Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Friday, April 17, 2020

HAFSATUL-KIRAM COMPLETE

adsense here
HAFSATUL KIRAM

           NA
  Rabiatu sk msh
 
                 1

Taafi minti 15 da kofin glass a hannunta ta cikoshi da hollandia milk mai sanyi, tana tsugune da zumbuleliyar hijabinta tana jiran ya amsa anma kamar baisan da mutum a wurin ba yaci gaba da aikin da yakeyi a computer



Cikin qarfin hali ta qara miqa mishi tare da cewa "gashi...., kamar wanda ke jira kafinta qarasa ya daka mata wata uwar tsawa da saida ta firgita damn a tsoracen take Yace "sau nawa zan fada miki bnson ganin wannan mummunar fuskar taki? Ki bacemun da gani.

Da sauri ta miqe jikinta na kyarma cikin rashin sa'a kofin dake hannunta ya fadi ya tarwatse dk ya 6ata mishi jiki da wasu talardun gaban nashi

Cikin zafin rai ya miqe yana huci ya bata wani kyakkyawan mari, nan da nan idonta ya kawo qwalla tana kallonshi a tsorace cikin bacin rai yake magana yace "bzan gaji da fada miki na tsaneki ba, ko kadan bnson kallon fuskarki, ko qarar tafiyarki na tsana a gdannan, wannan wane irin qaddararren aurene? Anya kuwa ba mayya aka haifa mana a family ba??

Da sauri ta zaro ido tana kallonshi yaja tsoki ya zauna, danne zuciarta tayi tace "kayi haquri don Allah" ya mata banza ta dauki takardun da sauri ta fara gogewa a zuciye ya qara miqewa ya daga hannu da niyyar marinta ta duqar dkai a razane saboda bata mnta da xafin na dazu b, tana jiran jin saukar wani.

Dai dai lokacin na shga gdan da sauri ya maida hannunshi yana kame kame, yasa hannu ya dago fuskarta da duqe taa rumtse ido, yana murmushi yace "meye na kuka kuma? Ki share hawayenki bari inje in canza kaya!

Kallonshi take cike da firgici da mamaki kafinta hangoni tsaye, da sauri itama ta fara qoqarin murmushi yaqe tace "tohm shknan, bari na kwashe, ya wuce dakinshi.

Ta qaraso wurina tana murmushi tace "kinga pa Aunty rabiatu abu na zubar mishi a jiki na dauka zaimin fada shyasa harna fara kuka.

Nayi murmushin qarfin hali nace "kinanan yanda kke hafsatul kiram tun kina qarama abu kadan ke sakaki kuka!

Umar ne dake tahowa bayan yaa canja kaya yace "Aunty ce a gdanmu? Sannu da zuwa Aunty gsky munji dadin zuwanki, ba tare dana kalleshi ba muka gaisa! Sannan ya fita hardasu dagoma hafsatul kiram hannu! A raina nace "maza kenan!!!

Rabiatu sk msh

HAFSATUL KIRAM       
           NA
  Rabiatu sk msh

              2
Kallonta nayi ina shrin tambyarta, ta miqe tsaye tana murmushi tace "Auntyna shne bki taho da takwarah ba? Gsky naaji dadin zuwanki, kamar kinsan ina da labaran dazan baki da yawa! Anma ki fara fadamin me zakici? Yau grki na musanman zan miki Aunty!

Sai magana nake anma taaqi ta tsaya da surutu dk qoqarinta na son boye damuwarta! Juyota nayi muna fuskantar juna nace "Ya isa hka!! Miye gskyr abnda idonah ya ganemin hafsa? Damn zamn da kukeyi da umar kenan dk soyayyar dake tsakaninku?

Girgiza kai tayi hawaye naa zuba a idonta tace "babu soyayyah tsakaninah da yaa umar Aunty, bai taba sonah b dk tsawon lokacinnan zama muke kawai!

Kimin alqawarin bzaki fada a gda ba, zan fada miki komi, dk taa rirriqe hannuwanah! Nace "bzan fadama kowah ba hafsatul kiram!! Share hawaye tayi sannan ta fara...

Kafin Aurenah da Yaa umar..*** ***

Kamar yanda kka sani Aunty, ni kadaice a wurin mahaifana Alh. Ahmad shahararren mai kudi, da haj fatima, wannan dalilin yasa suke matuqar ji dani, da duk wani danginmu!

Mahaifina su biyune a gdansu shida momie khadija yayarshi, mahaifiyatah ma su biyune ita da ke Aunty rabiatu, rayuwatah na taso cikin farin ciki da gatah, kuma dk da son da iyayenah kemin bai hanasu bni tarbiya ba, Alhmdlh naa samu ilmin addini sosai dai dai gwargwado.

Lokacin dana qare secondry momie khadija ita da kanta tazo har gida tafiya dani lokacin kuna moscow, ranar na shrya muka wuce kaduna cike da farin ciki duk da bnson rabuwa da momma anma inajin zama gdan momie khadija, itama yaronta daya yaa umar!

Shi kadai ne matsalatah ko kadan jininmu baizo daya b, shyasa ma bani shga harkarshi kullum ina cikin daki ina qara nazari akan littafaina na islamiya!

Lokacin da mukaje naa iske xahra taazo diyar Aminin daddynshi, kinsan zahra! Kinsan rashin tarbiyarta da kamunkai, da kuma wayewarta dk dasu taje gdan!

Randa naje gdan tana sanye da riga da wando sunyi matuqar matseta daqyar rugar ta rufe mata cibi, gashinnan yaasha gyara anma batayi qari ba, nina fara mata magana anma bata amsa ba sai wani irin kallo da takemun tana yatsina

Nidai ban kulata ba don nasan babu abnda zata nunamin, gata, ilimi, kyau, da kudi dk babu wanda bn fita ba! Wayewah indai irin tatace bni fatan in yitah!!

Love my princess Amrah

Rabiatu sk msh

[13:29, 4/6/2016] Rerbee'art sk: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄
                          🎄
                       🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
              🎄🎄🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                       🎄🎄
                          🎄
           NA
  Rabiatu sk msh

              3⃣

Da dare ina daki ina karatun Qur'ani mai aikinsu tazo kirana, damn da hijabi na ina kai aya na rufe na ajiye sannan na fito!

Momie tace "kedai zamn daki yai miki hafsa ko kadaici bakiji! Murmushi nayi cike da kunya naja kujera na zauna babu wanda ya min magana daga zahra har umar! Sai nice ta gaisheshi, yayi kamn baiji ba

Momie ta kalli  yaumar tace "son ga hafsatul kiram pa, tana gaisheka kaayi shru! Yace "lpy, tananan dai da qauyancinta!

Sai lokacin na dago na kalleshi, yaa umar kyakkyawan gaskene da bazan iya misalta haduwarshi ba, kaasa dauke idonah nayi dga kallonshi har saida ya dago kai muka hada ido gabana ya fadi nayi sauri na duqar dakai cike dajin kunya!

Wani uban tsaki yaja da har saida momie ta dago ta kalleshi tace " lafiyanka? Kamar baison magana Yace "ruwannan yayi sanyi da yawa, momie tace "ohk bari in magana a kawo mka wani! Zahra tace "nawa ma babu sanyi momie bari na zuba mishi, ta fara tsiyayawa a cup! Lokacin momie ta gama ta miqe tana cewa "shknan ma!

Momie na tafiya zahra ta miqe ta koma kujerar kusa da yaa umar ta miqa mishi cup dn ruwan tace "gashi yaa umar! Ya girgiza kai, tace "kasha babu sanyi! Yace "na qoshi!

Tashi tayi taje ta dafa kujerar da yake tana kai kofin bakinshi tace "nipa sai kasha ruwannan! Tana qara manne mishi jikinta na gogar nashi!

Abn daria abn takaici, kaasa daurewa nayi Abncin dana saka baki ma daqyar na hadiyeshi na miqe nabar musu wurin!

Daga ranar na daina dadewa a dinning, momie na gamawa zan bita mubar wurin, ko kadan bn shga harkar yaa umar da zahra, saboda yanda sukayi nisa kullum suna maqale da juna tana qara chusa mishi kanta

Nikam dai bnsan mena musu ba dk suka tsaneni bama kamar zahra tunda damn yaa umar bmu shri!  Momie kam naa matuqar qoqarin ganin mun shaqu da yaa umar! Ko fira suke tana yawan sakani, kafin inyi magana zahra zata amshe suci gaba

♥♥Rabiatu sk msh❤❤
[13:54, 4/6/2016] Rerbee'art sk: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄
                          🎄
                       🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
              🎄🎄🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                       🎄🎄
                          🎄
           NA
  Rabiatu sk msh

            4⃣

Akwai ranar da ina dakin momie ina sanya mata kayan guga a wardrobe tace min "umar ya dawo kuwa? Nace "wlhy bn sani b momie, anma inya dawo ay zai shgo ne! Tace "dubomin ki gani in yana dakinshi!!

Sanda nake dakin bayanan anma duk yayi datti yanda kkasan dakin maza yake dai, an baza kaya ko ina ga takardun office dk ya baza da wasu ledojin choculates dana cwts harda kwalin lemuka, mamaki ne ya kamani ynzu dl tsaftar yaa umar yake zama da daki a haka? Ko en aiki ay saiya saka su gyara mishi!

Wata zuciyar tace ki gyara mishi mana! Hkan kuwa akayi ina cikin gyara momie ta shgo! Tana murmushin jin dadi ta kalleni tace "sannu kinji hafsa! kinga kullum fadan dattin dakinnan nake mishi anma yaqi yrda a gyara mishi, yau gashi qanwarshi na rabashi da dattin nan!

Murmushi nayi cikin jin kunya tace "Allah ya miki Albarka hafsatul kiram! Kaina a qasa na amsa da Ameen!

Momie bata dade da tafiyah ba na kammala komi dakin ya fito yayi fess yayi kyau, na maida hijabi na ina niyyar barin dakin suka shgo shida zahra tana maqale dashi kamar ta koma jikinshi.

Da sauri na nufi hanya ina shrin ra6awa in wuce ya fizgoni na dawo baya, a tsorace nake jikina na kyarma hawaye ne suka fara zubomin, fuska a daure cikin bacin rai da kakkausar murya yace "waya sanyaki kaudamin kaya? Nace miki ina da buqatar gyaran dakine? Dk abnda kkaga na ajiye nasan inda yake kin tashi kin hademun!

Kaasa magana nayi tashin hankali qarara a fuskatah, daqyar na iya cewa "kayi haquri don Allah" wurgar dani yayi cikin huci yace "6acemun da gani.

Da sauri na nufi hanyar fita zahra namin dariar mugunta, hawaye ne suka zubomin cikin qunar zuciah daga abn arziqi zai gwasaleni, koda yake ni taimako ne na mishi bada wani manufa ba.

Tun a lokacin zamn gdan ya fita raina anma ganin yanda momie keson zamana gdan yasa kawai nake daurewa!

Lurv my princess Amrah😘

♥♥Rabiatu sk mashi♥♥

[19:14, 4/7/2016] Rerbee'art sk: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄
                          🎄
                       🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
              🎄🎄🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                       🎄🎄
                          🎄
           NA
  Rabiatu sk msh

              5⃣

Rannan momie ta aikeni kiranshi cikin faduwar gaba na shiga dakin, bai falo na wuce bedroom cikin faduwar gaba, Abnda na gani ne ya qaramun faduwar gaba na zaro ido ko motsi na kasayi

Yaa umar ne rungume da zahra bakinshi cikin nata, babu kayan kirki a jikinsu yana shafata ta ko ina, idanunsu a rufe.

Naayi matuqar razana tsayuwamah ta gagareni da saurina na juya tare da sakin qofar da sauri qafafuwanah suka harde da hijabina na fadi a wurin, duk hankalinsu ya dawo kofa suka fito da sauri.

Suna ganin nice ya jawo zahra ya qara mannata jikinshi yanamin mugun kallo yace "meya kawoki dakina kinamun leqe??

Kasa magana nayi hawaye na zuba a idona har lokacin na kasa tashi dga faduwar da nayi, ya takamun qafa na fasa qara ya duqu saitin fuskatah da sauri na matsa yana shrin shaqoni na gudu na tafi dakina.

Fadawa nayi saman gado ina sharar hawaye, nasha kuka sosae ni kadai cikin daki da naga bzaimun ba na dauko Qur'ani naci gaba da karatu! Sai sannan na samu nutsuwar zuciah, ina mamakin wannan tsana da yaa umar yamun

Bayan magrib momie ta shgo dakin ina saman sallaya! Na qirqiro murmushi tace "sannu da zamn daki hafsatu! Murmushi kawai nayi taci gaba "daddynki yaa daki koma wai naa riqeki da yawa, yaushe kkeso ki koma??

♥♥Rabiatu sk msh♥♥

[10:05, 4/8/2016] Rerbee'art sk: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄
                          🎄
                       🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
              🎄🎄🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                       🎄🎄
                          🎄
           NA
  Rabiatu sk msh

            6⃣

Duqar da kaina nayi nace "nan da can duk dayane momie dk sanda kikace, ina qoqarin maida hawayen da suka zubomin!

Mun dade muna fira da momie don indai tana gda bataso ta ganni nayi shru, saida aka kira isha'i har taa miqe zata tafi ta juyo ta kalleni tace "dazu dana aikeki kiran Umar me yace??

A rikice jikina na kyarma nace "ban iskeshi ba a dakin, tace "idan kin gama sallar kije ki ganomin inya dawo, kice ya sameni a daki.

Gabana ya fadi da sauri na dago kai dk naa zaro idanuna lokacin harta juya zata tafi, hawayene suka kwararomin, ko kadan bnson shga harkar yaa umar!

Babu yanda na iya, ina gama sallolina na tafi jikina babu qwari, zahra na falo tana kallo batasan wucewatah ba a hankali kamar mai koyan tafiya na qarasa dakin dk a tsorace nake!

Har bedroom dinshi na duba bainan sannan sauke ajiyar zuciah na juyo da sauri na nufi hanyar fita

A qofa mukayi karo dashi, da sauri na dago kaina tare da matsawa gefe a tsorace gabana na qara faduwa!

Gani nayi yana tangal tangal zai fadi da alama buge yake bnsan sanda nayi sauri na riqoshi ba na zaunar dashi samn kujera sannan na juya da sauri zanbar dakin, ji nayi yaa riqoni da qarfi ya jawoni na fada jikinshi yana bude ido yana lumshewa.

Cikin maye yace "ina zaki tafi ki barni? Yau sai naa cire hijabinnan inga abnda kke boyewa! Hankalina a tashe na fara qoqarin qwacewa anma ba qaramin riqo yaimun ba

Ya fara qoqarin hada jikina da nashi, sai tureshi nake inaci gaba da qoqarin qwacewa, wurin kiciniyar qwacewa ya fara ketamun hijabi dk hankalina ya tashi a rude nake gashi ko ihu nayi babu mai jiyoni!

Lurv my Princess Amrah😘

♥♥Rabiatu sk msh♥♥

[10:05, 4/9/2016] Rerbee'art sk: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄
                          🎄
                       🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
              🎄🎄🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                       🎄🎄
                          🎄
           NA
  Rabiatu sk msh

              7⃣

Duk ya ketamin hijabi, da naga ba cikin hayyacinshi yake ba na gartsa mishi ciwo da sauri na tureshi na qwace, saiga momie ta shgo a rude na koma bayanta jikina na kyarma

Cikin takaici momie ke mishi magana "yanzu umar bzaka daina wannan halin naka b haryanzu? Kullum cikin rantsuwa kake da zaka daina anma har yau kaqi ka canja hali? Fada sosae take mishi anma baice komi b sai layi da yake daqyar yake daga idanu

Momie tace "bxanyi magana dakai ba cikin maye, idan kaa dawo dai dai zaka gamu dani ne, sannan ta qaraso wurina tana tmbyata meya faru?

Tsabar rudewa bata bari na bata amsa ba, har lokacin jikina kyarma yake bakina ya kasa cewa komi da sauri na juya nabar dakin ina qanqame da jikina ina kuka!

Ranar banyi barcin kirki ba, cikin dare na tashi na hada kayana tunda safe momie ta shgo dakina kafinta fita office ta iskeni gaban kayana ina hawaye!

Gaisheta nayi kaina a qasa ina qoqarin maida hawayena, taa dade a tsaye kafin tajaa numfashi ta fara magana "bzan hanaki tafiya ba hafsa damn shawarar da nayi kenan, anma kiyi haquri hafsat kimin alqawarin bzaki fadama kowah ba, daga mata kai nayi ina hawaye ta dafa kaina tace "Allah ya miki albarka hafsatul kiram,

Ta dade tanamin nasiha sosae tana bani haquri, nikam godia nake ga Allah da bai bawa ya umar sa'a a kaina ba! Ta saka driver ya kaini gda

Su momie sunyi farin ciki da dawowatah gidanmu don nima naji dadi sosae na dan samu natsuwa, ko kadan ban bari su momie sun gano damuwatah ba!

Lokacin daddy harya nemamin admission har motah ya siyamin saboda zuwa makaranta, duk da nace bzan iya drivn ba sai dai driver ya dinga kaini, don ko motah naqi in koya.

♥♥Rabiatu sk msh♥♥

[10:31, 4/9/2016] Rerbee'art sk: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄
                          🎄
                       🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
              🎄🎄🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                       🎄🎄
                          🎄
           NA
  Rabiatu sk msh

            8⃣

Kwatam rannan ina kwance dakinah kiran momie ya shgo a wayata, ina dauka tace in sameta falon daddy

Zaune na iskesu momma da daddy, Aunty rabiatu, momie khadija da mijinta Alh basheer sai faruq daya sunne kai ya zauna samn kujera

A rude na gaishe da kowa gabanah na faduwa na samu wuri na zauna nima na sunnar dakai qasa

Daddy na ne ya kira sunana, a hankali na dago kai yaci gaba da mgn  "ga dan uwanki nan yaazo da maganar nemn aurenki, munyi farin ciki sosae, damn burinmu kenan mu hada aurenku da fatan kema bzaki qi amincewa ba!

Jikinah ya fara kyarma da sauri na dago kai ban iya tsaida hawayen firgicin dake zubomin ba, idan nace banison yaa umar naayi qarya! Kuma bzan iya qin umarnin iyayenah ba, anma idanna tuna abubuwan da suka faru kuma sai inji bzan iya amincewa ba!

Rasa amsar daxan basu nayi, kuka mai qarfi naji na qoqarin zomin, da sauri na tashi cikin sassarfa qafafuna na hardewa na tafi dakina na fada gado ina kuka!

Bnsan shgowarta b, sai dai naji ta dafani da sauri na tashi kaina a qasa, momie khadija ta fara magana cikin damuwah "bzanso mu takura miki ba muyi miki dole, idan har bakison faruq babu mai takura miki, anma alfarma nake nema a wurinki ki amince da aurennan don nasan ke kadai zaki iya taimakamin wurin canja faruq! Don Allah ki mnta da dk abnda ya miki ki amince da auren! Ko kinaso kicemin baki haqura da abnda ya muki ba?

Damuwah ce sosae a fuskar momie da bzan iya jure gani ba, share hawaye nayi ina murmushi nace na amince da wannan auren momie

♥♥Rabiatu sk msh♥♥

[10:50, 4/11/2016] Rerbee'art sk: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄
                          🎄
                       🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
              🎄🎄🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                       🎄🎄
                          🎄
           NA
  Rabiatu sk msh

             9⃣

Farin ciko sosae na gani a fuskar momie taa sanyamun albarka, ta fita ta yima su momma albishir suma sunyi farin ciki sosae, a ranar aka sanya lokacin aurenah da yaa umar wata daya!

Tunda aka saka ranar aurenmu bn qara ganinshi ba, anma yana kirana a waya hrda bni kulawa ta musanman, dk da inajin kamar momie ce ke tilastashi kirana, anma inajin dadi saboda son da nake mishi ba kadan bne!

Lokacin bikinmu bnyi wani hidima b, walima ne kawai da wa'azi sai dai su momma dake tashan shagalinsu,

Ranar juma'a aka daura aurena da yaa umar, Alhmdlh daurin auren yaa samu shaidar mutane da dama, unguwarmu b masaka tsinke!

Aka kaini gdana dake Abuja da yake a can yake aiki.

Da dare ina zaune tsakiyan gado bayan kowah ya tafi, nasha lullubi da qatuwar hijabi na har lokacin kuka nake ga kewar momie da tausayin kaina.

Wallahi Aunty yaa umar bai shgo gdannan ba sai qarfe dayan dare yaa wuce tun ina duban agogo har na gaji, zamn ya isheni anma na kasa kwancia.

A buge ya shgomin yana tafiya yana hada hanya kamn zai fadi da sauri na dago ina kallonshi ya fada samn gado kafafuwanshi a qasa.

Wasu zazzafan hawayene suka zubomin, bzan iya misalta halin dana shga ba, naa dade a zaune ina kallonshi kafin in miqe daqyar na gyara mishi kwancia na koma naci gaba da hawaye

Ranar farkon aurenah, ranar da kowacce Amarya take kwanan farin ciki, ranar tarihi, ranar cikar buri,........

Ni da baqin ciki tazomin, ranar da bzan taba mntawa da ita b, ranar bnyi brci b sbd baqin ciki da takaici, kwana nayi ina sallah ina kai kukana ga ubangiji!

♥♥Rabiatu sk msh♥♥
[15:02, 4/11/2016] Rerbee'art sk: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄
                          🎄
                       🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
              🎄🎄🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                       🎄🎄
                          🎄
           NA
  Rabiatu sk msh

             🔟

Washe gari duk da brcin dake idona ga gajia, hka na daure ina gama sallolina da azkar na shga kitchen na hada mishi break fast kusan kala biyar sai qamshi suke, dai dai cikinmu na dauko da niyyar jerawa a dinning

Hangoshi nayi zaune da kwalbar giya hannunshi da kofi yana zubawa, gabanah ne yayi mummunar faduwa, na qarasa na fara jerawa ko kallona baiyi b harna gama zuzzuba mishi na miqa mishi gabanshi

Idanunshi jawur ya dago kanshi yanamin mugun kallo duk na tsorata, miqewa yayi tsaye a zuciye yasa hannu ya ture kayan break fast dn qasa, wasu suka farfashe duk abncin ya zube.

Da yatsa ya nunani yace "karki kuskura ki qara nunamin wannan baqar fuskar taki, a idon dunia ne kke matata anma ni bzan taba iya kallonki a matsayin mata b, ke kanki kinsan ke ba sa'ar aurena bace! Yaja tsoki ya wuce yz brni a tsaye kamar warda aka dasa hawaye na tsiyaya a idona.

Tun daga ranar da aka kawoni gdan yaa umar har yau takaicinsa kawai nakesha, kullum qoqarin kyautata mishi nake, dk da baicin grkina bn taba fashin yi masa ba

Baisan cina ba, baisan sha na ba, ba ruwanshi damin sutura bai damu da ynda na kwana b sai nice ke zuwa gaisheshi, bbu haqqin auren daya taba saukemun.

Kullum cikin yi mishi addu'a nake bn taba gajia b, kullum dare nake rabawa ina roqa mishi shiriya!

Na kalli hafsatul kiram nace "ya lbrn zahra? Momie khadija tasan abnnan dake faruwa??

Bn taba fadama momie abnda yakemun ba, kuma bn tunanin taa sani! Anma tana yawan kawo mana ziyara, komai ita kemun suma sun dawonan Abuja da zama

Bnsan yanda suka rabu da zahra b, anma naaji lbrn taayi aure, anma nemn matanshi babu abnda ya canza

Kuma karki dauka wai waje yake fita yayi, cikin gda yake shgowa dasu, wani lokacin ma sai dai yamin wulaqanci ya fiddoni falo a dakina zasu kwana da wadda yazo da ita ta qarasa maganar da hawaye.

♥♥Rabiatu sk msh♥♥
[15:14, 4/11/2016] Rerbee'art sk: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄
                          🎄
                       🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
              🎄🎄🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                       🎄🎄
                          🎄
           NA
  Rabiatu sk msh
         
        1⃣1⃣

Cike dajin haushin faruq na kalleta nace "tashi ki shrya kayanki hafsatul kiram, bzan tafi in barki gdannan ba, bzaku zauna yaci gaba da wulaqantaki ba, kina yarinyrki zaki zauna da baqin ciki? Bzan taba yrda ba saina nema miki haqqinki.

Riqe hannuna tayi tana girgiza kai tace "bzan tafi ba Aunty, don Allah karki fadama kowa, akwai inda yafi qima da daraja a wurin mace fiye da gdan mijinta? Idan naje gda bbu abnda zai faru sai baqin ciki da bacin rai daxan saka iyayena a ciki in brsu cikin damuwa, bzanso hkan ba Aunty, bzanso abnda zai bata mna zumunci ba don Allah aunty karki fadama kowa!

Tausayi ta bni saboda irin kukan da take tana roqona kar in fada, kallonta kawai nake cike da tausayi kafin ince matah

"Kinsan kuwa idan dai akwai laifin faruq akwai naki a ciki?? Da sauri ta kalleni tace "laifina kuma??

Na daga mata kai nace "tabbas! Shekara guda tsakaninki dashi ace kin kaasa jawo hnkalinshi?? Tinda kke dashi yaa taba ganin surar jikinki?? Kullum cikin abaya kke koni zan iya cewa baifi sau daya na taba ganinki b hijabi b, haba hafsatul kiram aure pa dabanne, namiji kamar yaro yake mai lallashinsa yakeso! Cire kunya zakiyi ki nuna mishi soyayya, su da yake wulaqantaki kansu bsu fiki diri da qira mai kyau b, Allah yayi miki anma kibr mijinki cikin halaka yana kula matan bnza

Idan faruq abnda yakeso knan nizan maidaki kamn en matan nashi, ki cire kunya ki dnga tarairayar mijinki, ki dnga saka mishi irin suturar da yakeso

Girgiza kai tayi tace "Aunty son gsky nake yiwa yaa faruq nima son na gsky nakeso yamin, bzanso ya fada sona sbd sha'awah b nasan bzai dore ba, inaji a jikina wata rana zai soni, anma bzan canja dga ynda nake ba don in yaudareshi ya fadama sona! Idan zai soni ya soni a yanda nake! Ki tayani addu'ah kawai Aunty.

Kalamnta sun sanyayamin jiki, tabbas taa fini gsky indai namiji bai sonka, tohm kiyayyar tananan dk wani kissa da iyayi bzasu samo soyayyrshi ba, suma mutanen wajen jikinsu kawai yakeso bawai sudin yakeso ba!

Na share mata hawaye nima ina hawayen nace "shikenan hafsa Allah ya karkato miki hnkalinshi gareki ya sanya soyayyarki a zuciarshi ke kuma ya qara muki haquri da juriya, insha Allah zanci gaba da tayaki addu'a!

Tayi murmushi tare da rungumeni tace "nagode Auntynah! Nasiha na qara yi matah sosae, sai bayan isha'i nabar gdan cike da tausayinta hr lokacin umar bai dawo b!

🔅muje zuwah! Don ynxu labarin zai fara🔅

Lurv my princess Amrah😘

♥♥Rabiatu sk msh♥♥
08032133670

🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄
                          🎄
                       🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
              🎄🎄🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                       🎄🎄
                          🎄
           NA
  Rabiatu sk msh

         1⃣2⃣

12pm hafsatul kiram na zaune falo tayi jugum don duk irin daren da umar zaiyi bata iyayin barci sai taa jira yaa dawo.

Kamar kullum tare suka shgo da wata daga cikin en matanshi ta dora kanta samn kafadanshi suna tafe cikin nishadi

Baiko kalli inda take ba suna tafia yace "ki kawo mna coffee, sannan suka wuce dakinshi, kamar wadda qwai ya fashe mawa ta tashi ta nufi kitchen!

Wurin saukewa tana can tunani ruwan zafi ya zubar mata a qafa, da sauri ta ajiye, ta koma baya tana yarfe hannu wani irin azaba takeji har wurin yayi ja!

Muryarshi ta jiyo yana cewa "ke wace irin kidahuma ce? Komi aka sakaki saikin batama mutane lokaci??

Da sauri ta juye musu ta nufi dakin nashi! Rungume ta iskesu da juna yana shafa mata bayanta! A zafafe ya dago fuskarshi yace "idan jahilci yaa hanaki sallama knockn ma bzaki iyayi ba?

Rumtse idonta tayi cikin jin zafin kalamnshi, anma a zahiri sadda kanta tayi tace "yi haquri! Yaja tsoki ya juya yanama budurwarshi mgn a hnkali

Saman bedside ta d'ora musu qafarta mai toyewar tadan bugi gadon ta saki er qara ta tsugunne wurin ta dafe qafar tana hawaye!

Kallonta yayi yaga ynda qafar tayi jaa, muryarshi ba yabo ba fallasa bai mata tsawar daya saba b yace "jira kike sai naace ki 6acemun da gani!

Da sauri har hijabinta na hardeta tabar dakin! Hawaye naa zuba a fuskarta!

A qofar dakin ta jingina idonta a rufe tace "Ya Allah ka yafe mishi! Sannan ta wuce ta nufi dakinta!!

Kuyi haquri da typin kadan plz

Lurv my princess Amrah😘

♥♥Rabiatu sk msh♥♥

[15:24, 4/13/2016] Rerbee'art sk: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄
                          🎄
                       🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
              🎄🎄🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                       🎄🎄
                          🎄
           NA
  Rabiatu sk msh

         1⃣3⃣

Da safe taa gama jera mishi break fast a dinning, tana dakinta kiran momie ya shgo mata, da sauri ta dauka cikin girmamawa take gaisheta!

Sun gama gaisawa cikin kulawa momie tace "kuna tare da umar? Gaban hafsat ne ya fadi tace "eeh momie gashinan! Momie tace "tohm bashi wayar!
    Zaro ido tayi kamar gaban momie a tsorace, maganarta na hardewa tace "kin kirashi ne momie? Ni...yanzu....Yana...., sai kuma tayi shru dk taa rasa abnda zatace! Murmushi momie tayi don taasan basu tare tace "shknan kice mishi ya kirani, hafsatul kiram tace tohm "ta sauke ajiyar zuciah!

Momie na kashewa umar ta kira, da sauri ya janye budurwarshi dga jikinshi dk yaa nutsu ya dauki kiran, cikin tattausan lafazi momie ke mishi magana tace " ena hafsatul kiram? Yace "gatanan momie! Tace tohm bata wayar! Shru yayi alamar baida gaskia, momie ta sauke ajiyar zucia sannan tace "anya kuwa umar baka gudun haqqin yarinyrnan ya kamaka? Allah ya bka yarnya mai haquri anma bzaka daina cutar da ita ba?

Yace "momie ita tace nayi mata wani abn? Tace "kaji tsoran Allah umar mata irin hafsatul kiram wahalan samu ne dasu a zamaninnan namu! Shru yayi zuciarshi naa mishi quna! Momie tace "kuma ka kawomin ita kafin ka wuce office! Yace momie..., ta kashe wayan!

Har wani hucin 6acin rai yake wai baqauyiyar yarinyarnan zai dauka a motanshi!

Ya banka qofar dakin ya shga da sauri ta dago kanta a tsorace, ya wurga mata wata uwar harara yace "ke ko kunya bakiji ba kinje kin hadani da mahaifiyatah?? Ta sadda kai saboda ko kadan bataso tai mishi musu! Sai da ya gama fadanshi sannan yace ta tashi su tafi!

Ta miqe damn taayi wankanta tsaf da hijabinta jikinta don hafsatul kiram akwai tsafta, da son gayu kullum cikin qamshinta take mai dadi!

Lurv my princess Amrah😘

♥♥Rabiatu sk msh♥♥

[16:35, 4/13/2016] Rerbee'art sk: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄
                          🎄
                       🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
              🎄🎄🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                       🎄🎄
                          🎄
           NA
  Rabiatu sk msh

          1⃣4⃣

Tare da budurwarshi suka fita suna zaune gaba, ita dai dk jinta take a takure ta rasa inda zata ajiye idanunta, duk taa qagara su isa!

A qofar gidan yayi parking mai gadi na qoqarin budewa ya dakatar dashi, tsayawa tayi bata bude motan ba ya juyo ya galla mata harara ba tare da yayi magana ba! Da sauri jikinta naa kyarma ta buda motan ta fita yata tsaki a fili yace "duk dai yanda za'ai da jaki sai yaaci kara! Hawaye ne suka zubo matah, don tsabar qunar zuciah ma kasa matsawa tayi

Da gayya yaja motar da qarfi har yana bugeta ta fadi wurin ya tara mata qura yayi gaba! Ta share hawayenta tare da kakka6e jikinta sannan ta shge gdan tana qoqarin dai daita nutsuwarta!

Da murnarta ta shga gdan, momie taaji dadin ganinta, ta rasa inda zata saka ta sai nan nan takeyi da ita, tace "shi umar din bxai iya shgowa ya gaisheni bne? Hafsatul kiram tace "A'ah momie anata mishi wayane office da muna hanya shyasa yace sai ya dawo daukana! Momie tace "ki fadamin idan akwai abnda yake miki, tana murmushi tace "ba komi momie, yaa umar yana kulawa dani sosae! Hawaye suka zubo mata ta kasa dago fuskarta!

Duk yanda momie taso ta fahimci damuwarta bata bari ba, ta sake sosae dk da kunyar momie da takeji, da dare ma baizo ba sai wurin 10 hartaa farajin barci!

Momie ta hadesu su duka ta musu nasiha mai ratsa jiki shidai saurarenta kawai yake, kamar karta bar gidan momie don wani irin farin ciki takeji data dade batayi ba!

Da taje shga motar har taa bude baya zata shga ya daka mata tsawa yace "naayi miki kama da driver ne? Da sauri ta bude gaba ta zaune dk taa takure yajaa mota suka tafi.

A hanya tunani take yaune rana ta farko da suka tana kasancewa tare ba tare da yana cikin maye ba ko yana tare da wata, lallai ya kamata tayi amfani da wannan damar wurin tunasar dashi Abnda ya mnta.

A hankali ta rufe ido duk taa tsure a tsorace take tana jiran taji ta inda zai fara kai mata bugu, da zazzaqar muryarta ta fara magana "

"Yaa umar! Basaina fada mka ba kaasan illar shaye-shaye, kaasan illar zina, domin manzon Allah (S.A.W) Ya hanemu da shan giya, kuma Allah (S.W.T) yaa fada a cikin ayoyinsa na alqur'ani akan haramcin zina, kuma duk wani mai aikata zina bazai tabayin arziqi ba, kuma Allah yana fushi dashi kuma taafi kowanne aiki laifi a wurin ubangiji, Akwai hukuncin shari'a kuma! Zina bashi ce Yaa umar! Idan ba'ayi da......,

Wani wawan burki taji yaaja a tsorace ta qara maqure kanta jikin qofa sannan ta bude ido a tsorace don ita duk tunaninta Abnda take fadane ya bata mishi rai, gani tayi hnkalinta ma ba wurinshi yake ba dk abnda take fada baji yake ba, cikin tashin hankali ta maida kallonta bakin titi da yake kallo!

Lurv my princess Amrah😘

♥♥Rabiatu sk mashi♥♥

[13:35, 4/14/2016] Rerbee'art sk: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄
                          🎄
                       🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
              🎄🎄🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                       🎄🎄
                          🎄
           NA
  Rabiatu sk msh

          1⃣6⃣

Wata budurwah tsaye bakin titin, tana sanye da doguwar riga da bata ida kai mata qasa ba, taa matse jikinta sosae kanta ko dankwali babu da manyan kalaba a kanta!

Ya kalli hafsatul kiram ta sadda kai, yaja tsoki yace "a samnki zata zauna? Ki fice ki bata wuri! Kaasa maida hawayen da sukazo mata tayi, ta tashi jiki ba qwari ta koma baya ta xauna!

Ta bude motan ta shgo tana yatsina ta xauna! Yace "kinanan da kyaunki deezy, tayi murmushi tace "kuma inanan da soyayyarka zumanah! Hnkalinka kwance kaa wani mnta dani! Yace "waya isa ya mnta dake zuma? Allah ina sonki da yawa! Ya kamo hannunshi ya hada da nata kamar mai shrinyi mata kuka yace "naa rasaki a wancan lokacin, ynxu bzan taba bari ki gujemun ba! Rungumeshi tayi tace "bxan taba rabuwa dakai ba faruq.

Wacece deezy??
Budurwar umar ne tun lokacin da yayi karatu qasar waje, suna matuqar son junansu tunda suka gama ckul basu qara haduwa ba sai ynzu! Itama abuja take!

Hafsatul kiram sai ta zama er kallo, duk qoqarin da take na tsaida hawayenta taa kaasa hanasu zuba, haka yake tuqi suna shan soyayyarsu hannunshi daya ke tuqi daya na riqe da nata!

Sun dade kafinsu isa gdan saboda yana yake drivn a hankali, yanayin parking hafsatul kiram ta bude motan ta fita ta barsu, har jiri ne yake daukarta saboda tsananin tashn hankali!

Dakinta ta wuce damn taayi sallolinta tun gdan momie, hartaa kwanta momie ta kirata, tace "kunje gda lpy? Hafsat tace "lapia lau momie harzan kira kuma nayi tunanin kunyi brci? Tace "ina pa zanyi brci bnji ynda kuka isa ba, ina umar din?

♥♥Rabiatu sk msh♥♥

[14:39, 4/15/2016] Rerbee'art sk: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄
                          🎄
                       🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
              🎄🎄🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                       🎄🎄
                          🎄
           NA
  Rabiatu sk msh

          1⃣7⃣

Ta kalli gefenta hawaye suka zubo mata sannan ta tashi ta fita falo inda umar da deezy suke tace "gashi momie, sannan tasa hannu biyu ta miqa mishi wayar tace "momie ce! Da sauri ya ansa dk ya rude sukai mgn ya gama ya miqa mata wayar!

Deezy ce ta qare mata kallo sannan tace ma umar "wannan a gdannan take? Da alama yanajin ciwon abnda zai fada daqyar ya cije ya iya cewa "matata ce, da mamaki tana yamutsa tace mishi "ynzu zuma dk kyawawan en matanka wayayyu ka qare da auren wannan?

Yace "babu ynda na iyane zumah! Anma tunda gaki kin dawo gareni ynzu bnda wata damuwa! Tayi murmushin jin dadi sannan ta watsama hafsatul kiram harara!

Juyawa tayi tabar wurin ta wuce dakinta, inda sabo ya kamata ta saba, taa dade kafin barci marar dadi ya dauketa! Kamar kullum taa tashi tsakar dare tayi sallolinta, taa dade tana miqa kukanta wurin ubangiji bata koma brci ba saida tayi sallar asuba, ta shga kitchen ta hada mishi break fast sannan ta koma ta kwanta!

Batasan fitarsu ba, sai dai ta farka basunan! Tayi shru ita kadai, dk da taa saba da kadaici anma shru yaa isheta ga damuwa data ke matah yawa!

Dawowar deezy rayuwan umar yaa daina shgoma hafsatul kiram gda da en matah, itama deezyn bata qara kwana ba!

Sai dai taa daina ganinshi hafsatul kiram, bai shgowa gdan sai dare yaayi sosae kuma tunda safe zai fice!

Nan danan hafsatul kiram ta fara rama, kullum da hotan umar take kwana a qirjinta, don zaifi mata dadi ta dinga ganinshi tanajin muryarshi koda zai mata dukan tsiya akan tai rashinshi. (Allah sarki hafsatul kiram, ita nata son akan wanda bai dace ba ya fada).

♥♥Rabiatu sk msh♥♥

[14:53, 4/16/2016] Rerbee'art sk♥: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄
                          🎄
                       🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
              🎄🎄🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                       🎄🎄
                          🎄
           NA
  Rabiatu sk msh

           1⃣8⃣

Zaune take hafsatul kiram ta saka hotan Umar a gaba hawaye na zuba a idonta ita kadai ke magana cikin kalar ban tausayi "Yaa umar mai yasa zakamin wannan hukuncin? Zan iya jurar ko wanne hukunci daga gareka anma bnda wanda xai nisanta ni da ganinka? Meyasa ka tsaneni? Meye bkaso wanda nake da? Zan iyayin komi daxai sanyaka farin ciki, Rayuwatah ne kawai bn iya qararwa saboda inason inyita ne tare dkai! Anya kuwa akwai ranar da zaka so ni??

Daga bakin qofa taji an bata amsa da "A'ah, da sauri ta dago tana kallon deezy har lokacin hawaye na zuba a fuskarta, deezy taci gaba da magana "babu ranar da zumanah zai soki, ni kadai yakeso, kin gani ba? Igiyoyn aurenki da suke kanshi ba wani Abu bne, don bzaki taba mallakar zuciarshi da gangar jikinshi ba! Sunana deezy! Bzan taba yrda wata ta shga zuciar umar ba bayanni!

Hafsatul kiram bata tanka mata ba suka jiyo muryar Umar naa kiranta, tayima hafsatul kiram kallon sama da qasa ta juya ta fita! Zama tayi saman gadon tana ci gaba da kukanta!

A qofar fita falon sun jera shida deezy zasu fita momie ta shgo, sakin hannunta yayi ta matsa daga kusa dashi, wani irin kallo momie ta watsa mishi duk yaa rikice cikin in ina yace "momie deezy ce, ya kalli deezy yace "gaa momienah!

Harda duqawa ta gaishe da momie cikin jin kunyar kayan dake jikinta, fuskar momie ba yabo ba fallasa ta amsa sannan tace "deezy ko zaki bamu wuri muyi magana da d'ana? Tace "Tohm momie! Ta juya ta nufi hanyar fita, Umar Yace "ki jirani inzo, ta daga mishi kai ta fita!

Lurv my princess Amrah😘

♥♥Rabiatu sk msh♥♥

[15:47, 4/16/2016] Rerbee'art sk♥: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄
                          🎄
                       🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
              🎄🎄🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                       🎄🎄
                          🎄
           NA
  Rabiatu sk msh

            1⃣9⃣

Momie ta kalli Umar cikin mamaki tace "wai umar meka dauki aurene? Gidanka zaka shgo da wata macen? Har yau kai bzaka nutsu ba? Nayi zaton idan na aura maka hafsa zaka dawo hankalinka kasan me kake, anma kana cutar da yarinyar da babu ruwanta!

Yace "momie ki fahimceni nipa....! Daga mishi hannu tayi tace "naa riga naa gama fahimtarka umar, qarama tun wuri ka koyama kanka son hafsatul kiram, idan har bzaka iya bata haqqoqonta na aure ba nizan nema matah haqqinta! Da sauri ya kalli momie cikin mamaki! Ta daga mishi kai tace "tabbas nizan qwatoma hafsatul kiram haqqinta!

Juyawa tayi ta fasa shga wurin hafsatul kiram saboda yanda umar ya gama bata mata rai, tsaki taja tun farko sune suka sangarta shi da soyayyarsu wai danshi kadai ne suka haifa, ga hafsatul kiram nan da take ita kadai a wurin iyayenta hakan baisa sunqi bata tarbiya ba, yarinya mai nutsuwa, kawaici, haquri da biyayya!!

Umar kaasa motsawa yayi daga inda yake saboda tsananin bacin rai da tashin hankali, zuciar en maza taa baci kamar ta fasa qirjinshi ta fito!!

Juyawa yayi ya nufi dakin hafsatul kiram da batasan meke faruwa ba, fitar deezy momienta da daddy suka kirata suna fira cike da kewar gida, sai dai taji ya banko qofa cikin bacin rai, da sauri jikinta naa kyarma tace "momie, daddy zan kiraku! Bata jira mezasu ce ba ta kashe wayar!!

Miqewa tayi tsaye cikin tsoro jikinta na kyarma ya shaqota cikin zafin nama ya nannadeta cikin hijabin jikinta duk idanunta sun firfito sumane kawai batayi ba don tsananin tsoro!

Cikim daga murya yake magana "sau nawa zan fada miki ki daina shga tsakaninah da mahaifiyatah? Naa fada miki sau ba adadi bn sonki, bn qaunarki, na tsaneki! Baqin ciki yake qaramun ganinki a cikin gidannan! Bn taba tsanar abu ba duk duniar nan kaman yanda na tsaneki!

Jefar da ita yayi gefe guda ta fada saman gado ta saki wani irin kuka mai cike da ban tausayi! Juyawa yayi cikin fushi zaibar dakin yaci karo da momie tsaye bakin kofa!

Gefe yaja ya tsaya yanaci gaba da huci kamar zaki!

Lurv my princess Amrah😘

♥♥Rabiatu sk msh♥♥
[17:05, 4/16/2016] Rerbee'art sk♥: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄
                          🎄
                       🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
              🎄🎄🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                       🎄🎄
                          🎄
           NA
  Rabiatu sk msh

          2⃣0⃣

Momie tace "miye hka umar? Cikin huci idanunshi sunji jajir yake cema momie!

Kinji da kunnanki ba? Deezy kawai nakeso momie! Naa auri hafsatul kiram ne kawai saboda farin cikinki, anma bzan taba iya kallonta a matsayin matah ba! Raina qunah yake a duk lokacinda na tuna wai itace matatah hkan na cutar da zuciatah! Na auri hafsatul kiram saboda umarninki, kinyi farin ciki ba? Anma hkan bzaisa in zauna da ita a matsayin matah ba!

Ya juya ya fita fuuuu kamar mai shrin tashi sama! Da sauri hafsatul kiram ta tashi ta jawo akwati ta fara hada kayayyakinta! Momie ta qaraso inda take cikin sauri har tana hardewa tace "me kke shrinyi hafsatul kiram? Daina zuba kayan tayi sannan ta dauki jikkarta ta rataye kanta a qasa tana hawaye tace "gidanmu zan tafi momie, ni kadaice matsalar yaa umar! Bzanso in sakashi a damuwah ba, qara in tafi inyi nesa dashi!

Momie tace "kina nufin kin haqura dashi? Hafsatul kiram tace "naa haqura da yaa Umar momie, zam barshi yayi rayuwarshi da wacce yakeso! Momie ta dafa kafadarta tace "son da kke mishi pa? Shru hafsatul kiram tayi, Momie tace "duk son da kke mashi zaki tafi ki barshi??

Tace "Inason yaa umar momie, anma idan har naa kasa sakashi farin ciki bai cancanci kullum in dinga quntata mishi ba, yaa fada da bakinshi ba son ganinah yake ba! Momie banison abnda zai batama yaa umar rai! Ta juya taci gaba da tattara kayanta!

Momie tace "nasan kinyi haquri hafsatul kiram, kina da matuqar biyayyah! Naa kasa sama miki farin ciki a rayuwar aurenki, karki tafi kibar umar yana da buqatarki, naayi miki alqawarin zan nema miki 'yancinki anma don Allah karki tafi!

Rumtse ido tayi yanda momie ke lallashinta, bangare daya kuma ga farin cikin Umar da tsanar daya mata! Bataso ta tsaya wani tunanin dazai karyar mata da gwiwa, taa kasa hada ido da momie saboda wata irin kunyarta da takeji!

Kanta a qasa daqyar maganarta ke fita saboda tsananin kuka tace "kiyi haquri momie naa kasa zama suruka ta gari a gareki, naa kasa zama matar da danki zaiyi alfahri da ita! Kiyi haquri momie anma bzan iya ci gaba da cutar da zuciar yaa umar ba! Nice matsalarshi, idan na barshi xaiyi farin ciki, hakanne burinah!

Ta dauki akwati da jikkarta a rataye ta nufi kofa!

Lurv my princess Amrah😘

♥♥Rabiatu sk msh♥♥

[15:10, 4/17/2016] Rerbee'art sk msh: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄
                          🎄
                       🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
              🎄🎄🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                       🎄🎄
                          🎄
           NA
  Rabiatu sk msh

         2⃣1⃣

Kafin takai 'kofa momie tace "shikenan ki tafi hafsatul kiram!  Ta tsaya tana share hawaye ba tare data juyo b, momie ta matso kusa da ita tace "ki tafi hafsatul kiram bzan hanaki ba, shi baiji maganatah ba, kema da nake da yrda a kanki zaki tafi ki barni, shknan dik ku gujemun! Nasan kinyi haquri da yawa ko kadan bnga laifinki ba! Ta 'karashe maganar kamar mai kuka!

Da sauri hafsatul kiram ta jiyo, hawaye ta gani a fuskar momie, itama kukan ne ya qarazo mata cikin tashin hankali take cewa "kiyi haquri momie, ki yafemin don Allah! Babu inda zan tafi in barki!

Rungumeta momie tayi tace "bakimun komi ba hafsatul kiram, naaji dadi sosae Allah yayi miki Albarka! Cikin shessheqar kuka tace "anma momie ya xanyi da 'kiyayyar da yaa umar yamun? Momie tace "karki damu hafsatul kiram, Ynzu idanun Umar a rufe suke! Dole wata rana xaiyi dana sanin Abnda yake miki, kici gaba da haquri kinji! Amma don Allah ki daina maganar tafiya gda!

Tace "na daina momie, momie taa dade tana kwantar mata da hnkali da kalamai masu dadi, sai da ta tabbatar taa samu nutsuwa sannan ta mata sallama ta tafi!

Haka hafsatul kiram taci gaba da zaman haquri da Umar, duk abubuwan da take mishi bata fasa ba, in taayi mishi abnci sanda yaga dama yaci, randa bai dawo gidanba sai dai yanda ta ajiye ta daukeshi hka!!

Yau ta kama ranar birthday dinshi, sai tunani take meya kamata ta hada mishi? Girki na musanman ta mishi da rana! Anma har dare bai dawo ba sai dai ta fidda masu mai gadi!

List tayi ma maiyi musu ban ruwan fulawa ta aikeshi kasuwa duk abnda take buqata! Kudi sosae ta kashe, bai dameta ba indai zata faranta ran sahibul qalbeenta!

Har wurin qarfe sha biyu biyu bai dawo ba, qarfe daya duk tana zaune tana jiranshi! Sai caan taji tsayuwar motarshi! Miqewa tayi tana jiran shgowarshi!

Lurv my princess Amrah😘

♥♥Rabiatu sk msh♥♥
[15:54, 4/17/2016] Rerbee'art sk msh: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄
                          🎄
                       🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
              🎄🎄🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                       🎄🎄
                          🎄
           NA
  Rabiatu sk msh

         2⃣2⃣

Bud'e 'kofar d'akin yayi ya shgo cikin sa'a kuwa yau ba cikin mayen yake ba! Taa kashe fitilan dakin sai hasken kendir daya haske ko ina a cikin dakin taa jerasu gwanin sha'awa!

Ya dade tsaye yana qarema dakin kallo cikin mamaki kafin yaja tsoki yayi hanyar dakinshi, a hankali tace "don Allah ka tsaya! Dakatawa yayi bai dawo baya ba, tayi shru ta sadda kanta, ya juyo cikin 'kulewa yace "idan na tsaya mexan miki? Tace "inayi maka murnar qara shekara! Allah ya qara mka yawancin kwana, kalmomin bzasu iya furta irin farin cikin da nake ciki ba, babu kalmomin da zasu iya bayyana ynda nakeji a kanka!

Ga er qaramar kyauta dga gareni don Allah ka daure ka amsa! Ta miqa mishi tsadadden turare tare da nuna mishi birthday cake, miqa hannu yayi kamar abn arziqi ya amsa turaren, ya dauka wuqar yanka cake din ta saki ajiyar zuciah!

Ji tayi yana shafe matashi a fuskarta, duk ya 'bata matashi a jiki sannan ya fiddo turaren daga cikin kwalinshi ya jefashi da bango! Da razananniyar fuskarta take kallonshi hawaye na kwararowa a fuskarta kanta a duqe!

Har zaiyi magana ya fasa, yaja tsoki ya barta tsaye a wajen don wulaqancin yaa shgeta da yawa! Tana hawayen takaici ta gyara wurin ga wani irin matsanancin ciwo da kanta ke matah!

Ranar da fever ta kwana haka ta daure da safe ta tashi ta hada mishi break fast ta jera, sannan ta koma daki taci gaba da jinyar kanta! Ita kadai cikin gida take ta fama da rashin lafiya!

Haka ta yini da tsananin rashin lafiya har dare taa kasa fitowa, girki ma kasayi tayi sai dai tea taketa sha gashi ko magani bata dashi!!

Lurv my princess Amrah😘

♥♥Rabiatu sk msh♥♥

[2:03PM, 4/18/2016] Rerbee'art sk msh: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄
                          🎄
                       🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
              🎄🎄🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                       🎄🎄
                          🎄
           NA
  Rabiatu sk msh

           2⃣3⃣

Da dare Umar ya dawo, bai ganta falo ba tana zamn jiran dawowarshi kamar ynda ta saba ba, ya duba dinning bata ajiye mishi abnci ba! Dakinshi ya wuce yana tunanin kodai ta tafiyanta ne? Yace "data kyautawa kanta kuwa!

Umar ne zaune yana kallon ball, ya hango hafsatul kiram na fitowa sanye da riga da wando sun matseta sosae, taa zubo gashinta da yasha gyara ta rataya dan mitsitsin gyale a kafad'arta, tana tafiya cike da salo da rangwada bude baki yayi yana kallonta harta qaraso inda yake bai sani ba!

Ta miqa hannu ta ciro mukullan mota a aljihun gaban rigarshi sannan ta juyo ta nufi hanyar fita, cikin tsawa yace "ke! Ina zakije? Tace "inda kake zuwah kullum mna! Zan fitane nima inyo abnda kake yowah, ka kaasa tsaremun kanka ni miye amfanin na zauna ina tsare mka kaina?? Bka damu da zamanah a gdannan ba miye amfanin inta zama?

Cikim d'aga murya yace "kina da hankali kuwa? Kepa macece! Hafsatul kiran tace "su wanda kake fita kana tafiya wurinsu ba matah bane? Miqewa yayi cikin bacin rai da niyyar marinta, da zafin nama ta riqe hannun tace "bn gama ba!

Kallon mamaki ya bita dashi kafin ta maidashi ya zauna kamar wanda akaima satar kuzaru ta duqo saitin fuskarshi wannan karon cikin tattausan murya mai cike da damuwa take magana

Tace "kasan yanda mutum keji a duk lokacin da yayi qoqarin gamsar da jama'a babu abnda ke damunshi, anma babu abnda yake tafiya mishi dai dai?

Kasan yanda mutum keji idan yana murmushi a fili, anma yana kuka a zuciarshi?

Kasan yanda mutum keji idan mafarkinshi, burinshi, abnda yakeso ya kasa mallaka?

Kasan yanda mutum yakeji idan wanda yafiso ya tsaneshi ya fifitashi fiye da wani?

Ni kadai nakejin haka a zuciatah, nasan wata rana dolene kaima zakaji hkan! Zanci gaba da sonka da zuciyarda kullum take quna a kanka.

Zanci gaba da sonka da wannan marainiyar zuciar tawa! Soyayyatah nada qarfin da babu wanda zai iya maka kwatankwacinta har Abada!

Lurv my princess Amrah😘

♥♥Rabiatu sk msh♥♥
[2:59PM, 4/18/2016] Rerbee'art sk msh: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄
                          🎄
                       🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
              🎄🎄🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                       🎄🎄
                          🎄
           NA
  Rabiatu sk msh

         2⃣4⃣

Firgigit Umar ya farka daga barcin da yake, dafe kanshi yayi maganganunta na cikin mafarki naa dawo mishi, jikinshi yaayi matuqar sanyi, Abubuwa da yawa ke dawo mishi cikin kai. Tabbas akwai wani abu tattare da wannan mafarkin

Dai dai lokacin hafsatul kiram farka dafe da qirji, itama irin mafarkin da tayi kenan, innalil lahi wa inna ilaihir raji'un kawai take maimaitawa, istigfari kuwa taayi yafi cikin carbi! Hawaye ne a fuskarta, a fili ta furta "Ya Allah ka yafemin, ya Allah karka nunamin ranar da zanyiwa mijinah magana irin haka, Ya Allah karka nunamin ranar daxan sa6a mishi! Hannu tasa ta share hawayenta Hawayenta

Lokacin gari harya fara haske batasan sanda barci ya d'auketa saman sallaya ba! Miqewa tsaye ta farayi da niyyar shga kitchen ji tayi bzata iya ba, jikinta yaayi zafi sosae, ga wani irin jiri da takeji!

Miqewa tayi daqyar ta daura niqab ta fita ta ba daya dga cikin ma'aikatan gidan kudi ya sawo mata magani, komawa gida tayi don bzata iya jiranshi ba saboda wani irin jiri da takeji ga ciwon kai mai zafi!!

Umar ya fito da shirin tafiya office har lokacin jikinshi a sanyaye yake, ya duba dinning bai hango break fast ba, daga nesa ya dinga leqen kitchen kozai hangota anma batanan, ji da kanshi ya hanashi dubawa dakinta ya nufi hanyar fita!

Sai daya fita dga falon a hanya suka yaga dan aiken hafsatul kiran tsaye da leda yana jiranta da yake basu shga gidan, Umar ya kalleshi yace "wannan laidar pa? Cikin girmamawa Yace "hajia ce ta aikeni in siyo mata magunguna! Miqa hannu yayi jikinshi ba qwari ya ansa yace "yi tafiyarka kawai!

Komawa yayi cikin gidan, ya shga dakinta can ya hangota qarshen gado ta nannade wuri daya sai kyarmar sanyi take, matsawa yayi inda take ya tsaya yana qare mata kallo!

Jikinta ya bata ana kallonta, a hankali ta bude ido, ganinshi da tayi tsaye ya sanyata saurin tashi zaune! Gabanta na faduwa ta kasa hada ido dashi!

Saman bedside ya daura mata ledar magungunan sannan yace "baki lafiya ne? Daga mishi kai tayi muryarta na rawa saboda yanayin yanda takejin jikin tace "masassara ce kawai, nasan idan nasha magani zanji sauqi! Shru tayi wani irin farin ciki na ratsata, wai yau yaa umar ne da shgowa dakinta ba tare da yayi mata tsawa ba ko rashin kirkin daya saba!

Daga mata kafada yayi na nuna rashin damuwa, ya bude baki zaiyi magana kira ya shgo a wayarshi, dauka yayi da sauri yasa a kunnenshi sannan ya juya ya fita yana cewa "zumanah, haba kema kinsan bzan iya fita office ba tare da munyi waya ba!

Wani hawayene suka zubo ma hafsatul kiram tabi bayanshi da kallo, tabbas tana cikin damuwa!

Maganin tasha sannan ta koma ta kwanta tanajin wani irin radadi a cikin zuciarta! A haka barci ya dauketa cike da mafarkai kala kala! Masu dadi da marassa dadi!!

Lurv my princess Amrah😘

♥♥Rabiatu sk msh♥♥
[3:38PM, 4/18/2016] Rerbee'art sk msh: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄
                          🎄
                       🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
              🎄🎄🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                       🎄🎄
                          🎄
           NA
  Rabiatu sk msh

          2⃣5⃣

Sai kusan 11am ta farka, lokacin kan yaa rage mata ciwo anma jikinta babu qwari! Tana dafa bango har takai toilet, ta shga tayi wanka sannan ta fito! Lokaci daya harta fara ramewa damn b qiba ne da ita ba!

Mai ta shafa kawai da hoda, sannan ta dauki kayanta ta saka, taa dade tsaye a gaban madubi tana kallon kanta babu hijabi, hawayene suka zubo mata! Ta dauki wayarta tana kallon hotan Umar wani sonshi na qara shgarta!

A fili ta furta "kayi haquri yaa umar da ban zamo kalar matar da kakeso ba, naa kasa zama kalar matar da kakeso!

Kira ne ya shgo wayarta daya katse mata kallon Umar din nata, sunan Aunty Rabiatu ta ganu rubuce a secreen din, dadine ya ratsa mata zuciah damn tana kewar Auntyn tata, sai da ta zauna bakin gado saboda ynda takejin tsayuwar sannan ta dauka! Hafsatul kiram tace "Auntyna ina tunaninki sai gashi kin kirani, nace "haba hafsatul kiram anyama kina tunawa dani? Ya naji muryarki kamar baki lafiya??

Tace "laah waini Aunty? Babu komi qlw nake, nace "ki fadamun gaskiya kodai Umar dinne har yanzu? Tace "A'ah wlhy Aunty masassara nake anma da sauqi, anma ynzu komi yaa wuce tsakanina da yaa umar! Yana sona sosae, nace "wane irin da sauqi kunje asibiti ne? Hafsatul kiram tace "A'ah nasha magunguna pa! Nace "maganar kawai, anashan magani ne ba bisa qa'ida ba? Bari in kirashi yanzunnan ya kaiki asibiti!

Tace "Aunty naaji sauqi pa, har wayar taa katse! Ta jingina da gado tana tunanin masifar daxai sauke mata inya dawo, lallai maxa halinsu saisu!

Umar ne zaune cikin motah da deezy, yana wasa da yatsun hannunta yana kallonta idanunshi cike da soyayya! Yace "ke kadai nakeso zumah, ya kamata ki yarda da hkan, kawai tana zaunene a gdana anma ke kadai nakeso" cike da damuwa tace "ko kanason hafsatul kiram ko bakason ta matarka ce! Tana zaunene a gdanka a matsayin matarka, niko pa? bzaka gane irin sonda nake maka bne zuma! Wlhy idan har ban aureka ba zan iya kashe kaina, bzan iya jurar rashinka ba!

Yace "kima daina tunanin hkan, Umar naki ne ke kadai, ni kaina bzan iya rayuwah babu ke ba, ke kadaice farin cikinah! Kuma kin kusan zama mallakina.

Kiran daya shgo wayarshi ne ya katseshi, ya dauka ya kara a kunne, tohn kawai yake cewa har ya gama wayar, ranshi yayi matuqar 6aci, watau yarinyar nan ta fara had'ashi da dangin mahaifiyarta ba?

Kaasa daurewa yayi, sallama sukai da deezy yaja motarshi da gudu ya nufi gidan saboda yanda yakejin zuciarshi!

Hafsatul kiram taa shrya tana kwance bakin gado tana jiran dawowarshi har niqab taa d'aura, Auntynta ta kira tace ta shrya anma duk da hka zuciarta fargaba take!

Lurv my princess Amrah😘

♥♥Rabiatu sk msh♥♥

[12:44PM, 4/19/2016] Rerbee'art sk msh: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄
                          🎄
                       🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
              🎄🎄🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                       🎄🎄
                          🎄
           NA
  Rabiatu sk msh

         2⃣6⃣

Da qarfi ya bud'e 'kofar dakin ya shgo kamar zai 'ballata, ta miqe tsaye tana kallonshi a tsorace yace "ita batasan ina da abnyi bne da zatace saina kaiki asibiti? Naa fada mata baa lokaci ne dani ba anma taa wani matsa saina kaiki asibiti!

Kanta na a 'kasa bata bari hawayen da suka tarar mata sun fito ba tace "kayi haquru batasan kana busy bne, anma idanka bani izini zanje da kaina! Nasan bka da lokaci nizan mata bayani bzatasan bka kaini bma! Shru yayi yana kallonta a sanyaye yace "nina hanaki fitane? Kije dk inda zaki!

Wuceshi tayi ta fita, tana tafiyarta har bakin titi daqyar tana had'a hanya ciwon kanta naa qaruwa! Tsayuwar motah taji a bayanta bata waiwaya ba!

Sai dai yasha gabnta da mota baice komi ba ya bud'e mata, sai da ta waiwaya ko ina taga ko ba ita ba, sannan ta bud'e motar ta shga cikin mamaki da tsoro ta maida kanta gefe yaja motar suka tafi!

Tsadadden asibiti ya kaita, yananan aka dubata aka basu result da magungunan da zata dingasha! Fuskarshi ba yabo ba fallasa ya maidata gida! Tace "ngde, ya kauda kai gefe baice mata komi ba!

Da tasha magungunan taa d'anji sauqi anma duk da hka jikinta ba qwari, ciwon zuciah ne akace yana so ya kamata!

Ranar ma barci ta wuni yi bata samu taayi komi ba, sai data farka taga takeaway yaa ajiye mata! Hawayene suka zubo mata da ita kanta batasan dalilinsu ba!

Kwana biyu tayi tana jinya sannan ta d'an samu sauqi, bai zamn gdan anma yana ajiye mata abnci shma bzai mata magana ba sai dai inta fito ta gani!

Taaci gaba da yi mishi girki kamar yanda ta saba da gyaren d'aki anma taa daina zamn jiran dawowarshi falo, sun daina had'uwa kamar matar kulle kullum tana cikin daki!

Rannan ya sameta d'akin zaune kan sallaya tana karatun Qur'ani kamar wanda aka turo yayi mata tsaye samn kai cikin hargowa yace "waike me kke nufi da zamn d'akinnan? Wani sabon salo ne kija ace ina muzguna miki ba?

Da sanyayyar muryarta tace "naa lura ganinah ne ka tsana a gdannan! Ina takura maka shyasa nake 'ko'korin daina nuna mka fuskata! Shru yayi tana kallonta, kafin ya juya ya tafi jikinshi ba qwari!

Lurv my princess Amrah😘

♥♥Rabiatu Sk Msh♥♥
[5:39PM, 4/19/2016] Rerbee'art sk msh: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄
                          🎄
                       🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
              🎄🎄🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                       🎄🎄
                          🎄
           NA
  Rabiatu sk msh

          2⃣7⃣

Washe gari ya dawo dga office mai gadi yaa bude mishi gate zai shgo da motar, Yace "Ranka shi dade dazu an aiko hajia bata lafiya! Umar ya kalleshi a firgice yace "momie bata lafiya? Meya sameta? Yace "wlhy bn sani ba anma hajia taa tafi, tace idan kazo a fada mka! Shru yayi kafin yace "shknan.

Fasa shga gidan yayi ya juya ya nufi hanyar gidan nasu zuciarshi cike da tunani kala-kala.

Yanayin parking ya bud'e motar ya fita cikin sauri ya qarasa falon momie, kwance ya hangota hafsatul kiram naa gefenta da towel a hannunta taa jiqashi da ruwan sanyi tana d'ora mata a goshi, sai sannu take mata fuskarta cike da damuwah kamar ciwon a jikinta yake!

Gani tayi momie na qoqarin tashi zaune, ta taimaka mata ta zaunar da ita sai sannu take mata, Yana tsaye batasan da zuwanshi bma sai kallonta yake ynda take kula da momie yaa kasa dauke kai!

Qarasawa yayi kusa da momie da sauri hafsatul kiram ta miqe ta bashi wuri ya zauna yace "ya jikin momie? Shne bza'a kirani in kaiki asibiti b? Tace "da sauqi ai damn zafin masassara ne, ynzu kam Alhmdlh jiki yaayi sauqi da taimakon hafsatul kiram tun dazu take nan tana kula dani!

Baice komi ba, don hafsatul kiram ma fita tayi ta basu wuri lokaci lokaci take shga ta dubo momie!

Basu bar gidan ba sai bayan isha'i, a motar Umar duk yaayi suku-suku dashi

Tare suka shga gdan bayan yaa gama parking, babu mai yima wani magana cikinsu ya nufi dakinshi, itama harta juya zata tafi nata kamar ance ta jiyo!

Maciji ta gani yaa tafi sululu inda Umar yake, da sauri taa qwala mishi kira "Yaa umar!!!! Ya juyo yana kallonta baima kula da macijin yaa kusa zuwa inda yake ba!

Lura da hkan da tayi ya sanyata rugawa da hanzarinta ta riqe kan macijin idanunta rufe ta murd'e kan, yakai mata saara, anma bata sakeshi ba saida kan ya fita taa fad'i 'kasa luuu, da sauri Umar ya riqeta ta fada jikinshi!!

Lurv my princess Amrah😘

♥♥Rabiatu sk msh♥♥

[11:20AM, 4/20/2016] Rerbee'art sk msh: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄
                          🎄
                       🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
              🎄🎄🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                       🎄🎄
                          🎄
           NA
  Rabiatu sk msh

          2⃣8⃣

A rud'e ya d'auketa ya fita da ita zai saka mota, mai gadi Ya taso yana cewa "lapia ranka shi dade? Cikin rud'ewa yake mishi bayani! Yace "bud'emin gate asibiti zamuje!

Mallam mai gadi yace "ranka shi dade ay sai dai ayi mata na hausa, anyi sa'a kuwa bni rabuwa da maganinshi bari in dauko, da hanzari yaje d'akinshi ya d'auko, Umar dk yaa rud'e sai jijjigata yake, jiqa maganin akai ya d'ura mata a baki ynda zai shga cikinta! Yana shafa mata ruwa a fuskarta!

Tana bud'e ido ta fara kwarara Amai baqiqirin a jikin umar dk taa 'bata mishi jiki, shikam sannu kawai yake mata taa kasa magana jikinta baa qwari dk yaayi laqwas kallansu kawai take tana lumshe idi daqyar saboda wahalan da tasha!

'Daukarta yayi ya kaita d'akinshi, ya kwantar da ita saman gado yaa kasa canza mata kaya ko hijabin yaa kasa cire mata, sai dai ya kunna mata A/C, toilet ya shga yayo wanka ya gyara kanshi!

'Kasa ya saukar da filo saitinta ya kwanta, baiyi wani barcin kirki ba hnkalinshi naa kanta, itakam barcinta takesha cike da gajia ga wahala kuma!

Ana kiran sallar Asuba ta bud'e idonta a hnkali, lokacin yaa fita masallaci bai tasheta ba, ta shga toilet tayo alwalla ta fito ta tada sallah bata koma d'akinta ba, hannunta naayi mata zogi sosae, daurewa kawai take

Gari har yaa fara haske ya shgo tana zaune saman sallaya taa gama azkar, riqe tana da hannunta sai cije baki take saboda azaba ya shgo, ta miqe da sauri zata bar d'akin, Yace "ina zakije? Tace "break fast zan had'a mka, gari harya fara haske!

Yace "da baki lafiyar? Tace "ay zai bari ne, ta wuceshi zata fita ya riqota ya maidata kan gado ta zauna, ya ciro maganin Aljihunshi ya fara shafa mata a hannunta Yace "mallam mai gadi yaace idan aka shafa miki insha Allah zai daina miki zafi!!

Batace mishi komi ba, kallonshi kawai take riqe da hannunta, cike da shaqi batasan ma sanda ya gama ba, shima tsayawa yayi yana kallonta da sauri ta sadda kai, ya dafa kafad'arta da duk hannunshi, Yace "Tabbas hafsatul kiram, momie taayi gsky! Bzan taba samun mata kamarki ba, ke mace ta gari ce, kowanne namiji zaiyi alfaharin samunki a matsayin mace, naa dad'e ina cutar dake, don Allah ki yafemun hafsatul kiram, bnda wani farin cikin daya wuce samunki a matsayin mace! Kin sadaukar da taki rayuwar saboda ki ceci tawa kawai! Dk da kinsan zaki cutu, don Allah ki yafemun!

Lurv my princess Amrah😘

♥♥Rabiatu sk msh♥♥
[1:01PM, 4/20/2016] Rerbee'art sk msh: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄
                          🎄
                       🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
              🎄🎄🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                       🎄🎄
                          🎄
           NA
  Rabiatu sk msh

          2⃣9⃣

Dago kanta tayi ba tare dasun had'a ido ba tace "Ay kai mijina ne yaa umar, tsare haqqoqinka, yi mka biyayya, dabin umarninka yaa zamemin dole, ka daina kunyata ni wurin neman yafiya a wurinah! Ni matarka ce!!

Tashi tayi ta fita, ta barshi zaune jikinshi duk yaayi sanyi da kalamnta, kaasa motsawa yayi maganganunta naayi mishi yaawo akai

'Dakinta ta wuce ta kwanta, sai kallon silin take tana juye juye, jinta take a wata duniyar daban, taa kasa gane farin ciki take kome? Yanayin data kaasa ganewa kenan!

Tana cikin tunanibya shgo da shirin tafiyarshi office, ya ajiye mata take away Ya duqa saitin fuskarta ta rufe ido, Yace "ba rakiya? Tace "Allah ya kiyaye hanya, ya dawo dkai lafiya! Bai samu fuskar qarayi mata magana ba dk kunyarta yakeji ma yaayi sukuku, Yace "idan kina buqatar wani abu kimin waya! Batace mishi komi ba harya tafi!

Da marece Umar ne da deezy zaune wurin wani shaqatawa! Yaayi shru yaa rasa ta inda zai fara mata, fuskarshi cike da damuwa yaa kasa bud'e baki ya mata magana! Tace "zumah kaa kurani kaayi shru, gashi da alamar damuwah a fuskarka, hafsatul kiram ce ta 'bata mka rai ko?
     Ya girgiza kai yace "tabbas inada damuwah! Anma b daga hafsatul kiram bane, tabbas na cika son kaina, naa damu da farin cikinah ne kawai bn damu da nata ba, deezy naa cutar da rayuwar hafsatul kiran da yawa! Anma yaa isa hka, babu wani mijin da ya isa ya bautar da matarshi, ya quntata mata ya cutar da ita kamar ynda nayi mata, inason matata hafsatul kiram, kiyi haquri da soyayyarmu! Miqewa tayi tsaye kamar wadda aka tsikara!

Tana nunashi da yatsa tace "meka daukeni ne Umar? Kaa maidani kamar wata qwallon da zaka buga duk sanda kakeso? Kaason irin sonda nake mka anma duk sanda na saki jiki muna soyayya saika barni? Yace "ki fahimceni deezy, hafsatul kiram matatah ce, nasan dole zakiji ciwo a zuciarki, wannan ciwon shi hafsatul kiram ta dade tanaji a zuciarta! Bxan iya ci gaba da aikata kuskure guda d'aya a rayuwatah ba! Inason hafsatul kiram.

Bai jira me zatace ba ya ra'bata gefenta ya wuce, tace "ka saurareni Umar, bzaka ta'ba rabuwa dani irin hka ba! Ko waiwayenta baiyi ba ya wuce yabar wurin!

Yana isa d'akin hafsatul kiram ya wuce tana gaban madubi, tsayawa yayi yana kallonta yaa kasa d'auke idonshi a kanta, ba qaramin kyau tai mishi ba, wannan ne rana ta farko daya fara ganinta babu hijabi, juyawa tayi suka had'a ido taga ita kawai yake kallo ko qiftawa ba yayi! Sai lokacin ta lura bata saka hijabi ba kunya dk ta lullu'beta ta jawo hijabinta ta saka!!

Lurv my princess Amrah

♥♥Rabiatu sk msh♥♥
[1:56PM, 4/20/2016] Rerbee'art sk msh: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄
                          🎄
                       🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
              🎄🎄🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                       🎄🎄
                          🎄
           NA
  Rabiatu sk msh

          3⃣0⃣

Sannan ya saki ajiyar zuciah ya qaraso inda take, tsayawa tayi tana kallonshi ba tare dasun had'a ido ba, hannu yasa ya cire mata hijabin, ta sadda kanta kunya dk taa lullu'beta.

Hannu ya sanya ya dago da fuskarta yace "nafison ganinka a haka hafsatul kiram, kinyi matu'kar yin kyau! Tayi murmushi har lokacin idanunta a 'kasa, ya zaro takardu a cikin aljihunshi ya miqa mata, tace "na menene? Yace "ki gani da kanki!

Takardun asibiti ne, Awon H.I.V, duk babu ta dago ta kalleshi Yace "zan miki alqawari tsakaninah dake, daga Yau babuni babu wata mace, babu ni babu shan duk wani abin dazai sakani maye, ki yarda dani hafsatul kiram Inasonki sosae, zan sanyaki farin ciki har 'karshen rayuwatah!

Rumtse ido tayi dadi naa ratsa mata zuciah, ji take kamar taafi kowa farin ciki da dace, lallai maha'kurci mawadaci, 'bude baki tayi zatayi magana taama rasa me zata fad'a, murmushi kawai take a fuskarta!

Wayarshi ce tayi ringing, ya ciro ya duba sunan deezy a screen d'in, hafsatul kiram ya kalla yaga bashi take kallo ba ya maida wayar silent ya ajiye, wani kiranne ya 'kara shgowa bai d'auka ba harta qara katsewa, kusan sau biyar da yaga bata da niyyar daina kira ya kalli hafsatul kiram Yace "ina zuwa, da murmushi a fuskarta ta d'aga mishi kai ya fita falo ya d'aga wayar!

Muryarta da alamar kuka take magana "zumah don Allah karka gujemun, bzan iya rayuwarda babu kai a tare dani ba, inasonka karka cutar dani ta wannan hanyar! Yace "kiyi haquri deezy hafsatul kiram ita kad'aice matata, da ita kad'ai zan kasance har abada! Tace "kana nufin kaa daina sona?? Bai bata amsa ba ya kashe wayar! Ya juya ya koma wurin hafsatul kiram!

Wurgi tayi da wayar ta tarwatse zuciyarta kamarta fashe duk abnda ke kusa da ita saida tayi wurgi dashi, ta fad'a saman kujera ta saki wani irin kuka!

Lurv my princess Amrah😘

♥♥Rabiatu sk msh♥♥

[6:39PM, 4/21/2016] Rerbee'art: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄
                          🎄
                       🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
              🎄🎄🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                       🎄🎄
                          🎄
           NA
  Rabiatu sk msh

          3⃣1⃣

Hafsatul kiram taa kasa sakin jiki da Umar, shi kuma sai ji yake da ita yana bata kulawa, idan ya shgo bai bari ta zauna nesa dashi, data tashi zai bita inda zai dinga kallonta! Ko kitchen zata shga suna tare!

Ranar monday tana kitchen tana hada break fast sai abnda bata sanyashi ba yakeyi, mai ne ya fallatsar mata a hannu da sauri ta janye tana yarfe hannun, ya qaraso da sauri hankalinshi dk ya tashi, bata kulashi ba ta juya taci gaba! Baiga fuskar ta'ba hannun nata ba, cikin muryar damuwa yace "qonewa kikai? A'ah kawai tace mishi taci gaba da abnda take, damn mgnr knan tsakaninta dashi ko kad'an bata sakar mishi fuska!

Harta gama duk don son ta mishi magana yace "ki shrya in ajiyeki gidan momie! Da murnarta tace "dgsk?? Yace "da wasa nake! 'Bata rai tayi taci gaba da zuba mishi abnci, Yace "kinga ni dgsk nake, ki shrya dana gama saka kaya zamu tafi! Tohm kawai tace mishi!!

Tare suka shga gdan sai qoqarin jerawa yake da ita, tana shga falon da sauri ya kamo hannunta ya riqe, juyowa tayi tana kallonshi cikin tuhuma taa d'aure fuska, ya kashe mata ido ya jawo hannunta saitin bakinshi yana shrin mata kiss ta zaro ido tace "Yaa umar! Tana qoqarin janyewa, momie ce tayi gyaran murya dk suka waiwaya!

Har lokacin hannunta na sa'kale a cikin nashi sai qoqarin cire nata take anma yaqi saki duk kunya taa kamata! Momie sai murmushin dad'i take tace "Ynzu kam naa gani da idonah kaa canja, da sauri Yace "naa canja sosae mna momie! Tace cikin zolaya "anma hafsatul kiram ce sanadi! Itace ta canjaka da kyawawan halayenta!

Murmushi kawai yake bakinshi yaaqi rufuwa yace "tabbas momie hafsatul kiram ce ta canjani, naa canja sosae kuma ina sonta sosae, Naayi miki alqawarin zan riqeta amanah, zan sanyata farin ciki har qarshen rayuwatah! Bazan ta'ba bari tayi damuwah ba, momie cike dajin dad'i tace "gsky naji dad'i sosae, Allah yayi muku albarka! Yace "Ameen momie, na tafi office saina dawo, ya juya yana kallon hafsatul kiram ta sadda kai cikin jin kunya! Addu'a ta mishi sannan ya juya ya tafi!

Yana zama a office d'inshi sai gata ta shgo duk taayi kalar tausayi ta nemi kujera ta zauna, tamke fuska yayi yace "deezy sau nawa zan fad'a miki ki daina shga harkata? Naa fad'a miki ynzu babu wata alaqa tsakanina dake, soyayyarmu taaxo qarshe!

Idanunta jajir take kallonshi cikin 'bacin rai, a hnkali kamar mai rowar magana tace "kaa tuna naa fad'a mka mutuwa zanyi idan har bn sameka ba?? Idan har soyayyarmu taazo qarshe, Rayuwatah ma taaxo qarshe, ta zaaro wuqa ta saita a maqoshinta tana kallonshi!!

Lurv my princess Amrah😘

♥♥Rabiatu sk msh♥♥
[7:26PM, 4/21/2016] Rerbee'art: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄
                          🎄
                       🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
              🎄🎄🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                       🎄🎄
                          🎄
           NA
  Rabiatu sk msh

        3⃣2⃣

Cikin rud'ewa yake kallonta maganarshi na sarqewa yace "me kke shrinyi deezy?? Tace "naasan kana sona Zuma, don Allah ka fad'amin kace kana sonah, idan har na qirga uku baka fad'a ba zan kashe kaina ne!
Yace "haba deezy ki daina mna wannan ba wasa bne, ya miqe ya nufeta yana qoqarin amshe wayar! Ita tashi tsaye tayi ta fara jaa da baya tana cewa "ba wasa nake ba, wlhy zan kashe kainane a gabanka! Kawai ka fada, kace Ina sonki deezy, girgiza kai yayi zaiyi magana kafin yace wani abu taa yanka hannunta!

Jini keta zuba a rud'e ya rumtse idonshi yace "ina sonki deezy! Da gudu ta rungumeshi cikin farin ciki tana share hawaye, tace "ni daman naa sani, naasan kana sonah Umar, hafsatul kiram ce takeso ta rabamu, bxan ta'ba bari b, bzan ta'ba bari ta rabamu ba! Ta kwantar da kanta jikinshi tana ta sambatu!

Shikam tsayawa yayi kamar wanda aka dasa, yaa kasayin komi, ya rasa me zaiyi!!

Takarda ta d'auko da biro cikin takardunshi ta miqa mishi tace "ka rubuta mata takardarta ynzu hafsatul kiram, don Allah umar karka bari ta qara rabamu! Cikin mamaki take kallonta yace "kinyi haukane deezy? Tace "indai a kanka ne ka kirani da koma miye! Idan bzaka rubuta ba nizan rubuta kakai mata, harta fara rubutun ya fizge takardar ya kekketa yace "baki da hnkali deezy, taya kke tunanin zan iya sakin deezy? Ina sonta bzan taba rabuwa da ita ba!

Fara jaa tayi da baya hawaye naa zuba a idonta, bata ce mishi komi ba ta juya ta fita idanunta naa zubar da hawaye

Dafe kanshi yayi cikin tashin hnkali ya nemi wuri ya zauna, tunani ne ke mishi yawo a qwalwa! Yaa rasa samun mafita, ji yake kamar ya rufe ido ya bud'e yaga mafarki ne, bai ta'ba shga tashin hnkali irin hka ba!

Yaa tashi dga aiki yana hanyar zuwa gdan momie wayarshi tayi qara, numbr deezy ce kamar bzai d'auka ba kuma saiya d'aga, shru yayi daga can aks fara magana Muryar namiji ne Yace "daga asibiti ne an kawo mna patient mai wannan numbr taayi accident, da sauri ya taka burki yace "wane asibitin? Ana fad'a mishi da sauri ya juya motar ya nufi asibitin!

'Dakin da aka fad'a mishi ya shga tana kwance idanunta a rufe, a goshinta da hannu ne kawai taji ciwo sai dai har lokacin bata farka ba!

Tsayawa yayi yana qare mata kallo, tunaninshi dk yaa tsaya jinshi yake kamar bashi ba, shya biya duk kudaden da ake buqatah, likitan yace zasu iya tafiya data farka indai akaga babu wata matsala!

Har magriba bata farka ba saida ya fita sallah ta fara bud'e ido a hankali tana qare ma d'akin kallo

Hafsatul kiram ce taji shru bai dawo ba, kaasa daurewa tayi ta d'auki wayarta ta fara buga mishi taji ko lafiya, wayar naa kusa da deezy ta fara qara, dubawa tayi taga wayar umar ta miqa hannu ta d'auka, sunan hafsatul kiram ta gani a jiki ta d'auka tana murmushin mugunta!!

Hafsatul kiram tace "lafiya Yaa umar? Ina ka tsaya tun d'azu?  Deezy tace "lafiya lau yake hafsatul kiram gashinan tare dani, naasan abnda zaki tambaya kenan!

Lurv my princess Amrah😘

♥♥Rabiatu sk msh♥♥

[6:17PM, 4/23/2016] Rerbee'art: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄
                          🎄
                       🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
              🎄🎄🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                       🎄🎄
                          🎄
           NA
  Rabiatu sk msh

           3⃣3⃣

Hankalin hafsatul kiram ya tashi, jikinta har kyarma yake wayar ma fara gagararta riqewa tayi

Deexy taci gaba da cewa "nina rasa irin wannan qwaqwa taaki, zumanah Yaace baisonki yaa fad'a miki yaafi a qirga anma kin kaasa fita rayuwarshi, don tsabar rashin zucia dga Yaa fara nuna miki kulawa shknan kin saki jiki babu ko d'an jan ajinnan, ay nikam hafsatul kiram rakiyarmu kawai kikazo!

Kuka ne yaso qwacema hafsatul kiram, da sauri ta fara kokawar korar hawayen dakeson zubo mata cikin qarfin hali da jarumta tace "ay wanda yasan darajar aure shi ke yima mijinshi biyayya, bzaki ta'ba ganewa ba tunda baayi kke ba, bzan ta'ba rabuwa da Yaa umar ba matuqar igiyoyin aurenshi na akaina wnda naasan bzai ta'ba rabuwa dashi ba, soyayyar gsky dabn take deezy kuma naa tabbatar da Yaa umar nayimun ita to miye amfanin in tsaya ja mishi rai bayan nasan kuma zan haqura? Naa yrda dason da Yaa umar kemin, bzan ta'ba zarginshi ba deezy ki canza wani salon!

Cikin hargagi deezy ke mgn don bata ta'ba tunanin hafsatul kiram nada baki haka ba tace "ni kke fad'a mka haka? Kin mnta da umar naawa ne? Dawo dake ba'a bakin komi ba wurin ba wani aiki bne a wurina! Sunana deezy, idan har bn rabaki da zumanah ba ba sunana deezy ba!!

Hafsatul kiram tace "ki canza suna deezy, don Umar bana mata mararsa kamunkai bne irinki, cika bakinki bzai ta'ba tasiri a wurina ba! Ta kashe wayanta bata jira me zata ce ba!

Kifa kai tayi saman gwiwa ta fara kuka tana tunanin to meyakai Umar wurin deezy? Har isha'i bai nemeta ba baizo sun tafi ba! Batason ta bama zuciarta dalilin da zataji haushinshi kota zargeshi, shya sanyata share hawaye taci gaba da quncin rai kawai, koda momie ta tambyeta sai tace yana hanya!!

Sai da ya ajiye deezy gida don daman ba wani ciwo taji ba, sannan ya wuce gidan momie, koda momie ta tambyeshi inda ya tsaya cewa yayi wani abu mai mahimmanci ne ya tsaidashi!!

A hanya suna tafiya da hafsatul kiram zasu koma gida, duk haqurinta kaasa daurewa tayi tace "Yaa Umar dazun ina kaje dga wurin aiki? Duk yaa rikice zufa naa feso mishi daqyar ya iya cewa "ina taashi dga aiki aka kirani, kira mai mahimmanci shyasa na tafi! Daga kai kawai tayi Yace "wani abu? Tace "A'ah momie ce kawai ke cigiyarka!

Ajiyar zuciyah kawai ya sauke don ko kad'an ynzu baiso yayi abnda zai sosa zuciyar hafsatul kiram! Har sukaje gida dawo dai dai ba!

Lurv my princess Amrah😘

♥♥Rabiatu sk msh♥♥

[6:56PM, 4/23/2016] Rerbee'art: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄
                          🎄
                       🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
              🎄🎄🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                       🎄🎄
                          🎄
           NA
  Rabiatu sk msh

          3⃣4⃣

'Dakinta ta wuce shima ya wuce naashi don sunci abnci gdan momie gashi a gajiye take, tana shga shrin kwanciya tayi ta kwanta sai gashi shima yaa shgo!

Sauri tayi ta rufe ido kamar mai barci saboda kunyar kayan data saka dk sun bayyanar da surar jikinta, tsayawa yayi yana qare mata kallo wani irin Abu na fizgarshi daya kaasa daurewa sai da ya qarasa inda take ya tsugunna dai dai saitin fuskarta, rufe ido tayi a hankali yake matsar da fuskarshi saitin tata ya had'a bakinshi da nata! Rumtse ido tayi wani abu har cikin tsakiyar kanta! A hankali ya furta "Ina sonki hafsatul kiram, inason kyawawan halayenki, I've Fallen In Love With You And I'll Never Let You Go. I Love You More Than Anyone, I Just Had To Let You Know. And If You Ever Wonder Why, I Don't Know What I'll Say, But I'll Never Stop Loving You, Each And Every Day.!!

Hawayene taji suna qoqarin zubo mata da sauri ta juya ta gyara kwanciarta, hawaye naaci gaba da zubo mata yace "kada ki ta'ba juyamin baya hafsatul kiram, don Allah ki kasance tare dani!! Hawayen farin ciki ne kawai ke zubar matah, harya gama sambatunshi ya tafi dakinshi!

Ranar kwanan farin ciki hafsatul kiram tayi data tashi sallar tsakar dare taa dad'e tana kwarara addu'ar godia ga ubangiji!

Da safe kaasa daina farin ciki tayi, komai cikin annashuwa takeyi, tunda wuri ta gama had'a mishi break fast, ta shrya cikin riga da siket na material taayi kyau sosae!

Tana zuba ma Umar abnci kaasa daurewa yayi da kallonta ya kamo tattausan hannunta yana murzawa! Ta d'an marairaice fuska tace "yaa umar abncin pa?? Yace "kiyi aiki da hannu d'aya! Batace komi ba dk taa takura taci gaba da zuba mishi! Tana gamawa ya kamo d'ayan ma ya zaunar da ita yana kallonta!

Da sauri ta sadda kai Yace "don Allah ki daure ki bni damar da zaki kalli cikin idona koda sau d'ayane hafsatul kiram! Tsananin sonda nake miki bnda damar dazan iya bayyana miki, anma zaki iya gani a idanuwa nah! Ina sonki sosae hafsatul kiram!

Murmushi tayi tace "ngde! Har lokacin taa kasa dagowa su had'a ido! Yace "ki fadamin hafsatul kiram, kema kice kina sonah!  Taafi minti biyu kafin ta iya bud'e ba daqyar ta saka hannu ta rufe fuskarta tace "ina sonka Yaa umar! Da sauri ta gudu d'akinta, harya tafi basuyi sallama ba

Lurv my princess Amrah😘

♥♥Rabiatu sk msh♥♥
[7:28PM, 4/23/2016] Rerbee'art: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄
                          🎄
                       🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
              🎄🎄🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                       🎄🎄
                          🎄
           NA
  Rabiatu sk msh

         3⃣5⃣

Yana zuwa office wurin parking ya iske deezy tsaye tana jiran zuwanshi, da sauri ta qaraso yana bud'e motah yayi kamar bai ganta ba zai tafi tasha gabanshi tace "wai meyasa kakemin hka zumah? Wulaqancin yaa fara yawa! Don Allah ka gane irin sonda nake mka, bzan iya rasaka b!

Taa'be baki yayi yace "kin riga kin rasani deezy, bzaki ta'ba samu nah ba, zakisha mamaki na idan har baki rabu dani ba! Jiya kin saka naayi ma hafsatul kiram 'karya! Bzan ta'ba yafema kaina ba idan harna qara cin amanarta! Ki fita hanyata tun wuri! Ya wuce ta zai tafi!

Da qarfi tace "hka ka fad'a?? Kaa gama yanke hukuncinka ba, inaso ka sani idan har bn sameka ba bzan bari ta'ba bari wata ta sameka ba!!!

'Daga kafad'a yayi yana nata kallon matsalarki ce yace "ban damu ba, kiyi duk abnda zakiyi, ya juya ya barta wurin a tsaye tana huci ta shga motarta ta kwantar da kanta saman sitiyari zuciarta naa tafasa, wani tunani ne yazo mata a fili tace "tabbas qara in d'auka mataki da wuri! Tajaa motarta tabar wurin!

Hafsatul kiram naa zaune falo tana duba littafin hadith, suka bud'e 'kofar d'akin da qarfi suka shgo! Su biyu ne maza gardawan Qatti ko wanne da mugun makami a hannunshi!

Da sauri ta miqe tana kallonsu a tsorace dk taa rikice maganarta na hard'ewa tace "waya shgo daku gidana har cikin d'akina?

Deezy dake shgowa dga baya tace "nice nan na shgo dasu! Kinyi mamaki ba? Meya sanya? Miye dalilina? Nasan tambyar da zakimun kenan duk da kinsan amsoshnsu!

Naa lura ke kad'aice matsalarmu nida zuma, idan har yana ganinki bzai qara kulani b, bzan ta'ba yrda kiyi nasara a kaina ba, bzan bari ki rabani da zumanah ba, tabbas yau zan kawo qarshenki!

Ta maida 'kofar dakin ta rufe da makulli tace "yau zan kawo qarshen matsalata da zumah! Tana matsowa inda hafsatul kiram take.

Hafsatul kiram duk taa rikice taa rud'e sai jaa da baya take, juyawa tayi da niyyar rugawa deezy ta sanya mata qafa ta fad'i 'kasa ta saki qarar azaba!

Ta kalli qattin da tazo dasu tace "kuyi sauri mubar gidannan, minti biyu karta qara shan numfashin duniyarnan!!

Lurv my princess Amrah😘

♥♥Rabiatu sk msh♥♥

[4/28, 3:50 PM] ✍🏻rerbee'art sk msh: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄
                          🎄
                       🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
              🎄🎄🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                       🎄🎄
                          🎄
           NA
  Rabiatu sk msh

           3⃣6⃣

Rud'ewa hafsatul kiram ta qarayi jin furucin deexy ga wani irin buguwa da qugunta yayi sanadiyyar fad'uwan da tayi, Addu'ah kawai take a zuciarta dk tunaninta yaa kwance!

Umar naa office hkanan yaji gabanshi naa fad'uwa yaa rasa sukuni dk yaa kasa wani aiki ga takardu gabanshi! Tunanin hafsatul kiram kawai yake, wayarshi ya d'auko yace bari ya kirata dai yaji ynda take ko hnkalinshi yaa kwanta!!

Wani daga cikin qattin ne ya matso inda hafsatul kiram take fuskarnan taashi kallonta ma qara ma hafsatul kiram tashin hnkali yake, taa kasa furta komi saidai hawayen da take tana girgiza kai kamar tababba, deezy kam naa gefe sai murmushi take cikin nishadi

Wayar hafsatul kiram ce tayi qara da sauri ta jaa jiki wurin kujerar da wayar take ta miqa hannu ta d'auka zatasa a kunne, su duka qattin suka kece da dariya sannan wani yakai mata sara a hannun da wayar take, da sauri ta saki wayar ta kauce anma duk da hka sai da ya sameta jini ya fara tsiyaya!

Wata razananniyar qara ta saki tana kallon jinin dake zuba tana hawaye cikin kakkausar murya yace "ke har kina da damar d'aukar waya a gabnmu? Lallai jinkirin da mukai wurin kasheki ne yasa kka fara samun qarfin gwiwa! Ynzu zamu gama dake, yakai mata wani uban naushi a hanci, ta fasa uwar qara cikin azaba, jinta take kamar ba'a duniya ba, kanta naa juya mata kamarta cire fuskar ta huta!!

Akan kunne Umar sun mnta basu kashe wayar ba yayi wata irin zabura cikin rud'ewa bai tsaya wani tunani ba ya nufi hanyar fita, Abokinshi suka hadu kofar shgowa yana kallonshi dk yaa fita hayyacinshi yace "lpyrka kuwa Umar? Yace "qlw nake Ahmad don Allah kazomin da en sanda ynzu gidana! Ahmad yana zaro ido yace "lpy kuwa? Meke faruwa? Umar yace "kai dai kayi abnda nace plz, ya tafi zai fita idonshi rufe ya kusan  kaima bango karo!

Da sauri Ahmad yace mishi "gaa 'kofarnan, cikin rudewa Yace "na sani juyawa zanyi! Ya qara dosar wani bango cikin mamaki Ahmad yace "anya kuwa kana iya zuwa gdannan? Ni kaqi fad'amun abnda ya faru! Yace "zan iya mana jikinshi baa qwari ya fita wajen motarshi!

Ikon Allah ne kawai ya kaishi gidan saboda wani irin gudu da yake shararawa gashi dk a rude yake tafiya kawai yake, mai gadi ya taso ya bud'e mishi yana ganin yanda Umar ya shgo da motar yasa lallai babu lpy donshi baimasan da zuwansu deezy ba!

Lurv my princess Amrah😘

❤Rabiatu sk msh❤
[4/28, 6:54 PM] ✍🏻rerbee'art sk msh: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄
                          🎄
                       🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
              🎄🎄🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                       🎄🎄
                          🎄
           NA
  Rabiatu sk msh

          3⃣7⃣

Da gudu ya qarasa cikin gidan ya banka 'kofar falon da sauri ya jita a rufe, makullanshi ya jawo cikin hannunshi naa kyarma ya 'bude ya banka ya shga yana maida numfashi.

Su deezy dk sukayi cirko cirko suna kallonshi, dk taa rud'e tashin hnkali bayyane a fuskarta! Wata irin zuciyah ce tazo mishi dai dai lokacin 'yan sandan sun qaraso! Cikin zafin nama ya qarasa inda take ya cakumi wuyanta ya fara kai mata bugu, idanunta dk sun firfito cikin tsoro, ihu kawai take daqyar en sandan suka qwaceta dk taaji jiki, qattinma suna qoqarin guduwa en sanda suka cafkesu! kamar wani zaki ya koma ana janyeshi Yana shaqota Ahmad cikin d'aga murya yace "dukanta zaka tsayayi kota lafiyar matarka? Sannan ya saketa hnkinshi ya fara dawo mishi da sauri ya qarasa inda hafsat take jini naa zubar mata ta ko ina

Da sauri ya sungumeta hawaye naa zuba a idonshi ya nufi hanyar fita, ya sakarma deezy wani mugun kallo dake numfashi daqyar idonta daya jini yaa kwanta, ya kalli en sandan muryarshi cikin rauni da ban tausayRabiatu. kaasa fita tayi mgnr yana kallon hafsatul kiram da batasan inda kanta yake ba!

Ahmad ne ya motar zuwa asibiti ganin halinda Umar yake, a motarma ya kafa mata idanu ko qiftawa bayayi, ji yake kamar idan ya dauke idonshi akanta zata daina numfashi, hawayenma sun tsaya mishi sai dai wani abu da yakeji a zuciyarshi

Suna isa asibitin da sauri likitoci suka amsheta aka shga da ita emergency! Umar kaasa zama yayi dk yanda Ahmad ke bashi baki baimasan yanayi ba, kaasa motsawa yayi yaa kafe idanunshi wuri daya! Ahmad yace "ka daure ko kukan kayi zai rage mka damuwa, anma ina ganinka cikin halinnan nima bzan samu nutsuwar zuciyah ba, namiji kake pa! Hafsatul kiram addu'arka kawai take buqata!

Kaasa cema Ahmad komi yayi tunanin yanayin da yaga hafsatul kiram yayi yake, ko ina zubda jini take! Ta hanci da baki ga rauni a hannunta, likita ne ya fito da sauri Ahmad ya qarasa inda yake! Shikam Umar ko motsawa ma baiyi ba kallon likitan kawai yake!

Likitan Yace "tana buqatar jini ne cikin gaggawa, saboda taa zubda jini da yawa! Jikin Umar babu qwari yaje aka aunashi, jininsu yaazo dai dai cikin sa'a, har lokacin ko yaayi magana bata fita dk yaa fita hayyacinshi!  Shima gado aka bashi saboda yanda yanayin jikinshi...

Kuyi haquri da wannan plz🙈😉
Ina godia sosae ga masoyan hafsatul kiram, ngde sosae da kulawa...lov uh all😍

Lurv my princess Amrah

❤❤Rabiatu sk msh❤❤

[5/1, 10:54 AM] ✍🏻rerbee'art sk msh: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄
                          🎄
                       🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
              🎄🎄🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                       🎄🎄
                          🎄
           NA
  Rabiatu sk msh

         3⃣8⃣

Momy tayi tambaya meya faru dasu, a lokacin umar yana kwance bazai iya mata bayaniba,
   Bayan awa shida umar yafarka, kuma yasoma samun sauki, zafin da zuciyarsa takeyi ya rage sosai,
   Bayan ya farfado momy take tambayarsa meya faru dasu,
   Nan ya kwashe komai yagaya mata,
  Momy tace "wannan wace irin maccice, saikace batada imani, Allah yakiyaye gaba"
   Umar yace ameen,
 
Hafsatul kiram shiru shiru kakeji bata farkaba, harkusan dare, nan kuma hankalin momy dana umar yakara tashi, gashi gorar jinin da aka kara mata harta kare, amma hafsatul kiram shiru,
 
  Momy da umar suna zaune a gefen gadon hafsatul kiram misalim karfe goma nadare,
   A firgice hafsatul kiram ta sandara ihu, "wayyoo zasu kasheni, ya umar kacceceni" ta tashi da karfi,

Momy ta riko ta tana kuce kuce,  momy tace " ke hafsat momy cefa, kibude idonki kiganni"

A hankali hafsatul kiram ta bude idonta, suka hada ido da momy nan tafashe da kuka, ta rungume momy,

  Momy ta kankameta tana shafar bayanta "kiyi shiru kidaina kuka, insha Allah komai yazo karshe, kinji"
 
Hafsatul kiram tana shanshekar kuka ta share hawayenta, tafito daga jikin momy, momy tace kikoma kangado ki kwanta,

   Momy ta rika hannunta, kafin sukara bakin gado, taji kanta na sarawa, kamar zai fita, wani irin zafi takeji,
  Jiri yafara dibarta, tana hannun momy ta sulale ta fadi kasa,

   Tashin hankali nagano karara a fuskar umar, momy tayi sauri rikota tana jinjigata amma ina ta suma, a gigice momy tacewa umar "jeka kirawo likita"
  Umar yafi da gudu yaje yakira likita,
   Likita yazo yana dundubata yaga komai da sukayi mata normal, bawata matsala,
  Ya juyo ya kalli umar yace " batada wata matsala kawai shock ne ya dibeta amma ba wata matsala a cikin aikin da mukayi mata, likitan yadan dakatar da maganar sa, a lokacin yadaura hannunsa a kanta ya bude idonta daya, sannan yasake dora hannunsa a tsakanin wuyanta da kirjinta, sannan yaci gaba dacewa "karku damu bawata matsala insha Allah zuwa ajima zata farka, kufita waje kubata lokaci yanzu tana bukatar hutu"

  Jikinsu ba wani kwari suka tashi suka fita tare da likita,

Acen kuwa gefen deezy, a ranar sunsha dukan bala i a gurin yan sanda, saida sukayi musu likis, suka galabaita sannan suka daina dukansu,
   Da Kuma  zancen gobe za'a makasu a gaban kuliya wato kotu,
   ( su deezy ansha wuya 😂😛)..

Lurv my princess Amrah😘

❤❤Rabiatu sk msh❤❤

[5/1, 10:54 AM] ✍🏻rerbee'art sk msh: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄
                          🎄
                       🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
              🎄🎄🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                       🎄🎄
                          🎄
           NA
  Rabiatu sk msh

             3⃣9⃣

Washe gari,

Hafsatul kiram tafarka, cikin kwanciyar hankali, umar yaje gida yakawo musu kayan break
  Momy ta hada mata tea, mai kwairi tarika bata abaki, aka samu tadan sha, daga nan kuma takoma bacci,

  9:00am umar yakoma gida yayi wanka, sannan yadawo asibiti yasanar da momy cewa zaije koto,
  Momy tace Allah yabada saa,
  Umar yace "ameen, saina dawo, harya yabi hanya saikuma yadawo yace "inda wani abu da kuke bukata sai akirani asanar dani "
   Momy tace "toh,"
Tsaye yayi yana kallon hafsatul kiram, wani mugun tausayinta yakeji,
  Cen dai yajuyo ya wuce koto,

Koto tacika makil,
  Deezy da sauran kattinta  duk suna cikin kuliya,
  Lauyan gwaunati yatashi yana bayani sosai daga karshe yakare da cewa "wannan shari ar bata bukatar jan dogon lokaci, domin wadanda ake kara sun amsa laifinsu na yunkurin kashe wata, saboda haka ina rokon wannan koton datayi gaggawar yankewa wadan nan mugayen mutane hukunci, lauyan yadan rusuna kafin yace "nagode ya mai girma mai sharia, "yana gama fadan haka yakoma yazauna,

  Alkali yadan tsaya yana yan rubuce rubuce, kafin yadago kansa yace " abisa hujjoji da kuma kwararan dalilan da lauyan gwaunati yabayar, koto ta yankewa wadan nan mutane hukuncin zaman gidan yari shekara ukku, tare da horo mai tsanani, sannan kuma babu beli"

  Deezy ta kwalla ihu a cikin koton, tadafe kai tana kuka, cike da nadama, tayi matukar danasanin abinda ta aikata,

   Nan alkali ya daki tebur nan kaji koton tadau sautin "kotttt" kowa yamike tsaye saida alkali yafita sannan kowa yafiya,

aka ja su deezy aka wuce dasu gidan yari,

   Umar kuwa yayi godiya ga lauyan gwaunati sannan yadan ciro wasu yan kudade yabashi,  sannan yajanyo motarsa yadawo asibiti,

   Hafsatul kiram na farke yashigo dakin,
  Sukayi ido hudu, yasakar mata murmushi kafin yakarasa gurinta yace "ya jikin" tace "dasauki" yace "Allah yakara sauki " tace "ameen "

Satinsu daya a asibiti, hafsatul kiram tasamu kulawa sosai a gurin umar, duk abinda takeso siya ke mata, ita kanta mamaki take yadda taga umar yanuna damuwarsa sosai akanta,

saida hafsatul kiram taji sauki sosai sannan aka sallamesu,  suka dawo gida ..

Lurv my princess Amrah

❤❤Rabiatu sk msh❤❤

[5/2, 10:29 AM] ✍🏻rerbee'art sk msh: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄
                          🎄
                       🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
              🎄🎄🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                       🎄🎄
                          🎄
           NA
  Rabiatu sk msh

           4⃣0⃣

Gidan momie suka wuce, koda sukaje kowah ji yake da hafsatul kiram, duk da taaji sauqi sosae anma momie cewa tayi ta kwanta ta huta tunda jikin nata bai ida qwari ba!

Sai da dare yayi Umar yaji shru shru momie batace suzo su tafi gda ba, sai kame kame yake anma ta shareshi sai da yaga wuri yaa qure ne ya shga dakinta taa tsare hafsatul kiram tana cin abnci ya shgo!

Ta dago ta kalleshi tace "ashe bka tafi ba? Har ina cewa kaa tafi ko bankwana babu! Da sauri ya dago kai dk yaa 'bata fuska yace "bn tafi b Momie ita nake jita, tace "itawa? Ya saci kallon hafsatul kiram data sadda kai tana wasa da yatsunta yace "nidai momie kin gane pa, cikin shagwaba har lokacin bai saki fuska ba!

Kanne dariarta tayi ba tare data kalleshi ba tace "ba ynzu ba saita samu sauqi sosae don bzan bka ita a hka ba! Yace "taa samu sauqi pa momie kuma nima zan iya kulawa da ita! Tace "ba ynzu bpa nace!!

Juyawa yayi sumi sumi yabar dakin cike dajin haushi, kaasa tafiya yayi yabar gidan nan ya zauna falo yanata saqe saqe yake! Ga wata irin soyayyar hafsatul kiram da take fizgarshi, wani irin so yake mata da ko kadan baison ta mishi nisa ga tausayinta da yake lullube dashi!

Momie ce ta fito lokacin dare ya fara nisa, can ta hangoshi kwance saman doguwar kujera ya daga kanshi sama, da mamaki take kallonshi tace "har ynxu kananan knan? Baice komi ba sai dai ya tashi zaune, tace "idan ma nan zka kwana ne ay kaasan inda dakinka yake, taashi ka tafi tana nuna mishi hanya!

Miqewa yayi saida taga ya tafi sannan ta tafi dakinta harta shga ta dawo tana leqenshi, gani tayi yaa nufi dakin hafsatul kiram da sauri ta fito tana daga murya tace "ina kuma zkaje nan?? Sosa qeya yayi yace "momie bn mata sai da safe ba! Tace "taayi brci, zoka tafi bzaka kwanarmin anan bama!

Juyawa yayi ya fice dga falon duk baijin dad'in zuciyarshi yaaso ya tafi da hafsatul kiram.

Ranar kwana yayi juyi saman gado daya juya fuskar hafsatul kiram yake gani, qagara yayi gari ya waye yaje ya gano hafsatul kiram..

Lurv my princess Amrah😘

❤❤Rabiatu sk msh❤❤
[5/2, 12:39 PM] ✍🏻rerbee'art sk msh: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄
                          🎄
                       🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
              🎄🎄🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                       🎄🎄
                          🎄
           NA
  Rabiatu sk msh

          4⃣1⃣

Washe gari tunda safe umar wanka kawai yayi ya shrya cikin sauri ya nufi gidan momie

Hafsatul kiram ma farkawarta kenan ta shga wanka taa fito daure da towel ganin safiya ce batayi tunanin wani zai shgo ba, sai da tayi tsakiyar bedroom din ta hangoshi kwance saman gado ya tsura mata ido, da sauri ta zaro ido jikinta har ya fara kyarma taa rasa ynda zatayi, kunyar kanta takeji sosae

Da gudu ta juya da nufin komawa toilet, ya taso cikin zafin nama yasha gabanta yana riqe da hannunta, Yace "ina zaki koma ne? Shru tayi kanta a qasa kamar qasa ta tsage ta samu wurin boyewa saboda tsananin kunya! Ya dago kanta suka had'a ido da sauri ta rumtse idanunta ya saki murmushi yace "kinajin kunyar mijinki ko?

Batace komi ba don ko motsi taa kasa, shi kuma kallonta kawai yake wata irin sha'awarta naa fizgarshi, sai kallon bakinta yake dake matuqar burgeshi! Idonta rufe sai dai taji bakinshi cikin nata ta d'an zabura anma ta kasa bud'e idonta, cikin qwarewa yake kissn dinta dk jikinta yayi sanyi a hka har tsayuwar ta fara gagararta!

Motsin tahowar momie sukaji da sauri ta turashi ta dauki abayarta dake saman gado ta saka tana maida numfashi, momie na shgowa ta tsaya kallonshi cikin mamaki ta riqe baki tace "mezan gani hka?? Tunda safe ko farkawa bamuyi ba? Yana sosa qeya yace "gaisheku nazoyi kuma inga ynda ta kwana da jikin! Tace "ngde da gaisuwar, mai jiki kuma taaji sauqi!

Shru yayi ya rasa amsar dazai ba momie kamar ba itace tace bata ida warkewa ba, ji yake kaman yace tohm tunda taaji sauqi a bashi matarshi su tafi!!

Sai kuma baice komi ba har ya gama zamanshi yaga dai momie bata da niyyar fita ta barshi da matarshi, saiya fito kawai anan yayi break fast sannan ya wuce office cike da tunanin hafsatul kiram!

Momie mace ta samo wacce zata gyara mata hafsatul kiram, kullum cikin gyaran jiki ake mata da kayan karin ni'ima da ake d'ura mata, ita dai tana shane kawai! Kullum cikin gyara mata jiki ake, fatarnan tata taayi haske taayi kyau sai sheqi take, ga wani irin kyau da take qarawa kamar ka sace ka gudu!

Umar kam yaa samu wurin zuwa kullum yana maqale gidan momie duk da bata barinshi zama tare da hafsatul kiram, wani irin sonta ke qara shgarshi in yana tuna abnda ya mata a baya har zubda mata hawaye yake yana qara jinjina haqurin hafsatul kiram!

Yana matuqar kewarta da kyawawan halayenta, sanyayyar muryarta da sanyayyan yanayinta! Jinshi yake kamar yaafi kowa maraici da hafsatul kiram bata tare dashi!!

Lurv my princess Amrah😘

❤❤Rabiatu sk msh❤❤
[5/2, 4:22 PM] ✍🏻rerbee'art sk msh: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄
                          🎄
                       🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
              🎄🎄🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                       🎄🎄
                          🎄
           NA
  Rabiatu sk msh

          4⃣2⃣

Yau tunda yazo yake neman hanyar da zaiga hafsatul kiram, batasan da zamanshi a falo ba ta fito tana sanye da riga da siket na atamfa kanta yaasha en qananan kalaba ta d'aure ta da bant tsakiya, ta gabanshi tazo zata wuce sai dai taji ya riqo hannunta!

A tsorace ta juyo suka had'a ido sannan ta saki ajiyar zuciah da taga shne, ta sakar mishi murmushinta mai burgewa da zazzaqar muryarta cikin nutsuwa da tattausan lafazi tace "Yaa umar kaa wuni lpy?? Ya harareta da wasa yace "kin damu da hkan ne? Duqar da kanta tayi, ya d'ago fuskarta yace "banson shrunnan hafsatul kiram ki d'ago kimin maganan plz, meya hana momie ta bani matata??

Riqe baki tayi tace "ni inazan sani Yaa umar? Nimapa inajin tsoran komawa! Da sauri ya zaunar da ita suna fuskantar juna cikin zumud'i yace "tsoranme? Fad'amin! Dk taa marairaice fuska tace  "deezy bzata qara dawowah ba?? Dk taayi matuqar bashi tausayi tabbas hafsatul kiram taa juri abubuwa da yawa akan soyayyarshi, shikam dame zai iya saka mata??

Girgiza kai yayi cikin dauria yace "bzata taba dawowah ba hafsatul kiram, babu macen data isa ta shga tsakanina dake, naayi miki alqawarin ni naki ne har abada!

Sunkuyar dakai tayi taa kasa cewa komi can cikin zuciyarta wani dad'ine ke ratsata Yaci gaba magana "kewarki nake hafsatul kiram cikin kowanne bugun zuciyatah, dk sanda na rufe idona na bud'e, kullum cikin kewarki nake, gdanmu yaimin duhu sosae da babuke a cikinshi, daman haka ne idan mutum naa sonka bzakaji ZAFIN SO n ba, sai dai kana shareshi idan yana baka kulawa, sai randa ka fara sonshi ne zakaji ZAFIN SON a cikin zuciarka, ina fatan bn makara ba da roqonki yafiyarki!

Girgiza mishi kai take tace "don Allah yaa Umar ka daina roqona yafiyarka, wlhy ni bakamun komi ba, kaipa mijina ne kuma kana da haqqi a kaina! Don Allah ka daina!

Shima share hawayen yake dk dauriyarshi kalaman hafsatul kiram naa matuqar sanyaya mishi jiki, cikin qarfin hali yace "wai hafsatul kiram baki iya fushi bne? Tunda nake bn ta'ba ganin bacin ranki ba, ta yaya zan gane naa cutar dake? Don Allah idan na miki ba dai dai ba kina fad'amin!

Murmushin qarfin hali tayi tace "Mace ta gari mai neman Aljanna a qarqashin tafin qafar mijinta bzata ta'ba fushi dashi ba, baka ta'ba 'batamun rai ba duk dan adam ajizi ne yaa umar yana buqatar uzuri! Bn ta'ba bama zuciyatah damar da zata kamaka da laifi ba!

Shru yayi yaa kasa ce mata komi, kalamanta naa dusashe nashi, tabbas hafsatul kiram nada kaifin tunani da hangen nesa

Lurv my princess Amrah😘

❤❤Rabiatu sk msh❤❤
[5/2, 5:00 PM] ✍🏻rerbee'art sk msh: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄
                          🎄
                       🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
              🎄🎄🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                       🎄🎄
                          🎄
           NA
  Rabiatu sk msh

          4⃣3⃣

Momie ce tsaye kansu tace "shne zaka zo ka sakamun d'iya kuka ko? In kaayi haquri ay taa kusa dawowa ne, anma ka yrda ka qara matsa mata cikin gidannan zata dad'e ne bata dawo ba!

Tagumi ya zuba kamar maraya yana kallon momie tana fad'a dk yaa wani zama kalar ban tausayi tace ma hafsatul kiram tashi ki shiga,   ki kwanta ki huta ynzu za'a kawo miki abnci

Babu musu ta miqe ta tafi d'akinta sai da takai qofa ta juyo tana waigen yaa umar shima ita yake kallo da sauri ta shge d'aki cikin jin kunya!

Ranar tunda yaa fita bai dawo ba sai dare, ya shgo gdan cikin sand'a ya shge d'akin hafsatul kiram! Tana zaune tanacin dahuwar kazar da momie ta kawo matah ya shgo da sauri ta miqe tace "yaa umar baka tafi ba?

Yace "naa kasa daure zuciatah in tafi ne, Allah hafsatul kiram ina cutuwa da rashinki don Allah ki tausayamin kizo mu tafi, ta zaro ido tace "mu tafi ina? Momie bata ce bafa!!

Yace "momie bzataqi yrda ba idan kikaje da kanki kika fad'a mata ta kin warke ta barki mu tafi ba, ta zaro ido tana kallonshi tace "ni din bzan iya b?? Yace "shikenan bzaki tausayina ko hafsatul kiram?? Ki taimakeni plz naasanki da tausayi da taimako kuma!!

Tace "b hka bne yaa umar kaasan inajin kunyarta pa! Yace "haba hafsatul kiram taawa babu wahala pa nasan zaki iya! Basaikin kalleta ba, kanki na a qasa kina wasa da yatsun hannunki cikin kunyar nan taki kice "momie naa warke pa yaushe zan koma gidana??

Ta zaro ido tana kallonshi yayi murmushi itama murmushin tayi tace nikam bzan iya hkan ba! Yace "babu wahala pa ki gwada ki gani!

Tace "nidai a'ah yaa Umar! Ya dafe kai yace hafsatul kiram ni na kasa gane dalilin da yasa momie ta hanani kene! Ke kuma babu ruwanki hankalinki kwance! Kokin daina sona ne?

Da sauri ta girgiza kai zatayi magana kuma ta fasa ta sadda kanta, Yace "ki fadamun mana hafsatul kiram!

Dago kanta tayi tana kallonshi sannan ta ware manyan idanunta tace "momie!! Yace "kinajin kunyar momie ba? Mujd tare mu fad'a mata mu munso tafiya gida kinga bzata hana b

A hankali tace "momie gatanan bayanka tana jinka, da sauri ya juya wurin momie tayi tsaye taa bata rai hannunta a hard'e fuskarnan tata babu wasa take kallonshi

Lurv my princess Amrah😘

❤❤Rabiatu sk msh❤❤

[5/4, 3:48 PM] ✍🏻rerbee'art sk msh: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄
                          🎄
                       🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
              🎄🎄🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                       🎄🎄
                          🎄
           NA
  Rabiatu sk msh

           4⃣4⃣

Momie saida ta qaraso gabansu sannan tayi murmushi tace "Duk naa fahimceku, tana kallon Umar tace "bzaka koyama d'iyata rashin kunya ba, ynzu dai dare yaayi kazo gobe ka dauki matarka ku tafi!

Wani irin farin ciki ne ya bayyana a fuskar Umar don tsananin jin dad'i kamar ya rungume hafsatul kiram yakeji, yaa qagara sosae hafsatul kiram ta koma gidanshi ya fara nuna mata soyayyar da yake mata da kulawa....

Washe gari yana dawowa da shirin office gidan momie ya wuce, hafsatul kiram naa zaune ana zana mata qunshi a hannu ya shgo da fara'arshi cikin nishadi ya zauna! Suka gaisa da momie sunata fira, hafsatul kiram kau tunda ya shgo ta gaisheshi ta duqar dakanta!

Tana d'agowa suka had'a ido da sauri ya mata alamar yanason magana da ita, ta waro ido sannan ta girgiza kai tana nuna mishi momie, langabar dakai yayi yana mata alamar ta taimaka, d'aga kafada tayi alamar bzata iya ba sannan ta duqar da kanta.

Sai dai kawai ta ganshi yaa durqusa gabanta saman gwiwoyinshi da sauri ta waro ido taa rasa yanda zatayi don kunya, ya langabar da kanshi yana kallonta yace "nasan bzaki taba mntawa da abubuwan da suka faru a baya ba hafsatul kiram, nasan naa cutar dake, naa azabtar dake, A yau zan d'aukar miki alqawarin kulawa dake, sanyaki farin ciki bzan ta'ba barinki ki kuka ba har abadah! Ina sonki hafsatul kiram!

Duqar da kanta tayi tasa hannu ta rufe fuska, momie kam don tsananin jin dadi sai murmushi kawai take, taa shima Umar Albarka sosae sannan ta musu fatan zaman lafiya da farin ciki mai d'orewa!

Da dare suka tafi gidansu cike da farin ciki, suna isa gidan yana riqe da hannunta, ya bud'e mata qofar, cikin mamaki take kallon falon

Ya qawatashi da fitilu kala-kala yaayi matuqar had'uwa, ta juyo ta kalleshi ya kashe mata ido, tana qarema dakin kallo suka qarasa ciki

Har gaban cake ya kaita yana murmushi sannan yace "Happy birthday to uh my lovely wife! Sannan ya watso mata flowers masu kyau da qamshi ta rufe ido ta bud'e a cikin jin dadin ynda umar ya tuna da birthday dinta!!

Ranar ta zame musu ranar farin ciki, bayan sunyi alwala sunyi sallar miqa godia ga ubangiji, sun dad'e suna jero addu'o'i, kafin cikin zaquwa Umar yaja hannun hafsatul kiram zuwa gado!! Ganin irin kallon da yake mata yasa nasan wannan al'amari bai buqatar in tsaya daukar rahoto cikin hanzari na rufo musu 'kofar!!

Lurv my princess Amrah😘

❤❤Rabiatu sk msh❤❤
[5/4, 5:33 PM] ✍🏻rerbee'art sk msh: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄
                          🎄
                       🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
              🎄🎄🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                       🎄🎄
                          🎄
           NA
  Rabiatu sk msh

         4⃣5⃣

Soyayyah sosae da kulawa hafsatul kiram ke samu daga wurin mijinta Umar, ko motsi tayi yace "me take buqata?? Wani irin so yake mata fiye da duk tunanin mai karatu, ynzu bata da kewar gida duk sanda take da buqatah yana kaita don duk abnda zai sakata farin ciki yakeyi!

Bayan shekara shida 6..
Hafsatul kiram ce kwance saman qirjin Umar sai zuba mishi shagwaba take yana wasa da gashin kanta yace "kin shgo cikin rayuwatah kin canjata da kyawawan halayenki, i'm a changed person, koda yaushe inajin sonki a cikin zuciyatah, kome kike qaramun sonki yake...na yrda dake hafsatul kiram, ina sonki sosae! Ina matuqar alfahari dake.

Murmushi tayi ta d'ago tana kallonshi suna shaqar numfashin juna tace "ba zuciyatah kawai na baka ba yaa umar, naa mallaka mka kaina, ruhina, da dk wani abu dana mallaka komi naka ne, bnda abnda ya ragemin kullum cikin yi mka addu'ah nake mijinah, da ina da kyautar data wuce zuciyatah da naayi mka, ngde sosae da soyayyar da kakemun! Zan soka har abada, babu abnda zai rabani dakai, ta kwantar da kanta jikinshi!

Ya shafi gashin kanta yana murmushi yace "ke mace ta gari ce hafsatul kiram, ina Alfahari dake!! Da sauri Abubakar da qanwarshi zainab suka rugo suka rungume iyayensu nasu, tare suka had'a baki sukace, "Muma muna Alfahari dake sosae momie, muna alfahri da samun uwah ta gari!!

Hawayen farin ciki na share sannan na musu gyaran murya dk suka juyo suna kallona, Abubakar da zainab suka rugo sunamin oyoyo! Na kalli Umar nace "Don Allah ka qara riqe mana hafsatul kiram amana, mace d'ayace a cikin miliyoyi!

Girgiza kai yayi yace "A'ah aunty rabiatu, hafsatul kiram d'ayace a cikin duniyar nan, tun bayan labarin Rabiatul badawiyya da naji, bn ta'ba jin labarin macen dake matuqar biyayya ga mijinta ba kamar hafsatul kiram!!

Murmushin jin dadi nayi hafsatul kiram ta taso saitin kunne na ta rad'amun "Aunty yaa kamata kiyima masu karatu sallama hakanan, Allah yasa zasuyi koyi da Abnda suka karanta!!

Alhmdlh....
Anan na kawo qarshen wannan littafi nawa hafsatul kiram, ina fatan Abnda nayi kuskure Allah ya yafemun!!

🌿Hafsatu kiram🌿
Taa samu soyayyar mijinta babu boka, babu malam ba tare data bi wata hanyar ba ta nuna zaqewar, sai tsantsar addu'ah, haquri, juriya, biyayya, sadaukarwa, kau da kai, tunani da hangen nesa, mutumtawa da girmamawa!! Babu wanda zakaima wannan a soyayyar bai daukeka da qima da daraja ba ya fifita ka akan komi, duk mai haquri dk dadewa zai samu wadata, biyayya na da matuqar amfani a zaman aure! Allah ya bamu ikon farantama mazajenmu, yasa mana haquri dasu ya bamu ikon yi musu biyayya!! Allah ya bmu ikonyin amfani da abnda muka karanta muka qaru dashi

Sadaukarwa!!
Wannan littafi sadaukarwa ne ga hafsat Ahmad tijjani, Allah ya rayaminke da kyawawan halaye irinna hafsatul kiram, ya baki miji na gari ba irin Umar ba..ameen!!

Saqon godia ga..
Khausar luv da
Nana disco

Taki ta dabance:
My lovely sis princess amrah, kalamai bzasu iya bayyana ynda nake jinki a raina ba, kina tare dani a duk lokacin da nake da buqatar qawa ko er uwah! Allah ya barni dake

Jinjina ga duk
Online hausa writer's extreme hausa writers
Wisdom hausa writer's
Excellent hausa writer's
Best writer's
Da duk group din da nake ciki

Dole na ambace ku
Sis ummeterh
Zahra bb
Sadeeya afka
Khadija candy
Haneefa usman
Shafa'atu
Mrs Umar
Rash kardam
Asmeey b Aleeyu
Meesha luv
Baby Amrah
Sadeey
Autar hajia
Maman Abideen
Stylish
Jeeddah Aleeyu
Munay
Qurratul ayni
Bebeelo
Hajar
Allah ya bar zumunci, ya qara baseera!!

Ya za'ay na manta da?..
Abdul jega (mr smiles😃) Amanar Aure!! Allah ya qara maka hazaqa da baseera Ameen!!

WANI ZAMA ne tsakanin MARYAM KO MARYAMA, shin QADDARA ce KO RA'AYI?? Sai dai babu wadda taci AMANAR AURE a cikinsu, ko MIYE SANADI? DAN BAUTAR QASA Yace "BANI BANE. PRINCESS AMRAH tace "wacece MAI FARIN JINI a cikinsu? 'YAR AUTAH tace "tabbas HAFSATUL KIRAM ce tauraruwa! Hafsat tace "bani bace don duk qayatuwar labarina bzai kai LABARIN RABIATU ba!!

Littafan marubuciyar kenan!!
Wani Zama da
Labarin Rabiatu zasuzo muku tare da wasu mazan wasu matan!!
SUNANA ABDUl ma yananan tafe!! Ngde sosae masoyah na!! Kuci gaba da kasancewa dani, ina qaunarku gaba daya..
Domin gyara ko fad'in ra'ayinku
👇🏻
08032133670
Taku ce a koda yaushe

❤❤Rabiatu sk msh❤❤

adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *