da sanyinshi badai yawa..... Hannu na kyarma liman ya karba yanata was he baki ganin lemu sai zufar sanyi yake ....aa ILU hard a dawainiya

Aa ba komai ya liman ILU ya fada yana kara dukar da kanshi kasa ...

Nan take liman ya bude lemun ya fara sha sanyi na ratsa zuciyarshi ...kai ILU Allah yayi maka albarka ya kara daga lemu ya kwankwada... Ashe haka nan muke maka kallon mashirmanci Ashe kasan abinda kake ...ILU ne ya kalli basiru shima basiru ya kalleshi saura kadan su tuntsire da dariya mussamman basiru ya kara abar wurin ya yi dariyarsa mai Isar shi ....

Said a ya shanye rabi sannan ya kara kallon su... Waini ILU ya batun dorere yau dai karka bari kayi dorere ....nan ma gumtse dariyar ILU yayi... Ai insha Allah gobe bszanyi dorere ba sai wasu kuma....
Yar dariya liman yayi ai dorere ba dadi ILU liman ya fada yana kara shan lemu sanyi na ratsa shi...

Mikewa sukayi to ya liman mu zamu wuce... Inji ILU... A aha har zaku tafi ILU ...to nagode sosai Allah yayi maka albarka ga wani Dan kosai nan Ku tafi dashi ko zakuci anjima ....

Da sauri ILU ya dauka dama sai hararar kwanon yake... Godiya Nike ya liman... Sukayi mashi sallam a suka tafi....

Suna shan kwana basiru ya hau babbaka dariya harda faduwa kasa... Shi kanshi ilun dariya yake tare da fadin ....kai tsohon nan yasan dadi wai kaga yadda yake kurbar lemu yana yamutsa baki kamar an lasawa jariri Zuma .....
Cikin dariyar basiru ke fadin kai wllh ILU kai karshe ne ....

Kaga maza Muje ga maigari tun kafin ya shige gida.... Basiru na dariya suka bar wajen suka nufi gidan maigari...

Liman kau suna tafiya ya kwashe komatsanshi ya shige cikin gida ...yana shiga uwargidan shi talatu ta karbi kayan tare da fadin wannan ragowar namune ko mai gida ...

Fizge robar lemun liman yayi ...kai kudai mata kun cika kwadayi to Dana ILU ya kawomin saboda haka ba Wanda zai shashi.... Buzun buzun ya wuce dakinshi...

Dan murmushi talatu tayi... To liman asha lfy ta wuce kicin ajiye kwanoni...

Lokacin da suka isa gidan maigari har zai rufe gida... Aa wa Nike gani kamar ILU n malam... Eh nine ya maigari barka da shan ruwa ...yawwah ILU lfy dai ko...

Lfy lau maigari dama cewa nayi ya kamata inzo maku barka da shan ruwa.... Kai amma naji dadi sosai ILU ya malam da mutanen gidan....

Suna lfy ga wannan nace bari inkawo maka ba dai yawa...

Cikeda da faraa maigari ya karba ...yaji lemu karara..nagode sosai ILU kamar kasan Abu mai sanyi Nike bukata yanzu ...

Aa ba komai fa ILU ya fada... Mu zamu tafi said a safe.... To Allah ya kaimu ILU ngd sosai ka gaishe da malam...

Zaiji ya fada yana murmushi suka wuce ...tunda suka fito suke dariya har basiru yayi hanyar gida tare da fadin sai goben ILU nasan akwai bidiri garin nan.....

Yar dariya ILU yayi to basiru Allah ya kaimu ....

Tunda ya shiga gida yake dariya har iya da asabe suka fito dagadaki...

Iya ke fadin lafiyarka ILU ....uhm ai tunda kikaga ILU na wannan dariyar to akwai muguntar da zaiyi... Asabe ta fada tana Harar sa.....

*Muje zuwa labarin ILU*
[6/21, 4:27 PM] ابو Ψ΅Ω„: πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚
*AZUMIN ILU*
πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚

       *peg 17*
*MAMAN MAMY*......✍
09031711711 for comments

```har in bazakayi magana akan novel ba to karka dauki number nan plss```ngd

πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–
*RAMADAN KAREEM*
πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–

*Allah kasa muna cikin intattun bayinka Allah kayafemana zunubanmu badon yawan ibadun ba ya Allah*πŸ™πŸ»πŸ™πŸ»πŸ™πŸ»

Tun kafin ya iso inda su ILU suke ya hau balbalin masifa .....kai ILU bana hana fito da tabarmun masallaci a shimfida awaje a zauna ba... Wato kun raina arzikin mutane ko????

Basiru ne ya dubi ILU shima ILU ya dubi mudi cike da mamaki yake fadin mudi ina kaga tabarma anan iccen nan nefa da aka sare muka Dan baza ganyayenshi .....dariya basiru yasa wllh maigari najin azumin nan shifa da tsiya idanuwansa tabarma suke gane masa ba rairayi ba...

Aiko gaba daya suka kwashe da dariya ...dai dai lokacin maigari ya I so yana share zufa zai dasa wani balbalin masifar ya daga kai haka ya ga ba tabarma bace sukuti yayi yana kallon su.....

Da sauri suka dai daita Kansu da dariyar saboda sunsan halin maigari ba mutunci ne dashi ba....

ILU ne ya dubeshi ya maigari ka mance ne ka taho da but a ahannu ko ka mance nan masallaci akwai butocin yin sallah?? ILU ya fada yana kumshe dariya tare da kallon butar dake hannun maigari.....

Sai lokacin maigari ya dubi butar dake hannunshi ....lokacin da yayi alwallah ne sai ya mance bai ajiyeta ba ya taho da ita ....

Dan murmushi yayi ....kai dai bari ILU wllh alwalla nayi na mance ban ajiye butar ba nama rasa tunanin da nikeyi....

Yar dariya ILU yayi... To kodai azumin ne ya maigari??

Har maigari zaiyi magana aka kabbara sallah ...da sauri suka nufi masallacin gaba daya ba tare da an ida caftar ba...

Jamaa liman fa najin AZUMIN nan saboda karatun sallar ya fara gura gura ...inya karanta aya saiya Dan jima bai tuno ta gaba ba ...gashi sallar shaf shaf akeyinta wato yar faki inji yara ba yawa sai lada...

Jamaa sai mamakin liman suke ganin yadda ya rude yake Neman kasa yin Jam'i

Ahaka dai aka kammala sallar su ILU nata kumshe dariya ...

Bayan anfito ne dattawan garin aka tsaya ana tattaunawa ...malam ne ke tambayar liman lfy..

Uhm bari malam liman vya fada yana dafe ciki yau dorere nikeyi bansan ya akayi na makara ba ...duniya gaba daya ta zame min doguwa ...

Har malam zaiyi magana  maigari ya rigashi ...to ai nima dorere nikeyi nikam wani irin bacci nayi da ban taba yin irinsa ba tun da Nike arywa ta ...

Subhanallah liman ya furta a wahalce ...to ai nima irin baccin da kake fadi nayi.. Wato ni kamar ma matattace na koma ...ikon Allah to wannan wace irin masifar  bacci CE ta samemu ...ko kaima irin shi kayi malam??? Liman ya fada yana kallonsa

Azabure malam ke fadin ...aa nikam banyi irin wannan bacci n ba ..saboda tun lokacin da suka fara maganar ya fara zatgin da wani Abu akasa bare daya tuno kalaman ILU da safe da yake cewa.. Yau akwai kallo a kauyen nan ....

To Allah ya kyauta ...inji maigari yawwah malam dama inaso inyi maka godiya ...jiya ILU yazo yayi min barka da shan ruwa harda abin arziki gaskiya naji dadi ILU kam an fara hankali....

Liman ne ya karbe... To Ashe bani kadai yayi ma wannan abin arzikin ba ...nima jiya saiga ILU yazo min barka da shan ruwa da lemu mai sanyin gaske ...in gama ina gama shan shi da yan mintina na hau wannan mugun bacci n....

Kallon sa maigari yayi ..to ai nima ina gama shan lemun ko minti biyar baayi ba bacci mai nauyi yayi awon gaba dani ...

Malam ne sukaji yana babbaka dariya harda tafa hannuwa ...kallon shi sukai gaba daya lfy malam??

Uhm lallai sannunku ...ai kun shiga tarkon ILU Ashe Ku har yanzu Baku gama sanin waye ILU ba ...in banda abinku wake cin kudin ILU a kauyen nan bare har ya saya maku lemu mai sanyi ...

Shiru malam yayi saboda dariyar data kubce masa ...
Amma dai anyi jairin yaro wurin nan ..haba nidai nayi mamakin irin bacci n da nayi kuma na Dade INA tunanin kyautar da ILU yayi man ban sake shiga mamaki ba said a naji maigari yace shima ankai masa.. Oh! ILU ILU

Liman ya fada cike da takaicin abinda ILU yayi masa daga baya kuma sai dariya ta kubce masa tunowa da yadda sukayi da ILU da irin ladabin da yayi masa Wanda baisanshi dashi ba ....

Shi kanshi maigari dariyar yayi ..kaga jairin yaro yasa gaba daya na fita hayyacina saboda yunwa... Kila gara ni da liman .. Shifa liman takalman kafarsa daban daban ne saboda tsabar jin AZUMIN ...

Tuni liman ya turbune fuska wane irin gara kai ...maigari tun daga gida fa ka taho da buta ahannu da alama ba kasan ka taho da ita ba ....

Dariya malam yayi ...nidai yanzu don Allah kuyi hakuri ...ni kaina Dana haifi ILU bai ragamin ba in shegantakarsa ta motsa baiji bai gani ....

Aa ba komai malam ...to amma me yasa yayi mana haka ne ...liman ya fada yana shafe zufar dake keto masa ...

Uhm tun da kukayi masa dariyar dorere shine abin ya bashi haushi ni nasani yakace kuma sai kunyi ...ai arayuwar ILU ba abinda ya tsana irin kaGanshi cikin wani hali kayi dariya saboda haka saiku kiyaye....

Ikon Allah ...maigari ya fada.. Ba komai gobe ka turomin ilun da abokansa zan zartar masu da hukunci saboda in baa hukuntashi abinda zai rikayi kauyennan ba karami bane ....

Da dai ka barshi kawai ...liman ya fada saboda shi ya tsorata da lamarin ILU ...

Shidai malam baice kar a hukunta ILU ba...saboda ana iya ganin don yana dansa...

Amma yasan bazasu iya yimasa komai ba ...saboda ILU ya ishi kowa Riga da wando...

Ahaka sukayi ban kwana kowa ya nufi gidan sa ...

Malam na zuwa gida ya hau yima iya bayan I tayi dariya sosai suna cikin hakane ILU ya shigo yana fadin

WO! Ni ilu ilun malam wayace dani bani ba dara bataci gida ba .....

Malam ne ya dubeshi yana murmushi... To albishirinka jairin malam dara taci gidaje bama gida ba...

*hhhhhhh Muje zuwa labarin ILU donjin hukunci da maigari zai yanke masa anya maigari bai tabowa kansa ba*
[6/21, 4:27 PM] ابو Ψ΅Ω„: *B.W.A*

πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚
*AZUMIN ILU*
πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚

       *peg 18*
*MAMAN MAMY*.....✍

πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–
*RAMADAN KAREEM*
πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–

*Allah ka yafemana albarkacin wannan wata mai albarka*πŸ™πŸ»

```barkanku da shan ruwa masoyan ILU ```😁

Cikeda mamaki ILU ya dubi malam ...bangane ba ya malam ILU ya fada yana gyara bajejiyar rigar dake jikinshi ....

Eh ai bazaka gane ba... Yanzu kai ILU ka kyauta kenan kasa bay in Allah dorere ba gaira babu dalili....wllh ILU kazo ka natsu kullum shekaru na gaba amma ba hankali ....

Yar dariya ILU yayi ..kayi hakuri ya malam ..ILU zaiyi hankali nan bada dadewa ba ...kuma daman ai hakane ya kamata da mai dariyar mugun ta bakaga da liman namin dariya jiya ba har wani dukewa yake ...

Kai ar jairi... Malam ya katse masa tunani ..towai ma me kasa masu a lemun ...

Dan kwanbare kafada ILU yayi ba wani Abu bane ya malam Dan maganin bacci ne irin mai nauyin nan ...sai kuma ya dubi iya ...wllh iya yau liman yana jin jiki Ashe haka limamai ke rudewa sukaji yunwa ...sai kuma ya babbake da dariya ...

Takalmin dake kafar malam ya cire ya jefe shi dashi ya kauce yana fadin tuba Nike ya malam..

Ajiyar zuciya malam ya saki ..ai gashi nan kajama kanka da abokanka gobe maigari na Neman ku ya zartar maku da hukunci dai dai da laifinku kuma wllh ban bashi hakuri ba kuma kasan halin maigari Allah dai ya kyauta ...daga haka maigari bai kara cewa komai ba ya mike ya shige dakinshi yana murmushi yasan ILU da tsoro ....

Ragwaf ILU ya zauna yana yake mai kama da dariya dariya ...uhm wllh iya maigari ya kuskura ya sani kiwon awaki cikin AZUMIN nan zaisha mamaki nasan karshen hukuncinsa kenan ...

Dariya iya tayi ..a to ai in mutum baaiji bari ba yaji hoho duk kuma Wanda baiyi sharar masallaci ba yayi ta kasuwa ...ai gara ya turaka kiwon dani nace kajemin kiwon bazaka jeba ....

 Mikewa ILU yayi yana jujjuya wa dubi nifa iya babban yaro dani duk kauyen nan ba mai kyawuna ..sai ace in rika yin kiwo ...ai iya dani mai kudi ne wllh zaaga takama da iko ...

Hararsa iya tayi da wannan bajejiyar rigar taka zakayi iko da takamar ji cikin ka wane mai kudi zai zauna yayi katon ciki irin naka ....um ni kaga bari in tashi inyi sabgar gabana da wannan sokanar taka ..wai kudi ko yaushe zai yi kudin ..

Yar dariya...ILU yayi ya dubi iya data tashi ta nufi kicin tana dariya... Uhm insha Allah sai nayi kudi iya nasa an gyara maki kafafuwan nan naki da kike dungurawa ya kara babbakewa da dariya ....ILU fa lamarin yayi masa kyau mussaman suke labe bayan gidan liman suna kwasar dariya saboda kofar gida ya baje yana dafe ciki kamar ba namiji ba ...

Daga karshe liman bai kara komawa massalaci ba sai gaf da zaa kira sallar magariba ya fita yayi zaune bakin massalaci yana Jan cazbaha gsanin ban tausayi .....

Bayan an sha ruwa ne liman ya tsare ILU sai nasiha yake masa kamar zaiyi kuka... ILU kam sai to yake
 cewa in ta shiga tanan ta fita tanan ba alamun nasihar na shiga kunnuwansa baima gama nasihar ba ILU ya mike yana fadin ...ngd sosai ya liman Allah ya biya ..bai jira amsar dazai bashi ba ya kara gaba yana baje rigarsa..

Girgiza kai kawai liman yayi tare da fadin Allah ya shirya mana ILU ...

         *nima dai nace ameeen*πŸ˜‚

Washegari ILU ankusa ma kara ...saiga iya da asabe da ILU na cin abinci kwano guda saboda basu ma tsaya wani kasa wa ba saboda karancin lokaci ...

Washegari da wuri maigari ya aiko kiran ILU da abokansa ....
Fito wa ILU yayi yana dariya to iya mu zamu fita Allah dai ya fidda ai  ga rogo..
Dariya asabe tasa ...Allah yasa kar ta fita ai n ..

Dariya iya tasan ya harda dukewa.. Harara ILU ya zabgawa asabe ..ai asabe tuni na gano baki kaunata ...yayi waje yana fadin Muje ai maigarin ba Allah bane ...
Har ya kusa fita ya dawo ya dauki ashana ...ya dubi iya ki dakamana tasshi mai dadi ...

Cikeda mamaki iya ta dubeshi me zakayi da ashana da tasshi ...

Kila maigari zai soye ko ..asabe ta fada tana dariya... Binta yayi aguje ta shige daki tare da banko kofar...

Fita yayi yana haki... Zaki sani innadawo iya na tafi ...

To ILU Allah ya tsare ....

Said a ya biya ma basiru da mudi sannan suka dau hanyar gidan maigari ..basiru na fadin alkuran ba ruwana...

*Muje dai zuwa labarin ILU*
[6/21, 4:27 PM] ابو Ψ΅Ω„: *BRRILAINT WRITER'S ASSOCIATION*⚜

πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚
*AZUMIN ILU*
πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚

      *peg 19*
*MAMAN MAMY*

πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–
*RAMADAN KAREEM*
πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–

*alkhairan dake cikin wannan wata mai albarka Allah ka sada mu dashi ....ka yafemana ya Allah*πŸ™πŸ»

```sakon godiya ta gareku masoyan ILU tabbas sakonni na isomin akan labarin ILU kuma naji dadi sosai Allah yabar zumunci da kyautataawa..ameeen ya Allah ````πŸ’˜

Har suka isa ILU baice ma kowa komai ba ...kofar gida sukayi tsaye suka aika agayamashi gasu sunzo....

Said a maigari ya mula ya mulmule bai fito ba harda dai takai gasu ILU sun zauna ...sai can sukaji tafiyarsa da sauri suka mike tsaye ....

Har kasa suka gaisheshi yana murmushi ya amsa da gani kasan akwai muguntar daya shirya masu ...ILU ya duba ...

Gaskiya ILU ka birgeni kana da wayo da hikima sai dai basuyi maka amfani inda ya kamata tunda har ni maigari baka ragamawa ba ....amma ba komai zanyi maku hukuncin da zakasan cewa ka tabani .....
Tuba muke maigari inji basiru ..ni wllh bansan abinda zaiyi kenan ba ya daice kawai in rakoshi wurin ka ....da sauri ILU ya dubeshi ..kaji tsoron Allah basiru Kaine fa ka gaya min yadda zanyi dubeshi da kyau yamai gari daka kalli kunnuwansa zakasan akwai mugunta ....ni ILU sharrin zakayi min. .basiru ya fada yana zare idanu ..sai dai baiyi mamaki ba saboda yasan halin ILU ....

Dariya maigari yayi ..kunga niba musu na tambayeku ba ....wllh nidai maigari bansan anyi ba nadai San nayi dariya sosai ajiyan ...mudi ya fada yana Sosa keya ...amma mudi ka raina ma kanka wayo ..ILU ya katse shi ..to ai dariya ma babban laifi ce  abokinka ne maigari n da zakayi mashi dariya koko kanen babarka ne ...

Da sauri mudi ya to she baki ..ganin yadda ILU keta loda masu laifi ...

Murmushi liman yayi tare da girgiza kai wato lamarin ILU sai shi ...

Makulli ya dakko ya mika masu ..wannan makullin gidan awakai ne ...in kun bude Ku share shi tax zansa arika dubawa agani ..sannan inkun gama Ku korasu daji kiwo Ku tabbatar sun koshi sannan Ku maidosu Ku basu ruwa da abinci Ku rufesu ....sannan akwai kaji adayan gefen suma Ku share masu wurin su Ku samasu abinci ...
Zaku rikayin haka har nan da kwana ukku duk Wanda ya tsallake kwana daya baizo ba to zan kara masa kwana biyu .....

Kallon kallo su ILU suka rikayi tsakaninsu ....cikeda tausayin Kansu saboda aikin babba ne aikin da mutum biyar keyi ance ukku suyi ....

Don Allah a sassauta mana ..basiru ya fada idanu wa narai narai kamar zaiyi kuka ....murmushi maigari yayi ..kabar wahalar da kanka samari aikin nan sai kunyi shi ...

ILU ne ya dubi maigari tare day in murmushi n nan nasa mai nuna alamun ya hango hanyar dazai rama ...ba komai ya maigari mungode da wannan hukunci Allah ya kara daukaka da girma ...

Cikeda mamaki maigari yace ameeen ...saboda bahaka yayi tunanin ILU zaice ba yayi tunanin hakuri zai bashi ...

Shikau mudi Dan yake yayi cikeda tausayin maigari saboda yasan duk ILU yayi wannan murmushi n to tabbas mugun ta zaiyi ....

Ahaka suka bude gidan awakan ...war in kashi ne ya bugi hancinansu awakine fa sunfi talatin iyaye da yara can gefe kuma dakin kaji ne birjit dasu suma da nasu tulin kashin .....

Basiru ne keta balai ....wllh ILU kajamin INA zaman zaman a kajawomin aikin kashi INA azumi ...
ILU ne ya rada masa wata magana sannan ya radawa mudi nidai bansan me yace masu ba suka babbake da dariya ....

Said a suka share wurin tas suka kuma share wurin kajin sannan ILU ya zabi manya guda ukku ya tura cikin katuwar rigarshi kunsan yar shara da fadi kaji nata tsiyau tsiyau ya dannesu suka saki tumakai sukai cikin daji kiwo ....

Said a sukayi nisa sannan ILU ya fiddo kajin yana fadin wllh naji dadin hukuncin nan dama na Dade ina jin haushin kajin nan namai gari ...tula tula dasu ga nama ....

Basiru ne ya babbake da dariya yana kara kora awakai ...kai wllh ILU kai balai ne yanzu kana nufin mu zamuci kajin nan ...wato hukuncin baiyi amfani ba kenan ....

Kai basiru in bakaci ni ci zanyi sai dai yayita kiwon kaji yana sayar dasu binni ..kofa shi bai cinsu saboda tsabar mako bare matansa ko yaransa ..mudi ya fada yana gyara hannun rigarsa ...

ILU ne ya kara damke kaji Ku rabu dashi da ILU yake zancen dubi yadda ya samu tsakiyar awakai kiwo ga azumi ...dariya su kasa gaba daya ..

Sai da suka tabbar awakan sun samu wurin kiwo sosai sannan suka sakesu ...suka hau aikin kaji ...dama in Baku mance ba na gayamaku ILU ya dauki ashana to dama baka raba mudi da yar wuka gefen kugu saboda irin haka ...

Tsaf suka yankesu suka hau gashi ILU sai hadiyar yawu ake anga nama don ma ana azumi ba damar aci sai ansha ruwa ...

Basiiru ne ke fadin ni sai inga kamar fa sata mukayi ...hararsa ILU yayi amma kai basiru Dan rainanin hankali ne ...  EhEh sata CE amma bayan mungama hukuncin zamu fada mashi mu nemi yafiya ...

Arude mudi ya dubeshi taya zamu fada mashi ILU ...ba ruwanku wannan aikina ne ..kuma gobe waccan akuyar zansa maigari ya yanka ya nuna wata akuya kosassa da ita...

Basiru ne ya dubeshi ...ILU kana hauka taya zakasa maigari yanka lafiyayyar akuyarsa ...
[6/21, 4:28 PM] ابو Ψ΅Ω„: *B.W.A*

πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚
*AZUMIN ILU*
πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚

       *peg 20*

*MAMAN MAMY*......✍

*ba dai zan gajiya ba da godewa masoya ako INA ma suke tabbas ILU ya Tara masoya to Allah yayima masoyan sa albarka ameeen*πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–

Wata uwar harara ILU ya rafkawa basiru ....dad in a dakai gajen hakuri Allah dai ya kaimu goben ka ba idanuwan ka abinci ...ILU ya fada yana yana kara daga wata katuwar kaza mai manyan cinyoyi ....kai Allah yayi halitta wurin nan jar uba mudi kaga kaza kamar wani Dan akuya .......

Dariya mudi yasa hadda buga kafa ...kai wllh naji dadin kiwon nan amma ILU gobe ma zamuci ko???yar dariya ILU yayi ah sosai mana mudi ai naga maka gobe akuya zamuci mu ....ai mun dosa cin dadi har nan da sati biyu duk wani gefe na cikina daya lomake saiya taso .....

Hhhhhhh basiru yayi dariya to taya zamu yi sati muna cin kaji bayan maigari kwana ukku yabamu hukuncin sa ......ILU ne ya dubeshi I do cikin I do ai a bsyaninsa yace duk Wanda bai zo ba zai kara masa kwana ukku to jibi mu dukanmu bazamu zobs kunga kenan zai kara mana kwana kan cin kaji ....kai dai wllh kanka baija basiru ....

Eh din naji baija amma ni tsoro na daya muci naman maigari cikin azumi ai haram mukaci .....injiwa ai zamu rokeshi gafara bakiji me nace dazu ba ..kai basiru cin kajin nan fa ba dole don ni nan da kake ganina sai incinyesu duka banji komai ba bare dama anrabi da haduwa yaushe rabon da inci kaji mudi ya dubi mudi cdake gashin nama yana share zufa...

Kai rabu dashi ILU nidai wllh ci zanyi yana gani mai gari ko zakkar kajin nan bai bayar wa ..kuma basiru dake fadin haka baifi kowa hadamar nama ba ko ka mance lokacin da muna yara basiru fa don tsananin kwadayi mai tsiren bakin Santa yake ma wanke wanke in yayi ya yanmasa tsoka guda ....

Dariya suka sa gaba daya hadda basirun yana fadin to naji aiba filin tone tone bane ......

Ahaka suka gashe kaji Tass! Suka sakasu cikin Leda mai nata diga sai kuwa kamshi suke duk da bawani magi akasa ba sai kamshin suyar .....

Basu dawo gida ba sai gab da azhar anma fara kiraye kirayen sallah ...mudi aka ba rikon kaji su kuma suka tsaya hado kawunan awakai kaf ...

Said a suka sakasu gidan su sannan suka nufi hanyar fita ILU ne ya dubi bangaren kaji ....sannunku namomi sai goben kuma soyayya kuda ILU har nan da sati ...ILU ya fada yana gyara katuwar rigarsa ta gado saboda yawan sata da ILU keyi har ansanshi da ita da anhangoshi zaace ga ilun malam can kosu basiru wani lokacin da sunganshi da ita zasu fara fadin yar gado ta ILU Riga daya tamkar da dubu .....

Suna fito wa aka tsaya shawarar yadda zaakaiwa maigari makulli saboda kajin dake hannun su  .....ILU ne ya karbi makullan kujirani bari inkai masa ....

Zaune ya iske maigari yana alwalla azahar yana ganin ILU ya hau was he baki .....sannu ya maigari  inji ILU makullin ya mika masa gashi mun dawo ....

Karba yayi yawwah ILU sannunku kunsha kiwo Allah dai ya bada lada ...awakan sun dai koshi ko?? Yar hararssa ILU yayi a fake eh kwarai kau sun koshi sosai saika gansu ...

To shi kenan jeka sai kuma goben Ku dawo ina sauran ne... Tafiya ILU yayi tare da fadin suna waje ..kafin mai gari ya kara wata magana yayi waje yana gyara tashi da kwakwar dake kanshi ...

Dai daya suka raba kajin maana kowa ya tashi da dakwale guda guda ...mudi sai was he baki ake shi kanshi basirun murmyshin farin ciki kawai yake to bare uban gayya ai kunsan basai nace komai ba ...

Tun daga nesa su iya suka fara jin kirarin da ILU keyi ...ilun malam wane mutum bare buzunsa munga jiya munga yau gobe ma in Allah yayi gani zamuyi .....iya CE ta dubi asabe anya ILU na azumi ji fa yadda yake daga murya ..

Dariya asabe tayi uhum tasamu kenan duk in kikaji wannan kirarin
[6/21, 4:29 PM] ابو Ψ΅Ω„: *BRRLIANT WRITER'S ASSOCIATION*⚜

πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚
*AZUMIN ILU*
πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚

      *peg 21*
*MAMAN MAMY*.....✍

```allah yasa mudace duniya da lahira Allah kasa muna cikin intattun bayi```πŸ™πŸ»πŸ™πŸ»πŸ™πŸ»πŸ™πŸ»πŸ™πŸ»

*barkanku da shan ruwa masoyan ILUπŸ·πŸ·πŸ—
Nasan dai da yawa sun hadewa kajin maigari miyau duk da dai kunsan ILU da Rowa🀣🀣🀣🀣🀣🀣🀣

Gaskiya na yarda asabe ta samun iya ta fada tana kara kallon kofa... Har asabe zatayi magana ILU ya shigo buguzun buguzun tsayawa yayi yana masu murmyshin nan nasa..... Sai kuma yayi wucewarsa yana fadin duk Wanda ya zauna ai yaga zama ....

Iya CE ta dubi ledar dake hannun ILU sai mai ke diga.... Aa ILU andawo kiwon toya gajiya nasan dai baa rasa gajiya ba......
Dawowa yayi ya zauna bisa kujera yar zukunne ...bari kadai iya ai dawa tayi nama kiwo alhamdulilah hukuncin nan yayi min dadi saboda in zaayi wata ina zuwa kiwon nan banjin komai ya fada yana kara daga ledar dake hannun shi .....

Asabe ce ta dubeshi sosai ...uhm ILU kenan ai nasan ruwa baya tsami banza to meye kasamo acikin ledar nan ....

Yawwah tayani gani asabe nima abinda nikeson tambaya kenan kika rigani iya ta fada tana kara leka ledar ....

Mikewa tsaye ILU yayi yana fadin shi kenan iya asabe ta koyamaki ganin kwaf yanzu daga kuganni da Leda sai akama a like sai ansan ko meye ciki eh amma da ya malam ne ya shigo da Leda ko kwano bamai cewa meye ciki saini da aka raina ...

Dariya iya tasa oh! Ni salame na godewa Allah to ILU kaida malam daya ne .....hhhhhhh haka yake gani tunda ya girma asabe ta fada tana to she baki ....

Harara ya galla mata oho kodai me zakice sai dai kice wannan da kike gani ya daga ledar naman... Kazar daji CE gasassa kuma kwalelenku karma kusa rai kunji na fada maku .....

Kazar daji ...iya ta maimaita  nidai tunda Nike ban taba ganin ko jin wani yace kazar daji ba sai yau ...ILU nuna min ita in gani....

Barta basai kin gani ba tunda baki Santa ba shi kenan Ku dama tsaffi haka kuke koni watarana cewa zakiyi baki sanni ba ....ya nufi dakinsa yana fadin saura kuce Baku dakamin yajin da nace ba wllh yau inhana ayi koko da kosai gidannan ya shige tare da banko kofa yadda zaaji dadin boye kaza ....

Asabe CE ta dubi iya a firgice ...Allah dai yasa kin daka masa yajin kinsan halin ILU abinda ya fada zai iya aikata shi ...wah! Ai tuni na daka shi ai ni nasan halin ILU kamar yunwar cikina ...

Dariya suka sa gaba daya asabe na fadin ILU balai ne amma ni ban yarda da ledar can ba dagani akwai wani ciki.... Yi shirunki iya ta katse ta intayi wari munji sanya masa I do kawai...
Shiru sukayi ganin ya fito yanata kakaniyar rufe kofa ...

Saida ya rufe yabi da tsumma ya kulle sannan ya dawo ya dubi asabe ....saura ki bude min daki wllh na lahira sai yafi ki jin dadi bare na lura kwannan haye min kike ke kin girma ko??
Ya fada yana girgiza kafa ..

Kaga ILU banson Neman fitina yama zaayi ina gani ta bude maka daki ...da wannan babatun Naka ga ruwa can bayi nakai maka ka watsa kaji sanyi tun dazu nakai maka su ,...

Wuce wa yayi bay in yana fadin ato nidai na fadi duk Wanda ya bude dakin can yau ya budowa kansa kema iya kijama bunsurunki kunne naga alamar yana yawan shigar min daki banna rannan sauran tuwona ya cinye to yau ya bude min daki Allah saina targada shi tunda ni ba abokin wasansa bane yawwah ....ya ida shigewa bayi wanka...

Asabe CE ta dubi iya yaufa ya karo wulakanci ji yadda yake wani cika yana batsewa sai kace wani yace zai bude dakin in wani yaji saiya dauka buhun kudi ne ya aje ....

Kedai ba ruwanki ....dole yayi wannan fitinar ga azumi ga kiwo aini nayi tunanin abinda zaiyi ma sai yafi haka iya ta fada tana kokarin tashi ...

Tunda ni fito wankan yake takalar fada ba Wanda ya biye masa dama yafi Jan asabe itakam kwanciyarta tayi kamar mai bacci tana jinsa hadda fadin asabe in tana bacci wai minshari take kamar bijimin sa ita kuma iya intana tafiya kamar ana koyawa yaro tata ....da daidai yaga ba Wanda ya kula shi saiya yayi awallahr laasar ya fita yana fadin tumakan gidannan duk asabe ta koya maku kilbibi ...

Yana fita suka hau dariya tare da fadin morewa ILU kenan in yana fitinarsa ai banza a kyaleshi ....

        *bayan sallar magriba*

Can nesa dasu iya ILU yayi shimfida don karma wani yaga abinda ke cikin ledar a hankali yake yagar abinsa yanaci ga tashhinsa gefe yana dangwalawa ....

Malam ne ya dubeshi aa wai yau ILU me aka samu ne ??

Bakomai ya malam kazar daji CEdazu. Da mukaje kiwo muka kama shine muka gasa ko zakaci???

Aa ILU aci lfy kasan bandamu da irin wadanan abubuwan ba ...

Shi kenan ya kara afki ILU ya fada yana tura tsokar nama baki...

Aiba ya kara affki ba bazaka yanma su asabe ba ko kamanta I do guba inji malam...

Hmmmmm yanzu ina iya basu suci suce maka kamar kazar gida kasan su da. Santi shiyasa na hanasu...
[6/21, 4:29 PM] ابو Ψ΅Ω„: *BRRILAINT WRITER'S ASSOCIATION*⚜

πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚
*AZUMIN ILU*
πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚

      *Peg 22*
*MAMAN MAMY*....✍

🀡🏻🀡🏻🀡🏻🀡🏻🀡🏻🀡🏻
*ILU a BIRNI na nan zuwa soon labari mai cike da ban dariya yazo da salon nishadantar da masoya yazo da tsare tsare iri iri ina mai tabbatar maku Cewar azumin ILU somin tabi ne akan ILU a BIRNI*

     πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚kada kubari abaku labari yana zuwa after sallahπŸ€πŸ»πŸ’˜

*gaisuwar ban girma ga yan brrilaint hantsi leka gidan kowa⚜allah ne ka tafiyantar da alaamurranmu Allah ya karayimana jagora ameeen*πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»

Murmushi malam yayi kaidai ka basu koma me zasuce ....

ILU ne ya dubi iya ..zakici kazar daji ...
Ai ko kazar dawace inaci ..iya ta bashi amsa ...

Yar dariya yayi sannan ya yago nama mai Dan yawa ya mika ma asabe.. Ungo Ku raba in kuma kun raina Ku bani abuna ...da sauri asabe ta karbe ina mu ina raina wa ....

Shiru iya tayi tana taunar nama ita dai taji kamar kaza wannan data sani ...kasa daurewa tayi ...

Kazar daji kece ko ILU to gaskiya wannan kazar ta gari CE ....eh wllh da nima haka zance asabe ta fada tana kara taunar naman ...

Dariya malam yasa ...dama ILU ya fadi santi yayi maku yawa gashi tun kafin aje koina kun fara ...to dama bai Baku ba yaci abinsa ...

Ato ba said a na fada maka ba ya malam ai nan dagewa za suyi da tsiya kaza ce irin ta gari ...ILU ya fada yana taunar kashi. ...

Aa malam ayi batun gaskiya anshi ci kaji naman nan sai ace wannan ba kaza bace ta sosai iya ta fada tare da mikawa malam sauran naman dake hannunta ....

Ina ni bazan karba ba can tsakaninku dama kun saba ...mikewa yayi tsaye ni kunga wurin maigari zani inbashi hakuri hukuncin daya yankewa yarannan yayi tsauri sosai ya sasasauta masu albarkacin watan Ramadan ....

Da sauri ILU ya durkusa gaban malam yana sude hannu ba kadan yaji dadin kazar nan ba ...don Allah ya malam ka kyaleshi wllh hukuncin ba tsanani sosai ciki ka barshi kawai duka fa kwana ukku ne kacal zamuyi kuma koma ba don haka ba ai maigari uba ne garemu zamu iya yimasa ...

Shiru malam yayi cikeda mamakin ILU sai dai duk iya hasashensa bai gano komai ba ....amma tabbas yasan akwai wani Abu akasa saboda yasan halin kayansa...

Ajiyar zuciya malam ya saukar shi kenan ILU Allah ya kyauta gaba bari inyi alwallah in fita sallah kayi maza ka kammla ka fito...

To ya malam ILU ya fada cike da farin ciki ...

Malam na fita asabe ta kalleshi ..tsakaninka ga Allah INA kasamu kaza ILU...

Yar dariya yayi kwantar da hankalinki yanzu zan fada maku saura Ku gayama malam ai kunsan sauran basai na fada maku ba ..

Said a ya kara yagar masu naman ya basu... Iya kau sai was he baki ake ana cin kaza..

Said a ya bari takai masu karo sannan ya fara koro masu bayani ...sukuti sukayi suna kallonsa naman dake bakin asabe kasa ida tamnawa tayi itako iya sauran na hannunta ta rike ta kasa kaishi ga baki ....

Yana basu labarin yana dariya sannan ya kara da cewa ..kuma wllh naji maganar nan ga malam CE masa zanyi tare muka hada baki daku kune ma kuka soya ta ya ida kecewa da dariya...

Innalillahi wainna ilaihir rajuun ..ni salame iya ta fada tare da sakin sauran naman dake hannunta ...na shiga ukku yanzu ILU fitinar daka jajubo mana kenan kajin maigari ILU ...lahailahailal lahu sallalhu alaihi wa sallam asabe kina jin wannan bakin labari ....

Dariya asabe tahau yi hadda tafa hannuwa ...inajinshi iya ai wllh saida raina ya bani bakiga da malam yace zaije ba maigari hakuri ba wani kukan kura da ILU yayi gaban malam ...ai tun nan nasan akwai abinda yake aikatawa ...

Dubanta iya tayi shine kuma kike dariya ...ato iya kuka zanyi ai gara ma inyi dariyar in rage zafi kin dai San halin ILU.. Nikam ko give ya kawo nama ci zanyi ba ruwana ehee ....

Mikewa ILU yayi tare da sakin wata katuwar gyatsa ...alhamdulilah ya fada tare da daukar Dan tsinke ya fara sakace... To shawara dai ta rage gamai shiga rijiya ko kuyi shirunku kuci nama ko Ku fadawa malam duk daya garama kuyi shiru ku kuci nama shine zai fiye maku..ni kunga tafiya ta ya buga katuwar rigarsa yayi waje yana fadin waye yace damu ba muba ...

Oh! Ni salame iya ta fada tare da dunan asabe dake dariya ahaka sukaci gaba da tattaunawa akan lamarin ...iyace ke fadin shiyasa naga ya zunbula waccan katuwar rigar Ashe da aika aikar da zaiyi ...
To kedai bakin ki alaikum kar malam yaji... Wa ni na isa ai bama zan fara ba iya ta fada tana rike haba alamar mamaki...

ILU kam na fita ya hade dasu basiru... Tafawa suka hauyi suna dariya kowa na fadin yadda yasha perty da tasa kazar ...mudi ne ke fadin harna ka gara gobe tayi inga yadda zamuci akuya .....

Suna nan zaune kafin afara sallah suka hango maigari buguzun buguzun da babbar Riga ...ILU ne ya kece da dariya dubeshi da Allah shifa in da balai mai wayo ne...

Gaba daya sukasa dariya wane wsyau anata dibar kaji...

Ahaka aka gama sallah kowa ya watse ...

Da sahur ma bawani abinci karki ILU yaci ba saboda wannan dankwaleliyar kaza da ILU ya tada sai ruwa da yasha sosai .......

Washegari da lillimi aka tashi kauyen taba daya ba rana hakan yasa ILU kara shirin fita kiwo ...

Yana fitowa ya dubi iya dake zukkune tana ba dabbobi abinci asabe kuma na shara ...Toni zan wuce hajiya iya adaka tasshhin da yafi bani jiya dadi ....to adawo lfy iya ta fada atakaice ....
Ba girin garin ba tayi mai inji asabe ..bakuda Matsala ILU ya fada sannan yayi waje ...

Batare da bata lokaci ba suka kora tumakai daji yau baa Debi kaji ba ...

Saida ya kama kosassa akuyan nan sannan yasa suka saki sauran ...mikewa mudi ita yayi ..yanzu zan ruga inkira maigari da kunga munkusa isowa Ku taushe akuayar Ku rika fadin saura kadan ta ida mutuwa majine ya sareta Ku barni da sauran aikin ...dariya suka hau yi to ilun malam angama ..

Da gudu n gaske ILU ya nufi cikin gari yana fadin maigari akuya zata mutu a taimaka maigari!!!
Rigar nan tasa sai sama take iska na kadata

*hhh Muje dai zuwa labarin ILU*
[6/21, 4:30 PM] ابو Ψ΅Ω„: *BRRILAINT WRITER'S ASSOCIATION*⚜

πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚
*AZUMIN ILU*
πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚

        *peg 23*

*MAMAN MAMY*......✍

🀡🏻🀡🏻🀡🏻🀡🏻🀡🏻🀡🏻🀡🏻
   *ILU a BIRNI*
Hhhhhhh kardai kubari abaku labari ILU ya zabure ya shiga binni acan ne zaiyi suna saboda shakiyancinsa da   hikimarsa ....uhm badai a cewa komaiπŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ˜‚

Hankali tashe maigari ya fito daga gida shida wasu mutane ukku da suke magana .....yadda ILU yayi wata faduwa gaban maigari saika rantse da Allah wani mugun tashin hankali ne ta tun karo kauyen ...

Lfy ILU maigari ya fada afurgice ...inafa lafiya ga akuya can zata mutu maciji ya sareta ILU ya fada yana fitar da numfashi ....

Eyeee na bani ni uwaisu yanzu akuyar tawace zata mutu tashi Muje inganta yau naga ta kaina saiga maigari na Neman fashewa da kuka...

Cikin mutanen nan ne daya ke fadin haba maigari akan akuya daya zaka tayar da hankalinka duk yawan dukiyar dabbobi da kake da ita ....
Haba kafin su farga maigari ya nade babbar rigar shi ya sheka aguje yana fadin ta ina kukayi ILU ....ILU ne ya Mara masa baya yana fadin kara wuta dai maigari saura kadan Allah yayi mata cikawa ....oh! Jamaakuzo kuga yadda maigari ke sheka gudu kamar Wanda akace gaba dayan awakan zasu mutu....

Mutanen da ya bari ne dayan ya dubi gudan... Aminu tsayawa zamuyi bazamu bishi ba ...nima tunanin da Nike kenan ai basu tsaya wata shawara ba suka bisu aguje......

Tun daga nesa maigari ya hango yadda akuya ke bultse bultse taji maza ...ai maigari baisan sadda ya sauke rawanin dake kansa ba ya rike a hannu ...shi kenan ai wannan tana daya daga cikin manyan garke yau na shiga ukku ni uwaisu..

Uwaisu!! Mudi da basiru suka maimaita sunan suna kumshe dariya wai Ashe sunan maigari kenan basiru ya fada kasa kasa da kyar suka kumshe dariyar dake Neman tona masu asiri ....

Maigari ne ya dubi ILU ...ILU ya akai wannan alamari ya faru ...ILU ne ya fara matse kwallan karya dai dai lokacin mutanen maigari suka karaso sunata kallon akuya na shure shure kamar da gaske ...

Bari ya maigari tunda Nike ban taba ganin tashin hankali irin na yau ba... Kawai muna zaune sai dai mukaji akuya ta kwala ihu irin ihun da tumakai basu taba yin irin shi ba.... Mu duba haka sai mukaga katon majici tunda Nike bantaba ganin mai irin girmansa ba idanuwan sa guda ukku reras... Ukku kace ILU maigari ya fada yana zare idanu tare da marmatsawa alamun tsoro ....

Kwarai kuwa ukku kansa kuwa ko bai kai na mudi ba to kadan ya rage ..eyee mutanen nan suka fada suna kara kallon mudi .....sosai kuwa inji basiru ai inaga wannan macijin shine sarkin macizzai na nan yanki ....tuni jikin maigari ya dauki rawa cikin in ina yake fadin yanzu ya zaayi da ita ILU ba maganin da zamu bata ta warke.....

Afirgice ILU ya dubeshi magani... Tab Ashe kanaso mu mutu waya fadamaka irin wadannan macizan nayin Sara abaada magani ai sai dai a yankata kawai a cire dai dai inda ya sareta a zubar shi kenan kawai....

Yankawa! Maigari ya maimaita hankalinsa tashe saboda in akwai abinda yaki jini to asara ce.... Eh sosai kuwa mudi ya bashi amsa baima wuce yan mintoci ta karasa ba ...daya daga cikin jamaarsa ne ya dubeshi hakuri zakayi ranka ya Dade wani ganin ga Allah baiwa ne...

To shi kenan a yanka maigari ya fada yana matse yan kwallansa ....kici kaca aka danne akuya basiru ya danna mata wuka aka yanke ..maigari sai share zufa yake...

Da yake cikin mutanen sa akwai barinji cikin kankanin lokaci aka fede ta tas.... Maigari ne ya dubi ILU saika amshi wuka ka yanki inda macijin ya sareta a matsa can karshen gari a zubar ...da sauri ILU ya karbi wuka ya fara yanko cinyar akuya yana fadin daga nan dafin ya fara ....in taka ice maku saida ILU ya wafce Rabin akuya da kwatarta wai duk dafin ya shiga ciki ......

Ajiyar zuciya maigari ya saukar ganin uban tulin nama amma ance dafin maciji na ciki ....girgiza kai kawai yayi ya dubesu to Ku tabbar kun zubar da naman nan bayan gari kar wani ya ciyowa kansa ajamani balai ....yar dariya mudi yayi sha kuruminka maigari ai inda baka taba tsammani ba can zamu kai wannan nama ....

Yawwah to shi kenan sawa yayi mutanensa suka dauki sauran naman dayan sai kallon tulin naman nan yake cikeda mamaki ...ILU ne ya gallara masa harara to ko abaka kaci ne... Aa ILU nibance ba kawai INA takaicin zubar da nama maiyawan gaske ...uhm kaga aminu Muje bari kara daga min hankali maigari ya fada tare dayin gaba yana fadin maza Ku tattaro kiwon Ku dawo ILU ...

Baijira amsarsu ba suka wuce zuwa cikin gari da sauran naman daya rage ...

Saida suka bari sun kule sannan suka fara babbaka dariya mudi hadda faduwa kasa shi kanshi basiru dafe ciki yayi saboda dariyar ta fara motsa masa ciki ....ILU ma dariyar yake yana kallon naman...

Kai wllh ILU balai ne mudi ya fada kaga maigari buguzun buguzun dashi aakuyarsa zata mutu har kuka yayi fa h...

 Wai uwaisu! Inji basiru dariya sukasa gaba daya ...sunan yayi min dadi tunda Nike ban taba jin sunan maigari na gaskiya ba sai yau da dalili yayi dalili ILU ya fada yana dariya ...

Aikam yau naga uwaisu wai kunga yadda keyar maigari take haba shiyasa kullum kai cikin hula basiru ya fada yana kara gyara zama...

Sunyi dariya sosai har yadda maigari yayi saida ILU ya maimaita sannan suka fara yima nama gashin tsire ...ILU na fadin zaiga zubarwa ...

*09031711711 for comment* maman mamy ke cewa da fatan kowa yasha ruwa lfy
[6/21, 4:30 PM] ابو Ψ΅Ω„: *BRRLIANT WRITER'S ASSOCIATION*⚜

πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚
*AZUMIN ILU*
πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚

  *peg 24*
*MAMAN MAMY*.....✍

Yeeee barkanku da sallah masoya ina fata kowa yayi sallah lfy tare da fatan zakuji dadin kara kasan cewa tare dani acikin wannan novel ngd

πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»jinjina ta musamman ga yan group dina the top Hausa novel gaskiya inajin dadin yadda kuke kula dani akoda yaushe Allah yabar zumunci ameenπŸ™πŸ»πŸ™πŸ»

      *sokon barka da sallah ga yan BRRILAINT hantsi leka gidan kowaπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ*

Bayan sun kammala gashe naman ne basiru ya dubi ILU dake ta zabga murmushi kamar sabon ango...

Gobe kuma me zamuci mutumen ..yar dariya ILU yayi  sha kuruminka nawan ai gobe bazamu zoba saboda maigari ya kara mana kwana kan cin kaji ...dariya mudi ya sa yana kokarin kashe wutar da sukayi gashin... Uhm kace garken uwaisu ya bani kenan ...

Sai da suka raba naman dai dai sannan suka kado awakai gida suna tafe ILU na dariya yana baje bajejiyar rigarshi ....

Bayan sun sakasu gidan ne ILU ya basu ajiyar naman shi ya shiga kaiwa maigari makulli ...zaune ya sameshi ya buga uban tagumi kamar wadda uwarshi ta mutu ...
Sai da ILU ya gyara fuskarshi sannan yace... Ya maigari ga makullin angama aiki ...jiki sanyaye maigari ya karbi makullin tare da fadin ...gobe kuzo fa don duk Wanda bai zoba saina kara masa kwana kai ...yar dariya ILU yayi ba damuwa zamuzo ...

Yana fitowa suka tafa da basiru sannan suka hau hanyar gida ...

Yauma zaune ya iske su tsakar gida asabe CE ta tashi ta nufi ILU tana kallon ledar dake hannun sa tare da fadin ga ILU ga ILU kawo ledar in kai maka daki ....

Janye ledar ILU yayi tare da gallara mata harara ...oh ni ILU asabe yaushe kika koyi sa I do ne ina ruwanki da Leda ta ....

Kumshe dariya asabe tayi ..ILU laifi ne don danuwa ya tari  danuwa sa ...eh laifi ne matsa in wuce ko inbigeki wllh tunda Baku gaji da zama ba ai kunga zama  ....wucewa yayi tare da kallon iya dake kallon su tana dariya....

Iya iya iya baiwar Allah ana nan zaune ko wai Ku meyasa bazaku tashi Ku nemi na kanku ba kullum sai dai kuyi zaune kuyi ta zare idanuwa kamar mage....

Asabe CE ta kalleshi sannu mai Neman na kai ...duka yaushe ka fara fita ko yanzu da kake fitar ai akwai dalili da ba sai dai kayi kwance ba kana mana raki kamar wani karamin yaro ....

Matsawa tayi tasan ba karamin aikinsa bane ya kai mata bugu ..dariya iya tayi sosai tana kare masa kallo da bajejejiyar rigarshi da iska ke kadawa ...uhm gane hanya asabe ai ni bazansa ILU cikin masu Neman na Kansu ba zan dai iya sashi cikin layin yan Neman rigima ....

Murmushi ILU yayi sannan ya wuce da ledar sa yana fadin iya lafazinka iya kason kason ka ehee...

Aa yi hakuri ILU abin bai kai nan ba asabe ta fada tana dariya ....iya ma dariyar take tare da fadin ato duk ranar dai da maigari ya gane ba ruwa na  kuma aka bani ci zanyi tunda bani na aiki mutum ba.... Sosai kuwa iya ai koni ci zanyi wallahi yo in ruwana asabe ta fada tana gyara zama...

Shidai ILU baice kanzil ba ya shige dakinsa yana murmushi ...

     *bayan magrib*

Yauma gefe ILU ya koma da ledar sa ya fara cin naman shi yana dangwala yaji yau kam ko kosan da koko bai kalla ba ga lemunsa mai sanyi gefe yana korawa...

Malam ne ya dubeshi ...ILU yau ma kazar dajin CE ka samo ..nifa na kasa gane maka .....anya lamarinka akwai kamshin gaskiya ciki??

Nama ILU ya tura bakinshi ba wani Abu ya malam ka yarda dani ...ko akwai wani Abu asabe ??

ILU ya dubi asabe ...da sauri asabe ke fadin aa ba komai malam ba komai... Tasan halin ILU ta fada ta fadi wani Abu Allah kadai yasan tsiyar da zaya kulla mata ...

Yar dariya ILU yayi ..kefa iya akwai wani Abu ...hmmm kaga ILU in ka tashi zuwa kabar jirana shaaninka ai sai kai wa ya isa yasan halin da kake ciki ...

Dariya malam yasa tabbas yasan akwai wata akasa kawai dai suna tsoron ILU ne shima yasan halin yan kayan sa...

Barkanmu da sallah all inajiran ILU yazo mu zagaya mu gaida masoya.
[6/21, 4:30 PM] ابو Ψ΅Ω„: *BRRILAINT WRITER'S ASSOCIATION*⚜πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚
*AZUMIN ILU*
πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚
   
*peg 25*
*MAMAN MAMY*.....✍

*🀡🏻🀡🏻🀡🏻🀡🏻🀡🏻🀡🏻*
*ILU a BIRNI na nan zuwa gareku kar dai Ku manta da zuwansa zai iso gareku cikin salon kayatarwa ina fata zakuji dadin kasan cewa tare dani ngd*πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»


Uhm ILU kenan gara ka fada min gaskiya tun wuri kasan dai tayi war I dole inji....

Yar dariya ILU yayi tare da fadin ya malam kenan ai in tayi warin kowa ma yaji ....

Iya CE ta dubi ILU ..towai yau me kake nufi bazaka bamu kason mu ba... Nima dai kallon sa kawai Nike inji asabe ...

Dadina daku gajen hakuri ...zan Baku mana ai in banbaku ba sai kunsa yabimin ta wata hanya... Hhhhhhh oho dai abamu cewar iya tana gyara zama ....

Haka ya dibar masu mai Dan yawa ya basu .. Asabe na fara ci ta Dan matsa kusa da iya yadda ba Wanda zaiji abinda zata CE ...
.mun shiga ukku wllh naman akuya ne ko na tunkiya abin ya wuce kaji ...zaro idanu iya tayi itama ta fara magana kasa kasa ...

Aini nasan maigari kansa ya jawowa fitina bai sani ba yanzu babban tashin hankali na radda ya gane su mun shiga ukku ....uhm ai ILU baijin magana wllh cewar asabe amma kuma sai fizgar nama take...


Allah dai ya tsinewa mai gulma wllh asabe kiji tsoron Allah...

To ILU tsoron ka zanji inbanji tsoron Allah ba ...malam ka shiga tsakanina da ILU ....

Dubansu malam yayi ..aa niba ruwana cikin fadanku ai ke kinsan dai waye ILU sai dai kiva wani lavarinshi to kunfi kusa ...ni kunga ma tafiyata massalaci zani ...
Kai kuma yau dai kasan an kai azumi na 25 ka dage zuwa sallah dare saboda mu samu damar gayawa Allah bukatunmu kuma Ku dage salame kunsan wannan watan ya banbanta da sauran Allah yasa mudace..

Ameeen suka amsa gaba daya ...asabe ke fadin yaushe zaa sayo mana kayan sallah malam...

Murmushi malam yayi Baku da Matsala asabe zaayi maku da yardar Allah ....

Uhm dama kabar kudin ka ya malam asabe dai ko tayi kwalliyar nan ba kyau take ba can zaka ganta cikin su lantana kamar zabuwa ....

Gaba daya aka kwashe da dariya ita kanta asabe sai da ta dara amma kasa kasa tana fadin kai dai kasani ...


Koda malam ya fita bai zame ko ina ba sai gidansu basiru yasa akayo masa sallama da vabansu malam isiyaku ...

Yana fitowa ya hau wasge baki suka gaisa sosai tare da yima muna barka da shan ruwa ..

Malam ne yayi gyaran murya ...malam isiyaku abubuwa ne suka daure min kai ga yaranmu da mai gari yasa aiki ILU da basiru na wajenka naji ma ance hadda mudi Dan gidan haahimu..

Eh eh hadda shi malam isiyaku ya furta da sauri...
Yawwah to nidai gaskiya nakasa gane ma ILU kullum sai ya dawo da nama abin mamaki  nama mai yawa to shine nazo inji ko kaji wata magana daga bakin shi basiru n saboda ni nasan waye ILU ...

Numfashi malam isiyaku yaja ....to nima dai INA ganin basiru da nama don wani lokacin har yan kannansa yake yanmawa in na tambayeshi sai yace min guminshi ne yake ci ....

Guminshi malam ya maimaita Kalmar ....kwatsam saiga basiru ya fito yanata yan wake wakensa rusunawa yayi zai ya gaida malam zai wuce kenan malam ya kirashi....

.dawowa yayi ya zukunna .....yawwah basiru nasan kai kanada hankali kafi ILU tunani...
Tambayarka nikeson yi

Inaji malam basiru ya fada ....yawwah wai don Allah INA kuke samo nama ne....

Shiru basiru yayi saboda yanajin kunyar yayi ma malam karya ...

Cikin natsuwa ya fayyace masu komai ...
Salati suka sa gaba daya sai daga baya kuma suka babbake da dariya saboda jin drama da akasha wurin yanka akuya ...

Malam isiyaku ke fadin maigari ya samu dai dai shi ...malam ka kyaleshi da ILU shine dai dai shi...

Aa baayi haka ba isiyaku ai cutar tayi yawa amma kai basiru shine kuka biye masa ....

Wllh malam sai da na hana ILU ya kusan bige ni kasan halin sa in yayi niyyar yin Abu ...

Hakane malam ya fada tova komai bari inkoma gidan ngd isiyaku...
Nan yayi ban kwana dasu ya koma gida cike da tunanin halayen ILU...


Lokacin da malam ya koma kwance ya iske ILU sai sharar barci yake bakin nan dumu dumu da mai cikin nan yi sama kamar zai fashe ga kasusuwa gefe...


Wani wawan bugu malam ya sauke masa a firgice ya farka yana fadin Ku ke ganin mu bamu ke ganinku ba...

Sukuti yayi yana kallon malam dake kallon sa tuni iya da asabe suka fito suna kumshe dariya ...

Kai yanzu ILU ka kyauta kenan kajin maigari da akuyar maigari su ka cinye ...

Komawa ILU yayi kwance tare da fadin ...amma ya malam baka gajiya da hakilu wllh na aza ma biyoka karnuka sukayi nasan ka da tsoron kare Ashe kan wannan maganar ne ....

Malam ne ya dubi iya... Wai salame Kinji abinda ILU ya jawo mana ....

Dariya iya tayi naji malam ai ILU saiya tada karamin kauye ...to yanzu ya zaayi ...

Aa zuwa zanyi in fadawa maigari kawai malam ya fada tare day in hanyar waje..

Da gudu ILU ya bishi don Allah karka fada mashi ya malam ka bari mu kara cin kaji ukku da kwai don Allah...
09031711711 for comment

Hhhhhhh Muje zuwa labarin ILU
[6/21, 4:30 PM] ابو Ψ΅Ω„: *⚜ BRILLIANT WRITER'S ASSOCITON*πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚
*AZUMIN ILU*
πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚

     *peg 26*
*MAMAN MAMY*......✍


*wannan peg nakune sakon barka da sallah*🌹🌹
*hafsat abubakar rimi*
*Aisha lawal rimi*
*bilkisu my autarere*
*ina yinku irin sosai dinnan Allah ya Baku abinda kuke nema ameeen*πŸ™πŸ»πŸ™πŸ»πŸ™πŸ»πŸ™πŸ»πŸ™πŸ»Tsaye malam yayi cike da mamakin ILU wato shi baijin tsoron a fadawa maigari ta kara cin kaji yake...

Girgiza kai kawai malam yayi sannan ya fice zuwa massalaci yasan acan ne zasu hadu da maigari ...

Asabe CE ta babbake da dariya ..shi kenan masu Neman na Kansu Neman nakai ya tsaya kenan...

Kinga sai yazo muyita zaman sai muga zaman iya ta fada tana dariya ...

Harararsu ILU yayi ...to ai shi kenan kowa ma yarasa amma ko yanzu kasuwa ta watse ai Dan koli yaci riba kuma Allah da ya malam ya kyaleni da kila sai naci kaji ashirin...

Mikewa yayi tsaye dubeni asabe don Allah ban kara kiba ba kwana biyun nan da nikecin nama ya ida maganar yana washe baki ...


Umm eh ba laifi katon cikinka ya kara girma ...asabe ta fada tana kare masa kallo ...

Dariya iya keyi sosai ...yanzu dai ka tafi masallaci n kaji yadda zaayi..

Azabure ILU ya nufi kofar fita gidan har yana bige Dan guntun marfin kofar gidan ...haka zaai tsohuwa mai ran karfe kar ina nan a fadi abinda banyi ba ta kara tsawo...

   ILU alwalla fa...inji asabe

Nayi acan ya maido mata amsa da karfi saboda ya fita daga gidan ...


Tunda malam ya iske liman da maigari yake basu labarin abinda ke faruwa liman ko sai babbaka dariya yake banda maigari dake zare idanu zufa nata keto masa tabbas ya tsinke da lamarin ILU..


Malam ne ya kara da cewa ...saboda haka kayi hakuri ka kyale yaran nan inkuma ba haka ba wllh sai ILU yasa ka kuka... Ka ganni nan nida na haifeshi in ya tashi shegantar sa ba ragamin yake ba ...

To ILU aduniya ma wa yake ragamawa ai ILU gaisuwa kadai ke hadani dashi saboda na tsorata dashi sosai cewar liman yana gyara babbar rigarshi...


Numfashi maigari ya saukar ILU ilun malam tabbas ILU dabanne a samarin kauyen nan ...nikam daga yau na fita shaanin ILU na kuma godewa Allah da yasa aka gane da wuri ....abin haushin ko ni ban cika cin kajin nan ba amma tashin farko ILU ya rabani da biyu babban bakin cikina kuma daya rabani da uwar garke na bata haihuwar daya sai biyu ya ida maganar tare da dafe kansa gwanin ban tausayi....


Malam ne ya dubeshi ...kayi hakuri maigari ka ya fe masa ba don halinsa ba ...

Ya zanyi ai dole in yafema ILU ...

Gaba daya suka tashi saboda lokacin sallah ya gabato ...


         *DAREN SALLAH*

Kamar yadda kowane gari ake had a hadar sallah haka abin ya faru a kauyen su ILU kowa kagani cikin farin ciki da annashuwa anata yanka akuyoyi da zabbi da kaji ga nikan tuwo anata kaiwa gaskiya abin ya birgeni ni kaina yan mata anata kitso da kunshi ....


ILU ne zaune ... Wai iya mu me zaa yanka mana ne ....

Ato ILU ya zaayi insani ai daka tambaya malam ...

Wllh iya nakagara agama AZUMIN nan haka nan mu huta ...

ILU kenan to duka yaushe ne gobe nefa in Allah ya yarda ...ya batun dinkin ka am so kuwa..

Aa yau zan am so ai nadai bashi kudin shi ya kiyi min yaga dubun rashin mutunci...

Yama zaayi yaki yimaka ILU sai dai kace baisan hali ba.....
.

Malam ne ya shigo da zabbi a yanke ya mikawa iya ...agyara su in nasamu yadda nikeso zan kara da kaji...

Wayyo dadi ILU ya fada da karfin gaske Ashe zamuci dadi na kama kafa da hanji sai lokacin malam ya kalleshi...


Ashe kana nan to maigari na Neman ka gyaran kaji n da zai siyar kai da kafafu saika ture...


Azsbure ILU ya mike haba kaji inda ake sabgar arzuki ...iya nayi nan in asabe ta dawo ta amsomin wankin hulata wurin halliru ...

Yayi waje yana buga yar sharasa daya saba saw a ...

Malam ne ya dubi iya Allah ya shirya ILU... To ameeen dai inji iya ...wai da gaske maigari n ke Neman sa...

Eh ai kinsan yanzu na hannun damar sa ne ...

Dariya sukasa gaba daya ...


Tun daga nesa ILU ya hango samari nata aiki ya fara fadin..

Eh mai wuri fa yazo mazaje..


*hhhhhhhhhhhhacigaba da gashi*
*⚜ BRILLIANT WRITER'S ASSOCITON*

πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚
*AZUMIN ILU*
πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚

     *peg 26 and 27*
*MAMAN MAMY*......✍

*wannan peg nakune sakon barka da sallah*🌹🌹
*hafsat abubakar rimi*
*Aisha lawal rimi*
*bilkisu my autarere*
*ina yinku irin sosai dinnan Allah ya Baku abinda kuke nema ameeen*πŸ™πŸ»πŸ™πŸ»πŸ™πŸ»πŸ™πŸ»πŸ™πŸ»

Tsaye malam yayi cike da mamakin ILU wato shi baijin tsoron a fadawa maigari ta kara cin kaji yake...

Girgiza kai kawai malam yayi sannan ya fice zuwa massalaci yasan acan ne zasu hadu da maigari ...

Asabe CE ta babbake da dariya ..shi kenan masu Neman na Kansu Neman nakai ya tsaya kenan...

Kinga sai yazo muyita zaman sai muga zaman iya ta fada tana dariya ...

Harararsu ILU yayi ...to ai shi kenan kowa ma yarasa amma ko yanzu kasuwa ta watse ai Dan koli yaci riba kuma Allah da ya malam ya kyaleni da kila sai naci kaji ashirin...

Mikewa yayi tsaye dubeni asabe don Allah ban kara kiba ba kwana biyun nan da nikecin nama ya ida maganar yana washe baki ...

Umm eh ba laifi katon cikinka ya kara girma ...asabe ta fada tana kare masa kallo ...

Dariya iya keyi sosai ...yanzu dai ka tafi masallaci n kaji yadda zaayi..

Azabure ILU ya nufi kofar fita gidan har yana bige Dan guntun marfin kofar gidan ...haka zaai tsohuwa mai ran karfe kar ina nan a fadi abinda banyi ba ta kara tsawo...

   ILU alwalla fa...inji asabe

Nayi acan ya maido mata amsa da karfi saboda ya fita daga gidan ...

Tunda malam ya iske liman da maigari yake basu labarin abinda ke faruwa liman ko sai babbaka dariya yake banda maigari dake zare idanu zufa nata keto masa tabbas ya tsinke da lamarin ILU..

Malam ne ya kara da cewa ...saboda haka kayi hakuri ka kyale yaran nan inkuma ba haka ba wllh sai ILU yasa ka kuka... Ka ganni nan nida na haifeshi in ya tashi shegantar sa ba ragamin yake ba ...

To ILU aduniya ma wa yake ragamawa ai ILU gaisuwa kadai ke hadani dashi saboda na tsorata dashi sosai cewar liman yana gyara babbar rigarshi...

Numfashi maigari ya saukar ILU ilun malam tabbas ILU dabanne a samarin kauyen nan ...nikam daga yau na fita shaanin ILU na kuma godewa Allah da yasa aka gane da wuri ....abin haushin ko ni ban cika cin kajin nan ba amma tashin farko ILU ya rabani da biyu babban bakin cikina kuma daya rabani da uwar garke na bata haihuwar daya sai biyu ya ida maganar tare da dafe kansa gwanin ban tausayi....

Malam ne ya dubeshi ...kayi hakuri maigari ka ya fe masa ba don halinsa ba ...

Ya zanyi ai dole in yafema ILU ...

Gaba daya suka tashi saboda lokacin sallah ya gabato ...

         *DAREN SALLAH*

Kamar yadda kowane gari ake had a hadar sallah haka abin ya faru a kauyen su ILU kowa kagani cikin farin ciki da annashuwa anata yanka akuyoyi da zabbi da kaji ga nikan tuwo anata kaiwa gaskiya abin ya birgeni ni kaina yan mata anata kitso da kunshi ....

ILU ne zaune ... Wai iya mu me zaa yanka mana ne ....

Ato ILU ya zaayi insani ai daka tambaya malam ...

Wllh iya nakagara agama AZUMIN nan haka nan mu huta ...

ILU kenan to duka yaushe ne gobe nefa in Allah ya yarda ...ya batun dinkin ka am so kuwa..

Aa yau zan am so ai nadai bashi kudin shi ya kiyi min yaga dubun rashin mutunci...

Yama zaayi yaki yimaka ILU sai dai kace baisan hali ba.....
.

Malam ne ya shigo da zabbi a yanke ya mikawa iya ...agyara su in nasamu yadda nikeso zan kara da kaji...

Wayyo dadi ILU ya fada da karfin gaske Ashe zamuci dadi na kama kafa da hanji sai lokacin malam ya kalleshi...

Ashe kana nan to maigari na Neman ka gyaran kaji n da zai siyar kai da kafafu saika ture...

Azsbure ILU ya mike haba kaji inda ake sabgar arzuki ...iya nayi nan in asabe ta dawo ta amsomin wankin hulata wurin halliru ...

Yayi waje yana buga yar sharasa daya saba saw a ...

Malam ne ya dubi iya Allah ya shirya ILU... To ameeen dai inji iya ...wai da gaske maigari n ke Neman sa...

Eh ai kinsan yanzu na hannun damar sa ne ...

Dariya sukasa gaba daya ...

Tun daga nesa ILU ya hango samari nata aiki ya fara fadin..

Eh mai wuri fa yazo mazaje..

*hhhhhhhhhhhhacigaba da gashi*

*⚜BRILLAINT WRITER'S ASSOCIATION*πŸ–Š

πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚
*AZUMIN ILU*
πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚
        *peg 27*

*MAMAN MAMY*.....✍

🀡🏻🀡🏻🀡🏻🀡🏻🀡🏻🀡🏻🀡🏻
*ILU a BIRNI*
Yana zuwa soon gareku masoya kafin nan ina taya dauka cin masoyana murnar karanta AZUMIN ILU daga wannan peg din sai ince mu hade a ILU a BIRNI don jin yadda zaa kaya ngd

Tun kafin ya karaso aka matsa masa wuri kowa yasan halin ILU shiyasa ba kowa ke haye masa ba....

Ana kammala wa maigari ya hada hanjin  da kawuna da kafafu yaba ILU yace yaci gaba da rabo.... Haka ILU yayita basu abinda ya ga Dama wani ma kai biyu kafa biyu ya bashi kuma akarasa mai tanka masa..... Bayan uban kason daya tashi dashi sai da maigari ya kara masa da naman kaji mai yawan gaske ...ILU fa da maigari ta gyaru hadda nera Dari yasha ruwa...

Haka ILU ya ratso kauyen nan yana tayi ma kansa kirari yana dariya .. Duk inda ya wuce sai kaji ance Dan malam yaki halin malam ....saiya ida masu da cewa da karatu gwanda rawar disko ya baza rigarshi sama yayi gaba abinsa ....

Gidan su basiru ya biya ....kafin ma ya shiga basiru ya fito suka tafa... Yayi mutumen daga INA haka da Leda duk nama... Kai dai bari nawan ta samu ....shine nazo in gayyaceku kar inci ni kadai gaba daya ya kwashe labari ya fada masa ....sannan ya kara da cewa anjima INA gayyatarku kai da mudi gidan mu masha shagali ferfesunsu zanyi ya fada yana kara daga ledar naman...

Tuni basiru ya hau was he baki... Kai amma naji dadi mutumen muna nan zuwa ka jiramu ...daga haka sukayi ban kwana ya buga sai gida...

Yana zuwa ya hunce ya juye nama a tukunya ba wanki ba komai ya hau kakaniyar hura wuta...

Asabe CE ta kalleshi lfy ILU me zakayi haka...

Herhesu zanyi ko zaa hanani wannan naman gumi nane na halak ne maishi yavani da hannunshi ...

Yar dariya iya tayi to ILU wani yace na haram ne amma dai koma me zakayi ai ka fara wanke naman tukun... To ai nima shi nagani cewar asabe....

Ikon Allah wa yace maku bazan wanke ba bari nayi in hura wata sannan in wanke su tas!

Iyace ta dubi asabe itama iya take kallo kiri kiri bai iya Abu ba amma ya nuna ya iya... Shiru sukayi suna kallon ikon Allah...

Saida ya hura wutar sannan ya wanke naman ya Dora yaci gaba da bala wuta abinsa..

ILU bazakasa magi da albasa ba inji asabe... Kai asabe ya katseta yanzu nan zance ki dakko min kika rigani... Dariya ta kumshe ta nufi daki dakko masa...

Iya ya kalla... Acikin iya girki fah ba abinda zaku nuna min don inna ranbada wata sanwar ko gidan sarki albarka..tabe baki iya tayi gaskiya naga alama ai...

Ahaka ILU ya ranbada sanwarshi sai da yasa tarugu kusan ashirin masu Dan bazan yaji ....asabe na kallon shi taki hanashi tunda nuna wa yake ya iya ....

          *bayan magrib*

Kafin su basiru su iso ya dibarma su asabe yace suci shi ko dandanawa bazai yiba sai su basiru sunzo ....
Shidai malam da aka bashi cewa yayi ya koshi ...

Iya na fara ci ta fara shan ruwa saboda yaji ...asabe CE ta Dan matsa kusa da ita... Don Allah iya karki nuna da yaji kyalesu suci suji.... Wai Allah asabe kamar bakina zai cire na bani ni salame ...daure dai iya...

Tata dai iya girkina yayi dadi ILU yayi tambaya yana kara rungumo kwanon naman...

Eh sosai kuwa ILU ai ban taba shan romo mai dadin wannan ba ....asabe ta fada da sauri ganin iya ba Neman tona asiri..

Har zaiyi magana su basiru suka kwada sallama da sauri ya suri kwanon yayi waje yana fadin gani nan...

Yana fita iya ta ruga ta kwalhi ruwa ta hau watsa ma bakin ta ruwa tana maids numfashi asabe ma da gudun ta zuba ruwan tana fadin sannu iya ....

Wane sannu tasshi zai kasheni kin hanani magana haba tunda Nike...
Aa iya gara muyi shiru yadda mukasha kowa ma yasha yaji ...

Malam ne ya hau dariya... Maganinku kenan kome ILU yazo dashi gidannan sai kunce zaku ci ai yayi maganinku....

Iya CE ta sulale tana huro iska bakin ta tabbas yayi maganinmu...

Ku zo kuga yadda basiru da mudi ke gyara zama zaa sha lagwada sai was he baki suke....

Mudi ne ya fara kai lomar nama bakin shi ...runtse idanuwa yayi tare da fadin wash! Saboda yajin daya ratsa kokon kwakwalwar sa ...
Basiru ne ya dubeshi da nama bai kai ga sawa bakin shi ba yadai mudi lafiya naji kace wash!

Wash! Dadi ba mudi ya fada yana gyara hula ..dadi ne yayi min yawa basiru ci kaji girkin ILU yayi dadi ....mudi ya fada shi kadai yasan yadda take ji...

Tuni ILU ya hau was he baki tare da dakko naman zai kai bakin sa....

Um um um basiru ya fada yana tamnar nama ...mudi ne ya kalleshi yaya ....munafiki Ashe haka kaji tabbas nama yayi dadi basiru ya fada yana hararsa kasa kasa yana dafe kai....

Yawwah abokaina haka nikeso kunga kafin infara ci bari in debo maku ruwa ...to to yawwah daka kyauta cewar basiru yana daga kai...

Da sauri ILU ya shige gida yana shige wa mudi ya dauki takalman sa a hannu wllh nayi gidan kutumelesi yaji kamar zan mutu ..

Yasin baka barina basiru ya fada tare da ruko rigar mudi karamin aikin ILU ne yace sai mun cinye naman nan ....

Da gudu suka bar kofar gidan suna dariya ..

ILU yana fitowa yaga ba kowa da sauri ya duba kwanon ya aza sun cinye sai kuma yaga akwai sosai yayi mamaki sai kawai ya zauna ya fara dibar nama...

Yaci daya biyu sai Jan ruwa yake yana fyace majina sai lokacin ya dago abinda ya Hana su basiru cin naman ...kwafa yayi wllh dasai sun cinyeshi ...

Gida ya shiga yanata ruwan masifa ...an cuceshi  ba Wanda ya kula shi ahaka ya gama sababinsa ya aje naman yayi waje su asabe sai dariya suke masa ...

       *RAnar sallah*

Was he gari aka tashi da runguntsumin sallah ILU kam ciki yayi Lodi ansha farin yadi dinkin nan dai NASA na bajejejiyar Riga shi akayi masa yasa hularsa tashi da kwakwa da rakalmansa yan maradi masu kyau ...can wurin sallar idi suka hade dasu basiru nan fa suka hau labarin jiya suna dariya...

Ana kammala sallah aka nufi gidan su ILU..

Tsakar gida suka iske su iya zaune anata duba kayan abinci irin na yan binni...
Ya malam wannan daga ina cewar ILU yana kara kallon kayan...

Daga BIRNI danuwana ya bada akawomin harda kudi ka gansu ya nuna masa ...

Tab!
Wai da ya malam kana da danuwa BIRNI shine baka taba fada min ba ...don kar in da gwali arziki to wllh BIRNI zani...

Aa tsaya kaji ILU danuwana fushi yake dani saboda bani zuwa wurinshi kusan shekara goma sha biyar bansashi udanuna ba ..kai yanzu bance maka ga inda alhaji kabiru yake a garin kano...

Shi kenan ya malam da haka zamu gano gidan sa gashi nan ka fadi sunansa koko basiru

Kwarai kuwa nima zan bika.. Ai koni sai naje cewar mudi...

Yawwah kaga mu ukku ma zamu ...

Uhm malam ka barshi yaje tunda yasa kansa cewar iya..

Eh wllh kila ya karo  hankali inji asabe tana dariya ...

Numfashi malam ya daukar shi kenan gobe Ku shirya ...

Tsalle su ILU suka hauyi suna murna r zuwa BIRNI.....

*hhhh Ku tareni cikin ILU a BIRNI don jin mezai gudana ka nawa Ku shirya kar bar baki ILU da tawagarsa ngd*

Alhamdulilah Allah ngd maka daka bani ikon kammala AZUMIN ILU Allah yasa sakon yakai ...ya kuma nishadantar kamar yadda nayi fata

Godiya mai tarin yawa ga masoyana ako inama suke ngd ngd

          *MAMAN MAMY*

adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *