Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Tuesday, 3 September 2019

DACEWA COMPLETE HAUSA NOVELS PDF

adsense here
DACEWA COMPLETE HAUSA NOVELS PDF
_*DACEWA*_
     ( _when east meets west..._ )


 _By_
 _Mamuh geee_


 *1*
Yan mata biyar ne a 'dakin
Wasu a zaune suna kwalliya wasu kuwa a tsaye suna shiryawa.

Hayaniya suke sosai a 'dakin sbd shirin nasu na bikin babbar aminiyarsu ne wato *ANEESAH*.
manyan 'yan matane masu class da burgewa ga ilimi da wayewa tareda tsantsar Hutu,

Dukkaninsu idan ka tsaya ka kalla babu mummuna aciki saidai banbancin kalar fata wasu farare wasu chocolate.


Qofar toilet 'din 'dakin aka bude wata kyakkyawar dirarriyar budurwa ta fito 'daure da towel wadda zatakai kimanin shekaru ashirin da shida.

Kyakkyawa ce batada jiki amma hips dinta da boobs 'dinta sun girku sosai a jikinta duk da batada jikin.


Ahankali tazo gaban mirror ta zauna tana kallon 'yan matan tace,

     Wai Ku ko kunya bakwa ji sai rawar jikin shiryawa kukeyi ni danake amaryar wanka kawai nayo.


Eh wannan kuma kinga dama ne..'dayar ta fada tana gyara eyebrow 'dinta.

Wadda ke tsaye gaban wardrobe tana saka undies ta 'dan dakata ta juyo  tace,
   
      Are you guys  seeing wat I'm seeing?
Neesah yanda kike farin ciki da rawar jikin auren nan naki da Mr perfect amma tun jia na lura sai delaying komai kike yanxu.


Ajiyar zuciya aneesar ta sauke ta matso lotion 'din jarggens tafara shafawa a jikinta kafin tace,


Amirah I just don't know why but I'm having this strange feeling like am gonna lose sumtin,
Sumtin that is so precious to me.


May b kin fara tunanin yanda zaki rabu dasu Umma ne  ki tafi gidan.


Cigaba tai da shafa manta batareda ta qara cewa komaiba.


Amirah,Hafsat,siyams da asmy sune sunayen 'yan matan kuma friends na Amarya aneesah.

 Friends ne su tun a primary school har zuwa yanxu dasuke university.

Dukkaninsu iyayensu masu arziki be sosai
Hakama kowacce akwai ilimi da wayewa sosai a gidansu,

Amirah da siyams ba farare bane sa6anin asmy da aneesah dasuke farare.

Dukkaninsu 'yangayune wayayyun 'yan mata masu tsantsar class da burgewa
Duk wayewarsu da bokonsu hakan baisa sun 6ata rayuwarsuba irin ta 'yan matan zamanin  yanzu dansu tarkacen samari ma bai damesu ba har gwara Aneesah tanada soulmate kamar yanda take fada.


Aneesah na matukar son taheer kamar ranta kamar yanda yakesonta.,
Sun hadu ne a airport 'din qasar Germany lokacin dasukaje dubo qanwar mamynta da akaiwa aikin zuciya acan.


Soyayya suke sosai wanda har kowa mamakinta yake sbd Sam bata kula duk wani namiji amma yanxu kowa na mamakinta akan tahir soulmate 'dinta.


Aneesah su biyu kacal mahaifansu former chief justice Alh sanda da Dr maryam suka haifa
Daga ita aneesah sai qaninta naseer.

Naseer na matakin qarshe a secondary school yanxu.

Dadynta nada qanwa 'daya tilo dayake matukar so sbd su kadai iyayensu suka haifa kuma suka bari a duniya.


Haj Aysha itace qanwar dadynta tana zaune a Victorian island Lagos sbd mijinta shine chief commander custom.

Ummi nada yara biyu duka maza _JAMAAL_ shine babba 'dan kimanin shekaru ashirin da biyar sbd aneesah ta girmesa da kusan shekara biyu,

Jamaal ya gama karatunsa a qasar Europe inda yanxu yazama cikakken  US navy captain kuma acan yake zama.


Jamaal kyakkyawane mai sanyin hali matuqa ga rashin son hayaniya sbd Sam ko zama bai cikayi a qasarba sbd yanayin aikinsa,

Rashin zamansa yasa iyayensa ke matuqar sonsa sbd bama kamar dadyn aneesah dake jinsa kamar 'dan cikinsa.

Ahmad shine qanin Jamaal Wanda shi yanxune yake degree 'dinsa anan Lagos.

Sai khadija 'yar qanwar dadynsu Jamaal da ummin ke riqo wadda zatakai 19 to 20 years.


 Taheer ma hadadden namiji ne iya haduwa wanda zai kai shekaru talatin da biyu da haihuwa,
Taheer kwararren gynecology Dr ne a babban hospital anan abj.

Taheer na matuqar son aneesah sbd komai nata yayi masa hundred percent saidai Sam momynsa bata sonta sbd 'yar qawarta takeson ya aura dan kawai ita gani take Aneesah batada tarbiya sbd ganin wayewarta tai yawa.

Daqyar taheer da dadynsa suka shawo kanta ta yarda akan auren nasa da aneesah gashi har anfara shirye shiryen biki.
Bayan dukkaninsu sungama shiryawa suka fito gabaki 'dayansu daga bedroom 'din aneesah suna daria sbd siyams data dizga wani a waya yanxun.


Umma suka tarar a parlo zaune tareda wata baquwa suna tattaunawa akan shagulgulan bikin.


Aneesah ta zauna kusada umman tace,

Umma zamuje wata 'yar siyayyane bazamu 'dau time ba zamu dawo.

Kallon tuhuma  umman tajefawa su amirah kafin tace,
       Yanxu dan Allah da rana tsaka zaku fita wata siyayya alhalin kuna sane sarai baikamata ana gyaraba kuna fita yawo tunda dai bikin nan yariga ya matso.

Asmy tai saurin cewa,
      Insha Allah Umma bazamu da'deba.

Yanxu dai Ku kuka sani idan umminta tazo Ai nasan bazata bar wannan shashancinba.

Tashi sukai suka fice daga palon zuwa harabar gidan

A motar siyams suka fita sbd ita tabiya gidajensu ta 'daukosu.


Ceddi plaza suka nufa
Suna isa gurin suka fara shopping 'dinsu hankali kwance cikin 'yar hayaniyarsu ta qawaye.


Wayar aneesah ce tai ringin tana dubawa taga taheer ne ta saki wani lallausan murmushi tareda 'daga wayar tace,

     Soulmate ni Allah nayi fushi.

Sorry Luv I was very busy ne throughout the day...

Oh so ure telling me aiyuka sun sa ka manta da ni.

Heyy don't say that Luv,
U know that's not true.

Naji nidai pls my Dr kazo yau I'm missing you so bad.

Hmmn bby kobaki fadaba dole nazo sbd nima am missing my Queen so badly da bazan iya bacci ba yau idan bangantaba.

Mamuh๐Ÿ’‹_*DACEWA*_
     ( _when east meets west..._ )


 _By_
 _Mamuh geee_


 *2-3*
Har suka gama shopping suka bar gurin aneesah waya take da angon nata cikin nisha'di su kuwa su amirah sai tsokanarta suke.

Saida suka biya gidansu amirah ta 'dauko kayanta sbd ita tace agidansu aneesah zata kwana har agama bikin.


Tun a harabar gidan suka shedarda baqi sun fara sauka a gidan dan haka su asmy ajesu kawai sukai suka juya sbd yamma datai sosai.


Qanwar mamynta ce tazo daga kano tareda 'yayanta uku dukkaninsu yarane.

Da hanzarinta ta isa jikinta cikin murnar ganinta tace,
        Anty Mamee oyoyo.

Kallon mamy Antin tayi tace,
       Amaryar kenan anty kika barta tana yawo shine harsai yamma suka dawo.

Ai daga yau bazata qara fitaba tunda dai gashi kinxo idan umminta ta iso saikui ta fama dan Sam wlh aneesah batason zama kullum cikin qaryar zasu karbo saqo suke.


Sorry mamy daga yau andaina insha Allah"" cewar amirah data fito daga bedroom bayan takai kayanta.


Daki suka wuce sukai sallah magriba amirah tafito Palo gurinsu mamy
Aneesah kuwa toilet ta fada tayo wanka.

Ado tai sosai cikin wata maroon Turkey's gown bayan ga qamshi dake tashi ko ina ajikinta.

Palo ta fito ta zauna kusada Anty tana turawa taheer text na cewar ya shigo Palo yafara gaidasu mamy sbd yace mata ya iso.


Knocking yayi a parlon kafin yashigo tareda sallama.

Cikeda kunya ya gaidasu mamy kafin ya juya ya fita ta miqe tabi bayansa.

Qaramin palon gidan suka shiga ya zauna yana jifanta da wani kasallen kallo yace,

Amaryan Dr you look gourgeus.

Ajiyan xuciya tasaki ahankali sbd ganinsa gaba 'daya ya sanyaya mata jiki  tace,

    Soulmate kwanakin nan ina having wasu strange feeling narasa gane meke damuna.

Tsura mata ido yayi tsawon lokaci yana karanto fuskarta shima sai yaji jikinsa na Neman yin sanyi yace,

Kwantar da hnklinki luv it's nothing or may be kina tunanin yanda zakiyi missing su mamy ne.


Firar soyayya suka hauyi sosai kafin ya tafi bayan amirah tazo ta kar6i kudi masu matuqar yawa a hannunsa na fara shirye shiryensu.


Washe gari tinda safe gidan suka tashi fresh milk kawai tasha Anty Mamee tafara gyaranta dan dama tana gyaran amare.

Su asmy ma sunzo tun safe sai hayaniyarsu suke.

Bayan angama komai tashiga wanka tana fitowa saita jiyo hayaniyar isowar ummi.


Doguwar riga tasaka mara hannu ta fito palon cikin tsananin farin ciki ta isa gurin ummin ta zauna tace,

Ummi sannu da hanya?

Cikeda qaunarta ummin tace,
       Thank you baby,ya shirye shirye?

Murmushi tayi kafin tace,
     Ummi wane shirye shirye za'ayi bakyanan.

Bari kedai baby wlh naso zuwa tun last week amma Jamaal  yace najira yananan zuwa sai mutaho tare saigashi wani aiki ya riqesa
Yanzunma bazuwa yayiba na tahowata shizaizo 'daurin auren daga baya.

Murmushi kawai tayi batace komaiba   sbd Jamaal Sam ita batama tunanin idan tagansa zata ganesa sbd sun dade basu haduba dama kuma ko magana bata hadasu sai gaisuwa shima ba kowane lokaciba dan Sam ita batason halinsa sbd girman kansa ko kallon arziki bayayi mata duk da tana antynsa bare tasamu gaisuwa shiyasa bata damu dashiba Sam bareshi da bazai iya cewa ga kamanninta ba.


Daki ta raka ummi bayan tayi sallah taci abinci suka hau fira ummin na bude mata tsarabar wasu tsinannun English wears da nights gowns data kawo mata akwati guda.Washe gari gidan ya qarasa cika sosai sbd ranar ake bridal eve,

Makeup sosai Amarya tasha cikin wani tsadadden drylace dark blue

 Friends 'din amarya ma ankon peach lace sukai da blue head.

A babban hall 'din dake cikin bistry saga mall za'ai evening 'din
Hall ya cika ya tsaru matuqa sbd gaba 'daya gurin masu ilimi da wayewa ne agurin sai abin yayi tsari sosai.


Lokacin da ango da Amarya suka shigo gurin aka fara biki dai dai isowar habib qanin umman tahir.

Tunda idanuwansa suka sauka akan neesah gaba 'daya yaji nutsuwarsa ta kunce sbd wata zazzafar qaunarta da sha'awarta yaji lokaci 'daya sun damqesa.

Yawu ya hadiye yana lumshe fitinannun idanuwansa yana qara budesu akanta.

Habib qanin umman  tahir ne kuma gogaggen 'dan duniya sbd tsaf ya kware a gun neman mata duk da kuwa yanada matarsa.


Da gayya ya ringa 6arar da kudi duk lokacin da Amarya neesah ta fito fagen rawa Wanda ita kallo 'daya tai masa ta 'dauke kai tana ta6e baki sbd irin kallon qurullar dayake mata taji ta tsanesa nan taken.


Har aka tashi gurin bikin Habib hadiye yawu yake qarshe dai yabar gurin yana sakin wani fitinannen murmushin manufa.

Duk wasu shagulgulan biki an gudanar dasu cikin farin ciki ana gobe 'daurin aure ne sukai dinner da daddare Wanda har anyi an watse neesah na zaune cikin mota tana jiran tahir yagama sallama da wasu friends 'dinsa yazo sutafi.

Waya take da amirah tana fada mata idan tahir yakawota ta tsayar mata dashi zatai magana dashi.

Jitayi anbude motar anriqo hannunta ba musu ta fito dan ta 'dauka tahir ne,

Tana fitowa saitaga Habib ta fizge hannunta da qarfi tareda tamke fuska sosai tana masa kallon qarin bayani.

Manyan lovely eyes 'dinta suka rikitasa yaji wata muguwar sha'awarta na neman haukatasa sai kawai ya fiddo handkerchief ya shaqa mata wani Abu a fiska nan ta sulale ya tarota jikinsa ya cicci6eta ya saka motarsa yabar gurin da sauri.


Mamuh๐Ÿ’‹_*DACEWA*_
     ( _when east meets west..._ )


 _By_
 _Mamuh geee_


 *4-5*
Taheer na zuwa motar yaga bata ciki
Yayi saurin danna kiran numbarta sbd tunanin ko gajiya tai da jiransa tabi wata motar ta wuce.

Ringin 'din wayarta yaji daga bayansa ya juya saiya hango wayar a qasa.

Dauka wayar yayi ya fara dubbuba harabar gurin cikin mamaki.

Amirah yakira tana 'dauka yace,
      Pls amirah bby ta iso gida kuwa?

    Nope, akwai wani abu ne?

No kawai dai nazo mota bata ciki and I called her phone but abin mamaki wayar a qasa na tsinta.

Gaban amirah yafadi ta tashi daga kwancen datake tai qasa da murya sbd kada wani yaji ayi making big issue out of it.

Kadaka fadawa kowa bari ganinan tafe gurin yanxu.


A sulale ta fice ta hau napep
Tana isa ta tarar dashi duk hnklinsa ya tashi idanuwansa sun qada jajir sbd tashin hnkli.

Sake dudduna ko ina agurin sukai basu gantaba harsun juyo sai amirah ta hango head 'din neesah cikin flowers ta ruga da gudu ta 'dauko gabanta na faduwa

Tahir kuwa jikinsa ne yaqara 'daukar rawa ya damqi head 'din yana jin tsoron abinda yake shirin faruwa dashi ace amaryarsa ta 6ata a daren 'daurin aurensu.


Amirah wayarsu asmy tahau kira tana tambayarsu ko suna tareda neesah amma kowaccensu tace aa.

Wayar mamy takira ta tambayeta ko neesah ta iso gida.

Mamy tace,
   Aa, amma yakamata ace tadawo sbd fa dare yayi kuma dai Ai anriga angama dinner metake jira ne haryanzu.

Datse kiran amirah tai sbd batamasan me zata cewa mamyn ba.


Sake kiranta mamy tayi takasa 'dagawa sai abin yaba mamy mamaki sosai nan take ta zargi ba lafiya ba ta qara kiran amirar.

Murya na rawa amirah ta dauka.

Amirah lapiya kuwa?
Ina aneesah bata wayar zanyi magana da ita.


Hawayen datake dannewa suka gangaro mata ta bude baki murya na rawa tace,

     Mamy wlh an nemi neesah an Ras.....

What? Mamy ta fada da qarfi kafin tace,
      Kamarya amirah?
Ba mumbarku a gurin ba?
Ki kira tahir may be suna tare.


Mamy gani nan tareda tahir gaba 'daya ma baya cikin nutsuwa mun duba ko ina,mun kira mutane da dama amma duk ba'a gantaba.


Sulalewa mamy tayi  ta zauna da6as a kujesa cikin tsantsar tashin hankali.

Saurin riqeta Anty Mamee tayi ummi kuwa wayar ta kar6a da sauri tana cigaba da sauraren bayanin amirah.


Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun,,,,
Shine abinda ummi ke maimaitawa cikin tashin hankali.

Wayar abban neesah takira yana 'dauka tace,
       Yaya kadawo kuwa?
     
     Alh sanda dake zaune a babban palonsa yana kallon news yace,

    Eh tun 'dazu nadawo ina Palo na.

Fita tai da sauri ta nufi palonsa tana shiga ta fara fada masa halinda ake ciki.

Sakato yayi yana kallonta cikin rashin fahimta yace,

    Aysha ki nutsu ba abinda zai faru bari nakira tahir 'din naji.


Yanda yaji yanayin muryar tahir yasashi tashi tsaye yace,

    Tahir menake ji yanxu?

Abba wlh kaina a 'daure yake da wannan alamari sbd acikin mota nabarta dan na sallami wasu baqina sai kawai na tarar da batanan.


Kwantar da hnklinka tahir insha Allah za'a ganta.


Fitowa sukai dukkansu suka ha'dudasu tahir 'din sukai station.


Acikin daren 6atan Amarya neesah ya ya'du har gidansu tahir
Wanda wasunsu ke cewa tadai gudu ne bawani 6ata.


Kasa zama umman tahir tayi tafara kai kawo a 'dakinta cikin dogon tunani da wasi wasi,

Gskia bazata iya bari tahir 'dinta datake masifar so ya auri neesah ba sbd ga abubuwa nan marasa kyau na qara faruwa.,

Duk iya yanda ake tsammanin tashin hankalin to abin ya wuce nan dan tuni gidan bikin yakoma kamar gidan makoki gashi dare ya tsala sosai amma ba Wanda yasamu damar ko kwantawa bare rintsawa.

Duk iya yanda mamy taso daurewa kasawa tayi saidata zubarda hawaye sbd fargabar menene zai faru da aneesar dan bakowa zai yarda da duk abinda zai biyo bayan ganin nataba.

Ummi kam kuka take reras dan sosai Allah yasamata so da qaunar 'yar 'dan uwantaba.


Su Abba da dadynsu Jamaal  tareda tahir 'din da babban amininsa jafar kuwa har gabanin asuba suna can tareda jamian tsaro cikin tashin hankali gurin nemanta.


Amirah kuwa tasha kuka har idanuwanta sun kumbura hakama su siyams acikin Daren duk suka iso gidan aka zauna jigun jigun jiran tsammani.Koda akai sallar asuba da qyar kowa yatashi jiki a sanyaye sukai sallah
Har lokacin duk Wanda ka kalla idanuwansa a kumbure gashi har lokacin su Abba basu dawoba.Qarfe shida na safe su Abba suka dawo zuciyoyinsu a dugun zume da tashin hankali.


Mamuh๐Ÿ’‹


_*DACEWA*_
     ( _when east meets west..._ )


 _By_
 _Mamuh geee_


 *6-7*
Zama sukai a babban palon Abba suna sauraren bayanin da dady ke musu akan iya binciken dasukai.Tahir kuwa yana isa gidan ya tarar da wani sabon tashin hankali dan kuwa ummarsa ta yanke hukuncin ko anga neesah bazai aureta ba sbd itadai hankalinta yakasa kwanciya da abubuwan dake faruwa.


Zubewa yayi gabanta ya riqo hannayenta cikin tashin hankali yace,

    Umma dan Allah kadaki yankewa neesah wannan hukuncin sbd zai lalata rayuwarta data iyayenta

Umma yakike tsammanin mutane zasu dau zancen ace neesah ta 6ata kuma anfasa aurenta
Mutane 'dauka zasuyi wani abin banzar ta aikata har aka fasa aurenta kinga daganan samun miji zaiyi mata wahala kuma ma ba duk wannan ba Umma wlh ina son neesah kamar numfashina dan Allah kadaki rabani da farin cikina.


'Dauke kai tayi cikin tunanin abinda yafada to amma idan ta yarda ya auri  neesah za'ariqa gulmar 'danta akan ya auri wadda ta gudu yawon banxa daren aurenta

Nasa mai sauqi ne duk yanda yakesonta bayan kwana biyu zai hakura ya nemi wata.


Girgiza kai tayi da sauri ta miqe tsaye cikin tamke fuska tace,

   Tahir idan har ni ce na haifeka to tabbas bazaka auri neesah ba kuma wlh nagama magana yanxu kawunka zaije yasanar musu cewar mun fasa.


Quryar 'dakinta tashige tana gama fadar hakan tabarsa zaune yana rintse idanuwansa dasukai mugun ja.

 _11:00am_

Ahankali ta bude idanuwanta dasukai mata nauyi ga kanta datakejin yayi mata wani nauyi.

Da qyar ta tashi zaune zaune tana kallon 'dakin tana lumshe ido sbd har lokacin basu gama bude mataba.


Gabanta ya fadi da qarfi sbd tuno abinda faru hartazo nan.

Jikinta takalla taga komai nata na jikinta head ne kawai babu
Ta tashi a hankali ta sauko gadon amma jiri ya hanata tsayuwa sbd jinta take kamar abuge ko tsayuwa bata iyayi ga idanuwanta suma sun kasa gani sosai.


Bango tafara bi tana  tanga'di hartakai qofa takama handle da qyar ta bude tafito palo.


Zaune yake a palon yana kur6a wine a hankali yana waya da Umma tana sanar masa yazo maza dashi da Kawu zasu gidansu neesah su fada musu anfasa auren.


Wani shu'umin murmushi yasaki zaiyi magana sai ganinta yayi tafito tana bin bango.


Kashe wayar yayi tareda aje cup 'din hannunsa yataso yana murmushi yace,

There she comes my beautiful charming baby..

Hannu yakai zai rungumota ta 'daga hannu zata maresa amma takasa sbd ko gani batayi sosai hakama jikinta a mugun mace yake.


Sheqewa yayi da wata muguwar daria yana cewa,

      Baby kadama ki wahalar da kanki bazaki iya komai ba you can't even stand  dan haka kidaina qoqarin yin wani Abu.


Qara 'daga hannu tai amma sai hannun yakasa kaiwa.


Da qarfi ya fixgota jikinsa ya matse yana shinshinata yana lumshe idanu wani 'dadi na shigarsa.Rigarta ya fara qoqarin zamewa ta tattaro wani 'dan qarfi ta turesa tana qoqarin zubewa sbd layi ta


Damqarta yayi sbd ransa daya fara 6aci gashi zata 6ata masa time harsai Umma tasake kiransa.


Matseta yayi ajikinsa yana qoqarin kai bakinsa anata.,

Zubewa tayi qasa cikin baqin ciki hawaye nafitowa idanuwanta sbd ko kadan batada qarfin qwatar kanta.


Binta yayi qasa ya cicci6eta ya yanufi bedroom da ita cikin zaquwa dan jin yake idan baiyi gaggawar kusantarta ba yanxu zai iya rasa ransa.


Zip 'din rigarta ya bu'de yafara shafar lallausau fatarta yana lumshe ido harya gangaro kan qirjinta yana 'dora hannu akan qirjinta yaji nutsuwarsa ta qara kwancewa jikinsa yadau rawa yafara qoqarin rabata da rigar ta tattaro qarfi daqyar ta turesa amma ko motsi baiyiba sbd qarfinsa da nata ba 'daya ba.


Lasarta yafarayi tako ina
Jin yana qoqarin rabata da pant 'dinta ta 'daga hannunta daqyar ta lalubo bedside lamp ta 'dagota da qyar ta  kwada masa akai.

Wata raza nanniyar qara yasaki tareda zubewa gefenta a sume.


Fadowa tai qasan gadon ta rarrafa ta fito Palo da qyar takai kanta bakin fridge 'din data hango palon ta budesa da qyar ta lalubo robar ruwa
Bata tsaya la'akari da sanyin ruwanba ta bude robar ta juyewa kanta har fuskarta sbd tunanin ko zata rage jin mayen kota samu qarfin gudu.


Sanyin ruwa ya shigeta sosai ta girgiza kanta taji wani 'dan qarfi yashigeta hakama mayen ya rage.

Miqewa tayi da sauri ta nufi qofa ta fice daga gidan tafara sauri tana waiwaye gashi ko 'dankwali babu akanta ga rigarta saija da qasa take sbd yanayin 'dinkin bridal gown.

A firgice ya tashi ya dudduba yaga tabbas ta gudu

'Daki yakoma da sauri yashirya dan gwara yaje gida su sanarwa iyayen neesah sun fasa data rigasa ta tona masa asiri gwara yarigata.


Da mugun gudu ya isa gidan ko zama baiyiba suka 'dunguma zuwa gidansu neesah.


Tahir kuwa tunda garin ya waye bai fitoba yana 'dakinsa ya rufe kansa banda zubar hawaye ba abinda yake.
Mamuh๐Ÿ’‹


_*DACEWA*_
     ( _when east meets west..._ )


 _By_
 _Mamuh geee_


 *8-9*
Saida tayi tafiya sosai cikin qarfin hali sbd har lokacin qarfin jikinta bai gama dawowa ba ga rigarta datai mata wani irin nauyi sai ja da qasa take.

Jiri taji ya fara 'dibarta kanta ya fara jujjuyawa ta sulale qasa daidai wani mai napep yakawo yayi saurin tsayawa
Itakuwa tattaro qarfi tayi ta fa'da cikin napep 'din tana fada masa inda zai kaita cikin qarfin hali.Sosai su Abba suka razana da zancen janyewar dasu tahir sukai,
daddyn Lagos  ( _dadyn Jamaal_  ) kuwa ransa ne yayi mugun 6aci ya kalli su kawun yace amma dai wannan harkar qaranta sosai kuka nuna dan banga dalilin fasa aureba kuma tsabar wulaqanci saida yarage awa biyu 'daurin aure zaku fasa ance muku baza aganta bane ko kuwa duk cikin son zubar mana da girma.....

Alh hakuri dai shine abinda zan kuma baku sbd nima nasan hakan tozarcine gareku yi muku hakan amma wlh uwar yaron ta kafe akan aure dai baza'ayiba.

Abban neesah kuwa tsabar takaici da baqin ciki ko magana ya kasa yimusu sai kallon takaici dayake aika musu dadyn Lagos ne kawai keta faman fada.Mota ce qirar landcruiser 2018 baqa ta parker qofar gate din gidan nesa kadan sbd motacin dasuka fara cika layin na 'yan 'daurin aure.


Saurayine kyakkyawa ajin qarshe 'dan kimanin shekaru ashirin da Biyar zuwa da shida.
Ba baqi bane hakama ba fari bane saidai hutu dajin dadi tareda kwanciyar hankali yasa fatarsa haske tareda wani irin sheqi.

Sanye yake cikin wata dakakkiyar shadda sky blue light mai laushin gaske,

Hakama hular Kansa blue ce sai diamond Rolex watch dake daure a hannunsa da black half cover shoes na kamfanin _gorge phelex arman_ _Jamaal muh'd abdallah._

Babban amininsa yuseef daya 'daukosa daga airport yafito cikin motar shima cikin nasa adon na 'daurin auren.

Cikin gidan suka nufa kai tsaye,

Ahmad dake harabar gidan tareda wasu baqi yayi saurin qarasowa gurinsa yana cewa,

     Yaya Jamaal sannu da hanya.

'Dan sakin fiska yayi  ya amsa tareda wucewa kai tsaye Palin Abba dai dai fitowarsu gabaki 'daya daga palon.


Tsayawa yayi yagaidasu abban suka amsa kowanne rai ajagule kafin su qara wata maganar saigasu ummi da mamy sun iso gurin.
Ahmed ma matsowa yayi ya tsaya ganin kamar dukkanin iyayen nasu cikin wata damuwar bayan ta 6atan neesah.


Habib ne ya kuma bude baki yace to mu zamu tafi Allah ya hada kowa da rabonsa hakama Allah ya shirya muku 'yarku dan gskia abin da mamaki saidai kawai muce Allah yasa ta gane idanma wani ne ke hure mata kunn.......

Wani mahaukacin mari yaji yasauka a fuskarsa saida yayi baya kamar zai kife ya 'dago da sauri idanuwansa jajir ya kalli Wanda ya kwada masa Marin.

Cikin takaici yake kallon Jamaal amma sai yaga yayi masa wani irin kwarjini ya juya afusace zai fita ba zaro yaji saukar wani Marin yana 'dagowa yaganta a tsaye tana tsoyayar hawaye,

Ba Wanda ya lura da zuwanta saidatai marin ummi tayi wurinta da sauri ta cikin ga farin ciki ga baqin ciki.


A hasale ya kallesu 'daya bayan 'daya yace,
      A haka kuke son a auri yar tashar 'yarku?
Yarinyar data gudu ta kwana gidan namiji a daren 'daurin aurenta
Hakama ta 'daga hannu ta mari babba agabanku amma baku iya 'daukar mataki ba,

To tabbas wannan marin wlh saikinyi dana sanin yinsa arayuwarki dan saiya zamar miki masifa.

Kaima kuma kasan baka mari banza ba,
Sannan bazansan kunji haushin fasawarmu ba saikun samar mata miji a yau kun 'daura mata aure koda yake wane me juyewar qwaqwalwar ne zai auri ragin wani...

Hannu Jamaal yakuma 'dagawa zai kai masa wani marin abban neesah ya riqe hannunsa cikin takaici da baqin cikin ga zuciyarsa datai masa nauyi ya dafe tareda girgizawa Jamaal kai.


Mudai bamayi akaiwa wani idan kuma gskia ne ga 'dankunan mai zafin kai saiku 'daura masa mudai mun fasa.
Ficewa sukai daga gidan hannunsa nakan kumatunsa har lokacin.


Kukan baqin ciki mamy da neesah suka saki lokaci 'daya kafin neesah ta sulale ta zube qasa a sume.


Ummi ce takamota jikinta a tsorace kafin tasa ahmad ya daukar mata ita suka kaita sama 'dakin mamy.


Jamaal kuwa fitowa yayi shida yuseef suka bar gidan yana mamakin yanda Sam wani lokacin mata basada tunanin komai girmansu
Yanxu ita wannan taje tahau wata soyayya da Wanda Sam familynsa basada tunani bare mutumci,,,
     Unbelievable "" yafada ahankali yana yamutsa fiska.

Sosai gidan ya qara kaurewa da hayaniya ga 'yan 'daurin aure tuni suka cika layin da anguwar.


Tsit su Abban sukai a palon cikin jimami da kunyar yanda zasu sanar da jama'ar dasuka taru cewar anfasa 'daurin auren.


Jiniyar isowar gwamna da tawagarsa tacika anguwar suka kalli juna Abba cikin sanyin murya yace,

     Alh kaje kasanar da jama'ar an fasa 'daurin auren kada mubarsu suita jira.

Mamy najin haka ta fashe da wani kukan Anty mamee ta dafata itama cikin tsananin damuwa.

Jiki a sanyaye dadyn Lagos yafito cikin jama'ar yana gaggaisawa da mutane
Manyan senators da members, ga gwamnoni da manyan alqalai ga maroqa tako ina waqa suke,
 ji  yayi sam bazai iyaba ya juyo zai dawo cikin gidan saiga Jamaal yadawo yi musu bankwana zai koma tunda aure yafasu,


Kwarjininsa da cikar zatinsa da dakakkiyar shigarsa tasa
Maroqa na ganinsa suka zageyesa sunai masa kirarin ango sbd tunanin shine ango.


Kallon da baifi sakan gomaba da tunani yasa dadyn sakin ajiyar zuciya ya nufi cikin gidan.

Kallon abban yayi yace,
       Justice insha Allah nasamar mana mafita kafito yanxu afara gabatarda 'daurin aure lokaci na tafiya.


Abban baice komaiba ya miqe suka fita sbd yasan dadyn komai yaza6arwa neesah daidai ne. _DAURIN AURE_
2:00pm

Abbah shiyayi wallicin ango yayinda babban amininsa former justice rufai yayi waliyi Amarya neesah aka fara gabatarda 'daurin aure.


Babban sarkin maroqa yafara yadawa a loudspeaker
Yau ranar asabar sha biyu ga Satan biyu an 'daura auren _jamalu muh'd abdallah_  da _aneesah justice sanda_ akan sadaki naira dubu 'dari.


Yuseef ne yaji abinda maroqin me fada ya juyo yana watsawa Jamaal kallon mmamaki yana cewa,

Amma wlh gayen nan ka rainamin hankali,
Dama aurenka ne za'a 'daura ka rude da cewar na neesah ne.


Wayar dayake tun 'dazu da ayeesha ya kashe yana kallon yuseef cikin lumshe fararen oily eyes 'dinsa yace,

    Uhummm me kake fadane?


Harararsa yayi yace,

Kaga rainin wayon ya isa hakanan kuma......

Moroqane suka yanyamesu kafin yace wani Abu.

Kirari suke bakin rai yuseef ya fara yi musu 6arin kudi cikin farinn ciki batareda ya nuna damuwar komaiba.

Kallon mamaki Jamaal yatsayayi kafin shima dai yafidda kudi sosai yabasu batareda yasan meke faruwa ba.


Mamuh๐Ÿ’‹


_*DACEWA*_
   _(when east meets west)__By_
_Mamuh geee_


*10-11*
Maroqa cikin jin dadi suka cigaba da watso kirarinsu sbd ganin yanda Jamaal da Yusuf ke musu 6arin nerori.


Wayarsa ce tai ringing
Da kamar bazai duba ba saiya 'dago yaduba.,

Siririn tsaki yaja kafin ya 'daga wayar tareda barin gurin ya nufi cikin gidan.

Part din dayake amatsayin nasa duk lokacin dayazo gidan can ya nufa.

Komai fes sai qamshin rose air freshener da sanyin ac dake tashi ga dukkan alama Ahmed qaninsa anan ya sauka.


Zama yayi a sofa tareda crossing legs yana amsa wayar cikin rashin fahimtar me ayeeshar ke fada ahankali yace,

     Calm down pls ayeesha sbd I don't understand a single word acikin magananki.

Wani sabon baqin ciki da takaici suka taso mata amma gudun 6ata ransa saita danne tace,

      Captain I just got a massage from a friend cewan kayi aure,I mean wai an 'daura aurenka yau.


Lumshe idanuwa yayi cikin sanyin murya yace,

    Eshaah,,,,

Jiki a sanyaye ga wani bala'i dake cinta amma ta danne itama cikin sanyin muryar tace,

    Uhumm captain,

Eshaah me kikeson nafada miki yanxu?

Inaso kafadamin idan gskia ne ko sa6anin hakan.

Ayeesha you know me,koda auren nayi banga wani dalilin qin fada mikiba sbd I have every right nayi abinda nakeso so pls kadaki kuma jin irin silly talks 'dinnan kifadamin,okay?

Batareda hankalinta ya kwantaba tace,

      Insha Allah captain.

Yaso janta da fira amma jin duk tayi sanyi sai kawai ya kashe wayar daidai shigowar Yusuf yana sakar masa dariyar qeta yace,

Ango zakasha maifa.

Batareda ya 'dago ya kallesaba yace,

  So u are the good friend da ayeesha ke fada kenan?

Zama Yusuf yayi yana shafo sumar kansa bayan ya cire hularsa cikin dariya yace,

   Eh to kusan hakan ne duk da dai bansan me kake fadaba amma dai ni ina bayan ayeesha sbd bazan iya da rigimammiyar amaryarka ba dan ko kai da kake angon bansan ya zaku qareba.

Still bai 'dagoba yana daddana wayarsa yace,

    Yusuf can you pls stop talking bcoz I'm reading sumtin hia and ure disturbing.

Daria Yusuf 'din yasaki ahankali sbd sosai ya hango yanayin zaman dasu Jamaal 'din zasuyi,

A yanda yasan Jamaal miskili mai sanyin hali da ko oho da abu
Ga neesah mai masifar jin aji da ganin ita babba yarinyace uwa uba ga son girma Wanda hakan yasa Sam ko gaisawa basayi da Jamaal sbd tana masa kallon 'dan rainin hnkali da girman kai yayi masa yawa tunda ko kallo bata ishesaba dukda tana matsayin wadda ta girmesa.,

Sosai ya hango rikicin zaman gashi alamu sun nuna Jamaal baimasan da aurenba.

Wayarsa ce tayi qara yaduba yaga ayeesa ce.
Kallon Jamaal yayi yaga har lokacin hnkalinsa nakan wayarsa.


Hello ayeeshan captain.

Daga can 6angarenta Murya a sanyaye tace,

    Yaya Yusuf pls ka taimaki zuciyata daga halinda take shirin fadawa kafadamin gskiar zance pls Yaya Yusuf.

Tausayinta Yakama Yusuf sosai sbd shi shaidane akan irin tsananin son da ayeeshar ke yiwa Jamaal duk da shima yanayimata soyayya mai sanyi.

Ajiyar zuciya ya sauke ahankali yace,

    Ayeesha ki kwantar da hankalinki dan auren Jamaal na tabbatarda bazai hanasa aurenki ba sbd yana sonki,
So ki kwantarda hankalinki sbd shima auren a bazata yazo masa.


Kuka tasaki mai cin rai tanajin wani qaton baqin cikin Jamaal 'din matar daya aura koma wacece.

Kuka take sosai Yusuf na rarrashinta a wayar qarshema kashe wayar tayi tareda wurgi da ita tana fasheewa da wani sabon kukan baqin ciki.

Kallon seconds biyar Jamaal yayiwa Yusuf cikin nazarin kalamansa sbd kallo na karantar yanayin mutum 'dabi'arsa ce.

Alamar haqiqanin gskia ya karanto a fuskar Yusuf ya aje wayarsa tareda fuskantar Yusuf idanuwansa na qoqarin 6oye 6acin ransa ya bude baki zaiyi magana Ahmed gashigo palon da sallama yakalli yayansa cikin jinjina alamarin shima yace,

    Ya Jamaal su dady na kiranka.

Lumshe idanuwansa yayi ya bude dan zuwa lokacin idanuwansa sun fara canxa launi.

 Tsaye ya miqe tareda zuba hannayensa a ajihun wandon shaddarsa ya nufi qofa batareda ya kalli Ahmed da aka aikoba.

Qasan maqoshi sallamarsa ta fito sbd sosai yaji 6acin rai na shigarsa duk da baisan dalilin kiranba amma yafara zargin maganar Yusuf da ayeesha gaskia ne,

Danne yanayinsa yayi ya qarasa kujerar nesa dasu dadyn batareda yace uffan ba.


Abban neesah shikansa yayi shakkar wannan hadin na Jamaal da neesah da dadyn yayi sbd sarai yasan neesah da taurin rai da kafewa akan Abu  gashi Sam dama bawai wani kula juna sukeda Jamaal dinba,

Shima Jamaal duk sanyin halinsa akwai taurin rai da kafiya akan Abu gashi Sam baya wasa da kowa sbd bayason shirme ko raini a al'amuransa
Shiyasa yake hango ru'du sosai a zamanta kewar auren nasu.

Dady ma yasan da duk wannan saidai a ganinsa dole 'dayansu zai aje kafewar da girman kan yabi 'dan uwansa idan lokaci yaja.


Gyara murya dady yayi fuska a 'daure yace,

   Jamaal sakamakon tozarci da akaso yimana ta hanyar fasa auren aneesah yasa ni mahaifinka na yanke hukuncin nema maka aurenta  ayau dan haka yanxu aneesah matarkace ina fatan ka fahimceni kuma zaka zamo maiyimin biyayya.

Abban neesah ya kar6i zancen da cewa,

Kuma idan ma kanada wadda kakeso ko ayau zamu iya nema maka aurenta mu hadamaka da ita..


Sosai su abban suka hango tsantsar 6acin ransa duk da Jamaal din namijin gaske ne gurin iya 6oye 6acin ransa saidai idanuwansa ne suka nuna sbd ka'dawar dasukai.

'Dagowa yayi yakalli dadynsa kafin ya duqar da Kai a maze yace,

     Shikenan Abba ngd Allah ya qara girma.

Yana fadar haka ya miqe tareda ficewa a harabar gate din gidan ya hadu da Yusuf
Kallo 'daya yamasa ya 'dauke kai ya nufi mota Yusuf ya qaraso suka bar gidan.

Ta gefen ido Yusuf ya kallesa dan tabbas ran Jamaal din a 6ace yake,

Where are we going Yusuf ya tambayesa a tausashe?

 Airport,
Yafada tareda lumshe kyawawan idanunsa cikin wani yanayi.
Neesah bata farkaba sai wuraren 4,
Wanka Anty mamy takaita toilet tayi kafin amirah takawo  mata tea mai zafi tasha tareda magani.

Sallolinta ta ranka tana idarwa ummi da mamy suka shigo.

Ya jikin baby? Ummi ta fada tana dafa kanta.

Kwantarda kanta tayi a cinyar ummin tana cewa,
Ummi jikina da sauqi amma zuciyana ba da'di.

Mamy ce ta fita 'dakin dan kuwa taso itace zata fadawa neesah maganar aurenta da Jamaal dan tasan neesah straight forward take bata 6oye 6acin ranta tsaf zata fadawa ummi batason 'danta.

Ummi kuwa cikin farin cikinta tace,
      Baby dama dole zakiji rashin jin dadi sbd fasa aurenki but koyaushe dama Allah maji roqon bawane domin kuwa Allah yayi miki sauyi da mafificin alkhairi insha Allah.

Ummi ciwo nakeji sosai a zuciya na,
Ummi inason taheer  to the extend da bazan iya aure idan badashi ba.

Cikeda tausayi duk da zancen ya daki zuciyarta ummi tace,
     Baby kidaina fadar haka domin kuwa ke yanxu matar waninsa ce,.

'Dagowa tayi daga jikin ummin tana kallon fuskar ummin tace,
       Ummi.....
   Yes baby dadynku ya daura aurenki da Jamaal ayau.

Wani murmushin takaici tasaki kafin tace,
     Ummi wane Jamaal 'din?

Jamaal 'dan uwanki mana.

Zabura tayi tsaye cikin tsananin baqin ciki da tsantsar takaici tace,

Wallahi bana sonsa har cikin raina,
Kuma ma dan ba'a sona ba'a qaunata a rasa da Wanda za'a hadani aure dan an fasa aurena sai Jamaal,yaronda na girma dan cin fuska.

Kamota ummi tayi jiki a sanyaye tace,
     Baby kadaki 'daga hankalinki tunda kinga bakyajin dadi indai akan Jamaal ne wlh bazan ta6a bari yayi miki wani cutatarwaba indai ina raye....

Wlh ummi bazan zauna dashiba dan wlh bana sonsa kuma....

Saukar mari taji ta juyo a tsorace.

Mamy ce tsaye tana watsa mata kallon takaicin yanda take ciwa ummin fuskar wai batason 'danta.

Sai alokacin wasu hawayen takaici suka gangaro mata ta durqushe qasa tareda sakin kukan takaicin Jamaal da kowama daya hada auren.*R H F W F*


Mamuh๐Ÿ’‹
*_DACEWA_*
      _(when east meets west)__By_
_Mamuh geee_


*12-13*
Duk iya yanda su mamy suka tsammani aneesah to ta wuce nan dan kuwa kuka take tamkar ranta zai fita.

Amirah da ummi sunyi lallashinta harsun gaji amma ta kafe akan lallai ita bazata zauna da Jamaal ba.

Lokacin da Abba yakirata palonsa tsayawa yayi kallonta cikin takaici.

Kuka take sosai ga ummi datai zuru tana qara lallashinta duk da tanajin damuwar yanda neesar ke kukan qin Jamaal.

Ajiyar zuciya Abba ya sauke cikin sigar lallashi yace,

     Neesah kiyi hkr kema kiyi mana biyayya tinda shima dayake namiji bai bijirewa hukuncinmu bare ke  da kike mace,

Koba komai ba ga umminki nanba zaki zauna tareda ita tunda burinki kenan koda yaushe.

Hawayen baqin ciki ta goge da hannunta cikin dasashiyar murya tace,

Abba dan Allah nidai Ku za6amin wani zan zauna dashi amma wlh ni Sam banason Jamaal ko kadan amatsayin miji.

Harara mamy tasakar mata cikin takaicin taurin kai irin na neesah.

Tsuke fuska abban yayi ahankali kafin yace,
    To naji ra'ayinki saidai ni ba ra'ayinki na tambayaba dan haka ba ruwana da ra'ayinki kije kifara hada kayanki dan wlh aure babu mai warwaresa.

A razane ta kalli abban tana qoqarin danne baqin cikin dake barazanar fixge numfashinta.


'Daki takoma ta zauna bakin gado idanuwanta dasuka kumbura na qara tsiyayar hawaye.


Amirah ce ta matso cikin sanyin jikin tausayin qawarta dan gskia badan girman kan aneesah da shegen son girmanta da saitace to babu kamarta a fagen samun miji domin kuwa Jamaal ya damesu ya shanye a fagen class da duk wata wayewa da girma dasuke ganin sunada shi uwa uba ga kyau da naira.

Neesah dan Allah kidaina 'daga hankalinki domin kuwa tashin hankalin nan bazai baki abinda kikeso ba saima lalata abubuwa dazaiyi.

 Koba komai kiduba yanda ummi ke tsananin qaunarki duk tabi ta damu akanki amma ba kunya kike dagewa da bakya qaunar 'danta a gabanta,

Ni aganina ma dakinbi abin a tausashe to saiki ga ummin da kanta tabi bayanki kin samu abinda kikeso.

Kallon amirah tayi da kumburarrin idanuwanta tana qoqarin danne takaicinta tace,

    Wlh bazan iya Rayuwa da wannan baqin cikinba,
Yanxu kamarni a kallen ace wai anhadani auren da mutumin danake masa kallon qani agurina,
Cutatuwa zamuyi mu duka dan wlh bazan kwantar da kaina nayi biyayyaba gun qanina
Haka shima yanda nasan shegen girman kansa bazai ta6a kwantarmin da kaiba,
Kinga kenan antarwatsa min burin rayuwar danaso tsarawa a gidana na aure,meyasa taheer ya cuceni ya fasa aurena alhalin munyi alqawarin gina kyakkyawar Rayuwa a tare.

Su siyams ne suka shigo dukkaninsu fuska qunshe da daria sbd sanin a kwai qura agun neesah.

Fahimtar zasu iya kawo mata rainin wayo yasa ta miqewarta ta shige toilet.

Cikin kanne daria amirah tace,
      Allah kukai mata daria fada zakuyi dan gskia she seems very serious akan zancenta na bazata yarda da aurenba.

Asmy na tu6e doguwar rigarta tace,
     Neesah is different, dan nikam hundred percent captain Jamaal yayimin koba komai ai ba kowa yasan itace ta girmesaba sbd yanayin jikinsu ma ba 'dayaba.

Cikin daria siyama tace,
      Koba komai da gani zai iya haukata mace a fagen making love sbd yanayin qirarsa ta ingarman namiji.

Daria suka sheqe da ita gaba dayansu.
*******
Zaune take bakin gadon 'dakinta idanuwanta sunyi jajir sbd kukan data kwana ta yini tana sha.

Kallon wayarta tayi a karo na ba adadi tana jiran kiransa amma shiru.


Miqewa tayi ta isa bakin window ta tsaya cikin sabon takaicin halin ko inkula irin na Jamaal.

Jamaal kayi babbar sa'a zuciyata ta riga  tayi mugun nisa akan sonka da wlh saina zamar maka masifa da bala'in da bazakaga tahowarsaba
Amma ko ayanxu saika 'dan'dani mugun baqin dafina dayafi na kunama zafi,
Ko wacece ka aura saina zamar mata baqin macijin da bataji bare tagani saidai taita jin dafina acikin jininta.


Toilet ta fada tayo wanka tana fitowa ta shirya cikin doguwar riga ta fito palon inda ta tarar da umman ta nata faman fira da aminiyarta haj shema'u.

Kwanciya tayi a two seaters tareda danna kiran wayarsa.

Shiru number bata shiga saita kira ta qasar wajensa.

Ringin tafara harta katse bai daukaba.
Qara kira tayi harta kusa katsewa ya 'daga.

Taso yimasa rigima amma yanayin muryarsa dake a 'daure yasa ta fasa dan gudun 6ata ransa,
cikeda kissa a kasalance tace,
      Captain ka koma without informing me?

Shiru yayi mata,tasake cewa,
     Lafiya kuwa captain or.....

For god sake ayeesha how many times zan fada miki banason yawan tambaya just tell me dalilin kiranan.

Siririn kuka tasaki a hankali harda shesheka.

Shiru yayi yana sauraronta duk saiyaji tabasa tausayi sbd yasan dole ne tadamu akan aurensa kai tsaye.

Jingina yayi da kujerar palonsa dayake zaune ahankali cikin cool voice dinsa yace,

      Eshaah,
Eshaah meyasa kikeson kuka akoda yaushe bayan kinsan babason kuka.

Cikin muryar kuka tace,
      Koyaushe kukana akanka ne captain sbd soyayyarka dake azabtar dani.

Yanxu gashi kayi aure ni yanxu banida stand akan.....

Ok naji daina kukan sai muyi magana.

Share hawayenta tayi cikin son qara samunsa tace,
        Pls captain don't leave me, I promise I can wait har time 'din daka shirya kar6ana.

Tausayinta ya qara shigarsa sbd hakurinta yasa koda yaushe yake qara sonta.

Naji ammadai yanxu kidaina kuka I will call anjima sainaji idan kin daina kukan saina fada miki sumtin sweet OK?

'Daga kai tayi kamar yana kusa da ita.

Tana aje wayar ta kalli Umma data nutsu tana kallonta cikin farin cikin yau tasake tadaina kuka.

Ita kuwa murmushin fara samun nasara tayi cikin shirinta na tarwatsa rayuwar neesah datayi.
*********
Zaune take a palo tana waya da asmy mamy na asibiti burin aiki Anty mamy ma takoma,ummi kuwa tana 'dakin mamy waya takeda Jamaal.

 Abba ne yashigo palon  ta datse wayar datake ta gaidasa tareda cewa,
      Abba dama inason gobe zan koma makaranta kuma gashi motana taqi tashi.


Neesah keda zaki bar gari wace makaranta kuma,
Kibari idan kinje can saiki dora.

Cikin dakewa tace,
   Abba ni anan nafison na qarasa karatuna Kuma dan Allah Abba kabarni nayi zamana anan.


Kallonta yayi ganin da gaske take yace,
     Naji amma nama fasa abinda nayi niyya na barinki anan har Jamaal ya dawo tashi jeki ki hada kayan gobe zakibi ummi Ku koma can kafin Jamaal 'din yadawo.


Magana zatayi ya daka mata tsawa tayi dakinta cikin baqin ciki da takaici.
*R H F W F*Mamuh๐Ÿ’‹


*_DACEWA_*
     _(when east meets west)__By_
_Mamuh geee_*_Viawattpad@mamuhgee_**Balkeey Shuwerh I sincerely heart you*❤*14-15*
Tun acikin daren take kuka shiyasa koda ta tashi da safe idanuwanta sun kumbura.

Fushi take da kowa a gidan dan haka ko breakfast bata fitoba.

Ummi taso zuwa ta rarrasota amma mamy ta dakatar da ita ta hanyar miqewa ta nufi 'dakin.

Zaune ta tarar da ita gaban mirror 'daure da towel alamun wanka ta fito.


Akwatinanta mamy tajawo ta bude wardrobe ta kashe kayan ciki tsaf ta jere matasu a akwati ta rufe akwatinan ta matsar gefe tareda zama bakin gado ta fuskanci neesah.

Hawayen datake dannewa suka gangaro mata ta 'dauke kai daga kallon 6angaren mamy.

Neesah,
Neesah hakan dakike qoqarin yi baida banbanci da abinda su taheer sukai mana na fasa auren 'yarmu a ranar 'daurin aure.

Mune iyayenki dasukafi duk wani mai sonki qaunarki amma kike qoqarin bijirewa buqatarmu akan wani dalilinki na banza,

Shi Jamaal 'din da kike rainawa kina masa kallon wanda kikafi qarfi tabban idan bakiyi ahankiba wataran saikin zubar da hawaye akansa illaima na sonsa illaima na qaunarsa.


Jajayen idanuwanta ta kalli mamyn dasu murya a karye tace,

    Mamy dan Allah Ku tausayamin kadaku yankemin hukuncin dazai lalata farin cikina wlh ba laifina bane dana kasa sonsa,

Nayi iya qoqarin dannewa amma na kasa kodan sbd ummi amma wlh mamy bana son ko sunansa naji ana fada amatsayin mijin danake aure.

Takaicin neesar ne yafara kama mamy amma sbd son ta rarrasheta saita dake tace,

Neesah ki daure kiyiwa iyayenki biyayya kodan yanda dadyn Jamaal yayi saving 'din abbanki daga humiliation 'din dasu taheer suka tanadar mana a idon mutane,

A 6angare 'daya haka zaki sakawa ummi da tsantsar soyayyar datake yi miki tun kina qanqanuwa,

Neesah ko kunyarta bakyaji na yanda kika fito kai tsaye kika nuna bakya qaunar 'danta datake matuqar so.

 Hawaye suka gangaro a fuskar neesah batareda ta gogeba murya a qarye tace,
   
        Mamy har abada bazan qi jinin ummi ba amma wlh mamy bana sonsa amatsayin abokin Rayuwa.

Tsuke fuska mamy tayi tareda miqewa tsaye tace,

     Tunda lallashi baya yimiki sai ayimiki yanda zakifi ganewa,
Ki tashi ki saka kayanki 10:00 flight 'dinku zai tashi zuwa Lagos.
Kuma wallahi a matsayina na mahaifiyarki ban yafe ki ce komai ba akan tafiyar nan.

Ficewa tayi a fusace takoma Palo.
Baqin ciki da takaicin datake ciki bamai faduwa bane ta danne abinta cikin ranta tareda 'daukarwa kanta mugayen alqawaririka akan Jamaal dabaimasan tanayiba danshi tuni ya aje zancen auren a gefe ya maida hankali akan alamuran gabansa.


Abba sosai yayi mata nasiha hakama mamy duk da tana fushi da ita.

Nasir ma na gida a ranar sbd Saturday ce ba school
Sosai yashiga damuwar tafiyar antynsa duk da kullum sai sunyi fada sbd shegen son girmanta da rainasa datayi Wanda shi kuma bayason hakan dan yace so yake shima Idan ya qara girma yazama handsome cool guy kaman Jamaal.


Har suka iso Lagos batace qalaba hakama batai ko guntun hawayeba sbd alqawarin datai na bazata qara zubar da hawayenta a banxa ba.Ahmed yazo 'daukarsu daga airport danshi tuni suka dawo tareda dady.


Anty nee ya hanya?

Qin kulasa tayi sbd akwai 'yar tsokana a tsakaninsu itada Ahmed 'din sbd shi ya iya bi da ita a yanda takeso.


Murmushi ummi tayi tace,

    Ahmed kadaka dami baby bata cikin yanayin tsokana yanxu.

Tofa ummi yanxu fa sai kowa ya kama kansa sbd 'yar gaban goshi tazo kowama yanzu mai laifine Idan ya ta6ata.

Harara neesah ta 6alla masa duk da tana cikin damuwa.

Daria yayi dan yaga hararar yace,
     Sorry Anty babba kada idon su juye.

Koda suka iso gida dady baya nan mai aikin ummin ce inna  rabi ta iso tana musu barka da zuwa cikin farin ciki.


Babban gidane mai 'daukeda part uku,

First one na Jamaal ne mai 'daukeda parlour da qaton bedroom aciki,

Second one 'din kuma na Ahmed ne kusan irin na Jamaal shima,
 
   The third and last one 'din shine babba sosai na iyayensu,

Babban Palo ne a qasa da 3 bedrooms kowanne da toilet,

'Daya shine na Ummy sai 'dayan na khadija ne 'yar qanwar dady da ummin ke Riqo.

'Dayan kuma na saukar manyan baqin ummin ne,.

Sama kuma gaba 'dayansa na dady ne.

Ko'ina acikin gidan ka kalla abin burgewa ne gashi koyaushe qyal qyal a tsaftace sbd dukkanin 'yan gidan masu tsaftane uwa uba inna Rabi datake kula da tsaftarsa dan a yini zatai gyara ba adadi duk da bawai wata 'daudar yayiba.

Inna Rabi dattijuwa ce datake aiki a gidan tun Jamaal na yaro Wanda yanxu ta zama tamkar  'yar uwa a gidan sbd sabo da yarda dasukai da ita bama kamar Jamaal da yake qaunarta har ransa sbd yanda take tsananin qaunarsa tun yana yaro haryanxu daya girma muddin yana gari to duk hidimarta tasace.


'Dakin ummi neesah tashige dan dama ko zuwa tayi anan take sauka dan haka yanxuma anan zata zauna.

Tsabar karma ayi mata maganar zama inda ba nan 'dinba ta bude 'dayar wardrobe 'din Ummy ta Jere kayanta.

Tu6ewa tayi ta shiga toilet tayo wanka tana fitowa tayi sallah kafin ta zauna gaban mirror ta 'dan shafa mai sbd yanayin garin da sanyi.

Doguwar rigar shaking material tasaka mai yankaken wuya da qaramin hannu ta zari wayarta ta fito Palo sbd yunwa datakeji.


Daidai qofa sukai kusan karo da khadija dazata shigo bedroom 'din sbd dawowarta kenan daga schools ta tarar dasu ummin sun dawo shine takeson mata barka da dawowa cikin farin ciki.

Cak ta tsaya ganin neesah batareda ta tsammata ba,babban abin mamakinta neesah dasu ummin sukaje aurenta itace tafara fita harta biyosu.


Jiki a sanyaye tace,
      Anty neesah barka da zuwa.

Daqyar neesah ta amsa tana qaqalo murmushi kafin ta wuce zuwa palon tana kiran inna Rabi.


Khadija kasa qarasawa 'dakin tayi ta juya 'dakinta jikinta a matuqar sanyaye ga hawayen datake qoqarin maidawa.


Tana shiga 'daki tai wurgi da handbag 'dinta tareda zama bakin gado zuciyarta kamar zata qone.


Khadija ba mummuna bace hakama bazaka kirata da kyakkyawa sosaiba saidai tanada diri mai matuqar kyau da 'daukar hankali,

Khadija tun tashinta ta taso da tsananin hassadar aneesah sbd ganin gata,kyau,dukiya,wayewa duk neesah tasamu uwa uba tsananin soyayyar da kowa ke mata bama kamar ummin wadda ita bata samu koda rabinta agurin ummin ba.,

Duk wa'innan abubuwan kanta tasowa sbd babban burinta ne tazama rich,
Pure natural Beauty,
Classy and popular,
Sbd kawai tasamu damar zama matar Jamaal data reni sonsa tun batasan kantaba,

Amma duk neesah ce tasamu wannan,
Babban abinda yasama take jin sauqin damuwarta shine babu alamar so ko kusa atsakanin Jamaal da neesah saima rashin kula da ko oho da juna dabatasan yazatai da rantaba,

Halin khadija ne hassadar duk Wanda yafita saidai takasance mai dannewa da 6oyewa sai dai abin yayita cinta arai,

Neesah Sam khadijar bata gabanta kodama can,
Duk ranar data aje baqin halinta zata saki jiki suyi fira harda ummi,
Idan kuwa hassadar ta taso to ranar ko abinci bataci saita wuni ta kwana tana duhun rai,.

Shiyasa ko yanzu sarai ta lura da batai farin cikin zuwantaba.

Ita kuwa khadija ranar 'daki kasa fitowa tayi bare cin wani abinci,

Babban baqin cikinta kyawu da burgewa dataga neesah ta qara kuma yanxu ummi batada time 'din kowa saina neesah da abinda takeso.

Abu 'daya ta qullace a ranta bazata ta6a bari jituwa ko wani shiri bare soyayya yashiga tsakanin Jamaal da neesah ba sbd Jamaal natane ita khadija.

## *_Neesah_*
## *_Ayeesha_*
## *_khadija_* ๐ŸŒฒ *R H F W F*๐Ÿ„*_DACEWA_*
      _(when east meets west)_


_By_
_Mamuh geee_


*_Viawattpad@mamuhgee_**Thanks mum AbdulAhat,,,**16-17*
Da safe qin fitowa khadija tayi koda ummi ta tambayi lafiya sai cewa tayi kantane ke ciwo kuma yau batada lectures a school.

Neesah kuwa lafiya lau tai baccinta dan kusan rabin 6acin ran datazo dashi ya tafi sbd anan ne tasan ummi zatai mata duk abinda takeso bamai hanawa ciki kuwa harda raba wannan qaddararren auren zubar mata da girma.

Kodata fito Palon guraren 11 bakowa sai inna Rabi dake kaida kawon ayyukanta.

Zama tayi a sofa suna gaisawa da inna Rabin ta'dora da cewa,

      Inna ummi fa?

Ummi takoma sama bayan fitar alhaji.

Ok, to Ahmed fa shima yafita ne?

Aa bai fitaba tukun dan baima shigoba yayi karin safe,
Yau alhaji da ummi kawai sukai kari,
Ke,
Ahmed da khadija duk kun musu tawaye yau.

Murmushi tadanyi tana duba kiran daya shigo wayarta tace,
     
       Ammnnnn Inna pls kibani breakfast 'dina a 'daki Idan kuma Ahmed yashigo kice yasameni ina nemansa.

Tana gama fada ta miqe tai bedroom tareda amsa wayarta.

Sunkuyar da kai khadija tayi cikin nauyin zuciya sbd fitowarta kenan ta tarar da neesah da innar a palon suna magana.

Bayan shigewar neesah bedroom kasa qarasawa palon khadija tayi sbd 'dan guntun qarfin zuciyarta da ganin neesah ya wargaza.,

Juyawa tayi batareda taje taci nata breakfast 'dinba takoma 'daki tana danne hawayen dake qoqarin gangaro mata ba.

Koda Ahmed yashigo palon saida yaci abinci kafin ya nufi 'dakin ummi gurin neesah,

Zaune take gaban mirror har lokacin waya take dasu amirah.

Katse wayar tayi tajuyo gurinsa tace,
 
    Ahmed so nake ka kaini gurin da zan samu lafiyayyen gyaran kai a garin nan.

Ajiyar zuciya ya sauke yana cewa,

I thought wani laifin nayi danaji kiran nan.,
Ok to kishirya nan da 50 minutes zan dawo nakaiki yanxu zan kar6o saqo wani urgent saqo ne.

Dan Siririn tsaki tasaki tana 'daure fuska tace,

      Karka kuskura ka shanyani.

Daria yasaki yana ficewa yace,

      Insha Allah Anty neesah.


Ko 50 minutes 'din bai cikaba yadawo har lokacin ummi na sama sai kawai sukai ficewarsu.

A wani babban saloon daya hadu matuqa suka Parker ta fito tashiga tana yaba gurin ba laifi yayi.

Kasancewar weekdays ne babu mutane agurin sbd aiki
Mutum 'daya ta tarar a gurin ana mata gyaran kai itama.

Kallo 'daya neesah taiwa gurin ta 'dauke kai tareda kallon 'daya daga cikin 'yan matan shagon tayi  mata bayanin abinda za'ayi mata.

Kusan atare atare suka miqe bayan an kammalawa ko waccensu abinda yakawosu.

Tsaye suke gaban tangamemen mirror 'din gurin..

Siririn gyalen data yafo batareda 'dankwaliba neesah ke gyarawa,
Ita kuwa 'dayar powder ta qara shafawa tana gyara zaman hot red jambakin dake lips 'dinta.

Idanuwansu ne suka shiga cikin na juna ta cikin mirror gaban ko waccensu saidaya buga da qarfi.

Neesah ta fara 'dauke fararen idanuwanta cikin 'dan tamke fuska zuciyarta na tsananta nauyi.

Ita kuwa budurwar kafe neesah tayi da ido tunani kala kala na shigota.

Atare suka fito neesah ta nufi mota tashiga tana qara 'daure fuska
Ahmed kuwa harzai tada motar ya hangota ta nufo motarsa
Saurin kallon neesah yayi yaga fuskarta a tamke tana duba wayarta.

Fita motar yayi ya qarasa batareda yabari taqarasoba ya sakar mata fuska sosai.

Lafiyayyen murmushi tasaki tana kallonsa tace,

     Ahmed kaima tunda yayanka ya jonamin hawan jini yayi aure ka ajeni ko?

Dariya yayi yana cewa,
      Ayeesha me zai sakaki hawan jini tunda na tabbatarda captain bazai gujekiba kinyi masa mugun kamu da sanyin halinki alhalin kuma ba sanyin halin ne dakeba.

Dariyar data qara fitar da zallar wayonta da budewar idonta tace,

     Ahmed ina jinjina maka ako yaushe da kai kadai ke iya ganoni akoda yaushe,
Amma to ai ba laifina bane sbd captain Idan bada sanyin halina da biyayyar danake masa ba aida tuni nabi sahun sauran matan dayaqi jininsu.,
Dan haka kadakaga laifina soyayyar yayanka ce,
Kuma akansa zanmayi fiyeda hakan.

Jutawa tayi ta nufi motarta tana wani shu'umin murmushi tace,

Saimun sake haduwa brother Ahmed..

Shima murmushin yasaki mai ma'a noni ya koma mota sukabar wajen.

Ayeesha kabir 'yace 'daya tilo a gurin alh kabir zaki tsohon Senator anan Lagos,

Ayeesah tun tana yarinyarta ta iya kirsa da 6oye qiyayyarta ga maqiyinta,
Ta iya kwantar da kai da biyayya akan Abu muddin zata samesa sai dai Sam bata yafiya ko mantuwa akan Abu hakama Sam,

Ayeesha batada tarbiya ko kadan sbd gata da rashin kwa6a data taso cikinsa,
Kyakkyawace sosai hakama akwai wayewa da ilimi amma na boko kawai bana addini.

Tayi karatunta ne a qasar us inda acan ta hadu da Jamaal da farko Sam bata gabansa data lura da hakan saita ringa canza halayenta agabansa sbd ta lura shi mutum ne mai sanyi saita ringa nuna juriya,hakuri da biyayya harta samu tausayinta da soyayyarta ta shiga ransa batareda ya shedar da ainihin halintaba.

Ba wasu shekaru yabata ba saidai suzo mate amma yanda take kwantar da kai ta nuna masa girmansa sosai shiyafi burgesa da ita sbd shimafa akwai son a girmamasa.

Ahmed da ayeesha sun San juna sosai sbd aminiyarta husna da  Ahmed 'din yake tsananin so.

Jamaal kawai ayeesha ke boyewa halayenta sbd batada mutumci ko kadan uban kowa bata tsoro shiyasa Ahmed yasan halinta tsaf kuma yayi iya qoqarin fahimtar da Jamaal amma yakasa sbd Sam baimaga fuska ba.

Amma tabbas shi yasan ayeesha guba ce dazata iya tarwatsa gidansu gabaki 'daya bama kamar neesah dake basa tausayi da takaici gurin son girmanta da girman kanta tareda daukar kanta ayeesha ta lalata mata rayuwa.


*******
Kusan watanta uku kenan a Lagos ba laifi rayuwar garin ta'danyi mata saidaima miskilanci daya qaru dady ya nemar mata admission university 'din nan tafara karatunta ka sabuwar motar daya siya mata duk da haka wani lokacin tareda Ahmed suke zuwa dama can shima yake karatu kuma yanxu shine abokin yawonta kusan kullum suna gurin yawon shopping dan ita qa'idarta ne ko Biro or bathroom slippers zata siya to saidai a babban mall bare sauran kayan amfani shiyasa kusan kullum suna hanya.

Ga ummi data 'dau wani sabon so da tattali ta'daura mata
Hakama tana tsananin so da qaunar khadija itama saidai son neesah dabam yake aranta sbd 'dan uwanta yayanta wato abban neesah.

Abin duniya yataru yayiwa khadija yawa dan yanxu ko lectures bata ganewa sbd ba kullum take zuwaba ga wata uwar rama data sanyota gaba duk ta rasa sukuni kullum saitayi kuka kafin tayi bacci sbd kullum rayuwar neesah qara haskaka takeeyi,

Ummi tayi lallashinta akan tafada mata damuwarta saidai tace ba komai inna Rabi ma tayi lallashinta amma duk abanxa baqin ciki da hassadar neesah na Neman sadata da kushewarta.

Yau ansamu ta'dan saki jikinta ta fito palo suna zaune suna fira,
Ummi da inna Rabi sai neesah dake kwance kanta a cinyar ummi tana chatting da amirah akan binciken data sakata akan tahir da Habib.

Kallon neesah dake kwance jikin ummi tayi ta danne hawayenta tana gaida ummi.

Khadija Yaya ciwon kan naki?
Kodai wai asibiti zamuje ne ni naga sai rama kike koda wata matsalar ne uhumm?

Zama tayi tana maida hawayenta tadan saki fuska tace,

Bakomai ummi Kaine kuma yadaina insha Allah.

To Allah ya qara sauwaqewa.

Inna Rabi ta kalla tace,
    Inna abani abinci naci ka'dan.

Yawwa khadija kokefa bara na hadamiki yanxu kuwa.

Danne duk wata damuwarta tayi ta 'dan kalli neesah tace,

       Anty neesah ina wuni?

Qyaleta tayi taci gaba da chatting 'dinta saida takuma cewa,

     Anty neesah sannu da hutawa.

Daqyar ta bude baki tace,

     Uhummm.

Neesah Sam ta tsani mutum mai 6oye 6oye sbd ita kai tsaye take abinta bata 6oyo ko tauye kai sbd tanason rayuwar cikakken 'yanci saidai Sam bata shiga ko kallon duk wani Abu dabai dametaba.,

Tun bayanxu ba ta fahimci khadija Nada abinda take 6oyewa amma takasa fa'da Ai mata magani saidai taita duhun rai wanda ita agurinta ba dalili bane ka 6oye damuwa shiyasa Sam ita khadija batai mataba.

Wayar ummi ce tayi qara tana dubawa taga Jamaal ne tasaki murmushin farin ciki tace,
       
        Jamaal kan....

Ummi kadakice komai dan nasan  abinda zakice.,

To bani dalilinka na 'daga tafiyar?

Ummina pls kadaki tambayeni dalilin coz kinsan bazai wuce work,work, work ba.

Ok then yanxu fadamin when are you coming son?

Ummi ina nan tafe ranar Wednesday Insha Allah sbd wani dalilin da sainazo zan fada miki.

Cikin farin ciki tace,
   Ok son Allah yakawoka lpia.

Ameen ummi na.

Koda tagama wayar ta kalli fuskar neesah taganta a tamke ba walwala saita saki 'dan guntun murmushi kawai.

Khadija kuwa wani farin cikine ya dirar mata Wanda rabonta dashi tun zuwan neesah gidan.

Kar6ar abincinta tayi tafaraci cikin farin ciki Wanda yabawa ummi da inna Rabi mamaki matuqa.Mamuh.

_don't forget to vote#follow#and comments viawattpad@mamuhgee._
_Don't forget to follow,vote and comments@mamuhgee#*via wattpad.._Mamuh๐Ÿ’‹_*DACEWA*_
     _(when east meets west)__By_
_Mamuh geee_


*Viawattpad@mamuhgee**18-19*
Tunda neesah taji maganar dawowar Jamaal ta rage zama sosai a gidan
Kullum tana school sai yamma sosai take dawowa data dawo kuma zatai shigewarta 'daki.

Ummi na lure ta qyaleta gudun rigimarta,
Ahmed ne kawai yake samun ganin fara'arta harsuyi fira.

 Khadija kuwa sosai take al'amuranta cikin tsananin farin ciki.
Kowa yayi mamakin sabon yanayin nata amma sukai shiru itama batareda sunce komaiba.
Ranar Wednesday tun guraren 8:00 ta tafi school sbd Sam takasa samun sukuni cikin gidan,.Duk wata hidimar tarbonsa inna Rabi da khadija ne suka yita.

A da inna Rabi ke gyara 6angarensa idan zai dawo amma wannan karon khadija ce taje ta gyare komai ta kunna aircon tareda kunna fridge 'din dake palonsa bayan taje ta 'dauko ruwan Eva katon 'daya da drinks ta jera aciki.
 Rufo qofar tayi takoma 'dakinta tayi wanka tareda zaunawa gaban mirror har zatai kwalliya saikuma ta fasa gudun kada agano manufarta,

Riga da skirt na maroon atampa tasaka tareda 'daura 'dan siririn gyale akanta tadawo Palo tazauna tana charting da wayanta cikin walwala sbd tuni Ahmed yatafi airport 'daukosa.

A nutse yake tafiya hannunsa 'daya na cikin aljihun black fanfuego trousers 'dinsa sai 'dayan hannun yana waya da ayeesha dayake dakatarwa akan kadatazo 'daukarsa Ahmed yazo daukarsa.


Kyakkyawar fatarsa dake sheqin Hutu da kyau Ahmed ya tsaya kallo harya iso gabansa daidai gama wayarsa da ayeesha ya kalli Ahmed 'din yana saka 'dayan hannunsa cikin pocket 'din wandonsa.

Murmushi Ahmed yasaki yana cewa,
       Gskia Yaya zanzo na nemi Hutu kwanan nan natafi gurinka sbd nima nasamu lafiyar fata kodan nima na riqa jawa husna aji.


Murmushi kawai yasaki batareda yace masa komai akan abinda yafadaba yace,

     Idan ka gama shirmenka kasaka kayan a mota ka kaini gida coz I desperately wanah see my mummy.

Shigewa yayi  motan shikuma Ahmed yayi saurin
Saka kayan mota suka nufi gida.


Tun a mota ya kashe wayarsa sbd yasan Sam yanxu ba Hutu ayeesha ta dinga kiransa kenan..

Suna isa gida Ahmed ya nufi part 'dinsa kai masa kayansa shikuma ya nufi palonsu ummi kai tsaye.


Cikeda tsananin farin ciki ummi ta tarbesa zama yayi kusada ita yana riqo hannunta yace,

     Ummi da fatan na sameku lpia?

Lpia klau Jamaal,
Ya hanya?

Kasalallen murmushi yasaki yana cewa,
    Alhamdulillah.

A ladafce khadija ta taso har gabansa cikin sanyin murya  tace,

       Ya Jamaal barka da dawowa.

Batareda ya kalletaba ya qaqalo murmushi yace,

       Yawwa khadija,
Ya studies naki?

Tana 'dan qaqalo fara'a itama tace,

     Alhadulillah.

Da haka ta juya tabar palon jiki a mace sbd rashin ganin fuska a gunsa Wanda dama hakan suke tun farkon fari.Inna Rabi kam kasa zama tayi sai hidimar kawo masa abubuwan sha take cikin farin ciki dan har cikin ranta Allah yadora mata qaunar Jamaal tun yarintarsa.

Murmushi yasaki har fararen haqoransa suka bayyana cikin kulawa sosai yace,

    Innah,
Inna kibarshi hakanan bana buqatar ci ko shan komai yanxu Am ok,
     Saidai zuwa anjima may b.

To Jamaal amma mutum yayo tafiya yace ko ruwa bazaisha ba.

Inna kadaki damu anjima zanci kuma ke zaki bani da kanki dan nasan yanxu ummi ta canzani batada time 'dina.

Cikin so da qaunarsa ummi tace,

     Jamaal bani kadai na ajekaba kowama har inna 'din sbd kanada mata yanzu and all kulawanka da 'dawainiyanka yana kanta yanzu.

'Dauke wuta yayi fuskarsa na 'dan canzawa sbd gaba 'daya ya manta da zancen auren da neesah.

Anyways baida matsala da ita tunda bason auren takeba afterall bayajin zai iya zama da duk macen da bazata iya respecting 'dinsaba tabasa girman daya kamacesa amatsayinsa na mijintaba koba komai baida time 'din mata irinta.

Miqewa yayi daidai shigowar Ahmed bai kallesaba yana ficewa yace,

     Ahmed take my car out to man-u car wash I have important place to go anjima.

Sashensa ya shiga kai tsaye bedroom ya nufa saidaya kunna wayarsa yakira dady sun 'dan 'dau time suna mgn kafin ya kashe yafada toilet yayo wanka.

Koda yafito dogon wandon Judhench black yasaka tareda rigar blue rugbay shirt sbd shi mutum ne mai yawan jin sanyi komai qanqantarsa.

Kwantawa yayi sbd sosai yakeda buqatar hutawa.
Bata dawoba saida maraice shi 'dinma sbd kawai ta gaji ne sosai hutu kawai take buqata.

A galabaice tashigo gidan tana parking ta fito motar riqeda handbag dinta,
Doguwar rigar turkey straight gown ce ajikinta databi jikinta ta kwanta kalar ja sai 'dan siririn red Vail data yane kanta dashi.

Sam bata lura dashiba shiyasa kai tsaye take tafiyar kamar wadda kwai ya fashewa aciki.

Kamar ance ta 'dago takalli gefenta

Tsaye yake a varandan qofar palonsa ya zuba hannayensa cikin aljihun dogon wandonsa daya canza ga alama wani wankan yayi bayan yatashi bacci,

Kafeta yayi da ido batareda wani sabon yanayi ya sauka a fuskarsaba Wanda hakan ya tabbatar mata da kallon raini ne da tsantsar wulaqanci yake mata.

Ranta ne yai tsananin 6aci ta 'dauke kai a fusace taqarasa cikin Palo ko inna Rabi dake jera abincin 'dare a dining bata kallaba tawuce 'daki tana fadin,
   
      Wlh bazan yarda da kallon wulaqanci ba bari ummi tazo.
๐ŸŒฒ *R H F W F* ๐Ÿ„


Mamuh๐Ÿ’‹_Dont forget to#vote#follow#and comments via wattpad@mamuhgee_


_*DACEWA*_
     _(when east meets west)__By_
_Mamuh geee_


*Viawattpad@mamuhgee**20-21*
Wani sahirtaccen murmushi yasaki yana cewa,

     She is unbelievable.

Fitowar dady ce tasashi qarasowa gurinsa suka nufi masallacin jikin gidan nasu dan sallar magrib da ake qoqarin tayarwa.'Dakin ummi tashiga dan gabatarda sallah sai ganinta tayi zaune gaban mirror tana Shafa mai tafito wanka fuska a hade.


Cikin kulawa tace,
    Baby yaushe kika dawo?
      Kuma maiya sameki naga duk ranki kamar a 6ace.

Danne takaicinta da 6acin ranta tayi tace,

     Ummi nidai ki tara kowa na gidan nan kice kowama ya fita harkata dan gskia ummi bazan yarda anai mini kallon wulaqanci ba idan ba hakaba zan tattara nakoma hostel da zama.

Murmushi tasaki ahankali domin ta fahimci inda zancen ya dosa idan ba kuskure tayiba to lallai Jamaal ne ya ta6a ta,
Sarai tasan Jamaal zai iya hardai idan ya fahimci bataso ta tabbas ya dingi yi mata kenan harsai yaga tana neman zaucewa kan masifa.

Shafa kanta tayi tana cewa,

     Baby kyale koma wayene ni zanyuwa tufkar hanci saki ranki babu Wanda ya isa ya 6ata ranki a gidan nan indai ina nan.
********
Washe gari tunda safe ta shirya ko breakfast bataiba ta fito cikin adon Riga da skirt na coffee atampha da 'dan qaramin gyalenta kitchen ta leqa tacewa inna Rabi tabata Apple biyu.

Riqeda apple 'din da handbg 'dinta ta fito ta nufi part 'din Ahmed.

Zatai knocking saigasha yafito a gaggauce shima tace,

    Na 'dauka baka tashiba oya bani key 'din motana ina saurine.

Zaiyi magana wayarsa tai qara yaduba da sauri ya 'daga yana cewa,

     Ya Jamaal wlh inada test ne yanxu da safen nan amma idan nadawo zan kaima.,
Ok to ngd.

Kallonta yayi yace,
     Sorry Anty neesah wlh bankai wankin motar takiba amma muje atawa mana.

Harara ta sakar masa tareda cewa wlh bazan bika ba sbd daga can akwai inda zani.

Juyawa tayi a fusace takoma cikin gida tana qoqarin shigewa 'daki ta hango key 'din mota a saman center table batai wani dogon tunaniba ta 'dauka ta fito dan duk tunaninta motar ummi ce.


Kodata fito tuni Ahmed ya wuce dan haka kai tsaye ha'daddiyar sabuwar motar ta nufa dan dama tayita kwadayin hawanta amma anqi wanketa sai yanxu dataji ummin na maganar zata bikin auren 'yar qawarta.


Da mugun speed tabar gidan dan saura mintota ka'dan su shiga test 'din.

Baki maigadi yasaki yana mamakin yau wani yahau motar Jamaal akaro na farko bayan Ahmed dashima sai idan zai kaita wanki yake hawa.Guraren 11 yafito cikin shirinsa na qananan kaya sai qamshin turaren oriflame signature dake tashi ajikinsa.


Palon yashiga cikin siririyar sallama.

Ummi ce kawai zaune a palon tana kallon tashar TLC entertainment.

Kallonsa tayi tana amsa gaisuwarsa kafin tace,

       Dadynku yayita jiranka baka fitoba and you switch off your phone harya fita.

Na manta ne ban kunna wayana ba bayan sallar asuba I will call him yanxu idan na fita.

Khadija ce taqaraso palon 'daukeda breakfast 'dinsa jere a babban tray ta aje gabansa tana gaidasa cikin girmamawa.

Yana duba wayarsa ya amsa mata batareda ya kalli gefen datakeba.

Tea kawai yasha ya miqe yana cewa ummi zai fita.

A tsarge ta kallesa tace,

      Jamaal ina zakane naga kabawa fitar mahimmanci.

Kallonta yayi yana da kyau dan son fahimto mai yasa tayi tambayar.,

Dawowa yayi ya zauna kusa da tareda riqo hannunta yace,

Ummi meyasa kikai tambayar bayan baki ta6a tambayataba idan zan fita?

To yanxu nayi tambayar kuma inason nasani.

Ummi nasan tunanin dakike kuma tunaninki gaskia ne ummi sbd Inda kike tunanin zani can zani.

'Daure fuska tayi kafin tayi magana ya miqe yabar palon.

Dawowa yayi yana cewa,

Ummi pls Ahmed yace yabar miki key 'din motana jia da dare ko.

Eh bari naji ina inna Rabi ta aje.
Khadija kira inna Rabi.

Jiki a sanyaye ta miqe sbd sosai zancen Jamaal ya daketa dan tuni taji ciwon zuciya na neman kamata na nan take akan baqin cikin dake neman ruguzo mata muddin da gaske Jamaal neman auren wata yake.


Duk inda ake tunanin ganin key 'din anduba amma ba'a gansaba saida khadija ta fito harabar gidan ta lurada babu motar tayi tunanin Ahmed ne yafita da motar saitaga babu tasa hakama iya saninta jiya motar neesah ba gida ta kwanaba kenan ita tafita da motar,

Baqin cikinta da takaicinta ne suka ninku hawaye suka ciko idanuwanta ta juyo palon jiki a sanyaye hawayenta na qoqarin zubowa.

Bedroom 'dinta ta nufa batareda tabari kowa ya lura da yanayintaba.

Harzata shige tajuyo ahankali kai 'duqe tace,

     Ya Jamaal motarfa Anty neesah ce tafita da ita.


Tunda yake rayuwarsa baitaba yimata kallon second biyar bama shiyasa bawani kamanninta yasaniba amma jin abinda tafada yasatashi 'dagowa ya kalleta da oily eyes 'dinsa dasukai masifar yi mata kwarjini da razanata da hanzari ta fa'da 'dakinta ta rufo qofa tana sakin siririn kukan baqin cikin kullum neesah ce agabanta.


Duk iya yanda yaso 6oye 6acin ransa saida ummi tagane sbd tafi kowa sanin halinsa.

Ita kanta tasan neesah bata kyautaba....

Miqewa yayi tareda komawa bedroom 'dinsa ransa a matuqar 6ace amma zata dawo tasamesa he don't think he can tolarate her nonsense and stupidity coz yafitajin duk wani abunda takeji dashi infact he will put her to her place.

Zama yake qoqarin yi wayarsa tayi qara yana dubawa yaga ayeesha ce,
Banza yayi da wayar  saidayaji batada alamar hakura da kiran ya 'daga yana cewa they are all dsame#ladies.


Ranta a tsananin 6ace yake amma yana 'dauka ta tattaro nutsuwa ta danne 6acin ran tace,

Captain my Luv ba yanxu zakazo bane naga motanka yanxu a Royallunch hotel.


Ure mistaken,,, yafada kai tsaye yana lumshe idanuwansa dasukai jan 6acin rai.

Qaqalo murmushi tayi tace,

Yes my Luv nima at first dana gani na 'dauka mistake ne but wat confuse me is the lady who is driving the looks familiar,
I think I once saw her wit Ahmed.

Bu'de idanuwansa yayi a hankali zuwa lokacin sun rine sosai yace,


She and who?

Su biyu ne my love may be is her boy friend kasan yanxu wasu na 'daukan rayuwar banxa tsakanin namiji da mace shine wayewa but ni....


Quite pls ayeesha.

Sosai ta ankaro 6acin rai a muryarsa tasaki wani shu'umin murmushin samun nasara tace,

Sorry my Luv if I said sumtin wrong.

Kashe wayar yayi tareda kiran Ahmed yana 'dagawa yace,

Where are you?

Ina school,

Tun yaushe kake school 'din?

Tun safe.,
Da problem ne ya Jamaal?

Bai masa amsaba ya kashe wayar tareda miqewa ya nufi palon ummi.

Yanda tagansa itama saidata tsorata sbd tsantsar 6acin rai da masifar data hango a idanuwansa.

Key 'din motarta ya kar6a yafita da mugun speed.

Royallunch ya nufa yana ganin kiran ayeesha amma yaqi 'dauka sbd yanda ransa ke 6ace zai iya sakata kuka da bacin rai.Hannu ayeesha tasa ta 'dau kwalbar champaign 'din dake gabanta ta zuba a cup ta kur6a tana kallon Habib tace,

Trust me sweetheart our victories days just started from today.

Mamuh๐Ÿ’‹๐ŸŒฒ *R H F W F*๐Ÿ„_Don't forget to vote, follow and comments_[5:50pm, 3/22/2018] Mamu Gee: _*DACEWA*_
     _(when east meets west)__By_
_Mamuh geee_


*Viawattpad@mamuhgee**22-23*
Neesah na fitowa test suka fito makarantar tareda sabuwar friend 'dinta datai a school 'din mai suna zeey.,

A kasalance take driving sbd yunwar datakeji.

Kallonta zee tayi tace,

Yaya ne naga kamar bakyason driving 'din?

Tana kallon titi tace,
     Yes wlh yunwa nakeji kamar naje gida.

Cikin murmushin samun sauqin aiki zeey tace,

    Why not muje na kaiki wani babban gurin cin abinci na manyan ladies kamarki I knw u will love it and d place is so calm da quiet.

Kamar bazataba saikuma tace,

   Ok then muje inane gurin?

ROYALLUNCH.,,ta fada kai tsaye.

Suna isa gurin taji Sam gurin baimata ba bawai dan bai haduba hasalima gurin ya hadu matuqa dan gurin na manyane kawai dai kasancewarsa hotel ne yasa taji Sam bazata iya shiga ciki ba.


Zeey taso tashiga amma ganin neesah ta hade fuska saita share tareda bude motar tace,

Bari nayo mana take away saimu tafi school muci nima gurin naga bai kamacemu ba sbd mutumci da qimarmu muna matsayin mata.

Ok kawai neesah tace tana qoqarin duba wayarta.

Zeey na fita ta nufi wata mota qirar camry217 modl baqa batareda neesah ta luraba sbd hankalinta nakan wayarta datake daddanawa gashi dama bata kashe motarba Ac takesha abinta.

Zuge glass 'din motar akayi zeey ta watsawa ayeesha harara tana cewa,

     Wlh hkr na yakusa qarewa sbd waccan miskilar kishiyar taki,
Ke banda abinki ma wannan ai bazatai wuyar kishiba sbd shegen Jan aji da girman kai bazai barta tabi miji ba.

Habib ne ya katse zancen da cewa,

     Shiyasa nake masifar son babe 'din I like her ego and personality hmmnnn.

Kallon takaici ayeesha tasakar masa tana cewa,

  Can you pls stop that right now before I change my mind nasa ayimin raping 'dinta once and for all nayi maganin matsalata na huta.

Wani 'dan iskan kallo ya watsa mata yana cewa,

     Wlh nafiki zama 'dan iska muddin kikai ganganci ta6ata zakiga tsantsar tantirancina so gwara ki tabbatar kin tsaya a yanda muka tsara plan,
Neesah is mine alone and captain is urs.

Bude motar yayi yafito ya nufi motar neesah cikin farin ciki yana gyara agogon hannunsa.

Harara ayeesha tabisa da ita sbd Sam takasa samun yanda takeso akan neesah sbd wata stupid soyayyarsa.

Murmushi zeey tayi tace,
   
Kibarsa eshaa,idan munsamu buqatarmu tabiya akan neesah ni nasan yanda zamuyi dashi yanda ko sunanmu yaji saiya suma wlh.

Qaramin tsaki ayeesha tasaki batareda tace komaiba tsabar takaici ita yanxu duk ba wannanba tasamu ta zamo matar Jamaal 'din tukuna.


Shigarsa motar yayi daidai da isowar Jamaal gurin tsaf ya hango shigarsa motar
abinda yafi 6ata ransa kenan ta 'daukar masa maza a mota infact ace wai motarsa a hotel.


A fusace ya fito mota ya nufi motar
Idan ba Wanda yasansa ba Sam bazakace ransa a tsananin 6ace yakeba.


A zabure ta kalli Wanda yashigo motar..

Rantane yayi mummunan 6aci baqin ciki da takaici suka taso mata
Batasan sanda ta 'daga hannu ta wanka masa lafiyayyen mari ba
Amma ga mamakinta saitaga ya shafa wajen data maresa yana wani shu'umin murmushi.

Rantane yakuma 6aci ta kallesa a fusace tace,

Ka fitarmin a mota before I decide to do sumtin crazy.

Hannuwanta biyu ya kamo da sauri daidai Jamaal ya bude motar.

Saurin sakin hannuwanta yayi cikin sigar tsoro yana qoqarin fita daga motar.

Duk da bata tsoron Jamaal sosai ta firgita da yanayin daya samesu saidai batajin zata nuna masa hakan yaji 'dadi saita 'daure fuska tamau zatai magana ya fixgota waje tareda jefa mata key 'din motar ummi da handbag 'dinta yashiga motarsa harya fara tafiya saiya tsaya tareda qarewa Habib kallo tacikin glass yaja motar da mugun speed yabar gurin.
Mamuh๐Ÿ’‹๐ŸŒฒ *R H F W F*๐Ÿ„_Don't forget to vote, follow and comments_
[6:02pm, 3/22/2018] Mamu Gee: _*DACEWA*_
     _(when east meets west)__By_
_Mamuh geee_


*Viawattpad@mamuhgee**24-25*
Tunda take arayuwarta ba'a ta6a wulaqantata kamar yauba.,

Yau ita neesar da kowa ke rububice qaninta Jamaal ya wulaqnta cikin dubban mutane,

'Dagowa tayi zuciyarta kamar zata qone takalli Habib dake tsaye gefe yana sakar mata murmushin mugunta sbd buqatars data biya na yanda Jamaal yagansu.


Zeey ce ta qaraso da sauri takamata a kidime tana cewa,

Lpia neesah?
Ina motar?

Har lokacin kallon Habib take sbd wata sabuwar tsanarsa da qiyayyarsa datakeji.


Kuka takeson yi sbd zuciyarta dake mata zafi sosai amma tsabar taurin rai taqiyi sbd gani take taci baya idan tayiwa Jamaal kuka.


Tsabar baqin cikin ko motar ummi daya bar mata bata kallaba ta hau drop ta nufi gida tanajin tsanarsa shima nashiga ranta.


Harta isa gida tsanar Habib da Jamaal na kai kawo cikin ranta

A harabar gidan ta tarar dashi yana waya har lokacin fuskar nasa a ha'de take.

Kai tsaye shi ta nufa itama fuska a murtuqe.


Sarai ya lura da gurinsa ta nufo ya qara ha'de fuskarsa sosai.


Zata fara mgna ya 'dora mata oily eyes 'dinsa cikin tsuke fuska yace,

What?

Rantane yakuma 6aci tama rasa abinda zatai masa sai kawai ta juya a fusace tai cikin Palo.

Siririn tsaki yaja yanajin tsantsar takaicinta tareda qyanqyaminta na shigarsa cox yanxu yafara tunanin abinda yasa aka fasa aurenta shine shi aka maqala masa,.
Motarsa yafada yafice daga gidan.


Khadija dake tsaye qofar parlor tana kallonsu jitayi qirjinta yayi mata nauyi tayi 'dakinta da gudu tana danne hawayenta.

Neesah ta ganta taja tsaki tareda fadawa 'daki itama sbd kukan dake qoqarin zuwar mata itama tana dannewa.


Baki ummi dake zaune Palo tasaki tana bin qofofin 'dakunan nasu da kallo cikin mamakin abinda ke damun kowaccensu.


Tana shiga 'dakin ta sulale qasa tareda sakin kukan baqin ciki,
Tabbas yau taqara tabbatarda bazata iya Rayuwa da Jamaal ba sbd bazata iya 'daukar wulaqancinsa ba.Da safe ummi hankalinta tashi yayi matuqa sbd da wani mugun zazza6i su duka suka tashi bama kamar neesah da har lokacin bata daina tsiyayar hawaye ba.


Khadija kuwa duk zazza6in dake cinta hakanan ta shirya ta gudu school sbd ganin neesah zai iya 'Dora mata hawan jini.


Zama ummi tayi tana kallon neesah jiki asanyaye tace,

   Baby kidaina kukan nan ki sanar dani matsalarki nayi alqawarin magance miki ita muddin batafi qarfina ba.


Lumshe rinanun idanuwanta tayi hawayen dake ciki suka gangaro batareda ta bu'desu ba murya a karye tace,

Ummi in gaf da rasa numfashina,
Ummi rayuwata bazan ta6a samun farin cikiba muddin ina zaune da auren Jamaal akaina,

Ummi bazan iya Rayuwa da Jamaal ba sbd halayenmu sun nesa da juna,

Bu'de idanuwanta tayi ta 'dorawa ummi murya na rawa tace,

Ummi kisa araba aurena da Jamaal wlh bazan iya rayuwar aure dashiba.


Sosai jikin ummi yayi sanyi takalli neesah jikinta na tsananta sanyi tana karanto iya gskia neesah ke fadar zancen.


Baby tabbas yau da inada dama dana rabaki da Jamaal amma kasancewata mace na rasa wannan damar saidai ina miki alqawarin samun farin ciki matuqar kikayi hkr kikai biyayya.


Rintse idanuwanta tayi tareda zamewa takoma kwance.
Ummi ma jiki amace ta miqe ta fice.Jamaal kuwa a ranar ya tunkari dady da zancen auren ayeesha kai tsaye dadyn yace ba yanxu ba.

Bai tsaya 6ata time 'dinsaba ya kira abban neesah yafada masa kai tsaye,

Abban neesah kuwa babu wani shamaki ya amince tareda alqawarin zuwa wani sati sbd ganawa da iyayen ayeesha.


Mamy dataji sosai tashiga damuwa sbd sanin halin neesah na girman kai bazai ta6a bari taji 'dadin rayuwar aureba gashi har za'ayi mata kishiya da wuri haka batareda tasan wani da'din aurenba.

Abba bayan yakira dady sunyi mgn shima dadyn ya amince ummice ta tsaya tsayin daka akan bata aminceba.


Sam Jamaal yanxu baicika zama gidanba sosai sbd Fushun da ummin keyi dashi akan mgnar.Yau zaune suke Palo ummi na lalla6a neesah akan tasha magani inna rabi kuwa sai dariyarsu take.

Khadija Ce tafito 'dakinta tazo ta zauna kusada ummi  duk ta hargitse ga wata uwar rama datai.

Kallo ummi tabita dashi cikin damuwa da tausayinta zatai magana inna Rabi tarigata da fadin,

Ummi 'yayanki dai lpia tayi musu qaranci musamman ma khadija duk tabi ta rame.

Hmmmn inna Rabi wlh ita khadija nama kasa sanin damuwarta har gwara baby ita nasan matsalar aurentane da jamaal....

Wata mummunar qwarewa khadija tayi wadda ta haddasa mata wani yunqurin amai ta sbd jin maganar ummi ta qarshe wai Jamaal mijin neesah.

Ummi dake zancen Sam bata luraba sbd hankalinta nakan neesah sake shan magani taci gaba da fadin,

Sannan yanxu dan tsabar rigima yace wani auren zaiyi kafin yakom......


Kusan atare neesah da khadija suka aware gaba 'daya ruwan dake hannunta suka xube had glass cup 'din nafashewa itakuwa khadija miqewa tayi ta nufi janyar bedroom ko gani batayi sai kawai su ummi ganin sukai ta yanke jiki ta fadi asume.
Mamuh๐Ÿ’‹๐ŸŒฒ *R H F W F*๐Ÿ„_Don't forget to vote, follow and comments_๐ŸŒฒ *R H F W F*๐Ÿ„_Don't forget to vote, follow and comments_
[6:28pm, 3/26/2018] ‪+234 802 437 1121‬: _*DACEWA*_
     _(when east meets west)__By_
_Mamuh geee_


*Viawattpad@mamuhgee**26-27*

A rikice sukayo kanta ummi na kiran sunanta da qarfi amma Sam ko numfashi babu alamar yana tareda ita.

Shigowar Ahmed yasa ummi kallonsa a kidime tana nuna masa khadijar sunkutarta kawai yayi yafito su ummin suka biyosa zuwa asibiti.


Har suka fice neesah na zaune bata motsaba sbd baqin ciki da takaicin datake ciki na zancen auren na ummi tace zaiyi,
        Imagine ace ita qaninta zaiwa kishiya dan ya rainata,
Baqin cikinta 'daya da auren nasa shine  friends da sauran mutanen dasuka santa amatsayinta na babbar yarinya yanxu zasu riqa ganin itadin ma ba kowa bace a gun Jamaal 'din data raina,,,wato yafita zama 'dan rainin wayo,
To wlh bari ummi tadawo bazaiyi auren nan ba saiya saketa.


A zafafe ta miqe ta nufi hanyar bedroom taji an fixgota harsaidata fa'do masa cikeda tsoro ta 'dago idanuwanta suka shiga cikin nasa daya kafeta dasu,

'Daure fuska tayi tareda fixgewa da qarfi itama tana watsa masa irin kallon rainin dayake watso mata tace,

      Karka kuma ta6ani dan ni ba sa'ar ta6awankace ba so better stay within your limits and karkayi tunanin 'dan na hakura nadawo nan yana nufin na amince da zama da wannan auren sunan....

Fixgota yakumayi ta fado jikinsa ya matseta tareda kallon tsakiyar idanuwanta cikin ra'da yace,

Banajin kinada jikinda yakai matsayin ta6awa a guna cox na girmi tunaninki sbd ni mutum ne mai qyanqyami and I don't like wat is common to people especially downgrade pple and you see this body of urs is like a common market tomatoes,
And maganan zuwanki nan I think its your problem not mine.

Tureta yayi daga jikinsa ta fa'di qasa kan hannunta ya bugu,
Magan ganunsa sun qona ranta matuqa kamar ita ya kalleta yace kamar tomatoes take a kasuwa.

Cikin qunan rai ta 'dago da idanuwanta dasuka ka'da zatai mgn ya tamke fuska tareda watsa mata kallon zallar qyama ya fice daga palon batareda tasamu ta fadi 6acin rantaba.


Hawayen baqin ciki da tsanarsa suka gangaro mata ta miqe ta fa'da bedroom tana jin kamar zuciyarta zata qone.A asibiti saida khadija ta share 5hours kafin ta farfado kuma tunda ta farfado take hawaye ummi tayi lallashi da tambayar harta gaji amma ko magana khadijar taqiyi.

Sallamarsu Dr yayi bayan ya tabbatar musu da damuwa ce tayi mata yawa kuma tana gab da illatata matuqar ba 'a dau matakin rabata da itaba dan haka suje gida su rarrasheta ta fa'di damuwarta.


Har suka iso gida hawayen khadija sun kasa tsayawa gashi xuwa lokacin idanuwanta da duskarta tayi mugun kumbura sbd kuka amma takasa daina hawayen.

Hankalin ummi sosai ya tashi gashi suna dawowa sun tarar da itama neesah ta rufe kanta a 'daki tana kuka.

Zama ummi tayi bakin gadon bedroom 'din khadija tana kallon khadijar dake kwance ta rufe idanuwanta ga hawaye na gangarowa cikinsu jiki a sanyaye tace,

     Khadija na roqeki ki fadamin damuwarki sbd haryanxu zuciyata takasa yarda da cewarki ta wai karatu ne yayi miki yawa a school.


Bu'de idanuwanta tayi daqyar sbd kumburinsu murya a dashe tace,

     Ummi Ki yarda dani Allah karatune yamun nauyi a school,
Ummi da inada wata matsalar bayan wannan dana fa'da miki sbd banda wata uwar data wuceki a yanxu.

Ajiyar zuciya ummi tasake tana shafo kan khadijar cikeda kulawa tace,
       Idan kuwa karatu ne khadija saidai kiyi hkr dan kuwa kinbarsa kenan sai zuwa nan gaba qila dan banga amfanin karatunba matuqar yana barazana ga lafiyarki da rayuwarki saiki haqura kawai.


Lumshe idanuwanta tayi cikin tausayin kanta dan ko ummi batace tabar karatuba batasa ran idanma taci gaba dayi zata fahimcesa sbd halinda take ciki.


( _hassada mugun ciwo ce 'yan uwa dan Allah Ku tsarkake zukatanku_)Neesah ma duk yanda ummi tasojin dalilin kukanta kasa fa'da tayi sbd har lokacin bata daina hawayen baqin cikin maganganunsa.
*******
Kallon maganin hannun husnah tayi ta yamutsa fuska tace,

       Do u know wat husna I don't think I can use this dan gskia nima inada qyanqyami bare Wanda zanbawa duk da basani zaiyiba amma ina fargabar yaji warinsa a cikin koma mai zan saka masa aciki.


Harararta husnah tayi tace,

Wannan kuma matsalarki ce dan nidai nasan irin su Jamaal masu shegen girmankai da jan ajin tsiya sai an hada musu da asiri suke lanqwasuwa..

No no no, zeey tafada tana saukowa daga gado tace,

Samun kyakkyawan matsuguni a zuciyar irinsu captain hanyar 'dayace,
Wato amfani da kirsa tareda kwantar da kai ka nuna biyayyarka.

Yes zeey nima I prefer that akan wannan 'din sbd wannan zai sakashi ya soni ne kawai nikuma nafison qiyayyarta tafi soyayyata a zuciyarsa duk da nasan ba wai yana sonta bane hasalima yanxu tsanarta da qyamarta yake tun ranar da ya kamata da Habib.,

Zeey dake shafa lips stick gaban mirror ta juyo tace,

Nakuma tabbatarda saita gwammace Rayuwa a baqin kabari da zama dashi sbd muguwar tsanarta dazamu saka masa just kwantar da hankalinki qawata luck is on our side.


Shu'umin murmushi tasaki tareda 'daga wayarta ta danna kiransa..

Fira tashiga jansa cikin kwantar da kai duk da ita kadai ke firar iyakacinsa sauraronta sbd baya iyawa da surutun ayeesha.....lectures suka fito ta lura da yau miskilancin yafi na kullum ta kalleta cikin nuna kulawa tace,

     Neesah akwai abinda yake damunki ne? You look pale.

Yamutsa fuska tayi batareda tace komaiba har suka isa mota kafin sushiga amirah takirata tana 'daukar wayar tasaki ajiyar zuciya tana cewa,

      Thank god amirah you called ina tsananin buqatan magana dake.

To inajinki''amirah tafada daga can 6angaren.

Amirah asmy tazo lagos tun jia ina buqatan magana da ita since dukkanku bakwa kusa tace she's coming over today and now I can't reach her number so jst send me aunt fateema's Address I can't wait.

Zan turo miki address 'din yanxu idan kin isa ki kirani nima inason mgn da ita before su wuce Paris tomorrow.

Ok bye.


Duk wayan datake hankalin zeey nakai amma a kallo bazakai tunanin hankalinta na gunba.


Sai gaf da magrib suka fito school duk da gajiyar dasuka kwaso neesah tace bazata gidaba harsaitaje taga asmy sbd gobe zasu wuce Paris da iyayenta gurin checkup nata na ciwon heart datakeda shi.


Sbd nisan anguwar da hold up yasa har akai magrib suna hanya.

Kallon zeey tayi a fakaice sbd ganin tunda suka fito take exchanging texts a waya.

Suna gaf da isa gidan text yashigo wayanta tai banxa dashi,
Zeey ta kalli wayar takalli neesah cikin tsokana tace,

Neesah kamar anyi miki text ko?

Lumshe fararen idanuwanta tayi tana cewa,
        Ummn anjima zan duba idan nasamu time.

Qaqalo murmushi tayi tace,

     Inaga kiduba cox may be wani mahimmin saqone qilama amirah ce.

Juyowa neesah tayi ta kalleta sbd ganin damuwarta nason ta bude saqon.

'Daukar wayar tayi ta bude massage 'din.

""" _hey neesah itz me asmy ga address 'din dazaki sameni nan sbd ba gidan Anty fateema na saukaba_""

Sake maimaita karantasa tayi kafin tasaki 'dan qaramin tsaki tana juya kan motar zuwa address din da asmyn ta turo mata yanxu.


Ajiyar zuciya zeey tayi a 6oye tareda turawa Ayeesha saqo ta maida wayar cikin Jakarta.Zaune yake a palonsa yana kallon news dawowarsa daga masallaci kenan sallar magrib..

Wayarsace tayi ringing ganin unknown number yasa bai damu da daukaba.

Cigaba akai da kira yaqi 'dauka saiga kira da number ayeesha.

Saida yasaki qaramin tsaki ya 'daga wayar tareda ha'de fuska sosai sbd muryar namiji dayaji.

A ki'dime mutumin yake fadin,
     Bawan Allah koma ya kake dame wayarnan kazo yanxu da gaggawa a waffroad sbd tana ana gaf da lalata mata rayuwarta.

Kallon wayar yayi tareda zarar key yafito da mugun speed.
Suna isa address 'din lokacin ana sallar ishai ga anguwar tsit babu mutane da yawa.

Parking tayi tareda 'daukar handbag 'dinta tafito ta nufi cikingidan tana mamakin maiya kawo asmy irin wannan mataccen gidan sbd gidanma is like uncompleted building.

Ihun mace taji a 'dakin dake farkon shigowa gabanta na faduwa ta nufi 'dakin ta tura qofar 'dakin da sauri taja baya sbd ganin ayeesah a kwance kayanta duk a 6arke ga bakinta na jini alamar bugu sai maza hudu tsaye akanta.Koda ya parker bai lura da motar ta agurinba ya nufi cikin gidan da saurayin yayi masa kwatance daidai nan qartin suka fito da gudu jikinsa har rawa yake ya nufi 'dakin

Kuka take tana kakkama jikinta tana cewa,

Na roqeki kadakisa su keta haddina ki taimaki rayuwata kiji tausayina koma mainayi miki ki.....

Cikeda mugun tausayinta da sabuwar soyayyarta ya nufeta tareda rungumota jikinsa idanuwansa na ka'dawa zuwa jajaye .

Rintse idanu neeesah dake tsaye tayi.

Bude idanuwansa yayi akanta cikeda xafin rai ya taso ya yarfa mata wani lafiyayyen marin daya 'dauke ganinta na daqiqu...


Mamuh๐Ÿ’‹๐ŸŒฒ *R H F W F*๐Ÿ„_Don't forget to vote, follow and comments_


_*DACEWA*_
     _(when east meets west)__By_
_Mamuh geee_


*Viawattpad@mamuhgee*
*28-29*

Zafin marin yasata zubewa qasa kan gwiwowinta idanuwanta suka ka'da jajir amma Sam taqi yarda hawaye zubowa fuskarta
Kallonsa take ido cikin ido zuciyarta na quna,
Ji take kamar numfashinta zai bar qirjinta sbd mummunan baqin cikin Marin daya sharara mata.


Fixgota yayi tareda jefar da ita qasa idanuwansa sun rufe sosai da 6acin rai ya nufota tareda kamo wuyan rigarta ya 6arka da qarfi yace,

Kinason kisa ayi mata fyade sbd bakisan ya baqin cikinsa yakeba to yau zan 'dandana miki baqin cikinsa.

Yaga rigarta yayi qirjinta ya bayyana yakai mata wata muguwar cafkar da zafinta yasa hawayen datake dannewa suka gangaro hakama idanuwanta a rintse suke tsabar baqin ciki ko qoqarin hanasa bataiba sbd gangar  jikinta data daina aiki.


Ganin idanuwansa a rufe suke da 6acin rai zai iya abinda yace 'din tayi saurin sakin wani sabon kuka mai ta6a zuciya tareda  rungumosa ta baya cikin kuka take fadin,

Captain ba halinka bane karkayi na yafe mata koma wacece ita,,

Juyowa yayi ya rungumeta cikin jikinsa yana daidaita numfashinsa kafin ya dauketa ya fice gurin da ita.


Suna fita zeey ta qaraso gurin da sauri tana kallon neesah cikin mamaki da kulawa tace,

Neesah?

Jajayen idanuwanta ta bude zeey tai saurin ja baya cikin zatana sbd tsantsar fushi,6acin rai tareda qiyayya data gani kwance a fuskar neesah.

Murmushi tayi aranta dan tasan wannan qiyayyar ta Jamaal datake gani a idon neesah  bamai gushewa bace koda zata gushe to tabbas ba yanxuba.

A fili kuwa rungumo neesah tayi tana fashewa da kuka tace,

Neesah dan Allah karki cemin abinda nake zargi shi ya sameki?
Neesah dana sani da bazan bari kishigo ke 'daya ba.

Rintse idanuwa takuma yi ta jinjina tarin qiyayyarsa dake bin jini da jijiyoyinta.

Gyale zeey tajawo tareda rufawa neesar takamota suka fito har lokacin idanuwanta a lumshe suke.

Seat 'din gaba ta zaunar da ita kafin tazagaya ita taja motar.


Allah yasa koda suka isa gida ba kowa a Palo ta kaita har bedroom 'dinta tayi saurin fitowa ta nufi gida dan Sam ba yanxu take buqatar Jamaal ya Santa ba sai zuwa gaba.


Gaban mirror ta tsaya tana kallon jikonta da duk rabi yake waje sbd 6arkar da Jamaal yayiwa rigarta,.

Ihu tasaki mai qarfi tareda 'daukar qwalbar turare dake gaban mirror ta fasa madubin tana fashewa da wani irin kuka mai qarfi da ciwo dan wannan abin da Jamaal yayi mata baida bambanci da fyade.

A rikice ummi da inna Rabi suka nufo 'dakin amma gam suka jishi a rufe.

Bugawa ummi tahauyi tana kiran sunanta amma ko jinsu batayi sbd kukan datake tana dukan madubin.


Ahmed daya shigo palon yayi saurin qarasowa yana tamvayar lapia.

Ahmed bude qofar nan tun kafin ta illata ko kashe kanta.

Palon dady ya nufa da gudunsa ya 'dauko keys masu yawa yafara gwadawa jikinsa na rawa danko keys 'din da qyar suke tsayawa a hannunsa.


Jan jikinta data farfasa da kwalba ga gashinta duk a hargitse ta fa'da toilet tareda tu6ewa ta shiga bathtub dake cikeda ruwa ta kwanta tareda nitse kanta sbd bazata ta6a iya Rayuwa da wannan tsananin baqin cikinba da tarin tsanar datakeji tana yiwa duk wani Wanda ya danganci Jamaal 'din bare shi kansa dan gwara mata mutuwa da rayuwa.


Da qyar yasamu key 'din daya bu'de dakin har ture ture suke wajen shiga 'dakin
A tsorace ummi tace,
Nashiga uku ni ayshatu me zangani?

Toilet 'din ta nufa da sauri ba wani 6ata lokaci ta fada ai da gudu ta qarasa bakin tub 'din tareda sakin salatinda ba qarashe da qarfi tana kiran sunanta.

Inna Rabi ma qarasowa tayi cikin tashin hankali tasaki kuka tana cewa,

Allah yasa ba mutuwa 'yar nan tayi,

Ahmed da duk a ru'de yake ji yake kamar ya fa'da toilet 'din murya a qage yace,

Ummi Ku kamota Ku fito da ita mana sai Ai asibiti da gaggawa.

Qoqarin kamota suke amma sun kasa sbd jikinsu dake matuqar rawa sbd tashin hankali gata ba kaya bare Ahmed 'din ya 'dauketa,

Cikin kuka ummi tace,
Ahmed maza kiramin Jamaal yazo da gaggawa.

Ganin waya 6ata lokacine ya fita da gudu yai sashen jamaal,
A qofa suka ha'du dawowarsa kenan zai shiga,

Cikin son tattaro 'yar nutsuwa yace,

Ummi na kiranka da gaggawa.

Falon ya nufa da hanxarinsa danshi a tunaninsa ummin ce wani Abu ya sama sbd dady baya gari.


Tun a Palo yake jiyo kukan ummi tana kiran sunan neesah.,

Gabansa yayi mummunar fa'duwa sbd jin sunan wadda ake kira cikin kuka, qarasawa ciki yayi, yana arba da fasashin kwalabe da jini a tsakar 'dakin yaji qirjinsa yayi wani mugun nauyi da qyar ya isa qofar toilet 'din ya hangota kwance cikin ruwa bata numfashi
Idanu ya rintse da qarfi nauyin zuciyarsa na tsananta,

Patoranking half shirt 'dinsa ya cire tareda zura hannu ya fiddota ruwan jikinsa har wani rawa yake
Ummi da inna Rabi suka fito jiran ya kimtsota.

Rigar ya zura mata takai har gwiwarta ya sunkuceta bai tsaya bita kansu ummiba yasakata motarsa kafin sufito harya fita da wani mahaukacin speed da saura ka'dan ya tafi da qafafun mai gadi saida yayi wani mugun tsalle haryana fadawa cikin bokitin wankin dayake.


Fitowar Jamaal ba Riga 'daukeda neesah yasa khadija tabar bakin qofar tanaji qirjinta na cixo hawaye suka gangaro mata tai 'daki da sauri tareda rufo qofa ta sulale bakin qofar ta cusa kai cikin qafafu tana sakin kuka ahankali.


Ummi kuwa motar Ahmed suka nufa yajasu sukabi bayan Jamaal dake gudun tashin hankali.

Ahmed ma gudun yake cikin tashin hankali dan sai yanxu dayaga zai rasa neesah ya tabbatarda feelings 'din dayake ji akanta kuma a shirye yake daya fuskanci kowa yanxu akanta tunda batason Jamaal yazama dole arabata dashi.
_Kuyi Manage ba enough time_
Mamuh๐Ÿ’‹
๐ŸŒฒ *R H F W F*๐Ÿ„_Don't forget to vote, follow and comments_


_*DACEWA*_
     _(when east meets west)__By_
_Mamuh geee_


*Viawattpad@mamuhgee*
*_I sincerely heart you too my Raheenat (heenat)_**30-31*


Emergency ward suka nufa kai tsaye Ahmed idanuwansa har wani yaji suke sbd Jan dasukayi ji yake zai iya rasa ransa idan wani Abu yasamu neesah.


Zaune suka tarar dashi yayi crossing legs yana duba wayarsa,

Sarai yasanda qarasowarsu amma ko motsi baiyiba bare ya 'dago ya kallesu.

Jigum jigum sukai suna jiran tsammani
Ahmed kuwa kasa zama yayi sai kai kawo yake.

Almost 2 hours suna jiran kafin wata Dr yafita room 'din yana zare coat 'dinsa,

Ahmed ne ya nufesa da 'dan hanxari ummi ma baza idanu da kunnuwa tayi tana jiran jin abinda zai fada,

Shidai yana nan still ko alamar kulasu baiyiba
Dr ya kallesa kafin ya maido da hankalinsa gurin Ahmed 'din yace,

Well numfashinta ya dawo saidai raunikan data jiwa kanta suma anyi dressing nasu all she really needs right now shine abari tasamu isashen Hutu,
Dan haka zaku iya komawa gida gobe da safe Ku dawo.


Ajiyar zuciya ummi da Ahmed suka saki atare kafin Ahmed yakalli ummi cikin marairaice fuska yace,

Ummi kije gida I will spend the night hia.

'Daure fuska ummin tayi tareda kallonsa tace,

Bakada tunani ne zaka ce zaka kwana anan kana namiji tana mace kuma matar 'dan uwanka.

Ha'de rai shima yayi kai tsaye yace,

Na za6i kwana anan ne sbd nine na cancanta,
Nine nake tsananin so da qaunarta Wanda bazan ta6a 6arin cuta kusantotaba sa6anin mijin nata da kike fada na tabbatarda shine sanadin koma meyene yasa takeson kashe kanta.


Idanuwa ummi ta zaro cikin tsananin tsoro tace,

Ahmed me kakeson fahimtar dani?
Idanma namiji ne dole zai kwana aikafi kowa sanin Jamaal ne ya cancanta.

Juyowa tayi gurinda Jamaal 'din me zaune zatai magana taga wayam basa.

Ta maido da kallonta ga Ahmed da alamarinsa yafara bata tsoro tace,

Muje gidan ka 'dauko inna Rabi ita zata kwana anan 'din.

Kai tsaye ya yarda sbd dama Jamaal 'din ne bayaso ya kwana tareda ita.1:00am

Kasa kwanciya yayi ya zauna bakin gadonsa yana lumshe idanuwansa da har lokacin sunke qunshe da 6acin rai mai tsanani daya kasa tantance kona meyene.

 Rintse ido yakumayi da qarfi maganganun Ahmed na qara yawo cikin kansa.

Me Ahmed ke nufi?
Raini ne wannan dazai bu'di baki yace yana son matar dayasan aurensa na kanta ko kuwa dama can soyayya suke in secret?

Saurin rintse ido yayi yanajin 6acin rai da fushi.

Zamewa yayi ya kwanta idanuwansa a lumshe yana fatar wannan tunanin na Ahmed da kowama yafita ransa.
Da safe da wani mugun ciwon kai khadija ta tashi amma haka ta daure ta girka breakfast sbd ummi datace tayi.

Komai ta gama ta ha'da nasu neesah a basket ta aje tashiga 'dakinta tayo wanka ta shiryo dan itace zatakai abincin duk da zuciyarta ba qaramin dauriya takeba gurin ganin ta danne baqin cikinta da damuwarta.

Doguwar Riga baqa tasaka tareda siririn yellow Vail ta fito ta 'dauki basket 'din ta nufi 'dakin ummi.


Zaune ta tarar da ita a gado ta gaidata tareda cewa,

Ummi zan kai musu breakfast 'din daga can inason naje gurin saloon.

'Daga kai ummi tayi sbd yanda kan ke mata ciwo itama na rashin bacci da damuwar data kwana da ita jiya akan bala'in dataga na shirin afkowa tsakanin 'yayanta dan Abinda tagani jiyan a idanuwan Ahmed ya tsoratata sosai hakama tasan  tsaf Jamaal ya dame Ahmed ya shanye fagen taurin rai da zuciya mai tsanani.


A hankali ummi ta bu'de baki tace,

Ki gaidaminsu kafin na qaraso anjima Insha Allah.

To,,tace tareda ficewa jiki a sanyaye.

Tana Sanyo kan  motarta wajen gate din gidan daidai zeey zata shigo amma mai gadin ya dakatar da ita akan neesah batanan.

Tsayawa khadija tayi tareda sauke glass takalli zeey ba 'daurewa ba sakewa tace,

Neesah na asibiti tun jiya idan xaki ne muje can zani.


Shiga motar zeey tayi tana mamakin yanayin khadijar sbd yanda take ba wata walwala atareda ita.

Har suka isa ba Wanda yayi mgn
Tanayin parking suka fito atare suka nufi 'dakin gaban khadija sai tsananta nauyi yake duk taqara taku guda na zuwa 'dakin.


Har lokacin barci take Inna kuma na zaune tana gyangyan'di.

 neesah zeey ta nufa kamar zatayi kuka tana cewa,

Neesah Allah ya sassauta miki wannan jarabawa.


Ameen inna race  tana karbar kayan hannun khadija.

Ido khadija ta kafawa rigar Jamaal dake jikin neesah tanajin karyewar zuciya da hawaye na yunquro mata.

Abincin inna ta 'diba ta fita waje dan taci
 itama khadija juyawa tayi ta fice jiki ba kwari.


Miqewa tsaye zeey tayi tana shu'umin murmushi ta bu'de handbag 'dinta taciro wata kwalba tana dariya ta nufi abincin ta bude flask 'din ruwan tea tazube gaba 'daya abinda ke cikin kwalbar ta rufe flask 'din
Tana juyowa gabanta yayi mummunar yankewa nan take jikinta ya'dau rawa sbd khadija data gani tsaye bakin qofa tana kallonta.

Zufane ya yanko mata cikin rawar murya tace,

Um um um maganin.....

Wuceta khadija tayi ta zura hannu cikin basket 'din data kawo musu abinci ta 'dauki mukullin motar ta tafice cikin wani irin yanayi bawai dan bata ga abinda zeey 'din tayiba
Bata buqatar sanin koma meyene manufar zeey akan neesah dan tun kallon farko dataiwa zeey ta fahimci babu alkhairi a tattare da ita amma koma meyene ba abinda ya shafeta koma kashe neesah zatayi.


Yawu zeey ta ha'de tareda sakin ajiyar zuciya dataga khadijar ta fita batace komaiba alhalin ta ganta sarai.

Komawa kujera tayi ta zauna tana share xufa cikeda mamakin khadija.


Ahankali neesah ta bude idanuwanta daidai  shigowar Ahmed tareda Dr da nurses guda biyu.

Kallonta Dr yayi yana murmushi yace,

Finally sleeping beauty ta tashi.

Ahmed dake kallonta cikin murmushi yace,

Dr inajin kunyanka fa sbd wannan sunan yayi maka nauyi.


Dariya sukai dukkaninsu ita kuwa lumshe idanuwa tayi tanajin wata irin matuwar jiki.

Fita Dr da nurse 'din sukai bayan ya duba file 'dinta yayi rubutu aciki.

Matsowa kusa yayi tareda kafeta da fararen idanuwansa hannuwansa a har'de cikin wata sabuwar lallausar murya yace,

Antynahhh..

Har cikin ranta taji yanda yaja sunan ta bu'de lumsasun idanuwanta ta 'dora akansa.


Kashe masa jiki idanuwanta sukayi ya tako ahankali ya zauna bakin gadon kafin yayi wata magana ummi da Jamaal tareda khadija data dawo suka shigo 'dakin
Kyakkyawar fuskarnan ta Jamaal a ha'de.

Kujeja inna Rabi ta jawo masa tana murnar ganinsa

Zama yayi tareda amsa wayarsa dake ringin kallo 'daya yayiwa gurin dasuke ya 'dauke kai bai kuma 'dagowaba yacigaba da wayarsa.


Ahmed ma 'dan tamke fuska yayi yana gaida ummi dake binsa da kallon tsoro da firgici.


Zee ma a ladafce tagaida ummin.

Amsawa tayi tana shafo kan neesah cikin kulawa tace

    Baby Yaya jikin naki?

Kai ta 'daga alamar amsawa sbd batadaqarfin jiki ko ka'dan.

Inna Rabi kawo guri ta wanke bakinta ko tea ne tasha.

Da sauri inna tashiga toilet ta 'dauko bucket zeey ta 'dauko robar faro 'daya a fridge ta kama neesah ta tashi zaune ta wanke baki Ahmed sai sannu yake mata cikin kulawa.

Ummi da kanta ta hada mata thick tea ta matso tafara bata ahankali tanasha.

Zeey ji take kamar ta kar6i cup 'din tajuyewa neesah gaba 'daya tashanye.

Sosai tasha tea 'din hartaji tasamu qarfi sosai ajikinta.

Kallon ummi tayi ahankali tace,

Ummi zanshiga toilet fitsari xanyi.

To tace tana qoqarin kamata tace,

No ummi kibarshi zan iya.

Ahankali take takawa saita tsaya cak tana hadiye yawu
Dafe cikinta tayi tana qoqarin kiran sunan ummi amma kumfan jinin daya fara fita bakinta ya hana sai kawai ta zube sai ajikin Jamaal jini na fita bakinta tareda kumfa.


Ummi,Ahmed da inna atare sukayo kanta cikin tashin hankali saidai wani matsiyacin kallo da Jamaal ya watsawa Ahmed ya hanasa qarasowa sbd wata kyakkyawar runguma yayi mata data fa'do jikinsa.

Dr Ahmed ya fita da gudu yana qwalawa wani mahaukacin kira.
Ummi kuka tasaki tana kiran sunan neesah duk a rude.


A sace zeey takalli gefen khadija suka ha'da ido tai saurin 'dauke kai tana gyara tsayuwarta cikin hawayen tausayin neesah na kissa.

Khadija kuwa sinne kai tayi cikin hawayen dasuka 6alle mata na ganin neesah kwance jikin Jamaal tasamu kyakkyawar runguma daga garesa ga wani tashin hankali datake hangowa cikin idanuwansa duk da ba kowa ke iya gane fushinsa da 6acin ransaba bare tashin hankalinsa kasancewarsa miskili amma yau ita tana iya hango tashin hankalinsa..

Ficewa tayi da Sauri tana sakin wani wahalallen kuka
A kuma lokacin doctors kusan Biyar da nurses hudu sukayo 'dakin a gaggauce._Ayshart bellow naga saqonki na tabayar wayafi wani mugun hali,hassada,baqin ciki da zama maqiyin gaske a tsakain Ayeesha,,,zeey da khadija_

_gskia yanxu banida amsar baki saidai kiyi nazari ki tantance da kanki sbd dukkaninsu cutarsu a 6oye take_

_Kuma maqiyi mafi ciwo shine Wanda kasani yake cutarka a 6oye_

*_Hassada mugun ciwo CE Allah ya karemu_*
Mamuh๐Ÿ’‹
๐ŸŒฒ *R H F W F*๐Ÿ„_Don't forget to vote, follow and comments_


*_DACEWA_*
       _when east meeta west_ _By_
_Mamuh geee_


*_Via wattpad@mamuhgee_**32-33*


Emergency room aka koma da ita a gaggauce sbd jinin dake tsananta fita baki da hancinta.

Ummi zuwa lokacin banda sharar qwalla ba abinda take hakama inna Rabi da duk tsoro ya kamata.

Zeey ma dake tsaye sharar qwallar take afili amma cikin ranta adduar take Allah yasa hanjin neesar sun riga da sun karkatse.

Jamaal kuwa barin gurin asibitin yayi gaba 'daya dan bayajin zai tsaya matuqar Ahmed na gurin.
Ahmed kuwa saida ummi ta taso da kanta ta zaunar dashi da sbd tashin hankalinsa na qarfin hali dataga na Neman yardashi daga tsayen.
Awa uku suna jiran tsammani kafin doctors biyu suka fito  fuskokinsu a tsuke 'dayan Dr ya kalli Ahmed dashine namiji cikin 6acin rai yace,

 Bansan meyasa kuke wasa da lafiyar yarinyarnan ba hartakeson kashe kanta,
Jiya ta shiga ruwa danta kashe kanta and today kuma poison.,
Look inason kusani koma meyene takeso ko takeson arabata dashi to kuduba Alamarin sbd idan yanxu munsamu damar saving 'dinta to bamusaan mai zaifaru next time ba,,
And I'm really sorry to say poison 'din dataci yanada Qarfi sosai and she lost alots of blood dan haka first thing yanxu shine muna buqatar jini.

Will she be alright Dr?
Well I can't say anything about that for now all we need shine jinin kafin komai.

Kiran Jamaal jmmi tafara qoqarin yi cikin sauri saiji tayi Ahmed na cewa,
Muje Dr zan bayar da ko duka jinane asa mata matuqar zaiyi.

Riqosa ummi tayi yana lokacin da zaibi bayan Dr cikin qoasawa da sabon halinsa tace,

     Ahmed meyasa za'a d'ibi jininka bayan akwai Wanda yafi cancanta da bayarwar,
Kaga ka aje wannan sabon halin naka tun kafin kakai qarshen hakurin Jamaal sbd banason rigima ko wani tashin hankali musamman nasa tunda zuciyane dashi so stay away from his wife ok.


Takaici da wani baqin cikin Jamaal da zancen ummi ne suka qulesa yace,

      Ummi naji yafini cancanta amma shi Darling son 'din naki yana ina yanxu?
Bayanan sbd baya wannan tunanin da kikeyi sbd bata gabansa wama ya sani qila maiqi ta zarce ba sbd yaji da'din more rayuwarsa da wadda yakeso dan haka ni 'din da bakyason kusanci na da ita nine zan kula da ita to any extend,,for god sake ummi for how long zaki ringa tureni daga abu kina tura Jamaal sbd ko yaushe kinfi sonsa akai.....

Tasss,,,,
Ta saukar masa da lafiyayyen mari tana tsiyayar hawayen tashin hankali.

Bai motsaba saima kallonta yayi da jajayen idanuwansa yace,

Ummi for the first time yau kin 'daga hannunki akaina sbd Jamaal.

Juyawa yayi zuciyarsa a karye yabar gurin zuciyarsa na quna banda tsanar Jamaal ba abunda yake cinsa a rai.


Baya ummi tayi cikin tsoro da tashin hankali ta zauna da6as inna Rabi tayi saurin dafata tana matsar qwalla itama.

Zeey dake tsaye ta sulale tabi bayan Ahmed.

Har aka 'dibi jininsa bai bar jin ransa na qunaba sbd ji yake duk duniya ba Wanda ya isa ya rabasa da neesah koda kuwa ita kanta neesar zai iya yin komai idan tace zata rabasa da kanta.

Murmushi take tana tunin ba shakka sun samu hanya mafi sauqi dazasuyi amfanin da ita gurin wargaza Jamaal da neesah sbd wannan mahaukaciyar soyayyar da Ahmed keyiwa neesah,,hmmmn wat a foolish mistake Mr Ahmed.

Qarasawa tayi cikin 'dakin dayake kwance bayan an 'dibi jinin nasa qwalla tafara sharewa tace,

Mr Ahmed Allah yasaka maka da alkhairi daka bawa qawata jini kuma itama na tabbatarda  idan ta tashi babban farin cikinta ne ace Ahmed 'dinta ne yabata jini,
Ahmed 'din datake tsananin fa'dar yanda take sonsa cikin ranta.

Bu'de rinanun idanuwansa yayi akanta da Sauri.

Cikin kissa ta rufe bakinta da hannuwanta tana zaro ido tace,

Dama idonka biyu I'm really sorry pls hope bakaji abinda nake fadaba sbd sirri ne tsakanina da neesah.

Bude baki yayi ahankali yace,

Abinda kike fada gskia ne neesah naso na? Tell me pls.

Wani murmushin samun nasara tayi duk da tasan qaryace take tsara masa tace,

Yes Mr Ahmed neesah na tsananin sonka duk da banbancin shekarunku saidai kullum kukanta Jamaal ne daya zama babbar katangar qarfe a tsakaninku saidai babban tashin hankali da damuwar sune bazaku ta6a kasancewa atare ba matuqar Jamaal na Raye.

Shiru tayi tana kallon yanda ya kar6i zancen nata ta gefen ido.

Ficewa tayi tabarsa cikin dogon tunani akan zancen Nata domin zancen ya shigesa matuqa.

Tana barin 'dakin fita asibitin tayi gaba 'daya
Direct gidansu ayeesha ta nufa..

Saida tayi wanka kafin ta zauna gaban mirror tana kallon ayeesha daketa tsoki fuskarnan masifa na cinta sbd tun jia Jamaal bai 'daga waya daga bayama ya kashe wayar.

Murmushi tasaki tana kallon ayeesha tace,

Eshaaaa,,eshaa Jamaal bazai ta6a 'daukar wayarki ba ayanxu sbd babban abinda muke yaqi akansa kamar ma muna kusantasu da juna ne da kanmu bamu saniba sbd nafara hango wata zazzafar soyayyar neesah a idanuwan Jamaal saidai takaicin halayenta da girman kansa suke danne soyayyar.,

Lallai wannan matakin damuke akai bazai haifar mana 'da mai idoba dan haka tun wuri mu canxa tsari duk da na 'danawa Ahmed tarko zamu riqa amfani dashi batareda yasaniba sbd soyayya data rufe idanuwansa.

Kallon zeey ayeeshan tayi da idanuwanta dasukai jajir tanajin kamar ta kama da wuta sbd masifa.

Hummmmnn zeey kenan to Ai wannan tarkon dakike tunanin kin na'dawa Ahmed nice nafa na'da masashi sbd ganin zai kawomin matsala a aiki,

Da farko nayi niyyar aikasa lahira saina bari nafara cin amfaninsa tukun.

Kallon tambaya zeey ta watsa mata tace,

Banganeba...

Matsowa tayi gabanta ta zauna cikin kashe ido tace,

Zaki tuna ranar da husnah takawomin magani nasawa Jamaal zai qara sona?

To aranar naji tana waya a toilet Ashe itada Ahmed suka hada baki sbd maganin husnah ta kar6o musu subani nasawa Jamaal yasha yafara tsananin son matarsa neesah ya qyaleni batareda na zargi komaiba.

Hakan danaji saina juye maganin nazuva mata wani a robar
Maganin kuma har school naje nabawa wani bokinsa maqudan kudi akan yasan yanda yayi Ahmed yasha maganin.


Miqewa zeey tayi cikin jinjinawa qawarta tace,

Hmmmm kenan da Jamaal ne yasha haka Zara faru kenan?
Gashi yanxu Kansu sukaiwa dan kuwa mahaukacin so yakeyiwa neesah Wanda nasan yana gaf da neesah ta tsanesa matuqar ya bayyana mata soyayyarsa.


Tsaki ayeesha tasaki tana cewa,

Bazan iya jiran wannan tarkon yayi wani aikiba sbd komai zai iya faruwa tsakanin captain da neesah and I can't take this anymore
 dan haka gwara kawai na aika su liloh suyimin maganin matsalata for gud.

Wat bakida tunani be zakiyi hakan,?
Idann mukasaka su liloh za'ayi bincike kuma za'a iya ganowa dan haka kibari muyi mata irin kisan da bakowa zai ganeba za'ama 'dauka ita takashe kanta.

Yes kumafa hakane qawata.
****
Kodata farfado ummi kasa daina hawaye tayi sbd tausayin kanta Dana 'yayanta su kuwa Ashe neesah ce qaddararsu.

 Kallon ummi da idanuwanta suka kumbura da kuka tayi taji duk jikinta yayi sanyi da tsantsar qaunar da ummin ke mata amma haryau takasa mayar mata da qaunar datake mat..
Lumshe idanu tayi tana karanto jamaay a ranta,
Tabbas zata danne qiyayyarta ta rungumi Jamaal 'din sbd ummin kawai.

'Daga hannu tayi ta riqo hannun ummi
Murya a sarqe tace,

    Ummi ki kwantarda hankalinki naji sauqi kuma I promise I won't do this again.

Qago murmushi tsyi murya a sarqe tace,

Naji baby amma dan Allah karki kuma gwada haka harda shan poison kinji ko?

Batareda ta fahimci xancen wani poison ba tace,
Bazan sakeba ummi.

Ahmed ne yashigo 'dakin ummi ta tamke fuska ya qaraso gabanta cikin karyar da kai zai fara magana Jamaal yashigo yana zuba sanyayan qamshinsa.

Kallonsa sukayi dukkansu banda neesah data lumshe ido ahankali.

Ahmed cikin basarda ganin da yayi masa ya maida hankalinsa kan ummi da idanuwanta ke kawo hawaye yace,

Ummi dan Allah karkiyi fushi dani harki xubarmin da hawaye wlh aikin xuciyane da sharrin shai'dan.


Kallon ummin Jamaal yayi da sauri sai alokacin ya lura da fuskarta dake kumbure ya tabbatarda tana cikin damuwa.

Tabbas Ahmed ne yake neman sawa umminsa ciwon damuwa amma zai maganin abin tunda neesah ce matsalar zai mayar da ita cikakkiyar matarsa yaga abinda zai faru  coz tsaf zaisa arufe masa shege a prison 'dinsu na us yanda ma ko dady bazai samu damar ganinsaba.


Hannu ya zura a ajihun wandon black jins dinsa ya fara dosarta cikin takun qasaita
Ahmed dake bawa ummi hkr yaji gakasa qarasawa ya maida hankalinsa kansu Jamaal yana yaba tsantsar kyau da burgewa tareda class irin na Jamaal 'din amma yakasa tantance maiyasa zuciyarsa ke neman kaisa gun da ba gurinsa ba.

Jin qamshinsa na kusantota yasata bude fararen danuwanta akansa.

Cikin idonta yake kallonta tareda sakar mata murmushin dayasata qasa da kai.
Ba zato taji ya zauna kusada ita tareda riqo hannuwanta duka biyu yana kallon cikin idonta ya manna mata lafiyayyen kiss a tafin hannu Wanda yasata lumshe ido bataredata saniba.

Fuskarta ya nufa da tasa fuskar yana kallon pink lips 'dinta zai 'dora nasa akai sai jin qarar zubewar kuloli sukai  dukkaninsu suka waiwaya suna kallonta jikinta banda rawa ba abinda yake da sauri ummi tace,,

Lafiyanki  khadija?

Ahmed kuwa ball yayi da kulolin ya fice 'dakin afusace
Khadija ma bayansa tabi da gudu tana sakin kuka mai qarfi.

_wai wai wai zeey, ayeesha da khadija maiyasa bakuda masoya ne_๐Ÿค”Mamuh๐Ÿ’‹


*R H F W F*


_Don't forget to vote and comments_


[3:39pm, 3/30/2018] ‪+234 909 331 3008‬: _*DACEWA*_
     _(when east meets west)__By_
_Mamuh geee_


*Viawattpad@mamuhgee*
*34-35*


Baya yayi da kansa tareda sakin 6oyayyar ajiyar zuciya yana kallon fuskarta data rufe idanuwanta..

Mamaki yake yanda yau tayi sanyi babu wata masifa ko harara a tsakaninsu.,

Gefen ummi ya kalla yaga fuskarta 'dauke da murmushi tana 'dan kallonsu inna Rabi kuwa abincin da khadija tayi 6ari take kwashewa.

Lumshe idanuwa yayi har lokacin hannunta na sarqe cikin nasa yana matsawa ahankali.

Kwanto da ita jikinsa yayi yana tallabo fuskarta

Ummi na ganin haka ta fice annuri fal a fuskarta Wanda dukkaninsu sun lura da hakan bama kamar ita da jikinta yayi sanyi.

Qwace jikinta tayi bayan fitar ummi ta 'daure fuska shima miqewa yayi tareda 'daure fuskar ya fice daga asibitin batareda yabari ummi taga fitarsa ba.

Zamewa tayi ta kwanta tareda lumshe ido tanajan 'dan siririn tsaki sbd qamshinsa daya maqale ajikinta sai tashi yake.

Tabbas Jamaal yakai duk wani matakin qarshe da kawane cikakken namiji yake buqatar kaiwa
Amma batasan yaya zata iya rayuwar aure da qaninta ba sbd batajin zata iya tsayawa koda kallon sha'awa yayi mata bare har wata alaqar aure tashiga tsakaninta dashi.
*******
Kwananta biyu a asibitin aka sallamota suka dawo gida
Kuma har wannan lokacin babu Wanda yakuma sa khadija a ido sbd kullum tana rufe a 'daki tana jinyar zuciya.


Ahmed ne ya dawo dasu gida ummi da inna Rabi ne a baya neesah kuma a gaba ta zauna.

Parking 'dinsu yayi daidai da fitowar Jamaal daga sashensa yana waya da eyeesha.

Fitowa Ahmed yayi ya zagayo ya bude mata murfin motar yana cewa,

Carefull sis.

Kallonsa tayi tareda sakin murmushi tace,

Ahmed you seems to care sosai a two days 'dinnan.

Cikin son qular da Jamaal ya kashe mata ido 'daya yana cewa,

Do I have any other job than taking very gud care of you mah lady.

Daria tayi kafin tayi wata magana taji an 'dagata cak a tsorace taduba sai idanuwanta suka sauka cikin fararen oily eyes 'dinsa tai saurin maida kallonta gurinsu ummi saitaga sunbar gurin kallonsa tayi fuska a ha'de tazatayi magana ya sakar mata wani kallo daya sakata rintse idanuwanta cikin mamakinsa.

Ahmed kuwa a fusace ya juya yabar gurin xuciyarsa na tafarfasa.

Har cikin bedroom 'dinta yakaita tareda direta tsakiyar gado yana kallon tsakiyar idonta datake qoqarin rufewa.

Qoqarin zama yake bakin gadon wayarsa tayi ringin yana dubawa yakira sunan ayeesha ahankali amma sosai sunan yashiga kunnuwanta duk da qaramin sauti yakira sunan,,
Lumshe idanuwanta tayi tanajin saukar sunan har cikin ranta dan ta fahimci sunan matarsa ce dazai aura.

Ficewa yayi batareda yakuma kallon gefentaba abinda ya ta6a ranta matuqa kenan tun yanxu qanin data raina yafara fifita wata akansa alhalinma ita ba sonsa takeba.

An sanya ranar auren ayeesha da Jamaal sati uku masu zuwa sbd komawar dayakeson yi gurin aikinsa.

Ranar da aka sanya ranar daga neesah har khadija ummi kasa gane kansu tayi,

Ita neesah baqin cikinta duk kyawu da haduwarta ace ita za'ayiwa kishiya kishiyarma agun wanda ita har yanxu bata 'dauka miji ba yanxu friends zasu 'dauka batakai yanda suke 'daukar takaiba.


Khadija kuwa abin ma yafara bawa ummi tsoro sbd ciwo sosai ta kwanta hardasu qarin ruwa amma taqi fadar abinda ke damunta.
Ta 6angaren Amarya ayeesha sosai suke hidima duk da takasa gane inda alamarin angonta ya dosa sbd Sam ko wayarta bai cika 'daukaba a 'yan kwanakin amma koma menene bai dametaba sbd sosai tayi mummunan shiri akan neesah da zarar tashiga cikin gidan.

Sosai Ahmed ke farin ciki da auren yanxu sbd yasan auren ne zai qara nisanta Jamaal da neesah.


Ta 6angaren Jamaal kuwa ya kasa samun cikakkiyar walwala sbd ummi dake 'daure masa yanxu sosai.

Ana gobe ne 'daurin auren yashigo palon sbd su mamyn neesah dasuka iso a yau 'din.

Kallo 'daya ummi tayi masa ta 'dauke
Ya qaraso ya gaida mamy idonsa na kan neesah data miqe sanye da three quarter blue jinsa da farar armless robber  top ta bar gurin sbd ganinsa.

Qoqarin barin gurin yake Ahmed ya shigo riqeda babbar ledar shoprite fuskarsa na fidda farin ciki kai tsaye 'dakin neesah ya nufa bayan ya gaidasu ummi.

Kasa fita yayi ya juya ya nufi 'dakin fuskarsa a 'dan tsuke.

Tsaye take gabansa ta saka hijab mai 'dan tsawo ledar daya shigo da itace a hannunta tana murmushi tace,

Ahmed shiyasa nake tsananin sonka sbd ko yaushe kasan abinda antynka keso...

Shagala yayi da kallonta sbd sosai kalmarta ta farko ta ratsasa ya 'dago hannu ahankali ya nufi kyakkyawar fuskarta zai shafa yaji an riqe hannun.

Ya 'dan tsorata da ganinsa amma ya fuske ya fice 'dakin zuciyarsa a 'dan qule.

'Daure fuska tayi ta juya ta zauna bakin gado tana aje ledar hannunta ya matso zaiyi mgn ta miqe ta fa'da toilet tabarsa a tsaye.

Ka'da kai yayi ya fita yana ayyana abubuwa da dama a ransa.
*******Zaune take cikin farin ciki mai tsanani ta kalli zeey tace,

Zeeey finally yau dai nazama matar captain 'dina,
Farin cikin danake ciki yau bazai ta6a kwatantuwa ba.

Wani shu'umin murmushi zeey tasaki tana juya idanuwanta tace,

Qawata yau ranarki ce dan hakan nema na shirya baki wani dadda'dan farin cikin dazai qara faranta ranki.

Hummmm I trust you zeey,dan haka a shirye nake da kar6an farin cikin.

Miqewa tayi tareda 'daukar handbag 'dinta tace,

Ki saurari rahoto bayan zuwana gidansu neesah ayanxu.

Cikin farin ciki tace,

Wow zeey ure the best.

Ficewa tayi tana jujuya takardar dake hannunta cikin murmushi.Kodata isa gidan a 'dan cike yake amma ba sosaiba ta gaidasu ummi da mamy ta nufi 'dakin neesah daidai fitowarta wanka kenan.

Zeey nayi fushi tun shekaran jiya rabonki da gidan nan.

Sorry friend wlh banajin da'di ne shiyasa amma ya naga kamar gidan acike biki ake ne?

Um kawai tace tana xama gaban mirror.

Fakaitar idon neesah tayi ta zaro  envelope cikin Jakarta ta 'dora kan bedside drower tareda matsawa da sauri.

Zama tayi tace,
Ashe bikine shine baki fa'damin ba neesah.

Zatai magana Jamaal ya shigo 'dakin cikin ado na alfarma sai zuba qamshi yake.

'Dauke kai tayi tareda tamke fuska sbd towel 'din jikinta da ka'dan ya wuto bum bum nata.

Shikuwa kafeta da fararen idanuwansa yayi yana takowa ahankali sbd bai lurada zeey dake 'dakinba.

Yi tai kamar batasan da shigowarsa 'dakinba da sauri ta 'dauki envelope 'din tana cewa,

Menene wannan neesah it seems like hospital report..

Budewa tayi da qarfi tace,

Wat?
 a positive pregnancy result kuma da sunanki dama cikine dake kuma....

Zaro ido tayi cikin kirsa lokacin data kai kallonta kansa ta saki takardar tana rawar baki tace,

Um um it was all a frank to to to...

Idanuwansa dasuka ka'da nan take suka hanata qarasawa ya 'dauki takardar yafara karantawa..

Wani matsiyacin razanannan kallon takaici yafara watsawa neesah yana nufota.....Manage pls

 
Mamuh๐Ÿ’‹
๐ŸŒฒ *R H F W F*๐Ÿ„_Don't forget to vote, follow and comments_
[3:39pm, 3/30/2018] ‪+234 909 331 3008‬: _*DACEWA*_
     _(when east meets west)__By_
_Mamuh geee_


*Viawattpad@mamuhgee*
*36-37*Gabanta ya tsaya tareda 'daga takardar sama daidai fuskarta yana kallon fuskarta saidai Sam zuciyarsa takasa kar6an zancen shima saidai zaiso jin mai zata ce ita.

Kallonsa tayi idanuwanta na qoqarin danne hawayen dakeson gangaro amma Sam taqi ko bude baki bare tayi magana.

Gangarowa hawayenta sukai tai saurin rintse idanuwa sai kawai yaji ta qara qular dashi yayi wurgi da takardar a fusace ya bar 'dakin zuciyarsa na quna mai tsanani.

Zubewa qasa tayi tana qoqarin fashewa da kuka saita tuna da zeey na 'dakin kuma Sam bata bari tayi kuka gaban duk wani dayake baqo ko qasa da ita dan ita amatsayin yar korenta ta 'dauki zeey 'din.


'Dago da jajayen idanuwanta tayi ta kafesu akan zeey tana mata kallon tuhuma da jiran qarin bayani.


Faduwa gaban zeey yayi tafara Sosa wuya tana cewa,

Well I saw the envelope hia and and bansan na menene ba da bazan duba ba I'm really sorry nee.

Kallonta taci gaba dayi zuciyarta na kasa 'daukar zancen na zeey batadai ce mata komaiba ta miqe ta xauna bakin gado tunani da dama na shigarta akan wasu alamura daketa faruwa a 'yan lokutan.

Zeey kuwa da sauri ta fice daga 'dakin tabar gidan xuciyarta a tsinke sbd wannan tarkon nata baiciba saima tonuwa da asirinta yakusa yi.


Ba'ayi wani jere ba sbd ba'a nan zasu zaunaba US zasu tafi da zarar sun kwana biyu shiyasama shi da kansa yace baya buqatar komai.


Da daddare gidan yayi tsit sbd kowa ya tafi gurin dinner daza'ayi da daddaren.

Sam ummi bataso zuwaba amma mamy ta takurata zuwa,

Inna Rabi ce kawai a gidan sai khadija dake fama da zazza6i a 'dakinta hakama neesah na 'dakinta a kwance sbd itama zazza6in takeji ahankali.


Kansa ke masa ciwo ahankali tun lokacin daya baro 'dakinta.

Kama wayoyinsa yayi ya kashe sbd Sam baya tunanin zashi gurin wata dinner sbd Sam har yanxu yakasa jin farin ciki a matsayinsa na angon da aka 'daurawa aure ayau.

Sanin Yusuf zai iya shigowa nemansa yasa shi miqewa ya nufi cikin gidan.

Ba kowa a palon sai TV dake aiki
Kai tsaye bedroom 'dinta ya nufa yana shiga ya sawa qofar key.

Tsayawa yayi bakin qofar tareda zuba hannuwansa aljihu yana qare mata kallo.


Kwance take ta sanya rigar baccinta  mara hannu data kama jikinta ta lafe.

Kamshi da sanyin Ac yasa 'dakin wani irin ni'ima na fita acikinsa.

Takowa yayi ahankali ya zauna bakin gadon tareda zare bryans lee slippers dake qafarsa ya 'dora har qafafuwansa kan gadon.


Tun shigowarsa tajisa amma tayi banxa dashi ko motsi taqiyi saima lumshe idanuwanta datayi ta rufe sbd kanta dake tsananta ciwo

Ahankali hawayen dake cikin lumsasun idanunta suka gangaro batareda ta bude idon ba.

Baice mata komaiba ganin hawayen sai kawai ya jawota jikinsa ya rungume tareda lumshe idanu batareda yace komaiba
Itama luf tayi batareda tayi wani motsiba ko bude idanuwanta.


Shiru sukayi dukkansu idanuwa a rufe yanaji zafin zazza6in jikinta na shigarsa ahankali sbd kyakkyawan body contact dasuka samu.
Gurin dinner kuwa tunda ayeesha ta isa da tawagar qawayenta take kiran number ango amma Sam bata shiga babban baqin cikinta da tashin hankinta shine neesah ma na gida tsoranta kar wani Abu yashiga tsakaninsu.


Kallonta zeey tayi a fakaice sbd Sam ko kusantar ayeesha taqiyi sbd kar ayi zargin tasanta ma.

Alama tayi mata da idanuwa akan su zagaya baya suyi mgn.


Zeey 'dince ta sulale tafara fita can bayan motoci kafin ayeesha ta sulale tabi bayanta batareda kowa ya luraba.


Jikin wata baqar mota suka tsaya zeey tace,

Wlh ayeesha karki ji da wai Jamaal nacan tareda wannan tsinanniyar mai girman kan nan kuma ina tabbatarwa jikina na bani wani Abu nacan zai wakanu a tsakaninsu and trust me da zarar yafara kusantarta kasuwarki ta fa'di wanwar.

Cikin tsabagen masifa da bala'i tace,

Wlh duk tayi wannan kuskuren saina aika har uwarta lahira bare ita,
Wannan wannan aneesar ni wlh uwarta ta haifomin masifa da bala'i wallahi,
Ji nake kamar zan buga tsabar bala'i da baqin cikin danake ji a yanxu
Wlh Jamaal yaci sa'ar ba qaramin so nake masa ba da wlh tuni nasa an masa kaciya amma wlh ko a yanxu idan yakaini maqura sai in danne son na 'dau mataki akan wannan jan ajin da basarwar dayakemin.

Zeey ma a qule tace,

Wlh ne nama fara gajiya da wannan bala'in kawai musa a sheqata zuwa lahira kowama ya huta.

Waya ayeesha ta 'daga ta danna kiran liloh riqaqqen 'dan ta'addar daya qware a iya kisa da fyade tareda sata.

Bugu 'daya ya 'dauka murya a tsananin a buge.

Kasa bayani tayi sbd tsananin baqin ciki da masifa dake cinta saidai zeey ce takar6a tai musu bayani itama duk da itama a qone take da 6acin rai.

Bo'de motar daduke jingine akayi da qarfi
A tsorace suka juya har zeey na wayar hannunta na faduwa.

Ahme......bata qarasaba yakai mata wani gigitaccen mari tareda shaqureta cikin tsananin masifa jikinsa har wata rawa yake.

A tsorace zeey ta matso tareda riqosa tana qoqarin 6an6are ayeesha da idanuwanta suka firfito sbd mari ga shaqa.

Wani mugun naushi ya sakarwa zeey 'din a baki saida haqorinta 'daya ya fa'do ta qwalla wata razananniyar qara sbd azaba dakuma ganin haqorinta 'daya a hannunta.

Daurewa tayi bakinta na jini tace,

Ka saketa idan yaso ka'dau ko wane irin hukunci daga baya bayan kaji dalilinmu nayin hakan.

Wurgi yayi da ita harsaida head 'din kanta ya fa'di ya rufesu da duka ido a rufe dan ji yake ko kashesu zai iyayi.

 Saida suka daku kowaccensu fuskarta ta canza ma'ana kafin ya tsaya yana cewa,

Uhumm yanxu kubani hujjar Ku INA saurarenku kafin nakira Jamaal nafada masa yasan yanda zaiyi daku.

Ayeesha dago da idanuwanta dasuka ka'da jajir tayi sbd baqin ciki da dukan da tasha tace,

Munayin hakane sbd kai da ni kaina,

Jamaal ya tabbatarmin da har abada bazai ta6a son neesah ba hakama bazai ta6a rabuwa da itaba sbd karka sameta kuma yayi alqawarin azavtar da ita harsaita kashe kanta da kanta...

Zeey baki na jini ta kar6i zancen da cewa,

Nikuma neesah ta tabbatarmin da tabbas idan bada kaiba bazata iya rayuwar farin cikiba qarshema kashe kanta zatayi ta mutu kuma ko wancan karon data rufe kanta a toilet danta mutu Jamaal ne yaso raping nata taqi yarda shine yamata duka shiyasa taso kashe kanta a ranar
 nikuma sbd bazan iya ganin neesah cikin wannan halinba yasa na yarda muka ha'da kai da ayeesha dan mu rabata dashi tasamu farin cikinta ita kuma ayeesha tasamu mijinta ita 'daya.


Sosai zancensu ya shigesa nan take tausayin neesah da tsanar Jamaal tareda qudirin 'daukar fansa suka shigesa.

Kallonsu yayi yace,

To meyasa yanxu naji kuna maganar sheqata lahira?

Da sauri zeey ta goge jinin bakinta tace,

Dama ba kasheta zasuyiba 'dauko mana ita ne zasuyi mu 6oye harsai ya yarda ya saketa kafin asakota kuma na tabbatarda kaima zakaso hakan dan haka pls kazo mu hadu mu qwato neesarmu daga hannun maqiyinta.


Dogon tunani yayi yaga tabbas wannan itace hanya 'daya dazai samu neesah,
Wani murmushin gefen baki yasaki tareda kallonsu yace,

Well I'm all in,.

Juna suka kalla suka saki wani murmushin qeta da samun nasara tareda qullin mummunar fansa dazasu 'dauka akan wannan dukan daya musu bayan sun gama amfani dashi.


Dinner dai watsewa tayi sbd tafiyar Amarya batareda tabari kowa ya qara ganinta ba sbd ba qaramin dakuwa sukaiba dan saida Ahmed 'din yakaisu akai musu dressing fuskokinci kafin yakaisu gida sbd sai washe gari ne za 'akai Amarya ayeesha.

Mamuh๐Ÿ’‹
๐ŸŒฒ *R H F W F*๐Ÿ„_Don't forget to vote, follow and comments__*DACEWA*_
     _(when east meets west)__By_
_Mamuh geee_


*Viawattpad@mamuhgee*
*38-39*_ina roqon masu bina nema daga farko pls su sassauta su nema a groups sbd gskia ba qaramin shiga haqqi bane sbd yayi nisa sosai a gurin mai rubutawa sai a nema daga wasu tunda baza'a rasaba.._Koda su ummi suka dawo babu Wanda yatafi 'dakin neesah sbd sunsan zuwa wannan time 'din ta jima dayin bacci.


Neesah kuwa tuni bacci ya kwasheta cikin jikinsa sbd wata irin kasala da nutsuwa da haduwar jikin nasu ya sakar mata.

Gyara mata kwanciya yaji a jikinsa yana kallon sexy face 'dinta a ransa yana fadin,

Hmmnn stubborn girl sai shegen son girma.

Light kiss ya manna mata a wuya sai hancinsa ya shaqo sanyayen qamshin da fatarta keyi ya lumshe idanuwa sbd wani yanayin sha'awa dayaji na shigarsa.

Sake shigar daita jikinsa sosai yayi tareda 'dan matseta ya lumshe idanuwa batareda wani 6ata lokaci ba wani ni'imtaccen bacci yayi awon gaba dashi.

Zeey dai a daren ranar kwana tayi da mugun zazza6i ga fuskarta datayi sumtum sbd duka da haqorin daya fita daga bakinta.

Ayeesha kuwa a zaune ta kwana sbd Sam baqin ciki da tunanin 'daukar fansa ya hanata koda kwantawa bare ta rintsa.

Ta 6angaren Ahmed kuwa jiyake komaima zai iya akan neesah koda kuwa 'daukar ran Jamaal 'din ne sbd baya jin zai iya jurar ganin duk wani Wanda zai iya zama shamaki tsakaninsa da farin cikinsa ma'ana neesah.
*******
Very late suka farka shine ma yafara bude idanuwansa ya qurawa fuskarta dake wani sheqi ido ya shafo fuskar a hankali tareda zamewa ahankali ya fa'da toilets 'dinta.

Alwala yayo yazo ya gabatarda sallah yana idarwa ta bude idanuwanta akansa.

Fargaba,tsoro da tashin hankaline suka shigeta lokacinda ta gansa amma jin kai ya hanata nunawa sbd  alamun dai tabbas tare suka kwana anan dakinta.

Jikinta tafara duddubawa sai kawai jinsa tayi ya 'doro kansa ta wuyanta tareda xuro hannuwansa ya Rungumota da wata irin muryar data kashe jikinta qasa qasa yace,

Kwantar da hankalinki babu abinda qaninki yayi miki bare ki kai qarata gurin ummi.

Juyowa tayi da sauri ta kalli fuskarsa ya kashe mata ido 'daya
Saurin sauke kanta tayi cikin wata muguwar kunyar da bata taba sanin tanada itaba.,

  sakinta yayi ya fice yana murnushin ganin dama ashe tasan kunya.

Turus yayi ganin ummi da mamy a Palon zaune sai inna rabi dake kaida kawo.


Kallon mamaki ummi tafara aika masa tace,

Inna Rabi dama an bude qofar palon nan ne?

Cikin murmushi inna tace,

Aa haryanxu a rufe take.

Shafa kansa yayi tareda qarasowa gabansu yana gaida mamy cikin basarda kallon da ummi ke masa ya miqe yabar palon

Murmushi mamy tayi cikin farin tana kar6ar cup 'din kunun gya'da da inna rabi ke miqo mata.

Ummi kuwa miqewa tayi ta nufi 'dakin zuciyarta cikeda farin ciki.

Har lokacin tsaye take tsakar 'dakin tana mamakin zancensa,,,
Lallai Jamaal 'dinnan dama yana magana haka kuma ita yakewa zancen rashin kunya irin wannan.

Murmushi tasaki daidai shigowar ummi kamar tasan meya kawo ummin ta fa'da toilet da sauri batareda tabari ta hada ido da ummi ba.


Wani sabon farin ciki ya qara qule ummi takoma Palo gurin mamy da itama sai farin cikin take suka taru suka 'dora sabuwar fira zukatansu fes.Yinin ranar tsaf a 'daki tayi abinta zuciyarta fes duk da gidan akwai baqin ummi dazasu tarbi Amarya anjima idan ankawota.

Shikansa ba a gida ya wuniba yana gurinsu Yusuf a masaukinsu sunata firarsu duk da bayasa baki a firar tunda yaje ya kwanta ya lumshe idanuwa ya fa'da duniyar tunani.Qarfe Tara aka kawo Amarya ayeesha gidan a sashenta bayan ankawota gurinsu ummi sun sanya alkhairi.


Qarfe goma gidan yayi tsit kowa ya watse su ummi ma duk sun kwanta.


Parking yayi bayan ya duba agogon hannunsa ya tabbatarda kowa ya kwanta yafito motar tareda nufar sashensa.

Harzai bude qofar palonsa yashiga saiya ji yana sha'awar zuwa yafara ganinta kafin ya shiga gurin ayeesha.

Bedroom 'dinta yashiga daidai fitowar khadija zata 'dauko ruwa kicin.

Cak ta tsaya kallonsa qafafuwanta na rawa sbd dama ba isashiyar lafiya ne da itaba bare yanxu da idanuwanta sukai mata mugun gani wai Jamaal 'dinta zai shiga 'dakin neesah da tsakar daren nan.

Sam shi ko kallo bata ishesaba yashigewarsa 'dakin tareda turo qofar.


Kwance take a tsakiyar gadonta ta dunqule sbd sanyin ac dakuma window 'din dakin dake bude har iska na 'dago labulen.

Qarasawa yayi tareda aje kayan hannunsa ya zauna kan gadon tareda jawo  duvet blanket ya lullu6a mata tareda gyara mata kwanciya a jikinsa.

Bai ankaraba bacci ya 'daukesu ahaka dan har wani qara qanqamesa tayi.


Qarfe 'daya daidai zeey taredasu leloh da yaransa suka shigo gidan ta hanyar Ahmed daya bu'de musu qofa.


Dukkaninsu sanye suke da baqaqen kaya da bindigogi
Ita kanta zeey da Ahmed baqaqen kayane ajikinsu.


Ayeesha dake tsaye tsakar 'dakinta tana kai kawo kamar zata buga sbd baqin cikin daren farkonta gidan mijinta amma yaqi tahowa gareta.


Wayar zeey takira daidai lokacin dasuka iso bakin windon 'dakin khadija dake zaune tsakar 'dakin har lokacin tana dirzar kuka.

Jin motsin mutane a bayan windonta yasata tasowa ahankali tazo bakin windon.


Isowa ayeesha tayi gurinsu cikin san'da suka kalleta cikeda mamaki murya qasa qasa Ahmed yace,

Amma dai kinsan so kike ki 6ata mana aiki shiyasa kika fito sbd Yaya zaiyi tunanin ina kika tafi da tsakar daren nan.

Tsaki taji ahankali cikin takaici tace,

Ai wallahi saina qunsawa captain baqin cikinda zai kusa tafiya da ransa sbd wannan abin dayamin a daren yau.

Zeey tace,
Yanxu dai duk ba wannanba mu hanxarta muyi abinda yakawo sbd yau idanba satota mukaiba banajin zan iya koda numfashi da lafiyata.


A matse Ahmed ma yace,
Please Ku lura da kyau gurin shaqa mata qyallen nan sbd inason ta shaqesa da yawa yanda bazata farkoba harsai gobe idan munxo.


Motsi sukaji a razane suka juya leloh haryana seta bindigarsa zaiyi harbi ayeesha tayi saurin riqesa tana cewa,

Bakada hankali ne zakayi harbi aji qararsa asirinmu ya tonu.

A hasale zeey tace,
   Kibarsa idan ya saba da gidan prison yana marmarin komawa  tomu bamu sababa bakuma zamu ta6a zuwaba.

Ahmed kuwa kuwa yawu ya ha'de sbd ganin khadija ce tsaye bakin windon 'dakinta tana kallonsu kuma taji duk abubuwan dasuke fada da abinda suke shirin aikata.

Dukkaninsu sun razana da ganinta amma ga tarin mamakinsu babu mamaki ko tsoro a fuskarta saima Jan windonta tayi ta rufewarta.

Ajiyar zuciya suka saki lokacin da zeey ta tabbatar musu da bazata fada komaiba.


Suna isa bakin windon 'dakinta leloh daya kama windon zai haura ya diro da qarfi jikinsa na rawa.

A tare suka tambayesa lpia.

Jikinsa na rawa yace,

Captain 'din yana ciki kuma wlh ban shirya a rufeni prison 'din qasar us ba dan wlh wannan yana kamani sai can.

Kama windon zeey tayi ta leqa.

Tabbas shine atareda ita cikin kwanciyar hankali.

Cikeda qarin baqin ciki da takaici ayeesha takama windon ta leqa.

Yanayin data gansu cikine yayi masifar qone zuciyarta idanuwanta suka rufe ta fixgo kyallen hannun Ahmed daza'a shaqawa neesar zata dira ta shaqo mata har jamaal 'din ma kowama ya huta
Cikin rashin sa'a da rufewar ido ta zame ya fado qasa da qarfi saida qafarta ta amsa.

Qara tasaki sbd muguwar azabar dataji dan tama manta da dare ne.

Zeey,Ahmed,leloh da sauran yaransa biyu runtumawa sukai a guje dan neman tsira sbd ihun datayi sun tabbatarda kowa yajisa agidan.

Itama tashi tayi da masifar gudu tana 'dingisa qafa dan ta tabbatarda karyewace qafar tayi amma batajin zata iya tsayawa kowa yafito ya sameta Wanda dukkaninsu cikin rashin sani sunbar qyallen yashe a bakin windon.

Su zeey kuwa suna dosar gate a guje suka hango maigadi yafito 'dakinsa a guje Ahmed ya bu'de musu palonsa suka shigo ba Wanda jikinsa baya rawa tareda tausayin ayeesha dan sun San itakam ankamata.

Mamuh๐Ÿ’‹
๐ŸŒฒ *R H F W F*๐Ÿ„_Don't forget to vote, follow and comments_


_Don't forget to vote, follow and comments__*DACEWA*_
     _(when east meets west)__By_
_Mamuh geee_


*Viawattpad@mamuhgee**40-41*Kusan atare suka farka cikeda tsoro ta qanqamesa idanuwanta na fitowa waje.


Qoqarin zameta yake ya miqe sbd sosai kunnuwansa suka jiyo masa gudun koma su waye kuma tabbas ba gudun mutum 'daya bane sunada yawa.

Qin sakinsa tayi saima qara shigewa jikinsa tayi sbd mugun tsoron datake ciki.

Shafa kanta yayi ahankali yace,

Just stay right hia bari na dubo.

Sunkuyar S
Da kai tayi batareda ta bar jikinsaba kuma batace qalaba.

Tsoro qarara ya hango a idanuwanta ya miqe hannunsa cikin nata suka fito Palo daidai fitowarsu ummi duk a tsorace.

Kallonsa ummi tayi cikeda tsoro da mamaki zatai magana ya fice har lokacin hannunta na cikin nasa dan ita Sam batai tunanin tsayawa gurin su ummi ba sbd a tsorace take.


Tareda me gadi suka zagaya bayan windon 'dakin neesah inda anan ne yaji motsin tareda gudunsu.

Qafar baqin takalmin leloh 'daya tareda handkerchief fari tas daya jiqu da ruwan 6atarwa da mutum hankali tareda somewa.


Kallon jikin windon yayi da kyau nan idanuwansa suka sauka kan wani agogo.

Hannu yakai ahankali ya dauki agogon gabansa ya buga sbd idan baiyi kuskureba agogon Ahmed ne na diamond daya siyo masa wannan dawowar dayayi.


Sake kallon agogon yayi da kyau tabbas shine to me hakan ke nufi.

Miqawa mai gadi kayan yayi tareda basa kyakkyawan garga'di akan ya boye su karya sanarda kowa zasuyi bincike a 6oye.

 bayan sun zazzaga gidan basuga wani abinba suka koma ciki har lokacin su ummi na tsatsaye a Palo cikin tsoro da fargaba.

Zaunar da ita yayi ahankali kafin ya juyo da kallonsa gurinsu ummi yace,

Ku kwantar da hankalinku ba komai bane kawai ina zargin koma su waye sunason 'daukar _neesah_ ne.

Zaro idanuwa ummi tayi jikinta na 'daukar rawa tace,

Ya akayi suka samu shigowa gidan nan bayan da akwai maigadi.

Batareda ya kalletaba kai tsaye yace,

Da ha'din kan na cikin gidan suka samu shigowa.

Tashin hankalinsu ne ya tsananta hardai neesah da tuni idanuwanta suka kawo ruwa.

Ummi kuwa zubewa tayi a kujera sbd lokaci guda tunaninta akan Ahmed ya fa'da sbd tasan sarai zai iya 'dauke neesar.


Kallonta yayi cikeda tunani kala kala akan abubuwanda suketa faruwa a 'yan lokutan....

Tabbas akwai abinda ke faruwa a 6oye batareda sanin kowaba.

Lallai daga yau neesah na tashiga cikin tsananin tsaronsa da kariyarsa harsai ya gano meke faruwa.Miqewa yayi tai saurin 'dagowa ta kallesa kafin tai qasa da idanuwanta.

Sarai ya gano tsoron tafiyarsa take sai kawai ya share tareda barin palon ya nufi 6angarensa dan yasan ayeesha nacan cikin kewa da kadaici.

Tausayinta ne ya sauko masa dan yasan baiyi mata adalciba na barinta ita 'daya a daren farkonta.


Yana shiga kai tsaye bedroom 'dinta ya nufa.

Kwance take tana fidda sautin kukan azaba ahankali.


Ahankali ya qarasa bakin gadon cikeda tausayinta ya 'dagota ya rungume batareda yace komaiba.


Duk da tana cikin wata irin azaba sosai tai farin cikin kasancewarta kwance cikin lafiyayyen qirjinsa data da'de Rana qwa'dayi.

Shafa bayanta ya riqayi har tayi shiru ta lafe.
*******
Da asuba Su leloh suka samu damar ficewa daga gidan batareda ya tsaya sanar dasu takalminsa daya yar gurin gudu ba.Da asuba Jamaal na fita ta miqe da sauri tana 'dingisawa ta shiga toilet tareda zubarda ruwa qasa ta zauna cikin ruwan tanajin motsin shigowarsa ta saki qara da qarfi.

A 'dan razane ya shiga toilet 'din yaganta zube qasa tana kukan azaba.

Oh my god eshaa faduwa kikayi.

Kamata yayi ta tashi amma takasa sai hawaye take.

'Daukarta yayi yafito da ita ya kwantar tareda ta6a qafar tasaki wata qarar ahankali.

Kallon qafar yayi dakyau saiyaga kamar ta 'dan kumbura alamar ciwon bana lokacin bane.

Ganin kamar nazarin qafar yake yasata janye qafar tareda kwantawa jikinsa tana cigaba da tsiyayo hawayen kirsa.

Tallafoto yayi tareda lumshe idanuwa sbd tunanika da dama da tsakanin. Daren jiya zuwa yau suke shigarsa.


Neesah kuwa tun guraren qarfe takwas tafito Palo ta zaune haka kawai takasa samun nutsuwa ga tunanin rashin zuwansa gaida ummi yau da wuri dayake cin ranta.


Qarfe goma sha 'daya suna zaune da ummi da inna Rabi harda khadija suna fira itadai tsit take kwance kan qafafun ummi tayi nisa cikin tunani.

Qamshin turarensa na signature ne yafara isowa ta lumshe idanuwanta kafin ta bude taji sallamarsa ahankali tareda sallamar ayeesha.

Dummm taji a zuciyarta sai kawai taqi bude idanuwanta ta lafewarta.


A ladafce ayeesha ta gaida ummi da inna Rabi tareda kallon khadija ta ha'de yawun fargaba amma ga tarin mamakinta saijin tayi khadijar murya a shaqe tace mata ina kwana?

Baki ta washe tana amsawa duk da a tsarge take da kallon da khadijar ke mata.

Neesah ta kalla taji wani mololon takaici ya danne mata zuciya ta daure fuska a sake tace,

Anty neesah ina kwana?

Faduwa gabanta yayi tai kamar batajiba saima qara rintse idanuwa datai.

Kallon neesar yayi saiyaji ransa ya 'dan 6aci da yanda ta share ayeesha bayan yasan sarai tajita.


Ummi ce ta shafa kanta tace,

Baby bakiji Ayeesha na gaidaki bane?

Ba tareda ta bude idanuwanta ba can cikin maqoshi tace,

Banjiba,lafiya klau.

Murmushi ummin tayi ta maido da kallonta kan Ayeesha tace,

Lafiya dai naga kamar qafarki na ciwo ko?

Murmushi ta qago tace,

Eh 'dazu ne na fadi a toilet,
 daidai shigowar Ahmed ta kallesa yayi saurin 'dauke kai yana gaida ummi da Jamaal tareda inna.


Zama yayi yana cewa,

Antynah gud morning.

Bu'de idanuwanta tayi tareda tashi zaune fuskarta 'daukeda murmushi tace,

Dama ina nemanka ka kaini saloon.

Wani kallo ya jefa mata fuskarsa 'daukeda murmushi yace,

Ko ina kikeso zan kaiki Anty nee.

Wani kallon takaici ummi ke aika masa kafin ta maida kallonta gun Jamaal taga ko kallon gefensu bayayi wayarsa yake ta6awa kafin ya miqe yabar Palon.
********
Sati biyu kenan da faruwar al'amarin amma basu sake ha'duwa ba sbd taushinsa sosai takeji barin ma yanda yake tarairayar ayeesha yana bata kulawa akan qafarta koda a Gavan ummi ne shiyasa Sam ta fita al'amarin kowa a gidan sai Ahmed dake tsananin kula da ita ko a school ko a gida gashi qawarta zeey tayi tafia bare ta 'debe mata kewa.

Ta 6angarensama shareta yayi ya fita harkarta sbd yanda ya lura Sam bata qaunar ko ganin ayeesha duk da ayeeshar na binta matuqa gurin girmamata amma ko yaushe 'daure 'dauren fuska take har tausayi ayeeshan ke basa sbd yanda take tsananin kyautatawa neesan.


Ummi ma tana yabawa sosai da yanda ayeeshan take kula neesan tareda girmamata.


Zeey kuwa qarya tayiwa neesah akan tafiya tayi sbd fuskarta da har lokacin bata qarasa warkewaba.


Ahmed kuwa sosai yasamu yanda yakeso sbd fushin datake da Jamaal yasata basa time 'dinta sosai yaketa cusa kansa duk da ita batasan Inda yadosaba.


Kiran gaggawane yasamesa daga gurin aikinsa yafara shirye shiryen komawa tareda ayeesha acikin satin.Mamuh๐Ÿ’‹
๐ŸŒฒ *R H F W F*๐Ÿ„_Don't forget to vote, follow and comments_


*_DACEWA_*
     _(when east meets west)__By_
_Mamuh geee_*_Viawattpad@mamuhgee_**42-43*Koda taji maganar komawarsa a bakin ummi yitayi kamar batajiba aganinta meya dameta da tafiyarsa tun da can bare yanxu dayake da mata.

Shareta shima yayi duk da yaso ya tsaya harsai ya gudanar da bincikensa akan Ahmed da duk wasu abokanan aikinsa koma su waye amma zai bari saiya dawo.


Sarai ummi ta lura da yanda neesah ke 'daure fuska idan ayeesha ta shigo saidai tayi murmushi sbd da zarar ta tambayeta zata iya tada rigimar itadai a raba aure,
Ita babban burinta da adduarta shine Allah yasa neesan tasamu ciki ko ta saduda ta daina maganar raba auren.Ranar da zasu wuce qin fitowa tai ko palon sbd ko ganinsu bata buqatar yi.

Wanka tayo tana fitowa ta zauna gaban mirror ta fara Shafa cream 'dinta na jarggens,
Tana cikin fesa spray yashigo 'dakin da sallamarsa iya maqoshi.

Qin juyowa tayi bata kuma 'dagoba taci gaba da abinda take.

Tsayawa yayi bayanta tareda harde hannuwa yana kallonta ta cikin mirror.

Aje turaren tayi ta miqe zata bar gurin ya towel 'dinta
Tai saurin dafewa tareda 'dagowa rai a6ace zatai magana  saijin tayi bakinta ya sauka kan nasa sbd fuskarsa dake daf da tata.


Zaro idanuwa tayi tareda matsawa baya da sauri tareda tamke fuska sbd wani lazy smiling dayake sakar mata yana kallon tsakiyar  idanuwanta zuwa pink lips dinta.


Qara tamke fuska tayi ganin kallon nasa na neman sauyawa.

Wardrobe ta bude ta jawo doguwar riga tana juyowa still sai a jikinsa sbd ya kuma matsota sosai.

Ahankali ya shigar da ita jikinsa ya rungumeta tsam tareda sakin ajiyar zuciya a ciki.

Qoqarin qwacewa takeyi amma ta kasa saita lafe itama tanajin faduwar gaba da tsoro na shigarta Wanda ta rasa gane na meyene.,

Hawayen datake 6oyewa suka gangaro mata batasan sanda tasa hannu ta qanqamesa ba.

Rintse idanuwa yayi tareda shafa kanta haka kawai shima yakejin fa'duwar gaba da damuwa mai tsanani na shigarsa.

Murya can qasan maqoshi yace,

Am going back neee,
Do you need or want sumthing?

Batace komaiba saima hawayenta dasuka 6alle.

Shafa kanta ya qara tareda 'dago fuskarta yana kallo ta rintse idanuwanta hawaye na cigaba da gangaro mata.

Saukar light kiss taji a lips 'dinta tareda sakinta ya fice 'dakin da hanzari.

Koda ya fito ayeesha na motar Ahmed na jiransa ya fa'da suka wuce xuwa airport.


Zubewa tayi bakin gado tareda toshe baki kukanta na fita ahankali sbd haka kurin tsoro da fargaba ke shigarta.
**********
Tunda suka tafi ta qara zama wata iri sbd ta rage zaman gida sosai kullum a school suke yini ita zeey sbd yanxu su zeey babu wani tuggu tunda kusan sun samu yadda suke so sbd ayeesha na can tareda Jamaal 'din.

Plan 'daya suka tsayar shine suna dawowa zasu ha'da mata wannan tarkon da dole Jamaal zai tsaneta had abada bazai kuma ko kallon mai sunantaba.

A 6angare 'daya tsananin tausayi da qaunar Ahmed ke shigarta sbd gaba 'daya ya susuce baida wata damuwa saitata,
Baya iya koda cin abinci duk ranar dayaga damuwa ko hawaye a fuskarta,
Duk wani farin cikinta shine nasa hakama kullum cikin kyautata mata yake duk ya rame sbd a 'yan kwanakin wata irin wuta da ciwo dayakeji suna cin zuciyarsa akan neesah amma yaqi yake sosai da zuciyarsa ganin bai furta mataba ko nuna mata alama sbd Sam bazai juri ganin damuwa a fuskarta ba dan yasan tabbas zata shiga wani yanayin matuqar ta gane.


Ummi ma sosai take tausawa 'danta sbd tana lure da komai kuma tana hango tsananin damuwa daciwo a idanuwansa
Duk lokacin data zaunar dashi ta tambayesa meyene damuwarsa saidai ya kwantar da kansa kan cinyarta yafara hawaye yace ummi kiyimin addua  qila mutuwa zanyi sbd nikaina banajin da'din komai a duniyar yanxu.


Khadija ma dai ciwo ya tsanantar mata kuma Dr ya tabbatar mata da ciwon zuciyane yai mata mugun kamu dan haka yanxu a 6oye take siyan magani tanasha a 6oye amma Sam baya aiki sbd kullum da sabuwar qiyayyar matar jamaal ayeesha da hassadar neesah take kwana take tashi.


****
Tunda suka iso qasar ta rasa gane komai sbd Sam bayada time 'din zama gida kullum yana gurin aiki ga wani irin sabon miskilanci dake cinsa yanxu,

Abin na damunta amma daga baya data gane kukane bayason kuka tausaya mata yake idan ta fara saita koma kullum saitayi kuka
Tunda ga time 'din ya rage komai yana zama ya 'danyi wasan soyayya da ita har shopping da sauran guraren shaqatawa suna zuwa tare dan haka tuni yayi wani fresh sbd amarci da angwancewa da yayi duk da dai ba wani dacewa yayi ta hanyar making love da ita sbd Sam bata cikin jerin mata masu ni'ima duk da takawo budurcinta.


Haka suka cigaba da zama kwatsam saiga ciki ya bayyana.

Tashin farko da Dr ya sanar da ita tanada ciki yanka masa mari ne kawai batayiba sbs baqin ciki dan idan da akwai abinda ta tsana bayan neesah da Ahmed to yara ne bare ace wai ita da kanta zata haifesu.


Baro asibitin tayi bayan ta biya wani babban pharmacy ta siyo *****pills 3 sachet sbd batajin zata iya qara koda kwana 'dayane da cikin bare har Jamaal yasan tanada wani banxan ciki.

Tana isa gida kiran zeey nashigo wayarta saidata 'zauna ta 'daga wayar murya a cunkushe.

Lafiya dai Mrs cpt?

Saidata qaramin tsaki tace,

Inafa wata lafiya yanxun nan daga asibiti nake, can you imagine wai nice da ciki?
Wlh yau baqar ranace agareni dan Allah ji nake kamar na zaroshi na watsar a zinc.,


Cikin yanayin takaici itama zeey tace,

Gskia kam yanxu wayaketa wani ciki alhalin ko 'duwawuka baki gama bajewa a gidanba tunda haryanxu tsinanniyar na nan.,
To yanxu me kika yanke akan hakan?


Na riga na siyo magani zubar da sh***ge kawai zanyi yau 'din nan basai gobeba.

Kafin zeey tayi mgn taji qarar doorbell ta miqe ta bude masa tareda 'dan hugging 'dinsa kafin ta juya ta shiga bedroom suka cigaba da waya.


Zama yayi a palon yana qoqarin zame takalminsa ya hango envelope da sunan asibiti ajiki cikin hanbag 'dinta data bari palon.


Wat ya fada da qarfi cikin wani mugun farin cikinda baita6a yi ba arayuwarsa lokacin daya gama karanta result na cikin datake 'daukedashi.


'Dakin yashiga ba zato taji ya rungumeta tareda bata wani lafiyayyen  kiss sbd nan take wata irin muguwar soyayyarta da abinda ke cikinta sukai masa muguwar shiga.


Zamewa tayi tana masa kallon mamakin farin cikin dake fuskarsa dan rayuwarta bata ta6a ganinsa cikin farin ciki hakaba.


Result 'din ya nuna mata yana qara kai mata kiss a wuya yace,

Thank you my eshaa.

Qaqalo murmushi tayi tareda zamewa baqin ciki cikin ranta kamar ta rufesa da duka.

Miqewa yayi yakoma palo yana cewa,

Lemmi share this happiness wit my ummi sbd nasan abinda take farin cikin samu tuntuni kenan.


Yana fita ta 'dago wayarta ta mayar kan kunne sbd har lokacin zeey bata kasheba.


Wani shu'umun murmushi mai sauti  zeey tasaki tareda cewa,

Qawata lakacin dawowarku yayi sbd wannan damace dazamu jefi tsuntsu biyu da dutse 'daya.


Tunani ayeeshan tayi tareda sakin wata muguwar qaramar dariya tace,

Tabbas ciki zai zube neesah zata kar6i igiyoyin aurenta uku a hannunta.

Dariya zeey tasaki tace,

Hahhhhh lokacin damuka da'de muna jira gashi yazo a cikin sauqi domin matuqar cikin nan ya zube ba Jamaal ba ka'dai har ummi saita tsaneta hmmmnn wat a great and best plan.Mamuh๐Ÿ’‹
๐ŸŒฒ *R H F W F*๐Ÿ„_Don't forget to vote, follow and comments_


*_DACEWA_*
     _(when east meets west)__By_
_Mamuh geee_*_Viawattpad@mamuhgee_**44-45*Zaune suke a palo ummi na kallon wata drama a tashar cwtv
Itakuma neesah kwance take jikin ummin tana chatting da amirah,

Khadija ma tana palon zaune tana chatting sama sama sai inna dake kicin tana aikin abincin dare.

Wayar ummin ce tayi ringin tana dubawa taga Jamaal ne tai answering idonta nakan tv.

Wani farin cikine ya mamaye zuciyarta da fuskarta lokaci 'daya jin abinda ya fada mata bayan sun gaisa.

Cikin hamdala tace,

Yanxu dai ina fatar dai batajin matsala ko damuwar kowa komai ko?

Eh yace ahankali tareda miqawa ayeesha data fito wayar danta gaisa da ummin.

Hello ummi ina wuni?

Lpia klau ayeesha ina fatan dai ba wata matsala dakikeji ko?

Ahankali tace,

Eh ummi kawai dai inason nadawo gidane sbd abubuwan danakejin inason ci babu su anan 'din.

Hankali kwance ummi tace,

Dan wannan kam dole adawo dake sbd ma samun cikakkiyar kulawa.

Murmushin jin 'dadi tayi tana cewa,
Nagode ummi.

Yana kashe wayar ya jawota jikinsa yana kallon tsakiyar idanunta yace,

Gida kikeson zuwa?

Cikin sigar shagwa6a ta 'daga kai.

Gyara mata zama ajikinsa yayi tareda lumshe udo ahankali yace,

Zan maidaki gida tunda babyna nason zuwa gida.Tunda ummi tafara waya khadija ta 'dauke wuta sbd ta fahimci inda zancen ya dosa murya na tsananin rawa tace,

Ummi matar yaya Jamaal ce keda ciki?

Cak neesah ta tsaya daga abinda take sbd jiran amsarda ummin zata bayar.

Fuska 'daukeda murmushi tace,

Eh Allah ya kawo dawowama zatayi nan sbd kyakkyawar kulawa.

Cak kowaccensu kuzarinta ya tsaya neesah miqewa tayi ahankali ta nufi bedroom 'dinta ta rufo qofar
Khadija kuwa duk iya yanda taso danne hawayenta kasawa tayi saida suka sauko tai saurin miqewa gudun kar ummi tagani ta nufi 'dakinta itama ta rufo suka bar ummin nabin qofofin 'dakunansu da kallon mamaki na zallar kishi data hango daga yanayin kowaccensu..tirqashi ta fa'da aranta tana jinjina kai.Sati biyu da maganar saiko gashi sun dawo batareda zato ko tsammanin zuwansu ba dan lokacin ummi ce kawai sai dady daya dawo yana gari.

Khadija taje asibiti sbd ciwonta da yayi tsanani dan har wani kakin jini take wani lokacin,

Neesah kuwa tana school tun safe.

Cikeda farin cikin ganinsu ummi da inna Rabi suka hau hidimarsu dan tuni ayeesha tafara qirqirar tanason wannan batason wancan
Dan hakama ko yanxu bayan sun huta dawowa tayi gurin ummi tace inna Rabi tayi mata wainar filawa me kwai da cabbage aciki.

Jiki ko na rawa akayo mata ta zauna bawai dan tanasoba sai dan kawai ta qara saka soyayyar cikin acikin zukatansu yanda zasufi jin zafi idan wani abu yafaru.


Khadija ce tafara dawowa tana ganin ayeeshar zaune a palo tana cin wainar ta 'dauke kai gabanta na faduwa ta gaida ummi a sanyaye harzata shige 'daki ummi tace,

Khadija bakiga ayeesha bane ko sannu da jiki bazakiyi mata ba?

Ha'diye wani yawun kuka tayi batareda ta juyoba tace,

Ina wuni?
Ya jiki?ban lura bane ummi.

Tana fadin haka ta fa'da dakinta ta rufo qofa.


Sai da maraice tadawo agajiye take ta matsu taje ta cire hills 'din qafarta.


Kamar ance ta duba gefen part 'dinsa saita hangosa a tafe yayo wanka cikin qananun kaya black trouser da dark blue shirt,
Ya qara fari sosai sai 'yar qasumbarsa dake kwance luf tayi duhu ga wani qyallin fresh da fatarsa keyi.

'Dauke kai tayi tareda tamke fuska tashige palon.


Kallo 'daya tayiwa ayeesha ta 'dauke kai zuciyarta na mata nauyi Sam ko gefen bata sake kalloba bare tasan da ummi a palon ta fa'da bedroom 'dinta da sauri.


Koda yashigo palon direct bedroom 'dinta ya nufa
Koda yashiga tana  toilet kawai saiya zauna kan dressing chair din gaban mirror ya lalubo wayarsa a aljihu yaji yabarota part 'dinsa  sai kawai ya 'dauki novel 'din dake kan mirron mai suna _the prince of chikago gambler_ yafara dubawa.


'Daure da towel ta fito batada wani kuzari dan tunda taga ayeesha ta rasa kuzarinta saima zazza6i dake qaqarin kamata.


Sam bata lura dashiba saidata kawo daf dashi tai saurin matsawa baya tana ha'de rai dan mugun zafinsa takeji haka kawai.


Murmushin gefen baki yasaki tareda aje book 'din ya miqe tsaye yana kallon 'daurariyar fuskarta yace,

Well tunda naga bakiyi murna dazuwana ba I think qofa itace hanyana yanxu so saki fuskanki ni kaina inada abinyi agabana.

Ra6ata yayi ya fice batareda ya ko waiwayotaba sbd Sam ya tsani halayenta na ko inkula da girman kan da bazai bari tayiwa mutum kallon arkiqi ba koda so 'dayane.


Ranta ne ya qara 6aci tabi qofar daya fita da kallo yazo nan be kawai dan ya ca6amin maganar 6acin rai ya fita.

Zubewa tayi bakin gado tana jinjina alamarin cikin matarsa dan tasan ko ummi zata iya yin komai akan cikin sbd yanda take hango tsananin soyayyar datakewa cikin sbd soyayyar Jamaal data shafesa.
Tundaga ranar ya daina shiga harkarta sbd ganin ta kama kanta da kowa a gidan qarshema bata yini a gidan sai school shiyasa shima ya shareta ya maida hankalinsa gurin kulada ayeesha da kullum yanxu ke fama da ciwon mara kadan kadan.Yau tun safe ayeesha tafita da cewar gidansu zata ta yini.

Shine yakaita bayan yashiga ya gaida ummanta da dadynta ya fito

Daf dazai bar layin gidan motar Ahmed tashigo layin ya qurawa motar ido sbd ganin mace aciki,
Daf dazasu giftasa yaga qawar neesah  ce zeey zaune gaban motar.

Mamakine yakamasa sosai na ganinsu atare batareda neesah ba kuma a layinsu ayeesha.

Tafiyarsa yayi tareda sanya hakan cikin tattalin bincikensa akan Ahmed.


Suna pakawa zeey takira ayeesha a waya saigata ta fito tashigo motar tazauna tareda rufewa ta kalli Ahmed a gaggauce sukayi mgna ta fita sukuma suka wuce.


Da maraice ti6is tadawo tareda zeey data biyota zata kwana a gidan.


Bayan sunci abincin dare harsunyi wanka zeey tace,

Neesah pls kiban aron wayarki mana zan 'dan kira mumy naji kosun isa kano lpia.


Duba wayar tayi har cikin hand bag 'dinta bata gantaba tace,

Inajinfa nabarota a mota.

Lah kinga natuna ba Ahmed naga ya kar6aba dazu,,,

Yes hakane bari na karbo sbd kinmaga natuna zanyi waya da mamy.

Miqewa tayi itama tana cewa muje na rakaki.Ayeesha dake zaune tareda Jamaal a balcony tana hango fitowarsu ta miqe tareda zuwa 'daki ta dauko ledar kaya tace,

My captain yaudai ga Anty neesah can nasamu gani bari nakai mata tsarabar danayo mata.

Batareda ya 'dago daga aikin dayake a iPad 'din hannunsaba yace,

Ummhhn.


Ko palonsa basu shigaba saigasa ya fito da wayar a hannunsa zai kaimata.

Kar6a tayi tana cewa,

Let's go zeey,.

Ayeesha ce tai saurin qarasowa ta hawo stairs hu'du dake qofar palon tareda miqawa neesah ledar hannunta fuska a sake tace,

Inatason ganinki nabaki wannan tsarabace.

Tamke fuska tayi tareda 'fagowa zatai mgn idanuwanta suka sauka akansa yana tsaye yana kallonsu.


Wata 'yar kwalba Ahmed ya bude batareda neesah ta luraba bare Jamaal dake nesa yayi saurin zazzage mattacen baqin macijin dake ciki ya juya ya shige palonsa yana cewa,

Antynah gud night dan ni barci nakeji.

Murya a shaqe tace,
Tnx amma ki aje kayanki bana buqata.

OK tace tareda juya zatabar gurin a tsorace da qarfi zeey takira sunan neesah tana nuna mata qaton baqin macijin daidai ayeesha zata 'dora qafarta
a tsorace cikeda firgici neesah tasa hannuwa biyu ta ture ayeesha da qarfi sbd gudun karta taka ya sareta

Wani mahaukacin ihu ayeeshar tasaki sbd muguwar faduwar datayi nantake jini ya 6alle mata.

Wani iri mugun gudu dabai ta6a sanin yanadashiba ya fito aguje ya tallafota yana kiran sunanta da qarfi nanma su ummi suka fito a ru'de sbd sun jiyo ihun
Ahmed ma a ru'den yafito yana tambayar lpia,

Khadija dake zaune cikin rumfar shaqatawar kusada qofar palon Ahmed taga komai kuma sai ayau ta tabbatarda qiyayayyarta lami ce akan wainnan.
Mamuh๐Ÿ’‹๐ŸŒฒ *R H F W F*๐Ÿ„_Don't forget to vote, follow and comments_


*_DACEWA_*
     _(when east meets west)__By_
_Mamuh geee_*_Viawattpad@mamuhgee_**46-47**_I sincerely heart you labibah lawal thank you for all the care_*
*_page 'din na yau naki me_*..Jinin dake zubane sosai ya tsananta tashin hankali da fargabarsu tuni ummi tafara kiran innalillah sbd tarigada ta saddaqar da cikin ya 6are.

Sunkutarta yayi duk da jinin dake 6ata masa jiki suka nufi mota ummi da inna rabi suka shiga yabar gidan da mugun speed.

Qoqarin zubewa takeyi zeey tai saurin tarota sbd sosai take cikin tashin hankali dan Sam ta manta da cikin da ayeeshar take dashi yanxu shikenan tayi kisa tunda ta 6arar mata da ciki.

Hawayene suka gangaro mata na tausayin ummi yanxu shikenan ta rusa musu farin cikinsu dasuka kasa samu daga gareta sun samu daga wata tayi musu hasararsa.


Zubewa tayi gurin tareda sakin siririn kuka ahankali sbd har cikin ranta taji baqin cikin itace silar rasa farin cikinsu.


Ganin tana kukan datake mai tsima rai yasa jikin Ahmed yayi mugun sanyi ya matso zai kamata yaji an riqe hannunsa a tsorace ya 'dago.,
Khadija ce tsaye idanuwanta taf da hawayen tausayin kanta dana neesah a karo na farko ta kallesa cikin ido murya a sanyaye tace,

Ahmed karka shiga hurumin Allah sosai sbd samun sassaucin sauran lefukan da ka jima kana aikatawa.

'Dauke numfashinta tayi tareda kama neesah suka bar gurin.

Kallonsa zeey tayi zatai magana ya watsa mata idanuwansa dasuka kada rai a 6ace yace,

Tabbas danasan haka abin zai kasance dana qi biyewa kafirar baqar zuciyarku saidai na reni sonta a zuciyata na mutu dashi koba komai zan zama masoyi na haqiqa ko bayan raina zatai alfahari da ni amatsayin masoyi na haqiqa.


Wani kallon tsana da wulaqanci ta watsa masa kafin tace,

Ko yanxu ma lokaci bai qure maka ba saidai ka shirya kai da neesah ne zaku 'dandani 6acin ran Jamaal kun 6arar masa da ciki.

Qoqarin damqota yayi tai baya tace,

Don't  waste your energy tun yanxu
Save it you gonna need it later,
Da kana nufin ka dakemu ne ka daki banxa to bari kaji lokacin da kake zazzage qaton macijin a kusada qafar ayeesha kana tunanin ta kareka kar Jamaal ya hango to abinda baka saniba shine sosai tai seti da yanda ya hangoka tsaf dan haka saika shirya fuskantar 'dan uwanka da iyayenka.

Wucewa tayi tareda sakin dogon tsuki tana cewa,
Dama bakasan dawa kake wasaba.


Kasa komawa bedroom 'dinsa yayi sbd jirin dake neman 'dibarsa sai kawai ya durqushe agurin hawayen da baisan dasuba suka fara gangaro masa na tausayin neesah dakuma mummunan tashin hankalin da gidan zasu fuskanta ta rarrabewar kawuna.

Khadija nakaita 'dakinta ta fice zuwa nata 'dakin ta zube a qasa tana kuka Mara sauti sbd wannan abun datake gani su ayeesha nayi to tabbas bazata samu Jamaal ba har abada.

Zama zeey tayi kusada ita tareda rintse ido ta dafa hannun neesah dake zaune quryar gado idanuwanta jajir.Koda suka isa asibiti aka kar6eta batareda 6ata lokaciba aka tabbatarmusu da cikin ya xube gaba 'daya dan haka basai anyi wankin Mara bama shiyasa aka kasa gano magani tasha cikin tuni dama yafara zuba.


Duk iya yanda ummi taso daurewa saida tayi hawayen tausayin Jamaal sbd yanda idanuwansa suka ka'da jajir ko magana yakasayi sai zama yayi bakin gadon da ayeeshar ke kwance ya riqo hannunta da wannuwansa biyu ya rintse ido yanajin wani irin zafi a zuciyarsa.


Bata wani jimaba ta farka tana bude ido ta fashe da wani irin kuka.

Bude idonsa yayi tareda riqota yana qoqarin lallashinta

Ummi ma matsowa tayi tana cewa,

Ki kwantar da hankinki ayeesha Allah zai kawo miki wani insha Allah.

Ihu ta qwalla jin abinda ummin ke fada takallesa tace,

Na rasa babyna ko yananan?

Girgiza mata kai yayi yana qoqarin kamota jikinsa ta fasa ihu tana kuka cikin tashin hankali tareda fusge drip da canola dake jikinta tana rusa kukan daya masifar 'daga hankalinsu.

Qoqarin kamota yake tana turjewa kuka take sosai tana cewa,

Babyna,babynah inason babynah.

Tsuru inna rabi tayi tana kallonta cikeda mamakin kukan datake akan ta rasa cikin fari kuma agaban uwar mijinta.

Ummi kuwa tausayin ayeeshan da baqin cikin rasa cikin yasa itama hawayen take.

Daqyar ya qanqameta ajikinsa sbd ko magana baya iyayi
tsit 'dakin yayi banda kukanta dake fita ahankali bakajin komai tuni idanuwanta da fuskarta suka kumbura tsabar kuka kallo 'daya zaka mata tabaka tausayi idanbakasan komaiba.


Har gari ya waye suna zazzaune kuma har lokacin  kukan take saidai qarfinta daya qare hawayene kawai ke tsiyayowa ahankali.


Dr na shigowa da safe ya sallamesu shida ummi ne suka kamota ahankali take takawa harsuka isa mota.

Tana shiga motar ta fashe da wani sabon kuka ahankali ya shafo kanta yana kallon fuskarta dan har lokacin baya iya magana.

Da shaqaqqiyar murya tace,

Nidai ka kaini gida gurin ummana.

Girgixa mata kai yayi dan ganin yake idan ya bu'de baki yayi magana wuta zata iya fitowa sbd wutar bala'in dake cin zuciyarsa.

Ummi ma da ranta ke 6ace dannewa tayi a fuske tace,

     Muje akaita gidan idan hankalinta ya 'dan kwanta daga baya sai a dawo da ita.


Har cikin gida ummi takaita gurin ummanta dasai alokacin tasan meke faruwa hankalinta ya tashi matuqa.


Harsuka iso gida bamai iya magana acikinsu.


Tsit palon ba kowa dukaninsu suna 'dakunansu bawai dan basu tashiba saidan babu mai kwanciyar hankali da nutsuwa acikinsu.


A palo ya zauna ya rufe idanuwansa dasuke masa wani yaji yaji tsabar Jan 6acin rai.

Ummi kuwa 'dakin neesah ta nufa tana shiga ta tarar da ita zaune tsakiyar gado ta cusa kanta cikin cinyoyinta ba kuka takeba amma idanuwanta sunyi jajir hakama fuskarta sbd kukan data kwana tanayi.

Kallonta ummin tayi tabbas tanason neesah fiyeda 'yayanta saidai hakan bazai hana tayi mata fa'dan abinda tayiba.

Aneesah"" ummi takira sunanta da fuska a 'daure.

'Dagowa tayi zuciyarta na harbawa sbd ummin bata ta6a kiran sunanta ba.

Juyawa tayi fuska ba walwala tace,

Kizo Palo yanxu kisameni.

Jiki a sanyaye ta sauko gadon ta fito palon.

Tana fitowa ya rintse ido yanajin zafin zuciyarsa na qaruwa.

Jamaal "" ummi takira sunansa bai amsaba ya miqe tsaye tareda rintse ido yace,

Ummi bana buqatar sauraron komai dangane da wannan maganar sbd bana buqatar cigaba da zama da ita and pls ummi karku tirsasani sbd komai zai iya faruwa....

Da sauri Ahmed ya qaraso gabansa zaiyi magana Jamaal ya wanka masa Marika guda biyu a Jere.

Tasowa ummi tayi ta riqe Jamaal 'din
Cikin wani mugun 6acin rai yace,

Kaida ita wlh badan ummi ba saina nuna muku matsayinku.

Idonsa jajir shima ya 'dago murya a karye yace,

Ko yanxu ka nunamin tsayina zan 'dauka koyayane amma dan Allah ka yarda dani karka hukunta neesah ba laifinta bane zan dauki kowane irin hukunci nawa da nata.

Takaici da baqin cikin Ahmed 'din ne suka qara rufesa ya fixgo neesar ya jefawa Ahmed din harsaidata bugu a goshi jini yafara fitowa a hasale cikin karsashi yace,

Kuje can Ku qarata bana bugqatarta bare kai da har abada na cireka cikin jinina.

Kallon Ahmed ummi tayi cikin 6acin rai idonta taf da hawayen baqin cikin dake shirin afko musu tace,

Gskia ne dasa hannunka dumu dumu a 6arewar cikin?

Ido jajir yana kallon neesah dake kukan dake cin ransa yace,

Sharrin she'dan ne ummi amma dan Allah karkuga laifin neesah...wani wawan Marin takaici ummi tasakar masa tana huci kafin tayi baya inna Rabi tai saurin riqeta tana hawaye itama sbd ganin masifar data afkowa gidan.

Rarrafowa yayi yana hawaye murya na rawa kamar zararre yace,

Ure angry ummi and you have every right to be amma
Ummi kuyimin hukuncin komai amma dan Allah kice kar Yaya ya rabu da neesah ummi sonda nake yiwa neesah yakusa zuwa qarshe dan nasan kasheni sonta zaiyi amma bazan ta6a bari tarabu da Jamaal ba, ummi inason neesah,ummi sondanake mata bazai bari nabarta ta cutuba um...

Dukan baqin ciki Jamaal ya rufesa dashi tako ina shikuwa ko motsi yaqi yi sai kallon neesah dake kallonsa cikin wani irin yanayi na shiga zuciya tana kuka ahankali.

Ummi ma kukan take ahankali takasa koda motsi ga jini dake fita ta baki da hancin Ahmed amma har lokacin Jamaal yakasa daina dukansa.

Har lokacin idonsa nakan neesah batasan sands ta matso da gudu ta rungumo kansaba dayayi sharkaf da jiniba ta fashe da kukan sonsa da tausayinsa.


Zuciyarsa ce taqara tunxura da baqin ciki tareda zafin rai ya fixgo qatuwar electric flower verse ya 'daga a hasale zai qarasasu kowama ya huta da azabar  zuciya khadija dake tsaye tuni tana kuka kamar ranta zai fita ta qarasoda gudu ta gifta inna rabi ma tuni ta riqesa nan ya dafe zuciyarsa dake shirin bugawa yabar palon yana rangaji dan har lokacin tana rungume da Ahmed 'din da tuni ya fice hayyacinsa hannunsa gam cikin  nata.


Jiri takeji da zazza6in tashin hankali amma haka ta miqe da gudu ta nufi 'daki ta 'dauko key zeey dake 'dakin tana leqen komai ta taso da sauri ta kar6i key sbd neesan kanta bazata iya driving ba.


Harsuka fice gidan ummi bata motsaba  saima sabon kukan dayazo mata inna Rabi na rarrashinta jiki asanyaye da tashin hankali.


Baya take taredashi hannunta na riqe da nasa duk da itama tuni tafara ganin dishi dishi kafin idanuwanta suka rufe ruf.


Wani shu'umin murmushi zeey tasaki tareda qarawa mortar gudu  ta nufi hanyar barin gari.

Tafiyar 5 kilomita tayi daga cikin garin kafin ta gangara daji ka'dan shige gate 'din 'dan babban gidan leloh da yaransa.

Yaran liloh biyu suka shigar mata dasu ciki tabar motar nan takar6i mukullin motar liloh 'daya ta koma cikin gari a guje.


Qofar gidansu ayeesha ta parker batareda tafitoba takirata awaya ta fada mata tana qofar gida.

Ayeesha da tuni dama ta girgije tun bayan barinsu jamaal ta fito cikin Riga da wando black tareda blue facingcap da black speck ta fito riqeda handbag ta fada motar dama zeey bata kashe ba ta Figa da gudu suka bar qofar gidan.


Suna parking motar Habib nashigawo harabar gidan.

Wani kallo yake watsawa ayeesha yana cewa,

Finally dai today is our day of victory.

Cikin farin ciki mara misaltuwa tasaki dariya tareda kar6ar kwalbar hannunta leloh ta kur6a tace,

Yes and all tnx goes to our dearest zeey.

Dariya suka sheqe da ita gaba 'daya suka 'dunguma zuwa palon.Mamuh??
?? *R H F W F*??_Don't forget to vote, follow and comments_*_DACEWA_*
     _(when east meets west)__By_
_Mamuh geee_*_Viawattpad@mamuhgee_**48-49*Ahankali tafara bude idanuwanta dasukai mata nauyi dakuma qirjinta dake mata matuqar ciwo.

'Dakin tabi da kallo taga lafiyayyen 'dakine ta lumshe ido tana jin azabar ciwon kai da qirjinta yana qaruwa.

Dafa bango tafarayi ahankali ta tashi zaune saita hango Ahmed gefenta a yashe bayako numfashi gabanta ya buga nan take komai yadawo mata ta rarrafa kansa ta girgizashi jikinta na rawa hawaye na gangaro mata.

Ko alamar rai bata gani atareda shiba a ru'de ta rarrafa gurin qaramin fridge 'din dake 'dakin ta bu'de bataga ruwa acikiba  hasalima ko aiki bayayi ta miqe jiri na 'dibarta ta fa'da mataccen toilet 'din dake 'dakin daqyar ta samo ruwa da alama ma sun dade dan harsun fara canza kala amma bata damuba ta 'debo ta zuba masa a fuska.

Sam babu alamun zai motsa ta qara zuba masa amma bai motsaba.

Jikintane yasaki ta zube gabansa tareda rungumo kansa ta fashe da wani irin kuka mai ciwo da bata ta6ayiba a rayuwarta sbd har cikin tsakiyar ranta takejin sonsa ayanxu.

Kuka take kamar ranta zai fita hartana shaqewa..

Ahankali taji ya motsa kansa yana qoqarin 'dago kansa amma ya kasa.

Dariyar farin ciki da kukane suka zo mata lokaci 'daya ta 'dago ta kallesa hawayen jajayen idanuwanta na tsananta gudu murya a dashe tace,

Ahmed pls don't leave me...

Lumshe idanu yayi cikin azabar ciwon dayakeji daqyar bakinsa ahankali yace,

Anty neesah pls forgive me,
Son danake miki ne yasa idanuwana rufewa harna aikata abubuwa da dama pls forgive me.

Cikin sheshekar kuka tace,

Ahmed na yafe maka amma pls kar katafi kabarni daidai lokacin da zuciyata take tsananin buqatarka.

Lumshe idanu yayi yace,

Ina miki so mai tsani Anty neesah shiyasa ko ayanxu bana baqin cikin mutawa ahannunki saidai baqin cikina zan tafi nabarki cikin tarin maqiya marasa imani su ayee...

Numfashinsane yafara qoqarin sarqewa ga jinin daya qara 6allewa daga bakinsa.

Tashi tayi da sauri cikin tashin hankali tana waiwayensa ta nufi qofar 'dakin ta fita Neman taimako.


Zaune suke suna tattaunawa cikin farin ciki ga kayan drinks da snacks a gabansu..

Habib da ayeesha suke zaune kujera 'daya duk kusan Rabin jikinta cikin nasa
Sai zeey dake zaune ta 'Dora qafafunta kan table 'din gabansu
Leloh ma qafarsa akan table 'din take yana busa sigarinsa tareda korawa da giya.


Zeey ta 'dau remote ta rage volume  tareda kallonsu tace,

Guys time na tafiya muyi abinda yakamata kowa yakama gabansa sbd ni da anbi ta tawa datun kafin nazo nan dasu zan Parker motar a daji na kunna mata wuta duk su qone kowama ya huta.

Murmushi ayeesha tasaki tareda hararar Habib tace,

Wannan kwa'dayayyen yace saiya cire kwadayinsa akanta ya muka iya.

Liloh yasaki wata yar iskar daria yace,

Kuma nima saina huta da ita bayan yagama sbd kyawu irin nata bantaba ganinsaba dan haka zan 'dandana na tabbatar idan har ciki haka abin yake.

Koma me zakuyi kuyi dan a qaje nake danaga fitar numfashinta na qarshe bayan nagama ganin kun wulaqanta rayuwarta kunyi mata kaca.....

Idonta ne ya sauka cikin na neesah kafin ta qarasa maganarta ta miqe batareda wani tsoroba ta nufeta tana wani shu'umin murmushi.

Duk iya yanda taso danne mamakin da tsoronta kasawa tayi tafara binsu da kallo 'daya bayan 'daya idanuwanta na ka'dawa da mummunan 6acin rai kafin ta tsaida kallonta kan zeey tanajin wani 6acin rai na shigarta.

Daria zeey tasaki cikin kallon raini zatai magana neesah ta 'daga hannu ta yanka mata wani gigitaccen mari saiga ha6o ya 6alle mata ta 'dago a hasale zatai magana nesaah ta kuma watsa mata wasu marika biyu atare.

Atare dukkansu suka miqe suna kallon yanda idanuwan neesah 'din sukai jajir alamun takai qarshen fusata.

Baya zeey tayi tareda rarumo qatuwar kwalbar giyar leloh ta kwa'dawa neesah a kai tuni goshinta ya fashe da jini.

Sake 'daga fasashiyar kwalbar tayi ta soka daidai cikin neesah daidai nan Ahmed daya taso yana bin bango ya kara kwalbar tayi masa kyakkyawar suka a ciki.

Ihu neesah tasaki tareda 'daga hannuwa ta riqosa lokacin dayake qoqarin zubewa amma taji an damqota ta baya.

Kuka take tana kiran sunansa tareda qoqarin qwacewa sbd ganin ya zube jini na gangarowa daga jikinsa amma har lokacin idanuwansa ita suke kallo bakinsa na motsawa ahankali tana iya gano sunanta yake fada.

Hannu take miqawa ta kamo nasa daya ke miqo mata Habib yafara janta yana cewa,

Yaudai duk wani miyau na saina maida akanki kafin ya yayyagaki mu cinna miki wuta harke har wannan sabon tauraron zuciyar taki.


Janta yake da qarfi yana qoqarin turata 'daki tana ihu tana qoqarin qwacewa.

Lumshe ido Ahmed yayi cikin azaba kafin ya tattaro 'dan qaramin kuzari ya fixgo bindigar wandon leloh daya hango ya harbi Habib saura qiris yasamu neesah sbd hannunsa dake rawar rashin qarfi.

A kafa'da Harbin yasamu Habib ya zube gurin a sume.

Miqewa yayi da qyar  ya riqo hannunta yana nunasu zeey da bindigar duk da ba sosai yake ganiba sbd har lokacin jini sosai ke fita a jikinsa.

Qofa suka nufa yana nuna musu bindigar sbd ko mgn baya iyayi.

Mota neesah ta bude Allah ya taimakesu akwai key ajiki zeey bata zareba tashiga seat 'din driver Ahmed ya kalleta ahankali yace,

Neesah kitafi xan taresu harsaikin kai gida just know one thing neesah I love you,ina sonk.....

Shigar bullet 'din da wani yaron leloh ya harbo a gefen qirjinsa ya katse maganarsa
Neesah ta qwalla qara batasan sanda ta qarfi ya shigotaba ta fixgosa daga ciki ya fa'do cikin motar ta fixga da mugun speed sukabi ta cikin gate suka bar gidan.Mamuh??
?? *R H F W F*??_Don't forget to vote, follow and comments_


*_DACEWA_*
     _(when east meets west)__By_
_Mamuh geee_*_Viawattpad@mamuhgee_**50-51*Gudu take sosai tana kallon gefensa dayake kallonta da idanuwansa dake qoqarin rufewa yana murmushi jini na zubowa daga bakinsa.

Hannuta 'daya ta miqa ahankali ta kama nasa tana hawaye murya na rawa tace,

I love too Ahmed,, ina sonka har cikin raina so mai tsanani so am begging you not to leave me pls Ahmed., ina sonka...

Saukar harbi taji cikin motar tasu ta 'dago da sauri taga motarsu zeey ce taredasu leloh ta figi motar ta qara gudu.

Harbin motarsu suke tako ina inda ayeesha ta fixge bindigar hannun leloh ta saita kan neesah tana cewa lets finish this today.

Harbowa tayi Ahmed ya yunquro da 'dan qaramin kuzarinsa ya tare bullet din ya sauka a tsakiyar bayansa.

Wani wahalallen nishi yasaki tareda zubewa jikinta.

Sakin motar tayi tareda rungumosa tana rintse ido tace,

Let's die together my Ahmed.

Daji motar tafara gangarawa dasu Wanda hakan yafara Jan hankalin motocin dake wucewa suka fara tsayawa da sauri su leloh suka tsaya daga nesa dan kar agane su suka biyosu.


Wani qaton rami motar ke qoqarin fa'dawa bayan tafara kamawa da wuta Ahmed ya tattaro wani qarfi ya tura 6an6areta jikinsa tareda turata waje da qarfi ta window riqe hannunsa tayi tana ihu tana kiran sunansa ya kalleta a wahalce yace,

Neeees'''bai qarasaba sulbin Jinin hannuwansu yasa ta sulbuce daga hannusa ta ganngara gefe kanta ya daki wani qaton dutsi nan take ta sume motar ta fa'da tareda kamawa da wuta sosai.

Ajiyar zuciya suka sauke kusan duk  atare ganin yanda wuta kecin motar sun tabbatarda bamai Rayuwa tsakanin neesah da Ahmed.

Kallon zeey ayeesha tayi cikin samun wani cikakken kwanciyar hankali tace,

Finally I got all I ever wanted.

Cikin taya aminiyarta farin ciki tace,

Well then lets all wish you a happy married life wit your captain,,you alone.

Juya kan motarsu sukayi suka bar gurin hankalinsu a kwance.

Aliyu mamman aliyu shine babban aminin Ahmed yana kawowa gurin yaga daidai lokacinda motar ke qoqarin fa'dawa rami yakuma tabbatarda motar neesah ce ya fito motarsa da sauri amma kafin ya iso motar ta fa'da tareda kamawa da wuta amma yaga lokacin da neesah ta gangaro ta daki dutsi.

Gurinta ya qarasa da sauri ya 'daukota yana kallo motar ta cinye tas da wuta ga amininsa aciki duk da kuka yake sosai kamar qaramin yaro.

Motar police ce tareda tasa suka 'dauko gawar Ahmed daya qone qurmus bayan an kashe wutar tareda neesah dake sume kamar gawa suka nufo cikin gari.


Asibiti suka fara kai neesah tareda barin 'yan sanda biyu gadinta kafin suka nufi gudansu Ahmed da gawarsa Wanda isarsu yayi daidai da isowar dady daga tafiyarsa.


Koda aka ciro gawar gaban dady aka bu'de saura qiris ya zube saida aliyu yayi saurin tarosa daidai fitowar Jamaal sbd jiniyar dayaji tashigo har cikin harabar gidan.


Gabansane yayi mummunar sarawa yayi saurin dafa motar sbd mahaukacin jirin daya 'dibesa.

Xubewa yayi gaban gawar tareda dafe kansa hawaye suka gangaro daga idanuwansa a karo na farko arayuwarsa  tun tashinsa baita6a koda hawaye ba bare kuka sai yau dayaga gawar Ahmed.

Rawa jikinsa keyi sosai kamar qaramin yaro ko mgn yakasayi.

Khadija ce tashigo harabar gidan cikin motar ta tun kafin tai parking jikinta yayi masifar sanyi ganin kamar gawa gabansu dady tanayin parking ko key bata tsaya cirewaba ta fito da sauri jikinta na rawa.

Cak ta tsaya gaban gawar tareda qurawa gawar ido tagano tabbas Ahmed ne duk da ya qone sosai amma ta gane shine hannu ta 'dora akai tareda sakin kuka mai qarfi ta zube a qasa.

Inna Rabi ce ta fito da hanxari jin ihun khadija
Itama wani qaqqaran salati tasaki tareda fashewa da kuka ahankali.


Duk da tana cikin tsananin damuwarda ko motsi bata son yi sbd azabar ciwon kai dake damunta haka ta miqe jin hayaniya harabar gidan gashi inna Rabi data leqa bata dawoba.


Turus ta tsaya ganin gawa ga khadija daketa kiran sunan ahmed 'din tana kuka kamar ranta zai fita.

Jiri me qarfine ya 'dibeta tayi baya Jamaal ya dago tsalle ya tareta ta rintse idanu saiga hawaye sun 6alle masu qarfi sbd sobon son Ahmed 'dinta da wani mugun tausayinsa da kewarsa dasuka rufeta lokaci 'daya ta fashe da kuka ahankali mai shiga rai tana tunanosa.


Duk iya tashin hankali iyalan gidan sun shiga dan kowa kuka yake sosai sbd Ahmed 'din abin son kowane.

Har aka shiryasa aka rufesa aka dawo bamai iya magana sbd sosai mutuwarsa ta ta6a kowa na gidan musamman ummi data zabge lokaci 'daya ga wani irin ciwo da zuciyarta keyi.

Har washe garin rasuwarsa neesah bata farfadoba sbd likitoci sun tabbatarda sosai ta bugu akai.

Mamynta datazo ita ke jinyarta sbd inna Rabi ayyuka sun mata yawa na mutane dan gidan kusan acike yake sosai da mutane.


Sai ranar daza'ayi adduar uku ta farfado tana ihu tana kiran sunan Ahmed kamar zararra.

Daqyar aka samu ta saurara sbd allurar da akai mata ta kashe jiki.

Lamo tayi jikin mamy hawaye nabin fuskarta amma tanajin ra'da'di da zafi a zuciyarta amma ko juya idonta bazata iyayiba bare ta motsa sbd allurar da akai mata.

Duk iya yanda aka tsammata daga gareta alamarin ya wuce nan dan sosai
Zabure zabure takeyi duk lokacin da allurar tasaketa harsai ankuma yimata wata.

Cikin kwana 'daya tashin hankalinsu ya ninku bayan na rasuwar Ahmed sbd sabon alamarin dake tattareda neesah,

Kallo 'daya zakai mata tabaka matuqar tausayi sbd yanda ta yamutse ta rame kamar wadda tayi jinyar shekaru gashi kowane lokaci yanxu cikin bacci take sbd allura da ake mata koda yaushe sai hakan ya ta6ata matuqa dan wani irin haske da yellow yellow tayi kamar mai wani ciwon.

Kuka mamy keyi sosai sbd tsaf tarigada tagama hango ta6in hankali atattare da neesah ga rashin abinci da ciwo dake cin qwaqwalwarta sun sauyata sosai.

Doctors biyar ne suka taru suka duba result 'din hoton qwaqwalwarta suna jinjina alamarin.

Babban Consultant 'din cikinsu shiya 'dago ya kalli Abba da dady sai Jamaal dake gefensu tsaye shima duk ya rame yayi wani 'dan haske yace,

Well alhaji I'm really sorry to say this but a iya qwarewar bincikenmu mun gano buguwar da kanta yayi tareda mummunan firgitar rasa wani ko tsoron wani yasa qwaqwalwartata yanxu bazata iya aiki daidaiba saidai nan zuwa da 'dan wani time idan komai yafara ragewa daga firgicin datake cikin by god grace muna sakaran everything will fall to its normal place saidai yanxu kada a ringa matsa takurata sosai da tambaya ko kuma wani Abu dazai firgitata.

Ajiyar zuciya suka sauke atare Abba yayi masa godia suka miqe suka fito office 'din jiki ba qwari.


Tunda Jamaal yadawo gida ya kwanta a kujerar palonsa yakejin nauyin qirji Sam ko bu'de idanuwansa baya sonyi sbd Jan dasukai tun ranar da komai yafaru har rasuwar Ahmed dakuma ciwon neesah yakejin kamar zuciyarsa zata buga sbd komai ya qara shige masa duhu babban abinda yafi 'daure musu kai shine harbin bullet biyu dasuka gani ajikin Ahmed 'duk daya qone amma saida 'yan sanda suka gano kuma sun 'dauki hotunan guraren domin gudanar da bincike amma yanxu neesah da itace only hope 'dinsu itama tasamu ta6in qwaqwalwa.


Ayeesha ce da tun washe garin ranar rasuwar tadawo tana kukan munafurci Wanda ko kallo bata ishi ummi ma sbd ganin take duk cikinta ne sanadin komai har Ahmed 'dinta ya rasa ransa
Fitowa tayi daga bedroom ta zauna kusadashi tareda 'dan kwantawa jikinsa tace,

My us navy captain pls kayi hkr ka rage damuwarnan sbd tanasani damuwa nima kawai tunda sun Riga sun tafi sai mu haqura koba komai Ai haqqin kashe mana baby ne yafita a kan....


Idanuwansa daya bu'de ne suka masifar razanata ta miqe tareda ja baya da sauri.

Batareda yace komaiba ya maida idanuwansa ya rufe sbd ko kallonta baya buqatar yaci gaba dayi dan zai iya yi mata komai akan zancenta daya daki zuciyarsa.Khadija ma sannu ahankali ciwon zuciyarta ya kwantar da ita sbd damuwar rasuwar Ahmed data shigeta sosai ga wani irin tausayin kanta dana neesah dake shigarta akowace daqiqa.

Ummi ma dai sauqi sai agurin Allah sbd Sam takasa daina kukan rasuwar Ahmed saima wata sabuwar soyayyar neesah dake shigarta sbd saiyanxu tagane sona haqiqa Ahmed yayiwa neesah dan haka yanxu kamar amanar Ahmed take ganin neesah.


Ummi da kanta ta daure a daddafe ta shirya zata asibiti dubo neesah.

Shigowar ayeesha tayi daidai da fitowarsu ummi da mamar khadija dake gidan tun bayan rasuwar bata komaba.

Khadija ce tafito itama duk ta qarmaje ta zabga uwar rama sbd ciwo sake cinta.


Gaidasu ayeesha tayi tareda qaqalo murmushi tace,

ummi fita zakuyune keda bakyajin da'di.?

A 'dage mama ta kalleta sbd Sam ta tsani matar Jamaal dan ita 'yarta khadija taso 'daya daga cikin 'yayan ummi su aura amma ko yanxu ba sakin kari tayiba saita tattara wannan tsinanniyar ayeeshar ayeeshar ta watsar waje khadijarta tasamu  damar zama matar Jamaal suyi ku'di kamar yanda take buri.

Mama hatsabibiyar mace ce dazata iya tarwatsa gida cikin awa 'daya komai taronsu da ha'din Kansu.,babban burinta khadija ta auri Jamaal ko Ahmed sbd dukiyarsu da sunansu batareda tasan itama khadijar Jamaal take kwa'daitawa kanta tuntuni.

Tsaf mama ta tsani ayeesha kuma da manufar fiddata gidan kota halin qaqa yasata fasa komawa tacewa yayanta( _dadynsu Jamaal_) anan zatayi zamanta dan dama batada aure sbd babansu khadija da qanwarta maryaam ya da'de da rasuwa.

Murmushin qeta tasaki tareda kallon ayeeshar tace,

Asibiti zamuje dubo kishiyarki aneesah.

Jiri ne yakusa zubar da ita ta dafa kujera jikinta na rawa cikin tashin hankalin daya kasa 6oyuwa tace,

Neesah bata mutuba ne?

Ummi mama ta 'dan kalla sbd ganin tambayar ta ayeesha ta 6ata mata rai saita saki mugun murmushi tace,

Bangane wannan tambayar takiba da kinason ace ta mutu ne?

Yawu ta ha'de tafara kame kame
mama tasaki murmushi tabi tawuce sbd sarai taga takaicin maganar ayeeshan a idon ummi.


Suna ficewa Palon ta zube qasa zuciyarta na tafasa akan jin labarin rashin mutuwar neesah gefe 'daya taga alamar idan tayi wasa mama zatafisu iya tsula iskanci.

Da gudu takoma part 'dinsu ko gani batayi ta rarumo wayarta takira zeey ta fada mata.

Wani wawan ashar zeey ta sako tareda dirowa daga gadon datake kwance cikin  masifa tace,

Dole a daran yau basai gobe va muje asibiti mu qarasata sbd idan tadawo hankalinta mungama yawo.
Mamuh??
?? *R H F W F*??_Don't forget to vote, follow and comments_*_DACEWA_*
     _(when east meets west)__By_
_Mamuh geee_*_Viawattpad@mamuhgee_**52-53*_wannan page 'din na ta'aziya ne daban hakuri ga masoyan Ahmed da zukatansu suka ta6u_๐Ÿ™Zaune take tsakiyar gadon ta kwantarda kanta kan qafafunta idonuwanta qure kan qofa ko qiftawa batayi saidai sun ka'da jajir  duk ta qara zabgewa duk Wanda ya ganta saiya tausaya mata sbd ta canxa kamar ba neesah ba.

Mamy zaune riqeda remote tana ragewa Ac 'dakin sanyi sbd jin jikin neesar kamar da zazza6i.

Ummi ce a gaba kafin mama sai khadija.

Gurin neesah ummi ta nufa ta zauna jikinta na 'qara sanyi hawaye na taruwa a idonta sbd fuskar Ahmed take gani data kalli neesah.

Mamy gaisawa tayi da mama kafin ta amsa gaisuwar khadija dake raku6e kusada qofa tana kallon yanda yau neesah 'yar gayu da class takoma banbancinta da mahaukata ka'dan ne duk sbd aikin maqiya.

Rintse idanuwanta tayi wasu hawaye masu 'dumi suka gangaro mata ta lumshe ido tanajin damuwar rayuwar data tsinci kanta aciki Wanda sai yanxu take tabbatarda Allah ya hanata Jamaal ne sbd wannan azabar da neesah ke ciki ba qaddararta bace dan qila da ita'dince to da tuni su zeey 'din sun kasheta.

Shiru ya ratsa 'dakin na 'dan wani lokaci saiga Jamaal yashigo tareda ayeesha data biyosa damin ganin 'dakin da neesah take.

Kallon tuhuma mama ta watsawa ayeesah kafin ta saci kallon gefen Jamaal dake duba magungunan daya Dr kudi 'dazu da safe asiya tai fuskar mamaki tana fadin,

Meyasa ayeesah 'dazu kikayi mamakin da'akace neesah na raye harkina cewa bazai yiyu ace wani ya rayu a wutar nan ba?
A maganarki sai inaga kenan kina tsaye abin yafaru ko?

Dukkaninsu a bazata zancen yashigesu suka 'dora idanuwansu akan ayeesha don jiran mezatace ita.

Jikintane ya'dau rawa wani mugun zufa ya karyo mata ta kalli Jamaal taga ya kafeta da idanuwansa qasa qasa ai nan dabara ta fara kwance mata tana rawar murya tace,

Um..um...am..nazo wucewa ne dana dawo daga asibiti naga.....

Katseta mama tayi da cewa,

Wow wat miracle harkin iya fita keda kikai 6ari kuma idan ban mantaba a ranar aka dawo dake daga asibiti ina fatan dai ba wata matsalar ce tadawo miki ba harkika fita zuwa asibitin.

Wani yawun ta ha'de tana Neman abin cewa saikuma taji maman tasake cewa,

Kuma Kinga qanwarki nan khadija kwanakin nan tana fama da rashin lapia amma taqi zuwa asibiti sbd tsoron shiga mutane ne da ita kozaki fa'damin sunan asibitin dake hanyar barin gari saina kaita.


Cikeda baqin ciki da takaicin mamar daya cikata tace,

Nibansan wata asibitin bayan gariba.

Zaro ido mama tayi tace,

Aa kuma kikace zaki asibiti ne kikaga ha'darin a bayan gari?

Zaro ido tayi sbd shaf ta manta da haka tafada da farko.

Ummi da mamy takalla taga kowaccensu tayi nisa cikin nazarin maganganun a ranta tace nashiga uku wannan tsinanniyar matar zata kaini karshe na tona asirina da kaina dole nayi gaggawar sanar da zee a 'dau mataki akanta.

Jamaal kuwa ficewa yayi a 'dakin yana jujuya zancen mama da yanayin da ayeesha tashiga akan tambayar.

Wani mugun kallo ayeesha tabi mamar dashi tana qissima irin mummunar kisar dazatai mata.

Khadija kallonda ayeesha kewa mamarta ya ta6a zuciyarta sbd tagane manufarsa saidai bata tunanin zata bari sukai ga cutatar da mamarta zata takawa cin amanarsu da munafurcinsu burki kowama ya huta.

Mamy da ummi ne suka tafi gida sbd mamy zata 'danyi barci rana ta huta shima sbd mamar ta matsa ne akan taje ta huta ita zata zauna da neesar.

Bayan fitarsu khadija ta matso ahankali ta tsaya gaban mama tace,

Mama ki fita duk wata harkar ayeesha da mutanenta sbd they are very evil and  dangerous,
I know wat they are really capable of in fact they can kill without any hesitation so pls mama stay away from them banason wani Abu yasameki all abinda nakeso yanxu shine neesah tasamu sauqi nabata all the evidence nadanakedashi tayi facin 'dinsu kuma badan komai nakeyiba sai sbd Ahmed.

Dariya mamar tayi duk da tayi mamakin maganar khadijar sosai tace,

Karki damu khadija kawai dai yanxu ki sanar dani komai inason nasani.

Ayeesha itada.....
Shigowar zeey 'dakin tana kuka ya katse khadija fadar abinda tai niyya ta miqe tana kallon zeey dake kukan munafurcin tausayin neesah.

Babu Wanda yace mata qala harta qaraci kukanta ta miqe ta fita tana jin takaicin qin fitarsu khadija 'dakin.

Kallon mama khadija tayi murya qasa qasa tace,

Be careful mama these people are very very dangerous.

Fita khadijar tayi tareda rufo qofar ya rage daga mama sai neesah dahar lokacin ko motsi batayiba kuma idonta a bude.

Ga mamakin mama sai ganin neesar tayi ta rintse idanuwa hawaye sun gangaro.

Mamakine yakamata sbd Dr yace qwaqwalwarta bata aiki daidai to meyasa take hawaye alhalin batasan komaiba yanxu.,
Well idan kuwa neesah na hawaye it means akwai abinda take tunawa tana hawayen.


Gyara zama tayi sbd gwada tabbatarda zarginta ta yamutsa fuska tana cewa,

Wai meyasa haryanxu mamyn neesah bata dawoba nidaifa tsoro nakeji kar masu bibiyar neesah subiyo ta hanyar mamynta gashi ita bata hankalinta bare ta fa'desu a kar6o mamyn kafin itama su....kasa qarasawa tayi tace,

Allah karka bari komai yakuma faruwa da kowa.

Ta gefen ido ta qurawa neesar ido ga mamakinta saitaga idanuwanta a bude jikinta na rawa hawaye na ganganrowa da gudu daga idanuwanta.

Miqewa tayi ta qaraso gaban gadon takalli neesar da kyau tace,

Poor neesah,,,
Tell me neesah tun yaushe kika dawo normal sbd you can't fool me narigada Nagano ki.

Lumshe ido neesar tayi batareda tabada kantaba ta juyawa mamar baya.

Murmushi mama tayi tace,

You see neesah nasan matsalarki duk da khadija bata zayyane min komaiba but you see khadija nason taimaka miki amma bazan bar hakanba until nima zakiyi min wani Abu 'daya.

Idan kin amince I promise to stand wit you until you bring them down,
Koma meyene zanyi danki samu yanda kikeso just promise me zaki barwa khadija Jamaal ta aura.

Cikin wani sabon baqin cikin sunan Jamaal kawai data kira yasata miqewa idanuwanta na rinewa da qiyayyarsa datakejin tana qara kama kowace kusurwa ta jikinta takalli mamar murya a shaqe tace,

And why will I trust you bayan abubuwan dana gani da idanuwana suna faruwa da mutanen dana yarda dasu gashi na rasa Ahmed..

Kuka tasaki mai cinrai tanajin tsananin kewar Ahmed na cinta har cikin jininta.

Neesah keba maqiyiyata bace kuma banason kizama maqiyiyata shiyasa nake baki wannan damar domin dukkaninmu musamu abinda mukeso cikin ruwan sanyi after all koma mezakiyi you need evidence kuma this is the only option for you to get it.


Cikin kuka da takaici tace,

'Yarki na 'daya daga cikin mutanen dana tsana sbd she knows everything amma taqi fada gashi yanxu na rasa Ahmed bakusan ya nakeji ajikin zuciyataba jinake gwara na mutu nabi Ahmed sbd shikadai ne me sona and now I can never be with him.

Share hawayenta tayi tareda kallon mamar cikin ido tace,

Na yarda da shara'dinki sbd bana buqatar ko jin sunansa bare buqatar cigaba da zama dashi sbd zamana dashi ya qare har abada so you can take him all for your daughter but let me clear sumthing to you,,don't double cross me sbd zuciyata yanxu a bushe take nima zan iyayin komai ga duk Wanda yayi gangancin sukata,
And for you daughter zanji da ita idan nagama da manyan sbd wannan alqawarine na 'dauka duk Wanda keda sa hannu ko sanadin mutuwar Ahmed will pay ciki harda Jamaal,ummi kawai nacire duk da itama bazan iya cigaba da zama a gurintaba.

Idanuwan neesar take kallo tabbas banda qiyayya da bala'i babu abinda take hangowa a tsakiyar idanuwan.

Ajiyar zuciya tasaki tace,

Well let's say the deal is sealed..

Sabbin hawaye ne suka gangaro mata ta kwanta tana sheshekar kuka ahankali tana kiran sunan Ahmed ahankali sbd she's ready ta fight them koda zata rasa ranta.

Shigowar mamy yasa mama miqewa tana cewa,

Bari naje gida Nima na  'dan miqe.

Cikin murmushi mamy tace,

Ai kuwa angode sosai.

Tana fita a mota ta tarar da khadija bayan tagamo ganin likita dataje.

Harta tada mota ta hango zeey zaune cikin wata ash corolla8 tai saurin kallon mama taga hankalinta baya wajen taja jiki ba qwari sukabar asibitin.


Da daddare mama takalleta tace,

Khadija inason kifa'damin duk wasu bayanai dazaki bawa neesah idan ta warke.

Cikin kallon mamaki tace,

Mama karki shiga wannan alamarin idan neesah ta warke zan fa'da mata komai da kaina dan ko suwaye ma yanxu nafasa fa'da miki sbd banason kisa kanki a rigima.

No khadija kifadamin komai ina son nasani sbd inason protecting 'dinki takowane hali,
Inason nizan bada bayanin sbd koma suwaye su fuskanceni bakeba sbd karsu cutatar dake.

Jikin khadijar ne yayi sanyi ta miqe tareda cewa,

Zan fa'da miki komai gobe insha Allah mama.

Harsun kwanta taji takasa barci sbd zeey data gani a asibiti 'dazu.

Saukowa gado tayi ahankali tareda zura dogon hijab ta 'dau wayarta da kudin mashin ahankali ta fice.

Asibitin ta nufa ta tsaya 'daga nesa ka'dan da 'dakin.

Wata nurse taga tazo tashiga saikuma taga mamy tafito 'dakin.

Bataga fuskar nurse 'dinba saitaji tsoron abinda yasa mamy tabaro nurse
Ita kadai a 'dakin.

Ahanki ta lalla6a ta isa qofar 'dakin ahankali ta tura qofar.

Zaro ido tayi jikinta na rawa sbd ganin fuskar zeey sanye da kayan nurses ta na kallon neesar dake bacci tana dariyar mugunta ahankali.


Wayarta ta zaro ahankali ta danna video recording.

Sosai fuskar zeey tafito ta zaro wani qaton dogon syringe  zata yiwa neesah allurarsa saikuma ta tsaya tana tunani alamar ta manta wani Abu saita ciro wayarta daga aljihu ta danna kiran.,,

Ayeesha gani nasamu shigowa na manta a ina leloh yace na soka mata.

Cikin qaguwa ayeesha tace,

Ki soka mata koma a ina kika samu mudai ta mutu mu huta konasamu kan Jamaal nikadai.

Kashe wayar tayi ta 'daga syringe din zata da6awa neesah wayar kiran mama data duba bataga khadijarba yashigo wayarta
A tsorace zeey tajuyo sukai ido biyu da khadijar ta zaro ido cikin tsoro sbd ganin recording take.

Da gudu khadija tabar jikin qofar zeey tabiyota da mugun gudu.


Cikin mugun tsoro khadijar ke gudu gashi dare yayi kuma zeey a mota take.

Daqyar tasamu mashin jiki na rawa ta hau tafada masa inda zai kaita.

Pls qara gudu takusa kamomu wlh zata iya komai idan takamani.


Gudu mai mashin 'din yaqara sbd shima ya tsorata matuqa.

Gudu zeey keyi sosai dan ta kamosu tabi ta Kansu da mota kowama ya huta.

Wayar ayeesha takira tasanar da ita komai.

Suna isowa gidan tun bai tsayaba ta dira ta fa'da gidan tareda qalgama sakata ta nufi sashensu Jamaal da gudu sbd shi ka'dai takeson gani yanxu ta miqa masa wayar sbd harzancen ayeesha saidaya 'dauku.


Daf dazata isa taji saukar wani qaton ice a tsakiyar kanta tayi baya ta zube kanta na jini.

Janta cikin flowers ayeesha tayi kafin ta Lalla6a taje tabudewa zeey gida sukazo suka jata suka fitar waje zeey ta 'dago syringe 'din da dah neesah zasu sakawa ta sokawa khadijar shi tareda tatse mata ruwan ciki tsaf suka wuce suka barta gurin yashe tana shure shure.


Mamuh๐Ÿ’‹
๐ŸŒฒ *R H F W F*๐Ÿ„_Don't forget to vote, follow and comments_


*_DACEWA_*
     _(when east meets west)__By_
_Mamuh geee_*_Viawattpad@mamuhgee_**54-55*Kasa zama mama tayi tasake danna kiran khadijar.

Motsin dayaji yasa ya tashi baiga ayeesha ba amma yaji qarar ruwa a toilet alamar tana ciki saiya fito Palo.

Sakejin motsin yayi a waje ya ta6a qofar palon zai bude ya fita ga mamakinsa saiyaji qofar a bu'de.

Fitowa yayi yafara dudubawa daidai lokacin da mama tasake kiran khadija saiya hango hasken waya ahankali ya qarasa ya tsaya ya kalli wayar ganin hoton khadija gaban wayar yasashi 'dauka dan ya tabbatarda tatace ta yadda.

Juyawa yayi yakoma ciki daidai shigowar ayeesha ta gate tazo gurin tayita dudduba wayar bata gantaba ta lalla6a takoma.

Turus tayi jikinta na 'dan rawa ta ha'diye wani mugun yawu ganinsa tsaye tsakiyar 'dakin.

Cikin mamaki ya kafeta da ido sbd har lokacin ruwan toilet 'din aiki suke ya tsammaci tana ciki.

Tun kafin yayi magana tarigasa da cewa,

Am dama dana Shiga nan toilet 'din ruwan ciki ya tsaya sainaje na bedroom "dina ashema na manta nabar wannan akunne gashi yanxu ya kawo bari na kashe.

Qala baice mataba sai ido daya bita dashi yana naxarin yanayinta daya nuna duk a ru'de take da ganinsa a farke.


Hankalin mama yakai qololuwar tashi ta fito Palo tafara dudduba ko Ina ba khadija tuni tsoro da fargaba suka shigeta.

Motsinta ya fiddo da inna Rabi nan itama hankalinta ya tashi suka bu'de qofar palo suka dudduba harabar gidan.

Ummi ce itama ta taso jin motsi Allah yasa dady yakoma tana 'dakinta na qasa shiyasa tajisu.

Tuni mama jikinta yafara sanyi hawaye na Neman tsinke mata.

Wayar Jamaal ummi takira ta sanar dashi ba 6ata lokaci ya fito tareda wayar khadijar a hannunsa yace,

Yanxu bada da'dewaba naji motsi nafito amma wayarta kawai nagani a qasa.

Da hanxari mama ta kar6i wayar jikinta na mugun rawa tace,

Daidai ina ka tsinci wayar?

Nuna mata gurin yayi taqarasa gurin da sauri ta duqa tana dubawa taga jini kwance a gurin.

Durqusawa shima yayi cikin mamaki dan da farko Sam bai luraba,,

Jinin suka farabi har bayan flowers kafin kuma suka cigaba dabi inda jinin yabi har gate.

Jiki na rawar tashin hankali mama ta bude gate 'din tareda sakin wani razanannen ihu ganin khadija kwance shame shame cikin jini kamar gawa.

Cikin sauri Jamaal ya fito da mota gaba 'dayansu suka 'dunguma zuwa asibiti.

Suna isa aka kar6eta cikin gaggawa duk da tsakar dare ne asibitin akwai wadataccin doctors.

Zaman 'yan bori mama tayi tana risgar kuka zuciyarta na tafasa.

Jamaal kuwa zama yayi tareda dafe Kansa yana tunanin alamarin.

Idan har yanda sukabi jininta to tabbas
A daidai inda ya tsinci wayarta adaidai gurin akai mata koma menene kafin aka jata bayan flowers tukuna kuma aka kuma 'daukarta ya jefota wajen gate.,,

Idan kuma hakan ne to koma menene ko wayene hakan na nufin 'dan cikin gidan ne tunda aciki komai yafaru.

Lumshe ido yayi tareda tunano ranar da aka shigo gidan lokacin da akazo ta windon neesah,
Ko a wannan lokacin tabbas wani daga ciki ne ya  bude musu gida a zatonsa Ahmed ne to yanxu Ahmed bayanan to waye?Ana kiran sallar asuba doctors 'din dasuke ciki suka fito kowanne fuska ba da'di.

Dr sulaiman Wanda case 'din neesah ke hannunsa yanxuma na khadijar a hannunsa ya fa'da shiya kirasu office 'dinsa bayan ya zauna ya 'dago ya kalli mama dake tsiyayar hawaye kamar numfashinta zai 'dauke
Maida kallonsa gurin Jamaal yayi murya a sanyaye yace,

Captain maganar gaskia akwai matsala sbd patient 'din nan ba qaramar buguwa kanta yayiba dan harsaida mukai mata 'dinki yanxu.,,

To duk madai ba wannan ne babbar matsalarba
The biggest problem is she was injected by par*****POI's.

Murya na rawa mama tace,

Me hakan ke nufi Dr?

Girgixa kai yayi cikin tsananin jimami yace,

Jikinta ya mutu gaba 'daya,
Bazata iya tashiba,
Bazata iya motsiba,
Bazata iya maganaba kawai banbancinta da gawa shine numfashi..

Yanke jiki kawai sukaga mama tayi a sume.

Nurse Dr yakira suka 'dauketa aka nufi emergency da ita.

Ummi ma jikinta rawa ya 'dauka gashi dama yanxu lafiyartata sai ahankali tun rasuwar Ahmed.

Riqeta Jamaal yayi shima idanuwansa a rine sbd alamarin gidansu yafara basa tsoro.

Kallonsa Dr yayi yace,

And one more thing shine wannan alamarin is a serious case sbd allurar laifine saida ita dan haka zamuyi involving hukumar bincike ciki domin agano waya siyeta,gurin wa aka siyota kawai dai ka duba inda kuka 'daukota ka samo mana syringe 'din da akai allurar zamu fara tracing hannun daya riqe syringe 'din.

Ahankali yace,
Yes Dr nima zanyi farin ciki idan akayi hakan sbd alamuran sunfara zama ru'du sosai.


Bayan gari yayi haske ansamu mama ta dawo hayyacinta su ummi suka nufi 'dakinsu neesah dabaida nisa dana khadijar Duk a amenity suke.

Sosai hankalin mamy yatashi lokacinda ummi tasanarda ita halinda ake ciki
Neesah dake kwance zuru batareda sunsan tuni ta warkeba hankalinta yatashi matuqa idonta suka cika taf da hawaye shikenan ta rasa only hope datake dashi akan munafurcinsu ayeesha kuma tasan bako tantama wannan aikinsu amma tasan dole akwai dalilinsu nayin haka dole akwai abinda suka aikata khadijar tagani.
Zataso tayi magana da mama amma batasan ya zatayiba.


Jamaal kuwa gida yakoma ya koma ko shiga gate baiyiba ya fara tsayawa bakin qofar gidan ya fara dudduba syringe 'din.

Harya fidda ran ganinsa sai gashi yagani saidaya saka gloves tukuna ya daukesa yakoma asibiti direct office 'din Dr yaje yakai masa.

Kallonsa Dr yayi bayan ya kar6a yasaka cikin wata leda bag yace,

Well yanxu zuwa gobe zamu cire Tom print 'din dake jiki
Su kuma patients 'din zamu sallamesu gobe kafin daga baya zamu San yanda zamuyi mu samu Tom print na duka members 'din gidan.Har aka sallamesu neesah batasamu ganin mamaba saida suka fito domin tafiya gida.

Mamy ce riqeda hannunta sai inna Rabi dake gefenta 'daya.

Khadija kuwa kamar gawa haka aka 'daukota aka saka cikin ambulance sukuma suka shiga motar Jamaal duk da jitake kamar xuciyarta zata qone sbd ganinsa.


Koda suka isa gida ayeesha ta qyalla ido tagansu hankalinta ya tashi takira zeey tasanar da ita.

A 'daki aka kwantarda khadija neesah ma 'dakinta mamy takaita.

Har dare neesah na buqatar ganin mama amma mamar bata fitoba tana gaban khadijarta datake gani kamar gawa.

Tsakar dare bayan mamy tayi bacci ta lalla6a ta sauko gado tareda fitowa ta fa'da 'dakin khadijar.

A zabure mama ta tashi tareda zaro shar6e6iyar wuqa qarqashin filonta.

Ganin neesah tasaki siririyar ajiyar zuciya tareda maida wuqar ta sauko gado tana kallon neesah tace,

Meyasa kika fito idan wani ya ganki aka gano kinwarkefa.


Khadija ta kalla cikin jimamin dama ita mugunta fitsarin fako ce amma kuma ta tausaya mata duk da haka.

I'm really sorry mama akan abinda yasamu khadija but abinda nakeson fa'da miki shine nasan dole akwai dalilin dayasa sukai mata haka idan son samu ne inason nasani.

Shiru mama tayi cikin nazari kafin tace,

I must say my khadija is right this people are very dangerous amma zan nuna musa komai na duniya akwai na gaba akwai na baya.

Mamuh๐Ÿ’‹
๐ŸŒฒ *R H F W F*๐Ÿ„_Don't forget to vote, follow and comments_

*_DACEWA_*
     _(when east meets west)__By_
_Mamuh geee_*_Viawattpad@mamuhgee_**56-57*Washe gari mamy tayi shirin komawa Jamaal yakaita airport ta wuce dama neesah a matse take da mamy takoma sbd sam batason su ayeesha su cutatar mata da ita.

Yana dawowa ya tararda yusuf a gidan..mamaki yayi sosai yana kallonsa sbd koda safe sunyi waya amma bai fada masa zaizoba.

A palon ummi suka zauna suna Yusuf 'din na fira da ummi kafin Jamaal 'din yashiga 'dakin neesah don fito da ita Yusuf ya dubata.

Zaune gaban  mirror hawaye take sosai sbd kewar Ahmed data taso mata.
Half rubber gown ce ajikinta sky blue mara hannu sai gashinta da ummi ta 'daure mata tsakiyar kai.

Kallonta yayi sosai yanajin wata muguwar kewarta na cinsa sbd rabon daya ganta in one 'dinta tun kafin cikin ayeesha ya zube.


Danne 6acin ranta da tsanarsa tafara qoqarin yi tareda miqewa taje bakin window ta tsaya tareda folding hannayenta.

Matsowa yayi ahankali tareda kai hannunsa ya riqo nata.

Ajiyar zuciya ya sake tareda lumshe idanuwansa.

Rintse idanuwanta tayi sbd jitayi kamar wutar lantarkice ta jata.

Sakinta yayi tareda bude wardrobe ya 'dauko dogon hijab yasa mata tareda riqo hannunta suka fito palon.

Zaunar da ita yayi kusada ummi.

Kallonta tsaf Yusuf yayi tareda yimata sannu da jiki batace qalaba saidai idanuwa data bisa dasu.

Ummi ce ta miqe tashiga 'dakin khadija Jamaal kuwa wayarsa datai qara ya 'daga sbd ganin dady ne.

Fakaitar idonta yayi ya karka6a handkerchief 'dinsa ka'dan..

Tari tafara sosai Jamaal yayi saurin katse wayarsa yana kallonta Yusuf yayi saurin miqa masa glass cup cikeda ruwa yace,

Bata tasha zata samu relief.

Kar6a tayi da sauri tasha sbd sosai taji mugun tarin kamar maqoshinta zai fita.

Tana shanye ruwan ta aje cup 'din tareda miqewa ta fa'da bedroom 'dinta.

Sake kiran dady Jamaal yayi Yusuf ya fakaici idanuwansa ya 'dauke cup 'din da neesah tasha ruwa ya jefa cikin briefcase 'dinsa.

'Dakin khadija suka shiga nanma saidaya samu ya fakaici idanuwan kowa ya samu ya 'dauke remote 'din Ac da mama ta kunna ta aje.

Sosai yakeson Tom print 'din khadija amma ba dama can idanuwansa suka hango masa wayarta gaban mirror batareda kowa ya luraba ya zurata aljihunsa suka fito palo ya 'dauki remote 'din palon da ummi tai amfani dashi.

Harzasu fita ya bude murya yace,

Inna Rabi empty cup zanje dashi masaukina zanyi amfani dashine.

Kallon mamaki Jamaal ya aika masa amma baice komaiba suka fito daidai ayeesha zata shiga gurinsu ummin.

Dariya Yusuf yasaki yana cewa,

Amaryar captain kinsamu kinshigo kota kanmu kindaina bi.

Cikin sakin fuska tace,

Wlh aa hankula ne wlh sunqi su kwanta shiyasa,,yaushe kashiga garin namu.

Yau 'din nan nashigo wani aiki amma insha Allah zuwa nextweek nagama aikina nakoma sbd aurena nima dayake gabatowa.

Kallonsa Jamaal yakumayi sbd shi Sam baisan da wata maganar aurensaba.

Wata waya ya fitar ya miqawa ayeesha yace kinga matata dazan aura.

Kar6ar wayar tayi tareda duba hoton tace,

Eh tanada kyau Allah yabada sa'a.

Ameen yace tareda kar6ar wayar suka wuce.

Key 'din motar Jamaal 'daya Yusuf yakar6a har zai shiga saiga zeey tashigo gidan sanyeda dogon hijab
Kallo 'daya Jamaal yayiwa gefen ya 'dauke kai.

Yusuf kuwa kallonta yayi dakyau yacewa Jamaal wannan tana yawan zuwa nan gidan ne?

Yes and why did you ask?

Nothing I just want....kawai bari na tunkareta.

Matsawa yayi da 'dan hanzarinsa ya tareta yana murmushin yace,

Yan mata naganki ne kuma nakasa hkr sbd zuciyata ta kamu yanxu dai ina sauri  rubuta min number ki I will call anjima saimuyi mgna.

Cikin mamakinsa ta kar6i pen 'din dayake bata ta rubuta masa ta wuce.Yana barin gidan direct asibiti ya nufa  a office 'din Dr sulaiman ya fito da komai suka hau aiki akai.


Tashin farko tomprint 'din zeey yayi matching dana jikin syringe 'din.


Shiru sukayi na tsawon lokaci kafin Yusuf yakira Jamaal yace,

Pls Jamaal that lady Dana hadu da ita 'dazu dazan fito yatake a gidan.?

Close friend 'din neesah ce kaga karfa ka dameni da silly questions idan sonta kake kasameta karka dameni.


Kashe wayar yayi qwaqwalwarsa na qara 'daurewa.

Fita Dr sulaiman yayi yabarsa sbd kiran gaggawar da akai masa a emergency Ward.

Wayar khadija ya 'dauko tareda kunnawa sbd yaga last calls nata a ranar da abin yafaru.


Mamartace takirata last,,

Nazari yafara akan dalilin dayasa zeey 'din zatai mata haka...kodai taganta tana aikata wani Abu kokuma tanada abinda batason asani khadijar tasani.


Wayar yashiga yafara duddubawa..

Wani malalacin murmushi yasaki lokacinda yagama ganin videon.

Wani yakuma gani a ranar da cikin ayeesha ya xube.


Zama yayi tareda crossing legs yana yana jinjina kai cikin sauqi yagano komai batareda yasha wuyar daya tsammata ba.


Tattara kayan yayi tareda result 'din yasaka cikin jaka yafito tareda fadawa mota ya nufi  hotel 'din daya sauka barin jakar yayi cikin mota yatafi room 'dinsa.


Zeeey dake bibiyarsa sbd tun fitowarsa hankalinta yakasa kwanciya tabiyosa.

Murmushi tasaki tareda nunawa leloh  motar tace,

Leloh ka tabbatarda jakarcan batabar hotel 'din nan ba shikuma shegen zanji dashi.

Sauka leloh yayi ita kuma taja motar tabar gurin.

Mamuh๐Ÿ’‹
๐ŸŒฒ *R H F W F*๐Ÿ„_Don't forget to vote, follow and comments_*_DACEWA_*
     _(when east meets west)__By_
_Mamuh geee_*_Viawattpad@mamuhgee_**56-57*Washe gari mamy tayi shirin komawa Jamaal yakaita airport ta wuce dama neesah a matse take da mamy takoma sbd sam batason su ayeesha su cutatar mata da ita.

Yana dawowa ya tararda yusuf a gidan..mamaki yayi sosai yana kallonsa sbd koda safe sunyi waya amma bai fada masa zaizoba.

A palon ummi suka zauna suna Yusuf 'din na fira da ummi kafin Jamaal 'din yashiga 'dakin neesah don fito da ita Yusuf ya dubata.

Zaune gaban  mirror hawaye take sosai sbd kewar Ahmed data taso mata.
Half rubber gown ce ajikinta sky blue mara hannu sai gashinta da ummi ta 'daure mata tsakiyar kai.

Kallonta yayi sosai yanajin wata muguwar kewarta na cinsa sbd rabon daya ganta in one 'dinta tun kafin cikin ayeesha ya zube.


Danne 6acin ranta da tsanarsa tafara qoqarin yi tareda miqewa taje bakin window ta tsaya tareda folding hannayenta.

Matsowa yayi ahankali tareda kai hannunsa ya riqo nata.

Ajiyar zuciya ya sake tareda lumshe idanuwansa.

Rintse idanuwanta tayi sbd jitayi kamar wutar lantarkice ta jata.

Sakinta yayi tareda bude wardrobe ya 'dauko dogon hijab yasa mata tareda riqo hannunta suka fito palon.

Zaunar da ita yayi kusada ummi.

Kallonta tsaf Yusuf yayi tareda yimata sannu da jiki batace qalaba saidai idanuwa data bisa dasu.

Ummi ce ta miqe tashiga 'dakin khadija Jamaal kuwa wayarsa datai qara ya 'daga sbd ganin dady ne.

Fakaitar idonta yayi ya karka6a handkerchief 'dinsa ka'dan..

Tari tafara sosai Jamaal yayi saurin katse wayarsa yana kallonta Yusuf yayi saurin miqa masa glass cup cikeda ruwa yace,

Bata tasha zata samu relief.

Kar6a tayi da sauri tasha sbd sosai taji mugun tarin kamar maqoshinta zai fita.

Tana shanye ruwan ta aje cup 'din tareda miqewa ta fa'da bedroom 'dinta.

Sake kiran dady Jamaal yayi Yusuf ya fakaici idanuwansa ya 'dauke cup 'din da neesah tasha ruwa ya jefa cikin briefcase 'dinsa.

'Dakin khadija suka shiga nanma saidaya samu ya fakaici idanuwan kowa ya samu ya 'dauke remote 'din Ac da mama ta kunna ta aje.

Sosai yakeson Tom print 'din khadija amma ba dama can idanuwansa suka hango masa wayarta gaban mirror batareda kowa ya luraba ya zurata aljihunsa suka fito palo ya 'dauki remote 'din palon da ummi tai amfani dashi.

Harzasu fita ya bude murya yace,

Inna Rabi empty cup zanje dashi masaukina zanyi amfani dashine.

Kallon mamaki Jamaal ya aika masa amma baice komaiba suka fito daidai ayeesha zata shiga gurinsu ummin.

Dariya Yusuf yasaki yana cewa,

Amaryar captain kinsamu kinshigo kota kanmu kindaina bi.

Cikin sakin fuska tace,

Wlh aa hankula ne wlh sunqi su kwanta shiyasa,,yaushe kashiga garin namu.

Yau 'din nan nashigo wani aiki amma insha Allah zuwa nextweek nagama aikina nakoma sbd aurena nima dayake gabatowa.

Kallonsa Jamaal yakumayi sbd shi Sam baisan da wata maganar aurensaba.

Wata waya ya fitar ya miqawa ayeesha yace kinga matata dazan aura.

Kar6ar wayar tayi tareda duba hoton tace,

Eh tanada kyau Allah yabada sa'a.

Ameen yace tareda kar6ar wayar suka wuce.

Key 'din motar Jamaal 'daya Yusuf yakar6a har zai shiga saiga zeey tashigo gidan sanyeda dogon hijab
Kallo 'daya Jamaal yayiwa gefen ya 'dauke kai.

Yusuf kuwa kallonta yayi dakyau yacewa Jamaal wannan tana yawan zuwa nan gidan ne?

Yes and why did you ask?

Nothing I just want....kawai bari na tunkareta.

Matsawa yayi da 'dan hanzarinsa ya tareta yana murmushin yace,

Yan mata naganki ne kuma nakasa hkr sbd zuciyata ta kamu yanxu dai ina sauri  rubuta min number ki I will call anjima saimuyi mgna.

Cikin mamakinsa ta kar6i pen 'din dayake bata ta rubuta masa ta wuce.Yana barin gidan direct asibiti ya nufa  a office 'din Dr sulaiman ya fito da komai suka hau aiki akai.


Tashin farko tomprint 'din zeey yayi matching dana jikin syringe 'din.


Shiru sukayi na tsawon lokaci kafin Yusuf yakira Jamaal yace,

Pls Jamaal that lady Dana hadu da ita 'dazu dazan fito yatake a gidan.?

Close friend 'din neesah ce kaga karfa ka dameni da silly questions idan sonta kake kasameta karka dameni.


Kashe wayar yayi qwaqwalwarsa na qara 'daurewa.

Fita Dr sulaiman yayi yabarsa sbd kiran gaggawar da akai masa a emergency Ward.

Wayar khadija ya 'dauko tareda kunnawa sbd yaga last calls nata a ranar da abin yafaru.


Mamartace takirata last,,

Nazari yafara akan dalilin dayasa zeey 'din zatai mata haka...kodai taganta tana aikata wani Abu kokuma tanada abinda batason asani khadijar tasani.


Wayar yashiga yafara duddubawa..

Wani malalacin murmushi yasaki lokacinda yagama ganin videon.

Wani yakuma gani a ranar da cikin ayeesha ya xube.


Zama yayi tareda crossing legs yana yana jinjina kai cikin sauqi yagano komai batareda yasha wuyar daya tsammata ba.


Tattara kayan yayi tareda result 'din yasaka cikin jaka yafito tareda fadawa mota ya nufi  hotel 'din daya sauka barin jakar yayi cikin mota yatafi room 'dinsa.


Zeeey dake bibiyarsa sbd tun fitowarsa hankalinta yakasa kwanciya tabiyosa.

Murmushi tasaki tareda nunawa leloh  motar tace,

Leloh ka tabbatarda jakarcan batabar hotel 'din nan ba shikuma shegen zanji dashi.

Sauka leloh yayi ita kuma taja motar tabar gurin.

Mamuh๐Ÿ’‹
๐ŸŒฒ *R H F W F*๐Ÿ„_Don't forget to vote, follow and comments_


*_DACEWA_*
     _(when east meets west)__By_
_Mamuh geee_*_Viawattpad@mamuhgee_**58-59*Motar leloh ya nufa kai tsaye cikin taku dan kar aganosa.

Daf da zai isa Yusuf yafito daga reception 'din hotel 'din yana waya ya nufi motar ya bu'de tareda fiddo jakar ya rufe motar tareda ya jingina da motar tareda qara 'daga muryarsa yana waya tsawon lokaci kafin yakoma cikin reception ya nufi elevator yashige zuwa fifth floor room 'dinsa.

Lalla6awa leloh yayi yabisa haryaga room 'dinsa kafin yafito tareda kiran zeey yafara koro mata bayanin daya tayar mata da hankali.

Jikin na rawa ta danna kiran ayeesha ta sanar da ita tashin hankalin da suke ciki.

Jikuntane itama ya'dau mugun rawa sbd tasan duk abinda ya 'daga hankalinsa to lallai ba qaramin bala'i bane.
Murya a hargitse tace,

Zeey dole musan abinyi kafin gobe sbd idan jakarnan takai zuwa gobe a hannunsa mungama yawo danni indama ace mun kar da neesar ko mezai faru da sauqi amma kullum yaqi muke Abu yaqi ci yaqi cinyewa wannan masifa.

Cikin quluwa zeey tace,

Kawai Abu 'daya zamuyi daga yanxu duk Wanda yayi gangancin yashiga hanyarmu mu sheqasa lahira ciki har uwar shi Jamaal 'din sbd idanma ta tafi saikinfi samunsa yanda kikeso.

Tsaki ayeeshar taja tace,

Dama ai ita jira nake komai ya lafa sheqaqqiya sunanta,
Kawai dai yanxu zan cewa Jamaal Umma batada lapia sosai zanje na kwana da ita gobe nadawo idan yaso yau da daddare muje da hannuna zan harbe Yusuf sbd na nuna masa babban gangancin daya tafka na wasa dani.


Da maraice ta shirya tazo bedroom  'dinsa fuska duk damuwa da guntayen hawaye ta zauna kusadashi yana tura saqo ta email a laptop.

Bai juyo ba hakama bai daina abinda yakeba a hankali yace,

Uhumm?

Wani takaicine yataso mata na yanda duk wannan yaqin da bala'in datake akansa amma Sam bata gabansa qarin haushima Sam ko kallo wasu lokutan bata ishesaba hardai da cikinta ya zube shikenan komai ya qara tsananta.

Danne takaicinsa tayi murya a sanyaye tace,

My captain Umma ce batada lpia shine nakeson naje for today's night kafin zuwa gobe idan Anty hadeeza tazo daga jalingo saita zauna da ita.

Daka tawa yayi kafin ya 'dago ya kalleta for about 10 minutes kafin ahankali yace,

Eshaaa,,,,eshaa bazaki ita dubota harsaikin kwana acan.

Qyafta idanu tayi hawaye suka gangaro ta marairaice zatayi mgn yayi saurin rufe ido yace,

You can go je ki shirya I will drop you....

No no captain zanje da motana after all yau banason ka fita sbd karka manta 'dazu kace kanka yana ciwo.

Light kiss tabashi a lips kafin ta fice tana ta6e baki.


Direct gidansu zeey tanufa ta tararda matar baban zeey 'din a palo tana fira da baquwa
A 'dage ta gaidasu tareda shigewa bedroom 'din zeey.

A kwance take daga ita sai gajeran wando da vest.

Zama ayeesha tayi tana aje handbag 'dinta tace,

Yau kuma naga waccen mutuniyarki a palo da baquwa ko me suke qullawa.

Tsaki zeey tasaki tana 6ata fuska tace,
Oho musu nidai abinda nasani nazamar mata qadangaren bakin tulu sbd bata haifeniba dan haka bazata mulkeniba
Haka nima ban ajiyetaba ba ruwana da ita matuqar bata shiga gonataba.


Qarfe takwas kiran Yusuf yashigo wayarsa lokacin yana zaune palon ummi yana cin abinci ahankali sbd hankalinsa na kan qofar bedroom 'din neesah dayake ayyana yau a 'dakin zai kwana.


Ahankali ya 'daga wayar tareda cewa,

What now?

Easy man,,,inason na tambayeka wani Abu akan sabuwar budurwata zeey?

Ka kirani ne kawai kamin wannan tambayar ko kuwa sbd ni inada abinyi yanxu dan naga alamar kai bakada.

Dariya yayi sosai har jamaal 'din zai kashe wayarsa yayi saurin cewa,

Sorry captain,,,
Tattaro nutsuwarsa yayi tareda zama serious yace,

Captain there's something very important danakeson fa'da maka but dole in person nakeson fa'da maka ita.

Gyara zama Jamaal yayi yana cewa,

OK gobe zanzo nasameka.

No no dole sai yau sbd am afraid wani Abu zai iya giftawa kafin gobe.

Lumshe idanuwa yayi cikin yanayi na mamaki yace,

Akan menene haka harka damu akan dole saina fito yanxu.

Kai tsaye yace,

Akan Wanda yayi injecting khadija ne...

Cikeda mamaki yace,

Meka sani akan hakan?

Saikazo kawai"""Yusuf yace tareda katse wayarsa.

Miqewa yayi tareda zuwa 'dakin ummi yayi mata saida safe ya fice.

Mama dake tsaye tuni tagamajin wayarsa da Yusuf ta  shiga 'dakin neesah ta tararda ita kwance tana waya da amirah.

Saurin 6oye wayar tayi jin anbu'de qofa amma ganin mama ce saita saki ajiyar zuciya tareda tasowa ta nufi qofa tasa key tana cewa,

Badai jikin khadijar neba?

Juyowa tayi ta fuskanceta tace,

Yusuf yakira Jamaal yanxu yanason fada masa wani Abu akan mgnar khadija.

Nazari tayi kafin tace,

Let's pray kobai samu wani babban bayani akan yanda abin yakeba yasamu koda clue ne kinga munsamu damar bayyana komai koda babu evidence akwai yiyuwar ya yarda.
Wanka yayo yashiryo cikin qananan kaya dark blue ya shiga motar yafito gidan ya nufi hotel 'din.

Baqaramin mamaki yayiba ganin Yusuf 'din cikin nisha'di hankali akwance alhalin shi ya 'daga masa hankali.

Zama yayi tareda aje wayarsa da key 'din motarsa tareda tsuke fuska zaiyi magana Yusuf ya taresa da cewa,

Do you need anything,coffee, water, drink or...

Are kidding me,,,kakirani ne kabani coffee ne ko...

Calm down man.

Ransane yaqara 6aci yace,

Kagafa malam zan tafiyata.

Sorry dama inason sanarda Kaine I was the one investigating khadijas issue kuma nafara aikina tun 'dazu danaje gidan and masha Allah komai yazomin da sauqi but bazan fa'da maka komai yanxuba saida safe insha Allah.

Manyan oily eyes 'dinsa ya watsa masa yace,

Meyasa bazaka fa'damin yanxuba saiwani gobe.

Murmushi yasaki tareda miqewa ya nufi qofar toilet yana cewa,

Zaka fahimci dalilina nayin hakan zuwa goben.

Qaramin tsaki yaja tareda jingina bayansa da kujera tunaninsa na nauyi sbd baisan wa bincikensu zai nuna musuba.

Kasa komawa gida yayi sbd hankalinsa ya kasa kwanciya matse yakeda gari ya waye Yusuf yayi masa bayanin komai.

Kwanciya yayi a doguwar kujerar room 'din yaji sanyin ac yayi masa yawa sbd shi mutum ne mai yawan jin sanyi.

Tashi yayi Yakoma lafiyayyen gadon 'dakin ya kwanta tareda qudundunewa.

Shidai Yusuf yana zaune kan kujera yana aiki cikin laptop 'dinsa.


Qarfe goma sha biyu da mintuna ashirin da biyu suka shigo hotel 'din da farko securities sunso hanasu shiga amma yanayin shigarsu dakuma yanda ayeeshar taringa taunar chewing gum tana karkashe ido yasa sukabarsu sukashiga sbd tunanin kar****ai  ne wani yakirasu gurinsa.

Su uku sukazo dukkaninsu a matse  sai leloh dayake sanye cikin three quarter da armless shirt 'din maza.

Room 'din suka nufa kai tsaye bayan sun baro yaron leloh 'daya a mota batareda ya kashe motarba.

Rufe laptop Yusuf yayi bayan yagama tareda sakata cikin jaka yasaka cikin wardrobe ya rage hasken wutar 'dakin yashiga toilet.


Ahankali leloh ya bu'de qofar 'dakin suka shigo cikin duk da sunyi mamakin ganin qofar 'dakin a bude.

Rufe qofar 'dakin sukayi ayeesha ta zauna tareda crossing legs tana karka'dawa tace,

Leloh tayar mana da 'dan iska.

Matsowa zeey tayi gaban gadon tareda cewa,

No my Swt friend kin manta mutuwa cikin bacci ma tanada azaba after all a dazu damukai haduwar farko ya sace zuciyata dan haka bana buqatar ganin fuskarsa dan zan iya canxa ra'ayin kashesa.,,

Dariya leloh yasaki tareda zama kusada ayeesha yana kunna sigari yayi masa mummunan ja a furzo hayaqin yace,

Zeey Ashe akwai gayen dazai iya shiga wannan zuciyartaki?

Murmushi tasaki tareda kallon inda yake kwance tace,

Poor Yusuf,yashiga zuciyata sosai akaro na farko saidai gangancinsa na bincike akan matsalar khadija yaja masa sbd yanda yayi saurin Ganowar nan cikin lokaci qanqani zai gano mune muka kashe Ahmed,
Muka zubar da cikin  dayakeso,
Mukaita ha'dasa da neesah,
Mukazo saceta qarshema dai zaigano komai kuma kaga qarshenmu yazo batareda muncimma buriba shiyasa gwara tun yanxu daba komai yasaniba mu aikasa kafin mu aiko neesah sauran masu rabon zuwa.

Tsaki ayeesha tasaku tareda miqewa ta fizge bindigar hannun zeey 'din ta saita gadon zata harba Yusuf ya bu'de qofar toilet tsoro yasata harba bindigar ba shiri cikin rashin sa'a sai a qafar zeey leloh yasa hannu ya fixgo ayeeshar da qarfi suka bar 'dakin da mugun gudu ko qofafi basu rufeba direban yaja suka bar gurin a guje.


Tun lokacinda warin hayaqin sigarin leloh ya bugi hancinsa ya farka amma jin abinda suke fada yasa yakasa koda motsi.

Da sauri Yusuf ya qaraso gadon tareda ta6asa yana kiran sunansa.

Ras yaga idanuwansa a bude saidai wani mugun ja dasukai Wanda shima saida faduwar gaba tashigesa dan yasan zuciyar Jamaal ba kyau idan ransa ya 6aci.

Saukowa gadon yayi jikinsa har wani mazari yake ya kalli inda zeey ke kwance tana qoqarin Jan qafa ta miqe cikin tsoro da tashin hankalin Jamaal,,
Tuni jikinta ya 'dau rawa tafara ja da baya.

Kallon fuskarta yayi tareda tariyo maganganunta ya 'daga hannu ya yanka mata wani gigitaccen marin daya sata zubewa qasa hancinta da kunnunta na kawo jini
Ya 'daga qafa da qarfi ya taka qafarda bullet 'din yashigeta tasaki wata masifaffiyar qara tareda sumewa a gurin.

Dafasa Yusuf yayi cikin jimami tareda cewa,

Karka fitarda fushinka da 6acin ranka gaba 'daya yanxu kabari harsai kasan suwaye take taredasu,

Nasanda zasuzo shiyasa nakiraka kaji kagani da kanka sbd ba lallaine ka yardaba da fa'da maka akayi,,

Neesah da khadija sunsan komai gamedasu shiyasa suke qoqarin ganin sun kawar dasu Wanda hakan ya hana neesah nuna warkewarta.

Ya mutsa kansa yayi da qarfi yanajin xuciyarsa na Neman bindigewa babu abinda yakeso yanxu daya wuce ya daddatse zeey amma dole ya barta ta fa'da masa partners 'dinta.


Juyowa yayi tareda janyo zanin gado ya 'daurota aciki yafito batareda tsoron wani ya gansaba ya bude Boot yajefata ya rufe yabar gurin da mugun gudu kamar zai tashi sama.
๐Ÿค”๐Ÿค”๐Ÿค”gskia inaga zanje break 'din sati biyu sbd voters da comments sunyi qasa๐Ÿค”๐Ÿค”๐Ÿค”
Mamuh๐Ÿ’‹
๐ŸŒฒ *R H F W F*๐Ÿ„
_Don't forget to vote, follow and comments_


*_DACEWA_*
     _(when east meets west)__By_
_Mamuh geee_*_Viawattpad@mamuhgee_**60-61*Direct gidansa dake qarshen street 'dinsu ya nufa

A gigice mai gadi ya bu'de masa gate sbd jin horn 'din dayake a masife.

Ko kashe motar beyiba ya fito ya bu'de boot ya jawota kamar kayan wanki ya nufi bq ya bu'de ya jefata batareda ya warware mata zanin gadonba ya rufe qofar ya juya yabar gidan da mugun speed.


Koda ya isa gida qin fitowa yayi daga motar ya kwantarda kansa jikin seat tareda rintse idanuwansa yanajin zuciyarsa na quna har lokacin.

Ya 'dau tsowon minti goma sha biyar kafin ya bu'de idanuwansa da har time 'din basu dawo daidaiba ya bu'de motar yafito.

Part 'dinsu ummi yakalla jikinsa na saki sbd ba abinda yake qaunar gani yanxu sama da neesah.

Kai tsaye can ya nufa batareda la'akari da menene time ba.

A rufe yaji qofar palon ya lumshe ido cikin damuwar kasancewar qofar a rufe.
Part 'dinsa ya nufa yashiga bedroom tareda tu6ewa yayo wanka ya zube a gado zuciyarsa na qara azalzala da tsananin buqatar ganin neesah duk da yasan Abu ne mai wahala ta manta komai dan ya lura da tanada kafiya akan abu.


Da qyar yaga gari ya fara haske bayan sallar asuba ya fito yashiga motarsa ya fice.

Koda ya isa a kwance ya tarar da ita tana nishi hawaye nabin fuskarta data kumbura,,

Qafar ya kalla ta kumbura sosai sbd har lokacin bullet na cikin qafar,,

Cikin tsananin tsoro take kallonsa sbd ganin sa6on 6acin rai a tattared dashi.

Saiti da gurinda bullet 'din ke ciki ya taka da qarfi ta saki wata razananniyar qara tareda qara sumewa daga zaunen.

Ruwan qanqara ya kwara mata a gigice ta farfa'do yakuma taka qafar da qarfi nanma saidata kuma sumewa ya kuma zuba mata ruwan qanqara.


Tana farfadowa ko motsi bata iyayi sbd azaba...

'Daga qafa yayi zai kuma takawa cikin kakkausar murya yace,

Tell me su waye partners 'dinki?

Girgixa kai tayi cikin wasu irin azababbin hawaye sbd ko bakin bazata iya bu'dewa ba sbd galabaituwa.

Wani mahaukacin naushi yakai mata a baki saiga haqoranta biyu sun fa'do tareda jini cikin 'daga murya sosai yace,

Bazaki fa'daba kenan?

A wahalce tace,

Ni ka'dai ce.

Takaici da baqin ciki yasashi rufeta da duka da yana tattaka qafarta.

Saidaya tabbatarda bata motsi ya fice kayansa duk jini ya 'dan ta6asu.

Koda ya isa gida part 'dinsa yaje yayi wanka ya shiryo kafin ya nufo 6angaren.


Ummi da inna Rabi ne kawai a palon suna fira mama kuma na kan dining tana cin abinci.

Gaida ummi yayi kafin inna Rabi dan baima lurada mama ba.

Bedroom 'dinta ya nufa kai tsaye yashiga tareda rufowa.


Bai gantaba amma yaji motsin ruwa a toilet..

Bakin window yaje ya tsaye tareda zuba hannuwansa a aljihu ya lumshe idanuwansa.


'Daureda 'dan qaramin towel ta fito sai wani qaramin a hannunta sbd hadda wankan tsarki tayo na period data gama.

A jiqe dogon gashinta yake haryana 'digar ruwa
Fatarta sai qyalli take sbd lafiyayyen gyara da hutu datake samu.

Sam bata lura dashiba saidatazo gaban mirror ta gansa a tsorace ta juyo cikin rashin sa'a bedroom slippers 'dinta suka janyeta.

Ahhhhhhhh"""ta fa'da da qarfi lokacinda takai qasa kan qafarta ta dama taji azaba.


A 'dan rikice ya juyo yaganta qasa ya matso da sauri tareda riqota cikin lafiyayyar muryarsa mai kashe jiki yace,

Oh god fad'uwa kikayi,,let me help u up.

Banxa tayi dashi tareda fara qoqarin miqewa Cikin azaba,,
Wata qarar tasaki tareda kiran sunan ummi..

Kallonta yayi cikin mamakin yanda hartasan takira ummi afterall ma takaicinsa da haushinsa yake gani a fuskarta bayan yasan ba lafiya ne da ita.....

Unbelievable'''""yafa'da a ransa sbd gano alamar kenan tasamu sauqi...
Hmmnnn well since bata son asani let's do it the way she wants it afterall zanfi jin da'din hakan.


Qura mata oily eyes 'dinsa yayi yana kallon tsakiyar idanuwanta da itama shitake kallo fuska a tamke.,,
Hannu ya 'daga ahankali yakai fuskarta tareda tattara jiqaqqen gashinta ya maida mata baya tareda kashe mata ido 'daya.

Zaro ido tayi cikin takaici takuma zabura zata miqe yayi saurin riqeta tareda matsoda fuskarsa daf da tata tayi saurin rintse idanuwa da qarfi

A kunnenta yakai bakinsa saida ya hura mata iska ahankali yace,

Bazaki iya tashiba so gwara ki nutsu yau nine mai hidimarki.

Turesa tayi da qarfi tareda 'daure fuska tana qara riqe towel "dinta dake qoqarin kwancewa.

Qirjinta da hannuwanta ke kai ya kalla tareda duqawa ba zato taji ya 'daga cak ya zaunar a bakin gado tareda 'daga qafafun ya 'dora mata a gadon.

Wardrobe 'dinta ya bu'de ya 'dauko  mata bra da pant cikin undies 'dinta ya miqo mata kasa 'dagowa ta kar6a tayi sbd takaici wai ace jamaal ke ta6a bra da pant 'dinta bama ganiba


Sake budewa yayi ya 'dauko mata doguwar rigar atampa 'dinkin mara hannu.


Matsowa yayi ya zauna kusa da ita tareda 'daga bra 'din ya nufi qirjinta zai Zare towel 'din akai knocking qofa.

Fixge bra 'din tayi da sauri tareda turawa under pillow tana kallon qofar.

Miqewa yayi jiki amace sbd yayi niyar yamutsa tunanin neesar amma Allah ya qwaceta.

Da ido ta nuna masa qofar tana murmushin mugunta batareda data saniba.

Murmushi shima ya saki tareda ranqwafowa ba zato taji ya fixge towel 'dinta daga sama harsaida no**** 'daya ya bayyana tayi saurin riqewa tareda jifansa da pant 'dinta batareda ta ankaraba daidai nan ayeesha data gaji da bugawa ta bu'de qofar pant 'din ya sauka kan fuskarta..

A razane ta 'dago takalli Jamaal 'din ya fuske tareda ra6ata ya fice.

Gurin neesah ta maida kallonta jikinta har wani mazari yake sbd tsabar baqin ciki da kishi.

Juyawa tayi a fusace tabar gurin dan dama dawowarta kenan tazo duba ubanda yake a 'dakin dataji ummi tace yana ciki ta fake da dubo jikin neesar zata.


Ta6e baki neesah tayi tareda jawo bra 'dinta tafara qoqarin sakawa.


Ko Palo bata tsayaba ta fice takoma sashensu.

Zama yayi kusada ummi ya tattaro nutsuwarsa idanuwansa na canxawa yafara fa'dawasu ummi abinda ke faruwa.

Duk inda hankalin ummi yake tashi yayi sbd tsoro da mamaki,,

Mama kuwa hawayen baqin cikin  halinda suka saka mata 'yarta ne ya gangaro mata ta share tareda miqewa tabar gurin tareda alqawarin gobe komai zaizo qarshe sbd tashiryawa ayeesha trap 'din dazata tonawa kanta asiri da kanta.

Yusuf ne yashigo ummi ta jinjina masa tareda 'dorawa da fa'din,

Yusuf kuje ayi qoqarin miqata gurin hukuma sbd barinta a hannun Jamaal zai iya aikata komai cikin 6acin rai.

Murmushi Yusuf yayi yace,

Karki Damu ummi so muke mu kama sauran saimu miqasu gaba 'daya.

Miqewa sukai suka fice Jamaal na qara kallon qofar bedroom 'dinta qasaqasa.


Da yamma suna zaune a palo suna 'dan ta6a fira ahankali kiran mamy yashigo wayar ummi ta miqe ahankali tabar palon sbd amsawa.

Mama da neesah dake kwance kawai suka rage a palon

Gyara zama mama tayi zatai magana saiga ayeesha tashigo fuskarta a sake sbd so take ta bugi cikinsu taji ina akakai zeey dan ta tabbatarda zuwa lokacin kowa yagamaji.

Zama tayi cikin sakin fuska ta gaida mama kafin ta kalli neesah tace,

Mama naga neesah ba laifi kamar tana samun sauqi ko.

Cikin sakewar fuska mamar tace,

Kedai bari ayeesha Ai wlh neesah taji sauqi khadija ce tarage itama kwanakin nan sauqi yafara zuwa sbd alluran da kullum Dr sulaiman ke zuwa yanayi mata,,,,

Murmushi ta qaqalo tareda cewa,

Mama nikuwa wannan tsinanniyar qawar neesah dazan ganta dasai na kusa hallakata sbd wannan ai bala'i ce.

Bari kedai ayeesha nima haka nakejin kamar na shaqeta sbd abinda taiwa khadija amma Jamaal ya hana sbd wai da'aka tambayeta dalilinta nayin hakan sai cewa tayi soyayyarsace takaita ga aikata hakan hardafa ikirarin saitaga bayan duk wata matar Jamaal,


Ha'de fuska ayeesha tayi tareda qara kallon mama tace,

Wai itada kanta ta fa'di hakan?

Qwarai kuwa muma shiya 'daga mana hankali kada takuma samun nasarar cutatar da wani.,

Yanxu dai tasaka Jamaal yayi alqawarin zai yafe mata yabarta matuqar ta fa'da masa sauran
Sannan kuma abin haushi wai harya fara tausaya mata mudai tsoranmu karyace zai aureta bayan ta shiryu wlh duk wannan shiyafi 'daga hankalinmu.


Tafarfasa zuciyar ayeesha tafara sbd jin wai dama zeey son Jamaal take Ashe shiyasa tafita zaqalqalewa akan komai,
Sotake yanxu tafa'da masa sunana dan yasa arufeni ita kuma ya aureta kenan...
Tabbas zata nunawa zeey tafita zama kunama dan bazata bari takuma ganin wata safiyarba bayan ta yau.


Ta gefen ido mama takalli ayeesha tareda girgiza kai alamar tarkonta ya kama ayeeshar..
Muskutawa tayi taci gaba da cewa,


Wannan zeey mu bala'i ce shigowarta rayuwarmu dan da ace Jamaal baiyiwa ummi alqawarin harbe koma wanene ta fa'daba da wlh ni zan harbeshi da kaina.

Kasa controlling kanta tayi cikin tashin hankali da masifa tace,

Mama shi jamaal 'din ya nuna zai iya aurenta idan tafa'da masa abinda yakeson ji?

Haka ya nuna saidai mu bamuyi na'am da hakanba hasalima dazamu samu ta mutu dasai ummi tafi kowa farin ciki sbd dagake batason Jamaal ya qaro kowa.

Tsaye ta miqe cikin zurfi a tunani tanajin zuciyarta zata iya bugawa matuqar bata 'dora bindiga akan zeey ta watse kantaba.

Kamar daga sama taji mama na cewa,

A gidansa block 27 presidental Jolly street yakaita wat do you think will happen idan tafa'da masa komai?

Batareda ta tsaya sauraron sauran bayaninba tabar palon a bala'e.

Wani mugun murmushi mama tasaki tareda kallon neesah suka saki murmushi atare.Direct gidan yakoma bayan sun rabu da Yusuf.

A kwance take kamar gawa ko numfashi da qyar yake fitar mata sbd azababben halinda take ciki sbd qafarta tuni tafara wani kore koren alamar ru6ewa.

Tsayawa yayi akanta tareda zuba hannayensa a aljihun wandonsa ya kalli shu'aibu mai gadi yamai alama da hannu.

Bokitin ruwan qanqara ya 'daga tareda juye mata kafin ya lafta mata wata mahaukaciyar bulalar dukan jakai.


Ko ihu kasawa tayi sai wani 'dan marayan nishi tasaki.

A 'dage yace,

Are you ready to talk bitch***?

Numfashinta taja daqyar idanuwanta na rufewa
Murya na fita da qyar tace,

*_INNA RABI CE_*Mamuh๐Ÿ’‹
๐ŸŒฒ *R H F W F*๐Ÿ„_Don't forget to vote, follow and comments_


*_DACEWA_*
     _(when east meets west)__By_
_Mamuh geee_*_Viawattpad@mamuhgee_**62-63*Kallon mamaki da takaici ya aika mata
Sbd ganin alamar bata daku bane harta samu damar kawo sunan inna Rabi dayafi kowa sanin baiwar allar bazata iya hakanba.

Qar6ar bulalar yayi daga hannun shu'aibu ya bu'de clips 'din hannun farar longslv shirt 'dinsa tareda  nanna'de hannnun ya saita qafar ya zuba mata 'daya.

Jini da wasu kalar ruwane suka 6alle daga qafar suka fara zubowa.

A wahalce tace,

Wlh ba itaba ce zan fa'da.

Uhummn you're wasting my time.

Ganin tana shawarar fa'dane takaici yasashi miqaqa shu'aibu yace ya rufeta dukan mutuwa.

Ti6is shu'aibu yayi mata saida sukaga ta some bata numfashi suka fice shu'aibu sai sharce gumi yake danshi baiga mace mai shegen taurin raiba kamar wannan.

Har 'dare yana gidan Wanda zuwan ayeesha biyu amma takasa shigowa sbd ganin motarsa a gidan.


Sai dare yabar gidan yakoma gida Wanda yini ayeesha tayi cikin zullumi da tashin hankali dan har fa'dawa idanuwanta sukayi danko ruwa takasa kur6awa bare abinci,,
Tsoronta biyu ne kar zeey ta fa'da masa komai yazo yakamata qarshe maganar mama ta tabbata.


Koda yashigo yaganta Palo sai kaida kawo take cikin tashin hankali..

Qin tsayawa yayi yashigewarsa bedroom ya tu6e ya fa'da toilet yayo wanka.

Yana fitowa yayi shirin bacci harzai kwanta saiya fasa ya 'dauki jallabiya fara qal yasaka tareda 'daukar wayarsa ya nufi 6angarensu ummi.

Cikin sa'a basu rufeba yashiga ba kowa a Palo ya nufi bedroom 'dinta yashige tareda rufo qofar harda saka key.

Kwance take tayi a tsakiyar gadonta mai sanye da bedsheet fari qal ba 'digon komai
Itakuma black nightgown ce ajikinta mara nauyi Wanda rashin nauyinta yasa ana ganin kusan komai na halittarta.

Waya take da amirah kafin bacci yafara 'din fixgarta har baccin yafara nauyi.

Tsayawa yayi akanta tareda sakin wata 6oyayyar ajiyar zuciya.

Cire jallabiyarsa yayi ya kwanta kusada ita tareda 'dora kansa a akan pilon da kanta yake ya qurawa pink lips 'dinta idanu a haka barci ya 'daukesa shima numfashinsu na ha'duwa.

Cikin dare sanyi yayi masa yawa sbd ac 'din 'dakin a qure yake gaba 'daya.


Duqunqunewa yayi yashige jikinta tareda jawo dvet cover ya rufesu.

Baccin nutsuwa dukkaninsu sakayi haryayi lattin tashi sallah batareda yasaniba sbd rabonsa da irin wannan baccin harya manta.

Tashi yayi ya fice yakoma part 'dinsu a can yayi sallarsa tareda komawa kan gadonsa ya kwanta.


Tunda ta tashi takejin qamshin turarensa ajikinta..

Lumshe ido tayi tareda ayyano wani Abu gameda hakan.

Ajiyar zuciya tasaki tareda mirginowa zata sauka tasakejin kamshin duk ya kama gadon da pillow.

Mutuwa jikinta yayi ta sake lumshe ido..
Wayarsa tagani a kan bedside drower.

'Dauka tayi ahankali tareda ta6awa..

_4 missed calls from my eshaah_"""
Abinda tafara gani kenan agaban screen 'din nan take jikinta ya'dau rawa tayi saurin ajewa tareda miqewa ta fa'da toilet zuciyarta na bugawa da sauri.


Hartayi sallah tagama takoma ta kwanta bata kuma kallon gefen da wayar take sbd wani baqin cikin wayar da harma mai wayar dake damunta.


Har 11 tayi bata tashima kuma baccin yaqi zuwar mata tayi tsaki yafi cikin kofi kuma takasa gane taqa maiman abinda ya ta6a ranta sai kawai ta fashe da kuka ahankali tana kiran sunan Ahmed sbd duk dayana nan a raye da bazata shiga wannan damuwarba.

Kuka take sosai sbd sabuwa mutuwar Ahmed 'dinta tadawo mata.


Har kusan yamma bata fitoba kuma bata 'daina kukanba.

Abinci nema inna Rabi data kawo tabata daqyar ta iyashan milkshake shima dan ummi tazo da kanta ta matsa mata ne duk da su farin ciki sukeyi da cewa neesah ta warke.

Mamy ma anbuga ansanar dasu suka nuna farin cikcikinsu bama kamar mamyn dan harta fara shirye shiryen tahowa.

Tuni fuskarta da idanuwanta suka kumbura sukai jajir sbd kuka
Ummi kuwa sai rarrashinta takeyi sbd itama mutuwar Ahmed 'din takuma dawo mata sabuwa.


Lalla6awa ayeesha tayi ta fice daga gidan sbd ganin yau tun safe Jamaal yana bedroom 'dinsa yana aiki a laptop sbd anbuqaci dawowarsa gurin aiki.

Akan idon mama ayeesha ta fita tashigo 'dakin neesah ta tsaya daga bayan ummi tareda 'dagawa neesah kai.


Saukowa neesah tayi daga gadon da sauri tareda 'daukar key ta nufi qofa tana kuka.

Saurin riqota ummi tayi tana cewa,

Ina kuma zaki keda baki da'de da dawowa daidaiba?

Cikin kuka da tashin hankali ta qwace tareda nufar qofa tana cewa,

Gurin zeey zani dan yau saina 'dauki fansar Ahmed 'dina.

A ki'dime ummi tayo gurinta amma tuni ta fice ta fa'da mota da sauri ta fice gidan.

Harda ha'dawa da gudu mama tanufi 6anfarensu Jamaal ta qwanqwasa bedroom 'dinsa sbd ba kowa a Palo.

Siririn tsaki yaja tareda tasowa yana budewa ya tamke fuska ganin mama.

A ru'de tace,

Jamaal neesah ce yanxu Rana dawowa hayyacinta ta zari mukullai ta tafi gurin zeey wai saita 'dau fans...

Bata qarasaba ya juya ya 'dauko key ya fito da hanxari.

Fa'dawa motar mama tayi hakama ummi suka fito a guje ya nufi gidan.Kodata isa a nesa ka'dan tayi parking taqaraso da qafa leloh na gefenta.

Bata wani samu matsalaba da mai gadin sbd yasan ita matar Jamaal ce illadai shima dasun gamo sun fito kashesa zasuyi dan karya fadi itace tazo gidan.

Kar6an key 'din bq tayi suka nufi gurin suka bu'de.

Toshe hancinta tayi tareda yamutsa.

Wani shaqiyin murmushi leloh yasaki tareda kallon zeey yace,

Wannan badan tona mana asiri dakike shirinyi ba Aida ko ahaka muka qyaleki kin horu da azaba.

Bu'de ido zeey tayi daqyar tareda sakin shuumin murmushi tace,

Ayeesha dama nasan zakixo amma badan ki ceceniba saidan ki kasheni sbd karna fa'di sunanku.,
Hmm karki Damu bani zan fa'da sunankuba sbd ayeesha na da'de da gamawa dake.

Ayeesha har abada Jamaal bazai ta6a sonkiba sbd nasan bazan ta6a samun miji irinsaba wannan aikina ne.

Babanki tsohon saurayina ne da yagama lalata rayuwata ya gudu yabarni nikuma na 'dau alqawarin tarwatsa rayuwar iyalinsa shiyasa na bayyana amatsayin qawa gareki,,

You are so unbelievable eshaa,,
Kin 'dauka ni jakace dazan saddaqar da rayuwata a banxa gurin wannan yaqin batareda nasan zanyi achieving komaiba,

Inason Jamaal ya tsaneki tsana mafi muni dahar zai iya rabaki da duniya shiyasa na dage donmu kashe neesah sbd datz the only way dazai miki irin wannan tsanar da nakeso.

Duk wani mugun Abu damuke aikatawa nayi rerecording nasa da niyyar bawa Jamaal idan komai ya kammala sbd ni bandamu da rasa raiinaba matuqar maqiyina zai qasqantu yanda nakeso wannan  shi ake kirada tsantsar qiyayya.

Babanki da ummanki kuwa kina lahira ko prison zakiji saqon sheqawarsu barzahu ta hanyar ciwon aids.

Wata malalaciyar dariya tasaki cikin azaba.

Duk yanda ayeesha taso daurewa kasawa tayi jikinta ya'dau wata muguwar rawa zufa na keto mata ta fixgo bindigar leloh ta saita goshin zeey dake dariya har lokacin tace,

Koda zan fuskanci fushi da qiyayyar Jamaal to kina lahira bazaki samu ganiba...

Ke kuma kina ina lokacin?

Da sauri tajuya tana zaro ido amma ganin neesah ce kawai saita saki dariya tana cewa,

Wow my lucky day,,,yau zan kai karshen matsalata sabuwa da tsohuwa.

Murmushi neesah tasaki tareda qarasa shigowa 'dakin tace,

Matar captain you are so unbelievable,
Ke yanxu kina tunanin kinyi wining and its all over right?

Cikin murmushi itama tace,

Don't fool your self girl sbd kema kinsan after today its over.

Zeey data hango Jamaal, ummi da mama tsaye bakin qofa tasaki murmushi tace,

Yes its all over after today..

Ayeesha kuwa cigaba tayi da fadin,

You see neesah you can't beat me sbd I spend years ina fooling Jamaal ma dayake ganin shi namiji ne bare ke.,

Babban kuskuren dana tafka shine dana Kasa seta bindigar Dana harbi Ahmed daita tasameki straight to your heart,,

I hate you so much neesah kuma kema kinsani.

Nikuwa nasani tunda nagani kin sadaukar da cikinki kinxubar sbd cimma mummunan burinki akaina hargashi I lost my poor Ahmed and you know I can't forgive you for that.

Daria tasaki tareda gyara tsayuwa cikin girgiza kai tace,

Poor Ahmed,,, you know ban ta6a ganin love at first sight ba sai akan Ahmed dake saidai abin takaici da haushi soyayyar bata gaskia bace ta aikin sihiri ce dana qulla da kaina.,,

And maganar ciki karki Damu dan dama kobata hanyarkiba saina xubar dashi sbd ba haihuwa a tsarina.

Hawayen baqin ciki da karyewar zuciya suka gangaro mata nan take taji tana Neman zubewa qasa ta dafa bango hawaye na gangaro mata.

Cikin jin da'di tacigaba da cewa,

The good for nothing 'din harya mutu baisan wace irin soyayyace ke wahalar dashiba harnayi firing last Bullet straight to his h....

Wani gigitaccen mari neesah ta sakar mata sbd bazata iya cigaba da sauraron zancenba sbd sun cutatar mata da Ahmed iyaka.

Zafin marin yasata kifewa hancinta na jini ta 'dago a hasale zuciyarta na quna idonta ya sauka cikin na Jamaal yana tsaye yayi folding hannayensa yana sauraron duk abinda take fa'da ummi da mama na gefensa.

Zabura tayi taredayin baya da qarfi jikinta na wata irin maqyarqyata..

Dariya zeey ta bushe da ita tana cewa,

Finally it all over.....

Bindiga ayeesha ta 'daga zata harbe zeey 'din sbd zancenta na qara gigitata

Zeey tace,

Bani kike buqatar fara harbewaba.

Juya bindigar tayi kan neesah
Jamaal da ummi suka zaburo alokaci 'daya saikawai ta juyo da bindigar gurinsu tareda harbawa daidai saitin qirjin.........
_kuci gaba da hkr Ku bini yanxu muke fa_Mamuh๐Ÿ’‹๐ŸŒฒ *R H F W F*๐Ÿ„_Don't forget to vote, follow and comments_

adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *