Na Benaxir Omar
Tulunta tadauka tanufi rafi inda zata diba
ruwa, tana tafiya ne tamkar wanda iska zai
kwashe tsabar rashin jiki, irn bafulata
nannne dogaye tsirara, gashinta taayi
manyan kitso guda biyu dukka sunzubo
tagaba, tana isa bakin rafin tazauna ta ajiye
tulun , ta cire takalmanta ta tsunbulu cikin
ruwan tafara juyi, akalla takai minti ashirin
kafin ta fito jikinta yajike tsaf, gakuma ruwan
rafin sai wucewa yakeyi dasauri taciro wani
riganta data ajiye agefe tacanja sannan
tadibi ruwan tasakai tatafi, tana tafiya
ahankali ruwan nakanta, yadda takeyu zaace
kwai ta dauko akanta, tashiga cikin kauyen
nasu wanda ke dukku a cikin jahar gombe,
ahanyan gydanma taga bishiyan mangwaro
hakan yasa tasauke ruwan, tadauko dutse
tarinka jifa saidata sinko guda shida sannan
ta dauki ruwan tamakalo mangwaron acikin
rigan data cire a rafi, sannan ta isa gyda,
tana isa zauren gydansu ta leka ko zataga
innarta ganin bakowa yasa taje kicin ta ajiye
ruwan sannan ta hura murhu, tana hurawa
taji shigowar innarta, inna ganin murhu take
hurawa saidataja tsaki, yarinyannan Allah
shiryeki yanzu don girman Allah tun karfe 10
baki daura abincinnan ba saiyanzu karfe 1?
Tace laa inna yanzu dawowata daga rafi fa,
tace aidole kinje kinshige ruwa kaman gydan
ubanki ba?, wai meye hadinki da ruwa ne
kam? Ki kiyayeni
Amal ta kauda kai, haba inna wanka fa
nayi, kuma ina dawowa na tsinka miki
mangwaro naga kinaso, innar ko sauraronta
batayiba tafice mutum saikace yaro, akalla
amal shekaranta 16 anma takiyin hankali
tana abu na yan shekara 13; tarasa yazatayi
da amal,
Amal marainiya ce mahaifinta alh.usman
jado yarasu tun tana shekara biyar hakan
yasa innarta fatu tadauki nauyinta, tasata a
makarantar govt dake anguwansu, yanzu
haka amal na ss2 , amal da innarta sunsha
gwaggwarmayan rayuwa domin kuwa bayan
rasuwan mahaifinta danginsa sukayi keke
saisun dauki amal, haka innarta tayarda
anma bayan sunriketa amal sai wahala
takesha ba abinci ba makaranta bakomi,
hakan yasa innarta tanemi aiki na wanke
wanke agydan sarkin garin suna samun na
abinci ganin zata iya daukar nauyinsu yasa
taje dakyar da wulakanci da zagi akabata
amal anma duk ta jure, saboda bazata
zauna tana gani dangin miji su lalata mata
yarta ba, duk da garin fulani ne kuma suna
nuna kara akan dan fari,, agunsu ko zaa
kashe danki nafari ne bazaki yi maganaba,
anma fatu gani take zaa kashe mata yarinya
gwarA ta kwace ma kanta yanci , yin hakan
datayi bakaramin kananun magana tajawa
kantaba, mutane yazama sunA ganin tayi
rashin kunya anma agunta itakam wlh daidai
tayi, donhaka tasa amal a makaranta,ta
tarbiyantar da yarta, gashi Allah yabata
gaggararriyar yarinya amal bataji ko kadan,
yarinya ce mai taurin kai wacce aganinta
bazaa taba kwace mata hakkinta,ga son
mutane dakuma uwa uba neman tsokana,
amal tana primary tasha siyan fada, idan
taga zaayiwa kawarta fada saita baki kudin
tara da innarta tabata saita shiga fadan, in
Allah yasa tacito inbataciba anmata duka
inna tayi kwanan jinya, tahanata anma inaaa
amal babu, wani dadin abun shine tanada
kokari sosai, abunda yasa tayi suna kenan
kuma malamai suke sonta suke ragar mata
wani lokaci, ayau kuma ko da headmaster ne
yasa doka toh idan akwai wanda baya
tsoron sa kafa yashure itace amal, kuma ko
agabansa zata fada, in antambayeta,
bazatayi karyaba, in ae tayi in a a batayiba,
kuma ko kasheta zaayi bazata canja magana
ahaka har ta shiga secondry to nanma
labari bai canja ba, don tana girma kyanta
na kara fitowa, innarta takoya mata aiki da
duk wata ya mace yakamata tasani, innarta
nasonta sosai, koda ranta yabaci dazaran
taga amal takanji sanyi gakuma uwa uba
amal nada biyayya dabin nagaba, saidai duk
girmanka baka isa katake mata hakki ba, sau
dubu takan taimaki mutane da dabarunta,
amal doguwa ce siririya ,nakanyi mamaki ya
akayi iska baya kwasanta don rashin
kibanta, kana ganinta kaga bafukatana
saidai wankan tarwada ce, kiran kalangu, ga
dira diran idanu, ball eyes,da bakinta pink
lips ,kana gani kasan ba matan yaro bane,
tunda tashiga ss1 maza sukafarayiwa fatu
layi a kofar gyda anma amal ko ajikinta
dazaran yaro yashigo zatace ace batanan
inkuwa aka takura takora yaro da gudu,
kokuma tafito ta kada keyan kowaye takoma
gyda abunta, wannan yarinta da halin yan
fari shiyasa kowa yake kara sonta, tayi farin
jini sosai a anguwan, wannan itace AMAL
USMAN JADDO,
Bayan ta dafa shinkafa tadafa wake tazubo
musu a tray kasancewar itada innarta tare
sukecin abinci tadebo tazauna tana jiran
ummanta ta idar da sallan laasar, tana
idarwa tace kinyi sallahn ne kokuma? Idonta
ta lumshe kamar maijin bacci sannan tace
inna ko addini ya yadda naci abinci kafin
sallahn kar hankalina yarabu, innar batace
komi ba ta bare maggi yayinda amal ke zuba
mangyada ta xuba yaji sunaci, har suka
gama ba wanda yayi magana, saboda
innarta tamata tarbiyan inzataci abinci
kartayi magana harsai tagama, suna
gamawa tayi sallahn kafin ta kimtsa gydan,
dama tayi wsnka arafi donhaka tacanja kaya
tasa na islamiya tadauko qurani sannan tace
inna natafi, inna tace Allah bada saa , tana
isa islamiyan tasamu baacika ba, kuma
islamiyan nahade da masallaci donhaka
tadauko tsintsiya tafara shara kamar yadda
tasaba tashare tas anan dalibai sunfara
shiga, tashiga aji tana bitan haddanta,
malamin yashigo don karban hadda amal ne
a sit nagaba anma tana ganinshi ta kinkima
littafi tayi baya, yace lu'u lu'u kasan cewar
haka yake kiranta dawasu malaman,
bakyada gaskiya dawonan ke zaki fara
bayarwa, takalleshi tace laa malam wai
nakoma ne ko zanyi bita dakyau bangama
tabbatar da shigansaba, yace toh bari wasu
sufara. Har akazo kanta tabada shafi 10
wanda akabasu suyi tana karantawa ne cikin
sauti mai dadi, duk mai sauraron muryan
amal dole yakarajin sonta dakuma abinda
take karantawa, domin kuwa tsaf take fitar
da tajweed tana bawa kowani kalma
hakkinsa,
harta idar da shafi goman nan baimata
gyra ba, ta na gamawa tadauko hadiths
sukayi, sannan suka tashi, ahanyan komawa
gydansu dama akwai bishiyan guava, amal
kuwa nason guava hakan yasa ko yaushe
intana dawowa saita tsinka, mai guava
takawo kare saboda su amal, anma amal
don maita saitasan yadda tasa yara sunja
hankalin kare ta tsinka inkuma taga bazata
samuba ta jefe guavan su fado kasa dukka
kowa yarasa. Ana kiran magrib tashiga gyda
innarta tayi alwala zata shige kenan itama
ta ajiye jakan islamiyanta tayi alwala tabi
sawun innartan, ta idar da sallan ta kwanta
akan cinyan innar, tare dacewa inna tayani
tsifa kaina yafara damuna, innar takama kan
tana tsefewa, can amal tace inna kinga
saura wata daya mushiga aji shida daganan
nagama secondry. Innaci sainatafi birni
jamia, nadawo likita nagina miki gyda nabaki
mota, inna tace sosaima, adduan shine Allah
yabani kudin , can sai amal tace inna toh
innagama kafin result yafito sainaje birni
hutu gun gwaggo asama yayarki ko? Tace
ae kinga kema saikiga gari dakyau, anan ta
dauko comb ta tace kan tsaf ta kamashi
sannan sukayi isha, amal tazubo musu tuwo
wanda innar tayi da asmau take mskaranta,
sukaci sunata tadi, har akafara sallama amal
tarike goshi wayyo nikam zasu fara, ta amsa
sallaman tare dacewa wayene?, yaron yace
ana neman amal awaje, tace kace batanan,
yafita can wani yakara dawowa tace ace tayi
bacci, ahaka dai aketa zuwa kamar yadda
suka saba, amal tamike ta kwanta nan
tafara bacci, tare da mafarki wanda tasabayi
kullum , mafarkin kuwa akan tayi kudi tasiya
mota da gyda tazama likita,
washegari tatafi makaranta amal tanda
tsafta sosai bazaki taba ganin uniform dinta
ba wanki ba, hatta guga saidatasa innarta
tasiya mata charcoal iron saitasa gaushi tayi
abinta, da dan turarenta na 200 da innarta
tasiya mata, malaman sunaji da ita saboda
bayan kyau amal nada ilmi, ansha bata
student of the year, amal tanada daukan abu
, batada mantuwan ilmi, toh haka
makarantan yasa kowani gasa sai ansa
amal, intaje kuma saitaci, wannan karonma
akwai gasa da aka hada zaayi makarantun
govt wanda gov zaixo yagani da idonsa,
amal naciki donhaka jin zasuje birni yasa
amal tarinka murna tareda dagewa, debate
zatayi toh topic din da akabata taje tasamu
malaminta daya yarubuto mata komi, ta kara
xuwa gun wani malami shima yarubuta
saitahada biyu ta cire important point tafara
haddacewa, kunsan abunku da mai haddan
quran toh tabbas haddan komi aduniya bazai
taba mata wahala ba, haddan yamata sauki
tahaddaceshi lokaci daya ba inda inda,
donhar agaban murhu hadda take innarta
kuwa saidata tambaya aikuwa tace itakam
gaban gwamna zataje shiyasa takeso ta iya,
ranar abunsun tafito fes da ita tayi
kitso,tasha kyau, gashi uniform dinsu komi
fari kaman nurses, toh ga uniform din amal
kaman ajikinta aka dinka, sunshiga bus iya
dalibai uku wanda zasuje abun, amal debate,
sai kawarta nana itakuma quiz zatayi, sai
daya namiji akilu shikuma presentation,suna
motan amal gabanta sai fadi yake duk gasan
dasuke zuwa iya manyan mutane ke zuwa
anma gwamna baitaba zuwaba hakanne
yasa hankalinta yatashi, suka isa cikin garin
gombe inda sukaje filin stadium anan zaayi.
Makarantu kam gasunan dayawa kowa yazo,
anajiran gov, aikuwa saikagashi yazo su uku,
kana ganin sauran biyun zaka iya cewa
suma manyane a govt din nanfa aka fara
gasa, anyi quiz kam nana tasamu mark 84
itace 3rd to the highest, akayi presentation
inda akilu yasamu 86 shikuma 4th to the
highest, nan akazo nasu amal, malamin ne
yakirata yace amal kinga abunda zakiyi
shizaiyi determining zamuci ko bazamuci ba,
amal bakitaba bani kunyaba karkibani plx,
tayi murmushi sannan tace dnt worry
malam,i was born to win, itada abokiyar yin
debate din sukashiga filin inda suka zauna,
amal na opposing yayinda dayan ke
supporting topic din male education is worth
more than female education, nanfa mai
supporting tafara kowani point tabayar sai
amal ta ajiyeshi a kwanyanta dontayi
opposing, tana gamawa aka tafa sosai
dontakawo points, saikuma akazo kan amal,
tundaga fitan dazatayi akafara tafawa domin
tafiyan amal kadai ya isa ya janye hankalin
taro, kafin tazo tafara bayani a tsanake take
maganan kuma kowani hujjanta da misali
tagama tazo tayi opposing duk wani hujja da
wancan takafa, habawa zokuga tafi stadium
tadauka, kowa yaji dadi donhar gwamna
saidaya tafa yadda amal ke bayani da
confidence, anzo fadan mark inda amal ta
tashi da 99 kuma aciki da aka hada mark
dinsu makarantansu ne tazo highest
donhaka aka fara bada kyauta,
makarantansu tasamu kyautan miliyan biyu
daga gwamna, sannan da akazo fadan best
partispant amal ce taci tafito domin karban
kyautarta, gwamna yabata scholarship na
university aduk inda takeso, hade da dubu
dari biyar, murna agun amal bakanta ganin
check nakudi ahannunta tunanin innarta
shine aranta,
ahaka suka shige suka koma dukku
nanma suka samu yanmakaranta najiransu
habawa kowa murna, ji suke kamansu lashe
amal koba komai tadaga musu sunan
makaranta itama tayi suna don kowani gidan
tv da radio saifada suke amal usman kado
ita talashe kyautan da gwamna yayi, amal
nashiga gyda dagudu tarungumi inna tana
kuka take gayamata innama saitafara murna
suna godewa Allah, abufa wasa wasa amal
takara samun suna da matsayi agun yan
kauyensu kowa nasonta mazan kuma kowa
na kokari yaga shi yassmu shiga, ran
monday makaranta takara mika godiya wa
gwamna saikuma akafito dasu amal agaban
assembly aka nunasu don sunzama tauraron
hasken makarantan, duk wannan abun baisa
amal tayi kasa gwiwa agun haddantaba
babban farin cikinta shine saura mata izu
hudu tasauke daganan zasuyi graduation
dinsu
##$$$$$$A gidan gwamna kuwa fahad ne
zaune ya kunna gmtv don ganin labarai,
anan yake ganin gasan da akayi sunata
nuno fuskan amal murmushinta yadda take
partispating, popcorn yakeci anma saidaya
dakata kadan yayita kallon yanayin yarinyan,
tohfa gata batada wani jiki kana gani kaga
yarinya anma gaskiya he is impressed da
ilminta dakuma confidence dinta, ganin taci
gakuma kyautar da tasamu daga mahaifinshi
dakuma skul dinsu, dasauri yadauki biro
yarubta sunan makarantan, govt secondry
skul dukku, yadauki wayansa tare dacewa
hello, kaje dukku govt secondry skul, akwai
wata student amal usman kaddo kabincika
min komi, wen i say komi i mean evrtn abt
her. Nanda 24hrs, yanagama yakashe, kashe
tv yayi yasauka kasa don yaci abincin dare
##%%%$$$$$$$$$$ amal tazo tafara shirin
yayesu dazaayi, yayinda kudinta yashigo
hannunta itada innarta sunsamu sauyi sosai
agydansu sun saya kayan abinci sun ajiye
sun gyra gydan sannan suka karo kayan
sawa, amal tasiya su turare da kayan
kwalliya, duk wannan abun amal batada
kawa arayuwarta kowa nata ne, nan tadinka
sabon kaya wanda zasusa a bikin yaye
dalibansu na islamiya wanda zaayi nanda
kwana hudu,
Acikin gayyatan manya sun gayyaci mai
girma gwamna dasu commisionern ilmi
dakuma manyan malamai, ran taro kam sai
sanarwa yazo musu cewa gwamna bazai
samu daman zuwa ba anma babban danshi
fahad zaixo, su amal sunsha manyan liqab
saisu zo suzauna suna qiraa, fahad kam
ganin kowacce da liqab yagagara gane
wacece amal aciki saiyakasa kunne dan yaji
suna, anahaka kuwa akazo kan amal tafito
tafara karatu, tunda yake baitabajin
daddadan murya irinta amal ba yakare mata
kallo anmafa baiga komiba sai hijab da liqab,
shikam meye haka tawanisa liqab? Tana
gsmawa akadau kabbara, nanfa akayi komi
aka watse,
amal tasamu daukaka sosai acikin
kauyensu kowa yasanda amal kaddo ,
rayuwa tamusu sauki yanzu tunda sunaci
sunasha, sannan gakomi awadatace, inna
kullun acikin sawa amal albarka take duk da
batason gagaran amal, acikin satin suka fara
jarabawar gama aji biyar, bayan sun gama
ne amal taroki innarta taje birni hutun wata
biyu kafin sukoma, innar ta amince mata don
akwai wata yarta asama acikib garin gombe,
ana gobe zata tafi inna tace amal ba
barinkin bane nasan halinki sarai, don Allah
karki shigarma wani rikici, sannan ko kinga
badaidaiba inkinsan zaijawo miki matsala to
baruwanki kishare kawaiAllah yamiki albarka
yabaki miji nagari, amal tace amin innazama
likita ne zanyi aure ai, innar ta kada kai tace
zanso hakan, anma nasan dangin mahaifinki
kina gamawa zasu faramin tsintiri gwara
kinema tsayayye don inbaki fitarba zasu
hadaki da duk wanda ransu yabasu, amal ji
tayi kaman tabi dangin ubanta ta kashesu
dukka, haushi suka bata, basusan dadinta da
wuyantaba anma sunsan maganan aure,
washegari taje tasha dauke da jakanta
dakuma qurani ahannunta motar gombe
tashiga, suna isa gombe tahau keke tanufi
gra, anguwan da gwaggwo asama take,
tabuga gate din gidan nan maigadi yaleko
ganin amal yasa yace lafiya yarinya? Tace
matar gydan nake nema yace tana ciki
barimmiki iso, ince injiwa? Tace kace inji
amal kaddo, bayan minti kadan saigashi
yazo dasauri yabude mata tana shiga ya
nuna mata hanya sannan yakoma, gwaggo
na falo taga amal murmushi tafarayi lale lale
lulu , amal tashiga ta rutsuna sannan
tagaysheta ta amsa da faraa, tajuya takalla
yar gwaggon maisuna faiqa tana murmushi
tace faiqa yakike, faiqa ta kalleta sama da
kasa, sannan tace lao ba yabo ba fallasa,
anan gwaggo tace lallai faiqa takai amal
dakinta tasauka, jitayi kaman tasa hannu
akai tafara kuka, suna shiga tabude gefe
daya na wardrobe tace kisa kayanki anan
karki batamin daki, tajuya tatafi , tun asali
faiqa da amal basa wani shiri itadai amal
bata kulata yayinda itakuma faiqa take ganin
amal yar kauye bata wayeba, hakan yasa
amal tadena zuwa hutu gydan sai ancemata
faiqa na makaranta dake boarding skul faiqa
take, datasan zata sameta agydama
dabatazoba itakam, don dai kawai tanason
xuwa birni ne gakuma innarta nason tazo,
dare dare bayan sunci abinci amal nason
bacci don haka tadauko quraninta tayi bita
sannan tamike tabi gado anma ina faiqa taki
tabarta sai waya takeyi tana kashewa wani
zai bugo amal tarasa yazatayi , washegari
ma dasafe amal tamike tafara share share
nan gwaggo tafito tace mata tabari akwai
masu aiki hatta masu abinci itadai tayi
wanka ta shirya tayi wanka tazauna suka
karya, ananne taga faiqa tajidi wasu kayan
kwaliyya tayi gira tasa a ido kawai sai faiqa
tadawo tv, faiqa data lura tana kallonta tace
bakaiuyiya kizo ki kalla ki koya inbahakaba
bawanda zaice yana sonki, amal takalli
kanta a madubi tace ni powder zansa da
kwalli, faiqa taja tsaki haka zaki ta zama
bagadajiya, sun shirya amal kam hijabi tasa
hakan yasa faiqa ta fauce tare da cewa indai
zakibini bazakisa hijabi ba, biki fa zanje
sannan kidaukomin hijabi ? Kalan kisa araina
ni?,
amal tasamu daukaka sosai acikin
kauyensu kowa yasanda amal kaddo ,
rayuwa tamusu sauki yanzu tunda sunaci
sunasha, sannan gakomi awadatace, inna
kullun acikin sawa amal albarka take duk da
batason gagaran amal, acikin satin suka fara
jarabawar gama aji biyar, bayan sun gama
ne amal taroki innarta taje birni hutun wata
biyu kafin sukoma, innar ta amince mata don
akwai wata yarta asama acikib garin gombe,
ana gobe zata tafi inna tace amal ba
barinkin bane nasan halinki sarai, don Allah
karki shigarma wani rikici, sannan ko kinga
badaidaiba inkinsan zaijawo miki matsala to
baruwanki kishare kawaiAllah yamiki albarka
yabaki miji nagari, amal tace amin innazama
likita ne zanyi aure ai, innar ta kada kai tace
zanso hakan, anma nasan dangin mahaifinki
kina gamawa zasu faramin tsintiri gwara
kinema tsayayye don inbaki fitarba zasu
hadaki da duk wanda ransu yabasu, amal ji
tayi kaman tabi dangin ubanta ta kashesu
dukka, haushi suka bata, basusan dadinta da
wuyantaba anma sunsan maganan aure,
washegari taje tasha dauke da jakanta
dakuma qurani ahannunta motar gombe
tashiga, suna isa gombe tahau keke tanufi
gra, anguwan da gwaggwo asama take,
tabuga gate din gidan nan maigadi yaleko
ganin amal yasa yace lafiya yarinya? Tace
matar gydan nake nema yace tana ciki
barimmiki iso, ince injiwa? Tace kace inji
amal kaddo, bayan minti kadan saigashi
yazo dasauri yabude mata tana shiga ya
nuna mata hanya sannan yakoma, gwaggo
na falo taga amal murmushi tafarayi lale lale
lulu , amal tashiga ta rutsuna sannan
tagaysheta ta amsa da faraa, tajuya takalla
yar gwaggon maisuna faiqa tana murmushi
tace faiqa yakike, faiqa ta kalleta sama da
kasa, sannan tace lao ba yabo ba fallasa,
anan gwaggo tace lallai faiqa takai amal
dakinta tasauka, jitayi kaman tasa hannu
akai tafara kuka, suna shiga tabude gefe
daya na wardrobe tace kisa kayanki anan
karki batamin daki, tajuya tatafi , tun asali
faiqa da amal basa wani shiri itadai amal
bata kulata yayinda itakuma faiqa take ganin
amal yar kauye bata wayeba, hakan yasa
amal tadena zuwa hutu gydan sai ancemata
faiqa na makaranta dake boarding skul faiqa
take, datasan zata sameta agydama
dabatazoba itakam, don dai kawai tanason
xuwa birni ne gakuma innarta nason tazo,
dare dare bayan sunci abinci amal nason
bacci don haka tadauko quraninta tayi bita
sannan tamike tabi gado anma ina faiqa taki
tabarta sai waya takeyi tana kashewa wani
zai bugo amal tarasa yazatayi , washegari
ma dasafe amal tamike tafara share share
nan gwaggo tafito tace mata tabari akwai
masu aiki hatta masu abinci itadai tayi
wanka ta shirya tayi wanka tazauna suka
karya, ananne taga faiqa tajidi wasu kayan
kwaliyya tayi gira tasa a ido kawai sai faiqa
tadawo tv, faiqa data lura tana kallonta tace
bakaiuyiya kizo ki kalla ki koya inbahakaba
bawanda zaice yana sonki, amal takalli
kanta a madubi tace ni powder zansa da
kwalli, faiqa taja tsaki haka zaki ta zama
bagadajiya, sun shirya amal kam hijabi tasa
hakan yasa faiqa ta fauce tare da cewa indai
zakibini bazakisa hijabi ba, biki fa zanje
sannan kidaukomin hijabi ? Kalan kisa araina
ni?,
amal tace toh shina mallaka, nan faiqa
tahau sama taciro mata abaya tare da
gyalensa sannan tace ungo kisa , abayan
yanada kyau kuma yakarbi amal sosai, suka
shirya tsaf suka fito anan sukayi sallama da
gwaggo, gidan biki sukaje inda faiqa tajata
suka je fannin da amarya take da kawayenta,
kawaye wayayyu suka zamema amal tv sai
kallonsu take musamman yadda suka daura
dankwalinsu yayi kato yayi fanka itakam
akauye tamkewa take, donhaka dataga wata
kawar faiqa nason daurawa taje gunta
tazauna sannan tace don Allah ki koyamin,
takalli amal sannan tace gashi kuwa zaimiki
kyau nan tazauna takoyamata tsaf, tayi
kwalliya sannan suka zauna, sai tadi suke
wannan tana tadin saurayinta wannan ma
haka, anan akazo kanna faiqa , faiqa tace
nifa inaga inban auri fahad ba zanmutu, aka
kwashe da dariya, no kungane? I have a
crush on him sosai, gayen yahadu ga kyau,
ga ilmi, ga kudi , ga aji, donma yaga ubansa
gov .ne shiyasa yake wani abun, anma duk
girman kansa dole yasauke ya aure faiqa
mansur, ko shiwaye kuwa, nan kawayenta
sai tusata suke wannan yace kaza wannan
yace kaza, kowa na kyatsa kyau dai na
fahad, itakuwa amal tanata tunani wani irin
kyaune haka tanaso taganshi, daya daga
cikin kawayen saitace ji yadda kuje zakewa
wani zaice kuntaba ganinshi ne, alhali duk a
hoto kuka sanshi nfn more, sannan baisan
dakuba, faiqa ta ina zaki samoshi, tayi
dariya tace jiya nabada dubu biyar
anemomin numbanshi donhaka sai kufara
tara kudin ashogbe don super zanyi na wuni,
material na 40k. Saikunma less na 50k ,
ashogben almost 200k zanyi, saiku fara taro,
nan tamike saitafa mata sukeyi, saini faiqa
mansur mata agydan fahad aliyu, nice
uwargydansa kuma amaryarsa, zan kawar da
duk wata ya mace data shiga gabana
kokuma takatse min hanzari kowaye ita,
domin fahad nawane nikadai!
amal duk dabatasan wani namiji bane
anma saitayi tunanin anya faiqa tanada
cikakken lfy kuwa? Namiji yace yana sonki
yakuka kare balle ke kika fada,itadai tanason
rayuwansu na gayu anma batason irin
halinsu, ahaka suka gama suka koma gyda
alokacin ankawo wa faiqa numban fahad,
murna take kaman ta lashe kasa, tuni tayi
adyn dinshi a whatsapp suna idar da sallah
anma inaa faiqa ko abinci ta gagara ci tana
jira yahau, amal kam quraninta tadauka tayi
bitanta , taci abinci tayi isha sannan tafara
kallo, tara nayi tashiga ta kwanta, haka dai
faiqa ta hakura domin fahad sai washegari
yahau online kuma ma baiyi repling dinta ba,
hakan yasa takara cewa hy, yakai minti
goma kafin ya amsa da hello, nan taji dadi
sosai sannan tafara fahad wata masoyiyarka
ce dafatan zaka bata mazauni a zuciyarka,
can yayi replying da lol thnx, saikuma yayi
shiru, faiqa kam tanata janshi da surutu
harta gayamishi sunanta anma inzai bata
amsa ma a takaice yake bayarwa shima
intayu magana saita karo wani maganan
yake reply, ahaka washegari gwaggo tabawa
amal waya wata samsung mai kyau amal
taji dadi sosai donhaka tasiyi layin mtn
tafara amfani dashi,
Watarana amal tafito zata shiga kasuwa
adaidai gurin multipurpose mutane nacike
agurin kowa nata hidimanshi, amal taci
atamfarta mai kyau wanda gwaggo tadinka
mata tayi daurin da kawar faiqa takoya mata
tasa janbaki tahau takalminta mai tudu
wanda tsabar faiqa na yawan sawa yasa
takoyi sawa, kana ganinta kaga babbar mace
gashi yadda ta yafa gyalen na yan koyone
saidai kuma ya balain yimata kyau zaka
zata wani style ne kuma, wani mai mercedez
ne yaro ne ba babba ba yazo ya buge wani
tsoho, kuma sai ya tsaya shi da dan sandan
sai matsifa suke wa tsoho, amal abin yabata
mata rai bashiri taje gun ta tsaya tacire
gyalen ta yafashi a kafada, sannan ta tsuke
tace meye haka kun buge mutum zaku wani
fara mishi matsifa? Dan sandan ya kalleta
tare dacewa hajiya yana ganin mota fa ya
wuce yasan baikamataba, nan mai mercedez
din yace kekuma wayeke? Kidubi yadda
tsohon nan yasa nafasa glass din motata, ko
kanki nasiyar bazai hadamin kudin glass
dinaba da paint, amal ranta yabaci taja baba
tsohon, duk da akwai hold up atagurin
yawanci masu motoci sun tsaya ganin ikon
Allah, ta kalli police din tace, babana ne
commisionern ku, yanzu sunanka zaka
gayamin da department ayau zaa koreka,
dan rainin hankali, habawa saiga dan sanda
ya durkushe sai hakuri yake bata ko kulashi
batayiba yabita sannan tace saikamin
alkawarin bazaka kara tauye wa talaka
hakkinsa ba don kaga maikudi yace ae
nayarda, alokacin takalli saurayin dayace ko
kanta bazsi siya mishi glass ba, yayi cukus
shima yana kallonta
tace ka tsaya kallona da muzu muzun
idonka kaman na muciya, dakunga talaka
saiku na wulakantawa, wlh yatsana kadai
aka siyar sai yasiya motanka da kai kanka
kaza kawai, abun saiyabawa saurayin dariya,
Tajuya tafita ta yanki titi donji tayi tafasa
xuwa kasuwan,babanne yabita yayita mata
godiya, yata irinku ake bukata akasa, Allah
ya daukaki kizama wata, ki taimakawa
musulunci, Allah miki albarka ,amal tace
ameen baba kayi hakuri, tacire 1000 tabashi
yarinka godiya kuma dama abunda ta
mallaka kenan,
Acan bangaren titin inda hold up yarike su ,
fahad ne zaune yana tuki, sauri yake zaije
govt house yayi mantuwa anma ganin amal
ta bangaren titin tundaga farkon kade tsohon
har inda amal tashiga maganan da kudin da
amal tabayar yana kallo, yarinyan ta kashe
masa rayuwa, duk moves dinta yana sane,
daga zamansu na kauye har zuwa gombe
duk yana sane, ko ina amal taje sai yasani,
hatta siyo layin da amal tayi saidaya sani,
don ashagon tayi registern layin anan aka
karbo mishi numbanta, baikirataba don yana
watchn dinta ne, yanzu jiyayi ta tafi da
imaninsa, har gizo take mishi,
Kwance yake yana ta juyi, ji yayi anbugashi
bude idonsa mummynsa yagani tarike kugu,
kaikuma fahad meya sameka yau kamanta
dani, yace bakomi yana mikewa yana mika,
tazauna agefen gadon sannan tace bama
yauba kwannannan ka canja hatta faraa
dakakeyi da mutane kadaina, anmaka wani
abune? Yayi murmushi babu mummy, kawai
dai, ta tsare shi da ido kawai dai meye?
Yace wata ce! Tafdi bashiri tamike soyayya?
Wayyo fahad? Wacece? Aina take,?
Alhamdulilah Allah, yau fahad kai kake
maganan mace, yace ae mummy tsaya kiji
batafa san inasonta ba, kuma bata ma
sanniba, tsayawa tayi kaman anduketa,
banganeba toh kai kuma meyasa baka
gayamata ba? Yace mummy tsoro nakeji?
Tsoro? Tsoronme fahad? Macece fa, afadin
garin nan akwai inda zakaje neman aure a
hanaka ne? Infact kaf nja? Yace mummy
bazaki ganeba, anma kibarni zansan nayi,
sunanta amal, mummy tayi murmushi wow
amal sunan dadi, harnaji inasonta, yakalleta,
shiyasan datasan wacece ko yar gydan
wacece ko yar wacce gari ne bazata taba
yadda ba, uhmn shikam yazaiyi da ransa,
amal tadawo jinin jikinsa
amal tana isa gyda tayi alwala tayi
sallah tadauko shinkafa tafaraci, a lokacinne
faiqa tadawo gydan dauke da ledodi kayan
makulashe ne tunda ga kan snack har drinks,
amal tace daga ina? San hussien mukaje
dawani jaki zai gwadamin yanada kudi
nikuwa nalashe, dubu 30 naci, kinga har
atamfofi na dibo, amal takalleta sannan tace
kinga abunda kikeyi baki dace ba, ba kyau,
yayan wanine baban wani ne dan wani ne,
anma kince mishu jaki, faiqa ta wulla mata
harara kinga banson iskanci meruwanki
dani?; ke me kike sani? Mazan yanzu inbaki
kashesu ba zasu kasheki, gwara kici kudi
inzakici banason fiili, amal kam girgiza kai
tayi ta tashi tanufi daki, quraninta tadauko
tayi bitanta sannan ta ajiye tadauki wayanta
tafara danne danne, gashi dai tasiya waya
anma batada numban kowa daga na gwaggo
saina faiqa, saidai inta koma kauye acikin
kawayenta ma mutane hudu ne masu waya.
Daga yayan gidan mai anguwa sai gidan
galadima, kuma dukkansu nokia ne ma,
gashi ita ta mallaki samsung, tashuga tayita
bincikenta daganan tayi game dasauransu.
Ahaka har bacci ya kwasheta,
Fahad ne zaune da abokinsa faisal, duk
sunyi tagumi basusan yazasuyi ba, fahad
yace kaga a kauyensu bata kula kowa which
means inna bari taje kauye to zata dauka
duk shiriritan kauyensu ne , anma innaje
anan zata fito kobata fito ba, akwai cousin
dinta ancemin yarinyan yar gari ce tsaf
zatasa tafito,kuna danasa aturomin numban
cousin din nata ko zanbi takafanta naga
itama she is stalking me a whatsapp almost
evrdae saita kira, toh kaga naje kofar
gydansu kam ai akwai rikici, faisal yace ga
shawara. Karkaje da mota kaje da kafa,
hankalin cousin din bazai iso kanka ba, but
da mota dole zata zo taga waye. As in
kagane ai, gashi kai baka hawa mota daya.
So kaje mata as talaka inkaje mata if komi
yayi settling saika nuna i.d dinka
In much of sub-Saharan Africa, the term
"youth" is associated
with young men from 15 to 30 or even 35
years of age. Youth in
Nigeria includes all members of the Federal
Republic of Nigeria
aged 18–35. [13] Many African girls
experience youth as a brief
interlude between the onset of puberty and
marriage and
motherhood. But in urban settings, poor
women are often
considered youth much longer, even if they
bear children outside
of marriage.
aikuwa washegari ta tashi da asuba
taga message shima ga yadda yace
"Amal habibaty, jjiya nayi mafarkinki, nayi
mafarkin kinzama matata, nayi mafarkin ke
kadai ce tawa. Amal karki barni kowani hali
zamu shiga rayuwa zata mana tsauri nasani,
anma its a matter of time ohk i love u nd
sorry again abt jiya danace miki naje gydan
wata amal, gosh ba ita naso gani ba sai
kyawawan fuskanki " tsaki taja, donharta
fara tunani saikuma ta tuna ashe ba ita amal
din yake nufi ba, tsaki taja ta tashi tayi
alwala, anan talura ashe txt dinsan ne
yatasheta kasancewar kullum dakanta take
tashi gashi batada nisan bacci, bayan tayi
sallah quraninta tadauko takaranta,ta idar
tana addua ta tsinci kanta da adduan Allah
yabata saurayi mai kula da budurwa irin
wannan bawan Allahn, gashi batasan
sunansa ba, dasafe sunyi wanka sunyi shiri
tsaf, faiqa sai surutu takeyi, yau ban gaysa
da swty naba barin kunna whatsapp dina,
adaidai lokacin amal tadauki wayanta
saidata dauki wayan kuma saita fara tunanin
metakeson dubawa aikuwa adaidai nan txt
yashigo,
"Babyna nasan kintashi yanzu, nima gani
nayi wanka, zanje shago a kasuwa
inasiyarda doya ne a kasuwan mata, ina
anguwan arawa, kinga da dan rata kadan
kuma gashi da kafa zanje, anma badamuwa
Allah zai kawo mana mai albarka, baby na i
love u bye"
Shiru tayi saikuma ta tsinci kanta da
tambayan faiqa distance tsakanin kasuwan
mata da arawa, ke bawani nisa, amal tace
da kafa fa, faiqa ta kalleta tohfa da kafa
mutum daga arawa yaje kasuwan mata?
Inaa da nisa, kece zaki ko waye? Amal bata
bada amsaba hakan yasa tace aw mai jirgi
ne? Amal dai batace komaiba, tashi tayi
tabar gun, daki taje itakam waye wannan
bawan Allah? Meyakeso da ita? Ba ita yake
nema ba anma message sai yana turo
mata? Yakamata ta tsayar masa yakamata
ta gayamasa saboda karyaje yayita kuskure,
dare dare tana zaune saigashi yayi txt,
"babina ganinan zuwa gidanku, love u, plx
baby kisamin gyale i love it sosai, sainazo,,"
itakam haushi taji saiwani gun kuma taji
dadi atleast inyaje yagane ba ita bane zai
hakura ai yadena tura mata wannan txt din,
suna kallo maigadi ya leko yace ana neman
amal gabanta ne yafadi, toh yau kuma
wayene? Saida faiqa ta tambaya mota ko
jirgi yace jirgi mutumin jiya ne, dasauri amal
tamike da hijabinta harta fita kofa saita
koma taje tadauko gyalent tayafa, taga kanta
a madubi sannan tafito, yana tsaye kamar
yadda ta tsinceshi jiya
takarasa hannunta a kugu alamun
zatayi tsigala da matsifa, ya kalleta yadan
bata rai, bake amal dinba, dayan amal din
nace miki, tace ainasani, gydan nnan amal
dayane sai mutum daya faiqa anma barin
kira maka ita kaganta, tashiga tare da cewa
faiqa daallah zoki ga abu, faiqa dakyar tafito
acewarta batason raini kuma ita bata
tsayawa da masu jirgi, tana isowa gabanshi
takaleshi tana yamutsa fuska, tace kai gydan
nan amal daya ne, infact anguwannan gwara
kaja tsamin jikinka kafita kafin ranka yabaci,
tajuya tatafi amal ta kalleshi tace dafatan
kaji? Sannan plx karka karamin txt am done
wit u,, tajuya zata tafi yace alfarma plx tace
meye, kitaimaka min nasamu amal wlh
zanmutu inbansameta ba, tace awh haba?
Yace dagaske tace toh jirani ina zuwa
tashiga ciki tadauko piya piya da teaspoon,
tace ungo rike, yakarba tace inace
inbakasamu amal bane zaka mutu? Yace ae,
sannan ko kaina tace na kashe zan kashe,
tace gud, kafin tasa ka kashe kanka tunda
baka sameta kurba wannan, piya piya ne
muga ko haukan naka dayawa yake, yakarba
tazuba masa, a tunaninta zataga ya zubar
ko ya mata duka ko ya koreta anma inaa
saitaga bawan Allah yakurba kafin yakarasa
da gudu ta tunkude cokalin tare da karaa
tana cewa bakada hankali ne? Maigadi ne
yashigo da gudu alokacin fahad yafara rike
makgwokoro , karan da amal tayi yasa faiqa
tafito don ganin meke faruwa ganin mutum
zai mutu musu a tsakar gyda gashi
mamanta batanan yasa taje dagudu taja
amal, alokacin wayansa yayi kara dasauri
maigasi yadauka yayi kwatancen gydan,faisal
ne yazo a mota dasauri ya daukeshi sai
asibti, anan aka bar amal da faiqa wanda
faiqa tace suyi shiru karsu fadawa gwaggo
inta dawo, har maigadi anja masa kunne,
anma me? Ba daga nan bane, amal ta rude
saikuka hankalinta yatashi daki taje tarinka
sallah tana addua, ta cuci bawan Allah,
itakam meye mazauninta? Kisa? inya mutu
fa?
Faisal na salati ya isa asibiti dasauri aka
karbeshi ganin ansan dan gydan waye,
dasauri yakira hajiya saigata tazo anhana
motsi kwakkwara a asibitin, hajiya kuka
take, duk da faisal yaboye asalin meya faru,
gudun karya fadi gaskiya hajiya zata iyasa a
daure amal da duk wani wanda ke cikin
gydan kuma fahad bazai yafe masa ba, inhar
yafarka, donhaka sai yace mata baisan meke
faruwa ba adakinshi yazo yasameshi haka,
likita yatavbatar masa da yasha piya piya ,
faisal yace hajiya dakina ba piya piya ta iya
yiwuwa yaci wano abu ne daya kunshi
hakan, hakan yasa ta yadda don tayi imani
da Allah faisal bazai taba cutan mata da ba
koda kuwa da ransa ne, hakan yasa duk
kuka take, lokacin daya farfado idonsa na
kuka tace fahad mekaci? Dad dinka na
hanya, yace babu mom, hawaye ne ke zuba
a idonshi, yace mom ki kiramin faisal zanyi
magana dashi data kirashi saita tsaya awaje,
alokacin faisal ya turnuke fuska, dix wasnt
our plan, kana tsammani zamusha ne? Inta
gane angayama bazaka jawowa amal tashin
hankali bane, kasan daban kiraba su
zaanema awayanka kam, meya kaika? Kana
haukane mace zata sa maka abu kayi kuma
kayi? Shiru yayi da matsifanshi dayaga
tabbas kuka fahad keyi budan bakinshi
kawsi yace "faisal inason amal, zan iya
mutuwa idan narasata, faisal yace den stop
being a coward, yazaayi kana boye
soyayyan, cemska nayi kaboye identity ba
kankaba, yace zanfada mata, yaushe zaa
sallamen? Ya harareshi wannan kuma banda
idea,
Amal haka asuba yayi idonta wayam, takira
wayansa faisal yace suna asibiti anma ta
bukaci tasan sunan asibitin yahana, dazata
kashe wayan tace don Allah malam, bansan
sunan. Mai wayan ba, faisal yace FAHAD, ya
kashe, amal gagara sauke wayan tayi
akunnenta, sunan saurayin da faiqa take
mutuwa akai, toh anma wancan dan gwanna
ne, wannan kuma aiki yake, sannan kuma ai
faiqan taganshi toh bashi bane , anma
itakam tarasa meyasa ya kwanta mata arai,
lallaikam zatayi son maso wani, yanason
wata amal ita tananan, kuma daga gani son
dayakewa wancan bakadanba tunda har piya
piya yasha akan maganan, wayyo ita,
meyasa bata fara son wani a kauye ba,
dahakn bai faruba, gashi tafara son maso
wani, radadi takeji a ranta itakam yagama
da rayuwanta, feautures dinsa ne suke dawo
mata, wayyo ita!,
Fahad ne yadaga hankalinsa sai ansallamesa
Allah yataimaka sunbashi madara yayita
amai gakuma allurai dazasu resisting piya
piyan, randa yakoma gyda 364 missed calls
yagani, ga messages 64 , duk na amal ya
tambayi faisal yace nagaji ne da dauka evr
minuite take kira sai kawai nasa wayan a
silent, gashi zata kashe ma b3, daya bayan
daya yabi yakaranta messages din dukka
hakuri take bayarwa cike da mass fstan
sauki, fahad yayi murmushi sannan yace
abokina shan piya piya yamin amfani, i think
shes begining to like me, wow, ya rungume
faisal, faisal tsugit ya tsaya kallonsa lalle
abokinsa is sick
baigama murnansa saigashi takira
dasauri hannu na bari ya dauka, tayi sallama
da muryanta mai dadin sauraro ya amsa,
nan tafara basa hakuri akan ba dagangan
tayiba, sannan tace yayi hakuri bata samu
inane gydansu amal ba, ta bincika anma
bakanta yayi murmushi sannan yace xaki
tayani nemanta? Yace ae, tace toh shikenan
zanxo gyda sai muje nemantan, batace komi
ba takashe wayan tunani yakeyi shikam
yama zaayi ne yanzu? Nan ya bugi faisal zo
muhada plan, kaga nace zamuje neman
gydansu amal toh ga yadda zamuyi idan
naje gydansu zamu fito da kafa don nema,
nasan anguwan ko ya zamu tambaya
bawanda zai sani sabida ba amal agun, kai
zaka ajiye motan ka can da nisa saikazo
wucewa ill pretend bansanka ba daganan na
tambayeka kasan gydansu amal? Akwai
wani guess house agun na baba zanje nasa
yanzu ayi decorating sosai yadda zamuyi
having lunch nd daganan nafada mata, tunda
gurin is an open place basai nakarbo
mukullin gydanba ta tsakar gydan wajema
yayi, faisal tsuruu yayi yana kallonsa, karfe
biyar na yamma ya shirya tsaf faisal ya ajiye
fahad sannan shikumA yakaraso kofan
gydansu amal yayi sallama sannan suka
gaysa da maigadin yace yakira mishi amal
bayan yadawo yadauki dubu biyar yabashi,
baba yarinka godiya shikuma yamasa
alamun yayi shiru kar amal taji tagane
yamasa kyauta, anma yayi latti saboda tana
sanye da dogon riga ta yafa gyalen kansu
tayi tare da gaida maigadi sannan tace muje,
suna tafiya ahankali anma kowa da abunda
yake sakawa, itakam tanaso taga wacce
amal ce,wanda fahad zai iya komi akanta,
can ya nisa sannan yace, kinganni hauka
hauka ko? Tayi murmushi sannan yace
balaifina bane, anma idan kina soyayya zaki
gane mai nake nufi, ta gyada kai sannan
tace bantaba soyayya bansan yatake ba,
suna tafiyan saiga faisal yazo wucewa kamar
yadda suka tsara, dasauri fahad yace
salamu alaikum malam ina wuni bayan sun
gaysa yatambayi faisal inane gydansu amal
wata doguwa, mai dara daran ido, tanada
dimple haka da wushirya, da tawadan Allah
agefen kumatunta, faisal yayi dariya ooooo,
amal sarauniya can kwanan zakayi gyda
nafarko ne nasu, yayi godiya suka wuce,
amal kuwa tsulum ta tsaya duk abinda
yafada duk kwatancenta kenan, toh does dat
means itada wancan amal din suna kama?
No wonder shiyasa aketa musu kwatancen
gydansu anga suna kama, suka isa suka
buga gate din maigadi yabude sannan yace
sannunku, wakuke nema fahad yace amal,
maigadi yabude suka shiga, table suka gani
a tsakar gydan an tsarashi da kayan alatu,
ga wuta dew akunna abun gwanin shaawa,
kan table din fahad yanufa yazauna cikin
kwanciyan hankali
yayinda amal kuwa dasauri tace kazo
kaga abun mutane ka dale kazauna ka
sauka kafin azo adaureni nida kai,yayi dariya
sannan yace kizauna, ta tsaya tsum taki
zama sai wai waye takeyi, dakarfi yace nace
kizauna!, ta tsorata sosai hakan yasa
tazauna nantafara tunanu ko ya saceta ne
don alamun gydan yanuna bakowa aciki
shikenan tadebo ruwan dafa kanta, wayanta
ta ciro da zummar takira faiqa anma tuni
yakarba ya tsareta da ido , takaleshi takawar
dakai sannan tace banason wannan kallon,
yace saboda yana daga miki hankali ko? ,
takalleshi sannan tace Allah ya sauwaka,
yazaayi fuskan bako yazama kuma
yadagamin hankali, yace saboda sune suka
hanaki bacci da bakon baida lfy, tace luk
karka mayar dashi awanu abu, its just
caring, yace yes i knw, amal bakisan ko
niwaye ba, bakisan watannin danayi inabinki
ba, bakisan menasani akanki ba, tadaga
masa hannu sannan tace malam, ba abinda
kasani akaina, yace ohk tom naji, mikewa
tayi zata fita, tanacewa i dnt knw ya akayi
nabiyoka so useless ba amfanin zuwa,
bakada aikinyi bakasan meke maka ciwo
ba,tana tafiya dayawani fincikota juyawan
dazatayi taga ya damki hannunta idonshi
yayi jaa, kana ganinsa kaga wanda soyayya
take wahalarwa, yace amal haka kike gani
bansan menake ba, anma na yadda bansan
menake ba, sonki zai kasheni, zaimin illa,
wata nawa ina binki, amal dole kiyadda i
love u , ta finciki hannunta, kayi kuskure try
d next door bani amal kake nemaba wata
amal kake nema, yace toh ae zai iya yiwuwa
nayi kuskure anma kigayamin. Wacece amal
usman kaddo, tana govt sec skuk dukku,
shekaranta ,16_17 mahaifinta yarasu tun
tana karama, tana zaune da iyayenta, taci
gasan da akayi na gari sannan aka zo tayi
na qurani, tazo hutu gun yar mamanta nan
sati uku zata koma, batada saurayi bata
taba soyayya ba, idonta fal cike da hawaye,
yace amal inasonki, bansan yazan iya
gayamiki ba, plx ki amincemin, amal nasan
kema kina sona plx ki yardamin, tace naji
kabari nayi tunani, nan tadauki jakanta da
wayanta yabiyota abaya hartashige gyda
batace uffanba, haushin kanshi yaji ganin
yasa amal kuka, amal nashiga tafada kan
gado kuka takeyi sosai, wanda faiqa tazo
tasameta tagayamata meke faruwa, faiqa
tace kekuma sonss kike ko? Bazaki hakura
dashi kibari ki auri maikudi ba ko?* nikam
whatever it is fahad nanan memet, nidashi,
fahad na isa gyda yaga mahaifiyarsa a tsaye
tana jiransa, fahad sau nawa zangayama
inbakada lafiya kadena fita, yace comon
mum naje ganin amal ne, tace ohk tom
yatake? Yace lfy tana gaysheku, amal dinnan
yar gydan wacece plx? Yayi shiru sannan
yace bakowa, babanta bakowa bane, yama
rasu,tace bangane bakowa ba, to i mean
family name dinsu, yace mooom ba yarnan
bace yar dukku ce, saida cup din dayake
hannunta ya sulalo yafadi, fahad are u
stupid? Yanmata nawa ke binka kana
bouncasu? Yayan manya? Shine zakaje
kauye ? For God sake m disappointed in u,
yace mom kigama mitanki anma dolene na
auri amal, tace zamu gani, kowacece ko yar
gydan wacece kafin ka aureta zan dana wa
iyayenta warning , yasan mahaifiyarsa sarai
kadan daga cikin aikinta tasa anemo amal,
yadda bayaso amal tagane wayeshi yanzu
babu yadda zaayi arusa masa plan, yace
mom idan kika gwada wannan kuskuren
kisani cewa kinrasani har abada, wlh idan
aka hanani auren amal kece, kuma innabar
kasannan bazaku kara ganiba, shiru tayi
saboda tunda tske dantan baitaba mata irin
wannan kalamun ba, kana ganin idonsa kaga
yana makahon so
hakan yasa jikinta yayi sanyi, tare da
tunanin mezatace wa mahaifinsa, lalle yaron
ya bata tsoro inba tasan shiba kuma yana
gabanta zatace ba dan data haifa bane,
tamike tsum tafice tabarshi, ranan baiyi
bacciba yana tunanin ya amal zatayi ko tayi
reacting idan tasan asalin identity dinsa,
gashi mahaifiyarsa tana kokari karya masa
mission dinsa, donhaka ya mike yayo alwala
yayi sallah for the first time a rayuwansa da
wani abu yashiga masa duhu, yayi tunanin
yakai karan abun gun Allah, amal kuwa ta
kwanta bayan tagama karatun quraninta
tunaninta daya, yanzu yazatayi idan takoma
kauyensu? Yazatayi da ranta? Gashi tafara
sonsa faiqa. Ce ta kunna wakan dorobucci
sai tikan rawa take, amal tarasa ina zatasa
kanta, hawaye ne yafara zubo mata,adaidai
lokacin taga xt yashigo wayanta,
"Amal rayuwata tana cikin hatsari idan baki
amince wa soyayyata ba, inasonki zan iya
bada numfashina akanki"
Amal takara rikicewa itakam batasan
yazatayiba, ahaka bacci ya kwasheta,
washegari dasafe tana tashi taga wani mrn
message din, shima duk jaddada sonshi
yakeyi agareta, hakan ya tsumata sosai , duk
yadda fahad yayi yakara zuwa gunta taki
yadda shikuma bai sata doleba donma yana
tsoron zuwa gunta kar momy tasa ayi
tracing dinsa akaita gun amal tamusu wani
abu,
ahaka har amal takarasa hutunta ran
jumaa dasafe tafara shiri akan zata tafi
dayamma ran monday zasu koma
makaranta, hakan yasa tamishi txt akan
yazo suyi sallama itakam zata koma
kauyensu, hakan yasa dasauri yatashi don
yashirya yazo, dama har wannan lokacin
bawani shiri sukeyi da faiqa ba, gashi faiqa
da fahad na kulata ta whatsapp yanxukam
ma blocking dinta yayi tarasa yazatayi, waya
ma yasata a reject list hakan yasa tayi
tunanin takirashi dawayan amal, tana dauka
tayi dialing numba dama ta haddace, aikuwa
tana dialing taga fahad abun yamata
banbara qwai, takara dialing taga hakanne,
hakan yasa ta ajiye wayan tafito falo inda
amal ke zaune tare da cemata dama ke
makira ne bansaniba? Kin zauna kindauki
numban fahad kinsa awayanki, donkema ki
auresa ko? Shine shikuma munafiki harda
blocking dina baisan gyda daya muke
dashiba to yau karyanku yakare, taja amal
sukaje daki tadauki wayan tareda bata waye
wannan? Amal ta kalleta sannan tace shine
wanda kika tsana, wanda kike cewa karnaso,
shiri faiqa tayi can tace kut, toh bahaka
yskeba, asalinshi dan gwamna ne yacanja
miki kammani ne, fita daga dakin tayi
magsnan faiqa nadawo mata kai, no wonder
tafiyansa, maganansa, yanayinsa kaga na
masu kudi wanda suke cikin hutu, sannan
infact komai nasa daban ne, wani bakin ciki
taji, toh meye amfanin haka?, yanaso ya
gwadata ko meye? Adaidai nan maigadi
yace ana sallama da amal, kafin tamike har
faiqa ta fita,amal tabita a sannu sannan ta
tsaya agabanshi, yana sanye da kananun
kaya, sai alokacin ta kare masa ksllo, tabbas
gaskiyan faiqa ne, duk cikinsa alamun hutu
ne, hatta kayan jikinsa zakasan wanda taci
ubanta da kudi ne, faiqa gagara magana tayi
sai kallonsa take kaman zata hadiyesa
tabbas shine, ya akayi ds bata ganeshiba,
kodan bata taba tsammani zaikai hakaba,
can saitace fahad sunana kafin takarasa
yace faiqa, luk nayi blicking ne saboda ki
hakura dani, anma baikamata ki daukomin
amal ba, amal idonta yacika da hawaye tace
"azatona nayi saka da soyyanka nayi dinki,
azatona nayi gini azuciyanka da soyyaya,
azatona ruwan sama natara a roban
soyyayata saboda inzakaji kishi na baka
kasha, fahad ashe duk ginin danakeyi ka
ginashi akan karya, ga ci amanan soyyanmu,
idonsa na hawaye yace
32 PM] adda bena: 2 0 amal
karkiga laifina, sonki ne yajawo haka, ban
boye miki don na gwada miki ba, tsorona kar
ace kin gujeni, anma kiyi hkr, idonta jajur
tace kafita daga hidimata kayi assuming
bansanka ba baka sanniba, tajuya takoma
cikin gyda alokacin faiqa ta matsa da
zummar tamishi magana ko kallonta baiyiba
yajuya yatafi, faditayi agun tana kuka,
wannan wani irin bakin ciki ne?,mintsinin
kanta tayi tayi saboda in mafarki takeyi
tafarka anma bata motsaba, hakan yasata
kuka sosai, Allah sarki son maso wani, a
yamman ranan amal tashirya tsaf ta koma
kauye, duk da tana takure tacanja gaba daya
tayi sanyi dayawa, kullum zaka ganta a
takune, rike da quraninta, donma tarike
qurani da baasan mezai sameta ba, ahaka
suka koma makaranta tasiya duk abinda
yakamata sannan tacigaba da xuwa, yanzu
sun shiga aji shida hakan yasata karatu
faafaa koyaushe atakure ga fahad yaki fita
akanta, watarana tana aji malaminsu yazo
yace tazo ana nemanta, tafito gabsn aji taga
motocci hakan yasa taji gabanta yafadi
batayi tunanin suwaye ba taje gefen malamin
tare da tambayansa , malamin yace fahad
aliyu dan gydan gov shine yace anemo masa
ke, donhaka kije yanacan office din, gabanta
nafadi taje tashiga yana zaune sanye da
glass irin no respect dinnan yacire alokacin
suka hada ido, idonshi yayi jaa ya kumbura
kaman bashiba, saida taji zuciyanta yabuga,
yawani bushe yace amal kenan, zanbaki
lambar yabo a matsayinki na mace tafarko
data tsba hanani bacci da cin abinci, sannan
mace tafarko data sani kuka, ko kallonshi
batayiba nanfa yafara surutai wani abunma
batajin meyake fada, anma tasan cewa sarai
maganganu da sumbatu skan sonta yake ,
can kuma sai yafara kuka, hakan yasa tace
kayiwa girman Allah kafita hidimata, ina
zaman zamana da iyayena kar kaja mana
matsala, fahad inbanda kai da rawar ido , ina
kai ina ni? Donhaka kafita hidimata karka
sani acikin matsala, yaji haushi sosai
donhaka yabuga bencin dakarfi don saida ta
tsorata sannan yace, inagayamiki sako daga
zuciya anma kinamin wasu magana mara
manaa, takalleshi sosai, yadda ta tsareshi
yasa dole saidaya sunkuyar dakai, sannan
tace nida kai munsan waye mai magana
marar maana, kafita rayuwata nahuta, karka
takuramin, kuka tafarayi dasauri tabar office
din sannan tanufi bayan skul din, anan
tazauna taci kukanta. Biyota yayi hakan
yasa tace karabu dani bansonka, tunda yake
baitabajin munannen kalma, data daga mishi
hankali irin wannan ba,yace kinmene? Tace
na tsaneka, kafita rayuwata, harta shiga
gyda baidaaina kallonta ba, hawayen idonsa
ne suka zubo hakan yasa ysmayar da glass
dinsa yatoshe sannan yafita sallama da
principal din kafin yawuce,, yana hanya basu
karasa garin gombe ba yafars aman jini,
nanfa dasauri direban suka wuce dashi
asibiti sa,nnan suka kira mom dinshi tabbas
fahad yafita daga hayyacinsa dan har
oxygen ansa masa, momy kam kuka take
aganinta laifinsu amal ne, hakan yasa ta
umurce kanwarta fadila da ta harzarta taje
gydansu fahad. Tana isa tamata kwatance
sannan tace taje gydan su amal, tana shiga
gydan amal na zaune tsabar tskaicin abinda
tsyi da kyar takai loman tuwo abakinta
adaidai lokacin fadila tashigo, suna gaysawa
da innar amal, sannan tace nazone na isar
da sako, amal ta gyra zama anan fadila
tajata da lbrn fahad anma inaa amal ta
tsume tahada kai bansanshiba
fadila tace dakinsanshi dabaki sanshiba,
sako daga mahaifiyarsa kizabi daga naira
daya xuwa milyan goma ko nawa kikeso
zaabaki, kifiya harkar fahad, inbahaka ba
kinasa rayuwar mahaifiyarki dakuma naki ne
a hatsari, naji ance mahaifinki ya rasu, amal
ta kalleta sannan tace "kudinki yayi kadan
yasiya soyayyar danakewa fahad, sannan
baku da kudin dazaku siya wannan
soyayyan, inkuma maganar inbar muku
danku ne, naga bani nadauki kafa nabiyoshi
ba, donhaka dazaki taimakamin dakin isar
masa da sakona, kice mishi yafita hidimata
da harkata, idan baiji abunda nafada
mishiba, fadila tabude baki lallai yarinyan
nan baki da kunya aikuwa in ina raye bazaki
taba zuwa gydanmu da sunan aureba, amal
tace Allah sauwaka, inani ina gydan da
baasan mutumcin dan adam ba, fadila tafice
tabarta, tana isa takunnna wa momy
recordern datayi recoedrn, momy tace lallai
yarinyannan batasan dawa take ja ba, anma
fadila na tambayeki tanada kyau ne? Fadila
tayi shiru sannan tace gaskiya momy
tanadashi kuma tanada shiga rai, kuma kina
ganinta kinga mai confidence ,momy tadaga
mata hannu sannan tace ya isa haka joh,
saikace nace kifadamin dukka wannan
surutun,a lokacin aka basu daman ganin
fahad, yana farkawa yafara musu surutan
amal, momy takunna masa audio yaji yace
momy wlh nakara sonta, momy i love her,
alokacin tafara tsorata kodai dantan yayi
hauka ne, donhaka tabugawa maigirma
gwamna tareda cemasa yasa anemawa
fahad ticket ko dubai yatafi suhuta, hakan
kuwa akayi satinsa daya aka sallamosa, tuni
suka daukeshi suka kaishi dubai wai yahuta
yasan sarai abunda yasa sukayi hakan,
donhaka dasuka kaishi bayan kwana biyu
yahau jirgi yadawo abunsa, sai dukku
yanufa,
Amal nasharan tsakar gyda wani yaro yazo
yace ana sallama da ita, tace kace bananan
can yakoma yadawo yace wai acemiki fahad
aliyu ne, yana fita tabi sawunshi ganinshi
bakaramin dadi tajiba saidai tabata rai,
mekazo yimana anan? Ko ka kawo yan
gydanku ne sukasheni da mahaifiyata?
Hawaye nazuba a idonsa yace nazo baki
hakuri ne amal, amal inasonki, kitaimaka plx,
tace kadubi girman iyayenka kabar nan
innata intazo ranka zaibaci, tashige tabarshi
zaune agun, sallaya yadauko yashimfida
abunsa, alokacin yakira faisal yana
gayamasa faisal nan da nan yafara masa
fada, anma sanin halin da abokinsan yake
ciki yasa ya hakura yafara bashi hkr akan ya
hakura da ita, jin wannan kslman yasa fahad
yakashe wayansa ya balla sim din, adaidai
lokacin inna tadawo tazo shiga taga mutum
zaune a kofar zaure kana gani dai kasan ba
almajiri bane, tunda gashi fes fes yaro
kaman balarabe, yamike dasauri yagaysheta
ta amsa sannan yacr yazo gunta hakan yasa
tace yabita, amal na kicin tana tikan kukan
abinda ta tursasa zuciyanta ta aikata, domin
tanemawa uwarta da kanta mutunci taji
shigowarsu dasauri tashare idonta tare da
cewa mekuma kadaeoyi, inna ta daga mata
hannu ba gunki yazo ba, ki koma kici gaba
da aikinki, yana zsune ya zayyane ma inna
dalilonsa dakuma abinda ke faruwa, inna
tace amal na nema makanta mutunci ne,
donhaka kayi hkr, idan matarka ce zaka
aureta, anma yanzu kabi umarnin iyayenka,
bayason musu da inna hakan yasa yafita
idonshi jajur, yana tafiya jiri na dibansa,
harya fadi kasa, mutanen dake gurin ne suka
taimaka aka kaishi asibiti, anan wani
yaganeshi ya bigawa principal na
makarantansu amal waya, yana zuwa
yaganshi bashiri yakira p.A na gov akan gafa
fahad a asibitin dukku, abu kaman almara
momy harta musanta anma daga ita har
dady hankalinsu yatashi dasuka kira
wayanshi shiru, anan suka faisal aikuwa
yagayamusu cewa fahad na dukku ba shiri
saiga motocci sunzo aka kwasheshi sai
garin gombe, momy sai tafiya take a asibiti
tunaninta wani mataki zata dauka akansu
amal
bata idar da tunaninta ba. Sai ga mai
girma gov ya iso hankalinsa atashe, sannan
yace arasa wazaa wulakanta sai da na?, ina
likita? Likitan nazuwa gov yabasa umarnin
yafada masa meke damun dansa, nanfa
akace masa hawan jini ne, ke
damunsa,sannan inbaa san nayiba zai iya
rasa ransa, tsawa momy tamar tare dacewa
yazaayi kana barazan da rayuwar dana
agabana, katabbata kayi komi dazai sauka
masa, kafin mu isa u.s yanzu mun karbo
tickets, likitan ya kalleta sannan yace bazasu
karbe shiba, i mean jirgin bazasuyi risking
ba, jikinsa ba sauki fa, kuka momy tasaka,
saidana gaya wa yaronnan yahakura da
yarinyan, inashi ina yar talaka, alokacin
talura ashe gwamna kam yabar cikin asibitin
duk hankalinsa atashe, duk an tsagaita
mutane anhanasu sakat,
A can dukku kuwa wasune suka zo a mota
basu finciki kowa ba sai amal acewarsu
order ce daga matan gwamna, inna na kuka
anma batada gata, kowa sai tausayinta
yake, wasu kuma na madalla kasan abu yafi
karfinka anma karike inbahakaba ina amal
ina fahad?, wani daki akakai amal aka danne
hannayenta aka daureta saikuma suka
zaunar da ita, kafanta suka daura akan
kankara, jikinta nabari bakinta ma haka, can
suka jona hannunta da electric waya yadda
wayan ke jan hannunta wani kara tasaka,
tana cewa wayyooo fahaddd!!!!###adaidai
lokacin ya farga ido daga gadon asibiti
dakarfi yatashi akan gadon ya fisge calulan
dake hannunsa kasancewar bakowa adakin
likitan ya umurci kowa daya tsaya awaje,
gabansa yaji yana fadi, tabbas amal na cikin
tashin hankali, bude kofan yayi kenan yaga
momynsa tana zaune, zai wuceta ta kwala
masa kira anma sauri yakeyi, guardman din
momynsa ce ta fizgo shi tare da magana wa
sauran guard din suka shigo suka rikeshi
yana matsifa kusakeni nace! You are fired!
Kunbar aikinku daga yau, kusakeni amal
nacikin tashin hankali plx kutaimaken
alokacin sun direshi akan gado sannan
likitan dakyar ya masa alluran bacci, momy
kam tafara tsorata, adaidai nan akace suzo
su tafi a private jet kawai, donhaka suka
sashi a mota suka nufi lawanti. Anan suka
wuce sai u.s
#amal kuwa duk wahala da azaba datake
shaa bayadda basuyi da ita tace tahakura
koda kuwa abakine anma amal taurin kai
haka suka gaji suka barta alokacin da momy
tace su saketa anma su tabbata sunsan
yadda sukayi suka canja mata location
gudun karsu dawo kuma hankalin fahad
yakara komawa kanta . Donhaka nema aka
nemawa amal da mamanta gyda agarin
kumo suka koma dazama, anma alokacin
amal tacanja don dama dakyar tagama waec
dinta kotakan result din batabiba
donhaka rayuwanta yacanja , daga amal
mai faraa xuwa amal marar faraa, rayuwanta
yadawo na takuri, wataran haka zata rufe
kanta adaki ta yita kuka, gashi dai gyda har
gyda dakomi anbasu duk don tarabu da
fahad, ita tarasa ya akayi haka tassn
basuwani shakuba anma tarasa meyasa
tagagara mantashi, gashi ya mantata yatafi
yabarta ashe cewa dayakeyi bazai rabu da
itaba karya ne, yaudaranta ne? Lalle tayi
dana sani, ranan da asuba ta tashi anma
inta kalli gydan sai tatuna da cewa ashe
zunxo garinne dan fahad, gydan su fahad ne
komi sanadin fahad wani bakin ciki ne yake
rufeta sai kuka takeyi duk tunaninta fahad,
batasan lokacin data fitaba tafiya kawai
takeyi batasan inda take tafiyaba, tayi nisa
akan titin, duk kuka takeyi tare da damkan
zuciyanta ko zuciyan ta zaifita, buge wani
tayi saidaya tsorata yace haba baiwar Allah
kiyi addua mana anma halin dakikasa kanki
kamar ba keba, komeyene ai hakuri akeyi,
zura mishi ido tayi, alokacin tatuna ashe
bakin ciki zai iyasa tamanta da Allahnta? Ko
sallah batayiba tafiti? Innalilahi wainna ilaihi
rajiun, anan tajuya da zummar takoma gyda
ko zatayi sallah, sai istighfari takeyi, aikuwa
batayi kwakkwaran juyawa ba, wani mota
yana tandal akan hanya alamum mai tukin
yasamu matsala kanta yayiyo mezatayi inba
salati ba, aikuwa ji kuke kiiii yahau kanta
dasauri yafito don taimakonta alokacin
wannan mutumin zai dawo kawai yaga
yarinyan dayayi waazi ankade dagudu yaje
yataya mai motan suka shigar da ita,
sannan mai motan cikin tashin hankali yace
don Allah zanmayar da ita cikin gari don
Allah kasanar da iyayenta insuna nemanta,
anma yar wacce gari ne? Mutumin yace
daga kumo tafito yace zandawo da ita insha
Allah, bari muje dayaja motan ya fizga
dagudu ,
#inna kuwa tafito bataga amal ba anma sai
tayi tsammani ko tashiga bandaki ganin gari
yafara wayewa yasa tasan amal bata gydan,
dasauri tafito tana kuka, duk innar ma
tarame sanadin tashin hankalin da yartan ke
ciki, gawani tashin hankali salati takeyi
tanata cikiyar amal anma ba amal ba
kammaninta,
#######acan u s kuma sunsamu dakyar an
ceto ran fahad, anma likitan ya umurcesu
dasuyiwa yaro abinda ransa keso , momy ce
tabada shawaran suzauna agurin suyi
atleast wata ko biyu ne kafinnan ya manta
da ita, alokacin fahad kuwa baya gane abu
yadawo kaman mahaukaci mahaukaci, hatta
momynsa da amal yake kiranta
asibitin daya kaita dasauri suka karbeta
ganin sunsansa sosai, hankalinsa atashe ,
bai nutsa ba saida nurse din tafito tace
masa yaje likita na nemansa, anan likitan
yake gayamasa matsala ne babba tasamu
amal, domin kuwa acikin rashin kwanciyan
hankali ya kadeta, ga uwa uba yanzu tabuga
kanta sosai wanda zai iya sa tamanta kowa
dakuma rayuwanta na baya, saidai ahankali
tunanin nata zaidawo, hankalinsa tashi yayi
shikam yazaiyi daransa?, ganin hakane yasa
yaje yaja motarsa yanufi kumo, anan yayi
cikiyar mutumin saidai yayi mantuwa
baikarbi numban mutumin ko sunansa ba,
yanzu yazaiyi ya samosa? Hakan yasa
yashiga mota yakoma asibitin, awanta
takwas tana bacci, sai washegari ta samu ta
farfado, alokacin likitan yace masa hakuri
zakayi, yanzu kashiga kaduba ta, sannan ka
bita kaman jaririya batasan komi ba, yana
shiga ya tarar da ita a zaune, kanta ya
hargitse gata da yalwataccen gashi, tajuya
masa baya hakan yasa ya zauna agefen
gadon, tajuyo takalleshi, kallonta yakeyi
yarasa meyake tunani, yace yajikinki? Ta
kalleshi sannan ta gyda kai, hawaye ne
yafito mata, hakan yatayar masa da hankali
donhaka dasauri yakira likitan don aji meke
faruwa da ita, anma likitan ya gwada masa
cewa ya kwantar da hankalinsa ba abunda
zai faru, abinci yazuba mata tanaci tana
kallonshi, kamar wacce inkayi wa tsawa zata
fancama da gudu, yace sunana sadiq, but
frnds dina nacemin diqsa, kefa meye
sunanki? Ta gyada kai sannan tace diqsa
sadiq, ya tsura mata ido sannan yace
sunanki aliya kinji? Ta gyada kai, yace
yanzu insun sallameki zamu koma gyda, ta
daga kai sannan tace kai wayene? Yace ni
yayanki ne, sunana sadiq kinji? Kina cemin
yaya sadiq daga yauz ta daga kai, bayan
tacine, dare dare tana kwance ya shigo shida
mahaifiyarsa haj.uwani bayan tazauna
tausayin aliya ne yafadi mata sannan tace
sannu aliya, aliya takalleta ta wage hakori
sannan tace kema sannu, sadiq yace aliya
wannan mamane, sunanta momy, ta kalli
momyn sannan tace sannu momy,
Bayan sungama tazauna sai kallonsu take,
ta kalli momy takalli sadiq duk sai kallonsu
takez sukuwa abun yadaure musu kai, ahaka
momy tayi sallama ta tafi, inda aka kawo
mai musu girki ladi tazo ta kwana da ita,
Satin aliya daya a asibiti aka sallamesu, inda
ya dauketa yanufi gydansu dake g.r.a da ita
ya nuna mata dakin dazata zauna, dama tun
ran farko ya gayawa momynsa halin da
aliyan tashiga yaroketa ta taimaka tazauna
dasu kafin ta dawo hankalinta, kokuma kafin
ya binciko daga kauyensu amal
###innar amal kuka takeyi sosai ba dare ba
rana, inda mutumin da yaga lokacin da aka
tafi da amal ya bada sanarwan cewa yasan
inda take. Ko da innarsa tazo yamata
bayanin abunda yasani tareda cemata ta
kwantar da hankalinta amal zata bayanna ,
hakan yakara tada hankalin inna inda tace
ita lallai sai ankaita garin gombe taduba
yarta, anma ina bawanda ya yarda kowa
nabata hkrn cewa tayi hkr har adawo mata
da yarta, anma yau sati shiru, amal ina kike?
Kuka take sosai, gashi tarame ta jagube
5 a u.s kuwa dakyar da sudin goshi fahad
ya bar maganganun dayake daya lura
iyayensan basu daddara ba, sai ya gwada
musu yawarke kuma ya manta da ita,
yagwada musu bayason ayi maganar amal a
gabansa, hakanne yasa momy ta ce toh
sukara sati uku kafin sudawo, ya yarda
dahakan, agunsa kuwa sai addua yake Allah
ya kare masa amal ,
######amal kuwa tafara sabawa da momy
da yaaah sadiq dinta, hatta sallah saida aka
koya mata komai nata rayuwarta yacanju,
alokacin sadiq yaki xuwa kumo ya bada
cikiya ganin yadda mahaifiyarsa take cikin
farinciki kuma yafi shekaru baiganta
hakanba, donhaka duk lokacin data
tambayesa saiyace haryanzu shiru, amal
tasaba har fita tanayi suje kasuwa tare suje
yawo, tayi dinkuna sabbi, ya siya mata kaya
kala kala, komi da budurwa zata mallaka
yabata,
#a can kumo kuwa inna har ciwo yakamata
tarasa yazatayi tayi adduan tayi adduan
anma shiru, adduanta Allah yakare mata
yarta,
#yaune fahad da iyayensa zasu dawo nja,
donhaka Allah Allah yake su iso, aikuwa
suna isowa mota yashiga yanufo dukku,
anan aka basa lbrn amal sunkoma kumo,
zama yayi kam zaiyi hauka, wani mutumi ne
yace malam karka damu kumo bazata baka
wahala gurin neman taba, kaje Allah yabaka
saa, yazo zaitafi ne wata makwabciyarsu
amal tace malam gashi anguwansu amal din,
idan kaje bazai baka wahala ba, baisan
lokacin daya ciro bandir na dubu daya
yabataba, yaja mota batare da yaji metake
fadaba yanufi hanya, saidaya hau titi yatuna
ashe baisan inane kumon ba , yaga wani
yaro yadauko gyada akai yace yaro kasan
inane kumo? Yace ae, yace shiga muje
zandawo dakai, dake zaikai shekara 19
yasan meyakeyi yashiga bashiri sai kumo,
suna isa yaduba takardar bayan galadima
akasa, dasauri ya tsaya yakara daukan wani
sukaje , anan suka fara tambaya, amal da
inna , sunsha wuya kafin suka samu
kassncewar amal bakuwace agarin , anan
yashiga gydan da inna take yasamu batada
lafiya mutane suntaru, hakan yasa yace
asata amota sutafi asibiti, yana tuki harya
isa dukku ya ajiye wannan saurayin sannan
ya isa garin gombe, a asibiti aka kwantar da
ita yagagara tsugune balle tsaye, bayan
mintuna kadan likitan yabukaci yanemo
abinci dasauri ya nemi restaurant yashiga
yasiyo abinci yahada da kayan tea
dasauransu, anan akabawa inna taci da
allurai, fita yayi yaje yanemo faisal sukaje
nemo gyda batare da yagayamishi
mezaiyiba, yayi waya akasa furnitures,
dakomi har kayan abinci yasiyo kaya a san
hussien, faisal dai ido me nashi saida suka
gama sakomi sannan ya zauna a falon ya
shako wuyan faisal yace innar amal zansa
agydannan da amal, duk da bangantaba
nasan innarta tasa akaita wani wajene
saboda kar irinku su kasheta, wlh idan
kabari wani yasan dawannan maganan saina
kasheka tunda kaine munafikin daman, faisal
baice komi ba, alokacin suka koma asibitin
suka tarar da inna azaune, tana ganinsa
tahada rai, ya tsugunna yabata hkr tare da
gayamata abunda yafaru baigama ba yaga
itama tana kuka, alokacin tafara gayamasa
itama, tunda iyayenka suka nema mana wani
gyda amal batada kwanciyan hankali a
tunaninta kagudu kabarta, kullum sai kuka
batacin abinci ahaka wata safiya natashi
nanemeta narasata, ashe duk juyayin ka
yasa tana tafiya bata saniba mota yakadeta,
innalilahi wainna ilahi rajiun bata idda ba
suka sinci fahad agefe yarike zuciyansa yana
kokarin fadi duk da salatin dake yawo a
zuciyansa
faisal ne yamike yarikoshi tare da jingina
ajikin bango, dasauri yafita dan yakira dr.
Aikuwa take akabawa fahad gado, likitan
yayi niyyan kiran iyayen fahad anma faisal
ya gwada masa rashin dacewar haka, anma
kasancewar likitan nason samun matsayin
da yafida wato family dr. Saiya kira momy
aikuwa saigata a asibiti, faisal ya mugun
tsorata nan tace meya hanka kirana ? Yace
momy duk na rudene, anan tazauna tareda
cewa mekuma yafaru? Dakyar yassmu
yahada karyansa yace sunacin abinci ne
kawai yafara rike kirji, tayi tagumi alamun
damuwa aranta, sannan takira likitan tamishi
godiya tare da son sanin meke damun danta,
anan yace zuciyarsa ne dai labari bai canja
ba,anma dake yaga abun gaba keyi, yace
hajiya muhadu a office, tabishi tazauna tare
dacewa likita mekuma yafaru? Yace toh dai
gamunan, dalilin kiranki ma kenan, hajiya
don Allah inaga gwara kiyiwa yaron abunda
yakeso, don damuwa nacinshi kar azo ana
danasani, tayi shiru tace toh, yanzu amma
yajikinsan,? Yace dasauki zuciyar ce tabuga,
don Allah akiyayi wata bugawan inba hakaba
zai iya rasa ransa, jikinta sanyi yayi ahaka
harta koma, faisal kuwa yaje yasiya wa inna
komi dazata bukata da aka sallameta
yakaita gydan da fahad ya gwadamishi
sannan yace ta kwantar da hankalinta fahad
na tare da mamanshi daya kaita sun gaysa,
haka inna taci gaba da rokon Allah ya
bayyana mata yarta, anan nema taroki faisal
daya kaita gydan gwaggo asama inds
daganan gwaggo kullum itada faiqa suna
hanyan zuwa gun innan don debr mata
kewa, fahad kuwa da aka sallameshi yakoma
gyda ya guji kowa rayuwarsa takara
lalacewa duk wanda yasan fahad yassn
asalinsa bazaice. Shine ba yanzu duk ya
lalace, momy ce tazauna agefensa tare dace
masa yarona meke damunka? Mekakeso?
Yana kuka mai tsuma rai kaman yaro yace
momy inason amal, gashi innarta tace
tabata, moky ina zan ganta? Yakamata
mubada cikiya, tayi shiru duk taurin ranta
yanzu itakam tasauko da ta rasa ran danta
gwara tamishi duk abinda yakeso, nan tayita
bashi hkr tabashi lbrn abinda tasa ayiwa su
amal, haushinta yaji har ransa anma
mahaifiyarss ce bayadda ya iya, anan tace
zata gayawa dadynsa dama dadynsa baida
matsala itace ta tunzurashi yace bai yadda
ba, aikuwa adaren ranan daddynsa yadawo
daga u.s sunje wani conference nan ta
lallabashi akan maganan amal yakuwa
amince. Anan fa aka nemo hoton amal
akafara cikiya,
#can gydansu sadiqa kuwa momy na
karanta qurani amal tazo tazauna agefenta ,
tadauki dayan quranin tarike, kokarinta shine
takaranta, tazurawa quranin ido kaman zata
tuno wani abu, anma takasa, tarike sosai
tana kallo anma takasa, momy talura
donhaka tace kozan koyamiki ne? Amal ta
gyda kai sannan tace mata toh zomiyi,
aikuwa suna zama tafara karantawa amal
nabi, kanta ne taji na sarawa alamun
tanason tuna abu anma shiru , hakan yasa
tace momy kaina naciwo, ta kwanta, sadiq
ne yashigo yasamu hartayi bacci yakura
mata ido, yace momy naga ana cikiyanta a
tv, hankalinta atashe ta kalleshi , idonsa
yaciko da hawaye, tace toh yazamuyi? Dole
mu mayar da ita, ya girgiza kai sannan yace
momy kinsan ina sonta kema tunda tazo
gydan nan kinsamu farinciki da kwanciyan
hankali
anma momy yanzu murabu da ita
yazamuyi? Tace a a kam, dole takoma cikin
yanuwanta zaifi su da suka haifeta sunfimu
sonta, sannan ina gargadinka daka cire wata
aba so, saboda kana ganin yarinyannan
kasan akwai rikicin dayasa tabar gyda, infact
kawaifa kanemi mata ne, banason situation
azo ace kana wahala akan abu while basamu
zakayiba,yace toh momy idan tatashi saimu
tambayeta idan zataje tayadda saimu kaita
idan taki momy wlh mubarta Allah yagani
munfita kuma munada hujja, shiru tayi kawai
batace komiba tasan sadiq yanzu inyasa abu
aransa zatasha wahala fiyeda yadda tasha
abaya akanshi, amal daredare momy da
sadiq suka tiketa akan tafada musu ko zata
koma gyda iyayenta na nemanta, kuka
tafarayi wai ita sune iyayenta tayaya zaayi
suce zasu kaita wani guri hakan yasa sadiq
yaji dadj sosai,
#anyi cikiyan amal har angaji, fahad harda
gemu saida yatara, yayi sanyi sosai,yaron
dayatashi cikin gata shikadai agun iyayensa,
anma wai shine yau yadawo kaman bashiba
baa taba ganin dariyarsa, hakan yasa faisal
yake jansa suje yawo, smtyms yankari yake
janshi suje, anan yake samu yadan sake,
wani lokaci kuma gun innar amal ake zuwa
su tahira, tayita musu tadin amal, momy ma
saidatasa aka dauko mata inna suka gaisa,
ranar inna taji dadin karamcin dasuka mata,
anma abunku da bafulatani da riko ga rashin
mantuwa hakan baisa tamanta wulakancin
dasuka mata abaya ba wanda yayi sanadin
batar yarta, komi datake bukata suna mata,
dangin mahaifin amal ma wasu sun nuna
damuwa sa, yayin da wasu suna Allah wadai
aganinsu kwadayi ne yasa inna da amal
suka nanewa fahad,
#amal tayi wanka tashirya tsaf abunta
tadawo yar birni sosai yanzu tadan sake.
Sau dayawa inzatayi abu saitaso tuna
rayuwanta nabaya saikuma tagagara tunaea,
yau ma tadauko high hell zatahau, kanta ne
yasara taso tuna abu anma taji shiru, tahau
takalmin tafito, sadiq ma yafito yasha
shadda tace ina zamuje? Yace bauchi anma
zamu farabi ta yankari, tace tohm. Anan
suka shirya tsaf kowa yashiga mota sadiq
yafara jan motan harsuka isa yankari, taji
dadi sosai ganin dabobbi ga abubuwan
tarihi, sannan sukaje gurin ruwa taga maza
samari da yanmata kowadai na hutawa,
goran coke ne ahannunta tana tafiya tana
kalle kalle, tayi kyau sosai don glass ne a
fuskanta, tafiya take tana admiring ganyenki
datake gani, jitayi ance amal?? Bata amsa
ba anma tajuya, tana ganinshi kanta saidaya
buga, gabanta yafadi, tunaninta ya gushe,
cak ta tsaya batace komi ba, hannunsa yasa
yacire glass din, yashafa kumatunta kallonsa
takeyi tagagara motsi, hawaye shaar a
fuskansa,yace amal dama kina raye? Kika
barni cikin kunci?innarki tana nemanki?
Nima haka? Ina kika kai soyayyanmu? Amal
kibamsamin? Ta girgiza kai sunana aliya ne
ba amal ba, damkota yayi karyane, sunanki
amal usman kado, yar dukku, amal nine
fahad, masoyinki, amal kiyi hkr ba laifina
bane, iyayena, karkimin wannan hukunci
zaimin tsauri, innarki tana nemanki, fadi
zatayi yasa hannunsa yarikota adaidai
lokacin sadiq yanufo kanshi, me kakeyi akan
matata?, MATARKA??????????????
8 ya mutsukuta ya bugeshi kadan, fahad
ya tsaya ganin ikon Allah, ganin dayayi
tabbas fa amal ce kuma gashi zaa kara
guduwa masa da ita yasa yabisa da gudu,
tare dacewa tsaya, sadiq ya tsaya duk
hankalinsa yatashi adduaa yakeyi Allah yasa
ba dagaske bane, nadaman meya kawosu
yankari ne tadameshi, fahad alokacin faisal
yakaraso shima yana ganin amal ya zazzare
ido tre dacewa amal? Itakam abun yamata
yawa donhaka ta tashi daga rikon. Da sadiq
yamata, hawaye shagaf a idonta sannan tace
don Allah kuyi hkr kubarni, wayeni? Kuna
rudar min da kai, fahad kam ganin tana kuka
ne abun yadaga masa hankali donhaka yace
don Allah bawan Allah kazo muzauna muyi
magana da kyar sadiq ya zauna nan fahad
yakira innaa, yasa handsfree, yace inna ina
wuni nan ta amsa da faraa, anma muryanta
kanaji kasan yadushe akwai damuwa aciki,
sannan yace don Allah inna gawata kugaysa
tanajin lbrnki, tace toh, amal takarbi wayan
hannunta nabari tace hello? Havawa nanda
nan inna ta rikice amal? Yar nan? Ina kike?
Ina kika shiga? Saikuwa tafara kuka, amal
ma kukan take tace inna ina wuni, inna tace
amal kidawo kinji? Kibar damuwa, duk
abinda kikeso zanmikki, gaki ga fahad dinki
kiyi hkr kinji ko?, amal tace toh inna,nan
fahad yakarbi wayan bashiri inna tafara
godiya, dan nan bansan mexance maka ba,
Allah saka maka da alheri, ahaka yace inna
zamuxo gaba daya tace toh, nanfa yakira
mumynsa yace momy gani da amal , itama
cikin murna tace abata amal, amal takarba
suka gaysa itama taroketa ta taimaka
tadawo, bayan nannefa rikici ya tsoma sadiq
yace sai anje angayawa momynsa bazai bari
awuce da itaba,fahad kuma yace saidai
awuce, a karshe dai faisal ya lallabi fahad ya
hakura, suka dugunzuma sukaje gombe duk
saurin da akeyi fahad gani yake baa sauri,
dama gashi yaki shiga motansu yashiga
nasu amak gani yakeyi zaa canjawa amal
position,annanne suka dauki momy bayan
dogon bayani itama suka nufi gydan inna,
dama shikam fahad yakira momynsa yace
suhadu agydan inna, anan aka taru, inna
takira su faiqa da gwaggo saa, faida kam
harta hakura da fahad ganin irin yadda
hankalinsa yasauka akan amal itakam baza
ta iya irin wannan so maso wanin ba,
anan abudai yafara sadiq yayi narating
yadda yasamu amal inna tace hakkun haka
akayi angayamata saidai kuma bata karajin
duriyarshi ba, yabada labarin abunda likitan
yace dakuma irin zaman da sukayi, momy
tadaura daga inda ya tsaya, bayan sungama
ne sadiq yace wannan wahalan damukasha
ai yaci ace anbani ita a matsayin mata,
tsabar takaici fahad gagara magana yayi
wannan ma ai iskanci ne,faisal yayi dariya
anan yabasu labarin inda fah yafara ganin
amal da binciken dayayi akanta, da kyautan
dayazo yabata a haddansu,dakuma wayon
daya mata nazuwa gydansu faiqa dakuma
kwanciyan daya rinkayi a asibiti, har karshe ,
momynsa tadaura tana kuka ashe haka
danta yasha wahala takara masa wahala?
Nan tadaura tashin hankalin dasuka shiga a
u.s da wani turashi dubai da akayi yagudo
don amal. alokacin amal duk tunaninta
yadawo abun yabata mamaki bata taba
tsammani irin wannan soyayyan exist ba,
bayan momy tagama inna tadaura akan
yadda su momy sukayi dakuma wahalan
dasukasha a dukku dakuma yadda amal
tatafi, faiqa da gwaggo da momyn sadiq kam
aisai kuka , abun tausayi amal ma kukan
takeyi yanzu komi yadawo mata tatuna
abunda ya faru daddaya, wato rashin ganin
idon sani neyasa gaba daya tamanta da
abunda yasameta? Ko dama ciwon haka
yake yaxo yatafi? Anan momyn fahad
tabada hkr, sadiq kam ba bakin magana jin
wannan labari yadaga masa hankali dama
irin wannan soyayyan na existing?, anan
abinci da momy tace akawo daga govt
house ya iso, sukaci kowa da farinciki
momyn sadiq ne da sadiq hankalinsu yatashi
ganin zaa rabasu da amal. Anan inna talura
tace kubani aronta ko sati biyu tamin
daganan intanason zama agunku badamuwa,
fahad ne ya tsume don aganinsa zaa bawa
sadiq hanyane dama yayi soyayya da ita, ya
mutsuke yace a a inna taxauna agyda dai,
nanfa suka fara mishi dariya don sun gano
inda maganansa tanufa, haka dai aka lallaba
inna da amal sukayi saura bayan kowa
yatafi inna na rungume da amal tayi bacci a
zatonta kar amal takara guduwa, suna tafiya
gyda hankalin fahad ya kwanta, sai anan
yafarajin ciwon kai daya sabaji mai karfi,
gakuma gefen zuciyanshi saita dunkule,
ganin anga amal baikamata kuma yacigaba
dawasu kokekoke ba yasa yadauki kafansa
yayi asibiti, ranan likitan yasha mamaki,
fahad yagayamasa damuwansa nan likitan
yace ya kwanta adubashi, duk dahaka yace
yayi general scanning , yace yadawo
washegari, fahad yatafi anma da alamu
kowani ciwo ne yanacin jikinshi,
washegari ma yakara komawa, shikam
har abun ya damesa yace likita haryanzu
baku samo meke damuna dinva,? Likita yace
nasamo confirmation ne, nanfa sukayitayi
har kusan karfe 1 abu tun goma nasafe,
bayan sungama likitan ya bukaci dayaje
yaga oncologist, fahad batare da tunanin
komiba yaje, bayan sundawo ne likitan
yagaya masa meke damunsa, jikinsa a
sanyaye yafito, gyda yawuce yashiga
dakinsa yarufe tunda mahaifiyarsa tahaifesa
baitaba kuka irin wannan ba, yayi yagama
yayi addua yatashi yafito yanufi gydansu
amal yasamu tashirya taci kwaliyya, ga girki
tamasa yazauna yaci, bini bini ya kalleta,
tace masa meya sameka nekam?, ya yi
murmushi sannan yace watana shida
banganki ba ankina expecting karna kalleki?.
Tayi shiru, nanfa suka fara soyayyansu vabu
abinda yakai wannan farin ciki, anma taga
fahad yacanja yadawo wani iri tace
meyasameka ne? Yayi dariya yace gani
nakeyi kaman zamu kara rabuwa, tayi
murmushi sannan tace bazamu rabu ba, nan
tafara kwantar masa da hankali da
kalamunta masu dadi, saidare yatafi,
Ahaka amal ta watsake wataran takanje
gunsu sadiq wataran gydan innarta, har
gydan gwaggo asama tsna zuwa yanzu faiqa
dama tahakura rawan ido tasa agaba
inbanda tara samari babu abinda tayi amal
kuwa samarin suna zuwa anma bata kulasu,
nan tanemi admission a g.s.u tafara zuwa,
tasamu geology, nan tafara karatu gadan
gadan har lokacin fahad taga bai dago
maganan aureba, ko da momynsa tamasa
maganan cemata yayi momy ainafiki
matsuwa da aurennan ko, inashan maganine
malaria da typhoid yasani agaba gakuma
abubuwa danake handling innagama ai
zanmuku magana, kallonsa take yadda yake
maganan dakuma maganan dayakeyi, tace
lafiyanka kuwa fahad? Cewa fa kayi malaria
da typhoid, kataba ganin inda malaria da
typhoid ya hana mutum aure, tashi yayi
yabarta agun, talura akwai abinda ke
damunsa anma inaa yaki fada mata , sadiq
kuwa yaga fahad baida niyya hakan yasa
yasamesa yakamata ka yi maganan aurenku
kafin kana kallo wani ya janye mata hankali,
fahad yace hehehe, diqsa kenan, bakomi
aure lokaci ne zamuyi karka damu,
Wasa wasa saida sukayi shekara amal tun
bata fara maganan ba anma abin yafara
damunta, tagaji da koran samari ga uwa uba
fahad yaki maganan aurenta , ganin haka
yasa tace ko zata gwada masa maganan
daga baya tayi tunanin ko da akwai dalili
yasa tabarshi, abun mamaki kuma yazo
yakaru idan sunyi zasu hadu saiyaki zuwa,
yace aiki kaza aiki kaza, inyazoma basa
wuce minti kadan zaice suje yawo nan zai
kwasheta yakaita gydansu sadiq yakira sadiq
suyita tadi, abun tun baya damunta yazo
yafara damunta tarasa meke mata dadi,
alokacinma sadiq yazo yafara tsantsan
sonsa agareta abun yakara daure kanta,
tasha gayamasa yamanta suna soyayya da
fahad ne? Sayace yasani anma wanda ya
iya allonsa ya wanke
hakan yasa idan fahad yaxo akan suje
gydansu sadiq kokuma yadauko sadiq suzo
gunta, saitashiga daure fuska, ita aganinta
ko fahad zaigane. Anma inna fahad yaki
yagane, hakan yasa tazaunar dashi watarana
tagaya masa duk dahaka yanuna ko in kula
akan maganan, nanfa tafara tsorata kodai
idan namiji yaso mace yakanzo yadena
sonta ne?,
Fahad kuwa kukan dare yazame mishi alada
kullum daredare saiyayi kuka yayi sallah ,
bacci ya kaurace masa, ahankali yabude
account dasunan amal yasamata kudi
dayawa, akalla miliyan 20, duk da albashinsa
dayake kwasa da kudin filayensa nagun
momynsa da daddynsa duk ya sawa amal,
sannan yazo duk wasu filaye nashi da gyda
yasa sunan amal, watarana tana kwance don
zasufara exams din shiga aji uku taji
ankwara mata ruwa, dasauri tatashi, taga
fahad ne yana murmushi yace happy bday!
Tace wow, i really forgot yace oya come
here, yadaure mata ido yarufe da hankerchief
yariko hannunta harsuka fita waje sannan
yasake yabude, mota tagani agabanta benz
c63; ya damka mata mukullin, takalla da
kyau batasan lokacin data rungumeshiba
hannunsa yasa yadaga sama taredacewa
sakeni karki karyani, inaa bata saurareshiba
ya damkota kaman bazai saketaba, wanda
tuni tafara tsorata ta janye jikinta hawaye
tagani a idonsa sosai, tashare itama tafara
hawayen, sannan tace meya sameka plz
dear yajata suka zauna sannan yace mata,
amal ina sonki, kowanni numfashina akwai
tunaninki aciki, kece ruhita, tunanina yakan
gushe anma bakya gushewa, inaso nakoya
miki wani darasi arayuwa, bakomi mukeso
muke samuba, smtymz zamu samu but a
kurarren lokaci kokuma alokacin dabatada
amfani agaremu, anma saimu godewa Allah
daya babu wannan abu duk kankantar lokaci
d little time you have appreciate it,
value it, sannan respect other peoples
feelings, neva hurt dem kiyi tunanin kanki ke
kadai, kowa kina ganinshi ne but u neva knw
wat dey have gone true, evr1 has
responsibilities have deir weakness, my
weakness is you amal inasonki, kisaka
azuciyanki, inasonki fiyeda yadda nakeson
kaina, kuja take sosai, sannan tace nagode
my dear, and also abt d car ubangiji Allah
yakara budi nagode, yaji dadi sosai hakan
yasa suka danyi soyayyansu kafin yatafi
dama ta iya mota basai ankoya mata ba,
inna ma sai godiya take. Gadan gadan amal
suka gama jarabawa, suna hutu anan
momyn sadiq tace taje ta tayata hira aikuwa
lalle lalle fahad yasa tashirya taje, duk da
shigewan da sadiq kemata tarasa yazatayi,
alokacin fahad yasa momynsa suka
canjawasu amal gyda akabawa inna
dankareren gyda sonkowa kin wanda yarasa,
annan nema dakyar dangin mahaifin amal
sukazo akan maganan aurenta anma inna
tace surabu da ita, lokacin datake wahalanta
da yarta bawanda yaleko saida dadi yazo
zasufars mata zanga zanga tace amal nada
miji a aure zatayi auren insha Allah,.alokacin
kuma akafara maganan zabe inda mahaifin
fahad yake neman zarcewa kuma Allah
yabashi saa yacidin, momy daduk wani
danuwa natayasu murna, alokacin amal suka
shiga aji uku, nan hakurinta yazo makura
tayi niyyan ko me zai faru saita sanar da
fahad yagayamata ta yaushene aurensu,
alokacin ahmad yayi wani iri kanshi gashi
duk yazube dakanshi saurayi dai da aja sani
yanzu bashi bane, wataerana tanufi office
dinsa kaimasa sinasir data masa taji yana
waya da alamu kuma da mace yakeyi, yana
cewa yazanyi toh? Hakuri zanyi, nagayamiki
iya abunda zan iyayi kenan, har Allah
yakawomin mafita, a a plx kidena wannan
tunanin, plx, …..no amal bata saniba
haryanzu ni ina tunanin gayamata ne
dakuma right time dayaksmata, anma
nakasa, bansan tayaya zanfara gaya mata
ba, inaga zata iya samun hawan jini akan
maganan nan, bazaki gane yanda take sona
bane,,,, coolern abincin dake hannunta ne
yazube hakan yajawo hankalinsa kanta tuni
yakashe wayan, kuka tafarayi tareda cewa
dama cin amana ne abun? Kahanani aure
aida kagayamin kana nema dawata danasan
nayi, fahad kaci amanata ashe dama
soyayyan karyane? Fita tayi zata koma
dasauri ya damko ta, tana fuzga tana
surutai, kabarni maci amana anma ina bai
saketa ba, kukanta na daga masa hankali
nan tafara matsifa baitaba sanin amal nada
kishi irin haka va, inda take shiga batanan
take fitaba, kanta takama da bango tana
bugawa ya damkota anma taki bari, saika
gayamin meyasa kake cin amanata, ta ina
narage ka? Kalma daya cak! Tunda nafara
sonka banso wani ba anma ka gwadamin
iyakata nagode, jin kukan datakeyi ne yasa
da raunin murya yace amal likita tace, ta
harareshi inbanda kamayar dani karamar
yarinya duk maganan dakayi angayama banji
bane? Wato amal batasaniba kana tsoron
gayamata saboda ciwon hawan jini to naji
kuma ba ciwon dazanyi mayaudari, fuskanta
yayi ya damkota karki kara cemin mayaudari
tunda nafara soyayya dake bantaba cewa
wata inasonta ba, kalma daya narike miki, ta
kalleshi cikin zafin nama tace nafada!
Mayaudari!, cikin hawaye yace amal shes an
oncologist, sakeshi tayi hannunta nabari tace
likitan cancer fa kenan, ya daga kai, takara
cewa fahad kanada cancer kenan? Cikin
hawaye yakara daga mata kai, innalilahi
wainna ilaihi rajiun
rike kanta tayi tasamu madafa tazauna
ajikin kujeran, idonta jawur yayinda shikuma
ya sunkuyar dakai sannan yace inaso inmiki
bayani. Hannu tadaga masa alamun batason
jin mezai gayamata, tace karike abunka, bani
bukatan sani, tunda baka gayamun ba sai
yanxu zaka fada, ashe baka sona? Baka
kaunata? Yadago yakalleta kalman datake
fada sunfi ruwan zafi ciwo agareshi, tana
kuka tana magana, fahad dakana sona zaka
gayamin komi kankantar damuwanka, da
kanaso na bazaka boyeminba, ashe dan
wannan damuwan da ciwon shine zaisa
kahakura kadena sona?koma menene tunda
har ka bukaci kasiyar da soyayyata ga wani
daban wanda baisan zafin soyayyanmu ba,
shine kake nema ya aureni? Fahad ina
soyayyan dakakemin? Riko hannunta zaiyi ta
finciki hannunta tareda cewa karka fara!,
yarasa yazaiyi baitaba ganin amal tafita
masa a giya ba irin na yau, tafita a
hayyacinta,magana kawai takeyi, ganin
batada niyyan yin shiru ya damko ta da karfi
tare da zura mata ido, atake tayi shiru, tana
kokarin kwace jikinta, yace kalma dayane
amal, inasonki bakuma zandaina sonki ba
harna mutu. Haushi taji dayace har karshen
rayuwansa. Wayyo ita. Yanzu in fahad
yamutu yazatayi? Kanta taji na sarawa
anma tadaure sannan tace kasan me? We r
done , kabarni haka, gwara karabu dani akan
kasani soyayya dawani, tawuce tabarshi
agun,
Agyda tagagara ayyana komai, hatta abinci
bata iyaci, tunaninsa duk ya mamayeta,
shikanshi gwara ita duk tunaninsa ya guce,
faisal yakira tare da cewa suje gun momy,
momy na zaune a falo fahad yashigo sannan
yazauna, tana ksllonsa tasauke jaridan dake
hannunta ta kalleshi sannan tace lfy kuwa?
Ya girgiza kai cankuma sai yafara magana
muryanshi na rawa. Momy kimin aure, da
amal kuma nanda sati biyu, tayi jum sannan
tace fahad saurin mekakeyi zaamaka. Anma
kabari a tsanake mana, duk dahaka yanuna
shifa lallai lallai a hanzarta, tanuna masa
yajira mahaifinsa yadawo daga abuja
tukun,har suntashi zasu tafi faisal yakoma
yazauna tareda cewa fahad kaje inazuwa,
fahad kuwa yatafi, faisal ya gyra zama
sannan yace momy fahad nada heart cancer,
wani salati data doka idonta yaciko da
hawaye, tagagara magana jikinta sai bari
yake, faisal yamika mata files din fahad
hannunta na kwakwwara ta karba takaranta,
sai kuka dakyar tajawo wayanta ta danna
wayan abban fahad yana shiga yadauka tace
kadawo gyda , yanda yaji muryanta kafin
yayi magana ta kashe, anma dake hidimar
gabanshi nada yawa kuma yaji hankalin
matansa atashe yasan akwai matsala
hakanne yasa tuni yayi canceling duk wani
shedules dinsa yashigo jirgi sai gombe,faisal
kuwa harya tafi momy bata iya cewa komi
jikinta sai mazari yake, ysna fita fahad kuma
yashigo daukan ruwa a fridge yaga
mahaifiyarsa acikin wani hali, tuni yaje kanta
rikeshi tayi gam tana hawaye, fahad meya
sameka? Ashe ciwo ne ke cinka? Fahad
bazaka mutuba, Allah yatashi kafadunka,
yarike hannunta hawaye nazuba a
fuskanshi sannan yace momy inhar bakison
ganin damuwana, momy kuje kumin tambaya
agydansu amal, ta zura mishi ido tace fahad
bazaka bari inmun dawo daga asibiti ba? Ya
girgiza kai a a nafiso muje da ita a matsayin
matata, itakam damke hannunshi tayi yadda
baxai iya motsi ba,haka suka zauna, ba
magana, sunkai Allah awa biyu alokacin
yace mata bari yaje masallaci itama tuni
tashige dakinta tahau kan sallaya, tana kuka
tana adduan Allah yatashi kafadun fahad
dinta,sunahaka saiga mai girma ya iso
hankakinshi atashe yanufi dakin matar tasa
nan yaganta akan sallaya, yana zaune ta
kwanto jikinshi sai kuka, wayyo fahad na
mutuwa katashi mutafi asibiti baigane meke
faruwa ba sai tambayanta yake hakan yasa
tamika mishi takardan yakarba yana kallo
sake takardan yayi yacire hulansa duk
sanyin dakin saida yafara zufa innnalilahi
wainnailaihi rajiun sai salati yake. Yace ina
fahad din, bata bashi amsa ba yadauko
wayansa da niyyar yakira fahad saikuma ya
dakata don baida numban dan nasa, yace
ban numbansa, tamika wayanta yadauka
yakira,fahad na kwance kuka yakeyi
tsakaninshi da Allah don amal na fushi dashi
ganin kiran mahaifiyarsa yasa yadauka, tuni
yaji ance kana ina? Yace daki , zoka dakin
momynka kasameni yatashi cikin sanyin jiki
yanufi daki yana isa kuwa ya tarar da su
ksman masu zaman makoki, suka sashi
agaba kowa da abunda yake kitsawa, yace
tun yaushe kake da ciwon?fahad yajuya kai
sannan yace more than a year, gaban momy
yakara fadi, yace meyasa baka fada mana
ba? Fahad yace saboda bakwa da time dina,
dukkansu jikinsu yayi sanyi tunda suka
haifeshi baitaba sanin dadin iyaye ba,
kudinsu da mukkinsu yasa basa kukawa
dashi kansu suka sani basa masa uzuri, sai
dadyn nasa yace yanzu zamu shirya muje
muga likitan dake ganinka daganan ayi
moving treatment din waje, naka cancern its
rare, ashekara a duniya bai wuce asamu
mutane 10 masu shiba, nd baa wani mutuwa
so ka kwantar da hankalinka . Ya girgiza kai
yace ba inda zanje sai da amal, kudauramin
aure da amal. Dadyn yayi shiru sannan yace
bari zanyi handling dix week it means kenan
zaayi sauri adaura saboda muje asibitin, ya
girgiza kai, kafin yatashi yatafi yana shiga
yayima amal txt duk hkr yake bata duk da
tana shareshi anma baa minti daya kwararra
bata tunashiba, washegari momy ta aika wa
gwaggo asama, akan asamu dangin ta,
aikuwa tuni akaje dukku gun dangin baban
amal sukuwa ganin basusan zafintaba
gakuma alfarma daga sama yasa suka
yadda aka bada sadaki, wa kanin babanta
umarru, atake sukace a daura aure anma
dangin fahad suka bukaci abari ran asabar
sai adaura acikin garin gombe, inyaso ran
monday saisu wuce london inda zasu zauna
zasukuma rinkayin treatment, duk wannan
hidiman sadiq baisan anayiba don yaje lagos
yin wani course, momynsa kuma taje
kaduna, ahaka har ran daurin aure baa
gayawa amal ba, sannan kuma bata daga
wayanshiba, anma koyaushe acikin mata txt
yake, randa aka daura, faisal ne yafara mata
congrats saiga faiqa ma abin saiya fara bata
tsoro, takira faiqa anma faiqa ta gwada
mata itama haka taji bata tabbatar ba, ganin
mutane suncika gyda ne yasa tayarda, da
gudu taje dakin innarta taganta cikin
mutane, tace inna don Allah minti biyu, inna
tafito dama tasan hakan zaayi, tace wai
andauramin aure? Inna tace ae, dawaye?
Inna tace dawa kuwa? Sadiq mana, tunda
kince bakyason fahad din, bakya daukan
wayanshi bakya son komi nashi, duk da
kinsan baida lafiya, cikin hawaye tace inna
wlh inasonshi, wayyo inna kutaimakamin
kafin nahaukace bazan iya zama da kowa ba
sai shi
inna ta shareta tafice, aikuwa ganin
amal akayi sai kuka take tsakaninta da Allah
tanabinsu tanacewa wlh ita fahad takeso,
faiqa tadauko wayanta tahau yin video,
sukam sai kallonta suke abun sai mamaki
yake basu, fahsd kuwa yau ne yakamata ace
ranar farin cikin sa dazai godewa Allah
yakuma tuna da wannan rana har karshen
rayiwansa, saidai ji yayi kaman yayi hauka,
yana murna saidai yana ganin kaman yacuci
amal, yasan zaimutu toh akanme zai aureta?
Don ya lalata mata rayuwa, wayansa
yadauka da niyyan yakirata yaga call dinta
yashigo yana dauka tafara kuka, fahad
inasonka wlh inasonka, sundauramin aure
dawani wanda banasonshi, saida nagayama
kayi sauri anma ka tsaya wasa, wayyo fahad
na mutu, yace amal,!!! Kidaina cewa kinmutu
danifa aka daura auren, tace a a inna tace
da sadiq ne, yayi dariya sannan yace danine
wasa take miki shiru tayi sannan takashe
wayan, daga kanta dazatayi taga gaba daya
yan dakin kowa kallomnta yake, nan suka
kwashe da dariya, anan aka zaunar da amal
sai waazi ake mata kuka takeyi sosai, saida
aka gama mata sannan a daren aka kai
amal gidanta acikin gra, lafiyayyan gyda,
wanda kowacce mace tske mafarkin samu,
anan aka kaimata akwatunanta, tana zaune
abokan ango suka shigo sukayi rahansu,
faiqa ce azaune da kawayenta biyu
kasancewar amal ba kawa take dashi ba,
bayan sun watsene fahad yashigo , alwala
ya umurceta dataje tayi, sukayyi nafila,
yarike kanta yamata addua, sannan ya
umurceta dataje ta kwanta, dakinsa yaje
yacanja kaya bayan yayi wanka yasa rigan
bacci yarufo kofan yanufi dakin amaryarsa
Washegari daga gydansu fahad aka aiko da
abinci varieties, dayamma suka nufi abuja,
adaren ranan suka nufi
london da momy da amal dakuma fahad
sai faisal, suka nufi asibiti inda likitan yace
zasu daurashi akan magunguna, insha Allah
ba matsala, ananfa ne, kawai aka ce fahad
yanemi gyda agun yazauna, atake dadynshi
yasaya mishi gyda suna zaune shida amal
dinshi, ga treatment anamishi koyaushe
momynshi tadawo,
Inna kuwa suka kara canjamata gyda yanzu
hutawa take sosai, faiqa dakyar tasamu
tafitar da mijin aure duk burinta akan dan
gov haka tahakura acewarta gwara tasamu
mai sonta irin yadda fahad keson amal,
aikuwa tasamu wanu dan kasuwa dakyar dai
akasamu akayi auren, sadiq kuwa daya dawo
yatarar da mummunan lbrn amal tayi aure
haushi yaji sosai, anma ya yaiya, shima
kanshi ya sarawa masoyan balle kuma
yadda yaga sukasha wahala akan soyayyar
tasu dole a jinina musu,
Watansu goma cif suka dawo gyda nja inda
amal tazo ta tisin cikinta, watanta na sha
daya tahaifi danta namiji, ran suna akasa wa
yaro aliyu anacemasa affan, shikennan inda
masoyan sukaci gaba da soyayyansu, oh
soyayya dadi, amal na fahad, (toh muma
Allah yabamu masu sonmu har abada).
Taku har abada Benaxir Omar
Muhadu a next WACECE SALMA?