Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Saturday, March 28, 2020

FUREN-JUJI COMPLETE HAUSA NOVELS WATTPAD

adsense here
FUREN-JUJI COMPLETE HAUSA NOVELS WATTPAD
COMPILED BY
ESHAAT SMILER HOM OF HAUSA NOVLS DOCUMNTS
WASAPP 08066360176
FOR MORE..



i
FUREN  JUJI   
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯 
                 BY
                 1鈨�
   ZAINAB IDRIS MAKAWA

馃悗HUGUMA GROUP馃悗
Bissimillahi Rahamanin Rahim
  Allah ina rokon ka ka bani ikon gama wanan labarin lafiya da kuma nasara a cikin yin shi,
  Ya Allah zunun da zan kwasa a cikin sa kayafe min
  Ya Allah Alherin da ke cikin sa ka sadamu dashi ni da duk wani misullumi na duniya,,,,
  Ina mai rokon masu karatu da idan lokacin ibada yayi dan girman Allah kada a shagala a dinga aje karatu a aiwatar da duk abin alhari,,,,, nagode,,,,,, taku har kulun,,,,, ZEEE MAKAWA,,,,,,

 Sadaukar wa ga duk yan Family HARZAMI,,,,,,Tare da yan huguma group's


    Churching,  sith Domenic Church ne da kowa yasan babbace church ne, daga cikin manyan churching da muke da su a kasar Nigeria,
   Church ce da akasari turawa ne ke zama father ko pastors din gurin,
  Wanda daga karshe har suke daukan yaran bakaken fata zuwa kasashen su don karo ilimin addinin kirstanci,,,,
   A kasarin mabiya wanan church din yan kabilar IBO,
  Kusan duk wani babban gari nada wanan irin church din inda yan kabilar IBO ke yawan zuwa bauta,
   Wana katon church din da ake taro yai a cikin garin kwantagora da da ke can cikin jahar Niger state,
  Da, alamar buki sukeyi a gurin yau kuma bukin mai girma ne da ganin hakan,,,,,
    Saboda yawan abin hawan da yau ya cika haraban churching, da kuma jama,a mabiya irin wanan churching da suka zo daga wurare daban daban acikin wqnan kasar,,,
   Sai kida kawai, ke tashi kamar kunnuwa za su fashe wa mutum saboda karan, kida,
   Matan church din sunyi anko har kusan kala uku kamar yadda mazan su, su kayi na su kallar anko din don kowa da tashi kalar shigar,
   Wani matashine dan kimanin shekara ashirin da takwas,,  ke tsaye a harabar church din da alamar shima wurin taron ya zo,,,
  Dogo ne saurayin  fari sol dashi, gashin kan shi sai sheke da walkiya sukeyi a cikin hasken rana,
   Sajen fuskan shi yadan kwanta mai kamar shi yayi wa kan sa,
   Kallo guda zakai mai kadau ka ko bafullatan,ce , shi,
   Saboda duk zubin shi na fulani ne, sak
   Tsaye yake, bakin wata bakar mota mai kirar landrove, jeep,,,
  Farar shadda ce, kal  a jikin shi dinkin rigar ce ,mai gajeren hannu, a jikin shi,,
   Rigar an sa wasu manyan aninineya da akai ado dasu, a gaban rigar,
  Hannun shi daure da agogon company Rolex, irin na maza, dagani kasan na gold ne, agogon,,
   Sai wasu zubba da ya jera a yatsun hannun shi,,
  Kafar shi na saye da bakaken cover,shoes, sai sheki sukeyi,
  Sai, yar sarka da yasa a wuyar shi itama dai kallo guda zakai ma sarkan  kagane cewa ta , gold ce,
  Kusan duk wanda ya wuce shi  ta inda yake, tsaye , alokacin yana waya sai mai shi,
  yai mai hannu alamar gai suwa,, ta ban girma ko mutunci,,
  Hakan ne, ya nuna cewa wanan matashin sanane ne sosai a gurin wanan  taron, da akeyi,
   Komawa yayi cikin church din ya zauna saidai kuma baifi minti ko biyar da zama ba wayar shi ta kara kara, kira ya shigo mai again,,,
    Mikewa yayi yana ma shugaban nin su alamar daukan umurni a gurin su,
   Baiwani dauki lokaci ba a waje wanan karon ya koma cikin church din ya zauna inda yatashi, da farko,
   Daidai lokacin anfara yawo da turen ansan donations kamar yadda suka saba idan suna taro,
  Yana jefa nashi envelope din ya mike batare da ko daga ido ba ya fara tafiya a daidai yar siririyar hanyar da aka tanada don bin masu fita da shige ciki,,
    Sukuma church din duk sun mike maza da mata suna wakar yabo ga almasifu,,
 
    Motar shi ya nufa direct, ya bude yai mata key yabar harabar church din
  Daidai lokacin wani tsoho iyamuri yafito daga cikin church din yana  kokarin tsaida dan matashi mutumin da hannu,,
  Wanda shi a lokacin har ya fita daga cikin get din church din ko,,,
   Yana fita yai dan yi ajiyar zuciya, daidai da, lokacin da kuma,wayar shi ta dauki kara ke nan ,
  A hankali yadauko yana diba mai kiranshi again, sai ya ga sunar mahaifin shi a jikin wayar barobaro, (MY DAD,)
  Barin kiran ya yi har ya katse tukun sanan ya kira mahaifin nashi , da kan shi,,,
  Duk a lokacin yana tukin mota,abinshi, a ran shi yasan cewa kiran shi mahaifin shi zaiyi ya dawo,
  Yadaga wayar yana mai fadin Alo,
  A can dayan bangaren aka ansa mai da Alon ba,
   Joseph where are u going now,
  Sai kuma tsohon yaci gaba da magana cikin harshen IBO,
  Yana cewa Baba ina da uzuri ne na fadama cewa yau nake son in koma portacourt,
   No, no no Joseph it can b, possible,,,
   I want us to pray for our successful, at home today night,,
   Yace cikin IBO har na yi inviting din pastor yuhana ko,
   Saida yadan diba agogon hannun shi tukun sannan yai yar tsaki cikin ran shi,
  Saboda baya son wanan addu,an da mahaifin shi ke sa ana masu agida,
  Don inda sabo ya saba ko da hakan,don tun suna yara ake wanan gaiyatar pastor a gidan su,
   Muryan tsohon ya katse mai tunanen shi inda yake cewa Joseph kaji abin da nace ma ko,
  Ya ansa mai da fadin Yes,, Dad,,,
   Yana jin ajiyan zuciyar da tsohon yayi a cikin wayar,
  Daidai lokacin da ya karya kwanan shiga uguwar kwanar kuka, ta inda zai sada shi da green,land, super market
   A nan ya dan tsaya wani shago yace a bashi katin MTN,
  Mai katin ya ce na ,nawa za a dauko mai sai yace na dubu goma, ai sai mai kati yaja yai tsaye,
  Don shi a zaton shi, gatse ake mai,
  Shiko a lokacin hankalin shi na can yana bidan wani takarda da yake son yaba mai shi,
   Yana dago kai yaga ko mai shago ya kawo mai katin sai yagan shi tsaye gaban shi,
   Hannu ya mika don yakarba sai mai shagon katin ya ce mai a nadauka bakar magana kai min, sir
  Cikin mamaki yake kallon mai katin shiko ya koma da sauri don dauko katin,
  Saidai  mai shago ya tarar da katin bai kai na dubu goma ba don haka ya tsaya yi mai bayanin baikai ba ,
  Hannu ya mika yakarbi wanda yasa mu yana mai mika mai kudin da yakirgo dubu goma,
  Cikin mamaki mai shago yace ai na dubu bakwai kawai aka samu maigida
  Cikin hausar shi kamar ba haihuwar IBO ba yace, kabar shi kawai daidai lokacin da yata da motar shi yabar gurin,
  Mai shagon katin yai tsaye sororo ya bi shi da kallon ikon Allah,,,
   It's been a long day without you my friend and,i will tell you all about it when i see you again ,we have come a long way from where we began,oh i will tell all about it when i see you again,  (Wiz_Khalifa feat charlie puth)
   SEE YOU AGAIN,
   Baka jin komai a cikin motar sai wanan wakar ke tashi yana kokarin loading kudin da ya saya awayar shi, yana maming din wakan a hankali,,,
   Phase 2 ya karkata motar shi zuwa,  hanyar tudun wanda don yai saurin kai shi uguwar, phase 2,, din
   Daidai, roundabout din da ya mike zuwa,Kwangwara, da Kan Wuri,
   Ta, window motar ya ga ana mai hannu alamar ya tsaya, dan murmushi yayi dan ganin wanda ke kokarin tsaida shi a lokacin,,,,,
   Wuri ya samu a gefen hanya, ya parker motar shi daidai lokacin da wanda ya tsaida shi ya iso gurin,,
  Hannu suka mikawa junar su alamar gaisuwa a tsakanin su,
   Cikin nuna jin dadi daganin junar su yasa suka rike junar su, suna ta dariya,
   Kafin minti biyu sai ga gurin da suka tsaya yafara cika,
  Duk wanda ya gansu cikin farin ciki yake tsayawa ya basu hannu,
  Mutane da ke wuce wa sai kallon su sukeyi cikin mamaki,
  Komay ke faruwa haka aka tsaya a gefen hanya,,,,,,
 


   ZEEE       MAKAWA,
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
   FUREN JUJI
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
           2鈨�
           BY
ZAINAB IDRIS MAKAWA
馃悗HUGUMA GROUP馃悗

Fatan alheri ga dukkan wayanda suka nuna min kaunar su da kuma kulawa,
 
 
      Sai misalin karfe shidda da wani abu yadawo gida daidai lokacin da abokan shi ke shirin alwalal sallah magrib ,,
   Tun fitar shi yana can phases 2 tare da abokan shi
 Friendship din su ya dauko asaline tun a makarantar primary, daga nan kuma suka jona secondary,
  Tun a lokaci baida wasu abokai sai yaran hausawa
  Duk irin fadar da mahaifin shi da yan uwan shi ke yi mai bai sa ya daina bin diyan hausawa ba,
Kamar yadda akasan diyan IBO da rashin son dan bahaushe shi nashi halin na daban ne,
  Don har abincin su yake ci ,idan yaje gidajen su, ziyara lokacin yana karami,
  Bayan rasuwar mahaifiyar shi baban shi yaga cewa duk akidar shi kusan na hausawa ne yasa shi dauke shi zuwa kasan su don ya karasa karatun shi a can,
   Yana gamawa sai kuma akatura shi, kasar Malaysia yin karatu can,
   Acan Allah ya hada shi da dan wani millioner, dan yaren su na IBO
  Amma shi bai,damu da karatun da sukaje yi ba,
  Sai Allah yasa shi da ya maida hankali yana hadawa har da na Emzon yayi mai su test da sauran aiyuka,
  Exam ne kawai, Emzon kezama yayi a haka har Allah ya taimake shi suka kare karatun su,
  Bayan dawo wan su karatune Emzon ya jona Joseph, a business din harkan man petrol
   Daga haka Allah ya taimake shi ya cigaba tun suna yi da kudin Emzon har suka daina hada kudi a tsakanin su,,
    Wasa,wasa Joseph ya fara na shi harkan sai gashi ya canza wa uban shi sana,a daga saida manja, yakoma harkan petroleum, shima,,,,,,

    A kofan gidan su ya iske baban shi zaune a saman wani benci, da wasu yan dattijawa kamar shi
   Kwalaben giya ne suka tara birjik agaban su, sai shewa suke yi suna ta hayaniyar hiran irin bidirin dazun da akayi,,,
   Yadan dade zaune cikin motar shi kafin ya fito ya fitowa sai yai kokarin bin ta kofar baya don ya shige cikin gida,
   Muryan Mr Emanuel yaji cikin yar buguwa yana kiran shi yazo su gaisa da abokan shi,,
   Bsdon yaso ba ya karaso har inda suke zaune,
 Kwalban giya yake kokarin mika ma dan nashi yana wani irin dariya sama sama,
  Kai kawai Joseph ya kada mai alamar a,a ya taka tabaya yadan juya zuwa cikin gida,
  Yana shiga wanka ya wuce yi direct bayan fitone ya iske wayar shi na ringing,
   KB aka rubuta barobaro a cikin harshen hausa yace KB ya,ya dai,?
   KB ya ce mai yaga jibrin din da yake bida yadawo gari shiyasa ya kira shi don yafada, mai
   Yace ka gane ne KB yanzu kabani a wa biyu pls, zan zo in samay ka muje gidan su,
   Eneka sister shi ce tafado Dakin  tana cewa brother muna jiran ka a,palour pa,
   Saida yadan kara kamar minti goma yafito cikin wasu yan kananin kaya,
  Yasamay duk a rusunne pastor yana tsaye sai addu,a yake zabgawa suko suna ta fadin Amen, Amen,
   Bin sahun su yayi ya jona su a haka akai ta masu wana addu,an har zuwa wani lokaci,
   Baban shi dama a buge yake tatil da giya tun a nan ya tuntsire ya fara nasari,
  Joseph ya ciro kudi tare da dafa ma pastor baya har zuwa gurin motar shi, ya mika mai kudin yana nuna godiyan su da wanan ziyarar da pastorn yai masu,,,
   Daga nan baikoma ciki ba, ya wuce zuwa inda  KB, ke jiran shi su tafi,
   Gidan su jibrin Bala suka tafi cikin daren nan,
  Jibrin na cikin gida akace wai ana mai sallama,
   Bai wani bata lokaci ba yafito , yayi mamaki kwarai ganin Joseph yasa shi yin wani dan ihu, har saida yajawo hakalin mutane,masu wucewa, gare su,
   Yayi farin cik kwarai da,ganin Joseph yace Yusuf Joseph ke nan duk sai suka dariya a lokaci guda saboda, tuna wa da wani zamanin da yawuce a baya,
   Inda Joseph ke cewa shima sunan shi Yusuf Joseph, ne, kama yadda Kabiru lawal Jibrin Bala,sai Musa Aliyu,
   Shima Joseph sai ya cire Joseph Emanuel ,,
   Yace ya koma Yusuf Joseph,
  Dariya yayi yadankai wa jibrin din dan duka ga kafadar shi cikin dariya,
  Suka kara lalewa, da junar su, nan fahira ya barke a tsakanin su na yau she rabo,
   Sun dauki wani dan lokaci sanan sukabar uguwar yamman inda gidan su jibrin bala din yake,,
  Kafin su rabu Joseph ya debo kudi masu yawa ya mika wa jibrin din yana mai bashi hakkuri,
  Kan cewa bai san cewa zai kwana ba don bukin yazo na nada sabbin shugaban nin church din su da akayi, kuma duk ya kashe kudin shi ga jama,a
   Tun da ya aje KB a uguwar tukura, yasa kai zuwa gida ziciyar shi fam da tunanen halin yadda ya ga abokan nashi ciki,
   Duk da goma na dare ya wuce har da rabi hakan bai hana shi cin ma yan uwan shi zaune suna jiran shi ba,
   Ya bude falon kusan lokaci guda bakin su ke cewa brother welcome,
  Ya ansa masu da ce how you na dey,?
   Saida yadan shiga daga ciki tukun sannan yafito cikin wasu yan kananin kayan barci,
   Sai a lokacin ya tuna cewa bai co wani abinci ba don haka inda suke cin abinci ya wuce sakwara da miyar ego yaji egushi da naman shano,
   Ya wanke hannuwar shi ya fara ci, sai da ya gama  cin abincin sanan ya isa, inda yan uwan shi suke zaune yake tambayar su inda baban su yake,
   Da hannu suka nuna mai hanyar kofar dakin shi,
  Anan suka fara mai korafi kowa da abinda yake so amai da ga cikin su,,,
    Wa yanda zaiba kudi yaba su, wa yanda kuma zai, sayo wa abu yai masu alkawari,
 
    Tunda safe yai asubanci yabar gari yadauki hanyar lagos, saidai zuciyar shi fam yake da tunanen yadda ya yaga abokan shi suka koma cikin dan lokaci guda,,,
   Bayan tafiyan Joseph abokan shi suka dinga rumors a gari cewa Joseph yazo wasu su ce yadawo,
  Kafin wani lokaci sai maganganu ya karade gari wasu nacewa aiki yasamu mai tsoka,
  Wasu nace harkan business din zamani yakeyi watau, dai smuggling, wasu kuma suka ce ai dan shan jini ne,
  Inba haka ba ya zaiyi kudi haka cikin dan lokaci guda, kamar yafi su bida,
 
    KB ne a saman babur din shi, yana tafiya zuwa gidan wani dan uwan su don ya kai sako,
  Hadewa sukayi da jibrin a daidai junction, anan suka dan tsaya don su gaisa,
  A haka suka sako hiran Joseph cikin zancen su, inda suke yaba alherin da   yazo yai masu,
  KB yace wai ko kasan cewa mutane da daukar wa kan su wahala da nauyi wai har sun fassara dukiyar Joseph da wata, ma,ana,,,
  Cikin mamaki jibrin yace kai mutumina bari zancen nan pa,
  Yace wallahi man ni ma su jamil suka tare ni hanya suke ce min wai ko da gaske ne zancen da sukaji game da Joseph ance wai yayi fitacen kudi,
    Jibrin ya kada kanshi yace kai mutum mutum abin tsoro ne wlh,
   Yanzun nan har sun fassara wanan guy din dawatq ma,ana ko,
   Allah ya kyauta kawai suka iya cewa suka dan kara taba hira sukabar gurin cikin alkawarin kara haduwa nan gaba,
    Daidai wanan lokacin Joseph yana zaune a cikin kayattacen falon shi da garin lagos zaune yake cikin shigar kananin kaya,
   Kallo guda zakai mai ko ba,a fada maka ba zakasan cewa kaya ne, masu tsada a jikin shi,
    TV yake kallo a zahiri saidai gaskiya ba wai abinda ke faruwa a cikin TV yake kallo ba,
  Don dai zuciyar shi na can tana tunanen abokan shi na kurciya da yagani cikin halin taimako,,
   A hankali ya furzar da yar iska daga bakin shi yana dan bugun hannun shi a hankali,
   Jinkarar bude kofar da akayi a lokacin ya dan waiga don ganin wanda ya shigo cikin falon a lokacin,
   Inok ne ya shigo wani abokin shi ne da suke yawan mu,amula indan yana Lagos da shi,
    Inok yazo inda yake suka yar lalai hannu cikin nuna kulawa,
  Inok yana kaiwa zaune yace wa Joseph kai aboki nai muna sabon kamu fa,
  Duk da nasan cewa kaiba dan wanan harkan bane , nasan cewa wanan karon zaka kamu sosai indan har kaga cik din nan,,,
   Kwantar da bayan shi yayi a saman kujera yadan waigo inda Inok ke zaune yana murmushi ya ce nagode da gudun mawarka amma kasani cewa ni wanan harkan bata a gabana yanzun haka,
   Indadai wani business ne kasamo muna danafi kowa farin ciki da kai yau,
   Baki bude Inok ke kallon Joseph yana mamakin irin halinshi na ko in kula ga mata,
  Gashi dai yaro matashi mai jini ajika aman ba ruwan shi da harkan mata,,
   Sai cewa yayi wai kai joe wani irin guy ne kodai matane baka so sai maza,
  Cikin mamaki Joseph ya kalleshi alamar mamaki karara a fuskan shi yace
  God forbid bad things,,,,,
Me, Joseph doing such bad habit in my life never,,,,
  Daga haka yamike tsaye ya haye sama abinshi ya ma kulle kofar dakin shi yabar Inok zaune a falon
      Ido  kawai Inok ya bishi dashi har zuwa lokacin da Joseph yabugo kofar dakin da karfi
   Inok ya mike tsaye yana mai watsar da hannuwar shi alamar haka take gare shi,
   Sai da Joseph ya tabbatar da cewa  Inok yabar gidan sannan ya fito ya dauki makullin motar shi yabar gidan cikin kunar rai,
    Direct inda suke shan whisky ya nufa can ya zauna yadan sha kadan sanan yabar gurin zuwa gidan wani kawun shi da yake son ziyara da dadewa,
   A can gidan yakai dare tare da uncle Sam, inda suka dan taba hira gamay da halin da family su ke ciki,
  Kafin atafi saida yaiwa babban dan uncle sam , alkawrin samun aiki,
   Sai bayan yadawo kamar da kwana uku ne yakira nobar wayan jibrin da yabashi ranan da suka hadu ,,,
  Sun kai wani dan lokaci suna hira cikin mutunci inda suke ta hiran classmates din su,, da kuma irin gidajen da suke zuwa idan antashi makaranta,
     Sunyi dariya sosai idan sun tuna da wani abu da sukayi ada suna yara,,,,,,,
  A haka sukyi ban kwana da junar su har zuwa wani lokaci,,,,,,,,,
   Kwance yake yana barci a saman tangamay may gadon shi,
   Karar wayace ta katse mai barcin dayakeyi , a hankali ya diba kowaye yakirashi cikin dare haja,
  Monday yagani rubuce, acikin muryan barci ya dauki wayan ya kara a nunen shi yace,
  Hello, a bangaren Monday ya ansa da cewa hello sir,
  Anan Monday ke sheda mai cewa wai motar man su guda da aki loading zuwa westnorth ta samu matsala a hanya har mai ya tsiyaye,
 Awani dan kauye kuma sunyi iya kokarin su su tasarya abin ya gagara shiyasa ya bgo mai wayar,,
   Mikewa yayi zaune daga kwanciyar da yayi batare da yaba monday ansa ba ya kashe, wayar,shi,
  Wurin window dakin shi yanufa tsaye yake yana kallon hasken fitilun da yadan haska duhun dare, kamar yadda taurari suke haska sama,
  A fill ya furta Monday, I will delling with u, soon, gurin fridge ya wuce yadauko ruban ruwan sanyi ya kwakwade shi dukka, lokaci guda ya cillar da robon kasa,,,,
   A ranan barci rabi da rabi yayi don zuciyar shi na kuna ga irin rainin hankalin dasu Monday ke yi mashi,
  Don kashi na uku kenan suna mai wanan hasarar da kuma wawaso,
   Tunda safe ya shirya tafiya zuwa arewa batare da sanin kowa ba,
   Sai da yai nisa yai wa KB waya, yana msi tambayar shi idan har bai komai yana son ya raka shi wani uguwa,
   A suleja suka hadu, suka kama hanyar zuwa inda minday yace sun samu matsala,
  Har zuwa adamawa babu tanker motar dasuka hadu da ita a saman hanya, da zasu dawo kuma suka kara bi ta wani sabon hanya da akai masu kwatance
  Still a nan ma basuga komai ba, sai mota guda suka fani kuma ba ta company su bace ,
  Kiran monday yayi yace ya fada mai daidai inda motar tasamu matsala gashi a cikin North,
   Cikin rudani Monday yace what, You mean you are in North now yace mai of,course,
 Jin yadda monday ke in,inniya yasa shi kashe wayar shi,,,,,,,,,


ZEEEEE MAKAWA,,,,,,,,,,,,,,,
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
      FUREN JUJ
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
           3鈨�
            BY
ZAINAB IDRIS MAKAWA
馃悗HUGUMA GROUP馃悗

  Assalamu Alaikum yan uwa dan Allah kuyi hakuri don ina sane da sunan da yakamata in sa wa , wanan novel din sai dai a gaskiya ina ganin kamar akwai wace ta riga  tayi novel da wanan sunan, ( FUREN KAN JUJI)
  Hakan yasa na can za wa nawa suna namaida shi FUREN JUJI  dafatan zakuyi maneji dashi hakana,,, nagode,,,,,,,,

    Sai musalin shadayan dare suka isa cikin garin kwantagora,
   Gidan su KB ya wuce direct don ya sauke shi, tare da tsarabar da sukayo ma yan gidan su KB din,
  Tsarabar doya ce da manja,don saida buth ya cika fam,
  Acikin daren ya wuce zuwa gidan su dake can uguwar sabon gari,
   Duk da dare yayi amma yasamu yan gidan su sun dawo daga church suna kokarin cin abinci,
  Cikin murna da farin ciki suke tariyan shi, shiko ya na dan buga masu kafada ahankali,
   Inda mahaifin shi yake zaune saman dogon kujerar dake falon gidan nasu da gashi sai yar singilati da gajeren wando,
  Sai abin fitar da ke a hannunshi yanadan fifitawa a hankali,
  Daidai satin kafan uban yadan duka inda uban yadan dafa mai kai ya na cewa you are welcome, ba,,,,
   Joseph Why d, you like to travel in d night ?
  Sai kuma yaci gaba da fadin cikin har shen IBO,
   Dan Allah ka daina tafiyan dare saboda hanya da bai da kyau so sai,
   Murmushi kawai Joseph yayi yana cewa ba abin da zai faru by god grace,,,
   Kayan shi yasa aka shogo dasu inda uban ya kalli kayan yace
  Dat means u are going to stay long, ba,,,
   Yace cikin IBO yes dad akwai abinda zamuyi ni da abokaina a nan garin,
   wani irin ihu yayi kamar yadda IBO kanyi idan sunji abinda ya taba masu zuciya, yace hyyy Cineke God Woooo,
  Joseph Why ,u no dey, hear word,
  Nafada ma karabu da yaran hausan nan but still kaki,
   Kayi hankali kada su jefa ka a cikin wahala watara na,
  Kokarin shiga ciki yakeyi alokacin yace, nothing will happen Dad,
    Daga haka yai shigewar shi ciki ruwa ya watsawa jikin shi, sanan yafito ,
  Saman  kujerar dake falon ya, zauna gurin zaman mutum daya,
  Duk da agajiye yake sai kuma yunwar da yake ji, tuwon teba da miyar egusi, aka aje mai a gaban shi,,,,,,,,,

     Sai musalin shadayan rana yafito cikin shigar suit farare sol sai yar kwalar shirt din cikine kawai pink colour,
    Yar jakar da yashigo da ita ya bude yadauko rapan yan dari bibiyu dana dubu guda guda yasa a cikin aljihun shi,
   Wayan shi ya dauka yana latsa nobar KB yace
  Hello KB kana gida ne yace mai eh ai na kira wayar ka yana akashe,
   Yace ko zan samu kunu da kosai a gidan ku pls,
  Saida KB yai yar dariya sannan yace mai baran diba ko akwai, shi, a ciki don na shanye nawako,
   Daga haka suka kashe wayar su, inda KB yashiga ciki gurin mahaifiyar shi yana tambayar ta ko akwai kunu,
   Cikin mamaki umma ke tambayar Kabiru may zaiyi da kuna bayan wanda akasa mai,
  Yace mata Joseph ne ya bugo min waya yana son kunu da kosai,
   Ikon Allah tace shi,wanan yaron har yanzu yana cin irin abincin mu,
   Ba bata lokaci ummah ta hasa wutar dama kunu inda taba kabirun kudi yaje ko za,a samu kosai,
   Saidai sunyi kicibis da Joseph din a kofar gida yana Parker motar shi,
   Tare sukaje gurin sayen kosai ba,a samu ba don haka suka dawo gida,
   Ummah tasan halin Joseph tun suna yara, kuli,kulin suga ta aje mai tare da sugari ,
  Bakaramin murna yayi ba don yace rabon shi da kuli,kuli tun a wancan lokacin,
   Abin yaba ummah mamaki gani andawo mata da jug bakomai dik an shaye, kunun,
   Koda ta bude kwanon kulikuli sai kudi tagani aciki yan dubu dubu har guda goma,
  Cikin sauri ta,ce amayar mai da kudin shi, badon yabata wani abu ba tai mai shi,
  Koda yaron yaje saiga Joseph ya shigo rike da kudin a hannun shi,
   Salama yayi kamar musulumi har ummah ta amsa mai sai da ta daga kai sai taga ashe Joseph, ne,
  Tai saurin yin astangafullah a cikin zuciyar, ta, nan da na ta hada fuskan ta, ta tare shi da cewa haba Yusif don nadama ma kunu zaka bani kudi saboda may zakai mun haka,
   Saida yadan sha fa kan shi tukun sannan yqi yar murmushi
  Yace haba Ummah aiko baki bani kunu ba zan baki wanan kudin,
  Nabakine don neman albarka a wurin ku ba wai don abinda kin min ba,,,,
   Shiru Ummah tayi saboda maganar ta kashe ma ta jiki so sai,
   Sai bude baki tayi tana mai cewa Allah yai ma albarka Yusuf Allah ya karkato ka kagane hanyar gaskiya,
  Murmushi kawai yayi batare da yace mata komai ba,
  Hannu yasa a aljihu ya ciro yan dari bibiyu ya ba sauran mutanen gidan,
   Har zai fita saiga baban su kabiru ya shigo, gidan da alamar kasuwa yafito don kayan cefane ya sayo a cikin leda,,,
  Shima sun gaisa yabashi nashi Alherin, daga nan suka fita,
   A wanan ranan sun sha yawo da KB don duk gida jen da yake zuwa lokacin yana karami saida KB ya kai shi yai masu alheri,
  A karshe suka je gidan wata kawar maman shi da ta mutu,
  Matar a,na ce da ita salama, irin matan nan ne masu sana,ar Manja a cikin gida
   Hakan yasa tasaba da maman su Joseph din, sosai har yakai zata ita daukan man ja ko da jarka nawa take so,
  Sai sabo mai karfi ya shiga tsakanin su sosai,
  Har zuwa lokacin da maman su Joseph tasamu accident a hanyar ta na dawo wa daga kasar su bukin chrismatic,
   Har bayan rasuwan maman sukan je wurin Salama mai manja,
  Saida yabar kasar ne wanan alakar ta mutu tsakanin Salme da su,
  Yau kwatsam saiga shi yace KB ya raka shi gurinta,
  A bayan Neper gidan Salame yake,
  Gidan yana nan kusan yadda yasan shi bai wani can za ba,
  Sunyi sallama akace masu wasuke nema sai KB yace ace gurin salama suka zo,
  Mamaki salama tayi don jin ance wasu samari biyu ne da wata katuwar mota,
  Don ita a iya saninta bata da wani mai irin wanan motar,
  Balle yazo gurinta, tadauko tsohon hijab dinta ta saka akan ta cikin dan sarsarfa ta isa kofar gidan,
  Salama nan kamar yadda yasan ta saidai tadan kara manyata sosai fiye da ,dai,
  Yana mai, murmushi lokacin da ya hangota ita ko ,sai kallon mamaki take masu don har KB din bata gane ba,
   Tana isowa inda suke duk suka dan duka suna mata ina wuni, cikin ladabi,
  Ta, amsa masu tana cewa daga ina fa samari, kodai wani kuke bida, ne,
  Dariya suka dan yi KB ne yace mama Salama baki gane mu bane har da ni,
  Tadan kada kai tace gaskiya kan ban gane kuba,
  Cikin hausar shi da ke nuna cewa ba pure bace sosai yace,
  Mama kin manta da Dan ki yaron mama Ebele, Yusuf Joseph,,,
  Cikin mamaki ta kama bakin ta tana cewa ,a,a,a dan gidan mama Ebele mai man ja kai ne,
  Allah sarki ina ka shigr haka duk wanan dadewan haka,
  Nazata ai munyi bye da kai kenan kabar wanan garin
  Don nasha tambaya ana ce min kana kasar waje, kaje karo ilimi, can,,,
  Tace barin samo maku abin zama ko, har suna hada baki gurin cewa a,a barshi kawai mama,
  To barin kawo maku ruwan sha ko shimadai sukace tabar shi ,
   Sunzo kawai ne su gaishe ta,
  Sai takama sa masu albarka tana godiya ga karamcin da sukai mata na tunawa da ita bayan wani loakaci,
   Kudi ya mikawa KB yace yabata, amma tayi hakkuri zai dawo badadewa ba ,,,
   Saida kudin yabata tsoro don a gsskiya ta dade rabontq da kudi masu yawa hakan ga,
  Taitayi mai addu,a tana sa mai albarka da fatan gamawa da duniya lafiya,
  Nan yaga wasu yan tsofi maza guda biyu saman wani tabarma ya basu, dubu guda guda,
  Har ya bace sunayi mai addu,a da fatan alheri suna kuma tambayar kowaye,
  Salama ta fada madu cewa dan waje Ema mai manjane tsohuwar kasuwa,
  Tsohon guda yace Allahu akabar ashe FUREN KAN JUJI  ne shi, gashi yaron kirki amma ba jinsin kwarai,.
  Dan gidan Ema kan ai babu batun musulunta gare shi sam,
  Gudun tsohon mai dan magana da sauri sauri yace kasan abin Allah yawai gare, ai,
  In har mutum bai mutuba ba,a gama halittasa ba ai,,,,,,
  Su kace wanan gaskiyane,
 Allah ya taro shi ya gane hanyar gaskiya,,,,,,,
   Town holl akayi taron na matasa, tsofin daliban SANI BELLO,nursery _ primary &  Secondary school,,,
  Inda taron yabada ma,ana sosai ga cigaban da matasa keson kasar su ta samu nan gaba,,,
   Bayan wanan taron ne akai ta hotuna tare da exchange din nobar waya a tsakani,
   Koda suka bar gurin taron har duhu yafara don haka su KB da sauran friends suka nufi massallaci, daidai lokacin da suke alwala, ne shi kuma,
  Motar shi ya shiga yatayar duk kusan wanda ke gurin sai da yatau saya mai azuciya ta kasan cewar Joseph Christian,
  Gadai mutun har mutum amma babu alkibilar kwarai a rayuwa,
  Shiko yana barin gurin  Church ya nufa don ya samu evening preys,,
   Mr Emanuel yayi farin cikin ganin motar Joseph a harabar Church din a wanan lokacin da bai tsamani ganin dan nashi ba,
  Sunkai kusan goma nadare sanan suka dawo gida, inda nan suka zube a harabar gidan aka kama yan shaye shaye, su nan,,,
   Har safe Joseph na abuge don ba karamin giya baban shi ya dirka mai ba daren jiya,
  Don kawai jin dadin kasan cewar su tare cikin wanan lokacin,,,,,
  Sanmako su KB sukayi zuwa gidan su Joseph saboda  sunyi alkawarin yin sanmako zuwa wani kauye can guraren daki takwas,,,,
    A irin yanayin da suka samay shi yasa jikin su yan sanyi
  Don sam basu zaci cewa yana sha ba, don basu san shi da hakan ba,
   Tafiyar tasu dole suka fasa suka barshi nan ya zuba shirmay shi suka tafi abinsu,,
   Sai bayan karfe biyu ya farka a lokacin ya walwake sarai, wanka yashiga,
  Yana fitowa ya zauna cin abinci , saida ya koshi saboda irin yanayin da yake jin cikin shi kamar duk an kwakware mai kayan ciki,,,,
 Sai bayan ya koshi ne, ya tuna da zancen tafiyan su, cikin wani irin zabura yace, Jesus, Christ,,,
  Saida kowa ya kallo shi don jin abin da ya ambata,,,
Wayan shi ya lalaba cikin sauri,ya diba yaga ko da , KB yakirashi zancen tafitan su,
  Ga帽in babu called yasa shi saurin mikewa nan yabar abincin da yafara ci yanufi hanyar fita da sauri da dan makullin motar shi a hannu,
   A,majalusar su ya samay su sun cika kamar kullun,
   Can nesa kadan ya aje motar shi yafito ya kulle ko ina
   Hannu ya mika masu don su gaisa da kowa , amma fafir Jibrin yaki mika mai,
  Yunus wani bayerabe da ke cikin su yace wa jibrin ana baka hannu fa,,
  Jibrin yace ai na gani bazan karba bane kawai, duk wurin saida kowa yai mamakin jin kalaman jibrin din,
  Shi kanshi Joseph din abin yadamay shi amna sai kawai yabasar da zan cen yai yar murmushi kawai,
  Azuciyar shi yace indan kasan mutum to kada katambayi halinshi koda bayan shekara nawa ne,halin na nan,
   Don haka yasan akwai abinda yai wa jibrin ke nan, amma saidai shi a iya sanin sa bai mai komai ba,
  Saida , karfe shidda yayi jibri yace kai joe muje ka kaini gida,
  Babu musu joe din kamar yadda suke kiran shi idan sun so, shi ne guy name din shi,,,
   Tare da KB suka fita su uku, sundan fara tafiya ke nan Jibrin yace
  Kai joe samu wuri ka parker zamuyi magana ne,
  Ba musu ya parker motar shi inda Jibrin din ya fara magana cikin fushi kamar fada,
  Joseph yaushe ka fara shan giya, don dai iya sani na dakai baka irin wanan dabi,ar sam,
  Duk da ku a gare ku ba abin kunya bane, to kasani cewa mu kan agurin mu wani babban al,amarine,
  Muddin gari akasan kana wanan dabiar gaskiya dole muma mu rabu dakai don gudun zargi a gare mu,
  Saboda jama,a zasu iya fassaramu dakai duk abu guda mukeyi,
 Kamar yadda kasan mutanen ka na kyamar zaman mu dakai muma hakana namu mutanen suna ganin mu da rashin sanin ciwon kai,
  Abune kawai idan Allah ya hada, babu mai iya hanawa,
  Tunda Jibrin yafara magana Joseph yana rike da sitiyarin motar shi amma gaskiya bai tsamani maganar da Jibrin ke ma fushi ba ke nan,
  KB ne yakarbe da cewa duk addinan mu ba wanda ya yarda da shangiya balle har mu dauke shi kamar abin ado,
   Jibrin yace wai ma yaushe ka fara shan giya ne man
  Hannu yadaga masu yace is over pls,
  Yai ma motar shi giya suka bar gurin batare da wani ya kara magana ba,
   Saidai gabadayan su , sun sancewa shikenan kamar yadda yace is over din yadaina kenan har abada,,,,, 
 




   ZEEEE. MAKAWA,,,,,,,,,
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
     FUREN JUJI
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
             4鈨�
             BY
ZAINAB IDRIS MAKAWA

馃悗HUGUMA GROUP馃悗

 Mama Farida & Maman Walid
Kuna raina ko yaushe fatan alheri gare ko kamar yadda kuke min akullun,,,,
   

    Maryam , maryam, wai may kikeyi a ciki ne haka, ?
  Ki diba time ki gani yanzu kusan karfe biyar ake bida fa,
  Wallahi anty Assalam ne yaki tsaya in shafa mashi mai waishi saidai ya shafa da kan shi,
  Anty Dije wace ke kitchen tana kokari dora sanwar marance ,
  Itace ta fado dakin a hasale tana kokarin bugun Assalam din wanda ke gefe guda tsaye shi adole bai son anty ta shafa mai manshafi,
  Cikin sauri Maryam ta tare, da hannun ta inda anty tasamu hannun maryam din
  Maryam na gane cewa har dake cikin shagwaba Assalam wallahi,
  Aiku da malam ne idan har kun tafi kun iske an tare get,
   A gagauce Maryam ta shirya yaran cikin kayan islamiyar su, ta dauko yar jakarta wace yan mata kewa lakani da wankar gefe, taraya a gefen ta,,,,,
     Cikin sauri ta riko hannu Issalam wace ke tsaye tun dazu cikin shirinta tana jiran su tafi,
    Murya ta daga daga inda take tana fafin Anty mun tafi sai mundawo,,,,,
   
       Agajiye suka shigo garin na kwantagora daga kauyen da suka tafi cigiyar Dawaki da Rakumai wanda suke son suyi wasan Dabah dashi
    Direct gida kowan su yatafi, shiko Joseph yana shiga gidan su yatar da ba kowa agidan duk sun tafi gurin bidan kudi,
  Yar tsuki yaja azuciya shi yace bidan kudi tun bamuzo duniya ba kulun ana shago ba hutu,
   Wanka yayi don yadan ji sanyi a ranshi, bayan ya fito wanka ne yadawo falo ko zai samu wani dan abu yaci,,,,
   Saboda hura su KB suka sha a kauyen shi kuma bai iyan shan hura yan zu,
  Don koda da yake yaro yana sha bai bashi lafiya,
  Don,haka wurin fridge ya nufa ko zai samu dan abin da yaci a ciki,
  Giya yagani kala,kala ga sunan, tab acikin fridge din,
  Iya dibawan shi bai ga komai dazai danci ba sai giya kawai yagani,
   Har ya mika hannu yadauko kwalbar wani whisky da yake yawan sha,
  Muryan jibrin yaji yana cewa both religions din mu ba wanda ya yarda da shan giya,
  Giya tana zubar da darajan mutum,
  Da sauri ya dafarar da kwalbar inda akasane ba cikin fridge ba da ta fashe ko,,
   Ya mai da marfin fridge din da karfi ya rufe , yajuya da sauri yabar gidan,
  Har yafita sai ya tuna  da cewa bai dauko makullin motar shi ba, da handset din shi don haka sai ya koma ciki,
   Warin giya yaji yau falon nasu nayi a sakamakon bude fridge din dayayi sai kawai yaji warin na hawa mai kai,,,
  Maimakon ya shiga mota sai yafita get din su ya taka da kafa,don yatari mai achaba ya hau,
   A hankali yake tafiya har ya kusa shan yar kwanar gidan su sai yaga andanyi taro a gurin
  Kamar ance mai yatafi har zai wuce sai kuma ya isa gurin,
  Wata matace yagani tana ta rusa kuka ga wasu samari suna ta kokarin yin bico a wani fili,
  Matar na fadin wallahi bamu sayar wa kowa da filin mu, ba kudine kawai bamu dashi shiyasa bamu gina komai a ciki ba,
  Ya dan tsaye daga baya tana kallon ikon Allah, inda yawancin mutane gurin ke cewa ai fillin na matan ne ita da yatan ta,
  Sun gaji fillin nr gurin mijin ta da yarasu, lokacin yaranta suna kanani bata da halin gina filin
  Yanzu ko yaranta sundan girma shine tazo dasu don sugyara filin su dan samu wurin zama koda bukkah ne su dan haka saboda gidan haya yana mata wuyan biya,
  Sai gashi sun fara aiki kenan wani yazo yace ai yasayi filin a gurin kanin mijinta,
  Kuma har ya biya kudi dadewa, don haka subashi wurin shi,
  Matar nata kurma ihu tana cewa ta shiga uku babu inda zata ga yara gashi basu da kudin biyan haya
  Joseph na tsaye yana jin yadda matar ke gumza kuka duk wanda yazo yaji ba,asi sai dai ya ce Allah ya ktau mai shi ya wuce abin shi,
   Duk yunwar da yake ji sai yanemay ta yarasa ,
  Takawa yayi har inda mutumin da ke ciwa matar mutunci yake, yai mai sallama yana mai mika mai hannu, don su gaisai,
   Bayan sun gaisa ne yake tambayar mutumin ya maganar take ne,
  Da kamar bazai bashi ansa ba saidai yadda yaga Joseph din is serious sai ke ce mai
   Yar rainin wayo ce sun saida filin su dadewa shine yanzu tazo wai ita zata gyara wa yan marayun ta,
  Wazata nuna wa marayu nida tunda nataso banda kowa balle,
  Wani irin kallo Joseph yai wa mutumin don jin maganar rashin imanin da yayi,
   Hannun shi nazube cikin aljihun,farar wandon shi dayasa ya juya dakyau yana facing din mutumin,
  Ya yanzu may kake so kai tunda kaji mutane sun sheda cewa filinta ne ita da yaranta,
 Mutumi yace kadaina cewa filin ta fa malam kace filina,
  Daidai loacin matar cikin kunar rai tace karya kakeyi muna fukin Allah,
  Joseph ya waiga gurinta cikin hausar shi ya ce kai haba kibi a hankali mana mama,
   Ya juyo gurin mutmin yace to nawa ne kai ka sayi filin malam,?
  Mutumin yadan yi dumm can kuma sai yace wai dubu ashirin da biyar,
  Wani mutum dake gefe yace kai malam Bawa, dubu goma sha biyar fa aka sayar ma,
  Joseph yadaga masu hannu yace Ok yanzu fadi muji nawa zaka sayar mata ita da yaran ta,
  Nan da nan gurin yai tsit ana sauraren su,
  Malam Bawa yadan yi tunane can yace in an saye hamsin na sayar in ba asaya ba shikenan ni inada abin yi,
   Matar takara sa kururuwa tana cewa Allah ya isar mata ita da yaranta akan mutumin da kuma kanin mijinta,
   Nan da nan gurin ya shiga hayaniya kowa na fadin albarkacin bakin shi,
  Joseph yakalli mutumin yace mai in bazaka damu ba zan baka dubu talatin yanzu gobe ka turo in karasa maka sauran don ban fito da kudi ba,
   Ai ba laifi inji malam Bawa nan da nan mutane suka kama cewa wai kada akara mai ko kwabo abarshi hakana macuci, kawai,
  Gurin matar Joseph ya karasa yace mata mama nawa kudin hanyan ku tace mai dubu daya da dari biyar ne wata uku,
   Dubu biyar yabata yace taje tabiya haya saura,tasayi abinci suci
  Zuwa gobe zai nemay ta, zai san yadda za,ayi,
  Yazo zai wuce yaji wani mutun yanawa wasu mutane bayanin cewa Saida Dan kahirin can ya taimaka mata yaba malam bawa kudin shi,
  Duk da rashi ya baci murmushi kawai yayi ya tqre mai achaba da hannu ya hau yana cewa kaini Green Land,,,
   Ya samu majalissar su KB ta cika anata hira saman wani tabar ma wasu kuma zaune a saman wani benci,
   Gefe guda ya samu a saman tabar man yadan kwanta rigingine fuskan shi na kallin titi yana kallon masu wucewa,
     In akwai abinda maryam taki jini a rayuwar ta shine idan zasu wuce ta iske wanan majalissar ta cika,
  Duk da bata kallon gefen su amma tana tsarguwa don ji takeyi kamar duk ita suke kallo,
   Tunda ta tun karo gurin taga sun cika duk sai taji ba dadi aranta don haka sai ta dan kara sauri tana rike da hannun Issalam,
  Shiko Assalam na bayan su yana shuka tsiya wai bazai tafi ba don haka suka dan yi gaba suka bat shi,
  Saida yakawo dai tsakiyar inda majalissar matasan yake ya yanke jiki yafadi wurin kalle kallen shi,
  Aiko ya yanka wani irin ihu kamar wanda aka zare wa rai,
  Duk wanda ke gurin saida ya waigo inda yake kwance cikin kasa yana faman kurma ihu,
  Wasu daga cikin yan majalisar suna ce mai tashi ma na wani kuma na ce mai dan nema wurin shegen kallo har ka fadi,
  Dole Maryam tadawo baya ranta duk a bace,
  Joseph dake kwance yana kallon tun gilmawan su maryam har zuwa faduwan yaron wanda yai tuntube ya fafi kasa,
  Yataso daga inda yake kwance,yazo inda yaron yake yanata tsala ihu,
  Daidai lokacin Maryam ta iso gurin,
  Tadaga hannu zata kai wa Assalam duka a baya hakan yai daidai da tarewan da ,Joseph yayi sai ta samu hannun shi,
  Wani irin kamshin turaren,THE ne ya daki hancin ta ba shiri ta mike tsaye daga tsugun nin da tayi,
  Shikuma Joseph ya dago da yaron daga inda yake kwance cikin kasa, yana dan kakabe mai rigar shi da ta baci da kasa,
  Maryam dake tsaye tana ce mai bazakazo muje ba ko sai mun makara,
 Joseph yadago faren idon shi yadan kalleta ya ce ki tafi zan kawo shi,
  Shiru tayi tana nazarin mutumin kafin tayi kwafa ta wuce tana mai jan hannu Assalam tana gunaguni,
   Hannun yaron ya rike suka shiga cikin green land super market, tare can ya fito da yaron dauke da yar leda shake da kayan kwalama,
   Inda ya rike mai hannu zuwa inda yqga yara madu irin uniform din su na shiga,
  Har  bakin get din islamiyar ya aje yaron inda yadan rage tsawo daidai ta yaron yana ce mai to abikina shiga kayi karatu abinka kada kaba kowa chuculate din da da biscuit, kaji,
  Yaron yadan kara goge busashen hawayen dake makale a idon shi da bayan hannun shi yace har da anty ko da,Issalam?
   kada mai kai Joseph  ya yi waban karon alamar ya gaji da rigimar yaron,
  Yace mai duk kan  su karka ba kowa, daga haka yada ya wuce shiko Assalam nata dago mai hannu,
  Yana komawa gurin yaji Inus nacewa wai ina Joe ya tafine, ko dai har yanzu yana gurin rigimamayn yaron nan ne,?
   Ganin da sukayi mai dawo wa yasa sukayi shiru,
  Isowar shi yayi daidai da zuwan wasu mutane su uku a saman mashi,
  Yan tsofine mutun biyu sai wani matashi da yajawo su,
   Kowa dake gurin saida yai mamakin mai yakawo tsofin gurin su,
   Mai mashin din ne yai ma yan dattawan nuni da Joseph yana cewa gashi nan ai,
  Daidai lokacin da mutanen sukayi wa wa yanda suka tarar sallama, cikin daga hannu,
  Sai dan shiru ya biyo bayan hakan na wani lokaci,
   Shima Joseph mamakin nuna shin da akayi yake yi a lokacin,
   Cikin mutanen mutum gufa ya fara bayani kamar haka,
  Malam yat uwqr muce tasa may mu da kuka dazun take sheda muna abinda yafaru,
  Ai duk wanda ke gurin saida gaban shi ya fadi da jin maganar mutumin
   Don su azaton su wani abu ne yafaru, da wata da Joseph din,
   Mutumin ya cigaba da cewa shi ne muke tambayar kokai waye sai wanan saurayin yace muna shi yakawo ka nan,
  Mu zo ne muyi maka godiya a bissa arin taimakon da kawai hajjo,
   Mungode kwarai Joseph yace kai haba baba aida baku taso ba wallahi da kubari kawai ba komai,
  Ai taimako yi wa kai ne, ba wani abu ba,
  Koda yake zuwan naku nan yai mun da dadi sosai
  Ammmm KB zo don Allah KB dake zaune a kusa da inda ya tashi ya zo kusa da yan dattawan,
  Joseph yace don Alkah zaka samo masu gina sai a nuna maka filin aja ma matan da yaranta daki hudu da katanga,
   Ai sai yan dattawan na kokarin hada baki gurin cewa Allahu Kbar,
  Yaro halan kai dan gidan waye agarin nan don ban mu san ka ba
  Wani habibu ne yai saurin cewa dan gidan Ema mai manjane tsohuear kasuwa,
  Da mamaki suke kallon shi gudan mutumin yace ikon Allah,
  Dan gidan Ema kuma tau Allah ya kyauta ,,
  Mungode kaji Allah ya haskkaka zuciya, dukbda bai gane nufin su ba yadai ce Ameen,,,
    Mutanen da zasu wuce ya basu dubu biyu yace su biya mai achaba,
  Sai bayan sun wuce ne yadan yi ma abokan nashi dan bayani breifly,
  Daga haka bai kara cewa komai ba,duk maganar da kowa keyi yana ji amma bai tanka ba,
  Shi baima so kowa yaji wanan zancen daya yafaru ba in badon
  Wa yan nan dattawan da suka zo wai yi mai godiya ba,

     Tun shigowar su gida, yafara kiran mummy zo kiga kayan da aka sayo min ance inci ni kadai bada kowa ba,
  Maryam da ta shigo rike da hannun Issalam ta wani zunburo baki gaba tana cewa wallahi anty in har Assalam na muna haka ni bazan kara zuwa dashi makaranta ba,
  Dariya maganar maryam yaba a yayan nata, tace idan baki je dashi ba, ai sai ya zauna dama kece mai daurewa karya ai,
   Nan Maryam taba yar ta labarin abin da Assalam yai masu hannu takuma mika mata ledar kayan kwalamar da aka sai mai,
   Uwar ta karbe ledan tana cewa aiko bazai sha ko kwara guda daga ciki ba, tunda abin da yayi ke nan,
  Anty Dije takarbe ledan ta shiga dashi dakin ta,
  Wani sabon kuka yasa yana kokarin turje turje a kasa,
  Maryam ce tabi bayan anty da sauri tana fadin dan Allah kiyi hakkuri yaya,
  Abashi gobe ba zai kara ba, ai,
  Da mamaki anty dije ke kallon Maryam ce ta langabe kai kamar zatai kuka don ankarbe ma Assalam kayan shi,
  Sai kace ba ita bace ta kawo karan shi yanzu har tana ikirarin bazata kara fita dashi ba,
  Murmushi tayi tana cewa kai Maryam abarki kawai daidai lokacin da maryam din ta karbi ledan a hannu anty,
  Ido anty Dije ta bita dashi tana murmushi acikin zuciyar ta tana yaba irin son da yar kaunar nata takeyi wa yaranta,,,,,,,,,,   


Afuwan ba yawa pls,,,,,,,



   ZEEEE MAKAWA
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
    FUREN JUJI
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
            5鈨�
            BY
ZAINAB IDRIS MAKAWA
馃悗HUGUMA GROUP馃悗


  Maryam Abdullahi bobi, diyace ga malam Abdullahi bobi,
 Asalin , Mahaifin su daga wani kauyen kwantagora suke wanda ake cewa kamfanin bobi,
  Su malam Abdullahi yan asalin can ne saida zama yakawo kakanin su a cikin garin kwantagora da a cikin jahar Niger State of Nigeria,
  Sana,ar maihafin su shi ne saida kayan masarufi a cikin kasuwa,
   Yana da mata biyu inna  hussai da maman, tunga,
  Saidai da dadewa can ya, auri wata yar uwar shi daga bobi, saidai gaskiya  babu so a tsakanin su ,
   Don tana da wanda take so a can bobi, don haka ta tada hankalinta bata zauna,,  auren bai dauki wani lokaci ba ya mutu,
  Ashe akwai rabo a tsakani don haka aka samu cikin maryam,
  Bayan haihuwar maryam ne tai wani aure anan cikin kauyen Kampanin Bobi,
   Tunda aka haifi maryam sau guda aka taba zuwa da ita gidan mahaifinta,
   Duk yarinyar na ran malam Abdullahi amma yasan cewa kawo ta cikin iyalin shi wani sabon fitina ne,
   Saboda sun riga sun tsani uwar Maryam har abin ya shafi yarinyar don zuwan da akayi da ita ko kallonta ba wanda yayi,
  Sai Dije ce kawai taita nan, nan da maryam din tana nuna kulawar ta akai,
  Amma a lokacin Dije tana secondary bata kare karatu ba balle tayi aure,
  Bayan kare karatun tane ta hadu da wani dan makwabcin su Iliyasu ma,aikacin aikin custom ne,
  Sukayi aure tun lokacin da dije ta tsaida miji tasha alwashin cewa za ta dauko maryam su tafi tare,
   Amma sai uwar ta Inna, hussai tace mata sam bata yarda diyar ta ta dauko mata, wata wahala ba can daga kauye,,
   Don haka Dije tabar wanan zance kamar ta fita batun sai bayan auren su da ILiyasu ne
  Baba yaje dakan shi bobi ya dauko maryam da yan kayan ta yazo ya danka wa Dije ita amana,
  Tun wanan lokacin Anty Dije ke kula da yar  kaunar ta , ta cikin amana,
  Har zuwa lokacin da Allah yabata nata haihuwa,
  Assalam.shine nafarko sai Issalam, wace yanzu daga gareta ba,a kara samun wani ba, tukun har yanzu,
  Mijin Anty yana zaune a can jibiya ne bakin border don da lagos yake har ya taba zuwa da su sai da anty ta kusa haihuwan Assalam suka dawo,
  Inda mahaifiyar shi tace bata yarda ya koma da ita ba , don in yatafi da iyalinshi wai yana dadewa baizo gida ko kuma aike,
   Tun wanan lokacin anty ta zauna kwantagora bata kara bin mijin ta abisa umurnin uwar mijin ta,
  Saidai har yanzu abin bai canza ba don gwamma da da yanzu don yanzu baifi ya zo sau uku ba a cikin shekara,
  Saidai yakan aiko masu da sako akai akai,
   Maryan yanzu tana karatu ne a Girls day secondary school kwantagora,
  Tana Ss虏 yanzu su kuma yaran antyn ta sun fara nursery a wani preravent school,,
   Maryam ita ba fara bace kuma ba baka ba yar doguwa da ita bata da jiki tana da hanci madaidaici da ido masu dan girma,,,,,
   
    Yau kusan satin shi biyar da barin gari yana can suna ta harkan man fetur,,
   Saidai a kai akai suna yawan waya da abokan shi,
  Musan man KB da jibrin wanda dama sun fi shakuwa da su tun suna yara,
  Don duk irin wulakancin da ake mai lokacin suna yara na kasan cewar shi dan kirstan acikin su
  KB da jibri a gaskiya ba suyi mai sukan ja shi zuwa gidan su ,
  Idan kuma mahaifin shi yasani a lokacin yai mai dan karen duka,
  Har akwai wani lokaci da ana bukin babban sallah yabar gidan su tun da safe zuwa gidan su KB , da kayan shi dunkule a leda a cewar shi zai bi su gurin yawon sallah ne,
  A gidan su anyi bidan shi har angaji kasan cewa idan musulimi suna irin wanan buki su kiristan sukan killance diyan su a gida basu bari su fita ko ina,
   Hakan yasa shi yin asubancin barin gida zuwa gidan su KB din,
  Dashi akayi ai,kin komai na naman inda aka diban mashi zuwa gida dabara yayi da zai tafi yaba KB saura yace ya boye mai
  Baban su KB shi yaraka shi da yaga yana labe ,labe
  Suna zuwa tun daga nesa uban shi yafara yi mai sababi saida mahaifin KB ya bashi hakkuri,
  Wucewan mahaifin su KB kadan akasamay shi akai ta bugu kusan duk wanda ya girmay shi a gidan ranan sai da ya doke shi,
  Yana kallo naman da yaje kwadai yai wahalar aiki aka zuba a cikin ruwan kwata aka murje,
   Duk da haka washe gari saida ya koma, wurin KB da zai tafi kasuwa yadan dade gidan sanan ya wuce, kasuwa,,
  Iya gaskiya shi Joseph yana jin dadin zaman  da su keyi da su KB da sauran friends,
   Idan yana cikin su ana hira yakan ji kamar an yaye mai wani nauyi duk da ba magana yake yawan yi ba acikin su,
    Yadda suke hira ana challenges din juna ko kuma kuma yayi ta kallon yadda mutane ke ta faman zirga zirga,
   Abin yana burge shi so sai don idan a cikin yan uwan shi IBO yake sam babu wanan irin dabi,ar sai dai kawai kulun a na gurin bidan kudi,,,,
   Shidai dabiar hausawa tana mai a rayuwan shi don in ba haka ba da irin dukan da yasha yana  da ya daina kula su,,,,
 
     Don haka tun dawo war shi, kasar su yake tunane da nazarin irin sana,ar da ya kamata ya jona su KB aikai wanda zai jawo masi cigaban rayuwar su
     Batare da,sun dogara da wani ba ko kuma da aiki gwaunati, kamar yadda akasarin hausawa ke yi yanzu,
   Yau da ruwa aka tashi a garin na lagos don haka duk wanda yakai wani lokaci a waje go slow ta rutsa da shi,
  Joseph wanda shigowar shi ke nan garin a lokacin, da ake tsula ruwan,
  Tafe yake a hankali a cikin motar shi yana tafiya kamar wanda bai son yin,,,,
  Idon shine yakai ga wani motar daukar kaya watau tirela,
  Wace tayo dakon buhu,hunan shikafar yar gwaunati sai,dai,duk  ruwan sama yasa duk ta fara jikewa ga masu motar nata wahala, da shi
  Wani irin tunane yadar su cikin zuciyar shi wanda tasa shi dan yin murmushi a lokacin,
  Gidan shi dake cikin, Apapa ya wuce direct inda yasamu maigadin gidan yabude mai get ya shige ,
  Mai aiki naganin shi yatashi da murnan shi  yafara kokarin hada mai dan abinda zai ci, tunda yasan cewa ogan nashi baya cin abincin waje,,
   Yana ganin oga yasan cewa yau boza tazo don yasan cewa duk sanda ogan na shi ke gari duk kan su dake a karka shin sun yake wahalar kudi,
   Wanka Joseph  kafin ya fito har an hada mai girki mai lafiya,
  Bayan ya gama ne yasamu daya daga cikin kujerun falon ya haye,,,
   Don har zuwa wanan lokacin ruwa ake tsulawa, agarin
  Don haka yana kwantawa sai shawar da zu dayayi tafado mai a rai, daga karshe ya jawo wayan shi yadan dinga dan,na wa yana kiran abokan shi daya bayan daya suna gaisawa,
   Daga karshe ya kira KB inda suka dan dade suna hira akan ginar da ya bashi kula dashi na yan marayu
   Yai mamaki kwarai da jin dan kudin da aka kashe wa ginan,
  Inda ya yaba da irin saukin da aka samu a wurin kayan aikin unlike irin yadda anan inda suke harkoki basu tabuwa,
   Don haka yai alwashi a cikin zuciyar shi zai gyara gidan mahaifin shi da suke a ciki very soon,
    Kafin su kashe wayar KB ke tanbayar shi ko yaushe zai shigo KG, din,
  Yace mai sai nan da sabon wata daidai lokacin da zasu fara yin shirin programs din su na wasan Daba da za suyi,
   Sun dan jima a wayar suna hira sanan suka yi wa juna sallama, suka, kashe wayar ,,,
   Su na sallama da KB yakira Daddy shi inda a lokacin daddy yana zaune tare da yaran shi suna hira,
    Mr Emanuel yaji dafin kiran da Joseph yai mai a wanan lokacin,
  Don dama shima yana da niyar kiran shi akan maganar ginan da yaji cewa wai yana wa wasu hausa wai da sunar tai mako,
   Taupa Joseph yace a cikin ran shi watau abin duniya baya boyuwa kenan,
  Can kuma yace ai ba mamaki don kusan shiya kuda suke da mutane dole wani zai iya fadawa baban nashi,
  Muryan Mr Emanuel ce tadawo dashi daga tunanen da yakeyi inda yake cewa,
  Joseph u, no dey hear word,
  I always warn u about dis people,,
   Jin uban ya ci gaba da fada ne sosai yasa Joseph yai sauri katse shi da ce,
  Dad, am doing all dis b,cos of u
   Saboda kai ke zama ko yaushe a cikin su indan har mun nuna cewa bamu tare da su a fili a baza mu samu biyan bukatar mu ba,,
   Ajiyan zuciya Mr Emanuel yayi don jin kalaman dan nashi,
  Shima ta fanin Joseph din sanyayar ajiyar zuciya yayi,
   Don jin ya ciwo kan tsohon na shi cikin lokaci guda,
   Bai tsaya wani dogon magana ba yai sallama da dad din, ya, kashe wayar
   Don gudun wani sabon magana,
    Rigingine ya ke kwance saman gadon sai tuna nen maganar Dad yakeyi,
   Yasan cewa za su kara kwasar rikici da tsohon nashi,
   Idan har tsohon yaji cewa zasuyi wasan nin matasan kasar kwantagora a cikin su har da shi Joseph din wanda yaba da gagarumin gudun mawar shi a taron da za,ayi,,,,
     Cikin, gwanin ta yake tukin motar shi daidai lokacin da ya ke kokarin shiga get din gidan su,
   Mahaifin shi da aboksn shi, suna zaune saman wasu benci guda biyu, da ke harabar gidan,,
    Cike da sanyi jiki yake tunda yai arba da su zaune suna ta dirkan giya sai shewa sukeyi a tsakanin su,,,
   Nan da nan maganar Jibrin yazo mai arai inda yace komai darajan mutum idan ance yana shan giya,
  Kimar shi da girman shi ya zube ke nan a idon duk wanda ya ganshi a hakan,
   Don haka sai yaji a, lokaci guda duk wanda ke gurin kimar su ta zube mashu a idon shi,,
   Yan samarin da ke gefe suna karta suka zo suka tare shi cikin murna da jin dadin ganin shi,,,
    Buth din motar shi ya bude masu suka fara jidan tsarabar da yazo dashi zuwa cikin gida,
   Inda dattawan ke zaune suna dirkan giya yanu fa don kwasan blessing,
   Kirari wani daga cikin su ke mai irin kirarin yan gidan su da ake masu a can kasar su,
   Jin kirarin yadan sashi yin yar murmushi daga nesa saboda yana son wanan kirarin na kakan su da ake masu,
   Karasowa yayi inda suke yadan  yi kamar ya duka yace masu barkan ku da gida,
   Gabada yan su sukace mai blessing my child,
  Ya hanya ya ya kabaro lagos yai dan murmushi yace daga Abuja yake shine yace bari ya kara so nan,,
    Wani dan gajere mutum daga cikin su yadan kalle Joseph din daidai lokacin da yake zuba bommi a cikin wani cup,
   Yace waiting dis boy want, in dis town, no b last month i saw him,,,
  Baban Joseph da ya sha yai tatil yace cikin murya tsatsaye,
   Na, me send for him wooo, i wan tell him about d white men,
   Joseph da yaga kamar shirmay suke zubawa ga warin giyar bommin da su ke sha duk ya cika mai hanci,
  Sai cewa yayi sai anjimar ku yana kokarin shigewa,
  Wani daga cikin su ya dan yafito shi da hannu yana mai alamar yazo ya zauna
  Wani daga cikin sune ya iya bude baki yana cewa come nd join us my son,
   No tnxs kawai yace yana mai kokarin mikewa tsaye yabar gurin
     Tunda ya shiga gida baiyi marmarin fitowa ba saboda yan dattawan dake waje suna holewar su,,,,
    Sai sha daya na safe ya ke shedawa su KB yana cikin gari,
  Duk sunyi mamakin jin cewa yana gari don basu sa rai cewa zai shigo very soon haka ba,,
    KB ne ke ce mai ya na tafe yanzun nan,
   Sai Joseph din ke ce mai ya bari har zuwa yamma don dama wani program yazo yi a church din su,,,,
   
    Church kan ya ciki makil yau saboda kiran gagawa da akai ma duk wani mabiyin wanan church din
   Kamar irin su Joseph da iyayyen su ke ciki yazama dole su zo  wannan taron da ance mai ma,anace taron,
  Wasu turawane ke perching kamar kuma shawa da umurni suke ba sauran mutanen,
   Inda suke neman hafin kan duk wanda ke cikin addinin da ya kawo gudun mawa mai tsoka
  Indan an hada kudin daga baya sai su shiga daji inda kauya wa suke su fara masu wa,azi da kuma jan ra,ayi da abin duniya, har su samu galaban jan ra,ayin su
  Ihu da murnan jin wanan shawaran church din ya rude dashi, saboda suna ganin cewa zasu iya cin galabar yan kauye da,dama a, hakan,
  Kafin wani lokaci an fara yawo da ture ana karban gudun mawan gurin jama,a,
    Wani dan kyamushashen bature ya kara tashi yace
  Wani hanya kuma guda da zasu bullowa al,umma dashi ita ce
  Suna da wani baiwa da zasu iya kara jan ra,ayin mutane da shi cewa,
   Duk wanda baida lafiya za su warkar dashi indan har yaji sauki to ya zama dole ya bi akidar su,,,
   Sannan su kara tabbatarda cewa har wa yan dake a ciki idan su na da wata cuta zasu iya zuwa a warkar  amma da sun ji sauki ya zama wajibi a kara masu mukami acikin church,,,
  Joseph najin haka ya mike kamar mai waya a zuciyar shi yana cewa yan yaudara ne kawai  da cuta,,,,,,,


  ZEEEE  MAKAWA,,,,,,,,,
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
    FUREN  JUJI
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
             7鈨�

ZAINAB IDRIS MAKAWA


  Kusan duk wanda ke cikin wurin yana saye da rigar coat ce a jikin shi sai yan kali lqn ne ke da shiga irin ta hausan arewa ko su basu mutum uku ba daga cikin su,,,
   Daga ni meetings suke yi kuma meeting ne ma tsauri don duk kan su fuskan su babu wallawa a ciki,
   Kadan kadan hayaniya ke dan biyo baya musan man idan an fadi wani abinda ba,a yarda da shi ba agurin,
  A wajen harabar gurin kuma maza ne kaitai majiya karfi kashi, kashi, da alamar security ne su
  Sai wasu irin manyan motoci da sai inda idon ka ya tsaya,,,
  Kowani kusurwa na wajen an zuba jamian tsaro birjik
    Sunan mutum uku ne yanzun haka ake muhawara akai,
   Mr Inok ,Ishaya noma sai Joseph,Emanuele,
  Daya daga cikin su ake son ajewa a matsayin sectarianism din su na matasa masu harkan man petrol,
   Daga karshen zaben ya fada akan Joseph wanda akasari mutane ba,su so hakan ba ,,,,
  Wani dan Jos suka so Ishaya Noma,
  Wanan mukamin ya jawo mai ci gaba sosai tare da duk wani wanda ke kusa da shi,
  Abokan shi dana sanar shi sun hada mai party samun cigaba,
  Mutanen kwantagora sun zo mai murna, don kusan duk, yan abokan su sun zo,
  Wanan zuwan ya tayar masu da hankali so sai fiye da tsab manin su,
  Don duk daukan da suke mai ashe yafi da haka a fili,
   Sai bayan sun wuce ne Aisha ta samu wanan labarin kuma har an tafi, don haka ta lalashi Amina har ta yarda suka shiga motar kasuwa suka tafi har can,
   Bayan sun isa ne, takira nobar KB take sheda mai cewa gasu sun iso garin,
  KB yai mamakin jin  wai ga su sun shigo cikin garin
   Inda Joseph yake cikin abokan harkan shi KB ya rutsa yaje har cikin kunnen shi yai mai rada yaba sheda mai zuwan su Aisha
  Sai da Joseph yadan nuna kaduwa don bai taba tsan manin zuwan su ba,
  Wani yaron shi yakira yai mai nuni da KB yace su je tare azo da, su masauki
 Su kan su sun yi mamaki kwarai da irin masaukin da suka samu,,

  Washegari ne zaa ,gudanar da taron tayar murnan samun cigaban da su Joseph suka samu,
  Inda taro yai taro don duk bakon daya zo dana kusa dana nisa Joseph yasa an karama shi da wada tacen abinci da na sha daidai gwargwado,
   Fili na musan man yasa aka bawa abokan kurciyan shi a ce war shi, inda suka fito cikin musulunci tare da hasken musulunci a fuskan,
  Sai mamaki su akeyi yadda sukazo taya,shi murna haka da yawa,
  Anyi yan wasan ni da kuma raha kamar yadda akanyi inda wani abokin kasuwan cin shi da Lagos ya ba shi shawaran yai aure, hakana tunda Allah ya,wadata shi da arziki tun yana yaro,,,
   A haka taro ya,watse , wa yanda suka zo daga nisa suka fara niyar komawa gida,
   Sai, a lokacin Joseph yasamu kebewa da su Aisha cikin yar sakin fuska yake masu maganan,,,
  Inda yai mata godiya sosai da kuma bata, appointment, nan da two weeks zasu hadu,
   Aisha taji dadin wanan tafiyar da sukayi saboda irin guzurin da suka dawo dashi,
   Tun wanan lokacin ya rage samun lokaci kamar da, yanzu ya kwana biyu baizo kwantagora ba duk da aiken da mahaifin shi Mr Emanuel ke mai na cewar church members na son ganin shi,
   Aiki yakawo shi Abuja don haka yai amfani da wanan damar ya iso amsa kiran mahaifin shi,
   Yan church din sun gudar da,addu,an su gare shi tare da fatan alheri zuwa gare shi,
  Yaji dadin wanan adduan da akai mai don haka yaba gagarumin gudun mawa a church din nasu,
  Tun jiya Sunday da suka dawo church din bai kara fita duk da yawan wayan da friends din shi keyi don jin cewa yana gari,
  Bai samu fitowa sai bayan karfe biyu inda yace ma KB yazo su fita,
   Don motar shi ta na bukatar, wanki sosai, don haka,  yabar ta kanin sa ya fita mai da ita gurin wanki,,
    A,saman mashin din KB suka fita, fitan da yasa mutane suka san cewa Joseph yazo gari,
   Hmmm Dan Adam da kudi, kafin wani lokaci har yan kai koke sun isa gurin da suka san cewa zasu ganshi su yi maula,
  Mutanen mu ho, idan zuciya ta mutu koma mutum na iya yi don kawai ya samu kudi,
   Sai bayan sun gama maula ne sai a koma gefe ace ai dan kafirin nan yazo
  Ai yanzu ba asan sanar da yake yi ba sai dai kudi ake ganin shi da shi ba a san ida yake samun su ba,
  Wasu kuma, cewa suke yi ai Joseph mafiya yake yi yanzu sosai, irin na ya birni wanda ba,a gane akidar mutum,,,
 
    Maryam tana tsaye a gaban mirrow tana gyaran hijab din dake a wuyan ta,
   Issalam tazo ta bayan ta ta rugumay ta ,
  Issalam kada fa ki sa in fadi kasa wqnan rikon da kikai min,,,
  Yar wasan kokuwa suka fara yi da Issalam din kama ba zasu makaranta ba,
  Anty Dije ce ta leko dakin jin su shiru da tayi dakin,
  Cikin mamaki anty Dije tace, amma dai, maryam anyi uwar banza
  Yanzu ku shirya ku wuce shine zaki buge da wasan kokuwa da Issalam,
  Maryam na dariya daidai lokacin da Issalam ta kara kai mata damka ta na ko karin wai sai ta kayar da maryam a kasa,
   Daidai tana fadawa kan katifa, tace ma yar nata ai yanzu zamu wuce insha Allah,,
   Anty Dije na tsuki ta sake labulen dakin tace ai ku ,za,a daka a makarantan,
  Har ta kai kofa ta tuna Assalam baya dakin kira ta kwada mai,
  Daga bayi ya karba mata mama gani nan ina wanka,
  Cikin mamaki jin cewa yana cikin bayi har yanzu yasa anty mamaki
 Hanyar bayin ta nufa don ganin may yake yi a ciki har yanzu,
  Sabulu yasa a fuskan shi dumu dumu, bai ko san shigowar uwar tashi ba ciki,
  Sai lokacin da yaji hannun ta a jikin shi ta danko shi,
  Wani irin ra,zananen ihu, yasa wa uwar don yana ganin kamar zata buge shi, yasa yaron yaka ihu,
  Daga, maryam har Issalam duk bayin inda yake kwala ihun suka nufa,
  Wanka su ka samu Anty Dije tana mashi yana ta kokarin kubcewa,
  Bayan sun shirya ne suka wuce islamiya saboda sun makara, yau
  Allah ya taimake su ba su sami malam babba yadan fita don haka badu sha duka ba,,,

  Isowar su Joseph da KB a majalissar su ya yasa gurin yadan kaure da hayaniya cikin dan lokaci kadan,,
   Bayan dan gaishe gaishen da ya biyo bayan ne suka samu guri suka zauna
  Fira akeyi amma shi Joseph uffan bai ce masu ba sai dai idan anyi abin dariya shima yadara,
  Ana cikin hirane daidai lokacin da yan makarantan Isalamiya suka fara tasowa, a lokacin wayar shi tai kara alamar kira yashigo mai,
  Aisha ce ya gani baro baro a jikin screen din wayar tashi,
   Dan tashi yayi nisa kadan daga ind suke zaune, don ya karba wayan nata,,
  Tambayar shi take yi yana ina ne ?
 Don tana son ganin shi ne, kafin yabata ansa sai ji yayi an rike shi ta bayan shi,
  Da alama kuma dan karamin yaro ne don daidai iya gwiwar shi yaron ya tsaya,
   Kafin ya juya lokacin da yaji haka yake cewa Aisha yana zuwa pls,
 Waigowa yayi a hankali yana kokarin ganin kowaye yaron,
  Wani dan farin yaro yagani ya rike shi tsab yaron na cewa,
  Abokina kullun sai na diba ko zan gan ka idan zamu tafi islamiya amma bana ganin ka,
 Idan kuma na tsaya sai little, mum ta dinga zagina,
  Rage tsawo Joseph din yayi don dai bai fahinci ko may yaron ke tawa bayani ba,
   Maryam, dake tsaye gefe iyakar kuluwa ta kai har tafi nan,
 Don ji takeyi yau idan ta fara dukan Assalam bazata daina ba tunda har yasa ta tsayawa daidai gurin yan sa idon mutanen nan,
   Hannun Assalam Joseph yakama ya hade guri guda yana mai fuskantar yaron,
   Kafin yai magana sai muryan maryam suka ji tana cewa Assalam bazaka zo mutafi, ba ko,
  So kake dare yai muna a hanya kafin mu isa gida ko,
  Nunata da hannu Assalam yayi yana mai cewa dakace kada in basu sweet dina sai da little mum ta ba Issalam tasha,
  Joseph dai har yanzu bai fahinci yaron ba don ya manta cewa sun taba haduwa da yaron ,,,
  Yace wa Issalam bari ,zan saya ma wani mai yawa amma kaba kowa yasha kada kayi rowa kaji,,
   Jibrin dake kallon draman su tun dazu yadan taso daga inda yake saman wani benci yana cewa cikin turancin
  Ai yaron da ka taba dauka ne da ya fadi a gurin nan da zasu tafi,makaranta,
  Saida yadan yi tuna ne sannan yace ok ok na tuna a haba dai my friend kaine haka kazama big guy,,
  Yakara jawo yaron zuwa cikin jikin shi ya rungumay yadan dago kai yana kallon jibrin,,
  Yace wanan yaron baya mantuwa pa kadiba bafa yau ba wanan event din ya faru wai ama ace bai manta ba,
  Maryam kuka kawai ya rake tayi a lokacin saboda sukuwar da yayi da Assalam,
  Cikin zafin nama ta isa inda suke tana kokarin finciko Assalam, din,
  Kai Joseph yadaga yana kallonta yana cewa haba barshi mana pls,
  Wanan yaro ne fa shi ai baisan komai ba, yana fadin abinda ke a mind din shine fa kawai,
   Batare da ta saurari may yake cewa ba tace kazo muje gida kaji wallahi yau sai na ma mugun bugu Assalam,
  Jibrin da baiyi magana ba tun dazon ne yake cewa kutafi zan kawo shi gida,
  Cikin mamaki ta dago kai tana kallon mai magana don ita a iya sanin ta bata taba ganin jibrin a gidan nasu ba,
  Yagane kallon da take mai don haka yace mata ke wanan yaron fa nima yaro na ne kin ji,
 Kafin mamakinta ya kai karshe
  Taji yana cewa ke ba kaunar matan Isiya Custom bane,
  Kai kawai tadan gyada mai alamar eh ita ce, din
  Yace to kutafi kawai zan kawo shi,
 Still wani irin mugun kallon see u tai ma jibrin din alokacin,
  Yace ke nifa yaron gwago laure ne don haka ki wuce kawai,
  Jin an ambaci gwago laure yasa maryam fara kama hanya rai bace hannunta rike da Issalam tana ja kiiiiiiii,
  Anty tana kokari kauda abincin dare daga dan matsakacin kitchen din ta taga shigowar marya da Issalam a hasale,
  Babu Assalam a tare da su hankalinta na kofar hanyar shigow taga shigowar Assalam din,
   Kafin yatambaya maryam tace wallahi Anty gaskiya ba zan kara fita da Assalam ba tunda a gaskiya duk zamu wuce sai yabani kunya a hanya harda zuwa rokon fa naji yanayi,
  Ido waje Anty Dije tace roko fa maryam ina yake in ci abu kazan shi,,,
  Maryam tana kokarin shiga daki tabar Anty Dije a tsaye tsakar gida daidai lokacin da tace ya na can mana,
  Idon dayafi na dazun fitowa waje tace can ina Maryam,?
    Tare da wa yanda yake rokon ta fada kai tsaye kawai, tashige abinta,
 Wuf Anty Dije ta bita ciki daidai lokacin da Maryam ta kwabe, hijabinta daga kan ta tace mata tare fa dadan gidan gwago laure suke,
   Wani cikin su? Kenan inji Anty Dije
  Uhumm nima ban san sunar shi ba inji Maryan,
  Hijabin da Maryan ta kwabe 脌nty Dije ta jawo tana kokarin sawa,
  Daidai lokacin da sukaji ana sallama alamar shigowa cikin gidan
  Karar takalman Assalam ne ya sanar da su cewa tare da mai sallamar yake tafe,
    Assalam agaba da gudun shi cikin walwala da zumudin ya bude ledar dakw hannun shi
  Anty Dije tai saurin kai mai duka a hannu ya wurgat da ledar ya, koma baya da sauri ya fara kuka,
  Jibrin ne yace ma Anty Dije haba dai madam ya zaki buge shi tunda har kin gan mu a tare,
  Cikin yar dariyar da batakai cikiba take cewa jibrin wallahi jibrin yaron ga baida dabiar kwarai,
  Rokon ku fa yayi,
  Nan da nan jibrin yakai kallon shi ga kofar daki inda Maryam take tsaye tun shigowar su,,
   Hmm kawai yace yana kojarin komawa ya kamo hannun Assalam din
  Bai roke mu ba yadai fada muna cewa wanan time din da aka saya mai sweet saida akaba kaunar shi,
  Duk da joe yace kada yaba kowa,
  Daga Anty Dije har Maryam duk sai jikin su yai sanyi,
  Nan dai jibrin yaba Anty Dije labarin yadda akayi tun ranan farkon haduwar su da Joseph din
   Joseph da ke waje tsaye yaga Assalam ya firo yana kuka riko mai hannu yayi yana kokarin lalashin shi,
  Daidai lokacin Anty Dije da jibrin suka fito daga cikin gida,
 Tana daga ciki kadan suka gaisa da Joseph din tana mai yi mashi godiya,
  Yace kai haba ai ba komai bane wanan yaro ne Assalam bai san komai ba,
  Jin hausan shi da Anty Dije tayi yasa ta gane cewa ba bahaushe bane shi,
  Saidai sam batakawo cewa shi Christian bane, shi,
  Joseph yace wa Assalm yai shiru zai sayo mai game da mota wasan yara,,,
  Hakan yasa shi komawa cikin gida da sauri don yafada wa little mum da Issalam cewa za,a saya mai mota,,,,,,,

ZEEE  MAKAWA
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
    FUREN  JUJI
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
              6鈨�
  ZAINAB IDRIS MAKAWA



Zaune take gaban mirrow tana dressing kusan duk abinda mace zata bukata na fente fuskan zamani ta na dashi a gurin,
   Dogon rigar atamfa ce ajiye saman gadon ta gefe hade da dan kwalin shi da gyalen shi,,,
   A hankali tadauko rigar ta zura a jikin ta, ta gyara tsayuwar rigar cifcif a jikin ta ,
  Ta mika hannu ta dauko dankwalin ta fara daurawa a kan ta,
   Batafi minti shidda ba taga komai takara feshe jikinta da turare,har zuwa gyalenta,
  Kinsan da gyale da hijab sun fi daukar kamshi a kayan mace,
   Saboda hatsari mace ta dinga shafa turare a jikin ta yana kawo wa mata breast cancer so sai, wlh,,,,
   Amma idan kin dan sa wa top din ki is ok ko ina ki kabi zaki na kamshi so sai, har na wani lokaci (pls be aware)
   Wasu takalma ta jawo wanda sukayi matching colour da gyalen ta, da yan kunen ta ,,,,
    Tsaye take gaban mirrow tana kare wa kanta kallo,
   A, lokacin wayar ta yai kara cikin sauri ta dauko murmushi tayi don ta san ta bata lokaci,
   Haba Aisha kin san fa cewa ance ba makara don Allah kada kisa a rufe get ba mu shiga ba,
   Daidai lokacin ta rufe kofar dakin ta, don gudun kada yan kan,nen ta su shiga mata cikin dakin suyi mata barna,
    A kofan gidan nasu ta iske Amina kawar ta cikin motar saurayin ta suna jiran ta,
   Baka jin komai a motar sai sautin kida dake tashi kamar kune mutum zai fashe,
  Duk inda suka bi dule a waige su don jin,karar kidan motar da ya hayhake ko ina,
   Tunda ta shiga motar gaisuwa kawai ya hadasu da saurayin Amina
  Ba su tsaya ba sai wani mating wuri da aka killance a rubuta da manyar haruffa, kamar haka,
   SAFARA MOTEL,,,,,,
Sai wasu yan kananin gloves da ke haska wanan rubutun yana bada launi kalakala,
   Duk saurin da sukeyi sun makara don sun samu an rufe get, ko,,,
   Komawa Aisha tayi baya tadan jin gina bayan ta da mota, da sukazo da ita,
  Tunda har an rufe get yanzu dole sai ta samu partner da zasu shi ga,
   Sauriyi Amina ne keta faman zirga zirga bidan wanda yadace ya hada Aisha Sanda da shi,
   Sanin halinta na zama first class ya sa bai yi gigin hada ta da kowa ba,
    Wata mota ce ta dan no inda suke tsaye tunda ganisa kaji engine din motar kasan yar lafiya ce,
  Rangerover sport, ce ta dan no tun daga nesa aka kashe mai ido da hasken motar,
   Duk da bai san kowaye ba aciki yasan wanda yasan shine,
   Don haka yai tsaye guri guda har na cikin motar ya fito
  KB ne yafara fitowa ta gefen mai zaman, banza,sai kuma Jibrin wanda ya balle, marifin motar baya ,ya fito,
   Tunda ga nesa ya gane su KB don haka yasan cewa,
  Yanzu za ai solving din problem din su, ma,ana Aisha ta samu irin da zai hada su,
  Joseph ne yafito karshe sanye yake da dinkin shadda mai ruwan makuba ,
  Sai sarkar gold da zoben gold din guda biyu a hannun shi,
   A hankali yake takowa har zuwa in,da su KB suke tsaye da Lawal abokin su,
  Hannu sukayi da lawal din inda ba bata lokaci lawal ke fada ma su bukatar shi,
   Ya na mai nuna Aisha inda take tsaye, cikin second duk suga wai amma banda Joseph, wanda kamar ma bai gane may ake nufi ba,
  Inda lawal yaci gaba da fadin sun bar pass din su, a gida ne gurin sauri,
  KB ne ya waiga inda Joseph ke tsaye yana kallon ya ce,
  Man wanan taimakon ka ne, pls
  Cikin nuna rashin ganewa yake kara tambayar su, komai zai mata nan dai KB yakara mai bayani,
  Kafadar shi dan daga alamar ba damuwa ai,
  Shigowan su a cikin dakin taron ya haskaka so sai don mai MC yai announcement din shigowar su kamar yadda idan wasu sun shigo ake cewa ga yan kungiyar kaza nan sun iso,
   Kallo ya koma gare sai kuma dan kus kus yatashi a gurin kamar yadda aka saba, inda anga kirstan na shiga cikin musullumai adinga a queuzing din su ta hanyar da bai dace ba,
   Wanda yin haka najawo  ma su sanyin gwiwa, so sai,
   Mafi yawan mutane sai mamakin Aisha sanda sukeyi a cikin su ke don sanin cewa sunan ta na cikin fitattun yamatan da ke tashe agari,
   Kuma gashi kayan ta sundanyi shigen kala da na jikin Joseph din wanda shi bai ko dago da hakan ba,
   Zaman su bada wani dadewa aka fara program din bukin,
  Ana aka fara gudanar da abubuwan da aka tsara  a gurin,
   Zaune Joseph yake yadan tokare habar shi da hannayen shi dukka biyu,
  Yana kallon yadda ake guda nar da bukin abokin su, wanda yai aure,,,
  Wani can wanda Joseph din bai sani ba yazo ya ja KB da hira har suka bar kujerar,
   Jibrin dake gefe a zaune wayar shi taikara bayajin may ake cewa don haka ya tashi yadan koma can ta waje kadan ko zai ji kiran,,,
  Yanzu,daga Aisha sai Joseph ke zaune, a inda aka tanadar masu, suke zaune,
   Daga inda KB yake suna magana ya jiyo muryan MC na cewa ana bukata Joseph da Aisha su fito su taya ango farin ciki,
   Saida KB ya dafe kai don yasan cewa da wuya Joseph din ya fito tunda baida masaniyar hakan,,
  MC nata nata abinda akace text kb yayo mai cewa yafirmta dashi da yari yar nan suyi rawa,
   Kamar kada ya tashi sai yatuna cewa bazai kyautawa angon ba inda har bai fita ba don haka ya fara mikewa batare da ya kalleta ba yace mata sai ki tashi mu fita ko,
  Ba wani rawa sukayi ba sosai amma anji dadin fitar nasu don Joseph ya nuna kulawar shi ga ango,,
   Wasu yan mata dake ge fe zaune suna kallon yadda ake ta
  Su ka fara yan suraitai kamar haka,
  Au dama wanan  ba musullumi bane ke inji wa ya fada maki,
  Dayar tace bakiji lokacin da ake cewa ana son Yusuf Joseph yafito tare da,Aisha sanda
  Sai gudan tace kai amma anyi harasa wallahi guy kamar wanan kuma bai sallah,
   Dayar tace gaskiya ni saima kawai naji haushin shi ya kamani wallahi, ita kuma Aisha don kwadai sai wani shige mai  take ta yi,
  Wace ita ce cikon ta hudun masu hiran da tun da suka fara zance bata ce kala ba,
  Tace kai ku dai na daukar wa kan ku wahala ma,
  Iyaka,ku da shi kuyi mashi fatan alherin shiga cikin islama indan har yana da rabon shiryuwa, Allah yasa yagane gaskiya yadawo hanya,
   Sai ta farkon tai caraf ta ce a haka ?
  Wanan ai yai nisa baya jin kira, in bashi ba ai tun yana yaro da ya musulunta, ko,,,,,
 Ita dai wace bata maganar sai cewa ta yi ai abin daga Allah ne kawai, in Allah ya nufe shi da shiryuwa saiko ya shiru, yadawo hanya,
  Haka dai kusan ko wani kujera suke ta zancen su kamar yadda gurin buki ya tana da
  Kai kana kallon wani wani yana kallon ka,
    Ganin cewa dare ya fara yasa Joseph yai su KB magana akan cewa su zo su tafi don shi baya  yin dare sosai a waje,
  Don duk haka tarbiyar yaran IBO suke duk ganin kada su basu yarda,su kai karfe takwas na dare waje,
   Wana na daga cikin irin tarbiyar da suke wa yaran su,
  Idan kuma sana,a ce bakin karfe shidda andawo gida ke nan daga gurin sana,a,
   Saidai kuma tun karfe bakwai na safe anbar gida ke nan zuwa gurin bidar kude, (Allah ya kyauta)
  Wanan haduwar da Joseph yayi da Aisha itace silar haduwar su,
  Don tun a gurin da ta ce ya ara mata waya takira kawar ta don su wuce tasamu nobar shi,,,
  Da zai tafi ma lake mai tayi akan ya bata lift zuwa gida saboda dare yayi a cewar ta,
   Anan yabar su KB daga shi sai Aish sanda suka kamo hanyar zuwa gida,
    Da kwatance tai ta yi mai har suka iso gidan su, Aisha din,
   Koda ya Parker motar shi bai ce mata komai ba sai jiran yakeyi tafi ta yasamu ya wuce
  Ita ta tsaya wani yanga kamar wace bata da lakka ajikin ta
  A hankali ta dan waiga inda yake tana cewa nagode fa,sai wani lokaci ke nan kuma ,
   Kai ya kada mata yana mai cewa No ba matsala ai ,,
  Tana fita yafigi motar shi da karfi yabar uguwar zuwa, gidan su,,,,,,,,
 
  Gudu yake shararawa a motar shi tanyar ta zuwa kudu, don kirar da yasa na gagawa daga abokan sanar shi saboda meeting din da zasu yi don kara wa mai farashi saboda harajin da gwaunati ta saka masu,
    Shi kadai ne a cikin motar sai kidar da ya sa nawakar wani dan yaren su inda yake wa egwaii of Benin kirara,
   Wayar shi dake gefen shi tai babirashon, hannu ya mija yadauko wayar hankali shi na saman titin kadan don yafara jin kamshin okene,
   Ganin bakuwar noba yayi acikin wayar shi dan mamaki ya baiyana a fuskan shi kadan,
  Don gani bakuwar nobar kuma yasan cewa wanan wayar sai special mutanen sa ke kiran shi da ita,
   Kamar ya aje saidai ya dauka yana mai karata a kunen shi,
  Muryan mace yaji tana mai sallama a cikin hausa,
  Cire wayar yayi yadaga yana kallo don shi a bin ya bashi mamaki so sai wallahi,
  Sai kuma yace kila wrong noba ce,
   Karakara wayar yayi a kunen shi don yace is wrong noba,
  Saida abin mamaki daidai lokacin da ya kara wayar akunen shi a lokacin ne, yaji mai maganar tana cewa
  Yakake Joseph ?
Mamaki karara a fuskan shi ya ansa mata da lafiya,
  Wake magana ya ke tambaya cikin mamaki, saida tai yar murmushi har yana jinta daga inda yake
  Tace kana magana da Aisha Sanda ce,
  Aisha Sanda ?
Joseph ya kara nanata sunan cikin mamaki a fili
  Tace mai eh
 Wace kuka hadu a wurin dinner din hamza har ka kaini gida,
  Ok ok yace nagane ya kuke ta amsa mai da lafiya lau,
  Yau nake tambayar KB kai yace min ka wuce sai tadan shake muryan ta kamar mai shirin kuka,
   Tace shine bakazo munyi sallama ba katafi, ?
  Maganar ta ba shi mamaki sosai don dai ya san cewa bawai wani sanin juna sukayi ba ko sabawa,
  Amma sai kawai yadake duk da cikin mamakinta yake , ya ce , mata just sorry,
  Kamar ta na ganin shi kai kawai ta gyada mai kamar yana ganin ta a fili,,
  Wani irin ajiyar zuciya yayi yana mamakin maganar ta acikin zuciyar shi,,,
  Ita ko Aisha wani irin shu,umin murmushi tayi bayan sun aje wayan azuciyar ta tana kiyasta abinda, take planing akai,,,,
 
   Tsaye yake a cikin wani ma,aikatar tatan man petroleum, da ke kudu, yana son idon shi ya tabbatar mai da ko mota nawa daga con n motocin su , suka shigo,
  Wayar shi tai kara noba ce ya gani babu suna don haka bai san mai wanan nobar ba,
  Yadauka yana mai cewa hello,
  Aka ansa mai adayar bangaren, jin muryan mace kuma ba hausa tana cewa
  Hello mun wuni lafiya ya   kwana biyu ?
  Hello wake magana yace
  Mamaki ne ya kama Aisha jin cewa har yanzu ashe bata  shiga ba,
  Ansa mai tayi da cewa Aisha ce daga KG,
  Dan shiru ya biyo baya kadan sai can yake ce mata ok nagane
  Pls ki bani dan lokaci zan kira ina aiki yanzu pls
  Ba matsala race tana mai aje wayar cikin jin takai ci,
   Amina wace ke kwance gefen ta har tagama wayar ta numfasa tace wallahi Aisha kina bani mamaki
  Cikin dan jingina bayan ta da bangon dakin da suke zaune tace agani ki ko,
  Amina tace a ganin kowa ma,
  Kin fasan cewa ba musulmi bane wanan guy din don may zaki nace a kan shi dole sai kinyi halak da shi,
  Daidai lokacin ta dauko wani abin gyara kumba daga cikin jakar ta,
  Tafara dan kankare kumbar hannunta da abin sai can kamar bazatai magana ba tace
  Kina nufin don ba musullumi bane bazan yagi rabo na ba ke nan,
  Cikin mamaki kawar nata ke kallon ta don Aishan ta ba ta mamaki kwarai ta ya zatai mu,amula da wanda ba musullumi ba,
  Gaskiya ita bazata iya ba, iyakar harkan ta ga musulumai yan uwanta,,,
  Saboda yawan matsin da take mai dole yafara dan sakin jikin shi da ita har suna dan hira jefi jefi a waya,

  Tafe take ciki uniform din su na girls day secondary school, sauri takeyi don ta isa gida, saboda ta samu ta shirya da wuri zuwa islamiya,
  Don a kwaita da tsoron bugu bata son abinda ya tabi lafiyan jikin ta sam
   Wasu "yan matane mutum biyu cikin shiga ta isa da nuna lokaci ke tafiya,
   Tafiyar ta takeyi cikin sauri yasa sukayi kusan yin karo da daya daga cikin yan matan ne tai karfin halin cewa haba malam wani irin tafiya ne kikeyi babu ko tsari balle ki nuna ajin cewa ke ma mace ce,
  Maryam wace duk saurin da takeyi bai hana ta tsaya wa guri guda ba cak,,,,
  A hankali ta juya inda suke tadan kalle su murya a raunane tana mai cewa kuyi hakuri pls ban san cewa gurin ba zai muna bane,
  Daga haka ta juya batare da ta kara cewa uffan bata ci gaba da tafiya sai dai maganar na kona mata zuciya,
 Don may zasu ce ita bata da aji kodon batasa bujen da ya manne mata jiki bane, shine rashin wayewar da suke hange a gareta,


ZEEE MAKAWA
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
  FUREN    JUJI
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
             8鈨�
ZAINAB IDRIS MAKAWA



  Duk wani members din churching Catholicis suna zaune a gurin meeting din da,suka gaiyaci Mr Emanuel,
   Bayan pastor yayi gyaran murya  alamar kowa ya yi shiru
  Gaisuwa yafara kamar yadda sukeyi idan anyi wanan taron,
   Shiru gurin yayi nawani dan lokaci can pastor yakira sunan Mr Emanuel alamar suna da magana dashi ke nan,
  Hakan yasa Mr Emanuel ya maida hankalinshi da kyau don jin abinda za,a fada,
   Wanan taron munyi shine saboda kai da dan ka,
  Kai kawai Mr. Ema yadan kada alamar gam suwa,
   Yaron ka alamun sun nuna muna cewa baya son hurda da yan uwan shi Christan
  Sai yaran hausawa wanda muna gudun hakan ya jawo muna abin kunya nan gaba ,
  Hannu Mr Ema yadaga sama yai wani kyatawa yai round da hannun a kanshi yace
  Kai abomination, god forbid,
   Ya buga kafarshi a kasa
  Yace dat will never happen
 Never pastor never,
  Nan da nan jikin shi ya dauki rawa yana cewa imba
  Never sai kafa da yake kadawa ya tabure fuska dagani duk ran shi a bace yake kamar zai fashe,,,,
   Suma wurin sauran mutane sai fadin ra,ayin su sukeyi akan zance,
  Wani daga cikin su ne yamike inda yai yar gyaran murya yana cewa yana son cometi su ta diba da kyau tai nazarin ko waye Joseph,,,
  Yace shi a nashi halin Joseph ba zai yi haka na ba ,saboda yana da tunane so sai,
  Yace ai akwai wa yanda suna da kudi sosai daga cikin su amma idan anyi la,akari ko Church ba su zuwa yanzu,
  Amma shi in har yana gari yana attending din Church tare da su,,,
  Shi a ganin shi rayuwar shi ce hakana ta taimako mutane,
  Saboda in sun diba ai yanuna wa yanda ke zaune saman benci tare da su da hannu yace,
   Joseph na nin su har gida ya tai maka masu time to time,
  Yace ko ba haka bane, sukace gaskiya ne, hakane,
  Yace to shi yana ganin cewa wanan halin nashi haka take duk wanda yake tare da shi yana taimaka mai,
   Mr Ema dake gefe yatokare hannun shi da sanda hular shi ta gwalmade gefe guda sai kafa kawai yake buga wa a kasa,
   Jin jawabin na Mr Okarpo yasa gurin ya kara daukar hayaniya, so sai wanan karon,
   Mutane da yawa daga cikin su suka kawo shawaran cewa Joseph yaron kirkine,
  Shi yasa yake tare da duk wani wanda tunda suns tare ,,
   Don ya na taimakawa hausawa ba shine zai sa a ce yana son yin wani abinda ba daidai ba,
  Amma duk da haka su elders zasu kirashi su tsawata mai akan hakan,
  Da wanan shawaran taron ya watse kowa na fadar albarkacin bakinshi,,,
   Tunda Mr Emanuel yadawo daga gurin meeting din rayuwar shi take bace saboda shi a ganin shi an wa dan shi kullin sheri
  Saboda kawai cigaban da ake ganin ya samu,
  In bashi ba taya zasu dangata shi da wani akida cen,
  Yan uwan shi kaf ba musulumi ko wani akida ta daban,
  In ma hakane zaiwa Joseph din fada ya daina shigowa kwantagora gaba daya,
  Yana yi yana tula giya a cup yana shan ye wa kamar wanda bai da kimar ciki,,,
 
     Duk wani abinda zata bukata ta shirya shi a cikin dan kit din da tadauka don tafiya,
  Batare da ta fadawa koda Amina ba zatai wanan tafiyar da zatayi yau,
  Saida ta gama shirin ta tsab sanan ta fita tsakar gida inda, inda inna ke zaune bakin murhun ta na kasa tana gyara wuta ga koko a cikin wani dan roba mai marfi wanda ke nuna abinda ke a robar fili,
  Ganin Aisha waje da safen nan yasa inna cewa, wa azubo maki kokon ne ?
  Tawani ya mutsa fuska kamar wace akaiwa tayin kashi tace kai haba inna da safen nan haka,
  Kujera ta jawo gefen inna ta zauna tana fada ma inna cewa zata kauye gurin kakar su ta dibo ta,
  Shiru inna tayi cikin zargi take kallon yar nata wace ke magana cikin matse fuska sai kace aiba uwar ta take zance da ita ba,
    Har ta mike uwar tace kwana nawa zakiyi saida takai kofan dakin ta ce batare da ta waigo ba,
  Sai lokacin da kuka ganni kawai inna,
  Daga haka tashige tadauko dan kit troler din da ta shirya kayan ta aciki,,
  Tashan hanyar BCG ta nufa tana zuwa ana cewa Minna Abuja kaduna,
  Abuja tace kawai kai tsaye aka karbi dan troler kit din ta a ka nufin motar dake kan layi,,,,
  Musalin karfe ukun rana ta isa Abuja, wayar ta taciro takira layin shi,
  Kira nabiyu yadaga layin yana mai cewa hlo, cikin wata irin murya ta ke magana kamar ta mai shagwaba,
  Joe gani a Dikko fa,
 Cikon mamaki yace mata Dikko fa Aisha tace mai eh ,
  Kwatancen inda zata sauka, ta, tsaya yai mata, yace zai turo azo adauke ta,
   Joseph yayi maki kwarai da jin cewa wai gata a dikko, bayan jiya sukai waya yake ce mata yana Abuja yazo yin wani dan aiki ne ,
   Sai gashi kawai yana fitowa daga gurin meeting kiranta ya shigo mai,
  Wata mota mai kama da, Box ta faka a gaban ta kau da kai tayi kamar bata gasu ba,
  Sai hon da taji yai yawa yadan sata waigawa, driver motar ke ce mata itace Aisha ko ta karba mai ya nuna mata complement card din Joseph
  Hskan yasa ta yarda da shi ta shiga motar bayan ya bude bayan motar yasa mata kayan ta ciki,,,
   Wani gida mai hawa biyu suka shiga gidan bawani fadin fili ke gare shi ba amma ko kafin ka shiga kaima kasan cewa hadaden gida ne,
   Da,sallamar ta ta shiga don duk ta rude da gani daular duniya da ta gani,
  Jin da tayi yana ce mata hy Aisha,,u are, wel,come,
  Daidai lokacin da yake saukowa daga steps din gidan,
  Yar murmushi ta sakar mai tana wani nuna kamar alamar jin kunya,
  Zuwa yayi inda take tsaye yai dan hugging din ta yana mai ce mata bukin surprise ke nan,
   Kujera ya nuna mata ta zauna daidai lokacin mai aikin shi yashigo dauke da trey da drinks a ciki, sai cups guda biyu, a sama,,,
   Shi da kan shi Joseph din ya zuba mata drink din a cikin cup dai dai lokacin kuma yake tambayar ta ina kawar ta wanan karon,
  Tana karban cup din da yake miko mata ta ce, ba wanda yasan cewa nazo gurin ka fa,
  Cikin nuna mamaki yafada cikin yar muryan nan tashi, yace saboda may,
  Ta dan daga kafadar ta tace Just,
  Tace ban son kowa yasan cewa nazo gurin ka, shi yasa tadan kare zancen acikin yar shagwaba,,,,
   Bayan tai wanka ta kimtsa jikin ta wani dan kwalba ta dauko a can kasar handbag din ta,
  Wani dan ruwa ne aciki blue kamar ruwan turare ta dan shafa kadan a saman maranta,
   Sai kuma saman goshin ta daidai tsakiya ta man,na kadan,
    Body spray ta feshe jikin ta da shi mai mugun kam shi na ,
   Wani ribon ta dauko daga cikin handbag dinta, tadan feshe shi da kamshi ta daure kanta da shi,,,
  Duk da tana da gajiyar tafiya a tare da ita, hakan bai hanata binshi zuwa cikin gari ba,
   Sahad store ya nufa da ita inda ya bata damar daukar duk wani abinda take bukata yakuma ce mata kada taji komai,,
  Cikin yar kunya take zabar yan abubuwa kamar wace bata so, Joseph na tsaye gefe yana kallon ta,
  Ganin zata bata mai lokaci yasa shi kwasan mata abubuwar da mata ke yawan amfani da su,
  Kamar su manshafi turare, kayan makeup, sai kuma ya juya yanufi fannin sutura,
  Sayayyan alfarma yai mata,a wurin sai turamen zannuwa da ya jido kamar mai hada kayan lefe,
   Jin bills din kudin saida ya sa Aisha dan kaduwa amma sai taga kawai ya biya batare da jin darrr ba,
  Mamaki fal a zuciyar ta don bata taba zaton koda quarter haka ba, daga kowani irin mutum,
   Sai wurin kayan kwalama da suka nufa inda nan ma ba karamin kudi ya kashe mata ba,
   Wani Guy dake gefe ya ya matso kusa da inda suke tsaye yana cewa sannun ku da,zuwa ya hanya,
  Idan kuna son dinki express ga shagon mu nan zaku samu zuwa gobe insha Allah,
   Joseph ya dan kalli inda Aisha taja tai tsaye yana mai tambayar ta tana bukatar dinki, ne, kai ta gyada mai alamar eh
  Cikin turamay da suka sayo suka bada guda biyar, dinki, akan dubu Ashirin,
   Babata lokaci ya biya guy din sai yabasu nobar da kuma, card wanda zasu zo karba,
    Daga haka suka wuce zuwa gida da kaya niki niki,
   A,falo suka zube nan mai aikin gidan yakawo masu plate, tare da drinks da su, cultularies,
  A hankali take komai don abinda take gani ya wuce tsanmanin ta,,,
   A daki guda suka kwanta ita, da Joseph duk yadda Aisha take ganin ita yar bariki ce ta katsewa wa Joseph,
   Saida ta kwana da dimbin mamakin irin halin Joseph ,
  Duk yadda taso tambayar shi ba fuska saboda bala,in kwarji da yake mata, a idon ta,
 Kwanan ta hudu Abuja tare da Joseph iyakar shi da ita romance kawai da nuna concern a kanta,
  Kamar yadda ba ta fadawa Amina cewa ta na, Abuja ba shima Joseph, din bai fadawa kowa zancen zuwar ta ba, gurin shi,,,
  Mota ya bayar aka,dawo da ita har kwantagora, tare da kaya da ya saya mata, niki niki, ,,,
  Wa,iyazu billah yar musulumai zamani ke nan babu ruwan da dataraiya da kowani irin mutum ita dai kawai ta samu kudi shine gurin ta,
     Yadda ta canza kawai yasa Amina gane cewa gurin Joseph ta tafi,
  Cike da mamakinta take kallon ta don ganin irin abinda take fitar wa,
  Cikin dan rada take, cewa Aisha mutumiyar har kin fara bani tsoro wallahi don kin wuce sani na,
   Tana kokarin jera, kayan makeup din ta a mirrow dakinta ne tai yar dariya, tace da nai may fa,?
   Haba haba inji Amina Aisha ace har kuma Royce din mu ya wuce ga hausawa musulumai yan uwan mu ya koma ga Christian, haba dai haba gaskiya hakan baiyi ba,
   Wani irin kallo ta watso ma Amina daidai lokacin da ta bude akwantin da tashigo dashi,
  Kayan da Amina tagani ciki fam shi yasa ta kara zare ido waje,
   Tace, shin Aisha kina nufin ,,,,,, nuna kayan tayi da dan yatsanta don tama kasa furta ko a,
  Kwarai kuwa inji Aisha tana mai gyada ma Amina kai, tace
  Uban wa zai bani wanan koda kuwa sau nawa ina bin mutum motar shi ko wani mafaka
 Amma kinga wanan tana nuna kayan da hannun ta tace a free wallahi na,samay su Amina,,,,
   Ido waje Aminat ke kallonta cikin mamaki tace a free fa ?
   tace wallahi ko,
  Amma dai gaskiya mutane ba zasu gane cewa babu wani alaka atsakanin ku mai zurfi,
  Ina ruwana da mutane inji, Aisha, duk abinda zasu fada suyi ta fada mana,
   Manja da doyan da Irish da, tazo dashi ta dibar ma Amina mai yawa,
    Ita dai Amina sai mamakin kawar nata takeyi kawai,
   Ace yanzu har da arna suke mu,amula, kai gaskiya Aisha tayi nisa wallahi,,,
   Don haka, taja bakinta tai shiru kawai batare da tafadawa kowa,ba ita dai tasan cewa duniya ce zata fada ,,,,,
 
     Tsaye yake yana waya da kanin shi, Samuel wanda ke zaune tare da baban su a kwantagora inda Samuel ke fada ma Joseph meeting din da elders sukayi a kan shi,
  Yai mamaki matuka da jin zancen Samuel din don yasan cewa yana ikar kokarin shigurin ganin cewa ya kyautata wa Church din na su,
   Badon komai ba saidon kawai ya kare martaban gidan su daga alumar su,
    Cike da mamaki yasake tambayar Samuel labarin  mahaifin su,
  Dan shiru Samuel din yayi kadan kafin can,yace yana nan saidai gaskiya maganar tadan tayar mai da hankali,shi, 
   Kai kawai ya girgiza yana mai shafan fusakan shi in akwai abinda ya tsana yanzu shine yaga bacin ran mahaifin shi,,
  Sallama yayi wa Samuel din yana mai jin haushi elders din na su, akan jefa mai mahaifi cikin damuwa,
  Shin ina ma ruwan su dashi dazasu sa mai ido a harkokin shi,
   Yasan cewa koda ya kira mahaifin shi ba wani maganar da zai ji a gamay da elders din,
   A karshe ma yana iya ganin laifin Samuel da ya fada mai, zancen,
   Tun yana tuna zancen har ya share maganar, gurin fridge ya nufa yadauko goran ruwa, ya tutula ma cikin shi,har saida ya zuke gora guda gaba daya ya wurgat da rubo, a dustbin,
   Kiran wani Michael ne ya shigo mai a lokacin inda yake sheda mai cewa yason su hadu saboda maganar man Gas dayake son suyi a lokacin,
   Michael mutum ne mai iyali shi duk da bawani babban mutum bane sosai,
    Yasamu Michael da yaran shi suna wasan basketball, agidan shi
  Yaran naganin shi sukayo wajen shida gudu suna mai oyoyo,
  Rungumay su yai cikin jikin shi ya na dan shafa masu kumatun su,
  Sun san zuwan shi gidan su alherine don haka ledar Sweet din da ya riko masu ya mika masu,
 Murna da ihu suka hau yi suka shige cikin gidanan su binsu yayi da kallo
  Nan take alkawarin da yaiwa Assalam ya fado mai arai,
  Don yasan cewa yaro baya man,ta alkawari duk lokacin da yaga wanda yai mai alkawari bai cika ba sai ya tuna,,
  Don haka ya kudurta a ranshi cewa da yabar gidan mic zai wuce yaiwa Assalam sayayan shi ne,,,,,,



 ZEEE.  MAKAWA
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
   FUREN   JUJI
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
             9鈨�

ZAINAB IDRIS MAKAWA


  Yau gidan Anty Dije baka jin komai sai kamshin girke, girke ke tashi kala,kala,
  Duk wanan kamshin anayin shi a kan maigidan da zaidawo yau daga gurin aikin shi can garin Lagos,
  Tun jiya ya bugo masu waya yana mai sheda masu cewa yau zai iso, sanin da sukayi cewa ysna saman  hanya,
  Yasa su wanan girke girke da kara gyara gida duk da dai gidan nasu ko yau she fes yake,bazakace akwai yara agidan ba,
   Bayan sun kammala aiyuman su ne sun gyara guri sai kuma,suka shiga gyaran jikin su,
  Duk da zaman Iliyasu ma,aikacin custom ne hakan bai sa ya wadatar da matar shi da komai ba,
  Don dai da ka ganta kasan cewa zaman hakkuri takeyi kawai, don babu wani kama na nuna wadata atare da ita,
    Allah yasa mata hakkuri da dauri sosai don sam baka taba gane halin da take ciki,
   Cikin wanan halin hakkurin da takeyi bai hana yan uwan mijin ta,sata gaba ba da fitina
  Don su gani sukeyi ai duk wani bida na Iliyasu yana gurin Anty Dije da yan uwanta,
  Idan suna wanan zancen bata bata ranta saidai tayi murmushi kawai,
  Don takan ji dafin rashin gane sirinta da basuyi ba har suke ganin cewa komai na hannunta,
 Basu san cewa dan uwan su ne mai laifi ba,
  Harkokin shi kawai yake yi a can bariki abin shi,
 
     Maryan zaune tana kwalliya a gaban madubi da ke kuryan dakin anty Dije
  Wanda har in tana son yin kwalliya mai tsayi dole sai ta shiga har kuryan dakin na anty Dije,
  Sauri take yi ta tafi karbo ma anty Dije dinkun nan ta a uguwar Rimaye,
  Waje wata yar uwar maman su Anty Dije din don matar ta iya dinkin zamani sosai,
 Atamfar code,viore ne mai ruwan makuba da milk, ajikin ta,
   Dinkin riga da zani ce tai daurin baya ta kulle shi a tsakiyar baya,
  Turaren Anty Dije tadan fesa kadan
  ,  Saida tagama hada komai tadauko dan wani karamin hijabin ta, ta sa sai takalman Bella, da tasa, a kafar ta,
   Cikin yar muryan nan nata take sallamar Anty Dije a hankali don gudun Issalam kada taji ta tace zata bita,
  Don ance tayi sauri ta dawo, dawuri saboda kila dasu anty zatayi amfani
   A gidan mama Asabe tasa mu bata karasa hada dinkin ba don haka tabukaci mama Asabe ta bugawa Anty Dije ways ta sanar mata cewa da dan saura kadan kafin a karasa,
   Tana zaune tana jiran dinkin saiga wata budurwa yar gayu ta shigo gidan
  Daganin yadda sukeyi da mama Asabe kasan sun saba sosai,
   Inda maryam take zaune budurwar takalla tace ma mama Asabe
  Asabe ina kika samo wanan yar budurwan mai kyauwo haka,
   Saida mama Asabe tadan kalli gefen da maryan take zaune tana mai ci gaba da dinkinta tace,
  Diya tace, tazo karban dinkin su ne
   Kanyan anty da ake dinkawa tadan taba sanan ta kai zaune saman kujerar roba fara dake dakin da mama Asaben take dinki a ciki,
  Turamay zani tafitar guda biyu masu ba,lain kyau daga cikin bakar ledar da tashigo da shi a hannu,
  Kai inji mama Asabe amma dai wanan zanin akwai kyau wallahi kamar su sukayi kan su,
   Budurwan tana wani ya mutse fuska tace niko kinga Asabe zanin bai suyi min kyau ba
  Kodon bani kawai akayi shiyasa ban ga kyaun shi ba,
  Mama tana dinki ta ce kedai yar rainin wayo ce taya za,a baki abu kice kin raina,
  Amina halinki sai ke wallahi,
  Ai ma, mutum abin arziki irin wanan zukakan zanuwar haka ki ce wai ke basuyi maki ba,
   Gyalen da ta yafa ta kwabe, ta koma, daga ita sai wata yar rigar t,shirt ajikin ta,
  Ta mike ta bude fridge din mama Asabe ta dauko roban ruwan Goje water tadan fara kwakwada,
  Maryam dake zaune gefe tana mamaki da kallon ikon Allah,
   A, ranta tace wanan duk cikin wayewa ne haka kuma,
   Ka cire hijab a gidan mutane, idan maigidan yafado fa ya zatayi,
  Muryan Amina yadawo da ita daga tunanen da takeyi
   Amina ke cewa mama Asabe bayan ta gama shan ruwan da tadauko a fridge,
  Tsaraban Aisha ne fa Aisha mama Asabe, ta tambaya da mamaki,
    Ita fa inji Amina kinsan ta da,kwashe kwashe, wani dan Arne ta samu yake kashe mata kudi haka,
  Arne fa inji mama Asabe mai dinki, Amina tace wallahi ke dai,
   Niko bayerabe ne musullumi ai ban iya zama da shi balle iyamuri kirsta,
  Mama Asabe tace ke ko indai musullumi ne ai ba matsala, tunda Allah bai hana aure a tsakani ba
  Amma ace kirsta gaskiya abin baiyi ba,
   Amina tai wani irin turo baki tana mai daga kafada da watsar da hannayen ta alamar nuna oho ba ruwan ta,
   Mama Asabe tace amma dai Amina nagane zancen ki har da kushi a ciki
  Nan gardama ya kaule masu tsakanin ita da mama Asabe
  Daidai lokacin da mama tagama hada dinki tana kokarin nikewa tasa a cikin leda ta miko ma maryan, din,
  Tamike tana mai ce madu sai anjimar ku, mama tace ku rage min tsarabar Lagos in ankawo maku
  Dariya maryam tayi kawai ta ce to mama zan fada mata in naje,
   Ganin motar Ya Iliyasu a kofar gida ya tabbatar mata da isowan shi, gari,
  Cikin nuna farin ciki da jin dadi ya iso duk daxtasan cewa ba wai wani abu zaizo masu da shi na marmari ba,
  Amma dai tana murna Allah yakawo masu shi lafiya
  Yana zaune saman kujera rungumay da yaran shi ta shigo dan matsakaicin falon nasu,
  Har kasata kai tana mai sannu da zuwa yai yar dariya yace little mummy ance min an aike ki ,
  Tai mai anzo lafiya da murnan ta shima a cikin fara,a yake ansa mata,
  Iyalin iliyasu sun cewa ko ba komai indai har yana gari suna cikin farin ciki a ko yaushe
  Don gidan su yacika da baki masu zuwa da yan bukatun su akai akai,
  Kasan cewar zukatan mutane ya mutu yanzu don ba,a maida roko bakin  komai ba,
  Sai kaga mutum magidanci bai aikin komai sai bin gida,jen masu dan abin hannu ana rokon su, na cefane,
 
   Yau kwansn iliyasu biyu da dawo wagarin don kusan sati guda yake yi idan ya zo garin,
    Zaune suke suna hira shida Anty Dije bayan fitan wasu mata yan uwan shi da suka shigo
  Wani almajiri ne yai, sallama a kofar gida ya ce ana kiran Assalam wai a waje ,
  Daga Anty Dije har mai gidan ta, saida suka kara tambaya cikin mamaki,
  Maryan wace ke kitchen tana kokarin gyara kitchen din
  Zuwa tayi tadan leka don taga kowaye ya aiko kiran Assalam haka,
  Tsaye suke jingine da wata mota mai kamar ruwan kakin soja,
   Dan lekawa,tayi kadan daidai yadda basu ganinta tadawo cikin sauri ,
  A,kofar shiga falo ta hadu da ya iliyasu, da ke kokarin fita waje don yadiba,
  Duk kan su maryam suke kallo don jin ko waye a wajen,
  Inda Anty Dije take tsaye ta nufa tace cikin murya kasakasa wanan mutumin ne fa wanda Assalam yake lakewa,
  Iliyasu da ke tsaye ke tambayar maryam waye ne a wajen wai,
  Murya cikin taushi anty Dije tace wanan abokin jibrin din gidan baba bala dana fadama,
  Kasancewa duk wani abu mai muhinmanci sai anty ta fadawa mijn ta don gudun zargi,
  Dan shiru yayi can kuma sai yakama hanyar wajen
  Basufi minti koda uku ba sai gasu sun shigo cikin gidan duk kan su,
  Shi maigidan shi ne gaba, sai su biyu a bayan shi,,
   Ya iliyasu nacewa jibrin nadauka ma ko wani bako ne da naga ka tsaya a waje kana cewa wai akira ma Assalam,
  Bayan sun zauna a falo ne suka dan taba hira a tsakanin su inda aka gabatar masu da abinci,
  Duk da Joseph baiso cin abincin ba am a saida ya illiyasu yasa shi ci
  Sannu sanu daga hiran su yafara sake jiki har zuwa lojacin da Assalam suka dawo daga gidan kakan nin su,
   Dagudu Assalam ya fada jikin Joseph yana murna,
  Batare da yai magana da kowa ba ya mike tsam rike da hannun Assalam zuwa gurin motar shi waje,
  Sai a lokacin Ya Illiyasu yake tambayan jibrin ko waye Joseph din,
  Nai yai mai kwatance da mahaifin shi da kuma mahaifiyar, shi,
  Saidai bai fada mai ko waye Joseph din ba ayanzu
  Yadai bashi labarin haduwar su da Assalam har yadda jinin su ya hadu,
  Lokaci guda don yace ma ya illiyasu kusan ko yaushe su kayi waya sai yatambaye shi labarin sturbonboy,
 Abinda da da mahaifi, duk mai son mutun akace yaso dan shi,
   Hakan yasa ya illisu jin dadi har a cikin zuciyar shi,
  Ganin su mukayi Assalam da kaya nike nike sun shigo harda keken yara,
 Gaba daya muma fito waje muna kallon wanan irin shakuwar
  Bayan sun aje kayan ne yaya yagaiyace su cin abin cin dare a gidan shi,
  Joseph din yaso ya doje yaki zuwa saboda yana son ya shiga evening services yau,
  Amma ba yadda ya iya kawai sai ya amsa gaiyatar yaya din,
   Saidai su uku suka zo tare da KB akazo wanan karon,
  Abincin hausawa mukayi yau tuwon shinkafa fara da miyar Alaihu da yakuwa, sai yar kabewa da mukasa da busashen kifi,
  Mundauka cewa baza suci abincin ba sai gadhi duk an cinye sai kwano kawai,
   Duk kan su sunyi mamakin ganin anyi girkin mutanen da a gidan matashi kamar ya iliyasu,
  Saboda sanin da sukayi yanzu kiuyya bai bari mata suyi girki mai kama ciki, da dare,
   Saidai kawai aima namiji taliya ko indomie da dare ko dafa duka,
    Saboda kiuyyuya kawai, don kada a motsa jiki,
  Hira sosai sukeyi yan sungama cin abincin kamar sun dade da sabawa da junar su,
  Shiko Assalam yana manne a jikin Joseph har yai barci,zuwan wanan lokacin,
  Ganin haka ya iliyasu yaba Joseph bakin cewa duk lokacin da yazo kuma yana son ganin Assalam yashigo kawai gurin anty Dije,
   Kuma miyar da yace yana so na hausawa yadinga fada mata ai mai, irin da yake so,
    Wanan shine silar kara shakuwar yan gidan su Anty Dije da  Joseph,
 


ZEEE MAKAWA
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
  FUREN     JUJI
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯


 ZAINAB  IDRIS MAKAWA,


   Zaune suke a majalisar su,inda suke hira duk marance ( yamma ) akantitin B C G titin da ya mike zuwa kaduna , minna Abuja tare da,wasu yan kauyu kar dake hanyar,
   Duk marance a nan su KB ke yada zangon su, suyi ta hira ko aita shan matar juna a tsakanin su,
   Wanan abin ko yaushe yana kara burge Joseph don saman yan yaren su basu da lokacin hakan ,
  Ko yaushe ana cikin kasu ko bakin titi gurin bidan kudi,
   Yan zun kuma sai dai in har yaso shiga taro saidai ya yaje koda clubs ko kuma wani park ire iren wuraren sheke aya amma ba irin haka ba da hausawa ke yi,
  Shiyasa shi har gobe yana sha,awar tarbiyan bahaushe,
   Joseph jin shi yakeyi kamar bai da wani harkan komai a gaban shi,
   Zuciyar shi na mashi fes a duk lokacin da yake cikin irin wanan yanayin,
  Wani matashi mai suna sulaiman ne yazo sama wata mashin rober,rober yanata,washe baki,
  Ya sayo sabuwar abin hawa, sai sam barka kowa ke mai a lokacin saboda ya huta da yawo a kasa ko saman kabukabu,
   Kowa sai zuwa yakeyi yana duban man shin din cikin kulawa, da yiwa Suleiman fatan alheri,
   Joseph dake waya a lokacin kuma yana kallon su sai abin ya daure mai kai so sai
  Don saboda mashin kawai da ko gabadayan su zai iya sai masu wanda ma yafi wanan tsada suke ta ma suleiman murna haka,
   Sai kawai yaji tausayin su yakara kamashi duk da sunan wai suna aiki gwaunati ke nan amma gashi yar mashin kawai na basu sha,awa,
    Jesus crisis yace a zuciyar shi don ba karamin sa,a ya taka ba shi da Allah ya maishe shi haka cikin su,
  Don ai a da duk tare suka taso kuma yan zun ne yasamu wanan ci gabar duk da dai basu san ko shi waye ba to amma dai sun san yana da shi,
    Muryan Nasir ce tadawo da shi inda yaji Nasir na fadin cewa
  Allah yasa ko yar Suzuki yasamu ya saye shima, hakadai duk sukayi ta hira a tsakanin su inda kowa ke fadin albarkacin bakin shi,
   Har zuwa goma na dare suka kai agurin suna hira sannan KB yadauke shi sama wata rubaban mashin din shi zuwa gida,
   Tun da safe yabar gari ya ko gurin harkokin shi don ci gaban shi,,
  Tunda yadawo yadawo da kudin tallafawa mutane da dama aran shi,
  Din shi a ganin shi duk wanda kuka wahala tare har Allah yabaka samu daga cikin ku to bai kamata ka manta da yan uwa ba,
   Sanar,ar da suka fara shigo da dan yar Gas dama ainihin pure Gas din,
   Gani harkan ta karbu yasa shi yin kokarin gani sun gyara system din business din yadda ya kamata,
 
    Shigowa da mai din kasar arewa yasa shi kawo KB daga cikin wa yanda za,aiwa interview din zama members nan gaba,
  Waya yai ma KB yace su hadu Abuja next week Wednesday, don su dan tatauna, akai,
  KB duk da bai sam komaiba bai yi kasa a gwaiwa ba ya shirya zuwa Abuja din, don ansa kiran da joe ya mashi,,
 Cikin lokaci ya samu isa Abuja inda yasamu, har Joseph ya cika mai duk wani form da ya kamata,.
   Briefly Joseph yai mai bayani sai gashi kawai, ankira shi don yashi ga ciki duk da bawasu tambayoyi bane masu tsauri amma dai Joseph din yana darrr kada kb ya kasa amsawa duk da baida shakku akan shi, don yasan cewa yana da kokari,,
  A cikin ikon Allah KB yai nasaran lashe interview din ,,,a cikin masu yi harda Joseph a cikin su,
   Murna da farin ciki a gurin su baa musalintawa, duk da har yanzu bawai KB ya gamsu da kowace irin aiki bane,
  Amma dai gani masu taron ya tabbatar mai da ba karamin aiki bane,,
   Wanan abin ya jawo ma Joseph surutu acin abokan harkan shi,
  Don sai cewa suke yi ya dauk hausa ya sa acikin harkan shi ya bar yan uwan su sun fadi,
  Wanan damar a cikin sune ya kamata wani ya samu ba,a cikin northern side ba,
  Suko hausawan dake cikin su sun yi mamaki kwarai daganin Joseph ya kawao candidate din shi bahaushe,
 Tun a wurin akaba KB sabuwar  mota da kuma gida inda zai dinga besing a Abuja
  Sai sabuwar office da aka bude masu washegari,
   Kabiru gani al,amarin yakeyi kamar a mafarki wai yau shine da wanan abin da bai taba tunane samu ba,
  Sai gashi Allah ya bashi cikin dan lokaci guda, don haka bakaramin nasiha Joseph yai mai ba don ya fada mai cewa sai yasa ido ga harkan so sai kuma ya rike gaskiya don akwai bata gari wa yanda zasu iya batasgi cikin dan lokaci,
  Don zasu iya hada mai tracks kalakala don kawai ama wani hanya,shi a kore shi,

    Kwantagora ta dauki zance kwaaaaa cewa KB yadawo da sabuwar mota, ya samu aiki,
  Amma ba,a san kowace irin aiki bane haka da har ya samu wanan cigaban cikin lokaci guda,
  Wasu suka fara cewa ai yafara irin harkan Joe ne Joe din ya jefa shu cikin kungiya,
   Wanan zancen har ya fada a kunen KB da yan uwan shi,
  Inda mahaifin shi yakira yin mitin tare da duk wani dan uwanshi tare dashi KB din,,,,
   Anan KB ya fada masu cewa wallahi har ka ce ta sanar man Gas wanda duk wani Gas da zai shigo nan arewa saida sa hannun su a ciki,
  Nan dai yai masu bayani har suka fahinta suka kuma yi mashi fatan alheri a harkan,,,
  Saodai cikin gari kan wasu sun yarda wasu ko ba su yarda ba har yanzu,,,
    Sadiya Mohammad jodi wata sabuwar matashiya ce mai tashen budurci a cikin gari
  Tun ranan da taga Joseph tare da su Aisha Allah yasa mata son shi a rai saidai kawai matsalar ta da akace mata ba musullumi bane shi,
   Don har ta kasa boyewa a zuciyar ta saida ta samu jibrin tai mai magana akai,
   Dayake akwai wasa a tsakanin su yasa Jibrin duk inda ya ganta sai yace mata ta Joseph ita kuma sai tace aa, saidai Yusuf,
  Wanan wasa ko yaushe jibrin kewa sadiya, indan sun hadu ita ko bata gajiya da bashi ansa kamar kullun,
   Maryam ce zaune tana wanki a bakin famfo gidan su.
  Wayan Anty Dije yai kara alamar kira ya shigo mata, a lokacin
   Maryam tamike cikin tafiyar ta maikama da rangwada kasan cewa ba wani jiki gareta ba,
   Daukar wayan tayi don ganin bakon noba ke kira, cikin yar siririyar murya tace Assalamu Alaikum,
  Hello Anty kuna lafiya ya yara da gida,
  Wayan ta dan daga ta kalla,sai kuma ta kara manna wayar a kunen ta,
  Wake magana ne tace ?
Anty Hadiza nake nema pls aka bada ansa,
  Bata nan ta,shiga makwabta yanzu, dan shiru yayi sai kuma yace Assalam na kusa pls,?
  Baya nan shima tare suka tafi, ok in tazo ki fada mata Joseph ya bugo mata,
  Joseph kuma ? Joseph fa, kai is wrong noba pls
  Kada ka kara bugowa nobar matar aure ce pls
  Dan murshi yayi har tana iya jin shi, alokacin yace ba nobar maman Assalam bane?
   Tsuki tayi tana fadin mukan ina muke da wani arne wai Joseph da zai kira Anty
  Daidai lokacin da ta gama fadi ta kashe layin,
  Tana ta faman fada wai kawai don suyi magana da matan mutane suke kiran wrong noba,,,
   Shiko  joseph dake zaune a saman wani leda cushion ya rike wuyan shi da hannu bibiyu ya furzar da iska, daga bakin shi,
  In akwai abinda yafi mai munin ji shine ace mai arne, ko kafiri,,,,
   Tun yana yaro yai hating din wana kalman a rayuwan shi,
  Don in mutane suka ga su jibrin ko kabiru tarrme dashi lokacin sai yaji sun ce  baku barin yawo tare da dan kafirai ko ko dan arna ko,
   Wani bukin Christmas daya kawo masu abinci kamar yadda su ma suke bashi abinci sai cewa wasu mata sukayi
 Ku fita mu na da abincin kafirai a cikin gida kada muyi amai
  Wa zai ci abincin arna jagwagwalen banza kawai babu ko tsarki,
  Shikuma yadai san cewa duk wani tsabta a lokacin mamanshi tanayi,
  Kuma shi har gobe idan ya kewaya yana tsarki kamar yadda ya ga kowa nayi,
  Amma sai ake ce mai wai baida tsarki haba mutane ne,????

   Anty Dije tana shigowa tare da su Assalam daga makwabta ko daki bata shiga ba,,,
   Maryam ke fada mata cikin fada cewa wani kafiri ya bugo mata waya wai sunan shi Joseph nikan nace wrong noba ne
  Dan rainin wayo kawai Anty Dije dake tsaye sororo tana kallon yadda maryam ke ta faman halako fada,
  Tace kafirin banza kafirin wofi don ma bakiji hausan shi ba wallahi kamar fa hausan mutum kwarai,
 Anty Dije tace maryam ina fatan duk wanan zancen baki fada a waya ba dai ko,
  To may ye Anty in ma na fada mai kawai ina aikina kafirin banza ya kirani, ya bata min lokaci,
  Saida Anty ta zauna take cewa maryam mutumin nan ne fa abokin Assalam,kike ta surfa ma masifa,
  Barin wankin tayi tana kallon Anty Dije tace Anty ce min fa maishi yayi sunan shi Joseph fa,
   Shine mana Anty takara ce mata da dan karfi wai anty shi kafiri ne dama ba musulumi ba,
  Ke baki sani bane dama
  Hmmmm lalai mishon bat da musulumi,
  Wallahi anty ni na dauka cewa musullumi ne shi duk ganin da nake msi,
   Dan guntun kara dake gefe anty tadan duka ta dauko tana cewa wallahi ke dai kamar ace mai musulumi
  Don dai gaskiya ya duk halin shi na kwarai ne, wallahi,
  Daga inda maryam take tsaye tace furen juji kenan shi,
  Ga halin kwarai amma ba alkiblan kwarai,
  Dama malamin mu na islamiya ya fada muna ce wa akwai irin wa yan nan mutane acikin yan Ahal,kitab,
  Saidai basu da yawa so sai daga cikin su, masu halin rayuwa irin na mumunai
   Daga haka ta tabe baki taci gaba da wankinta tana cewa  Assalam abokin Christian, shiko sai dariya yake mata don bai san ma,anar maganar ta ba,,,
  Yinin ranan sai maganar ta dan tsaya mata a rai kawai tausayi yabata mutum kamar wanan ace baya sallah Allah ya kyauta kawai take cewa aranta
  Sai ma daga karshe takama jin haushin shi, da takaicin kawai,,
    Mr Emanuel yanzu girma ya fara kama shi don haka yanzu iyakar shi zama gixan man su ya daina yawan harkoki kamar da
  Kamar su saida manja, saida robobin aiki irin na mata duk suna da shagunar su acikin garin kwantagora,
   Yau ma kamar kullun zaune yake  saman wata far kujera kamar kulun da yamma haka yakeyi sai zuwa shidda yake wuce wa church wani lokaci,,
  Wani musa mai aski ne yazo inda yake don sun saba da musa,wanzami tun tuni
   Saboda zaman uguwa guda, da suka taba yi ada,
  Shine sabon su yai karko har zuwa yan zu
  Musa yakan dan biyo ya samu dan abin ihisani akai akai
   Bayan sun gaisa ne yake kokarin zama gefen da Ema mai manja yake, daidai lokacin yake cewa
   Ashe taimakon da yaron ka yayi wa dan gidan Tanimu kafinta ke nan
  Mr Ema ya ce taimakon may ke nan fa, acikin hausar su irin ta IBO,,,
  A, ba ance ya samo mai babban aiki a Abuja ba har ma yai kudi lokaci guda,
   Wani yar Mr Ema yaji kamar an datsa mai mashe a zuciyar shi,
  Sai da yai kokarin boye ma musa wanzan da halin da ya shiga tukun sanan yace har ya fara aikin ne ko,
  Musa wanzan yace kai tun yaushe aiki kan har mun fara cin moritar ta,
  Don nafito zan wuce kauye nagan shi yana magana da wasu masu aikin gina wai yana son ai masu katangar gidan su,,
  Wani iri mr Ema yakaraji a ran shi watau ke nan har maishi yadan fara karfi da tai makon Joseph din,
  Alhalin ga yaran su cikin gari birjit da suka gama karatu suna ta bin shi yasamo masu aikin yi yana cewa ba aiki yanzu,,,
  Musa na ta zuba shi bai ko jin may yake cewa a lokacin,,,
  Kai musa pls zan tofi wani anguwa ka tafi kawai zamu hadu gobe ke nan,
  Daga haka ya tashi sai gurin motar shi ya nufa rai bace
  Gidan shi ya nufa cikin fada yake kwada ma Samuel kira
  Ya wurgat da sandar da yake yawan rikawa mai alamar sandar sarauta,
  Lokacin Samuel yafito daga cikin gida inda yake daka sakwara,
  Call your brother for me pls,
Cikin mamaki Samuel din yace ok Dad,
  Kira daya na biyu ya dauka
  JOSEPH da kakausar murya yakira shi hakan yasa Joseph din sani wani muhinmin magana ya faru
  Don haka yai shirin sauraren baban na shi,,
  How may time D I warn you about dis hausa boy's,,, ??
  Baba what's going on. Sai kuma yace cikin yaren su maya faru baba,
  Ya akayi ka samo ma yan gidan hausawa aiki bayan nayi ma warnings akan MAKu da su,
  Sosai yake mai masifa shi dai sauraren shi ya keyi batare da ya ce uffan ba,,
  Daga karshe kuma sai ya sasauta muryan shi zuwa lalashi,
   Yace You have to be,careful with dis people they are very dengerous,
   Haka dai yai ta ma mai nasiha shiko yai shiru kamar mai saurare,
  A karshe ya sheda mai cewa yana jin kunya abokan shi da yan churches din su su ji cewa yai eanan aikin,,,,


ZEEEE.  MAKAWA. 馃憦馃憦
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
   FUREN    JUJI
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
           1鈨�1鈨�

ZAINAB IDRIS MAKAWA


Why why mutane suke da gulma haka,  may ye aibun taimaka ma KB dayayi da har za,a fada ma Dad din shi,
  Wai may yasa mutane basu kaunar suga cigaban yan uwan su ne musan man hausawa,
  Don dai yasan cewa wanan maganar daga bakin hausa yafito zuwa kunen mahaifin shi,
  Zubur ya mike tsaye daga inda yake daga shi sai dogon wando da singlet a jikin shi,
  Gurin window dake facin din titin da ke unguwar su ya nufa,
  Fitinlo ne karara suka haske ko ina sai kuma duhun dare da ya gauraye gari lif,
   Ya kai wani dan lokaci a gurin tsaye yana kallon sararin samaniya kawai,
  Daga karshe bayan yasamu mafita yai wani dan ajiyar zuviya mai nauyi,
  Fridge ya bude alcoholic ke ciki kala kala duk sunyi rabar sanyi yadda yake so,
  Hannu ya mika da niyar yadauko wani mai berry a ciki,
  Caka hannu shi ya tsaya daidai wuyar kwalbar
  Muryan Jibrin ne ke mai yawo a kwakwawa duk addinin mu bai yarda da shan giya ba,
  Duk wanda ya ganka a lokacin kana cikin maye baya kara kallon ka da dara a idon shi,
  Don duk sanda ya gan ka wanan yanayin mayen dayagan ka aciko zai fado mai zuciyar shi
  Kaga kimar ka da mutuncin ka yazube a idon shi,
  Idan kuma ka samu iyali za,a dinga goranta masu cewa uban su dan giya ne, ai,
  Cikin sauri kamar wanda akai ma tsawa ya dauke hannun shi saman kwalban,
  Marfin fridge din ya buga da karfi kamar zai balla ,shi,
  Da karfi ya fada kan gadon ta baya yana mai rike goshin shi da hannayen ,,
    A haka wani irin barci mai nauyi ya kwashe shi bai farka ba sai misalin karfe tara saura na safe ,
  Dan hasken ranar da hudu ta cikin labulen window dakin ya haska mai idon shi,,,
    Mika yayi ya gyara kwanciyar shi don ya cigaba da barci amma sai kuma ya kasa ci gaba da barcin,
  Mikewa yayi yashiga bayi yai wanka bayan fitowan wanshi ya na daure da towel
   Yazo bakin gado ya rusun na kan shi saman gado
  Nan yafara jero addua, our father whose as at heaven ,
  Hello be there name,,,,,,,,,,,,,
   Bai tsaya ba saida yakai karshen addu,an shi kamar kullun yadda ya saba yi duk safe kafin yafita,
   Saida ya kintsa tsab ya sauko inda yasamu break fast din shi an shirya mai komai tsab
  Jin gidan shiru yasa shi daga murya yana kiran Uchee, da karfi,
  Uchee da ke can yana gyara cikin gida yazo cikin ladabi,
  Cikin muryan nan tashi mai nuna sanyin hali a koda yaushe yace ma Ucheen ya na duk bear dake cikin gidan shi a kwashe su a zubar da su,
  Jin maganar Ucheen yayi kamar a mafarki cikin sauri yadago kanshi ya kai wa ogan kallo,
   Joseph da kanshi ke duke yana dan kada ruwan zafin da ya zuba a cup,
  Batare da ya daga kai ya kalli Uchee ba yace
   Yes I Mean it,,,,
   Uchee zuciyar shi fam da farin ciki yasamu gara basa, yau,
  Duk yawan giyar gidan oga a ce wai ya kwashe ya zubar,
   Ba bata lokaci ya kwaso su jiki na rawa yafita dasu gidan,,
  Saidai a kasan zuciyan shi yana mamakin ko may yasa ogan nashi ya ce ya fita mai da su gaba daya,,
 
    KB ne ya kira Joseph din wanda duk yinin yau bai fita ko ina ba yana zaune a cikin gidan shi da ke cikin birnin Lagos,,,
   Cikin kasala yadauki wayar don bai son yin wani dogon motsi yau,
  Hello, KB ya kake ne yau ya, Abuja,?
   Yace a lokaci guda sai KB ya amsa mai da cewa lafiya kalau gashi ma zai tafi suleja dibo wasu motocin da suka samu matsala,
  Kuma suna dauke da mai a cikin su,
  Duk da Joseph din yai kokari wurin bashi amsa sama sama,
  Hakan bai hana KB gane cewa Joseph din yana cikin wani irin yanayi yau din,
   What's wrong with u, today,,,?
  KB ke tambayar shi a karshen maganar su da Joseph din,
   Nothing ma,,
Inji Joseph din yaba KB amsa a takaice, kawai, daga haka suka kashe wayan,
  KB din ne yadan shiga tunane don saboda dan zaman da sukayi da Joseph yakai kowa na iya gane mood din wanin su,,,
  Duk abinda KB keyi hankalin shi na gurin Joseph don shi a zaton shi ko baida lafiya ne
   Don yasan cewa ciwon Joseph kamae fitina ce ga duk na kusa dashi,
  Saboda irin mutanen da basa ciro ne da wuri ranan da duk zasuyi sai duk wanda ke tare da su hankalinshi ya tashi, 
    A hanyar shi ta komawa cikin garin Abuja yakara kiran wayar Joseph din saidai wanan karon muryan da dan sauki sosai a saman da zu,
   Ejoma, yarinya ce matashiya yar kabilar IBO mazauna cikin garin kwantagora,
  Tana zaune tare da yayanta da mijin yayanta wa yanda suka kawo ta garin kwantagora da zama,
   Tun bayan gama karatun secondary din ta ta shaku da wani yaron hausawa,
  Dan cikin gari shakuwar su ta samo asaline ta yawan zuwa sayen abu da Aminu Aliyu ke yawan zuwa yi a,shagon su Ejoma Ibire,
   Har takai sun kulla, soyayya da Aminu din batare da kowa yasani ba,
  Sai da abokan mijin yayan Ejoma suka gan su tare shine suka fada ma mijin yar nata,
  Ranan tasha fada har d a duka agurin yayyen nata so sai hakan bai masu ba saida suka fada ma pastor don yai mata preach
  Duk wanan abin bai raba Ejoma da Aminu ba illa ma kara shakuwar da sukayi so sai ,
   Har ta kai Aminu yai mata alkawarin cewa zai aureta
  Hakan yasa har ta yarda dashi har suka kai ga kara aikata masha,a a tsakanin su hakan yasa Ejoma ta fara bijirewa yayanta da mijin yar nata,
   A karshe saiga ciki, shiko Aminu Aliyu yana jin ta ce ciki gare sai yace ai sam bashi yai mata ciki ba,
   Duk yadda yayanta suka so a sulhuta maganar sam Aminu yaki yarda da zancen cewa ai cikin sane,
   Hankali duk wani IBO dake zaune ya tashi da jin wanan labarin na zance  Ejoma ,,
     Ganin haka yasa mijin yarta ya koreta gidan nasu yace saidai ta koma can gurin Aminu,
 
    Wayan shi yake kokarin ajewa bayan ya gama waya da wani Abokin shi da ke zaune a janhoriyar Benin republic,
  Inda yake kwadaita mai yadda sana,ar motoci da shimkafar kasar wane ke da riba so sai a harkan,,,
 Kiran Samuel ce ta hana shi aje wayan dai yai niya,
  Inda Samuel ke sheda mai cewa mahaifin su yana fama da ciwon kafa sosai duk kwanakin nan,
   Don har takai ko shago da gidan mai bai iya fita yanzun nan,
  Hankalin Joseph din ya tashi sosai don yasan yadda yakanyi fama da ciwon kafar na shi
  Sanadin ciwon kafar ya samo asaline tun wani hatsari da yasa mu a saman mashin,
   Joseph yakira mahaifin nashi inda yake tambayar shi lafiyan jikin nashi
  Amma sai Mr Ema din yace mai a meke ,you, no worry my child,
  Na small problem ,
I go manager amm,,,
   Yasan cewa zai shigo kaduna sati mai zuwa don akwai wani wanda yake son gani a kaduna din,
   Hakan yasa bai cewa mahaifin komai, ba,

     Musalin biyar na na yamma ya shigo garin kwantagira bayan dan banzan gudun da ya dinga shararawa shi kadai acikin mota,
   Tun kwanar shiga gidan su yafara ganin abin hawan su duk ya cika kifar gidan su,
  Hankali shi ya tashi matuka daga ganin taron IBO haka,
   Hon yayi mai karfi wanda dole suka bude mai get,
  Da kyat yasamu inda yadan parker motar shi a can gefen cikin gida,
  Tun bai fito daga cikin motan ba ya hango wata yarinya a tsugune gaban elders nasu,
  Yana ganin haka ya san cewa wani case sukeyi mai karfi,
   A hankali ya fito daga ccikin motar saidai ganin mutane a gidan ya hana shi bude bayan motar don ya fitar da tsaraban da yazo da shi,,,
   Tun daga nesa yake jin yadda yarinyar ke gumza ta na ihu da kuka mai ban tausayi,
  Tana, mai ba da hakkuri sai kawai yaji wani iri a zuciyar shi
  Don komadai may tayi yakamata,su yi considering din ta a mace ce fa,
   Ko kallon su baiti ba ya wuce ta gefen su batare da ya tsaya gaishe su yadda ya saba ba,
   Wanan ya kalli wanan wancan ya kalli wan can,
  Su na mamakin shi don basu san shi da halin rashin mutunci ba,
  Samuel wanda ke labe tunda aka fara case din shine ya ke taron dan uwan shi cikin mutunci,
   Nan yake washe baki babu ko ga ruwa ya fara labarta ma Joseph cewa
  Na, Ejoma Ebere one hausa boy givern bele,,,
  D hausa boy now say no b him do amm,
   Na yin d elders wan punish har,,,
  Y ,she, give her self to musulim boy,
   Me ,I know ask u ooo,
Joseph ya ce ma Samuel wanda da har zai ci gaba da zubawa,
   Roban ruwa yadauko ma kan shi daga cikin fridge din,
   Ganin cewa Samuel baida niyar kawo mai komai
  Eanka yafada don ya sauke gajiyar shi,
  Daga cikin bayin yakre jin karar motocin su da mashunar su suna watsewa
  Saida ya shirya tsab yafito cikin wasu kananan kaya,
  Abin mamaki wanan yarinyar Ejoma yagani rakube bayan kujera a falon su, har yanzu tana dan sheshekan kuka,
  Sai a lokacin yake gaisawa da mahaifin shi wanda ke zaune ya mike kafar dake mai ciwo saman wani tsohon tebur,
  Joseph y u know greet my people,?
   Baba me i don't have problem with dem woo,,
  Waiting dis girl do here Dad ?
  Yace mai zata zauna har asan yadda za,ayi da ita ne,
  Don ta je tana bin yaran hausawa ga irin hawalan da wo mata, nan,
   Wayan Joseph din ce tai kara a lokacin wanda hakan ne yasa shi samun sararin guda daga fadan baban,
  Motar shi ya shiga ya bar gidan nasu don yasan cewa fadan sai ya kawo kan shi a karshe,,,,
   Tafiya yake yi kawai don yasan cewa KB bai gari kuma ,
     Don haka zuciyar shi ta raya mai cewa yaje wurin little friend kawai ya ganshi,,
      Anty Dije ta gama abinci kenan tana ko gyara ko ina na gidan,
  Daga waje yadan tsaya duk da cewa an bashi umarni akan ya shigo ko yaushe yake bukata,,,,
  Amma sai yaji cewa bazai iya shiga ciki kai tsaye ba
  Don haka daga daga,waje kadan yadan tsaya yace  Salamu Alaikum don Allah ko Assalam na ciki,
   Cikin mamaki mai ma Assalam sallama duk suke
  Shiko Assalam har yagane murya da wani irin ihu yafita kofa inda Joseph ke tsaye yadaga shi sama cak yana dan juya shi,
  Sai suka kama dariya a tsakanin su, daidai lokacin da duk sauran yan gidan suka leko ta kifar falo suna kallon su,
   脌nty Dije ke cewa a, Joseph shine baka shigo ba ka tsaya daga nan kana cewa kana ma Assalam sallama,
  Dan sosai kai yayi da key din motar shi yace ai zan shigo nakira Assalam ne yai min jagora,
   Falon  anty ta bude mai yashigo daidai lokacin da maryam ta dauki buta don zuwa yin alwalar sallah magrib,,
   Bayan sun gaisa da Anty dije sai kwai ta fara gabatar mai da abincin a lokacin don dama har ta gama komai,,,
   Cikin nuna jin kunya yace mata ya gode bazai ci ba
   To ke nan kai kana jin tsoron cin abincin mu Joseph shine shi Assalam, ka ke kawo mai sweet, time to time,
  No haba Anty gaskiya ba hakana bane,
  Kawai dai naga cewa nashigo late evening ne kin rida kin gama cooking din ki ko
  Idanzaka ci kaci kawai don sama mu a aje extra ko yaushe,
   Badon yaso ba yadan dauki spoon ya fara ci a hankali,
   Yamai yar jin nauyi da kunya duk da cewa daga shi sai Assalam ne a falon zaune,


ZEEE   MAKAWA
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
   FUREN    JUJI
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
          1鈨�3鈨�


ZAINAB IDRIS MAKAWA
 

    Daga karshe hukuncin da aka yankewa Ejoma baima Joseph dadi ba,
  Don Samuel ne yakira shi ta waya kamar yadda yabar mai maganar cewa ya kirashi ya sanar dashi duk yadda akayi,
   Don haka yai kokarin samun nobar ta yace ta shigo motan da zai kawo ta Lagos,,,,
 Wanan shine silar zaman Ejoma a Lagos cikin karkashin kulawan Joseph,,
 
    Yadauki lokaci mai tsawo bai,shigo garin kwantagora,
  Don har takai mutane sun fara maganan rashi shigowar shi ,
   Saboda kawo yanzu angane amfaninshi a cikin al,uma, duk da zaman shi furen juji bai hana mutane kai koken su gurin shi ba,
   Shirin kwanciya yake yi dai lokacin wayar shi tai kara,
   Mika hannu yayi ya dauko wayar daga saman sidedrower, din shi,
  KB yagani barobaro a screen din wayar yar murmushi  yayi don ganin mai kiran nashi a daidai wanan lokacin,,
  Yadai man inji Joseph yace wa KB
  Kayi wuyan gani fa mutumina, shiru haka muna ta cigiyan ka a kasar
  Dariyarn nan tashi ta kasaita yayi da KB yafadi haka na,
  Yana dariya yana shafar sumar kanshi da ya kwanta mai lun har zuwa fuska,
  Yace ai lamari ne na rayuwa sai a hankali, yanzu haka tun tree weeks ago olf man ke ta kirana, wai yaji ni shiru,
   But ina son inyi kokari in shigo, uffer week, don akwai yan aiyukan da zanyi ma Dad,
   Dariya KB yayi a bangaren shi yace ai ban zata zaka iya kai wa har  dis time baka shigo ba kodon mutumiyar don tana ta bugo min waya wai bata samun ka,
    I beg forget about her ni don old man da mutanen arzikina zan shiga,
   Wai ya labarin jibrin ne mun kwana biyu ba muyi waya ba da shi,
   KB ya ce bari kawai man ai old man din jibrin yasamu problem wallahi don ya biya kudin zuwa saudiya amma an cinye kudin case din har minna,
  Wanan dalili har saida tsohon yai ciwo sosai haka yasa su jibrin cikin wani irin tashi hankali,
  Wani iri Joseph yaji a zuciyar shi da kyat ya iya furta wa a hankali may yasa mutane suke hakane wai,
  Mutumin nan ysi iya kojarin sa ya hada kudin shi sai cikin dan lokaci ku kwace,
  KB yace wallah ma noman wake yayi dis year sosai ,
   Sai yahada da saida dabbobin shi  shine yabiya masu su uku shida matan shi,
   Kaikaikai, haba dai gaskiya akwai tausayi wanan abin,
  Kawai dai bari za muyi waya da jibrin din in masa jaje,
   Da,wanan zancen ya kwana a zuciyar shi  yana mamakin irin tsoron Allah da mutane basu da shi yanzu, sam
   Tunda safe ya bidi layin Jibrin inda yake fada mai cewa KB ke fada mai abinda yasamu mahaifin shi,
  Nan jibrin yakara mai bayanin duk halin da ake ciki tun farko,
   Wai kudin harda yawa ne Joseph ke tambaya, Jibrin din,
   A,kaiko akwai yawa ma,na har fa mutun uku ne,
  Nan dai jibrin ke mai bayanin yadda kudin yake da kuma yadda ake komai,
  A haka sukayi sallama bayan sun dan taba hiran yau she rabo a gana,,,
    Tukun mota yakeyi don zuwa depot, yadibo wasu motocin su,,,
  Amma azuciyar shi yana tunane cewa a she ma bawasu kudine masu yawa na ake biya,
  Shine har zakaga wasu musulumai gasu da halin zuwa amma sai su tsaya tara duniya,
  Basu damuwa da kokarin zuwa sauke faralin da aka sa masu,
  Yanzu diba fa wanan mutumin noma yayi da karfin shi ya biya kudi don kawai yatafi ya sauke farali,
  Amma aka samu marasa imani su ka yaudare shi saboda , tsaban damfara da yaudara, wanda yasamu ta rashin imani,
   Wanan zancen yasa shi yin tuna nen cewa ya kamata yakai kakanshi tayi ziyara a Jerusalem,
  Haka kawai ya tsinci kanshi da nishadin jin dadin wanan tunanen, da yayi
   Don haka bai tsaya wani bata lokaci ba yafara masu shiri tafiya ita da shi,
   Don haka ya yanke shawaran sheda ma maifinshi wanan zancen
   Zaune Mr Ema yake a kofar gidan shi kasan cewa yau lahadi bai zuwa ko ina,
   Ganin mai kiran nashi yasa shi jin zuciyar shi tayi mai fari kal,
  Don dai yasan cewa Joseph na matukar kokarin shi wajen kulawa da shi,
  Bakamar sauran yaran kabilar su da  da,zaran yaro ya girma yafara cin gashi kanshi, yadaina yawan kula iyayye ke nan,
   Ajiyan zuciya yasake daidai lokacin da yake daukar wayan, ya ce Hello Son how are u, ???,,,,,,
 Shi din ma Joseph din ajiyar zuciya yayi mai kara yace mai, l,am fine Dad,
   Yace ina ta kokarin kiran layin M,T N dinka baya shiga shine nace barin kira layin Airtel, dinka ko zai tafi,
   Daddy din murmushi yayi yace ai matsalar services ne kawai,
 Ya kuke can ya aiki inji Mr EMA, yana tambayar dan nashi,
  Joseph din yace everything is fine Dad,
    Mr EMA yace God bless you my child,,
  Amen yace da murya mai yar karfi,
  Dan shiru ya biyo baya, sai Joseph din ne yadan kauda shirun da cewa
  Dad dama ina son shedama cewa zamu tafi Jerusalem ni da Grandma,
  Which Grandma,?
   My mother mother,
  What Mr Ema ya fadi da karfi kamar wanda yaji tsoron hakan,
  Kana cikin hankalinka yaushe har ka fara hurda da ita,
  Idan ma baka fara ba bana son kafara saboda kasan cewa is weaked worman,
   Don ana suspect din cewa itace ta kashe mamanku,
   Yayi yar murmushi har uban najin shi yace bazata yi komai dashi ba ai
  Don shi gaskiya bai yarda da zancen da akeyi a kanta ba,
  Fada sosai Mr Ema ya,dinga yiwa Joseph akan cewa ya janye tafiyar da ya shirya yi shida ita,
   Har sukayi sallama yana mai jaddada ma dan nashi cewa yafita harkan kakan shi ,,,,   

     Kwana biyu da yin wayar yana cikin damuwa sosai
   Idan kagan shi basai an fada maka cewa bai ciki dafin rai ba,
   Don haka yaje gurin wane father, yai mai bayani
  Inda father din yace mai aida ita muguwa ce bazata tafi wan wurin ba,
   Sai a lokacin hankalin shi ya kara kwantawa da kakar tashi wace yan uwan mahaifin shi suka azama kahon zuka wai muguwa ce,
    Tabbas yaji dadin zancen wqnan pastor din don ko ba komai wanan tagiyan zai wanke zargin da ake wa matar,
    Don haka saida yaga komai ya kammala yakama hanyar zuwa Niger state of Nigeria,
   Ya iso cikin dare don haka gidan su Anty Dije ya nufa don ya kai mata tsaraba,, duk da yana jin yunwa, sosai,
   Gashi yanzu in dai yana kwantagora sai abincin gidan Anty Dije yake iyaci,
  Saboda kawai yardan da yayi da matar don daidai da rana daya bata taba nuna mai kyama ba kamar yadda ya fahinci cewa sauran musullumai nayi mai dan kyan kyami,
   A falon gidan ya samay su gaba daya suna kallon season film na india,
  Cikin murna da dauki duk wanda ke falon ya tare shi, banda maryam wace  ke kwance saman dogon kujera tana, kallo, alokacin,
   Anty Dije tace Oyoyo da bakin dare, haka shine baka fada muna cewa kana hanya ba Joseph,
    Yai yar dariya yace tafiyan haka tazo min wlh Anty, kawai yau naji ina son shigowa kwantagora ne,
  Bayan sun gaisa Assalam yana makale ajikin shi tun shigowar shi,
   Yadan kalli Anty yace a tura yara su kwaso maku kaya a buth ko ,
  Inda maryam take kwance Anty ta kalla tace Maryam tashi mana kitafi ku kwaso,
   A cikin zoboro baki tai kicin da fuskanta, tace a shagwabe sannu,
  Batare da tajira ansawar shi ba ta wuce tana kokarin daura dan kwalin ta, akai,
  Har takai kusan kofa tace a bude buth din yake ne, ?
  Key kawai ya miko mata batare da yai magana ba don ko banza dama shl tsarda magana gare shi,
 Tayi gaba tana turo baki gaba tana zumbure zumbure,
   Har takai  bakin kofa sai Anty Dije  tace idan fa baki iya ba kada kimai barna, Maryam,
    Wuce wa kaiwai tayi don takaicin da take ji,
   Kayane shake ga buth irin tsarabar kasar kurmi yakawo masu,
   Maryan tunda ta samu da taimakon yaran shiya aka gama kwasan kayan
  Ko kara juyowa hanyar falon batayi ba kawai tashi ge ciki abin ta,
  Yadan kai wani lokaci suna hira da anty dije san nan yai mata sallama yatafi,
  Inda Assalam yasa masu kuka sosai, wai sai ya bishi,
  Sai bayan tafiyar shi ne Anty Dije takewa Maryam fada akan irin yadda take nunawa Joseph din,
  Anty Dije tace abinda yasa take janshi ajiki dayan biyu ne,
  Na farko dai ko Allah zai sa ya gane gaskiya, jin haka saida Maryam tadan daga ido ta kalli Anty din, tace a haka anty,
  Kiga mutum kasurgumin ARNE haka har kike ganin cewa zai iya tuba,
  Maryam kina ko da tunane akwai abin da yafi karfin Allah ne Maryam,
   Kinga kuma na biyu yadda yake ra ayin yaran nan kamar wasu jinin shi,
  Duk saboda Assalam yazo muna kingako badadi in dinga nu a mai tsana ko kyama a fili
  To yanzu yaya zaki yi da wanan kayan da yakawo maku,
  Don dai ni gaskiya bazan iya cin komai na kafiri ba,
  Anty Dije tarasa abinda zatace wa yar uwan nata,
  Wace gata yar karama sai shegen akida kamar wata malama,
   
   Washe gari tunda safe ya nufi gidan su jibrin don gaida mahaifin jibrin din,
  Yadda yake zato abin yafi nan don duk dan dattijon yaramay yayi baki,sosai,
   Sundan dade zaune a dakin baban jibrin din da zaitafi yaba shi dubu hamsi yace ai sai mai lemo,
   Sam yaki karban kudin saida kyat yakarbi kudin da farko Joseph ya zata ko baison abin hannushi ne,
  Saida dattijon ya yace mai yarage sunyi yawa yabashi ko kadan ne,
  Yace baba lemo kawai za ,a sai maka kasha,,
 Bayan fitar su waje ne Joseph din ke cewa jibrin yanzu may ake ciki akan zancen,
  Nan dai Jibrin ya sheda mai cewa kotu tace mutumin yabiya shi nan zuwa karshen shekara,
   Joseph yace har lokacin ba,atafi aikin ba ke nan,
  Jibrin yace kai haba har wasu na shirin zuwa ma alokacin ,,
   Kai haba impossible inji Joseph gaskiya asan yadda za,ayi musamu baba su tagi wanan shekaran,
  Jibrin yace yaya zamu man tunda duk dan abi da ke ga baba shine ya hada yabiya masu
  Joseph dake kokarin bude mota yace ma jibrin a ina zamu samu kujerar, ne,
  Mamaki karara a fuskan  jibrin yace kai bafa maganar wasa bane man kudin mutum uku baba ya bita fa,
  Joseph yace and so what,
  Indai har zamu samu ai sai su tafi,
  Murna jibrin zaiyi ko kuma may
  Saidai kuma a zuciyar shi ya na tunanen in har mahaifin su zai yarda da zuwa makka da kudin Joseph,
  Don haka ba bata lokaci suka shiga cigiyar kujerar makka
  Saida kyat suka samu a wani local government kusa da kwantagora magama local government,
  Saidai an masu karin kudi sosai akai amma haka ya juye madu yabiya, don dai kwai yadda yake jin kada a wuce baban jibrin bai samu zuwa aiki hajji ba kamar yadda ysi niyya,,,
  Maganar nazuwa gurin baba aikuwa baba yace sam badashi za,ayi awanan aikin ba,
  Ina zai tafi aikin hajji da kudin kafiri,
   Da tambaya dakomai malamai sukace ya halatta su tafi tunda shi yaga dama yabasu kudin shi kyauta,,
  ,,,     

ZEEEE MAKAWA
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
   FUREN  JUJI
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
          1鈨�4鈨�

ZAINAB IDRIS MA KAWA


  Wanan tafiyan na mahaifan Jibrin da Joseph ya ba kudin zuwa Saudiya ya jawo muhawa sosai a cikin gari,
  Har takai wa yanda basu san shi ba yanzu sun fara samun labarin shi,,,
    Dashi akai komai har zuwa rakiyan su airport a Minna inda zasu tashi, zuwa kasa mai tsarki  ,,
   Wanan abin yabawa Joseph mamaki sosai don tun a nan sun fara ibada
   Daga can ya wuce zuwa Abuja gurin zancen business din da suke so sufara jonawa,
   Wanan tafiyar tankar tafiyar don jibrin a kayin don itace samuwar aikin jibrin din,,,
   Anbashi In charge na supplying din duk wani shinkafa da mangyada da za,a shigo dashi daga wata kasa,
  Zuwa kasar arewa da kewayen ta, kamar su Cameron da Chadi, Niger
  Bakaramin sa,an samun wanan nasar yayi ba don mutane da dama sunyi ta korafi akai,
  Wanan abin yaiwa mutane da yawa dadi saboda jibrin mutum ne mai tsimakon nakasa da,shi sosai,
   Lokacin tafiyan su Joseph da kakar shi yayi kawai sai ji Mr Ema yayi cewa Joseph yafita tare da ita, zuwa Jerusalem,,,
  Wanan fitar mutane kauyen suka,dinga mamakin cewa tunda ita witch ce yaya zata iya zuwa can wurin bauta,
    Wanan tafiyar ta daure wa Joseph kai sosai saboda abinda yagani a can ya banbamta da yadda suke gudanar da tasu,addinin a nan,,,,,
   Saboda sai yaga cewa ai duk kusan al,adun da akeyi acan kamar al,adan musuluman Nigeria ce da sauran duniya,
   Hatta da alwala indan bakayi ba ba,za,a bari kashiga cikin massallacin ba,
   Abubuwa da dama yagani a can sai kuma yaga cewa ai har da musulumai daga wasu kasashe suna zuwa yin bauta a cikin wanan masallacin mai tsohon tarihi  watau masallacin, BAITI,MUKADIS,,,,
     Ya dawo gida zuciyar sa fam da tunane kalala, acikin sa,
   Kakan shi mai suna Ciyoma, tun acan tadinga wani irin kuka na farin ciki tana mai samai albarka,
   Addu,an gamawa da lafiya da duniya yadinga mai aciki tasako zancen da ake mata zargi dashi tana mai cewa,
  Tagode Allah da jikanta ya zama abin kwatance a cikin jamar su, har yafidda ita daga zargin mutane, cikin wani irin magana kamar waka,
  Joseph dake zaune yana kallon ta a cikin dan gurin shan iska da suka tsaya a wani airport,
   Yana saye da wani katuwar rigar sanyi,a jikin shi yataso daga inda yake zaune tun fara maganar ta,
  Ya rugumay ta ajikin shi don maganganu da take fadi sun ratsa mai zuciya sosai a lokacin
  Tunanen mahaifiyar shi wace a yanzu bata da rai ya fara ji dama ace tana da rayuwa ne da yanzu suna tare da ita a wanan gurin,
   Saboda yasha tayawa mahaifinshi cewa suzo wanan gurin ziyara amma sai Mr Ema din yace bai son abin wahala shi,
   Wasu hawaye masu dumu suka silalo mai daga ido zuwa kasar fuskan shi,
   Yanajin mutuwar uwar su kamar yanzu ne abin yafaru mata mai hakkuri da sanin ya kamata
  Don yana da wayon shi irin yadda mahaifin shi yadinga wahal da ita a lokacin zaman su,
   Jin hawayen Joseph na diga mata a wuyar ta ya sa yar tsohuwar dagawa daga cikin jikin shi ta dubi fuskan shi,
  Ta ce Joseph my child don cry pls,
   Kara rike kakan tashi yayi saboda yadda yake ji a zuciyar shi ba dadi
    Sun kai wani lokaci a haka sanan nan ya ja ta da kyar zuwa wurin da kayan su yake gefen wasu kujeru da aka tanadar wa matafiya,,
   Sun iso gida Nigeria cikin farin ciki da walwala a zukatan su saboda, sun tafi inda kowani dan addin Christian ke burin zuwa,,,
   Ta Abuja suka,sauka don haka yasa wani abokin shi ya kwaso su, daga airport,
  Zuwa gidan shi da yake sauka a Abuja,indan yazo,
  Sai da ya huta san nan ya kira KB yana sheda mai cewa sun dawo shi da kakar shi,
   Kwanan su biyu abokanan shi suna ta zuwa yi mai barka da dawo wa,
   Tun wanan tafiyar tasu josepy yasa wa ranshi cewa ba,zai kara barin wanan yar tsohuwar kakanshi cikin wahala ba saboda tana bukatar hutu a rayuwar ta yanzu,,
    Kwantagora suka nufa daga Abuja inda tsohuwa ciyoma bata so hakan ba don dai ita taso ne takoma gida,
  Don yanzu bata son wani alaka ya hada ta da mahaifin su Joseph tunda ya iya rabata da 'ya'yan diyar ta,
  Inbadon Allah ya bata jika mai albarka ba wanda yasan darajan ta,
   
   Sai bayan tafiyar Joseph Jerusalem ne labari ya iso ga mahaifin shi irin tai makon da yai wa jibrin again,
  Abinda takai shi har da hawan jinin shi ya tashi mai dama ko yan uwan Ema IBO sun san shi mutum ne wanda baya son taimakawa na kasa dashi,
   Cikin dare suka isa don tun a hanya sukai waya da Samuel nan Samuel yake sheda mai abinda yafaru
   A cike da rashin son taimakon da mahaifin shi baison yana yi ya iso fam a zuciyar shi,,,
    Murna sosai yan uwan shi sukayi daganin kakar su wace tun suna kanana so sai rabon da su ganta
   Mr Ema yana dawo Church gurin service din dare yai arraba wanan tsohuwar duk shi ba wai wani girmuwar shi tayi ba sosai
    Nan da nan anurin fuskan shi ta gushe  mai sai da kyat ya iya controlling din zuciyar shi,,
   A nuse Joseph yafito daga dakin shi don zuwa tariyan baban shi,
   A fusace ya ke karba mai inda yafara mai sababi na rashin bin umurnin shi da Joseph din baiyi,
  Yace saboda kaga yanzu kana cin gashin kan ka shiyasa ban isa in sa ma doka kabi ba,
  Kafada min may hujjan ka na taimakawa yaran hausawa kuma musullumai,
   Joseph har in bazaka daina hurda da wa yan, nan mutanen ba ina warning dinka kadaina shigowa kwantagora pls,,,
   Joseph wanda kan shi ke duke tunda mahaifin nashi ya fara fada yadago a hankali ya fara magana acikin natsuwar nan tashi yace
   Dole in taimaka masu baba saboda sun min abinda yafi haka alokacin da nake bukatar hakan,
   Rai bace Mr Ema yadaga kai cikin mamakin kalamin dan nashi yace,
   Kana nufin cewa ba,zaka iya rabuwa dasu ba ke nan,
  Shiru yayi mai wanan karon yana dai sararon shi kawai,
   Barin falon yayi saboda yasan cewa yanzu wani ,zafi ba ,zai lankwasa Joseph din ba,
 
     Aisha tayi farin ciki sosai da jin cewa Joseph yana gari don tun cikin dare ya kirata yake sheda mata cewa ya shigo,
   Tasan cewa ita kan kakanta ta yanke saka kenan don ba karamin abu take samu gurin shi ba,
   Duk dai iyakar ta dashi kawai yan wasan ni kuma ba wani mai yawa ba,
   Sosai ta shirya ma wanan zuwan nashi saboxa gana da yan bukatoci akan shi da yawa,
   Shiko tunda safe ya fita zuwa wani kauye shida KB don yana gari,
  Basu dawo ba sai zuwa dare marance,su ka , iso, garin ,
   Bayan yai wanka ya shirya zuwa ganin little friend din shi,
   Wanda kusan ko yaushe yana tuna yaron haka kawai son Assalam ya shiga zuciyar shi,,
   Tsaraba sosai yakawo ma Anty Dije da yaranta don gaskya saida Anty ta kasa yin godiya,
   Ita kanta Anty wasu materials madu kyau da tsada yasako mata ciki tare da dogayen riguna,
   Issalam tana gama ganin kayan tace ina na little mummy din mu,
   Da sauri Anty Dije tace mata ai nawa tare da natane zamu raba,
    Wani inji Maryam dake kokarin bude fridge a lokacin don ta debo kayan miya,
    Kai ta girgi,za wa Anty tace a nutse na yafe nikan gaskiya ban so,,
   Issalam tazo har inda take gaban fridge tace kina so mana little mummy bake ki,kace mama tasaya maki anko ba,
  Hannun yariyar maryam ta hado guri guda tace Issalam  nagode ban so nace maki
  Anty ce tace ke kyale zata karba ai wasa take yi,
  Cikin mamakin maganar anty dije ta dago kai kalle ta, da niyar magana,sai kuma ta shiru kawai don irin kallon ki shiga taitayin ki da anty tai mata,a lokacin,
   Assalam ne yace mama don ba,a sayo mata nata bane wai bata so ko,???
   Nace maku bana so kawai simply ta fadi a nutse daidai lokacin da take kojarin barin gurin,
   A hankali yabita da kallon mamaki saboda sai yanzu yafara fanin tsana karara a cikin idon wanan yarinyar,
   Ya rasa dalilin wanan tsanar da yar karamar yarinyar ke mashi haka,?
    Bayan tafiyan shi Anty taima Maryam fada sosai har takai maryam din yin kuka don dai ita gaskiya bata ra,ayin wanan mu,amular da su anty keyi da wanan Arnen sam, 
     Washe gari maryam na tsakar gida zaune da farantin shinkafa akan cinyar ta, tana gyaranwa  tana raira kira,ar ta, ahankali,
       Joseph yai sallama suka shigo tare da Aisha
  Wacce tai kwalliya cikin wasu irin haddadun buje da riga masu kyau,
   Kallo guda tai masu ta kau da kai gefe guda don bata son kara daga kai,
   A hankali tace masu bata nan amma tace indan kazo ga abinci a falo,
  Daga haka bata kara wani zance ba sai kokarin ci gaba da aikin gabanta tayi kawai,
   Aisha ce cikin magana kamar rada tace wanan yarinyar na lura bata da kirki wallahi,
  Ji yadda takewa mutane magana wani iri kamar tana jin warin su,
  Baice mata komai ba asali ma kamar bai jita ba,
   KB ne yai sallama sosai irin ta musulunci duk da bawai ta sake mai fuska bane amma dai ta karba mai cikin girmamawa da nuna kula,
    Daga inda take tanajin suna hira akan wani guy wanda cikin su yake saidai yanzu mahaifin shi bai bari yana binsu sosai,
   Wai yana zuwa aikin a gonar mahaifin shi ko yaushe ,
  Joseph ne ke cewa gaskiya Umar na ban tausayi don ranan da na ganshi bazaka ce yataba rike biro ba arayuwan shi,,
   KB yace Umar din ai yace zai zo zuwa anjima don yana son ku hadu dashi,
 
    Cikin dan lokaci jibrin yai suna a cikin gari wurin yan kasuwa da sauran manyan mutane,
   Don jibrin mutum ne wanda ya iya business so sai da jama,a,
  Ga kuma tausayi da sanin ya kamata, akan harkokin shi,
  Musan man dayake yana kara samun taimako daga gurin ubangidan nashi a asarice,
  Ta yadda mutane bazasu iyagane cewa business din shi bane,
  Saidai su dauka na company ne kawai,
   Joseph ya koma gurin wanan matar abokiyar mahaifiyar shi mai manja,
   Inda yake sa ana kawo mata kayan masarufi tana sayar wa talkawa cikin sauki,da rahusa,
   Ta yadda tallaka ba zai yi mugun wahala ba, sosai wurin samun abinci,
   Tuni sunan su ya fara fice ga al,umma tun mutane suna zargin su har aka gane cewa business ne sukeyi tsantsar ta don ci gaban mutane,
  Matasa da  dama sun samu abin yi yanzu wanda hakan yasa emirate taji dadin zaman Joseph a tare da al,uman su,
  Wani  abin sha,awa kuma shine idan ya samu labarin cewa a unguwa suna samun matsalar ruwa ko wuta sai yasa sai yasa a tona masu famfon burtsatse ko kuma ya sauke masu transformer,
  Ya sayo motoncin noma birjit ya tura kauyo ka mafi kusa don tallafawa,
  Dalilin da mutane suka sa mai furen juji ke nan,don dai yanzu yan kwamintin su na chu sunkirashi mitin yafi a kirga amma yaki halarta,,


ZEEEE MAKAWA,,,,
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
   FUREN   JUJI
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
          1鈨�2鈨�
ZAINAB IDRIS MAKAWA



   Ejoma  ce zaune a saman wani dutse dake ta, bayan dakunar kwanan su zaune,
  Duk abin duniya yakai mata ko ina sai tunane take yi lokacin da Amina ke mata kalamai masu ratsa jiki
  Har yake mata tayin shiga cikin addinin su yana cewa zai aure ta zai zamay mata tamkar uwa ko uba,
  Dan siririn hawaye ne ya silalo mata daga cikin idon ta ya biyo ta kumatun ta,
  Muryan Aminu ke mata yawo a kwakwalwal ta inda yake cewa bai taba ganin wata mace mai irin surar jikin ta da yaji yana so ba aduniyar nan in har zata amince mai shi yayi alkawarin aurenta,
  Wa yan nan kalaman ne sukayisukayi tasiri a zuciyar Ejoma har ta yarda da maganganun Amina yai galaba akanta,
  Don Alokacin tana ganin kamar cewa tafi ko wata mace dace, da masoyi,
   Kamshin turaren shi na THE wanda ya hade dana JOJOBA,
  Shiya dawo da ita daga tunanen nadamar da takeyi a lokacin,
    Kamar ya wuce inda zai tafi amma kuma sai yanan yarinyar da irin yadda yaganta zaune a takure yasa shi jin wani irin tausayin ta alokaci,guda ya tsargu mai a zuciya,
  Cikin yaren su na IBO yake mata magana, a cin taushin harshe,
  Yake mai ce mata may ke faruwa da itane har hakan yafaru da ita,
  Wani sabon hawaye tafara shirin sakowa saida ya dakar ta da ita,
  Cikin daga mata hannu yace
  Hy ,I don't want dis your cry, cry pls,,,
 Just tell me what happen with u,
  Nan takoro mai da duk abinda yafaru tunda ga farko, tana fadi cikin sheshekar kuka,
   Yana tsaye hannu cikin Aljihu yana saye da farar suit, sai bakin wando,
  Wata yar jar ,T-shirt ke ta cikin rigar suit din nashi,
   Ya kafa farin glass a idon shi wando ,zaka iya ganin fararen idon shi kar daga cikin glass din,
  Yakai wani dan lokaci a tsaye yana nazarin yarin wace duk taba shi tausayi,
   Don yasan cewa wanan abin yana daga cikin destiny' din ta ne dama,
   Bayan dan tunanen daya yi na yan dakikoki, sai ya dan nisa kadan wanda ko ita ba lalai ne in har taji ba,
  Nobar wayan Aminu yabukata daga gurin ta, ba, bata lokaci ta bashi dama nobar na a kanta ta haddace shi tsab,
   Tana mika mai bai tsaya ba ya juya kawai ya wuce abin shi, batare da yace ma mata komai ba,
    Tuki yakeyi amma zuciyar shi jin ta yakeyi kamar zata fito daga cikin jikin shi,
   Why some people are not trusted,
  Why men's are cheating girls nowadays,
  Some say girls are to blem too,
  Amma shi a gurin shi ai mace abin tausayi ne sosai,,
  Amma wasu maza sun dauki mace abin wulakantawar su duk lokacin da suka gama da ita,
   Sosai maganar Ejoma ya tsaya mai a rai gashi ta bijirewa iyayen ta,
   Shikuma saurayin yayi rejecting din ta at last, su kuma yan uwan ta mai makon suyi hakkuri da ita,sun ki sun dauko ta sun kawo ta nan ,,
   Unguwar su jibrin ya nufa don KB baya,gari yana Abuja,
   A wayar shi yakira,jibrin din yana maisheda mai cewa yana son su hadu,,
   Inda yake yai mai kwatance gurin wani aikin hannu da yake koyo,
 Joseph saida suka,sha kwana sundan yi tafiya kadan  batare da ya waigo inda,jibrin yake ba ya ce,
  Ko kasan Aminu Aliyu masuga,
 Jibrin wanda tun shigar shi motar baiyi magana ba ya sai yanzu,
  Yace dangida namasuga, ke nan ko don naji kace namasuga wanda ke uguwar jankidi,, ko ?
  Joseph wanda yakai iyakar kaduwa yace ban san ko a ina yake ba,
  Yana mai karya kwanar filin kwallo yake ce ma jibrin ina son ganin shi ne,
  Ok kawai jibrin ya ce mai da yace hakana,
   Nokia shi ya ciro cikin aljihun shi ya kira wani kanin shi Abdullahi,
  Yake tambayar shi ko yasan inda Abdullahi yake zama,
   Gurin da Abdullahi yai masu kwatance suka tafi,
  Aminu yana zaune saman mashin din shi lipan wani abokin shi yana tsaye suna magana ya ji ana mai horn da mota abayan shi,,,
   Abokin ne ke ce mai ga wata hadadiyar mota fa kamar suna magana nake ga,,
  Aminu wanda ya juya bayan shi sai gefen shi kawai mutum zai iya hangowa,,
   Jibrin ne ya isa inda su Aminu suke yai masu, sallama, nan yake sheda ma Aminu cewa,, suna son ganin shi pls,
   Bayan Aminu ya saurari duk abinda jibrin ya tambaye shi ne,
  Ba musu ya ce masu lalai yana tare da Ejoma sai dai ai ba wai lalai dole bane ace shi kadai ke taraiyya da ita,
   Maganar shi taba Joseph mamaki, duk bayanin da suke yi bai yi magana ba sai kallon su kawai yake yi,
    Daga karshe Aminu ya dan bugi kafadar jibrin yana cewa,,
  Haba jibrin may zanyi da kafira ina zan kaita, kai min adalci mana kaima,.
  Kasan cewa ba abinda zanyi da arniya kamar Ejoma a gidan mu,
   Jibrin Joseph yace cikin wata irin murya mai nuna gajiya da sauraron magana,
  Muje kawai dan Allah, is ok hakana,
  Ido yabi su dashi har suka bace mai dagani,
  Inda abokin shi yake ya koma yana tsuki yace ji mun wa yan nan fa wai akan zancen Ejoma Ebere ne suka zo suna bata min lokaci,
  Ina ni ina KAFIRA ,,, ARNIYAR banza, wace ko kama ruwa batayi,
  Dariya mai karfi abokin shi ya shiga yi don jin kalaman Aminu,
  May kake ma dariya haka ne wai
  Nuna shi da yatsa yayi cikin dariyar yace bata kama ruwa kai sai yanzu ka san da haka bata kama ruwa,
   Lokacin da kake holewa da ita duk wanan baizo ma arai ba sai yanzu,
  Malam kawai kayi JAHADI mukan mu je  Onitsha musha bukin gaban dodon tsafi,
   Kai dan Allah shere kawai da banzaye kaji ni duk in rasa wace zan aura sai ARNIYA
   Kaifa mutumi dafa cewa kayi zaka musuluntar da ita ka aure ta to yanzu ina zancen musuluntar ya tafi,
   Kai jafar ka ga alamar musulunta a,wanan yarin balle har kai zancen yinta,
  Jafar yace gaskiya tunda tana,son ka musuluntar ta ba wani abubane mai wuya,
  Kai malam kaga idar har kana ra,ayi zaka  iya,don wanan ai taimako ne,,,
 Ka jin tsoron Allah Aminu,
  Kamar yadda baka so a diyar ka ko wata yar uwanka wallahi su ma haka ne wanan abin yake da zafi a gurin su,
  Kamar ace kaunar ka ko diyar ka ta hada connection da Dan ,Ahalkitabi, ya zakaji a zuciyar ka,
  Har kuma ace ya bata ma yar uwar ka, ko diyan ka,, shin zaka ji zafin abin da yai ma ko kuwa,???
   Duk wanda yan dake, gurin su kace gaskiya da ciyo wanan abin hakan bai kamata ba,
  Zafin maganar su ya ji don haka ya hau mashin din shi, ya,buga ya bar gurin cikin fushi,,,,

     Da hannu guda yake tukin motar hannu shi guda yana yi yana shafan fuskan shi a hankali,
   Wata bangararen zuciyar shi kuma maganar Aminu ce ke mai yawo a kai,,,
   Tsawon lokaci suka dauka yana tafiya a hankali da motar,
  Ba, wanda yai ma wani magana tunda suka fara tafiya,daga shi har Jibrin din,,,
 Gidan Anty Dije kawai zuciyar shi taraya mai yatafi  alokacin,,
  Kofar gidan Anty Dije yai parking jibrin baiyi mamakin hakan ba don yasan cewa yakanzo gidan,
   Sai a lokacin ya dan kalli jibrin din yace mai, ina son in,gaida sune,,,,
   Bayan shigar su cikin gidan sun samu Anty da yara a falo suna karatun hadda,
   Nan suka zauna suna kallon yadda anty ke wa yaran karatu cikin fasaha,,,,,
 Joseph yana zaune gefe duk sai yaji yaran sun kara birge shi,,,
  Saida suka gama ne Anty Dije ta waigo inda suke suka fara gaisawa,
  Nan sukan dan fara hiran karatun yarw sai kuma na yanayi dake zuwa,,,,,, saidai hiran duk akan zafin da aka fara ne a lokacin,
   Maryam maryam Anty Dije ce ke kwalawa maryam kira a wanan lokacin
  Maryam wace ke daki tana gyarawa ta ansa daga can,,,,,,
  Daidai kuma lokacin da wayar da ke a cikin aljihun rigarJoseph tai kara,
   Aisha ya kike,  ?maryam wace ke shigowa don amsa kiran Anty Dije
   Idon shi, a lumshe yake magana yadafe goshin shi,
   Batare da ta kalle su ba tace Anty gani
  Baki gaida mutane ne maryam , ?
   Wai may yasa baki iya gaida mutane, maryam, sai a lokacin ya bude idon shi da suke a lumshe,
   Ya sauke su ga wace ta shigo falon
  Cikin kwantar da murya kamar ta shagwaba, ta dan rusun na tace ina wunin ku, a kunya ce,
   Jibrin ne ya amsa mata da lafiya lau,
  Jin gudan bai amsa mata ba yasa tadan saci kallon shi inda yake zaune,
   Dammmm gaban ta yafadi don gani wanan dan Christian din da tagani kuma gashi da shiga kamar ta yan musulumai,
    Shiko ido yazuba mata kamar itace yake kallo, hakan yasa ta wani daure fuskanta ta ma,u,,
   Don ita dai gaskiya bata ga abinda zaisa su anty su kama hurda dashi ba,
   Sai muryan Anty Dije ya bugi kunnenta tacewa maryam dauko ma su abin sha dan Allah,
   In har ba kunnenta ke mata karaba da,zata shigo kamar Aisha taji yace,
   Amma kuma sai gashi taji yana kamar magana da maishi ta tsigar soyayya,
   Tir tayi da Allah waddai da irin halin wasu diyan musullumai masu kokarin watsar da daranjan su da kima, soboda kwadai, suna, hurda da diyan kafirai,
   Ruwa da goran kunun aya, tadauko hade da cups sai dai har yanzu wayar yake yi,
  Ji tayi yana cewa ina gidan Anty yanzu haka,
  Cikin wani irin mamaki ta kalli inda yake zaune, yadan kwanta Abayan makarin kujerar,
  A cikin zuciyan ta tace ji wai Anty Allah ya tsari anty da zama antyn ka,
  Kwantacen gidan tajiyana ma wace suke wayar tare,
   Gaskia bazata iya zuba ma kafiri ruwa ba,don haka ta dan gware ruwan da cups din tafito,
    Amma tana mamaki  jin cewa, wai gidan Antyn shi, sai kace wani dan uwar mu, can Allah dai ya raba mu,
   Tana tafiya ita kadai har tana tuntube,tana guna,guni, a fili ,,,,,   
     Ba,afi yan mintina ba sukaji sallama Aisha, tana sanye da wasu materials dinkin redemaid, tasa yellow,
  Da wasu takalma masu tsini a kasan su, rataye da wani handbag na company Gucci,,,,
   Joseph dake zaune yai mamaki kwarai da ganin Aisha har gidan Anty, don bai taba tsan manin cewa zata biyo shi nan ba,
  Cikin girmamawa ta gaisa da Anty Dije duk da bawai sanin ta Anty Dije tayi ba ,sun gaisa a mutnce da ita
  Sai ta juya inda su jibrin suke zaune tana mai kallon su, yar karamar harara ta sakar mai,,
  Tace ance mun an gan ku,a tudun wada, lokacin Anty Dije ta mike don ta basu guri,
   Joseph da sai a lokacin ya iya magana tun shigowar Aisha yace, Anty 
  Ina son zamu, wuce ,don ina son zanga Dad dina kafin gobe,
  Ku bari mana kudanci a binci dan Allah saboda ku na kara yawan shi,
   Da wata kasalaliyar murya ya ansa a hankali da kinbari wallahi mun gode,
   Jibrin ne yace kai Man ka tsaya kawai kaci abinci don ko mun tafi ba abincin, zakaci ba acan,
   Juyawa jibrin yayi yanamai kallon inda Anty Dije take tsaye kusa da kofa ya fara bata, labarin abinda yafaru da Ejoma yarinyar da yanzu haka tana gurin baban Joseph da zama,,,,,,,
   Dawowa tayi inda ta tashi tana maimata Innalillahi ,cikin tashin hankali, da nuna damuwa,
  Kai kawai take iya girgiza a lokacin saboda tana mamaki, yadda za,ace diyan muna musullumai suna bibiyar diyan arna suna lalata dasu,
  Cikin sauri ta kalli inda Aisha take zaune sai wani irin salo takeyi a gaban Joseph,
  Nan ta kara yin tir da irin masi rayuwa irin na Aisha saboda kwadan duniya ka wulakanta kanka,
  Don dai shi wanda takeyi kashi baima san cewa tanayi ba don ko kallo ta baiyi ba tunda tashigo,
  Wanda ma nunawa yayi da bai ji dadin shigowar nataba
   Ita dai Anty Dije fatan ta koyau she Allah yasa Joseph ya gane hanyar gaskiya,
  Sai a lokacin maryam tashigo falin cikin shirinta na isalamya,
 Kallo daya ta watsa masu inda suke gabadayan su,
  Wata uwar tsana da takaicin ganin su ya rufto cikin zuciyar ta
  Annurin fusakarta duk yagushe, ta bata rai, tana mai murtuke fuskan ta,tankar taga wani mugun abu,
  Duk wanda ke falin yaga irin mugun kallon da maryam ke watsa masu a lokacin,
  Amma sai suka dauka kila halinta ne hakana kawai,,,,,,,
 
   Barci yake yi amma kuma yana mafalkin garin da yafi kauna lokacin da yake yaro,
  Watau garin mahaifiyar shi da yafi kowa kaunar ace za,a tafi wanan garin,
  Kusan wata biyu kenan ko yaushe yana cikin ganin wanan nahiyar a mafarkin shi ko kuma tunane,
  Don haka yanasa wa ranshi son zuwa ya dibo yar tsohuwa mai munhinmanci tilo guda data rage masu,
  Watau mahaifiyar maman su wacr tun suna yara aka hana su zuwa gurin ta cewa wai ita witch ce
 Inji dangin uban su, haka yasa busu saba da ita ba sam,,,
  Yadda yaso shine sai yaga yadda zancen Ejoma ya kai karshe sannan zai koma Lagos, gurin sanar shi,
   Amma sai elders sukace sai nan da karshen wata zasu kara zaunawa,
  Don haka yabata gudu taboye yadda zata iya taimakawa rayuwar da abin bukata,,,,,,

   
    Gari ya nuna alamar hadari kamar ,ruwan sama, zai iya fadowa kowani lokaci,
  Zaune take da dauri zani a gaba duk da tana da riga a jikinta amma daurin gaba tayi,,,
   Wake take tsinta a wani tire maidan fadi, sai wakan su na yan church take rewa cikin wata murya maiban tausayi,
  Cikin sauri take aikin duk da ta tsufa,
   saboda yanayi, da garin ke ciki don ruwa na iya zubowa ako wani lokaci
  Wani kare ne kwance gefen benci da take zaune, daganin shi zaka ce ko shi kadai ake kiwo a gidan saboda koshi,
  Jin karan motar da karen yayi yana nufo gidan su shi yasa shi mikewa tsaye yana haushi cikin karfi,kamar zai tashi sama,
   Horn din mota ce duk ya ruda gidan yar tsohowar dake zaune a lokacin tana kokarin mikewa don jin yadda karen ta ke  ta haushi alokacin, guda. 
   Jin horn din mota  ya tabbatar mata da cewa a,kofan gidan ta ake horn, din
   Sam bata kawo cewa bakon ta bane don rabon da ta, ga wani yazo gurin ta har ta manta, lokaci,
  Don tun lokacin da diyar take zuwa da mijinta dayaran su idan sun zo daga Arewa,
  Bayan fitinar da akayi ita da dangin mijin yarta yasa duk suka dauke kafar su da ita,
  Duk da tasan cewa ita ba muguwa bace sheri ne kawi irin tasu,
   A hankali ta dan fito daga can ta bayan gidanta inda take girki don taga ko waye a vidan ta,
   Duk da girman da yayi da kuma nuna cewa yana cikin daula,
  Hakan bai hanata gane jikan nata ba,, a lokacin don rabonta dashi yanzu kusan shekara ashirin ke nan,,,,   

ZEEE MAKAWA
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
   FUREN     JUJI
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
         1鈨�5鈨�

ZAINAB IDRIS MAKAWA

  Alhamdullah Allah yakawo yau, maryam sun zana jerabar su ta karshe a girls day secondary school, kwantagora,
    Fitowar war,ta kofar class din tai wata ajiyar zuciya gami da fesar da watar iska irin na relief din nan,
   A hankali take tafiya zuwa bagin get don tafiya zuwa gida jitayi an jawo ta, Assamau musa ce classmate din ta mai photo ta nuna mata tana da bukar suyi photo,
  Fara photon nasu ne wasu yan gidan jodda suka shigo akayi da su
  Maryam wace kawo yanzu duk ta kagara ta wuce, gida
   Don ta huta saboda duk kwanakin nan bata samun barci don mathematics ce zasu zana karshe,
   Gani zasu bata mata lokaci da yawan daukar photona ya sai ta, sa kai kawai zuwa fita daga school compound din,
   Wata mota tagani tana jiran wata yariyan batai mamakin haka saboda ga abin hawa na birjit a waje suna jiran yan uwansu wasu kuma samarin su,
   Tabbas in ba karya idon ta ke mata ba wanda tagani bakin motar KB ne, don ko ina zata gane shi yanzu don yawan zuwa gidan su da sukeyi ko yau she muddin suna gari,
   Kai takar kamar bata gan shi ba sai tafiya takeyi cikin sauri don ta isa gida,
   Horn takeji a bayanta kamar kada ta waiga fon tasan cewa ba asaman titi take ba ita,
  Sai ganin motar KB tayi gaban ta ya Parker dan zuge glass din motar yayi yana mai dan lekowa ta window motar,
   Sai a lokacin tawaiga batare da ta daina tafiya ba,
  Ta furta a hankali ina wuni,, dan murmushi ya sakar mata ce little mum babu gaisuwa ,
  Dan murmushi tayi wanda ya baiyanar mata da fararen hakora ta da suke a jere ras a cikin dan karamin bakinta,
    Tace ai na gashe ka ko, ?
  Yace zo muje mana mu saukeki a hanya , gani wata classmate din ta zaune a bayan motar yasata dan kara yin murmushi tace ku tafi kawai ai zan hau achaba yanzu,
    Ganin zai kara mata magana yasa ta tsaya badon taso ba don dai kada mutane su samasu ido
  Don yanzu ba,a raina sa,ido ga dan karamin abu,
    Tana kutsa kanta a cikin motar wani irin sanyi da kamshin wanda bata iya tantance ko motar ce ko kuma masu motar ke wanan uban kamshin haka,
   Ga sanyin AC ya hade da kamshi wanda zai iya sa mutum acikin wani yanayi, (A,uzu,bikalamatilllah ,tamattah), tace yayin da take kokarin zama a motar,
   KB ne ya juyo a hankali yana mai cewa taufa malama ce injin muka dauko,
   Maryam da sai yanzu bayan ta samu natsuwa, ta sheda ko wace su KB suka fara dauka a motar
   Wata, fatima Indagi ce yar gidan nufawa asalinsu mutanen garin Bidda ne zama yakawo su kwantagora,
  Har suka zama yan gari yanzu don sun san kowa kowa yasan yan gidan su,
   Bawai wani shiri sukeyi ko a school da ita ba don haka ko kallon inda take,Maryam batayi ba,
    Baka jin komai daga cikin motar sai kida ke tashi ta yadda ko na wajen motar zai iya jin kidar daga waje,
   Maganar shi yasa maryam gane cewa yana cikin motar wace tun shigowar ta motar kanta na gefen glass tana mai kallon waje,
   Dammmm sautin da kirjin ta yabayar ke,nan a lokacin da taji muryan shi a motar yana cewa,idan ka sauke su mu wuce uguwar JANKIDI pls, zanje inga Abdulsamad,,,
  A hankali kwance yake maganar batare da ya kalli cikin motar ba gefen KB din,
   A,kofar gidan su Maryam, din  suka para tsayawa don su sauke ta,
  Daidai lokacin Assalam yadan fito ta wajen gid脿 y脿 na kallon motocin a ke wuce wa
   Kokari takeyi ta balle murfin motar daidai lokacin da Joseph din ya dan dan,na gurin da duk security din motar suke,
   A lokacin kuma Maryam ke fadi cikin siririyar murya,
    Nagode, ta furta a hankali ta yadda ba wai lalai ne wani yaj abinda tace ba,
   Hannu kawai shima yadan dago mata alamar ba matsala,
   Da gudu Assalam yazo ya rungumay mata yana oyoyo little mummy, dan jakar hannun ta yake kokarin karba daga hannun ta,
   Sai a lokacin yai arba da Joseph wanda ke a gaban mota zaune,
  Sake jakar yayi ya sheka da gudu gurin motar yana washe  bakin ganin Joseph din,
    Juyawa maryam tayi abinta batare da da tasaya koda kallon su ba
     UNGUWAR JANKIDI, wani unguwane acikin kwantagora, inda wane abokin sanar mahaifin Joseph yake zaune,
  Emeka ake ce mai ,,,kusan tare sukazo neman kudi agarin, tun suna matasa,
  Saidai Allah da ikon shi , cikin wani watan Azumi, sai kawai aka wayi gari wurin wani tafsirin marance da ake yi, Emeka ya kawai sai ga Emeka yace yazo ya musulunta ne,
   A ranan yakarbi musulunci a hannun babban malamin dake wa maza tafsir, a kusa da gidan sarki,
   Ranan duk wani IBO da ma sauran Christies hankalin su ya tashi sani cewa kowaye Emeka da sukayi,
   Duk wani hanya dazasubi don suga cewa sufitar dashi a cikin musulunci abin ya faskara garesu,
   Har kudi suka hada mai uban yawa suka kaimai wai yadawo cikin su amma sam yaki karba,
  Daga baya da sukaga yaki sai suka fara shawaran yadda zasu cuta mai har ya karaya, yadawo masu,
   Wuta suka fara sama shagon shi a tsohuwar kasuwa inda shagon ya kone kurmus,
  Da sukaga baizo wurin su ba sai kuma wani dare suka turo har gida aka sace duk dan abinda yasaura a hannun shi suka gudu,
  Yan kwamitin su sukazo mzi da makuddan kudi suna mashi tayi akan yadawo cikin su,
  Amma san Abdullsamad yaki dawowa, yace shi ya shiga kenan,
  Maimako yan uwa musullumai su tausaya mai su mai tallafi ko wani gudun mawa sai kawai aka shere shi nan,
  Ganin wahala yai yawa yasa matar shi gudu tabar shi ta koma kasar su, inda takoma ma Christian din ta,
   Tabarshi nan tare da yaran shi ma,za uku, suna ta buga,buga,
  Yanzu har takai ko suturan sawa baida shi dan gidan shi rabi ya zube baida kufin gyara saifai kawai Allah ne ke rufa masu asiri su samu abinci,
   A haka ya auri wata musulma ma sanar saida shinkafa a bakin kasuwa,
   Yakan je gurin Mr Ema jefi,jefi in abin yadaure mai da yawa,
  Saidai duk sanda yatafi zai dawo da tarin bakin ciki a zuciyar saboda irin yadda Mr Ema kan ta sake mai maganganu,kuma duk kyautar, da zai mai bawanda zai amfana dashi bane, daga dari biyar tsanani dubu biyu,
   Rigar shi duk ta yage yage a baya, hakana yake sawa yakoma kamar mahaukaci,
  ( Allahu Akbar munada wanan raunin wallahi musullumai bamu tallafawa wa yanda suka tuba yanzu,,,,,,,)
   Mama manja ce ta fadawa Joseph cewa yana bukatar taimako sosai saboda sani da tai ma iyayensu tare a da,can,,,
   Yai mamakin jin cewa har yanzu Emeka Abdullsamad yana agari batare da yasani ba,
   A hankali suke gangaro da motar su zuwa cikin unguwar wanda akasari duk tsofafin gina ne a gurin,
   Zaune suka hango shi saman wani tsohon icce dake kofar gidan shi ,
   Cikin wata tsohuwar rigar atamfa duk ta kode ga farin gashi duk ya dan cika mai fuska,
   Yana zaune kai dagani kasan cewa yana cikin halin hau ula,i,,,
  Har suka faka motar su baidago kai ya kalle su ba,
  Saicewa yakeyi a fili Subbahanallahi, Walhadullahi Allahu,Akbar,,
  Sallama KB yamai daga inda suke nufo shi ya karba masu tare da daga hannu har saida yakai aya, tukun,
   Sam bai gane Joseph ba a lokacin saidaga baya bayan ya mika masu hannu sun gaisa, duk da kallon mamakin da yake masu namay yakawo su gurin shi,
   A fuska yadangane Joseph din cikin yare yai mai kirarin gidan su,
  Inda Joseph din yadan duka agaban shi yai mai yar gaisuwa irinta al,adansu
   Abdullsamad yadan bugi kafadar Joseph din alamar ya karba mai gaisuwa,,
    Joseph  yace mai baba kana garin nan shine kashige haka shiru, ,,
   Murmushi yayi yadan mike ya ciro wata tsohuwa ashirin a aljihun shi yana kokarin zuwa wani shago xuwa sayo masu pure water leda,
  Cikin sauri Joseph yace mai a,a yabari kawai ,acikin nuna damuwa da kulawa yace ma Joseph kabari in shayar daga kai daga cikin dan abin da nake dashi pls,
   Yanamai daga hannu alamar ban hakkuri agare shi,
  Dole badon sun so ba yakarbo masu ledan ruwa, gida biyu yadawo katakata cikin sauri ya mika masu,
   Sukaiyi mai godiya Joseph wanda ke ji alokacin kamar ya zubar da hawaye don tuna kowaye Emeka,
  Yace mai ina sauran yaran shi suke, nan yake sheda masu cewa, mutum uku suna nan tare dashi,
   Saura kuma sunan can garin su tare da maifiyar su,
   Dan shiru ya biyo baya duk kan su kowa da abinda yake anyanawa acikin zuciyar shi a lokacin,
  Joseph ne kauda shieun take cewa yaso koda zai samu ganin yaran koda mutum guda ne daga cikin su don yana son suyi wani yar shawara, nobar wayan babban ya basu, wanda uban yace yana koyon sanar Carpenter ne yanzu,,,
   Kudi yabashi dubu hamsi yace mai nada wani sati zaiga sako in ya koma,
  Sundanyi hira kadan sannan sukayi sallama, dashi suka barshi, cikin tausayawa da irin halin da yake ciki a yanzu,
   Ganin wana bawan Allah yasa zuciyar Joseph a cikin wani irin
yanayi, wanda ya hanashi sukuni,
    Kasancewar yau jumma,a ne mutane sai haraman zuwa massalaci sukeyi gungu,gungu mata kuma suna gida sun chaba ado kamar sallah,
   Gidan 脌nty Dije ma ba,abarsu a baya ba don daga manyan har yaran cikin kwalliya suke suma,
   A,wasu gije har abinci akeyi ta musanman don farincikin da darajan wanan ranan,
  A wasu giden masu dan hali kuma zakuga ana ta rabawa yara dan abin sadaka wasu da safe wasu kuma sai bayan ansauko daga jumma,a,
   A lokacin da kowa ke ta haraman zuwa sallah jumma,a daidai lokacin ya shigo gidan na Anty,
  Wanda a yanzu duk sun saba da irin zuwan shi sun,san cewa inhar yana gari to baida gurin hutu sai guri su
   Saboda har cikin ranshi yana son yananyi irin na antyy Dije
  Don mace ce wadda tasan kanta dama duk wani wanda yake tare da ita,
    Alwala maryan keyi da buta a yar tsakar gidan su inda Assalam ke tsaye wai yana jiran tayi tabashi,
  Muryan Maryam din ne ke cewa kai Assalam wazai kaika masallacine wai tunda Daddy baya gari
  Joseph yanuna da hannu shi yace da Uncle zamu tafi ma na, ko uncle,?
  Yana mai tambayar shi, cikin azama,
  Yace mai eh Assalam, tare zamu,
  Maryam wace ke kokarin wanke kafar ta ta waiga da sauri takalli inda Joseph din yake,
  Muryan Anty Dije ne ke cewa, kai Assalam kabar uncle ya huta pls, kabari har Daddy ya dawo sai ya kaika,
  Kuka yaron ke kokarin yi alokacin ciki sauri Joseph yace No, bar shi inkaishi mana anty,
  Buta yaron yadauka yafara alwala kamar yadda manya keyi,
  Ba abinda ya fadowa Joseph a rai sai zuwan su jereselem, da kakar shi,
  Inda sai kayi kusan duk wasu abu da musullumai keyi na ibada,
  Gashi Assalam karamin yaro wai har yasan cewa zai gana da ubangiji yayi tsarki,
  Muryam Assalam ce takatse shi yana cewa nagama uncle, mutafi,
  Ga mamakin kowa mikewa Joseph din yayi yakama hannun yaro
  A hanya yaga wasu idon sani yafarka motanisa yabasu yaron yace suje dashi
  Ana tasowa suka kawo mai shi yatada mota yajuyo tun ba,a tashi ba,
   Kayan su fruit yadan tsaya suka saye a hanya sanan suka karaso gida
  Daga Anty har maryam sun matsu suji ya akayi da suka fita, tare zuwa masallaci da,Assalam,
  Kayan fruit din suka shigo dashi nikiniki a cikin ledoji ,,
  Maryam wace tafito cikin kwaliyar ta ko kallon su batayi a da suka shigo gidan,
   Da kanshi ya nufi har gurin fridge ya aje kayan a hankali daidai lokacin Anty Dije ta sallamay tafito, daga daki
  Yadda taga Maryam tayi mai sai kawai bataji dadin hakan ba,
Daki ta shige abinta don makada asata wani aikin,
  Dakun Anty ta fado rai bace sanan tahau surfanta da sababi,
 Maryam ta bude baki da zumar yin magana hannu Anty tadaga mata alamar batason jin komai daga gareta,
  Tace baki da hankali ko wayo zance inba wqutaba yazaki nunawa mutumin da ake fatan shiryuwan shi haka a fili,??
 Gaskiya ki gyara hali Maryam don kowa ma haka kike masu,
  Kada ki kore min jama,a pls,
  Maryam batace komai ba don tasan cewa yau ta batawa 脌nty Dije rai sosai don batai mata fada haka gaskiya,
   Murya na rawa tace don Allah kiyi hakkuri anty bazan karaba insha Allah,,,,,,


ZEEEE MAKAWA,,,,,,馃憦馃憦
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
    FUREN    JUJI
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
           1鈨�6鈨�

ZAINAIB IDRIS MAKAWA

   Zaune take a bakin gadon da ke cikin dakin su tai tagumi da hannu guda,shiru tayi sai tunane takeyi
  Don tunda take da anty bata taba ganin fushinta ba sai yau,
  Yau din ma akan wani bare kafiri , wanda ba musulmi ba ma,
   Wai may yasa za,a dinga takurawa rayuwan tane haka akan sai ta yi abinda zuciyar ta bai son aikatawa,
  Motsin da taji  shi ya sanya ta dago kai da sauri don ganin ko waye  shigowa, dakin,
  Anty Dije ce tashigo dakin tana rike da wani dan ledar mai nuna tambarin shago ajikin shi,
   Yar kujerar dake dakin ta zauna a hankali, tana fuskantar yar kaunar nata wanda tun dara bata fito ba,
   A hankali Maryam din ta dago kai karo nabiyu takara kallon antyn nata, sai kuma ta sunkuyar da kanta kasa tana kallon kasa,
   Cikim natsuwa Anty Dije ta fara magana maryam don nai maki fada yau shine kike fushi,
  Kinfi son in barki ki dinga yin abinda bai dace ba ko yau she, ?
  Dago kai maryam tayi da niyar yin magana suna hada ido dayar nata,sai kuma ta kasa fadin abin da tai niya,
  Indan har kinga cewa wullakanta dan adam na da kyau sai kici gaba,
  Tanafadar haka tamike tana cewa sai kizo ki ci abinci in kinga dama,
  Dago fuska tayi caba caba da hawaye, ta dubi yar nata tace,
  Murya kasa kasa  tace nifa ba fushi nakeyi ba anty,
  Fuskan Anty kumshe da murmushi tace Allah ya kyauta amma dai gaskiya ki gyara hali duk wanda zo gidan nan sai yai min korafi akan halin nakasa irin naki maryam,
 A dan tsorace ko mamaki tadago fuska, takalli yar uwan,
   Kuka tajeyi a hankali irin na bantausayin nan tace yanzu anty nice mutane kewa korafi,
  A ranan wuni zungur maryam tayi a daki tana ta faman fushi da kowa don har Issalam mutumiyar ta bataga fuska ba,,,
  Tunda safe tafito itace farkon fitowa tsakar gida tafara shara da kokarin dora masu abin kari kamar kullum,
    Saida anty Dije tagama duk abinda takeyi san nan ta fito waje tasamu yar uwar ta tana
  Sun gaisa kamar wani abu bai faru ba a tsakanin su,
  A tare suka kara aikin sanan maryam tai wa yara wanka kamar yadda ta saba yi,
 
    Tuki yakeyi akan hanyar shi ta zuwa Lagos gaba daya hankalin shi naga tunanen Assalam
 Yaro karami ya iya yin alwala batare da ankoya mashi ba,
    A hanya ya tsaya yaiwa kakar shi da Ejoma da suke zaune tare da shi a gidan shi na Lagos,
   Tsaraba, a wani dan kauye da ake tsayawa kafin ashiga garin, lagos,
   Tunane ya cigaba da yi na yadda zai, yi da mahaifin shi,
   Don kwata,kwata baya son zancen kakar su a rayuwan shi,
  Wanda shidai a iya zaman su yasan cewa mutumiyar kirki ce ita,
   Ya iso gari lafiya saidai yasamu G/ma bata jin dadin jikin ta,
  A yadda Ejoma ke fada mai tun wucewar shi kusan sati ke nan G/ma bata jin dadi amma ta hana a fada mai, wai don kada yadamu,
   Wanka yayi ko abinci bai tsaya yaci ba tashiryo cikin waso kananin kaya sai kamshin turare ke tashi
    Mama dake zaune saman kujera two siter yazo inda take ya zauna asaman hannu kujerar da take yadan rankafo kanshi saman kafadar ta kadan
   Yana tambayar ta a hankali ki may ke damun ta sai ce mai tayi batajin komai ita,
  Cikin dabara Joseph ya lalaba yar tsohuwar suka tafi asibitin da yake zuwa,
    Likita ya dibata da kyau inda yace ba wani abu damuwace ke da munta kawai sai dai yadan rubuta mata yan magananuwa don tasha,
  Bayan sun dawo gida dakanshi ya hada mata tea mai kauri ya hada da maganin ta yakaimata,
  Zaunawa yayi gab da ita yana dan bata a hankali har tadan samu tasha,
   Alokacin yadan mike tsaye da niyar barin dakin don yaje yadan huta, saboda yana tare da gajiya,
  Hannun shi mama ta riko da sauri ya jiyo don yasan cewa da magana kenan,
   Komawa yayi ya zauna gab da ita saida suna fuskantar juna a wanan lokacin,
  Fuskan yar tsohuwar fam da damuwa tace My child something bad wan happen to you,
  Joseph yadan kamo hannuta ya hade cikin nashi yana yar murmushi yace,
  Mama nothing will happen to me just cool your mind pls,
  Tace it ,will ,my son
I see am in my dream,
 Dariya yakari yi mata yana mai rungumota zuwa jikinta,
  Kalamai masu kwantar da hankali ya ke mata don yaga cewa ta saje zuciyar ta,
  A hankali ya mike ya kamata zuwa kan gado ya kwanatar da ita tare da jawo bargo ya rufa mata,
   A,hankali yabar dakin yana mai rufo mata kofar dakin,
  Saidai may yana fita daga daki sai kuma maganar mama ya dawo mai sabo a zuciyar shi,
  Fridge ya nufa  yabude yadauko giran ruwa mai sanyi ya dan kwa kwada,
   Hakalinshi a tashe don yasan cewa akwai abinda ke damun mama din saidai ba zai so ji ba don shi bai yarda da camfi ba rayuwan shi sam,,,
    Maimakon ya shiga dakin shi kamar yadda yai niya sai kawai yasamu kan shi dazama saman daya daga cikin kujerun dake falon,
   Yakai wani lokaci a gurin zaune yana tunane shi kadai bakajin karar komai a falin inbada na,urorin daje ta aiki a cikin falon,
   Azuciyar shi yake tunane don yasan cewa maganar irin su mama ,g tasu al,adan ba karamar magana bace,
  Da wuya su furta bai faru ba, to amma shi gaskiya har yanzu bai yarda da zance tsafi ko kuma wani believe ba can,
    Yakai wani lokaci gurin zaune yana iya na,zarin shi akai,
  Daga karshe dai ya mike jiki ba kwari ya shige don ya kwanta,
   Abakin gado yake a cikin shigar shi ta kayan barci bayan yagama komai, ga irin al,adan yakeyi kafin ya kwanta,
  Bible ne rike a hannu shi gwiwowin shi suna kasa kan shi a saman gado idon shi a rufe yafara jero addau,oin da yasaba yi kafin yashiga kwana
   Saidai wanan karon ya dan sauya addua,n shi bakamar yadda yasaba ba,
   A hankali ya mike zuwa kwanciya saida a lokacin kuma watan shi tai kara alamar sako ya shigo mai,
   Samuel ne ke sanar mai cewa Dad na fada dashi cewa anfada mai wai Joseph din yatafi gurin Abdullsamada
   Mamaki yayi so sai dajin haka don haka sai yai alwashin cewa daga wanan karon ba zai kara, daukar zance Dad ba na hana shi yin alheri ga duk wanda yaga dama nan gaba,
   Abdulsamad wanda ko ganisa mutum yayi bai san shi ba,a da dole ya tausaya mai,
  Balle shi da yagirma a gaban shi
  Shi agare shi may,ye amfani samun mutun ace bai iya taimaka wa na kasa da shi,
   Gaskiya duk abinda zaiyi wanan karo saidai ayi ta don dai shi yayi niyar tallafawa Abdullmalik din,
   Da wanan tunanen a zuciyar shi ya kwanta barci sai juyi yakeyi a tafkeken gadon nashi,

   Aisha wace tai shawaran zuwa Lagos gurin Joseph
   Don dai tagane cewa idan ta cin mai can tafi samun kudi, bisaga in yazo nan garin
  Don anan mutane sunayi mai yawa ga bukatun yau da kullun,,,
   Saidai tayi rashin saa yace mata aranan ya wuto zuwa kaduna don halartan wani taro da zasuyi akan karin farashin  da,suke son yi
   Bata hakkura ba don haka kaduna tasamay shi
  Saidai yana gurin meeting a lokacin don haka driver ya tura yadauko daga tasha zuwa inda yai masauki,,
  Sai gab da magriba yadawo yace ta shirya su, wuce zuwa Abuja yanada uzuri kala,kala acan don haka ba zai samu damar tsayawa kaduna din ba,,,
    Waya yakeyi alokacin don haka sai yaga kawai Aisha tana kokarin har hada kayan ta,
  Yana gama wayan yakai kallon shi gareta yace, sai naga kamar lokacin sallah yayi ko,?
  Bazakiyi sallah ba kafin mutafi, inafa zai fi maki don sai dare nasan zamu karasa,
  Tana wani jan kafa kamar bata son yin sallah a lokacin,
  Har ta idar yana zaune sai dan,ne danen wayar shu kawai yakeyi,
  Duk da bawai yasan ya ake sallah ba yadai fahinci cewa batai wani dadewa ba a gurin yin sallah,
   Don haka da mamaki yake ce mata har kin gama ko,??
   Don haka mikewa yayi yadauki duk wani belongings na shi dake daki zuwa waje,
    Sai cikin dare suka samu isah don haka masaukin shi ya wuce direct, don KB yasan da zuwan shi,
  Yasa an gyara komai duk da dai dama gidan kullun acikin gyara yake,
   Shikan Joseph suna isa a cikin daren nan fita yayi zuwa gurin wani mutum da yake son gani,
   Aisha tun tana jiran shi tana yar tsuki, har barci ya dauke ta, bada sanin ta ba,
  Kodo Joseph yadawo yasamu tayi barci don haja ko take away din da ya zo masu dashi batasamu ci ba,
   Kiran sallah da akeyi daga wani unguwa wanda da alama ba nisa daga gidan Joseph din shi yata da Joseph din a lokacin wanda dama al,adanshine haka duk wani Christian mai rikon addini yana tashi daidai wanan lokacin,
 Don yin morning prayers din su kullun,
  Aisha tana kwace shemay shamay saman gado, tana barcinta abinta,
  Yar rigar barcin da tasa don daukar hankalin Joseph, har barci ya kwashe ta yadan kware gefen ciyar ta a fili,
  Don haka yana fitowa yin burshe, ya isa har bakin gadon inda ake kwance ko motsawa batayi ba,
  Yana mamakin wanan irin barci haka ace mutum bai tashi ya yi morning prayer, haka,
   Hannu yakara kaimata yana dan dukar cinyar ta data dan kware wurin barci,
   Yana cewa baki tashi kiyi salkah kadafa time  ya wuce ki,
   Sai wani mika takeyi shiko sai kallon mamaki yake mata alokacin
  Yaga cewa ai Assalam yarone amma duk yake tare dasu akai kiran sallah
  Zakaga yaron na kokarin tashi zuwa yin sallah,
  Amma ita gata da girma ta yaga bata damu da ta tashi yi ba,,,
  Kallon inda yake tayi ido tafa da kwana, tace mai kabari kawai inda na tashi ai zanyi,
  Wani irin mamaki ya kama shi azuciyar shi yana mai cewa O God help me with dis ,
  Aisha sallah ma bazaki tashi kiyi ba sai kinga dama,
  Haba kiwa kanki fada mana ai dis is bad wlh, abindan lokaci kadan,,
  Tai wani mika badon taso ba ta tashi buguzun,bugunzun zuwa cikin bathroom, ko minti nawa bata kai ba saigata tafito wani dan yalalon gyale ta yafa
  Joseph wanda yai daidai da gama addu,an shi ya na kokarin rufe Bible din shi ya kalle ta yana mai kada kai cikin mamaki don ganin gyaken da ta yafa wai zatai sallah, dashi,
   Kwanciya ya yi rigingine ya kallon yadda take dangwara goshi kamar wace keda wani uzuri ,a gaban ta,
    Ba,afi mintuna ba ta sallamay tafado mai saman gado gaba dayan ta,
 Kokari takeyi ta fara romancing din shi sai yai dabara yadan jaye ta daga jikin shi yana nai ce mata zan dan fita jugging ne yanzu kafin gari ya haska,
  Yajaye daga jikin shi yana mai kojarin daga wa don ya sauka saman gadon,
  Sunan shi takira cikin wani irin muryan yaudara idon ta ya canza kalla a lokacin, tana mai ce mai
   Wai may yasa kake min haka ne pls ta ya zan bata time dina zuwa gare ja amma kai kullun sai ka kawo min uzurin da baikai yakawo ba,
  Tana kokarin kara jawo shi zuwa gareta yai saurin karasa mikewa daga saman gadon
  Yana maice mata ki tambaya kiji ni Joseph ba irin wa yan nan mazan bane da kike tsan mani,
  Wanan ma da kikaga ina maki just don kada kiga kamar banda,time dinki ne,
  Amma tunda kinga hakan ma bai isheki ba
   Ya nakai kofa yace pls ki daina zuwa don hakan ma na itmya jamin matsala,
  Mamaki da tsoro kalaman shi suka jefata ita Aisha,da mutum nawa ke kokarin kawa gareta ne yau har wani ke fada mata haka,
  Inbadon tasan cewa tana moriya dashi ba ko a haka da yagane cewa tawuce wanan kalamin gareta,,,,
  Bayanshi tabi da kalllo har yabar dakin cikin shirin zuwa dan motsa jiki,
  Hmmm Aisha bata san waye Joseph ba da batai tunanen hakaba daga gare shi,,,,,,,




ZEEE    MAKAWA
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
   FUREN    JUJI
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
          1鈨�7鈨�

ZAINAB IDRIS MAKAWA

  Alhamdullah jerabawan su maryam yafito yanzu ,yaya I,lliyasu ya samo mata guri bi karatu,a FCE kwantagora, inda zata karanta bio,chemistry,
  Maryam taji dadin wanan abin so sai ba maryam ba kawai har baba
  Don har gida yazo yai ma Anty Dije da mijin ta godiya akan kula mai da yar shi da,sukeyi tsakani da Allah,
  Maryam wandda yanzu girma da wayo yazo mata ta roki Anty ta barta taje gurin mamanta, acan Bobi kafin ta fara karatu,
   Anty bata kiya ba saida tace sai ta fadawa baba don kada, yazo yaji daga baya yai fada
  Baba bai,yi fada sai fatan adawo lafiya da yai mata yabata dubu daya yace tasai masu tsaraban man shafi da sabulun, wanka,
   Cikin kwana biyu akai mata yan shirye,shiryen tafiya,
  Duk da bawai maryan ta saba da mamanta bane amma dai tai ta zumudin zuwa kauyen,don tagane su,,,
   Ranan da zata tafi tunda safe ta hana idon ta barci don zumudi,
   Har saida Anty ta kasa kan,newa tai mata, magana
    Maryam wai,dama dai ashe kin dade kina son yin wanan tafin ne ko,
  Yar kunya taji da kuma nauyin Anty nata, saita dan sune kanta tace ,aa anty kawai dai ina son zuwa ne inga yadda garin yake wallahi,
   Har inda zata shiga mota Anty ta rakata tare da yaran su,,
   Inda yaran ke kuka sai sun bi little mummy su inda zata,
   Shiru take zaune cikin mota sai tunane takeyi yadda zata riski mahaifiyar ta ,
  Don dai tasan cewa zaman kauye na maida mutum  iri, sai tausayin mahaifiyar ta ya,kamata
  Tace Allah sarki mama ita kuma nan Allah yai nufin zaman rayuwan ta,
   Haka tai ta tunane azuciyar ta har suka isa garin kamfanin,Bobi, saidai tai mamakin ganin garin a saman babban titin zuwa minna da kwantagora,
   Tana sauka idon wa yanda ke zaune a bakin titi yayo kanta caaaaa
  Wani yaro tagani ya tafiya sai,tai mai sallama nan take tambayar shi gidan liman hamza,nan yaron yai mata kwatace akan tabi wani dan lungu, zata ga wani gida mai katon icce a kofar gidan tashiga nan ne gidan, tana bi kuwa sai gata a kofar gidan,,
  Da sallamar ta tashiga mata uku tafara gani su guda tana daka guda kuma tana duke tana wanki dayar kuma tana wanke wanken kwanoni,
  Duk kan su daurin zani agaba, ga yara manya da kanani nan jagwal da su, wasu majina ahanci wasu kuma kunu ya bushe masu a baki har hanci,,,
   Sun karba mata sallama cikin mamare ki wace don ganin tada sukayi da kaya a tare da ita,
   A cikin ladabi ta durkusa har kasa tana gaishe su ,
  Abin mamaki sai ganin mata takeyi suna bulowa daga wani dan lungu, ashe ganin tsoro taiwa gidan matane, ciki fam kusan su goma,
   A cikin sanyi muryan nan nata take cewa, don Allah mama Rukaiyan saleh nake nema,
   Wata mata wace ke daure da wani zani blue mai photo barewa ce tace taufa gani nan,
   Sai wata wace ke gefe tsaye tun shigowar shin kodai Mamuce,,
  Maryam tace maryam ce sai salati suka hau alokaci guda,
  Suna murna da farin cikin ganin ta, cikin sauri suka fara kwasan kayan ta zuwa ciki dashi,
   Maman ta tace a kai ta, dakin abokiyar zaman ta, wace suke cewa Ladi,
  Anan akai mata masauki ita, da kayanta, kafin wani lokaci har an kewaye ta da abinci kala kala,
  Da yake kauye ne duk sunyi abin sanar su tasayarwa,
  Kwarai mahaifiyar Maryam taji dadin ganin Maryam, da kuma wanan ziyarar da takawo masu,
   Bayan kowa ya watse akabar Maryam da mahaifiyar ta, a hankali maryam ta dago kan ta takalli mahaifiyar ta wace ke tsugunne a gefen dan gadon ta,,
  Tace mun samay ku lafiya mama, cikin kariyar murya take maganar kamar wacce zatai kuka alokacin,
   Mahaifiyar tace takauda kukan da cewa yasu wajen yayan naki ina fatan duk kuna lafiya ?
   Kikara rike yar uwar ki da amana kin daiga yadda itama tarike ki amana,
  Ba maicewa ga yadda kuke da ita ,don ko da nake nan ina jin irin zaman da kukeyi da ita
  Duk wani abinda ta hore ki dashi kiyi kokarin rike shi,
  Allah ne kawai zai iya saka mata da alherin sa,,
  Saidan hiran sauran jamar su da sukayi inda take tambayar ta ko kwana nawa zatai masu ta sheda mata sati guda zatayi ta koma,
  Daga karshe ta gabatar mata da tsaraban da tazo masu dashi
  Nan mama tai filla,filka da kayan saida ta,tabatar dakowa na gidan yasamu tsaraban,
   Maryam taji dadin zama tare da mahaifiyar ta duk da a kauye suke sam bata nuna masu kyama ko nuna wayewa,
  Dan zamanta har da karatun addini suka dan samu daga gareta,
  Duk safe za,a kawo mata abin kari daga ko wani shiya nagidan hakama da rana ko dare kowa da kwanon shi da zai aiko mata,
  Ana gobe zata koma har daga makwabta aka dinga kawo mata tsaraba irin na kauye,
   Badon sun so ba washegari tabar su takamo hanya dawowa ita kadai,
   Tunda motar ta tashi sai taji zuciyar ta duk ba dadi ya cushe mata guri guda ji take kamar kada su rabu da su,,
  Hannu tas tadan share hawayen ta da taji yadan gangaro mata,
   Sannu a hankali sai gasu Allah ya kawo su cikin gari lafiya,

   Zaune  yake a kofar gidan su Anty dije Assalam na rike a hannu shi yana yar wasan lilo da hannu Joseph din,
  Mai mashin din da ta hau ne yazo har kusa da inda suke zaune,
   Ido yabita dashi har lokacin da ta sauka ta mikawa mai mashin kudi,
   A,lokacin mai mashin din ya sauke mata wani buhu,da ke shake da kayan tsaraba da tazo dashi,,,
  Joseph ya sauke hannun Assalam a hankali shiko Assalam naganin ta yaje ya kankamay ta ya,na, ihun da murnan ganin ta,
  Suna can suna murna basu san lokacin da Joseph ya dauki buhun kayan da kuma yar trolley din ta zuwa cikin gida,
    Saida suka gama ihun su koda zasu diba basuga kayanta ba ,kuma basuga Joseph ba
  Sai ganin shi sukayi ya na fitowa da ga cikin gida, yana kakabe hannun shi, da handcarchef, din shi,,
   Da mamaki take kallon shi don sam,batai tsanmanin cewa zai iya daukar mata kaya dakamshi zuwa cikin gida
  Juyawa tayi daidai lokacin da ya iso inda suke tsaye, cikin yar karamar murya tace ta gode duk da tasan cewa bawai dole bane ya amsa masu,
    Tadawo da sati tafara shiga makaranta daukan lectures,
  Maryam yarinyace mai hazaka ga karatu dama duk kowani famni ba,abarta a baya ba, tana kokartawa,
   San,nu,a hankali kanta yafara wayewa kamar kowace budurwa da ke makarantar,
   Yau ma kamar kullun shiri takeyi don gudun makara,,saboda tasan cewa suna da lecture din wani bakon malami da zai dauke su,
  Gashi sun samu labarin cewa baida wasa ga aikin shi duk wanda yazo bayan shi bazai shiga ma aji ba alokacin kuma, dole kowa yasai handout din shi,
   Yau har da break fast anty tayi da ita ta tsaya tasha amma maryam sauri take yi tace idan taje can zata samu dan abinda taci,
    Ta dade a bakin titi kafin ta samu abin hawan da zai kaita amma sai suce bazasu je har can ba yanzu da safen nan, sai da kyat tasamu wani yace zai kaita a dari biyu tace ba komai,su tafi,,
   Hakan ya jawo mata makar har time din da za,a fara lecture din yadan gwauta da minti biyu kacal,
  Amma jin cewa da tayi ance baida sauki lecturer din wurin rashin nasiha,
   Yasa taja baya kawai tasamu wani mota ta dan kwanta saman motar, kadan
  Rayuwar ta yai matukar baci sosai da rashin samun wanan lecture din da batayi,
  Tana tir da halin rashin imani,ko, nasiha nawa su, mutane,
  Tsaye yake kanta yana magana amma Maryam batasan cewa, da mutum yana mata magana ba, alokacin,
   Motsin da taji ne kamar kusa da ita shi yasanya ta dago kai da sauri don gani kowaye gurin,
   Wani black, handsome guy ne tsaye agaban ta,sajen fuskan shi yah karawa fuskan shi wani daraje,da girmamawa,
    Cikin shigar dinkin shadda yake,dinkin wanda ya tsaya mai,daidai ciyar shi sai guntun hannu, da a,kaiwa dinkin,
   Yana saye da wani farin glass wanda bazata iya tamtace, ko na magani ne ko fashion ne kawai,
   Duk da indon shi nada glass bai hanata,gani kwayar idon shi ba da kuma kallon mamakin da yake mata,
  Batasan lokacin da taisauri ta mike ba daga kwanciyar da tai, a  saman motar mutane,
    Yana tsaye hannayen shi rungumay a kirjin  rungumay
  Ganin ta tashi yasa yai saurin kokarin wuce wa,
 Saida kuma yaji ta saki wani dogon tsaki, tare da yin kwafa,
  Dawowa yayi yana ce mata lafiya dai ko naganki a haka, ko kina son wani taimako ne,
  Dan tsaki taja tana kokari gyara jarkar dake rataye a kafadar ta,
  Wani mugun malami ne yabata min rai don yaga Allah yabashi baiwa ya,manta cewa wani dama ne ubangiji yabashi
  Saiga shi ,shi yana amfani da damar yana cutawa diyan mutane, da, damar ta shi
   Tadan daga kai a karo na faron tunda tafara mai magana cikin bacin rai, tace ,,
  Wai ace duk samakon danayi don kada in makara, shiga,lecture din shi, saboda ance shi mugune in,,, in an, makara bai bari mutun yashiga,
  Sai ga shi,,abin hawa yabani matsala wallahi,
  Amma abin haushi wai minti biyu kacal na dora a saman lokacin da ya,fara lecture,
  Sai,gashi wai ya rufe ba mai shiga kuma,,Abin haushi ance bai yiwa Allah don mugganci, shi,
  Tun da tafara fuskan shi  na a,kanta,
  Fuskanshi dauke da murmushi yace too bad,
  Is alright, may sunan guy din ne wai,,,
  Ido ta,dan zaro waje tace kai may ye, zakai mai wa yanda ma suka dade tare dashi sun yaba shi da mugun hali ,,,
      Fadamin sunan shi kawai ko zan iya taimaka maki akai,
  Taidan wani far da ido taba alamar tunane, can tace,
     Hmmm wai,ko A,A, MASUGA suke ce mashi ba, ko wa ma something like dat dai,
   Ya na kokarin bude motar shi, yakalle ta ido cikin ido, yace mata,,
  Ok ki,samay ni a block C idan kin,je office na uku daga daman ki, ,ki shi ga zaki samay ni, ciki,zan yi kokari in gani, may za,ayi akai,
  Bawani jin darrr ko kuma tunane, wani abu dakaje yadawo, gareta, sai cewa tayi, to kawai ta amsa mashi alokacin, har yashiga motarshi yana kokarin tayar wa,
   Sai bayan ya wuce ne tai dan ajiyan zuciya cikin bacin rai tace shikuma wanan din ma kowa ye a makarantar da zaice, zai tunkari, AA Masuga,
   Tunda duk sakkon datayi tun da farar safiya ya hana yashiga ciki,
   Next lecture tashige abinta batare da ta damu da zuwa gurin da ake jiranta ba,,,
  Don ita a ganin ta mugun malamin ya riga ya cuce ta ko,,
  Zaune yake yana aikin tura sako a cikin system din shi yanayi yana gyaran dan farin glass din da ke man,ne a fuskan shi,
  Saidai a cikin zuciyar shi maganganun yariyar dazu ke mai yawo a kwakwalwan shi, yana jin muryanta tana fadin ,,,,
  Allah yabashi dama saidai shi yana amfani da wanan baiwar yana cutar, da,diyan mutane dashi,
  Yau ko karyawa ban tsaya nayi ba saboda kawai in,samu shiga kafin time din shi yayi sai,dai abin hawa yaban matsala saboda, minti biyu, kawai kacal, na  kara
  Shine ka gan,ni ana ya hanani shiga, saboda daukar alhaki
  A cewar wanan yarinyar da ke ta fadamai magana tsakani da Allah
  Kai ya girgiza da yakai nan yana mai furzar da wani irin iska daga bakin shi,
    A gaskiya wanan maganan ta soki zuciyar shi don dan abu kadan kejawa mutun matsalal rayuwa,
  Shi baiyiwa mutane uzurin matsalal suba taya shi Allah zai sa wani yai mai nashi watarana,
  Idan ma har bai yi nasiha ba sai wani yazo yayi don komai dadewan ka a wuri dole watara bakai, bane a gurin,,,
   Ire,iren wanan tunanen yadinga yi a zuciyar shi yanayi yana kallon agogon dake daure a dogon hannun shi,
  Dan tsaki yaja don rashin ganin yarinyar batazo ba balle ya karasa jin korafin jama,a akan shi,,,
  Maryam ko wace sai kusan uku na rana tasamu kan ta sai a lokacin ta tuna cewa ,wani yabata appointment dazu da safe,
   Bashiri cikin sauri tajuya zuwa block din da aikai mata kwatance,
   A hankali ta kwankwasa kofar office din yana zaune hankalishi naga aikin da yake idon kafe da farin glass din dake idon shi,
    Batare da yadago kai ba yake cewa mai kwan kwasawar come, in, batare da yadaga kai ba still
  Da sallama abakinta ta shigo office din wani irin sanyi da kuma kamshi, turaren maza na Minkaeel, ne , ya,daki hancin 
   Sai da yaji muryan mace ce yadan dago kai yaga kowace,ce har zai maida kanshi ga abinda yakeyi
  Ido biyu sukayi da maryam wace ke cikin shigar doguwar jallabiya sai dankwalin da ta yane fuskanta da shi,
  Wanda iya round din fuskant脿 kawai zaka iya gani ,duk sauran jikin ta a rufe yake lif,
   A hankali cikin dishasshiyar murya take gaishe shi cikin ladabi,
  System din dake gaban shi yadan rufe kadan ya na mai fuskantar ta,
  Cikin kujeru biyu dake office din suna fuskantar wanda yake zaune ya nuna mata,
   Malam kayi hakkuri pls sai yanzu muka , fito, daga lectures,
   Cak taji numfashin ta ya tsaya daidai lokacin da tai tozali da wani dan prem dake kafe a gaban tebur din shi
  An rubuta da wani ruwan gold cikin wani sallo A,A MASUGA,,,,

ZEEE MAKAWA,,,,
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
    FUREN    JUJI
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
           1鈨�8鈨�

ZAINAB IDRIS MAKAWA,


  A,A masuga ido ya kura mata batare da ya dauke kan shi ba don ganin irin re,action din da tayi lokacin da idon ta yakai ga prem din,
  Murmushi yayi yadan gyara zaman glass din dake idon shi, dai dai lokacin yake ce mata,
  A nutse, ya,ce,ya, sunan ki malama,, cikin wata irin tsadadar murya yake magana kamar bai son yi,
   Kusan minti uku bata iya cewa komai ba har lokacin
  Murmushi yayi shi ya fargar da ita daga dogon tunanen da tafarayi naganin gata a gaban hukumar makarantar an gurfanar davita akan sai takawo shedan cewa A,A masuga mugune,
     Kara tambayar ta yqi yana mai cewa ,cewa nayi ya sunan ki ne, ?
   Murya kasa,kasa ta furta cewa Maryam Abdullahi, Bobbi,
   Jin yayi shiru tadan dago kai ta kalli inda yake cikin sauri ta dukar da kanta,
  Don shima din ita yake kallo a lokacin,
  A,dan kunyace ta furta don Allah kayi hakkuri ban san,,,,,
   Hanni yadaga mata yana mai gyaran murya yace
  Naji duk bayanin da kikai min dazu akan AA masuga
  Maryam wace kan ta ke duke sai a lokacin tadan dago kai takara kallon shi a karo na biyu don jin da tayi tace A,A masuga,
   Azuci kuma cewa tayi jidan rainin wayo ko har yanzu yadauka ban gane shine ba yaci gaba da shanmata na ,,
   Kamar daga sama taji ya kira sunan ta in full,
  Adan tsorace, ta dago kanta, saidai wanan karon fuskan shi a daure take tamau, bakamar dazun ba, daya dan sake ta,
   Kai ta mayar kasa don ji takeyi gaban ta yana ba da dammmm,
   Yace, naji dadin wanan maganar da kika fada min da don tun da nake ba wanda ya taba fada min cewa abin baidace,ba,
  Nikuma azato na hakan taimaka wane ga dalibai, ban yi la,akarin cewa zai iya illikanta rayuwan wasu ba,
  Kokuma in ci hakkin wani ta irin hakan da nakeyi ,
   Yace kin san may ?
 Kai ta dake kasa, ta girgiza mai,,
   A hankali yaci gaba da mata yan tambayoyi , saidai wanan karon a kunyace take bashi ansa,
   Sallama tai mai gami  da bashi hakuri,
   Yace haba dai ita taimakon shi, ta tayi  tunda har ta iya fada mai gaskiya,,,,
   Shiru yadan biyo baya sai shi A,A din ne ya ita cewa muje in kaiki gida don time yayi ko ,
   Don kada ki rasa abin hawa,
  A ranta tace wake kai ta gida da, da bata dare,
   Amma a fili dan murmushi tayi, tana mai cewa da kabar shi ai zan samu bus,
   Batare da yai magana ba ya mike tsaye, yana mai hada yan tarkacen shi a cikin yar briefcase din shi,
   Maryam tarigashi fitowa yana biye da ita a baya don sai da ya tsaya yadan rufe office din shi,
   Amma may suna fita fafir Maryam tace yabar shi kawai bazata shiga ba,
  Saida ya nuna mata cewa bai son jayayya, sanan ta daure suka tafi, a cikin motar shi, kirar  Peugeot  NEW MODEL,,,
   Tafe suke ba mai magana acikin su sai dai kidar da ke tashi a motar na siliado,
   Sun kusa shiga gari ne yadan joyo inda take yana cewa,
   Wani unguwa zamu tafi ne, ?
   A hankali Maryam tace furta da ka sauke ni a round about kawai sai in karasa,
   Batare da bata amsa ba ko tsaya yace wani unguwa pls, ?
   Cikin ,ciki ta furta kwanar kuka,
   Kwanar da zai sada shi da unguwar ya karya, daidai kusan uguwar ya ce gidan wa,
  Illiyasu costume, kallon ta yakarayi da kyau don jin gidan da take,
  Yace ke kaunar matar shine ko, kai ta gyada mai a hankali,
   Daidai kofar gidan ya aje ta, 
  Ya ce toh nagode, maryam da taimakon da kikai min,yau,
    In sha Allah zan gyara ga dalibai   zaku samay ni masauki da rangwamay,
    Kan ta na kasa cike da jin nauyi,
   A hankali tace nima nagode malam da fahintar gaskiya da kayi,
   Murya cike sa cike da amon murna yace ai ni ban san may zan kara fada kuma,
  Ta bude gambun motae a hankali tafita shi kuma a hankali ya fara ribas da motar shi,
   A nutse ta rika takawa har zuwa kofar gidan su, inda taga wasu a zaune, saida sun bada baya,
  Kallonta yayi a glass din motar har tashige shi kuma ya harba yabar shi yan,
  Zuciyar shi fam da tunanen kalaman yarinyar,
 Har ta shige gida batare da ta lura da wanda ke wajen gidan nasu ba alokacin,
   Shigewar ta yabi bayanta da kallon mamaki a ran shi yana mamakin yau she tagirma haka,
   Maryam na shiga gida tasamu Anty Dije, tana aiki, taimata sannu da gida tafada Wanka don ta dan ji dadin jikin ta,
    A marairaice maryam ta ke cewa Anty Dije, kamar mai shirin yin kuka
  Anty tunda safe banci komai ba tun da na fita gida,
   Yar karamar harara Anty ta sakar mata tana cewa, ,oho maki, danace ki tsaya ki karya ba ki ,kikayi ba waike kina dokin zuwa makaranta,
   Yar guntuwa tsuki tayi tace kuma wallahi duk sakkon danayi ban samu lecture din ba anty,
   Baki Anty ta tabe mata tace anfada maki ana samu cikin zafi ne,
  Aikomay zakayi kayishi a cikin hankali, don rashin cin abinci na iya jawo maki ciwon ulcer,
  Falo tadosa don ta zauna ciki ta ci abincin ta tana kallo,
  Ganin mutum tayi a zaune yana cin abinci shi a hankali,
    Juyawa tayi da sauri da niyar barin falon a lokacin, sai kuma tatuna cewa ba su gaisa ba don haka ta tsaya cikin ladabi tace mai  ina wuni,
   Da wata irin dasashiyar murya ya amsa mata, a hankali,
  Sai ta juya kawai tabar falon ,shiko mamaki yaji kwarai da gaisuwar da yasamu cikin mutunci gare ta yau,,,

    Wanan shigowan da su Joseph sukayi tare da abokan ahi shigowa ce ta musam man sukayi
   Don bukin sallah da za,ayi inda matasa ke bukatar a bukin hawan dawakai wato Dubba,
   Don haka basu samu wani zama ba sosai kamar yadda suka saba,
  Don yawan zirga,zirgan da suke yi tsakanin birni da kauye gurin ganin cewa komai ya kammala,
   Yau ma kamar kullun sun dauke shi zuwa wani kauye duk da shi kauwaici yake masu don ganin cewa suna kokarin sashi cikin al,umurorin su,
  Amma shi gaskiya duk irin wanan abin bawai yadamay shi bane shi harkokin business din shi kawai ke gaban shi,
   Amma a zuwa yanzu abin da yake gani gurin su jibrin da KB dama sauran abokan su yana bashi sha,awa sosai ,
  Duk masifan da mahaifin shi zaiyi  yayi mai sunyi mai preaching kala kala akan ya daina bin diyan musulumai,
 Kawo yanzu,   Yasa an gyara mai gidan mahaifin shi amayar mai dashi hawa biyu sai kuma katon parking space mai girma da saura guraren da ake samu masu kawata gida,
  Amma duk wanan baisa Mr Ema kyale dan nashi ba, da fitinar ya daina tallafawa mutane musanman musullumai,
   Yasa ma Joseph din ido ne kawai don yasan cewa Joseph din yanzu ya wuce sanin shi,
  Wanan hurda da kuma al,adun da Joseph keyi na hausa baima ma Mr Ema dadi sam,
  Yau ma kamar kullun cikin fushi yake wa dan nashi fadan cewa yaran hausawa sun asirce shi ne,
  Saboda labarin dayazo mai cewa da gudun mawan Joseph acikin wanan gagarumin bukin da matasa ke ta kokarin hadawa don cigaban masarautar su,,
   A fuce yace baya son Joseph ya kara zuwa garin yafi bukatar ya daina zuwa da ace yazo yana hurda dasu haka,
  Wanan maganar harta kai Joseph yai yun kurin gina gidan shi inda zai dinga sauka inda yazo,
  Sai da baban yaga cewa zaiyi hara sosai ya kuma kara bidan dan nashi sulhu,
  Inda ya ke sheda mai cewa hausawa shu,uman mutane ne yana gudun nan gaba ne kada su ja,ra,ayin shi akan wani abu can,
    Maryam wace yanzu, haduwar ta, da A,A MASUGA, yazama mata, wani sanadin alheri,
   Don kwana biyun nan shi ke, zuwa da kanshi ya diba yagani ko ya karatun ta ke tafiya,
   Tun maryam na dari,dari har ta fara dan sake jikin ta dashi suka dan fara sabawa,
    Duk wanda yasan Maryam ada yanzu in ya ganta bazai sheda cewa ita bace saboda,
  Tazama cikakiyar yar jami,a saidai har yanzu wanan hali nata yana, nan kamar da ba ta yawan kula samari kamar sauran yan mata,
  Mutana suna zaton cewa ita, sister din A,A masuga ne,
   Saboda yawan ganin da ake masu tare ko kuma yawan kulata da yake yi,,
  Kwanan nan gidan Anty Dije cika yake yi sosai sasboda gab suke da fara program din su
  Duk may neman Joseph indai yana cikin garin kwantagora a gidan anty dije zai samay shi saboda bai son su samay shi a gidan baban shi don gudun fitina,
 
   Tafe suke tare da A,A masuga,,,,da wani abokin shi,, acikin motar shi sai faman waya yake, yi da alamar da mutanen gidan su yake waya don yadda taji yana bada ansa yasa tagane hakan
   Yana gama wayan yai yar ajiyar zuciya tare da shafo sumar kan shi tundaga, fuska, zuwa baya,har kusan wuyan shi,,
     Sai a lokacin yadan waiga inda maryam ke zaune hankalinta a titi, tana kallon yadda abin hawa suke ta zirga zirga kasan cewar yamma tayi a lokacin,
    Maryam ya furta a kasalance kamar yadda yake kiranta kullun,,
  Wanan, kiran shi ya,katse mata kallon titin da take yi tun dazu,
   May yafaru naji kin yi shiru, ko , yadan kalle ta na minti guda,
   Cikin nuna kulawar sa yace kan ki na ciwo ne, naga kin yi shiru,
   Kanta ta girgiza tace a,a babu wani ciwon kai ,
   Illa masu son yin bukin nan dake son takurawa rayuwan mu,
   Ace bamu da hutu sam a gidan mu in har wanan dan Christian din yana gari,
   Baki makam A,A masuga ya tabe yace lalai kam ku samu aiki,
   Yace wai may ye alakar shi da ku ne, ma wai da naga ya na zuwa gidan ku duk lokacin da yake gari, gashi shiba musulmi ba ba bahaushe ba,
   Batare da tai magana ba tai dan guntun murmushi irin na iya fuska, kawai,
   Aiko kamar kar su karasa kofan sai ganin jama,a fam sukayi ana t hayaniya kamar ana wani buki,
  Da kyat malam masuga yadan samu ind ya Parker motar shi a gefe don tafita,
  Aiko idon jama,an dake gurin ca,aaa akan motar don suga ko waye zai fito cikin motae,
  A hankali ta bude marfin motar tare da yin yar guntuwar tsuki wanda duk inda kake zaka ji,ta,,,,
   Dan harara malam ya watso mata daga inda yake yana cewa
  In bake ba wake gudun taron mutane ?
   Batare da tace mai komai ba ta,kauda kai zuwa inda taga su Joseph zaune suna diban wasu takardu a hannayen su,
  Diba guda tai masu takauda kai gefe guda cike da jin haushi, don wani iri taji a ranta,ganin yadda yake kokarin shige masu,
   Koda A,A masuga ya tsaida mota tafita , ko kallon inda suke bayi ba nan tabi ta gaban su ta wuce kawai abinta batare da ta tsaya gaidasu ba,
   Kamar may rada taji ya furta sunan ta a karo na farko ke nan tun sanin tada shi,
   Wasu takardu yamika mata na cewa don Allah taba Anty Dije ta aje mai akwai wanda zaizo ya karba a gurin ta,
   Kamar ta wuce don ita aganin ta yama raina mata wayo ,
  A matsayin shi na kafiri, Arne, zaice zai ai,keta sai kuma fadan Anty ya fado mata a rai
  Dole ta tsaya ta mika hannu ya miko mata, cikin rashin ko inkula,
   Tana shiga rai a bace ta yi kokarin mikawa anty takardan tai shigewar ciki,
 
   Ana cikin wanan hada,hadar shirin hawan dabar da suke yi wanda mutane sun hana Joseph din tare da mabiyan shi shakat,
   Har su maryam dake tare dashi a gida koyau she zakaji ance ana wai sallama da Joseph din,
  Ita dai maryam mamaki taje ji na wanan halin da ga mutane na kokari zubar da mutuncin su da Allah yai masu akan kwadai,
   Don haka ko tana gida bata yawan zama a waje don gudun damuwar jama,,a
   Yau malam A,A bai zo school ba yai tafiya zuwa wurin wani seminar da zasu a kwara state,
   Mashi ta tare don komawa gida duk A,A din yace ya hada ta da wani friend nashi ya dinga taimaka mata, zuwa gida,
   Amma ita maryam din sai taga cewa bazata iya bin wanan mutumin ba don kawai kariyar mutuncin ta,
   Mai,mashin tatara ta hau, duk da tace mai kada,yai gudu da ita, amma kamar zuga shi tayi a lokacin
  Haka yakw kokarin wuce motoci da ita a baya makale,
  Daidai kwanar sabuwar junction suka hadu da motar yan matasan masu tashe agari,
   Cikin wata jar mota haka kallo guda mai jan motar yai mata,ta kauda kai duk ita ma dai taji kunyar yadda take dane bayan mashi, mai mashi nata,gudu da ita,
   Kallo mai kamar harara ya watso mata, wanda ita ma din kusan irin kallon ta watsa mai a lokacin, ta mayar mai da martani,
   Kai Joseph ta girgiza don in a kwai abin da yai hating she yaga mace a saman mashin ana gudu da ita kamar bata san zafin ta ba,
   Bai san har lokacin da yafurta a fili ba yace nonsense,kawai,
   A rashi yake tunanen ya furta sai gashi ashe afili ya fadi hakan,
   Jibrin dake gefen shi ya kyalkyale da dariya yace kaganeta ashe,
  Kai kawai ya gyada mai alamar eh, a hankali ya furta may ye amfanin hawar mashi a diya mace pls,
   Maryam ko rana isa gida ta samu anty tasayo zogala, ai cikin murna ta shiga sallah kawai ta idar tafito waje don ta gyara masu zogalar,
   Bayan ta yanka su albasa, da attarudu da tatasai sai man kulikuli da ta lema masu asaman takawo garin kulikulin ta cakude wuri guda sai ruwa mai sanyi da ta dauko,
  Da shikafa tai niyar zubawa taci bayan ta debi daidai zamar ta asaman wani tabarma da ta shimfida don ta ci gwaben ganyen, da tayi,
  Shigowar su ,suma ke nan a gidan, inda, jibrin ke gaba, wani lawal na binsa, sai Joseph tare da wani tajudeen a baya,
   Shigowar ya fara rage mata dokin da takeyi nashirin cin ganyen da tayi,
   Jibrin ne da shigowar su , yadan kalli inda maryam take zaune yace mata,
  Ke ashe har dadi kuke ji indan kun hau irin wanan mashin din dake kusan tashi sama da ku,,,
   Baki kawai maryam ta hangame cikin mamaki da maganar jibrin,
   Saidai taso ta furta cewa wani abu amma sai ta kasa, cewa komai don wani irin al,ajibi jin maganar da tayi,
  Don dai ita tasan cewa ba gwanar hawa mashin bace ko banza
   Yau ne kawai da take kokarin ganin cewa ta iso gida da,wuri don ranan da yai yawa a garin,
   Ji tayi wasu hawaye masu dumi sun gangaro mata a fuskan ta, ga wani malolon bakin ciki da ya tokare mata makogoronta,
   Takai wani dan lokaci a gurin zaune takasa tashi,
  Saidai tana kiyasta irin daukar da sukai mata a matsayin yar iska kenan ko,
   Bataji zuwan Joseph da Assalam inda take zaune  tana hawaye ba,, sai ganin shi tayi gaban ta,
  A hankali ya sauka bisa gwiwowinsa, yace little mummy kiyi hakuri amma gaskiya jibrin ya fada maki,
  Banza tayi da shi sai kuma wani wawan harara da ta sakar mai, har Assalam saida ya dan ji tsoro ya dan shige jikin Joseph,,
  A raunane ya kara cewa kiyi hakkuri wanan ba abin bata rai bane,
   Kala batace mai ba sai mikewa da tayi tsam ta nufi kofar da sauri,,,,
    Ido yabita, da shi don dai shi baiga abin bata rai aciki ba,,,,,,,,,


  ZEEEE   MAKAWA,
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
    FUREN     JUJI
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
           1鈨�9鈨�

ZAINAB IDRIS MAKAWA,,,


Buki sosai akayi a wanan bukin hawan Dabar da akayi don matasa masu ji da lokacin su sun halarci wanan bukin nadaukaka masarautar kasa kwantagora
  Wanda ke tatare,da tsohon tarihi acikin ta kamar sauran manyar masauratar da ke a kasa shen hausa,
   Anbuga a jaridu da kuma sauran kafafen yada labarai, na kasa,,
   Inda bukin yasamu karbuwa fiye da zaton may karatu,
   Ana gama wanan bukin da kwana biyu Joseph yabar garin kwantagora , saboda gudun fushin mahaifin shi da yasan cewa yana hake dashi,
  Duk irin abubuwan da ya wakana agurin duk Mr Emanuel nada labarin komai tankar a gaban shi akayi, duk shagallalikukan
   Don haka joseph ko kasan bai tsaya ba ketarawa yayi zuwa kasashen waje da niyar yatafi, yadan huta a can,
 
    Tun bayan wanan  abubuwar, maryam babu ruwanta da zancen, wani wasan da akayi
  Wanda ita take gani kamar duk wanan abin bai cikin irin tsarin rayuwar ta,,
   Ita bata masan cewa masu takura masu a gida, basu garin ba tun bayan bukin da gari yayi kamar zai tsage, don cinkoson jama,a
   Don ganin da su tun zancen da suka ce ta hau mashi a na gudu da ita kamar wace bata san zafin kanta ,
  Ita ko a nata zaton gani takeyi kamar suna ganin cewa bata san darajan kanta ba ne tunda har take hawan mashin da na miji,
  Idan har ta tuna da wanan kalamin sai taji duk yanayin ta ya sauya,,
   Saboda ba karamin ci mata fuska take ganun sun yi ba,
  Takan yi tsuki tace wai gwano baya jin warin sa, su da suke hurda da yan iskan yan mata
  Shine har zasu samata kazafi akan hawa mashi, idan bata hau mashin ba da may zatai tafiya to,,,
 
    Wata rana da la,asar bayan Maryam ta dawo daga wani gida da anty ta aiketa karbo, mata sakon wasu kaya da aka turo mata ta daga kano,gurin wata mata,,
  Don yanzu Anty tana dan taba business irin da matan gida ke dan yi,
  Domin kariyar mutuncin su saboda hana, bani bani gurin maigida,
   Wani mutum tagani dattijo zaune a kofar gidan su, tun daga nesa take kallon mutumin a cikin mamaki, saboda ganin shi da tayi gab da kofar gidan su,,
   Saboda a gaskiya bata taba sanin shi acikin masu zuwa gidan su ba,
  Koda kuwa gurin mijin yar ta ne, bai daga cikin masu zuwa gidan,,, sam,
  Gashi kuma kaman nin sa sun nuna cewa kamar yana tare da lalura,,,
  Tafiya take yi a hankali, cikin dan shakku,kamar za,a kamata,
  Tana karasowa gab inda mutumin ke zaune sai mutumin ya mike tsaye da sauri ganin cewa gidan maryam ta dosa a lokacin,
  Cikin dan tsoro da kuma ladabi maryam ta dan duka kadan tace Baba ina wuni, ?
  Yace yauwa "ya ta lafiya kalau,
  Dan Allah ko gidan nan kike yan mata, ?
  Maryam dake dan ja baya baya kadan da kamar tace mai a,a sai dai ta daure tace mai eh a nan take,
  Hausar shi na nuna mata cewa mutumin ba pure hausa ba ne,
  Ya ce dan Allah yan mata ina son ki min iso a gurin mai gidan nan,
  Cikin mamaki Maryam ke kallon shi tace mai baya gari,
  Shiru taga mutumin yayi cikin damuwa yana mai dan ya mutse fuskan shi,,sai kuma taji duk yaba ta tausayi,
  Ita a zaton ta ko yazo maula ne irin yadda wasu masu kararen zuciya ke yi a wanan zamanin,
  Kaga mutum majiyi karfi amma sai ya kare bi  gida jen masu hannu da shuni yana maula,.
   Mutumin ya katse maryam da cewa ko zan samu ganin hajiyar gidan don magana ce tazo dani mai muhin manci sosai
    Shiru Maryam tayi saidai gaskiya mutumi yabata tausayi sosai don ganin yanayin shi,
   Marayam ta fadi cikin ladabi barin shiga in fada mata,
  Bayan shigar ta da kaman yan mintina saiga Anty Dije ta leko sanye da hijabin ta,,
  Daga nisa kadan suka dan gaisa da mutumin sai kuma yar shiru tabiyo baya,
  Don Allah hajiya kiyi hakkuri pa don nasan cewa ba wai kin san,ni bane,,,
   Sunana Abdullsamad anan gari nake, ni dan uwan yaron dake yawan zuwa gidan nan ne,
  Watau Joseph,,,,,
Daga Anty Dije har maryam dake ta kofa tsaye wace ta takawa yar uwar ta baya don gudun wani abu ya samay ta,
  Sai da suka dan kadu jin mutumin ya ambaci sunan Joseph,
   Jin haka yasa anty ta dan kara gyara tsayuwar ta tana mai cewa lafiya dai ko malam,
  Don a zaton su yazo masu da wani tashin hankali ne, a yadda suka gan shi,,,
  Yadan hada hannun shi guri daya ya nuna alamar cewa a,a babu komai gaskiya sai Alheri,
  Sai a lokacin anty dije tadan rage jin abinda take ji
  Sai yadan waiga kamar may son yin wani maganar ta,siri ko kuma mai muhin manci sosai,
   Hakan yaba anty damar gane cewa maganar da yake da ita kamar ta siri ce,
 Don haka ba bata lokaci ta dibi inda Maryam take tsaye tun farkon fitowar su tace maryam bude mai kofar falo tukun,,,
   Bayan an bude mai yadan shigo daga cikin ya zauna maryam takawo mai ruwa sanyi tare da dan abin tabawa,
  Ya dauki yar ledar ruwan goje water da ta aje mai ga plate ya dan tsosa kadan yace Alhamdullah,
   Nagode da wanan ruwan da kuka shayar dani Alkah yakara budi da daukaka,
  Daga Maryam har Anty sunji dadi sosai da wanan kalamin tashi,
  Hakan yakara basu damar sake jiki dashi don dama darrrr suke dashi saboda rashin sani ko da may yazo,
   Sai maryam taji kawai mutumin ya kwanta mata arai,, saboda kalaman bakin shi na alheri ne,
   Saboda ta lura cewa yana da addini atare da shi ,
  Tsabar talauci ne kawai ke damun shi ya koma haka
  Wani irin mugun tausayin bawan Allah sukaji cikin lokaci guda,
Maryam sai tunane take yi a ranta cewa,ashe daman wanan mutumin yana da yan uwa musulumai,,,
   Maganar bakon ne ya katse ta, da cewa, dan Allah kuyi hakuri nazo maku a bazata, tare da kuma bakon al,amari,
  Dama taimako da kuma shawara ne nakawo maku, akan cewa,
  Wanan yaron da ke zuwa gidan ku Joseph don Allah tunda har naku yazo daya dashi ina son ku dan tallafa mai ,
  Nan da nan daga Anty har maryam suka dan kali junar su,
  Suna mamaki har may zasu iya tallafawa Joseph dashi su,,,
  Ai kuma sai mutumin yai shiru ,alamar maganar da zai furta tana da nauyi,
  Zuwa wani dan lokaci kamar mai tuna ne,,,,,,
  Can kuma sai yace, ku yi mai tayin musulunci a hankali pls,
  Yafadi cikin taushin murya,
  Duk da dai nasan cewa abune mawuyaci , amma nasan cewa zaku iya insha Allah,,,,
  Yakara fadi a raunane, cikin nuna damuwa sosai a fuskan shi,
   Shiru wurin yayi daga anty har Maryam dake tsaye kamar mai wancin gadin, yar uwar nata, Saida maryam takai zaune a gefen hannun kujera, dake kusa da ita,
  Saida Anty tadan nisa sai tadan daga kai zuwa kallon malam,Abdull samad tace
  A gaskiya malam kazo muna da mawuya cin abu amma da ace mai gida na yana gari ne kaga sai kuyi magana dashi ta yadda za,a fahinta,
  Katseta yayi dace wa ai koku da yake, zama daku a hankali zaku iya dan jan ra,ayin sa don dai yana da bukatar haka din
  Idan har kunyi la,akari da yadda rayuwan shi take,,
 Yakare zance shi da cewa ina fatan Allah ya baku sa,a
  Gaba dayan su alokaci guda suka ansa da Ameen ya Allah,,,
  Basu tashiba saida malam Abdullsamad ya basu labarin dalilin musuluntar shi, da kuma irin kalubalin da har gobe yake samu, daga mutanen shi nada,,,watau Christian,
   Yace musam man mahaifin Joseph da yafi kowa son kuntata mai,
  Saida duk kan su,  suka tausaya ma halin da rayuwar ya shiga sukai mai fatan gamawa da duniya lafiya,,
   Anan yai masu sallama ,akan cewa idan maigidan yadawo zai zo sukara,tataunawa da shi akan zancen Joseph din In sha Allah,,,,
   Da zai tafi Anty Dije ta kawo dubu daya tabashi tace ya hau mashi zuwa gida
  Yai ta sa mata albarka yana ta godiya kamar wanda,taba wani abu mai yawa,
   Tun fitar wanan bawan Allah, duk sai jikin su,yai sanyi lokaci guda tankar, an aiko masu da wani labari, mai kashe jiki, duk su kai shiru zuwa wani dan lokaci,,,
  Kowa da abinda yake sakawa acikin zuciyar shi akan zancen,,,,,,,,

   Barci takeyi amma sai juyi takeyi kamar wace aka danne ta daga saman ta,
  Sai shure shure take yi da kafarta kamar mai bidan ceto,
  Zubur ta samu ta mike tana mai kumar ihu cikin wani irin karaji tace, JUSES crisis,,,,
  JOSEPH,,,,, tafadi da karfi tana mai dafe, kirjin ta,
  Guda guda take mai da numfashin ta sai wani irin zufa da takeyi kamar wace ke cikin ovon
 Wanan mafarki yana damun ta sosai yanzu,
   Har takai yanzu sam bata son tai barci asuba saboda , da wuya tai barci a wanan lokacin batai mafarkin nan ba,
   Still masu farin kayan da take gani suna kokari jan Joseph din cikin  korarayen haki,, ko yaushe yau,ma su din ne dai tagani, suna ta kokarin jan shi,,,,
  Sai,dai ta yau mafarkin nata yadan bam,bamta dana kullun,
  Don dai yau,taga Joseph sosai a cikin mutanen,,,,
   Tana bin shi ta kamo shi amma sai ya kubce daga rikon da tai mai,     shine mafarin wanan shure shuren da take ta yi, a lokacin da take mafarkin,
   Bible din ta dake gefe tadauko ta gyara daura dankwalin ta da kyau, nan ta fara jefo addu,oi da tasaba yi kamar kullun, har zuwa wani lokaci,,,,
   Koda gari ya waye ranan sai ya kasance mama choima ta kasa sake jikin ta sam bata walwala, yau,
  Duk abin duniya yadamay ta akan dan jikan na,ta
  Tsoro take ji don tasan cewa akwai abin da zai sami Joseph din,
   Saidai ta rasa ko may wanan mafarkin ke nufi, haka nan,
  Ejoma ta lura da cewa yau mama tana cikin wani yanayi don ko yaron Ejoma da take kokarin rike mata yau sam bata ko kalle shi ba,
  Inda take zaune tayi tagumi, Ejoma tazo tazauna gefen ta,
  A hankali Ejoma ke kallon mama, sai can tace,
  Mama yau may ke damun ki ne, wai ? da naga baki walwala, sam,
   Kamar kada ta fadawa Ejoma wanan maganar,
  Sai,dai kuma ta fara ba Ejoma labarin tun fara mafalkin nata akan Joseph din,,,
  Da irin yanayi da take ganin ahi a ciki yanzu,,
 Ejoma,tadan kwan,tar wa mama da hankali ta dan dafa kafadar mama kadan  tace
  Kinsan cewa shi mutum ne mai harka da mutane kala,kala, mama,
  Don haka dole,
 yasa ko da yaushe kike ganin shi tare da irin wa yan nan mutane,,
   Har wani lokaci Ejoma da mama Choima suna zaune suna zancen duk akan Joseph din,
  Joseph din ne ya bugo masu waya yana tambayar lafiyar su,
   Anan mama tashiga tambayar shi labarin yaya yake can ya kuma aiyukan shi,,
  Inda yake kara mata karfin gwiwar da cewa yana tafe kwanan nan,
  Amma ita sam bata,yarda da zancen shi ba, don har yanzu idon ta na hasko mata masu fararen kayan da suka rike mai hannu suka wuce da shi tana ta kurma ihu,a daji,,,,

   Shiko Joseph yanzu yakai kusan wata, hudu a can
  Har kasar chaina, yake tare da wani abokin karatun shi,
   Cikin dan kankanin lokaci mr Sonny, da suke tare ya dan kara gwada mai wasu yan dabarun kasuwan ci,
  Allah da ikon shi  ya kara daukaka shi sosai, ga harkan business,
   Ga harkokin shi na Nigeria su ma suna ci gaba,
  A, sannu yasamu ya kulla, a,laka  da wayan nan mutanen suka yarda zasu zo Nigeria su kafa irin wanan masana,antar,
  Wanan harkan duk ya,samay shi da ga taimakon da  hamshakin maikudi a kasar IBO yai mai hanya, abokin karatun shi
  Wanda tun kare karatun su shi yana can zaune yana harkokin shi, da turawa da chainawa,
   Mr Sonny shine ya basu sunar Joseph saboda yabawa da hankalin shi da yayi,
 Don tun a can da yasan halin Joseph sosai da rikon amana,
   Abin mamaki,Joseph nadawowa,da wanan harkan,
   Saiga shi ya dauki yaran hausawa cikin ma, aikatar company da aka bude Bunue,watau makurdi, wanda su yan kabilar su sam basu so hakan ba,

A, bangaren su maryam da Anty dije kuwa,
   Tun bayan tafiyar wanan tsohon sai maganar tazauna ma maryam a zuciyar ta
  Tunane takeyi ta yadda zata fara aiwatar da wanan shirin kamar yadda aka basu shawara, su tallafa mai,
  Don haka tasawa zuciyar ta cewa zata bada nata gudun mawar amma ba tare da sanin kowa ba,,
   Don haka shiri na farko da tafara yi shi sayen sabon sim card na layin,MTN,
  Sabanin wanda kowa yasan ta dashi a da tana amfani dashi,
   A cikin wayar anty Dije ta samu nobar wayan shi tai serving a sim din ta,,,
   A wani dare bayan ta gama komai tana shirin kwanciya ne
  Sai zance malam Abdulsamad yafado mata arai,
Tashi tayi tsam daga inda take kwance,ta dauko wayanta,
  Ta rasa may zata rubuta da farko,sai can wanan
   Sakon farko da tafara tuwa shine,
  Come to the light of life, islam,,,,,
  Joseph dake  zaune yana searching din wasu kaya a cikin laptop din shi yaji sako ya shigo mai a wayar shi,,
  Kamar ya share kada ya karanta saidai ya mika hannun shi yadauko wayar, a hankali,
  Da niyar,yadan diba sakon yaci gaba da aikin shi,
   Sosai yai mamakin ganin wanan sakon awayar shi  batare kuma da da sanin mai nobar ba,, Nan da nan duk wani abin da ke gaban shi ya dushe mai,
   Kafin wani lokaci idon shi ya kada yai jajir kamar yaci gauta ja,
   A hankali ya runtse idon shi, yana sauke numfashi a hankali, ya fida wani huci ta bakin shi,
   Tsayin lokaci babu abin da ya iya yi ko tunawa, wayar ya kara dauka ya diba sakon,
    Ahankali, maganar mahaifinshi ya fado mai a rai,
  Inda yake yawan ce mai hausawa basu da kyau, don wata rana zasu iya canza ka Joseph,,
   Sai kuma inda Mr Ema ke cewa kadaina yawo da yaran hausaw don basu da tabbas,
   Cikin wani irin yanayi ya aje wayan kamar mai tsoron wayar, na shi alokacin,,,
 Da kyat ya iya mikewa zuwa cikin bedroom din shi jikin shi,duk ba kwari,
   Duk da ya kwanta da ya runtse idon shi ba abinda yake gani sai wanan sakon na wayar shi,
  Come to the light of life, islam,,,
Rintse idon shi ya karayi kamar wanda bai son tunawa da sakon,
,,,,,,
  Maryam wace ke zaune bakin dan matsakaicin gadon su ita da Issalam,
   Takai wani lokaci tana jiran replay din shi saidai taji shiru ba wani alamar da wani sako tafe,
  Haka ta hakkure ta kwanta tare da tunane kasadar da tayi na tura mai wanan irin sakon duk da tasan cewa ba wai zai gane cewa ita bace,
  Amma dai tasan cewa kasada ne haka din, don ina ruwan ta da addinin shi,
  Tsuki tayi gami da juyawa tana may ganin laifin kanta, dayin katsalandar da shiga harkan da ba nataba,
  Sim din tacire a hankali ta samu wani guri inda tasan cewa, ba mai taba ganin shi  gurin, taboye
   A hankali taja bargon ta  dake gefe aje, tai rufe jikinta da shi ta,na mai lumshe idon ta,
 Sai dai sam barci yaki daukar ta don tana tunane akan sakon da ta tura,
  May ye,wai, amfani abokan shi su jibrin da KB da bazasu iya fadakar da shi gaskiya ba,
  Tsuki tayi gami da kara juyawa ta wani gefe tanamai cewa
  Ina zasu iya fada mai gaskiya tunda suna samu kudin agurin shi a kai a kai,
     Wai may yasa mutane kudi ya rufe masu ido ne haka da yawa,
  Kudiba fa, ba kunya yadda suke rawan kafa akan ARNE, wanda suke darajawa da kiman,tawa saboda kudi,,,
  Shin wai basu san cewa shi kanshi yasan cewa sun fi shi daraja ba da kima mutunci, saboda hasken addinin su, yafi na shi,,,,
  Amma saboda kwadayi duk sun zubar da damar tasu,
 Kara jan bargon ta tayi ta lullube lif daga haka barci mai nauyi ya dauke ta, zuwa wata, nahiyar,,,,,

  A,A masuga ne zaune a office din shi yai tagumi da hannun shi, guda ,
  Ba komai yake tunane ba sai wanan yariyar da yafara ji a, cikin zuciyar shi,
   Watau Maryam wace duk wani tsari da kuma diri da yake bukata ga mace tana dasu,,
   Kafin ya kai karshen tunanen shi yaji an turo kofan office din nashi,
   A hankali yadago kai da idon shi da suka dan sauya yanayi yana mai kallon kofar ,
   Da sallamar ta ta,shigo office din cikin shigar atamfa, da dan hijabin ta mai kara mata kyau ko yaushe,
   A nutse take kamar kullun yau madai kamar ba sabo a tsakanin su har yanzu,
   A mutunce ta dan durkusa ta gaishe shi, sannan ta dan samu kujera guda ta zauna,
   Sai a lokacin A,A yadago ido ya zuba mata su kamar na yan mintina,
   A kunyace maryam ta kauda kanta daga kallon shi, saboda bazata iya jure kallon namiji ido da ido ba,
   Yar murmushi yayi har fararen hakoran shi suka dan baiyana fili,
   Magana yake yi mai kama da rada,maryam kina kokarin ki min illa a wani part na jikina,
  Cikin dan razana da dago idon ta,akaro nabiyu suka kara yin arba da juna,
  A,A yace yes, ba wai, ba gaskiya ce nafada, saboda duk second ina ganin ki a zuciya ta Maryam
  Cikin mamaki maryam tace mai malam ni kuma  ? ta fadi cikin sanyin murya,,
  Kai yakada mata a hankali, yace akwai wata maryam ne nan a tare da ni,
   Ido ta dan kura mai sai kuma tai saurin kawar wa , azuciyar tako tace ban taba tsan manin cuta da ga gare ka ba malam,
   Ansar da yaba tane yasa ta gane cewa zancen zuci ya fito fili,
  Don ji tayi yace har abinda yafi haka zaki iya ji daga gare ni ai,
  Zan cena sam babu maganar cuta ko yaudara acikin ta,
   Gaba daya suka kurawa juna ido cikin dan mintina,
  Maryam ce tai saurin kawar da na ta  idon again
   Saboda in badon a zaune take ba  da zata iya faduwa don kaduwa,
  Sannu a hankali A,A masuga yaciga bada kafa gwaunatin shi a zuciyar maryam,
   Cikin jin kunya da kuma nauyi Maryam tai mai sallama daniyar wucewa yau ita kadai,, don dai wani irin nauyin malam din take ji yau,,,,
  Tafe suke ya na,takara kafa gwaunatin shi gare ta, ita ko har yanzu ta kasa gaskan ta zancen nashi a cikin ranta,,,,


ZEEE.  MAKAWA
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
    FUREN    JUJI
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
          2鈨�0鈨�


ZAINAB IDRIS MAKAWA

  Masoya novel din furen juji ina maku fatan alheri aduk inda kuke ina kara maku fatan gamawa da duniya lafiya ,
  Rahama ,daukaka azurta,dacewa da alheri ubanginji Allah ya hada ku dashi,
   Don nasan cewa bawai novel din kuke kauna ba kishin addinin mu ta isalama yasa kuke kaunar novel din, fatan alheri gare ku ko yau she馃憦馃憦馃憦馃憦馃憦馃憦馃憦馃憦



   Tsaye yake a cikin dakin shi yana daura agogon a hannun shi wanda ke mai masifar kyau aduk lokacin da ya makala agogo a hannun shi,
   Jerked din shi yadan aza saman wuyan shi, hannun shiguda ya rarimi yar Case din shi, da ita,
   A cikin sauri yake kokarin yin komai hakan kawai zai sa mutum yagane cewa yana da wani abu mai muhinmanci yau agaban shi,
   Da dan sauri sauri yake saukowa daga step din yana kokarin gyara tie din dake makale a wuyar shi,
   Tun bai karasa sauko wa ba Ejoma dake tsaye a bakin dinning table take mai wani irin kallo,
   Kofa yanufa don yau baiko tsaya zuwa gurin kakar shi ba,
   Brother, abinda Ejoma ta furta ke nan kamar yadda take kiran shi, where, are u going
  Your break fast is ready now,
  Tafada cikin yar shagwaba kamar yadda yan kabilar su keyi wa yayyen su,
  Dan tsayawa yayi, cak,  Agogon shi yadiba ya dan ya mutsa fuskan shi kadan yace mata,
  Cikin dan sakin fuska sorry sister, i don't have time for dat pls,,
  Kai Ejoma ta kara dan langabewa tadauki cup  tea ta,nufi inda yake tsaye har a lokacin yana kokarin gyara nicktie, din shi,
 Cup din tea din dake hannun ta tamika, mai tana cewa brother i beg drink dis ,even small now,
  O my god, Ejoma iam telling ,u now, dat iam, late,
  Ba yadda ya ita dole ya karba ya dan kurba tsa,tsaye, kadan kadan,
  Yamika mata cup din cikin sauri yabar falon don gudun kada Ejoma ta jawo mai wata matsalar kuma
  Yana fita Ejoma dake tsaye tadan bi bayan shi da kallo tana dan girgiza kanta,, Busy man ta furta,
   Ba laifi don yasa bakin nasu basu karaso ba, gurin da za ai taron,
  Wasu yan kasan Cameron da Guinea ne zasuyi wani dan meetings da su ta yadda zasu dinga tura masu mai acikin farashi mai sauki,
  Sai kuma kada watau ( Cotton) zasu yi harkan business din shi dasu,
   Sosai Joseph din ke jin dadin meeting din tare da bakin nasu saboda akwai abubuwan da ya fahinta so sai a fan,nin kasashen biyu,,,
   Tsawon wani lokaci suna wanan, taron har zuwa daidai da lokacin sallah a zuhur,
  Kawai sai mutum guda daga cikin su baki,ne so sai wulk da shi,wanda ke cikin shigar bakaken coth
  Tare da wani daya wanda shiko wasu kanan kaya yasa sun bala,in yi mashi kyau sosai,
    Mutumin farkon ne yafara daga hannun shi yadan kalli agogon hannu, wanda ke nuna karfe, daya da wani abu na rana,
  Mikewa yayi zubur yana mai ce ma sauran abokan meeting din I want to pray,
  Joseph da a,lokacin yake kokarin diba wasu takardun dake a gaban shi yai sauri daga kai ya kalli mutumin
  Wanda shi azaton shi tun farkon shigowar su yadauka dan bishon ne,
   Wai a,she muslumi ne, diban shi yakara konawa ga gudan da ke kojarin sance agogon hannun shi
  Kamar yadda yaga su KB na yawan yi idan zasu yi, alwala,
  Duk a cikin mamaki yadinga kallon su a zuciyar shi kuma cewa yayi,
  Ashe shi musulumi bawai dole ta kam ki wani hali zaka iya sheda shi ba ke nan kamar yadda yaga sauran, musullumai suna rike tasbaha ko kuma rawani ko sa tufafi mai nuna sheda,
  Kafin ya farga yana a cikin tunanen sai gani wa yan nan biyu dake gefen shi sun mike suma zuwa yin sallah,
   Ya kai wani lokaci yana ta al,ajabin wanan abin da yagani a tare da wa yan nan baki nasu, sosai,
   Wayar shi tai kara don haka yafita tadan waje kadan daga dakin taron,don,yar karba call din,
  Abakin wani daki dake gefen inda,suke taron yaga takalma mutane agurin,
  Sautin ladani sallah yaji har inda yake yana fadar Allahu,Akbar, Sami,al,llahu limal,hamd
   Kamar ance ya waiga hango su yayi still suna cikin shigar tufafin da Joseph ke tunanen zasu hanasu yin sallah,
   Can karshe yanufa ya ci gaba da maganar da yake yi,
  Har zuwa dawowar shi sun rarage sallah sun idar suna zaune suna lazimi,
   Ya zauna bada wani jimawa ba saiga su Aoudullah sun shigo duk kan su fuskan su cikin fara,a,
  Nan suka fara mikawa mutane hannu suna musabi,a da duk wanda ke gurin,
  Sau guda yadan daga kai ya kalle su yai saurin kawar da kan shi,
  Sai dai haka kawai ya kalli yan uwan shi Christian dake ta harkokin su cikin rashin damuwa,,,,,,

    A gajiye tafito daga dakin daukar lectures din din su yar jakar ta na sabale a kafadar ta,
  Tasan cewa A,A yana aji a lokacin don haka bata wahal da rayuwar ta zuwa office din shi,
   Saboda yanzu ma duk ta rage yawan zuwa gurin shi don guje wa shedan,
  A,kwai wani dan korido wanda zai sadaka da wata department namasu yin computer science,
   Iccen da ke gurin andan kawata shi da wasu kuherun kasa da akayi wa farin penti,
   Can ta nufa da niyar zuwa ta zauna, kafin lokacin shigar ta lecture yayi,
  Wata matashiryar buduwar ce zata dan girmay ma maryam kadan,
  Zaune take ta hada kai da gwiwa alamar a cikin tashin hankali ,take,don tayi zaune tayi tagumi,
  Gefen ta maryam ta zauna tare da fadin Bissimillahi,
  Hannu tasa acikin yar jakar ta tadauko wani dan bunch din digestive, biscuit, da wani dan lemon kwali,
   Gefen da yariyar data tarar a zaune tadan kalla karo na farko tunzuwan ta tazauna gurin,
   Mikawa yarinyar ledar biscuit din tayi tana mai mata Bissimillah,
   A hankali yariyar tadaga kai da idon ta da sukayi jawur, a lokacin, ta,dan girgiza wa Maryam kai alamar a,a, tafurta nagode,
   Sau guda maryam ta dan tauna biscuit din sai taji kawai bataji dadin yadda ta lura da cewa yarinyar na kokarin share hawayen ta da gefen gyalenta,
  Lafiya dai ko Maryam tai katsalandar din tambayar yarinyar,
  Wani kuka tasake lokaci guda tace wallahi yar uwa matsalar malam nan ne ke damuna ace mutane yan uwanka musullumai su dinga maka sheri,
  A hankali Maryam ta aje kwalin lemon da tafara dan zuka a lokacin ta mai da hanjalinta gun yarinyar,
  Yarinyar tace ni sabuwar zuwa ce a wanan school din, gashi na kusa kamalla duk wani abin da yakamata inyi amma gashi HOD din mu yaki samun hannu a takarda na wai bai yarda da results dina ba,
  Wani irin mugun tausayi yarinyar taba Maryam jin bakinta kawai tayi yana tambayar yarinyar wani department ne,
  Tace computer science, zubur Maryam ta mike ta kokarin gyara gyalen da tai rolling din kanta dashi,
  Shigar shi office ke nan yana kokarin dauko ruwa acikin dan karamin Fridge din dake office din,
   Da sallamar ta shigo office din sam bai zaci zuwanta yanzu ba don yasan cewa sai ta gama abin da takeyi takan zo su wuce gida, watarana ma sam baya ganin ta saidai suyi tayin waya,
   Ganin ta yanzu yasa yasan da matsala fuskanta ya dan kalla yaga damuwa fal acikinta,
  Daidai lokacin da yake zama yake cewa lafiya kuwa Maryam,
   Ido tadan tsura mai yau babu ko kiftawa, yai mamakin hakan sosai a, ranshi don yasan cewa ba halinta bane hakan,
   Zai yi magana sai yaji muryan tana cikin rauni tana magana,a hankali,
  Malam banaso sam, sunan ka, ya dinga fitowa daga cikin azzaluman malam makarantar nan,
  Masu kokarin kayarda ditan mutane, daga cigaban su,
  Kafin taci gaba yadaga mata hannu alamar ta tsayar da zancen ta hakana,
  Cikin mamaki yake tambayar ta komay ke faruwa da har tazo mai a haka,?
   Nan ta kwashe yarda sukayi da wanan yariyar ta fada mai,
  A, cikin mamaki yake tambayar cewa yaushe akai haka da shi,sam bai ma san zancen ba
  Can yace ina ita yarinya tana daga waje inji Maryam,
   Da sallama maryam suka dawo tare da wanan yarinya,,,
  Cikin ladabi tagaida malam din wanda ke dan rubutu a wani dan pepper,,
  Yadago kai yakali inda suke yana mai mika mata hannu alamar takawo takardun ta, dake hannun ta,
   Ba,bata lokaci taciro su daga cikin handabag din ta, ta mika mashi su, jiki na rawa, kamar zata fadi don tsoro,
  Tai mamaki kwarai da taga yasa mata hannu batare da bata lokacin komai ba cikin yan mintuna
  Ita ko yanzu kusan wata daya da rabi ke nan tana ta faman  bin, ai, mata wanan aikin abu ya faskara,
  Sai gashi yau Allah yakawo mata shi a cikin sauki ta samu an mata,
   Yana gamawa yadago ido ya kalli yariyar yace mata kin taba gani na akan wanan takardan,
  Tace duk lokacin da nazo sai messenger ya ce min baka nan komaya yace ance bazan samu ba karshe ma sai ce min yayi ance takarduna basa yi wai,,,,,,
 
   Bayan fitowar su ne wanan yariyar ta rungumay Maryam tsam a jikin ta tana ta zuba godiya anan take sheda mata cewa sunan ta Safiya,
  Tundaga wanan ranan suka kulla friendship mai 脿karfi a tsakanin su har takai in har guda baiga guda ba, bai jin dadi,
  Yau tsawon kwana biyu kenan Safiya bata shigo makaranta ba,
  Don haka Maryam tashiga cikin damuwa sosai,
   Nobar wayan ta takira wanda kwana biyu kenan nobar bata shiga koda takira sai ace is switch off,
   Yau kira guda Allah yasa nobar yashiga, batare da wani bata lokaci ba aka dauka a dayan bangaren,
    Nan take jin cewa ai safiya mahaifiyar tace bata da lafiya suna asibiti da ita,
   Maryam taima safiya alkawarin zuwa dubata, insha Allah,
   Sukayi sallama tare da aje wayan cikin nuna tausayi,
  Maryam ta fadawa Anty abinda yasamu mahaifiyar safiya,da ke asibiti kwance,
  Itama dai anty ta tausayawa safiya da mahaifiyar ta,
   Cikin wata raunaniyar murya tace wa anty idan tasamu time weekend zata tafi ta dibo maralafiyan,
   Anty Dije tace Allah yasa don dai ke ce da kanki kikayi wanan alkawarin don nasan cewa bazaki tafi ba,
   Cikin dan marairaice murya, Maryam tace, insha,Allah zan kokarta in tafi, ai saboda safiya nada kokari wlh,,
  Da dare suna zaune a harabar tsakar gidan su suna shan iska
  Saboda dauke wutan neper da akayi yau garin yai zafi,
   Sallama suka akofar shigowa gida, Maryam wace ke kwance saman wata tabar roba da suka baza tana karatu don tana da test a cikin satin nan,,,,
    Cikin mamaki gaba dayan su suke cewa muryan baba ne fa,
   Cikin farin cike duk suka mike suna tariyan shi,
  Wani tabarma aka dauko wa baba yazauna tare da jawo Isslam da Assalam zuwa jikin shi,,,
    Sun gaisa sosai da baba sai shiru yadan biyo baya,
   Baba yace wa Anty Dije yazo ne yadibi lafiyan su, da kuma zancen maryam,
   Maryam wace ke zaune gefe guda gaban ta yaba da damm,
   Nan baba yake tambayar Anty may ake ciki ne da zancen
  Anty Dije wace ke dan gefe tsugunne tadan kara gyara zaman ta tace wa baba,
  Baba maryam fa karatu takeyi yanzu dan Allah ba ba kayi hakkuri har tadan karasa sai ai zancen auren ta,
  Baba ya ce, a,a Dije banaki tanaki bane saidai kin san cewa yanzu mutane ba sui ma baya,
   Kin,ga gara tun inada rai muyi mata aure kada in mutu in barki da nauyi ke kadai,
   Maganar taso taba anty Dije dariya sai dai ta yar murmusa kawai tace
   Insha Allah baba kana da rai maryam zatayi aure kuma kaida kanka zaka aurar da abinka,
   Amma zancen cewa zaka tallafa min sa abinda zan aurar da ita don Allah baba ka daina wanan zance,,
   Allah zai hore min duk wani abu da za,ai mata, baba ya ce haba Dije ayi haka,?
   Da ki bari in saida yar shanun da nake kiwo sai in baki ki kara don kinga mahaifiyar ta nasan ba komai za,a samu a gurin ta ba tun da a kauye suke,
   Daga Anty har maryam saida tausayin dan tsohon ya kama su,
    Anty Dije tace cikun wasa baba kaje ka saida shanun ka kuci abinci da iyalin ka,
  Allah na nan zai rufa asiri insha Allah,
  Mudai fatan shine kai mata addua Allah yabata miji na gari,
    Ameen Ameen baba yafara fadi yana mai jerowa yqr diyar tashi dayake kauna aboye kuma take bashi tausayi kasan cewar ta ita kadai a gidan,
   Bayan tafiyan baba nan su ka zauna suna tausayin mahafin nasu mutun wanda baison hayaniya kuma bai shiga harkan kowa,
   
      Auren KB yataso sosai da ma so yake ya karasa ginar shi sai ata da zancen,
    Don haka yanzu da ya karasa ginan ya ta da zancen,
  Saboda yana bukatar yai azumin bana da matar sa,
 Saidai gidan matar sun dan kawo mashi tasa matsalar cewa basu shirya ba,
   Nan KB din yabude masu wuta babu sassautawa, cewa shi fa yana bukatar matar kafin watan ramadan,
   Maryam dake kitchen tanawa anty aikin abinci tanajin yadda KB ke fadawa wani wanda bata fahinci kowaye ba acikin waya,
   Saidai daga karshen zance taji KB din nacewa nifa gaskiya na kashe kudi masu yawa a wanan harkan,
   Sannu sanu taji yana rage tsauri帽 masifar da yaketa zubawa a waya, da alamar wanda suke wayar ya dan lalashe shi ne,
   Cike da takaici maryam ke aikin ta tana sauraren kb wanda ke zaune a falo shida mijin anty dije, da ita anty dijen,
   Jin ya ambaci sunan Joseph yasa ta tuna dashi saboda da,dewan da yayi bai shi garin ba,
    Zancen tsohon nan yafado mata arai ganin cewa ga mijin antyn ta agari gashi bai zo ba akan zancen,
   A cikin hikima da dabara ta tunawa anty da zancen nan anty ta kwashe komai ta fadawa maigidan ta,
  Shiru yadan yi yana tunanen zance,
  Can yace wa matar shi kin san wanan wani babban al,amari ne,
   Don dai da wuya Joseph ya can za zuwa wani addini tunda har kikaga yakai war haka bai nuna wani alama ba,
  Don haka kawai kubar wanan zancen kada ku dauko min magana at last,
   Maryam dake sauraren bayan nin mijin yar nata sai taji wani haushin shi yakama ta,
  Bata san irin halin mijin yar uwar nata ba da rashin son tallafawa addini,
  Wanan ai taimako ne amna sai gashi yana kakaucewa,
  Batare da wani kwakwaran magana ba mijin yar nata yabar gari,wanda hakan yakona wa Maryam rai,
   Dadare bayan tagama komai ta sa wanan sim din nata na boye ta dauko tasa,a wayar ta,
   Tai rubutu kamar haka
A TRUE BELIEVERS, BELIEVE IN ISLAM,,,,,


ZEEEE  MAKAWA,,,,,,,,
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
    FUREN      JUJI
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
           2鈨�1鈨�

ZAINAB IDRIS MAKAWA

Tun Mr Ema yana fushi da dan shi kan laifin da yayi sai gashi yanzu shi da kan shi ke bukatan dan yazo gari,
  Saboda irin dadewawar da yayi bai shigo garin ba,
  A, gaskiya kuma baida time yanzu kamar da, da bai wani aiki mai yau, don yanzu ko kasar bai faye zama ba,
   Duk wanda yadade baiga Joseph ba idan ya gan shi yanzu yasan cewa akwai canji so sai,
    Yanzu ya zama mai dole ya shigo badon komai ba saidon kare mutuncin church din su,
   Church din su da ke fuskantar barazana daga sauran churches din dakw garin,
  Taro ne zasu yi nakasa mai girma wanda saboda hadin kai irin nasu duk inda mabiyi wanan church din yake dole ne yazo da jamar, sa, saboda da ci gaba,
   Yan churching su Joseph sun gano cewa ana so a zarta su daga wata kungiyar kirtawa,
   Don hakane suka hada wanan taron na ci gaban su,
   Shiri so sai Joseph yaiwa wanan tafiyar saboda irin dadewar da yayi bai shigo garin ba,
   Maman Choima da Ejoma da danta, sai shi  Joseph din dake jan su da kan shi tun daga Lagos,
  Tanks god ya furta a hankali kamar yadda yasaba maganar shi cikin natsuwa,,,
   A,lokacin da yahango irin aikin da yaita turowa ana gyara masu gidan su,
   Ginan yayi mai sosai don tun daga nesa yahango ginan ya fada da anguwa sosai,,
   Baka jin komai a motar sai muryan wata mawakin IBO mai waken churches, Rabeca Gebrin,
   Joseph nason wakokin wanan mawakiyar mai zakin murya saboda iya fitar da baitoci da takeyi ga Jesus,
   A hankali shima yake marming din wakar inda kusan daidai da mawakiyar bakin su ke tafiya,
   "Keddo, "Edema yye Jesu, Na,belewawooo,,,,
    Shima bin wakae yakeyi yana dan dukar sitiyarin motar,tashi,,
   Kyawon motar kesa mutane na waiga wa don bakuwar motace da nobar Lagos,
   Mr Ema yai murna kwarai daga ganin dan nashi wanda sun kusa shekara guda bai,zo ba, gashi yai, wani irin fresh,
  Yazama full getle man, ya aje wani irin saje da yadan kewaye mai fuska gwanin sha,a wa,
    Duk Wanda ke gidan yau murna sukeyi da zuwan Joseph tare da su Granny, da Ejoma,
    Kamshi kakeji duk inda kabi kala,kala, a cikin gidan jen yan mabiya churching Catholic,,
    Shi kan shi Joseph yaji dadin yadda ya, samu mahaifin shi a cikin koshin lafiya,,,
    Inda mahaifin yake ya iso ya dafa kasa da hannu guda yana mai daga kafa guda ta baya,daidai saitin kafar mr Emanuel,
   Kan yaron nashi yadafa yana mai yi mai addu,a,acikin ki,rari,,,,
  Dan murmushi yayi yana mai mikewa cikin jindadi, samun blessing din ya yi daga mahaifin shi,
    Daga Maman Choima da Ejoma duk sun zo inda yake sun gaishe shi,
  Ya amsa ba yabo babu fallasa,tunda baida yadda,zai da halin dan shi wanda yasha warning din shi kan su,,,
    Bawani abinci Joseph yaci ba sosai don haka suka ci gaba da shirye shiryen su,

   Yau kam churchi ya yayi mugun cika makil da mabiya wanan akidar ta Catholics,
   Bukine sosai babu kama hannun yaro anan aka shirya wani kungiya, wanda zasu dinga bi kauyuka suna jan ra,ayin mutane da abubuwan duniya,
    Joseph na daya daga cikin wa yanda suka bada gudun mawar su don asai kayayyaki, da za,a rabawa kauyawa, dakuma masu bukata daga cikin su,,,
    Wani irin ihu church din yadauka bayan jin abinda sukatara har yafi abinda suke tsanmani samu da farki yawa,
  Wani dan gajeren mutum ne tsaye da lassifika yana cewa
"PRESS THE LORD;
  Sai sauran su karba mai cikin murnan jin dadi suce "HALELOYA'
   Nan take masu kida sauka hau kada ganga duk kowa ya mike akafara wankan JESUS DEY HEAR, HE, DEY,,,,,
  Duk wurin yarude da wani irin ihu sai tafi kake ji, da rawa maza da mata,yara da manya,,,,,,
    A hankali yazamay jikin shi daga cikin su yana dan tabe kamae may zuwa yin wani abu,
    Sai alokacin ya zaro wayar shi daga cikkn aljihun shi yana ta kokarin bidan nobar waya,
   Bai tsaya ko ina ba sai gidan, su 脌nty Dije, ta kofar gidan gidan ya tsaya yace ace yana wa Assalam sallama,
  Anty Dije bata gida maryam cs da yara kawai a gida suna kallo a falon gidan,
   Shigowar yaron da aika aiko kiran Assalam ne yadan sa su daga labuken falo,
  Maryam na zaune da waya a hannunta tun kusan minti ashirin suke waya da A,A, din ta,
   Sam bataji yaron ba har fitan Assalam din sai dai ganin shigowar Joseph da assalam tagani ya na rike gam da hannun shi,
   Muryarsa mai,taushi yai sallama da ita tankar musullumi,
   Tuni zuciyar maryam ta tsinke, don ta rasa da wani kallama zata ansa mai sallamar tashi,
   Mikewa tayi zaune daga kishingiden da take saman kujera,
   Ganin da yayi tadan dadirce yasa shi samun daya daga cikin kujerun falon yazauna
  Yana mai jawo Assalam zuwa jikin shi cikin nuna kulawa da kuma yar fara,a man,ne a fuskan shi,,,,
    Sannu da zuwa ta iya furtawa a lokacin
  A dakile ya amsa mata da yaiwa, saboda sanin halin miskilanci irin nata,
   Issalam dake zaune tun shigowar shi ta tashi cikin murna ta nufi gurin shi tana cewa Uncle sannu da zuwa, kamar yadda uwar su tace su dinga ce mai,
    Wani irin laulausar murmushi yasake mai yar sauti yajawo ta zuwa kusa dashi yana fadin,
   Wai, wai, wai Issin mama may aka baki haka kikai girman nan,
    Sai a lokacin Maryam tadan kalle shi a karo na farko tun shigowar shi falon,
  Cikin sauri takauda kai a zuciyar ta tana fadin Wa,subbahanallahill, Azeem,
   Saboda yada taga Joseph yakoma lokaci guda ,
   Yazama wani irin, handsome guy, ,sai ka rantse kace ba,a kasar nan yake ba,
   Sanye yake da dinkin shadda sai shining shaddan keyi sky colour,
   Ga wani sarka da zakai ma kallo guda kagane cewa ta gold ce,
   Akawo ma ruwa tasamu bakin ta da iya furtawa a lokacin,
   Harara ya dan sakar mata ta gefen ido yace No ki barshi kawai,
   Sai yaci gaba da hiran da yakeyi da yaran suna ta kwasan dariya, don jin dadin kasancewa dashi,
   Wayan ta ta dauko taima antyn ta text cewa ga wanan kafirin mai zuwa yazo,
  Saiga Anty ta kira layin maryam din tana tambayar ta Joseph take nufin yazo ?
  Maryam tace eh shine,
Mikewa Maryam tayi tana mai hada kayan wayoyin ta da kuma wani takarda da take dibawa,
   Ba,a dauki wani lokaci ba Anty Dije tadawo daga unguwar  in  da ta tafi karban, bashin ta,
    Da murna Anty Dije ta tari Joseph suna ta kwasan dariya ,
  Maryam dake daki duk sai taji haushin Anty Dije don may zata dinga washe baki da kafiri,
   Sosai yake dan ba,Anty labarin irin abubuwan da suka dan faru dashi bayan wucewar shi,
  Maryam mamaki irin shakuwar su tankar yan uwa takeyi,,
  Don dai ko yan uwan su da suke mahaifi guda basu shaku da Anty kamar haka ba,
   Wanan dibgegen motar da ya aje a kofan gidan su Anty Dije yasa mutanen gari sanin cewa yashigo gari,.
    Kafin wani dan lokaci mutane sun farga da zuwan shi,
   Abokin Damo, Tsari, sai ga KB da jibrin su ma sun shigo garin,
   Abinda maryam bata so shi yadawo don kagin wani lokaci gidan su fam da yan zuwa maula,
  Don sun figane masu samay shi a gidan anty Dije bisaga gidan mahaifin shi,
   Dayake gab ake da afara azumin watan Ramadan,
   Kowa kagani kokarin wanan shirin yakeyi, sam shi da ba musullumi ba bai san cewa wanan lokacin ya gabato ba,
  Sai da wani dan uwan Jibrin yazo gurin Jibrin din neman taimakon abin da zai dan sai abinci,,,
  Dubu biyar Jibrin yaba mutumin yana mai cewa kayi hakuri akwai mutane da yawa,
  Mutumin ya juya yana zabga godiya,saboda dama duk tunane ya ishe shi, ta inda zai dan samu abin da zai fara sayen abinci kafin ai masu albashi,,,,
   Haba dai man wanan mutumin fa kamar cewa yayi yanason abinda zai sayi abinci azumi ko,?
  Joseph ne ke tambayar Jibrin din,
  Jibrin yace haka yace, sai Joseph yadan kada kan shi alamar takaici,
  Yo aiko sukarin azumi bazai sai masu ba, haba, haba man,,,
   Kiramin shi pls,
 Dubu hamsi yabawa mutumin nan ya rasa irin godiyar da zai ma Joseph don murna,
  Yau shigan safe yai ma gidan nasu Anty, Dije saboda yana son shan kunun gargajiya da kosai,
   Yana Sanye da farar T,shirt anrubuta agaban rigar, snow, da wani jan kala,
  Sai dogon wando mai kyau ruwan baki,wani farin agogo ya makala a hannun shi na D&G,
  Sai kafan shi dake saye da wani farin takalma rufafu masu kyau gani,
   Maryam ce Anty tasa ta gabatar mai da kunu wanda yasha kayan yaji sai kamshi ke tashi,
   Da kosai wanda shima yaji hadin kayan markade, da aka soya su tare,
   Aikin kullun yake yi waya, don ko zama yayi kafin ya tashi sai yayi waya da kusan mutum ba iyaka,
  Yana daga cikkn abinda yakesa shi zama a gidan anty in yana gari don yakan samu time din yin waya,
  Tunda tadoso wurin fuskan shi na kallon gefe bayan shi ne,
   Tana isowa yajuyo fuska a daure, tamau, yace dan Allah kawo min ruwa mai sanyi pls,
   Mikewa tayi bayan ta aje dan tire din da tadauko kayan karin a ciki,
  Wani harara ta,dan na masa, alamar kama raina ni,ke nan,
   I don't have your time don ni ba yar aikin ka bace,
  Azuci take tunanen ta fada ashe, har afili, ana jinta,,,,,
  Cikin rashin damuwa yace mata sorry pls just bear with me for sometimes,
   Da sauri maryam tabar falon cikin jin nauyi da kunya don sam batai tunanen maganar zai fito fili har yaji ba,
   Tun shigewar ta bata kara fitowa waje ba saboda nauyin da taji,
  Saidai tana jiwo hiran shi da Anty yana tambayar ta a gamay da azumi, Ramadan dake tafe,
  Cikin hikima yakewa Anty Dije tamabayoyi tana bashi ansa yadda yakamata,
  Maryam dake waje tana tunanen cewa anty zata sako mai zance addini aciki sai taji shiru,,
  Ba wani tambaya ne yakewa Anty Dije ba, illa abinda mai azumi ke bukata, yasamu idan yai azumi,
  Saboda azumin mu da nasu ba iri daya bane, don su daga sha biyun dare zuwa sha biyun rana suke azumin su,,,
   Bayan wanan maganar tasu da kamar kwana biyu,
  Basai ga kaya niki niki wata mota Peugeot mai budaden baya ta,o dasu ,
  Sukace Anty Dije akace sukawo wa inji Joseph yace zai bugowa ya suyi magana shi yatafi, Abuja,
   A cikin wayane yake mata bayanin cewa ta rabawa mabukata da sukafi bukatar taimako, wa yan nan ka ,,,
  Sai kuma ga su gero da sauran kayan hatsi ankara kawowa,
  Nan akaita bawa mutane sadaka saboda ba wanda yasan ko daga ina ne kayan suka fito,
  Sai daga baya mutane suka fara ganewa cewa Joseph ne ya base  taimakon,
  Har gida wani mutum yazo yasamu Anty Dije da masifa cewa don may zata yaudare shi ta bashi abin kafiri yai azumi dashi,
  Inda yake shiga banan yake shiga ba taso yatara mata mutane,
  Kafin ma yabar gurin saibmutane gungu,gungu sunzo abasu sadaka idan akwai (Dan Adam,)
  Unguwa unguwa yasa adinga dama kunu da sugar ana bawa almajirai sadaka,
  Allahu akbar nan zancen ya tadu a gari cewa ai ya musuluntane kawai a boye,
  Saiga shi magana har wurin mutanen su ya kai bayan sun bukaci yazo,
  Nan yabugo masu waya cikin bacin rai yana sheda masu cewa ba ruwan su da shi balle su sa mai ido a harkokin shi
  Shi yana yi ne "for god sake,,
 Don haka bawai su za su nuna mai ga wanda ya kamata ya ba, ba,
  Basu gane mai ba ganin cewa yawuce sanin su ko don haka dole suka sa mai ido da halin shi,,,,
    Irin abin da yakawo ma gidan su Anty Dije ya ce ta rabawa yan uwan tav abin ba,a cewa komai,
  Bakomai yasa yai haka ba don kawai yadda yaga ta kamanta mai gaskiya ga abubuwan kamar yadda yasa ayi,mai,,,
   Malam A,A ma ya yowa Maryam kayan shan,ruwa nagani na fada,
 Kamar su kayan tea manya gwagwani, millo, sugar eggs, butter, cooker oath, cornflakes, dasauran su kamar yadda akeyi wa mace wace zaka aura wanan sayayyan a kasar kwantagora,
  Maryam taji dadin wanan kayan da malam,A,A yakawo mata badon komai ba saidon dama tana kyamar na gurin Joseph,
  Duk da tasan cewa dole wata rana tayi amfani da dayadaga cikin abin da yakawo a gidan,,,
 
   Ansa lokacin bukin KB sallah da sati guda don haka abubuwa suka dan cabe w anty saboda tana cikin masu gudanar da tsarin bukin
   Duk da gidan amarya sun nuna cewa basu so asa masu Anty Dije acikin har kan su,
  Don a cewar su, suma za,su iya gudanar da komi da kan su,
  Don gani sukeyi cewa maganar Anty yan matasan ke kokarin bi,,,,
   Sun manta cewa mutunci na iya sa komai don dai ita sanadin dantane duk yajawo mata wanan badakalar,,,,

ZEEE    MAKAWA
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
    FUREN     JUJI
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
           2鈨�2鈨�

ZAINAB  IDRIS  MAKAWA


Bakaji komai sai karan  na,ura, dake  ta shi cikin make,ken falon
   Wanda komai da ake bida na hafuwar falo ya hadu,
   Jin shirun da wurin yayi zakai tsan manin cewa ba kowa acikin gidan alokacin,
   A, hankali yake dan tafita saman walking exercise machine din shi yanayi yana goge dan zufan da ke tsiyayo mai a goshin da wuyan shi,,,
   Sanye yake da wani bakin wandon roba har kasa mai dan ratsin fari a gefe, sai, bakar singlet maikama da wondon wanda baida hannu,
   Wayan shi sake gefe guda ne tai kara a lokacin badon yaso ba yasauko dan daukar wayan
  Anty Dije yagani baro,baro a screm din wayan, shi,
  Yai mamaki kwarai da ganin wayar ta da sassafen nan don bata taba kiran shi irin haka ba ,,
  Asanin shi madai shine mai kiran Anty din indan har yana da bukatar magana da su,,,
  Yana goge zufan jikin shi yana kuma mamakin kiran da safe hakan ga,
  Jiran wayan yakeyi ya katse saiya kirata da kan shi don haka yakewa mutane da dama,
  Kiran farko Anty dije tadaga wayar anata bangaren,
   Cikin dassashiyar murya ta ke mai magana Joseph gamu asibiti da mutumin ka yau two days kenan,
   Cikin daga murya ya ce what, Assalam baida lafiya har two days ban sani ba,
   Tace wallahi muna ce ko abin baikai haka ba, shine, yasa ban fadama ba,
   Yanzu ma shike tace wa wai baigan ka ba shine yasa yana buga ma,
 Wai, May ke da munshine Anty, Anty tace yadawo daga school da zazzabi ,
   Shine daga baya ya abin ya koma mai combustion, fever,
   Cikin matsanacin tsoro da firgici, ya furta O God, da sauki dai yanzu ko, Anty tace eh to yau dai abin bai buga mai ba, gaskiya,
  Assalam din ne akabawa wayan cikin dasssashiyar murya irin ta marasa lafiya yake cewa uncle, zan sha Keisha sweet, da apple juice,
  Wani iri Joseph din yaji a lokacin don yasan cewa yaron baida lafiya a yadda yaji muryan shi, cikin waya,.
 
  Joseph baisan cewa ya shaku da yaron ba sosai, sai yau din
  Don haka, yinin ranan haka yayi shi cikin rashin kuza,ri don ji,ya keyi kamar ace yana agarin shima, a,lokacin don yaga yanauin yaro,,
   Gashi yai ta kiran su amma nobar nasu baya shiga,
   Sai zuwa dare yasamu layin, nasu, yashiga nan yakara tambayar su ,lafiyan yaro aka ce mai da sauki,,,
    Jin haka yai tunane don yasa irin halin hausawa musullumai, duk irin halin da suke ciki sai suce ai da sauki,,,
   Don haka ya yanke shawaran tun da safe yakama hanya kawai,
  Don haka ya kwana dashirin tafiya, duk wani abinda zai bukata don tafiya yai ready din su,
   Karfe shidda na safe ya bar garin Lagos zuwa kwantagora batare da,ya fadawa kowa ba, cewa ga shi tafe,
   Ganin cewa tun jiya batai wanka ba yasa ta cewa maryam tazo ta zauna da yaron
  Ita zata tafi gida tadan watsa ma jikin ta ruwa ko zataji dadi,
    Lafiya lau suka rabu da Anty Dije, Assalam din na saman gado yana,dan wasa da wayan Anty,
  Saida zata wuce takarbi wayan a hannun shi, a, lokacin yaron yadan kai kanshi saman filo,
   Maryam da hankali ta ke ga wayar ta batasan cewa yaron na cikin wani hali ba,,
  Wani irin kakari tayi yaron nayi ashe hakoran shi ne ke hadewa, yana bada wani,irin kara
  Cikin matsana cin tsoro da firgici maryam ta mike tsaye, ,da gudu ta kwasa tai hanyar waje cikin rudewa,
  Karo tayi da mutum yana kokarin shigowa dakin,
  Kamar daga sama ta ganshi tsaye kofar dakin a lokacin ,
   Cikin rude take kurma ihu tana ce mai ya mutu, tana nuna inda Assalam yake kwance cikin mawuyacin hali,
   Gurin gadon yayi da sauri, ya dago yaron dake ta faman karkadawa,
  Daukan shi ya yi din rudewa zuwa office din doctor,
  Maryam na bishi a baya cikin wani iri tashin hankali,
  Duk saurin da takeyi kamar mai gudu baisa ta cin masu ba,
   Karban yaron sukayi suka cewa Joseph ya fito  waje, ya tsaya,
   Maryam na ganin  yafito batare da yatmron ba takaraso da guda tana ce mai ya mutu ko ?
  Innalillahi wa,ina alaihi raj,un take ta na,natawa cikin tashin hankali,
   Waya ta dauko daga cikin yar pos din hannunta tana kokarin kiran layin Anty Dije,
  Joseph wanda tun fitowar shi yake jingine da bangon dakin likitan,.
   Fuskan shi murtuk, kamar bai taba farinciki ba, yana mai kallon sama,
   Ganin tana kokari kiran layin wayar, Anty Dije ne yasa shi yi mata magana akaro na farko tun zuwan shi,
   Yace "pls don't call dem,,
   Wani kallo tai mai na baka da hankali,
   Daurewa yayi cikin jin haushi yace may zaki ce masu,
  Mamakin tambayar da yai mata tayi amma cikin dakewa ,
  Tace in fada masu cewa yarasu, mana,
   Ido yazoro waje yace waya fada maki cewa ya rasu da zaki fada masu,
  Cikin mamaki take kallonshi don sam bata fahince shiba saboda rudewan da tayi,
   Fuskan shi a,daure yace mata suna dibashi ne
  Shiyasa na fito nan gurin har su gama aikin su,tukun,
   Wani irin ajiyar zuciya mai sauti maryam tasake tana mai furta Alhamdullah,
   Kafin wanin su yakara wani magana a,ka turo kofan wata yar nurse ce ta miko mai wani takarda tace ance kayi sauri ka sayo wanan,
  Cikin sauri Joseph ya wuce sayen maganin sai a lokacin maryam dake tsaye tun dazu cikin tashin hankali takai zaune saman wasu kuherun karfe da akajera akofar dakin likitan,
   Jafin yadawo aka fito da yaron zuwa dakin da yake da farko saida da alamar barci yake yi,
   Da Joseph zai dawo saigashi da kayan tea manya,manya gwangwani da kuma kayan shaye shaye,
   Nan ya zube kayan yadan je bakin gafo gurin yaron yadan dade tsaye yana kallon shi sanan yadan juya inda maryam take yana ce mata,
   Idan ya tashi ki hada mai tea mai kauri pls sai a bashi maganin nan,
  Zadu dawo zuwa dare sukara mai allura, amma dan Allah ku bashi tea ko kunu yasaha, sosai pls,
   Daga nan ya juya yabar dakin cikin tafiyar shi ma kama da ta yanga,
   Sai a lokacin maryam ta nisa tana mai kara mamaki da irin rayuwar wanan mutunin,
   Allah ya sa yagane gaskiya tace daidai lokacin da tamike ta dan fara gyara kayan da suka wawa,tse adakin,,,,
  Sallah tai haraman yi don har lokaci yadan gwauta, bata samu yi ba saboda rudewa,,,
    Sai zuwa tara na dare Anty Dije tadawo inda tasamu Maryam zaune gab da Assalam ta kura mai ido,
  Tunda tashigo dakin hankalin ta, na gurin su don yadda taga Maryam din a lokacin,
  Kayan da tashigo dashi a hannunta taje tana tambayar Maryam maynee, halan naga kin wani kura mai ido
  Maimakon Maryam tai magana sai kawai tasa kuka wi,wi,wi,
   A rane anty ke kara tambarya ta wai may akayi,
  Kuka yaci karfinta takasa magana,balle tai mata bayani,
   Jin anturo kofan dakin yasa Anty waigawa don taga kowaye yashigo,
  Joseph tagani yana sagale da yar jarket din shi a kafadar shi,.
  Cikin mamaki Anty Dije kallon shi sai tambayar shi,take tambayar shi yaushe iso,
  Yai yar gajerar murmushi yana kojarin karasawa inda Assalam yake kwance,
  Saida yakai bakin gadon yadan taba jikin yaron yaji da sanyi babu zafi kamar dazu,,
  Sanan yadan juyo yana gaisawa da Anty dijen, sai alokacin ne ya jai kallon shi ga Maryam wace ke ta faman sharar kwalla,,
Ido yadan zuba mata nadan second, sai yakawar da kanshi daga gareta da sauri,
  Azuciyar shi yace dazun ma dayaron ya shiga conscious, batai kuka haka basai yanzu,
   Gefen gadon da yaron yake yadan samu gefen bakin gafon yadan zauna
  Nan suka fara hira yadda abin yafarawa yaron tun farko,
  Yace likita yace, harda typhoid, da kuma malaria ke damun shi,
   Maryam wace ta dauro alwalar sallah isha,i, tazo tada sallah duk alokacin suna ta maganar assalam din,
   Bayan tabidar ne Anty Dije ke cewa ki hada wanan kayan ki sauri ki je maryam kin san cewa issalam bata yarda dakowa in bake tagani ba
  Ga Joseph nan sai ya sauke min ke idan zai wuce,
 Gaban maryam ne ya fadi a lokacin don ita sam bata son wani alaka da zai hadata da shi,,
   Joseph tashi katafi ka huta ka debo gajiyar hanya,
   Anty yatafi kawai zan kira a kaini, yanzu, Anty dije tace  Maryam ko da na bargida Issalam fa taki zuwa gidan su Salma,
  Da dabara nasamu nakai tacan nasan cewa yanzu haka tana can tana masu rigima
  Maryam zatai magana anty tace don Allah tashi ya sauke ki kada dare yakara yi,
   Wayan maryam din ne yai kara aloacin cikin murya mai shakewa ta ce, Assalamu Alaikum,
   Ido Joseph na akan ta don ya nason subar asibitin don yaje gida kafin maihaifin shi yashiga barci,
    Cikin shagwaba taje cewa gata nan zatabar asibitin zuwa gida yanzu,
   Tunda suka fara hanya ba wanda yai wa dan uwa magana
  Sai shine ma yai dan magana cewa ta danyi hakkuri yasai wani abu a kingays super market,
  Batare da yaji maitace ba yabude motar yashige abinshi,
  Kara kiranta A,A yakarayi a karo na biyu yana maice mata yana son ya wuce don badadewa zaiyi ba,
  Gashi Joseph kuma yasa security lock ya kulle motar don kada sanyi A,C ya rage,
  Batare da ta ganshi tafe ba. Dan guntun tsuki tayi daidai lokacin da yabude motar zai shigo,,,
   Ledoji ne birjit a hannuwar shi yazube su a gefen shi,
  Suna karasawa A,A, natada motar shi daniyar zai wuce abin shi,
   Ganin su ya sa yadan dakata sai dai bai san kowakeda qanan dirkekiyar motar ba haka,
  A hankali ta sauko daga motar daidai lokacin da shi kuma yafara tatara ledojin da yasiyo a super market yana kokarin bude kofar gefen shi,,,,,
    Cikin rawan jiki ta take saurin fita don gudun bacin ran A,A din gareta,
   Dan ma,kullin gidan da Anty ta bata dazata wuto take kokarin daukowa daga cikin pos din ta,
    Joseph yagane cewa hankalinta na gurin mai motar dake tsaye ya kun,na dim,light din motar,
   Da kanshi ya je har bakin kofar gidan yakarbi dan makullin daga hannunta ya bude gidan,
  Saida yakai duk kayan da suka dawo dashi daga asibiti zuwa cikin gidan,
  Maryam wace har lokacin ta gurin mai motar tadan rankwafa suna magana dashi
  Ganin cewa ba,ta,daniya barin gurin mai motar yai mata bayani cewa ga kaya nan tabawa Issilam
  Yasa shi tada motar shi yana mai yi muzu horn yai tafiyar shi,
  Maryam wace alokacin take cewa A,A, ya daina hadata da kafiri Arne,
  Yaga tashin motar shi nan yadan mata dariya cikin barkwanci yake ce mata yau dai na hana shi tsaya wa,
  Maryan wace ranta yakai kololowat baci ta wuce zuwa ciki batare da ta,tsaya yi mai saida safe ba,
  Shiko A,A da gangan yake mata wanan wasan don yasan cewa tayi hating din Joseph din,
  Tun zuwan shi bai hutaba akan ciwon Assalam don duk wani zirga,zirga da sayen magani yakan shi tun zuwan shi
  Da har yana cewa zai dauke yaron zuwa Abuja, Turkish hospital,
  Saiga shi yaji sauki sosai kamar bashi bane mai ciwo da duk yatayar wa mutane a hankali,
 

Kuyi hakkuri pls ba yawa yau


ZEEE  MAKAWA
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
    FUREN    JUJI
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
           2鈨�4鈨�

ZAINAB IDRIS MAKAWA,

 Ganin haka da mahaifin Joseph yayi kuma yasan cewa Joseph din sanane, a gurin ya sa shi matsa mai sai yazo gida,
  Inda yake kwantagora, saboda idan yana kusa dasu hankalin su ,zaifi kwanci,
  Joseph da yaga cewa baban nashi ya matsa mai sai kawai ya shirya tare da duk wani wanda ke gidan suka koma Enugu da zama,
  Saboda can ma akwai business din da suke yi sosai a shigowa dashi mu san man da har yanzu yana kokari wurin ganin sana,ar mahaifin shi tana ci gaba,
   Yau ya kasance ranan sunday sai ya shirya tare da su mama da Ejoma wace ke dauke da dan karamin dan ta wanda suke kira da Jecob,
   Irin church din su da suke zuwa wan da aduk cikin churches yafi karfi da kuma yawan manyan mabiya,
  Musan man ma yan kabilar IBO sunfi yarda da wanan church din saboda da kasa shen,turawa suke hurda su,
  Duk wani tallafi da kuma koyarwan churches daga kasan turai ake kawo masu dauki,,
  Shigan couth baka da shirt din ciki, light blue, sai bakaken takalma, agogon shi na yau ta company Rolex, ce daure a hannun shi mai ruwan gold,
  Itama maman Choima watau kakan shi tana saye da wani farin lace mai duwatsu,
  Ejoma buje da riga ta sa  iya gwiwar ta wanda ke nuna cewa ita din har yanzu ba macen aure bace,
  Don in matar aure ce zata sa zani ko wani kayan da zai dan sauka mata har kasa kadan,.
   Samuel kanin shi yana tare da su alokacin shi a shigar wasu kayan maz masu tsada irin na samari,
   Bayan yan baya nai da sauran addu,oi, da aka gabatar a church din sai kawai wani sabon zance yazo
  Wani pastor mai wata katuwa far riga anmata alamar cross da jan kyale,
  Ga wani babban hula da yasa akan shi yana rataye da wani katon,chasbi, a quyan shi,
   Wanan pastor ganin shi yana nufin wani babban sako zai gabatar,
  Don haka sai kowa ya natsu don sauraron shi aji may za,a gabatar,
  Bayan gaisuwa da kuma nuna yabo gare su, sai ya fara mika sakon shi, akan cewa har yanzu mutanen su suna yawan sakaci a kasan nan,
  Don gashi har population din muslim ya nunka nasu kusan kashi saba,in da biyar,
  Wanan ya nuna cewa, za, nan gaba idan basuyi hankali ba kasan zai koma duk na musulumai zalla,
  Su diba suga ni daga cikin su wasu suna barin akidar kwarai ta YESU, Al, MASIHU, suna komawa cikin isalama,
  Daga can wani mai zakin murya cikin masu sauraron pastor ya amsa da fadin JESUS CRISIS,,,
   Pastor yace yes gaskiyane  wasun su suna barin wanan Christianity din suna komawa isalama,
  Don haka suyi kokari suga cewa duk wanda wani nashi ya koma cikin musulunci, sun bi duk hanyar da yadace su dawo dashi,
  Tunda musuluman da suke komawa gurin su basu iya tallafa masu gurin ganin sun ci gaba,
  Don haka da wanda ya koma da mawanda acikin isalama yake , kofa a bude take don basu gudun mawa wanda zai jawo hankalin su zuwa ga Christianity don ganin cewa takara ci gaba da bun kasa,
  Wata matashi mai wasu kaya blue ta amsa da babban murya tace HELLO ,LUYA,,,,
  Sauran ma suka amsa mata da makamancin abinda tace,
  Pastor yacigaba da fadin, akwai kasa,shen duniya da dama inda Christian suka kai yaran su mata don su musulunta su haihu, su
  Sai duk church din yadauki guna guni jin wanan maganar da pastor yayi cewa sun aura ma diyan su musulmai,
  Pastor yai yar gyaran murya don kowa ya samu natsuwa alokacin, do su fahince shi,
  Bayan kowa yana tsu sai yace su wa yan nan yara nasu bawai musuluntar gaskiya sukayi ba,
  Sunyi shine da wata manufa ta inda indan sun haifi yara dole yaran zasu dan kawo nasu akidar Christian acikin al,adun musulmai,
  HALLELUYA,,, inji wani katon arne yafadi hakana don jin fasan han da shugaban nin su sukayi,
  Guri ya rude da murna da tafi wasu harda buga gangan churching sukayi,
  Pastor yadan sa akayi shiru nan yace now,over to you, people's,
  Sai kowa yai shiru, sai yace yakamata duk wani mai saida sana,a wanda za,shigo dashi musanman a, Arewa cin Nigeria, to yakamata ya san abin yi aciki,
  Kamar su manja, lemon, gari, da sauran su,
  Dole su ma su san hanyar dazasubi su cutawa hausawa don suga cewa, an rage yawan musulumai
  Ko kuma su gurbata masu addinin su, sudinga hada abinda suka san cewa baida kyau musulmi yaci,
  Su zuba aciki don gurbata musulunci nan gaba ,
   Su tura yaran su aiki a gidajen musulmai don su gurbata tarbiyan diyan su,kanana, da cutar da mazajen su da shayar da su guba gaba dayan su,,,
  Wata daga cikin su tamike tana cewa Sir, akwai yan uwan mu sosai acan Arewan suna zama har mada christoci, hausawa mazauna arewa,
  Idan sun saye fa suma, acikin rashin sani,
 Yar murmushi yati yace dole ai akwai matakin da suka dauka kafin su aiwatar da hakan,
  Yace zasu sa gamai tsada ga mai araha dole kowa yasan hausawa da son banza,
  Mai arahn ce zasuyi ta siya subar mai tsadar, already dama wanan sakon yakai ga sauran yan uwa ko,
  Wani irin shewa suka sa tare da yin ihun jin dadi a lokaci guda,
 Sai rawa da waka yabiyo baya tare da jin dadi,
  Mai,karatu kamar yadda ki, kasan cewa Joseph bazaiji dadi wanan zance,ba, dole baza,a rasa wasu masu irin ra,ayin shi daga cikinvsu,
  Kasancewar irin girman da churching ke da shi da al,iman da yatara a cikin sa,
  Kawai sai ganin wani dan matashi sukayi mai kamar shekara ashirin ya hau, munbarin maganar church din,
  Jin microphone na son magana kowa yai shiru aka juya don ganin kowaye,
  Michael wanda atare da iyayen shi yazo church din wanda ko hwanan hawar dayayi saman munbarin basu san ya hau ba,sai,ganin shi kawai sukayi asama,,,
  Nan Michael yafara magana kamar haka, wai may yasa mu Christian kullun maganar mu akan muslim ne,
  Maya sa su, basu damu damu ba, sai mu zamu dinga damuwa da lamarin su,
 Shin hakan na nuna cewa sun fi mu power in religion ne kokuwa,
  Su ma ai yakamata su dinga kawo muna wani hari amma sai banga sunayi ba,
  Wurin yagauraye da surutu, alokaci guda kowa na fadar ra,yin shi,,
  Joseph yaiwa su mama nuni da su tashi su tafi maman,Choima a lokacin tana wani daga hannu an yi masu wa,azin kwarai yau,
  Ejoma wace ke lura da yanayi Joseph itace ta riga kowa sauein mikewa tabi bayan Joseph din,,,

  Sun dawo gida cikin gajiya saboda dadewar da sukayi yau a church din,
  Mutane na taganin cewa yau an masu magana mai anfani sosai, ta yadda zasu samu galaba akan musulumai,
  Mamaki zullumi,da jimamay duk sun cika zuciyar Joseph,
  May yasa musulumai basu irin wanan sukar akan su,
  Don may ko yaushe basu da zance sai ta yadda za,a halaka musulumai,
  Alhalin su musulmai basu da wanan lokacin duk da su ma suna da laifi don suna yawan nuna kyamar su gare su,
   Hannu bibiyu yasa ya tallabo habar shi dasu ya kurawa TV da ke aiki ido tankar mai kallon abinsa akeyi a cikin TV,,
  Ejoma wace ke tsaye akan shi tana fadamai cewa akawo mai abincin sa a nan ne,
   Saida tai da karfi tace broda, yai yar firgigit yai wani ajiyan zuciya mai yar sauti,
  Ejoma takara gabatar mai da abinci a karo na biyu,
  Yace mata zaidai sha fruit kawai idan ya tashi yanzu yana son fitane,
   Ejoma tai yar fuska tace mashi please broda kadan ci ko kadan kafin kafita,
   Yai yar murmushi ta karfin hali yace ai bance banci ba kinsan cewa nayi breakfast kafin mu fita dazu,
   Ta dan zuburo baki tana nuna bacin ran ta saboda rashin cin abincin shi ko yau she,,
  Mikewa yayi yace su tafi yaje yaci yawuce tana biyansa abaya tana cewa sai kai broda na,. 
   Yai murmushi don yana jin dafin kulawar da Ejoma ke gwadawa lafiyar shi akoda yaushe,
    A,daidai wanan lokacin wayar shi takara ana kiran shi,
  Ganin mai kiran shi yasa shi saurin daukar wayan kaunar shi Ruth ce ke kiran shi,
  Da sauri yadaga wayar yana mai fara zolayar ta amma sai yaji muryan ta tana kuka tana fada mai cewa mahaifin su ciwon shi yatashi na suga da hawan jini,
   Da sauri ya mike tsaye daga saman kujerar da yazauns don ya fara cin abinci,
   Mikewa yayu kamar wanda aka mintsina ya fada da karfi yace, yaushe
  May yasa ba,a fada mai ba sai yanzu, nan dai yai,ta fada akan rashi fada mai da ba,ayi ba sai yanzu yace mata zai shigo zuwa gobe,
   Daga haka ya mike baiko kara kallon gurin abincin ba, yana tafiya yana fadawa Ejoma,
    Haka kawai yaji wanan karon ciwon mahaifin nashi ya,taba mai zuciya, sosai fiye da koyaushe da a,ke bugo mai,

   Tunda safe yakama hanya zuciyar shi fam da fargaba tare da zullumi acikin ta don yadda yaji Ruth tana kuka a wayar
  Tafiya yakeyi amma hankalishi baya atare dashi sam ji yake tankar ya tashi sama da mota ahida Samuel ne acikin motar,
  Samuel wanda ke ganin irin gudun da yayan nashi keyi amma ya kasa magana a,ramshi dai yana addu,an Allah kai su lafiya,
  Sun kusa kawo wa kwantagora saboda irin gudun da yake shararawa a saman titin,
  Daidai wani kwana baiyi aune ba saiga wata motar irin ta kwasan shanui din nan, a wani kauye, ta debo shanaye zuwa wani kauye
Aiko nan suka jamay motar su Joseph tashi kusan kasar motar,,,,,
   
   Bude idon shi kawai yayi yagan shi a gadon asibiti kwance,
  Andaura mai ruwa a hannun damar shi,, ga yan nurse nan na,ta yawo akan shi,
   A hankali ya dan kara lunshe idon shi ya mayar dasu ya rufe
  Yana kokarin son ya tuna ko a ina yake haka, don yakasa gane ko may ke faruwa dashi, alokacin,
  Zubur ya so, mikewa sai,dai ya ji andafe shi da karfi,
  Samuel, kawai ya iya furtawa a lokacin muryan Samuel din yaji yana cewa broda iam here,with u,
  Daga haka ya lumshe idon shi bai kara sanin inda yake ba kuma,
  Kusan duk wanda ke gurin zugun suke,cikin mawuyacin halin damuwa,
   Daga KB har jibrin duk sun halarci gurin duk tatare su da yan uwan Joseph din keyi alokacin,
   Anty Dije tare da yaran ta da Maryam dake tare da kawar ta SAFIYA, wace tazo yi wa Maryam din yini,
  Anty Dije tace su shirya sutafi diban Joseph din a asibiti,
   Ba yadda maryam ta iya ,dole suka shiriya, don bin Anty asibitin kamar yadda ta umurce su,
  Amma afili cewa tayi wa anty haba ai gaida mara lafiya lada gare shi duk dadai ba musulmi bane shi din,
  Sanan kuma aiko don Assalam dole ne in tafi in dibo shi Anty,,,,
   Malam A,A masuga sukaiwa magana, yazo kai su,,
A, cikin shiga ta alfarma suke daga su har yaran don daka gansu kaga wayayyun yan birni, daga shigar su kawai zaka gane hakan,
  Leda tab da kayan fruit da kuma abinci a wani basket mai kyau, wanda aka dan lulube kulolin da ke ciki da wani kyale mai kyau,
   Shiko Mr Emanuel hankalinshi yai mugun tashi yadda yaga yaran gari hausawa suna tazuwa duban dan nashi mara lafiya,
  Bai,taba tsan manin cewa jama,ar da ake fadi yanadasu sun kai haka ba sai yanzu,
   Don haka tun da yaga Joseph din yadan samu lafiya yabukaci abashi, shi su koma gida adinga zuwa diba shi,,,
   Yayi hakane don ya rage yawan masu zuwa ganin shi kin san yadda yare suke da chanfi,
   Motar A,A masuga ta Parker a cikin haraban gidan Mr Ema din wanda yasha shuke ,shuken flowers masu kyau,
   Sai wani katon kare da suka gani daure da sarka, kaca, yana ganin su ya mike daga kwancen da yake yana wani gurnani, da haushi,
  Wa,iyazu,billahi inji Maryam,
  Cikin sauri maryam tayo baya inda anty take tana kokarin shige mata,
   A,A dake bayan su yai yar murmushi ya ce matsoraci, kada ki kada Anty pls,
   Amma jin maganae A,A din baisa ta rage shigewa jikin Antyn ba,
  Daidai kofar shiga falon gidan sukaga wani dan dattaijo zaune ya rike wata sanda mzi yar adon kamar kan mutum,
  Fuskan shi murtun kamar bai taba dariya ba arayuwar shi,
  Cikin ladabi suka gaishe shi har su Assalam yadda yaga su Anty sunyi haka shima yayi,
  Duk da shan tokan da Mr Ema yayi yana ganin ladabin su dole jikin shi yai la,asar,
  Duk da bai san ko suwaye ba,
  A,A ne ke fasa mai cewa sun zo gaida Joseph ne,
  Da hannu ya nuna masu kofar wani falo cikin hausar shi tayare mai nuna kasaita,
  Yace ku shiga yena ciki,
   Wani makeken falo ne agaban su A,A dake gaba yai yar sallama irin ta kafirai,
  Suma sukayi kamar yadda sukaji yayi, suna bin sa a baya, baya,
   Wata yar tsohuwa suka gani zaune a falon saman wani tafkekiyar kujera ta alfarma,mai kyau da laushi,, tare da wasu yan mata biyu sai wani dan karamin yaro da sukaji sunan shi wai Jacob,
   Yan matan suka amsa masu tare tare da nuna masu kujera su zauna,
   Nan suka gaida su cikin mutunci kamar yadda suma suka tare da mutunci,
   Maryam sai kallo takeyi tana dan yatsine fuska duk da gidan yai madu bazata
  Don kamar ba,acikin kwantagora suke ba, lokacin,
   Malam A,A yace madu munzo gaida Joseph ne ko yana ciki,
   Yar tsuhuwar nan taiwa yan matan wani yare, na IBO tana mai yamutse fuskan ta,
   Sai gudan mai wani dan guntun buje iya cinya tace yana barci pls,
   Maryam kallo guda tai masu takauda kanta gefe guda don takaici,
   Ejoma ce tace wa Ruth da yaren su haba kibari su shiga mana tunda har kikaga baba yabar su sun shigo,
   Ku shiga ciki ta nuna masu hanyar wani dan siririn corridor, tace yana ciki,
    Nan suka mike suka shiga inda aka nuna masu, yana gurin,
   A lokacin KB da Jibrin duk suna gurin shi atare da shi,
  Wani da ga cikin yan uwan Joseph mai hausa badarniya yace kutafi pls yana barci ne,
   Maryam ta bata fuska tare da hararan mutumin Ejoma wace ashe tana bayan su tace kabari su shiga baba yabarsu suka shigo
   Dan takawa sukayi suka isa inda yake kwance saman wani tafkeken gadon mai cin kusan mutun shidda,
   Idon shi a rufe kamar mai barci saidai ba barcin yakeyi ba,
   Yana jin duk abin da akeyi,
  Kafar shi da hannun shi suna daure da wani bandeji fari kal,
   Duk wa yanda ke gurin sunyi zugun ga wani a tsaye da alamar likitane,shi,
  Assalam naganin shi yace little mummy kamar Uncle Joe,
   A hankali ya bude idon shi don jin muryan Assalam da yayi,
  Kallon su yakeyi gaba dayan su da suka shigo dakin, alokacin,
   Dan murmushi ya kago a fuskanshi duk da zafin ciwon da yake ji,
  A hankali suke gaishe shi fuskan su fal da nuna tausayin sa,
  Shima dai da kyat yake karba masu, gaisuwar cikin nuna kulawar shi ,
   Yanabinsu daya bayan daya da kallo har idon shi ya sauka,akan maryam
  Irin kallon da yai mata yasa A,A dan juyawa don yaga ko itace yakewa wanan kallon,
  Saidai yaga Assalam rugumay a jikin Maryam din ,
   Wanda alama yanuna yaron yake kallo,


ZEEEE MAKAWA
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
    FUREN    JUJI
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
           2鈨�5鈨�

ZAINAB IDRIS MAKAWA


 A cikin cijewa da daurewa ya furta sunan Assalam a hankali,
  Yana mai kokarin yi mai alamar da ya karaso gurin shi,
   Malam A,A shida KB suka gane mai yake nufi da yaron,
  Suka ce Allah wai kazo inji uncle, cikin sauri Assalam yadan make hannun shi alamar bai zuwa, ya shige cikin jikin Maryam wace ke rike dashi tun shigowar su,
  Dariya kowa yasawa Assalam din  wanda ke gani kamar ba Joseph din daya sani, bane a kwance,
 Don ganin irin bandejin da akasa mai fari kal a hannu da kafa,
   脌nty Dije tace Assalam baka zuwa gurin uncle yau,
  Joseph dake kokarin nuna daurewar shi, da kuma cije bakin shi don ciwon da yake ji,
   Ganin irin wanan yanayin da yake ciki ne yasa maryam duk taji tausayin sa ya kamata a,ran,ta,
    Bata san lokacin da furta a hankali ba murya kasa,kasa, da Sannu ya jikin,
   Da, sauri Anty Dije har A, A, suka waiga ta don jin furucin ta yau akan Joseph wanda arayuwar ta taki jinin shi saboda baya sallah,
   A hankali cikin cije bakin sa yadan furta, a hankalo cikin dauri, Thank, 'God,
   "Nagode,
Yace cikin murya maiban tausayi, irin ta marasa lafiya
  Sai a lokacin jin dakin yayi tsit alokacin maryam ta dan tsargu, da cewa kila ita ake kallo,
  Da wutsiyar ido tadan kalli, gefen ta aiko ita dince malam A,A kewa kallon mamaki shida anty,
  Kata na a dan sunkuye a kasa ta ce a hankali safiya mudan fita daga waje har su fito,
  Tayi hakane don tafitar da wani abu azukatan su,a lokacin,
  Yin hakan ko yadan wanke ta ga A,A wanda zuciyar shi tadan rude duk da yasan cewa ba wanan ga Maryam
  Don ita yarince mai kishin addainin ta sosai,ba,ata taba hurda arne ba arayuwanta ko ta arziki ne,
  Daidai zasu fitane saiga Aisha da Amina cikin shiga irin ta wayayyun yan mata
  Dauke da wasu irn manyan ledoji a hannayen su,sai tako sukeyi guda, guda,
  Wani irin mugun kamshi duk ta gauraye gidan da maryam ke ta tsandar zama, tun shigowar su,
   Joseph yadan so yamike amma san yakasa cikin dauriya yace wa su maryam da safiya, nagode sai anjiman ku,
   Aisha tabi su da kallon mamaki don sam bata gane cewa maryam bace
  Ita a,zaton ta wasu yan matan shine can sukazo gaishe shi,
    Har ta fara masu kallon kunyi kuskure yan mata,
  Sai idon ta ya sauka akan Anty Dije wace ke zaune saman wani kujera dake facing din inda Joseph yake tana dauke da Issalam,
   Dan dariyar yake tayi don ganin tare da Anty wa yan nan zukazukan yan mata suke,
   Nan suka gaisa sama sama da,su suna mai kara tambayar ya jikin shi,
   Aisha don nuna kosawa da kuma waye wa sai zare dan gyalen da tayafo saman jikin ta tayi
  Tana kokarin zubawa Joseph abincin da suka shigo dashi,
  Shikuma daga kwance yai nuni da a,a yana kokarin nuna wanda su Anty Dije sukawo,
   Wani iri Aisha taji a lokacin, azuciyar ta tace ya kamata fa tai maganin wanan matar haka wace Joseph ke kulawa tankar yar uwar shi,
  Amma afili sai tai wani murmushi, Mr Ema yashigo yana fada cewa bai yarda kowa yakara kawo ma dan shi wani abu ba,
   Yanata fada da su Ejoma da Samuel har maman Choima,
   Joseph cikin karfin hali ya dan nuna Anty yace she, is my sister I always eat from her when I was in the town,
   Da mamaki Mr Ema ya waiga gurin Anty Dije don ganin matar da Joseph yace  itace mai bashi abinci,
   Kara cika mai ido tayi don sai yaji bai iya cimata mutunci akan yadda yake rufe idon shi yai wa wasu,
    Kamar zai yi magana sai kuma ya sa kai kawai yafita, yabar dakin,
   Sai a lokacin Assalam yadan rarafa zuwa gurin Joseph ya zauna gap da shi,
    Su maryam suna falo zaune ana kallon kallo tsakanin su da mama da Ruth,
  Ejoma ce tafi tadanzo inda suke zaune cikin matsuwar su Anty su fito subar wanan gidan maikama da kurkuku,
   Jin takon su fitowa yasa saurin mikewa don shirin tafiya,
    脌nty tace bazaku shiga kuyi sallama dashi ba,
  Kai maryam ta kada mata alamar aa,
   Sun danbar gidan maryam tai yar siririyar ajiyar zuciya mai nuna wani alama,
 Sai a lokacin A,A yace gaskiya ya na jin jikin sa sosai karfin haline kawai,
   Anty tace ai ga yadda ake fafi ba,a sa rai cewa sun fita daga cikin motar,
   Maryam da sai yanzu tai magana tace da yamutu a kafiri kenan,
  Kai, kai inji anty Dije wacce sam bata son wanan halin na maryam akan wanan mutumin watau, Joseph,

   Dalilin wanan accident din na Joseph aka dage bukin KB
  Wanda shi KB din da kan shi ya bidi alfatman cewa yana son adan daga bukin don wasu bukatu nashi,
  Shiko yana ganin cewa hakan baidace ba ace yana bukin shi ga Joseph a kwance ba lafiya wanan ne dalilin daga bukin da yayi,
   Sannu, sannu akwana atashi Allah yaba Joseph sauki,
  Tun yana dan iya fita kofar gidan su har yadan fara bin abokai suna kaishi yawo cikin gari,
   Yau ma kamar kullun dayake damana ya sauka akasa ruwan sama yafara samuwa,
  Hadari aka hada sosai ko ina a gari yayi jajir da alamar akwai iska atafe da wanan hadarin
  A lokacin Joseph yana tare da yaya illiya  hira wanan hadarin yataso,
  Sanin cewa bawai, kafar mai lafiya gare shi ba sosai a lokacin
  Hakan yasa shi barin har iskan yadan rage ko agama ruwa,
  Iska sosai akayi sai dan yayafin da ya biyo bayan hadarin wanda ba wani ruwa mai yawa akayi ba
   Suna fita waje sukaga yadda iska yaiwa mutane barna sosai agari,
  Yaya illiya na cewa subbahanallah shi kuma Joseph cikin kidimay wa yace, Allahu Akbar,
  Da sauri yaya ya kallo shi da wani irin mamaki, don ji yayi kamar ba shi bane yace hakana,
  Sai kuma Jesus crisi muna ciki haka akai wanan iska haka,
  Bayan sunyi sallama da yaya illiya, ya kama hanya zuwa gida,
  A hankali yake tafiya zuwa gida, a lokacin saboda yana dan lalaba kafar shi ne,
 Kusan zuwa unguwar su yaga gidan wani malami da ake cewa,,MUSA, JA, don mutumin fari ne sol, da shi,
  Yasan shi tun yana yaro yakuma san gidan shi a cikin uguwar tasu,
   Gidan yaga ni duk katagar gidan azube duk mai wucewa yana ganin shi,
   Malam musa ja Joseph yagani yayi tagu a saman dakalin kofar gidan shi,
  Ga matan shi duk mai wuce wa yana gani sai kuma wani makwabcin malam musa ja,
  Shima gidan shi tsohon gina ne sosai don duk haka su ka taso suka ga ginan har yanzu suna dan maneji da abin su,
   Har yai kamar ya wuce sai kawai yaji bazai iya ba don  haka ya yo ribas baya da motar shi,
  Cikin dan dangyasawa ya isa ida mutanen suke tsaye cirko cirko
  Ya ce malam yau kuma abinda yafaru ke nan Allah ya sauwaka,
   Sukayi mai godiya kula masu da yayi ya juya yana mai jumamay abin
   Abin na malam musa da makwabcin shi yafi yawa,
  Don su ga zubewar gatanga ga kwanon ginan ya hankade ya kware sama,
   Sun dade da mahaifin shi a waje suna maganar wanan irin iskan da tazo wa mutane yau,
   Nan Joseph ya ba mahaifin shi labarin makwabtan su, abinda iskan yai masu,
   Yayi tsan manin zai ji yace masu koda sorry ne sai kawai yaga ya yi murmushi,
   Shiko Joseph duk tausayi su malam musa ja ya kamashi da wanan tunanen ya kwanta,
  Saidai sam barci yaki daukar shi saigani irin halin da yaga su malam musa da makwabcin shi aciki yakeyi,
  Wayar shi ya lalubo, nobar Hamza yakira,don su KB da,Jibrin ba su gari,
   Nan yai mai irin bayanin abin da yake so yai mai tunda safe saboda yanzu dare yayi ko,
  Waahe gari hamza ne tare da wasu magina sukayi wa Musa,ja, sallama
  Hamza yai masu bayanin cewa wani bawan Allah ne ya ruro shi a gyara masu gida amma yace kada a fadi sunan shi,
  Gyara sosai akayi don dakuna hudu akaja wa musa ja, shima makwabcin shi am mai daidai irin da ya rushe,
   Aikin cikin yan kwanaki aka gama komai kamar yadda yaso,
    Kafin agama aikin Joseph yasamu kira na gagawa yabar gari, zuwa diban depot din su da gwaunati ta bude
   Ya koma da kwana biyu saiga su malam musa,ja sun samu labarin cewa, ashe Joseph ne ya taimaka masu daga wurin wani ma,aikatan ginan da sukai masu,
    Aiko Mr Emanuel maimakon yai murna saiko ya hau masifa dasu ta inda yake shiga bata nan yake fita ba,
  Harda cewa wai hausawa sun yi wa dan shi charming,
  In ba hakaba ba ai yu,yu yadinga madu wanan dawainiyar ba haka,
   Anan mutanen gari suka san cewa Mr Ema baison irin taimakon da Joseph kewa mutane daga cikin dukiyar shi,
  Kowa ya shiga fadin albarkacin bakin shi, akan Joseph, din,
   Joseph yasha fada mai tsanani sosai gurin mahaifin shi akan irin taimakon da yakewa hausawa
  Karshe yai warning din shi kwarai da gaske akan in har yakarajin haka zai dauki mai mataki mai tsanani,
   Bayan sun gama wqyan Joseph din yai yar ajiyar zuciya yana madaga wayan nashi yabishi da kallo
  Kamar wayan ce taimai magana hakanan har ta bata mai rai,
 
    Y脿u ta kasance ranan litani,itace ranan da ko bature na tsoran ta,
   Cikin sauri Maryam ke komai don gudun makara,
  Sai,dai duk saurinta, yau din ta dan makara,
  Tun,da ga bakin gate ta hango malam A,A shima kusan a lokacin, yake shigowa, school din,
    Daurewa tayi kamar bata gan shi saboda yawan jama,a dake gurin,
  Yana gama parking yai kokatin kiranta da waya sam maryam bataso haka ba,
  Saboda bata son mutane sugane cewa akwai alakar, soyayya a tsakinin su dashi,
   Daidai lokacin da yakaro inda take tsaue tana jiran isowar shi,
  Da murmushi fam a fuskan shi ya karaso gurin ta,
   Yadan dubi agogon hannun shi yace yau dai  babu saurin shigewa ajivda guri don gadhi kusan tare muka iso yau din,
 Maryam tai yar murmushi tana, dan kauda kanta gefe cikin kunyan shi da takeyi kamar kullun,
  Ta ce aiko yau saboda nadan bata lokacine har na makara da bazaka gan ni ba sai tashi,
    Yai yar mushin jin muryan ta cikin dadi, yace, tau yaudai karfe nawa zaki fito,
  Tace mai sai biyar,
Yai murmushi yace to saboda zan zo in dauke ki muje gaida hajiya ta da tazo,
 Gaban maryam ne yafadi don jin abin da malam din yace,
   Duban shi tayi da mamaki tace a hankali haba malam kaga haka zai yi ace ban ko fada a,gida ba zan tafi gaida mama,
   Maryam ke nan may ye aciki don kn tafi daga nan ko haka
  Ina iyaka dai ku,gaisa da ira, kawai ko,
  Gaskiya bazan je ba sai na fadawa Anty tukun duk abin da tace shike na,
  Daga haka tajuya tai cikin makaranta abinta, shiko binta yayi da kalo cike da mamaki irin halin maryam,
   Har suka tashi daga school bata kara jin motsin A,A ba
  Abinda yasa ke nan tagane cewa yayi fushi ne da ita rashin yarda da maganar shi don zuwa gai,da mahaifiyar shi da tazo daga Abuja,,
  Koda ta dawo bata boyewa Anty komai ba ta fada mata yadda sukayi da ,A,A din
  Anty tace kin kyauta Maryam shi yasa har kullun nake alfahari da ke wallahi, na kasan cewa yarinya mai la,dabi da biyayya dakuma sanin ya kamata
  Amma tunda har ya roka sai yazo ta nan gida yadauke ki ku tafi yafi mutunci,,
 Don yafi ace kin bishi daga can sam babu mutunci a hakan ,
  Kiranshi tayi cikin lalashi tai,maganar kamar haka,
Malam munyuni lafiya, sai kawai naji shiru ina ta jiranka tun da zu,
 Uhummm kawai yace kin gama jamin aji ko maryam,
  Don kinga banda yadda zanyi da kaina ko amma babu komai
  Anty ta yarda ki tafi ko tadan marairaice muryanta tace eh ta yarda,
 Ok  yace sai ki shirya kafin inzo, don muje mudawo da guri,
  Zani da riga tadaura sai  hijab da tasa wanda yai dan shige da kayan jikin ta,
   Turaren ta shafe jikinta dashi na black oud, na mata, takalmin ta flat shoes tadan sa,
  Ba bata lokaci A,A din ya iso saidai ya ganta da Issalam yai yar murmushi don yasan hakan wani hikima ne na manya,
   Gidan gaskiya yakai gida don dagani kasan cewa, akwai wadata a gidan,
  Wani katon falo ne suka dosa, maryam tana rike da hannun Issalam,
  A,A ne gaba suna bin,shi baya da sallamar shi ya shiga gidan,
     Wasu matane zaune su biyu saman wasu laulausar kujeru ga carpet amalala akasan irin ta masarautar nan,
  Hira matan biyu keyi, alokacin amma una sallama sai an,nurin dayar wace itace fara, yadushe,
  Nan da n ta bata rai kamar batai farin ciki da ganin su ba,
  Maryam gabanta yafadi duk bawai sanin ta tqyi ba
  Amma bataga farin ciki ba ga fuskokin su,
  Kasa maryam ta zube tana mai gaishe su cikin ladabi,
  Kanta na kasa tana rike da hannun Issalam tankar za,a kwace mata ita,
  Shima dai gaishesu yayi a cikin ladabi, ,yakuma ji dadin yadda maryam din tai wa mahaiyar tashi,
  Dayar matan mai fari da kiban jiki, wace da ka ganta kasan yar Royal family ce,
   Tace ka kaita gurin su ,Assy, su gaisai sai kadawo,
  Dakin ya nuna mata saboda shi baya shiga,dakin kan,nennashi
  Saidai maryam dn nadhiga sai taga dakin babu kowa don haka sai tayo baya daniyar komawa falon ,
  Muryam matar taji cikin fada tana cewa
  May kake nufi da kawo min wqnan bakauyar yarinyar Dan mama,
  Cikin murya mai taushi yace ita nake son in aura mama,
  Abinda maryam taji yakusa sata sakin fitsari alokacin
   Amma sai ta daure ta fara,addua daga bakinta,har cikin ranta,
    Kafita idona wallahi na fada maka nariga nama mata ba yau ba
  Da akwai abinda nake jira shiyasa ban ta da zancen ba shi ne don baka da kunyazakaje kadauko min wanan yariyar wai matar da zaka aura,
   To tun wuri ka ba kanka shawara tun ba,a jimu ba,in ba hakaba zan bata maka rai sosai wanan karon,
  Daga haka maryam tafito daga inda take tsaye tun farin maganar su,
   Firgit ya waiga don yaga ko taji zancen mahaifitar tashi,
  Amma sai yaga fuskan ta da yar fara,atana cewa zan koma mama sai anjimar ku nagode cikin halinta na alkun ya,
 Hararan ta uwar tayi da wani irin yanayi na bayabo ba fallasa,
  Sai dayar matace ma tace to ku gaida gida mun gode ko,
  Ko a mota sam maryam bata nunawa A,A cewa taji zancen shi da mahaifiyar shi bba
   Ba karamin kokari maryam tayi ba wuri control din mind din ta,don ko anty  takasa fadawa wanan zancen,ba, aranta tabarshi,
    Dasauri tagama abinda takeyi aranan tashiga daniyar ta kwanta ko zata danji sanyi aran,ta,
  Sai taji yanzu maganar ta dawo mata sabo,
  Batasan lokacin da hawaye masu zafi suka fara gan garo mata ba,
  Jin hannu tayi an dafa mata kafadar ta, ko bata waigaba tasan ce wa Anty Dije ce,
  Wani sabon kuka tasake cikin tashin hankali, ita ma antyn kukan takeyi,
  Saida sukayi mai isar su suka bari don kan su,
  Nan maryam ta kwashe abin da taji mahafiyar ,A,A nafadi tafada mata,
  Shawaran da Anty Dije tabata shi ne tabari suga matakin da A,A, din zai dauka,,,,,,,

ZEEE  MAKAWA
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
    FUREN     JUJI
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
            2鈨�6鈨�

ZAINAB IDRIS MAKAWA,,

Assalamu Alaikum yan uwa musulmai kutayani yiwa Anty na Anty NAFISA ALIYU HARZAMI,,Addu,an, samun sauki,,cikin dan lokaci,
 

    Rayuwa yau da kullun batabar komai a sannu a hankali maryam ta fara walwale wa, daga damuwar da tashiga,
  Saidai shawaran anty yai mata amfani, sosai don har yau A,A Masuga, bai nuna mata komai,
  Sai kara nuna mata kulawa da ya,shiga yi fiye da, farko,,,,,
    Wanan dalilin yasa ta manta zancen mahaifiyar shi a rayuwar ta ,
  Don dai tasan cewa bada ita zata zauna ba da shi ne,
  Shikuma bai nuna mata gazawan shi ba akanta kullun kara son ta yake ji saboda irin kyawawan halaiyar

   Akwana atashi hasarar mai rai, saiga lokacin bukin KB yazo,
  Don haka suka fara zama busy da aiyukan buki duk a gidan su KB din ake sha,anin to amma angwanai suna,zamane a falon yaya illiya dake fuskantar baban titin cikin garin,
   Wanan bukin yadan sa maryam dan sakin jikin ta da su KB
  Don duk wani abin bukata, dasuke so maryam ce zasu kira saboda abokan su da suka,zo daga nisa,
   Matar malam suke cewa maryam inda itako abin na mata dadi arai,sosai,
   Ilimi, arziki, kyau, wayewa, wani abune, wanda baiwa ce daga Allah,
  Shike ba duk wanda yaso ako wani lokaci, ko yanayi,
  Wai duk taron nan na buki KB da matasa masu jin kan zu keyi,
  Zuwan Joseph a cikin su duk sai ya dakushe sauran, kamar ba,ayi da farko,
  Yana isowa buki ya canza sallo, nan take komai aka fara yin shi acikin morewa rayuwa, dakuma wada ta,
   Baki sun zo daga nesa saboda wanan bukin na KB wasu daga ban garen sanar shi ta Gas
  Wasu kuma abokaine da aka hadu ta wani sha,ani, aka zama daya,
   Maryam ta kira safiya don ta taimaka masu da aiki, tare da,wasu makwabtan su yan mata, biyu, sai kan,nen mijin Anty Dije su uku,
  Shanu Joseph yasa,aka yan ka anan bangaren ango, da suke ,
  Yasa Anty Dije tayo hanyan yan kwatakwali togo, masu aikin girkin abinci,
   Nan da,dan guri ya kici may da taron hayaniya, ga raguna uku da yasa a gyaro akawo duk wurin anty inda yace anan za ai masu nadu girke,girken,
  Saboda bazai kai gidan su ba don mutane wasu baza su ci ba idan ance acan akayi,
   Duk wanan aiyukan da mutanen da akadauko sukeyi bai hana maryam da kawayen ta zakewa ayi shi da su ba hurjanjan suke aikin su tsakani da Allah,
  Abincin da akafitawa baki da shi a wani guests house, bai ko isa ba saboda irin haduwar da abincin yayi,
   Hakan yaba Joseph da jibrin dadinkar kayan hada hadadaen abinci, don kara yawan shi,
   Suna tsaye a filin tsakar gidan Anty shi da jibrin cikin shigar kananin kaya masu tsada,
   Dagani basai an fadama irin haduwar su,ba,
   Jibrin yace gaskiya anty kin muna abinda ma bamu zata ba zokiji yadda bakin mu ke santin abubuwan da aka kawo masu,
   Anty Dije ta nuna masu maryam da su safiya tace kun ga wa, yanda sukai maku can, don ni har fada naso yi da su da farko,
   Kallon inda su Maryam suke sukayi gaba dayan su, alokacin suna kokarin yi masu tuwon dare,
 Jibrin ne ya tako har gurin su,yakaraso yana ce masu sannu ku fa, yan mata, da kokari,
   Suka amsa mai kowace tana kokarin nuna kanta gareshi,
   In ka dauke maryam da kawarta dasuke can ta cikin kicin suna hada perpepsoup, din kayan cikin rago,
   Ga mamakin maryam sai kawai ganin jibrin din tayi har cikin kitchen inda suke ya biyo su,
  Yana ma safiya wace ke kokarin hada jajage a tukunya,
  Wani irin kallo wanda ke da ma,ana ga wanda akeyiwa,
   Haba Maryam baki bari ta huta hakanan sai ki dinga bata wahala,
   Maryam da mamaki take kallon jibrin din yau wanda zata iya cewa bai ma san sunan taba sam,
  Don basu maganar komi a tsakanin su sai gaisuwa,
  Saigashi yau yakira sunan ta harda ba,a yake mata, akan wata,
   Maryam da ta gane nufin shi sai ta ce mai ya jibrin ko ka manta a kitchen kake yau,
  Yadan waiga cikin nuna ko oho yace an, hana maza shiga kitchen ne,
  Dariyan da maryam ta kumshe saida ta fasa,shi a fili,
   So sai take kyalkyallan dariya har dan diplo din ta na lutsawa fararen hakoranta da ke boye ko yaushe yau su,ka haska, a fili,
  Ba jibrin dake kusa ba har Anty da Joseph dake ta waje saida hankalin su yakai garesu,
  Suna mamakin may jibrin ya cewa maryam haka yau take wanan dariyar,
   Basuyi aune ba saiganin jibrin sukayi ya karbi cibin miyar hannun Safiya yana motsa miyar duk gidan kallo yadawo gare shi,
  Ba fatima ba harda Joseph saida ya murmusa yau,
  Da sauri yafito yana yarfar da hannun shi wai zafi dan ruwa zafi ya dan tsirgo mai a hannun shi,
  Dariya aka karasa mai ba shiri ya jawo handcarchef din shi yana goge hannu da zufa,
   Hmmm kawai,, Joseph yace daga karshe don ganin irin tabar da jibrin ke yi,
   Har ya kai gap da fita waje ya waigo cikin irin tafiyar nan tashi yace, ,
  Meet, me outside pls,
 Jibrin har ya fara tafiya sai kuma yadan waigo ya kalli inda maryam take tsaye yace,
  Kauna ta zan gan ki in ,nadawo, pls,
  Aiki sosai suka sha ranan nan, ana gobe daurin aure suka shirya wani irin gagarumin friend's day, wanda abokai da yan,uwa za,su,halarci wanan bukin,
   Maryam dai dama bawai ta na zuwa irin wanan bidi,ar bane don haka sam bata sa rai cewa zata,ba,
  Amma sai ga anty tashigo da,wasu din kunan wasu indian materials masu kyau da daukan ido guda biyu,
   Ita da safiya saidai kowace da kalar nata, dinki daine iri daya, sak,
   Sunji dadin wanan kayan sosai sai dai da anty ta,bukaci zuwa gurin bukin duk suka,bata fuska
   Jibrin ne shigo dai dai lokacin, yace yauwa Maryam wallahi ina ta sauri don inzo in samay ki,
   Don ban da nobar wayan ki da na kiraki tun can in fada ma,ki,
  Gefe dan je da ita, inda ba mai jin su, yace yauwa, Maryam dan Allah magana zan yi da ke a kan kawar ki,
   Maryam tace wata ciki, yace haba kindai gane mana, wanan da kuke tare koda yaushe,
  Wallahi tun ranan da na fara ganin ta naji ina mutuwar son ta, sosai,
  Don Allah maryam ki taimaka min kada son ta, kawar ki ya kashe maki yaya maryam,
   Maryam tace, a,a a, gaskiya ba ruwa na kasan halin yan matan ku kada,su samin kawa a gaba,
   Ke maryam ban don sheri ni kin taba, gani na da wata, wai budurwa,
    Kai ya jibrin wa,yan nan yan gayun yan matan naku da suke biyo ku har gida,
   Wa,wai su Aisha ai ni wa yan,nan ko kallin arziki badu isheni, ba balle,
   Wallah kasan koni kaina har gobe zargina sukeyi don wani kallo, naga suna min,
   Kai maryam, idan sukai mata wanan kallon wallahi, sai naci uban su su dukka,
   Da mamaki jin yadada ya ke kalamsi akan safiyar ta,
   To ya jibrin Safiya fa ba, irin yan matan ku ba ne don ba wata yar gaye bace,
  Kaga bazaku dace ba, don kun fi karfin ta gaskiya kabari tasamu,dai,dai ita,
   Kai maryam don Allah kada wanan yadamay ki, ai ninr zan haskata sannu a hankali ko,
  Wallahi auren ta nake son yi kuma bawai ina son abin yai wani dadewa bane,
   Amma yanzu ki, fara hada mu, insamu in kafa kaina agurin ta,
  Sanan , don Allah, ko anty kada kibari taji mubar abina tsakanin mu, har ya zama gaskiya,
    Shiru maryam tayi tana  dan nazarin maganar, shi ,ko gaskiya yake fafi ko kuma yaudara ne,
   Can tace shike nan ya jibrin, tunda kace haka yanzu yakake son ayi?
   Yauwa maryam kinga, indan zamu tafi gurin friends day,
   Sai kiyi kokari ki hadamu a mota guda dag nan zan fara kafa kaina gareta,
   Bayan rabuwan su sai maryam taji abin yai mata dadi, saidai tana zullumi kada yazo ya yaudare ta daga baya don su gogagun ne sai manyan yan mata,
    Maryam wai may kike yi ne tundazu baki gyara guri,ba balle ki shirya ba,ga,kina da alamar zuwa ba fa,
Anty ina magana ne da yaya jibrin dama yanzu nake son in hada
   Ta waiga inda Safiya take tana dan gyaran dakin da suka bata, da tarkace dazu da suka taru,
   Tace ma safiya barin dawo musa labule dake safiya, akwai alheri tafe insha Allah,
    Safiya ta kama kallon ta, kawai don bata san ko may maryam din zata fada mata ba,
  Saida suka gama duk abinda sukeyi acan cikin dakin maryam suna shirin tafiya don har anty ta shirya yara ko,
   Safiya ce ta kasa hakkuri ta ce maryam wai may ye kika ce zaki fada min dazu,
   Hannunta maryam tadan riko kadan, ta dan kura mata ido na wani dan lokaci,
  Sai kuma tai shiru, tace wallahi har na rasa ko ta ina zan fara zancen,
    Ikon Allah inji safiya, wace itama maryam din take kallo,
    Fada min don Allah kin sani, cikin duhu wallahi,
   Maryam tadan nisa sai kuma tace wallahi safiya,duk ma na shiga rudani wallahi,
  Dama wanan ya jibrin din ne yace in fada maki wai yana son ki kuma waida aure,,
   Kai haba maryam don Allah ki daina wanan zance ina,ni ina wayan nan mutane
   Aina fada mai haka safiya amma sai yace min shi wallahi da aure yake son ki,
   Hmm maryam amma kin san cewa mu gidan mu talkawane lis,don bamu da komai,
  Don haka ba,an sa kaina cikin wahala ba wallahi,
  Inda dai talaka ne iri na ba zan ce maki no ba ,
  Kai safiya wayasan gobe ban da Allah, balle har ki saurin yankewa kanki hukunci haka,
   Ni shawaran da zan baki yanzu shine tun da har shi ya nuna yana sonki to
  Sai ki gwada sa,arki mugani ko Allah zai sa shine mijin naki,
  Iyaka dai ki kara kama kan ki sosai dashi kin san su sun saba da rayuwar, wayewa,
    Maganganun maryam sun sa safiya tadan yi sanyi ,don gaskiya tafada mata,
  San ai aure yin Allah ne bawai zabin mutum bane, sai in Allah dama ya nufa,
   Maryam ta mike adaidai lokacin da tajawo kayan da zasu sa agaban tace,
  Kada ki cuci kanki safiya don nima kinga lokacin haka, nayi amma sai nazo na fadawa Anty,
  Don alokacin ina ganin cewa  ga yan mata nan wayayyu a cikin FCE amma zai buge da cewa, yana sona sai kawai nadauka yaudarata zaiyi kawai,
  Ashe abin ba haka bane,,hadine daga Allah,
   Marya tamike tsaye tana kokarin walwale kayan don su diba dinkin tace,
   Tace don Allah safiya ki daure yau ku dan gana dashi, don muji ta bakin shi
   Kinfa yace min ma wai shi zai tafi dake gurin hall din ajima,
   Kinga ko inda bada gaske yakeyi ba da aibazai yi kokarin nuwa duniya ke ba,
   Dan siririn ajiyar zuciya, safiya ta sake tace maryam bawai ban son hakan ya kasance bane,
  Ina dai gudun abinda zai jawo min fitina ne kin san halin da mahaifiyata take ciki kada in dauko mata magana,
   Amma ba komai tunda naga kin yarda dashi don nasan cewa bazaki kaini mugun wuri ba,
     Wayar maryam ne yai kara,a,lokacini ko bata dauka ba tasan cewa A,A din tane akan layin,
    Cikin kashe murya ta dauki wayan nan yake sheda mata cewa tajirashi zai zo ya kai su gurin bukin,
  Duk da dai bata gaiyyace shi ba tun farko,
  Maryam tadan kara kwantar da muryan ta tace malam nasan cewa baka wani hurda da sune shi yasa ban fada ma ba,
  Yai yar dariya, yace wallahi jibrin ne ya fadamin dazu da muka hadu gidan mai dashi,
   So ki bani nan da minti ashirin zan iso, insha Allah,
   Kayan da su maryam suka sa yai bala,in fitar dasu sosai,
   Saboda  bawai samun irin materials din akeyi ba akon,ina don haka sai yazama wani abin kallo, ga jama,a,
   Tsab suka fito gaba dayan su a lokacin, Safiya sai faman koda shigar maryam takeyi ita ma maryam din hakane,
    Jibrin yazo har ciki da kan shi yana fadawa maryam cewa tafadawa safiya yana waje yana jiran ta,
    A,Daidai lokacin A,A ya iso don tafiya dasu kamar yadda yace zaizo yakai su,
   A,lokacin  wani kanin mijin anty Dije ya zo don yakai su
   Sai ya tar da za a kaisu amma Anty dije sai tace ya tsaya ya kai ta ita,
  A hankali suka fito saida ga motoci nan gurin zakace ko a gidan ne ake bukin,
    Har bakin motar jibrin Maryam ta raka sadiya tadawo,
   Ta bude motar A,A, tashiga
  A,A din yadan waiga yakalli inda maryam take yace,
  Ina ita safiya din, kuma,?
  Tana can a motar jibrin tare zasu,
 Tafada a takaice,
Wani irin kallo A,A din yai ma ma maryam.
     Yace kina da hankali kuwa, yarinya tazo maki buki sai ki bari tabi wani kato,
  Maganar yaba Maryam mamaki, tace jibrin fa nace ma malam,
   Yai yar tsuki Mtsss, maryam ban zaci har zaki amince da safiya ta bi wa yan nan da kowa yasan yan duniyar yarane, ne ba,
    Yaran da duk gari ankasa gane sanar su har zuwa yanzu
   Tunda yafara magana maryam kallon shi kawai, takeyi
  Tace haba malam nafada ma cewa ba abin,in da zai samu safiyan,
 Ya dan daga mata hannu yanu nna mata alamar ya isa hakanan,
Har suka kai gurin bai kara mata magana ba,
  Gurin yacika fam da jama,a lokacin har, kujeru sundan kare daga ciki,
 Wasu ne sukazo suka yiwa su maryam kwantace da wasu kujeru a can gaba,
   A kusa dasu taga harda su anty dije suna nan gab dasu,
  Basu wani dade ba akafara program din inda aka r da Amarya da ango,
   Kujerun wasu yan mata dake dan nesa dasu kadan,
  Taga ana dan nuno su a hankali bada wani jimawa ba taga A,A ya mike zuwa wajen yan matan,,,,

ZEEEE.  MAKAWA,,,
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
    FUREN     JUJI
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
           2鈨�7鈨�

ZAINAB  IDRIS  MAKAWA

  Jinjina gare tare da fatan alheri ko yaushe Anty Nafisat, Aliyu Harzami, UmmuFadleeh safeenat Abuja, Mamam farida,Maman Walid, Maijidda Harzami, Mariya SB, Jamila  Sifiyanu,Anty na hafsat Yusuf, da members din Zeee makawa novel, da members na takari novel Ina maku fatan alheri dacewa da Rahaman ubangijin mu, da kuma gamawa da duniya lafiya,
  JUMM,AT, MUBBARAK馃憦馃憦馃憦馃憦馃憦馃憦馃憦馃憦


Zaune take daga inda A,A yabar ta ko zataga dawo wan shi sai kawai taga tun yana yar kus,kus,da wanan matar da taga yaje gurin ta har sun kwasa sun fita,
   Shigowan Joseph tare da,Aisha yasa ta dan daina kallon hanyar dataga A,A din ya bi, yafita,
  Joseph da Aisha tare da Amina sun shigo cikin wani irin shiga ta alfarma,
 Don dai ko makiyin su dole ya yaba ma shifagar su,
  Aisha ba kunya tana make da Joseph gam saboda ta bushe fitilar ta bata kunya kowa agari,
   Yan wasan gidan mai Jauje na kwantagora sun fito sun yi wasa,
  Sai wani mawaki makwabcin garin kwantara daga KB state garin Yauri Sani Aiyu dan Dawo shima yafito yai nashi wasan
  Nan masoyan Joseph da bakin su suka dinga barin kudi ga mawaka,
  Daga karshe aka dan yi traditional show na yaren da ke cikin kwantagora,
  Toran kawa, kambari, Dukkawa, Dakarkari, pure hausawa, da sauran su,
  Wayan Maryam wace takai iya wuya, yai yar tsuwa, alamar sako ya shigo mata,
  Budewa tayi sako tagani kamar h脿ka Ki, yi hakkuri pls Maryam, bazan samu mayar, da ke, gida ba ,
  Ku komatare da Anty pls,
  Abinda aka rubuta ke nan a sakon , atake maryam ta fahinci, sakon daga, A,A masugane,
   Wani iri maryam taji a ran ta, maganar da ya fado mata arai shine, muryan mahaifiyar A,A alokacin da suka je gaida ita,
    Daga haka tamike tsaye daga inda take zaune,
  Tafiya takama yi cikin tashin hankali take dan takawa,
  Sai muryan Safiya taji a gaban ta tana cewa, banga motar A,A ba a waje maryam,
   Dan ajiyar zuciya tayi don ta riga tayi nisa gurin tunane ,
  Tafe suke a motar jibrin sai hiran wasan nin da akayi akeyi amma ita sam hankalin ta bai tare da ita,
   Abinda zuciyar ta ke tambayar ta shine wacece wanan da A A yaje gurin ta,
  Har tasa shi fita hall din taron yakuma iya wucewa ya bar maryam din, a gurin,,,
 Har suka isa gida ,hankali maryam atashe yake  gashi suna da  aiki so sai don gobe daurin aure su zasuyi abincin  reception,
    Jiki ba kwari ba ku,zari haka ta, daure, tayi aikin cikin bacin rai tun bata walwala har ta dan sake jikin ta don taga amfara tambayar ta komay ya,samay ta,
   Shiko A,A tun fitar su waje da kaunar maman, da suka hadu agurin bukin,
  Sun kwashi lokaci da ina yana kokarin fahintar da ita akan maryam din,
  Amma sam laminde taki fahintar shi sai ma kokarin kiran mahaifiyar shi takeyi ta sheda mata cewa bai rabu da yarinyar ba, ashe,
   Hakan yasa yabar gurin cikin bacin rai batare da ya tsaya fada wa maryam zai wuce ba,
  Safiya wace tun dawowan su jiya gurin friends day,
   Ta fuskan  kawar ta,na cikin damuwa, amma batason agane,
  Itakuma bawai sun samu lokacin kebewa da ita ba ce,
  Saboda haka yau da suka gama sa abinci a cikin take aways suka gyara inda sukayi aiki,
  Sai sukayo wanka kafin a tafi daurin aure, don da andawo guri zai cikia ne, da jama,a,
  Bayan sunan da shirya suna zaune su biyu a dakin maryam,
  Safiya ta dan kali maryam wace tadan kurawa wani kwali ido kamar mai karatu,
   Amma kallo daya zakai mata ka fahici ba wi kwalin take kallo ba a zahiri,
   Tadan jima tana kallon maryam ahakanan tare da tunanen may ke faruwa da maryam din hakana wai,
   Daga jiya zuwa yau ?
Ganin bazata daina wanan tunanen ba yasa safiya dan taba maryam, din wacce tai furgigit, cikin dan firgita,
   Firgigit tayi alaman dawowa daga hayacin ta, sai yar ajiyar zuciya da take sakewa,
   Wanda hakan yakara sa safiya kara kallon ta da kyau, ta ko hango tashin hankali a tare da maryam din,
  Safiya tadan marairaice muryan ta tace maryam, wai make damun ki ne tun jiya fa na fanci kina cikin wani yanayi,
   Kallon safiya maryam tayi kamar kartai magana saidai kuma tace,
  Bari safiya ina cikin damuwa, tun jiya wallahi, jiya bayan zuwan mu gurin taron nan,
   Sai A,A yaga table din wasu mata da alamar yan uwan shine safiya,
   Yace min yana zuwa yatafi gurin su, sundade suna magana dashi sai suka batmr holl din gaba dayan su har shi,
  Ban kara ganin shi ba,sai text da yayo min cewa wai in bi Anty zuwa gida bai,samun dawowa kaini gida,
   Shine har zuwa yau din bai kirani ba baikuma yo min koda text bane,
  Nan kuma ta kwashe yadda akayi lokacin da taje gidan su gaida mahaifiyar shi,
   Safiya da ta gama sauraren maryam tai ajiyan zuciya,
   Tadan riko hannun maryam tace gaskiya maryam kina cikin tsaka mai wuya,
  Amma dai kiyi hakkuri pls kada ki sa wanan maganar a ranki,
  Ita mahaifiyar shi da take fadin haka danta yafi ki ne,?
  In,badon so ba may zakiyi da shi maryam,tuna duk inda aje son mace da tsari kin kai harkin zarta,
   Maryam tace wallahi Safiya ina son A,A shima yana so na,
  Matsalar mudai itace mahaifiyar shi yanzu, don ga yadda naji kalaman ta sam bata ra,ayina dashi,
   Safiya tace wallahi maryam kamar yadda anty tace din,nan haka zaki dake dashi kiga gudun shi,
  Yace yafasa mana yagani in baisha mamaki ba don dama ahi ya tare wa mutane guri,
   Maryam tace nidai safiya kin san cewa bazan nuna mai cewa naji maganar da sukayi da mahaifiyar shi ba sai in shi ya gwada min wani alama daga haka,
   Amma bari mu gani in har bai kiraki ba yau tau tabbas sunci karfin shi ke nan,
   Idan har bamu ganshi ba yau tun da kince yau ce ranan zuwan shigurin ki da ma,
   Yau wa safiya wallahi har naji dan sanyi daduk na rasa abinyi
  Gaskiya naji dadin wanan shawarar da kika bani har wani dan sanyi ya ratsa zuciya na,
   Safiya ta mike tajawo jakar kayanta da tazo dashi tana kokarin ciro kayan da zata sa,

   Shiga ce ta dinkin shadda gezena fara kal, yayi
Saidaukar ido shaddan keyi irin dinkin yan Mali, akaiwa shaddan,
   Agogon shi kawai zai fadama cewa akwai shegun agurin ,
   Wata hulla da ta,shiga da kayan yasa mai kyau da ita sai kuma wasu takalma, yan company, BELLA, yasa a kafar shi
  Kamshi dai ba,a maganar shi don yasa turare sunakai kala, biyar, alokaci guda,
  Kudi ya dauko yan dubu, dubu da yan dari biyar biyar yasa a kowani aljihun rigar shi,
  Motar da yashigo da ita tunda yazo bai shigeta ba tana aje,
  Itace yashigo yau zuwa gidan su KB inda za,a dunguma zuwa daurin aure,
  Jama,a sun ciki gurin makil, ana jiran motocin da za,a kwashe su,
  Sauran motocin da yashigo dasu yasa aka kwaso, akadinga dibar jama,a zuwa gurin,
   Duk wani abinda sharia ya tanadar gamay da daurin aure an gabatar a gurin a,lokacin,
   Joseph da tunda yake baitaba zuwa daurin auren musulmai ba sai wanan karon sai abin tazama mai sabon al,amari,
   Yaji duk abinda akeyi ya burge shi don komai a cikin tsari da kwanciyar hankali akeyin shi,
  Tunanen farko da yafara yi a ran shi shine, may kesa musulumai suna kashe auren su dayawa haka
  Dik da irin wanan, dokokin da akebi kafina mallakama mace,
  Idan har zai iya tunawa yadda yaji KB nahiran abinda yakashe akan wanan bukn to bai kamata kalman saki ya shigo ga auren yaran musulmai ba,
  Don yasan cewa musulunci batada banbancin al,ada,
  Da mai kudi da tallaka duk abuguda za,ayi agurin auren su,
  Hannu shi yadan daga ya shafi fuskan shi da yakeji kamar yawan jama,a yasa shi jin zufa agurin,
  Sai alokacin yadaga kai yakalli irin yawan al,umman da aka tara agurin wai duk akan auren KB wanda yasani,
   Jin ance fatiha yaga kowa na shafawa shima yadda yaga anyi yayi yashafa atare da kowa,
  Tare da Jibrin da kb da sauran abokai,suka mike inda maroka suka biyo su caaaa nan suka fara zuba masu kudi,
   Gidan Anty Dije akawuce don kwasan kayan abincin da za ai reception da shi awani katafare  hotel mai suna NOMA FAMILY'S MOTTELS,,,,
  Gurin yai mugun tsaruwa sosai anan suka kama guri, don haka duk kusan matasan da suka hakarci gurin sun isa Noma motels
   Anci ansha komai yawadatar da jama,a sam,barka a gurin,
  Sai shirin yin Dinners wanda za,a yi da karfe hudu na marancen ranan,
   Maryam dake takure tun safe tana zullumin shawaran da sukayi ita da kawar ta,
  Sai kawai taji kiran A,A yashigo mata alokacin cikin wata kasallaliyar murya yake mata magana cewa,
  Bai samu kiran ta yadan yi tafiya ne zuwa mariga, shida wani kanin mahaifin shi,
  Amma zai zo su tafi gurin dina tare zuwa anjima in ya shirya,
  Bayan sunyi sallama, da shi takalli inda safiya take ta na mai yin ajiyar zuciya alokacin,
  Don da dabai bugoba tadauka cewa tayi missing din A,A dinta ke nan
    Wanan dinner ya hadu sosai don anyi abubuwan da yakamata agurin Maryam da A,A dinta sukan kebe a waje gurin wasu Flowers da aka shuka agurin
  Yadan kalle ta cikin kulawa yana mai shafan kanshi,
    Sai alokacin Maryam ta gano yayi wata yar rama akwanankin nan so sai don agaskiya ba haka yake ba da,
  Gabanta yafadi damm tace a ranta kodai saboda fitinar magabar sune yasa shi ramay wa haka,
  A,A ne yadan kauda shirun da cewa, maryam ina fatan bakiyi fushi ba jiya dana barki ko,
   Wallahi wasu yan matsaloline sukadan sani nadan fita daniyar inje in dawo sai kuma ban gama da wuri ba,
   Dan shiru sukayi alokaci daya shiko yana sauraren ta ne ko, akwai abinda zatace, da shi,
   Amma sai kawai yaga tayi shiru, bata da alamun zatai magana,
  Maryam shirun ki wani lokaci nasan maganace kawai,
  Ki daure ki fada min may ke faruwa ne naga fuskan ki da akwai alamar damuwa acikin ta,
  Shiru tayi kamar baza tai magana ba amma kuma sai ta yar nisa kadan, tace,
   Malam shin akwai maganar mu kuwa ko dai da matsala aciki,
  Ita kanta batasan lokacin da wanan maganar yafito mata abaki ba,
   Shiko A,A saida yadan razana aran shi yace kodai wani yafadawa maryam abinda ake ciki ne shida mahaifiyar shi,
   A hankali ya kira sunan maryam din ta dan dago kanta ta,kalle shi sai takawar da sauri,
   Yace ma kika ga ni har zaki ce hakan,
  Kai tadan girgiza mai alamar a,a ba komai,
   Maryam ki daure ki fada min dan Allah may kika gani har ki ce haka,
   Joseph wanda alokacin yadan fitowaje daga cikin hall din da ake taron,
   Don yadan amsa call din wani yauron shi dake kiran shi can wani sabon depot da aka bude,
   Waya yake yi da Chukuma, kamar ance yadaga indon shi sai hango A,A da maryam a tsaye gurin wa yan,nan furan,nin suna zuba hirar su ta soyayya,
  Kallo guda yai masu ya kauda kai garesu yana mai ci gaba da wayan shi,
   Saida yagama wayar da Chokuma ne har zai koma cikin holl din sai kuma idon shi ya kara sauka inda suke tsaye,
  A cikin zuciyar shi yace wanan yarinyar itace har ta isa fira da saurayi haka,
 Haba is too early ma,
  Yai yar tsuki ya shige ciki abin,shi don bai iya ganin, takaici,
   Yarinya kamar ustaziya amma ta iya abubuwan da bai kamata ba da dama,
Itace hawan mashin yau kuma harda hira,
  Daidai lokacin da yake kokarin juyawa ne idon maryam ya sauka gareshi,
  Inda takalla malam A,A yabi da kallo sai bayan Joseph din kawai yagani yana kokarin shigewa cikin hall din,
   Maryam tsakanin mu ba dake yanzu yakamata mu fahinci junar mu sosai fiye da da,
   Nayi alkawarin bazan taba auren macen da ba tsarina ba,
  Ko kuma wace batada Qualities din abin danake so daga mace,
 Ra,ayinane in auri mace, mai sirin,classic, atare da ita,
   Wanda nasan cewa ta tara duk abin da nake muradi,
  Bakowane zai iya hangowanan abin ba sai namiji mai irin ra,ayina,
   So ki fada min ra,ayinki agamay dani pls, kada kuma kiji kunyar gayamin gaskiyar ki ,
  Duk da nasan bazaki iya ki kalleni ki fada min kai tsaye komay ke acikin, zuciyar ki ba,
  Magan ganun da A,A yai ta zuba ma gwaunatin shi don yaga yakarawa maryam karfin son shi komai wuya komai ritsi,
   Maryam har mamaki yabata don jin yadda yatakarkare yana kokarin boye mata gaskiya,
   Gashi ita kuma ta kasa fada mashi cewa taji maganar mahaiyar shi aranan
  Yaya ma zata kalle shi, tace mai hakana don tasan zai ji mugun nauyin hakan,
   Akarshe dai sai cewa tayi kasan aure nufin,Allah ne mallam, in Allah yakaddara hakan nafi kowa farin ciki da hakan,,,,,,,,,

  Zaune yake tsakiyar saman gadon shi yayi dadaya da wasu takardu yana dibawa,
  Abinda yafado mai alokacin sai irin yadda yaji, masu daura auren KB nayi wa juna alkawari,
   Gyara zaman shi yayi yanamai tuna yadda yaga ana yawan cewa wai ai wani ya saki matar shi,
  Ko kuma yadda yaji mutum na alkawarin cewa ya dauki nauyin ci da sha da suturan matar shi amma sa kaga matan gasunan a wahalce,suna wahala,
   Kayan dake watse saman gadon ya dan har,hada saboda yagaji da aikin dayakeyi tun dazu,
  Yana shirin shiga cikin bathroom don yadan watsa ruwa yana son zuwa club gurin wani mutum,
  Wayan shi dake yashe a gefen filo, ce tai kara cewa, ana kiran shi
  Dawowa yayi yadauki wayar nobar wanda yagani yana kiran shi, yasa shi saurin daga wayar shi,
Muryan Abdullsamada ce cikin wata irin sallama , yana cewa ya kake Joseph
  Yana cewa baida kudi a,wayan shi da zai ishe shi yai maganar da yake son yi,
    Amma ga Ibrahim nan Dan shi zuwa gurin shi daga haka wayar ta mutu dip,
 Alamar kudin nashi sun kare,ke,nan, tausayin mutumin yakama shi sosai,
   A ranshi yace,, may yasa wanan mutumin ke wanan wahalar haka, nan ya tuna da sanin da yai mai ada suna yara,
 Manya,manyar shaguna gare shi guda biyu, tab da kaya yana bada sari da kuma sayarwa cikin fararshi mai sauki
  Tunawa da yayi dattijon yace mai yaron shi ai zo gurin shi ,
  Baisan ko yaushe bane zaizo don haka  wayar ya dauka yakara kiran Abdulsamad din,
  Nan dai ya sheda mai cewa, yaron wajen shi ne ya ce kan cewa zaizo gurin Joseph din,
   Sai zuwa,safe yaron iso inda Joseph din ya tura azo mai dashi,
  Ibrahim yaro matashi dan kimanin ashirin da haihuwa, kamili ne mai rikon addini,
  Nan Joseph ya barshi har zuwa lokacin, da zai samu inda yasa shi cikin sana,ar shi,
   In gari ya waye Ibrahim zai tafi wani massalaci mai nisa can kasan unguwar su,
  Idan ya dawo kuma ,zai tsaya yadinga tillawa har zuwa wayewan gari,
   Gashi da ladabi don har  yan aiki yana basu girma sosai,,
  Joseph a hankali yake kiwon halin Ibrahim don ya gwada shi yagani,
  Idan kuma gurin abinci ne baida tsanda ko ra,ayi kamar wasu yara duk abin da aka bashi ,zai karba,
  Sai wata rana Joseph yana daga ciki, sai ya dinga jin maman Choima tana fada tun yana sama yadan fara saukowa zuwa inda take.
  Don jin komay ke faruwa,take fada haka sai ya iske da Ibrahim ne take masifa,
  Wai,duk lokacin da sukayi abinci suka bashi sai bai cin nama yadawo masu dashi,
  Joseph ya,dago kai a hankali, ya kalli Ibrahim, wanda ke tsaye gefe kan shi kasa,
  Ibrahim may yasa kake haka inji Joseph, ?
  Ibrahim wanda yadan gyara tsatin shi cikin ladabi yace ,
  Brother bawai ina masu wulakanci bane, saboda addini na ya haramta min cin naman da ba musullumi dan uwana ya yanka ba,
   Shiru Joseph yayi yana kallon Ibrahim yaro karami da,wanan akidar, acikin zuciyar shi,
  Maman choima dake jiran taji Joseph yai mai cin mutunci don ita tana ganin rainin wayo yai masu,
  Ji tayi Joseph yace idan abincin bai kwanta makaba arai zan dinga baka kudi kana zuwa gurin musulmai kana siya inaga zaifi,
   Aiko nan tsohuwa tahau fada cewa ya daure mai gindin yai madu wulakanci,
  Yakoma inda yafito mana waya kirashi da yazo zai ma mutane wulakanci,
 Joseph yace cikin wata murya ta warning ma,ma stop dat pls,,,, 
Maman ta wuce cikin kitchen, tana kallon naman,tana jujuya shi a, hankali,.tana masifa,,,,,,,,,,,


ZEEE   MAKAWA
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
    FUREN  JUJI
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
            2鈨�8鈨�

ZAINAB IDRIS MAKAWA,,,

Tafe yake cikin motar shi baka mai kama da siffan wani kifin ruwa, motar bakace wulk da ita,
   Yana rataye da yar suit shi a gefen kafadar shi sai hannu yake sawa yana dan sa,sau,ta nicktie, din shi, dake makale a wuyar shi,
    Air freshness yake son ya dauko ya, dan kara fesawa motar shi don shi al,a,dar shi ce sa kamshi duk inda yake,
   Dan save din motar yajawo daniyar dauko dan kwalban dake dauke da ruwan, freshness din,
  Wasu takardu suka fado daga gurin da yajo kwalban,
  Takardun da ya manta tun shekaran jiya ne a motar shi,
  Ibrahim yake son ya ba ya cika wani form, da yake son ya,je gurin computer training,
   A gagauce yadan fesa kamshin, sanan yajawo takardun ya aje a gefen shi ta yadda zai iya tunawa,don kada ya manta,
  Bayan ya Parker motar shi, yafito a,gajeyi don tun safe suke vurin wani taro da,akayi,
   Da takardun a hannun shi ya wuce zuwa dakin Ibrahim,
   Har yasa hannu zai tura kofar dakin, sai muryan yaron yani yana rera katun alkur,ani mai girma cikin wata irin murya maidadin sauraro,
  Maimakon ya shiga sai yadan tsaya har nakamar minti biyar yana da yaron ke fidda,harufan ya da ya dace a cikin natsuwa,
  Juyawa yayi yakoma hanyar cikin gida don ba zaiso ya katse mai karatun dhi
  Tunda bai san lokacin da ya farawar ba, balle kuma ya katse shi,
  A,hankali ya tura kofan falon ba kowa aciki a lokacin sai TV dake ta aiki, shi kadai
  Tashan wasu Christos ne wai peace TV, rawa suke kwasa da i,ho,ce,i,hoce,
  Wani iri yaji aran sa kawai sai yaji haushin su ,daukan remote din yayi ya kashe TV,
  A hankali ya fara tafiya a saman steps din da zai sada shi da bangaren shi sama,
   A kusan hawan karshe maman Choima tafito saye da wani dogon riga kanta daure da dankwali ta tsuke shi tam,
  Tace wa Joseph, So, you, are back,?
   You na welcome, wooo,
Thank u mama,
Your food don ready since,
 Cikin wanan turancin may kama da yare ta dinga jefo mai magana tanayi tana hadawa da,harshen IBO din,
  Ruwa ya watsa sai a lokacin yadan ji zuciyar shi tadan rage mai suyar da bai san dalilin yin ta ba,
   Yaso ya koma gurin Ibrahim don yai mai bayani amma sai kuma ya kasa saboda gajiyar da ya kwaso,,
   Don haka baima,sauko kasaba kamar yadda yasaba, indan yadawo yakan je gurin mama su dan yi hira,
  Don kawar mata da zaman kadaici duk da yasan Ejoma tana iya kokarin ta da yar tsohuwar,
  Washegari, musalin karfe takwas na safe, Joseph yasamu ya sauko tare da takardun Ibrahim na jiya a hannun shi,
  Dakin nashi ya nufa don yakai mai yasamu ya cika idan zai fita yau sai ya tafi dasu ya mayar,
   Tun daga yar hanyar da zata sadaka da dakin Ibrahim zaka ji muryan shi rarara, yana karanta suratul Maryam,
   Jin maryam mu da yake ambata aciki yasa Joseph tsayawa guri guda cif,
   Yace a hankali maryam in ,Qur'an, ?
   Ji kawai yayi yai kundunbale fadawa dakin yaga may yaron keyi haka,
   Ibrahim wanda ke zaune kamar a tsugune can wani dan sakon gado yana rike da Qur'an din shi yana mai karantawa,
  Jin kamshin turaren Joseph dayayi a dakin yasa shi dan bude indon shi da suke a lumshe,
   Don ya tabbatar da kamshin da hancin shi ya shako mai na Joseph din shine agaban shi ,ko,kuwa,?
    In ko har shi din ne to ko jiya ma da,dare da ya jiwo wanan kamshi tabbas shi din ne a gurin duk da bai bude ido yatabatar da hakan ba,
   Daidai ya kai A,ya" yadan dakata kadan yana mai cewa Sadakallahul,Azeen,
  Ina kwana yai mai acikin yaren su na IBO, Joseph ya dan daga mai hannu yana mai cewa,sorry for disturb pls,
  Takardun ya mika mai yace mai, ya cikia inda bai gane ba yasa may shi yai mai bayani,
  Daga haka yajuya kawai yabar dakin yana jin wani irin abu kamar kasala tana lu,lube shi,
  Sai zakakkan muryam Ibrahim ke mai yawo a kunuwa shi kamar a ciki yake wanan karatun,.
   Lumshe idon shi yayi yabi bayan kujerar da yake zaune yadan kwanta,,

   A hankali maryam ta ajiye, plate din da ta debo abinci, agaban Anty nata,
   Wacce ke kwance saman dogon kujerar da ke cikin falon nasu,
  Anty Dije tadan dago kai kadan ta kalli maryam wace ke kokarin juyawa don komawa dauko ma yar nata ruwan sha,,,
   Cikin murya ta wanda je jin jiki Anty tace wa maryam ,
  Maryam ba,zan iya cin wanan abincin ba don sam bakina bai min dadi wallahi,
   Cikin dan marairaice murya Maryam tace anty dan Allah ko kadan ne kidaure ki danci, zaifi rashin cin da bakya, son yi,
   Da taimakon maryam Anty Dije tadanci abincin kusan spoon, hudu, gana biyar ta mayar tana mai cewa ta koshi,
  Bazata iya karawa ba haka don ji take tankar zata amaye dan wanda taci,
  Gudun kada tai amai Maryam ta kyale yar nata tana mai tatara plate din zuwa kitchen,
   Ido Anty tabi maryam dashi tana mai jin dadin irin kaunar da yar uwar nata ke yawan nuna mata ita da yaran ta,
  Ringing Tone din wayar Anty Dije ne ya karade gidan nasu a lokacin,
   Da sauri maryam ta isa inda,wayan take tana ruri, don ganin mai kiran yar uwar nata,
 Yusuf Joseph tagani baro,baro a screen din wayar,
  Kurawa wayar ido tayi har saida ya katse don kan shi,
  A hankali Anty tadan dago kai daga inda take, kwance tana son tasan kowaye ke kiranta ya katse,
  Don tana,son kaunar nata ta fada mata kowaye a layin,ke,kiranta,
    Tana kokarin aje wayar ne wani kiran nashi yakara shigowa again
  Dole ta nufi inda Anty take kwance, da hannu take mata tambayar waye akan layin,
   Joseph tace tana kokarin kara mata wayan a kunen ta,
  Da hannu taimata alamar, ta dauka kawai sai ta maida kanta saman hannun kujer a hankali,
   Cikin muryan mai,kama da ta maijin kasala take magana,
  Hello, ina wuni ?
   Mai wayar batada lafiya ,
  Juses crisis,
Dif maryam tayi tana mai cewa wa,iyazu,billlah,
  Jitayi tankar ta aje wayan do haushi,
  Sai jin shi tayi yana cewa may yasa may ta haka,
  Zazzabine ke damun ta yau kwana biyu ke nan,
  Jin wa,iyazu,billah da tafada dazu yadan sosai mai rai don yasan kalmace ta nuna wani tsari ga tsanar, abu,
     Don haka yanzu sai yadan gyara harshen shi da cewa ayya sorry fa ina gaisheta pls anjima zan bugo mata,
  Kagin ma ya kashe har maryam ta kashe wayar bin wayar yayi da kallo,
  Sai mamaki kuma yake a ran shi cewa may yasa musulmai ba su iya boye felling din su in suka ji an ance Juses,a gaban su,
   Maryam ko a hankali ta juyo gurin Anty tana fada mata abinda yace mata,
   Yinin ranan duk a kwance anty ta ti shi saboda yanayin jikin ta duk ba dadi,
  Ganin tana wahala da yawa yasa maryam bugawa yaya illiya waya tana sheda mai abinda ke faruwa xa yar uwar nata,
  Wace duk kwanakin nan akwance take bata jin dadin jikin ta,
  Ga wani amai dake zo mata yanzu duk abinda taci sai ta fitar dashi koda ruwa ne,
   Hakalin Maryam ya tashi sosai cikin dare da Joseph yabugo muryan ta kamar na mai kuka take mai magana,
  Tana sheda mai yadda ciwon ke matsawa yar uwan ta yanzu sosai,
  Shiru yadan yi nawani lokaci har maryam din na,,zaton ko cewa ya kashe wayan ne,
  Tace cikin siririyar murya, hello,,
  Yace ina jinki kunje asibiti, ta girgiza kanta alokacin kamar yana ganin ta tace a,a
  Saidai zuwa gobe insha Allah zamu tafi yaya yau ya bugo waya yake cewa mutafi goben,
   Ok to barin yi magana da shi Illiya din tukun 'I will call you back,,,
  Ok tau nagode tace tana mai kokarin aje wayar a lokacin shikuma yana mai ce mata ina Assalam yana lafiya ko?
  Cikin kosawa da yin wayar tace mai yana lafiya sai anjima,
  Itace kuma still dai ta,katse wayar kamar yadda ta yi dazu
  Yai shiru yana dan mamakin irin halin Maryam na rashi son mutane
  Yasaki ajiyar zuciya yana mai kara nazarin ta,
  Tuna wa yayi da zancen kiran illiya don haka nobar shi ce ya kira,,
  Bayan sun gaisane yai mai jajen ciwon matar shi sai, ya,kecewa
  Dama ya bugo waya ne don ya tambaye shi ko yana iya tura mai doctor lawal yadiba matarshi
  Don yadda akace mai tana jin jikin har ta kasa daukar waya daya kirata,
   Ya, illiya yai murna kwarai da wanan taimakon da Joseph yai mai na turawa har gida a diba mai matar shi,
  Saida Doctor Lawal ya iso gidan sanan Joseph yakira yake sheda masu cewa gashi nan shigowa,
  Mamaki ne yakama maryam sosai don ganin cewa yasan yadda shari,ar musulunci yace ayi,
  Am.a kuma da,tai tunane saitaga babu mamaki don yana tare da su jibrin yau da gobe dole yasan komai,
  An mata allurai dakuma yan magunguna, sai fitsarin ta da akace akai gobe,
  Bayan fitar doctor dakamar yan min tina sai,gashi ya kara kira yana tambayar ta
   Ta girgiza kai tace ban san may doctor yace ba yadai mata allura,
 Nan yai mata sada safe yana mai jaddada mata cewa ta tabbatar da cewa Anty tana shan maganin ta,
    Joseph yaso ya shivo saidai yana tsoron irin masifar da tsohon shi ya za,zaga mai,
   Inda ya bashi umurni da cewa indan har bashi yace yana son yazo ba kada ya fara yashigo garin kwantagora,
  Tunda badon su ya haife shi ba da zai dinga kashe masu kudin shi abanza hakana,
  Fada sosai yaiwa Dan nashi lokacin bukin KB da sukayi inda labarin komi yazo kunen Mr Ema din a lokacin ne yai kamar zai daki Joseph din don haushi,
    Jikin Joseph a sanyaye don badamar zuwa yadiba halin da Anty nashi ke ciki, don gudun masifar mahaifin shi wanda sam bai son hurdan shi da yaran varin da yake amfana dasu,
    Hannu yasa yadan shafo sanjen fuskan shi da ya kwanta mai lub a fuskan,
  Ya furzar da yar iska mai dan dumi daga bakin shi,
 Ibrahim ne yafado mai arai don haka yatadashi inda yai mai shatar mota zuwa kwantagora da kayan dubiya irin ta marasa lafiya,
   Anty Dije tayi mamaki kwarai da irin kayan da Joseph ya bayar ,akawo mata tundaga Lagos har KG,
    Lemo, Abarba, Ayyaba, Apple, kwakwa, carrot, water millow, pears, da,sauran su bar manja da garin can saida ya siya mata,
    Waya anty tasa aka bugawa Joseph tana son tsi mai godiya na taimakon da yai mata, ga likita ga  kayan marmari, da yayo mata,

  Likita ya tabbatar da cewa Anty Dije tana dauke da shigar ciki na wata biyu da da kwanaki,
   Maryam tafi kowa murna da wanan labarin cikin, wanda har uwar mijin ta tafara zance wai ya karo mata tunda anty tabar haihuwa,
  Da sun dan samu matsala dasu yanzu zasu fara mata gorin taki haihuwa kuma ta hana auri wata,,,,


ZEEE MAKAWA
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
  FUREN     JUJI
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
           2鈨�9鈨�

ZAINAB IDRIS MAKAWA,,,


Yan uwa musulumai ina mika gaisuwa gare ku ,akan wa yan nan yaran makaranta yan garin misau da ke cikin jahar Bauchi da suka samu harin mota ta hanyar su zuwa kano ziyarar Arewa 24,wanan satin da yagabata suka mutu su ashirin ta re da malaman su,,
   Masoya TAKARI novel da FUREN JUJI ina fatan za muyi masu adduan fatan samun Rahamar ubangiji, tare da mika ta,aziyar mu ga yan,uwa, da, iyayyen wa,yan nan yara, Allah ubangiji kasa Aljannan Fiddausi tazama makomar su,馃憦馃憦馃憦馃憦

 Mahaifin , Ibrahim Abdulsamad, yaji dadin yada yaga dan shi ya koma cikin dan kankanin lokaci,
  Bakamar yadda suke zube a cikin gari ba da babu mataimaki,
  Babu wanda ma yasan cewa suna cikin wani halin bukata na rashin yan uwa da galihu,
   Yana ji yana gani matar shi ta gudu mai da yan shi mata, zuwa kasan su,
  Wanda bakomai yasa shi kyaleta dasu ba sai tsabar yawan talauci dake cin shi,
  Ki abinda zasu ci tunda yai gobara shagunar shi suka kone kurmus,
  Amma sai yara,daya daga cikin musulmai wanda zai taimaka mai da wani abin,
  Gashi har zuwa yanzu yan uwan shi na da suna kawo mai tayi akan ya koma akidar shi tafarko,
  Babu komai acikin wanan sabuwar akudar da yadauko, illa wahala,
   Dariya kawai yakan masu yabasu amsar cewa shi yabar su ke nan har abada
Bazai kara dawowa cikin banyar bata ba saidai ya mutu a hakan,
  Girman da yaran shi suka farayi ne yadan rage mai wahalar don suna zuwa yin dako a bakin kasuwa sukawo dan abin da suka samu ayini asarrafa,
  Ko shi Ibrahim saida bukin KB da akayi ne yasan cewa suna da alaka da Joseph,,
  Lokacin da yaga irin yadda Joseph ke yi agurin yazo yana fadawa mahaifinshi cewa baisan cewa IBO bane saida yaji  yana yare acikin waya,
   Abdulsamad yai dariya inda yakewa diyan shi bayanin ko ya suke da Joseph,
  Nan ne ibrahim yace zai je gurin shi ya ziyar ce shi yagani ko za,a samu wani cigaba anan,
   Maihaifin na Ibrahim baiki ba don yasan kowaye Joseph zai iya taimama wa ibrahim din,
  Sai ko gsshi cikin ikon Allah ibrahim din yazo cikin kamata alheri don bai taba zaton cewa yaron zai can za cikin dan lokaci guda haka ba,
  Ga sakon kudi har dubu hamsin anbashi yakawo wa mahaifin shi tare da tsaraba,
  Kwanan shi biyu da zuwa inda yakoma shedawa Anty Dije zai koma,
  Sako tabayar akai ma Joseph din wani robber da akai sild din shi
  Sai kuma kilishi cikin envelop, mai yawa cikin wani babban leda tace Ibrahim yakai wa Joseph,

  Bakaramin mamaki  Joseph yayi ba lokacin da Ibrahim yagabatar mai da sokon da Anty Dije ta aiko mai dasu,
  Dambun nama ne cike a roban sai kuma kilishi mai yawa,
  Daga kilishin har Danbun Joseph yarasa wani yafi dadi daga ciki,
   Sai mamaki yakeyi yana kada kai cikin jin nauyi, kamar a gaban anty din yake,
  Shi yana gani kamar ta ksshe kudin da yakai dubu dari akan wanan abin,
  Bai daga daga gurin ba sai da ya kira ta acikin waya yana mata godiya daga karshe ma yarasa may zai ce mata,
   Mamaki kwarai anty tayi don jin yadda yake zabga mata godiya akan dan abinda baikai yakawo ba,
  Shida ta lodo mata tsaraba har saida ta ba makwabta da kuma gidajen su ita da mijin ta,
   Amma,shi gashi ko dubu ashirin bata kashe mai ba yata zabga godiya,
  Shin shi Joseph din nan wani irin zuciya gare shi ne wai gashi da bawai, yasan kaidar zumunci ba ne a ddini,
  Amma yarike ta tam kamar wata yar uwar sa ta ji,
   Ita dai fatan ta dai,akullun Allah ya kebo Joseph, yadawo cikin Islam's,
   A hankali Joseph ya maida tsarabar anty wani abincin shi na daban koda yaushe yana amfani da abinshi kadan kadan,
 
    Wani irin gurnani take yi wanda har a fili zaka iya jin yadda takeyi wanan karar,
  Joseph dake shirin hawa sama yagama kallon national news, a TVC,
  Da sauri yai hanyar dakin na maman choima wace ke faman wani irin Gumza takar ana shirin yankar ta,
   Da karfi Joseph da Ejoma ke kokarim daga ta daga kwanciyar da tayi tana fidda wanan sautin,
  Cikin wani irin kara tabude idon ta tana mai cewa Joseph's da karfi,
   Firgigit take kallon su da sauri ta rugumo Joseph din daga jikin ta,,
   Sai kuma ta fashe dawani irin kuka tana magana maiban tausayi, cikin kuka,
  Tana mai cewa,Joseph they want to carry u away from us,woooo,
  Joseph da ya rungumo tsohuwar zuwa cikin jikin shi, yace mata sowaye,
  Cikin kuka tace bata san su ba amma tana yawan gani su,,a tare dashi acikin su,, koyaushe,
   Sai yaune babban su ya ce har da ita zai wuce in,har tana rike shi,
   Shine wanan gumzar da take tayi cikin barcin ta da ihun da take ta kwasa yanzu,
   Joseph yadan tallabo kan kakar tashi, zuwa jikin shi yana mai lalashin ta
  Tunda yaga cewa tadan kwantar da hankalinta yasamu ya sata kwantawa don ko zata samu barci,
   Yamike zuwa dakin shi jiki a sanyaye, zuciyar fam da tunane kala kala,
  Ashe haka wanan yar tsohuwar ke wahala idan tace mai tayi wanan mafarkin,,
   Hankali shi yatashi matuka yana tunanen may ke shirin samun shine haka,
  Washegari, tunda safe Joseph yabar gida zuwa gidan wani babban pastor da ke zaune a cikin Lagos,
   Saidai bayan bayanin da Joseph yai mai sai ya umarci da azo mai da wnan tsohuwae wurin shi
  Joseph yakoma yazo da maman choima acikin shirinta na irin manyan matan IBO,
  Pasto ya riko hannun mama zuwa yan wasu lokota,
  Can sai ya sake yadan daga kai yana mai kallon Joseph wanda ke zaune gefen su saman wata far kujera, yana mai rike habar shi da hannu guda yana dan shafa, gemun shi,
 Idon da pastor yadan tsura mai baisa Joseph ya canza daga yadda yake zaune ba tun farko,
  Pastor yadan kada kan shi yai yar gyarar murya wanda yasa duk suka kura mai ido,
  Don jin irin bayanin da zai masu gamay da mafarkin da takeyi,
 Mama inji pastor kada ki damu wanwn bawani abin damuwa bane danki zai zama wani abu ne nan gaba shiyasa kike ganin wan nan abin,
  Amma,zai bata holy water wanda zata dinga wanke fuskan ta dashi har zuwa sati,
  Idan ta kara wanan mafarki sai su dawo, duk kan su,
   Sukai godiya Joseph ya kawo kudi yabawa pastor pastor yaka da kan shi alamar aa ba,zai karba ba,
  Yace we are just send to help, the, neediest,
  Yai masu addu,a a baki dayan su inda sukai sallama dashi zuwa  gida,
   Tun,daga wanan ranan maman choima ta fara amfani da ruwan holy water, kamar yadda pastor ya umurce ta tayi,
 
  Shiri yakeyi sosai saboda tunda safe yake son takama hanya zuwa kano don dibo wasu kaya da wani tsoho yai mashi tallan kayan company,
   Duk shirin da,Joseph keyi hankalin shi na gurin kakar  shi wacce ta nuna batason zuwan shi garin kano sam,
 Saida ya gama,shirin tsab ya sauko cikin shigar kananin kaya,
  Kayan ya karbe shi sosai don ya fitar mai da surar shi tsab,
  Karfafan namiji mai duk wani siffa mai nuna karfi daga jikin da namiji
  Saidai Joseph ba mutum bane mai son magana don haka ko murmushi da wuya kaga yayi ta, kasafai,
   Guda guda yake tako hannu shi guda na acikin ajihun wandon shi guda kuma yana dauke da yar briefcase din shi,
    Direct saman kujerar da maman choima take zaune ya nufa inda shima yazauna gefen hannun kujerar,
  Yadan langabo kanshi zuwa saman kan maman Choima din,
 Mama ,I, gona miss u, wooo,
  Kamar yadda yasaba fada mata duk lokacin da zaiyi tafiya mai yar nisa, dasu,
  Cikin muryan da tanu cewa ta manyanta tafara magana,kamar haka,
  My child , god dey with u,for D whole time , u go spend there,,,
  Ejoma dake gefe ta amsa da fadin Ameen,,
   Joseph yamike tsaye yana dan gyara, wandon shi, tare da yi masu sallama,
  Motar da zaitafi da ita Ibrahim ke ta faman gogewa da kakabewa,
  Nan sukayi sallama da ibrahim din yabashi dan kudin da zai yi amfani dasu kafin yadawo,
  Adduan dayaron ke mai kullun tasashi jin dadin rayuwar shi aduk lokacin da uai mai ita,
 Ahankali ya furtawa ibrahim din da Ameen, tnxs brother,
  Yaja motar shi yai gaba yanama Ibrahim horn alamar bye,bye,
 
   Abamu na Allah da Annabi,
 A taimaki almajara sadaka saboda Allah,
 A,wani gidan mai daidai shiga garin kano, wasu almajirai ne suka baibaiye wata mota, da wani matashi acikin wani yaddi mai ruwa toka,
  Da sauri saurin ya ja glass din motar,shi sama saboda gudun kada su damay shi,
  A daidai lokacin Joseph ya parker tashi motar kusa da ta saurayin,
  Daga cikin motar shi yakewa saurayin kallon mamaki,
  Wata yar jagora wani tsohon makaho da, ta kurawa Joseph ido tun lokacin da ya tsayar da motar shi,
  Da kai yai mata alamar tazo ba bata lokaci tasake sandan dan tsohon makahon da take ja zuwa inda Joseph din yake,
   Dan Allah ki karbi wanan duk almajirin dake gurin nan ki bashi sadaka,
  Kafin yakara sa mika mata sai gawani dan dukaken mutum mai yar wani doro abaya ya iso gurin cikin sauri,
  Ataimaka ma almajiri da sadaka Alhaji,
  Malam haru, gashi yabamu yace duk wanda ke gurin abashi saboda Allah,
   Kafin minti biyu duk sun baibaye motar Joseph Alhaji yadda kai muna Allah yai maka
  Allah yasa agama da duniya lafiya,
  Wata yar tsohuwa da aka jawo duke a nanade cikin wani keken, turawa,
  Tace, Allah ya tsare Allah yabada sa,a Allah Allah yasa afi,haka arayuwa,
   Daidai lokacin mai zuba mai a motar ya gama zuba mai man da ake zubawa,
   Yaciro kudin shi ya mika mai, ji yayi ana gardama bada yaran almanirai masu bara ba,
  Yakara yafutu yaron dake tsaye cikin yagagun kaya gaban rigar a bude, robar baran shi duk tayi dauda
  Ya,mika mai kudi, sukai dubu biyar yace su raba aikuwa nan guri kaure da suratai,
  Shika har ya harba motar shi zuwa cikin gari don yasamu ya isa inda akai mai masaukin kwana,
  Kafin gobe, su tafi tsohuwar maikatar su diba abinda suke so aciki, su saya,
   Alhaji sabo, wani tsohon mai kudine wanda yasamu kariyar arziki
  Yanzu baida komai sai sayar da yan kaddarorin dake gare shi, yake akai kai don ya samu dan abinda, suka ci shi da iyalin shi,
   Yakira abokan sanar ashi sukai mutun biyar don su sai waban injin din amma sai suyi mai tayin tsiya ta yadda zai fadi warwas,
  Shine wani yaron shi na da dake lagos yai ma su Joseph talla ko za,su saye, suyi amfani da shi,
   Tun,cikin dare, da ya shigo Alhaji sabo ya zo har masaukin shi don su gana saboda in har yakai gobe
  Mahassadan shi na ita bata zancen su soke al,amari don ganin cewa bai farfado ba ko kadan,
   Bayan sun gaisa Alhaji Sabo yafadawa Joseph irin halin da yake ciki da kuma yadda makiyan shi suka sashi agaba don kada ya farfado,
   Joseph yai nazarin wanan bawan Allah sosai har yaji yana son ya tallafa mai,
  Dama da Sonny ne zasu sai wanan kayan suyi masana,an ta dashi can,Lagos din,
   Don haka sai yaba Alhaji sabo shawaran cewa, may zai hana ya canza sana,a yagani,
  Amma yabashi shawara ya tafi yai nazari akai, duk abin da ya gani yafada mai
   Kamar masu jira aiko tunda suka ga su Joseph tare da jibrin da KB dasuka iso kano aranan suka samay shi
  Sai aka fara zuwa gaisawa da su tamkar an san inda suka fito,
  Daganan aka fara tambayar ko daga wani gari suke,
 Wata irin masanan ta zasu yi ai ko yakamata sukira wa, yanda suka san kan injin su diba  masu don gaskiya injin din ya dade, da, lalace,
  Tun nan Joseph yagane cewa agent, din mahassadan Alhaji Sabone,
  Ganin irin body guard din dake biye da Joseph da mutanen shi gashi kuma suna ta son yin suka amma ba fuska,
   Bayan sun gama dibawa Joseph yasa adibo mai enginers masu aikin kwarai daga lagos zasu biyu jirgi, su zo
 Su di mai kyau engine din idan baiyi mugun baci ba,
   Bayan Joseph yakoma masaukin shine yake ba su jibrin labarin hiran shi da Alhaji sabo,
  Gashi kuma sunga zahiri duk da bawai sun bada fuska ba a gun mutanen,
    Bayan ma,aikatar sunzo sun diba engine din sai suka tabbatar da cewa dan gyaran da za,ai mai kadan ne don komai nashi lafiya lau yae
  Kuma na,da ne mai kyau yanzu ba,a samun irin, shi so sai,
   Tausayin wanan bawan Allah Joseph yaji sosai sai yaga yakamata yai mai hanya,
  Shikuma Alhaji Sabo kamar yasan cewa Joseph na wani planing akan shi,
  Sai gashi ya gaiyaci Joseph har gidan shi gurin iyalin shi,
  Gidan ba, laifi baba ne amma, dai da alamar porvaty, aciki,
  Amma akwai addini, ga ladabi da sanin ya kamata atare da su,
   Wani dan karamin yaro a gidan yazo da sauri yadinga fito da butoci yana direwa agaban mutane,
   A, gaban Joseph yadire wani butan silver mai ruwan gold,
  Har zai wuce sai Joseph yajawo shi zuwa jikin shi yana tambayar shi sunan shi,
  Amma sai ya ce wa Joseph, barin muyi sallah kada mu makara sai in fada ma,
   Joseph yasake yaron yana mamaki yadda yara kanana suke iya akidar addini tun suna yara,
  Shin wai duk haka musullumai sukewa yaran sune tun  suna kanana ko kuwa,,
  Murayan dan yaron ya katse Joseph din yana cewa uncle  kayi alawala, kada mu makara mu tsaya baya kaji, ba kyau,,
  Joseph yai murmushi yace kayi kawai zan biyo ka a baya ina jiran wani ne,
 Sai yaji wani irin nauyi da kunyar hakan 
  Tunda yake baitaba jin nauyi ba sai yau, dan karamin yaro na sa shi ahanya,
  Kafin su fito daga sallah Joseph yabar gidan,  cikin yar damuwa,
  A can masaukin shi yana isa ya jefar da top din  shi a saman kujerar dake dakin
  Gurin fridge yanufa yadauko goran ruwa ya ballemarfi ya kafa a abakin, shi sai roban duk ya kwakwade ruwan, cikin roba,
 Ya wurgat da roban can gefe guda saman gado yafada jagab,
  Sai kuma yakai kwance tabayan shi yana mai lunshe idon shi kamar mai barci,
  Ringing din wayar shi tasa shi bude idon shi, dake lunshe kusan yan mintina,
  A, cikin sauri yajawo wayar don kada kiran ya katse
  Nobar anty Dije ce ke kiranshi,bayan sun gaisa,dashine take sheda,mai cewa Asalam ne ke magana dashi,
  Yana karban wayan sai ce mai yaron yayi, uncle wai bazakazo gurin walimar saular su little mummy ba,
  Da farko baigane may yaron ke nufi ba, saidaga baya,
Ya,fahinta da abin dayaron ke nufi, Anty Dije ce takarbi wayan take mai baya yadda akayi,
  Wai cewa yai Joseph din zaizo sai kace i, bazai zo ba,
 Tana fadin hakan kawai sai yagane cewa akwai abin da akace wa yaron agamay dashi,,,,,


ZEEE      MAKAWA
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
   FUREN     JUJI
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
           3鈨�0鈨�

ZAINAB IDRIS MAKAWA,,,

Duk, abinda ya kamata Joseph yayi ya aiwatar a kano, Don haka sai yai shirin komawa gida,
  A cikin dare, Sonny ya bugo mai waya cewa ya fi bukatar su aje wanan engine din a garin Abuja,
   Aboda haka yanzu dole Abuja Joseph zai ratse don neman gurin da zasu yi wanan aikin,
  Dashi da Jibrin ne ke ta faman yawon neman guri, inda ya kamata,
  Wani sabon side ne suka samu a NYanya, acan zasu yi wanan masana,antar,
   Tun da aja fara wanan aikin sau guda Joseph ya dan zo Lagos yaga su mama,
  Sam yafita duk wani zancen zuwa kwantagora yanzu saboda baida lokacin hakan bukatar shi kawai ya ga wanan masa,nantar yasamu kafuwa kamar yadda suke so,

  Ma,aikatar dake aikin gurin yau ma kamar kullun su halarra sun fara aiyukan su,
  Kwasam sai suka dinga jin wani irin ihu na tashi tankar mace na ihu tana neman taimako,
   Wasa wasa sai jin ihun sukeyi yana karuwa kafin kamar a inda suke, aiki karan ke, fitowa, sai gani sukayi wani irin iska mai karffi yana kada ganye da ciyawon dake gurin,
  Mutun daya daga cikin su yafara yar da abin digar da ke a hannun shi,
   Ya,arta ana,kare, ganin haka sauran ma,aikatar gurin suka fara, arcewa, kowa sai kwasan gudu yakeyi ba mai tsayawa jiran wani,
   Suna ji suna gani gurin ya gagare su aiki dole suka bido nobar jibrin wanda alokacin shima yana shirin zuwa diba su,
    Dariya ya fara yi lokacin da suke fada mzi yana ta faman kyalkyalar dariya
  Yana isowa ya shima yaji wanan sautin tun daga ne sa aiba girama,ba, arziki ya fada motar shi sai maida nunfashi guda guda yake yi,
   Sai da yatabbatar yabar unguwar ya dauko wayar shi ya buga ma Joseph,
  Kwance yake daga shi sai rigar barcin shi dark blue yana saye da wani dan gajeren wando,
   Kwance yake tare da Aisha ya rungumay ta, a cikin jikin shi sai kwasan barcin su sukeyi,Aishan, wacce ta shigo jiya da,dare,
  Dukkan su suna tare da gani kowan su nada gajiya atare da shi,
  Karar wayan da Jibrin shi da KB suke ta bugo mai a jere da juna yasa Joseph a hankali bude idon shi
   Hannun shi yamika saman side drower din shi inda wayar shi ke ta faman tsuwa,
   Saida yai yar tsuki alamar jin haushi kiran a wanan lokacin,
   A,llo, yace cikin lumsherwar ido, idon shi wanda ke cike tab da barci, alokacin,
   Cikin tashin hankali Jibrin ke magana man an samu matsala fa,
  Kai Jibrin wanan kira haka tun da safe, haba,haba kasan fa ina son hutu,
  Kai Baba anfa samu matsala sosai nake fada ma,
  New side ba lafiya fa,
 What's, Joseph wanda ya mike zubur daga kwanciyar da yake,
  Aisha ta dan yi kojarin rungumo shi ai bai san lokacin da ya ture taba gefe ya mike zaune,
  May kake son fada min ne Jibrin may ke faruwa ne wai,?
  Jibrin yace wallahi gurin sam baya shiguwa, saboda wani mugun sound da ke fitowa a cikin kasa,
   Juses crisis, inji Joseph Jibrin yace lalai dai kam kara fadi,
  Don nima daga can nake don na sauka cewa abin wasa ne dafarko, sai gashi naga abin ba dama wallahi,
   Bathroom ya fada don yadan watsa ruwa tunda ba maganar sallah gare shi,
  Cikin sauri ya shirya Aisha tana kwance cikin A,C yadan kalle ta ya kada kai yace Aisha kitashi kiyi sallah mana,
  Ban san may yasa bakya son yin sallah in time ba fa,
  Tai wani mika tana kara,shigewa cikin bargon dake saman ta,
   Tace, ai zan tashi yanzu, inyi na,gajine sosai wallahi
   Cikin sauri ya fesa turare a jikin shi yadauki wayoyin shi yasa a aljihun shi,
   Aguje yabar gurin, inda su Jibrin ke fada mai cewa sun na,nan ne ya,nufa,
  A bakin hanya yasamay su inda duk bayanin da suke mai sam bai dauka ba aranshi,
  Mota yashiga tare da wani William, suka nufi gurin,
  Tun a saman hanya suke jin wanan sautin tankar mace na kuka tana neman taimako,
  Bakin shi dauke da irin addu,oin su ya nufi gurin gadan gadan gadan,
   Wani irin matsanacin ihu yake ji tankar kunnuwar shi zasu tsage a lokacin,
   Sai kuma yaga kamar kasa na motsi, da girgizawa,
  Iska yafara ji yana gabato gurin da yake kamar za,a daga shi jin sautin na  tankar yana motsowa inda yake yasa shi saurin dawo,wa baya a,hankali sai jin sautin yakeyi tankar kasa zai tsage,
   Hannu shi guda a cikin aljihu guda kuma yana rike da wayar shi,
  Dole ya dan hada gudu don kara girgiza kasan gurin ke yi,
  A mota yasamu Mr William, yana jiran shi, ba bata lokaci suka tada mota suka bar gurin kamar walkiya,
   William ne yake bashi shawara su je, gidan wani pastor, masaka su dauko shi
  Zowan pastor da mukar, raban shi yafi komai kara  bata zancen don wani irin,
  Iskane yafara lailayewa yanagi sararim samaniya, gurin na baki, kamar hadari,
  Kwana biyu ana wana badakalar abu yaki tsayawa sai kara rikicewa duk mai maganin su na Christian an dauko amma abu yakiya,
  Jibrin ne yabada shawaran adauko, Abdul, mudallabi mai almajirai a gwada agani,
  Ta cikin waya suka buga  ma malam waya suna son don Allah yazo ya taimaka masu,
  Malam din yace gaskiya bazai samu zuwa har Abuja ba yanzu,
  Ganin mallam zai kine yasa, KB yai ma wani kanin mahaifin shi waya aminin wani shehin malami malam Dahiru,  tare da,wani malam Lawi,,,
  Allah ya taimaka suka ci karfin malam Abdulmudalabi,
  Sukazo tare gurin tun safe suka kamo hanya sai musalin, karfe biyun rana suka isa gurin,
    Kamar ko, yau she gurin na gumza kamar kullun,
  Malam tun isar su yafara cewa Allahu Akbar, Allahu,Akbar,
   Qur'an din shi dake cikin wata jakka da ya ratayo yadau ko,
  Tare da shimfida wani daddaduma mai laushi sai turare da yadan yayafa agurin,
 Suna sauran kusan makamanci yadda malam yayi sukayi,
  Suratul Suleiman su,ka,fara karan tawa,,
Sai suka  sauran ayoyi dake koran Aljannu,
   Kuka akeyi mai ban tausayi yanzu, malam da kan shi saida yai hawaye, idan yaji yadda abin ke wani gumza,
   Yadan dakatar da karatun da yakeyi yai gyarar murya, yana cewa,
  Macen ce ke wanan kukan saboda wai nan gidan su ne na kaka da kakan ni,
  Shine yanzu za,a zo ab kore su batare da sanin suba, to su bazasubar gurin ba,
  Saboda tayi sabon haihuwa har an fara taba mata diyanta,,,,,
    Joseph dake tsaye nisa kadan yace No mu ba.u san cewa tana gurin ba ,,aida bamu zo ba gakiya,
  Karatu malam yaci gaba dayi har wani lokaci, sannan suka ce zasu tafi masauki har zuwa gobe,
  Masauki mai kyau aka kai,su, inda har zuwa yanzu Joseph bawai ya yarda da zancen su malam bane tunda yaga pastor ma yayi yagaza, aganin shi aiduk guda ne,
   Sosai malam yatashi cikin dare yai aiki irin yadda yakamata har na tsawon kwana bakawai,
   Cikin daren na bakwai din ne, malam yakammala da su mazauna gurin na boye,
  Tunda safe suka shirya shida sauran malamai zuwa gurin da ake yin ma,aikatar,
   Kamar kullun saidai yau gumzar yarage so sai fiye da kullun,
  Sai iska ke kadawa kamar hadarin sabon damana,
  Su malam sai karatu suke zubawa , tamkar zasu tashi sama,
  Allahu Akbar, Kabiran Allah mai girma dadaukaka,
  Wani irin halitta ne kamar macijiya saidai sun ban banta agurin kai da maciji
  Yafito cikin wani rami da yaran shi zaban tsoro, duk wanda ke gurin, saida hankalin shi ya tashi,
  Hanyar gabas suka bi uwar na gaba ana wani irin kuka kamar na agwagwa,
  Saida suka gama wucewa ita da yaranta kaf. Sai ga wani shirgegen irin halittan
  Ashe wai shine, na mijin, su, shine yasa, ya tsaya baya, sai kuka sukeyi zabar tausayi, suka harba cikin daji, wani zugun kurmi dake gabas kowa na, kallon su wanda Allah yaba ikon zuwa kallo,
  Saida suka bace wa ganin mutane, sanan Joseph yai wa i irin ajiyar zuciya ya waiga inda malam,Abdullmudalabi yake yai yar murmushi mai kama da yake,
   Suko su malam sai kara cigaba da karatu sukeyi da kara neman wa gurin tsari, na har abada daga sauran ire,iren abun boye wa yan da bamu gani,
  Sosai Joseph mamakin irin wanan baiwar ta su malam yakama shi,
  Saidai kuma yaji muryan malam na cewa ai Alkur,ani maigirma baibar komai ba,,
  Don shi warakane tare da kuma kariya ga duk wani masifa,
  Malam yaci gaba da bayani cewa daga mutane dabboi da aljannu, duk suna amfana daga Alkur,ani mai girma,
  Bayani kala,kala, malam yai ta ma jama,an, dake zagaye da shi suna mamakin wanan ikon Allah,.
   Ranan Sonny yashigo Abuja wanda sai video, kawai na wanan al,ajabin yagani bai samu gani live ba,
  Yacewa Joseph inbadon harda shi yagani cikin video ba da sai yace bada gaske bane,
  Nan dai yakara tambayar, cewa ko anyiwa gurin addu,a sosai,
  Kyauta ma tsoka harda motocin shiga su malam suka dawo dashi akan wanan aikin,
  Shikadai ke cikin dakin shi saboda ya sallami Aisha badon taso wucewa shidai ne ya matsa mata da cewa takoma gida hakanan,
   Waya yake yi da maman Choima da Ejoma yana mai ba su, labarin irin abinda yafaru da su a can sabon gurin da suke aiki,
   Chaaay O there's God woooo,
  Joseph i, warn, u  not to go there , but ,u refused,
   Dis, things go kill person wooo,
  Ranan saida takai shi church don aima spirit, din shi addau,a,
   Sosai yabawa baban shi labarin abinda yafaru da su tsab,
  Baban ne, yace mai ai irin wanan,aikin dama sai irin  malaman din, nan,
 A ran shi yace So even Dad knows something about, dis malams,
   Tundaga wanan ranan Joseph tashiga wani hali acikin zuciyar shi,
  May yasa pastor yakasa yin wanan aikin da su malam sukayi,
   Ko yaushe al,amsrin musulmai is amazing, to him,
  Alhaji Sabo yazo har Abuja don yaiwa, su Joseph ja,je, abinda yafaru dasu,,
  Sunkai wani lokaci zaune tare da dan tsohon mai mutunci da kamala,
   Wanda, ba ruwan shi da,kowa sai al,amarin gaban shi kawai,
   Ana,gobe Alhaji Sabo zai koma Kano, Joseph ya shirya ystafi har masaukin dan Dadtijon,
  Inda yasamay shi yana sallah acikin wani irin natsuwa,
  Duk da ga girma ya kamashi amma sallah shi yakeyi hankali kwance,
   Zaune inda Joseph yake ya kurawa Alhaji sabo ido tamkar yau ya fara ganin ana sallah a rayuwar shi,
  Ganin shi bai sa tsohon yadakatar da sallah ba har sai zuwa lokacin da yakai iya adadin da yake bukatan,
  Sanan ya tsaya yashafa tare da jero kyawan adduoi,
   A hankali ya shafa addu,aan da ya idar a fuskan shi yana yin hamdallah,
  Sai lokacin ya wai,go inda Joseph, yake zaune, ,yana mai yi mai murmushi cikin kulawa,
   Sosai suka tatauna akan harkan business din kada watau cotton, wanda kowa yasan mutanen garin kwantagora da wanan sana,ar,
 Sosai Alhaji yai murna, saboda dama yadade ya son wanan sa,ar, ta kada watau, cotton ,,
   Tafe yake a motar shi yana kallon yada fitilun suka haska,ka titi,
   Abin yadaure mai kai sosai yaya,, za,a ce pastor ya kasa korar wanan abin sai malam,
  Gashi kuma shi malam din yace waida Alkura,ni mai girma suka yi wanan aikin,
   Wani irin ajiyar zuciya yasake don gane yadda al,amarin zancen yake,
 
   Batare da sani kowaba washe gari ranan jumma,a, da musalin shadayar rana,
  Joseph ya shirya yai  shiga mai kyau da ma,ana ya kulle ko ina na gidan shi,
 Makullin motar shi ya sura, yajefa, ta a cikin, aljihu, rigar shi,
   Ta,fe yake a hankali. cikin motar shi duk tunane ya cika mai zuciyar shi fam
  Wani dan guri yasamu nisa da inda yaga jama,a suna ta taruwa,
   Saida ya tabbatar da komai ya kam,mala kamar yadfa yake bukata,,
  A,hankali ya fito ya kulle motar shi ya taka kamar kowa har zuwa cikin haraban, masallacin
  Watau Central Mosque, inda yaga gurin yaimai wani irin mugun cikafam, da al,ummar Annabi,,,
   Kowa sai abinda ke gaban shi yakeyi ba mai magana da wani wasu sallah wasu tasbihi,,
    Wani wanda yagani yana yawo da ani abu kamar tire yaiwa bayanin komai,
  Cikun dauki da zumudi mutumin yai wurin lima yana mai bayani shida sauran members din masallacin,
  A. Wani dan daki aka kai shi,   Anna sallamay sallah liman yafara sanarwa,
Yau Biyu ga wata, zulhaji, wanan bawan Allah mai suna Joseph yakarba shahada,
  Say wani ya rike mai hannun liman na fadin,
  LAILA,HA,ILLANLA MUHAMMADAN RASULLALAH,,,,,
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
   FUREN     JUJI
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
          3鈨�2鈨�

ZAINAB  IDRIS  MAKAWA,

 Abu, kamar wasa magana tafara zagaye gari, cewa Joseph ya musulunta,
  Duk inda dan IBO yake cikin garin kwantagora da kewaye hankalin su ya tashi sosai,
  Don su agare su wanan mugun labari don in, su na son mutuwar su to suna son jin irin wanan labarin,
  Hakalin yan church din su Joseph yai matukar tashi sosai,,
 Meeting suka hada duk wani elder dake a church din ya halarci wanan taron,
  Batare da sanin Mr Ema ba wanda, sam baiyar da cewa dan shi na ita wanan abin ba,
  Saboda su kaf tarahin su basu da yan uwa, musulmai, balle ace danshi ya shiga islama,
   Sun wakilta wasu daga cikin su da zasu tafi har gurin Joseph din su samay shi face to face suji ta bakin shi,
   Saidai sun sha bam,bam da Joseph din don yau yabar Abuja zuwa Lagos gurin kakar shi,
   Sun yi kokarin bincike gurin maigadin shi amma basu gane komai ba don haka suka dawo da mamarai a ran su,
  Shiko Yusuf ya isa Lagos lafiya da yake tafiyan jirgine,
   Barci yayi sosai bayan isar shi sai musalin sha, biyu da rabi yafarka,
  Inda yashiga bayi yai wanka tare da dauro alwala don sallah azuhur,
   Key din motar shi ya dauka zuwa wani massalaci dake cikin unguwar na su,
  Tare da shi aka gabatar da sallah azuhur, na wanan ranan,
   Ibrahim wanda sai yamma yake dawo,wa daga gurin koyon computer da yake zuwa,
  Yadawo cike da murnan ganin Joseph a yazo gari don yasan cewa ganin shi alheri ne babba,
   Amma sai yaji Joseph cikkn yaren IBO yana ce mai yatashi su tafi masallaci kada su rasa jam,i,
  Kamar a farki yaji zancen Joseph din don bai taba tsan manin haka ba daga gare shi,
  Dashi akai jam,i Ibrahim wanda duk imani da,mamaki  ya kashe,shi
  Saida yakasa tambaya don bai san ta ina zai bullo mai ba,
   Yusuf nagama addu,an da yadaga hannuwan shi biyu sama yana,roko tun bayan sallamay sallar ta,su,
   Ya,shafa a fuskan shi da gangar jikin shi baki daya,
  Sai a lokacin, yadan waigo inda Ibrahim yai mutuwar zaune,
  Hannu ya mika mai tankar yadda sunna ta tanadar wa musullumi yai wa dan uwanshi musulmi,
  A, lokacin ne ya mike tare da jawo hannun Ibrahim suka fito daga cikin massalacin,
  Cikin wani irin murya maikama da wanda kasala takama ya fara magana,
   Ibrahim katayani gode ma ubangiji na daya nufe ni da bani ikon gane gaskiya,
  Ibrahim baisan lokacin da ya,rungumay Yusuf ba zuwa jikin shi sai she,shekar kuka yafara,
  Bayan shi Yusuf yadan fara bubugawa shima, yana dan fidda kwalla masu zafi a idon shi,
   Murna yakamata kai min Ibrahim ba kuka ba a wanan lokacin,
  Ibrahim cikin dasashiyar murya irin ta mai kuka yace mai Dad yasani kuwa,
  Murmushi mai daci Yusuf, yayi wanda baikai ciki ba yace bai sani ba tukun, yai yar ajiyar zuciya, yace,
  Amma ,zai sani soon insha Allah,
   Ibrahim zan tafi da kaina in tunkari mahaifina da zance,,
  Duk da nasan hakan zai shafi rayuwar shi ta fan,ni daban,daban,
  Amma hakan ba zaisa in daina abinda nai niyad yiba don kaina,
  Musuluntata bata, jeka nayika bace, Ibrahim,
  Nayita ne don ra,ayin kaina daganin dacewar hakan,
  Yanzu ma na fara zurfafa acikin ta har sai ranan da naji cewa banda sauran numfashi a duniya,
   Don haka na shirya tunkarar duk wani kalubalin da zan samu dayin hakan
   Kara rungumay shi Ibrahim din yayi yana mai cewa masha Allah Allah mungode ma ubangiji Allah ka karawa Annabi daraja da daukaka,
  Yusuf din yakarba da fadin Ameen, tare da hannun Ibrahim don su shiga gida,
  Saidai yaiwa Ibrahim kashedin fada ma su mama yace sai ya fara fada wa, mahaifin shi tukun,
  Ibrahim yace ina mai baka goyon baya brother har zuwa lokacin da zasu gane gaskiyan ka akan hakan
   Ibrahim ya matse hawayen da ya cika mai ido,, yadan kalli Yusuf yace komai ukuba ko tsanani brother kada kabar addinin ka,
  Babana yadade yana maka fatan kasancewa a hakan saiga shi yau Allah ya karba masu addu,an su a cikin sauki,
  Kayi irin musuluntar da ake fatan yin shi domin Allah badon ra,ayin wani abuba,
   Bayan sun shiga cikin gidane maman Choima da har yanzu bata kaunar ganin Ibrahim atare da su, tai mai wani irin kallo na kaidin wa,
   Saboda lokacin da Yusuf baya gari sam baya shiga gidan saboda ita,
A, tare sukaci abinci shida Ibrahim ranan ibrahim wanda bai damu da yadda maman Ejoma ke mai ba.

  Bayan kwana biyu Yusuf, Joseph, ya shirya masu tafiya gaba dayan su zuwa Niger, State,
   Tun safe sai zuwa magrib suka isa, cikin garin a gagauce Joseph ya aje su mama yace masu zai kai Ibrahim gida yadawo,
   A,lokacin Mr Ema yana kofar gidan shi kamar yadda dattijan arewa ke zama a kofar gidajen su,
   Gani Joseph din yasa shi jin sanyi aran shi don yasan cewa zai wanke zargin da yan church din su ke mai,
  A,masallavin uguwar jankidi, indagidan Abdullsamad yake nan sukayi sallah su atare da mutane
  Murna gurin, Abdullsamad bai ko musaltuwa,
    Yai ma Yusuf nasiha akan yadda zai tunkari mahaifin shi akan zancen,
  Da murna sosai mahaifin nashi tare da yan uwan shi suka tare shi,
  Sai murna sukeyi da zuwan shi fiye da yadda ma kullun da yake zuwa,sukeyi
   Sun ci abinci kamar yadda aka saba sun  dan fara,hira can, mahaifin shi ya jefo zancen,
  Musuluntar da ake cewa yayi a,gari inda har mutanen, su sunfara yimai wani kallo,
  Joseph yadan sunkuyar da kan shi kasa ahankali, sai yadago sukayi ido biyu da mahaifin nashi,
   Yusuf yace a hankali is true Dad iam now Muslim,
Cike da mamaki mahsifin nashi da mama suna kojarin hada baki gurin tambayan, abinda su,ka ji kamar yace,
   Yusuf yadan yi shiru can yace Iam Muslim now,
  Cikin wani irin fushi mahaifin shi ke magana acikin harshen IBO
  Mafarki kakeyi Joseph ko ko wasa,indan har haka kai ma,za kadaina don ban son irin,hakan,
   Baba bawasa acikin zance na sam, gaskiya nafada bana cikin addinin ku yanzu
  Wani irin ihu Mama choima ta sake wanda yai kama da ihun mutuwa,
   Mr Ema wanda ya suma azaune bai masan ida yake ba alokacin, sai Yusuf din ne ya dan kula,
   Yai kanshi ya na girgizawa a hankali yana mai kiran sunar shi, zuba mai ruwan sanyi yayi, yadan farfado,
   Duk da acikin dare ne suke wanan abin bai hana wasu makwabta jin hayaniyar su ba,
   Abokin Mr Ema ne yashigo lokacin don jin cewa Joseph ya shigo, gari, saboda shim a matse yake da yaji gaskiya don yai wa mutanen su, sheri,
    John yayi matukar kidimay wa don ganin irin yadda abokin shi yake zaune jagwab, sai wani abu yakeyi kamar kaza tasha ruwa,
   Mama Choima wace tsananin rudewa yasa ta faduwa kasa tana ta rusa ihu, da shure shure,
  Tana ta zabga gwalanci cikin yaren su,na IBO duk a kidime take wanan sanbatun,
   Yusuf wanda ahalin yan zu ya mike da ga tsugunin da yai a gaban mahaifin shi,
  Y
Wanda shi da kanshi Mr Eman bayan yafarfado yai wa Yusuf din hannu alamar yajaye daga gurin shi
  Ke nan baya son ganin shi agaban shi Yusuf wanda zuciyar shi tariga ta keykeshi bai jin ashhh,
  Ya mike tsaye batare daya tsaya ko ban hakkuri ba, yakama hanyar zuwa dakin shi,
  Hey stop, there mr man, don't enter my house, pls,
  Yusuf yai tsaye kamar mai tunane nadan wani lokaci sai kuma ya juya kawai yai hanyar fita waje,
  Cikin wani karaji maman choima, ta mike tsaye ta je tasha gaban shi tana mai tare shi da hannu,
  Kada katafi my son idan katafi ,zasu kara rudin ka su cutar dakai da addinin su,
   Mahaifin shi yace mata tabar shi ya tafi tunda yanaganin kamar cewa suna son shine don Allah badon kudin shi suke son suyi amfani da shi ba,
   Yusuf Joseph yadan dago kai yakali mahaifin kamar wanda zaiyi magana sai kuma ya fasa,
  Ganin irin kukan da mama keyi yasa shi juyawa zuwa vikin gidan nasu,
 Mr Ema wanda baikara yunkurin korar dan nashi ba wandda a shirye yake, da yabar gidan,
   Tun shigan shi dakin shi sai yaji duk tausayin mahaifin nashi da kankashi,
   Harma da yan uwanshi da,ke tafaman kuka cikin tashin hankali,
  Amma saidai ina yai nisa ko acikin Isalama, baya jin kira,
  Zima yana mazu fatan Allah yas su gane gaskiya sudawo hanyan gaskiya,
  Sai cikin dare sosai barci yadauke shi, ko shi sama sama,
  Don tabatar wa cewa yana cikin musulunci da shi aka tafi, sallah asuba wanda yai daidai da yadawo daga masallaci sukayi kicibis da maman chiloima
  Wace tafito tin cikin dare takasa barci, suna yin ido biyu dashi sai ta hau wani irn gumza da ihu cikin kuka tana magana kamar mara hankali,
   Kai kawai yakada yana mai murmushi abinda yaga tanayi wanda shi sam tama fara bashi dariya a,lokacin
  Acikin takon shi maikama da kasaita, yafito,
  Bakajin komai mai sai karan takon takalmin shi daya karade falon
   Zazzaune suke kowanin su ya kurawa abincin dake saman table din ido,
  Wanda sam yau duk kyau abincin bai,basu sha,awa,
  Fita yai niyar yi a,lokacin, batare da yako kalli inda suke zaune ba,
  Mama ce tai karfin halin yimasa magana da cewa son kazo kaci abinci kafin kafita,
  Mahaifin shi wanda yai kicimkicim da fuska, ya zauna ya hade hanna yen shi guri guda yatokare habar shi da su,
    Yusuf wanda alokacin yafara kyamar abincin su don ganin irin dan bujen dake ajikin su ga,wani gashi doki da suka jibga,akan su,
    Inda take ya,dan taka cikin tako irin nashi ya dan rungumota tabaya yana cewa yanzu zai dawo ai bazai dade ba ai,
    Cikin fushi Mr Ema yace ya sake ta tunda baidamu da damur su ba,
  Sai yanzu yagane komay yasa tun farko ya ke bin diyan hausawa da musulmai
   Mr Ema cikin daga murya yake fada da Yusuf yana cewa,
  Tunda naga mahaifiyar ka ta haife ka  lokacin watan da musulmai suke azumi,
  Har suna zo muna murna wai na haifi, yaron lokaci mai kyau,,,,
  Sai yadukar dakai kasa cikin bacin rai yakasa cigaba da bayanin dayakeyi,
  A wanan lokacin members na church din su sun kai su goma sha, suka shigo,
  Daya bayan daya Yusuf yakalle su basai an fada mai ba yasan komay ke tafe dasu daga shi har mahaifin nashi,
  Kallo guda Yusuf yai masu ya kauda kai don dai kawai bazai ita masu rashin kunya bane da halin shi da yau yai masu,
 Wani dan tsamurare daga vikin su maikamar shagada
  Yace Joseph what's going on pls,?
  A hakali yadago kai da idon shi da yai jawur yace,
  Iam now Yusuf not Joseph
  Mamaki karara a fuskan su wanan ya kalli wanan wancan ya kalli wancan,
  Maman Choimal wace sai hawaye takeyi cikin tashin hankali, ta na dan kada kafar ta cikin fitina,
    Wani daga cikin mutanen wanda bai,karkare kai sauran shekaru ba ya ce Umm,ba,
  Look mr let's have a serious talk pls,
  Yafara magana acikin yaren su, kamar hakan ga,
  Joseph may yasa kai wanan clash, din pls,
  Mace, dukiya, ko suna, friendship?
Ido Yusuf ya kura mai don shi dai ma tausayi yake bashi shi mai maganar alokacin,
  Don haka murmushin takaici yai mashi yana mai sauraren shi a natse,
   Mai maganar yaci gaba da cewa idan har saboda soyayya ka koma ai muma muna da mata madu kyau daga cikin mu,
  Idan kuma dukiya kake bukatan kari kafadi daga milliyan zuwa sama zamu hada maka
  Haka kuma idan suna kake,,,,
  Da hannu Yusuf ya dakatar dashi alamar ya isa hakanan
 Baison karasa sauran shirmayn fon jin maganar yakeyi kamar may tatsuniya,
  Sosai yabude idon shi yau gare su yafara da cewa,
  Kudi mace, suna  duk ni Alhamdullah, yana,mai pointing din kan shi,
  Ra,ayi ne kawai bawai don wani abuba nashiga nadaiyi nazari naga cewa itace hanya mafificiya, dazata fissheni, arayuwata,
   Daga haka yamike yana mai hada hannayen shi gurin daya yana cewa da kaga yai pls kada wanda ya kara maganarr,
  Daga haka yasa kai fuu, yafita ya gidan batarecda yai ma kowa sallama ba,
 



ZEEE    MAKAWA,,,,,
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
   FUREN     JUJI
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
            3鈨�1鈨�

ZAINAB IDRIS MAKAWA,,,

Yan,uwa dan girman Allah ku tayi rokon Allah ya yafe min akan typing erow, da nasamu,
  Tun jiya duk ina cikin rudani wallahi bayan nagama na yi posting ina karanta, wa sai naga inda yanu min wai suratul Suleiman,
   Ina fatan dani daku Allah zai yafe muna,
Ina tajiran gyara daga gare kuma tun jiyan amma sai naji shiru shiyasa nafito da kaina na nuna maku gurin, dafatan zaku yafe min,馃憦馃憦馃憦馃憦馃憦馃憦馃憦


Tunda ya furta wanan kalman sai ji yayi jikin shi yai mai wani irin sanyi, duk baida wani lakka, ko kuzari,
  Muryam liman ce tadawo dashi inda yake yana cewa, welcome to Islam
   Which name do u, want, in islam, neme,
  Joseph yakada kai yana mai cewa, a,a I will used my normal name Yusuf,
  Masha Allah in ji liman,
  You have a beautiful, name, my son ,
  May Allah bless, u for the rest of your life,,,
   Daga haka aka fara shirin yi mai sadaka fisabillilah,
  Hannu yadaga yana mai nuna godiya da cewa ya yafe abar ma massallaci
    Liman yai mai alkawari da cewa duk lokacin da yake son karin haske  yana iya zu don ai mai,
  Tafe yake a cikin motar shi yana sharara gudu zuwa gidan shi dake Girki,
   Yana shiga maigadi ya bude mai get,da gudu ya shige kamar wanda ake bi a baya,
  Baitsaya ko ina ba sai bakin fridge yadauko kwalban wani drinks mai kamshi
  Gaba daya ya tsotse stewvery, din ya wurgar da kwalban,
   Saman kujera dake cikin falo ya zauna jagab gaba daya yazube a sama,
  Yadafe kan shi,da hannu shi guda guda kuma ya rike gefen kujerar da yake sama kwan ce,
  Dad ya furta a, hankali, sai kuma sai ya furzar da yar iska daga bakin shi,
   Daga kwancen ya rintse idon shi sai kuma ya mike zubar yashige cikin bed room din shi,
   Wanka yayi yafito cikin shigar shi ta wani yadi mai dan laushi,
  Makulin motar shi ya dauka bai tsaya jiran komai ba ya kulle gidan, yafita,
   Direct wani shago dayake yawan wucewa a cikin erea, one, yanufa,
  Islamic center, aka rubuta bar,baro, agurin, bai tsaya jiran komai ko tambayan wani ba
  Inda yaga an rubuta Books Shop center, da kuma, ya shiga,
  Nan ya fara yar zagayawa a, hankali yana diban ire,iren littatafan da suke dashi,
  Idon shi yakai akan wani littafi da akai ma wani ado da green flowers,An yi,rubutu kamar haka
  TEACH YOUR SELVE ISLAM,,,,
  Yadauka sai kuma idon shi ya hango mai gurin saida  cassette, nan ma yadiba yaga inda aka rubuta Suffatin Sallatin Nabiyi,
  Ire, iren wa yan, nan abubuwar koyar da,addini a saukake, ya saye aguri inda yabiya su kudin su ya fita,
   Cassette din ya fara sawa inda ya tashi daidai lokacin sallah la,asar,
  Yadinga yin yadda duk mai koyarwan na cikin cassette din ke yin kwatance,
   Har kusan dare ya kulle shi kadai a cikin gida,yana ta koyan yadda malam ke koyar da sallah a,cikin harshen hausa da turanci,
  Kafin wani lokaci yadan hadda,ce abin da ya sauwaka akai,,
  Kwanan shi biyu cikin gida bai fita ko ina ba saidai yana waya da maman choima da Ejoma,
  脌mma dai duk sun fahinci cewa kamar bai jin dadin jikin shi
  Don haka suke ta bugo mai waya, akai kai don jin ko may ke damun shi,
   Yadan fita waje ya sha iska don ya mike kafaer shi,
  Koda ya dawo sai ganin miscall, din Anty Dije yayi har biyu,
  Sai a,lokacin yadan ji kamar dan nishadi a ran shi,
  Fadar Asalamu Alaikum kalmace da tun yana yaro yahaddace ta akan shi don haka yau ma maimakon fadar hello da yasaba fada yau ga mamakin Anty Dije sai taji ya ce mata,
  Assalamu Alaikum warahamatul,
  Jin abin Anty tayi wani banbarakwai kamar bata taba jin kalman ba,
   Sai,ma ta rasa abinda zatace ansa, mai, dashi,
  Joseph yakake kwana biyu,
 Yaune karo na farko, da ya taba jin haushin sunan shi,
  Sai kuma a yanzu ya tabbatar wa kanshi da ya musulunta na tsakani da Allah,
  Littatafai da cassette din da yasayo na addini sun taimaka mashi so,sai gurin wayar da kai,
  Don ya samu haske sosai ta wanan hanyar, karatun da kallon da ya kashe kwana biyu yana koya daga malamai masu hikima,a saukake,
  Murmushi yaiwa anty kawai don jin Joseph din da tace mai,
  Anty kuna lafiya ya, jikin ki ya yara, ta amsa mai da lafiya kalau wallahi,
  Ya, aiki Joseph ina fatan kun rarage dai ko, sai kuma yakara ba Anty Dije mamaki da cewa wallahi Anty Dije aiki Alhamdullah,
  Wanan karon mamaki saida yasa tadan daga wagar dake hannun ta  ta dan kalla kamar wayar ne Joseph, din,
   Bayan gama wayan nasu ne, mamaki duk ya cika,Anty Dije don jin sabbin kalaman da Joseph yau yake furtawa gare ta,
   Amma sai ta danga ta hakan da yawan zaman da yake yi cikin musullumai hausawa,
  Don akasarin Christian din arewa da wuya ka iya banbanta su da musullumai,
  Saboda akidojin su duk kusan irin na hausawa ne ita al adan hausa na isalamace,
   Daga haka kawai sata basar bata kawo komai aranta, ba gamay da Joseph din,
   Yau Monday yafito da shirin zuwa gurin aiki su inda suke son ya bunkasa masu,
  Mutum na farko da yafara kiran Joseph shine Alhaji, Sabo,
   Jin yadda Joseph yai mai sallama yasa shi saurin cewa Joseph nake magana da shi pls,
  Amma sai Joseph din yace, mai Yusuf dai ko,?
     Mamakin abin da Joseph din ya ce, Alhaji ke yi
  Cikin ba,a yace mai ato dayake ku a wurinku Joseph da Yusuf gudane ba
   Alhaji dani dakai yanzu duk guda ne ga cewa Annabi Mohammad SAW,
   May kake nufin fada min newai,
  Maganar gaskiya Alhaji, shine nayi shahada ni ma, cikin yardan ubangiji,
  Allah,hu, Akbar,Allahu,Akbar, yace har sau uku, yai mai fadal Alhamdullahi, Alhamdullah,
  Nayi maka murna dan uwa barka da shigo cikin wanan hasken,
  Alhaji sabo bai bata lokaci ba ya shigo Abuja gurin Yusuf,
   Wanan zuwan na Alhani sabo taiwa Yusuf dadi sosai don ya kai shi gurin manyan malamai na addini sunkara haska mai haske ga abubuwa,
   Sunyi mamakin yadda cikin dan lokaci kadan har ya haddace, wasu abubuwa masu amfani sosai daga addini,
   KB yadawo daga weekend din da suka tafi yi gida, don haka kai tsaye suka wuce gidan Joseph don su gana dashi akan rikicin da ya taso a ma,aikatar su jibrin 
  Tundaga kofar da zai sadaka da cikin falon zaka ji karatun alkur,ani mai girma na tashi cikin muryan wani matashi mai zakin murya,
  Wani irin kallon mamaki sukai wa junan su, alokaci guda,
  Cak Jibrin ya tsaya don a ganin shi ba gidan shi bane suka zo wata,kila sunyi batar kai ne,
  KB nai yai kundun balar shiga cikin gidan kai saye,
  Daidai lokacin da yake ruku,u, a cikin raka,a ta biyu,
  Nunfashin su ne ya tsaya cak, kamar a mafarki suke ganin abin don sam basu taba tsan,manin haka ba,
   A,lokaci guda suka, kali junan su tare da kara matsawa kusa da inda yakai goshin shi a kasa yana sujada,
   Cikin mamaki suka karasa gab dashi suna mai wani irin kallo,
  Yusuf din ne dai yai sallamay sallah shi yana mai daga hannu yana addu,a,
  Har kasa inda yake zaune suka durkusa suna mai kallon shi a cikin mamaki,
  Yana shafawa gabadayan su suka rungumo shi zuwa jikin su
 Kowansu sai hawaye yake fitar wa don murna,
  Shiko Yusuf ya rasa ko kukan may yakeyi, daga ciki,
   Bayan sun samu natsuwane, suka bukaci dan, jin sanadin wanan abin,
  Bai boye madu sanadin shigar shi ba da dalilai dayasa har yai sha,awan shiga wanan akidar ta isalama,
   Shiru sukayi nadan lokaci gudu jin yadan dakatane gaba dayan su sukayi hamdallah,
  Jibrin yace masha Allah irin musuluntar da ake so Allah yabaka, ,
  Badon wani bukata ba,
  Badon mace ba,
  Sanan badon yin suna ko kwadayin wani abuba,
  Gaskiya mun gode ma Allah daya baka dama da ikon shigowa cinkin musulunci,
  Allah ubangiji  yabaka, ikon bauta,madhi acikin tsarkakaken zuciya,
  Suka amsa dafadin Ameen,gaba dayan su a lokaci guda,
  Jibrin ne yace Old man yasani kuwa, acewan mahaifin Yusuf din,
   Yusuf yadan gyara zaman shi yasa kan shi saman kujera mafi kusa da shi,
   Saida yanisa sanan yace nasan zamu kwasa dashi sosai
  Amma dai insha Allah ba matsala Allah zai kawo saukin abin,
  Nan dsi sukai ta hiran su ,cikinjin dadi da a,nan shuwa,
  Wanan zancen kamar an harba bindiga a kasuwa ne don nan a nan labari ya cika kwantagora cewa Joseph ya musulunta,,,
   Wasu nacewa karyane wasu, nace ai hakan zai iya yuyuwa idan sunyi la,akari da irin halinshi
    Abukamar yaki agidan su Joseph din don mahahaifin shi kamar mahaukaci ya koma, da yasamu labari
  Sam bai yarda ba kiran Joseph din yayi a waya, Mr Ema tare da sauran abokanshi
Zaune ansa, waya a handfree anajira aji Joseph din abinda zai ce
 Kamar bazai dauki wayan ba don yasan akan,maganar da za,ai masa,
 Sai dai  ya daure yadauka muryan dan nashi yaji  ,,normal saida yadan girgizakadan,
  Joseph yes Dad, ya karba,mai kamar yadda yasaba ansawa, idan ya,kirashi
    I,want to know the true, of what, we hard here about your,
  Baba what's going on there, now,?
  Nan baban nashi ke fada mai cikin fada, cewa yarabashi yawo da yaran hausawa ga irin disgrace din da suka jamai
  Fada sosai baban yakamayi sukima sauran mutanen dake gurin sai cewa sukeyi,
  Ehhyya congurat, wooo,
Na,now we hear the true,
  Wani iska mai zafi ya furzar tare da shafo kanshi har zuwa kasan wuyan shi,
   Abubuwa da dama yake sakawa aran shi gamay da maganar mahaifin nashi,
   Baikai ga mafita ba har tashi zuwa yin sallah, don lokaci da yaga yagabato mai,
   Can wani unguwa mai nisa yake zuwa yin sallah, tare da mutane,
Tun lokacin da yaji cewa, yin sallah acikin jam,i yafi lada,

Anty Dije ranan da maigidanta yabugo mata yana fada mata,
  Jin maganar tayi kamar a mafarki, alokacin,wani irin ihun murna tayi tana cewa Alhamdullaha, Alhamdullah,
  Allah mun gode ma,
Joseph ya musulunta, maryam wace har takawo kofan falo alijacin taja tai tsaye,
  Musuluntafa Anty, kikace,
  Wanan kasurgumin Arne ai yayi nisa ko,
  Subbahanallah Maryam bari mana, musulmi ne fa yanzu shima

Yau ba yawa kuyi hakkuri pls,馃憦馃憦馃憦馃憦馃憦

ZEEE MAKWA
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
   FUREN     JUJI
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
          3鈨�2鈨�

ZAINAB  IDRIS  MAKAWA,

 Abu, kamar wasa magana tafara zagaye gari, cewa Joseph ya musulunta,
  Duk inda dan IBO yake cikin garin kwantagora da kewaye hankalin su ya tashi sosai,
  Don su agare su wanan mugun labari don in, su na son mutuwar su to suna son jin irin wanan labarin,
  Hakalin yan church din su Joseph yai matukar tashi sosai,,
 Meeting suka hada duk wani elder dake a church din ya halarci wanan taron,
  Batare da sanin Mr Ema ba wanda, sam baiyar da cewa dan shi na ita wanan abin ba,
  Saboda su kaf tarahin su basu da yan uwa, musulmai, balle ace danshi ya shiga islama,
   Sun wakilta wasu daga cikin su da zasu tafi har gurin Joseph din su samay shi face to face suji ta bakin shi,
   Saidai sun sha bam,bam da Joseph din don yau yabar Abuja zuwa Lagos gurin kakar shi,
   Sun yi kokarin bincike gurin maigadin shi amma basu gane komai ba don haka suka dawo da mamarai a ran su,
  Shiko Yusuf ya isa Lagos lafiya da yake tafiyan jirgine,
   Barci yayi sosai bayan isar shi sai musalin sha, biyu da rabi yafarka,
  Inda yashiga bayi yai wanka tare da dauro alwala don sallah azuhur,
   Key din motar shi ya dauka zuwa wani massalaci dake cikin unguwar na su,
  Tare da shi aka gabatar da sallah azuhur, na wanan ranan,
   Ibrahim wanda sai yamma yake dawo,wa daga gurin koyon computer da yake zuwa,
  Yadawo cike da murnan ganin Joseph a yazo gari don yasan cewa ganin shi alheri ne babba,
   Amma sai yaji Joseph cikkn yaren IBO yana ce mai yatashi su tafi masallaci kada su rasa jam,i,
  Kamar a farki yaji zancen Joseph din don bai taba tsan manin haka ba daga gare shi,
  Dashi akai jam,i Ibrahim wanda duk imani da,mamaki  ya kashe,shi
  Saida yakasa tambaya don bai san ta ina zai bullo mai ba,
   Yusuf nagama addu,an da yadaga hannuwan shi biyu sama yana,roko tun bayan sallamay sallar ta,su,
   Ya,shafa a fuskan shi da gangar jikin shi baki daya,
  Sai a lokacin, yadan waigo inda Ibrahim yai mutuwar zaune,
  Hannu ya mika mai tankar yadda sunna ta tanadar wa musullumi yai wa dan uwanshi musulmi,
  A, lokacin ne ya mike tare da jawo hannun Ibrahim suka fito daga cikin massalacin,
  Cikin wani irin murya maikama da wanda kasala takama ya fara magana,
   Ibrahim katayani gode ma ubangiji na daya nufe ni da bani ikon gane gaskiya,
  Ibrahim baisan lokacin da ya,rungumay Yusuf ba zuwa jikin shi sai she,shekar kuka yafara,
  Bayan shi Yusuf yadan fara bubugawa shima, yana dan fidda kwalla masu zafi a idon shi,
   Murna yakamata kai min Ibrahim ba kuka ba a wanan lokacin,
  Ibrahim cikin dasashiyar murya irin ta mai kuka yace mai Dad yasani kuwa,
  Murmushi mai daci Yusuf, yayi wanda baikai ciki ba yace bai sani ba tukun, yai yar ajiyar zuciya, yace,
  Amma ,zai sani soon insha Allah,
   Ibrahim zan tafi da kaina in tunkari mahaifina da zance,,
  Duk da nasan hakan zai shafi rayuwar shi ta fan,ni daban,daban,
  Amma hakan ba zaisa in daina abinda nai niyad yiba don kaina,
  Musuluntata bata, jeka nayika bace, Ibrahim,
  Nayita ne don ra,ayin kaina daganin dacewar hakan,
  Yanzu ma na fara zurfafa acikin ta har sai ranan da naji cewa banda sauran numfashi a duniya,
   Don haka na shirya tunkarar duk wani kalubalin da zan samu dayin hakan
   Kara rungumay shi Ibrahim din yayi yana mai cewa masha Allah Allah mungode ma ubangiji Allah ka karawa Annabi daraja da daukaka,
  Yusuf din yakarba da fadin Ameen, tare da hannun Ibrahim don su shiga gida,
  Saidai yaiwa Ibrahim kashedin fada ma su mama yace sai ya fara fada wa, mahaifin shi tukun,
  Ibrahim yace ina mai baka goyon baya brother har zuwa lokacin da zasu gane gaskiyan ka akan hakan
   Ibrahim ya matse hawayen da ya cika mai ido,, yadan kalli Yusuf yace komai ukuba ko tsanani brother kada kabar addinin ka,
  Babana yadade yana maka fatan kasancewa a hakan saiga shi yau Allah ya karba masu addu,an su a cikin sauki,
  Kayi irin musuluntar da ake fatan yin shi domin Allah badon ra,ayin wani abuba,
   Bayan sun shiga cikin gidane maman Choima da har yanzu bata kaunar ganin Ibrahim atare da su, tai mai wani irin kallo na kaidin wa,
   Saboda lokacin da Yusuf baya gari sam baya shiga gidan saboda ita,
A, tare sukaci abinci shida Ibrahim ranan ibrahim wanda bai damu da yadda maman Ejoma ke mai ba.

  Bayan kwana biyu Yusuf, Joseph, ya shirya masu tafiya gaba dayan su zuwa Niger, State,
   Tun safe sai zuwa magrib suka isa, cikin garin a gagauce Joseph ya aje su mama yace masu zai kai Ibrahim gida yadawo,
   A,lokacin Mr Ema yana kofar gidan shi kamar yadda dattijan arewa ke zama a kofar gidajen su,
   Gani Joseph din yasa shi jin sanyi aran shi don yasan cewa zai wanke zargin da yan church din su ke mai,
  A,masallavin uguwar jankidi, indagidan Abdullsamad yake nan sukayi sallah su atare da mutane
  Murna gurin, Abdullsamad bai ko musaltuwa,
    Yai ma Yusuf nasiha akan yadda zai tunkari mahaifin shi akan zancen,
  Da murna sosai mahaifin nashi tare da yan uwan shi suka tare shi,
  Sai murna sukeyi da zuwan shi fiye da yadda ma kullun da yake zuwa,sukeyi
   Sun ci abinci kamar yadda aka saba sun  dan fara,hira can, mahaifin shi ya jefo zancen,
  Musuluntar da ake cewa yayi a,gari inda har mutanen, su sunfara yimai wani kallo,
  Joseph yadan sunkuyar da kan shi kasa ahankali, sai yadago sukayi ido biyu da mahaifin nashi,
   Yusuf yace a hankali is true Dad iam now Muslim,
Cike da mamaki mahsifin nashi da mama suna kojarin hada baki gurin tambayan, abinda su,ka ji kamar yace,
   Yusuf yadan yi shiru can yace Iam Muslim now,
  Cikin wani irin fushi mahaifin shi ke magana acikin harshen IBO
  Mafarki kakeyi Joseph ko ko wasa,indan har haka kai ma,za kadaina don ban son irin,hakan,
   Baba bawasa acikin zance na sam, gaskiya nafada bana cikin addinin ku yanzu
  Wani irin ihu Mama choima ta sake wanda yai kama da ihun mutuwa,
   Mr Ema wanda ya suma azaune bai masan ida yake ba alokacin, sai Yusuf din ne ya dan kula,
   Yai kanshi ya na girgizawa a hankali yana mai kiran sunar shi, zuba mai ruwan sanyi yayi, yadan farfado,
   Duk da acikin dare ne suke wanan abin bai hana wasu makwabta jin hayaniyar su ba,
   Abokin Mr Ema ne yashigo lokacin don jin cewa Joseph ya shigo, gari, saboda shim a matse yake da yaji gaskiya don yai wa mutanen su, sheri,
    John yayi matukar kidimay wa don ganin irin yadda abokin shi yake zaune jagwab, sai wani abu yakeyi kamar kaza tasha ruwa,
   Mama Choima wace tsananin rudewa yasa ta faduwa kasa tana ta rusa ihu, da shure shure,
  Tana ta zabga gwalanci cikin yaren su,na IBO duk a kidime take wanan sanbatun,
   Yusuf wanda ahalin yan zu ya mike da ga tsugunin da yai a gaban mahaifin shi,
  Y
Wanda shi da kanshi Mr Eman bayan yafarfado yai wa Yusuf din hannu alamar yajaye daga gurin shi
  Ke nan baya son ganin shi agaban shi Yusuf wanda zuciyar shi tariga ta keykeshi bai jin ashhh,
  Ya mike tsaye batare daya tsaya ko ban hakkuri ba, yakama hanyar zuwa dakin shi,
  Hey stop, there mr man, don't enter my house, pls,
  Yusuf yai tsaye kamar mai tunane nadan wani lokaci sai kuma ya juya kawai yai hanyar fita waje,
  Cikin wani karaji maman choima, ta mike tsaye ta je tasha gaban shi tana mai tare shi da hannu,
  Kada katafi my son idan katafi ,zasu kara rudin ka su cutar dakai da addinin su,
   Mahaifin shi yace mata tabar shi ya tafi tunda yanaganin kamar cewa suna son shine don Allah badon kudin shi suke son suyi amfani da shi ba,
   Yusuf Joseph yadan dago kai yakali mahaifin kamar wanda zaiyi magana sai kuma ya fasa,
  Ganin irin kukan da mama keyi yasa shi juyawa zuwa vikin gidan nasu,
 Mr Ema wanda baikara yunkurin korar dan nashi ba wandda a shirye yake, da yabar gidan,
   Tun shigan shi dakin shi sai yaji duk tausayin mahaifin nashi da kankashi,
   Harma da yan uwanshi da,ke tafaman kuka cikin tashin hankali,
  Amma saidai ina yai nisa ko acikin Isalama, baya jin kira,
  Zima yana mazu fatan Allah yas su gane gaskiya sudawo hanyan gaskiya,
  Sai cikin dare sosai barci yadauke shi, ko shi sama sama,
  Don tabatar wa cewa yana cikin musulunci da shi aka tafi, sallah asuba wanda yai daidai da yadawo daga masallaci sukayi kicibis da maman chiloima
  Wace tafito tin cikin dare takasa barci, suna yin ido biyu dashi sai ta hau wani irn gumza da ihu cikin kuka tana magana kamar mara hankali,
   Kai kawai yakada yana mai murmushi abinda yaga tanayi wanda shi sam tama fara bashi dariya a,lokacin
  Acikin takon shi maikama da kasaita, yafito,
  Bakajin komai mai sai karan takon takalmin shi daya karade falon
   Zazzaune suke kowanin su ya kurawa abincin dake saman table din ido,
  Wanda sam yau duk kyau abincin bai,basu sha,awa,
  Fita yai niyar yi a,lokacin, batare da yako kalli inda suke zaune ba,
  Mama ce tai karfin halin yimasa magana da cewa son kazo kaci abinci kafin kafita,
  Mahaifin shi wanda yai kicimkicim da fuska, ya zauna ya hade hanna yen shi guri guda yatokare habar shi da su,
    Yusuf wanda alokacin yafara kyamar abincin su don ganin irin dan bujen dake ajikin su ga,wani gashi doki da suka jibga,akan su,
    Inda take ya,dan taka cikin tako irin nashi ya dan rungumota tabaya yana cewa yanzu zai dawo ai bazai dade ba ai,
    Cikin fushi Mr Ema yace ya sake ta tunda baidamu da damur su ba,
  Sai yanzu yagane komay yasa tun farko ya ke bin diyan hausawa da musulmai
   Mr Ema cikin daga murya yake fada da Yusuf yana cewa,
  Tunda naga mahaifiyar ka ta haife ka  lokacin watan da musulmai suke azumi,
  Har suna zo muna murna wai na haifi, yaron lokaci mai kyau,,,,
  Sai yadukar dakai kasa cikin bacin rai yakasa cigaba da bayanin dayakeyi,
  A wanan lokacin members na church din su sun kai su goma sha, suka shigo,
  Daya bayan daya Yusuf yakalle su basai an fada mai ba yasan komay ke tafe dasu daga shi har mahaifin nashi,
  Kallo guda Yusuf yai masu ya kauda kai don dai kawai bazai ita masu rashin kunya bane da halin shi da yau yai masu,
 Wani dan tsamurare daga vikin su maikamar shagada
  Yace Joseph what's going on pls,?
  A hakali yadago kai da idon shi da yai jawur yace,
  Iam now Yusuf not Joseph
  Mamaki karara a fuskan su wanan ya kalli wanan wancan ya kalli wancan,
  Maman Choimal wace sai hawaye takeyi cikin tashin hankali, ta na dan kada kafar ta cikin fitina,
    Wani daga cikin mutanen wanda bai,karkare kai sauran shekaru ba ya ce Umm,ba,
  Look mr let's have a serious talk pls,
  Yafara magana acikin yaren su, kamar hakan ga,
  Joseph may yasa kai wanan clash, din pls,
  Mace, dukiya, ko suna, friendship?
Ido Yusuf ya kura mai don shi dai ma tausayi yake bashi shi mai maganar alokacin,
  Don haka murmushin takaici yai mashi yana mai sauraren shi a natse,
   Mai maganar yaci gaba da cewa idan har saboda soyayya ka koma ai muma muna da mata madu kyau daga cikin mu,
  Idan kuma dukiya kake bukatan kari kafadi daga milliyan zuwa sama zamu hada maka
  Haka kuma idan suna kake,,,,
  Da hannu Yusuf ya dakatar dashi alamar ya isa hakanan
 Baison karasa sauran shirmayn fon jin maganar yakeyi kamar may tatsuniya,
  Sosai yabude idon shi yau gare su yafara da cewa,
  Kudi mace, suna  duk ni Alhamdullah, yana,mai pointing din kan shi,
  Ra,ayi ne kawai bawai don wani abuba nashiga nadaiyi nazari naga cewa itace hanya mafificiya, dazata fissheni, arayuwata,
   Daga haka yamike yana mai hada hannayen shi gurin daya yana cewa da kaga yai pls kada wanda ya kara maganarr,
  Daga haka yasa kai fuu, yafita ya gidan batarecda yai ma kowa sallama ba,
 



ZEEE    MAKAWA,,,,,












[1:32PM, 2/26/2018] 鈥�+234 814 858 5998鈥�: 馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
  FUREN     JUJI
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
            3鈨�4鈨�
ZAINAB IDRIS MAKAWA,,,

  Barkan da jumma,a yan ,uwa Allah ubangiji yasada mu da alherin dake cikin wanan ranar mai albarka,馃憦馃憦馃憦


Maganar da Abdulsamad ya fadawa Yusuf gamay da mahaifin shi ya tsaya mai arai, sosai,
  Don haka yasan cewa ko shi bai tsira ba ke nan don mahaifin nashi zai iya yin fiye da haka akan church din nasu,
   Don haka ya sa a,zuciyar shi cewa, dole ya dauki duk wani mataki wanda yasan cewa ,za,a iya kawo mai hari akai,
   Washe gari ya kasance ranar jumma,a ce, don haka tunda zai fito ya fito da kayan da zai shirya kanshi a ciki
  Don barci kawai yakaishi gidan su cikin dare sai dai ya kula da cewa kamar an,masa bincike a dakin,
   Murmushi yake yayi shi kadai a cikin dakin, don haka duk wani abin da yake bukata ya hada su guri guda,
  Tunda safe da zai fita yakwasa sai gidan, 脌nty shi Dije itace yakai wa ajiyar kayan shi masu muhinmanci, dake gidan nasu,
   Maryam wace ke zaune a lokacin gaban mirrow tana make-up,
  Taji muryan shi ya na ta kwada sallama akofar shigowa gidan ,
 Haka kawai taji zuciyar ta ya tsinke mata, kamar mai tsoro,
   Zubur ta dan yi ta mike a gaban mirrow saboda ta sheda ko muryan waye, ke sallamar,
   Saidai, yau ta tsinci kanta da dan jin nauyin ansa mai sallamar tashi,
   Saboda irin yadda tai hating din shi a matsayin shi na Christian a da,
   A,ciki ciki ta ansa mai sallamar tashi, kamar wace ke rowar magana,
   Dankwalin da tafara daurawa rike a hannun ta tadan leko tawaje don tabashi izinin shigowa ciki,
  Saboda Anty Dije tana bayi gurin wanka alokacin,
  Ido biyu sukayi dashi, yana saye da wata riga mai hannu iya damtsen hannu, sai wani dan ado da akaiwa hannun rigar kamar kwalar riga ta wuya,
   Shima wuyar rigan irin hannun rigar ce akai yi ta,
  Sannu da zuwa ta furta acikin muryan ta makama da ta rowa kullun,
  Sai kuma can tace tadan shiga wanka yanzu zata fito
  Abinda kawai ta iya fada ke nan a darare, kamar mai jin tsoro,,
  Fuskan shi a natse kamar kulun yace ba matsala ga wanan pls ki bata ta aje min zan je in dawo,
   Sigar da yake maganar shiya sata dan dukar dakai don komai nashi a kasaice yakeyin shi,
   A, hankali yatako har, gaban,ta ya mika mata jarka
  Wace batasan ko tamaye ba,ita,dai ta karbane kawai,
  Har yabar gidan tana tsaye a inda ya barta rike da jarkar da ya miko mata,
   Karar rufe kofar shiga gidan ce tasa,
  Da sauri ta juya zuwa ciki, sai yanzu ma taji haushin fitar da tayi da tasani ma kawai ta amsa mai ata cikin daki,
   Turus tayi a folon ganin, 脌nty Dije zaune tana shiri abinta acikin natsuwa,
  Anty ce tace tomay zance tunda kin ce masa na shiga wanka ko,
  Inda take ta nufa da jakar ta aje saman wani kujera tafita batare da tai wani magana ba,
   Yusuf kuwa yana barin gidan su Anty, kasuwa yatafi
  Abinda yaksi shi kawai shine yasamu shago babba mai kyau yasaya,
  Allah yabashi sa,a yasamu shago irin wanda yake so,
  Ba bata lokaci akai komai yasa hannu ya biya,
  Kafin tabar gurin har cikin IBO dake layin sun sheda wa mahaifin shi cew gashi a kasuwa yana diban shago,
   Ganin lokacin sallah jumma,a yana gabatowa shiyasa yai haramar komawa, gidan su Anty
   Tafe yake yana shawara a,ranshi cewa gobe zai tafi gurin mahaifinshi,yasanar dashi,
  Cewa ya sai ma Abdulsamad shago saboda Allah da Annabi
  Saboda duk irin halin kuncin da ya jefa Abdulsamad din saboda akidar addini yasani,
  Don haka zai fara sanar dshi cewa sun san mugun halinshi akan wanda duk ya canza addini daga cikin su,
  Yasan idan har yafada mai garan dagaran zai samu saukin duk wani kulli da zasuyi mai,
  Yana cikin shawarar ne azuciyar shi har ya kawo kofar gidan Anty Dije,
  Wanda kawo,war yai dai,dai da lokacin da A,A  shima yake kokarin aje motar shi don sauke maryam,
  Da ya dauko daga school, don yau jumma,a bata wani dadewa, a school din
   Sun,na zaune acikin mota, suna dan taba hira saidai kafarta guda yana a tawaje da sauran jikinta,
  Hikimar yin haka gareta shine kare zargin yan unguwa masu sa ido a masu zama da maza cikin mota suna masu suna,
   Kallo guda yai masu ya,kauda kai, gefe, guda batare da yakara ba,
  Don yarasa komay yasa sam baya son yagan su atare da wanan guy din,
  Yasamu Anty ta aje mai abin karyawa a falon ta bayan sun gaisa ta gabatar mai da abin kari, kumallo,
  Sai yaji wani irin kara girmamata yashige shi shiyasa yake son al,amarin ta, don tana saurin fahintar shi,
  Muryan ta yaji tana cewa, tasan cewa baici komaiba har yazu saidai tana gani abincin yai sanyi ko zuwa yanzu,
  Ya zauna ke nan da niyar fara ci maryan tashigo gida cikin takon takalmanta da ke fidda sauti,
  Tundaga kofa tai arba dashi cikin sauri takawar da kanta gare ahi adaidai, lokacin da yake kokatin zuba ruwan zafi a cup
 Duk da takwaso nata kalar yunwa baisa ta tsaya don ta,karya ba sai shigewar ta tayi kawai aciki
   Anty Dije ce tasa mata kira don tasan cewa itama bataci komai ba tau tabar gidan
  Alokacin maryam harta cire hijab dinta daga ita sai wani English wear buje da riga masu kamar son shagewa a jikin mutum,
  Sam har ta manta da cewa akwai mutun a gidan nasu,
  Don haka bata tsaya sa wani hijab ba kawai falon ta fado
 Duk yadda taso ta tare jikinta hakan bai yi ba saboda kayan sunyi mata masifar kyau,
  Shiko Yusuf kallo daya yai mata yakauda, kan shi gare ta
  Abinda baka ra,ayi ko ya yake bazaka sahi arayuwa,ba,
  Tunda bawai wani abune atsakanin su ba baiko dauki ganin ta haka dayayi dawata manufa ba, shi,
Itako sai kokarin kamay,kamay takeyi, don kada yakalli surar jikin ta,
   Wayar shi ce ta sa kara alamar kira,,
  Aisha ya furta a hankali, sai kuma alamar yar murshi dayayi alokacin
  Hakan ya,tabbatar masu gabadayan su cewa da Aisha yake wayar,
  Maryam ta juya bayan tace wa Anty ba ta jin yunwa,,
  Tashige abinta batare da tatsaya jin kwam ba awayar da yake yi,
 Bai wani dade ba yai ma anty dije sallama yace zai je ya shirya yazo tadauki Assalam su tafi, massalaci,
    Shiga,sosai yayi na Muslims farar shadda ce dinkin ta,zarce
  Wani hula yasa mai ruwan, siminti, sai takalma shige hular kan shi,
 Kamshi agurin shi ba,a maganar, yana rike da wani bakin tasbaha kiran China,
   Bai wani tsayawa ba don yana sauri, luckily ya samu an shirya Assalam ko, suka tafi,
  Maryam wace ke tsaye daidai kofa ta sauke wani sanyayar ajiyar zuciya,
  Ta waiga ida anty take tace cikin tabe baki yayi sa,a gaskiya da Allah yanufe shi yakarba kira,
  Murmushi Anty Dije taimata tace abin ai daga Allah ne maryam,
  Shiyasa mutum idan kasan farkon shi aibakasan karshen shi ba,
  Sun isa massalaci anata zuba sahun a ko wani bangare,
  Tareda Abdusamad sai jibrin da KB da suka uso da ranan nan, sai Ibrahim da yake acikin su,
   Ido akan su caaaa wasu duk da a cikin massalacine harda leke sukeyi idan an nuna masu shi,
 Hakan sai bai wa Yusuf dadi ba saboda irin yadda ake mai babu ko boyo, aciki,
  A, cikin zuciyar shi yace, to komay kuma ya yi da ake mai haka,
  Don shi ai tsan mani yayi za,ai farin ciki da kasancewar shi acikin wanan massallacin mai,albarka wanda yatara dinbi musulmai,
   Duk da ana sallah amma wasu yan gulma idon su yana kan shi don suga yaya zaigi sallah shi,
  Bayan an sallamay sai kawai sukaji ana, musuluntar nashi a she mahaifin jibrin ne yabada wanan sanar wan
  Aiko mutane sai nunafarin cikin su sukeyi don dama andade ana rade radi,
  Da kyat suka samu su kabar harabar massalacin don yawan jama,a  masuyi mashi barka,
 
  Labari ya iske Mr Ema cewa ga abinda yafaru a massalaci wanda wasu musulman mune suka kwarmatawa wasu daga cikin Ibon garin,
  Mr Ema shida yan tawagar church har mada na wasu churches din sukayo kwamiti zuwa gidan Sarkin Sudan, cikin fada,
  Don su azaton su, zadu ita shawo kanshi, jira sukeyi su gama aiwatar da shirin su,
  Sai gashi anyi anoucement, a massalacin jumma,a cewa ya musulun ta,
  Sarki yasa aka tare su, cikin  dan mutunci,
 Inda yasa sugabatar da abinda,ke tafe dasu
  Rankashidade, muna karan wasu yaran musullumine gurinka cewa su ja yalon mu zuwa ciciin Muslims,
  Batare da bakin mahaifinci ba,
 Eheh, shine munzo mu fada ma,ka, shewa, muna son abamu yalonamu, afido dashi daga shikin isalama,wanda ya ciga,,,
  Bayan mai martaba yagama jin korafin su ne, yadan magana da galadima,da waziri,
  Galadima ya ari bakin mai sudan yai masu bayani kamar haka,
  Muna son kuzo da yaron na ku nan don muji ta bakin shi, sanan, a kira wa,yanda suka maidashi ciki,
  Fita sukayi daga wajen fadar maimartaba Sarki Sudan
  Suna ta kus,kus ta yadda zasuyi su kawo Joseph gurin sarki,
  Shi Mr Ema dakanshi, ya kira Joseph da wayar shi, kira daya ana biyu ya dauka,
  Joseph come nd meet me in mai Sudan palace now,now
  Yusuf wanda ke tare dasu KB suna wani estimate, din kaya,
  Abin yabashi mamaki ya kalli su KB yace masu cikin bacin rai wai Dad dina ne fadar mai sudan,
  Duk kan su cikin mamaki, sukace gurin mai Sudan fa,?
  Sun so su bi shi sutafi tare amma yusuf din yace su bari kawai zai iya zuwa,
Mr, Ema tare dasu Ekewa, da su Barnabas Mr Ema wanda ke zaune cikin damuwa ya saye da wani rigar yadi mai hoton giwa, dajan colur, sai wani jar hula dayasa akan shi,
  Yana rike da sanda a hannun shi,,maikama da kan gunki
Kallo guda zakai ai kane cewa yau rayuwar shi ba tada dadi sam,
 Su na ganin shi sukayo kanshi caaa kamar zasu ciye shi danye acikin yare suke magana suna cemai, ya taimaki rayuwar shi kada ya bari wasu su rude shi,
  Kowa daga cikin su da abinda yake fadi, don dai kawai ya amsa cewa bai musulunta ba,

  Zazaune suke gaba dayan su a gaban,mai sudan, Inda mai Sudan yasa akara fadar abin da sukazo dashi
  Yusuf na sauraren yai shiru saboda ladabi har lokacin da aka gama bayani akan komai,
  Maimartaba ya kurawa  Yusuf ido har nawani dan lokaci,
  Sai yagano cewa Yusuf wayayye ne bazai ce Yes ba, yace No ba kuma
  Don haka sai sarki yace mai samari kaji bayanin da iyayyen ka sukazo, dashi,
  Zaman shi ya gyara cikin ladabi yakalli inda maimartaba yake, yace,
  Assalamu Alaikum warahamatullah,
  Sauran musulamai dake gurin suka karba mai kamar yafda sharia ta ce ayi,
  Suko gaba dayan su suna jin wanan kalaman da ya fara magana da ita, suka dau da cewa
 Emba, Juses crisis,
Oluwa, inji wani pastor yan olumba,olumba, yace cikin kada kai alamar takaici wai,,
  Yusuf yace a gaskiya babu gaskita daga cikin zancen su,
  Saboda ni yanzu nakai munzalin da ,zan daukar wa kaina duk abinda nake ra,ayi,
  Heh  Joseph come to your sense pls ?
 Don't deceive your self
Magan ganu iri iri suka dan fara cikin, jin haushi da takai ci,
 Nan da na fadawa suka daka masu tsawa dole suka natsu sukayi shiru
   Yusuf yaci gaba dacewa,
Nazama musulmine ba tare da sda shawaran kowa ba,,
  Ra,ayinane kawai yabani shawar gane hanya afificiya ta isalama,
 Kai Na, lie, woo,
Wani bafade dake, kusa da mai maganar ya watsamai bulala tauuu,
  Yace mai cikin daka tsawa behavi your self
 Ganin haka yasa du natsuwa dole zuciyar su na suya
  Yusuf yaci gaba da cewa, banzama musulumi ba saida nasamu kwararar hujjoji daga Alkur,ani maigirma,
  Eyy,Eyyyy, he's finish wooo,
 Abinda sukace gabadaya kusan lokaci guda ke nan,
  Watau, Joseph ysi nisa har da Alkur,ani ya,yarda dashi,,
  Yusuf yace saida na hada duk wani hujja wanda zanyi depending a kai sanan nida kaina nakai kaina wurin limamin central mosque na Abuja ya musuluntar da ni,
  Saboda haka duk wani wanda ke zargin cewa wani ne yajani zuwa cikin islama ba gaskiya bane,
   Ni YUSUF ban musulunta akan abin duniya ba ko mace ko aboki,
  Na musuluntane saboda Alkur,ani maigirma,
  Sai duk wanda ke cikin fadar musulumi suka dauka gaba daya dafadin Allahu Akbar,
  Yace nakai lokacin da zan zabawa kaina abinda nake so daga addini, sana,a da kuma iyali,
 Cheer, God wooo,
 He, don go far,

  A nan maimartaba yai masu warning akan cewa duk wani wanda ke son kawo mai fitina ko tashin hankali acikin kasa ashirye yake da yadauki mataki akan mai shi tunda har wanda suke magana yace ra,ayin shine shiga addinin da yakeso don yakai shekara talatin, yanzu,
  Kuka sosai Mr Ema yadinga yi acikin fadar mai martaba yana fadin cewa a taimake shi amayar mai da danshi cikin Christianity,
  Amma ba wanda ya bashi goyon baya haka suka tallabe shi zuwa bakin motar dasukazo dashi yana kuka, wi,wi,
  Yana kiranan sunan joseph yana zuba gwalancin su,
  Shiko yusuf dama yarigasu barin gurin don haka gidan Anty Dije yakoma,
  Saboda yadan samu relief of mind, din shi sai,dai kana ganin yadda idon shi ya rine kamar garwashi zaka gane cewa, yana cikin tashin hankali,
   Yadan dade yana waya da Alhaji sabo inda yake fada mai abinda yafaru dashi yau da mahaifin shi,
  Maryam wace ke cikin bayi a lokacin tana jin abinda yake fadi har zuwa lokacin da yashigo ciki da rinanun idon shi,
   Falo yazauna jagab saman kujera two siter dake cikin falo,
  Maryam wace kafin yashigo,,tafito ko daga bayin
 Tana cikin shigar atamfa, buje da riga masu ruwan multi, colour,
  Dinkin yai mugun karban jikin ta kayan da tasane tai adon jin ma,a dasu, da rana,
  Taso taje ziyara gidan su safiya amma sai taga yau Anty bata jin dadin jikin ta sai tafasa shine tashiga bayi ta gyara jikinta don tana fashin sallah,
  Acan ne taji muryan Yusuf din yana waya dawani yana fada mai irin yadda yaji gamay da mahaifin shi,
  Wani irin tausayin sa taji don tasan da zafi ace mahaifinka na kuka akan ka,
 Inbadon addinin gaskiyabace kamar yadda Yusuf din yace da sai ya fasa yakoma gurin mahaifin shi
  To amma ba,zai iyaba sam ya shiga isalama kenan har mutuwar shi acewar,
  Bashiga bafita shiga sojan badakkare,
 Tana bude labulen dakun tafitowa suka hada ido, ya sakar mata rinanun idanun shi da suka kada sukai ja ,
   Kan ta, takawar gefe cike da jin tausayin shi alokacin,
  Direct gurin fridge tanufa tabude tadauko kwalin madarar youghot mai sanyi mai hoton bafillata, na company Mrs Ghali, youghot,
   Ta hado da cup din glass bata tsaya ba sai,gurin shi direct,
  Ta, dan rage tsawonta ta fara zuba wa acikin cup din a hankali,
  Sai a likacin yuduf ya bude idon shi dasuke lumshe yasauke su akanta,
Ta mika masa youghot din a hankali, batare da ce mata kala ba yakarba ,
  Yakafa kai a hankali yana lumshe ido don sanyi da gardin youghot din,
  Saida ya shanye glass guda a hankali ya cire cup din abakin shi murya kamar mai rada yace nagode Maryam,,, 
  Maryam ta mike daniyar barin gurin don jin ajiyar zuciyar da yayi,
  Yace may ye sunan wanan madarar,
 A, hankali tace Mrs Ghali, youghot,
 Masha Allah yana da kyau,,,



ZEEEE MAKAWA
[1:32PM, 2/26/2018] 鈥�+234 814 858 5998鈥�: 馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
  FUREN      JUJI
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
           3鈨�5鈨�
ZAINAB IDRIS MAKAWA,


   Garin duk yai mai zafi, gabadaya baya jin dadin rayuwar shi sam,
  Don haka ya yanke shawarar ya koma gobe ,gobe tun bai dauki wani lokaci ba,a garin saboda bai ita jure ganin mahaifin shi a haka
   A ranan bai kwana gidan su ba hotel ya kama,,
   Da safe ya shigo gidan cikin shirin shi na tafiya, yaso yatafi batare da yayi sallama da Antysa ba,
  Amma sai yaga cewa zai dade bai shigo ba don haka yakamata su,yi sallama, da Assalam din shi,
   A bakin kofa sukayi kicibis da maryam wace ke kojaein fita siyo madu breads na break fasta,
   Idon shi ya kade yayi ja, kamar mara lafiya,ya wani fada,
  Dan Rabawa maryam tayi gefen shi ta wuce inda zata,
  Saidai jikin ta ya,ba,ta, cewa yana kallon ta bayan ta wuce,
   Maryam tashigo rungumay da breads har guda biyu, a gefen hannun ta,
  Anty Dije tace kagani ai nace kabari,ta dawo ba nesa ta, tafi,ba,
  Nan Maryam tagane cewa tafiya zai yi, acan cikin ziciyar ta sai taji tausayi shi yai dan mata yawa,
  Don ta san cewa hakan nada nasaba ga maganar da taji yanayi jiya awaya
   Bayan maryam tashiga a,gagauce ta hada mai ruwan shayi tafito dashi rike a cup, tanufo shi,
   Idanu ya zaro don bai tsanmani hakan ba,daga wanan yariyar
   May yasa yanzu take sasauta mai fiye da,da,?
   Bakin,ta na dan rawa, tace, gashi na hada mai ai Anty,
   Sai yau zata ce magana mai kama da ta mutunci tashiga tsakanin su,
  Hararan ta ya yi ,yace, wanan ai yai min yawa, ga kuma zafi,
   Kanta na kasa duke saboda bazata iya jure irin kallon hararan da yai, mata ba,
   Muryan Anty ce ya katse su adaidai lokacin da yake shirin karban cup din tea din
  Anty Dije wace je cewa  gaskiya, Yusuf wanan tafiyar dai kamar ba shiri zakayi ta,
  Nan da nan idon shi suka canza zuwa tsantar bacin rai,
  Ba Anty Dije ba har maryam da ta dauko mai wani dan stol a falon su saida, taji wani iri,
  Yace cikin dasasar murya, mahaifina ke son kawo min matsala Anty,
  Yaki hakkuri da zancen musulunta na sai daga hankalishi yake yi,
  Duk da nasan cewa zuga shi akeyi akaina, lokacin yadan fara kokari kurba shayin da maryam takawo mai,
  Ammakin shi sai yaji baida mugun zafin da ya,zata zaiyi,
  Idon shi yadago ya kalli inda maryam take tana kokarin aje mai wata yar kujera irin ta zaman mata, hannu ta na dauke da ruwan pure water leda,
   Itama anty zaune takai saman farin kujerar roban da maryam ta aje mata dan nisa kadan da Yusuf din,
   Nan yaci gaba da fadawa Anty Dije yadda duk suka kwashe da maihaifin shi tare da sauran yan kabilar su,
   Yadago idon shi rinannu ya sauke su ga, maryam daniyar yace mata ta kwashe kayan tea din ya koshi, saboda bai faye cin abinci da safe ba haka,
   Idon ta suna a rintse tana mai jin zafin labarin da yake fadawa Anty ta,
   Muryan shi da taji yana cewa nagode zan tafi kada inyi rana ahanya, don gobe akwai inda zantafi indan Allah yakaini,lafiya yau,
   Sai ji tayi bakin ta na furta,zancen da takeyi a zuciyar ta,
    Kadaure da,duk wani, kalubalen da zaka samu daga gurin su saboda bara,zana ce kawai suke kokarin yima,
  Ko zasu iya juya ka idan sunyi hakan don kawai suyi galaba akan ka,
  Kawai ka bar su suyi tayi watarana zasu daina gaba daya don zasu saduda,dakan su,
   A,cikin mamakin ya ware idon shi yana kallon ta, yau itace ke nuna concern din ta akan shi saboda yazama musullmi dan uwan ta,
  Ashe dama saboda akidar addini take gwada mai wanan tsanar, tunda yaga suna dan hurda da Jibrin, sai KB ne ba su shiri har yanzu,
   Saida takai aya tai shiru dan kanta daga haka tajuya da nufin tabar gurin,
  Anty Dije ce tace mata maryam amma fa kinsan cewa mahaifin shi, ne taya zai yi mashi haka,
   A ladabce tace to, anty baki ganin cewa suna iya jan ra,ayin shi yakoma masu,,
  Murmushi yayi yana mikewa, tsaye yadan kalli inda take yace, kina ganin kamar zan iya komawa cikin su ko,?
   Kanta ta sada kasa saboda kallon ido da idon da suke fuskanta a,tsakanin su,
   Yace ai,ni na shiga ke nan insha Allah sai mutuwa kuma,
  Ya juya gurin Anty Dije yana mai ce mata idan Assalam ya tashi sai ta, massa sallama,shi yatafi,
  Kudi masu yawa yadebo daga cikin aljihun shi ya aje wa anty a gefen , yasa kai yafita,
  Bayan fitar shi, wajen minti uku Anty takasa koda motsi balle magana, saboda yawan kudin da ya aje mata,
  Maryam ce ta zo da zuciyar ta daya ta dauki kudin tafara kirgawa,
  Abin a tagani, yasanyata saurin dago kai ta kalli yar nata, cikin mamaki tace dubu dari Anty,
   Da sauri anty ta dago kai ido waje tace dari,fa Maryam,?
   Dan tsuke fuska Maryam tayi, tana kokarin mikawa Antyn ta kudin,
 Allah yakai idon yar uwar nata a fuskarta, cikin mamaki tace wa Maryam, may kuma akati,
  Maryam wace dama ta cika fam, tace to shi ance masa kina kwadayin kudin shi ne kokuwa,
?
  Cike da mamaki yar ta ke kallonta don maganar ya daure mata kai,
   Ban fhince ki ba inji Anty Dije,
 To may da,zai wani baki kudi haka, batare da wani, dalili, ba, ni wallahi ban son abinda mutum zai min gori akansa sam,
  To ke Maryam may ye naki aciki da har zaki dinga wanan zance,
  Dama tun jiya yake ce min, zai bar kudi wanda zan dinga mashi sadakar kosai da, sugar duk jumma,
  Sai a lokacin Maryam ta danji dadi har cikin ranta don azaton ra yagan su mabukata ke nan, shi yasa yabasu kudi,
 
   Kwana biyu bayan tafiyar shi sanan mahaifin shi yasan cewa yabar gari,
  Don haka ya kara daukaka fushin shi, don yasan cewa da gaske Joseph keyi yabar Christianity ke nan har abada,
  Ya jijiga kan shi shi kadai a zaune saman kujer da ke bakin gidan man shi, yace impossible,
   Waya yadauka yakira wani aminin shi dake zaune a Lagos din
   Yusuf wanda a lokacin yadawo agajiye daga inda suka tafi can kusan boarder,
   Ya zube saman kujerar dake cikin falon nashi, yana mai da numfashi guda guda
  Kokari yakeyi yadan sasauta aninin da ya ke saman wuyar rigar shi don yadan ji shahakat,
   Ido biyu yayi da wasu murda murdan katai cikin bakaken kaya da wani bakin glass a idonun su,
  Addu,an da yagani cikin teach your self islam da yana ce saida ya haddace yai saurin zo mai arai,
  A zuciyar shi yace bari ya fara gwada, wanan damar yagani,
 Batare da ya nuna razana daganin su ba yace
 LA,ILLA HA,ILLAH ,ANTA SUBBAHANAK INNI KUN TUN MINAL ZALLIMIN,,,,,,,
  Cikin nuna rashin jin tsoro yace masu cikin natsuwa,
  what's, do you want from me,?
   Zagayowa sukayi inda yake zaune suma suka dan zauna mutum guda daga cikin su ne ya tsaya saitin kan shi da bindiga a hannun shi yana wasa da ita tankar bawani mugun abu yarika ba,
    Mafi tsawo da kauri daga cikin su ne yadan gyara tsayin glass din idon shi yace,
  Bama son komai daga gare ka,saidai kai kawai muke bukata, yana mai nuna Yusuf din da yatsar hannun shi,
   Daga haka wanda ke tsaye ya sai mai wani kyale ya toshe mai hancin shi dashi,
  Sai farkawa yayi yagan shi a cikin wani daki mai kama da dakin gwauraye,
  Don yar katifa ce a kasa kawai sai wani dan tarin kaya mai kamada kayan wanki,
   A hankali ya bidakin da kallo cikin mamaki, yadda har suka kawo shi nan batare da sanin shi ba,
   Kusan minti goma sha da farkawan shi yaji anturo kofar dakin,
  Wasu dattijai ne su uku cikin shigar coth da wando bakake
   Fuskan su babu walwala acikin ta sam, sun kai wani lokaci suna kallon shi batare da sunyi mai magana ba
  Guda daga cikin su ne yadan rage tsawon shi kamar yadda Yusuf din zai iya jin shi daga inda yake a kwance,
  Yace  mai ,Mr joe Y ,d u chose to live ur parents religion's,
  And you even go to the wrong part,
  A, hankali ya dago kanshi ya kalle shi tare da yin murmushin karfin hali irin ta, mayaudara yace,
  That's where I want my life to be,,,,
  Girgiza kai yayi alamar wanan yayi nisa, sosai baijin kira,
 Dafa mai kafada mutumin yayi yana mai cewa kada ka yi taurin kai dan samari,
   Bazan so ace wani abu makamancin haka yasamu daga  cikin ku ba saboda ba,karamin, embraced zaka jawa zuriar ku ba,
   Yusuf wanda kan shi yake a duke, yadan dago kan shi cikin wata malaciyar dariya,
  Yace may ye na embracing acikin ra,ayin addini kuma ina, kowa abinda yake so zai yiwa kan sa zabi,
  Mikewa mutumin yayi ya fara tafiya zuwa hanyar kofa,
  Saida yakusa fita dakin yai wa sauran dake kokarin bin bayan shi,
  Yace masu No Need of westing our time here,
  Wa yan nan kaitan mutanen da suka dauko shi, daga gidan shi sune suka baiyana adakin
  Bisa ga umarni wa yan can mutanen da suka fita suka fara dukan shi,
  Sai addu,an daya iya abakin shi yake karantowa, Allah yakawo mai dauki,
   Ya jibgu so sai a gurin su,suka dan fita, zuwa,, shan taba waje,,
  Mutum guda daga cikin sune yadawo, daga baya yakawo mai ruwa a ledan pure water,
  A hankali ya dan duka wajen shi cikin kashe murya, yace mai I will, free soon,
  Daga haka yamike yai waje da sauri, gurin yan uwan shi,
  Can cikin dare rashin sallah da bai samu yi ba duk ya damay shi,
  Kamar daga sama yaji karar jiniyar yan sanda ya ji ya tunkaro, uguwar da suke,
  Ba,afi yan mintina ba yakama jin karar bindiga, natashi duk unguwar yakaure da karan bindiga, zat tashin hankali,
   Shiru yaji har nawani, dan lokaci, sai can yaji motsi alamar ana zuwa daidai kofar dakin da yake aciki,
  Gaba daya suka hankado dakin cikin irin hikimar su ta yan kaki,
   Kwance yake a daure, a hannu da kafa, shi a takure waje guda,
  Kafin yan wasu mintoci har sun sance shi ko,
  Da taimakon su, suka dan tallabashi zuwa, bakin motar,
  Asibiti suka wuce dashi don diba lafiyar jikin shi Alhamdullah baiji wani mugun ciwo ba sai yan kananan raunuka da yasamu kawai ajikin shi,
   Yusuf, yasamu sauki don har an sallamay  shi bincike yanuna cewa sanadin musulutar da yayi ne yasa akai mai wanan ta,asar
    Saidai wai ba,a san ko suwaye ba shi da kan shi yace a kashe case din don yasan cewa yana iya samun hannun  mahaifin shi aciki dumu dumu,
   Tun daga hospital yasa a sai, masa,ticket din fita waje,
  Saboda yana son yaje yadan huta har komai ya samu natsuwa,
  Kafain tafiyar shi yayi ta samun kiran waya daga yan uwa musuluma na kwantagora suna masa jaje dafantan Allah yakara tsarewa
  Saura kwana biyu ya wuce mai gadin sho yashigo yana sheda mashi cewa, yana da bako a waje,
  Tun daga nesa ya sheda shi ,daya daga cikin wayan nan da suka kawo mai hari ne suka sace shi,
  Shine mutumin da yace wa Yusuf zai yi Free din shi a lokacin da yaje a hannun su,
 Nan dai mutumin ke fada mai cewa, abokan mahaifinshine wa yan, nan mutane,
  Duk abinda yagani da sa hannun mahaifin shi aciki,
  Yaji cewa zasu mai dashi dan defar life shi yasa yaje ya report din su gurin yan sanda mafi kusa,
  Amma cewa yayi ma police yana tuhumar akwai wanda akasato a gidan nan don yana jin ihun mai shi 
  Godiya sosai Yusuf yai masa in da yakawo alheri mai tsoka ya ba wa mutumin,
   Amma sai yace aa shi abinda kawai yaje bukata yasamu aikin yi,
  Don dama rashin abinda zai yi ne gashi da iyali, shiyasa ya shiga wanan harkan,
   Kwarai Joseph ya tausayawa mutumin, don yasan talauci ne yasa shi ,shiga harkan da bai dace ba,,,



ZEEE         MAKAWA
[1:33PM, 2/26/2018] 鈥�+234 814 858 5998鈥�: 馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
   FUREN     JUJI
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
           3鈨�6鈨�

ZAINAB IDRIS MAKAWA


   Kiraye, kirayen, sallah asuba ya kaure ko ina da musulmi sukafi yawa acikin duniya baki daya,
  Shima Yusuf wanan kiran,sallah na asuba ya tashe shi a lokacin,
   Duk da karfe bakwai na safe jirgin su zai tashi suwa, South korea, inda sonny deon yake zaune,
   Massalacin da ya saba zuwa, yin sallah jam,i can yanufa ,
  Batare da jin wani shakar komai, ba ko tsoro,yafito kai tsaye,zuwa, yin jam,in,
   Bayan ya idar da sallah yadade, zaune gurin yana lazimi har zuwa dan waye wan gari kadan,
   Yana isa airport batare da bata lokaci ba jirgin su yadaga yabar kasan, don sai sun dan yi tsaye, tsaye, hanya kafin su isa,
   Sun dan yi nisa kdan yadauko Alkur,anin shi da Jibrin yabashi mai fassara yafara karantawa, a nutse gwanin sha,awa, kamar yadda yaji anyi bayani adinga yi,
   Daidai saitin kujerar shi akwai wani matashi bahaushe zaune yana ta faman dakilar wayar shi,
   Saurayin na hankalce da Yusuf wanda har abincin da aka aje masu baiko kalla ba sai karatun shi yake a natse,
   A, hankali matashi yataso saboda burge shi da yusuf yayi
  Sallama yai mai tare da mika mai hannu, inda yake gabatar da kanshi gare shi
   Yunus baba shola, daga Ibadan Nigeria amma shi ma,zauni Lagos,
  A, hankali Yusuf ya mika mai hannun,shi guda da ya dan dago daga karatun da yakeyi,
   Shimadai din fada mai sunan shi yayi cewa Yusuf Emanuel, daga, Abia, Umahia,
   Da ya fadi hakan sai da Yunus yakara daga idon shi yakalli kamilin saurayi mai suna biyu,
  Don sam natsuwar da kulawar shi ga addini baiyi kama da wanda ya fito ta wanan tsatson ba,, sam,
   Murmushi Yusuf yai mashi mai nuna gamsuwa da abinda zuciyar shi take tunane , akai,,,
   Such is life, yadan kara murmusawa,irinta gwanayen murmushi,
  Yunus yaciro wani dan karamin kati daga aljihun wandon shi ya mikawa Yusuf,
  A hankali yakarbi katin yadan karanta abinda ke jikin katin sai dan daga kai ya,kalli Yunus din,
   Daidai tsakiyar inda yake ya sa katin, tare da kara kallon saurayin dake tsaye har yanzu akan shi,
  Yace my Nice, to Meet You,
  Sai a lokacin Yunus ya mayar mai da kalar murmushin da yake mai tun dazu,
  A daidai lokacin wata yar matashiyar ma,aikaciyar aikin jirgin ta iso gurin, cikin shigar irin uniform din su,
   Tambayar su tayi gaba dayan su, a lokaci guda tace The You need some help,?
  Juyawa Yunus yayi cikin daga mata kafada yana mai cewa a,a,
   Shima alokacin ya koma gurin zaman shi tunda yaga bawani cikkaken ansa zai samu daga Yusuf din
   Sai alokacin yadan, dauki, goran ruwan da aka aje mashi agaban shi yabude ya kwankwade dukka alokaci guda,
    Kara komawa yayi daci gaba da karatun shi batare da ya kara kallon kowa ba,
   Saida jirgin su ya sauka a inda zasu fara yada zango ne , yadan fito don ya, samu dan abinda zai danci, don shi yanzu sam bai yarda da abincin jirgi na saboda bai san koda may aka hada ba,
   Drinks din da ya tabbatar baida surki a ciki, ya saya tare da wani dan corn dake cikin leda,
  Dakin da yakama acikin airport, guest house din a lokacin yadan dauko wayar shi ya kunna
  Miss call yaga ni har kusan guda, uku, ajere daga Anty Dije
   Baiji dadin hakan ba, ga shi kuma ba service anan balle yakira,
   Ya kai wani lokaci yana hutawa adakin yana kuma yi yana kallon agogon hannun shi, don gudun makara,
   A hankali ya mike da niyar tashi don shirin tafiya
  Card din da Yunus yabashi ce, tafodo kasa, yaduka yadauka yana mai kara bin katin da kallo kamar mai son nazarin wani abu daga katin,
   Can da sauri ya kara kallon katin yadan, kada kai ya furta da cewa,
  Alh Yunus Sikiru Shola Akani, Computers plazas,
  Yanzu yagane sune  keda wanan katon plazas har guda biyu acikin Lagos,
   Yana fita suka kara hadewa da wanan guy din dasuka hadu ajirgi shi yafawa Yusuf magana cewa,
   Shima gaba yayi ke nan ba,a nan zai tsaya ba kenan,
  Duk da yagane shi amma baiyi wani daukin nuna mai cewa yasan koshi waye ba yanzu. Saboda kariyar mutuncin shi,
    Kusan atare  suka shiga jirgi wanan katon duk da sin samu sauyin jirgi a wanan karon,
  Bawani dogon hira sukayi ba sosai saidai shi Yusuf din yafahinci cewa, Yunus mutum ne mai saurin saboda, jama,a,
  Don har yana mashi hiran cewa, tafiya zaiyi akan wasu wayoyin hannu da suke, so abugo masu irin shi,
   Nan dai suka dan taba hira sai gab da zasu saukane Yusuf shima yabashi nashi card din,
  Sosai, Yunus din ya nuna farin cikin shi akai tun ajirgi sukayi sallama tare da yuwa juna alkawarin kira idan sun dawo gida Nigeria,
    Ya samu, Sonny ya aiko adauke shi, kusan minti goma da suka wuce,
  Sunny yayi murna kwarai da ganin Aminin shi kuma abokin shi,
    Saida yaci abinci yakoshi tukun sannan Sonny din ya,shigo gurin shi tare da wata fara budarwa yar kabilar Koreans,
  Tufafin jikin ta kusan tsirara za,ace take don kusan komai nata afili yake,
  Sau guda yadaga kai yakalle ta bai kara ba, suna rungumay da junar su har, zuwa inda Yusuf yake zaune saman, dogon kujera,
   Sonny din ne ke,tayawa Yusuf fita zuwa club, din dare don more rayuwa,
   Kai Yusuf yakada mai alamar a,a, bazai tafi ba Sonny wanda hannu sji ke ta faman shafar budurwan shi,
  Yace mai akwai fa fine,fine bear, akwai kuma young bebies, agurin
  Fadar haka kawai da Sonny yayi sai yaji wani irin haushi acikin zuciyar shi
 Sonny zaicigaba da kwadaita mai fa,idar fitan,sai Yusuf cikin wani murya maikama da tsawa yace mai,
   You can go pls all dis is forbidden in my religion, alcoholic, ladies games, etc,
  Wani malalacin dariya sonny yasake yana mai cewa which religion forbids all dis things,
  A gadarance Yusuf yace mai Islam,
 Da yatsa yanuna yusuf yace you islam when,?
  Sai kuma yakara bushewa da dariya har yana yar tabawa cikin dariyar tashi,
  Hannun yariyar da suka shigo maikama da tana yawo tsirara,
  Yaja yana mai cigaba da dariyar zolayar da Yusuf yai mai cewa wai shi muslim nne
  Shiko Yusuf suna fita sai yaji kamar har yanzu dakin na warin yariyar dazu,
   Window's din dakin yadan sake don iska ya shigo mai,
  Dogayen benayen da suka cika garin masu mugun tsayi da kuma sha,awa yadan tsaya yana kallo ,
  Bai dade gurin ba ya shiva bayi ya kara watso ruwa tare da dauro alwala don yin sallah raka,a biyu kamar yadda yagani cewa mutun yayi sallah raka,a biyu aduk lokacin da ya tafi wani bakin guri don neman sa,ar tafiya da kuma tsari,daga miyagun kaddarori,
    Wani jallabiya yadauko mai laushi dakuma santsi daga cikin kayan shi yasa,
  Yadan kai wani lokaci yana istigifar akan neman yagiyar ubangiji ga kurakuran da ya tab ka abaya,
   Har zuwa lokacin da barci yadaukeshi batare da yasani ba xuciyar fam da kewan mama da Ejoma
  Wanda mahaifin shi ya rike su can kwantagora, wai kada yaje dasu yafasu cikin irin harkan da ya shiga, watau islama,,,,,,

   Maryam wace, ke zaune ita kadai a gidinnwata bishiyar lim dake cikin harabar makarantar tasu,
  Idan ka ganta azaune zaka dauka cewa karatu takeyi a lokaci ashe sabanin hakan,
  Bata komai sai tunanen yadda A,A ke mutuwar nuna mata kauna, akoda yaushe,
  Amma sam fafir yaki yarda ko sau guda ya je su gaisa da mahaifin ta
  Kamar yadda Anty Dije ta bukace ta da tafafa mai yaje su gaisa da baba ko hankalinshi zai dan kwanta a yadda koyaushe cikin tambaya yake ita Maryam har yanzu ba tasamu wanda ya tsaya mata bane, ?
  Duk yadda taso yaje sai doje mata yake yi don kullun acikin uzuri yake na cewa, akwai abinda yake jira kafin yaje,
  Dafarko tazaci ko dan irin abinda zaibawa babane idan yatafi baida sai taga ba haka bane
  Yauma kamar baya anty Dije takara tunatar da ita akan zancen cewa yayan ta iliya zai zo yakamata yazo su gaisa da shi,
  Amma sai take ganin ai baidace, takara mai magana ba don tana son taga iya gudun shi,
 Firgigit ta zabura don jin antaba a baya. Ahankali ta sauke ajiyar zuciya don shiga yanayin da tayi,
   Safiyace wace yanzu zama da jibrin yasa ta takarayin wani clean, tazama budurwan kwatance acikin kawaye,
   Cikun murmushi tacewa aminiyar nata, A,A ko karatun,?
  Maryam tadan nisa tace bako daya, tana kokarin boye damuwar ta,
   Saida Safiya ta zauna tukun ta kalli maryam din wace ke nuna alamar ba komai dake damun ta,
   Maryam inji Safiya wace takurawa maryam din ido kamar mai son fahintar wani abu daga gareta,
   Kada ki sa zancen namijin da ba aure kukayi ba arai tun yanzu
  A,A dai yana son ki amma yan uwan shi ne matsalar ku,
  Saivs lokacin maryam tadan daga kanta takalli Safiya,
  Safiya tace a yadda naji ance mahaifiyar shi tana son hada shi aure da diyar dan uwata,
  Amma shi A,A baya son wanan hadin sam, ra,ayinshi na gare ki,
   Saidai ya bukaci mahaifiyar nadhi da ta yarje ma,shi yaure ku daka biyun,
   Maryam ta kwalalo idon ta waje tace biyu da wa, kam,
  Hannu ta daga tace pls Safiya ki daina wanan zance dan Allah inma har wasa kike yi,
   Tana kokarin mikewa Safiya ce, tadan jawo ta da style takoma ta zauna,
  Indan harda so wanan bakomai bane maryam ni shawarana kawai ki bi, a hankali pls,


 Kuyi min afuwan pls yau banda caji,


ZEEE MAKAWA
















..馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
  FUREN     JUJI
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
          3鈨�8鈨�

ZAINAB IDRIS MAKAWA,,


  Yusuf yadan samu natsuwa sosai a zaman shi tare da Sonny saboda shi Sonny ba mutum bane mai son shiga har kan wani,
  Wanan damar da yusuf yasamu yasa,shi samun sakin jikin  shi har ya manta daduk wani tashin hankali dayaje ciki,
  Ganin yau jumma,a ce juma,a biyu kenan bai samu yin sallah jam,i ba
  Don haka yasa a ranshi cewa yau zai shiga gari yadan zagaya don yadiba ko zai samu wani guri da musulman garin ke yin sallah jumma, din,
  Tun ranan Thursday ya shirya cikin shigar wasu kanan kaya kamar yadda yake yi kulun,
   A daida, fita ta wajen gidan, suka hade da Sonny wanda ke shirin shigowa,
  Kallon mamaki yaiwa Yusuf din yana mai tambayar shi ko ina zai tafi haka,
  Ba boyo ya sheda mai cewa ga inda zashi searching din gurin bautar su na ranan Friday ne,
  Haba joe in ji Sonny yakamata ka fada min sai mu fita tare in taya ka dibawa, ai hakan zaifi katafi kai kadai,
   Zuciyar yusuf tayi fes jin abinda Sonny yace yasan kuma har cikin ranshi yafada,
   Basu sha wani dogon wahala ba sosai don wani abokin hurda Sonny musulimi suka kira shi yai madu kwatancen gurin suka tafi,
  A zahiri idan kaga gurin zaka dauka wani, ma,aikatace sai dai in kashi ga,
  Sundawo gida Yusuf na cike da farin ciki har bai iya boyewa,
  Sonny ya fahinci haka sosai inda ya yake tunanen irin yadda wanan addinin yai tasiri aran Yusuf cikin lokaci guda,
  Saboda yasan Yusuf din sosai lokacin da dukkan su suke bearing din Christianity
  Baibada wani munhin manci akai ba kamar wanan yadda ya ga time din sallah su five times a day baya wuce joe din,
   Shin wai su muslim din nan wasu irin mutane ne masu karfin zuciya haka da taurin rai, akan abinda suka yarda dashi,
    Basu dawo gida ba saida suka biya gurare da dama aranan, inda Yusuf yai yan sayayan yan abubuwan bukatun shi indan zai dawo Nigeria,
   Washe gari tunda safe,Yusuf ke ta shirin shi na zuwa massalaci batare da bata lokaci ba yafito cikin shiga mai daukar hankali, sai kamshi ke tashi ga carpet din sallah shi da yar karamar tasbaha a hannun shi yarika,
  Da mamaki Sonny ke kallon shi don shi har ya manta zancen zuwa mosque yau, da Yusuf zai yi,
  Amma sai yaga ashe cewa shi Yusuf din bai manta ba abin na zuciyar shi,
  Tausayi sosai abokin nashi yabashi sanin cewa yayi nisa sosai ga wanan akidar,
 Al,amarin sai ya burge Sonny kawai, don ya yarda da mutane ke cewa wai islam is a teitorim religion,
  Sai ya fahince cewa rayuwa ce ta saukake, aciki babu takurawa juna ko sa ido ga harkan wani,
   Don haka shi da,kan shi ya bukaci kai Yusuf din, mosque, aranan,
   Motar shi maikyau mafi  tsada suka shiga inda tun a kusan haraban gurin zakaga irin yadda maza da mata da yaran su ke ta dandazon zuwa gurin bautar nasu,
  Kowa kagani cikin shiga ce ta alfarma ko ina lif a rufe daga mazan har matan su,
 Gwanin ban sha,awa gaduk wanda yagan su, kowa kula dan uwa tankar yan ciki daya,
   Sai zuwa wani lokaci mai tsawo suka dawo daga, massalacin daka kalli Yusuf kasan cewa yana cikin annuri, aranan,
  Saboda yadda yake ji tankar andauke mashi wani nauyi ne arayuwar shi,
  Sai yanzu yake tabbatar wakanshi da cewa ba karamin sa,a yayi ba nafitowa daga cikin kafirci cikin duhun kai,
  Indan har su wa yanda sukayi zamani da Annabi Isah yan uwanshi da yan yaren shi da akasa su yarda dashi da sakon shi,
  Suka kan su sun tabbatar dacewa akwai wani wanda zaizo bayan ahi Isah din kamar yadda yake da magabata agaban shi (watau, annabawan da sukazo kafin shi)
  To su yanzu da suke bin akidar Christianity don wa sukeyi tunda an fada masu a littafin su cewa zai zo,
  Hannun shi yadaga yashafi sajen shi dake kwance a fuskan shi lif,
  Yana mai hamdalah acikin zuciyar ashe afili har da hannuwar shi yadaga sama yashafa,
  Sonny wanda ke kallon shi mamaki yakara kamashi sosai sai ti yake yi yana dan satan kallon Yusuf din,
  Wanda ahalin yanzu yaga yadda yaimai wani irin kwarjini

   
   Washegari da safe, bayan ya idar da sallah yazauna yayi irin addu,oin da yasaba yi,
  Gurin yin exercise yadan fita har zuwa lokacin da gari ya washe sosai,
  Sanan ya,shiga wanka yafito ya hau tebur don yin break fast,
  Sonny yafito cikin shigar zuwa office yadan zauna tare, Yusuf suka karya nadan wani lokaci,
   Yusuf din ne ke fadawa Sonny yana son ya koma gida don ci gaba da harkokin shi don gudun kada su tsaya mai duk da yasan ba abinda zai faru insha Allah,
   Sonny mamaki ne yakama shi sosai yace yadawo ya zauna kusa da Yusuf din yana mai ce mai,
  May zai sa bazakai zaman ka anan ba, kawai ka share kowa,
  Don har na fara maka planing din din abin yi don ka kauda zaman banza,
   Amma ni naga kawai gara kabar zancen komawar ka yanxu har zuwa wani lokaci zai fi,
   Yadan dafashi yana mai cewa ya daure yaba su, dan time tukun kafin ya koma,
   Wanan zance na Sonny abin dibawa ne sosai don hakan zai sa su dan fita zancen shi,
   Amma kuma baya son yabar harkokin shi na can gida, sam
  Don haka yakira KB da Jibrin tare da,wani babban amin nin shi amanar kulawa da harkokin shi in secret,
  Bayan wata guda daga can ya wuce saudiya ya gabatar da aikin umurah,
  Yaji dafin wanan tafiyar tashi so sai don yakara yin hamdallah da rayuwar shi,
  Sosai suke business kamar a gida Nigeria suke, don Sonny mutum ne wanda bai ma natare da shi keta sam,
  Ba karamin riba yasamu ba daga wanan zaman da yayi acan
  Gashi ya murje yayi kyau yayi dan jikin jin dadi ba mai muni ba saboda yawan exercises,

   Alhamdullah Anty Dije ta sauka lafiya,tasamu Da namiji wanda bayan sati akasawa yaro sunan Abubakar Sadiq,
  Wanan sunan yaiwa maryam dadi sosai kasancewa suna A,A dinta ke nan,
   Sosai akasha buki sai kace sabon haihuwa ne kamar na farko,
  Inda Jibrin da KB suma sun zo har gida sun,wa Anty Dije barka
   Shi kanshi maigidan wanan haihuwar ba karamin dadin shi yaji ba don ga haihuwa ga samun girma daya yi agurin aikin su,
   Kayan goyo sosai yazo wa maijego da jariri da inda har dangin shi suka dan fara tsegumi akai,
  Wai ta tare guri taki bari wata ta shigo itama tadan lakaci arziki,
   Sai ita da yan uwanta ke cin abin su, ita dai bata biye masu ba sai harko kinta take yi kawai,
  Anci ansha sosai agurin kamar yadda yakamata a duk wani taro,
  Sai washegarin suna bayan an watse ne baba yazo da kamshi don ganin jariri
  Maryam ce ta dauko mashi shi cikin showel, fari kal,
  Bayan an gagaisa ne baba yaiwa yaron addu,a tare da yiwa uwa fatan gama shan ruwan zafi lafiya,
  Sai dan shiru yabiyo baya, alokacin ne yadan dago kanshi cikin fuskan damuwa yana cewa anty wace ke tsugune gefe guda saman wani dan karamin kujerar mata,
   Ya zancen maryam ne wai yaji shiru, dafarko yaji zancen rigirigi yanzu kuma yaji sakwot,
   Dije yakamata ku mai da hankali kinsan dai in badon a gurin ku take ba ba,zan barta har takai haka ba ba wani matsayi
   Don ni bokon bandauke shi wani abu mai muhunmanci ba ga diya mace,
   Har wasu yan uwa na acan gida suna ganin kamar cewa nine ke ra,ayin tayi karatun bokom
  Kinsan yadda nike da yan uwa na duk da bawai wani arziki ke gare ni ba amma ganin ina acikin gari har yanzu akwai hassada a tsakani na dasu,
   Anty Dije ta dan gyara zaman ta datayi mai kama da tsugun ni ta fuskanci baba da kyau,
  Tace baba gaskiya muma bamu so akai war haka batare da wani matsaya ba akai,
   Da farko ya nuna muna agaskiya baizo da wasa ba,
  Katseta baba yayi da cewa
  To aimu,bamuga alamar hakan ba, saurayi yadade tare da budurwa har tsawon wani lokaci amma babu wani magana mai karfi aciki,
   Gaskiya Dije idan har bazai wani motsa ba yakamata kufita zancen shi kada kice zaki biye wason ran yariyar nan,
  Kodai ba yanzu za ai auren ba to ya motsa ma na asancewa,yana ciki,
  Ya turo da manyan shi su shiga cikin harkan hakan zaisa kiwa yasan matsayin sa,
   Daga anty har Maryam kansu na duke akasa don jin maganar da baba keyi acikin bacin rai,
  Daga haka yamike yana cewa kunji maganata ke nan nafada maku nagaji da surutun mutane haka,har aciin iyayen ku ke Dije ina shan surutu,
  Itama Anty Dije mikewa tayi alokacin tana cewa baba yayi hakkuri insha Alkah komai zai zo karshe badadewa ba,
  Har baba ya bargidan kan maryam yana kasa aduke, cikin ladabi,
   Daren ranan Maryam bata samu yin wani barcin kirki ba kamar yadda tasaba gatada karatun test nan da kwana biyu,
  Saboda maganar tazo mata abazata don bata tsanmaci baba zai yi wanan zancen ba,
  Washegari haka ta tashi bawani kuzari atare da ita saida Anty taimata magana sannan tadan sake ranta,
   A makaranta duk yadda taso taboye wa safiya abin bai yiyu ba,
  Don haka safiya sai taji kawai itama bataji dadin ganin aminiyar cikin damu ko yaushe kan zance guda
  Gaskiya yau zata fada mata gaskiya cewa ta rabu dashi kawai takama masu zowa son ta da gaskiya,.
  Don ko a kwanaki wani abokin Jibrin yai masa zancan ta,
   Zaune suke a cafeteria su na son dan shan, drinks,
   Maryam wace ta dade da lulawa duniyar tunane, ko bata ko san ida suke ba a lokacin,
   Safiya tadan mata kyatci da hannu a fuska tadanzabura kamar wace taji tsoro,
   Dan ajiyar zuciya ta sake tare da kallon safiya din tana kokarin kako murmushi,
 Safiya tadan kai mata harara cikin murde fuskanta,
   Wai Maryam mayke damun ki hakane pls,?
 Tadan gyara zaman ta,tace bari kawai safiya wallahi ina cikin damuwa,
  Tun jiya da baba yazo muna barka haihuwa,,
  Dakata Maryam, wallahi ki,yiwa kan,ki fada ki danai irin wanan dogon tunanen kadafa ki jawa kanki matsala ina fada maki kullun,
   Akan namijin daba ki tabbatar ko zaku zauna tare zaki halaka kanki,
   Tadan kara nisawa tace ,baba yazo jiya yaiwa anty Dije tas akaina,
  Maganar baba tajiya yasa nakara sanin cewa, A A ba sona da aure yakeyi ba kawai dai,yana son amfani dani, ne ya nunawa duniya,
  Don haka maryam da kullun aitawa yar uwata fada akaina,
  Gara kawai in rabuda shi in huta Allah yabani wani yafi min safiya,
   Subbahanallahi maryam kada kuyi saurin fadar haka mana,
  Nan da nan idonta yakawo hawaye, kamar zatai kuka,
  Wallahi safiya hakan yafi min don bazan yarda kullun mahaifina yaita bata ranshi akaina ba,,
  Dan shiru sukayi a tsakanin su, nadan wani lokaci
  Safiya tace kenan kina nufn duk son dakikewa A,A ya tashi abanza kenan,?
  Saida ta share kwalar da ya silalo mata tukun sanan tace,
  Gaskiya kan safiya rabuwa dashi zaifi min
  Yanzu ke maryam bazaki canza shawara,ba akai,
  Ki tunkare shi kiji may yake ciki akai, ?
  Maryam ta katse Safiya da cewa ,
  Wani, ?  Allah ya kyauta min, shi bai mun magana aure, ba  nice zan masa,
  Kawai dai fita batun shi, zanyi, yafi mun,
 A,a maryam sam gaskiya, bai kamata muyiwa A,A haka ba kada mu kasa mashi uzuri pls,
  Muzo mu kamashi da laifin daba tashiba shi baima san yayi ba,
  Yanzu dai musan yadda zamuyi kafin lokacin don musan mafita
   Amma dai kin san bazan iya tun,karanshi da wanan zancen ba,
  Kadafa ki manta har yaya illiya yakirashi kan zancen amma sai ya doje kawai,
  Shine yanzu kike ganin nizan iya tunkaran shi da wani zance can,
  Kenan ma nice mai son ya aureni bashi ba,,
   Kai gaskiya duk zancen ya,daure min kai wallahi,
   Amma ki barni dashi kawai zan san yadda mukayi dashi,
  Sam bazan nuna mashi cewa ma kin san da wanan zancen ba,
  Maryam takara goge hawayen da ya kara makale mata tace nagode kwarai safiya da wanan shawarar taki,
   Haba maryam kifi karfin haka fa agare ni mayye na wani godiya bayan duk yiwa kaine hakan,
  Safiya tace daga gobe zan insha Allah zan tunkare shi,
   Shi ko A,A yadauka duk gajiyace tasa maryam rashin shigowa school yau,
  Saida wani ke ce mai ai yaganta ta shiga napep zuwa gida yadauka malam din bai shigo bane,
  A,A yai mamakin ji cewa  Maryam tashigo school ya batare da tai mai waya ko ta iso inda yake ba,
  Don haka ba bata lokaci yadauki waya ya kira ta,yanamai tambayar ta ko da gaskakene yau tashigo school din,?
  A dakile taba shi amsa da cewa eh, kawai ta kashe wayan ta zuviyar ta na mata kuna, sosai,
  Mamaki fam a zuciyar shi don tunda yake da maryam yauce rana ta farko da ta taba mai irin haka,
 Wanan abin yai matukar bashi mamaki da daure mai kai alokaci guda don sam bai kawo komai ba sai tunane, may ke faruwa,?
   Dadare yazo gidan su amma sai tace ace mai bata nan kawai haka yasa yakara rudewa,
 
  Washegari Safiya ta samay shi a office din shi yana zaune yana aiki acikin computer tar shi yana saye da riga shirt mai dogon hannu fara,bakin wandon Jean's a jikin shi, sai yar farar glass da ya manna wa idon shi,
  Da sallamar ta tashiga office din nashi yana ganin ta yadan yi murmushi yana mata iso data shigo,
    Bayan sun gaisa ne safiya ta fara shedawa A,A yadda mahaifin Maryam, yasa ta aga ita da yar ta duk dadewanan nan
   Shiru yayi har zuwa lokacin da takare zancen ta da cewa mahaifin maryam ya dibar mata wa,adi,
  Hankalin shi a tashe yake batare da yaiwa Safiya magana ba
  Itama dai din kallonshi takeyi, don ganin irin reaction din da ya shiga lokaci guda,
   Saida yaji ta tana huce da iskan bakinta yadan gyara zaman shi yana cewa,
  Safiya, wallahi duk na ma rasa may zan ce dake,
  Sai kuma yasoma share zufa duk da sanyin A,C dake office din nashi
  Aiko magana zakayi don musan mafita, daga cikin
 Yadan ce cikin marairaice murya, wallahi safiya akwai abin da nake planing akaine, shiyasa,
  Bawai sharewa nayi ba yadda kuke nufi, ba
  Safiya tace malam ba fa wai aure akace kuyi yanzu ba fa
  Kawai da ka gabatar da magabatanka suga iyayenta don manya su shiga shiga cikin zancen,
  Saida ya kara share, fuskan shi karo na barkatai,
  Safiya tace kaga aure sai lokacin da katashi ke nan,
  Yace nasan da haka safiya amma abin dibawa anan shine kokari nakeyi ingama abubuwan dake gabana tukun
   Su kwantar da hakalin su bawai zan yaudareta bane,o something like dat,
   Kawai dai zan samu, illiya idan yazo muyi magana akai,
  Safiya tace malam idan har bada magana mai karfi zaka je ba kada katafi pls,
    To safiya idan sun min haka basuyi min adalci ba gaskiya
  Kallon shi safiya tayi da mamamki,
  Tace malam waiko kasan duk maganar da kayi da mahaifiyar ka ranan da kukaje da maryam gaida ita duk a kunen maryam ne
   Ido waje yake kallon safiya da mamaki da kaduwar jin zancenta,
  Nan dai takwashe komai tafada mai wani rin nauyi da kunyane suka lulube shi lokaci guda,
  Safiya takare zancen ta da cewa malam don Allah kada k bawa maryam, baya ka guje ma,ta
 Sai kuma sai zuciyar ta yai sanyi tana batun sa kuka,
 Tamike tabar office din batare da ta saurare shi ba,,


ZEEE.   MAKAWA
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
  FUREN     JUJI
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
           3鈨�9鈨�

ZAINAB IDRIS MAKAWA,,

  Alhamdullah Yusuf ya kammala wani course da yadan kara tsayar da shi kasar Korea,
  A harkan business ne dama ya tsaya don kara ita fasaha akan, kasuwanci
    Don haka yanzu kimanin watan shi takwas ke nan rabon shi da kasar shi,
  Duk abinda yakeyi yanzu hankalinshi yakoma gida Nigeria musan,man kakar shi wace yabar ta kwantagora, tare da Dad din shi,
  Saboda yasan cewa babu shiri atsakanin su saboda banbancin churches din su, da suke bi,
   Yasan cewa yan church din su Dad basu kaunar mabiya Olumbo,
  Sonny ya na hankalce da Yusuf din duk kwanakin nan baya son walwala sosai,
     Lafiyayyen abinci tare da abin sha daga yayan icce,aka hada masu a matsayin dinner yau,
   Sai da Yusuf ya idar da sallah shi na isha,i tare da,shafa,i da wuturi,
  Sanan ya koma yai wanka yafito cikin shirin shi,
  Yayi mamaki Kwarai da ya samu Sonny a zaune yana jiran shi,,
   Yusuf yadan bashi hakkuri tseda shi da yayi har zuwa wani lokaci,
  Cikin daga hannu Sonny wanda,yake saye da wata far coth da wandon shi fari, sai bakar shirt da yasa daga ciki,
  Yadan, dago wa Yusuf, hannu alamar ya share ba matsala, kawai,
  Nan suka zauna suka fara cin abincin su hankali a kwance,
  Saida suka dan dauki lokaci batare dayin wani magana ba sai karar cibin da suke cin abinci  kawai kake ji yake tashi,agurin,
  Sonny ne yadan dago kai yakalli Yusuf wanda dabi,un cin abincin shi yanzu duk ya canza,ba kamar da ba can, baya,
   Murmushi mai sauti Sonny yayi wa Yusuf wanda hakan yasa shu dago kan shi yana mai kallon shi,,
  Sai kuma ya daure fuska acikin yar damuwa yace,
  Man this your religion is good, and have a nice characters,
   Unlike Christianity,
  Da sauri Yusuf yadago kai ya kalle shi,
  Yace ma Yusuf man see how yo pray everyday,
  Bayan yawan sallah da kuke yi a kullun, batare da damuwa da ko kowa ba, alokacin yinta,
Amma su Christian saudaya kawai suke zuwa church a cikin sati, inda wasu ma bawai dole su tafi ba,,
Littafinku mai tsarki muslumai dayawa sun haddace shi a kan su ,
   Littafin ku mai tsarki Alkur,an, yana nuna abu guda ne ga kowani irin yare za,a fasssara shi,
   Zaku iya shiga kiwani irin massalaci kuyi salkah aduk lokacin da ta riske ku
Ba kamar Christian ba suda da angan ka sai an tambaye ka wani church, kake zuwa a cikin sati,
  Idan kafadi wanda ba nasuba, zasu iya bata rai, dakai afili,
  Dazaran ance kai musulumi to daidai kake dakowa daga cikin musulmi, kuma a nuna ma so da kauna alokaci guda,
  Sai kuma duk abinda ka iyayi dazaran kace Allah shikenan an yarda da zancen ka,kowace iri ce,
  Amma su Christian dazaran kace God zaka zama abin zargi ke nan in ma bakai hankali ba sai antara ma taron,mutane,
  A bincike ka, wani irin God, kake zance shi god din yan Catholic ne ko god din Anglicans, kona na living faith, kok, shin na deeper, life,
   Duk da su ma musulmai suna da wayan nan akidodin a tare da su amma sai kayi nisa sosai a cikin su zaka iya ganewa,
  Amma su kan Christian a filli suke nuna nasu,
  Zaka iya jin ance maka ai jabun pastor ne wani
  Banda musulumai da ko yaya imanin ka yake zasu iya binka sallah, a jam i
  Gashi su musulmai aduk lokacin da suke azumin su na watan ramadam mai tsarki, duk duniya zasu sani sanan sauyi zaizo wa kowa daga musulmai har Christian alokacin wanan azumin
    Amna baka taba jin wani abu maka mancin haka acikin bautar Christian,
  Idan wani abin al,ajabi yafaru musulmai zasu yarda da cewa daga Allah, ne amma su Christian sai su ce wai in Jesus, name, wasu kuma suce karfin shedan ne,
  Zaka ga idan mai wa,azin musulumai yana waazi, musulumi koda karamin yaro ne ya kewaye shi yana saurare har zuwa lokacin da za,a tashi koda kuwa mutum nada abin yi alokacin ba zai tafi ko ina ba, ko fitsari azasu yarda su tagiyi ba don kada afadi wani abinda basu ji ba,,
   Idan ka lura da musulmi yana girmama pastor afili, badon komai ba sai don sanin cewa shugabane na addini,
  Amma,su Christian suna jin haushin limamen musulumai sosai,
  Yadda zaka ga musulmai suna girmama shugaban nin su sai kaga su Christian suna kokarin gardama da pastor cin su,
 Kai abubuwa da dama nayi searching din su naga akwai bambanci halaiya so sai a tsakani,
 
   Tunda ya fara dogon sharhin shi Yusuf yadakatar da cin abincin da yakeyi yana mai tsura mashi ido,
  Acikin zancen Sonny din Yusuf yagano cewa akwai wani magana mai muhin,manci, da Sonny din ke son yi dashi,
  Hakan yasa ya tatara hankalin shi gabadaya yana mai sauraren shi,
  Yyana kaiwa karshe sai ya kalli Yusuf da kyau ya aje cokalin da ke hannun shi a cikin plate din da yake cin abinci,
  Yakara duban Yusuf din sosai, yace a yar fahintar da nayi yanzu Joe nagane cewa muna da banbancin addini sosai ni da kai,
  Kaga zancen mu hada harkokin mu kamar yadda muka saba ada bai taso ba ,
   Kagane ko?
       Yusuf yace,,
Fadi maganar ka kawai ina sauraren ka ai,,
  Sonny yadan girgiza kai yana mai cewa don haka na yanke shawara nakuma rubuta komai a rubuce har an sa min hannu, cewa
  Nabar maka duk wasu kaddarori da suke a hannun ka saboda nasan cewa kana bukatar taimako yanzu a rayuwar ka so sai,
  Nayi hakane don in kareka daga duk wani barazanar da za,a yi kawo maka na cewa zasu iya gurgunta ka daga cikin har kokin ka,
   Wata irin karfafan ajiyar zuciya Yusuf ya sake da yaji wanan zancen na Sonny,
   Fuskan shi dauke da alamar damuwa mai fayyace mamaki aciki,
   Magana Yusuf din ya fara cikin wata irin murya mai ban tausayi don duk mamakin wanan hukuncin na Sonny ya ruda shi,,
   Kawai sai yaji Sonny din ya kaure da wani mahaukacin dariya alokaci guda,,
  Sai kuma ya koma ya tsuke fuskan shi ya fuskanci Yusuf din karo na biyu yana mai kura mai ido cikin ido,
  Yace may zakace min Joe, koka manta cewa da taimakon ka muka kai wanan matsayin da muke aciki ni da abokina
  Inda Allah bai hada mu da kai ba ka dage har saida kaga mun gama karatun mu aida ba mu kai haka ba, ko ?
  Mikewa yayi ya zagayo har zuwa kujerar da Yusuf yake zaune yadan duko yarankwafo zuwa gare shi yana mai magana kamar cikin rada,
   Yace , don't say thanks pls,?
  U deserved it
Yusuf wanda kanshi ke a duke don jin zancen yake tankar a mafarki,
  Ya dan dago kai ya kalli Sonny din kara na biyu cikin mamaki,
   Murmushi na gamsar wa Sonny din yai mai alamar eh,
   Haka suka tashi gurin inda Yusuf kewa Sonny adduan fatan shiryuwa hanya madaidaiciya ,
  Batare da sanin Sonny ba Yusuf ya gai,yato su jibrin tare da KB inda sukazo mai tare da,Abdulsamad,
   Saboda yanzu suyake ji tankar yan uwan shi na jini,
      Sunyi mamaki sosai irn dinbin dukiyar da Sonny ya tara a kasar mutane haka bayan ga kasar shi can na haihuwa suna bukatar shi,
   Sun yi wa Sonny godiya sosai dafatan kara samun daukaka a dukiyar shi,
  Shiko sai mamakin irin yadda suka dauki joe tankar dan uwar haihuwar bawai kawai saboda addini suke nuna mai haka ba,
  Sosai Sonny yaji dadin zuwan su inda ya mai dasu kamar wasu manyan guest din shi,
  Satin su guda sukadawo gida cike da farinci, dakuma alheri mai yawa,
    Saida Yusuf ya tabbatar da cewa komai da ya turo su Jibrin da shi da KB sun kammalla mai
  Sannan ya fara shirin komawa gida Nigeria, tare da karfin gwiwa atatare da shi,
 
    脌nty Dije ce zaune a saman tabarman robar da ta shimfida a,waje saboda zafin da akeyi a garin tankar rana zai dafa mutum,
  Gefen ta Abubakar ne a kwance cikin net na yara yana barcin shi hankali kwance,
   Maryam ce ta fado gida a daidai wanan lokacin, cikin gajiya tashi gida da sallamar ta a bakin ta,
   Anty Dije tadan daga kai, takalle ta gami da ajiyar zuciya,
  Tacd don Allah maryam, huta kidan taimaka min muyi aikin nan,
   Maryam wace tanawo wani farin kujerar roba dake aje a gefe guda, ta zauna,
  Tace wai Allah ana dai zafi gaskiya, sosai shi yasa yau ma banko tsaya jiran safiya ba na sa kai kawai na wuto,
  Kallon ta Anty Dije tayi cikin yar  tuhuma kamar zata daure sai kuma ta kasa
  Tace shi A,A din ya daina dauko ku ne yanzu,?
   Maryam wace tambayar yazo mata a bazata,
  Shiru tayi saboda ta rasa ansar da zata ba Anty Dije a lokacin,
  Kara maimaita tambayar tayi wa yar kaunar nata,
  Wacce dama duk kwanakin nan tana lura da bata acikin walwala tun lokavin da baba yazo da zancen ta,
  Dan hawayen da take kokarin makalewa, ne yadan digo daga idon ta,
    Ki tashi ki dauki abinci kici inji Anty saboda ta fahinci, cewa kuka kaunar nata  take shirin yi,
   Tausayin irin hanlin da yar uwan nata take ciki takeyi
  Saboda ta san cewa tana cikin wani hali saboda so,
 Maryam ta share hawaye ta da bayan hannunta ta mike zuwa cikin da kunar su,
 Kallo anty Dije tabi bayanta dashi tana mai mata fatan alheri a rayuwa,
  Fatan dai Allah yai wa Maryam din zabi na alheri, a rayuwa,
   Tunda maryam tashiga ciki tana zaune, a bakin gadon ta ko, takalma bata cire ba akafar ta,
  Wayar ta dake a cikin jakar ta ce tai kara alamar kira,
    Kamar ta share kamar kullun saida tace bari yau ta dauka taimai kashedi ya daina kiran ta kwatakwata,
  Cikin wani irin murya mai birkita maryam a duk lokacin da taji shi,
  Wanda yasa gaba daya duk maryam din ta rikice, alokaci guda ta rasa duniyar da take,
  Wani irin taji aranta na yadda sam bazata iya fada mai maganganun da ta shirya fadamai ba,
 Maryam ta saki wani irin  ajiyar wanda shima A,A din yaji kamar yazo inda maryam din take alokacin yabata hakkuri duk da irin kunyarta da yake ji,
   Shima A,A din anashi bangaren ajiyar zuciyar don jin cewa maryam din tadan sauko daga fushin da ta dauki lokaci mai tsawo tana yi dashi,
  Yakara cewa cikin wata irin murya ransarauniya maryam yadade ga A, A gaban ki tuba yake yi,
  Murmushi ne ya subuce mata tai shi a hankali, duk yadda taso tai magana alokacin ta kasa,
  Yace Maryam ina fatan zaki bani dama in zo in maki bayanin irin abin da ake ciki,
   Shiru tayi saboda sam bata san may zai ce mata ba idan har yazo din,
  Tasan dai bai wuce yace mata kawai tayi hakkuri ya aure su su biyu kamar yadda safiya tace yace,,
 Wani irin ajiyar zuciya tasake tace, idan zuwar naka bazai zai haifa min alheri ba kawai kabarshi
  Yar dariya tayi irin ta mazan da suka san kan su,
  Ya Allah dai ya kai mu anjima ki dubi hanyata nagode,
  Idan ta ta lumshe tanamai jin wani iri atare da ita
  Ajiyar zuciya tayi mai fitar da sauti tana mai bude idon ta, da suka sauka a saman na Anty Dije,,,,,,


ZEEE.  MAKAWA

馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
   FUREN      JUJI
馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯馃尯
          4鈨�0鈨�

ZAINAB IDRIS MAKAWA,,,

Yan uwa musulmi barka mu da jumma,a , Ubangiji Allah yasada mu da Rahama da Albarkan da ke cikin wanan ranan,
  Allah ka yafe muna kurakuraren mu Allahuma Ameen,馃憦馃憦馃憦馃憦馃憦馃憦


  Sanye yake cikin wasu, fararen coth, da wani, farare, takalma rufaffu, kayan sun karbi,
 jikin shi, sosai, sai idon shi dake saye da dan farin glass karami,
   A hankali yake ta,kowa daga matakalar jirgin, guda ,guda, hannun shi,guda yana cikin aljihun wandon shi,
   Jirgin su a airport din Lagos ya sauka, inda masu taron shi suka zo,,
   Gurin screening yanufa batare da wani bata lokaci ba akai mashi, duk wani screening yadda yakamata,
  Daya daga cikin driver s din da suka zo daukan shi yakar bi wata yar case da ke hannun shi,
   Bawani bata lokaci su,kabar airport din shi da wa yanda suka zo tariyan shi,
   Sannu a hankali yakarewa gidan shi kallo gidan da yakewa kallo tankar wani sabon guri da bai taba zama ba,
  Saboda gyaran da ya turu da kudi akai mai,
    Anan falon ya zube saboda yana tare da gajiya, ba abin da yake bukata sai ya dan watsa ruwa ajikin shi,
  Ko zaiji dan karfi karfi ajikin nashi, kafin ya samu dan abin da zaici,
   Motsin da yaji ne ya sanya shi saurin daga kai, don ganewa idon shi kowaye,
 Hakan yai daidai da Ejoma, wace ke sauko daga wani dan steps da yafito wani part na gidan,
   Da saurin ta tazo daniyar rungumar shi kamar yadda su ka saba idan yadawo koda gurin aiki ne,
 Da sauri yadan jaye jikin shi daga gareta amma yana mai,mata murmushi,
   Dan yaron dake rike a hannun ta ya daga sama cikjn wasa yana zagaya da shi,
  Sauke yaron yayi yana mai kallon Ejoma wace ke saye da wani bakin buje da yafitar mata da surar bayanta baro,baro, gashi dan guntu, daidai iya katarar ta,
   Ejoma ce tafara magana bayan taga ya, sauke yaron daga daga shin dayayi,
   Tace brother we don base, woo,
  Shima murmushi yai mata yana cewa where my grandma ?
  Grand mother dey for village since, tree months ago,
   Murya kasa kasa yake tambayar ta ya akai haka ,
  Ejoma tadan tabe baki tukun sai tace,
  You know Dad no dey allowed her to go to her church,
   A dan tsora ce ya dago fuska cikin mamaki da jin mamakin zancen ta,
  Saikuma ya maida mamakin nashi zuwa dan murmushi mai sauti, saboda tunawa, da sanin kowaye mahaifin shi,
    Fuska kumshe da murmushi yace ma Ejoma is alright, i, will go and seen soon,
   Daga haka ya haura zuwa sama inda dakin shi yake don yadan watsa ruwa,
  Cikin daga murya Ejoma ke cewa brother your food is ready on the table,
    Yakai wani lokaci a sama sannan ya sauko daidai lokacin da Ibrahim shima yashigo gidan, don taron shi,
   Duk atare suka taru suka ci abinci, gabadayan su,
    Tsab ya mike yashiga wani dan bayi dake makale a cikin makewayin,
  Alwalar sallah azuhur yadauro alokacin amma saboda gajiya nan ya tsaya a falo saman sallaya,
   Addu,oin da yajeyi bayan sallah ne ya gabatar alokaci har tsawon wani lokaci,
   Brother are still bearing the Muslim,
   Idanu ya zuba mata don mamakin kalamin ta, saboda yaji abinda tace kamar a mafarki,
  Don haka ya shafa addu,an shi ya fuskan ce ta, da kyau,
   Gyaran murya yayi yace mata dama ana canza addini ne anyhow,?
   Sai ta girgiza kanta tace ba haka bane kawai dai taji Dad na cewa evils spirit din da suka shige shi har ya juya zuwa Islam,
  An, kore su dakarfin addu,oin pastor's masu yawa daga cikin pastocing su,
    Wani iri Yusuf din yaji a cikin zuciyar, wanan maganar ya kasance mara misaltuwa agare shi,
  Shin dama ashe har yanzu Dad naga bakar shi na cewa sai ya canza addinin shi da yake ra,ayin yi a rayuwar shi,
   Gaskiya zai dauki wa Dad duk wani mataki da yakamata yadauka wanan karo,
  Ai bashi kadai bane, dan shi yafara zama musulmi, da zai ce ba zai hakkura ba ,
   Koda kuwa Dad din zaiyi barazanar kwace mai duk wani dukiya da ya mallaka a rayuwar shi batare da yabar mai koda kwandala ba,
  Ya tuna da labarin da Abdul samad yabashi, na,wani matashi , da yai zamani da manzon Allah S,A,W
   Maisuns Mus'ab Ibn Umair, matashine, mai ji da kanshi a cikin garin makka,
  Matashin ya fito daga wani family mai karfin arziki sannan,sannan ya kasance dangata sosai daga duk wani matashi na zamanin,
  A wancan lokacin kaf samarin Makkah suns jin jins mashi wajen ado, don ko turaren ma dayake amfani dashi alokacin abin kallo ne,
  Sannan mahaifiyar shi takasance mai tsananin sonshi wanda hakan ya haifar da shakuwa mai karfi gaske a tsakanin su,
  Tufafin da Mus,ab Ibn Umair yake sawa, da takalmin shi masu matukar, tsadane so sai,
   A lokacin da manzon Allah SAW ya fara wa,azi da kira ga mutanen makkah akan subi addinin Allah, watau musulunci,
  Yawan wa,azin da yake saurare daga Annabi yaji ya gamsu zai shiga addinin islama.
   Hakan yasa ya fuskanci tsanani da azaba da rashin galihu,
   Inda yakoma yakassnce tankar almajiri, duk wanda yaganshi bazai gane shine shiba
  Dan yadda ya koma ma abin tausayi don hatta suturar jikin shi duk sun yayyage,
  Sai watarana mahaifiyar shi tace ya kai Mus,ab kadawo vikin addinin mu kafita,wanan addinin na islama, da kashiga
    Amma sai Mus,ab yaki suka dinga azabatar da shi azaba mai tsanani, amma yaki ya tsaya akan addinin shi na islama,
   Daga karshe ya koma gurin Annabi Muhammad, (SAW),
  Ya hakkura da duk wani daular duniya da ake kwadaita mashi, anan

  Yusuf yanisa ya waiga inda yake tsaye a bakin window,
  Yace a ranshi kida Dad zai kwace mai duk wani abu da ya mallaka bazai fita cikin addinin islama ba,
  Shi yanzu yasan cewa yafi karfin duk wani barazana da mahaifin shi zai mai akan dukiya,
    Kwana biyu kawai yayi da hutawa, ya shirya don zuwa ya dibo, kakarshi wace bai san halin da take ciki ba a yanzu,
    Ba karamin tausayi matar yake ji ba a matsayin ta na wanda, ta rage mai yake gani kamar uwar shi,
   Tana zaune ta mike kafa a saman wani tabarman roba, a gefen da dan inwa yakai acikin gidan nata ,
  Sai ganin shi tayi kamar a mafarki don sam batayi tsan manin cewa zata kara ganin shi arayuwar taba ,
  Tadade rungumay dashi a jikin ta tana kuka tana wani gwalanci irin na yare,
  Sai kuma komay ta tuna tasake shi da sauri tana ta tatabashi kamar tana tuhumar ko ba shi bane a gabanta,
  My child are still in that religion ?
   Mumushi yayi ya jawo goshinta ya man,na da nashi yace mata
  Even you mama you will joined me, very soon
  Dan tura shi tayi baya yawuce tangal, tangal kamar zai fadi,
  Dariya tabashi a yadda yaga tanayi don daga hannun ta tayi tana wani kewaya shi a saman kanta tana cewa over my death body,
  Komawa tayi ta zauna tana wani bubuga kafa wai ita tayi fushi,
   Direct wuce yayi zuwa cikin dan falon ta na ginar kasa wanda saboda tsufa har yana batun zubewa,
   Photo mahaifiyar shi ce yai tozali da shi, wace ke saye da wani zanin irin na matan IBO,ta daura wani dankwali daurin gwagwaro,
  Murmushi takeyi da aka dauke ta kamar zatai magana
  Yadade yana kallon photo yana maiji dama ace ta musulunta ka fin ta mutu,
  Shigowar grandmother, yasa,shi barin gurin zuwa saman tsofin kujerun dake falon,
   Itama zama tayi saman kujerar dake gab dashi, tana mai mai kallo cikin da muwa,
    Shine yafara magana yana mai tambayar ta may yasa ta dawo kauye da zama,
  Bayan tasan cewa babu wani wanda zai kula da ita anan yanzu,
   Yace ga gidan shi can abirni babu kowa aciki mai yai hana taje can ta zauna,
    Saida mama tadan waiga kamar akwai wani gidan wanda zai ji abin da zata fadi alokacin,
   Tadan kara gyarazaman ta har kusa dashi tace,
  That your father is very wicked,
 He can killed person, woo
     Nan take sheda mai cewa bayan tafiyan shi taji mahaifin nashi na waya da wasu cewa a kama Joseph ai masa duk wani horo da ya dace dashi don yadawo cikin Christianity,
  Murmushi yai mata don dama yasan cewa shine ke turowa ai mai wanan wulakancin,
  A ranan Yusuf bai yarda ya kwana wanan dan kauyen da yar tsohuwar ba dawowa sukayi tare,
  Inda taga duk gidan ya canza mata saboda gyare,gyaren da akayi wa gidan,
  Sosai gidan ya canza mata cikin dan lokaci har ta rasa gane ko ina ne part din ta na da,,
  Ganin Ejoma da tayi tazo taron ta yasa ta gane cewa lalai agidan shi suke,
 
  Wanan karon sosai ya shirya ma shiga garin na kwantagora
  Badon komai ba sai don ya tunkari mahaifin shi wanda ke ta yi mashi bita da kulli,
   Motorcine har guda uku yatanada don wanan tafiyan,da yake son yi kafin ya fara harkokin gaban shi,
 Saidai wanan karon ba,a gidan mahaifin shi zai saukaba kamar yadda ya saba,
  Hotel lafiyayye aka kama masu tun kafin su iso garin,
 Har abincin da zasu ci an tanadar masu shi, KB ne yai wanan hidimar,

   Zaune take tana kwalliya a bakin mirror saboda tana expecting din zuwan A,Adin ta,
   Muryarda taji yana sallama tuni zuciyar ta, ta tsinke
  Zabura tayi saye a dan tsorace, tadan saurara ko kunnuwar take mata karya,
  Bashi bane a zahiri don sam ba su  tsan manin cewa zai zo a wanan lokacin ba,
   Muryam Anty Dije ce ya kara tabbatar mata da cewa shi din dai ya shigo,
  Inda taji Anty na tacewa  sannu da zuwa Yusuf
Kaine tafe babu ko labari, zuwa balle a shirya ma,zuwan naka,
  Wani murmushi yayi mai sauti yace bana son ku wahala ne ai shiya sa ban fada maki ba,
  Sigar dayake magana kawai zai tabbatar ma da ya kara samun canji a rayuwa,
  A,hankali yake karasowa zuwa inda anty take dauke da Abubakar a hannun ta,
    Ya saye da wani yadi mai laushi baki ajikin shi sai wata yar jar hular dara dayasa wa kanshi,
 Gadan gadan yanu yau,fi inda take da yaron dagani duk hankalin shi na gurin yaron, wanda bai taba gani ba, sai
   Cak yadauki Abubakar yafara dan wasa dashi ,daidai gitowar Maryam wace kamshin ta kawai kawai, zai saka gane tafito,
  A hankali ta iya furta mai sannu da zuwa,daga haka tasa kai da niyar fita kawai,
 Gabantane yafadi saboda ganin yadda Yusuf ya canza gabadaya cikin lokaci guda,,,,,,,


ZEEE. MAKAWA

adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *