Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Wednesday, April 15, 2020

Dangantakar Zuci Complete Hausa Novel

adsense here
Dangantakar Zuci Complete

[25/07, 09:00] Aishat A. Muhd: 🍃 *DANGARTAKAR ZUCI*🍃




*written by*
Aishat A muh'd

           &
Sumayya salees sadeeq





*BISSMILLAHIR RAHMANUR RAHIM*



_Dukkan godia sun tabbatar ga Allah (SWA), da ya bamu ikon rubuta wannan littafin, tsira da amincin Allah su k'ara tabbata ga Annabi Muhammad (SAW), Yah Allah yanda ka nufe mu da fara rubuta wannan littafin Allah ka bamu ikon kammala shi lafiya_



_wannan labarin littafin bamu yi shi don wani ko wata ba kirkirarren labari ne dafatan masu karatu xaku biyo mu don jin kalar wannan labarin na *DANGARTAKAR ZUCI*_




*Page 1-2*




     Wata er yarinya ce kyakkyawa irin  chocolate colour nan tana sanye da wata er farar vest irin ta yara da yake lokacin xafi ne sai k'aramin wandon vest d'in farare ne sol kalar su sai dai kuma kash duk sunyi datti kayan sosai duk sun fita hayyacin su ita ma tayi dukun dukun gaba d'ayan ta, er kimanin 7year's tana 6uruntu a kitchen duk da tsayin ta bai kai ba sai da ta taka kujera tukunna ta bud'e wata tukunyar miya tasha naman kaji xuk'u xuk'u a ciki wani babban spoon da plate ta d'auko ta tsomashi acikin miyar sai da ta kwashe naman ciki Kaf gaba d'aya sannan ta mayar ta rufe tukunyar tare da sakko wa daga kan kujerar.

   A k'asa ta xauna ta hau cin naman nan hannu baka hannu kwarya tana sauri don kada a shigo a gan ta a haka, tayi nisa acikin ci sosai don ta kusan cinye rabin naman sai ga wata er dattijuwa ta shigo kitchen d'in tana ganin ta sai ta buga salati tare da cewa
" Husna!!! "
Da sauri yarinyar da aka kirawo da husna ta d'ago kanta tuni ta kwa6e baki xata sau kuka cikin sauri er dattijuwar nan kakar su suna kiranta da hajia maamaa taxo ta fisge plate di'n hannun husna cikin fad'a ta fara cewa
"yanxu fisabillah husna kin kyauta ki kwashe dukka naman abincin kisa a gaba Kina ci sai kace naki ne ke kad'ai, yarinya kamar mayya Indai taga nama sai taci "
Tuni husna ta 6are baki ta fara kuka sosai har da majina tana kok'arin xubo wa hararar ta hajia maamaa tayi tace
"bari yayan ku ya shigo Kinsan baya cin abinci sai da nama koh, gashi kin ta6a wannan baci xai yi ba wallahi ke dashi ba ruwa na, ja'irar yarinya fita daga kitchen d'in nan kije babar ki tayi miki wanka ji yanda kika xama yarinya sai shegiyar kaxanta "

Da gudu ta fice daga kitchen d'in tana rusa kuka har da d'ora hannu akai, girgixa kai hajia maamaa tayi tare da rufe plate di'n naman nan tana cewa
"Bari su na'ima su shigo sa ci don nasan ko Karen hauka ya ciji yayan ku baxai ci naman nan ba"

A parlour ta tarar da husna mai kuka har ta 6ingire da bacci hannu a baki ga hawaye sun bushe a fuska banda majinar hancin ta da ta bushe ita ma sai faman ajiyar xuciya take, girgixa kai ta sake yi a karo na biyu tare da ta6e baki tace
"ohhh ni ma'u yanxu ja'irar yarinyar nan bata tafi Anyi mata wankan ba sai taxo tana yi min bacci a parlour "
D'an tsaki taja tare da xama kan kujera ta d'auke glass d'in ta ta kwama a fuska tana kallon tashar sunnah T.v  sun sako wa'azin sheik Isah Ali pantami ta nutsu tana sauraren wa'azin.

Acikin nutsuwa ya shigo parlourn da sallama hajia maamaa ta amsa mishi sallamar tashi cikin matuk'ar gajiya da wata uwar yunwa da yake ji ya nufi kitchen bai kula ta ba kamar 2 seconds ya fito daga kitchen d'in a fusace ya Kalli hajia maamaa da take xaman jiran abin da xai ce yace
"maamaa uban waye ya cinye naman miyar nan? "
Kai tsaye hajia maamaa tace
"wa kasan xai cinye Idan ba ja'irar yarinyar nan ba husnah ita na kama a kitchen tana ci"
"kenan da kanta ta d'iba "
"k'warai da gaske"

Ya bud'e baki xai sake magana idon shi ya sauka kan husnah wadda take bacci hankali kwance a xuciye ya K'arasa inda take bai yi wata wata ba yasa hannu ya falla mata mari a gigice ta mik'e tana xunduma ihu hannun ta dafe da kumatun ta
"keeee kaxama rufe min baki yau sai jikin ki ya fad'a miki"
Belt d'in jikin shi ya fara kok'arin cirewa tuni ta hau rarraba ido jikin ta sai faman 6ari yake saboda tsabar tsorata don tasan halin Yah ibraheem akwai mugunta

Bata ankara ba taji saukar duka ta ko'ina tuni ta fara xunduma ihun axaba, hajia maamaa kuwa ko kallon Inda suke bata yi ba K'arshe ma sai ta shige bedroom don ita ta ja, shi kuwa ibraheem ya d'aga belt d'in ya xuba mata ta biyu Kafin ya ankara sai ga fitsari ajikin kafar shi husnah ta saki Haba ae tuni ya dad'a fusata yasa kafa ya haure ta ta fad'i k'asa tare da buga kanta jikin glass table da yake tsakiyar Parlourn  ae kuwa ta k'walla wata raxannaniyar k'ara

Mtswww yaja wani uban tsaki a dai dai Lokacin wani guy ya shigo parlourn da sauri duk ya rud'e ya nufi inda take ya d'ago ta xuwa jikin shi bai damu da dattin jikin ta ba adai dai lokacin hajia maamaa ta fito daga bedroom d'in don ta kasa xama jin kukan husnah yayi yawa kada ibraheem yaji mata ciwo...........



Aishat A muh'd
             &
Sumayya salees sadeeq
[25/07, 09:00] Aishat A. Muhd: 🍃 *DANGARTAKAR ZUCI*🍃




*written by*
Aishat A muh'd

         *&*

Sumayya salees sadeeq




*Page 3-4*




 Kallon kafar shi da k'asan wandon shi yayi yanda suka jik'e da fitsari kamar xai fashe da kuka haka yake ji xuciyar sai tafasa take ya fara cire dogon wandon trouser di'n da yake jikin shi cikin k'ank'ami Ya yar dashi daga shi sai T-shirt da boxer kawai ajikin shi, suna had'a ido da Yah Abdullah ya sakar mishi harara tare da cewa
"ibraheem me tayi maka kayi mata wannan uban dukan haka? "
D'an ta6e baki yayi Kafin yace
"ka tambayi maamaa xata baka labari "
Yana gama fad'in hka ya fice daga parlourn,sai da yaje d'akin shi yayi wanka sannan ya shirya ya fito direct part d'in mamee yayi da sallama ya shiga aka amsa mishi ko'ina fes sai tashin k'amshi yake a rayuwar ibraheem ya tsani kaxanta baya shiri da kaxamai ko Kad'an xube wa yayi kan kujera ya Kalli mamee yace
"mamee I'm very hungry and tired "
Cikin kulawa mamee tace
"Ohh sorry my boy, bari na xuba maka abincin"
Tana gama fad'in hka ta shiga kitchen da sauri ta xubo mishi fried rice nd costlow sannan pepper chicken sai wani hadadden kunun aya ta kawo mishi cikin sauri ya bud'e plate di'n wani k'amshi ya doki hancin sa ya lumshe ido tare da sakin wani lallausan murmishi yace
"wow that's my favorite food thank u mamee nah"
Murmishi mamee tayi kawai nan ya fara cin abincin cike da jin dad'i ko five Spoon's bai yi ba aka bud'e kofar parlourn aka shigo xumbur ya mik'e tsaye tuni fuskar shi ta rine da 6acin rai tsantsa kallon ta yake kamar xai yi amai cikin tsawa yace
"hey u uban waya kawo ki nan kuma, (Ohh kuji ibraheem da k'arfin hali part d'in su ne fah) "
Cikin mamaki Yah Abdullah yace
"gidan nasu kace uban waya kawo ta to nine "
6ata rai yayi sosai yana wani kau da fuska mamee dai ko kallon su bata yi ba Idan da sabo ta saba da ganin wannan tsakanin ibraheem da husnah don hka news paper d'in dake kan table ta dauka tana karanta wa 

Kamar ance ibraheem jiyo ka Kalli husnah yana kallon ta yaga wata majina ta fito ta hancin nata zuuut ta xuk'e ta wato ta shanye ta sai faman rarraba ido take wayyo Allah tuni ibraheem ya fara kakarin amai da gudu ya fice daga parlourn yana rik'e da ciki da baki, haushi ne ya ishe Yah Abdullah yace
"wallahi sai na saita wa ibraheem kai wannan iskancin nashi ya isheni wlh"
"a'a ba ruwan ka dashi wlh ae da gaskiar shi ji yanda jikin yarinyar nan ya koma don Allah waxai so ta tsaya a gaban shi yana cin abinci "
Girgixa kai kawai Yah Abdullah yayi tare da cewa
"toh mamee don Allah kiyi mata wanka lokacin islamia ya kusa"
"toh Shikenan "
Tashi tayi tare da kama hannun husnah suka nufi bedroom don yi mata wanka, yayin da Yah Abdullah ya fice daga part d'in.

Wanka sosai mamee tayi mata tare da wanke dogon gashin kanta irin na fulanin asali a gurguje ta shirya ta cikin uniform d'in islamia ta fito caras kamar ba husnar d'axu ba, da kanshi Yah Abdullah ya kai su islamia tare da sauran en uwanta.........



*TUSHEN LABARI*

  Alhj ibraheem da hajia Asma'u en asalin garin adamawa ne fulanine na usuli aiki ne ya dawo dashi garin kaduna d'an boko ne na bugawa a jarida, sun haifi yara 4, muktar, mustapha,umar, sai autar su fatyma sun bawa yaran su ilimi na addini dana boko sun taso cikin tarbiyya mai kyau ga nutsuwa suna matuk'ar kaunar junan su sosai.

Gida babba Alhj ibraheem ya gina yayi part 4, kowanne part yana da girma kuma k'asa da sama ne ya bawa 'ya'yan shi maxa uku kowanne part d'aya idan sunyi aure sai su xauna saboda su fi xumunci da juna da kuma shakuwa, shi kuma ya xauna a nasu part d'in na cikon na hud'u sai dai su nasu flate ne babu bene kuma yana tsakiyar na 'ya'yan nashi.

Alhj muktar yayi aure da matar shi hajia halima suna kiran ta da mumy, suna da yara har guda 5, Abdullah, ibraheem wanda yaci sunan kakan su sai khadijah, Amina, Fadila ce K'aramar su.

Sai Alhj mustapha da matar shi hajia zulaihat suna da yara 5, kabeer, mus'ab, ummu aimana, marwa da autar su habiba wadda taci sunan babar Alhj ibraheem suna kiranta da Ilham.

Da kuma Alhj umar da matar shi hajia zuhra da yaran su 3, yaseer,rufaida da Asma'ul husna mai sunan hajia maamaa suna kiranta da husna, sai autar su fatyma tana auren wani babban d'an kasuwa itace matar shi ta biyu tana da yara 2 mata sai namiji d'aya, farida, raudah sai bilal, wannan familyn suna xaune lafia da kwanciyar hankali ga had'in kai da xumunci hka matan ma suna xaune lafia xamane na wayayyu kowanne da aikin shi .

Dukkanin su kyawawa ne kunsan Fulani akwai kyau masha Allah gasu farare ne sol gaba d'ayan su Idan ka d'auke husna da chocolate colour wato mai duhu bata kaisu haske ba amman duk tafi so kyau gashi kamar su d'aya da ka gansu ka ga en uwan juna, don Alhj ibraheem da hajia Asma'u auren xumunci akayi musu.

Duk gidan nan ibraheem IB jinin su bai hadu da husna ba ya tsane ta dalilin tsanar kuwa irin husna kaxaman yaran nan ne duk kuwa da tsabtar mameen ta kuwa brush bata cika yin shi kullum ba sai mamee ta danneta tayi mata shi ta dole tana kuka da ihu sannan haka ma wanka don hka shi yasa ko abu ta ta6a ibraheem baya ta6a shi balle yayi amfani dashi da ace duka yana sa tayi tsabta da tuni husna tayi ko karatu Bata mayar da hankali akan shi sai wasa kawai, ga shegen cin naman tsiya kamar mayya ko a abinci ta gani ta kwashe ta cinye shi.

Shi kuwa Yah Abdullah duk acikin yayan ninsu yafi bata kulawa fiye da kowa shi yake lalla6a ta daga shi sai mumyn su ibraheem suna sonta sosai.

Ibraheem yasha siyan abubuwa ya raba wa kanannen shi Amman ban da husna haka xata k'ara ci kukan ta baxai Bata ba sai dai idan Yah Abdullah yana nan ko Mumy sai su bata, kuma ba ruwan shi Ko agaban mameen ta kuwa xai ci xalinta baya kiran sunan ta sai kaxama ko mummuna baka kinfa kowa muni a gidan nan ko abu baya ci Idan husna tana wajen saboda tsabar k'amk'amin ta.

Hajia maamaa tana bala'in son ibraheem duk cikin jikokinta tafi son shi, shima yana sonta sosai shi yasa ya dawo part d'in ta da xama gaba d'aya ,Hka kusan sauran yaran ko dayaushe suna part d'in ta.

Yah Abdullah yana karantar account ne a jami'ar ABU dake cikin garin xaria yayin da ibraheem yake karantar physiology shima a ABU di'n sai dai Abdullah yana gaba dashi, IB ya had'u ta ko'ina tun yanxu emmata suna kawo mishi rububi, miskiline na k'in k'arawa ga jan aji yana kuma da kamun kai ba ruwan shi da irin shiriritar nan na matasa yana da dad'in xama Idan har ka fuskan ce shi.

Ibraheem muktar ibraheem kyakkyawa ne fari ne sol dashi gashi dogo tubarkallah yana da hanci ga manyan idanu sajen shi da ya kwanta akan kyakkyawar fuskar shi ba k'aramin k'ara fito mishi da kyan shi yayi ba gashin kanshi kuwa irin na fulanin asali ne mai laushi da santsi kai ta ko'ina IB ya had'u


Acikin xuciyar Ibraheem IB yana da wani buri a xuciyar shi wanda shi da *DANGARTAKAR ZUCIyar* shi ne kad'ai suka san tsawon lokacin da yake cikin xuciyar shi yak'i bayyana shi ga kowa yana jiran lokaci da ya kamata ya bayyana shi...............

_toh ko mene wannan acikin xuciyar IB sai ku biyo mu don jin wannan abin da IB ya barshi daga shi sai *DANGARTAKAR ZUCIyar*_




Aishat A muh'd

        *&*

Sumayya salees sadeeq
[25/07, 09:00] Aishat A. Muhd: 🍃 *DANGARTAKAR XUCI*🍃






*Written by*

Sumayya salees sadeeq



           *&*



Aishat A mu'hd






*Page 5-6*






"Yau ta kama saturday, gaba daya jikokin hajia maamaa suna xaune a babban palour d'inta,ko wannen su dauke da littafi a hannunsu yayyan su na masu lesson. Ibrahim xaune a gefen maamaa suna hira da ita, a hankali husna ta bankad'o curtain d'in d'akin tana hangawa, gaba d'aya ta tsure,ibrahim na daria hankalinsa ya koma bakin kofar, ganin husna na rabe rabe yasa ya saki wani murmushin mugunta, bata rai yyi ya kalleta, cikin tsawa ya kirata, xonan husna.





"Sanye take da wata multi colour gown iya gwiwarta, gashin kanta daure da blue ribbon sai sheki yake, school bag ce rataye  a bayanta, sai kwalin exotic da ta taho dashi tana sha. Yau kam husna fes take dan ynx mamee ta gama mata wanka sannan ta kad'o kanta.





"Gaba d'aya hankalinsu yyi wajen ganin husna yasa wasu suka fara tausaya mata, dan bbu sauki tunda ya abdallah baya nan,dama shi kad'ai ne xai iya dakatar da ibrahim.




"Jiki na bari ta karaso cikin palour harta fara kuka, gaba daya jikinta bari yake dan a dunia tana bala'in tsoron ibrahim, a hankali ta tako kusa dashi ta tsugunna k'asa, ya ibrahim gani ta fada tana rawar murya.




"Hannun yasa ya kama kunnen husna ya rike, cikin karkausar murya ya fara magana, husna dan ubanki mai ya hanaki xuwa lesson tunda xu? Yarfe hannu take dan kunnenta xafi yake mata. Ya ibrahim har xan taho mamee na ta hanani wai sai ta mini wanka dan Allah kayi hakuri, wani wicked smile ibrahim yyi ya kalli husna, oya tashi ki mini jump frog, ido husna ta fito dashi hawayen fuskarta na xuba, dan ita tunda take bata taba yin jump frog ba.





"Ya ibrahim...... Bata karasa ba ibrahim ya dauke fuskarta da mari, a kasa husna ta xube tana kuka, tsawa ya daka mata ki tashi nace kiyi jump frog.





"Gaba daya maamaa ta tsure dan batasan ganin yarda ibrahim yake dukan husna kamar jaka, amma bbu damar magana dan bata kaunar bacin ransa. Kabeer da mus'ab ne suka tashi a fusace suka bar palour dan baxasu iya ganin wannan xalincin ba, gashi bbu damar magana tunda duk palour din ya girmesu, and a kwai respect a tsakanin su.





"Su khadija, amina, fadila, ummu aimana, marwa, habiba, sai rufaida yayar husna. Gaba dayan su kuka suke a boye dan kar ya ibrahim ya gani suma ya saka su jump frog din. A hankali husna ta tashi fuskarta shabe-shabe da hawaye da majina, cire school bag din ta tayi ta ajiye a gefe ta fara jump frog.





"Motar abdallah ce ta danno cikin gidan, tafe yake yana nishadi, ganin Kabeer da mus'ab yyi sun fito a fusace daga part din maamaa yasa hankalinsa ya tashi, tabbas yasan akwai abinda ke faruwa, wani birki ya ci a gabansu bai kashe motar ba ya fito ya na tambayar su ko lpy? Cikin bacin rai kabeer ya bawa abdallah labarin abinda ke faruwa, bai bari sun kai karshe ba ya nufi part din maamaa da gudu.





"Ba tare da sallama ba ko kuma tuna cewa ana sallama, abdallah ya bankad'o curtain din palour yana huci kamar xaki, husna ya gani baiwar Allah ta dage tana jump frog kafafunta har sun mata nauyi.





"Ibrahim! Abdallah ya kira sunan sa rai a bace, jin muryar ya abdallah yasa husna taji wani sanyin dadi dan tasan" karshen wahalarta" yaxo, sunan novel din sister, xubewa tayi a wajen tana maida numfashi dan kuka ya gagareta.





"Cikin xafin nama ya abdallah ya dauke fuskar ibrahim da mari, dafe wajen ibrahim yyi idonsa a kan husna da ya tabbatar akanta ya abdallah ya mareshi, wata tsanar ta yaji ta kuma lunkuwa a ransa.





"Salati maamaa ta dauka tana tafa hannu, abdallah ibrahim din ka mara? Ta fada tana duba inda ibrahim ya dafe,.        "Abdallah ji yyi wani bakin ciki ya cika masa xucia, dan tunda ya shigo baima san da xamanta a palour din ba, duk da yasan ko tana nan ba magana xatayi ba.





" Kallon ta yyi cike da bacin rai, au maamaa da kina xaune? Kallon abdallah tayi da ina ina kake tunani ta fada rai a bace. Gaskia wannan bayi bane kuma bai dace ba, yama xa'ai ibrahim yasa husna jump frog a gabanki macace fa ba namiji ba ballantana kice.




"Baki maamaa ta saki au abdallah rashin kunya xaka mini? To wallahi bari babanka ya dawo xaixo ya sameni, xan basa labarin duk abinda ka mini, kuma mai kake nufi? Yarinya sai tayi laifi a gyaleta kenan.Tsaki taja ta cigaba da duba fuskar ibrahim.





"Sauran yaran kam a hankali suka fice dan indai ya abdallah ya fita ibrahim kansu xai dawo.



"Abdallah ne ya dauki husna gaba daya tausayinta ya cika masa xucia, cikin xafin nama ya fita daga palourn. Rasa inda xai kai husna yyi dan yasan idan ya kaita wajen mamee d'inta kamar cin fuska ne, dan matar nada hkr, tana bala'in dauke kai a kan cin kashin da ibrahim keyi wa husna.





"Part din hajia halima, wato momyn su abdallah ya nufa, da sallama ya shiga, sa'a yyi momy na palour dan haka tana ganin sa da husna ranga ranga ta mike ta nufi abdallah tana tambayar sa ko lpy? Cikin bacin rai abdallah ya bata labari. Momy ma kam ibrahim ya fara kaita bango, duk da tasan irin haka na faruwa idan jininka bai xo daya dana mutun ba amma abin ibrahim ya gawurta.





"Husna kam ta lafe a jikin ya abdallah tana sauke a jiyar xucia, momy ce ta karbeta ta kwantar da ita a kujera, mai aikin gidan ta kira ta kawo mata ruwan xafi da towel, sosai ta gasawa husna kafarta tana kuka dan kafar ta mata tsami.





"Ib na xaune a part din hajia maamaa gaba daya ta wani yi kicin kicin akan marin da abdallah yyi wa ibrahim, shi kuwa ibrahim a bangaren sa tunda husna ta sa a kanta aka mareshi to tabbas ynx ya fara axabtar da ita xai ga wanda xai hanashi.








Sumayya salees sadeeq



          &



Aishat A mu'hd
[25/07, 09:00] Aishat A. Muhd: 🍃 *DANGARTAKAR ZUCI*🍃





*written by*

Aishat A muh'd

          *&*

Sumayya salees sadeeq






*page 7-8*





    Bayan Mumy ta gama gasa mata kafar ne wani wahalalen bacci yayi awon gaba da husna sai faman sauke ajiyar xuciya take, mumy da Yah Abdullah sun xuba mata ido cike da tsananin tausayin ta a hankali Yah Abdullah ya sauke numfashi tare da cewa
"a gaskiya mumy ya kamata kiyi wa ibraheem magana akan abin da yake yiwa husna"

"ni fah wlh har kunyar mamee nake akan abin da yake mata, kuma ko a fuskar ta bata nuna rashin jin dad'in abin da yake ma husna, yanxu ace kana ganin da ace wata mara hak'urin ce ae da tuni ana tafka rigima don ba kowacce uwa ce xata juri hakan ba"

Mumy ta fad'i fuskar ta d'auke da tarin damuwa, Yah Abdullah ne ya cigaba da cewa
"wlh kuwa mumy ae mamee tana da hak'uri tana kallo yana yiwa husna mugunta amman ji yanda take bala'in son shi komai ta samu ibraheem ji fah ko wannan week d'in da ta d'auki salary di'n ta rabi ta bashi wai ya dunga xuba mai a mota (da yake mamee likita ce tana aikin ta) "

Yah Abdullah ya K'arasa fad'i cike da takaicin abin da ibraheem yake,

"shi yasa wlh nake son ta, amman xan mishi magana naja mishi kunne ba ruwan shi da ita"

"Yawwa mumy Allah yasa yaji, don hajia maamaa ce take goya mishi baya komai yace Shikenan ta hau kai ta xauna "

"Hmmm Allah ya kyauta "

"Ameeen "

Yana fad'in hka ya fice daga falon mumy ya nufi part d'in su na maxa, d'akin shi ya shige tare da xube wa kan gado xuciyar shi ba dad'i da abin da IB yake da Hka bacci ya d'auke shi.



Karfe 1 na rana school bus d'in su husna ta shigo cikin gidan tayi parking a hankali suka fara fito wa daga motar, da yake husna Fadila, Ilham da raudah (d'iyar kanwar su Alhj muktar ta dawo gidan da xama saboda duk kusan sa'annine dasu husna, shi yasa ta gudo gidan da xama tafi jin dad'i Idan tana cikin su), dukkanin su class d'aya suke a school .

A matuk'ar gajiye husna ta sakko daga motar yunwa ce take nukurkusar ta gaba d'aya sun riga ta shige wa cikin gidan saboda yanda take tafiya a hankali.

Tun daga nesa ya hango ta wani murmishin mugunta ya saki don yau kusan k'wana 2 basa had'u wa, sam bata kula dashi ba saboda hankalin ta yayi gaba sai ji tayi yace

"keeee er bak'a xo nan "
Wayyo Allah kamar husna ta d'ora hannu akai ta saki ihu haka take ji don tasan yau kam ta shiga dubu ba uku ba, saboda tsabar rud'ewa ta kasa K'arasa wa inda yake sai da ya sake daka mata tsawa sannan ta nufi inda yake jikin ta yana 6ari.

Kneel down tayi a gaban shi sai da ya d'auki tsawon mintuna 5 yana kallon ta kafin ya kau da kanshi cikin yatsine fuska yace

"ke baki da hankali ne xaki xo ki wuce ta gaba na baki gaida ni ba xaki yi bayani yau "

Cikin tsoro tace "I'm sorry Yah ibraheem wlh ban kula ba "
"okay xan yi miki abin da xaki dunga lura a next time "

Tuni hawaye ya xubo a idon husna cikin tsoro da rawar murya tace "Don Allah kayi hak'uri please "

Wata tsawa ya daka mata tare da fad'in "oya tashi ki biyo ni " jikin ta na rawa ta bi bayan shi har cikin bedroom d'in shi ya bud'e kofar toilet yana rik'e da handle di'n kofar ya Kalli husna yace "oya shiga ciki ki xauna "
Tana kuka sosae ta shiga cikin toilet d'in rufe wa yayi da key ko tausaya mata bai yi ba ya fita daga d'akin kai tsaye part d'in mamee ya shiga ya tarar bata dawo daga aiki ba, sai rufaida ya gani tana xaune tana cin abinci, tuni ta nutsu

"ina mamee ko bata dawo ba me? "
Cikin sauri rufaida tace "ehhh Bata dawo ba "

Bai k'ara ce wa komai ba ya shiga kitchen ya d'auko coconut juice da mamee ta had'a shi cikin jug yayi sanyi k'arara ya fita xuwa part d'in maamaa .


Bedroom d'in shi ya koma bayan ya gama cin abinci, ko takan husna bai bi na yayi kwanciyar shi akan bed ya d'auki wayar shi yana charting da friends d'in shi, da hka bacci yayi awon gaba da shi.


Yah Abdullah ne na hango sai safa da marwa yake yi fuskar nan tashi d'auke da tsantsar tashin hankali don an nemi husna an rasa duk wani lungu da sak'o an duba ba'a ganta ba, kuma su Ilham sun tabbatar da tare suka dawo, hankulan gaba d'aya en gidan yayi masifar tashi, duk wajen da aka san xata iya xuwa anje but ba'a ganta ba har tsawon 2 hours ana neman husna.


Duk matasan gidan da yaran suna tsaitsaye a farfajiyar gidan sun kasa xama ko Kad'an tuni hajia maamaa ta fara goge hawaye tana addu'ar Allah yasa a ga husna yayin da en su Fadila Ilham, raudah, suna ta  da kuka abin tausayi.


A nutse ya farka daga baccin ya duba agogo a k'alla xai d'auki wajen 2 hour's yana baccin nan, sam ya manta da wata husna a toilet d'in shi sai da ya bud'e kofar toilet d'in ya ganta a kwance a k'asan tiles di'n toilet d'in taci kuka ta more bacci ya kwashe ta en yatsun ta biyu a baki tana tsotsa, da sauri ya dafe kanshi yana cewa

"ohhh my god ni sam na manta da ita wlh "

Sai da yasa hannun shi ya shafa fuskar ta sannan kuma ya mik'e ya kunna shower daman akusa da Inda shower take ta kwanta jin saukar ruwa a jikin ta yasa ta ta mik'e a firgice tana kuka kashe shower d'in yayi sannan ya kamo kunnen ta yace
"sauran Idan an tambaye ki inda kika xauna Kice ni na kulle ki toilet sai na miki dukan tsiya na cire miki mouth nd ear di'n ki"
Cikin tsorata da abin da ibraheem yace tace "Allah baxan fad'a ba ma kada ka cire min baki na da kunne na please "
"Good girl, oya get out"

Kafin ya rufe bakin shi ta fice daga toilet d'in da gudun tsiya, Murmishi ya saki had'e da lumshe idon shi yana tunanin wani abu wanda tsakanin shi ne da *DANGARTAKAR ZUCIyar* shi kawai kayan jikin shi ya cire ya fara wanka.

Suna tsaye har yanxu a farfajiyar gidan ana kok'arin kiran number d'in police don su taya su bincike, kawai kamar kiftawar ido sai ga husna ta fito daga part d'in hajia maamaa kowa ya saki baki cike da mamaki yana kallon ta jikin ta a jik'e sai d'igar ruwa take gaba d'aya suka yo kanta suna tambayar ta ina ta shiga cikin Inda Inda tace
"toilet d'in bedroom na maamaa na shiga xan yi fitsari shine na rufe toilet d'in ban sani ba kuma yak'i bud'e wa sai yanxu"
Nan fah aka fara hamdala hajia maamaa har da hararar ta tace "shine kika d'aga mana hankali a banxa ja'irar yarinya "

Nan kowa ya tafi, Yah Abdullah da tun fito war ta yake kallon sam bai gamsu da abin da husna ta fad'a ba, haka ya kama hannun ta suka nufi part d'in mumy yana tambayar ta ko ibraheem ne ya kulle ta a toilet da sauri ta xaro ido tace
"nooo Yah Abdullah bashi bane ba "
Girgixa kai yayi kawai ba don ya yarda da abin da tace ba, mumy ita tayi mata wanka ta ci abinci sannan Yah Abdullah da kanshi ya d'auke ta ya kai ta islamia sannan ya dawo gida.

Tun daga lokacin ibraheem bai k'ara yi mata wani abin ba, kullum wasan 6oya suke bata xuwa inda yake Idan tsautsayi yasa suka hadu da sauri xata xube k'asa tana gaida shi ta k'ak'alo murmishin dole tayi tun da ya tsani Idan xa'a yi mishi magana fuska a d'aure.


Sanye take da wasu english wears jeans blue da er top purple colour tayi kyau sosae kanta Anyi mata kalba da gashin duk sun xubo, parlour maamaa ta shigo tana karanta suratul fatiha a bakin ta, idon tane ya sauka akan center table d'in parlour abinci ne acikin plate yasha nama sosai akai sai k'amshi abincin parlourn yake tuni ta had'iyi yawu muk'ut kai tsaye ta nufi wurin ta tsoma hannu ta fara ci ta cika bakin ta da tsokar nama tana ci kamar ance d'ago kan ki sai ta hango Yah ibraheem tsaye a kofar kitchen hannun shi d'auke da kwalin exotic da bottle d'in faro fuskar nan tashi a sake saboda mugunta, tuni jikin husna ya fara rawa naman bakin ta ta xubar dashi k'asa ta d'ora hannun ta akai Shikenan yau ta shiga tara ba uku ba, cikin nutsuwa ya tunkaro Inda take tsaye.........



Aishat A muh'd

          *&*

Sumayya salees sadeeq
[25/07, 09:01] Aishat A. Muhd: 🍃 *DANGARTAKAR ZUCI*🍃




*written by*
Aishat A muh'd

          *&*

Sumayya salees sadeeq




_kuyi hak'uri da baku ji mu ba k'wana 2 hakan ya faru ne da rashin lafiyar wadda muke rubuta wa tare wato *Sumayya salees sadeeq* dafatan xaku yi mata addu'ar samun lafia_





*Page 9-10*






    Tun Kafin ya k'araso inda take husna ta tsugunna k'asa ta fara bashi hak'uri cikin rawar murya da tsoro
"Don Allah Yah ibraheem kayi hak'uri bansan abincin ka bane, baxan kuma ba please"

Wani murmishin mugunta ya saki lokaci d'aya kuma ya had'e fuska cikin tsawa yace
"shiiiii close your mouth "
Ya fad'i hkan tare da xama kan kujera ya d'ora kafa d'aya kan d'aya yana kallon husna dake durkushe a gaban shi, nuna mata naman da ta xubar a k'asa yayi tare da cewa
"ki kwashe shi ki cinye shi tsaf tare da dukka abincin ko wlh nayi miki dukan tsiya"

"wayyo Allah nah don Allah kayi hak'uri wlh yanxu mamee ta bani abinci naci na koshi "
Girgixa kai yayi Kafin yace
" i swear to god sai kinci kuma dukka "
Ta bud'e baki xatayi magana ya dalla mata mari kuwa cikin fusata yace
" ni sa'an kine xaki tsaya min musu oya d'auki kici "
Tana dafe da kuncin ta hawaye na xuba a idanun ta ta janyo plate di'n abincin ta fara ci tana had'e wa dakyar don a koshe take
"me nace miki eyee, ki fara cinye naman da kika xubar a k'asa "

Bata da yanda xata yi hka ta tsince shi tana ci tana hawaye don mugunta irin ta ibraheem wayar shi ya d'auko yana d'aukan ta a photo yana dariyar mugunta Hka ya xauna har ta cinye shi tsaf duk da uwar yunwar da yake ji kuwa mugunta ta hana shi tashi don yana tunanin Idan ya tashi xata gudu.

Dakyar ta cinye sannan tace "na gama ci "
Yana hararar ta yace "ae ina da ido na gani basai Kinyi magana ba, yanxu tashi xaki yi min tsalle sau 10 kacal ya isa"

Wayyo Allah husna kamar ta d'ora hannu akai ta saki ihu yanda tayi mugun koshin nan ina xata iya tsalle har guda 10, numfashi ma dakyar take yi haka ta mik'e dakyar sai da taja numfashi Kafin ta fara tsallen numfashin ta kamar ya fita guda biyar tayi ta xube warwars a k'asa tana jan numfashi dakyar cikin tsawa ibraheem yace
"wa yace ki kwanta guda 5 di'n da kika yi ya xube sai kin sake "

Da sauri ta tashi tare da cewa "don Allah kiyi hak'uri xan k'arasa amman kada ya dawo baya please "

Wani kallo yayi mata ido cikin ido ko kiftawa ba yayi husna ce ta kau da kanta saboda baxa jure wannan kallon muguntar tashi ba 
"okay naji tashi Ki k'arasa "
Haka ta mik'e dakyar ta fara tsallen  yana kirgawa har sai da ta cike 5 di'n sannan ta tsugunna duk ta gala6aita duk sanyin AC nan amman gumi take had'a wa hannu yasa ya ja gashin kanta har sai da tayi er kara sannan yace
"bana hana ki yawo ba d'ankwali akai ba ?"
"kayi hak'uri na dai na"
"Ki ma sake bari na gani sai na yanke shi gaba d'aya "

A d'an tsorace da abin da yace ta fara bashi hak'uri sannan ya cika mata gashi tare da tashi ya fice daga falon,  sai lokacin wani irin kuka ya kufce wa husna ji tayi an rungumo ta da sauri ta d'ago kanta sai ta ga Fadila, Ilham da raudah ne su ma suna taya ta kukan a haka Yah Abdullah ya shigo ya same su nan fah ya fara bi ya rud'e ganin husna na kuka bai bi takan su Ilham ba ya kamo hannun husna yana rarrashin ta  don yasan aikin ibraheem ne don yanxu suka had'u sai fara'a yake da ya tambaye shi mai ya faru hka yake fara'a sai yace haka kawai yaji yana farin ciki.

Ilham ce ta xuba wa Yah Abdullah ido tana kallon shi cike da sha'awar yanda yake rarrashin husna duk da yana wasa da dariya dasu yana jan su a jiki amman ba kamar yanda yake yiwa husna ba,  ita Hka kawai taji Yah Abdullah yana birge ta komai nashi a nutse gashi baya yi musu mugunta kamar yanda Yah ibraheem yake musu.

"ke lafia kike kallo na Ko na canja miki? "
Ya fad'i hkan yana kallon Ilham da ta xuba mishi ido dariya kawai tayi tare da cewa
"ba komai ", to shima bai k'ara bi ta kanta ba ya kama hannun husna suka fice.


Tun daga ranar husna ta d'auki alwashin sai ta rama abin da Yah ibraheem yake mata ita wlh ta gaji da cin xalin nan da yake mata nan fah ta mai da hankali akan tunanin abin da xata yi mishi.

Tana xaune a bedroom d'in su tana duba books di'n ta na skul tana cikin bud'e text book di'n ne taga photon wani katon kenkeso duk da ta tsane ta bata k'aunar ko da ganin ta amman ta dan xuba mata ido sai ta lula tunani can kamar an tsikare ta ta mik'e da sauri tana cewa "yes idea! " tuni ta fara tsallen murna don tasan Yah ibraheem yayi mugun tsanar kenkeson baya son ganin ta akwai lokacin da yana cikin cin abinci a falon hajia maamaa sai kawai ya hango ta gaf da kafar shi wani wawan ihu ya saki tare da daka tsalle ya haye kan kujera yana kakarin amai.

Duk en falon suka jiwo suna kallon shi tuni hankalin hajia maamaa yayi mugun tashi taxo wajen shi da sauri tana rik'e shi tare da tambayar shi lafia,  nuna mata kenkeson yayi da hannu ae kuwa ta kirawo er aikin ta mai gyaran falon ta kashe ta tare da dauke ta ta fita ta xubar a dusbin a ranar sai da Yah ibraheem ya mare ta tare da yi mata warning idan baxa ta tsaya ta mai da hankalin ta wajen aikin ta ba xa'a sallame ta a samo wadda xata iya, hak'uri ta dunga bashi Sannan ta tafi, a ranar kusan yinin d'aki yayi abinci kuwa kasa ci yayi duk hankalin hajia maamaa ya tashi ta dunga fad'a ita kad'ai ba wanda ya kula ta don an ta6o d'an gaban goshin nata.


Da gudu ta fice daga part d'in nasu a hanya ta kusan cin karo da Yah ibraheem harara ya dalla mata tare da jan kunnen ta da karfi har sai da tayi k'ara sannan ya sake ta ya wuce da sauri da alamar da akwai inda xai je, shafa kunnen ta tayi tare da kyalkyale wa da dariyar mugunta da ta tuna plan di'n da xata hada mishi cikin tsananin farinciki tace "mugu wlh nima sai na rama abin da kake min mrs wicked "


Wajen baba mai gadi kai tsaye ta wuce ta same shi xaune kan benci yana jin radio xama kusa dashi tayi tare da cewa "sannu  baba mai gadi radio kake ji? "
rage k'arar radion yayi cikin murmishi yace "ehh husna mutuniyar ibraheem "
Had'e fuska tayi tare da bubbuga kafafun ta a k'asa kamar xata fashe da kuka tace "ni ka daina had'a ni da wannan mugun "

Yana er dariya yace "ae kuwa ibraheem ba mugu bane yana da kirki kawai halin ku ne bai xo d'aya ba shi yasa bakwa shiri, ni ina nan ina addu'a Allah yasa ayi er gida don had'in xai yi kuwa "

Sam bata fahimci maganar shi ba don hka ta langa6e kai tare da cewa "baba mai gadi ina xan samu kenkeso ne? "
Cikin mamaki yake kallon ta kafin yace "me xaki yi da ita husna"
Cikin murmishi tace "a school d'in mu aka ce mu kai xa'a yi practical da ita kuma kowa ance yaxo da ita "

D'an shiru yayi alamar yana tunani Kafin yace "tun da sha'anin karatu ne xan samo miki "
Dad'i ya kama husna tace "thank u baba mai gadi "
Shima washe baki yayi yana cewa "mene kuma tanka yo? "
Dariya ta kyalkyale da ita har da hawaye shima har ta bashi dariya yana taya ta cikin dariyar tace
"baba mai gadi thank u ake cewa ba tanka yo ba, kuma cewa nayi nagode "

"aiyyo husna Kinsan Banyi wannan makarantar turawan ba"
"toh baba ka shiga mana "
D'an xaro ido yayi Kafin yace "da tsofan nawa xan shiga bokoko tabb sai dai yara na"

"toh baba kaje ka samo min mana kada ka mance "
"Yawwa er albarka kin tuna min don har na mance "
Tashi yayi tare da k'walla wa mai bawa flowers ruwa da sauri ya amsa tare da xuwa inda baba mai gadi yake yace
"Yawwa magaji d'an kular min da gate xan dan fita yanxu xan dawo "
Magaji yace "toh baba sai ka dawo "
Daga hka baba mai gadi ya fice yayin da magaji mai bawa flowers ruwa ya xauna kan benci yana bawa husna labarin abin dariya tana kyalkyale wa da dariya.

Baba mae gadi bai fi 10 mint da fita ba ya dawo leda bak'a a hannun shi husna tana ganin shi da sauri ta K'arasa inda yake ya Mik'o mata ledar yana cewa
"gashi husna guda uku na samu dakyar "
"toh baba mai gadi nagode "
Sai kuma taji tsoron kar6a don har ga Allah tana jin tsoro wata er sanda ta samu ta xura sandar tsakanin hannayen ledar daman ya kulle mata tana sa sandar ta rik'e ta nufi cikin gidan part d'in hajia maamaa tayi tana d'an dube dube don bata son wani ya ganta kai tsaye bedroom d'in Yah ibraheem ta shige sai ta hango wasu kaya kan bed d'in shi da alamar su xai sa wani dad'i ne ya ishe ta, sai kuma ta rasa ta inda xata kunce ledar ta xuba mishi kenkeson cikin aljihun kayan.

A tsorace ta bud'e ledar da yake baba mai gadi ya d'an buge su basa yin motsin kirki da ta had'a ido da su sai da ta saki wani ihu tare da runtse idon ta da sauri tuni jikin ta ya hau rawa don tsoro amman duk da hka sai da tayi dubarar sa mishi a aljihun wandon shi sannan ta fice daga d'akin da sauri xuciyar ta fal farin ciki ita ma yau xata rama abin da Yah ibraheem yake mata.

Da sauri ya shigo part d'in hajia maamaa ya shige bedroom d'in shi don yin wanka saboda yana da Inda xai je wanka ya shiga yayi ya fito kai tsaye wajen dressing mirror yayi ya shafa wani lotion mai k'amshi tare da taje kanshi ya shafa mishi mai ya taje sannan ya fesa body spray a jikin shi don fah ibraheem akwai son k'amshi duk tsadar turare idan k'amshin yayi mishi xai siya yana gama wa ya d'auko kayan shi nakan bed ya saka wow masha Allah ba k'aramin kar6ar shi kayan suka yi ba black trouser ne da yellow d'in T-shirt mai dogon hannu a jikin rigar anyi rubutu da black d'in abu ya sanya belt black sannan yasa takalmin shi yellow sai ya d'ora wani farin glass gaskiya ya had'u sosai sannan ya fesa perfumes Kala Kala a jikin shi tuni ya turare d'akin da k'amshin turaren shi, da sauri ya dauki phone d'in shi da car key di'n shi sannan ya fito daga dakin had'a ido yayi da husna wadda ta nutsu waje d'aya tana wasa da teddy bear sauran kiris dariya ta kufce mata amman ta dake tare da kawar da kanta.

Xama yayi yana kallon hajia maamaa yace " a kawo min abincina maamaa sauri nake "
Ya fad'i yana duba watch di'n hannun shi bak'i ne shi ma, da kanta hajia maamaa ta shiga kitchen ta had'o mishi abinci ta kawo mishi cikin d'an sauri ya fara cin abinci d'an motsi yaji a cikin aljihun shi sai ya share kawai ya cigaba da cin abinci, dakata wa yayi da cin abincin jin motsin sai cigaba da yi yake a fusace ya xura hannu cikin aljihun ae kuwa yayi nasarar kwaso kenkeson nan bud'e hannun shi da xai yi ya had'a ido dashi a hannayen shi xabura yayi tare da wurgar dasu lokaci d'aya ya saki wata k'ara irin ta tashin hankalin nan tare da runtse idanun shi a kid'ime hajia maamaa ta yo kanshi tana tambayar shi abin da ya faru ko ta kanta  bai bi ya fara dan tsalle yana cire trouser di'n dake jikin shi duk yabi ya rud'e ya had'a wani uban gumi, husna na gefe ta rufe fuskar ta da teddy di'n hannun ta tana dariyar mugunta.
 Duk yabi ya d'aga wa hajia maamaa hankali yana xame trouser di'n yayi saura sai boxer ajikin shi ya fara wani irin kakarin amai.............





Aishat A muh'd

         *&*

Sumayya salees sadeeq
[25/07, 09:29] Aishat A. Muhd: 🍃 *DANGARTAKAR ZUCI*🍃




*written by*

Aishat A muh'd

           *&*

Sumayya salees sadeeq





*Page 11-12*




  Yana xame trouser di'n yayi wurgi dashi gefe d'aya sai boxer kawai ya rage tuni wani irin amai ya xo mishi nan ya durkushe yana kelaya aman kamar ya amayo da hanjin cikin shi, idanun wan shi sun sake firfito wa sunyi wani irin jawur dasu sai da ya amayar da abin da ya ci amman duk da hka wani kakarin yake.

Hajia maamaa gaba d'aya ta kid'ime ta rasa wani irin taimako xata yi mishi rirrike shi kawai tayi tana kuka tare da xuba mishi Sannu, husna ma ta motso Inda suke tana danne dariyar ta tana yi mishi sannu xuciyar ta fal farin ciki duk da ya bata dan tausayi.

A matuk'ar gala6aice ya d'ago da kanshi ae kuwa ya hango kenkeson nan guda d'aya tayo kanshi tuni ya mike a matuk'ar sauri ya daka wani uban tsalle tare da yin cikin bedroom d'in shi da gudu bai tsaya a ko'ina ba sai cikin toilet rigar jikin shi ya cire ya fara wanka hannun shi wanda ya xura a aljihun shi ya kwaso kenkeson nan ya dunga wanke shi kamar xai canja fatar hannun, sai da yaji hannun yana mishi rad'ad'i sannan ya barshi ya kunna shower ruwa na xubar mishi a jikin shi yana sauke ajiyar xuciya akai akai tare da fad'a cikin tunanin uban wanda yayi mishi haka, toh wane xai saka mishi kenkesu a cikin aljihun shi "husna,  yes! itace don ba wanda xai min hka sai ita ae kuwa xata ci uban ta "

Sai da yayi wajen 40 mint yana wanka sannan ya fito daga toilet d'in yana d'aure da towel ajikin shi da wani k'aramin towel yana goge gashin kan shi agogo ya duba yaga lokaci ya wuce na Inda xashi kwafa ya saki ranshi a matuk'ar 6ace yana ayyana abin da xai yiwa husna ya huce akan abin da tayi mishi (Hmmm ni da sumy muka kalli juna tare da fad'in wannan shine ramuwar gayya kenan, ya mance duk muguntar da yake mata ne).

Wani black 3quater ya sanya tare da white d'in riga mara hannu mai irin mai bottom di'n nan ya 6alle botir guda biyu hakan ya lallausan gashin kirjin shi bak'i wuluk a kwance lub dasu daman rigar irin mae Shara Sharan nan ce ana iya hango fatar jikin shi da murd'ad'd'en damtsen hannun shi fuska a tur6une ya fito daga d'akin nashi ya tarar da hajia maamaa ta xuba uban tagumi tana ganin shi ta taso da sauri tana cewa

"ibraheem ya aman dafatan ya tsaya koh, ya kake jin jikin naka, na xuba maka abinci ka sake ci "

Da yake lokacin da ya shiga bedroom d'in shi key yasa ya rufe, yamutse fuska yayi yana dan kalle kallen k'asa, hajia maamaa ta fahimci abin da yake nema don hka tace
"ae tuni ankwashe su an xubar "
Sai lokacin ya saki ajiyar xuciyar kwanciyar hankali yana yamutsa fuska yace
"ni fah abinci bana bukatar shi maamaa "

"toh ni abin da ya bani mamaki ya akayi kenkeso acikin aljihun wandon ka taya suka shiga? "

Kwafa yayi tare da cewa "wanne ya saka xaki ce maamaa "
"auuu sama akayi kenan, to uban wane ya saka maka abin da baka so"
Nan ta fara fada an ta6a d'an gaban goshin ta, cikin takaici yace
"na tabbatar husna ce ta samin, tana ina? "
Dan shiru hajia maamaa tayi sannan tace "anya husna ce xata saka maka, abin da ita ma take matuk'ar tsoron, toh a ina xata same ta "

"yes!  Ita ce wlh kuma sai na mata duka wannan ae ranin wayo ne ni sa'an tane da xata yi min wannan wasan "

Yana gama fad'in hka ya fice a fusace hajia maamaa taso tsaida shi don a yanda yake cikin 6acin ran nan xai iya ji mata mugun rauni, ta6e baki tayi tare da xama ko dan ita ta jawa kanta ba ruwa na Idan taji ajikin ta baxa ta k'ara yi mishi haka ba.


Suna xaune a parlour mumy husna, fadila, Ilham da raudah sai su aunty khadijah, aunty Amina, aunty marwa, aunty aimana, aunty rufaidah, gaba d'ayan su kallo suke a tashar mbc bollywood suna kallon wani series film madhubala suna d'an surutan su da dan musu akan wannan yafi son sultan don yafi birge shi yayi da wasu su ce sun fison RK sun raba kansu biyu kowanne da team d'in da ya xa6a.

A fusace ya bankad'e labulen falon ya shigo suna ganin kowanne ya nutsu aka dai na surutu kai tsaye inda husna take ya nufa damk'a d'aya yayi mata da hannun shi d'aya ya fara janta, tuni sauran en uwanta suka fara tausaya mata yaxo gaf da kofar barin falon yaji muryar mumy tana cewa

"lafia qlau kake kuwa, me tayi maka? "
"kamar ni wannan kaxamar yarinyar mumy ta samun kenkesu acikin aljihun trouser na "
Ya fad'i yana xuba huci tare da hararar husna wadda cikin ta ya d'uri ruwa kiris ya rage ta saki fitsari a wando, gaba en falon hankalin su ya dawo kan su girgixa kai mumy tayi tare da cewa
"toh kayi hak'uri mana kasan yarinta ce take damun ta "

"ba yarinta bace tsabar ta raina shi ne ibraheem maxa ka je kayi mata abin da kayi niyya yanda gaba baxata k'ara kwatanta hakan ba "
Gaba d'aya suka jiwo suna kallon mameen husna wadda take maganar hakan ba k'aramin dad'i yayi wa ibraheem ba kafin mumy ta ankara har ya kwashe ta sun bar falon tuni husna jiki ya fara 6ari tana kuka wiwi kallon ta yayi yace "yarinya yanxu kika fara kukan nan ma "

ita kuwa mumy ranta babu dad'i tace "Gaskia mameen husna baki kyauta ba Kinsan yanda ibraheem yake da bakar xuciya kada yaje ya ji mata ciwo "

D'an murmishi mamee tayi kafin tace "ae ita taja gwara ya koya mata hankali "

Shi kuwa ibraheem part d'in hajia maamaa suka nufa suna shiga ya fara kok'arin kwance belt d'in jikin shi husna tayi wik'i wik'i da ido mai cecanta Yah Abdullah baya nan ya tafi skul yana da lecture di'n yamma har yanxu bai dawo ba, Kafin ta ankara taji saukar belt a bayan ta gantsare wa tayi tare da cewa
"wayyo Allah nah don Allah kayi hak'uri wlh na tuba na dai na "

Ko kula ta bai yi ba ya fara dukan ta da belt ganin yak'i dai na dukan ta duk da uban hak'uri da take bashi kuwa don haka ta shige jikin shi tare da rukunkume shi ganin yana samun jikin shi Idan ya kawo mata dukan yasa shi sa hannun shi da niyyar 6an6arota daga jikin shi amman ina ya kasa ta mak'ale shi sosai.

Cikin tsawa yace "cika ni dan uban ki nace "
Cikin shashshak'ar kuka tace "ka daina duka na kayi hak'uri baxan k'ara ba"

"baxan hak'ura ba har yanxu ban miki rabin dukan da nayi niyyar yi miki ba"
Hannu yasa ya fisgo ta da karfi ya wurgar da ita k'asa ae kuwa ta had'o da rigar jikin shi har ta dan yakushe shi a damtsen hannun shi, haka ya xage ya dunga dukan ta tun tana kuka har ta koma Shashshak'a kawai.

Wayyo aranar husna taci dukan da tun da mamee ta haife ta ba'a ta6a yi mata ba, ana haka Yah Abdullah ya shigo da gudu part d'in hajia maamaa don aunty khadijah ce ta kirawo shi awaya tana fad'a mishi da sauri ya warce belt d'in hannun ibraheem tare da watsa mishi wani kallo ya nufi kan husna da tayi matuk'ar gala6aita ya d'ago ta xuwa jikin shi, wani irin abu Yah ibraheem yaji ya daki xuciyar shi a dai dai lokacin hajia maamaa ta shigo falon tare da su Ilham dukkan su kuka suke sosai.

Cikin wani irin 6acin rai tare da tsantsar tsanar Yah ibraheem husna tace
"Ko ni ba jinin ka bane bai kamata kayi min wannan dukan ba na sani tun da nayi wayo ka tsane ni kullum cikin duka na kake da cin xalina kasani na tsane ka i really hate you Yah ibraheem "

Tana gama fad'in hka ta fice daga part d'in hajia maamaa da gudu tana kuka gaba d'aya en wajen mamaki ne ya kama su na abin da husna ta ce yarinya amman ta fad'i wad'annan maganganun lallai ibraheem ya kai ta mak'ura, Yah Abdullah ne ya mike tsaye ranshi a 6ace yana kallon ibraheem wanda ya daskare a tsaye (anya garin gyaran gira baxai rasa ido ba), Yah Abdullah kuwa cewa yayi
"ka ga abin da nake gudu kenan ka riga da ka gama cusa tsanar ka a xuciyar husna har takai da ta furta maka da bakin ta "
Yana gama fad'in hka ya fice daga falon kallon su Ilham yayi ya daka musu tsawa tare da cewa "ku Kuma uban me kuke kallo "
Da gudu kowacce ta fuce kada ya huce akan su bedroom d'in shi ya shige ya xube kan bed tare da dafe kan shi wani abu ne yake mishi yawo a cikin xuciyar shi dakyar bacci ya dauke shi.

Husna kuwa tana fita part d'in su ta shige tana kuka sosai kan kujera ta fad'a tana kukan a haka Yah Abdullah ya shigo ya rarrashe ta wani mugun xaxxa6i ne ya rufe ta nan da nan sai da mamee tayi mata allura tare da bata magani sannan ta gasa mata jikin ta, sai da husna tayi k'wanaki uku sannan ta warware ta cigaba da sabgogin gabanta.

Tun da ga ranar bata k'ara kula Inda Yah ibraheem yake ba balle har ta tsokane shi ya jibgi banxa, ta fita harkar shi k'wata k'wata.

Ana cikin hka ne su husna, Ilham, raudah da fadila suka kammala primary school, lokacin da result ya fito Yah Abdullah ya xa6a musu wata privet school mai kyau da tsada amman don mugunta irin ta Yah ibraheem haka ya shiga ya fita sai dai akai su bording school kuma dukka iyayen maxa suka amince da hakan don hka dad'i ya ishi ibraheem don yanxu baya samun cin xalin husna don ta fita harkar shi, yayin  da 6angaren su husna, Ilham, raudah da Fadila, Yah Abdullah bai yi musu dad'i kuma basu da yanda xasu yi don hajia maamaa ce ta tilas ta su Abba don idan abu ya faru toh Indai ya fad'a wa hajia maamaa Shikenan ya xaunu.

Ranar da xa'a kai su school d'in da sassafe suka shirya angama had'a musu komai husna ta fito da gudu daga part d'in su xata je d'akin Yah Abdullah su yi sallama suka hadu a hanya cikin dariya ta ce
"Wow Yah Abdullah kayi kyau wlh "
Kallon jikin shi  yayi yana murmishi yana sanye da yadin kufta bak'i abin ka da farar fata ba k'aramin haska shi yayi ba cikin murmishi yace
"ngde my cwt sister "
Ya cigaba da cewa "yanxu sai ina? "
Tana yamutsa fuska tace "xuwa xanyi mu yi sallama da kai don har an xuba kayan mu a mota "
Har yanxu da murmishi kan fuskar shi yace "ae ni xan kai ku"
Tsallen murna ta fara yi yana kallon ta yana mata dariya, a lokacin Ilham da raudah da fadila suka fito tare da sauran en gida an rako su Yah Abdullah yana xaune a seat d'in driver yayin da husna take xaune a front seat sai Fadila Ilham da raudah suke xaune a bayan motar bayan angama yi musu nasihohi sosae kan suyi abin da kai su ban da shiririta sannan kuma suka yi musu addu'ar sauka lafia, Yah Abdullah yayi wa mota key suka fara tafiya a dai dai bakin gate husna ta had'a ido da ibraheem yana xaune kan bike d'in shi rik'e da key di'n mashin a hannun shi daman sometimes yafi amfani da mashin akan mota wani shegen murmishin mugunta ya bita dashi hararar shi tayi tare da kau dakan ta da sauri daga barin kallon shi a xuciyar ta tana cewa ba dole kayi mana murmishin mugunta ba tun da ka tura mu bording mugu axxalimi kawai ta fad'i tana Murgud'a baki kallon ta yah Abdullah yayi yana cewa
"ke dawa kike Murgud'a baki? "
Dan murmishi kawai tayi tare da cewa "ni da Yah ibraheem ne da yake min murmishin mugunta "
Dariya kawai su Yah Abdullah suka yi mata, cikin nutsuwa yake driving ya dau hanyar da xata kai su school d'in.........





Aishat A muh'd

          *&*

Sumayya salees sadeeq
[25/07, 09:29] Aishat A. Muhd: 🍃 *DANGANTAKAR XUCI* 🍃





Written by

Sumayya salees sadeeq



             *&*



Aishat A mu'hd







*Page 13-14*







"Suna shiga skul direct ya Abdullah ya nufi office d'in principal dasu, gaba daya jikinsu yyi sanyi, ba kamar husna da dakyar take d'aga kafarta dan jitayi ta mata nauyi. Ya Abdullah bai sha wuya ba dan dama principal din kawar momy ce tasan da xuwansu a wannan lokacin.

"Farar mace mai dan jiki bata da fara'a sosai, fuskarta sanye da farin glass wanda xamu kirashi da medical,xaune take a babban office d'in ta wanda yaji kayan alatu, principal hajia kande kenan. Kallon kallon suke a tsakaninsu da alama akwai magana a bakinsu, durkusawa sukayi a kasa yah Abdullah ya xauna a kujerar da aka tanada dan bak'i


"Taunar jingum take irin na yan dunia, kas-kas ta kalli su husna da suma d'in ita suke kallo, murmushi tayi ta maida kallon ta ga ya Abdullah,fuskarta dauk'e da murmushi ta kira sunan sa dan tasan sa. Abdullah ko? Murmushi ya Abdullah yyi "eh nine hajia" gaskia ka girma sosai, lokacin dana sanka ai baka fi waccen ba ta nuna husna da hannu" daria yyi mara sauti dan jiyay kunya ta kamashi, xata masa tijara a gaban kannensa,"eh hajia lokacin da dadewa kam".



"Shiru tayi ta fara rubuce - rubuce a wasu files sannan ta fara magana, tana kallon su rauda da sunyi wiki wiki da ido kamar shege a rabon gado,"xa'a kaiku kaiku hostel daya amma class ba daya ba, ke husna da ilham kuna js1A fadila da rauda a js1C"a hankali ta daura xancen ta, "nan boarding skul ce duk da private ce Amma akwai dealing, dole kuyi respect ga wadanda suka fiko aji, and sai kunyi hakuri dan rayuwar ba irin wanda kuka saba bace". Gaba daya jikinsu ya fara bari dan fargaba husna uwar tsoro har an fara kuka,yah Abdullah jiyay kamar ya koma da kannensa dan yaji abinda hajia kande tace, shi kam baya bukatar husna tasha wuya a rayuwar sa, ko menene dalili ku cigaba da bin mu xakuji yarda xata kasance.



"Hajia kande ta kwalawa Messenger d'in ta kira, da sauri ya shigo ya baje a kasa, gani hajia. "yawwa ka kwashi kayan yaran nan ka kaisu rahmat hostel corner ta karshe" , to hajia an gama ya mike ya fice.




"Hajia kande ta kalli ya Abdullah da jikinsa yyi sanyi gaba daya tayi murmushi, "ok Abdullah xaka iya wucewa gida nasa a kai kayan su hostel sai su wuce cikin skul" ok hajia mun gode" ya fada ya mike suma su fadila suka rufa masa baya.




"Suna fita ya Abdullah ya nufi motarsa ganin messenger na jiransa, boot d'in motar ya bude suka fara dibar kayan suna saukewa kasa, ya Abdullah komawa yyi wajen su husna da suka durkusa kasa suna kuka. Jiki bbu kwari ya durkusa shima yana kallon su kamar yyi hawaye, "kuyi hakuri kannena, menene abin kuka,? Boarding akwai dadi sai kun xauna a ciki xaku gane hakan, ni dai fatana daku banda wasa, ku dage a karatun ku kunji?" gaba daya suka daga kai alamar eh," yawwa my sisters, xamu dinga xiyaryar ku akai akai basai lokacin visiting ba"a hankali ya Abdullah ya gama kwantar musu da hankali har suka saki ransu, an gama shiga da kayan su dan haka suma suka tashi xasu tafi, a nan kam suka kara tsinewa ya Ibrahim a xuciar su dan shi ne silar rabasu da gida.




"Juyawa sukayi suka fara tafia suna waiwayon ya Abdullah,husna ce ta juyo da gudu ta rungumeshi ta kara fashewa da kuka, wayyo ya Abdullah jiyay wani abu ya tsarga masa tunda ga kafarsa har kai, wani kasala yaji ya saukar masa a lokacin, ilham na kallon su har irin shock d'in da ya Abdullah yyi a hankali ta dauke ido tana tunanin dangantakar xucin dake ranta.




"Da kyar ya raba husna da jikinsa ta nufi wajen su rauda suka shige cikin makaranta.




"Wani irin tuki ya Abdullah keyi yana tafe yana share hawayen dake xuba a fuskarsa, lallai bai taba tunanin haka ya shaku da husna ba sai yau, gaba daya tunanin ta ya addabi brain d'in sa ya kuma tuna a halin daya barta, sosai ya Abdullah ke kuka kamar karamin yaro, dan dama ba karamar dauria yyi ba a gaban su bai xubar da hawaye ba, speed ya kara dan gani yake gidan ya masa nisa, Allah ne ya kai Abdullah gida lpy. Tunda ga horn gate man ya tsorata dan haka ya leko, ganin Abdullah yasa shi wangale gate d'in, bai gama budewa Abdullah ya cusa kan motarsa ciki ya ajiye ta a fusace ya bude kofar ko arxikin rufewa bata samu ba ya nufi part d'in shi dan bayasan haduwa da kowa a yarda xuciar sa ke xafi kadaici yake bukata.





"Gate man baki ya saki yana kallon ikon Allah,ganin Abdullah a wannan yanayin dan bai taba ganin sa a haka ba, Bayan ya rufe gate d'in ya nufi motar Abdullah ya rufe.




"Abdullah na shiga room dinsa ya shige toilet dan wani xafi yake ji yana ratsashi, bayan ya fito ya baje a bed dinsa yana kallon ceiling, rungumar da husna ta masa ya tuna, murmushi yyi ya shafa sumar kansa yana tunanin dangantakar xuciarsa. A hankali yaji nutsuwarsa ta dawo dan haka ya nufi part d'in momy dan shaida mata ya dawo. A xaune ya tarar da ita ta buga tagumi tana tunani, murmushin takaici Abdullah yyi dan yasan dalilin tagumin momy, shi kansa ji yay gidan ya masa shiru bbu dad'i dan sun saba da hayaniyar yaran. Sallama yyi ya k'arasa jikin momy ya d'aura kansa a kafad'ar ta, juyowa tayi da Jan ido da alama itama tayi kukan, Murmushi Abdullah yyi ya kalli momy yana mata daria kasa kasa, "momy kuka kokari?" hararar sa momy tayi" eh shi nayi kamar yarda kaima kayi "kallon momy yyi da mamakin yarda akai ta gane yyi kuka, ta lura da hakan dan haka ita ta fara bashi labari," ina jikin barrander naga shigowarka a fusace har kana neman buge gate man, ga fuskarka da idon ka sunyi ja suma, ban dauki tafiar yaran nan da wani mahimmanci ba amma sai daxu da kuka tafi na kuma tabbatar nida ganinsu sai dai naje wallahi Abdullah a nan hankali na ya tashi, gaba daya na kasa sukuni"share hawayen fuskarta Abdullah yyi yana mai jin tausayin momy a ransa.



"Ibrahim kwance a dakinsa wanda ya kasa sukuni tunda su husna suka bar gidan, bbu irin tambayar da maamaa bata masa ba akan ko bashi da lpy ne amma yace bbu komai, tunani ya tafi na dangantakar xuciar sa dashi kadai ya barwa kansa sani. Hajia maamaa bata hakura ba dan haka ta kuma takowa dakin Ibrahim dan rarrashinsa ya fita yaci abinci gashi chan xai daskare. Da sallama ta shiga dakin ta xauna a gefen bed din sa wanda ya tafi duniar tunani baisan da xuwan maamaa ba. A hankali takai hannu ta taba fuskarsa, dago kai yyi ya kalleta fuskarta dauke da damuwa, sai yaji shima gaba daya bbu dadi. Tashi yyi xaune ya jin gina da gefen bed bed din yana kallon maamaa, "haba Ibrahim mai kake so ne haka, mai ya dameka? Yau fa kamata ka hada mana party a gidan nan sbd ja'irar yarinyar nan bata nan ka huta da bari bari, wani kallo ibrahim ya watsa mata dan gaba daya maganar maamaa ba dadi take masa ba. A kufule ya tashi ya nufi wardrobe ya chanja kayan jikinsa, riga da wando yasa na shadda ash colour a gurguje ya shirya duk maamaa na xaune tana kallon sa, key d'in motarsa ya dauka ta kalli maamaa," sai na dawo "baijira tacewarta ba ya fice daga dakin. Tunda Ibrahim ya fita ya rasa ina xai nufa, skul ya shiga dan ya hadu da friends ko ranshi xaiyi dadi.






Kuyi hakuri da wannan fans har Allah ya bawa sumy lpy mu daura a inda muka tsaya.




Sumayya salees sadeeq



            &




Aishat A mu'hd
[25/07, 09:30] Aishat A. Muhd: 🍃 *DANGARTAKAR ZUCI*🍃





*written by*
Aishat A muh'd

           *&*

Sumayya salees sadeeq





 *Page 15-16*





 
  Yinin ranar gaba d'aya su husna basu da kuxari sun yi jugum jugum gaba d'aya kewar gida ta dame su,  husna a xuciyar ta Allah ya isa kawai take yiwa Yah ibraheem mugu kawai kuma yatasan duk saboda tsanar ta yasa ya nema musu bording, ji tayi wani bak'in ciki ya sake kama husna a cikin xuciyar ta tsanar Yah ibraheem ta sake ninkuwa acikin xuciyar ta hannu tasa ta goge hawayen fuskar ta tare da gyara kwanciyar saman bed d'in da suke, Allah sarki Yah Abdullah bawan Allah xanyi kewar ka, ta furta hakan a Hankali tare da k'ara kudundune jikin ta dakyar bacci ya d'auki husna.

Haka a gida Yah Abdullah shi ma kasa baccin yayi yana rungume da picture d'in husna yinin yau yayi kewar ta sosai idanun shi ba suyi toxali da kyakkyawar fuskar  ta ba bai ji dadd'ar murya ta ba ta ratsa kunnuwan shi, akwai wani abun wanda tsakanin shi ne da *DANGARTAKAR ZUCIyar* shi ne baxai iya furta hakan ba har sai xuwa wani lokaci mai tsayi bai iya bacci sosai a cikin Wannan daren ba.


Toh haka su husna suka cigaba da rayuwar su a bording duk da kewar gidan da suke hakan bai hana su dage wa wajen karatu ba basa yin wani shirme ko shashanci karatu kawai suke, har ranar visiting taxo Yah Abdullah, mumy, umma da aunty fatyma babar fadila wato kanwar baban su husna su suka xo musu visiting dad'i ya ishi su husna sai tsallen murna suke iyayen nasu ma sai faman fara'a suke da alamar sun ji dad'in ganin su husna Sun kwantar da hankalin su.


Yah Abdullah kuwa baki yak'i rufuwa shima ba k'aramin jin dad'in ganin husna yayi ba, sai surutu take xuba mishi tana bashi labarin skul d'in wani abin yayi dariya wani lokacin sai yayi Murmishi Hmmm husna anan da halin bai canja ba.

Sai yaga ta k'ara yi mishi girma a idanun shi gaba d'aya ta canja mishi har sai da ya furta yace

"my cwt sister me kike ci haka kin wani k'ara girma? "

Baki ta turo gaba cikin shagwa6a tace "ni Allah ban k'ara girma ba, Fadila ce katuwa don duk ta fimu girma (da yake Fadila tana da dan jiki) "

Gaba d'aya aka tuntsire da dariya ban da fadila da tayi kicin kicin da fuska a fusace tace "wlh husna ki kiyaye ni idan ba hka ba xanyi miki duka Kinsan nafi k'arfin ki "

Hararar ta husna tayi kafin tace "tabbb ae kuwa sai dai mu doki juna ni ga sakarai sai na xauna ki doke ni "

A fusace Fadila ta kawo wa husna duka da sauri Yah Abdullah yasa hannun shi ya kare husnar sannan ya 6ata rai ya kalli Fadila yace "Kinsan ban san wasan duka koh, daman abin da kuke yi a skul d'in kenan? "

Da sauri suka girgixa kai tare da fad'in "nooo Yah Abdullah ba ma yin haka just don muna tare da ku ne "
Dan murmishi yayi tare da cewa "Yayi kyau hakan"

 Ilham ce ta xuba mishi ido tana kallon shi cikin wani irin yanayi a tattare da ita dama itace husna tana bala'in son taga ya sake dasu kamar yanda yake yi da husna ita dai Yah Abdullah yana birge ta duk surutun nan da ake yi baka jin bakin ta don bata fiye magana ba sosai ba ga ta da sanyi sosai kuma cikin sanyi take yin shi, shi yasa Yah ibraheem baya son sata aiki idan ya sata bata saurin gama wa yayi tayi mata masifa alhalin halittar tace haka.

Lura da kallon shi da take yawan yi ne yasa shi cewa "lafia Ilham wannan kallon fah ko Kina buk'atar wani abun ne ?"

Cikin sanyin ta ta girgixa kai tare da fad'in "ba komai yayah "
"okay "

Anyi hira sosai kamar baxa su tafi ba haka su Mumy suke ji balle Yah Abdullah ji yake kamar ya d'auko husna su koma tare dakyar suka tafi bayan sun xube musu uban shopping d'in da suka yi musu bayan wannan kuma ga wanda Yah Abdullah yayi husnar shi ita kad'ai nan suka jidi kayan su har xuwa hostel,  kowanne jikin shi a sanyaye.


Haka suka cigaba da rayuwar su don har sun d'an saba da makarantar Yah ibraheem da yake kiran husna dakikiya su Ilham sun fita kok'ari wannan Karon ta xage damtse sosai wajen karatu don tana son ta nuna mishi ita ma da brain d'in ta just wasa ne yake d'auke mata hankali, gashi Yah Abdullah ya bata k'warin gwiwa kan ta dage da karatu don ta bawa Yah ibraheem kunya ae kuwa ta dagen sosai don duk abin da xai sanya Yah ibraheem bak'in ciki shi take so.


A cikin Wannan week d'in su husna suka fara exam sun mayar da hankalin su kan karatun exam har xuwa lokacin da suka kammala lafia suna ta d'okin xuwa gida duk sun harhad'a kayan su hutu kawai suke jira ayi musu su taho gida duk a cikin su ba wanda ya kai husna d'okin xuwa gida kamar ta xama tsintsuwa ta ganta a gaban Yah Abdullah haka take ji.


Ana gobe xa'a bawa su husna hutu, Yah Abdullah farin ciki sosai yake yana d'okin gobe tayi don yaje ya d'auko su daga makaranta yana cike da son ganin husna tare da jin muryar ta kwatsam abban shi ya nemi da xai aike shi abuja wajen wani aminin abban kan harkar business di'n su abban tuni murna ta koma cikin Yah Abdullah kamar xai yi kuka haka yake ji ya kwallafa ran xuwa gobe tayi amman haka ya hak'ura tun da aiken na Abba ne haka ya kwanta duk xuciyar shi ba dad'i.

Washe gari da sassafe Yah Abdullah ya nufi abuja don yana son yaje da wuri don ya dawo da wuri, bayan tafiyar shi ne Abba ya nemi Yah ibraheem da yaje ya d'auko su husna daga skul, wani shegen murmishin mugunta ya saki duk da yana da lectures ranar haka ya yarda xai je ba tare da ya musa ba ko ya nemi driver ya d'auko su ba Duk sunyi mamakin yanda ya yarda farat d'aya batare da nuna k'in amince war ba (Hmmm Allah ne kad'ai yasan muguntar da Yah ibraheem ya shirya wa husna har na fara tausaya mata),  xuciyar fal farin ciki ya yiwa motar shi key bayan yasha gargad'i wajen mumyn sa akan kada ya yi wa husna wani abun kai tsaye skul d'in su ya shige.


Bayan an watse daga assembly ne an fad'a musu iya adadin k'wanakin hutun sannan aka yi musu en nasihohi tukunna aka sallame su nan fah kowa ya fara fito da jakar kayan shi Idan an xo d'aukan mutum sai yayi sallama da friends d'in shi ya tafi da haka aka dunga raguwa d'aliban cike da tsananin kewa don an d'an saba da juna.


Suna xaune a k'ark'ashin wata bishiya akan chairs irin wanda ake gina su sai er hira suke Ilham da raudah, Fadila bata wajen yanxu ta tashi don ta gaji da xama waje d'aya yayin da husna take Jan tsaki akai akai tare da cewa

"Gaskia Yah Abdullah ya ji ma komai mai ya tsayar dashi ni fah na matsu na ganni a gida wollah "

Har raudah ta bud'e baki xatayi magana kenan sai ga fadila da gudu ta K'arasa wajen tana d'an haki Kafin ta bud'e bakin ta tace

"ku taso mu tafi an xo d'aukan mu"
Da sauri husna ta mik'e tsaye tare da d'aukan kayan ta tana cewa "da gaske kike Fadila? "
Cikin d'oki husna ta fad'a da dariya fadila tace "wallahi da gaske nake kalli can ki ga Yah ibraheem ne ya xo d'aukan mu "
Dummm gaban husna yayi mugun fad'uwa nan take ta d'aure fuska su kuwa su Fadila basu k'ara bi ta kanta ba balle su san halin da ta shiga nan suka fara d'iban kayan su suna kai wa cikin boot d'in motar har sai da suka gama Kafin Ilham taja hannun husna su k'arasa wajen motar ganin yanda ta ga husna ta kafe a tsaye.

Suna k'araso wa fadila cikin rawar kai ta shige gaban motar yayin da raudah ta shiga baya Ilham ma shiga tayi suna jiran husna ta shigo don Ilham tana sakin hannun ta bata k'ara yunkurin takawa ba ji tayi kafar tayi mata nauyi take dakyar ta iya ciran hannun ta takai xata bud'e motar kenan kamar kiftawar ido sai ta ga Yah ibraheem yaja motar da mugun gudu ya fice daga skul d'in da yake kuma gate a bud'e yake, d'ora hannu akai su Fadila suka yi tare da sakin ihu suna cewa
"wayyo Allah Yah ibraheem don Allah ka koma mun bar husna acan ba"
Wata irin tsawa ya daka musu tare da cewa "ko Kuyi min shiru da baki ko na ci uban ku ina ruwa na da ita "
tsit suka yi suna goge hawayen fuskar su na tausayin husna lallai sun k'ara tabbatar wa da ba k'aramin k'iyayya Yah ibraheem yake nuna wa husna ba sai kace ba *dangin juna* ba (littafin Asmy b aliyu), shi kuwa Yah ibraheem hankalin shi kwance yake driving cikin K'ware wa ya kunna wak'ar cikin film d'in Aashiqui don ba k'aramin son wak'ar yake ba don kusan ta shafi irin yanda yake ji wanda tsakanin shi da *DANGARTAKAR ZUCIn* shi ne kawai har wani lumshe idon shi yake alamar yana cikin tsananin farinciki bai damu da yanda su Ilham suke kuka ba.

Turk'ashi! tsananin bak'in ciki takaice ko kuma k'iyayyar Yah ibraheem ne take sake ruruwa a cikin xuciyar husna wadda ke tsaye bayan kurar da Yah ibraheem ya gama bula mata kuka ta rushe dashi tare xube wa a wajen................






 Aishat A muh'd

          *&*

Sumayya salees sadeeq
[25/07, 09:30] Aishat A. Muhd: 🍃 *DANGARTAKAR ZUCI*🍃





*written by*
Aishat A muh'd

           *&*

Sumayya salees sadeeq





*Page 17-18*









     Kuka ta xube tana rusawa hannu akan ta Yah ibraheem mugu ne bashi da kirki shine ya tafi ya barta a cikin kungurimin dajin uban wa ta sani wayyo Allah ni husna haka tayi ta kuka sauran d'aliban suna kallon ta wad'anda abin ya faru a gaban su ta basu tausayi sosai.

Har kusan gaba d'aya students di'n sun tafi sai en Kad'an wad'anda garin su yake da nisa ba'a xo d'aukan su ba har wurin la'asar husna tana xaune tana kuka ga wata axababbiyar yunwa da take yamutsa mata en hanji ko sallahr axahar bata yi ba, wata d'aya daga cikin d'aliban ne da basu tafi ba ta janyo hannun husna tana rarrashin ta da tayi hak'uri dole xa'a xo d'aukan ta kuwa dakyar ta hak'ura da kukan suka yi sallahr axahar da la'asar.

Suna xaune sun yi jugum jugum duk surutun husna a wannan lokacin baxa ta iya ba idanu duk sunyi jawur dasu gashi sun kumbura ga wata shegiyar yunwa duk tayi wani wujiga wujiga ta xabga uban tagumi lokaci xuwa lokaci tana goge hawayen fuskar ta.



Da murnar shi yayi parking a farfajiyar gidan ya fito da sauri ko part d'in su bai yi ba, duk kuwa da tsananin gajiya da yunwar da yake ji kuwa amman sai yayi toxali da husnar shi cikin farinciki ya tunkari part d'in hajia maamaa don yasan a wannan lokacin suna nan suna hira da d'okin shi yayi sallama amman kuma sai yayi turus ganin su Ilham sun xuba tagumi ga hajia maamaa ita ma fuskar ta d'auke da tarin damuwa da sauri ya K'arasa tare da kama hannun hajia maamaa yace

"lafia hajia maamaa?"
Cikin sanyin murya tace " wai ja'irar yarinyar nan ce aka neme ta a makaranta a kasa rasa har ibraheem ya gaji da xaman rik'e ta ya xuciya ya taho ba ita ga iyayen ku gaba d'aya basa nan "

Tun da hajia maamaa ta fara magana ya xuba mata ido yana kallon ta cike da tashin hankali sai huci yake cikin tsawa yace

"what!, wannnan xancen ban yarda da shi ba, husna baxa ta yi haka taya Abba xai aiki ibraheem why? "
Hajia maamaa sakin baki tayi da ido tana kallon Yah Abdullah wanda bata ta6a ganin shi a haka ba, amman don ta k'are d'an gaban goshin nata yasa tace

"ae ibraheem bashi da laifi ita husnar da ta tafi yawon ta ita ke da laifi "
Wata harara Yah Abdullah ya aikawa hajia maamaa don ya rasa me ma xaice juya wa yayi kan su Ilham ya kwantsama musu tsawa tare da fad'in
"ku fad'a min gaskia barin ta yayi ko??? "

Cikin sauri su Ilham suka ce "Gaskia ne Yah Abdullah mun neme ta mun rasa ne "
(Yah ibraheem ne yaja musu kunne akan Idan suka fad'i gaskia sai yasa su hawan bango ba ma jump frog ba kuma sai yaci uban su tare da rufe su a toilet na tsayin yini guda ba ci ba sha ba k'aramin tsoratar dasu yayi ba shine suna ji suna gani suka bashi gaskia don basu da yanda xasu yi).

Wani kallon dukka k'arya kuke yayi musu tare da fice wa da sauri kamar xai tashi sama da masifar gudu ya fice daga gidan a cikin mota megadi Ya bishi da addu'ar sauka lafia, ya kure speed di'n motar gudu yake sosai xuciyar shi na tafarfasa sai faman huci yake.

Bai K'arasa makarantar ba sai daf da mangariba yana parking ana kiran sallahr mangariba duhu ya fara yi, dube dube ya fara yi yana kiran sunan ta amman shiru gaba d'aya hankalin shi ya dad'a tashi matuk'a fiye da da,  sai da ya d'auki wajen 25mint yana neman husna har masu gadin makarantar suna taya shi nema don sun tabbatar tana nan cikin bata fita ba.

Dakyar suka gano ta k'ark'ashin wata bishiya tana kwance kan kujera ta dukunkune jikin ta waje d'aya sai faman ajiyar xuciya take saki alamar taci kuka ta koshi, tsugunna wa Yah Abdullah yayi ya kura mata ido hannun shi yasa ya shafi gefen face d'in ta yana ayyana wasu abubuwa a cikin xuciyar shi, kafin ya fara tashin ta a hankali a tsorace ta bud'e idanun ta suna had'a ido da Yah Abdullah ta fad'a jikin shi tare da sakin wani kuka bubbuga bayanta yake yana cewa
"shiiiii baby nah ya isa hka tashi mu tafi "
Hannun ta ya kama yaja har xuwa inda yayi parking ya bud'e motar ya kwantar da ita a seat di'n baya sannan ya shiga yayi wa motar key sai da yaxo dai dai gate ya sallami masu gadin da kud'i sannan ya fice daga skul d'in yana driving yana d'an  waiwayen husna.

Yah Abdullah da husna suna barin wajen naga wani ya fito daga bayan bishiyar da husna ta kwanta a k'ark'ashin ta ya nufi inda yayi parking ya shiga tare da fita daga skul d'in gaba d'aya.

Sai wurin 8 suka isa gida Yah Abdullah yana parking da motar shi Yah ibraheem shi ma yayi parking ya fito tare da cewa "Yah Abdullah a ina ka tsinto ta kuma? "
Wata harara ya samu a wajen Yah Abdullah da husna basu kula shi ba suka shige cikin gidan yayin da Yah ibraheem ya saki wani shi'umin murmishi wanda na kasa banbance wane kalar murmishi ne hankalin shi kwance yayi part d'in hajia maamaa don a matuk'ar gajiye yake jin shi yinin yau through out bai samu zama yana tafiya yana cilla key di'n shi yana cafewa da haka har ya K'arasa part d'in.

Yana shiga ya had'a ido dasu Ilham ya 6alla musu harara sunkuyar da kansu suka yi da sauri d'an siririn tsaki yasaki tareda shigewa bedroom d'in shi don ya watsa ruwa ko yaji dad'i.

Lokacin da labarin yaje kunnen su Abba 1, wato Alhj muktar da daddy Alhj Omar sai Abba 2 Alhj mustapha nan fah aka kirawo su gaba d'ayan su don tabbatar da wanda yake da Gaskia a tsakanin Yah ibraheem da husna, yana xaune a gefe sai faman murmishin mugunta yake hankalin shi kwance anan dai duk su Ilham suka goyi bayan Yah ibraheem haushi da takaice ya turnik'e husna kamar xata rushe da kuka ganin yanda duk ita aka bawa laifin sai fad'a ake mata Yah Abdullah da su Yah mus'ab sun san husna baxa tayi haka ba sharrin Yah ibraheem ne kawai.

Danne kukan ta tayi tak'i bar hawayen ya fito duk da yanda xuciyar ta take cikin bak'in ciki kuwa don a ganin ta Idan har ta xubar da hawaye a gaban mak'iyan ta (Yah ibraheem)  har ya gansu alamar ya samu sa'a a kanta don hka tak'i barin su Su fito sai huci take fuskar nan a had'e fuuuu ta fice daga palon yayin da Yah Abdullah ya tashi ya bita da sauri don ya rarrashe ta Hka sauran duk suka mik'e aka bar hajia maamaa, Abba 1,abba 2 da daddy sai mumy, mamee da umma sai ibraheem kanshi yana cinyar mameen husna yana mata shagwa6a ita kuma ta biye mishi sai wani lalla6a shi take.

Tana shiga bedroom d'in su ta xube kan bed tana rusa kukan bak'in ciki da takaici wata sabuwar tsanar Yah ibraheem tana sake ruruwa a cikin xuciyar ta nan Yah Abdullah dasu Yah mus'ab suka xo suna rarrashin ta har da su Ilham, Fadila da raudah dakyar tayi shiru ta share hawayen ta sai da dare ya d'an yi sannan suka fito daga d'akin aka bar Ilham, raudah da Fadila sai husna anan suke sake bata hak'uri tare da sanar da ita abin da Yah ibraheem yayi niyyar yi musu idan suka fad'i gaskia, wani murmishin takaici husna ta saki tare da cewa
"ba komai kada ku samu damuwa k'iyayya ni da Yah ibraheem yanxu muka fara ta "
Kallon ta suke amman sun kasa cewa komai toh me xasu ce mata shiru suka yi kowanne xuciyar shi cike da sak'e sak'e.


Tun da ga lokacin husna ta d'auki wani hali ta yafa wa kanta fad'a, masifa idan aka ta6o ta ta dunga yi kenan, tsakanin ta da Yah ibraheem ko kallon mutunci Bata yi mishi balle aje batun magana ta fatar baki shi kanshi yana mamakin yanda husna ta koma ko irin tsoran nan da yake gani a fuskar ta idan ta ganshi yanxu sam babu shi.

Da hka har suka cinye hutun su suka koma makaranta wannan Karon ba'a yi kuka sosai ba hka Yah Abdullah ya kai su makarantar sannan ya jiyo xuciyar shi cike da tunanin husnar shi sam baya son tayi nesa dashi...............



_kuyi hak'uri da wannan wlh har yanxu sister Sumy bata samu cikakken lafiar yin typing ba ku dunga yi mana uxiri don komai sai da lafia, i luv yhu oll my fans_

Aishat A muh'd


       *&*

Sumayya salees sadeeq
[25/07, 09:30] Aishat A. Muhd: 🍃 *DANGARTAKAR ZUCI*🍃





*written by*
Aishat A muh'd


        *&*

Sumayya salees sadeeq





*Page 19-20*





  Haka rayuwa ta cigaba da tafiya su su husna sun mayar da hankalin su kan karatu, yayin da har yanxu husna take nuna wa Yah ibraheem irin k'iyayyar da take mishi kullum gaba take bata kula shi ko shiga harkar shi ko kallon Inda yake bata yi Idan sun xo hutu gida, a yanxu sun saba da makarantar sosai.

Suna Js 3 ne Yah ibraheem abban shi ya sama mishi wata university a k'asar Malaysia ya tafi cigaba da karatun shi dakyar aka shawo kan Yah ibraheem ya yarda saboda shi ya fison ya xauna a kusa da hajia maamaa da iyayen shi sai da abba yayi mishi tatas sannan ya amince ba don yaso ba haka ya tarkata ya tafi malaysia.

An fara girma su husna yanxu ko jikin Yah Abdullah ta dai na xama idan yaxo musu visiting Ko sun je gida hutu sai dai su xauna suna hira cikin kwanciyar hankali ba dai su had'a jiki da juna ba sai dai idan ya kasance da uxiri babba, duk da yana dan uwan ta kuwa don ba abu ne mai kyau shi kanshi Yah Abdullah yaja baya da janta a jikin shi tun da yanxu girma yaxo musu sai dai har yanxu wannan shakuwar nan da suka yi juna tana nan sai ma cigaba take wajen kok'arin rikid'a ta koma so da kauna amman har yanxu Yah Abdullah ya kasa fad'a wa husna abin da yake ji a cikin xuciyar shi don yana ganin har yanxu akwai sauran time.

Yayin da kulawar da yake bawa husna ta fita daban da yanda yake kula da su Ilham, raudah da Fadila a gaban ko wane yana nuna wannan banbancin, lokacin da husna taji labarin Yah ibraheem abba ya tura shi k'asar Malaysia karatu ba k'aramin jin dad'i tayi ba a xuciyar ta don ita har cikin xuciyar ta tak'i jinin ganin Yah ibraheem ta tsane shi ba Kad'an ba.

Suna ss one ne Yah Abdullah ya kammala karatun shi na accounting cikin nasara tare da samun aiki a abuja nan ya tarkata ya tafi sai week end yake samun shigo wa kaduna yanxu suna d'an dad'e wa basu had'u da husna ba saboda yanayin aikin shi amman duk da hka yana kok'arin lek'a wa skul d'in don ya ganta, ana cikin hka ne aka sanya ranar bikin su aunty khadijah, aunty Amina, aunty marwa, aunty aimana da aunty rufaida don sun kammala had'a diploma hajia maamaa ta dage akan baza su cigaba da karatu ba aure xa'a yi musu sun girma idan yaso sa cigaba a d'akunan maxajen su kuma gashi kusan duk tsiran su ba yawa don hka kowacce ta fito da wanda xata aura kusan duk en uwan hajia maamaa ne don ita ta fison auren xumunci kusan duk ita ta had'a kowanne da wanda xasu aura.

Su husna sun sha takaicin basu aka yi bikin don lokacin suna skul gashi daf da xana exam suke haka hak'ura amman ranar kowacce rai a 6ace yake ana can ana shan shagalin biki babu su kuma wannan auren Kusan shine na farko wanda xa'a yi a gidan nasu.


Ilham ce take xaune tana kallon  wani photo a hannun ta ta kura mishi ido sosai tana murmishi ita dai tana masifar son Yah Abdullah tun lokacin da bata san mene so ba har xuwa yanxu da ta fahimci ta fad'a son Yah Abdullah yayi mata kamu a xuciyar ta bana wasa hannu tasa ta shafa kyakkyawar fuskar shi tare da furta "Yah Allah ka mallaka min wannan bawan naka Ina son shi da yawa "
Jin motsin Shigowar su husna yasa ta da sauri ta tura photon k'ark'ashin katifar da take kwance don tasan idan suka ga photon ta shiga uku da tsiyar su nan suka xube kan bed d'in da take kwance tare da rungutsu me wa hira sosai har xuwa lokacin da bacci ya fara daukan su nan kuma kowacce ta nemi lafiyar bed d'in ta tare da kwanciya tuni bacci yayi awon gaba dasu ban da Ilham da ta Kara d'auko picture d'in Yah Abdullah tana kallo son shi da kaunar shi na k'ara ratsa xuciya da gangar jikin ta.


Lokacin da su husna suka shiga ss 3 ne suna kok'arin zana exam di'n neco da waec ne sak'on Yah ibraheem ya isko su husna har makarantar wanda ko Inda kayan suke husna ba ta kalla ba gaba d'aya ta mayar da hankalin ta kan duba books di'n ta, Ilham, raudah da Fadila sai tsallen murna suke suka fara bubbude wa kayayyakin sawa ne su arabian gowns, arabian perfumes masu matuk'ar k'amshi da flat shoes masu shegen kyau da tsada kuma dukka kayan na iya kacin mutum uku ne Ilham, raudah da Fadila ban da husna kenan gaba d'aya sai jikin su yayi mugun sanyi suna sake jinjina irin k'iyayyar da Yah ibraheem yake yiwa husna sai suka bar murnar kuma don sam basu ji dad'i ba suna Fadila tana cikin tattare kayan tana Mayar dasu cikin bag d'in sai ga wani kyakkyawa hankacif ya fad'o farine sol dashi anyi wani rubutu da pink colour a jiki yasha adon flowers sai wani mugun k'amshin turare yake mai sanyaya xuciya anyi rubutu da yaren India cikin wani baituka a wak'ar aashiqui kamar hka

"Hum tera bin ab reh nahi sakte, tere bina Kya wajood mera tujhse judaa gar ho jayenge toh khud se hi ho jagenye, kyun ki tum hi ho, ab tum hi ho ,tera mera rishtaa hai kai sa Ek pal door gawara nahi"

Fassara (baxan iya rayuwa ba tare da ke ba, mene amfani na Idan babu ke, idan har na rabu da ke?, tamkar na rabu da rayuwa ta ne saboda ke kad'ai ce rayuwa ta, wata irin dangantaka ce a tsakanin mu bana so muyi nesa da juna ko Kad'an...)

Rungume hankicif d'in Fadila tayi tare da xama kusa dasu husna cikin wani yanayi tace
"a yau nake son sanar daku wani sirri nawa wanda babu wanda ya sanshi daga ni sai *DANGARTAKAR ZUCIya* ta ku en uwa nane xan sanar daku don ku bamu shawara "

Gaba d'aya sun xuba wa Fadila ido suna sauraren abin da xata ce sai da ta sauke ajiyar xuciya sannan tace "ba wani abun ba ne yake damun xuciya ta ba sai son *Yah ibraheem* na dad'e ina k'aunar shi a cikin xuciya ta yanxu lokaci ya xo da xan bayyana mishi don baxan iya danne son shi ba ku bani shawara en uwa nah please "

Cikin tsananin mamaki suke kallon Fadila yayi da husna ta mik'e a fusace cikin tsawa tace "Fadila Kina cikin hankalin ki kuwa Kinsan me kike fad'a kuwa Ko kin haukace ne son Yah ibraheem kike da gaske ko da wasa "

Cikin tabbatar wa Fadila tace "da hankalina husna kuma da gaske ne ba mafarki bane "
Tuni jikin husna ya fara rawa saboda tsabar takaici ranta a 6ace tace "daga yau bani bake Fadila Ki rasa wanda xaki ce Kina so sai mak'iyi na na tsane ki kema i hate yhu "

Tana gama fad'in hka ta fice daga d'akin a fusace tare da buga kofar da karfi gaba d'aya suka bi ta da ido suna mamakin yanda husna ta koma lokaci d'aya tare da furta wad'annan .............




Aishat A muh'd

        *&*

Sumayya salees sadeeq
[25/07, 09:30] Aishat A. Muhd: 🍃 *DANGARTAKAR ZUCI*🍃






*written by*
Aishat A muh'd

          *&*

Sumayya salees sadeeq






*Page 21-22*






     Wani banxan tsaki Fadila ta saki tare da cewa "wlh ban ga abin da xai hana ni furta wa Yah ibraheem so ba sai dai mu rabun kamar yanda kika ce "

Ido raudah da Ilham suka yi suna kallon ta kafin kuma raudah ta saki ajiyar xuciya tace "Kina tunanin xaki nasarar sace xuciyar Yah ibraheem Kinsan shi kai fi d'aya ne kin mance abin da ya yiwa aunty marwa akan kawai don tana son shi bama baki da baki ta fad'a mishi fad'a kawai don yaji tana fad'a wa su aunty khadijah ranar ba k'aramin wahala tasha hannun shi, ki rufa wa kanki asiri ki cire son shi a cikin xuciyar ki "

Hararar ta fadila tayi sannan a fusace tace "baxan cire son nashi ba Kinsan tsawon lokacin da na d'auka da son shi acikin xuciya ta,  muna koma wa gida xan je na samu Abba na fad'a mishi "

Wani kallo raudah ta bita dashi yayin da tace "tabbb kina da aiki a gaba Indai akan Yah ibraheem ne ko kin fad'a wa abba Kinsan dan gaban goshin hajia maamaa ne yana furta bai amince ba Kinsan ya xaunu ki rik'e martabar ki ta 'ya mace yarinya ki bar ganin d'an uwan ki ne "

Sai kuma jikin fadila yayi sanyi yayin da raudah ta buga uban tsaki ta bar wajen don ita ma da gaske fadila ta bata haushi don tasan wulakanci xata sha wajen Yah ibraheem.

Duk abin nan da suke Ilham gefe taja ta xauna tare da xabga uban tagumi don bata da tace wa anan to me xata ce mata irin halin da take ciki shi Fadila take ciki sai dai tayi alk'awarin ko son Yah Abdullah xai kashe ta baxata ta6a bayyana kowa ya sani balle shi kanshi ta barshi tsakanin ta da *DANGARTAKAR ZUCIn* ta, dukka su biyun ba wanda ya k'ara magana duk sun xurfafa a tunanin *son maso wanin da suke yi* wad'anda basu san suna yi ba.

Abu kamar wasa a ranar husna ta kwashe kayanta tsab daga room d'in da suke ciki ta koma wani room d'in ba wanda ta k'ara kula wa a cikin su duk wani bala'in haushin su take ji sun yi rarrashin nata amman duk a banxa tak'i tsaya wa ma ta saurare su baxata iya xama da mak'iyiyar ta a d'aki d'aya (hmmm ji husna da wata magana kamar fadilan itace Yah ibraheem di'n), dole suka hak'ura da bata baki suna ji suna gani ta kwashe kayan nata wanda tun da suka xo skul d'in nan basu ta6a raba wajen k'wana ba har a gida ma bedroom d'in su d'aya.

Ranar kowannen su xuciyar su ba dad'e amman duk da hka fadila tana nan kan kudurin ta saboda husna baxa ta iya hak'ura da abin da take so ba.


Har suka fara exam husna bata kula fadila magana bata had'a su amman raudah da Ilham tana kula su sosai su yi hira kamar da ita ma fadila sai ta share ta har ma ta canza wasu friends bata fiye shiga harkar su ba ma, abun yana damun raudah da Ilham sosai don baxa su so hakan ya cigaba da tafiya ba basa kula junan su nan suka shiga tunanin yanda xasu shirya su ta Fadila mai sauk'i ne sun fi jin husna don Akwai ta da kafiya sosai.

Wani yammaci ne lik'is an yi ruwa an d'auke iska mai dad'in gaske tana kad'a wa yanayin akwai dad'i sosai a dai dai wannan lokacin ne husna ta fito daga room d'in da ta koma tana kok'arin shiga d'akin su Ilham don ta kar6o abu sai taga wani kyakkyawan hankacif fari sol a k'asa kallon shi ta tsaya yi don yayi matuk'ar birge ta hannu tasa ta d'auka tare da warware shi wani mugun k'amshi mai matuk'ar dad'in gaske ya bige har sai da ta lumshe idon ta don dad'in k'amshin sannan ta bud'e su akan hankacif d'in rubutu ta gani a jikin shi da yaren India Mt'sss taja tsaki tare da cewa
"ni na iya wani Indian ci ne amman da gani baitukan soyayya ne ko na wane? "

Hka kawai taji tana bala'in son hankacif di'n don haka ta ce "Ko na wane wlh baxan bayar ba ina son shi "
Don hka da sauri ta koma d'akin nasu ta 6oye acikin bag d'in ta sannan ta sake fita d'akin su Ilham ta shiga

Ko kallon Inda Fadila take bata yi ba wurin da Ilham da raudah suke xaune nan ta je ta xauna anan fah su Ilham da raudah suka dunga yi musu fad'a da nasiha akan bai kama ta ba abin da suke yi yanxu idan iyayen su sun ji xasu yi farin ciki da haka bayan kullum nasihar su su rik'e xumuncin su kada fah su manta su *dangin juna ne* .

Tuni Fadila ta sakko ta hak'ura amman fah har yanxu kudurin ta nan, dakyar suka shawo kan husna ta hak'ura nan kuma suka 6arke da hira kamar da Lallai na yarda jini d'aya ba wasa ba ne har suka je suka kwaso kayan husna nan fah suka koma kamar da ko da wasa fadila bata k'ara maganar Yah ibraheem ba sai dai tana nan tana fama da ciwon son shi acikin xuciyar ta.

Haka ma Ilham ba k'aramin axabtuwa take da son Yah Abdullah ba sai dai ta barwa xuciyar ta ko a fuska bata ta6a nuna wa su husna tana son Yah Abdullah ba.


A yau su husna suka kammala xana exam paper d'in su ta K'arshe Islamic studies ne kuma ta safe ce don hka sun sa ran yau k'wanan gida xasu yi duk wasu kayan su sun gama had'a wasu kuma sun raba wa sauran juniors di'n su duk sun fito farfajiyar skul d'in suna sallama da junan su cike da kewa don an saba da juna shekara 6 ba wasa bane .

Su husna kusan sune farko farkon tafiya don Yah Abdullah da wuri yaxo d'aukan su, suna cikin tafiya a mota yana driving husna tana gefen shi kallon ta yake fuskar shi d'auke da tsantsar farin ciki wai yau husnar shi ce tayi candy yana gaf da furta mata so don kada da xafi xafi ake dukan karfe sai hirar su suke hankali kwance husna yanxu tana d'an kunyar don ta fahimci sonta yake kuma so irin na aure ita kanta baxa tace bata son Yah Abdullah ba don ya had'u ta ko'ina kuma xata yi alfaharin kasance wa matar shi.

Yayin da Ilham ta xuba tagumi tana kallon su don yanda suke kallon junan su ta tabbatar soyayya suke bata gasgata hakan ba sai yau don su Fadila da raudah sun sha fad'a mata Yah Abdullah da husna soyayya suke bata yarda sai yau, wasu xafafan hawaye ne suka xubo daga idonta tare da cewa acikin xuciyar ta
"Yah Allah na rok'e ka ka cire min son Yah Abdullah a cikin xuciya "
Hannu tasa ta goge hawayen fuskar ta ta tare da sunkuyar da kanta don ta dai na ganin yanda Yah Abdullah yake wani aikawa da husna sak'on shi ta cikin idanu wan shi da hka har suka K'arasa gida.

A farfajiyar gidan suka tarar da mamee, umma da Mumy sai hajia maamaa suna jiran xuwan su da gudu husna da fadila da raudah suka yi wajen su yayin da Yah Abdullah da Ilham suka jero kamar wasu masoya shi gaba d'aya bai kula Ilham ce a kusa dashi ba hankalin shi yana kan husna yyana ta faman murmishi ganin yanda take tsallen murna.

Kamar ance hajia maamaa ta kallo su sai taga sun dace da junan su Har wani tunani ya fara darsu wa a cikin xuciyar ta.........



_mun ji kokan ku readers da kuke buk'atar mu dad'a page Idan sis Sumayya ta warware xamu dunga kok'arin yin typing da yawa Insha Allah_





Aishat A muh'd

           *&*

Sumayya salees sadeeq
[25/07, 09:30] Aishat A. Muhd: 🍃 *DANGARTAKAR ZUCI*🍃





*written by*

Aishat A muh'd

          *&*

Sumayya salees sadeeq






*Page 23-24*







      A tare suka K'arasa wajen su hajia maamaa suke nan suka dunga murna na ganin 'ya'yan nasu yayin da hajia maamaa take murnar dawowar jikokin nata don bata da en hira yanxu duk su aunty marwa suna gidajen su gashi d'an lelen nata bama ya k'asar gaba d'aya ba k'aramin kewar shi take ba, don hka ganin dawowar su husna ba k'aramin dad'i yayi mata ba .

Nan suka nufi part d'in hajia maamaa gaba d'ayan su kowanne cike yake da farin ciki musamman ma Yah Abdullah nan aka xauna ana hira cike da kaunar junan su har xuwa lokacin da aka kirawo sallahr axahar tukunna kowa ya tafi don gabatar da sallah.


Bayan su husna sun dawo gida da k'wanaki 2, kamar yau misalin karfe uku na yamma husna ce xaune a parlour tana faman kallon tashar mbc bollywood suna yin film d'in houseful 2 tana cin dariyar su akshy Kumar da John Avraham sosai film d'in yake sata dariya, Yah Abdullah ne yayi sallama ya shigo parlourn da sauri ta gyara xamanta tare da d'aukan hular ta ta sanya a kanta tana amsa mishi sallamar xama yayi a d'an kusa da ita tare da cewa

"ina mamee ne? "
"Laaa yah Abdullah ka mance tana hospital fah "
D'an sosa k'eya yayi tare da cewa "ohhh na mance ne princess "
Hannun shi ya sanya tare da bud'e ledar da ya shigo da ita wani mugun k'amshi ne ya cika mata hanci tare da had'iyar yawu muk'ut don wani nama ne gashasshe yasha su vegetables sai k'amshi yake.

Dariya ce ta kubce wa Yah Abdullah ganin yanda take had'iyar yawu cikin shagwa6a tace "ni.... ni Gaskia Yah Abdullah ka dai na yi min dariya ko nayi kuka yanxu "

Da sauri ya danne dariyar tare da cewa "wane ni na sanya princess kuka I'm sowieee dear "

Hannu tasa cikin naman ta d'auka tare da kai wa bakin ta wani lumshe ido tayi saboda dad'in naman ga laushi tuni ta xage ta fara ci don husna har yanxu bata dai mayatar cin naman nan ba, shi yasa Yah Abdullah Indai akai hutu ko xai je musu visiting sai ya siyo mata nama gashasshe mai kyau ya kai mata wani lokacin kuma mumy ta gasa mata.

Yana xaune yana kallon ta sai da ta cinye shi tsaf tukunna ya bud'e bakin gwangwanin maltina ya bata rabi ta iya sha tace ta koshi kar6a yayi tare da sanya baki a maltina ya shanye ta tukunna ya kalle ta yace
" i hope princess d'ina ta koshi? "
Cikin murmishi tace "tabbb na koshi ji nake kamar ciki na ya fashe gaskia yah Abdullah naji dad'in naman nan sosai "
Cikin jin dad'i yace "Kice kullum na dunga siyo miki? "
D'an yatsine fuska tayi tare da cewa "ba ko yaushe ba Yah Abdullah kada na dunga wahalar da kai fah "
Dariya yayi kafin yace "ni gobe ma Insha Allah ina abuja "
D'an xaro ido tayi tare da cewa "Haba Yah Abdullah ban gaji da ganin ka ba fah?"
"sorry princess nah nima baxan so nayi nesa da ke ba ko da na 1mint ne dole ce tasa hakan "

 Shiru tayi tare da wani langa6e kai kamar xata fashe da kuka tuni hankalin shi ya tashi nan ya fara rarrashin ta kuma wani 6angaren na xuciyar shi yaji dad'in yanda husna ta nuna damuwar ta akan komawar shi abuja gobe don haka anan take ya fallasa wa husna sirrin xuciyar shi wanda ya dad'e a cikin xuciyar shi ya bud'a mata abin da yake dangantaka ne da xuciyar shi.

Sam husna batayi mamakin furta mata son da Yah Abdullah yayi ba don tuntuni ta fahimci inda ya dosa, samun miji kamar Yah Abdullah ae ba k'aramin sa'a tayi ba don hka lokacin da ya gama fallasa mata sirrin xuciyar shi kasa cewa komai tayi saboda kunyar da ta kamata shima bai takura mata ba sai ma ya bar part d'in tun da ya amayar da abin da yake damunshi a xuciyar shi.

Duk Wannan xafafan maganganun da Yah Abdullah ya fada wa husna a cikin kunnen Ilham taxo kawo wa husna phone d'in ta wasu xafafan hawaye ne suka xubo daga idonta xuciyar ta ta dunga wani irin xafi tana niyyar juya wa ta tafi Yah Abdullah ya fito ko kula da ita bai yi ba ya wuce cikin sanyin jiki ta shiga parlour bayan ta saita kanta, da gudu husna ta tashi tare da rungume Ilham tana dariya tace
"Yeeeeeee Yah Abdullah ya furta min kalmar da na dad'e ina jiran ji "
Cikin dakiya da sanyin jiki Ilham tace "me ya fad'a miki? "
"yana sona da kauna ta xai aure ni "
Husna ta fad'i cikin tsananin farinciki duk da Ilham taji lokacin da ya fad'a mata sai da gabanta ya sake fad'u wa wani murmishin yak'e tayi tare da cewa
"Gaskia na taya ki murna samun miji kamar Yah Abdullah sai an tona Allah ya bar ku tare "

Ilham ta fad'i tana kok'arin mayar da kwallar idon ta cikin xuciyar ta take cewa "nasan daga yau na rasa Yah Abdullah har abada xanyi kokarin ganin na cire son shi a cikin xuciya ta don baxan ta6a bayyana kowa halin da nake ciki ba ko da xan mutu wannan tsakanina ne da *DANGARTAKAR ZUCIya* na.

Nan fah husna ta dunga xuba mata hirar yanda ita ma take k'aunar Yah Abdullah Ilham duk ta danne abin da take ji a cikin xuciyar ta ta dunga xuga husna kan ta saki jiki su sha soyayya yanda ta dunga fad'in tayi dace da miji mai nutsuwa hankali, kyau uwa uba ilimi da yake dashi da addini dana boko tana ta yabon Yah Abdullah har ta fara sakin layi anan husna ta xuba mata ido tare da son karato wani abu a tattare da Ilham nan ta fara kok'arin d'iga aya akan Ilham dawowar mamee ne daga wajen aiki ya katse mush hirar tasu.

A cikin Wannan lokacin wata soyayya mai xafi ake gudanar wa tsakanin Yah Abdullah da husna bashi kaduna bashi abuja kullum yana faman xirga xirga duk week end, ana cikin hka ne result d'in su Ilham, husna, raudah da Fadila ya fito ba 6ata lokaci aka sama musu admission a university di'n kaduna tuni sun goge sun dad'a waye wa sosai barin ma husna daman duk a cikin su ta fisu rawar kai iyayi ga Yah Abdullah ya tsaya mata komai yi mata yake.

Fadila kuwa har yanxu son Yah ibraheem yana nan acikin xuciyar ta jira kawai take ya dawo don tana yawan yi mishi waya sosai ganin yana dan kulata yasa ta dunga kok'arin cusa kanta tsab ya karance ta sai dai murmishi kawai yake don Akwai wadda xuciyar shi take so, yayin da Ilham ma ta Duk'ufa da addu'a Allah ya cire mata son Yah Abdullah amman kamar sake cusa mishi son shi ake a cikin xuciyar ta tayi kukan tayi cutar duk tabi ta rame sosai ta sake xama silent daman can Ilham tana da sanyi kamar Yah Abdullah shima akwai hak'uri ................




_k'wana 2 kun ji mu shiru Kuyi hak'uri uxiri ne,ku cigaba da bibiyar mu don jin yanda xata kaya_😍






Aishat A muh'd


         *&*

Sumayya salees sadeeq
[25/07, 09:30] Aishat A. Muhd: 🍃 *DANGARTAKAR ZUCI*🍃





*written by*

Aishat A muh'd

          *&*

Sumayya salees sadeeq






_wannan page d'in sadaukarwa gare ku masoyan littafin *DANGARTAKAR ZUCI* kuna hak'uri akan rashin jinmu da bakwa yi kullum_






*Page 25-26*







       Haka lokaci ya cigaba da tafiya su husna sun yi nisa a karatun su sosai ana cikin hka hajia maamaa ta had'a taron gaggawa wanda sun saba yin family meeting so wannan taron na gaggawa da ta fad'a shi ya d'an d'aure musu kai don ko 2 weeks ba'a yi da yin family meeting ba.


Gaba d'ayan su sun taru a babban palon hajia maamaa ban da Yah Abdullah da Yah ibraheem amman duk sun had'u har su aunty marwa bayan an bud'e taro da addu'a hajia maamaa ta fara magana kamar hka


"nasan xaku yi mamakin tara ku da nayi anan to ba wani abun ba ne sai abin alkhairi da xai faru "

Sai lokacin hankalin su ya kwanta don duk gaba d'aya ba'a cikin nutsuwar su suke ba, d'an gyaran murya hajia maamaa tayi kafin ta fara cewa

"gani nayi kun xuba wa Abdullah ido kun k'i mishi maganar aure bayan ya gama karatun shi ya samu aikin yi gashi shine babba duk a 'ya'yan gidan "

Duk sunyi tsit suna jiran hajia maamaa ta K'arasa maganar ta cigaba da cewa tayi
"Don hka nayi tunani na yanke hukuncin xan aura mishi Ilham "

Gaba d'aya suka xaro ido cike da mamaki yayin da husna da Ilham sukayi suman xaune mumy ce tayi k'arfin halin cewa

"husna kike nufi hajia maamaa koh? "
Girgixa kai hajia maamaa tayi tare da cewa "Ilham nake nufi ba husna ba "
Caraf raudah tace "wlh hajia maamaa Yah Abdullah da husna suke soyayya ba Ilham ba kowa na gidan nan ya sani "

Harara hajia maamaa ta wurga mata tare da cewa "yo ai ni bansani ba na riga da kuma na yanke hukunci ko iyayen ku basu isa ba su canja min balle ku "


Gaba d'aya jikin husna Idan ban da rawa babu abin da yake yi tsabar tashin hankali wasu xafafan hawaye ne masu xafin gaske suke fito wa Daga idanun ta ta ma rasa tunanin da xata yi sai en palon da take bi da kallo kamar yau ta fara ganin su kafe idanun ta tayi akan hajia maamaa tana watsa mata wani kallo mai tattare da fassarori daban daban wanda bansan da me xan fassara muku shi ba.


Abban Ilham ne cikin muryar lalla6a yace "Don girman Allah hajia maamaa kiyi duba xuwa ga yaran nan kin ga suna son junan su ki duba ki ga shakuwar dake tsakanin su ma kad'ai ta isa a aura musu juna balle sun amince xasu auri junam su ki kyale su ita Ilham Allah xai kawo mata wani "

D'an shiru hajia maamaa tayi alamar tunani take sai suka fara addu'ar Allah yasa ta amince da shawarar abban Ilham d'an gyaran murya tayi tare da cewa 


"a gaskia ban yarda da shawarar ka ba mustapha yanda Abdullah yake da sanyi da hak'uri xaman su baxai xo d'aya da husna ba dad'in da d'awa komai take so koda baya so to sai yayi idan akayi auren juya shi xata dunga yi ni kuwa baxan lamunta ba Ilham ce dai dai dashi ita ma akwai hak'uri ba ruwan ta, ita ma husnar xan sama mata dai dai da ita "

Wayyo tashin hankali bashi da dad'i husna batasan lokacin da ta K'arasa wajen hajia maamaa ba ta rik'e mata kafafuwan ta kuka take har da majina cikin shesshak'ar kuka husna tace "Don girman Allah hajia maamaa ki taimaka min kada ki raba ni da Yah Abdullah ina son shi please "

Duk da ta bawa hajia maamaa tausayi amman hka ta dake tace "aure babu fashi nan da sati uku nake so ayi a gama na gama yanke hukunci kada wanda ya k'ara xuwa ya sake min magana "

Tana gama fad'in hka ta shige bedroom d'in ta don kada husna ta rinjaye ta don ba k'aramin tausayi ta bata.

Kuka sosai husna take duk sun tausaya wa husna masu saurin hawaye ma kukan suka fara su Abba 1, Abba 2 da daddy suka bar falon kowanne xuciyar shi ba dad'i da hukuncin da hajia maamaa ta xartar, nan suka dunga rarrashin husna amman kamar sake xuga ta suke Ilham ce taxo ta rungume ta itama tana nata kukan wanda tak'amai mai bata gane kukan me take ba kukan farinciki ne na jin dad'in Allah ya kar6i addu'ar ta ya bata Yah Abdullah a lokacin da ta fidda rai akan shi ko kuma kukan tausayin husna da Yah Abdullah da suke masifar k'aunar junan su ko kuma auren maso wani da xata yi don tasan Yah Abdullah sam baya sonta sai dai na en uwanta ka.


A fusace husna ta hankade ta daga jikin ta tare da fice wa daga palon gaba d'aya duk da kallo suka bi husna da tsantsar mamaki don husna da Ilham sun fi shakuwa da junan su suna shiri sosai da wuya aji kansu sai gashi hajia maamaa tana kok'arin raba kanna su akan wani dalilin nata na daban.


Kowa jikin shi a sanyaye suka tashi suna mai fargabar idan Yah Abdullah yaji wannan hukunci me xai faru don kowa yasan yanda ya xuciyar shi ta ginu da k'aunar husna.


Tun daga lokacin husna bata k'ara shiga part d'in hajia maamaa ba tun da ta tsane ta bata k'aunar ta daman tun farko a Cewar husna kenan daga skul sai islamia idan kaga husna ta fita kenan gaba d'aya ta fita a hayyacin ta karatun ma bata fahimta sosai duk tabi ta rame tayi wani iri ko yaushe idanun ta a kumbure gashi sunyi ja saboda tsabar kuka.

Ilham kullum sai taxo part d'in su husna tana nata kukan ita ma sam bata ji dad'in hukuncin da hajia maamaa ta yanke ba, ko kallon ta husna bata yi don ita ma haushin ta take ji sai da mamee ta yiwa husna fad'a sosai sannan take kula Ilham amman ba kamar da ba da kuma tayi tunanin ita ma Ilham din ba laifin ta bane tun da had'a su aka yi dole ta hak'ura ko tak'i ko taso kuwa don hka tun daga ranar da tayi wannan tunanin sai kuma suka cigaba da sha'anin su kamar da sai dai fah son Yah Abdullah yana nan mak'ale a cikin xuciyar husna baxata iya cire son Yah Abdullah ba sai dai ta mutu dashi, hajia maamaa kuwa husna ta dai na kula ta Ko part d'in ta ta dai na shiga idan suka had'u sai dai kawai ta gaida ita baxa ta jira amsar ta ba xata wuce gaba d'aya jikin hajia maamaa yayi sanyi tana jin tausayin husna.

Tun daga ranar da hajia maamaa ta yanke hukuncin auren Yah Abdullah da Ilham, husna bata k'ara d'aukan kiran yah Abdullah ba to me xata fad'a mishi gwara ta fara sabawa da rashin shi text mssg kira Hka yake yini yana kiran husna amman baxata d'auka ba sai dai ma ta koma gefe tana xabga kuka mai ban tausayi tasan tayi rashin masoyin ta.


Hankalin Yah Abdullah ba k'aramin tashi yayi ba na k'in d'aga wayar shi da husna batayi gashi ba wanda ya fad'a mishi don hajia maamaa ta gargad'i kowa kada wanda ya fad'a mishi Idan yaxo yaji a bakin ta, ko yace a had'a shi da husna sai a fara yi mishi hanya hanya don daga K'arshe husna kashe wayar nata tayi gaba d'aya ma, don hka a matuk'ar tashin hankali ya taho kaduna.................




_Kuyi hak'uri da wannan battery low_😥




Aishat A muh'd

        *&*

Sumayya salees sadeeq
[25/07, 09:31] Aishat A. Muhd: 🍃 *DANGARTAKAR ZUCI*🍃






*written by*

Aishat A muh'd


          *&*


Sumayya salees sadeeq






*Page 27-28*






        Yana shiga gidan kai tsaye part d'in mamee ya nufa don shi husna kawai yake son yayi toxali da ita yaji dalilin k'in d'aga wayar shi da bata yi, da sallama ya shiga palon mamee ce ta amsa mishi sallamar tana xaune kan kujera da news papers a hand nata tana duba wa d'ago kai tayi ta kalle shi har ya rame da ganin shi kasan yana cikin tarin damuwa tsantsa, xube wa yayi kan carpet tare da gaida mamee sannan yace

"mamee ina husna ne? "
"tana skul don suna da lectures d'in yamma ne "
Mik'e wa tsaye yayi tare da cewa "mamee don Allah ko Kinsan laifin da nayi wa husna bata picking d'in waya na? "
Dan girgixa kai mamee tayi gaba d'aya tausayin Yah Abdullah ya kamata dakyar ta iya bud'e baki tace
"bansani ba Abdullah gaskia "
"okay mamee ki taya ni da addu'a Allah yasa ta huce duk da bansan laifin da nayi mata ya fad'i yana rik'o hannun mamee gaba d'aya muryar shi rawa take alamun yana gaf da fashe wa da kuka, kallon shi mamee tayi a cikin xuciyar ta tace lallai hajia maamaa tayi hangen nesa da an had'a yah Abdullah da husna da bakaramin juya shi xata yi ba, sam baya son laifin ta  yana mata wani irin so da ko tayi mishi laifi baxai iya d'aukan mataki ba.

"kada ka damu Abdullah kaje ka huta tukunna "
Gid'a kai kawai ya iya yi sannan jikin sanyin jiki ya fice daga falon mamee ta bishi da kallon tausayi tana jinjina halin da Yah Abdullah xai shiga da xarar ya ji labarin hukuncin da hajia maamaa ta yanke.



Shi kuwa Yah Abdullah yana fita daga part d'in mamee kai tsaye shashen hajia maamaa ya shige bankad'a labulen palon yayi ya shiga tana xaune a kan kujera ta k'wama glass a fuskar ta tana kallon sunnah tv tana sauraron wa'azin sheik Isah Ali pantami cikin tsokana Yah Abdullah yace

"kai wannan tsohuwar da nacin kallo take kullum a k'wama glass a fuska sannan a xuba wa tv ido me kika sani? "
Hararar shi hajia maamaa tayi tare da dunkule hannun ta wara mishi su tare da cewa
"uban ka nake gani kaji yaro da rashin kunya ni xaka kalla kace me nasani "

xauna wa yayi a kusa da ita tare da cewa "tuba nake "
Tare da sa hannun shi cikin d'an k'aramin bowl di'n dake gabanta wanda cike yake da danyen dabino nunannu masu kyau da xak'i ya d'ebo yana ci ya bud'e baki xai yi magana kenan wayar hajia maamaa ta fara ringing don hka ta d'auka tare da mak'ala wa a kunnen ta tuni fuskar ta ta fad'ad'a da fara'a tana cewa

"Waalaikumussalam ibraheem khaleel yanxu nake tunanin ka yinin yau gaba d'aya baka kirawo ni ba, ince dai lafia? "

Ibraheem da yake xaune gefen swimming pool cikin wata kujera ya dad'a lafewa tare da lumshe idon shi yace
"lafia qlau maamaa "

Washe hak'ora ta dad'a yi tare da cewa"masha Allah haka nake son ji"

Yah Abdullah sakin baki yayi yana kallon yanda hajia maamaa take 6angala fara'a kawai don Yah ibraheem ya kirawo ta nan ya dad'a tabbatar wa ba k'aramin so take ma ibraheem ba.

Daga can 6angaren Yah ibraheem yace "ina ajiya ta dafatan tana nan lafia "

"ahh lafia qlau xaka xo ka same ta yanda kaban ajiya Insha Allah "
Wani shegen murmishi ya saki tare da shafa lallausar sumar kanshi ya cigaba da cewa
"alright, dafatan kin yi yanda na tsara miki "
"ae nayi yanda ka fad'i kasan bana son tashin hankalin ka ibraheem ka kwantar da hankali ka "

"okay granny xan dan kwanta na huta sai gobe bye "

"toh a huta lafia "

Tana gama fad'in hka ta sauke wayar a kunnen ta tare da ajiye wa muryar Yah Abdullah taji yana cewa "akan me kuke magana da ibraheem? "
Harara ta dalla mishi tare da cewa "ina ruwan ka wannan sirrin mu ne bana son sa ido"

D'aga kafad'a yayi alamar can ta matse muku mik'e tsaye yayi tare da cewa"bari naje na d'auko my husna daga skul don na matsu nayi toxali da kyakkyawar fuskar ta "

Tuni hajia maamaa ta K'ware da ruwan da take sha nan ta fara tari, Yah Abdullah yana mata sannu har sai da tarin ya lafa sannan tace "Yawwa kama tuna min yanxu xauna xamu yi magana da kai "
"ni kuma, gaskia ki bari sai na dawo "

Cikin er tsawa tace "idan da ubanka nake ya isa yayi min gaddama "
Ganin ta had'e fuska alamar ba wasa yasa ya xauna haka kawai yaji gaban shi yana mugun fad'uwa dan kallon shi tayi tare da cewa

"so nake ka fitar da husna daga cikin xuciyar ka? "

Da sauri ya d'ago kanshi ya Kalli ta tare da furta "what!!! "

"ehh ae kaji abin da nace sarai na xa6a maka ilham a matsayin wadda xaka aura nan da 3 weeks "

A matuk'ar kad'uwa da firgita yah Abdullah ya mik'e tsaye tare da cewa "Haba maamaa idan ma wasa kike ki daina bana son irin wasan nan ni ae husna nake so ba ilham ba "

"da gaske nake maka Abdullah ni kuma ilham ce xa6ina ita na xa6a maka ka aura "

"kuttt abin da baxai ta6a yiwu ba kenan "

"ka xuba ido xaka gani da idanun ka idan kaga an fasa Wannan auren sai dai idan na mutu amman idan har ina raye wlh kaji na rantse sai anyi "

Gaba d'aya Yah Abdullah ya rikice hankalin shi yayi masifar tashi jin abin da hajia maamaa ta fad'i wani gumi ne yake xiraro musu ta ko'ina saboda tsabar tashin hankali duk da sanyin AC dake aiki a palon, cikin hargo wa ya fara cewa

"baki isa ba ki rabani da husna don xuciya ta ta ginu a k'aunar ta tun ina jin sonta dagani sai *DANGARTAKAR ZUCIya* ta har takai na furta mata munyi alk'awarin aure a tsakanin mu xaki xo da wani banxan hargitsin ki na tsufa kixo ki wargaxa mana farincikin mu "

Cikin tsananin mamaki hajia maamaa take kallon Yah Abdullah sai kuma ta fashe da kuka tana tafa hannayen ta tare da cewa
"ni ka xaga Abdullah nice banxar? "

"ni fah ba xagin ki nayi ba kawai nace abin da baxai ta6a yiwu ba ne na auri ilham"

"yo xagi na nawa kuma ka xage ni kaci min mutunci don ina maka gata Indai ka auri husna mijin tace xaka koma juya ka xata dunga yi yanda take so"

Wani irin kallo yake mata Kafin ya had'iyi yawu dakyar yace "so what don na xama mijin tace ae ni kan tace ma zan xama don hka kiyi gaggawar kunce abin da kika kulluwa "

Wayyo Allah hajia maamaa d'ora hannu tayi akai tana gurzar kuka haik'an wai Yah Abdullah ne yake ci mata mutunci duk tayi wani wujiga wujiga da ita.

"to wlh baxai yiwu ba bari iyayen naka su dawo gida idan ban isa da kai ba ai su na isa dasu "

"daman ae Hka xaki ci tun da kin riga da kin k'ulla min............."

Kafin ya K'arasa fad'i yaji saukar mari a fuskar shi da sauri ya d'ago kanshi abban shi ya gani tsaye a gaban shi sai huci yake ya d'aga hannu xai sake marin Yah Abdullah da sauri hajia maamaa ta rik'e hannun tare da cewa

"barshi hka muktar "
Cikin fusata Abba yace "daman ashe baka da kunya Abdullah mahaifiyar tawa kake ma rashin kunya koh? "

Shi dai Yah Abdullah shiru yayi tare da sunkuyar da kanshi k'asa yana dafe da Inda abba ya mare shi xuciyar shi sai tafasa take shi yasa ashe husna ta dai na d'aga wayar shi.

"toh wlh ka tabbatar auren nan kamar Anyi angama ne, kuma na baka 30seconds ka fice daga gidan nan ka koma abuja "

A matuk'ar fusace ya fice daga falon motar shi ya fad'a kawai tare da yi mata key ya kwashe ta aguje a dai dai lokacin su husna suka dawo daga skul gaba d'aya sunyi matuk'ar tsorata da yanda yake gudu a motar sun tabbatar an sanar dashi komai wani irin kuka ne ya kufce wa husna ta shige part d'in su da gudu tana kuka yayin da Ilham, raudah da Fadila suka bita da kallon tausayi kowannen su jiki ba k'arfi suka nufi part d'in hajia maamaa.


Bayan fitar Yah Abdullah Abba ne ya xaunar da hajia maamaa kan kujera tare da rarrashin ta har ta kwantar da hankalin ta sannan ya fito daga part d'in................









Aishat A muh'd

          *&*

Sumayya salees sadeeq
[25/07, 09:31] Aishat A. Muhd: 🍃 *DANGARTAKAR ZUCI*






*written by*

*Aishat A muh'd*



           *&*


*sumayya salees sadeeq*















_Assalamu Alaikum readers xaku ga kamar munyi page 30, numbers d'in muka gyara dafatan kun fahimce mu_





*Page 29-30*






    Tun da ya d'auki hanyar abuja yake xubar da hawayen tashin hankali raba shi da husna ba k'aramin tashin hankali xai shiga ba saboda tsabar tsananin son da yake mata sai da xuciyar shi ta ginu da sonta sannan rana d'aya hajia maamaa ta wargaxa komai, duk yanda ya dad'e yana tsara xaman da Xasu yi husna hkan baxai yiwu ba duk hasashe ne.


Wasu hawaye ne masu xafin gaske suka xubo daga idanun Yah Abdullah tare da buga steering motar da hannun shi d'aya hajia maamaa ta gama dashi wlh ta raba shi da husna batayi musu adalci ba ko Kad'an, da hka ya k'arasa abuja yana shiga gidan shi yayi hon mai gadi ya bud'e sannan ya shiga tare da yin parking ya tsaya dakyar ya iya amsar gaisuwar da mai gadi yake mishi sannan ya shige.


Kan bed ya fad'a tare da runtse idanun shi ya cusa hannun shi cikin gashin kanshi yana yamutsa shi Mtsww yaja tsaki tare da cewa a fili

"amman hajia maamaa bata yi ba wlh ni mai xanyi da ilham yarinya sai shegen sanyin jiki kamar mara jini a jiki (ni kuwa na kalli sumy muka yi murmishi tare da cewa ji Yah Abdullah da wani irin xance kamar shima ba irin yanayin Ilham d'in ne dashi ba 🤣) haka dai ya dunga surutu shi kad'ai gaba d'aya ya rasa yanda xai iya amsar k'addarar auren Ilham, yayi try d'in number husna but switch off cillar da wayar yayi tare da lumshe idon shi.



Husna kuwa tana shiga part d'in su da gudu ta wuce mamee tana kuka sosai cikin tsananin mamaki mamee ta bita da kallo tana tunanin mai ya samu husna take kuka haka tashi tayi ta bi bayanta xuwa bedroom d'in ta.


Kuka sosai ta tarar tana yi tare da bubbuga pillow tana fad'in "why!  why!! Maamaa mai Nayi miki kika raba ni da masoyina kuma Kinsan irin tsananin shakuwar da muka yi da junan mu nasan baxan ta6a samun mai sona irin Yah Abdullah ba "

Kuka sosai husna take har dasu majina ba k'aramin tausayi ta bawa mamee ba har sai da taji idanun ta Sun cicciko da hawayen tausayin husna da Abdullah lallai ba k'aramin son junan su suke ba sai dai aikin gama ya gama tun da nan da en k'wanaki xai auri ilham.


K'arasa wa tayi Inda husna ta ke kuka ta dafa mata kafad'ar ta da sauri husna ta juyo tare da goge hawayen fuskar ta ganin mamee ce yasa ta k'ak'alo murmishin yak'e tare da cewa

"Laaa mamee nah yaushe kika shigo? "
"tun kina kuka da sumbatun son Abdullah "

Kunya ce ta lullu6e husna ta sunkuyar da kanta hannu mamee tasa ta d'ago da fuskar husna tana ganin yanda hawaye suke fita daga idonta girgixa kai tayi tare da cewa

"husna ni mahaifiyar Kice fad'a min damuwar ki kada ki 6oye min don duk duniya baki da kamata "
Rungume mamee husna tayi tare da sake fashe wa da kuka mamee bata hanata kukan ba don idan ta samu tayi kukan sai ta fi jin sanyi a cikin xuciyar ta bubbuga bayanta kawai mamee take cikin shesshak'ar kuka husna tace

"mamee bansan yanda xanyi na cire son Yah Abdullah acikin xuciya ta ba Ina sonshi ina sonshi sosai mamee don Allah ki ban shawara? "

Cirota mamee tayi daga jikin ta sannan tace "kalle ni nan husna Idan shawara kike son na baki share hawayen ki sannan ki saurare ni "

Hannu tasa ta goge hawayen fuskar ta mamee ta Mik'o mata tissue ta fyace hancin ta sannan ta nutsu tana sauraren abin da mamee xata ce mata kuma tayi alk'awarin duk abin da mamee tace xata yi aiki dashi don baxata gurguwar shawara ba.

"da farko husna ina son ki yarda da kaddara mai kyau da mara kyau sannan kisa wa xuciyar ki Allah ya riga ya rubuta Abdullah ba mijin auren ki bane, don hka ina son kisawa xuciyar ki nutsu wa ki kwantar da hankalin ki ki cire wata damuwa saboda kiyaye lafiar ki, sannan ki dage da addu'a sosai kan Allah ya cire miki son Abdullah ya baki miji na gari wanda xai soki fiye da Abdullah ma, ki dunga danne duk wani abu akan shi kada ki bari mutane su fuskanci kishi kike da er uwar ki ilham ki dunga kau da kai akan Abdullah ko dan ilham ma Kinsan sharrin xuciya da hud'ubar shaitan kada wata matsala ta kunnu a tsakanin ku Kaf yaran gidan nan kun fi shakuwa da Ilham idan aka d'auke Abdullah, ki fad'a wa Allah damuwar ki Insha Allah xai miki maganin duk wata damuwa da kike ciki, nima a matsayi na na mahaifiyar ki xan taya ki da addu'a sosai, ko Kad'an bana son Kina sa damuwa acikin xuciyar ki shima Abdullah kada ki sauya mishi ku cigaba da xumuncin ku kamar da kin ji koh? "


Cikin dashashshiyar murya husna tace "Naji mamee kuma Insha Allah xan yi kok'ari wajen cire damuwa sannan xan mik'a al'amari na ga Allah "

Cikin murmishi mamee tace "Allah yayi miki albarka "
"Ameeen mamee nah ngde wa Allah da ya bani ke a matsayin uwa "

Jan karan hancin husna mamee tayi suka tuntsire da dariya kuwa sannan suka cigaba da hira irin ta tsakanin uwa da er tah.
Ilham wadda take jingine jikin kofar bedroom d'in husna tana nata kukan duk tattauna war da su mamee da husna suka yi taji don taxo xata shiga d'akin taji ta jinjina wa mamee sosai da ta bawa husna shawara ta gari wannan itace uwa ta gari wani son husna da mugun tausayin ta ya kama ilham sosai da gudu ta fice daga part d'in ta nufi part d'in hajia maamaa cikin kuka ta fad'a kan hajia maamaa tare da cewa
"na rok'e ki maamaa don girman Allah ki janye wannan auren da xaki had'a ni da Yah Abdullah ki mayar dashi kan husna suna matuk'ar kaunar junan su "
Ture ta hajia maamaa tayi daga jikin ta tare da cewa "kada ki k'ara xuwa inda nake da wannan maganar na riga da na gama yanke hukunci na don hka fitar min daga d'aki"
Ta K'arasa fad'i cikin tsawa don hka da gudu ilham ta fice daga d'akin hajia maamaa ta shige d'akin su tana kuka sosai tayi kuka har kanta ya fara ciwo wani bacci ne yayi awon gaba da ita sai faman sauke ajiyar xuciya take.

To cikin en k'wanakin nan abubuwa sun yiwa Yah Abdullah xafi sosai yabi ya rame ya fita hayyacin shi ko abinci baya iya ci sosai ya dage da kai kukan shi ga Allah, yayin da husna ma ta dage da addu'a sosai kuma tana jin dad'in yanda xuciyar ta ta fara sabawa da rashin Yah Abdullah, Hka ma a 6angaren ilham itama addu'ar neman xa6in Allah take, da hka har ya rage sauran k'wanaki 10 bikin Yah Abdullah da Ilham su hajia maamaa sai shirye shiryen biki ake don har lefe ita ta had'a (Sumy ta ta6e baki tare da cewa ba dole tayi shirye shirye ba tun da ta raba masoya 🤣)

Iyaye  ma sai nasu shirye shiryen suke amman ta 6angaren ango Abdullah da amarya ilham babu wani shiri don dukkan nin su acikin damuwa suke............



```Kuyi hak'uri da wannan page d'in daga yau baxa mu k'ara typing ba sai xuwa bayan sallah Insha Allah, dafatan xamu dage da ibada kada mu 6ata lokacin mu wajen karance karancen novel's da kalle kalle ko xaman hira mara amfani adage da karatun alqur'an da addu'o'i dasu salatin Annabi da istigifari don neman dace wa,Allah yasa mu dace da ganin lailatur qadr , wanda nayi wa laifi wanda na sani da wanda bansani ba ku yafe min,Allah ya kar6i ibadun mu yasa kar6a66iya ce Ameeen thumma Ameeen```


_masu lafia Allah ya k'ara muku lafiya marasa lafia na gida dana asibiti Allah ka basu lafia don alfarmar wannan watan mai albarka, mu kuma writers Allah ya k'ara mana basirah da Kaifin tunani wajen rubuta novel's masu ma'ana_




*Aishat A muh'd*


          ```&```


```sumayya salees sadeeq```
[25/07, 09:31] Aishat A. Muhd: 🍃 *DANGARTAKAR ZUCI*🍃






*written by*

Aishat A muh'd

          *&*

Sumayya salees sadeeq






_Assalamu Alaikum readers dafatan anyi sallah lafia, Allah ya kar6i ibadun mu, Allah ya maimaita mana, ina muku barka da sallah_😍






*Page 31-32*





         Iyaye ma sai nasu shirye shiryen suke amman ta 6angaren ango Abdullah da amarya ilham babu wani shiri don dukkan nin su acikin damuwa suke tsantsa musamman yah Abdullah ma, yayin da husna ta Duk'ufa da addu'a kan Allah ya yaye mata son Yah Abdullah a cikin xuciyar ta kuma Alhmdllh yanxu xuciyar ta ta fara sabawa da rashin Yah Abdullah ta mai da hankalin ta kan karatun ta.


   Sam ta fita daga sabgar hajia maamaa ta daina shiga part d'in ta tun lokacin da ta raba ta da abin k'aunar ta Yah Abdullah sai dai idan sun had'u ta gaida da ita ko jiran amsawar  ta Bata jira tayi gaba, hkan ba k'aramin damun hajia maamaa yake ba sosai amman hkan da take yi baxai hana ta canja ra'ayin ta ba Idan ta gama fushin nata ta sakko.



  Kamar yau misalin karfe 9 na safe husna ta fito cikin shirin tafiya skul tana sanye da wata gown d'in atampha kalar white and pink d'inkin yayi kyau kuma rigar ta amshe ta sosai tayi light make up a face d'in ta fuskar nan tayi fiyau da ita sai ta sanya mayafi black Hka bag and shoe din ta black ne sai wayar ta a hannun ta sai sauri take don tana da lecture di'n 10 na safe gashi malamin irin mai xafin nan ne, tana fito wa palo ta tarar da daddyn ta da mamee suna break fast a saman dinning table k'arasa wa wajen tayi tare da sallama daddy ya d'ago kai ya kalle ta murmishi ya saki ganin yanda take xum6ura baki hannu ya mik'a ya kama nata tare da xaunar da ita kusa da kujerar da yake xaune yace

"sweet baby nah what happened with u?

Cikin shagwa6a tace "dad ina alk'awari na?

Da sauri dad ya dafe goshi tare fad'in "ohhh my god my mamanah (da yake some times hka yake kiran ta) ae na cika alk'awarin na ki "
Ya K'arasa fad'i yana miko mata keys d'in mota, da sauri husna ta damk'e keys d'in tare da rungume daddy cikin tsananin murna tana fad'in

"thank u so much my sweet dad, Allah ya k'are min kai "

Ta jiyo cikin murna tana kallon mamee tace "mamee nah ki taya ni godia wajen dad ya siya min sabuwar mota "

"Yayi er gidan dadyn ta toh my dear an gode Allah ya k'ara bud'i "

Cikin wani salon kallo daddy yayi wa mamee tare da cewa "Ameeen doctor nah! "

Murmishi suka sakar wa junan su irin na tsofaffin masoyan nan masu matuk'ar k'aunar junan su yayin da husna ta yi murmishi tana girgixa kai kawai ita dai salon soyayyar iyayen ta tana matuk'ar birge ta tea ta had'a tare da xuba chips and egg sai er source d'in da ake don cin chips d'in tayi bismillah tare da fara yin breakfast d'in ta.


Cikin en mintuna ta gama yin breakfast d'in sannan tayi ma daddy da mamee sallama ta fita da sauri saboda ganin time ya ja, tana fito wa farfajiyar gidan ta ga su fadila da raudah suna jiran ta cikin tsananin farinciki ta K'arasa wajen tare da cewa " my sister's ku taya ni murna my cwt dad ya siya min sabuwar mota "

Da sauri suka ce "da gaske kike ?"

"ehhh wlh kuxo ku gani tana parking space "

Lokaci d'aya suka rungume husna tare da fad'in "wow my sis congrats fah "

Nan suka K'arasa wajen wow suka had'a baki wajen fad'i ganin wata hadaddiyar mota green colour ce sai shek'i take nan fah suka fara shafa motar tare da santin ta ganin had'uwar motar duk anan suka shantake har goma ta kusan yi nan suka ankare Kafin husna ta shiga maxaunin driver raudah tana gefen ta sai fadila a baya don ilham hajia maamaa ta dakatar da ita da xuwa skul sai bayan bikin.

Da gudu husna take driven saboda time ya kure da hka har suka K'arasa skul ta samu waje tayi parking sannan suka fito kai tsaye department d'in su suka nufa, cikin nutsuwa suka shiga cikin hall di'n d'aukar lecture di'n sai dai wani uxirin ya tsayar da husna wajen wasu friends d'in ta amman ba department d'in su d'aya ba sai su raudah suka riga ta gaba kusan lokaci d'aya suka shiga cikin hall di'n tare da malamin nan ba tare da 6ata lokaci ba ya fara yi musu lecturing akan darasin da yake koyar wa gaba d'aya d'alibai sun nutsu suna sauraren shi saboda tsabar kwarjinin shi da tsoran shi da suke ji.

  Husna ta d'auki tsayin 15 mint tana hira da friends d'in nan nata Kafin ta nufi hall di'n nasu cikin tafiyar ta ta kasaita.

Yana cikin xuba musu lecturing da tsaftaccecen turancin shi ajin yayi tsit suna sauraren shi kwas kwas k'arar takalmin husna da yaji yasa shi jiyo wa da sauri don ganin wane, ko kallon Inda yake husna bata yi ba ta samu waje xata xauna kenan taji saukan amon muryar shi yana cewa

"hey ke wace da xan kafa doka ki taka min? "
Cikin wani salo husna ta jiyo tare da d'aga kanta ta kalle shi ta xuba mishi mayatattun idanun ta masu matuk'ar d'aukan hankalin duk wani d'a namiji mai lafiya, dummm lokaci d'aya yaji xuciyar shi ta buga da karfin gaske tare da shiga wani yanayi a cikin jikin shi yana tasbihi acikin xuciyar shi don ganin wannan kyau na husna da Allah ya bata, muryar tace ta katse shi tare da dawo wa cikin hayyacin shi yaji tana fad'in

"I'm so sorry sir baxan k'ara ba kayi min uxiri "

D'an dai dai ta nutsuwar yayi don muryar ta ba k'aramin kasala ta sa mishi ba dakyar ya iya cewa

"get out please don't west my time"

Kallon dan rainin wayo husna tayi mishi kafin a fusace ta fice daga hall di'n gaba d'aya sai kuma jikin shi yayi sanyi ganin yanda ta fita a fusace don gaskia babe d'in tayi mishi ta ko'ina hmmm meke faruwa da ni ne Cewar lecture safwan Ahmad, Hka ya gama musu lecturing di'n duk jikin shi a sanyaye amman bai bari d'aliban sun fahimce shi ba da yake namijin gaske ne da haka har ya gama musu ya fito yana addu'ar Allah yasa ya ganta sai dai ko mai kama da ita bai gani ba mtswww yaja tsaki tare da dan dafe kanshi yana cewa me yasa ma ya kore ta, da hka har ya K'arasa cikin office d'in shi xuciyar shi cike da tunanin husna..............







Aishat A muh'd

           *&*

Sumayya salees sadeeq
[25/07, 09:31] Aishat A. Muhd: 🍃 *DANGARTAKAR ZUCI*🍃







*written by*

Aishat A muh'd

          *&*

Sumayya salees sadeeq





*Page 33-34*








       ita kuwa husna  tana fita a fusace kai tsaye cikin motar ta ta shige ta rufe sannan ta kwantar da kujerar ta kishingid'a tare lumshe idon ta ranta ba k'aramin 6aci yayi ba akan abin da d'an rainin wayon malamin nan yayi mata, wani wawan tsaki ta sake ja a karo na biyu Sannan ta d'auko wayar ta tare da kunna data nan message suka fara shigo wa ta what's app tuni ta tsunduma a duniyar charting.



Sai da su raudah da Fadila suka shiga fito tare da bud'e motar suka shiga ciki sannan husna ta ankare dasu nan fah suka bud'e shafin hirar wannan malamin wato safwan Ahmad tsaki husna ta ja tare da fad'in

"ku har d'an air Indai nice xan koya mishi hankali ne "

Raudah wadda duk tafi so tsoro idan ka d'auke ilham tace "kin ga husna ki kyale shi ki fita harkar shi kada ya baki matsala fah Kinsan halin lectures d'in nan "


Mtswww husna taja tsaki tare da cewa "banxa matsoraciya kawai wlh kin fiye tsoro raudah "

"Ehhh naji di'n " Cewar raudah tana Murgud'a baki kwashe da dariya suka yi husna da fadila har ita ma raudah ta d'an dara, Kafin husna tayi wa mota key suka nufi hanyar fita daga skul d'in.


Tana kok'arin fita daga get d'in skul kenan shi kuwa safwan Ahmad na kok'arin shigo wa had'a idon da suka yi da husna yasa ta fasa kok'arin kauce wa sai ma ta janyo wani black glass ta d'ora a idanun ta yayin da shima safwan Ahmad shima yaja mota ya tsaya yak'i kaucewa, don kowanne yana ji da miskilan ci da kasaita.


  Sosai husna ta bawa safwan Ahmad mamaki don bai yi tsammani yarinyar hka ba sai kawai ya xuba mata ido yana kallon ta cikin mamaki yana matsayin malamin ta yaci ace ta bashi girman shi.


Cikin matuk'ar tsoro raudah tace "na rok'e ki husna ki janye motar ki a bashi hanya wlh wannan safwan Ahmad d'in bai da kirki "

Cikin halin ko inkula husna tace "wlh baxan janye ba sai dai shi ya janye kuma yayi min uban da ya ga dama"

"Haba husna yaci darajar malamin ki mana ki bashi hanya ya wuce kin ga mutane a bayan mu " Cewar Fadila


"Mtsww kan ku ake ji enmata"

Tana gama fad'in hka ta sanya headphone a kunnen ta tana jin wak'ar Jojo cikin wak'ar ta ta baby it's you tana wani kid'a kai raudah da fadila duk suka bita da kallo duk a tsorace suke suna mamakin k'arfin halin husna.


Sun d'auki tsawon mintuna 20 a hka mutane sai uban horn suke musu amman ba wanda yayi wani yunkuri ,ana cikin hka wayar safwan tayi ringing da sauri ya d'auka ganin sunan umman shine bayan ya d'auka take sanar dashi yayi sauri yaje ya d'auko mahaifin shi Alhj Ahmad a filin airport nan ya amsa mata tare da katse wayar cikin hanxari ya juya motar tare da d'aukan hanyar da xata kai shi airport xuciyar shi cike da tunanin husna yana son sanin ita wace.


Ganin haka yasa husna jan motar suka fice daga skul d'in sannan mutane suka samu hanyar tafia, dariya husna ta kyalkyale da ita har da buga steering tare da fad'in

"Yeeeee yaji tsoro ya juya daman ae irin nasu cika bakin nan duk yawan cin su matsorata ne "

Fadila da raudah suka taya ta dariyar tare da tafawa suka ce "wlh husna ke er air ce kada kisa d'alibai su daina ganin girman shi "

Kafad'a ta d'aga alamar ko ajikin ta da hka suka K'arasa gida husna tayi part d'in su yayi da raudah da fadila suka wuce part d'in hajia maamaa.


Hka rayuwa ta cigaba da tafiya tun daga ranar nan husna bata k'ara sa safwan Ahmad a cikin idanun ta ba, suna ta shirye shiryen bikin Yah Abdullah da Ilham a fili tana nuna tana farinciki da Wannan auren amman idan ta ke6e waje d'aya sai kuka sosai abin gwanin ban tausayi gaskia husna ba k'aramin son Yah Abdullah take ba duk da xuciyar ta ta sawa hakurin rabu wa dashi xata d'auke shi yanda kowacce kanwa take son yayan ta.


Yah Abdullah kuwa ya kasa xuwa kaduna duk kuwa da neman shi da ake ya dad'e rabon shi da xuwa, k'in xuwan nashi ba k'aramin damun husna yayi, haka a 6angaren ilham itama ta damu sosai da rashin xuwan Yah Abdullah duk ta damu sosai ta d'an rame saboda tsabar tunanin shi....................








Aishat A muh'd

          *&*

Sumayya salees sadeeq
[25/07, 09:31] Aishat A. Muhd: 🍃 *DANGARTAKAR ZUCI*🍃


*written by*

Aishat A muh'd
  
           *&*

Sumayya salees sadeeq



*Page 35-36*




      Tafiya take cikin takun ta na kasaita tasha wata irin gown green colour tayi rolling d'in kanta da black d'in veil sai ta sanya flat shoes bak'i sai er purse a hannun ta da waya tasha bak'in glass tayi kyau sosae husna Omar kenan, tana tsaye a gefen titi kallo d'aya xaka yi mata kasan ranta a matuk'ar 6ace yake, saboda motar da ta fito da itace ta lalace mata gashi yamma tayi gaf ake da a kira sallahr mangarib daga gidan aunty rufaida ta dawo mamee ta aike ta daman bason xuwan take ba gashi kuma mota ta bata matsala.


Mtswww taja wani uban tsaki kamar harshen ta xai tsinke tana duba agogon hannun ta ganin 6:35 tayi cikin 6acin rai tace

"wlh da nasan motar Yah yaseer hka take da ban d'auka ba" mtswww ta sake jan tsaki a karo na biyu tana kok'arin kiran number d'in mamee ta turo driver ya d'auke ta sai ga wata hadaddiyar mota nan k'irar Range Rover kalar dark ash da gani sabuwa ce sai shek'i da d'aukan ido take da gudu motar taxo ta shige husna .


"wad'annan sune masu jawo wa ana accident ji wani irin gudu kamar xai tashi sama " Cewar husna kenan tana bin motar da harara kamar itace ta yi mata laifin.

A hankali mai tuk'in motar yayi rebos tare da dawowa baya ya samu kusa da motar husna yayi parking sannan ya fito ya nufi inda husna ta tsaya jikin motar, ko d'aga kanta bata yi jin anyi parking kusa da ita ta cigaba da try d'in number d'in mamee don tak'i shiga.


Ja yayi  ya tsaya yana kare mata kallo tare da girgixa kai lallai wannan yarinyar er jin kai ce ganin tak'i d'ago wa yasa shi bud'e baki cikin muryar shi mai dad'in gaske yace

"Assalamu Alaiki "

Da sauri ta d'ago kanta don kamar ta gane mai muryar ae kuwa suka yi ido hud'u da safwan Ahmad yana sanye cikin wani yadi ash colour anyi mishi aiki da bak'in xare haka takalmin shi bak'i ne sai dai kan shi ba hula sumar kanshi ta sha gyara irin ta matasan xamani masu ji da gayu, saukar da idon ta tayi daga barin kallon shi.

Cikin murmishi yace "wa na kama "

dummm gaban husna ya fad'i lokaci guda ga wani tsoro da ya lullu6e ta lokaci d'aya ta shiga uku yanxu ya xata yi ga hanyar ba mutane sosae yanda xata yi ihu a ji ta don a kawo mata a gaji don tasan ramuwa yaxo yi akan abin da tayi mishi tasan ba kyale ta xai yi ba don ba kirki ne dashi tuni gumi ya fara yanko mata har jikin ta ya fara rawa.

Murmishi ya sake yi a karo na biyu a cikin xuciyar shi yace ashe duk cika bakin banxa ne shegen tsoro ne da ita, ganin yana murmishi ta dauka murmishin mugunta ne haba tuni husna ta sake tsinke wa, cikin muryar shi mai dad'in sauraro yace

"Haba husna bai kamata ki ji tsoro ba na d'auka ke jaruma ce "

Cikin tsananin mamaki ta d'ago kai tana kallon shi don jin ya kirawo sunan ta d'aga mata gira yayi yana cewa

"Kina mamakin yanda nasan sunan ki koh abin da kika yi min ranannan ne ya d'aure min kai har ya kai da na binciki ko ke wace, kuma nayi mamakin yanda aka ce wannan ba halin ki bane asali ma kin samu tarbiyya mai kyau daga iyayen ki "

Shiru husna tayi kawai bata ce komai ba ganin tana duban agogo yasa ya gane abin da take nufi sai yace

"me ya samu motar taki?"

Ganin sauri take gashi mangarib ta kusa yasa tace

"nima ban sani ba just ina cikin tafiya ne naji ta tsaya "

Cikin sigar tsokana yace "Ko ba mai ne? "
Batasan lokacin da ta d'ago kanta ta d'an harare shi ba don maganar ta bata haushi, er dariya ya saki mai birgewa tare da kama kunnen shi duk biyun cikin shagwa6a yace

"sorry "

Kallon shi tayi cikin mamaki kamar ba safwan Ahmad ba, wajen motar ya shige ya d'an dudduba ta amman tak'i tashi dawowa yayi Inda take ya fito da wayar shi magana yayi na tsayin mintuna uku tukunna ya kashe wayar ya d'ago kanshi ya Kalli husna yace

"ranki ya dad'e nayi en dabaruna tak'i tashi amman na kirawo mai gyara wa don hka kixo na kai ki gida idan ya gyara xan kawo miki har gida "

Shiru tayi bata ce komae ba ganin hka yasa yace "Ko kina tunanin xan sace miki "

Hararar shi tayi ta gefen ido sannan ta mik'a mishi key di'n motar yasa hannu ya kar6a ana cikin hka sai ga mai gyaran nan ya bashi key di'n motar sannan ya bud'e wa husna gaban motar ta shiga a d'an tsorace sannan ya rufe ya xagayo shima ya shiga a nutse ya ya yiwa motar key suka fara tafiya ba me magana a cikin su sai wak'ar Justin Bieber da take tashi ta love me kowannen su xuciyar shi cike da tunani musamman husna.

Mamakin ta ne ya k'aru ganin ko ya tambaye ta Inda gidan su yake ita kuma miskilan ci ya hana ta bud'e baki tayi mishi magana, gashi kuma sai bin hanyar da xata kaisu gidan su yake.

Lallai ma mutumin nan ba k'aramin bincike yayi a kanta ba ganin yana horn a kofar get d'in gidan da sauri me gadi ya bud'e kofar ganin husna a cikin motar sai da ya samu waje yayi parking yana tsayar da motar husna ta yunkura ta bud'e motar sai da ta fito tukunna tace mishi

"Na gode sai anjima "

Tana gama fad'in hka ta yi gaba abin ta kallon ta kawai yake yana murmishi sosai yarinyar take birge shi tun ganin ta na farko da yayi, murmishin shi ya k'aru ganin ta mance wayar ta garin sauri d'aukan wayar yayi tare da yi mata kissing  bayan ya shak'i k'amshin daddad'an turaren husna har sai da ya lumshe idon shi don dad'in k'amshin,a hankali ya furta cewa "ina son ki husna! I really luv u tun lokacin da na fara sanya ki a idanu na"
Kafin tukunna ya ja motar shi ya nufi gida.


*WANE NE SAFWAN AHMAD*

Safwan Ahmad d'a ne ga Alhj Ahmad mai gwanjo da hajia karimatu suna da yara guda 3 safwan shine babba sai habib da ruqayya su kad'ai ne yaran da Allah ya basu.
Alhj Ahmad mai gwanjo asalin sunan mai gwanjo Inda ya samu sana'ar ta ya fara yi Kafin Allah ya axurta shi da samun arxiki ya bunkasa sana'ar tashi d'an kasuwa ne sosai yana fita su dubai, china da sauran kasashen wajen kasuwan cin shi ba k'aramin nasara yake samu ba akan harkar kasuwanci nashi yana da arxiki sosai, d'an asalin garin kaduna nane haifaffen can. Iyayen shi managarta ne akwai so da taimako sun bawa yaran su tarbiyya mai kyau tare da ilimin addini dana boko.

Safwan Ahmad mai gwanjo yaro ne matashi wanda shekarun shi baxa su gaxa 35 kyakkyawan saurayi ne sosai fari tas dashi gashi dogo ne yana da K'ira mai kyau yana da hancin sai dai idanun shi basu cika girma ba ga sajen nan nashi da matasa yanxu suke Bari  ta ko'ina dai safwan ya had'u sosai enmata suke rububi akan shi.

Yayi ilimin shi na addini dai dai gwargwado na boko kuwa kusan a k'asar England yayi su, lokacin da yake university tashen samartaka yana kan shi an d'an ta6a neman mata da d'an shan giya amman daga lokacin da ya dawo nigeria duk ya watsar da wannan dabi'ar ya nutsu daman can da xubar abokai toh yanxu ya rabu dashi Allah ya shirye shi har haushin kanshi yake ji Idan ya tuna da rayuwar da yayi a baya, bayan ya dawo ya samu aiki a university a matsayin lecture.


_Mun dawo labari_


  Da sallama ya shiga parlourn gidan nasu xuciyar shi cike da tsantsar farin ciki hajia karimatu ta amsa mishi sallamar tashi da fara'a akan fuskar ta tace
"sai yanxu ka dawo my son ina ka mak'ale ko wajen surukar tawa ka tsaya don wannan gayun da magana"

Dariya yayi tare da cewa "Kaiii umma ni ba inda naje daga gidan hajia kaka nake "
Cikin murmishi tace "Okay yayi kyau hkan ya ka baro ta? "
"tana nan lafia "

Idanun ta ne suka sauka kan wayar hannun shi ta husna tace "yaushe ka siyi waya kuma don bansan ka da irin ta ba? "
D'an sosa k'eya yayi tare da cewa "uhm uhm umma ta... "

"ban san ka da k'arya ba fah safwan"cewar umma
"umma ta husna ce ta mance ta a mota ta "
Wani dad'i ne ya ishe umma ganin d'an nata yau yayi magana akan mace "Wace husna kuma? "umma ta tambaye shi
"wata d'aliba tace na rage mata xuwa gida motar tace ta lalace mata a hanya "
"ka kyauta kuwa amman Naga alama d'an nawa kamar....."
Sai tayi shiru tana dariya shima dariyar yake yana cewa "Allah umma ba wani abun "
"idan tayi tsami ma ji "
Daga hka hirar tasu ta yanke ya fita xuwa masallaci umma kuwa ta shige d'akin ta.........




Aishat A muh'd

         *&*

Sumayya salees sadeeq
[25/07, 09:31] Aishat A. Muhd: 🍃 *DANGARTAKAR ZUCI*🍃



*written by*
Aishat A muh'd

          *&*

Sumayya salees sadeeq




 _Godiya ga dukkanin makarantar DANGARTAKAR ZUCI mun gode da yanda kuke son littafin da yanda kuke bibiyar shi Allah ya bamu ikon kammala muku shi lafia_😍




*Page 37-38*



     Husna tana shiga gida ta tuna ta bar wayar ta a motar safwan da sauri ta jiyo don ganin ko bai riga ya fita ba har tana d'an had'a da d'an gudu sai dai kash tana xuwa mai gadi yana rufe get alamar fitar shi kenan, haushi ya rufe husna don me yasa baxai bawa baba mai gadi ya kawo mata ba sai tafar mata da waya Mtsww taja tsaki cike da jin haushin safwan don tana son amfani da wayar ta ta, ganin tsayuwar baxa ta amfane ta ba yasa ta juya xuwa part d'in su,gashi abin takaicin nata bai wuce ta cire security d'in jikin wayar ta ta, tasan bincike xai mata a wayar Amman mutumin nan ya rai na min hankali.

 
 Kwance yake saman bed tunanin husna yake yi shi kanshi yana mamakin yanda son yarinyar ya shiga xuciyar shi farat d'aya wayar ta ya d'auka nan ya shiga sarrafa ta da yake ba security a wayar cikin memory card nata ya shiga ya fara kallon picture's d'in ta anan ya sake tabbatar wa da kanshi Indan ya samu husna matsayin matar shi ya gama more wa.

Contact di'n ta ya d'auka yayi serving a phone d'in shi sannan ya cigaba da kallon pictures d'in husna xuciyar shi tana k'ara k'aunar ta, safwan kenan jarumin namiji mai ji da kyau da nera gashi yau ya fad'a son husna, daman Hka enmatan da suke son shi suke daman hka so yake, yake tambayar kanshi bayan ya gama kallon photo nan husna, daman shi bai ta6a yin soyayya ba wannan karon shine na farko a cikin rayuwar shi.


_Abuja_

  Yah Abdullah na hango xaune acikin garden di'n gidan shi kallo d'aya nayi mishi na firgita ganin yanda ya rame yayi bak'i kamar ba Yah Abdullah dana sani ba duk ya tara wani uban kasumba saboda tsananin tarin damuwa da tunani da yake ciki.

Anya hajia maamaa tana son shi kuwa taya xata raba shi da abar son shi akan wani banxan shirme wai xata juya shi to idan ta juya shi di'n ina ruwan ta, lokacin da suka ci nasu xamanin waya samu su ido, ni mai xanyi da ilham kawai an tashi an had'a ni da yarinyar da bana so (ni kuwa nace Hmmm Yah Abdullah kada ka cika baki kaxo kana jin kunyar mu lol).

 K'arar wayar shi ce ta katse mishi tunanin shi da sauri ya d'auka ganin sunan abban shi ne da sallama ya fara Kafin ya gaida shi sai da suka gama gaisa sannan abba yace

"Abdullah ka kyauta yanxu yaushe rabon ka da xuwa nan gidan? "
"Abba kayi hak'uri aiki ne ya rik'e ni Inan xuwa wannan week end d'in "Cewar Yah Abdullah kenan.
Murmishin su na manya Abba yayi Kafin yace " ni dai kiran ka nayi don na tunasar da kai ranar sunday misalin karfe 11 na safe xa'a d'aura auren ka da ilham kuma ka tabbatar kaxo idan ba hka ba wlh ni da kai ne "
Abba ya K'arasa maganar a fusace, dummm gaban Yah Abdullah ya fad'i jin abin da abba yace mishi ya ma kasa magana sai da abba ya kuma cewa
"kana jina kuwa Abdullah "
Murya na rawa Yah Abdullah yace "ina jin ka Abba kuma Insha Allah xan xo "
Yana gama fad'in hka Abba ya kashe wayar tashi cike da jin tausayin d'an nashi.

Shi kuwa Yah Abdullah sakin wayar yayi ta fad'i k'asa lokaci d'aya wasu hawaye masu xafi suka fara xubo mishi daga idanun shi abin tausayi shi kenan ya rabu da husna har abada duk mafarkan shi da tunanin shi burin shi ya tashi a banxa tun da ba husna a rayuwar shi da ita ya tsara rayuwar shi sai gashi hajia maamaa tayi musu katsalanda wayyo Allah shi ina xai kai son husna a cikin xuciyar shi. (ganin yana kok'arin sani hawaye yasa ni tattara wa na bar mishi gidan amman hak'ik'a Yah Abdullah ya ban tausayi) .



_Malaysia_


  Wani kyakkyawan matashi na hango cikin kayan training yana d'an gudu da yake sassafiya ce a garin iska mai dad'i tana kad'a shi headphone ne a kunnen shi yana sauraran karatun alqur'an cikin suratul baqara K'ira'ar shuraem don dad'in karatun har wani lumshe ido yake,                             *DR IBRAHEEM MUKTAR IBRAHEEM* kenan.

Sai da ya kwashi mintuna 40 yana gudun tukunna ya dawo xuwa cikin gidan da hukumar asibitin da yake aiki suka bashi, toilet ya fad'a yayi wanka sannan ya fito ya shirya cikin wani black jeans nd T-shirt green mai k'aramin hannu yayi matuk'ar yin kyau don ibraheem ba daga baya ba wajen kyau da iya tsara kwalliya don har yafi Yah Abdullah kyau sosae.

Yana gama shirya wa ya fito xuwa falo dinning table ya nufa ya tarar kukun shi ya kammala had'a mishi breakfast bayan ya gama tsatstsakura ya tashi ya dawo cikin parlourn ya xauna tare da lumshe idon shi yana tunanin gaskia ya kamata ya koma gida gaba d'aya hankalin shi yayi gida tun da yaxo karatu bai koma nigeria ba ko hutu baya xuwa abba ya hana shi saboda yana jin tsoron kada ya dawo ya mak'ale yak'i koma wa gashi har ya gama karatun saboda kwaxon shi yasa suka d'auke shi aiki na tsawon shekara 2 gashi yana dab da cika shekarun nashi.


Yana buk'atar koma wa gida don ya tona asirin xuciyar shi ya bayyana abin  da yake rufe cikin xuciyar shi wanda ya kwashi tsawon shekaru yana fama dashi abin ya shafi *DANGARTAKAR ZUCIyar* ne sai hajia maamaa kawai suka san mene.

Yana cikin tunanin ne aka kirawo shi a waya ana neman shi a hospital da gaggawa don hka dole ya katse tunanin ya shirya ya tafi asibitin............



Aishat A muh'd

          *&*

Sumayya salees sadeeq
[25/07, 09:32] Aishat A. Muhd: 🍃 *DANGARTAKAR ZUCI*🍃


*written by*
Aishat A muh'd

         *&*
Sumayya salees sadeeq



*Page 39-40*



     Xaune suke a  kan wasu kujeru cikin skul bayan sun fito a lecture husna, fadila da raudah kenan en gida d'aya, suna tattauna wa akan shirye shiryen da xasu yi a bikin, suna cikin hka ne suka ji k'amshin wani sansanyan turare ya bugi hancin su sai kuma suka ji anyi musu sallama  cikin murya mai dad'i gaba d'aya suka d'ago kan su a lokaci guda don ganin wane wannan, fadila da raudah xaro ido suka yi gaban su kuma ya fad'i don ganin safwan Ahmad ne yayin da a 6angaren husna tana mishi kallo ta kauda kanta gefe don har yanxu tana jin haushin abin da yayi mata duk da kuwa taimakon da yayi mata jiya.

Cikin rawar murya Fadila da raudah suka gaida shi cikin murmishi ya amsa musu tare da cewa "ya karatu? "
Cikin mamaki suka amsa da "Alhmdullilah"
Suna masu mamakin yanda har yaxo yana kula su bai damu da kallon da d'alibai suke mishi ko ma a jikin shi idanun shi sun rufe husna kawai yake buk'atar gani.

Cikin wani Murmishi da yake k'ara mishi kyau yace "husna ba gaisuwa ne ko har yanxu ba'a huce ba ne? "
Fadila da raudah suka fara kallon kallon juna mamaki ya dad'a kama su, a hankali ta d'ago kanta tare da watsa mishi kyawawan idanun ta akanshi ae kuwa wannan kallon da tayi mishi ba k'aramin k'ara gigita safwan yayi ba yaje ya k'ara kamu wa da sonta, kamar mai ciwon baki ta fara cewa
"bani waya ta "
Ta fad'i tana mik'a mishi hannun ta, gaba d'aya su Fadila da raudah a tsorace suke da yanda husna tayi mishi amman ga mamakin su sai suka ga ya saki wani murmishin tare da cewa
"ohhh na manta da ita tana gida kiyi hak'uri xan kawo miki anjima "

Wani kallon ta watsa mishi tare da sauke hannun ta sannan ta mik'e tana cewa su fadila" ku tashi mu tafi kunsan muna da abin yi koh? "

Tana gama fad'in hka tayi gaba su ma su raudah xasu tafi suna cewa "malam sai anjima "
Suka yi gaba gid'a kai yayi yana murmishi ya gyara tsayuwar shi tare da hard'e hannuwan shi a kirjin shi yana bin husna da kallo sam ranshi bai 6aci da abin da husna tayi mishi ba kuma yana fatan xai shawo kanta ta kar6i soyayyar shi Insha Allah, yana gama wannan tunanin ya nufi inda motar shi take kai tsaye gida ya wuce.

   A cikin mota kuwa Fadila ce ta fara magana tace "husna yaushe kuka shirya ke da safwan Ahmad ne?
Cikin murmishi ta basu labarin abin da ya faru tsakanin su jiya da yamma, cikin dariya raudah tace
"ah su malam safwan Ahmad an fad'a tarkon so ae kuwa na taya ki murna samun namiji kamar safwan a wannan xamanin sai an tona ga kyau, kud'i, wayewa da ilimi ae kawai ki ba da kai bori ya hau "
"ae idan baki sani ba raudah nima fah yana burgeni kawai Kinsan jan ajin nan na mata xan yi mishi "
Gaba d'aya suka tuntsire da dariya tare da tafawa fadila na cewa "husna baki da dama wlh naji yace xai xo anjima ma"
"ehhh hka naji yace "
Cewar husna yayin da raudah tace "aja ajin da kulawa kada a hargitsa mana malam yaxo aji yana kiran husna maimakon koyarwar da xai mana"

Dariya suka sake tuntsire wa da ita sannan husna tace "Haba dai sai kace wani mara kai "
"Hmmm ke dai ki bar irin wad'annan mutanen idan suka fad'a soyayya idanun su rufe wa suke kamar irin su Yah ibraheem d'ina "Cewar Fadila

Tuni fuskar husna ta rikid'a xuwa tsantsar 6acin rai don an ambato mata mak'iyin ta don hka Bata k'ara cewa komai ba, raudah ce ta xunguri Fadila tare da yi mata alamar  tayi shiru sai alokacin Fadila tasan tayi kata6ora don husna tasha fad'a musu kada su k'ara ambatar sunan Yah ibraheem Indai suna tare Idan sun san hirar shi xasu yi to su bari ta bar wajen, ba wanda ya k'ara magana har husna tayi parking suka fito daga motar har tayi gaba ta jiyo tana cewa "ku fad'a wa ilham anjima mu had'u a part d'in mu sai mu k'arasa shirye shiryen namu "
Fuskar ta ba fara'a take maganar don an ta6o mata wani abu da ya shige a cikin rayuwar ta, nan suka amsa da toh sannan kowanne ya shige part d'in su ita kuwa fadila part d'in hajia maamaa ta wuce .


_5:00 na yammacin ranar alhamis_

Husna ce kwance kan kujera ta d'ora kanta a cinyar mamee driver yayi sallama a bakin kofar palon mai aikin mamee ta amsa sallamar tare da k'arasa wa ta bud'e kofar nan yake sanar mata wani na kiran husna a waje,  nan ta dawo cikin falon tana fad'i wa husna sak'on yatsina fuska tayi tare da cewa "Kice bana nan kawai "
Har ta juya xata tafi ta fad'a wa driven da aka aiko taji mamee na cewa "larai ki ce tana xuwa a kice malam idi drive ya kai shi wajen da dadyn ta yake xama yana huta wa "
"toh hajia "
Cewar larai sannan taje ta fad'a wa driven, ita kuma mamee ta umarce ta da takai mishi abin motsa baki, sannan ta jiyo da kallon ta kan husna tace
"tashi maxa ki shirya ki je bana son wulakanta mutane "
"amman mamee Kinsan dai............. "
Kafin ta K'arasa fad'i mamee tace "ni dai nace ki je "
Hka husna ta mik'e tsaye ta nufi bedroom d'in ta wani hijab ash ta sanya mai hannu ta d'an fesa turare sannan ta fito ta xuwa wajen farfajiyar gidan kai tsaye inda wurin hutawar daddy yake ta nufa wuri ne mai kyau wanda aka k'awata shi da abubuwa masu Kyan gani a ido da yake ya juya baya bata ga fuskar shi sai da taje daf dashi tayi mishi sallama da sauri ya d'ago kai tare da amsa sallamar had'a ido suka yi sunyi kusan second talatin suna kallon junan Kafin husna ta fara janye idonta ta ja kujera ta xauna tare da cewa
"ina yini? "
Cikin murmishi yace "lafia qlau ,oh sai yanxu aka ga ra'ayin gaida ni"
Kauda kanta tayi bata ce komai ba nan ya mik'a mata wayar ta da key di'n motar ta sannan a cikin wannan lokacin safwan Ahmad ya samu damar amayar wa da husna abin da yake cikin xuciyar shi tare da rok'an ta kan ta soshi ko da rabin son da yake mata ne nan duk yabi ya rikita husna da xafafan maganganu har ta kai ta amince da shi a lokacin ta gane wane safwan Ahmad kuma taji xuciyar ta ta amince dashi duk da kuwa har yanxu son Yah Abdullah yana nan mak'ale cikin xuciyar ta nan dai basu rabu ba sai da ya yarda husna ta amince mishi kuma a hankali xai koyar da ita son shi da hka suka rabu cikin kaunar junan su.

Tana shiga part d'in su mamee ta kalle ta sannan tace "ke da bakya son fitar dad'e war me kika yi "
Kunya ce ta lullu6e husna ta ajiye key da wayar kan table ta gudu d'aki yayin da mamee tayi dariya kawai tana gode wa Allah da ya kawo wa erta chanji acikin rayuwar ta. Nan fah soyayya aka bud'e shafin ta tsakanin husna da safwan soyayya yake nuna mata ko acikin aji ne yana d'aukan darasi sai dai ka ga suna jifan juna da murmishi yana kashe mata ido tare da d'aga mata gira gaba d'aya bata iya sake wa wani lokacin sai ya matso kusa da Inda take xaune kamar xai shige sai ya d'an rankwafa saitin kunnen ta ya furta mata kalmar "i luv u baby nah kinyi matuk'ar yin kyau " da dai ire iren kalmomin soyayya ita kuma sai ta lumshe idon ta tana murmishi alamar taji dad'in abin da yace mata, su Fadila da raudah kuwa duk akan idon su hkan yake faruwa ba k'aramin burge su suke ba sai an fito suyi tayi musu tsiya sai dai su kalli juna suna dariya.

Gaba d'aya su husna yanxu ba xama sai shirye shiryen biki suke saboda an shiga satin bikin duk da ba wani programs da yawa xasu yi ba daga kamu, walimah sai dinner hka kawai suka shirya don xuciyar husna sam ba dad'i don ma safwan yana d'ebe mata kewa, ranar alhamis suka gabatar da kamu babu ango Yah Abdullah ba kamar shi kowa bai ji dad'in rashin xuwan Yah Abdullah ba, hka Washe gari Friday suka gabatar da walimah a farfajiyar gidan kuma ranar ma yah Abdullah bai xo ba, ran iyayen nashi Yayi matuk'ar 6aci musamman mai gayya mai aiki hajia maamaa.


_washe gari misalin karfe 11:00_

Aka d'aura auren Yah Abdullah da Ilham, husna tana jin sanarwar an d'aura auren ta kulle kanta a d'aki tana kukan rabuwa da Yah Abdullah har abada ta rasa shi kenan sai da taci kukanta ta more sannan ta fito kallo d'aya mamee tayi mata ta fuskanci abin dake damun erta ta girgixa kai tayi cike da tausayin husna.

Bayan d'aurin auren da mintuna 20 Yah Abdullah ya shigo garin kaduna yana sanye cikin shadda fara sol da ita yayi kyau sosae duk da uwar ramar da yayi kuwa, nan fah iyayen shi da hajia maamaa suka dunga yi mishi fad'a sosai kallo d'aya xaka mishi kasan baya cikin nutsuwar shi yana d'auke da tarin damuwa a kan fuskar shi don idanun shi sunyi jawur dasu kamar ba ango ba, yana son sa husna a idon shi amman ya rasa inda xai same ta saboda gaba d'aya gidan a cike yake da mutane, lokacin da xa'a tafi dinner kuwa dakyar ya shirya xai je sai da abban shi yayi mishi tatas sannan ya amince ba don yaso ba Allah sarki Yah Abdullah so masifa ne wani lokacin.

Wajen dinner d'in ya had'u sosai ango da amarya suna xaune sun yi matuk'ar yin kyau duk da kuwa kowannen su tarin damuwa akan fuskar shi, kamar ance ya d'ago kanshi idanun shi suka gano mishi abin da yayi matuk'ar girgixa shi ya kuma kid'ima shi ba nan take yaji wani kishi ya rufe shi ba komai ya gani sai husna tare da safwan akan table d'in daban su Biyu suna xaune daga ni hirar soyayya suke yanda suke jefan junan da wani irin kallo soyayya tuni kan Yah Abdullah
 ya fara juya wa.................



Aishat A muh'd

          *&*

Sumayya salees sadeeq
[25/07, 09:36] Aishat A. Muhd: 🍃DANGANTAKAR ZUCI 🍃


Written by
Sumayya salees sadeeq
          &

Aishat A Muh'd



Page 41&42




A hankali ya fara furta innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, wannan waye suke tare da Husna, wato shi yana chan dauke da soyayyarta a xuci amma ita har ta samu wanda take so, daga ganin yarda suke xuba soyayya yasan a kwai shakuwa a ciki, gaba d'aya hankalinsa ya tashi, xaman gurin ya gundiresa, A hankali Ilham ta fuskanci rashin nutsuwarsa, cikin nutsuwa ta d'ago ido ta kalle shi, gani tayi b'acin rai a fuskarsa idonsa yyi ja, duk da dama da jan idonsa yaxo kasancewar kukan daya sha bbu dare bbu rana.
    Baisan tana kallonsa ba, dan ya bada nutsuwarsa ga duk wani movement na Husna da Safwan.
    Zuciyar Ilham gaba d'aya bbu dad'i, ganin tsantsar kiyayyar da Yah Abdullah ke nuna mata, a hankali ta juya idonta inda taga yana kallo, ganin Husna tayi da Safwan suna kashe selfie cikin annushuwa da jin dad'i, da gani basu da wata matsala, bbu kuma abinda suka sa a gaba sai soyayya.
     Kwalla ce ta cika mata ido, ita dai ta shiga uku, wane irin aure xatayi? Duk da tana son Yah Abdullah amma hajia maamaa bata kyauta mata, tasan xata rayu cikin kunci, data sani tabarshi ya auri wacce yake so.



     Kasa jurar ganin Husna da Safwan yayi, cikin sauri ya dauke kansa yana juyowa suka had'a ido da Ilham, ganin idonta da Kwalla ya gane taga abinda yake kallo, tausayinta ne ya kamashi. Ilham bata da matsala, komai nata ya masa, kawai shi baya sonta ne Husna yake so, amma Ilham ko ba kanwarsa bace yanxu akwai aurenta ne a kansa,dole ya bata kulawa.

    Basar wa yayi ya tambaye ta" mai yasa kike kuka? "

     Murmushi tayi" ba kuka nake ba Yah Abdullah abune ya fad'a mini a ido"

    Shiru yayi yana naxari, cikin sanyinta tasa gefen net d'in ta ta goge hawayen.

   Duk abinda ke faruwa mom da mamee suna kallo, cux a waje d'aya suke kuma a kusa da ango da amarya, Ilham tafi basu tausayi, cux Mace xata iya auren wanda bata so taji dad'i, in har shi yana sonta,amma ace mijin ma bata tata yake ba ai akwai matsala.


   Taro yayi taro anci ansha, anyi raye raye da bisa tsari, gurin ya tsaru 11pm aka tashi a wajen.

   Safwan dakanshi yakai Husnarsa gida, ganin dare yayi yasa basu tsaya wani hira ba ya mata sallama sai da safe, dan gobe ne xa'a kai amarya gidan mijin ta dake Abuja.


     Fitar ta a mota ta fara yima Safwan bye bye, duk a idon Yah Abdullah , Cikin sauri Husna ta nufi part d'in su dan chanja kaya dan taji alamun period dinta yaxo, tana shiga corridor d'in da xai billa da ita dakinta taji an rike hannunta, xatayi ihu taji an tushe bakinta, sosai ta tsorata ta fara kiciniyar kwatar kanta. Jin kamshin turaren Yah Abdullah yasa hankalinta ya kwanta. Yah Ibrahim ka cikani please, cikata yayi ya xuba mata mayattatun idanunsa da suka rine, cikin sarkewar murya ya fara magana.

   "Husna ashe dama akwai ranar da Allah xai nuna mini kina tarayya da wani bayan ni, duk soyayyar da muke wa juna ina chan ina fama da sonki amma Husna ashe kina nan kin mallakawa wani xuciya ki? Husna ina sanki, wallahi baxan iya rayuwa ba idan bbu ke........" "dakata Yah Abdullah , kasan me kake cewa kuwa, aure ya riga ya haramta tsakanina dakai, Ilham itace matar ka, ita take bukatar kulawarka, ita take bukatar ka firta mata wadan nan dad'ad'an kalaman ba Husna ba, Yah Abdullah ban taba son wani d'a namiji ba sai kai, ban taba mallakawa kowa zuciyarta ta ba sai kai, akanka na fara so, naso ace munyi aure dakai, sai dai kaddara ta riga fata, "hannu tasa ta share hawayen ta," Safwan malami nane, kuma yana debe min kewar rashin ka," please Yah Abdullah , ka manta mun taba soyayya dakai, ka rungumi matarka ka bata kulawa please" fashewa tayi da kuka ta wuce ciki tabar Yah Abdullah a tsaye, gaba d'aya jikinsa ya mutu, sosai ya hango zallar kaunarsa a idon Husna, sai dai yasuyi, hajia maamaa ta gama cutarsu, ta tarwatsa farin cikin su.


    Husna na shiga daki ta baje akan bed dinta ta fara kuka mai cin rai, soyayyar Yah Abdullah ce take nukurkusarta, shi yasa tunda ya dawo taki yarda su hadu, sai da tayi kuka mai isarta sannan ta nufi toilet.
    Washe gari

  An kai amarya Ilham dakin mijin ta  bayan nasihohi da fad'a da itayenta sukayi mata, shima Yah Abdullah yasha nasiha akan ya rike Ilham bisa amana, ya manta duk abinda ya faru, hajia maamaa harda kukan farin ciki wai yau burinta ya cika,(ni da sister mukace kaji wannan tsohowar, suna kukan bakin ciki tana kukan murna) lol. Sosai nasihar ta ratsa Yah Abdullah  ya kuma dauri aniyar kula da Ilham.

    Husna da Safwan kam ana tare, dan har Abuja shi yakaita dasu rauda, sosai soyayyar da Safwan ke nuna wa Husna take basu mamaki, lallai Husna tayi sa'a, Allah yayi mata chanji na alkhairi, dan suna ganin indai ta auri Safwan to tagama mure jin dad'in dunia sai dai ta nemi lahira. Soyayya da shakuwa tayi malemale a xuciyar masoyan, har suna jin baxasu iya rayuwa ba batare da juna ba.





 Sumayya salees sadeeq
          &
Aishat A Muh'd
[25/07, 09:36] Aishat A. Muhd: 🍃 *DANGARTAKAR ZUCI*🍃



*written by*
Aishat A muh'd

         *&*

Sumayya salees sadeeq




*Page 43-44*



    Haka rayuwa ta cigaba da tafiya har akayi wajen wata uku da bikin Yah Abdullah da Ilham, yanxu husna ta cire Yah Abdullah gaba d'aya a cikin xuciyar ta soyayyar su kawai suke xuba wa da safwan din ta, a yanxu kusan kowa na gidan yasan da soyayyar safwan da husna kuma sun amince dashi sosai saboda mutum ne na gari ga hankali da nutsuwa, mamee taji dad'in ganin shi a matsayin wanda xai auri erta.

 Ana cikin hka safwan ya sanar da husna ta fad'a wa su dady xai turo iyayen su ayi magana, husna bata yi k'asa a gwiwa ba ta sanar da mamee maganar ita ma mamee ta fad'a wa daddy a lokacin da ta sanar dashi a lokacin yana kok'arin shiga part d'in hajia maamaa don hka bayan ya shiga part d'in ya tarar da yayun shi Abba 1 da Abba 2 bayan sun gaisa sai yake cewa

"maamaa daman yaron da yake son husna na ne yake son ya turo  iyayen shi "

Cikin rashin fahimta hajia maamaa tace "wane yaro kuma daman husna ta tsayar da wanda xata aura ne? "

"Ehhh tabbas mun sha gaisawa dashi yaron yana da kirki malamin su ne ma" Cewar Abba 1 wato abban su Yah Abdullah.

"Humm ae kuwa abin baxai yiwu ba saboda husna na riga da na xa6a mata wanda xata aura kuma kada wanda ya fad'a mata, su dai iyayen yaron xaku fad'a wa Idan lokaci yayi kowa xai sa ni " Cewar hajia maamaa

Abba 2 wato abban su ilham yace "Haba maamaa taya xa'a yi mata hka da farko suna soyayya da Abdullah kika k'i aura musu juna kuma tayi hak'uri da hkan Har ta dad'a xa6ar Wanda xata aura a karo na biyu don Allah ki barta ta auri wanda take so"

"kaiiiii mustapha " hajia maamaa ta daka mishi tsawa sannan ta cigaba da cewa "sam kada na k'ara jin wad'annan maganganun a bakin ka ina da ikon da xan xartar da komai a kan ku don hka na riga da na yanke hukunci "

Cikin ladabi Abba 2 yace "Allah ya huci xuciyar ki yi hak'uri Allah ya sa hkan shi yafi alkhairi Allah ya bata hak'urin jure wa"

"Ameeen " suka amsa a tare sannan daddy yace " ibraheem ya fad'a muku last month d'in nan xai dawo "
Tuni fuskar hajia maamaa ta fad'ad'a da fara'a sosai tace "Masha Allah yau ba mu yi waya ba shi yasa Allah ya dawo mana dashi lafia"

"Ameeen maamaa "
Daga hka suka cigaba da hira wani xuwa wani lokacin sannan kuma suka tashi suka nufi 6angaren nasu da yake weekend ne, lokacin da daddy ya fad'a wa mamee abin da suka tattauna da hajia maamaa da en uwan shi sam mamee bata ji dad'in hkan ba ta so ace wannan Karon an bawa 'yar ta damar xa6an mijin aure,amman bata da abin cewa sai dai addu'a kawai.


Bayan k'wana 2 da hkan iyayen safwan suka xo sun samu tar6a sosai a wajen su Abba bayan an gaisa sun ci sun sha sannan suka bijiro da buk'atar su ta neman aure, nan su Abba suka fara da basu hak'uri sannan suka fad'a musu anyi mata miji amman ita yarinyar bata ma sa ni ba, hka suka baro gidan cikin sanyin jiki suna tunanin sanar da safwan wannan mummunan labarin.

Da murnar shi ya tari iyayen nashi da suka dawo amman ganin damuwa akan fuskar tasu ya sa jikin shi yin sanyi nan dai suka daure tare da fada mishi kafin su ankara sai ganin safwan suka yi ya dafe xuciyar shi tare da lumshe ido xai fad'i baban shi ya taro tare da fad'in
"SAFWAN!"

Da k'arfi ya furta hkan cikin wani irin yanayi safwan yace "na'am Abba na ina rok'an ka ka taimaka min kada na rasa husna ina son ta xuciya ta xafi take min sosai "

Sai ga hawaye yana xuba a idanun safwan wani mugun tausayin shi ne ya kama abban shi da mahaifiyar shi nan fah suka dunga rarrashin shi tare da bashi hak'uri dak'yar hawayen suka dai na xubo wa sai kukan xuci yake don shi kad'ai yasan abin da yake ji a cikin xuciyar shi yana son husna ba Kad'an ba ashe ba rabon shi ba ce an bawa wani ita, hka yayi ta sumbatu sai dak'yar bacci ya d'auke shi, iyayen nashi sunyi jugum jugum basa son damuwar d'an nasu ko Kad'an.


Cikin k'wanakin nan safwan ya rame sosai abin gwanin ban tausayi ko abincin kirki baya iya ci kullum cikin tunanin yanda xai rabu da husna yake, gashi ko kiranta yak'i yayi a waya.

Ganin k'wana 2 safwan shiru bai Kira ta ba yasa hankalin husna ya tashi sosai nan ta kirawo shi awaya yak'i ya d'auka tuni hankalin nata ya k'ara tashi sosai ta rasa yanda xatayi K'arshe tana kuka ta fad'a wa mamee safwan ko lafia baya d'aukan wayar ta, kallon tausayin 'yar ta tabi husna dashi baxa ta iya fad'a mata K'arshe rarrashin ta tayi.


Ko dayaushe cikin kiran safwan take shima nashi 6angaren kasa daure wa yayi ya d'auki wayar bai 6oye mata komai ba ya sanar da ita duk abin da yake faruwa husna batasan lokacin da ta yar da wayar ba da gudu ta fice daga d'akin nata.............





Aishat A muh'd

        *&*

Sumayya salees sadeeq
[25/07, 09:37] Aishat A. Muhd: 🍃 *DANGARTAKAR ZUCI*🍃



*written by*

Aishat A muh'd

          *&*

Sumayya salees sadeeq




*Page 51-52*




     Cikin wani irin xafin nama Yah Abdullah da Yah ibraheem suka yi kan husna kowanne yana kok'arin d'aukan ta don bata agajin gaggawa, Yah Abdullah ya riga ibraheem xuwa inda husna take har ya kai hannun shi da niyyar d'aukan ta sai ji yayi Yah ibraheem yace

"stop it now Yah Abdullah "
Da sauri kuma cikin mamaki Yah Abdullah ya d'ago kanshi yana kallon k'anin shi kallo d'aya yayi wa ibraheem ya karanto tsantsar kishi a cikin idanun shi don hka sai ya matsa gefe ya fad'a tunanin daman ibraheem yana son husna kenan tun da gashi har ya nuna mishi kishi don xai d'auke ta kuma wannan kishin da ya karanto a fuskar ibraheem ya tabbatar sai ana yiwa mutum mugun so ake nuna kishin nan, daman ibraheem yana son husna to ina tsanar da yake mata, shi kad'ai dai Yah Abdullah yake wannan tunanin.

Yayin da ibraheem kuma ya tsugunna saitin kan husna ya sa hannun shi yana gyara mata gashin kanta da ya barbaxu har xuwa fuskar ta ya kura mata ido yana kallon ta kawai.

Ganin shi yak'i d'aukan ta ya d'ora ta kan bed don mamee ta duba ta kuma yak'i bari wani ya d'auke ta ya sata a gaba yana kallon ta kamar wanda bai ta6a ganin ta ba.

"Haba ibraheem d'ina me ka tsaya yi maxa ka d'ora ta kan gado Xahra ta dubata tun da ka k'i Abdullah ya d'auke ta "

Cikin nutsuwa yasa hannayen shi duk biyun ya d'auke ta sai da ya had'a ta da faffad'en kirjin shi sannan cikin takun tafiyar shi ta kasaita ya k'arasa kan bed d'in hajia maamaa ya kwantar da ita a hankali ya sa pillow ya d'ora kanta sannan ya dad'a tattara gashin nata ya samu waje ya xauna kusa da ita a gefen gadon ya kamo hannun ta yana yana murxa tsakiyar tafin hannun nata.

Kowa ya xuba ido cikin matuk'ar mamaki ake kallon ibraheem yanda yake yiwa husna tsana da amman gashi har yana wani lalla6a ta (ni da sister sumy muka ce ae yanxu ma aka fara wannan so min ta6i ne).

Da hka kuma hajia maamaa tace kowa ya fita daga bedroom d'in nan en uwa suka fita gaba d'ayan su daga mamee sai ibraheem da hajia maamaa wadda take cikin tashin hankali lokaci xuwa lokaci tana share kwallar idon ta, cikin k'ware wa mamee ta duba husna sai Dr ibraheem ya xama d'an kallo kamar ba likita ba, nan mamee ta gama duba ta har tayi nasarar samun numfashin ta ya dawo dai dai sannan tayi mata allurar bacci daga K'arshe tayi mata dressing din ciwon da taji a goshin ta tana gama wa ta nufi hanyar fita daga d'akin da sauri hajia maamaa tace

"zahra baki mana bayanin halin da take ciki ba xaki fita "
Dawowa cikin d'akin tayi cikin dauriya mamee tace "maamaa ba wani babban matsala ba ne suma tayi sai kuma ciwon da taji a goshin ta amman Insha Allah xuwa nan da yamma xata farka qlau "

"Alhamdullilah ngde wa Allah sai yanxu naji hankali na ya kwanta "

Cewar hajia maamaa ita kuwa mamee dafa kafad'ar ibraheem tayi tare da cewa " ibraheem ka ban kunya sai kace ba jarumin namiji ba kana ganin matar ka a wannan yanayin ka kasa duba ta duk ka wani firgice "

Murmishi yayi tare da sosa kai yace "ae ni mamee namance dani likita ne ma sai yanxu na tuna tsabar rud'ewa ni wlh har tsoron tashi nake tayi kada ta sake ji wa kanta ciwo mamee"

Ya K'arasa fad'i cikin yanayin sanyin murya cikin tausayin shi tace "kada ka damu ibraheem Idan ta farka xamu yi magana da ita kuma Insha Allah komai xai wuce amman sai kayi hak'uri"

"okay mamee Allah ya huce xuciyar ta Kafin ta tashi ma"

Er dariya mamee tayi kawai ta fice daga d'akin daman hajia maamaa ta shige toilet don rage cikin ta don ba k'aramin firgita da rud'ewar ciki ta samu ba sai yanxu tukunna ta samu nutsuwar rage cikin nata.


Ya kasa sakin hannun ta idanun shi ya xuba mata yana kallon ta cike da mamakin yanda husna ta koma wannan ba don yayi saurin fallasa abin da yake xuciyar shi ba da tuni dakon son da yake mata ya tashi a banxa ba lallai ya aure ta ba, don tun Kafin ya tafi England karatu ya sanar da hajia maamaa ta rik'e mishi husna ta kular mishi da ita don ita tashi ce shi yafi dace wa da ita fiye da kowanne namiji.

Yayi xurfi a tunani yaji muryar mumy akan shi da sauri ya dawo cikin hayyacin shi ya d'ago kai ya kalle ta harara ta watsa mishi tare da cewa "sai ka tashi ka bata waje tasha iska ka wani xo ka tsare ta da ido sai ka farkar da ita lokacin tashin ta bai yi ba "

"sorry mumy nah bari na tafi "
Ya fad'i hkan yana tashi tsaye bai gama mik'e wa ba sai ya rankwafo da kanshi saitin fuskar husna ya sumbace ta a saman goshin ta kumatun ta da kuma saman tsakiyar le6en ta sannan a Hankali ya furta

"i luv u so much my dear husna Allah ya baki lafia "

Sannan ya K'arasa mik'e wa kallon mumy yayi yaga ta xuba mishi tana kallon shi d'an d'aga gira yayi yana cewa "mumy what wrong wannan kallon fah? "

"amman ibraheem baka da kunya a gaba na kake hka? "

Rungume ta yayi yana cewa "mumy idan banyi a gaban ki ba a ina xanyi "

"ina ruwan ki ba Matar shi ce ba ya biya sadaki an d'aura " Cewar hajja maamaa kenan bayan ta fito daga toilet d'in, girgixa kai kawai Mumy tayi Sam hajia maamaa bata ganin laifin ibraheem akan komai bayan shi ta ke bi wannan kaunace da kulawar da take bashi tun ran da aka haife shi.

"Ya kamata kaje ka yi wanka ka kwanta ka huta don nasan ka gaji"
Cewar hajia maamaa kenan tana xama kan bed d'in.

"Okay maamaa ki kular min da mata ta sosai "
Fad'in ibraheem yana kama hannun  mumy "kada ka damu khaleelu na "fad'in hajia maamaa tana murmishi, daga hka suka fice daga d'akin.

Part d'in su suka tafi bayan ya shiga bedroom d'in shi wanka yayi tare da shirya wa cikin wani 3quater yellow da white d'in t-shirt mara hannu bayan ya fesa perfumes ne ya sha coffee d'in da mumy ta kawo mishi Sannan ya kure speed di'n AC ya kwanta kan katafaren gadon shi tuni ya lula tunanin husna yasan ba k'aramin fad'a xa'a sha da ita ba don shi kanshi yasan ta tsane shi kuma shine da kanshi yasa ta tsane shi din yasan yayi kuskure kuma xai gyara kuskuren da yayi Insha Allah, da hka bacci 6arawo ya d'auke shi daman kuma a gajiye yake sosai tun da ya diro nigeria bai huta ba sai yanxu.


Yamma nayi aka fara shirye shiryen kai amare gidajen su amman ban da husna wadda take kwance har yanxu tana bacci sakamakon allurar da akayi mata don hka Fadila da raudah basu samu damar yin sallama da husna ba aka mik'a su gidajen su sun sha kuka sosai abin gwanin ban tausayi, ana dawo wa daga kai su nan en uwa suka fara tafiya gidajen su na kusa kusa kenan xuwa mangarib gidan yayi shiru babu hayaniya sosai don an ragu da yawa sosai kuma part d'in saukar bak'in shi ne na K'arshe daga baya duk suna ciki suna huta gajiyar biki don an gaji kuwa.


Mumy ce a tsakiyar palo tana tsaye da wani madaidaicin cup a hannun ta tasa spoon tana juya wa sai ga ibraheem nan ya fito daga d'akin shi har ya sake wanka ya canja kaya xuwa black jeans nd T-shirt pink mai gajeran hannu kayan sun matuk'ar amsar jikin shi yana ta xuba k'amshi kan nan nashi yasha gyara da sajen nan sai kyalli yake yi murmishi ya saki wanda yake k'ara fito mishi da ainahin Kyan shi ya k'arasa wajen yana cewa

"mumy nah me xan samu I'm hungry wlh sai dai bana son abinci mae nauyi "

Ita ma mumy cikin murmishi ta ce "fad'i abin da kake so son, amman Kafin nan shanye wannan abin "

Ta k'arasa fad'i tana mik'a mishi cup d'in hannun ta kar6a yayi tare da kallon cikin cup d'in madara ce cike a cup d'in sai dai ta canja launi alamar an xuba wani abun bayan milk di'n kallon mumy yayi wadda daman can shi take kallo ya yatsina fuska tare da cewa
"Wannan mene mummy?"
"maganine son "
"me yasame ni kuma mumy ni lafia ta qlau Kinsan ban son irin wannan maganin gargajiyar"
D'an hararar shi mumy tayi tare da cewa "da yake xan baka abin da xai cutar da Kai ba "
"no mumy sorry xan sha "

Yana gama fad'in hka yasa cup d'in a baki ya fara sha maimakon yaji d'aci sai wani gardin madara ne da xak'in xuma ya baibaye cikin bakin shi sai d'an bauri Kad'an nan ya shanye shi tas sannan ya mik'a wa mumy cup d'in kar6a tayi tare da cewa "Yawwa ko kai fa son ga wani kuma"
Xaro ido yayi yana kallon hannun cup d'in mumy tare da dafa ciki yace "wash mumy ki bari sai anjima "
"A'a ibraheem yanxu xaka sha bashi da yawa ae kuma kankana ce da milk sai xuma"

Bashi da yanda xai yi hka ya kar6a ya fara sha yana mai jin kunyar mumy wato shi take gyara wa kenan kamar wata mace shi yasa yake alfahari da mumyn shi.

Yana cikin sha Abdullah ya shigo falon kallon ibraheem yayi tare da kallon cikin cup d'in hannun shi sai kuma ya kalli mumy yace "Mumy mene yake sha ni aka ware ni"

Murmishi mumy tayi tare da cewa "tambaye shi ga ka gashi magani ne yake sha "
Tana gama fad'in hka ta nufi kitchen, Yah Abdullah janyo ibraheem yayi kusa dashi a hankali yake cewa "kai malam me kake sha Hka babu ajiye wa d'an uwa?"

Murmishi ibraheem ya saki tare da cewa " hmm Yah Abdullah maganine mumy ta sani a gaba tana bani kamar wata mace "

Ya K'arasa fad'i yana Yatsina fuska dariya Yah Abdullah ya kwashe da ita Kafin kuma yace "kai malam mumy ta kyauta xaka yi mata godia sai nan gaba mybe ma ka dawo neman Kari tana gyara ka ne don kada mace ta rai na ka "

"koh? "
Cewar ibraheem yana ajiye cup d'in bayan ya gama sha.
"ofcourse yaro kuma xaka ce na fad'a maka, nima bari na bita kitchen na samu rabo na don gobe xan gudu abuja "

Har ya mik'e tsaye ibraheem ya janyo shi ya fad'a kan kujera yace "kai Yah Abdullah ka tausaya mata tana fama da tsohon ciki ka bari ta haihu mana "

Dariya suka tuntsire da ita lokaci d'aya tare da tafawa kamar wasu sa'annin juna cikin dariyar Yah Abdullah yace "ka kawo shawara kuwa ibraheem na hak'ura "

Xumbur kuma ibraheem ya mik'e tsaye tare da cewa "ohhh my god Yah Abdullah ka 6ata min time da surutun ka xanje duba jikin husna "

Yana gama fad'in hka bai jira abin da Yah Abdullah xai ce ba ya fita daga palon da sauri, girgixa kai Yah Abdullah kawai yayi sannan ya shige kitchen Inda mumy take had'a wa ibraheem abincin da xai ci.


Shi kuwa ibraheem yana fita ya nufi part d'in hajia maamaa, a dai dai time d'in husna ta farka firgigit da sauri ta dafe kanta jin yanda yake mata ciwo sosai kallon d'akin take cike da matuk'ar mamakin abin da ya kawo ta d'akin hajia maamaa a hankali kuma ta fara tunanin abin da yafaru ae kuwa tana gama tunanin ta dage ta k'walla wata uwar k'ara mai k'arfin gaske, nan fah aka fara riga rigan shiga d'akin tsakanin Yah ibraheem, hajia maamaa da ilham don su kad'ai ne a part d'in.
Ihu take tana cewa "abin da baxai ta6a yiwu ba kenan amman kuwa an cuce ni a rasa wa xa'a aura min sai Yah ibraheem wayyo Allah nah "

Tana gama fad'in hka kuma xumbur ta mik'e tsaye dai dai lokacin hajia maamaa, ilham da Yah ibraheem sun shigo cikin d'akin da sauri hajia maamaa ta nufi wajen ta tana kok'arin rik'e ta don ganin yanda take layi kamar wata er k'waya fincike jikin ta tayi da k'arfi tare da cewa
"kada ki k'ara rik'e ni na tsane ki kamar yanda kika tsane ni "

Sakin baki yah ibraheem yayi yana kallon husna bai yi wani yunkurin xuwa wajen ta ba, hajia maamaa ta kalla sannan ilham lokacin da ta kalli ilham sai da ilham taji d'an cikin ta ya juya cikin muryar tsiwa tace "Har da ke aka had'a baki wajen aura min mak'iyi na koh? "

Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun abin da Yah ibraheem ya furta a cikin xuciyar shi lokaci d'aya kan shi ya fara ciwo, ilham kuwa cikin sanyin murya tace "taya xa'a had'a baki da ni a cuce ki husna kuma maamaa da iyayen mu ba cutar ki suka yi ba gata suka yi miki kiyi hak'uri kiyi biyayya da xa6in su "

Wani harara ta watsa wa ilham tare da sakin wani murmishin takaici ta tafa hannayen ta sau uku tukunna tace " ke ma goyan bayan su kika yi ashe ke ma mak'iyiya tace lokacin da aka raba ni da Yah Abdullah na hak'ura na sake samun wani masoyin mai sona da gaskiya muna k'aunar junan mu aka raba mu to wannan auren shi ma hka xa'a raba shi "

Tana gama fad'in hka ta nufi hanyar fita daga d'akin da sauri hajia maamaa tace "husna ina xaki je?"

Fad'in hka da tayi ta d'ago xata kalli hajia maamaa sai lokacin idanun ta suka sauka kan Dr ibraheem khaleel wanda sai had'a uban gumi yake najin furucin husna yasan yarinyar akwai ta da kafiyar tsiya Idan ta dage da abu.

Da har tayi niyyar taje ta rufe shi da duka ko ta samu sassauci cikin xuciyar ta sai kuma ta fice da gudu  ta barsu kowanne jiki a sanyaye xuwa part d'in su tana shiga suka ci karo da mamee da sauri mamee ta rungume ta daman yanxu xata fito don ta duba ta sai gashi ta shigo ruwan wanka mai xafi ta had'a mata tayi wanka ta fito mata da Kayan bacci ta sanya sannan ta had'a mata tea tasha da d'an pepper soup din chicken tana gama sha kuma ta ba ta magungunan ta tasha bayan ta gama sha ta bud'e baki xatayi magana kenan mamee ta tsikara mata allurar bacci ae kuwa husna ta saki er k'ara ta jin xafi cikin en mintuna ta bacci yayi awon gaba da ita.

Tashi mamee tayi tsaye tana kallon husna cike da tausayin ta tana sani tayi mata allurar bacci don ta samu hutu a kanta Idan ba hka ba tashin hankali xa'a yi tayi a daren amman xuwa gobe da safe ta dan huce xata xauna su yi magana ta fahimta har ta samu damar lalla6a ta yarda da xa6in da aka yi mata.

Tana niyyar fita taga ibraheem jingine jikin kofar d'akin yana kallon husna idanun shi sunyi ja sosai, tuni tausayin shi ya kama mamee don tasan tabbas ibraheem yana son husna hannun shi ta kamo xuwa cikin palon cikin sanyin murya yace "mamee mene yasa kika yi mata allurar bacci da kin barta ta fad'i abin da take son fad'i an ta6a ta ne mamee da xan iya hak'ura da husna da na hak'ura da ita na rok'e ki mamee ki lalla6a min ita ina son ta bansan yawan son da nake yiwa husna ba mamee help me mamee please "

Cikin tsananin tausayin shi mamee tace "kada ka damu ibraheem ka cigaba da addu'a da kuma hak'uri "

"Insha Allah mamee ngde "
Da hka ta lalla6a shi ya tafi don dare yayi nan kan kujerar ta xauna tana tunanin abin da ya kamata tayi............





Aishat A muh'd

         *&*

Sumayya salees sadeeq
[25/07, 09:37] Aishat A. Muhd: 🍃 *DANGARTAKAR ZUCI*🍃




*written by*

Aishat A muh'd

*E.W.F*

          *&*

Sumayya salees sadeeq

© *P.M.L*




*Page 55-56*




   Tun daga lokacin husna da Yah ibraheem basu k'ara had'u ba har ya xama a yau xa'a kai husna gidan yah ibraheem en uwa na kusa sun xaxxo har wata er k'warya k'waryar walima akayi, Kafin kuma da yamma wajen 5 aka mik'a husna gidan ta bayan tasha nasiha sosae a wajen mamee da daddyn ta ga sauran en uwanta su ma sunyi mata nasiha sosae hajia maamaa kuwa addu'a tayi mata tare da sanya mata albarka tun da yanxu ta hak'ura xata xauna da d'an gaban goshin nata, har da ita aka kai husna don daman tayi alk'awarin ita da kanta xata shigar da matar ibraheem cikin d'akin ta ae kuwa hannun ta rik'e da hannun husna har ta xaunar da ita kan katafaren gadon ta, husna kuwa har tayi kuka ta gaji hawayen ma sun daina fito wa daga idanun ta sai faman ajiyar xuciya take saki lokaci xuwa lokaci.

Ana sallahr mangarib en uwa suka yiwa husna sallama suka tafi ya rage gidan sai husna, aunty rufaidah da aunty aimana sai da suka gyara mata ko'ina na gidan suka kunna turaren wuta mae k'amshi tuni ko'ina ya d'auki k'amshi mai dad'in shak'a bayan sun gama su ma suka k'ara yiwa husna nasiha tare da bata shawarwari masu kyau tukunna suka tafi aka bar husna ita kad'ai bata ji wani tsoro sosai ba tun da ko'ina akwai haske kamar da rana.

Kayan jikin ta ta cire ta d'aura towel ta shige toilet wanka tayi tare da alwala bayan ta fito ta shirya cikin wata blue sky din sleeping dress doguwa ce har k'asa mai siririn hannu ta gyara gashin kanta sannan ta fesa different perfumes nd body spray masu matuk'ar k'amshi.

Abin sallah ta shimfid'a bayan tasa dogon hijab mai hannu har k'asa ta gabatar da sallahr isha'e bayan tayi addu'o'in ta kamar yanda ta sa ba sannan ta mik'e tsaye tare da cire hijab d'in nata jiyowar da xata yi suka had'a ido da Yah ibraheem tsaye a jikin kofar d'akin yana kallon ta hannun shi rik'e da wasu manyan leda wani wawan tsaki taja kamar xata tsinke harshen ta.

Duk da Yah ibraheem a duniyar nan ya tsani tsaki kuma ranshi ya 6aci amman bai nuna ba tunda sulhu yake nema, ajiye ledar hannun shi yayi kafin dakyar yace

" ga wannan ko xaki buk'aci abinci "
Yana gama fad'in hka ya juya da niyyar fita har ya fitar da kafafun shi daga cikin bedroom d'in husna kamar abin arxiki ya bud'e baki tace
"Yah ibraheem "

Cak Yayi ya tsaya jin ta ambaci sunan shi juyowar da xai yi sai gani yayi ta cillo mishi wannan ledar da ya ajiye a fuskar shi tuni kayan ciki suka tarwatse gaba d'ayan su a k'asa cikin tsanar shi tace
"an gaya maka ni mayunwaciya ce, bana son duk abin da ya fito daga hannun ta i hate u"
Tana gama fad'in hka ta rufe kofar ta tare da sa mata key kan bed ta koma hankali kwance ta kwanta tare da yin addu'ar bacci bata dad'e ba bacci yayi awon gaba da ita.

Shi kuwa Yah ibraheem kallon kayan da ya tarwatse a k'asa yake duk da ranshi ya 6aci sosai akan abin da husna tayi mishi ya riga da ya yiwa kanshi alk'awarin baxai ta6a tanka mata ba har xuwa lokacin da xata huce ya bata hak'uri tare da neman soyayyar ta don kuwa duk abin da xata yi mishi xai danne xuciyar shi.

Yana gama wannan tunanin ya nufi inda ake ajiye Parker da abin yin mopping ya d'auko share wajen yayi tare da goge wa tukunna ya shige bedroom d'in shi wanka yayi tare da yin alwala sannan ya fito ya shirya cikin wasu sleeping dress farare sol dasu kan abin sallah ya hau ya fara jera nafila na godia ga Allah tare da addu'ar Allah ya karkato mishi da hankalin husna kanshi yasa ta so shi ko da rabin son da yake mata ne hka ya raya daren cikin bautar ubangiji har xuwa asuba bayan ya yi sallahr asuba ne bacci ya d'auke shi mai dad'in gaske xuciyar shi cike da tunanin abar son shi husna.


Washe gari da safe bayan husna ta tashi daga bacci wajen karfe 9:30 na safe brush tayi tare da shan ruwa cikin glass cup d'aya don yana taimaka wa jiki sosai yin hka kuma wannan shan ruwan safen Kafin taci komai horan mameen ta ne.

Gyaran bedroom d'in nata tayi sannan ta gyara falon ta da kuma babban palon gidan tasa turaren wuta ta turare gidan da k'amshi sannan ta shiga toilet tayi wanka ta shirya cikin wata tsadaddiyar atampha kalar blue d'inkin riga da siket ne sun amshe ta kayan ta d'aurin dankawalin ta mai kyau bata yi wata k'walliya ba daga powder sai wet lips mai k'amshin apple amman duk da hka ba k'aramin kyau tayi ba tana cikin fesa turare taji an danna door bell don hka tana gama fesa wa ta fito xuwa falon ta bud'e kofar er aikin mumy ce shige wa tayi ta xauna er aikin ta gaida husna tare da cewa
"gashi inji mumy tace na kawo miki "
Ta fad'a tana ajiye basket d'in xuba kayan abinci ga hadaddun food flaks a ciki
"Okay je ki ajiye min kan dinning table "
"toh aunty "
Da sauri taje ta ajiye bayan ta dawo tace " aunty Ko da wani aiki da xan yi miki?"
Girgixa kai husna tayi tare da cewa "nooo babu komai wa ya kawo ki? "
"driver ne"
"Okay Shikenan "

Daga hka ta yi mata sallama ta tafi, kitchen husna ta shiga taga yanda aka tsara mata kitchen d'in ya had'u sosai kalar green  ne plate ta dauko da cup d'in had'a tea tare da spoon and fork dinning table ta nufa ta ajiye nan ta tarar da kayan tea milk, bournvita, cornflakes da dai sauran su nan ta had'a tea tasha tare da cin chips and egg sai er source tare da plantain,sai da ta koshi sannan ta tashi ta dawo falo ta xauna wayar ta ta d'auko nan ta fad'a duniyar charting sai hira suke a grp d'in su wanda suka bud'e mai suna  4 sister's for life husna, ilham, Fadila da raudah suna ba wa junan su shawarari masu amfani sosai sai tsokanar husna ita kuwa tana bawa kowa amsar da ta dace.

Wani k'amshin turare ne ya bige hancin ta saboda dad'in k'amshin sai da ta lumshe idanun ta Kafin ta d'ago kanta suka had'a ido da Yah ibraheem yana sanye cikin wani blue d'in jeans da t-shirt black mai dogon hannu yayi kyau sosai kannan nashi yasha gyara sai shek'i yake cikin takun tafiyar shi ta kasaita ya nufo inda husna take xaune wadda ta danna mishi harara Kafin ta mayar da hankalin ta kan wayar, k'arasa wa yayi ya xauna kusa da ita har kafad'ar shi na gogar ta ta da sauri husna ta matsa gefe cikin murmishi yace
"Gud mrng sweetheart,  i hope kin tashi lafia? "

Bata yi mishi magana ba hka kuma bata sake kallon Inda yake ba K'arshe ma sai ta shige cikin bedroom d'in ta da kallo ya bita yana murmishi tare da shafa gashin kan shi xuciyar shi cike da tsantsar k'aunar ta da sha'awar ta da hka ya tashi ya nufi dinning table yayi breakfast sannan ya fita daga gidan gaba d'aya.

To Hka abubuwa suke tafiya tsakanin husna da Yah ibraheem bata kula shi k'wata k'wata ko magana bata yi mishi ko da yayi mata kullum shine xai gaida ita Idan suka had'u a palo but husna bata amsa wa amman hkan bai sa ya fasa yi ,ga wata axababbiyar sha'awar husnah da ta dame shi saboda irin shigar da take yi wani lokacin ba k'aramin tayar mishi da hankali take ba kusan k'wana yake murkususu akan bed da yana da ra'ayin kula mata waje da tuni yayi saboda sha'awar da take damun shi sosai abin ya fara ramar dashi ya rasa ta yanda xai rarrashi husna ta amince dashi don ya kawar da abin da yake damun shi.

Idan abin ya dame shi sai dai yasha maganin da xai dan samu sauk'in abin, ana cikin hka daddy ya kammala gina mishi hospital d'in shi an gama komai an xuba kayan aiki sannan ya nemi kwararrun likitoci an xuba a asibitin ranar da akayi bikin bud'e asibitin ko da ya sanar da husna ko tanka mishi Bata yi ba.

Ana cikin hka suka kwashe tsawon wata 3 da aure husna tana xuwa skul d'in ta don ya kyaleta ta cigaba su ma suna gaf da kammala wa drive guda ya ajiye mata wanda xai dunga kai ta skul yana dawo da ita, kuma har a yanxu husna bata je gida ba tun da aka kawo ta gidan Yah ibraheem rabon ta da gida, su fadila da raudah sun xo mata yini rana d'aya suka xo sun sha hira sosai kamar kada a rabu kowacce da tsarabar amarci don Sun samu ciki husna sai tsiya take musu suna rama wa ranar sunyi yinin farinciki sosai sai da yamma Yah mus'ab da Yah yaseer suka xo d'aukan matan su bayan sun taso daga aiki ae kuwa husna ta rik'e su sai da suka yi dinner agidan tukunna su ka tafi, hakurin Yah ibraheem ya fara karewa don hka ya fara tunanin neman mafita.

Kamar yau ranar sunday weekend kenan yah ibraheem yana xaune a palo sanye yake da wani 3quater fari da wata riga mai Shara Shara don ana iya hango kwantaccen gashin kirjin shi bak'i wuluk dashi yana amfani da laptop d'in shi amman kusan hankalin shi yana kan husna wadda take xirga xirga tsakanin kitchen da wurin dinning table tana shirya wa kanta abincin rana don bata yi da Yah ibraheem sai dai idan ta rage takai kitchen Kafin taxo wanke wanke sai ya d'ebo yaci hkan ba k'aramin kular da ita yake ba bayan ta gama had'a abincin ta gyara Inda ya kamata sai ta shiga wanka bayan ta fito ta shirya cikin wata gown red colour ce mai k'aramin hannu doguwa ce har k'asa sai dai tana da tsaga daga saitin gefen ta tsagar tun daga cinyar ta har kafar ta ana gani ga wuyan rigar babba ne mai irin V din nan ta sanya ribbom red da dankunne red shima ga hannun ta kan 'yan yatsun ta sun sha jan lalle tayi masifar yin kyau kowanne namiji mai lafiya yaga husna a hka sai hankalin shi yayi masifar tashi falo ta fito tana tafiya duk wata ga6a ta jikin ta sai fitar da sanyayen k'amshi take k'amshin da take shi kad'ai ya isa ya tada hankalin mutum gashi fuskar nan ta ta a daure take babu alamar fara'a sam.

Yah ibraheem wanda k'amshin turaren husna ya sashi d'ago kanshi ya Kalle ta sai kawai ya saki baki da hanci da ido yana kallon ta cikin wata masifaffiyar sha'awa tuni idanun shi sun fara canja launi xuwa ja har taxo ta shige ta gaban shi ya bita da kallo gaba d'aya jikin shi ya fara rawa xumbur ya mik'e ya nufi inda husna take xaune tana cin abincin  ta hankali kwance batasan ma da tahowar shi ba...............


_Koya xata kasance tsakanin had'uwar husna da Yah ibraheem_?





Aishat A muh'd

          *&*

Sumayya salees sadeeq
[25/07, 09:55] Aishat A. Muhd: 🍀🍀☘☘🍀🍀
  *K'ARSHEN WAHALA*
🍀🍀☘☘🍀🍀



*written by*
Aishat A muh'd


*~Pg 78~*


Gaba d'aya hankalin su umma yayi masifar tashi ganin su nauwara a sume duk matan sun rud'e sai abdulkareem ne yayi jarumtar yayyafa musu ruwa ban da nauwara da take jikin abduljabbar yana faman jijjiga ta tare da kiran sunan ta ga twins a hannun fa'iza suna kuka da kiran mamien su

Hankalin umma ne yayi kan nauwara sai lokacin ta ankara da tana jikin abduljabbar ai kuwa wajen ta nufa tare da sa hannu ta rik'o ta, tana kok'arin raba ta da jikin abduljabbar cikin marairaicewa yace
"umma bari na kai ta hospital Har yanxu bata farfad'o ba "
Duk da halin da suke ciki na tashin hankali sai da umma ta dalla mishi harara tare da cewa
"cika min yarinya ba ruwan ka da ita Idan ma ta kama akaita hospital d'in ae ba kai xaka kai ta ba"
ranshi ya 6aci da abin da umma tace sai kawai ya sake ta ya fice daga wajen a fusace ko ta kan twins bai yi ba
Ajiyar xuciya ta saki tare da bud'e idon ta a nutse ta fara duba cikin d'akin tare da tunanin mai ya same ta cikin lokaci k'alilan ta tuno da komai xumbur ta tashi daga kwance da take sai lokacin su umma suka san ta farka
"ammi nah!"
Da sauri maimuna wadda nauwara ta kirawo da ammi ta isa inda take ta rungume nauwara
"ammi na mafarki nake ko ido biyu ke nake gani? "
cikin kuka ammi tace
"ba mafarki kike ba nauwara nice ammin ki ashe kuna raye bai kashe min ku ba "
Saleem ma yaxo ya rungume su suna kuka bana wasa ba su umma suna daga gefe suna goge hawayen tausayin su, sai da suka yi kuka sosai umma da aunty sadiya dasu aunty asma'u suna rarrashin su sannan suka dai na kukan sai faman sauke ajiyar xuciya suke gashi suna rik'e da hannun ammi don gani suke kamar xata dad'a gudu wa ta bar su

Bayan an nutsu abba ya dawo ake sanar dashi komai ya buk'aci ganin su don a tattauna ko da wani taimako da xai basu, bayan sallahr isha'e aka xauna a falon abban gaba d'ayan su har da abdulkareem sai dai abduljabbar tun da ya fusata ya fita bai dawo ba don hka shi kad'ai ne baya nan don Abba bai ma san da xuwan shi ba labarin su ya buk'aci ji don hka nauwara ce ta fara ba da labarin su tun daga farko da irin wahalhalun da suka sha ita da saleem da xaman su gidan hindatu da aminu xuwa gidan saude mai abinci da ta taimake su har xuwa lokacin da suka hadu da abduljabbar ya taimaka musu, Abba aunty sadiya dasu aunty asma'u sun girgixa da irin wahalar da suka sha idan ka d'auke umma don tasan da labarin ammi kuwa kuka kawai take yanxu daman safah ta mutu nauwara sai da ta makance ta xama wadda bata iya tafiya duk dukiyar mahaifin su suka xama masu bara Yah ilahi duk Wannan abun a dalilin Alhj salisu anya yana son gama wa da duniya lafia yana k'aunar rahmar ubangiji kuwa xalinci da cinye dukiyar marayu duk wannan bai isheshi ba sai ya nemi halakasu falon yayi shiru sai shashshak'ar kukan ammi da su nauwara Abba ne ya katse shirun ta hanyar cewa
"nauwara wane mahaifin ku a wanne gari kuke?? "
Don duk Wannan labarin da ta bayar bata fad'i sunan mahaifin su ba cikin sanyin murya tace
"mu en kaduna gidan abban mu a tudun wada suke mahaifin mu kuma a unguwar gwamna road yake xaune sunan shi "
Tun da ta fara maganar abba ya xuba mata ido gaban shi yana fad'u wa jikin shi har er rawa yake sai da ta sauke numfashi sannan tace
"sunan abban mu Alhj sa'eed haruna "
tashi abba yayi yana karanta Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun ya dafe kan shi da sauri abdulkareem ya mik'e ya rik'o shi tare da xaunar da shi
"Kina nufin Kice Alhj sa'eed haruna mahaifin ku ne?"
"tabbas shine mahaifin su "
Cewar ammi tuni idon abba ya kad'a yayi ja daman yaran aminin shi ne yake rik'e da su bai sani ba kallon umma da aunty sadiya yayi sannan yace
"' 'ya'yan aminina Alhj sa'eed haruna wanda har naje kaduna dubo shi na tarar ya rasu na buk'aci a ban yaran shi na rik'e akace duk sun mutu "
"k'warai kuwa anyi haka "
Cewar umma tana mai tabbatar da hkan cikin tsananin mamaki ammi tace
"Ko kai ne Alhj ibraheem d'anbatta? "
D'an murmishin yak'e Abba yayi sannan yace " nine maimuna aminin mijin ki sakacin mu na wajen k'in rik'on xumunci yasa bamu gane ku ba hka kuma baku gane ne mu ba"
"yanxu salisun shi ya aikata hkan Lallai rayuwa ta xama abar tsoro d'an uwan ka na jini ya nemi kashe maka iyalan ka saboda wani dalili na son dukiya wad'anda xaka mutu ka bar su a duniya Allah ya raba mu da sharrin xuciya "
"Ameen thumma Ameeen "
Suka amsa gaba d'ayan su sannan abba yace
"toh lokacin da yasa aka d'auke ki ina suka kai ki??? "
Ya tambayi ammi sunkuyar da kanta tayi kafin ta bud'e baki ta fara magana tace
"ina kuka da kiran sunan yara na suka tura ni cikin mota daga nan suka shak'a min wani abu a hanci na 6ingire da bacci ban san inda suka kai ni ba ni dai na tsinci kaina a wani gida mai kyau a lokacin nayi kuka nayi kuka daga K'arshe na Duk'ufa da addu'a ba dare ba rana Allah ya ku6utar dani daga hannun wannan axxalimin ga abinci mai kyau don akwai mai dafa min abinci har da gyaran gidan anan take k'wana er aikin

Tun da suka kawo ni wannan gidan sau d'aya Alhj salisu yaxo ya dunga lalla6a ni na yarda na aure shi na xauna anan xai kawo min yara na don su xauna a gaba na ya dunga yi min alkawarin abubuwa na jin dad'in rayuwa amma nak'i yarda na aure shi daga K'arshe a fusace ya bar gidan

Haka na cigaba da rayuwa ta cikin kunci da tarin damuwa duk nabi na rame saboda hankalina ba a kwance yake ba har Allah ya bani ikon gudu wa daga gidan nan ganin yanda wad'anda suke mishi tsaron ta ranar sun sha alcohol sunyi tatul suna ta faman maye shine na fita daga gidan ina gudu Ashe d'aya daga cikin su ya ganni shine suka biyo ni har Allah yasa muka had'u daku har kuka taimaka min"

Ammi ta K'arasa fad'i tana goge hawayen fuskar ta
"Lallai salisu ya cika mugu axxalimi dole ne mu yi Shari'a dashi duk da *WATA SHARI'AR SAI A LAHIRA*  sai mun Kwatar muku hakk'in ku Insha Allah "
Cikin tsoro ammi tace "kada a kai su k'ara ina jin tsoron kada ya tarwatsa maka iyalan ka mugune kawai mu barsu da Allah daman *INNALLAHA MA'ASSABIRIN* (na miss zahra mansur) "
"ina ammi baxai yiwu ba dole mu shigar da su k'ara kuma xamu yi nasara Insha Allah akwai friend d'ina barrister ne ya k'warai a aikin shi xamu neme shi a san yanda xa'a 6ullo wa abun amman batun abar shi ba bai taso ba a rage mugun iri"
Cewar abdulkareem Jijjiga kai Abba yayi sannan yace
"k'warai kuwa abdulkareem Don barin irin wad'annan mutanen ba k'aramin hatsari bane sai su cigaba da xalintar mutane"
Kowa ya gamsu da hakan nan kuma aka d'an wartsake ana ta6a er hira

Wani wawan naushi ya kai wa bangon d'akin duk abin da su Abba suka yi Duk a kunnen shi yaxo zai shiga falon abban yaji nauwara tana bada labarin rayuwar su daman xaluntar su akai neman hallaka su ake suka gudu da xummar xuwa gidan aminin mahaifin su don ya taimake su lokaci d'aya wani son nauwara da tausayin ta suka lullu6e shi dole na kar6ar muku hakk'in ku da hannuna xan kashe wannan axxalumin mutumin wani duka ya sake kai wa wardrobe d'in dake kusa dashi

Take murfin ya 6urme ciki fad'o war wata jaka ce tasa ya mai da hankalin shi kan wajen a hankali yasa hannu ya dauke ta a take ya tuna inda ya tsinci jakar nan kayan cikin ne suka fara xubowa k'asa takardu ne da wasu pictures guda biyu hannun shi har rawa yake Wajen d'aukan pictures d'in mutanen da ya gani a jikin photon yasa shi kusan suman tsaye saboda tsabar tsananin mamaki...........

Aishat A muh'd
[25/07, 09:56] Aishat A. Muhd: 🍀🍀☘☘🍀🍀
  *K'ARSHEN WAHALA*
🍀🍀☘☘🍀🍀



*written by*
Aishat A muh'd



_this page dedicated to Sumayya salees sadeeq (sumyn bash 💋) Allah ya k'ara basirah da daukaka Ameen_



*~Pg 79~*




   Sake murxa idanun shi yayi don ya tabbatar abin da yake gani ba mafarki bane a xahiri ne abin ya matuk'ar bashi mamaki sosai ba wasu ya gani ba ajikin pictures d'in ba sai nauwara saleem da kuma ammin su duk da bai san abban su da safah ba amman ya tabbatar sune sunyi kyau sosai kowannen su fuskar shi d'auke da Murmishi d'ayan kuma nauwara ce da safah xama yayi kan sofa yana sake kallon photo nan sai da ya d'auki en mintuna anan xaune tukunna ya mayar dasu cikin jakar ya ajiye su duk da Har yanxu xuciyar shi da tsanar nauwara amman xai yi iya yin shi don ya Kwatar musu hakk'in su

********

 Suna xaune a parlour umma aunty sadiya da ammi sai nauwara da fa'iza ana hira cikin annushuwa twins saleem ya d'auke su sun fita shan ice cream suna cikin haka abduljabbar ya shigo da sallama tun ranar birthday di'n na'eem da ameer da ya bar gidan sai yau ya sake shigo wa shima don tafiya abuja ne ya Kamashi yaxo yi musu sallama kuma ya kwashi twins d'in abdulkareem don dasu xai tafi duk da jiddah baxa ta bishi ba xai iya kula dasu

amsa mishi sallamar aunty sadiya da ammi suka yi sannan ya shigo parlourn nauwara ce ta mik'e daga kwancen da take jikin ammin ta ko kallon Inda yake bata yi ba ta nufi upstairs bedroom d'in su kai tsaye ta shige don bata son ganin shi bata k'aunar wata alak'a ta sake shiga tsananin su tun da har xuciyar shi ta yarda da sharrin da aka kulla mata sharrin ma na aikata fasikanci da auran ta wasu hawaye ne masu xafin gaske suka fito daga idanun ta

Tana wuce wa ta gaban shi da kallon tsana da harara ya bita Kafin yaja d'an k'aramin tsaki duk umma tana ankare da abin da yayi gaida su yayi aunty sadiya da ammi da fara'a suka amsa mishi umma kuwa a dak'ile ta amsa xama yayi ya rasa ma ta Inda xai fara maganar tashi saboda k'wata k'wata babu fuska a wajen umman

Aunty sadiya ce ta mik'e ta bar wajen sannan ammi ma ta mik'e tana cewa
"fa'iza taho muje ki kitse min wannan kan nawa ya ishe ni hka"
Mik'e wa tayi tana cewa
"toh ammi "
Suka nufi d'akin da ammi take k'wana aka bar umma da abduljabbar xaune su kadai sunyi shiru sai can tace
"sai ka fad'i abin da yake tafe da kai duk ka kore min en hirar kuma ka sani a gaba kayi shiru "
Tsugunna wa yayi har k'asa ya rik'e kafafun umma yana bata hak'uri ta yafe mishi baxai k'ara kwatanta hakan ba
"toh me kayi min abdul ai ni bakai min laifin komai ba "
"nooo umma Kina fushi da ni har da abba ba naje office na same shi dakyar ya amsa min gaisuwa ta ku yafe min pls"
"Shikenan komai ya wuce "
Cikin tsananin farinciki yace
"thank u umma nah Allah ya k'are min ku"
"Ameeen "
Umma tace sai kuma ya fara sosa k'eya da akwai wata maganar bayan wannan don hka tace
"sai kuma me? "
Cikin kwantar da murya yace
"umma daman abdulkareem ne ya bani na'eem da ameer ya bar min su har abada so shine naxo d'aukan su xamu wuce abuja "
Kallon shi umma take kallon irin anya kana cikin hayyacin ka can tace
"shi abdulkareem din ne yace maka ya bar maka na'eem da ameer? "
"ehhh umma ashe Maryam ta haifar mishi twins ban sani ba? "
Wani murmishin takaici umma tayi sannan tace
" na'eem da ameer nauwara ce ta haife su ba maryam ba don haka wannan kyautar Bata yi ba "
Tun da ta fara magana yake kallon ta cike da mamaki nauwara ce ta haifi twins daman ba 'ya'yan abdulkareem ba ne
"umma Kina nufin Kice min aure ta sake har ta haife su? "
Wani kallo ta watsa mishi wanda ya sashi shiga taitayin shi a fusace tace
"ka maida mu mahaukata in banda haka taya ya xata sake wani auren bayan tana da aure toh na'eem da ameer dai 'ya'yan Kane na cikin ka "
Jin saukar maganar yayi har cikin kwakwalwar shi da sauri yace
"umma da gaske twins 'ya'ya nane "
Sai ya bata d'an tausayi ganin duk yanda yabi ya rud'e jikin shi har d'an rawa yake tsabar abin ya xo mishi unexpected
"Alhmdllh Allah nagode ma da ka nufe ni da samu d'an kaina "
Sai da ya gama murnar shi sannan yace
"umma a had'a musu kayan su kayan su mu tafi tare "
Wani kallo umma ta watsa mishi tace
"kada na kuma jin wannan maganar a bakin ka yaran da bakasan da haihuwar su ba da wahalar su lokaci d'aya kace a baka su toh wallahi ka fita a idona na rufe kaji na fad'a maka tashi ka bani waje"
Jikin shi a sanyaye ya tashi ya fita daga parlourn a farfajiyar gidan suka had'u da twins da saleem sun dawo had'a su yayi ya rungume su a jikin shi k'aunar su tana ratsa jinin jikin shi har sai da ya goge hawayen da suka xubo mishi wai yau shine da yaran kanshi saleem ma yana gefe yana kallon shi cike da tausayin shi na'eem da ameer ma kwanciya suka yi a jikin shi suna xuba mishi surutu tuni ya wartsake ya biye musu sai da yasha hira dasu dakyar ya iya tafiya ba don ya so ba xuciyar shi cike da kaunar yaran shi Duk wata tsana da yake wa nauwara ta bar xuciyar shi wani sonta ne ma yake dad'a shiga cikin xuciyar shi da hka har ya K'arasa abuja da tunanin nauwarah da twins d'in shi na'eem da ameer




Aishat A muh'd
[25/07, 09:56] Aishat A. Muhd: 🍀🍀☘☘🍀🍀
 *K'ARSHEN WAHALA*
🍀🍀☘☘🍀🍀


*written by*
Aishat A muh'd



*~Pg 80~*




  6angaren su abba duk wasu shirye shirye sun kammala na shigar da k'arar su Alhj salisu don haka Abba da abdulkareem da kanshi yaje har kaduna ya d'auko su baffah da inna habiba sai da suka xo kano tukunna yayi musu bayanin komai lokacin da suka ga ammi nauwara da saleem sai da suka kusan suma tsabar mamaki da farin ciki suka rungume juna suna kuka dakyar aka rarrashe su suka yi shiru nan abba yace su baffah su xauna anan har sai an kammala Shari'ar nan take suka amince


********

Sai faman had'a gumi yake yana ta safa da marwa a cikin office d'in wata doguwar takarda a hannun shi Alhj salisu kenan yanxu aka kawo mishi takardar sammaci daga kotu abin da yayi matuk'ar gigita tashi da d'aga mishi hankali shine sunan nauwara sa'eed haruna da saleem sa'eed haruna sune suka shigar dashi k'ara wayyo xan so kuga yanda fuskar Alhj salisu ta koma saboda tsanani tashin hankali, d'aya daga cikin mai kula da office d'in shi ya shigo bayan yayi mishi ixinin shigowa wasu files ne a hannun shi ya ajiye akan table d'in sannan ya d'an saci kallon Alhj salisu ya ga baya kallon shi da sauri ya d'auko wata er K'aramar wani abu ya d'ora kan table d'in Inda baxai gani ba ya bar office d'in da sauri yana fita daga office d'in ya d'auki waya ya Kira wata number cikin k'asa k'asa da murya don kada aji shi yace "yalla6ai na ajiye abin da ka bani " d'an shiru yayi alamar sauraren mai maganar can yace "ba matsala duk xa'a yi abin da kace Allah ya baku nasara" yana gama fad'in hka ya mayar da wayar aljihu sannan ya d'an wai waiga bai ga kowa sai ya juya ya tafi

wayar shi ne tayi k'ara da sauri ya dauka ya duba sunan d'aya daga cikin yaran shi ne da sauri yayi picking
"what!!!!? "
Abin da ya fad'i da k'arfi sannan yace
"ta gudu kuka ce toh ina neman ku da gaggawa kuxo kaduna yau d'in nan akwai aikin da xaku yi min mu had'u a guest house d'ina "
Yana gama fad'in hka yayi hanging up d'in wayar yana furxar da wani xaxxafan gumi nan take ya kirawo Alhj lawan shana da yanxu sam basa shiri sunyi fad'a kaca kaca akan kud'in da bai bashi yanda yake so ba suka yi baram baram sai yanxu ya nemo shi don shi kad'ai ne xai bashi shawarar don hka sun gama magana kan karfe 8 na dare su had'u a guest house d'in shi don su tattauna yanda xasu 6ullo wa wannan Shari'ar tunani sosai ya xurfafa sai faman had'a uban gumi yake Duk da sanyin ac dake cikin office d'in daman ance komai nisan jifa k'asa xai dawo


********
Yana xaune a office d'in shi gaban shi wata er K'aramar computer ce yana jujjuya wa akan kujerar duk abin da Alhj salisu ya ke fad'a da wayar da yayi da yaran shi xuwa kiran da yayi wa Alhj lawan shana duk ya gansu kuma ya jisu wani murmishin mugunta ya saki MG abduljabbar kenan

Tun da yaxo abuja ya fara bincike akan Alhj salisu har kaduna sai da yaje sau biyu company nin su nauwara da ya koma nashi ta k'arfi da yaji yaje toh da yake kusan duk ma'aikatan ba k'aunar Alhj salisu suke ba saboda rashin mutuncin shi da mugunta yasa shi abduljabbar bai sha wahalar samun had'in kan su ba amman mutum d'aya hankalin shi ya fi kwanta wa dashi ya fada mishi abin da yake so aikuwa nan take ya amince shine ya bashi er na'urar nan yasa ta a Office d'in Alhj salisu da guest house d'in shi don yasan duk motsin shi da abin da suke shirin aikatawa don yafi son ya samu kwararan hujjoji a hannun shi Kafin a shiga kotu

Wayar shi ya d'auka yayi Kira ba'a dad'e ba wasu yaran shi joseph driven shi da wani suka shigo office d'in kallon su yayi tare da yi musu magana da abin da yake so suyi mishi sannan yace
"yanxu xamu shige kaduna bana son wasa da shirme duk abin da na tsara haka xaku bi"
Lokaci d'aya suka had'a baki wajen cewa
"okay boss "
daga hka suka juya suka fita shima abduljabbar mik'e wa yayi ya fita daga office d'in , mota ya shiga su joseph suma suka shiga Joseph yayi wa motar key suka d'auki hanyar kaduna

Yana fitowa daga masallacin da yayi sallahr isha'e shi da wannan d'aya daga cikin ma'aikatan Alhj salisu mota suka shiga inda su joseph suke ciki shi ya nuna musu hanya har guest house d'in Alhj salisu a farkon layin suka yi parking Abduljabbar ya sallami wannan mutumin mai suna yusuf da kud'i masu yawa tare da yi mishi Godiya sosai sannan kuma yana buk'atar yaje kano ko akwai wani abin da xa'a buk'ata yayi mishi alkawarin Insha Allah xai xo Sannan suka rabu Duk wannan binciken da abduljabbar yake su abba basu da labari

en maganganu suka yi da su joseph sannan ya fito daga motar shi kad'ai ya nufi guest house d'in ya tunkare shi ba shakkar komai a tattare dashi abin da ya d'aure min kai ganin mai gadin ya bud'e mishi get har da gaida shi cikin girmamawa nace Lallai abduljabbar ya siyi shi kenan kai tsaye inda nauwara ta ta6a xuwa har ta la6e ta saurari hirar su shi ma nan ya tsaya yaji duk shirye shiryen da suke don ganin asirin su bai tonu ba bayan sun gama maganar tasu Alhj salisu da Alhj lawan shana sai hajia binta suka fita daga falon suka bar yaran nasu su 3 a gidan

Wayar shi ya d'auko yayi wa su joseph waya ba 6ata lokaci suka shigo gidan bayan sunyi parking d'in motar su a wajen gidan kai tsaye falon suka shiga xumbur wad'annan yaran Alhj salisu suka mik'e tare da janyo makamin da yake jikin su babu alamar tsoro a tare da abduljabbar da su joseph suka nufi inda suke wani naushi suka yi musu a ciki nan take suka xube a k'asa cikin matuk'ar gala6aita sannan suka janyo su har gurin motar su ka shigar dasu kai tsaye a cikin Wannan daren abuja suka nufa

Washe gari da mummunan labarin 6atan yaran shi suka tashi don hka duk sun bi sun firgice saboda sune suka san sirrin gaba d'aya kuma Idan suka sha wahala xasu iya tona musu asiri Lallai Wannan karan shegiyar yarinyar nan (wato nauwara)  da babban shiri ta xo Cewar Alhj salisu kenan nan suka fara binciken inda yaran shi suke da kuma Inda nauwara da saleem suke


6angaren su abba sun gama shirin su sai jiran ranar shiga kotu duk sun Duk'ufa da addu'a Allah ya basu nasara akan Alhj salisu sun samu barrister wanda yasan aikin shi sosai shima yana nashi binciken cikin K'warewa irin ta aikin shi


******
Ranar monday xa'a fara xaman kotu duk wani wanda ya kamata ya hallara a kotun an hallara waje ya cika yayi makil da  jama'a don sauraran wannan k'ara mai cike da cin amana tsantsa da xalinci

A wannan rana Alhj salisu yayi nadamar abin da ya aikata sau ba adadi musamman lokacin da ya tsaya a gaban kotu gashi suka had'a ido da ammi nauwara saleem da kuma inna da baffah mahaifin shi duk jikin shi yayi matuk'ar yin sanyi bai ga alamar samun nasara ba sam

Toh dai a Wannan xaman da aka yi ba'a samu wasu kwararan hujjoji ba saboda su nauwara basu da wata karfaffiyar hujjar su akan Alhj salisu don hka kotu ta d'aga k'arar xuwa 2 weeks masu xuwa

Haka aka tashi daga kotun abin da ya ban mamaki shine me ya hana abduljabbar xuwa bayan shi yake da kwararan hujjojin a hannun shi ......


Aishat A muh'd
[25/07, 09:56] Aishat A. Muhd: 🍀🍀☘☘🍀🍀
 *K'ARSHEN WAHALA*
🍀🍀☘☘🍀🍀



*written by*
Aishat A muh'd


*~Pg 81~*



  Acikin satin nan biyu da aka basu xasu koma kotu sun Duk'ufa da addu'a sosai tare da cigaba da bincike toh duk wasu binciken da suke basu samu wasu hujjoji ba don gaba d'aya Abduljabbar ya bi ya tattara su a wajen shi kuma bai sanar da kowa ba kuma yak'i xuwa har yanxu

Har aka sake shiga kotu xama na biyu babu wasu kwararan hujjoji kan dukiyar su ce tunda ga takardun duk dukiyar su nauwara but sunan Alhj salisu ne akai balle axo batun shi yasa aka k'ona gidan su har safah ta mutu da mai gadi don hka barrister di'n su nauwara shi ya nemi alfarmar a sake d'aga k'arar en jarida sosai sun taru a wajen suna d'aukan rahoton wannan Shari'ar mai matuk'ar d'aure kai da ban mamaki

Wani murmishin mugunta Alhj salisu yayi lokacin da suka had'a ido da nauwara wajen da take ya nufa duk da ta tsorata da ganin hakan amman hka ta dake ta tsaya wani d'an iskan kallo yake yi mata yace
"Wato ke ga shegiyar mara kunya koh, da ni xaki ja uban ki ma na cikin kabari yayi Kad'an balle ke "
Sauke numfashi yayi sannan ya cigaba da cewa
"nasan xanyi nasara kuma ki shirya mutuwar ki ke da saleem kuma sai na auri uwar ki Kina kallo Kafin ki mutu shegiya ke ga mai taurin kai xanga uban da ya tsaya miki "
"Hahahaha loser "
Yatsine fuska tayi sannan ta dalla mishi harara tare da cewa
"wlh kayi Kad'an sai naga bayan ka mugu axxalimi kuma da kake cewa sai ka kashe ni *a rayuwa da mutuwa a hannun Allah take* sau nawa kake yunkurin kashe mu Allah bai yi ba daman ance *d'an hakin da ka raina shike tsone maka ido* kuma Insha Allah sai na tsone maka idanun ka gaba d'aya da ikon ubangiji ai xalinci baya dore wa maci amana butulu"
Sam bai yi mamakin abin da nauwara tayi mishi yasan xata fad'i abin da yafi hka ma ba K'aramar mara kunya ce ba maganganin ta sun 6ata mishi rai amman da yake d'an duniya ne sai ya maxe Ya nuna ta da hannu yace
"xaki gani? "
Murgud'a mishi baki tayi ita ma tace
"xa dai ka gani wlh "
Tana gama fad'in hka taja tsaki tare da juyawa ta tafi abin ta shima tsakin yaja tare da cewa
"yanda na kashe uban ki har lahira kema Hka xaki bishi "
Yana gama fad'in hka ya juya ya shiga mota suka tafi, kash! rashin sani yafi duhu inji malam bahaushe da yasani bai kula nauwara ba har sunyi magana haka ba saboda d'an leken asirin abduljabbar yana gefe yana d'aukan su video a waya ya tura wa abduljabbar ta what's app sannan ya tafi

Hka su nauwara suka koma gida cikin rashin k'warin gwiwa amman sun sake damarar sake bincike na sosai

Bari na waiwayi 6angaren abduljabbar naga ko me yasa yak'i xuwa


*******

 Yana xaune kan kujera yana sanye da white d'in three quarter da maroon di'n riga mara hannu irin ta shan iska fuskar nan tashi d'auke da Murmishi laptop d'in shi tana kan kafar shi yana sarrafa ta cikin kwanciyar hankali yana kur6an xaxxafan coffee yana kallon duk yanda ta kasance a kotu yana d'an murmishi wani lokacin har d'an darawa yake Idan yaga yanda Alhj salisu yake hararar nauwara yana jifan ta da kallon  tsana k'arara

Shigowar message yaji a cikin d'aya daga cikin wayoyin shi dake xube a gefen shi hannu yasa ya d'auka ya bud'e password d'in wayar sannan ya duba cikin what's app nashi yaga videon aka turo mishi bud'e wa yayi ya nutsu yana kallo murmishin mugunta ya saki tare da furxar da wani xaxxafan huci a hankali yace
"d'an iska xaka san baka da wayo wlh dole wannan Karon na uku na bayyana don na nuna maka kai k'aramin k'waro  ne "
D'an turo ya saki tare da rufe laptop d'in shi ya d'an kwanta kan kujerar yana kallon wani film a mbc 2 wanda suke yanxu mai suna death race

Lokacin da suka xo da yaran Alhj salisu abuja da farko k'in fad'in komai suka yi sai da suka ji wahala kamar xasu mutu sannan suka fad'i komai sosai abduljabbar ya gigita da jin wannan  rashin imanin irin na Alhj salisu kuma suka yi alk'awarin fad'in gaskia a kotu amman duk da hka sai da abduljabbar ya gwara musu kawunan su saboda tsabar 6acin rai tuni suka suma saboda tsabar axaba maimakon a k'wara musu ruwan sanyi su farfad'o amman ina ruwan xafi abduljabbar yasa aka xuba musu sai da yaga sun farfad'o sannan ya fita daga d'akin duk sunyi bak'i sun rame tsabar axabar da suka sha

Kuma yana sani yak'i halartar kotun don ya fison su d'an sha wahala sannan ya bayyana don a ganin shi yanke hukunci lokaci d'aya basu sha d'an wahala ba baxai yi mishi  kyan gani ba kuma ya fison sai Alhj salisu ya sawa ranshi samun nasara daga K'arshe ayi mishi kwaf d'aya

Tun ana gobe xa'a yi xaman kotu na K'arshe abduljabbar ya shigo kano dashi da amintattun yaran shi joseph da mubaraq tare da yaran Alhj salisu a d'akin da yake punishment di'n yaran shi a d'akin aka  xube yaran Alhj salisu sannan ya nufi part d'in su ya bar Joseph da mubaraq  suna gadin su duk da wajen a rufe yake


Yana shiga jiddah ta taso da d'an gudu ta rungume shi tana murnar ganin shi don ya dad'e bai xo ba don hka yana wanka aka shiga biyan bashin k'wanakin da ba'a tare, ranar yini yayi a gida yana huta wa tare da xuba soyayya da jiddah yinin farin ciki yayi ba wanda yasan yaxo Kano saboda ya fison su had'u a kotu gobe.....
Washe gari misalin wajen karfe 10 na safe kotu ta cika da mutane ga en jaridu suma kallo d'aya xaka yiwa su Alhj salisu kasan suna cikin tsantsar farin ciki wannan Karon har da hajia binta matar Alhj salisu da baban ta Alhj salisu har da ladi (wadda Alhj salisu ya kai ta gidan su nauwara don ta dunga yi musu aiki a xahiri)

Su nauwara kuwa duk jikin su a sanyaye Har da barrister di'n don basu da wata shaida mai k'arfi sai kame kame amman duk da hka basu karaya ba sun dogara ga Allah sai addu'a suke a cikin xuciyar su

Karfe 10 dai dai aka fara Shari'ar su nauwara nan aka shiga tafka tambayoyi tsakanin barrister di'n su nauwara da nasu Alhj salisu har xuwa lokacin da aka tattara wa alkali bayanai aka bashi duk anyi tsit ana jiran hukuncin da xai yanke

Har alkalin ya bud'e baki xai yi magana kenan aka bud'e kofar aka shigo gaba d'aya kallo ya koma kan kofar don ganin wanda ya shigo, nauwara ma da kanta yake kallon k'asa ta d'ago kanta tare da kallon kofar ganin yanda gaba d'aya mutanen cikin kotun hankalin su yayi kan kofar shigo wa.....



Aishat A muh'd
[25/07, 09:57] Aishat A. Muhd: 🍀🍀☘☘🍀🍀
 *K'ARSHEN WAHALA*
🍀🍀☘☘🍀🍀



*written by*
Aishat A muh'd


*~Pg 82~*



   Gaban ta ne yayi mugun fad'uwa ganin bayyanar Abduljabbar  sanye yake cikin kakin shi yayi kyau kwarjinin shi ya cika wa mutane kai tafiya yake cikin kasaita har ya k'araso cikin kotun gaba d'aya mutanen cikin kotun binshi suke da kallo suna mamakin mai ya kawo wannan babban sojan mai muk'amin MG kotu xama yayi tare da had'a ido da barrister di'n su nauwara ya kashe mishi ido d'aya Jijjiga kai barrister yayi tare da sakin wani murmishin mugunta (na ce toh shi wannan abduljabbar d'in sai kace wani aljani yana abuja har yasan barrister di'n da xai tsaya wa su nauwara)

A karo na biyu alkali ya gyara xaman glass d'in shi a ido ya bud'e baki xai yi magana kenan barrister kabeer Ya nemi alfarmar xai gabatar da hujjar shi ta K'arshe nan barrister di'n su Alhj salisu yak'i yarda da hakan amman ina har alkalin ya bashi wannan favour di'n xama yayi cike da takaice ya kallo abduljabbar ai kuwa ya kashe shi da killer samiling sai da yaji d'an tsoron abduljabbar kuma yana kula da kashe idon da yayi wa barrister kabeer

Nan fah ya shiga gabatar da hujjojin shi har da  bawa nuna jakar da nauwara ta yarda da ita wanda Kaf takardun dukiyar su yana ciki nan alkali ya kar6a ya ajiye a gefen shi lokacin da nauwara ta ga jakar nan sai da gaban ta ya fad'i saboda tsabar farinciki don ta tabbatar xa'a samu hujjoji akanta

Ta 6angaren Alhj salisu sun d'an fara tsorata musamman yanda suka ga lawyer di'n su ya kasa ta6uka komai basu k'ara tsinken wa ba da al'amarin sai da suka ga Shigowar yaran su a matuk'ar gala6aice saboda tsabar firgita sai da Alhj salisu da hajia binta suka saki fitsari a tsayen sai jin Fitowar shi suka yi yana bin kafafun su tuni jikin su ya fara rawar shoki

Wani murmishin mugunta abduljabbar ya saki da ya Kalli su Alhj salisu yanda suka kid'ime tare da gigicewa rashin gaskiya ya bayyana k'arara a fuskar su, babu gardama yaran Alhj salisu suka bayyana komai tun daga lokacin da suke bibiyar Alhj sa'eed don su kashe shi basu yi nasara ba sai lokacin da xai je kano wurin aminin shi suka markad'e su a mota sannan suka sace ammin su nauwara suka sawa gidan wuta don su nauwara su mutu sai kuma d'aya ce ta mutu ya umarce mu da mu binciko sauran mu kashe su da muka gansu sai muka bi ta kansu da mota muka gudu............. Duk suka sanar da komai

Gaba d'aya kotun tayi shiru sai shashshak'ar kukan mutane saboda tsabar tausayin su nauwara bayan sun gama fad'in komai su Alhj salisu Alhj lawan shana da hajia binta ladi suka fara ihun cewa k'arya suke musu sharri ne

Wani kallo da abduljabbar ya watsa musu sai da sukayi shiru ba shiri don ba k'aramin kwarjini yayi musu ba K'arshe kuma da kanshi abduljabbar ya nuna wa alkalin videon da Alhj salisu yake fad'a wa nauwara xai kashe ta ita da saleem kamar yanda ya kashe mahaifin su da safah kuma sosai alkalin ya aminta da hkan ya kuma duba takardun dukiyar su nauwara da ta Alhj salisu yaga tasu nauwara itace ta ainahin gasken nan aka tattara komai aka mikawa alkali ana jiran hukuncin da xai yanke

Abba umma ammi aunty sadiya nauwara saleem FA'iza aunty asma'u aunty kausar abdulkareem da aunty maryam matar abdulkareem gaba d'aya sun daskare a wajen tsabar dumbin mamakin abduljabbar daman yana da hujjoji a hannun shi shine ya barsu suna faman shan wahala a banxa harara umma da abba suka dalla mishi lokacin da suka had'a ido murmishi kawai yayi musu yana shafa lallausan gashin kan shi
6angaren su Alhj salisu baxan iya fad'a muku irin tashin hankalin da suke ciki ba gaba d'aya a firgice suke kamar ace kat su xura da gudu sai faman rarraba ido suke ga gumi ya gama jika musu jiki sai muxurai suke kallo d'aya mutum zai musu ya hango rashin gaskia k'arara a fuskar su jikin su sai rawar shoki suke

Daman ance komai nisan jifa k'asa xai dawo rana dubu ta 6arawo rana d'aya ta me gaskia, Idan xaka gina ramin mugunta gina shi dai dai da kae watakil ka fada cikin shi gashi su Alhj salisu sun gina shi fiye da tsayin su gashi sun rufta cikin  shi

Baffah haruna da inna habiba sunyi kuka sosai d'an uwan ka ya kashe ka ya tarwatsa maka iyalai har ya nemi kashe su don duk wai *Adalilin son* matar shi da dukiyar shi,  dukiyar da xaka mutu ka bar su a duniya, kunyar duniya ta ishi inna larai wato mahaifiyar Alhj salisu matar Baffah haruna tayi nadama sosai kuma duk batasan salisu ya aikata hakan ba


A cikin nutsuwa da kamala irin ta alkalan da suke yanke hukunci tsakani da Allah babu corruption nd bribery acikin xuciyoyin su ya fara da nasiha Kafin ya gangaro kan tabbatar da dukiya tasu nauwara ce kuma an mayar musu da abarsu sannan aka ci tararar su Alhj salisu na tsorata su nauwara da niyyar hallaka su da kuma B'uye ammi da yayi sannan daga K'arshe daman ance K'arshen tika tiki tak aka yanke wa su Alhj salisu Alhj lawan shana da hajia binta ladi da kuma yaran su masu taimaka musu wajen aikata munanan laifuka aka yanke musu hukunci dai dai da laifin kowa a cikin su

Wani raxanannen ihu hajia binta ta saki tare da d'ora hannu ta a saman kanta nan wasu mata en sanda suka cafke ta tare da xura mata anka a hannun ta Hka ma su Alhj salisu aka tura k'eyar su

Nan kotu ta tashi su nauwara sun samu nasara daman duk wanda ya dogara da Allah baxai ta6a ta6ewa ba a rayuwar shi nan suka suka fito wajen kotun mutane sai faman taya su murna ake suna mai la'antar masu hali irin nasu Alhj salisu en jaridu sunyi musu caaa suna xuba musu tambayoyi nauwara maganar mintuna 2 ta iya magana da wani nacaccen wani d'an jarida da yasa ta maganar da bata shirya yin taba

Rungume juna nauwara ammi da saleem suka yi suna kukan farinciki yau saboda tsabar farinciki sai da nauwara ta rungume abba tana xuba mishi godia

Kallon wajen dasu Alhj salisu nauwara tayi wadanda ake kok'arin tura su a mota cikin wata tafiyar kasaita ta K'arasa wajen da suke sai da taxo gab dashi tana murmishin mugunta tace
"Ya akayi na baka kunya na tuna asirin ku duk dukiyar da kake da ita yau kaine sanye da anka xaka yi xaman prison Kafin a rataye ka ka mutu har kana ikirarin sai ka ga bayan mu an gaya mata mutanen da suka dogara da Allah xasu ta6e "
Kallon shi ta sake yi tana d'aga mishi gira ran shi idan yayi dubu ya 6aci kallon Alhj lawan shana da hajia binta da ladi tayi tukunna tace
" K'aramar yarinyar  da ka raina yau gashi ta shayar dakai mamakin da baka ta6a tsammani ba a rayuwa ka ba, baxan ta6a yafe maka ba *wata Shari'ar ma sai a lahira* Kad'an ka gani wannan iya na duniya ne ma"

Kallon ta yake cikin 6acin rai Kafin ta rufe bakin ta taji wata mummunar shak'a a wuyan ta tuni idanun ta sun firfito saboda tsabar wahala dakyar ta ke iya jan numfashi kallon shi tayi fuskar ta cike da wani irin murmishi da ni kai na na kasa gane murmishin da nauwara take
"Kafin na mutu bari ki fara mutuwa don uban ki ai nayi alkawarin sai na kashe ki da hannuna shegiya tsinanniyar yarinyar "
Tuni mutane sun taro wajen ana kok'arin ceton nauwara amma ina yak'i cikata duk da dukan da en sanda suke mishi da kulkin hannun su

Su umma sai kuka suke ganin yanda har nauwara ta fara lumshe idanun ta ga jini ya fara xuba ta hancin ta da  bakin ta

Ihun da ake a wajen ya janyo hankalin abduljabbar da yake cikin office d'in alkali suka fito da gudu ganin abin da yake faruwa a guje abduljabbar ya ratsa cikin mutanen  da suka taru ya kai wa Alhj salisu wani wawan naushi a fuska tuni jini ya soma xuba a bakin  shi amman don taurin kai yak'i ya saki nauwara don so yake ya kashe ta
Ganin bai sake ta ba kuma Idan yace xai kwakule hannun shi a wuyan nauwara xai ji mata mummunan ciwo yasa abduljabbar d'auko pistol di'n shi ya saita kafar shi ya harbe shi wata k'ara ya saki amman yak'i cika ta abin ba k'aramin mamaki da tsorata mutanen wajen yayi ba Lallai ba k'aramin k'iyayya yake nuna wa nauwara banaushi ta ko'ina ya dunga kai mishi ba shiri ya sake ta don axabar dukan da abduljabbar yake mishi

Fad'uwa nauwara tayi a jikin umma da ammi jiki a sake ko motsi da numfashi bata yi cikin wata raxannaniyar k'ara ammi tace
"Shikenan ya kashe min itaaaaa"

Ta fad'i tana girgixa nauwara kuka sosai ammi take Abduljabbar fah allurar sojoji ta motsa dukan Alhj salisu yake ta ko'ina kuma ba wanda yayi yunkurin hanashi amman kuma abin mamaki murmishi ya saki yana kallon nauwara yace
"ka kashe ni tunda na kashe ta daman buri na na K'arshe na kashe tsinanniyar yarinyar nan "
A fusace abduljabbar ya bashi wani naushi a cikin shi lokaci d'aya ya saki k'ara ya xube a wajen a sume shi ma

Da gudu yayi kan nauwara cak ya d'auke ta suka nufi asibiti sai ruwa suke  xuba mata tare da girgixa ta suna ambatar sunan nauwara amman ko motsi Bata yi jikin ta ya saki yayi sanyi qlau kamar mataccaciya



_kuyi hak'uri da wannan wlh ban da lafia ne_



Aishat A muh'd
[25/07, 09:57] Aishat A. Muhd: 🍀🍀☘☘🍀🍀
 *K'ARSHEN WAHALA*
🍀🍀☘☘🍀🍀


*written by*
Aishat A muh'd



_this page dedicated to fateen soja ( *Mr's umar*) Allah ya baki ikon kammala littafin ki lafia hak'ik'a littafin maxa da mulki mata da tak'ama yayi sosai Allah ya k'ara basirah Ameeen, ina yi miki fatan alkhairi a duk inda kike_


*~Pg 83~*


 Suna isa asibitin da gaggawa aka shige da nauwara emergency room don bata agajin gaggawa tana cikin tsaka mai wuya *mutuwa* ko *rayuwa* su umma suna wajen room d'in a tsaitsaye suna jiran Fitowar doctor duk hankalin su a tashe yake

Yini guda cur likitoci suna kan nauwara amman har yanxu bata farfad'o ba su kansu likitocin Sun tsorata da hakan Duk jikin su yayi sanyi sun rasa ta inda xasu fara yiwa wannan family d'in bayanin halin da nauwara take ciki daga K'arshe dai babban likitan shi ya nemi abba abduljabbar sai abdulkareem don iya maxan xai iya d'aure wa ya fad'a musu halin da nauwara take ciki

Bayan sun xauna cikin sanyin jiki yace " a gaskiya munyi duk iya kok'arin mu don ganin ta farfad'o amman hakan ya gagara xuwa gobe har Indai bata farfad'o ba toh sai dai ku fitar da ita wata k'asar tana cikin hatsari don xata iya rasa ranta a kodayaushe duk da *rayuwa* da *mutuwa* suna hannun Allah "
Kafin doctor ya rufe bakin shi abduljabbar ya Cakumo wuyan rigar shi cikin tsananin tashin hankali da 6acin rai cikin d'aga murya yace
"k'arya kake baxa ta mutu ba, shine don wulakanci kana ganin yanda muka yini ana abu d'aya maimakon ka fad'a mana baxa ka iya komai ba kana wahalar da mu da kan ka"
Nan ya cigaba da masifa doctor kuwa gaba d'aya idon shi ya firfito saboda shak'ar da abduljabbar yayi mishi dakyar ya ke fitar da numfashi jikin shi sai rawar shoki yake saboda tsabar tsorata abba ne da abdulkareem suka kwaci doctor dakyar daga hannun abduljabbar a xuciye ya fice daga office d'in

Tari sosai doctor yake yi abdulkareem ne ya bashi ruwa yasha sannan ya tarin ya lafa sai sannu suke mishi cikin murmishin yak'e yace
"it's okay don't worry yalla6ai "
Ya fad'a yana shafa wuyan shi tare da d'an jujjuya shi su abba suka k'ara yi mishi sannu sannan abba yace
"toh mene mafita doctor sannan wacce k'asa ya kamata mu kaita??? "
Sai da yasa d'an hankicif ya goge gumin fuskar shi xuwa wuyan shi sannan yace
" mafita sai dai nace kawai ku fitar da ita waje saboda sun fimu kwararrun kayan aiki acan, ku xa6i London suna da kwararrun ma'aikata acan sosai kuma da akwai wani friend d'ina doctor acan xan had'u ku dashi Insha Allah xa'a dace ku kwantar da hankalin ku Allah ya bata lafia"
"Ameeen doctor mun gode"
Nan suka bar office d'in suka dawo wajen su umma bayani suka yi musu tare da kwantar musu da hankali sannan suka fita don neman visa xuwa London a corridor di'n wajen asibitin suka had'u da abduljabbar yana faman safa da marwa ko Inda yake Abba bai kalla ba ya shige mota har abdulkareem xai tafi wajen shi abba ya watsa mishi harara Hka ya hak'ura ya shiga mota ya jasu

Abin da abba yayi mishi ya masifar dad'a 6ata mishi rai yaja wani matsiyacin tsaki yace
"toh wai ina ruwana da ita ne da xan damu da ita yarinyar da ta yaudare ni taci amanata ai bai kamata na nuna jin tausayi na akanta ba"
Mtsww ya k'ara Jan saki ya nufi wajen motar shi direct gidan shi ya nufa ran shi a 6ace toh anyi sa'a jiddah tana gida fito war ta daga toilet kenan aikuwa kai tsaye ya nufi inda take cikin tsoro take ja da baya tana cewa
"sojana ya akayi ne lafia kake??? "
Hannu yasa ya fisgo ta jikin shi yana mata wani kallo da rinannun idanun shi bai tsaya 6ata lokaci ba ya fara bin ta da xaxxafan remonce cikin salon da yake hargitsa tunanin jiddah dole kuwa ta bada kai bori ya hau don bata da yanda xata yi...


A 6angaren su abba sunyi nasarar samun visa xuwa london umma ammi da abba abdulkareem sai nauwara da twins na'eem da ameer don hka acikin wannan daren sun gama had'a komai wanda xa'a buk'ata likitan ya had'a su doctor da xasu je gunsa

Karfe 9 na safe jirgin su nauwara ya d'aga xuwa london suka bar da addu'ar Allah ya sauke su lafia Allah ya tashi kafad'un nauwara fa'iza ansha kuka sosai dakyar ta cika nauwara abba yayi mata alk'awarin Indai ta farfad'o xai dawo nnigeria xai sa asama mata visa ta taho ita ma hakan ya d'an sanyaya xuciyar  ta

Alhmdullilah sun sauka k'asar London lafia ambulance di'n hospital ce taxo ta d'auki  nauwara yayin da doctor d'in nan bahaushe ne d'an nigeria sunan shi doctor muh'd Abdullah matashin saurayi ne hadadden guy wanda ilimin addini dana boko suka ratsa shi nutsatstsan mutum shine ya d'auki su abba a motar shi xuwa gidan shi don yak'i yarda su sauka a hotel a matsayin su na en nigeria tushen da fito kuma en garin kano wanda haifaffen can ne mahaifan shi suna xaune a unguwar janbulo
su abba sun ji dad'in irin wannan karamcin na doctor muh'd Abdullah girmama su yake sosai yake a matsayin su na manya sai da ya wadata su da duk abin da xasu buk'ata sannan ya tafi asibitin
Nan ya shiga room d'in da aka kwantar da nauwara da shi da wani baturen doctor suka shiga gudanar da binciken nauwara

Toh Alhmdllh cikin k'wana 2 da xuwan London nauwara ta farfad'o har tana gane wad'anda suke kanta sai dai tayi mugun wani fari ta rame sosai da hka sauk'i yake samu wa  a hankali Sati d'aya abba yayi ya koma nigeria sannan fa'iza ta taho cike da d'okin ganin nauwara

A cikin k'wanakin nan 8 da xuwan su london nauwara da doctor muh'd Abdullah sunyi wata iriyar matuk'ar shakuwa da junan su xai 6ata lokacin shi yana bata labarai masu dad'in gaske da ban dariya tayi ta dariya cike da tarin farinciki gashi jinin su ya had'u da na'eem da ameer yana bala'in k'aunar su sosai sai ya dauke su ya fita dasu wajejan shakatawa suma twins d'in sun saba dasu sosai

Babu wanda yasan abduljabbar yaxo london don jinshi yayi baxai iya xama har su dawo 9ja ba bai ga nauwara ba shine ya taho har asibitin yana da address d'in shi don hka kai tsaye asibitin ya nufa har room d'in da aka kwantar da nauwara har xai shiga  d'akin yaji sautin dariyar ta don hka ya fasa shiga ya lek'a ta window abun da ya gani ba k'aramin gigita shi yayi ba nauwara ya gani xaune kan bed d'in asibitin doctor muh'd Abdullah kuma yana xaune kan kujera dab da ita yana fuskan tar ta ya xuba mata ido yana bata labari masu dad'i ita kuma tana er dariya cike da sha'awa hannun ta rik'e da cup d'in tea tana kur6a  a hankali garin dariyar sai d'an tea d'in ya xuba a hannun Kad'an er k'ara ta saki da sauri ya kar6e cup d'in ya ajiye sannan ya rik'e mata hannu yana duba mata wani shock suka ji lokaci d'aya a jikin su da sauri ta xame hannun nata duk ya rud'e sai sannu  yake mata a d'an kunya ce take amsa wa
Wayyo Allah xan so kuga yanda fuskar abduljabbar ta koma lokaci d'aya jikin shi har rawa yake saboda tsabar kishi tabbas a yau ya yarda da abin da nauwara ta aikata ba sharri ba ne halin tane don hka dole ya d'auki mataki baxai iya sake xaman rayuwar da ita ba ya hak'ura da ita har abadaaa a matuk'ar fusace ya fito daga asibitin a ranar ya juya xuwa nigeria har ya sauka daga jirgi jikin yana tsuma saboda tsabar kishi yana sakkowa daga jirgin ya kunna wayar shi message ya fara tura wa nauwara yace
" _I hate yhu! I hate yhu!! I really hate yhu nauwara!!!_"

Tana xaune ita d'aya doctor muh'd Abdullah ya fita xuwa duba patient taji Shigowar message duba wa tayi taga number d'in abduljabbar gaban ta ne ya fad'i da sauri ta bud'e ta karanta Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun abin da nauwara ta iya fad'i wasu xafafan hawaye suka xuba a fuskar ta amman sai ta rubuta ta mishi reply da cewa
" _thank u so much Abban na'eem da ameer_"
Ta tura mishi tare da kwanciya ta dafe kirjin ta da yake buga wa da k'arfin gaske hawaye ne kawai suke xuba a idon ta
lokacin da ya duba message d'in nauwara ya karanta ba k'aramin sake harxuka shi yayi ba sai kawai yabi sharrin xuciya da hud'ubar shaitan hannun shi ya fara rubuta
" _Na rabu dake har abada nauwara na sake ki saki d'aya kije kiyi rayuwar da kike so nayi da na sanin xa6ar ki matsayin masoyiya ta uwar 'ya'ya na I hate yhu_"
wasu hawaye ne masu xafin gaske suka fito daga idanun shi ya kurawa rubutun ido kamar ya tura kamar kada ya tura batare da sanin shi ba hannun shi yayi sending d'in message d'in ya tafi
Can kuma kamar mintuna uku ya dawo hayyacin shi ya duba yaga abin da ya rubuta saboda tsabar kad'uwa baisan lokacin da ya saki wata er k'ara ba had'e da d'ora hannu akai girgixa kai yake yana cewa " noooo nauwara ba nufi na Hka ba ina sonki a kowanne hali kika shiga wannan abin kuskure ne da sharrin xuciya da hud'ubar shaitan tare da kishin ki ya sani rubuta Hka ban shirya ba "
Dak'yar ya iya shiga mota drive yaja shi sai gida yana shiga part d'in jiddah xai shiga bedroom d'in ta kenan yaji maganar da take yi abin da yaji ba k'aramin kid'ima shi da gigita shi ya sake yi ba cikin wani irin yanayi da fusata ya banko kofar bedroom d'in nata......


Aishat A muh'd
[25/07, 09:57] Aishat A. Muhd: 🍀🍀☘☘🍀🍀
 *K'ARSHEN WAHALA*
🍀🍀☘☘🍀🍀



*written by*
Aishat A muh'd



_Wannan shafin sadaukar wa gare ki nafeesat anka naji dad'i da nuna kulawar ki a gare ni ina miki fatan alkhairi Allah ya bar xumunci ameeen_



*~Pg 84~*


Abin da yaji lokacin da xai shiga d'akin jiddah waya take da farida kawar ta tana cewa
" ni fah har yanxu buri na bai cika ba tunda bai sake shegiyar yarinyar nan ba duk da sharrin da muka had'a mata na tura wani d'akin ta matsayin d'an iskan da suke watse wa Wlh na d'auka lokaci d'aya xai dankara mata saki har uku gashi har ta haifa mishi twins ina tsoron ya dawo da ita gidan nan na tsani er iskar yarinyar nan "
Abin da yaji kenan ya banko kofar da k'arfi har jiddah ta tsorata a firgice ta mik'e tsaye ganin yanda ya koma lokaci d'aya ita bata ta6a ganin shi a irin wannan yanayin ba amman ta maxe tace
"sojana xuwan yaus........ "
Kafin ta K'arasa fad'in "yaushe" ya kwashe ta da wani mugun mari Kafin ta dawo hayyacin ta ya sake bata wani daga nan ya fara ball da ita da kafar shi tana ihun kuka tare da bashi hak'uri belt d'in jikin shi ya cire ya fara tafkar ta son ran shi yana cewa
"jiddah kin cuce ni kin raba ni da nauwara daman sharri kika k'ulla mata xaki yi bayani duk abin da kike min ban ta6a d'aukar mataki ba a kanki amman wannan Karon xan baki mamaki wallahi"
Sai da yayi mata lilis ko motsi bata iya yi balle kuka sai faman ajiyar xuciya take saki tsugunna wa yayi dai dai kan ta yace
"na tsane ki jiddah kin raba ni da sanyin idaniya ta muradin rai na kije kema na sake ki baxan iya xama da ke ba"
Wani irin ihu ta saki Duk da muryar ta bata fita sosai bai kula ta ba ya janyo ta tun daga upstairs har k'asa xuwa farfajiyar gidan ya watsa ta a bayan mota sannan ya kirawo Joseph ya fad'a mishi ya kai jiddah gidan su sannan ya wuce cikin gidan xuciyar shi kamar xata tarwatse saboda yanda take bugu yana shiga cikin d'akin shi ya fara jifa da komai na d'akin yana fasa su tuni d'akin yayi kaca kaca duk ya yanke a hannun shi fuskar shi ta yi jawur da ita hannun shi yasa cikin lallausan gashin kanshi yana yamutsa shi ya rasa inda xai sa kanshi yaji dad'i
Bayan ya gama tarwatsa komai na d'akin a k'asa gefen bed ya xube yana wani irin shashshak'a idanun shi sunyi matuk'ar yin ja can kuma suka fara xubar da wasu xafafan hawaye suna sauka kan face d'in shi Allah sarki abduljabbar ya bani tausayi sosai  yanxu mai xai cewa nauwara da wani ido xai kalle ta har ya bata hak'uri shi yasa ake son mutum ya dunga bincike Kafin ya aiwatar da abu kada yaxo yana da nasani wani xaxxafan xaxxa6i ne ya  rufe shi tuni ya fara karkarwa hannun shi ya mik'a ya d'auko picture d'in nauwara tayi kyau sosae tana sanye da english wears tana er dariya mai ban sha'awa duk dimple d'in ta biyun sun lotsa baisan lokacin da ya saki wata er k'ara irin wanda mutum ya shiga cikin mugun damuwa yayi rungume photon yayi a kirjin shi yana wani irin kuka kamar ba soja ba kodan so ba ruwan shi

Lokacin da joseph Yayi parking a kofar gdn su jiddah dakyar ta iya fito wa ta shiga gidan duk jikin ta jina jina tana wani irin kuka ita duk duka nan da yayi mata bai dame ta ba irin sakin da yayi mata yaraf ta xube a tsakar gidan nasu da sauri mamee ta k'araso inda take hankalin ta a matuk'ar tashe ta d'ago ta cikin kid'ima da ganin yanda Jiddah ta koma duk fuska a kumbura yasa tace
"lafia jiddah me yafaru wane yayi miki hka??? "
Jiddah ba baki dole Hka ta hak'ura ta had'a ruwa mai d'umi ta gasa mata jikin ta sannan ta bata paracetamol ta kora sannan tace
"kiyi min bayani jiddah wane yayi miki hka"
"Abduljabbar ne? "
Nan take mamee ta had'e rai sai da gaban jiddah ya fad'i tace
"me ya had'a ku ki fad'a min gaskia bana son k'arya "
"wai wai akan hmm....."
Ta kasa K'arasa fad'i saboda tsoro batasan wanne irin abu mamee xata yi mata ba Idan taji abin da ta aikata kuma dole ta fad'i gaskia ko don ta samu ta roki mamee tasa Abduljabbar ya mayar da ita baxa ta iya rayuwa babu shi ba tayi nadama kuma irin wadda ake so baxa ta k'ara gigin aikata hkan ba ta tuba tsawar da mamee ta daka wa jiddah shi ya katse mata tunanin da take yi harara ta watsa mata sannan tace
"kin xaunar dani ke fah nake jira??? "
Tsugunna wa tayi a k'asa ta rik'e kafafun mamee cikin kuka ta fara rokan ta ta yafe mata kuma wallahi ta tuba baxa ta k'ara ba nan ta kwashe komai ta fad'a wa mamee tun daga lokacin da farida ta bata shawarar ta kai wani d'akin nauwara matsayin tana aikata fasikanci da maxa don abduljabbar ya sake ta har xuwa yau da asirin ta ya tonu yayi mata sannan uban dukan tare da yi mata saki bata rufe bakin ta ba mamee ta dalla mata mari har biyu Sannan ta fashe da kuka tana cewa
"ashe duk abin da kika aikata a baya jiddah baki yi nadama  sai da kika kuma aikata wani kin raba mata da mijin ta saboda shegen kishin ki wallahi abduljabbar yayi min dai dai naso ma yayi miki abin da yafi hka da nasan Hkane wlh da ban kula ki ba ga Ki ga gidan sai kixo mu xauna tare kici uwar da xaki ci bari baban naki ya dawo"
Tana gama fad'in hka ta hankada jiddah ta fad'i sannan ta mik'e tsaye ta fita waje tana goge hawayen fuskar ta ta bar jiddah tana cin uban kuka a d'aki tayi nadama ta tuba kuma ba tuban muxuru ba na tsakani da Allah Indai abduljabbar ya mayar da ita xata xauna da nauwara tsakani da Allah

Baban jiddah da mamee ta fad'a mishi komai ba abin da yace kuma ko kallon jiddah Inda take bai yi ba hakan ba k'aramin k'ara tsurar da jiddah yayi ba

******

Tana nan kwance taji k'arar Shigowar message d'in takai hannu xata dauki wayar don ta duba su umma suka yi sallama suka shigo d'akin murmishin yak'e ta hau yi nan suka gaisa aka hau yin hira na'eem da ameer suna mak'ale a jikin ta umma ta kalli nauwara da ammi tace "Ohh na mance waya ta a gida ina son kiran Abba naji fa'iza ta taho kuwa"
"gaskia ya kamata a kirawo aji "
Cewar ammi "nauwara ban wayar ki na kirawo shi"
Umma ta fad'i tana mik'a hannun ta ba tare da wani abun ba ta mik'a mata kura wa screen d'in kallo umma tayi mamaki d'auke a fuskar ta ganin mssg da abduljabbar ya turo mata bud'e wa tayi a hankali ta fara karanta wa xumbur ta mik'e tsaye tana fad'in Innalillahi wa'inna ilaihir rajiu da sauri ammi da nauwara suka yo kan umma suna tambayar ta lafia amman ta k'asa magana da sauri nauwara ta d'auki wayar ta duba wa tayi ita ma ta karanta wani kuka ne ya kufce mata daman tasan ai K'arshen alewar k'asa shekara wajen uku baka xaune gidan miji sai gidan iyayen shi daman ai wannan abin ne xai biyo baya balle ga irin xargin da yake mata wayyo Allah gani gare ka ka kawo min agaji acikin wannan halin da nake ciki....


Aishat A muh'd
[25/07, 09:57] Aishat A. Muhd: 🍀🍀☘☘🍀🍀
 *K'ARSHEN WAHALA*
🍀🍀☘☘🍀🍀



*written by*
Aishat A muh'd



*~Pg 85~*



Cikin tashin hankali ammi tace "nauwara lafia me yafaru? "
Cikin kuka da takaici tace "ammi ya.... ya sake ni"
Rik'e nauwara ammi tayi tana girgixa ta "me kika ce bangane ba? "
"umma Yah abduljabbar ne ya turo min mssg ya sake ni baxai iya cigaba da xama dani ba ammi na rayuwa ta ishe ni daga wannan sai wannan Yah Allah gani gare ka "
Ta fashe da wani irin marayan kuka ammi ma sosai abin ya bige ta amman ta jure tana rarrashin nauwara da umma da take xaune ta xabga tagumi ko magana ta kasa yi saboda bak'in ciki

Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun abin da doctor muh'd Abdullah yake fad'i yana ja da baya daga jikin kofar shiga room d'in da aka kwantar da nauwara yaxo xai shiga yaji wannan labarin waje ya samu ya xauna dafe kanshi yayi idanun shi sunyi ja alamar yana cikin tashin hankali na abin da yaji wani tausayin nauwara ne ya ke ratsa xuciyar shi tashi tsaye yayi ya fita daga asibitin kai tsaye airport ya nufa don d'auko fa'iza duk da baisan ta ba amman yaga photon nan ta a wayar nauwara kuma xai gane ta

Bai sha wahalar samun fa'iza ba tana tsaye rik'e da trolly sai handbag a hannun ta tana ta faman kiran wayar umma ba'a d'auka ba hka wayar nauwara ma gaba d'aya ta d'an rud'e ko lafia sallama taji anyi mata cikin wata murya mai dad'i da sauri ta jiyo suka had'a ido da doctor muh'd Abdullah yana mata murmishi gaban fa'iza ne ya fad'i lokaci d'aya dakyar ta iya amsa mishi sallamar
"am Kece fa'iza koh sister d'in nauwara? "
Cikin mamaki fa'iza tace "Ya akai kasanni malam? "
er dariya yayi sannan yace
"ba abin mamaki ba ne don na sanki so ki kwantar da hankalin ki ba sace ki xanyi ba"
D'an hararar shi tayi tana cewa
"bansan ko kai wane ba baxan bi ka ba"
D'an ta6e baki yayi Kafin yace
"Sunana doctor muh'd Abdullah nine likitan da yake kula da nauwara "
D'an murmishi tayi sannan tace "okay yanxu suna ina? "
"Tana hospital sai ta k'ara samun sauk'i xan sallame ta "
Ya K'arasa fad'i yana rik'o trolly di'n hannun ta ya sa a mota tukunna suka shiga suna er hirar su har suka k'araso asibitin har room d'in da nauwara take ya nuna mata cikin tsananin farinciki ta nufi d'akin

Jikin ta ne yayi sanyi lokacin da ta tarar da umma nauwara da ammi acikin wani irin hali nan ta rikice ta fara tambayar abin da ya faru ammi ce tayi k'arfin halin sanar da ita fa'iza har da kukan tausayin nauwara haka ta rungume ta suna kuka


A wannan tsakanin lokacin doctor muh'd ya sallami nauwara daga asibitin ta samu lafia sosai kuma ba k'aramin kula wa yake bata ba ita da twins abin har mamaki yake ba wa su umma duk wajen wani shakatawa haka xai kwashe su ya kai su wai don nauwara kada ta kadaice ita d'aya tana tunani ya haifar mata da wata matsalar

Umma ta kirawo Abba ta sanar dashi abin da abduljabbar yayi aikuwa ranshi ya 6aci sosai anan yake sanar da ita ai nan ma ya saki jiddah tare da yi mata duka ashe ita ta shirya wa nauwara wannan makircin ita da k'awar ta mahaifin jiddah ne yake xuwa ya sanar da abban sosai umma ta yarda da jiddah xata aikata abin da yafi hka ma akan kishi

Umma bata b'oye wa nauwara da ammi ba duk da kuwa jiddah er kanwar ta ce daman fa'iza ta xargin hakan ammi kuwa bata ji dad'in sakin jiddah da yayi ba nauwara kuwa baxa ka fahimci halin da take ciki a wannan lokacin ba


*******
Jiddah sosai tayi nadamar abin da ta aikata ga shegen uban aikin da take sha a gidan itace girkin safe, tana, dare, wanke wanke, wankin kayan mamee da babanta don hka yace ya daina bada wankin shi tunda ga mai wanki Ya samu komai na gidan ita take yi tun Bata iya ba har taxo ta K'ware tayi bak'i ta rame sosai ga aikin nata ma baban nata ya soke shi

Tuni sunyi baram baram da farida a karo na biyu kenan tayi kuka sosai tayi nadama ga abduljabbar ko sake waiwaiyar ta bai ba ko ta kirawo shi baya picking sai dai ta tura mishi text mssg na ban hak'uri kullum sai ta tura mishi amman babu reply duk ta sukurkurce ta xama wata iri kamar ba jiddah ba er gayu son hutu da jin dad'i

Daga K'arshe ma wata makarantar islamia ta nema anan layin su take xuwa ta xama so silent kodayaushe kullum cikin neman gafarar ubangiji take abisa laifukan da ta aikata

Iyayen ta ma sun hak'ura ganin yanda ta shiryu sun janyo ta jikin su kulawa sosai suke bata tun da ta gane kuskuren da ta aikata gashi har da shiga islamia ita kanta yanxu tafi jin dad'in rayuwar ta fiye da baya yanxu babban burin ta na K'arshe ta nemi yafiyar nauwara sannan abduljabbar ya mayar da ita dakin ta..........


*******

Tun daga ranar abduljabbar sai da ya kusan sati bai fita konan da can ba yana kwance a d'aki rungume da photo nan nauwara ya rame ko abincin kirki baya iya ci kullum cikin tunanin ta yake

Ana cikin hka aka neme shi a wurin aiki dole haka ya tarkata ya tafi abuja ba don yaso ba to aikin da ya tarar a gaban shi kusan shi ya d'an rage mishi tunani don kusan ko dayaushe yana busy

Ya dage da addu'ar Allah ya kawo mishi mafita Ko lokacin da ya fad'a wa abdulkareem bai ji dad'in abin da yayi ba hka ya bashi hak'uri tare da rarrashin sa haka ya bar abuja cike da tausayin abokin nashi yana cikin tsaka mai wuya


********
Alhmdllh sauk'i ya samu wajen nauwara   ta dawo normal k'asar London ta kar6e ta don ta k'ara kyau fatan ta ya murje tayi wani irin fresh haka ma twins sunyi k'ara girma kamannin abduljabbar yana dad'a fito wa yaran sun shiga ran doctor muh'd sosai

Da hka suka share watanni 3 a london tukunna suka fara haramar koma wa 9ja doctor muh'd wani katafaren shopping malls ya kai su kowacce ta xa6i abin da take so nauwara da fa'iza sai na'eem da ameer
Nauwara kasa d'aukan komai tayi sai wani perfume designer mai matuk'ar sanyin k'amshi shi kawai ta d'auka kallon ta yayi cikin wani irin salo yayi k'asa da muryar shi yace
" mameen na'eem don Allah ki saki jikin ki ki dauki duk abin da yayi miki please "
Kallon shi tayi fuskar ta d'auke da Murmishi tace
"Haba doctor ai na d'auki turare wannan ma ya isa ngde"
Bai k'ara ce wa komai ba yayi gaba ya fara diban kayayyaki bin sa da kallo tayi ba tun yanxu ba ta gama karantar shi kiris yake jira ya bayyana mata abin da ke cikin xuciyar shi

Toh Hka yayi mata shopping na daban masu matuk'ar kyau da tsada har fa'iza tana tsokanar shi ita ma fa'izan ta yaba da doctor muh'd di'n yana da halayya masu kyau kuma xata yi farinciki da hkan Indai wannan had'in ya tabbata

Yau misalin karfe 7 na dare flight d'in su nauwara xai tashi xuwa 9ja suna tsaye a jikin motar doctor muh'd a cikin airport d'in ammi umma suna xaune acan wani 6angare a xaune kan kujera fa'iza da twins sun gama sallama da doctor muh'd sun tafi wajen su umma aka barshi da nauwara a tsaye cikin wani irin yanayi yace
"Shikenan xaki gudu ki barni sai kuma yaushe " cikin sigar xolaya tace "sai watarana "

Had'e fuska yayi yanda yayin ya bata dariya don shi mutum ne ma'abocin fara'a harara ta yayi yace
"hmm nauwara dole kiyi min dariya mana kin gama sa xuciyata ta saba dake xaki ce min sai wataran "
Shiru tayi ta sunkuyar da kanta tana d'an wasa da xoben hannun ta cikin sanyin murya yace
"a yau nayi niyyar tona miki xuciya ta nauwara ina son ki kuma da aure wlh tun lokacin da na d'ora idanu wana akan ki naji ina k'aunar Ki sauran en watanni na dawo nigeria da xama gaba d'aya naso tare ma xamu koma so hkan bai samu ba "
Tun da ya fara maganar shi kanta na sunkuye daman ai ta dad'e da ganin alamun hkan a tattare shi haka dai yayi ta tona mata asirin xuciyar shi ta yanda ta kamu da son ta sosai ta tausaya mishi ita gaba d'aya xuciyar babu son wani d'a namiji Idan ba gwarxon ta ba abduljabbar kuma baxa ta6a son wani ba kamar shi sai dai wani ikon Allah,  suna nan tsaye har xuwa lokacin da aka kirawo sunan ita ce ta kusan ta K'arshen shiga jirgin saboda yanda doctor muh'd ya tsare ta da xaxxafan Kalaman shi..........





Aishat A muh'd
[25/07, 09:57] Aishat A. Muhd: 🍀🍀☘☘🍀🍀
 *K'ARSHEN WAHALA*
🍀🍀☘☘🍀🍀



*written by*
Aishat A muh'd



*~Pg 86~*


   Sun sauka a 9ja lafia aunty sadiya ce taxo d'aukan su cikin tsananin murna suka rungume junan su bayan an gama gaisa wa suka shiga mota suna k'arasa wa gida bayan aunty sadiya tayi parking suka firfito daga motar part d'in umma suka nufa ko'ina tsaf an gyara shi sai k'amshi turaren wuta da air freshener yake ga girki Kala Kala akan dinning table wanda aunty sadiya da kanta ta shirya musu

Kowa bedroom ya nufa don yin wanka sannan axo aci abinci, nauwara tana d'aure da towel tana kok'arin riga fa'iza shiga wanka don baxa ta iya xama har tayi wa na'eem da ameer sannan tayi ba wayan tane ya fara k'ara alamar kiran ta ake d'an tsaki taja fa'iza nayi mata dariyar k'eta hararar ta tayi a fusace ta k'ara sa wajen Kafin ta d'auka har fa'iza, na'eem da ameer sun shige toilet da gudu abin dariya ya Bata ma ganin sunan doctor muh'd yana yawo akan screen d'in wayar yasa ta d'aukan wayar bayan sun gaisa yake cewa
"kin min adalci kuwa Ummu na'eem har kin mance dani ko, ina nan cike da kewar ki son ki ya hana xuciya ta sukuni ki tausaya wannan bawan Allah ki kar6i soyayyata"
Ya K'arasa maganar cikin sanyin murya hkan da yayi ba k'aramin tausayi ya Bata ba tare da sanyayar mata jiki sauke ajiyar xuciya tayi a hankali sannan tace
"Haba taya xan mance da likitan da ya ceto rayuwa ta a lokacin da aka fidda tsammani da Cigaban rayuwa ta muma munyi kewar ka"
Sai lokacin taji sautin murmishin shi tare da sauke ajiyar xuciya yace
"ina twins da fa'iza, umma da ammi dafatan an je gida lafia"
"lafia klau "
"Masha Allah"
Sun d'auki tsawon mintuna 10 suna waya sannan suka yi sallama ta waigo ta Kalli fa'iza da take shirya twins tace
"doctor muh'd yana gaida ke "
Cikin murmishi fa'iza tace "ina amsawa naga alama da wannan doctor muh'd ya samu shiga dashi xa'a yi "
Wani kallo nauwara ta bita dashi fuska a d'aure sai ta juya ta shiga toilet ta bar fa'iza sororo a tsaye cike da dumbin mamakin yanda ta canja lokaci d'aya ba dai duk abin da Yah abduljabbar yayi mata har yanxu akwai son shi a xuciyar ta ba toh idan ba hka ba mene dalilin canjawar ta gaba d'aya a lokaci d'aya

Gaba d'aya kowa ya hallara a dinning table ana cin abinci bayan an kammala suka dawo cikin parlour ana er hira yayi da nauwara ta ke6e kanta waje d'aya ta rasa wanne abune yake damun xuciyar ta amman tabbas tasan baxai wuce son Yah abduljabbar da kuma abin da yayi mata kasa jurewa tayi sai da tayi kuka ko taji sauk'in abin da yake damun ta

Bayan dawowar su nauwara da Sati d'aya suka tarkata sai kaduna garin gwamna garin da raban shi da ita tsawon wasu shekaru tun a hanya take kuka don tunawa da mahaifin ta a gidan baffah suka sauka sun samu tar6a sosai en uwa na nesa da na kusa sun xo taya su baffah murnar samun jikokin su a ranar aunty safiyya kanwar Alhj sa'eed ya duro k'asar 9ja don bata k'asar tun bayan mutuwar yayan ta da iyalan shi mijin ta aka tura shi wani course a k'asar Switzerland a lokacin da suka ji labarin su nauwara basu mutu ba da ammi suka fara shirye shiryen taho wa daman mijin nata ya kammala abin da ya kai shi Switzerland di'n don hka suka taho gida nigeria

Aunty safiyya ta sha kuka sosai tana rungume da nauwara a jikin ta saleem na gefen ta a xaune amman hannun ta yana rike da nashi motsi Kad'an ta jiyo ta kalle su xuciyar ta cike da tarin farinciki ta tausaya wa nauwara sosai lokacin da taji labarin ta


A hka rayuwa ta cigaba da tafiya nauwara da saleem sai da sukayi wajen wata d'aya a kaduna cikin en uwa sun k'i su dawo umma gajiya tayi da rashin dawowar su ta Shirya ta tafi kaduna ta sako su a gaba suka dawo kano amman ammi tayi xamanta acan

Jiddah da maman ta sun xo gidan umma jiddah ta bawa umma hak'uri sosai da nauwara ta roki su yafe mata kuma sun yi hak'uri yafe mata amman sunyi mamakin canja war jiddah sosai ai daman idan ka hana tukunyar wani tafasa to kai ma taka baxa tayi xafi ba balle ta tafasa rayuwa ai juyi juyi ce wai kad'o ya fad'a ruwan xafi a Wannan duniyar da rayuwar da muke ciki wanda cin amana tsantsa butulci hassada da rashin gaskia yayi yawa acikin xuciyoyin mu kana xaune da mutum tsakani da Allah amman baka san abin da yake k'ulla wa ba cikin xuciyar shi ba wani ma gaba d'aya so yake yaga baka duniyar Allah yasa mu fi karfin xuciyar mu Allah ya bamu ikon aikata dai dai a rayuwar mu Ameen


Kamar yau misalin karfe 5 na yamma nauwara tana xaune a bedroom tana sanye da wani Pakistan rigar blue ce da adon flowers fari sai dogon wandon rigar fari ne shima ta gyara gashin kanta ta xubo shi bayan ta bata daure shi da ribbom ba tana waya da doctor muh'd yana fad'a mata acikin wannan week d'in xai dawo bata ankara ba taji na'eem ya kar6e wayar ta dake mak'ale a kunnen ta cikin sauri tasa hannu ta kamo shi tare da kok'arin kar6ar wayar sai ya cilla wa ameer wayar caraf yaron ya cafe yana dariya yayi hanyar fita daga d'akin da d'an gudun shi kunnen na'eem ta d'an ja sannan tabi bayan ameer shima na'eem da gudu ya fice ya bisu
Gaba d'aya twins su rikita ta idan ta kama ameer tana kok'arin kar6ar wayar sai ya cilla wa na'eem suna mata dariya duk Hayaniyar da suke doctor muh'd yana jinsu sai faman murmishi yake xuciyar shi na k'ara son nauwara yak'i kashe wayar don so yake yaji K'arshen wannan wasan uwa da 'ya'yan ta kuma adai dai lokacin nan MG abduljabbar yana tsaye a kofar shiga falon ya xuba musu ido yana kallon su cike da sha'awa wani son nauwara yana dad'a ratsa cikin jikin shi da xuciyar shi gyara tsayuwar yayi yana harde hannuwan shi a kirjin shi shi ma yana son ganin K'arshen wasa nan
Duk tabi ta gaji ta tsaya cak tana mai da numfashi tana kallon na'eem da ameer da suke tsaye d'an nesa da ita na'eem wanda wayar take hannun shi ya d'ago ta sama yace
"mamee mu cigaba da wannan playing game di'n mu ga wane xai samu sa'ar kar6ar wayar "
"yes!  hkane na'eem good idea dama aunty fa'iza da bros saleem suna nan "
Ameer ya fad'i hkan suna tafawa da na'eem Kafin su ankara nauwara tayi kansu da gudu da k'arfi suka saki ihu xasu gudu cikin xafin nama ta rik'e rigar na'eem ta amshe wayar ta nan suka fara kukan shagwa6a tare da bubbuga kafafun su a k'asa hararar su tayi sannan tana huci tace
"Allah kuna son na doke ku kullum sai kunsani gudu a gidan nan to ku kiyaye ne "
"mamee ai  Idan kina Hka baxa kiyi k'iba ba irin auntyn mu a skul"
"ofcourse na'eem nima bana son mamee tayi jikin auntyn mu "
Ameer ya fad'i yana wani yatsina fuska ba k'aramin dariya suka bawa nauwara ba hka ba abduljabbar da yake tsaye yana kallon shi shima doctor muh'd da yake sauraren su ta waya dariyar yake yi sosai tama rasa me xata ce musu sai hararar su tayi ta juya xata nufi upstairs sai naga na'eem ya Kalli ameer sun kashe ido d'aya wani abu na'eem ya fito dashi a jikin aljihun wandon shi shi da ameer kowa d'aya d'aya sadaf sadaf suke bin bayan ta abduljabbar dai yana tsaye yana kallon mai su twins xasu sake yiwa nauwara d'ora mata lizard di'n roba sukayi kan rigar ta sannan da sauri suka ja da baya kamar had'in baki suka fara ihu da tsalle suna cewa
"wayyo Allah mamee bayan ki a jikin rigar Ki lizard guda biyu sun mak'ale "
A matuk'ar firgice ta jiyo tace "da gaske na'eem "
Cikin tsalle tsalle da ihu na'eem yace " I swear mamee sai motsi suke "
Kafin ya K'arasa fad'i nauwara ta saki wani ihu tare da fara tsalle kamar yanda su na'eem suke su kuma sai kunshe dariya suke yi jin motsin abu a jikin rigar ta yasa ta ta dad'a rikice wa ta rud'e sosai batasan da tayi hanyar fita daga falon ba duk ta kid'ime karo tayi da abduljabbar da yake kok'arin xuwa ya cire mata fad'o wa tayi jikin shi tare da Kank'ame shi shi ma k'ara rungume ta yayi tsam a jikin shi sannan yasa hannu ya cire mata lizard di'n ya xubar dasu k'asa yana d'an hararar twins da suke mata dariyar k'eta sunkuyar da kansu kasa suka yi
Jikin ta sai faman 6ari yake saboda tsabar tsorata hannun shi yasa yana bubbuga bayanta cikin sanyin murya ya rad'a mata a kunne
" shiiiii calm down nauwara lizard di'n roba ne twins suka sa miki "
Saukar sautin muryar shi a kunnen ta shi yasa ta d'ago wa da tare da barin cikin jikin shi lokaci d'aya ta had'e fuska ko kallon Inda yake bata yi ba taja d'an siririn tsaki ta shige falo kallon su na'eem tayi ranta a 6ace ta daka musu tsawa da sai da suka tsorata suka shige jikin abduljabbar suna b'uya alama yayi musu da hannu su je su Bata hak'uri don hka cikin sanyin jiki suka K'arasa wajen ta tare da durkusawa a k'asa suka rik'e kunnuwan su duk biyun suka marairaice fuska kamar xasu yi kuka cikin had'in baki suka ce
"I'm sorry mamee baxa mu k'ara ba wannan shine last please "
Shafa kansu tayi cikin murmishi tace
"alright my guys, muje ku shirya mu tafi shan ice cream "
Rungume ta suka yi suna cewa "yes! Mamee thank u, i luv yhu so much "
Suka bata peck a kumatu da goshi sannan sukayi upstairs da gudu Duk abin nan da suke abduljabbar yana tsaye yana kallon su cike da kaunar su Bata Kalli Inda yake ba ta juya xata tafi taji maganar shi cikin sanyin murya yace
"nauwarahhh d'an tsaya xanyi magana da ke please "
Tsaya wa tayi bata jiyo ba ganin hka yasa ya K'arasa gaban ta ya tsaya sai da ya d'an tsorata ganin yanda fuskar ta koma 6acin rai ne kwance akan fuskar yana kallon fuskar ta yace
"ina neman afuwar Ki akan abin da na aikata miki kiyi hak'uri rashin sani ne "
"hak'uri kace fah!!!?"
Yanda tayi maganar sai da ya xaro idon shi saboda bai ta6a ganin Wannan yanayin a tattare da ita sai yau Kafin ya ankara ta kewaye shi ta tafi cikin sassarfa take hawa stairs baki sake yake bin ta da kallo Lallai yakai nauwara bango dole ya fuskanci hkan daga gare ta sai yayi hakuri don yasan nauwara tana son shi 6acin rai ne na abin da yayi mata dafe kanshi yayi idanun a lumshe yace "Ohh Yah Allah ka kawo min agaji Yah Allah kasa nauwara ta huci daga fushin da take dani "
Yana gama fad'in hka ya xube akan kujera yana sauke ajiyar xuciya.......




Aishat A muh'd
[25/07, 09:57] Aishat A. Muhd: 🍀🍀☘☘🍀🍀
  *K'ARSHEN WAHALA*
🍀🍀☘☘🍀🍀



*written by*
Aishat A muh'd



_Hak'ik'a samun k'awa kamar ki sai an tuna ina alfahari da ke my saNaz i really luv u, Allah ya k'ara xumunci, Allah ya barmu tare, Allah ya kare min ke a duk inda kike Allah ya cika miki buri kanki na alkhairi Ameeen_😘😘




*~Pg 87~*




  Yana nan xaune suka fito a shirye duk sun canja kayan jikin su alamar wanka tayi ita dasu na'eem da ameer tana rik'e da key d'in mota a hannun ta d'aya hannun tana rik'e da waya mak'ale a kunnen ta hira suke da doctor muh'd yana tambayar ta K'arshen wasan su ita da twins sai abin ya bata dariya don hka ta dunga er dariyar ta cike da jan aji, ya xuba mata ido kallon ta kawai yake don tayi bala'in yi mishi kyau tana sanye da wata yellow da bak'in gown tayi rolling da veil bak'i da adon flowers yellow sai tayi amfani da black shoes marasa tudu sosai maganar da tayi ita ta dawo dashi hayyacin shi wanda ta kusan haddasa mishi bugawar xuciyar shi
"Haba doctor kada ka damu Allah ya kawo ka lafia kai dai idan kaxo xaka ga irin kewar ka damu kayi "
D'an langa6e kai tayi tana sauraran abin da yake cewa ganin Yah abduljabbar ya xuba mata ido da alamar ranshi ya fara 6aci don hka ta dad'a shagwa6e wa tace
"ah ka wuce nan a wurina Bari naje na dawo xamu shan ice cream ne"
Cikin mamaki tace "kishi kuma? ",
"Haba kasan bana kula kowa sai kai saboda xuciya ta..........."
Kafin ta ankara taji an warce wayar da sauri ta d'ago kanta karaf suka had'a ido da abduljabbar idanun shi sunyi jawur dasu sai faman huci yake duk da ta tsorata da ganin yanayin shi amman sai ta dake cikin d'aure fuska tace
"lafia ina waya ka kar6e min? "
Wata harara ya watsa mata kafin kuma a fusace yace
"da uban wa kike waya?"
Sam ta manta dasu twins a wajen ta turo baki gaba sannan tace
"da my sweet darling nake Mag........ "
kafin ta K'arasa fad'i taji an murd'e bakin nata da k'arfi axaba ta ishe ta ga ba bakin yin ihu umma ta kawo agaji sai da yaga ta jigata idanun ta sunyi ja ga hawaye yana fita a idon sannan ya cikata wani wahalalen numfashi take sauke wa wata er k'ara ta saki jin ya kamo gashin kanta da hannun shi cikin tsawa yace
"wlh na sake jin Kinyi waya da wani katon sai nayi 6a66allaki a gidan nan "
"wlh baka isa ka hanani kula kowa ba kuma wallahi baxan yarda da wannan muguntar ba ina ruwan ka dani da bakin ka kace ka tsanane fah naje nayi rayuwar da nake so "
Lokaci d'aya jikin shi yayi wani bala'in yin sanyi a hankali ya cika mata gashin kanta ya xube kan kujera tare da nutsar da hannun shi cikin gashin kanshi, kallon shi tayi taja tsaki tare da kama hannun su twins wad'anda har sun fara kuka ganin mameen su na kuka da kanta tayi driving d'in xuwa wurin shan ice cream da pizza nd shawarma ta siyo sannan suka dawo gida

Lokacin da ta shiga falo ba k'aramin mamaki tayi ba ganin har yanxu abduljabbar yana nan Inda ta barshi sai dai yanxu ya kwanta a rigingine kan kujerar ta6e baki tayi ta shige kitchen don sanya ice cream a frige sannan ta fito ta tarar na'eem da ameer sun sake dashi har suna bashi labari yana d'an murmishi tare da shafa musu kan su ganin ta fito daga kitchen yasa shi mik'e wa tsaye yana cewa
"taimaka min da abinci I'm hungry "
Bata Kalli Inda yake ba tayi gaba tana cewa
 "ka nemi house girl ta baka ni bani da wannan time d'in "
"nauwarah bakya afuwa ne,  na baki hak'uri kinki ki hak'ura "
"ehh baxan hak'ura ba din "
Jin alamar ya biyo bayan ta yasa ta watsar da ledar hannun ta ta shawarma ta xura a guje ta fad'a d'aki tare da murxa key
Sunkuya wa yayi ya d'auki ledar ya dawo falo wajen na'eem da ameer wanda gaba d'aya hankalin su yana kan tv suna kallon cartoon a tashar mbc 3 suna shan ice cream di'n su hankali kwance

Sai da ya cinye shawarma biyu Sannan ya tashi ya d'auko fresh milk mai sanyi yasha cikin glass cup d'aya sannan yaji shi dai dai don k'wanakin nan ba k'aramin hora kanshi da yunwa yake ba

A hka umma ta dawo ta ganshi Ko kallon Inda yake bata yi ba ta haye stairs fa'iza ce ta gaida shi ita ma ta wuce saleem ne ya xauna kusa dashi ya gaida shi sannan suka fara er hira bai nuna mishi komai don yana son abduljabbar sosai guy d'in yana birge shi kuma yana nan yana addu'a sai sun mayar da auren su da aunty nauwara sai da aka kirawo sallahr mangarib sannan suka tafi masallaci acan suka hadu da abba dakyar abba ya amsa mishi gaisuwar shi duk jikin abduljabbar yayi masifar yin sanyi dole ya nemi su abba su yafe mishi ko yaga dai dai a rayuwar shi iyaye sun fi k'arfin wasa fushin su ba k'aramin tashin hankali ba ne akan shi

Har falon abba abduljabbar ya bishi ya dunga bashi hak'uri akan laifin da yayi tare da alkawarin baxai sake aikata hkan ba sharrin xuciya ce da rashin bincike dakyar abba ya hak'ura sannan yayi mishi nasiha sosae akan saurin yanke hukuncin cikin fushi daga K'arshe ya nemi da dole ya mayar da jiddah d'akin ta don baxai xauna a haka ba laifi ne tunda ta riga ta aikata ya wuce sannan tayi nadama sosae don taxo ta bamu hak'uri har da nauwara kuma ta hak'ura ta yafe mata

Bashi da yanda xai yi ya amince da abin da abba yace tunda sulhu yake nema can kuma yace
"am uhm abba don Allah nauwara fah ina son na mayar da ita "
Wani kallo abba ya watsa mishi ba shiri yayi shiru fuska a d'aure yace
"ai nauwara Kun rabu har abada tunda kayi kunnen uwar shegu da abin da umman ka tace gwara ta xa6i wanda xata iya jin dad'in xama dashi wanda xai dunga bincike Kafin ya xartar da hukunci "
Da k'arfi abduljabbar yace "nooo Abba kada kace hka ina son ta idan na rasa ta xan iya shiga wani hali ka taimaka min Abba na same ta nayi alkawari baxan sake aikata hkan ba please "
Sosai ya bawa Abba tausayi amman ya dake yak'i nuna mishi yaji tausayin shi don yana so ya shiga taitayin shi gaba baxai sake aikata hkan ba
"ni na gama magana tashi ka ban wuri xan huta"
Kallon abban yayi sannan yace "I'm sorry Abba Idan na 6ata maka rai Gud nyt "
yana fad'in hka ya fice daga falon jikin shi a matuk'ar sanyaye Kai tsaye part d'in shi dake cikin gidan ya nufa ko'ina tsaf a gyare xube wa yayi kan bed bai ankara ba sai jin saukar abu mai d'umi yaji afuskar shi alamar hawaye ne ya kasa rik'e su har sai da suka xubo mishi kusan Kwana yayi baiyi baccin kirki ba sai juye juye xuciyar shi a kuntace

Tun daga ranar nauwara da abduljabbar basu sake had'u ba da junan su duk da yana bala'in son ganin nata kuwa amman ba fuska wajen umma

Misalin karfe 5 na yamma nauwara tayi parking d'in motar su a bakin jifatu store suka fito ita da fa'iza daga motar sun ci gayu cikin wata atampha d'inkin fitted gown kowannen su sai dai different colours na atamphar sunyi matuk'ar yin kyau Idan ka Kalli nauwara baka ce ta haifi na'eem da ameer ba kai tsaye cikin jifatun suka shiga nan suka fara duba abubuwan da suke buk'ata tana cikin duba perfumes taga wanda take nema takai hannu xata dauka sai taga wani hannu daban ya d'auke shi da sauri d'an d'ago ido tayi don taga wane wannan karaf suka had'a ido da wani kyakkyawan matashi yana murmishi a fuskar shi ta juya xata tafi taji yace
"nauwarah ina saleem?? "
cikin tsananin mamaki ta juyo ta kalle shi har yanxu murmishi ne a fuskar shi
"Kina mamaki ne Inda na sanku nasan baxa ki gane ni ba da saleem yana nan xai gane ni"
"don Allah malam kai wane, ina kasan mu? "
"Aminu ne"
Ya fad'a mata "wanne aminu kuma? "
"Aminu mijin hindatu wanda kuka xauna a hannun shi "
xaro ido tayi cike da tsantsar mamaki da farin ciki take kallon shi tace
"don Allah da gaske kai ne "
"wallahi nine nauwara tun lokacin da kuka shigo na gane ki ban k'ara tabbatar da hkan ba sai da na kirawo sunan ki dana saleem naga kin jiyo sannan na gane ki"
Nan suka gaisa tace "ina aunty hindatu da yara "
"sunan tare ma muke dasu ai xaku gaisa "
Cikin er dariya tace "ah mai xai hana kuwa"
Fa'iza wadda take gefe tana kallon su nauwara ta gabatar mishi da ita suka gaisa suna tsaye suna er hira duk nauwara ta tak'ura sosai da yanda aminu yake kallon ta tsoron ta kada matar shi hindatu ta xo yana wannan kallon nata.......

( _dafatan mai karatu baku mance aminu wanda ya taimaki su nauwara har suka xauna a hannun shi Kafin hindatu matar shi ta kore su daga gidan_)




Aishat A muh'd
[25/07, 09:58] Aishat A. Muhd: 🍀🍀☘☘🍀🍀
  *K'ARSHEN WAHALA*
🍀🍀☘☘🍀🍀




*written by*
Aishat A muh'd



_wannan page d'in sadaukar wa ne ga maman abiddeen (malam Amina), nd my friend hafsat A aliyu i really luv u guys , Allah ya bar xumunci ameeen_😘



*~Pg 88~*




       Suna nan tsaye hindatu ta K'araso inda suke tana rik'e da hannun yaran ta ta 6ata fuska sosai ganin mijin ta tsaye agaban wasu kyawawan emmata cikin murmishi aminu yace
"hindatu baki gane Wannan ba? "
Ya fad'i yana nuna nauwara wadda take murmishin yak'e kallon ta tayi amman ta kasa tuna ta don hka ta yamutse fuska tayi kafin tace
"ni fah bansanta ba wacce? "
Cikin dariya yace "nauwara ce fah "
xaro ido tayi cike da mamaki tace
"Wacce nauwara?? "
"wanda kika kora daga gidan ki da k'anin ta saleem don nasan baxa ki mance lokacin ba "
Wata irin kunya ce ta lullu6e hindatu ganin yanda nauwara ta koma nan take tayi mugun nadamar abin da ta aikata cikin tsananin kunya da sanyin murya tace
"nauwarah kiyi hak'uri akan musguna muku da nayi ke da saleem ki yafe min"
Cikin murmishi nauwara tace "Laaa kada ki damu aunty hindatu wlh mun yafe miki"
"ngde nauwara ina saleem? "
"saleem yana gida "
"Allah sarki ki gaida shi, Kinyi aure ne? "
Wannan tambayar da hindatu tayi ita tasa aminu xuba wa nauwara ido hankalin shi a tashe yana tsoron me xata ce, cikin d'an murmishin yak'e tace
"ehh nayi aure har da yara na twins na'eem da ameer "
Wani mugun gumi ne ya tsatstsafo wa aminu lokaci d'aya naji wai nauwara tana da aure har da yara wayyo Allah yanxu ya xai yi da dumbin k'aunar ta da yake
"Allah sarki Allah ya raya su cikin addinin islam"
"Ameeen "
Fa'iza da nauwara suka amsa sannan ta cigaba da cewa
"ki ban address d'in gidan ki xan xo Insha Allah "
Kallon juna nauwara da fa'iza suka yi ta d'an yi shiru Kad'an Kafin tace "Ayyah ni yanxu bana tare da mijina, sai dai na baki address d'in Inda nake? "
Wata katuwar ajiyar xuciya aminu ya saki Har sai da su nauwara suka kalle shi sai ya wayance da Cewar
"subhannallah na tausaya miki Allah ya baki mafi alkhairi "
"Ameeen ngde "
Nan dai sukayi exchange numbers sannan sukayi sallama kowa ya kama gaban shi xuciyar aminu cike da tsantsar farin ciki burin shi xai cika Insha Allah na auren nauwara.


Bayan sun dawo gida nauwara take bawa umma da saleem labarin had'u wa da aminu da suka yi sannan ta  bawa saleem contact di'n aminu wanda shi ya buk'aci da ta bawa saleem d'in.

Tun daga lokacin aminu ya tak'ura mata da waya kullum har ta fara gajiya da hkan Kafin daga K'arshe ya bayyana mata abin da yake cikin xuciyar shi to ita dai har yanxu bata ce mishi komai Hka xaratan maxan nan uku suka rikirkita nauwara kowanne da nashi salon shi abduljabbar da gadara yake nuna mata kan dole sai ta koma gidan shi, duk da xuciyar ta tana cike da kaunar abduljabbar har yanxu amman ta hak'ura da sake xama dashi Idan ta tuna yanda ya rufe ido yayi mata abin da baxa ta ta6a mance wa ba a rayuwar ta.
 Shi kuwa doctor muh'd a hankali yake tafiyar da ita cikin sanyi kuma da alama xai yi nasara don tana sauraren shi su yi hira sosai a waya amman sai dai har yanxu bata furta mishi tana son shi ba amman bai karaya ba,  ta 6angaren nauwara kuwa doctor muh'd yana d'an birge ta ba laifi shi yasa take tsaya wa har su d'au long time suna waya kalaman shi cikin sanyaya wa babu gadara kamar abduljabbar tana ganin xata iya xama dashi don ya had'u ta ko'ina ga nutsuwa da hankali kuma yana abin dariya
  Aminu ku sam baxa ta iya auren shi ba ta d'auke shi matsayin yayan ta na jini duk da shi di'n ma ya had'un gashi d'an boko ne kusan dai en jarida akwai nutsuwa da hankali ga yawan cin su Akwai sanin ya kamata yanayin shi kusan iri d'aya da wannan d'an jaridar nan na freedom radio nura bello (bal nur),don hka sam bata sashi matsayin wanda xata aura ba duk da yanda yake kalamance ta da daddad'an kalaman shi.  (toh fah wannan shine runguntsimi acikin wad'annan gwaraxan maxajen nan ko wanne xai yi nasarar mallakar nauwara???)

Acikin wannan lokacin ne doctor muh'd ya tarkata yayo nigeria gaba d'aya dakyar ya iya bari gari ya waye saboda tsabar son ganin nauwara, lokacin da ya xo a waya ya kirawo ta fa'iza ce ta fito ta yi mishi jagora xuwa parlourn umma tana tayi mishi tsiya har k'asa ya tsugunna ya gaida umma sun d'an yi er hira tukunna tabar falon lokacin nauwara ta shigo falon da sallama tana rik'e da hannun twins da gudu na'eem da ameer suka K'arasa wajen shi suna murnar ganin su hugging di'n su yayi gaba d'aya cikin jin dad'in ganin nasu nauwara tana gefe tana kallon su don fa'iza ma biye musu tayi suna faman surutu, lokaci xuwa lokaci yana d'ago kanshi ya watsa mata wani kallo wanda ya kunshi abubuwa da dama sai faman nok'e kai take cike da jin kunyar shi fa'iza ce ta kama hannun na'eem da ameer tace
"let's go guys mu bar wad'annan love birds di'n naga alama wannan doctor kiris yake jira ya fara korar mu "
Dariya suka tuntsire da ita gaba d'aya na'eem yace "Laaa aunty fa'iza mamee ce bird di'n? "
"ehh man but wannan love birds ake kiran su"
Ya bud'e baki xai sake magana fa'iza ta jasu da sauri suka fice daga falon aka bar nauwara da doctor muh'd sun d'anyi shiru Kafin doctor muh'd ya katse shirun ta hanyar cewa
"mameen twins anya Anyi farin ciki da xuwan nawa kuwa"
"me kagani "
"ah banga alama bane, don nasan har yanxu ba'a bani wani matsayi a xuciyar ki ba"
Ya K'arasa fad'i cikin sanyin murya sosai taji tausayin shi don hka ta sake suka sha hira sosai har xuwa lokacin da ta rako shi wajen motar shi xai tafi bud'e gate mai gadi yayi wata mota black Mercedes Benz ta danno cikin gidan irin yanda akayi parking kasan wanda yake driving ba'a cikin nutsuwar shi yake ba gaba d'aya idon su yana kan motar

Sai da gaban nauwara ya fad'i ganin Fitowar abduljabbar daga motar jikin shi sanye da black jeans nd T-shirt yellow irin mai dogon hannun nan fuskar nan tashi a murtike take babu fara'a Ko Kad'an idanun shi cikin wani black glass yayi matuk'ar yin kyau Ko kallon Inda su nauwara yake bai yi ba ya shige cikin gidan cikin tafiyar shi ta kasaita
Hamdala tayi a xuciyar ta ganin bai kula su ba shi kuwa doctor cewa yayi
"wannan shine abban su twins don naga suna kama sosai "
"Ehh shine"
Jikin shi a sanyaye sukayi sallama ya tafi ko rufe gate ba'a yi ba motar aminu ta shigo gidan wani wawan tsaki nauwara ta ja don wlh ta gaji hutawa take son yi dakyar ta k'ak'alo murmishin dole suka gaisa nan yayi ta xuba surutun shi bata kula shi daga ehh sai a'a suna cikin hka abduljabbar wanda ya kasa xama ya fito sai kuma yaga wani daban bana d'axu ba Lallai Wannan yarinyar er rainin wayo ce kowanne mutum take jajibo musu ta kawo musu gida xai koya mata hankali wlh a fusace ya nufi wajen da suke tsaye a jingine jikin mota..........




Aishat A muh'd
[25/07, 09:58] Aishat A. Muhd: 🍀🍀☘☘🍀🍀
  *K'ARSHEN WAHALA*
🍀🍀☘☘🍀🍀



*written by*
Aishat A muh'd



*~Pg 89~*



  A fusace ya K'arasa wajen aminu ya mik'a mishi hannu alamar su gaisa wani kallon kaskanci yake watsa mishi kafin ya juyo kan nauwara wadda ta had'e fuska tana jiran taji da mai yaxo Kafin ta ankara taji ya fisgo hannun ta yana janta har xuwa falon umma suka bar aminu a tsaye baki bud'e yana tunanin shi kuma wannan wane, don baisan abduljabbar kuma bai ta6a ganin twins ba da yasan wane shi kamar yanda Dr muh'd ya gane shi ba tare da an fad'a mishi ba, haka yaja motar shi jikin shi a sanyaye ya bar gidan

Suna shiga cikin falon ya wurgar da ita kan kujera har sai da ta buge auuch ta furta don bakaramin xafi taji ba ranta ya 6aci sosai da wannan abin da abduljabbar yake mata dole ta d'au mataki kuwa, kafar shi ya d'ora d'aya kan kujerar ya sunkuyo da kanshi saitin fuskar ta yana kallon ta fuskar nan tashi a murtike cikin tsawa yace
"na fuskanci so kike xuciya ta,  ta tarwatse na mutu na barmiki duniyar gaba d'aya don na fuskanci bakya k'aunar ganina nauwara "
Sauke numfashi yayi sannan ya cigaba da cewa
"Kinsan yanda nake bala'in kishin ki shine kike kwaso wasu kaxaman samarin ki cikin gidan nan da uban me suka fi ni iyeee tell me?"
Hararar shi tayi kafin tace
"wlh ka daina kiran su kaxamai don sun fi min kai sau dubu kuma kallo xan auri d'aya daga cikin su saboda na tabbatar su masoya nane na gaske Duk abin da nayi baxa su guje ni ba"
Kafin ta rufe bakin ta taji saukan wani lafiyayyen mari a kuncin ta wani irin ihu ta saki tare da dafe kumatun ta cikin masifa yana nuna ta da hannu yace
"wallahi ki kiyaye ni bana d'aukar rai ni, a gaba na ki furta xaki auri wani daban ba ni ba ki rubuta Ki ajiye ba wanda xaki aura sai ni, kuma daga yau kada ki k'ara kawo wani d'an iska cikin gidan nan naga ya miki "
Cikin wani 6acin rai hawaye suna xuba daga idanun ta ta fara tafa hannun ta sannan tace
"dakyau abduljabbar kawai ka fad'a min kai tsaye wannan gidan ku ne kada na k'ara shigo muku da wani dad'in abin ba daga sama na fad'o ba ina da gidan xan koma daga yau na bar maka gidan nan xan koma Inda na fito "

Kusan suman tsaye abduljabbar yayi cike da mamakin nauwara wai shi yau xata kirawo da abduljabbar kai tsaye Lallai ya kai ta bango kada fa garin neman gira ya rasa ido
"babu Inda xaki nauwara muna tare sai dai shi ya bar gidan"
Da sauri suka juya bayan su umma suka gani a tsaye ranta a 6ace k'araso wa tayi ta rik'e hannun  nauwara ta Kalli abduljabbar tace
"wlh ka kiyaye ni abduljabbar ina sane da yanda kake tak'ura mata a gidan nan ana so dole ne ko kuma dole sai ta koma gidan ka ne? "
Kwantar da kai yayi tare da marairaice fuska yace
"Haba umma nasan ke ma wlh kinaso ta dawo gida na da Zama ki lalla6a min ita ta yarda please "
Harara umma ta watsa mishi kafin tace
"yaushe na fad'a maka haka ni ba ruwa na nauwara wuce mu tafi "
Suka tafi suka bar abduljabbar a tsaye a wajen ya rasa inda xai sa kanshi yaji dad'i gaba d'aya ya girgixa da jin kalaman nauwara ta dai na sona kenan wata xuciyar ta ce mishi hka da sauri yana girgixa kai yace
"noooo baxai yiwu ba nasan nauwara tana har yanxu nasan rama abin da nayi mata take"
Sauke ajiyar xuciya yayi tare da cewa "i luv yhu nauwarah!  i really luv u baxan iya bari wani ya aure ki ba, Kece uwar 'ya'yanah "

Yana gama fad'in hka ya fice daga falon, wasu hawaye ne masu xafin gaske suka xubo daga idanun nauwara duk abin da yake tana kallon shi ta upstairs ya matuk'ar bata tausayi amman dole sai ya gane kuskuren shi a hankali ta furta
"i luv yhu too much my Abduljabbar "
Tana gama fad'in hka ta shige cikin bedroom d'in xuciyar ta ba dad'i


Cikin wannan lokacin aminu da Dr muh'd sun hurawa nauwara wuta kowanne yana son ya turo magabatan shi wurin Abba duk tabi ta kid'ime ta rasa yanda xatayi, Hka 6angaren abduljabbar Abba ya hura mishi wuta Lallai sai ya mayar da jiddah shi kuma wallahi baya k'aunar sake xama da ita ya tsane ta tun da ita tayi sanadiyyar raba shi da nauwara don hka ko Kad'an yak'i yaje gidan su, shi so yake ya shawo kan abba ya yarda a mayar da auren shi da nauwara da twins d'in shi su su bar nigeria di'n baxai dawo ba sai jiddah ta hak'ura dashi ta auri wani sannan xasu dawo don xai iya ajiye aikin shi akan nauwara (toh readers kunji tunanin MG abduljabbar).

Jiddah kuwa gaba d'aya tayi sanyi da abduljabbar ganin ko ta kirawo shi  baya picking ko message ta tura mishi babu reply har ta hak'ura da kiran nashi ta fara fitar da ran sake xama dashi ta Duk'ufa da addu'a sosai Allah ya xa6a abin da yafi alkhairi, suna mutunci sosai da nauwara yanxu har waya suke da junan su gashi tana yawan xuwa gidan don kawai taga twins don tana bala'in k'aunar twins komai ta samu haka xata kawo musu ko ta aiko musu .

Kiran ta awaya text messages na ban hak'uri Hka kullum abduljabbar yake turo wa nauwara amman bata d'aukan wayar tashi, text mssg di'n kuwa ko karanta wa bata yi take goge wa, ya damu iya damuwa bashi Kano bashi abuja kullum cikin xirga xirga tsakanin kano da abuja har ya fara bawa aunty sadiya, kausar da saleem tausayi sosai suna bayan shi da ya mayar da nauwara don duk basa son Dr muh'd da aminu, saleem har ya tsani suxo gidan don har maganar ya ta6a yiwa nauwara amman hka ta runtse idon ta ta kore shi daga d'akin sam tak'i sauraren shi.

Tuni abduljabbar ya xuge 'ya'yan shi sun fara canja wa Dr muh'd da aminu fuska ko wajen su basa xuwa idan sun xo, kuma duk lokacin da suka xo na'eem da ameer sun fara 6ata rai kenan har sai sun tafi, tun basu gane abin da twins suke ba har sun fara fahimta don akwai lokacin da Dr muh'd ya kawo musu ice cream, chocolates, sweets biscuits ya mik'a wa na'eem Amman sai yaron ya yamutsa fuska yace
"ka barshi mun gode don dadyn mu yana siyo mana"
Cikin mamaki nauwara da Dr muh'd suke kallon su amman ya daure yace
"na dadyn ku daban wannan daban don hka oya kar6i kuje kusha"
"nooo mun fison na dadyn mu thank u "
Ameer ya fad'i hkan tare da kama hannun na'eem suka shige cikin gida ko k'ara waiwaiyar su basu yi ba, kunya ta rufe nauwara kamar ta nutse a k'asa cikin sanyin murya tace
"I'm sorry Dr akan abin...... "
"ba matsala nauwara "
Dr muh'd ya katse nauwara duk ta kasa sake wa can ya sauke numfashi Kafin yace
"anya twins ba suna taya baban su kishi ba, a yanda na fuskance su suna so ki koma wurin baban su right"
Cikin mamaki take kallon shi d'an murmishin yak'e yayi yace
"ki daina mamaki na gama gane su "
"Indai har kina sona ki bani damar turo magabata na a cikin Wannan week d'in "
Girgixa kai tayi can kuma tace
"ba damuwa Allah ya kaimu ya xa6a mana abin da yafi alkhairi "

Cikin jin dad'i yace "Ameeen thumma Ameeen "

Daga hka suka yi sallama ya tafi ta dawo lokacin da ta shiga falo na'eem da ameer taga suna waya da abduljabbar fuskar su d'auke da farinciki suna ganin ta suka kwasa a guje sai bedroom d'in umma kwafa tayi tare da cewa
"xan kama Kune xaku yi bayani ne"

Acikin wannan satin ne Dr muh'd ya aiko manyan shi aka gama magana sun bayar da duk wani abu da ake gabatar wa wajen neman aure har da sadakin su, sannan suka tafi aka rabu cikin farinciki
A ranar abduljabbar yaji labari a bakin twins sun kirawo shi a waya har da kukan su hankalin shi ba k'aramin bashi yayi ba a lokacin ya bar duk wani aiki ya taho kano

Bayan sallahr isha'e ya k'araso gidan kai tsaye d'akin su nauwara ya nufa lokacin tana waya da ammi a fusace ya K'arasa inda take ya kar6e wayar tare da kashe ta cikin jin haushin shi tace
"malam wai lafiar ka qlau ne kasan da wa nake waya ka kashe min"
Yana mata wani kallo yace "bai shige wannan saurayin naki ba mai wuya kamar marikin lema"
Haushi ya ishe nauwara a fusace tace "Ehh da hka naga ni nake son shi "
Dalle mata bakin ta yayi da hannun shi da sauri ta dafe bakin nata don da xafi a tsiwace tace "Wlh kada ka k'ara duka na ka cuci wanda xai aure ni " kallon ta yake xuciyar shi na tafasa shi yanxu ya xai yi yabi yarinyar nan ta fad'a tak'i ta amince bare Ya gwada ta rarrashi ko xai dace bata ankara ba taga ya tsugunna a gaban ta ya dure dukka gwiwowin shi a k'asa cikin matuk'ar marairaicewa da sanyin murya yace
"na had'a ki da Allah nauwara kiyi hak'uri ki yafe min, ki yarda ki koma gida na wlh duk wata kyautata wa xan dunga yi miki baxan k'ara cutar da ke ba please "
Kallon shi take cike da matuk'ar mamaki ganin shi tsugunne a gaban ta yamutsa fuska tayi sannan tace "ni fah na gama xaman gidan ka"
"Da matsayi na da Shekaru na na ajiye su a gefe gani a durkushe gaban ki ina neman alfarma tare da baki hak'uri ki koma gida na mu rike yaran mu "
"ni fah kayi hak'uri ka nemi wata ka aura ko ka mayar da aunty jiddah "
Kallon ta yake xuciyar shi na tafasa da xai iya hak'ura da nauwara da wallahi a yau ya barta har abada amman sam baxai iya ba
"da girma na a gaban ki na tsugunna ina baki hak'uri ki k'i hak'ura koh"
Shiru tayi bata k'ara magana ba daga bayan su suka ji ance "mamee kiyi hak'uri ki yafe wa daddy please "
Da sauri ta d'ago kai taga na'eem da ameer fuskar su sha6e sha6e da hawaye hararar su tayi ta fice daga d'akin, rungume su yayi yana rarrashin su dakyar suka yi shiru sannan ya samu ya ja su xuwa part d'in shi na cikin gidan ranar abduljabbar bai yi cikakken bacci ba sai faman juyi yake da tunanin yanda xai 6ullo wa al'amarin
 Wani shegen murmishin mugunta ya saki da ya tuno hanya d'aya xai bi don ya samu nauwara ta dole ma, don hka nan take bacci mai dad'in gaske yayi awon gaba da shi baccin da ya dad'e bai yi irin shi ba......


Aishat A muh'd
[25/07, 09:58] Aishat A. Muhd: 🍀🍀☘☘🍀🍀
  *K'ARSHEN WAHALA*
🍀🍀☘☘🍀🍀



*written by*
Aishat A muh'd


*note* _namance ban sanar daku lokacin da aka yanke na auren nauwara da Dr muh'd ba, so su yanke 2 month's na auran_



*~Pg 90~*



   Washe gari da safe bayan an kammala breakfast nauwara da fa'iza suka fito cikin shirin tafiya kd xasu je suyi 2 weeks acan su dawo.

Bayan sunyi sallama dasu umma suna yi musu addu'ar sauka lafia, suka fito farfajiyar gidan suna tsaye driver yana sanya musu kaya a boot a dai dai lokacin abduljabbar ya fito daga part d'in shi jikin shi sanye da black trouser nd T-shirt blue yayi kyau sosae cikin tafiyar shi ta kasaita ya k'araso wajen fa'iza ta gaida shi yayin da twins suka rungume shi suna fad'in
"good morning papa "
Yana murmishi yace "morning my sweet kids, ina xuwa hka da safen nan "
Cikin dariyar farinciki suka ce "kaduna xamu je gidan baffah da ammi "
Murmishi yayi yana jan kumatun su yace
" Good Agaida min da baffah da ammi "
"okay papa "
Peck suka bashi a kumatu shima yayi musu sannan suka ce
"byeeee papa"
Suna fad'in hka suka shiga motar daman nauwara tuni ta shige ita da fa'iza .

Kallon ta yayi ta had'e fuska sosai ta wani kau da kai gefe alamar bama ta son ganin shi abun ma dariya ya bashi amman duk da hka sai da ya xura kanshi ta window d'in motar a kunnen ta ya rad'a mata
"babu ko sallama koh, wannan 6ata ran da kike baya yi miki kyau, Indai don ni ake 6ata rai ayi hak'uri na daina tak'ura miki "
Turo baki tayi tare da d'an d'ago kai ta saci kallon shi wani mugun fad'uwar gaba tayi lokacin da suka had'a ido ganin yanda yake murmishin muguntar nan kuma ta tabbatar Indai abduljabbar yayi wannan murmishin to akwai muguntar da ya had'a Yah Allah kayi min tsari da muguntar abduljabbar ta fad'i hka a cikin xuciyar ta, barin jikin motar yayi yana d'aga wa na'eem da ameer hannu alamar byeee

Yana tsaye a wurin har motar su ta fita daga gidan sannan ya juyo ya shige part d'in umma xuciyar shi wasai da ita sai nishadi yake abin sa ita kanta umma tayi mamakin ganin shi a haka yanda yake ta fara'a har ta fara tsargu wa anya abduljabbar ba wani abun yake shirin aikatawa ba rabon shi da ta ganshi a Hka har ta mance har ta kai da tambayar shi tace
"abduljabbar lafian ka qlau kuwa? "
Yana murmishi yace "me kika gani umma? "
"gani nayi sai fara'a da nishad'i kake, kamar wanda aka yi mishi da albishir da aljannah "
Kwashe wa yayi da dariya yana kallon umma wanda take binshi da kallon mamaki yace
"uhm umma kin ban dariya wlh, amman babu komai just yau na tashi da farinciki ne "
Kallon shi umma tayi sosai sannan tace
"Ko wani abu ka shirya wa nauwara ne"
"Laaa umma ni ba komai fa, ni yanxu ai na hak'ura tunda har ta tsayar da wanda xata aura"
"Allah yasa Hkane har xuciyar taka"
Umma ta fad'i hkan ba tare da ta yarda da abin da yace ba yanda yake son nauwara anya xai hak'ura Hka farat d'aya, shi kuwa sai faman murmishi yake har ya gama breakfast ya fita daga gidan.


Alhmdullilah su nauwara sun isa kaduna lafia a gidan baffah suka sauka da yake kuma ammi tana gidan don baffah da inna sun ce tayi xaman ta a wurin su ta d'ebe musu kewa, Hka ta xauna suna matuk'ar bata kulawa sosai Idan kaga ammi a lokacin baxa kayi tunanin ta haifi su nauwara ba.

Su baffah sunyi matuk'ar farinciki da xuwan su nauwara kyautata wa sosai suka dunga yi musu, a hka suka kwashe tsawon wajen Sati Biyu a kaduna sunje gidan aunty safiyya nan ta nuna mata ita wlh ta fison ta koma gidan abduljabbar ,murmishi kawai ta iya yi har ta gaji da amsa Cewar baxa ta koma gidan shi ba koma kowa ya bud'e baki xai ce ta koma gidan abduljabbar Abba, umma aunty sadiya da fa'iza su kad'ai suke Goyan bayan nauwara ta auri wanda suke so, kuma ta fuskanci ammin ta gaba d'aya ta nuna mata ita abduljabbar take son ta koma gidan shi su hadu su rik'e yaran su gashi dai dai da twins sun fison daddyn su, duk tabi ta rikice tunani yayi mata yawa ta rasa yanda xatayi kawai sai ta Duk'ufa da addu'a Allah ya kawo mata mafita, amman fa har acikin xuciyar ta tafison auren Dr muh'd hankalin ta yafi kwanciya akan shi, sai dai har yanxu bata ji sonshi axuciyar ta ba.

A haka suka cinye sati biyun suka dawo kano ta tarar umma ta xage tana ta shirye shiryen bikin ta duk wani abu da ya kamata tayi shi tayi sai jiran xuwa lokacin.


Abduljabbar ya daina Kula nauwara sam ya fita daga harkar ta sha'anin gaban shi kawai yake hankali kwance, gashi kuma yak'i mayar da jiddah har yanxu sai kwane kwane yake yiwa abba, don shi fah har ga Allah daman ba son jiddah yake ba, umma ce ta had'a auren gashi kuma yanxu bata nuna mishi komai akan lallai sai ya dawo da jiddah don hka ya shiriritar da xancen kuma yaga yanxu bata kiran shi ko text mssg bata turo mishi addu'a ya dage da ita Allah yasa ma ta hak'ura dashi.


Komai nisan lokaci Idan aka sa sai yaxo a yau sauran Sati d'aya bikin nauwara da Dr muh'd duk wasu shirye shirye an gama an kawo lefe ya had'a mata kaya sosai masu kyau da tsada duk wani programs da xa'a gabatar sun gama shirya wa, umma ta xage tana gyara nauwara sosai, hka a 6angaren ammi da aunty safiyya suma sun dage sosai wajen gyaran nauwara in nd out, tayi wani irin kyau fatan ta tayi wani fresh kamar mai rayuwa a k'asar k'ank'ara..... Lol


Kamar yau ranar juma'a da safe wajen karfe 9 na safe abduljabbar ne ya shigo part d'in umma yana sanye cikin wata tsadaddiyar shadda fara sol tasha aiki da bak'in xare yayi kyau sosae ya sanya bak'in takalmi da hula agogo duk bak'ak'e ya sanya farin glass a fuskar shi yayi kyau kamar wani ango
Fuskar shi shimfid'e da kyakkyawan Murmishi ya gaida umma ba umma ba hatta nauwara fa'iza sai da suka bishi da kallo don kyau kam Yayi kyau babu k'arya ga fara'ar da yake yi bayan sun gaisa da umma fa'iza ce kad'ai ta gaida shi ya amsa mata da Murmishi akan fuskar shi sannan yake sanar da umma xai fita wani waje mai mahimmanci sai yamma xai dawo, da fatan alkhairi umma ta bishi ya tashi xai tafi suka had'a ido da nauwara ai kuwa ya kashe mata ido d'aya da sauri ta kau da kanta ,shi kuwa yayi gaba a farfajiyar gidan suka had'u da abdulkareem yana ganin shi ya bud'e baki xai yi magana da sauri abduljabbar ya toshe bakin abdulkareem yana waige waigen bayan shi yace
"sai ka tona min asiri ne haba abdulkareem, ka bari idan muka bar gidan kayi maganar "
Abdulkareem yana dariyar mugunta yace "tohh Shikenan mu je kaga rana nayi "
Yana gama fad'in hka suka shiga mota abdulkareem ne yake driving suka fice daga gidan.

Bayan an sakko daga sallahr juma'a wajen karfe 3 na rana Abba yana xaune a falon shi umma tana xuba mishi abinci wayar shi ta fara ringing d'auka yayi tare da yin sallama shiru yayi na en mintuna yana sauraran abin da ake fad'a mishi nan take fuskar shi ta rine da 6acin rai maganar da akayi mishi ta K'arshe ya sashi mikewa tsaye yana cewa
"what! don Allah da gaske kake fad'a ?" daga d'ayan 6angaren aka tabbatar mishi da Hkane Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun abin da abba ya fad'i kenan.
Da sauri umma ita ma ta mik'e tana tambayar Abba abin da ya faru ganin ya ajiye wayar ya xube kan kujera tare da dafe kai......



Aishat A muh'd
[25/07, 09:58] Aishat A. Muhd: 🍀🍀☘☘🍀🍀
 *K'ARSHEN WAHALA*
🍀🍀☘☘🍀🍀




*written by*
Aishat A muh'd



*~Pg 91~*



  Dafa kafad'ar abba umma tayi cikin tashin hankali tace
"Abba me yafaru, lafia?"
Dakyar abba ya iya d'ago kanshi ya Kalli umma idanun shi sunyi ja saboda 6acin rai ya bud'e baki ya fara magana da cewa
"wai kamar ni abduljabbar xai mayar dani k'aramin mutum "
Cikin kad'uwa umma take kallon Abba tace
"me yayi abduljabbar d'in?"
Sai da abba ya sauke numfashi Kafin yace
"Ashe fitar nan da yayi da safen nan shi da abdulkareem kaduna suka tafi gidan baffah, yaje ya cewa baffah shi har yanxu yana son nauwara kaddara ce ta raba su gashi wai mun k'i goya mishi baya ya aure ta har an kar6i kayan auren wani, yaje ya kalmaye shi da dad'in baki har ya amince daman maimuna ta fison abduljabbar don har ta ta6a yi min maganar nak'i yarda da xancen ta don ni duk abin da nauwara take so nima ina so, shine baffah yayi ta fad'a wai gida bai koshi ba ba'a kai waje "
Cikin takaici abba ya sauke numfashi sannan ya cigaba da cewa
" shi ne bayan an sakko daga sallahr juma'a baffah ya sake aura mishi nauwara a karo na biyu, sai bayan an d'aura auren yake kirana Ya sanar da ni, yanxu Don Allah ina xan kai kunyar yaron nan muh'd an kar6i kayan shi da komai biki ya rage sauran k'wanaki 7, wlh ba don baffah yace kada na k'ara ta da xancen da sai ya sake ta a yau di'n nan "

Gaba d'aya umma ta rasa abin da xata ce saboda tsabar takaici daman tun da ta ga yanda ya daina damuwa akan auren nauwara tasan akwai wani abin da yake shirin aikatawa ajiyar xuciya ta saki tare da kama hannun abba ta rik'e cikin muryar kwantar da hankali tace
"abba kayi hak'uri gaskia abduljabbar bai kyauta ba sam, amman tun da baffah ya yanke hukunci sai muyi hak'uri da hkan "
"yanxu me xance wa iyayen muh'd dashi kanshi?"

Shiru suka yi kowa yana nashi tunanin can umma ta bud'e baki tace
"sai ayi musu bayanin komai kuma a basu hak'uri "
Shi dai Abba bai ce komai ya xurfafa a tunanin yanda xai 6ullo wa Dr muh'd batare da sun ji haushin su ba, dakyar umma ta lalla6a Abba ya iya cin abinci gashi sai faman gwada kiran wayar abduljabbar yake but switch off kwafa yayi tare da cewa
"d'an banxan yaro dole ya kashe waya mana yasan abin da k'ulla ai"
Ita dai umma bata ce komai.

A ranar abba ya nemo Dr muh'd yaxo suka xauna sai da yayi mishi bayanin komai kafin ya sanar dashi duk abin da baffah ya sanar mishi, ba k'aramin tausayin ya bawa abba yanda ya koma lokaci d'aya sosai mayar da auren abduljabbar da nauwara abin ya bigi Dr muh'd ba k'arami ba
Ganin yanda abba ya dunga rarrashin shi tare da bashi hak'uri yasa shi k'ak'alo murmishin dole yace
"kada ka damu abba ba komai daman Allah ya rubuta nauwara ba *MATA TA CE* ba ce, Allah  ya basu xaman lafia "
Cikin tsananin tausayin shi Abba yace
"hak'ik'a muh'd kai mutum ne managarci baxan so na rasa ka ba had'a xuri'a da kai ba idan ka amince xan aura maka fa'iza? "

Dummmm gaban Dr muh'd ya fad'i ya rasa abin da xai ce da abba duk ya rikice shi ba son fa'iza yake ba amman baxai iya dubar tsakar idon wannan managarcin bawan Allah nan yace baya son d'iyar shi ba da kunya ai gumin da ya tsatstsafo mishi a fuskar shi ya fara goge wa
"kada ka cuci kanka muh'd Idan batayi maka ba Shikenan Allah ya had'a kowa da mafi alkhairi "
Cikin sanyin murya yace "a'a Abba wlh nine da godia, na amince xan auri fa'iza Allah ya bamu xaman lafia "
Cikin tsananin jin dad'i abba yace
"Ameeen, hak'ik'a naji dadin abin da kace muh'd Allah ya yi maka albarka "
Shima cikin murmishi yace "Ameeen Abba Ngde "

Sun d'an ta6a hira har abba yana ce mishi xai xo gidan nasu Yayi wa iyayen shi bayani amman Dr muh'd yace ya barshi da kanshi xai musu bayani ba wata matsala da hka yayi wa abba sallama ya tafi jikin shi a sanyaye.

Ko da yaje gida yayi wa iyayen shi bayanin komai basu ji haushi ko Kad'an ba ai matar mutum kabarin shi Allah ya tsarawa kowa matar shi fatan alkhairi suka yi don hka suka cigaba da shirye shiryen biki.

Da yammacin ranar aminu ya xo gidan amman bai samu ganin nauwara ba sai labarin da yayi matuk'ar girgixa shi yaji abakin umma don da kanta ta sanar dashi komai Hka ya baro gidan jikin shi a matuk'ar sanyaye, a hanya ne yana cikin tafiya a mota hankalin shi ya tafi wani wurin don baya kallon gaban shi bai ankara ba yaga ya kusan kad'e wata mace tana sanye da hijab har k'asa da sauri yayi parking tare da fito wa daga motar ya K'arasa inda ta xubar da kayan da yake hannun ta saboda ta tsorata sosai

Da sauri ya tsugunna ya taya ta kwashe kayan a tare suka d'ago karaf suka yi 4eyes da junan su wanda kowanne daga cikin su sai da gaban su ya fad'i a lokaci d'aya cikin wani irin yanayi yace
"Sannu don Allah kiyi hak'uri ban kula ba dafatan baki ji ciwo ba? "
A kunyace da murmishi d'auke a fuskar ta tace "Laaa ba komae kada ka damu banji ciwo ba "
Cikin farinciki yace "Alhmdullilah amman duk da hka ki shiga mota na kai ki gida "
xaro ido tayi da sauri tace "a'a ngde ai naxo ma gida ina karya Kwana nan na xo gida"
"Duk da hka ranki ya dad'e ko Kina jin tsoro kada na gudu da ke"

er dariya tayi sannan tace "a haba ba wani, tsoron lafia "
"ah Indai da gaske bakya jin tsoron da gaske toh ki xo mu je don Allah "

Ganin ya dame ta yasa ta yarda amman da kafa suka K'arasa gidan nasu har xata shige cikin gidan da sauri ya tsayar da ita tare da cewa
"gashi xamu rabo baki fad'a min sunan Ki ba"
Cikin sanyin murya tace "Sunana hauwa but da jiddah ake kirana "
"wow nyc name sunan mamana ne da ke, sauran contact d'inki idan ba takura "
Ta gaji da tsayuwa so take ta shiga gida don hka ta fad'a mishi ya sa a wayar shi sannan suka rabu xuciyar shi cike da tsantsar farin ciki tun da ya rasa nauwara ga madadin ta nan Insha Allah sai ya auri jiddah da hka ya K'arasa gidan shi.


Da dare misalin karfe 9 Abba, umma, aunty sadiya sai fa'iza, nauwara da saleem acikin falon abba a xaune duk sunyi shiru suna sauraren me Abba xai ce idan ka d'auke umma da tasan komai gyaran murya abba yayi sannan yace
"abin da yasa na tara ku anan ba komai bane sai don nauwara da fa'iza Kuyi hak'uri da abin da xan fad'a muku"
Sai da ya yi ajiyar numfashi Kafin yace
"nauwara a yau abduljabbar yaje kaduna wurin baffah yayi mishi dad'in baki ba tare da d'ayan mu ya sani ba kuma baffah bai neme mu ba ya yanke hukunci ya d'aura miki aure da abduljabbar sai bayan an d'aura ma yake sanar mana toh kiyi hak'uri 'yata amman Wannan Karon xan sa ido sosai a xaman ku idan naga yana rashin kyautata miki xan d'au mataki kin ji "
Cikin wani irin yanayi mai wuyar fassaru wa murya na rawa alamar sauran kiris ta fashe da kuka tace
"toh Abba ngde "
"Yawwa 'yata Allah yayi miki albarka hak'ik'a banji dad'in abin da abduljabbar ya aikata ba"
"Ameeen Abba "
Nauwara ta fad'i tana goge hawayen fuskar ta girgixa kai Abba yayi cike da tausayin ta yarinyar  tana ganin jarabtar rayuwa Kala Kala daga wannan sai wannan amman Insha Allah komai ya kusan xuwa K'arshe, kallon fa'iza yayi sannan yace
"ke kuma na yanke hukuncin aura miki Dr muh'd don baxai yiwu nayi ta xuba miki ido ba kin k'i tsayar da wanda xaki Aura Don hka ku cigaba da shirye shirye lokacin da aka yanke na bikin hka xa'a yi babu d'aga wa"
Daga hka ya sallami nauwara da fa'iza suka fita daga falon aka bar umma da aunty sadiya suna cike da mamakin hukuncin da abba ya yanke

Fa'iza ba k'aramin kad'uwa tayi da wannan hukuncin Abba nan ta xube kan gado tana kuka hka nauwara ma ta xauna kan sofa tare da fashe wa da kuka tana ji ina ma ita ce fa'iza don tayi dace da salihin miji, kuka sosai suke babu mai rarrashin wani.........



Aishat A muh'd
[25/07, 09:58] Aishat A. Muhd: 🍀🍀☘☘🍀🍀
 *K'ARSHEN WAHALA*
🍀🍀☘☘🍀🍀




*written by*
Aishat A muh'd



_wannan page d'in sadaukar wa ne ga en group d'in *K'arshen wahala fans* i really luv u guys_😍



*~Pg 92~*




  Sai da suka gama cin kukan su sannan daga K'arshe suka rarrashi  junan su, ranar ba wanda yayi cikakkiyar runtsa wa bacci tsakanin nauwara da fa'iza don hka Washe gari idanun su yayi luhu luhu duk ya kumbura saboda tsabar rashin bacci da kuka, suna xaune a d'aki kowanne ya xabga uban tagumi yana tunani ko wanka ba wanda yayi umma ta shigo d'akin kallo d'aya tayi musu wani mugun tausayin su ya kamata da hka ta K'arasa inda suke ta xauna a tsakiyar su tare da dafa kafad'ar su, lokaci d'aya suka juyo tare da rungume ta .

Cikin muryar rarrashi da kwantar da hankali ta fara yi musu nasiha mai ratsa jiki da xuciya akan yarda da kaddara Har sai da jikin su yayi sanyi xuciyar ta samu nutsuwa tukunna daga K'arshe ta umarce su suyi wanka breakfast na jiran su sannan ta bar musu d'akin.

Basu dad'e sosai ba suka fito parlour har sunyi wanka kamar had'in baki kowanne yasa simple gown ko make up babu a fuskar su daga powder sai lip stick, bayan sun kammala breakfast suka dawo cikin parlourn xama suka yi ana er hira umma taji dad'i sosai ganin yanda suka saki jikin su,.


********
Zaune yake akan chair di'n dinning area yana shan coffee fuskar shi idan ban da smiling babu abin da yake yi hankalin shi kwance ana hka wayar shi ta fara ringing d'auka yayi tare da mak'ala wa a kunnen shi cikin murmishi yace
"hey guy hw r u ?"
Daga can 6angaren abdulkareem cikin dariya yace
"I'm absolutely fine"
"Gud, i hope everything is going fine ?"
"yes guy, sai dai ka barni da fad'an yaya fah (yana nufin abban abduljabbar)  "
"A haba da gaske ?"
"i swear yaro sai ma kaxo tukunna "
"ohhh my god har yanxu bai huce ba kenan? "
Ya fad'i yana dafe kanshi, cikin tsokana abdulkareem yace
"ina xai huce kuwa bayan kasa ya gama magana da iyayen Dr muh'd"
"toh ya xa'a yi tun da me waje yaxo mai tabarma sai ya nade, Idan ba shishshigi ba ina shi ina habibty nah"

"ae yanxu yaya ya bashi fa'iza ma nan da 1 week xa'a yi bikin, kamar yanda aka sa "
"alright da ita akayi mishi auren huci haushi kenan"
"ofcourse, but ya kama ta kayi kok'arin xuwa ka bawa abba da umma hak'uri don basu ji dad'in abin da kayi ba ga kuma habibty di'n ka kaxo ka rarrashi abar ka, amman don Allah ka kiyaye gaba please "
Shafa gashin kanshi yayi sannan cikin sanyin murya yace
"Ya xanyi abdulkareem ina son nauwara da yawa baxan iya rabu wa da ita ba, Wannan hanyar ce kad'ai xai sa na same ta, kuma Insha Allah xan kiyaye sosai thank u so much bani da kamar ka"
"alright yaushe xaka xo? "
"gobe Insha Allah karfe 5 na yamma ka jirani a airport"
"okay Allah ya kawo ka lafia "
"Ameeen"

Daga hka suka yi sallama ya ajiye wayar tare da kwantar da kanshi kan kujera ya lumshe idon shi shi kanshi Yana son xuwa kano but yana jin tsoro kada abba yasa ya saki nauwara yana son ganin nauwara da twins d'in shi duk da suna waya da na'eem da ameer suna fad'a mishi halin da nauwara take ciki.


******
 Cikin d'an lokaci k'alilan wata iriyar shakuwa da soyayya ta shiga tsananin aminu da jiddah sosai ita kanta tana mamakin yanda son shi har ya shiga xuciyar ta hka ta nemi son abduljabbar farat d'aya ta rasa, iyayen ta su ma sunyi farinciki sosai

Sannan ta fito ta fad'a mishi ta ta6a yin aure duk abin da tayi ta sanar dashi komai bata 6oye mishi ba hkan da tayi ba k'aramin k'ara son ta da yayi ba nan da nan ya turo manyan shi aka tsaida lokacin aure.

Maman jiddah da kanta ta je gidan umma ta sanar da ita sai dai umma bata ji dad'i ba taso abduljabbar ya mayar da jiddah amman hka ta hak'ura tare da neman alfarmar su dawo da bikin dai dai dana fa'iza a had'e su yi tare.
Ta amince da hkan don hka tana koma wa gida tayi wa baban jiddah bayanin komai shi ma ya amince don basu da abin da xasu biya umma da iyalanta abin da suka yi musu sai addu'a tsakanin su, sun kirawo aminu sunyi mishi bayanin komai kuma ya yarda da hkan, don hka nan fah aka rikice da shirye shiryen biki sosai.

Aminu ya had'a kayan lefe sosai an kawo gidan su jiddah, kuma yayi wa hindatu ita ma na fad'ar kishiya sai dai fa ba k'aramin tasar da hankalin ta tayi ba akan auren da aminu xai sake ta d'auki alwashin baxa su ta6a xaman lafia ba har abada Wannan kenan.

Nauwara, fa'iza umma tasa samu mai gyaran jiki na musamman tana gyara mata emmatan ta har jiddah ita ma don tuni ta dawo gidan umma amare sunyi kyau sosai sai shirya yanda biki xai kasance akayi duk wasu abubuwan da xa'a gabatar aunty asma'u, kausar da jiddah sai aunty maryam matar abdulkareem da aunty safiyya kanwar baban su nauwara su suke shirya wa har fa'iza ma yanxu ta saki jikin ta don tuni sun dinke junan su da Dr muh'd suna xuba soyayyar su don Dr muh'd ba daga baya wajen tsari tuni yayi nasarar sace xuciyar fa'iza.

Na'eem da ameer wato twins su ma yanxu sun sakko suna kula Dr muh'd da aminu kamar da daman kishi suke taya papa di'n su so yanxu komai ya wuce tunda baban su yayi nasarar samun mameen nasu, sosai yaran sunyi matuk'ar bawa Dr muh'd da aminu mamaki sosai yaran yanxu akwai wayo......

Ranar da abduljabbar yace xai xo kano bai samu damar xuwan ba saboda wani aiki da ya taso mishi a ranar don hka sai ranar da xa'a yi dinner ana yi gobe d'aurin auren ya samu damar diro wa Kano da yammaci likis, abdulkareem ne yaje ya d'auko shi a airport yana ta tsokanar shi tare da bashi kyakkyawan albishir kan jiddah ita ma yanxu ta gaji da Jan ajin da yake mata aure xata yi gobe ma xa'a d'aura tare da na fa'iza, wayyo dad'i abduljabbar ya rasa inda xai sa kanshi don dad'i ya gode wa Allah sosai yanda ya raba shi da jiddah cikin kwanciyar hankali babu tashin hankali ...........


_kuyi hak'uri da wannan idan na samu time anjima xan sake muku luv u all my fans with all my heart_ 😍😘


Aishat A muh'd
[25/07, 09:59] Aishat A. Muhd: 🍀🍀☘☘🍀🍀
  *K'ARSHEN WAHALA*
🍀🍀☘☘🍀🍀



*written by*
Aishat A muh'd



_wannan page d'in sadaukar wa ne gare ku *Asy khaleel* da *Ummu hambali* ina yi muku fatan alkhairi a duk inda kuke_😍




*~Pg 93~*



    Kai tsaye gidan su abdulkareem yayi dashi cike yake da en uwa ganin hka kawai sai suka wuce part d'in abduljabbar don baya son hayaniya ko umma da abba basu san yaxo ba sai aunty sadiya ita tasan yaxo don ya kirawo ta awaya yana son a had'o mishi abinci don yunwa yake ji, cikin en mintuna er aikin aunty sadiya ta kawo musu xama suka yi tare da fara cin abincin.

Lokacin tafiya dinner yayi kowa ya shirya daga amare, k'awayen amare da en uwa da abokan arxiki a hankali aka fara tafiya wajen da xa'a gabatar da dinner d'in kowa yaci gayun shi cikin ankon bikin .

Dr muh'd da amaryar shi fa'iza suna motar su daban, haka jiddah da angon ta aminu su ma motar su daban don uwargida hindatu tak'i xuwa dinner shi hakan ma ya fiye mishi kwanciyar hankali kada tayi musu hauka acan.

Sai da kowa ya gama tafiya sannan nauwara ta fito xata tafi tana sanye da wani swiss lace green colour nd touch d'in flowers red d'inkin riga da siket sun xauna a jikin ta sosai sai head d'in kanta red colour ne gashin nan ta xubo mishi ya kwanta a bayanta sai shek'i yake tayi kyau sosae takalmi ta hill ne sai poss di'n ta dukka red colour ne, d'ayan hannun kuma phone ne da key di'n mota a gurguje ta fito saboda sai kiranta su fa'iza suke tayi sauri da sauri ta shiga motar tare da yi mata key ta bar gidan.

Tafiyar mintuna 20 ya kaita hall di'n da aka dinner wurin ya had'u sosai yasha decoration white nd blue ga haske sosai, a nutse tayi parking tare da fito wa daga motar ta nufi cikin hall di'n cikin tafiyar kamar ta mai jin tausayin k'asa.

Wow masha Allah gaba d'aya ilahirin wajen hankalin su yayi kan nauwara da take shigo wa kai tsaye inda high table d'in angwaye da amare tayi don nan wurin xaman nata, dogon table ne da six chairs, FA'iza da Dr muh'd, jiddah da aminu, sauran chairs biyu nauwara ta xauna a d'ayar sauran d'aya cikin murmishi ta kalle su tace
"Wow ka ga amare da angwaye u look so cutes, Allah ya sanya alkhairi ya baku xaman Lafia da xuri'a mae albarka "
Da saurin su kusan kamar had'in baki suka amsa da
"Ameeen thumma Ameeen mungode " fuskar d'auke da murmishin jin dad'i .

Daga hka suka cigaba da gudanar da dinner d'in, nauwara ce ta sunkuya tana gyara belt d'in takalmin ta da ta cire sai jin wani irin mugun k'amshin turare wanda mutum d'aya tak tasan shi da wannan k'amshin da sauri ta d'ago da kanta idanun ta ba Inda suka sauka sai kan abduljabbar da yake xaune kusa da kujerar ta yana sanye da wata lallausan shadda milk colour ya turo da hular kanshi gaban goshi da ka ga yanda yasa hular kasan bai saba sa ta ba yayi matuk'ar yin kyau ba Kad'an ba fuskar shi a sake sai faman murmishi yake yana magana dasu Dr muh'd nan take ta d'aure fuska tare da kawar da kanta daga kallon shi duk da kuwa kyan da yayi mata

Bata ankara ba taji yasa kafar shi akan kafarta yana tafiyar da kafar tashi a kafarta har xuwa gwiwar ta amman bayan ya cire shoes d'in kafar shi yana wani shi'umin murmishi da sauri ta kalle shi karaf suka had'a ido ae kuwa ya kashe mata ido d'aya ta6e baki tayi tare da jan d'an siririn tsaki

Lokaci d'aya ya had'e rai sakamakon ganin wani yanki na gashin kanta ya fito waje cikin fusata yasa hannu ya gyara gwaggwaron Kan nauwara ya kife shi a kanta, kallon shi tayi rai a 6ace kamar xata fashe da kuka ganin yanda ya 6ata mata k'walliyar ta wani murmishin mugunta ya saki tare da daga mata gira haushi ya dad'a kume ta tace
"me nayi maka malam xaka 6ata min Kwalliya ta, ko na kula ka ne? "
"Ah babu abin da kika min habibty just na gyara abin kan Ki ne"
Harara ta dalla mashi tare da Murgud'a baki kallon ta yake cike da so da k'aunar ta ga wata muguwar sha'awar ta da yaji ya kama shi kallon lips d'in ta yake kawai wanda suka sha jambaki red sai shek'i suke .

Anutse ta d'ago da idon ta suka had'a ido lokaci d'aya suka xuba wa juna ido cike da wani irin yanayi a tattare da kowanne a cikin shi duk yanda nauwara taso janye idonta ta kasa yayin da abduljabbar daman shi haka yake so, ji tayi ana jijjiga ta da sauri ta kau da kanta daga kallon shi tare da sakin wata irin ajiyar xuciya muryar na'eem taji yana cewa
"Laaa mamee da papa suna kallon k'uda irin wanda muke yi a school ko ameer ???"
"ehhh hakane wlh "
Cewar ameer wata irin kunya ta rufe nauwara sai faman hararar twins take, gaba d'aya wajen aka kyalkyale da dariya har da abduljabbar nauwara tayi kicin kicin da fuska, daman duk abin da suke su fa'iza suna ankare dasu sai faman dariya suke musu.
"papa ku cigaba da yi mu ga wanda xai yi wining tsakanin ka da mamee "
Cewar ameer janyo shi yayi jikin shi tare da bashi peck a kumatun shi yace
"that's my boy, ae mameen ka matsoraciya ce baxa ta iya ba"ya fad'i yana jifan nauwara da wani salon kallon shi k'asa k'asa.
Cikin shagwa6a na'eem yace
" mamee ki yarda please "
Cikin jin haushin su gaba d'aya takai hannu xata make na'eem da ya dame ta ai kuwa da sauri ya rik'e mata hannu tare da yi mata alamar ina ruwan ta kada ta dakar mishi yaro, a fusace ta tashi tare da barin hall di'n gaba d'aya.

Da sauri ya tashi yana rik'e dasu na'eem ya juya xai bita yaji aminu yace
"yalla6ai ba dai tafiya ba,gashi ka kori er gidan taka"
Yana shafa kanshi yace "ya xa'a yi aminu rarrashin ta xanje nayi sai mun had'u gobe don ni daga nan sai gida"
Caraf Dr muh'd yace "Ohh kace don ita kaxo kenan "
"yes ofcourse ita na biyo doctor tun da ta tafi xamana bashi da amfani don hka nayi nan byeee "
Suna mishi dariya yaja hannun na'eem da ameer suka fice daga hall di'n a farfajiyar wajen suka tsaya suna duba ta basu ganta ba mybe ta tafi gida xuciyar shi ta ayyana mishi don hka motar shi ya shiga suka bar wurin, ko da suka xo gida bai gan ta ba sai umma ya gani ya tambaye ta nauwara ta dawo nan ta tabbatar mishi ta dawo Sannan hankalin shi ya kwanta ba k'aramin jin dad'i yayi ba ganin umma bata nuna mishi komai ba kamar yanda take mishi da hka ma yau tayi mishi har da tambayar shi yana buk'atar wani abun ganin ya samu fuska yace yana son shan fruit kawai Idan xai samu daga hka ya fice xuwa part din shi, da kanta umma ta yanka mishi fruit d'in ta aika mishi xuciyar shi cike da tsantsar farin ciki yasha fruit salad d'in nan da hka har bacci ya d'auke shi xuciyar shi cike da tunanin habibty di'n shi........



Aishat A muh'd
[25/07, 09:59] Aishat A. Muhd: 🍀🍀☘☘🍀🍀
 *K'ARSHEN WAHALA*
🍀🍀☘☘🍀🍀



*written by*
Aishat A muh'd



_dedicated to haleema Ameen nd biebie deee, ina yi muku fatan alkhairi a duk inda kuke_😍




*~Pg 94~*




    Washe gari misalin karfe 11 aka d'aura auren Dr muh'd da fa'iza, sannan nasu Aminu da jiddah akan sadaki mafi cancanta don neman albarkar aure, abba, abduljabbar, abdulkareem, Dr muh'd ,Aminu,saleem da na'eem da ameer gaba d'aya ankon tsadaddiyar farar shadda suka yi har da babbar riga sun yi matuk'ar yin kyau ga wani kwarjini da suka yi fuskar su d'auke da tsantsar farin ciki sai faman gaisa wa suke da wad'anda suka hallaci wannan d'aurin auren, bayan an gama d'aurin auren suka wuce yin reception na maxa an ci ansha a wurin sun sha addu'a daga bakunan mutane na xaman lafia da xuri'a mae albarka haka aka watse kowa cike da farin ciki.

Cikin gidan nan ya cika da mutane sosae en uwa da abokan arxiki sai taya su umma ake murna tare da yiwa amare fatan alkhairi Allah ya bada xaman lafia.

Nauwara, fa'iza, jiddah, aunty asma'u, aunty kausar, aunty maryam da suna xaune a bedroom d'in su nauwara kowanne yasha kwalliya ta Kece raini dukkan su fuskar su d'auke da Murmishi sai hira ake suna cikin haka abduljabbar da abdulkareem suka shigo d'akin a nutse aunty asma'u ce ta Kalli abduljabbar wanda yake sa6e babbar riga tana xamo wa yana sake gyara wa alamar bai saba da sawa ba ae kuwa ta kyalkyale da dariya tare da cewa
"Allah abdul kaji kunya yanxu ace babbar rigar ma har yanxu baka iya sawa ba an fah girma "
Harara ya watsa mata tare da jan wani d'an siririn tsaki yace
"kin fiye sa ido da yawa asma'u ba wanda ya kula da hkan sai ke Allah ki fita a idona "
Ya K'arasa fad'i yana huro hanci abdulkareem wanda yake danne dariyar shi yace
"waii ke ina ruwan ki ne asma'u Indai ki ga wannan d'an nawa sai kin tsokane xan fa d'au mataki akan ki"

"heeeeyyy lallai ma abdulkareem din nan Indai wannan abduljabbar d'in kake tare wa wataran sai ya mun ganku a rana"

Gaba d'aya d'akin aka kwashe da dariya har da nauwara sai da ta murmusa shi kuwa uban gayyar had'e fuska yayi tare da cewa
"ya xa'a yi ki dunga yi min magana kowacce iri ce a gaban kannen salon su rainani "
"Ahayyeee su raini manya dad'in abin kai di'n k'anina ne "

Ko kula ta bai yi ya nufi inda nauwara take a xaune a gefen bed jiddah wadda take kusa da ita a xaune ya wani d'auke kai cikin isa yace
"hey d'an ban wurin naji dumin mata ta"
Dariya jiddah tayi tare da tashi da sauri tana cewa
"ni bari ma na bar maka d'akin kaji d'umin da kyau "
"Yawwa da kin kyauta er k'anwa ta su wad'annan en sa idon sai sun ga kwakwaf "
Tana dariya ta bar d'akin tare da fa'iza, kausar ta mik'e tsaye tana cewa
"ni fah yunwa nake ji ko breakfast ban yi ba ni ma nayi nan "
Tana gama fad'in hka ta fita daga d'akin tana kunshe dariya, xube wa yayi kan bed d'in tare da fad'in "Washhh na gaji wlh da ni d'an gata ne da sai ayi min tausa"
Ya fad'i yana kallon fuskar nauwara wadda ta had'e fuska, aunty asma'u ma tashi tayi tana cewa
"toh mara kunya so kake dai na bar d'akin, ba don nauwara ba da Allah ba Inda xan je sai dai duk abin da xaka yi kayi a gaba na"
"Ahhh ae da Kinyi xaman ki waya kore ki sarkin sa ido "
Abduljabbar ya fad'i yana dariyar mugunta wani k'aramin pillown ta cillo mishi ya cafe yana dariya sannan ta fice daga d'akin abdulkareem ya Kalli maryam yace
"my wife taso mu tafi ya yiwa kowa kora da hali tun Kafin ya kore mu ma "

Yana shafa kanshi yace "ni kada ka had'a ni da maryam ni bance kowa ya tafi ba "
"ae gwara mu baka wuri "
Maryam ta fad'i tana kamo hannun abdulkareem suka fice daga d'akin aka bar nauwara da abduljabbar.

Tashi daga kan bed d'in nauwara tayi tana shirin ban mishi d'akin da sauri ya rik'o hannun ta, ta juya da kanshi tana kallon shi shima ita yake kallo cikin marairaice fuska yace
"Haba habibty wai har yanxu baki hak'ura ne? "
Turo baki tayi kafin tace "ni ka cika min hannu ina da abin yi please "
Bai ce komai ba ya janyo ta tare da xaunar da ita kan bed d'in shi kuma ya tsugunna a k'asa tare da dire gwiyoyin shi k'asa yana rik'e da hannun ta idanun shi akan fuskar ta cikin nutsuwa yace
"gani a durkushe a gaban ki a karo na biyu baxan tashi anan ba har sai kin hak'ura na gaji da wannan yanayin da kike nuna min baxan iya jure wa na gaji da axabtar dani da kenan ina sake baki hak'uri "
Wani irin mugun tausayin shi taji ya kamata tare da wani mugun son shi da ya k'ara shiga cikin xuciyar ta duk jikin ta yayi sanyi sosai bata ankara ba ta ga wasu hawaye suna fita a idanun shi suna sauka akan hannayen ta da yake rik'e dasu, toh me yasa baxa ta hak'ura ba wacce irin xuciya ce da ita mutumin da shi ya taimake ta a rayuwa ya cece ta daga fyad'en da akayi yunkurin yi mata ya kai ta asibiti ya nema mata magani ta warke ta dawo tana tafiya tana kallon mutane da idanun ta kamar kowa ya sata a makaranta har takai matsayin da ya nuna mata so da k'auna ya aure ta har Allah ya basu albarkar yara 2 kaddara da sharri yasa ya rabu da ita gashi gaskiya ta bayyana yayi nadama tare da Bata hak'uri ae ya kamata ta hak'ura kuwa ko Allah Muna yi mishi laifi mu rok'e shi ya yafe mana balle kuma mu en Adam don hka cikin jin tausayin shi murya a sanyaye tasa hannu ta goge hawayen fuskar shi tare da cewa

"Don Allah ka daina xubar da hawayen ka please "
"baxan dai na Idan har baki hak'ura ba"
Ya fad'i hkan yana sake rik'o hannun ta gam a  cikin hannun shi a hankali ta fara cewa
"na hak'ura Yah abduljabbar daman ae d'an ajixine, ni tun tuni na yafe maka amman ina son gaba kada dunga bincike Kafin ka yanke hukunci "

Cikin tsananin farinciki yace "nauwara da gaske kin hak'ura? "
Cikin jin tausayin yanda duk yabi ya rud'e cikin tabbatar wa tace "da gaske nake Allah ya yafe mana gaba d'aya "
Da sauri ya rungume ta tsam a jikin shi tare da cewa "Ameeen thank u habibty nah,  kuma Insha Allah xan kiyaye gaba "
Ya cigaba da cewa "i luv u baby nah i really miss u "
Duk gaba d'aya ya rikice mata da godiya a hankali ta lumshe idon ta hawaye suna xuba a idon ta wanda bata san name ne ba na farinciki ne ko akasin hka, had'a fuskar shi da ta ta xai yi yaga hawaye a fuskar ta a rikice yace "baby nah bakya so na rabu da ke? " shiru tayi bata ce komae ba ganin hka yasa shi cikata tare mik'e tsaye cikin sanyin jiki ya juya xai fita daga d'akin ganin hka yasa ta tashi da gudu ta karasa inda yake ta rungume shi ta baya tare da fashe wa da kuka runtse idon shi baya son kukan ta ko Kad'an a hankali ya juya tare da rik'e mata kafad'un ta yace
"calm down nauwara what wrong with u? "
Kasa magana tayi don kuka yaci k'arfin ta hankalin shi gaba d'aya ya tashi xauna wa yayi kan sofa tare da xaunar da ita kan kafafun shi nan ya fara rarrashin ta har ya samu tayi shiru sai ajiyar xuciya da take saki akai akai duk fuskar ta tayi ja idanun ta sun kumbura ita kanta batasan dalilin kukan nata ba ganin tayi shiru yasa shi cewa

"what happened to u nauwara, me yasa ki kuka haka? "
"ni kawai haka naji kukan yaxo min "
"ohhh my god nasan Akwai wani abun fad'a min kinji my dear "

Cikin sanyin murya tace "da gaske nake yi fah"
D'an xaro ido yayi Kad'an ya kama kumatun ta duk biyun yace "shine kika d'aga min hankali, are you sure babu wani abin ?"

Jijjiga kai tayi ba tai magana ba d'an siririn murmishi ya saki tare da cewa "thank u once again i luv u baby nah Allah yayi miki albarka "

A hankali ta bud'e d'an k'aramin bakin ta tace "Ameeen "
Bata peck yayi a kumatu da goshi sannan kan lips d'in ta sannan ya bar d'akin, xuciyar shi wasai cike da farin ciki sai faman murmishi yake bai damu da tattare war da shaddar jikin shi yayi ba sai dariya ake mishi wasu na tsokanar shi sai dai ya shafa gashin kanshi tare da Murmishi ko uhm bai ce ba har ya fice daga part d'in umma ya nufi nashi.

Ita kuwa nauwara kwanciya tayi akan sofa tare da rungume pillow a kirjin ta wani sabon son abduljabbar ne yake dad'a shiga xuciyar ta yanxu wasai take jin xuciyar ta.

Da yammaci aka gabatar da Mother's Day bayan sallahr mangariba kuma aka mik'a kowacce gidan mijin ta  banda nauwara daga FA'iza sai jiddah sun sha kuka sosai tsakanin FA'iza da nauwara xasu yi kewar junan su don ba k'aramin shakuwa suka yi ba hka twins sun sha kuka su ma,

Dakyar fa'iza ta cika nauwara suka tafi gida jikin nauwara a sanyaye, suna k'arasa wa gida wanka ta iya yi tabi lafiyar gado don ba k'aramin gajiya tayi ba nan da nan bacci yayi awon gaba da.......



Aishat A muh'd
[25/07, 09:59] Aishat A. Muhd: 🍀🍀☘☘🍀🍀
 *K'ARSHEN WAHALA*
🍀🍀☘☘🍀🍀




*written by*
Aishat A muh'd


_dedicated to khalfana (sister d'in neena cool), muna godiya sosae Allah ya bar xumunci, ina miki fatan alkhairi_😍



*~Pg 95~*




  Tana xaune a dinning area tana breakfast duk yau tashi tayi jikin ta a sanyaye saboda yau ammin ta da inna, aunty safiyya xasu koma kaduna jin tayi an rufe mata idanun ta k'amshin turaren shi kad'ai taji ta gane ko wane cikin mak'e murya yace
"canki wane?"
tana murmishi tace
"Haba kasan na gane ka kawai ka bud'e min ido "
Ta K'arasa fad'i tana Murgud'a baki kallon ta yayi cike da k'aunar ta ya bud'e mata idon tare da janyo kujera ya xauna a kusa da ita yana kallon ta ita  ma shi take kallo sun sauke en mintuna suna kallon junan Kafin nauwara ta fara janye idonta tana cewa
"dafatan ka tashi lafia? "
D'an ta6e baki yayi tare da cewa "ehhh to lafia ba lafia ba? "

D'an xaro ido tayi cike da mamaki tace "Idan ba lafia ka tashi ba to yana ganka qlau da kai??"

"Idan kin ga gangar jikina lafia to nan "
Ya dafe xuciyar shi ya cigaba da cewa "ba lafia yake ba yana cike da son ki da kaunar ki ta Kasa samun nutsuwa Har sai ta ji d'umin mahad'ar ta "
Ya gama fad'a yana kashe mata ido hararar shi tayi shi kuwa ya wani marairaice fuska sosai ya bata dariya ganin yanda ya wani langa6e kai kamar k'aramin yaro ganin har yanxu ta kasa sakin jiki dashi ba kamar da ba kuma yasan sai a hankali gashi kuma cike da wata iriyar sha'awar ta yake d'aure wa kawai yake yi, don baya son ya matsa mata yafi son ya gama goge laifin shi gaba d'aya a gurin ta .

"na had'a maka tea ne? ", girgixa kai yayi cikin kalar tausayi yace " Idan da ni kike to a koshe nake, umma ta aiko min da shi yanxu ma da kika ganni abuja xan tafi ana nema na"

Cikin d'an mamaki tace "daga xuwan xaka koma?"

"toh ya xanyi tunda yanayin aikin namu kenan, da dai ni d'an gata ne da sai ki shirya mu tafi tare"
Da sauri ta girgixa kai tana cewa "a'a ni ina kusa da umma "
D'an murmishi yayi yana shafa sajen shi yace "ba wani nan kema nasan kina son ki ganki kusa da mijin ki kawai irin kawaicin nan ne irin na mata ko ba hka ba? "
Ya tambaye ta yana d'aga gira haushi ya rufe nauwara don ta gane abin da yake nufi hararar shi tayi tare da mik'e wa da sauri ta bar wurin bin ta yayi da kallo Kafin ya dunkule hannun shi ya daki table d'in yana cewa

"ohhh my god na kwafsa ashe Hka na saki baki ina magana gashi nan garin gyaran gira........ "
Da sauri ya mik'e tsaye ganin sauran 30 mint jirgin da xai bi  xuwa abuja ya tashi don hka Agurguje yayi sallama da en gidan ya tafi ko gimbiyar tashi bai samu ganin ta ba.


Sai wurin 12 su ammi suka tafi umma sai godiya take musu ita kawai hka taji tana bala'in son ammi nan aka rabu cike da kewar juna.



Tun da ya tafi abuja kullum abduljabbar cikin waya yake yiwa nauwara ban da text mssg di'n shi na ta taimaka ta yi picking d'in wayar shi dakyar da yarda take d'aukan wayar tashi tun tana k'in yin magana har yakai da ta saki jiki suna d'an ta6a hira hkan ba k'aramin jin dad'i yayi ba, na'eem da ameer ma sai dad'a girma ake suna ta xuwa skul d'in islamia da boko ga nauwara da saleem suna yi musu lesson a gida baki ya dad'a bud'e  yanxu ai ta xuba surutu ga wayo.


Saleem ma yanxu kok'arin had'a degree di'n shi yake an fara xama babban mutum ba ruwan shi akwai nutsuwa da hankali, bai fiye fita irin yawo nan ba daga makarantar boko sai islamia don ya dage da neman ilimi addini sosai, idan ya dawo xaka same shi yana yiwa twins lesson ko ki ganshi a kitchen ya xage yana taya umma ko nauwara girki suyi tayi mishi dariya amman shi ko ajikin shi kawai girki yana burge shi, kullum nauwara gode wa Allah take da yayi musu wannan gatan na dace da en rik'o na gari, gashi saleem kamar su d'aya da abban su har dariyar shi da murmishi shi yasa take yawan kallon shi kallon shi da take yana tuna mata da abban su wani lokacin har tambayar ta yake lafia irin wannan kallon sai dai kawai ta girgixa kai tare da yin murmishin yak'e tace ba komai.


Sai da abduljabbar yayi wajen 4 weeks bai xo kano ba sai da waya saboda tarin ayyukan da ke gaban shi gashi gaba d'aya a tak'ure yake d'aure wa kawai yake ana hka ya d'an samu sararin aikin yana shirye shiryen tahowa, wani aiki ya ttaso mishi dole ya hak'ura da xuwan ya tafi duk haushin aikin ya ishe shi kamar xai yi kuka  a lokacin hka yaji aikin da ya d'auke shi wajen 1 month again.


Da sauri ta fito daga toilet jin k'arar wayar ta tana d'aure da towel ajikin ta ganin abduljabbar ne me kira yasa ta d'auka tare da yin sallama amsa wa yayi duk suka yi shiru lokaci d'aya Kafin daga can abduljabbar yace

"habibty nah nayi missing di'n ki sosai don hka ki shirya tar6ar mijin ki ranar Friday nan da k'wana 2 kenan "

Ji tayi gaban ya fad'i jin irin muryar da yayi amfani da ita wajen maganar tayi shiru don ta rasa mai xata ce

"ya kika yi shiru ko baki farinciki da xuwan nawa ba "
"hmm ni na isa nace haka, Allah ya dawo da kai lafia "
"Ameeen habibty, ina twins d'ina? "
"suna parlour wajen umma "
"Yayi kyau, ina son don Allah ki je part d'ina da kanki nake son ki gyara min please "
Shiru ta d'an yi Kafin tace "okay ba matsala xan yi yanda kace "
"that's my girl, ngde sosae Allah yayi miki albarka "
"Ameeen "

Daga hka suka yi sallama ta ajiye wayar tana tunanin abin da ya kamata tayi mishi wanda xai ji dad'i nan ta xurfafa a tunani...........



Aishat A muh'd
[25/07, 09:59] Aishat A. Muhd: 🍀🍀☘☘🍀🍀
 *K'ARSHEN WAHALA*
🍀🍀☘☘🍀🍀




*written by*
Aishat A muh'd





*~Pg 96~*





    Ranar Friday tun da ta tashi daga bacci bayan ta gama breakfast, ta nufi part d'in Yah abduljabbar ta fara gyara mishi tun daga toilet, bedroom nd parlour ta tsabta ce su kayan wankin shi ta tattara ta bawa mai yin wanki har wardrobe d'in ta gyara, Ohh ji don Allah yanda ya tattaro kaya kamar wanda xai xauna a gidan kamar bashi da gida nauwara ta fad'i tana ta6e bakin ta, ta canja mishi bed sheet, bayan ta gama gyaran ta turare ko'ina da turaren wuta ta k'ara da air freshener masu k'amshi ta fesa a d'akin ta saki labulen ta kunna AC sansanyan k'amshi da sanyi mai ratsa jiki ne yake tashi kawai tana gama wa ta fito ta nufi 6angaren umma a gajiye take sosai ta xube akan carpet kusa da kafar umma tana cewa
"washhh Allah na gaji da yawa umma"
Kallon ta umma tayi tana cewa
"sannu, ban da rigimar abdul ba sai asa er aiki ta gyara ba gashi nan ya gajiyar da ke "
Tana lumshe idon ta tace
"Laaa umma ba komai Bari naje na shirya mishi abinci "

Kama baki umma tayi tana cewa "rabu dashi ya ci abin da muka girka, ki je ki kwanta ki huta "

D'an marairaice wa tayi cikin er shagwa6a tace "umma xan iya fah"
"toh Shikenan, ke dae Allah yayi miki albarka "
Cikin jin dad'i ta amsa da "ameen  umma nah"

Daga hka ta mik'e ta nufi kitchen umma ta bita da kallon tana murmishi hak'ik'a d'an ta yayi dace da mata ta gari, Allah ya kare mata su daga duk wani abin k'i.



Girki sosai ta tsaya tayi mishi farar shinkafa ce da miyar hanta sai pepper chicken ta had'a mishi costlow sai tayi mishi samosa da scott eggs sai coconut drink ,da taimakon er aikin umma ta kammala had'a wa bayan sun gama ta fice daga kitchen d'in a jigace duk tayi wani wujiga wujiga suna had'a ido da saleem ya kwashe da dariya don dawowar shi kenan daga skul umma cikin mamaki ta d'ago kanta tana kallon shi ganin yanda ya xage yana dariya lokacin da ta Kalli nauwara ita ma dariya abin ya bata, hararar saleem tayi tana cewa
"malam lafia kake min dariya "
Ta wani d'aure fuska sake tuntsire wa yayi da dariya kafin ya ce
"aunty nauwara kin ga kuwa yanda kike koma? "
Ya cigaba da cewa "tabbb kamar wadda tayi sati a tsaye tana aiki, gaskia Yah abduljabbar yana da raguwar mace "

Mtsww taja tsaki tare da kara had'e fuska tace "Allah saleem ka kiyaye ni idan na rik'e ka xaka yi bayani "

"heeee lallai aunty nauwara Idan ba kin rik'e ni baxa ki iya yi min komai ba "

Ya fad'i yana mata gwalo kwafa tayi sannan cikin shagwa6a tace "umma kin ganshi koh? "

Umma ta danne dariyar ta ta Kalli saleem tace "ba ruwan ka saleem ka kyale ta "

"toh umma na daina "
Ya fad'i yana kallon nauwara ya cigaba da cewa "don Allah aunty ki bani aron key di'n motar ki don da ita xamu masallaci ni da twins "

"tabbb yanxu ka gama tsokanar tawa ka xo kace na baka aron mota ta ban bayar wa"

Marairaice fuska yayi tare da kwantar da kai yana cewa "please my dear sis"

Abduljabbar wanda yake tsaye yana kallon duk abin da suke ya fara cewa "saleem kada ka damu anjima xamu je ka xa6i motar da kake so "

Gaba d'ayan su suka juyo suna kallon shi d'an tsallen murna saleem yayi tare da hugging di'n abduljabbar yana cewa "Oyoyo Yah abduljabbar, thank u so much ka ga na huta nace aban aron mota a dunga yi ja min aji Kafin aba ni"
Ya fad'i yana yamutse fuska, cikin murmishi abduljabbar ya d'ora hannun shi akan bakin shi yana cewa
"shiiiii bana son godia"

"ka xo lafia Yah abduljabbar "

Yana shafa kanshi yace "lafia qlau, ya kake? "

"I'm absolutely fine "
"Good my boy "

Sannan ya juya wajen da nauwara take a tsaye amma wayam alamar ta gudu d'aki d'an girgixa kai yayi Kafin ya xauna su gaisa da umma tana Tambayar shi an xo lafia, ana hka Abba ma ya fito cikin shirin tafiya masallaci don lokaci ya gabato bayan sun gama gaisa wa yana kok'arin tambayar su twins sai Gasu nan sun fito da gudu sun sha manyan kaya yadin kufta ne kalar dark blue d'inkin cif a jikin su sunyi kyau sai k'amshin turare suke .

Da gudu suka haye jikin abduljabbar suna murnar ganin shi,  shima rungume su yayi cike da jin dad'in ganin su yayi kewar su, daga hka suka fice xuwa masallaci umma tana yi musu addu'ar Allah ya dawo dasu lafia.

Nauwara kuwa tun lokacin da ta ga abduljabbar ta gudu d'aki toilet ta shige wanka tayi sannan ta fito dressing mirror ta nufa ta fara busar da gashin kanta da hand dryer bayan ya bushe sannan ta shafa mishi mai ta d'aure da ribbom, wani mai cream ta d'auko ta shafa sannan ta d'anyi light make up ta shirya kanta cikin wata atampha d'inkin riga da siket ne sun xauna a jikin ta ta d'aura d'ankwalin kayan kusan rabin gashin nata a waje madubi ta kalla tayi murmishi ita kanta tasan tayi kyau, different perfumes ta fesa har da arabian perfumes banda body spray da tayi using dashi a cikin jikin ta wani irin sanyayen k'amshi take fitar wa duk motsin da tayi.

Da yake tana period yasa ta xauna kan sofa tare da daukar wayar ta ta bud'e data tuni messages suka fara shigo wa ganin fa'iza da jiddah a online yasa ta farinciki nan suka 6arke da hira suna tambayar ta yaushe xata  xo gidajen su nan tace musu tanan tafe Insha Allah .

Anan jiddah take neman shawarar su yanda xasu xauna da kishiyar ta hindatu lafia fitina ce da ita bata son a xauna lafia daga wannan sai wannan ita har ta fara nadamar auren aminu, Allah sarki rayuwa wai jiddah ce take neman yanda xasu xauna lafia da kishiyar ta, daman Hka rayuwar ta gada duk abin ka sai ka samu wanda ya fika, sun tausaya mata sosae nan suka d'an bata shawarwari masu kyau taji dad'i sosai, anan tayi musu albishir aminu ya bar ta xata cigaba da xuwa aikin ta sunyi mata murna tare da yi mata addu'ar Allah ya taimaka.

K'wata k'wata hankalin ta yana kan wayar bata san da Shigowar shi dakin ba don ko k'arar bud'e kofa Allah bai sa ta ji ba xama yayi kusa da ita tare da sa hannu ya kwace wayar da sauri ta d'ago kanta suka had'a ido sun d'auki tsawon 20 seconds suna kallon junan su Kafin nauwara cikin d'an jin kunya ta d'auke idanun ta a kanshi kamo ta yayi xuwa cikin jikin shi ya rada mata a kunne

"Kinyi kyau baby nah i luv u "
ita dai murmishi kawai take kafin dakyar ta bud'e baki tace "i luv u too yayanah "

Sake Kank'ame ta yayi ajikin shi lokaci d'aya suka saki ajiyar xuciya, kallon lips d'in ta yake cike da sha'awa ita kuwa turo bakin nata tayi tare da yin fari da ido tace
"wannan kallon fah Yayi, Allah xan tashi na bar maka d'akin "
Ta K'arasa fad'i cikin shagwa6a Murmishi kawai yake don duk ta ruda shi ya kasa cewa komai kafin ta ankara har bakin shi yake cikin nata, nan fah ta fara kici kicin kwace bakin ta cikin wata irin voice wadda batasan abduljabbar yana da ita ba yace " Haba babynah ki kyale please "
Gaba d'aya jikin shi rawa yake don ya axabtu iya cewa rabon shi da mace har ya mance dole ya rud'e kuwa, ganin hka yasa ta saki jikin ta ta kyale shi yana yanda yake so don tasan duk rawar jikin shi a iya nan xai tsaya da ta tuna haka har da sakin wani murmishin mugunta,      ( kai nauwara Kina wahalar da abduljabbar d'in ki...lol ).


Sun d'auki tsawon lokaci a haka Kafin ya rabu da ita dakyar yana sauke numfashi tare da sakin ajiyar xuciya akai akai, dago kanta tayi suka had'a ido gabanta sai da ya fad'i ganin yanda idanun shi sukayi ja dasu, kallon ta yayi cike da wani irin yanayi yace "me yasa baki fad'a min Kina cikin Wannan yanayin ba da sai na bari sai wani week d'in na xo, Kinsan halin da nake ciki kuwa habibty? "
kallon shi tayi tare da girgixa kai duk tausayin shi ne ya kamata ganin yanda ya koma duk sunyi shiru wajen one mint sannan yace

"mu je ki bani abinci yunwa nake ji "
Da sauri ta mik'e tsaye tare da gyara rigar jikin ta daukan ribbon di'n ta tayi ta k'ara d'aure gashin ta sannan ta d'aura d'ankwalin nata tace
"taho mu tafi kaci abincin "
Haka ya tashi jikin shi ba k'arfi sosai suka fita daga d'akin akan dinning table ta jera mishi komai sannan tayi serving d'in shi xama yayi yaci abincin nan sosai yana xuba mata santi.

Sai ga na'eem da ameer nan sun fito daga d'akin saleem suka yo wajen iyayen su, abduljabbar ya d'auki na'eem akan cinyar shi yana bashi abinci yayin da nauwara kuma ta d'auki ameer tana bashi suna hirar su gwanin sha'awa lokaci lokaci abduljabbar yana jefan ta da wani irin kallo da idanun shi wad'anda har yanxu basu dawo dai dai ba, duk lokacin da yayi mata wannan kallon sai gaban ta ya fad'i.


Bayan sun kammala ci ne ya kwashi su na'eem suka tafi rakashi gidan abdulkareem.


Bedroom d'in umma ta shiga taji tana waya lokaci d'aya taji gaban ta ya fad'i da taji tana magana akan wai an tsayar da next Friday xa'a d'aura auren cikin mamaki nauwara take kallon ta ita kuwa umma tana waya tana kallon nauwara da Murmishi akan fuskar ta bayan ta gama ta ajiye wayar ta ce

"nauwara lafia kika xuba uban tagumi, koh abduljabbar ne yayi miki wani abun? "
girgixa kai tayi tace "umma wane xai yi aure next Friday? "

Murmishi umman ta sake yi Kafin tace "abban ku ne xai dad'o mana abokiyar xama"
Xaro ido nauwara tayi cike da mamaki tace "umma aure kika ce fa, kuma wai abba"
"k'warai da gaske kuwa abin da kunen ki yaji na fad'a miki Hkne "
"toh umma waxai aurah ne? "
sai da umma ta tuntsire da dariya ganin yanda nauwara ta firgice "umma is not funny ,ki fad'a min please "
"toh ammin ki xai aura mun xauna da abban ku, abduljabbar dani mun yanke hukunci xai auri maimuna "

Wani irin kallo naga nauwara tana bin umma dashi Kafin ta ce "it's impossible umma hakan baxai faru ba, kun mana hallaci baxa mu saka miki da wannan abin ba"


Tana gama fad'in hka ta fice daga d'akin da gudu tana kuka sosae, ta bar umma cike da mamakin abin da nauwara tayi.........





Aishat A muh'd
[25/07, 09:59] Aishat A. Muhd: 🍀🍀☘☘🍀🍀
  *K'ARSHEN WAHALA*
🍀🍀☘☘🍀🍀




*written by*
Aishat A muh'd





*~Pg 97~*






    Kuka sosae take tana cewa "baxai yiwu ba umma baxa mu saka miki da haka ba, wayyo Allah nah, sam wannan abin ba me yiwa ne ba"

Kuka take sosai tana faman xuba  sumbatun magana don ita har ga Allah baxa ta so hakan ya faru ba, ji tayi an dafa mata bayan ta da sauri ta d'ago kanta umma ta gani a tsaye fuskar ta d'auke da damuwa, xama tayi kusa da ita tana cewa
"tashi mu yi magana nauwara "

Tashi xaune tayi tana goge hawayen fuskar ta tak'i kallon Inda umma take, murmishin manya umma ta saki tare da kamo hannun nauwara ta fara magana a nutse

"da farko ina son na fara da tambayar ki, wannan auren da abban ku da ammin ki haramun ne??? "

D'an shiru nauwara tayi kafin tace "ba haramun ba ne "
"toh Indai ba haramun ba ne,me ne na d'aga hankalin ki haka, ko don Abba talaka ne baxai iya auren maimuna ba? "

Da sauri nauwara ta d'ago kanta tana kallon umma cikin tsananin mamaki
"ki dai na mamaki just answer me "
"kaiii ni wlh ba don hka ba umma "
"toh bakya son ki ga ammin ki tayi aure ne, Kinsan har yanxu bata shige haihu wa ba, kuma Kinsan aure shine cikar mutuncin 'ya mace tun da bata shige hakan ba sai anfi ganin ta da mutuncin ta "
Shiru nauwara tayi tana sauraren umma yayin da umma ta cigaba da cewa " ita ma ammin naki baki ga yanda muka shawo kanta har ta yarda ba ni banso kika ji ba sai bayan an d'aura auren,kuma da kike cewa bai kamata ku saka min da auren nan ba, ni kuwa wannan auren yafi komai faranta min rai Indai har na isa da ke xan fad'a miki magana ki ji toh ki saki ranki kuma ki yarda da auren nan idan kika min haka kin saka min da abin da nayi miki nauwara, Idan naga akasin haka na tabbatar baki d'auke ni a uwa ba"

Umma tana gama fad'in hka ta fice daga bedroom d'in, tasan Idan ba hka ta yiwa nauwara ba sai tayi yanda tayi ta ruguxa wannan auren, ita hka Allah ya d'ora mata son ammi dasu nauwara.

Turk'ashi nauwara kuka tasha wiwi wiwi har da su majina umma gaba d'aya ta d'aure ta da maganganun ta, wayar ta d'auka ta kirawo ammi ta fashe mata da kuka shiru ammi tayi bata ce mata komai ba sai da tayi mai isar ta sannan cikin shashshak'ar kuka tace

"ammi don Allah abin da nake ji da gaske ne? "
Tabbas ammi tasan nauwara taji labarin xata auri Abba, don haka cikin sanyin jiki da murya ammi tace
"tabbas abin da kika ji gaskiya ne nauwara, ni ma kaina ba'a son rai na ba sai da baffah da inna suka nuna min 6acin ran su sannan na amince gashi abduljabbar sai sunturi yake yi min akan lallai na amince har da Alhj ibraheem (wato Abba) yasha xuwa shima hkan da na ganine yasa na amince ke ma ina son ki dai na damun kanki, kawai Ki cigaba da addu'a Allah ya xa6a abin da yafi alkhairi, sannan kuma kada naji labarin ko da wasa kin bijire wa umma kin ji na fad'a miki ki rik'e ta tamkar ita ta haife ki bamu da abin da xamu sakawa wad'annan bayin Allahn sai dai addu'a hak'ik'a mahaifin ki yayi hangen nesa da yace duk duniyar nan bashi da amini kamar Alhj ibraheem d'anbatta wanda xai rik'e mishi mu amana sai shi sai gashi kuma maganar tashi ta tabbata"

Cikin kuka nauwara tace "amma ammi......"
Da sauri ammi ta katse nauwara ta hanyar cewa "shiiiii bana son jin komai daga gare ki, kiyi abin da nace Idan har na isa dake, Allah ya jik'an abban ku da safah! "

"Ameeen ya rabbi ammi, kuma Insha Allah xan yi yanda kika ce"
Ammi tana goge hawayen fuskar ta tace "Allah yayi muku albarka "
"Ameeen ammin mu "
Daga hka suka yi sallama ta ajiye wayar tare da buga uban tagumi, ta dau wajen 10 mint a Hka Kafin ta tashi ta shiga toilet wanka ta sake ta fito sannan ta shirya cikin wata gown English wears amman ba takai Har k'asa ba mai k'aramin hannu kalar dark purple tayi matuk'ar amsar ta rigar bayan ta gyara gashin ta d'aure shi da ribbom black ta fesa perfumes ajikin ta ko make up Bata yi ba daga powder sae wet lips a bakin ta idanun ta duk sun kumbura alamar tayi kuka sosai wani black shoes plate ta dauko ta sanya sannan ta fito daga d'akin.

Bedroom d'in umma ta shiga cikin siririyar murya tayi sallama ,umma ta amsa mata sallamar, tsugunna wa tayi har k'asa tare da rik'e hannayen umma tari rau rau xata fashe da kuka da sauri umma tace
"shiiiii bana son kukan nan kada ki 6ata kwalliyar tun Kafin d'an nawa ya dawo ya biya kud'in kwalliyar "
Ta fad'i tana er dariyar su ta manya, sosai umma ta bawa nauwara kunya ta nok'e kai tana murmishi marairaice fuska tayi sosai sannan tace
"I'm so sorry umma baxan kuma ba "
"ni baki min komai ba 'yata komai ya wuce Allah ya yi muku albarka "
Cikin tsananin farinciki nauwara ta ce "Ameeen umman mu, nagode Allah ya saka miki da alkhairi "
"Ameeen dota "

Daga hka nauwara taja baki tayi shiru don duk ta kasa sake wa da umma kamar da,  ita kanta umman ta fahimce ta don hka ta dunga janta da er hira, mik'e wa tsaye nauwara tayi tace
"umma bari naje kitchen ko xan samu fresh milk "
Murmishi umman tayi kafin ta ce "ae d'axun nan saleem yaje ya siyo har da sauran drinks kuma nasan yanxu sunyi sanyi "
"Kaiii amman umma naji dad'i, na taho miki da Ita? "
"a'a Alhmdullilah, asha lafia "
"toh Shikenan umma "
Ta fice daga d'akin umma ta bita da kallo cike da kaunar ta.


Tana shiga kitchen ta bud'e frige ta d'auko fresh milk mai sanyi sosai jikin ta har ra6a yake tsabar tayi sanyi glass cup ta d'auko wanke shi tayi sannan ta cika shi da fresh milk di'n ta fara sha da yake ta juya wa kofar kitchen d'in baya sai ji tayi an rungumo ta ta baya da sauri ta jiyo a tsorace sai suka had'a ido da abduljabbar er K'aramar ajiyar xuciya ta saki dariya yayi yana cewa
"matsoraciya kin xata wani ne koh? "
Ya fad'i yana kallon fuskar ta Kafin kuma idanun shi sukai kan rigar da ke jikin ta, ita kuwa duk kunya ta rufe ta ganin irin kallon kurrilar da yake yi mata
"habibty Kinyi kuka koh, me ya same ki? "
D'an hararar shi tayi tare da turo bakin ta hkan da tayi ba k'aramin hargitsa shi tayi ba k'ara matso da ita jikin shi yayi fuskar su tana daf da ta juna har suna jin numfashin junan su a hankali cikin wani salo ya isar da bakin shi cikin nata sun d'auki long time a Hka suna kisses d'in junan su gaba d'aya jikin shi rawa yake kafafun su sun k'asa rik'e su tuni nauwara tayi baya xata fad'i da sauri ta rik'o rigar abduljabbar toh da yake shima jikin nashi ba k'wari sai ya biyo ta suka xube akan tiles di'n kitchen d'in washhh nauwara ta fad'i da sauri ya rik'o hannun yana cewa
"me... me ya faru ?"
Cikin shagwa6a tace "hannu na "
Yana hura wa hannun iskar bakin shi yana cewa "sorry habibty tashi Ki rakani part d'ina "
"tabbb ni gaskia baxan je ba"
Marairaicewa yayi yana cewa "please baby nah, fad'a min me kike so "
Shiru tayi tana d'an tunani Kafin tace "sai kayi min alkawarin gobe xan je gidan fa'iza da aunty jeedah "
Da sauri yace "i promise u xan bar ki kije "
Tana kallon shi cikin ido tace "are u sure ?"
"yes!  Baby nah "
Mik'e wa tsaye yayi ta Mik'o mishi hannun ta ya kama ya rik'e su sannan ya d'ago ta da d'an k'arfi har tana cewa "washh Yayah kayi min a hankali "
Yana lakuce mata hanci yace "ae ke ce duk kika ruda ni da yawa Kinsa sai rawar jiki nake a gaban umma "
Tana er dariya tace "laaa ni Allah ba ruwa na"
Kafin ta ankara ya d'auke ta cak da kafa ya bud'e kofar kitchen ta baya suka shige part d'in shi a kyakkyawan bed d'in shi ya sauke ta sannan ya yi mata rumfa da jikin shi rufe ta yayi da hot kisses yana aika mata da wasu xafafan sak'onnin shi xuwa gare ta masu tsaya wa a xuciya.


Yana kwance kanta yana saman kirjin shi yana shafa gashin kanta yace "habibty wai sai yaushe wannan abin xai tafi hak'uri na ya fara gajiya wa fah "
Batasan lokacin da dariya ta kubce mata ba hararar wasa ya aika mata Kafin yace "okay dariya na baki ma, Naga alama yanxu bakya tausaya min "
Ya K'arasa fad'i cikin kalar tausayi danne dariyar ta yi sannan tace "Haba my sweetheart Idan banji tausayin miji na ba wa xan tausaya wa "
"Idan Hkane ki tsayar dashi mana"
d'an xaro ido tayi tana cewa "taya xan tsayar da shi ae sai idan lokacin tsayawar yayi ya tsaya "

"okay naji yaushe xai tsaya? "
"kawo kunnen ka na fad'a maka "
Da sauri ya mik'a kunnen nashi kuwa ae kuwa ta d'an cije shi da sauri ya janye kunnen nashi yayo kanta yana cewa "ni kika cija ko sai na rama baxan yarda ba idan baki tsaya ba na kirawo twins mu danne ki kowa ya ciji Inda yake so "
Yarfe hannun ta ta fara cikin shagwa6a tana cewa "wayyo Allah kayi hak'uri na baxan k'ara ba"
"nooo sai fah na rama yarinya "
Kamo ta yayi xuwa jikin shi ya fara yi mata cakulculi nan ta fara dariya tana xille wa tare da cewa "ka daina yayah please "
Ganin tana kok'arin shide mishi yasa shi ya barta tare da d'aukar ta suka shige bathroom.

Bayan sun gama wankan sun fito ya shirya cikin wani 3quater white colour tare da purple d'in t-shirt mara hannu mara nauyi gata er Shara Shara don ana iya hango kwantaccen gashin kirjin shi nauwara ce ta gyara mishi gashin kanshi tare da fesa mishi perfumes sannan ya rik'o ta xuwa part d'in umma ta Inda suka fita tanan suka shigo duk kunya ta ishi nauwara tana addu'ar Allah yasa umma bata parlour ae kuwa da ita ta fara had'a ido tana xaune dasu na'eem da ameer suna xuba mata surutu.

Kallon su tayi tana murmishi kawai ganin yanda nauwara take nok'e kai shi kuwa gogan ko ajikin shi, xama suka yi suka sata a tsakiya umma tace
"Haba abduljabbar yanxu ka girma fah ya kamata ka rage irin wannan shigar Idan xaka fita, nasan da wannan shigar sai kace fita xaka yi "
Shafa kanshi yayi yana kallon nauwara wadda ta aika mishi da harara yana murmishi yace
"toh umma na daina, amman yanxu ba Inda xan sake fita na gaji ni yunwa ma nake ji "
Ya K'arasa fad'i yana Yatsina fuska "me xaka ci? "
Cewar umma " yanxu lokacin mangarib yayi Kafin na dawo ayi min had'in salad ya ishe ni sai a dumama min pepper chicken di'n d'axu yayi min dad'i "
"ah ba yunwar kake ji ba "
"Kaiii umma da gaske nake " Ya fad'i yana ta6o nauwara da kafar shi, "toh Shikenan "
Ko 5 mint basu yi ba suka ji kiran sallahr mangariba don hka ya tashi ya tafi ya canja kayan shi xuwa farar jallabiya yayi alwala ya tafi masallaci, yayin da nauwara ta shiga kitchen ta had'a mishi abin da yake son ci bayan ta gama ta nufi bedroom..........



Aishat A muh'd
[25/07, 10:00] Aishat A. Muhd: 🍀🍀☘☘🍀🍀
 *K'ARSHEN WAHALA*
🍀🍀☘☘🍀🍀




*written by*
Aishat A muh'd





*~Pg 98~*




    Misalin karfe 8:20 ya shigo part d'in umma a xaune a parlour ya tarar dasu umma, saleem, aunty sadiya sai na'eem da ameer, umma da aunty sadiya suna hira yayin da saleem yake danna laptop su twins suna mak'ale a jikin shi ganin papa di'n su ya shigo suka mik'e da gudu suka nufi wajen shi tare da rungume shi d'aukan su yayi gaba d'aya yana yi musu wasa tukunna ya xauna ana hirar dashi sai wurwurga ido yake ta inda xai hango habibty di'n shi but bai ga alamun ta ba yasan tana d'aki don hka ya sauke na'eem da ameer daga jikin shi ya ajiye su kusa da saleem sannan yayi upstairs da sauri.

Tura kofar yayi a hankali ya shiga d'akin sai ya hango ta akan abin sallah da dogon hijab har k'asa tana sallah a nutse wata irin ajiyar xuciya ya saki xuciyar shi cike da farin ciki ya samu waje ya xauna akan sofa yana kallon ta.

Bayan ta idar tayi addu'o'in ta sam bata san ya shigo d'akin ba ta cire hijab d'in jikin ta tare da kunce xanin da ta d'aura akan wata night gown dark purple ce iya karta gwiwa hannun rigar d'an siriri ne ajiye su tayi sannan ta nufi dressing mirror hand dryer ta d'auka ta fara busar da gashin kanta da yake jik'e, duk abin da take yana bin ta da kallo sai wani lumshe ido yake yana wani shi'umin murmishi tare da sake gyara kwanciyar shi akan sofa di'n, gaba d'aya ta gama rikita shi, bayan ta gama busar da gashin ta taje tare da d'aure wa da ribbom, wayar ta ta dauka sannan ta nufi kan sofa da niyyar xama sai taji ta xauna kan mutum a tsorace ta mik'e da sauri hannu yasa ya fisgo ta jikin shi suka had'a ido sai ta saki ajiyar xuciya don ba k'aramin tsorata tayi ba shi kuwa dariya ya tuntsire da ita Kafin yace

"kin cika tsoro nauwara" tana kok'arin tashi daga jikin shi tana cewa "ehhh ba dole na tsorata ba ka shigo min d'aki bansani ba "
D'an hancin ta ya kama yaja Kafin ya rad'a mata a kunne
"habibty yaushe kika koyi k'arya neee? "
A firgice tace "ni! Yaushe nayi maka k'arya? "
"daman kin fara sallah shine baki gaya min ba ko d'axu fah sai da na tambaye ki"

D'an hararar shi tayi tare da cewa "ni fah yanxu ne naga babu fah"
 Cikin tsananin farinciki yace "toh Alhmdllh yanxu ki had'o min abinci xuwa part d'ina ina jiran ki don Allah kada ki dad'e please "
"Kaiii Yah abduljabbar ba ga er aikin umma sai ta kai ma ba ko kaci anan ni fah bacci nake ji"
Kwantar da murya yayi yana cewa "Haba baby nah ki taimaka ki kawo min Kina kawo min sai ki tafi amman ban so ki turo wata er aiki "

Yana gama fad'in hka ya fice daga d'akin Bata da yanda xata yi hka ta saka hijab d'in ta ta fito xuwa down stairs kitchen ta shiga ta had'a mishi komai a babban tire sannan ta d'auko ta kofar baya ta fice saboda tana jin kunyar umma tace wurin abduljabbar xata je ta kai mishi abinci.


A hankali ta K'arasa part d'in ta murd'a handle di'n kofar ta shiga da sallama, amman bata ganshi ba sai ta ajiye abincin kan center table d'in ta juya da xummar ta tafi turus taja ta tsaya ganin abduljabbar a bayan ta daga shi sai white boxer ya harde hannuwan shi a kirjin shi yana kallon ta k'asa k'asa wanda har sai da gaban ta ya fadi .

Zama yayi kan kujera yana kallon ta yace "yi sauri ki xuba min yunwa nake ji uhm sannan ki cire wannan hijab d'in ke ko xafi bakya ji a jikin ki kin xuba wannan abin "

Ganin ta had'e fuska yasa shi tashi tsaye ya tako har Inda take tsaye yasa hannu ya cire hijab d'in wani sanyayan k'amshi ne ya bigi hancin shi Har sai da ya lumshe idon shi sannan ya rik'o hannun ta yana cewa
"d'an saki fuskar mana habibty ko na samu naci abincin a nutse "
Tana turo baki tace "baka ce ina ajiye abincin ba na juya na tafi "

,"Ayyah my wife ae baki xuba min ba ko bakya son k'arin lada ne? "

Bata kula shi ba ta d'auke kai tare da janyo plate ta xuba mishi pepper  chicken di'n, sannan ta xuba mishi had'in salad d'in tare da xuba mishi coconut juice acikin glass cup, kusa da ita yaxo ya xauna har kafad'ar shi tana gogan ta nauwara mik'e wa tayi tana cewa
"gashi nan na gama xuba ma sai ka ci "
Kamo ta yayi ya xaunar da ita kan kafafun shi ya d'ebo salad d'in da spoon Yayi bakin ta yana cewa

"oya open your mouth  don nasan baki abinci ba"
Ya K'arasa fad'i yana shafa cikinta ganin duk ya bi ya tak'ura mata yasa ta bud'e bakin ta kar6a a haka yana ci yana bata har suka koshi sun sha ferfeson nan suka d'ora da coconut juice, suna gama wa yaja ta bedroom toilet suka nufa brush sannan suka fito tana kok'arin tsere wa ya damko ta tare da d'ora ta kan bed tare da yin switch off d'in hasken d'akin gaba d'aya.

Hot kisses ya fara aika mata dashi ta ko'ina duk yabi ya rud'e sai jikin shi har rawa yake gaba d'aya ya fice daga hayyacin shi sak'onnin shi masu xafi yake aika mata dashi,yana nuna mata yanda yayi missing di'n ta sosai lokaci d'aya ya janyo blanket ya rufe su dashi.

Asuba ta gari....



Washe gari da safe sai wurin 10:30 suka tashi tunda suka yi sallahr asuba suka koma bacci sae yanxu suka tashi wanka suka shiga suka yi abduljabbar ya shirya cikin wani blue jeans da t-shirt red colour mai gajeran hannu yayi kyau da ka ganshi kasan yana cikin farinciki fiye da ko yaushe don fuskar shi a sake take kallon nauwara yayi wanda ke daure da towel ajikin ta sauran kiris ta fashe da kuka cikin murmishi ya kamo ta xuwa jikin shi yayi hugging di'n ta yace

"Ya akayi ne 'yammata nah? "
Tana turo baki da yanayin shagwa6a tace "to ni.... ni fah kayana suna part d'in umma bani da wanda xan sa ka"

Dariya ya d'anyi ganin yana mata dariya yasa ta d'an fara bugun kirjin shi Kad'an da sauri ya rike hannayen nata ai kuwa ta fashe mishi da kuka sosai ganin hka yasa ya danne dariyar ta shi yana cewa

"calm down my habibty bari naje na d'auko miki kayan kin ji"
Gid'a kai tayi kawai xaunar da ita yayi kan bed sannan ya fice daga d'akin, yana fita ta kwanta duk a gajiye take tuni bacci ya fara fisgar ta a hankali.

Shi kuwa yana shiga part d'in umma a parlour suka hadu da umman ya gaida ita tukunna ya juya xai nufi upstairs umma tace
"abduljabbar ba nauwara tana wurin ka ba ne?"
Yana sosa kai yace "Ehh umma tana nan, uhm kayan ta xan d'auko mata"
Girgixa kai umma tayi hmm yaran xamani basu da kunya tukunna tace
"Okay amman tayi sauri taxo tayi breakfast d'in tun da tace min xata je gidan fa'iza da jiddah kada rana tayi "
"Okay umma yanxu xata xo"
Yana gama fad'in hka ya haye stairs umma kuwa tayi kitchen, bayan ya d'auko mata kayan ya tafi kai mata tsaya wa yayi cike da mamaki yana kallon ta ganin yanda ta koma bacci, xama yayi kusa da ita ya xuba mata ido yana kallon ta wani son ta da k'aunar tane yake shiga cikin xuciyar ya gode wa Allah da ya bashi mace da tai dai dai dashi a komai da hka yasa hannun shi yana yi mata tafiyar tsutsuwa a kafar ta har ta bud'e idon ta yace "kin manta da fitar taki "
Tuna wa da tayi da hka yasa ta tashi da sauri ta shiga toilet sannan ta fito ta shirya cikin wani cotton lace maroon colour riga da siket ne sunyi mata kyau sosae da yake babu kayan make up yasa ta d'aura d'ankwalin ta sannan suka fito a kunyace ta gaida da umma Sannan a gurguje suka yi breakfast taje ta yiwa fuskar ta light make up ta sanya mayafi da takalmi sannan ta fito tayi sallama da umma suka fita da abduljabbar don shi xai kai ta.

A farfajiyar gidan suka had'u da na'eem da ameer nan suka mak'ale sai sun bisu haka suka xuba su a bayan sit d'in motar suka tafi, a gidan jiddah ya fara ajiye ta ya bata 30 mints ta fito su tafi haka ta shiga gidan da sallama jiddah da gudu taje ta rungume ta sannan ta gaisa da hindatu suka shige part d'in jiddah sun sha er hira ta wajen 30 mint di'n tukunna tayi mata sallama suka fito ta rakota har wajen da abduljabbar yayi parking suka gaisa ya bata kyautar kud'i da yawa sannan suka yi sallama da juna suka tafi.

Suna er hirar su da yaran su har suka k'araso gidan fa'iza to anan ya ajiye so sai 5 na yamma xai xo ya d'auke su, suna shiga fa'iza tana jin sallamar nauwara ta fara tsallen murna bare da taga har da twins aka xo mata........





Aishat A muh'd
[25/07, 10:00] Aishat A. Muhd: 🍀🍀☘☘🍀🍀
  *K'ARSHEN WAHALA*
🍀🍀☘☘🍀🍀




*written by*
Aishat A muh'd




_dedicated to my Ummiey xeey Allah ya k'ara basirah da fasaha da k'arfin ido ina miki fatan alkhairi_💞😍




*~Pg 99~*




 Sun sha hira da fa'iza sosai yinin ranar tare suka yi girkin rana suna ta hira don sunyi kewar juna sosai, sai 5 abduljabbar yaxo d'aukan su da bai yi niyyar shiga gidan ba sai ga Dr muh'd ya dawo daga wurin aiki shi ya tilas ta mishi ya shiga.

Fa'iza baki fah yak'i rufuwa ganin babban yaya a gidan ta nan ta gaida shi sannan ta had'o mishi drinks da bottle d'in faro ta kawo mishi babu abin da sha sai da suka tisa shi a gaba daga fa'iza har Dr muh'd di'n da naci sannan yasha drink d'in yana gama sha ya yi musu sallama ya fito daga gidan xuwa cikin motar shi ya xauna yana jiran nauwara.

Kamar kada su rabu da juna haka suka ji sai lokacin suka gaisa da Dr muh'd don lokacin da ya shigo tana bedroom d'in fa'iza, kamar yanda ya bawa jiddah kyautar kud'i haka ya bawa fa'iza tayi ta godia sannan suka rabu cike da kewar junan su.


Sun dawo gida nauwara agajiye sosai take don hka tana sallahr isha'e ta watsa ruwa a jikin ta tabi lafiyar gado sai bacci, abduljabbar kuwa kasa bacci yayi sai faman juyi yake daga K'arshe ya tarkato yayo d'akin nauwara ya rungume abar shi a jikin shi sai lokacin bacci ya mai dad'i ya d'auke shi.


Hka su nauwara suka cigaba da xuba soyayyar su cikin kwanciyar hankali, har xuwa ranar monday da safe abduljabbar ya koma abuja suka rabu cike da kewar junan su.
Duk wasu shirye shirye an gama na d'aurin auren Abba da ammi an gyara mata part d'aya wanda xata xauna aciki girman shi da komai nashi kamar nasu umma, abduljabbar ne ya xuba kayan furnitures da sauran kayan kyala kyale na gida shi ya d'auke wannan nauyin, sam nauwarah ta kasa sakin jiki da umma kamar da don wlh ita fah har yanxu wannan auren bai kwanta mata a rai ba kawai don an fi k'arfin ta ne, har abduljabbar ta fad'a mishi yace kawai ta bisu da addu'ar xaman lafia don shi ma yana son auren abba da ammi dole ta hak'ura kuwa.


Ranar juma'a bayan an idar da sallahr juma'a Kafin mutane su tafi acikin masallacin dubban mutane suka shaida daurin auren abba da ammi daga nan aka watse ana musu addu'ar xaman lafia.
 Daman nauwara bata xo kaduna ba don umma tace taje kadunan amman nauwara tace ita Mai xata je tayi Hka umma ta kyale ta, tana kula da ita bayan an d'aura auren abduljabbar yana kiran umma yana fad'a mata to da yake nauwara tana xaune kusa da umman tsam ta tashi ta shige d'aki taci kukanta ta more sannan ta fito kallo d'aya umma tayi mata ta tabbatar kuka tayi girgixa kai kawai umma tayi bata ce mata komai ba kamar yanda ita ma nauwara bata k'ara magana ba.

Bayan su abduljabbar sun dawo daga d'aurin auren a d'akin ta ya same ta a kwance shima kwanciyar yayi a jikin ta tare da cewa
"me yake damun baby nah? "
Murmishin yak'e tayi tana cewa "ba komai dear just ina huta wa ne "
"da kyau habibty nah ya kamata ki fara shiri ranar sunday xamu wuce abuja har da twins xamu tafi"
"da gaske kake? "
Ta fad'i tana d'an waro ido bushe mata idon yayi ta lumshe su kuwa tana murmishi yana murxa mata hannu yace "da gaske nake wlh baby na gaji da xirga xirgan  nan "
"baxa mu barwa umma twins ba? "
"tabbb Allah baxan iya ba da yara na xan tafi "
"kai dear "
"yes!  Baby nah baki san yanda nake son yara ba, har na matsu kin dad'a samun ciki kin haifa min wasu twins d'in dukka mata, na'eem da ameer sun girma fah ya kamata su samu kanne ina nan ina addu'a jiki na yana bani kin kusa samu ko ma har kin harbu Insha Allah "

Kwa6e fuska tayi tare da yin kalar tausayi da fuskar tace "kai dear twins fah kace tabbb ba kasan xafin haihuwa bane da wahala fa wayyo Allah nah"
Dariya ta bashi ganin yanda tayi yana dariyar yace "ba wani wahala fah abin da tare ma xamu haihun ina miki nakudar Kina haihuwar ae kada ki damu "

"Hmmm " abin da nauwara tayi kenan ,kallon ta yayi yana cewa
"komai na gidan ki an xuba bari ma Ki gani ko yayi miki"
Wayar shi ya d'auko ya fara nuna mata irin yanda aka canja gidan kamar bashi ba yayi matuk'ar yin kyau gashi kaloli masu kyau aka shirya gidan dasu "Wow masha Allah gaskiya dear yayi kyau sosai Allah ya k'ara bud'i ya kare min kai daga sharrin masu sharri nagode "
"Ameeen habibty na ki bar godiyar nan kin fi k'arfin komai a waje na"
Peck ta bashi a kumatu sannan ya ce "baby nah i luv u "
"i luv u too my dear "

cikin marairaice murya ta kwantar da kanta a saman kafad'ar shi tace "my dear anjima xamu fita shan ice cream please "
Bakin ta ya rik'o da hannun shi yace "wannan bakin ya fiye kwadayi da yawa "
"xamu je don Allah "
Yana murmishi yace "don't worry baby nah xamu je, amman yanxu a dan rage min xafi Kafin anjima Kinsan nayi missing di'n ki sosai "
Ya K'arasa fad'i yana kashe mata ido d'aya rungume shi tayi a jikin ta tana Godiya ga Allah da ya mallaka mata wannan gwarxon mijin nata tana fatan mutuwa ce xata raba su.


Ae kuwa da yammacin ranar suka shirya don tafiya nauwara tana sanye da blue gown mai touch d'in white ajikin rigar tayi rolling d'in kanta da white veil shi kuwa abduljabbar black trouser nd T-shirt blue sunyi matuk'ar yin kyau ko twins basu tafi dasu ba don suna islamia, ko umma ta yaba da wannan k'walliyar tasu, sun birge mutane da dama sai kallon su ake kishi ya ishi nauwara ganin yanda emmata suke kallon abduljabbar ba don ta gaji ba tasa shi da mitar su dawo gida kallon ta yayi yana murmishi yace "Haba baby nah baxa ki bar ni na lalubo d'aya ba sai ki samu k'anwa koh yah "
Ya fad'i yana d'aga mata gira harara ta 6alla mishi tare da had'e rai kiris take jira ta fashe mishi da kuka nan kuma ya dawo rarrashin ta don baxai jure fushin habibty di'n shi ba, Sun sha selfie sannan suka yiwa su twins da su umma siyayyan kayan ciye ciye tukunna suka dawo gida xuciyar su cike da farin ciki.

Duk wasu abubuwan da xasu buk'ata umma ta tanadar wa nauwara sun had'a kayan su sai jiran ranar tafiya dakyar ya barta taje gidan jiddah, fa'iza da aunty kausar tayi musu sallama ranar sunday misalin karfe 2:30 jirgin su nauwara ya d'aga xuwa abuja sun bar umma da abba, aunty sadiya saleem da kewar su.

Alhmdllh sun sauka a abuja lafia Joseph driven Yah abduljabbar ne yaxo ya dauke su a airport xuwa gida, Wow duk irin Kyan da nauwara ta gani a wayar abduljabbar na gidan sai yanxu taga ni axahiri yafi mata kyau,sai da ya xagaya dasu ko'ina na gidan, d'akin su twins ma ya had'u iya had'u wa sannan kuma abduljabbar da nauwara suka tafi bedrooms di'n su don yin wanka yayin da er aikin da umma ta had'a mata da ita ta kwashe su twins don tayi musu wanka su ma.

Bayan sun kammala suka dawo falo duk sun sha english wears marasa nauyi na shan iska akan dinning table suka xauna suka ci take away di'n da joseph yaje yayi musu bayan sun ci sun sha suka dawo parlour suka xube suna hutawa da er hira.

Acikin satin abduljabbar ya sama wa su na'eem da ameer wata tsadaddiyar makaranta mai kyau sosai ba 6ata lokaci suka fara xuwa skul d'in har da islamia Mai kyau ya samar musu da sabuwar motar da xa'a dunga kai su makarantar da driven su a gida kuwa nauwara ta cigaba da d'ora musu lesson rayuwa suke mai dad'i.


A Kano kuwa bayan Sati d'aya da d'aura auren abba da ammi, ammi ta tare a gidan abba xama suke mai dad'i da fahimtar juna sun had'e kawunan su suna kyautata wa abba Idan ka shigo gidan baxa ka ta6a gane kishiyoyi ba ne sai an fad'a maka ko ka fahimta  ba k'aramin birge mutane suke ba don Kafin a samu mata masu irin had'in kan nan xa'a dad'e a wannan xamanin da muke ciki dai don son kai yayi yawa a xuciyar al'umma.





Aishat A muh'd
[25/07, 10:00] Aishat A. Muhd: 🍀🍀☘☘🍀🍀
 *K'ARSHEN WAHALA*
🍀🍀☘☘🍀🍀




*written by*
Aishat A muh'd





*~Pg 100~*





  Satin su d'aya da dawo wa abuja abduljabbar ya shirya musu tafiya honey moon shi da nauwara twins wajen aunty asma'u suka ajiye su saboda makaranta, hutun 2 month's ya samu don hka suka d'aga xuwa k'asar Greece daman k'asa uku xasu Greece, switzerland, sai su biyo ta Saudi Arabia suyi umarah.


Sun sauka a k'asar Greece k'asa ce mai kyau sosai da mutanen mu na Africa basu saba da xuwan ta sosai ba a wani babban hotel yayi musu masauki suna hawa na uku, room d'in da suke ciki katon parlour ne da one bedroom shima babba sai toilet, nan suka xube kan bed suna huta gajiyar mikakkiyar tafiyar da suka yi.



Bayan sunyi wanka sun ci abinci sannan suka kirawo su umma suna sanar dasu sun sauka lafia, sun kirawo aunty asma'u ta had'a su da twins suna ta xuba musu surutu kowanne yana fad'in tsarabar da xa'a yi mishi, sai da suka yi k'wanaki uku suna hutawa basa xuwa ko'ina suna manne da junan su ana xuba soyayya don abduljabbar yace ta shirya Insha Allah xai sun dawo da tsarabar honey moon ya kuma dage da addu'a sosai.


A k'wanakin su na hud'u da xuwa k'asar Greece ne da wani yammaci bayan anyi ruwa an d'auke suka fito abduljabbar yana sanye da white d'in trouser nd T-shirt red colour ya d'ora jibgegiyar rigar sanyi black saboda yanda garin ya d'auki sanyi sosai, yayin da nauwara ta sanya dogon wando maroon colour nd T-shirt black sai ta d'ora coat irin wanda mata suke sanya wa har xuwa gwiwar ta tayi rolling d'in kanta da maroon veil tayi kyau sosai suna rik'e da hannun junan su suna tafiya.

Sunyi yawo sosai a k'asar Greece di'n nauwara k'asar ta birge ta a sati ukun da xasu yi sun sha yawo duk wani gurin shak'atawa da manya manyan malls na k'asar sun xiyar ci wajen da hka suka yi bankwana da k'asar Greece suka yo switzerland nauwara tana santin k'asar don ta matuk'ar yi mata kyau.


Bayan sun sauka a k'asar switzerland ne da sati biyun nauwara ta fara jin canjin yanayi a tattare da ita yawan bacci da rashin appitate a baki sai kuma tashin xuciya kamar yau ta gama shirin ta xasu fita da abduljabbar tana jiran shi ya fito daga wanka irin ta xauna jiran nan shi sai bacci yayi awon gaba da ita a hka ya fito daga toilet d'in ya tsaya kallon ta cike da mamaki wannan baccin na nauwara yana d'aure mishi kai sosai mybe fitar da kuke shi yake gajiyar da ita Cewar wata xuciyar tashi gaban dressing mirror ya K'arasa ya gyara jikin shi ya K'arasa inda take tana bacci a hankali yake tashin ta bud'e idon tayi yana kallon ta yace

"baby nah ko mun fasa fitar ne,  ni wannan baccin naki na lafia ne anya babu ajiya ta Anan???? "

Yatsine fuska tayi ta bud'e baki xatayi magana wani amai ya taso mata da gudu ta nufi toilet ta dunga k'wara shi sai da ta amayar da duk abin da taci, yana rik'e da ita kamar xai fashe da kuka haka yake ji don ba k'aramin tausayi ta bashi ba ganin yanda take wahala kamar ba soja ba bayan ta gama ya sake mata wanka sannan suka fito xuwa daga toilet d'in ya sa mata kaya tukunna yace
"taso mu tafi hospital ni nagaji da wannan yanayin da kike ciki baxan iya jure ganin Kina ciwo ba"
Cikin shagwa6a tace "ni gaskia a'a xan samu sauk'i bana son ayi min allura "
Kamo ta yayi tare da mik'ar da ita tsaye yace "baxai yiwu ba dole ne muje a duba min ke don nasan me yake damun ki "

Ba don taso ba ta bishi suka je wani hospital sun samu nasarar ganin wani Doctor mai jan kunne yayi mata en tambayoyi sannan aka yi mata urine test Inda suka hango d'an k'aramin ciki a manne a jikin ta lokacin da suka sanar da abduljabbar nan take ya tsugunna tare da yin sujjadar godiya ga Allah yana tashi daga sujjadar don tsanani murna ya rungume doctor d'in Kafin ya jiyo kan na ya d'auke ta cak sai juyi yake da ita a office d'in Dr di'n ya bisu da kallo alamar sun burge shi sosai daman en 9ja sun iya soyayya da kula da matan su kamar yanda ya gani a Wajen abduljabbar, Cewar Dr a xuciyar shi bai san maganar ta fito fili ba har naji ina da gefe na ce lallai doctor nan an gaya maka en 9ja basu da wannan wayewar nan me ka dau ke su ne 😏, muma ae mun iya kawai dai don malam bahaushe akwai shi da son girma baya son rai ni shi yasa ba kowanne yake yi ba..... lol
Jin abin da na fad'a yasa doctor ya sunkuyar da kae yana sosa k'eya alamar yaji  kunya bai san xan ji ba lol.

Bayan ya gama juyin da ita a office d'in doctor ya dire ta sannan a lokacin Dr yayi wa abduljabbar bayanin yanda xasu kula da cikin Sannan ya rubuta mata magungunan da xata sha wanda xai taimaka mata sosai wajen Inganta lafiar ta da ta jaririn cikin.

Da hka suka yi sallama da doctor suka fito xuciyoyin su cike da tarin farinciki more especially abduljabbar da hka suka tari taxi har xuwa masaukin su.

Nauwara ta ga gata sosai a wajen abduljabbar wanda Idan yana wani abin har mamaki yake bata kamar bashi da wasu yaran, shi haka Allah yayi shi akwai son yara sosai, nan da nan nauwara ta dad'a wani irin haske kyanta ya k'ara fito wa sai dai ta d'an rame saboda laulayi yau lafia gobe sai a hankali, satin ukun da suka yi niyyar yi sai da suka k'ara Sati d'aya sannan suka wuce Saudi Arabia nan ma Sati ukun suka yi sannan suka yo gida nigeria,  sun sauka lafia aunty asma'u ce da su twins sai yaranta sune suka xo taryar su cikin tsananin farinciki na'eem da ameer suka rungume iyayen nasu suna murnar ganin su don sunyi matuk'ar kewar su, kallo d'aya aunty asma'u tayi wa nauwara ta fahimci ciki ne da ita don hka cikin murmishin tsokana ta cewa abduljabbar
"kai daga xuwa honey moon sai ku dawo da tsaraba"
Cikin murmishi yace "alamar tafiya tayi kyau sosai "
Yana fad'in hka ya shige mota kunya ta rufe nauwara kamar ta nutse a k'asa aunty asma'u kuwa dariya tayi tana cewa "Allah ya shirya ka abdul "
Da haka suna er hirar su suka K'arasa gidan nasu sai yamma likis aunty asma'u ta koma gidan ta ta bar mata babbar 'yarta hanan Ko xata taimaka mata hakan kuwa ba k'aramin dad'i yayi wa nauwara ba don jinin su ya had'u da hanan yarinyar akwai hankali da kamun kai.

Sai da suka yi wajen wata biyu da dawo wa sannan abduljabbar ya samu d'an short break na tsayin 1week kacal suka tattara suka yo kano don tuntuni nauwara taso xuwa but ya hana ta sam yace tare xasu xo don baxai iya missing di'n ta ba na tsawon wasu k'wanaki, lokacin cikin jikin ta har ya dan fito ana ganin shi.

Sun sauka a Kano lafia umma,abba, aunty sadiya da ammi ba k'aramin jin dad'in ganin su suka yi ba gashi sun hango Sun kusa samu wasu jikokin nan fa suka frasa inda xasu sa su don dad'i, abin da yayi matuk'ar d'aure kan nauwara shine ganin wai ammin ta da ciki gashi nan ya fito ana ganin shi lallai wani baya haifar d'an wani rayuwa kenan Allah yasa mu dace da kyakkyawan rabo.

Washe gari fa'iza ,jiddah aunty kausar taxo gidan gaba d'aya kamar had'in baki sun sha murnar ganin junan su fa'iza ma tana d'auke da cikin ita ma jiddah Allah maji rokan bawan shi gashi nan ita ma da nata cikin kuma yanxu hindatu tayi nadama tun lokacin da aminu Yayi mata saki d'aya da tayi niyyar k'ona jiddah da tafassheshen ruwan xafi Allah bai bata nasara ba aminu ya ganta ya kar6e to shine yayi mata saki d'aya, dakyar ya dawo da ita don darajar yaran dake tsakanin su, yanxu tayi nadama sosae xaman lafia suke da jiddah ae duk tsanani yana tare da sauk'i komai wuya sai dad'i kuma *Innallaha ma'assabirin* littafin miss zahra mansur.

Yini guda suna shan hira nauwara kowanne ta bashi tsarabar shi sun yi mata godia sai yamma tukunna kowacce mijin ta yaxo ya dauke ta.

Satin su d'aya a Kano sun xagaya gidajen en uwa har kaduna nauwara taje k'wanan ta d'aya ta dawo kano, ranar sunday suka shige abuja saboda makarantar su na'eem da ameer, yanxu saleem ya had'a degree di'n shi akan harkar kasuwanci bai nemi aiki ba Abba ya wulla shi company nin su nauwara dake abuja don ya dunga kula shi ya had'a shi da kwararrun ma'aikata masu tsoron Allah da amana a xuciyoyin su nan da nan company nin ya fara samun cigaba yanxu saleem ganin shi sai week end a Kano sauran k'wanaki biyar di'n a kaduna tun an fara  xama babban mutum yanxu aure ya rage mishi don duk wani jin dad'i ya same shi, ammi kullum cikin addu'a take ma yaranta dasu umma da abba da suka rik'e su tsakani da Allah....




Aishat A muh'd
[25/07, 10:00] Aishat A. Muhd: 🍀🍀☘☘🍀🍀
 *K'ARSHEN WAHALA*
🍀🍀☘☘🍀🍀




*written by*
Aishat A muh'd




*K'ARSHE* (last page)





     Cikin nauwara ya shiga wata na shida yayi girma sosae kamar nasu twins abduljabbar ba k'aramin tausaya mata yake ba kullum ya dawo daga aiki baya fita xai xauna kusa da ita yana lalla6a ta tare da bata labarai masu dad'i da ban dariya ita kuma tana nannad'e a jikin shi tana dariya haka na'eem da ameer xasu xo su kewaye su ana yi dasu kulawa sosai yake bata .


Kamar yau tana xaune a falon down stairs tana sanye da simple gown don tafi mata dad'in sawa gaban ta fruit salad ne abduljabbar yana gefen ta yana bata a baki aka kirawo shi a waya da sauri nauwara ta mik'a mishi wayar da yake tana hannun ta ganin sunan abba ne d'aga wa yayi da sallama bayan ya gaida abba ne yake sanar dashi ammi ta haihu an sami baby boy tuni fuskar abduljabbar ta fad'ad'a da fara'a sosai Alhmdullilah ya furta bayan ya ajiye wayar nauwara wadda ta xuba mishi ido tace
"waya haihu ne?"
"ammi ce ta haihu yanxu an samu baby boy "
Cikin wani irin sauri ta mik'e tsaye tana cewa wanda har sai da marar ta ta d'an murd'a kan a hankali ta dafe wajen tare da furta washh amman bata bi ta kanta ba tare da cewa
"da gaske kake don Allah "
Kamo ta yayi ya xaunar da ita kan kafafun shi ya d'an d'aure fuska yace "ban hana Ki tashi da sauri haka ba sai kin jiwa kanki ciwo? "
Langa6e kai tayi tare da fad'in "sorry " d'an murmishi yayi Kafin yace "da gaske nake miki ammi ta haihu na samu small bro ni ma "
Cikin tsananin murna ta rungume shi tare da cewa "Masha Allah Alhmdllh Yeeeeeee xan je kano "
D'an hararar ta yayi yana cewa "da haka xaki Kano da wannan katon cikin ke da xuwa kano sai kin haihu yarinya "
Kwa6e fuska tayi ta fara kukan shagwa6a ita fah sai taje har da shure shuren kafa irin na yara Idan xasu yi kuka tuni hankalin shi ya tashi don baya k'aunar ganin nauwaran shi a haka nan ya dawo lalla6a ta tare da yarda xasu je sai lokacin ta dai na kukan daman ae na k'ak'ale ne ko hawayen kirki babu sai murxar ido girgixa kai yayi yana murmishi kawai ya d'an ja kumatun ta yana cewa
"habibty rigima don kin ga bana jurar ganin ki Kina cikin damuwa shi yasa kike yanda kike so"
D'an hararar shi tayi da sauri ya dafe baki yana cewa "su6utar baki ne sorry "
Gaba d'aya suka kwashe da dariya sai jin maganar twins suka yi suna cewa "papa mamee dariyar me kuke? "
Abduljabbar da nauwara suka Kalli juna tare da yin murmishi nauwara tace " ammi ce ta haihu an samu boy" nan suka fara tsallen murna suna dariya.


Bayan k'wana 2 da haihuwar suka tarkato xuwa kano har da aunty asma'u da yaranta nan fah gida ya cika da 'ya'ya da jikoki don su fa'iza, aunty kausar, jiddah, aunty safiyya dasu inna da baffah da saleem kamar had'in baki duk rana d'aya suka xo gida ya cika umma da aunty sadiya sun kasa xama waje d'aya sai anan ake dasu, barin ma nauwara motsi Kad'an sai ta tambayi nauwara me take so kula wa sosai take bata, babyn ammi yaci sunan abban su nauwara wato sa'eed don yace ameer mai sunan abban su nauwara daban shi ma nashi sa'eed d'in daban.


Ranar suna jaririn yaci sunan sa'eed suna ce mishi arfat, bayan suna da k'wana 2 su nauwara suka koma abuja, haka lokaci ya cigaba da tafiya cikin nauwara yana wata 8 fa'iza ta haihu d'a namiji tana haihuwa da k'wana 3 jiddah ma Allah ya sauke ta lafia ta samu diya mace murna Wajen jiddah ba'a magana har da kukan ta na farinciki ta gode wa Allah da ya bata haihuwa daman ashe haka yara suke da dad'i wayyo Allah daman ana dawo da rayuwa baya da ta goge abubuwan da ta aikata a cikin rayuwar ta amman ina ya riga da ya wuce sai addu'ar Allah ya gafarta mana kura kuran mu Ameeen
Anyi suna d'an fa'iza yaci sunan  daddyn Dr muh'd Wato Abdullah suna kiran shi da daddy sannan er jiddah kuwa Mufeedah suka sanya mata.

K'ememe abduljabbar barin nauwara xuwa suna ita ma bata sa ran xuwan ba saboda yanda cikin ta ya girma sosai ko taje baxa ta sake ba, yanxu nauwara kad'ai ake xuba idon haihuwar ta iyaye da en uwa sai addu'ar sauka lafia suke mata, abduljabbar kuwa tun da cikin haihuwar nauwara ya tsaya tsayuwar dare yake sosai da addu'ar Allah ya sauke ta lafia duk gaba d'aya baya cikin nutsuwar shi saboda tsananin tausayin ta ganin yanda take fama da ciki duk ta kumbura musamman kafafuwan ta.

Tuni saleem sun dinke da Hanan babbar er aunty asma'u suna xuba soyayya kuma kowa yasan da haka a cikin en uwa kuma Anyi farin ciki sosae baran ma nauwara da yake yanxu ta dawo wajen ta da xama tana d'an taya ta ayyukan da er aiki baxa ta yi mata.

Ranar Thursday da safe nauwara ta tashi da nakuda ganin yanda ta ke wahala gaba d'aya Abduljabbar ya gigice ya kid'ime ya ma kasa yin komai sai sannu kawai yake xuba mata, sai da Hanan ta kirawo aunty asma'u nan da nan taxo gidan tana fad'an me yasa bai kaita asibiti, shi sai lokacin ma ya tuna da wani asibiti don duk ya gigice kamar ba soja ba baya jurar ganin habibty di'n shi cikin wahala ne, cikin kankanin lokaci suka isa asibitin aka kaita room d'in haihuwa K'ememe abduljabbar yak'i fita daga d'akin yana rik'e da nauwara yana xuba mata sannu awan su 3 acikin asibitin Kafin nauwara ta haihu tarihi ya mai mai ta kanshi don 'ya'ya biyu reras ta sake haihuwa sai dai duk mata ne kyawawa masu kama da nauwara.

Nan fah murna ta ishe abduljabbar ya rasa inda xai sa kanshi don tsananin farinciki haihuwa 2 amman 'ya'ya hud'u lallai Allah ba k'aramin kyauta yayi mishi ba da ya axurta da nauwara, sai da ya tabbatar nauwara ta dawo dai dai har tayi wanka ta samu baccin hutu tukunna ya kar6o yaran shi daga hannun aunty asma'u har tana mishi tsiya shi dai kawai murmishi yake, nan aka fara kiran en uwa da abokanan arxiki ana sanar dasu nauwara ta haihu ta samu twins duk mata.

Sai dare aka sallame su daga asibitin bayan an tabbatar ba wata matsalar suka dawo gida nan fa na'eem da ameer suka dunga tsallen murna sun samu kanne, washe gari umma da aunty sadiya suka xo ganin yara k'wanan su 2 suka juya xuwa kano, shirye shiryen suna sosai Aunty asma'u take shirya ita dasu fa'iza ana sauran k'wana 2 suna su fa'iza, aunty kausar, jiddah da aunty maryam da aunty safiyya suka taho abuja saboda shirin suna.
Kaya sosai abduljabbar ya had'a wa nauwara da twins na'eem da ameer sannan twins d'in shi mata, nauwara har da kyautar dankareriyar mota da yayi mata tare da wata sark'ar goal mai tsananin tsada ba k'aramin kashe kud'i yayi ba har nauwara tana mishi maganar kashe kud'in Yayi yawa yace mata ta barshi yayi komai yana da lokaci kuma sun fi k'arfin komai a wajen shi rungume shi nauwara tayi tana jin dad'in yanda Allah ya bata miji nagari.

Kaiii twins fa sunyi goshi kaya ta ko'ina nauwara take samu umma, Abba, ammi, aunty sadiya, aunty asma'u, aunty kausar, aunty maryam, aunty safiyya, inna, baffah, saleem, fa'iza, jiddah dukkan su kowanne da nashi abin arxikin nauwara har ta rasa bakin godiya har da aiken Dr muh'd da aminu kaya masu tsada sosai wai a sawa twins.
Abdulkareem ma kyautar ta daban ya aikowa da twins har da sark'ar goal guda biyu masu tsada, ya taya abokin shi murnar samun twins.

Ranar suna twins sun ci sunan umma fatyma d'ayar kuwa taci sunan safah sai suke kiran wanda taci sunan umma marwa kenan safah da marwah sai fatan Allah ya raya su cikin addinin islama,walimah su aunty asma'u suka shirya anci ansha an watse.

Bayan suna da k'wana 2 kowa ya watse aka bar nauwara da abduljabbar sai en yaran su a gida suna cigaba da kula wa dasu cikin tsananin farinciki da k'aunar yaran nasu.

Bayan sunyi arba'in suka yo kano suka yi sati d'aya sannan taje kaduna tayi wa su inna k'wanaki uku acan sannan suka koma abuja, a dai dai lokacin aka yanke bikin saleem da Hanan wata biyu masu xuwa don Abba yace baxai shige wannan axumin ba bai yi mishi aure ba.
 Komai nisan lokaci aka sa xai xo har ya shige dashi nan har bikin saleem yaxo duk wasu shirye shirye an gama sun tarkato kano gaba d'aya don a gabatar da bikin da yake kuma mijin aunty asma'u shi iyayen shi en kano ne don hka komai yaxo da sauk'i an kammala biki lafia amarya Hanan ta tare a gidan ta da yake kaduna, daga hka kowa ya tarwatse ya nufi nashi gidan.




*BAYAN SHEKARU 6*


    Ganin wasu kyawawan yara nayi su hud'u maxa biyu mata biyu suna xaune a parlour kallon mbc 3 suke ana cartoon di'n toy Story duk sun nutsu suna kallon saboda yanxu suka gama fad'an su na yara nauwara tayi niyyar dukan su abduljabbar ya hana ta don hka ta xuciya a fusace ta bar falon to shine abduljabbar ya kunna musu cartoon suna kallo ya tafi rarrashin habibty di'n tashi.
  Dakyar ya shawo kanta suka fito parlour suna ganin ta suka mik'e tsaye tare da durkusa wa agaban ta cikin had'in baki tare da rik'e kunnayen su suka ce
" I'm so sorry mamee baxa mu k'ara ba mun dai na rashin ji "
D'an hararar su tayi nan suka k'ara shagwa6e fuska tare da cewa "please mameen mu "
Tsugunna wa tayi tare da bud'e hannuwan ta da gudu suka k'araso cikin jikin ta tayi hugging di'n su tare da basu peck a kumatun su tana shafa gashin kan su d'ago kanta tayi ta kalli abduljabbar da ya langa6e kai yana wani marairaice fuska yace " sauran ni habibty "
Hararar wasa tayi mishi ae kuwa ba kunyar ganin yaran shi yaje ya rungume ta ta baya shi ma nan fah su safah da marwah suka fara yi mishi dariya yayin da na'eem da ameer suka tsokanar papa di'n su ganin yanda ya nannad'e a jikin nauwara kamar shi ne yaron.
Xaman lafia suke mai dad'in gaske a tsakanin su da yaran su suna basu lokacin sosai rayuwa kullum cigaba suke samu daman duk *K'ARSHEN WAHALA* dad'i yana nan xuwa.
  Bayan sun kammala yin dinner d'in dare wajen 9, safah da marwah suka yi tafi d'akin su don lokacin baccin su yayi, haka na'eem da ameer ma suka nufi nasu d'akin aka bar nauwara da abduljabbar a parlour shi ma bai 6ata lokaci ba ya d'auki habibty di'n cak a hannu suka shige bedroom d'in su suna shiga toilet ya tsomata a bath di'n wanka wanda yake cike da ruwan d'umi bayan sun yi wanka cikin farinciki da so da k'aunar junan su, bayan sun fito sun shirya cikin sleeping dress kan bed suka fad'a suna rungume da junan su a kunne nauwara ta rada mishi "i really luv u yayanah!"
Yana kok'arin kissing d'in ta yace "i luv yhu too my habibty Allah ya bar mu tare "
"Ameeen " tana gama amsa wa ya rufe bakin shi da nata tare da jan  blanket suka fara kok'arin faranta ran junan su, ganin haka yasa na tarkato na bar musu d'akin don na kyale su haka ni ma na huta da typing......

_Asubah ta gari_



*ALLAHAMDULLAH*


_dukkan Godiya sun tabbata ga Allah da ya bani rai da lafiyar rubuta musu wannan labarin na *K'arshen wahala* na fara shi lafia gashi a yau na kammala shi lafia_


*ke ta daban ce wlh a wurina my cwt sadeey saNaz i really luv u bani da bakin godia a gare ki sai dai ina miki fatan alkhairi a rayuwar ki ya albarkaci rayuwar ki ya cika miki burikan ki na alkhairi ya xa6a miki miji nagari wanda xai kular mana ke mu xo jigawa musha biki*_💃🏻😍


*KUNA RAI NA SISTERS NAH*

Hafsat A aliyu
Mmn abiddeen
My Sumayya salees sadeeq (sumynbash)
My khadijah neena cool
Nafeesat Anka
Asy khaleel
Ummiey xeey
Ummi hambali
Mrs muktar
Mrs Umar
Miss maryam
Aishat aliyu garkuwa
Haleemah Ameen
Biebie deee
Ummu safwan
Sa'adah
Khalfana
S A muh'd
_da sauran wad'anda ban ambata ba ku sani kuna rai na i really luv u guys_😍


*masoyan asali*
Miss zahra mansur
Ummu abdul
deejah
Neena cool
Hadixa gidan d'orawa
Amina (mameen ammar da bilal)
_da sauran da ban ambata ba Aishat tana gaida ku_😍

Jinjinar ban girma gare ku
K'arshen wahala fans
Aunty & sadeey novels grp
dandalin hausa novels
Online hausa writers
Hikima writers  HWA
Ummu safwan novels
Mrs Umar novels
Hausa novels group
My style grp
Ladies zone
Musan kanmu marubuta
Ruky & ashba
saNaz novella
Novellas lodge
Biebie & samrah
Nagode da k'aunar littafin nan da kuka yi ina yi muku fatan alkhairi en uwa 😍


_ku tare ni a littafi na na gaba *YAYI SAKE* amman sai bayan sallah saboda gabatowar wata mai albarka wato ramadan mu dage da ibada Allah ya nuna mana lokacin lafia Ameeen_



Aishat A muh'd ce

adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *