Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Saturday, 6 June 2020

SULTHANA Complete Hausa Novel

adsense here
SULTHANA Complete Hausa Novel
Compiled   by   Umar  Dalha.πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
           πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
                 *SULTHANA*
            πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
    πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

By *Ummy Abduol*

              *Page 1 to 5*

 Yarinya ce da bazata wuce shekara sha uku bah rak'ube jikin katanga cikin duhun dare sai rawar sanyi take, bata ankara bah ruwa ya tsuge kamar da bak'in kwarya. Dasauri ta koma zauren gidan ta samu guri ta k'ara rakubewa dukda zauren yana zuban ruwa hakanan ta zauna tana matsar kwalla a hankali..


Ruwan sama ake tsugawa a garin kamar da bak'in kwarya, dakyar ta sulale k'asa ta kwanta tana Cigaba da rawar d'ari,  Haka barci ya dauketa.
Kiraye Kirayen Sallan Asuba taji, a hankali ta gyara kwanciya saboda sai lokacin ta samu barci sosai, bata gama gyara kwanciyar bah taji tokari. Koba'a fada mata bah tasan Baffa neh, dasauri ta Mik'e zaune tana soshe soshe tana k'ara kallan Baffa dak'e tsaye ya hasketa da tochila.
"Dan Uwarki kinaji ana kiran Sallah bazaki tashi bah, waike Wacce irrin dabba ce zaki tashi koh saina mangareki"
Dasauri ta mik'e ta shige cikin gida tana cigaba da soshe soshenta.

Mama ta hango bak'in rijiya tana jan ruwa, ta k'arasa dasauri ta rik'e gugan
"Mama kawo naja mik'i"
D'an murmushi mama tai
"Aa Sulthana barshi, dauko butta na zuba mik'i kiyi Alwala"
Bah musu ta dauko buta ta k'araso bakin rijiyan, dai dai nan hafsatu ta fito daga dak'in barcinsu tana sosa kai dagowan dazatai taga hango mama na zubama Sulthana ruwa a buta
"Lallia ma Sulthana, dan tsabar iskanci mama ce baiwar ki?? Har tana jawo ruwa tana zuba mik'i a buta"

Nan da nan jikinta ya soma rawa dan tasan halin hafsatu sarai, yanzu ta kamata taimata dukan tsiya
"Haba Hafsatu, menene dan nazuba mata ruwa, yanzu tazo zata amsa na hanata"
Saurin K'arasowa wajan Hafsatu tai
"Haba mama ya k'ike irin wannan maganan, Baffa ya gaya mata duk aikin da zata rink'a yi a gidan nan ciki kuwa harda jan ruwan nan, Anma saboda iskanci tak'iyi saike zaki ja."
Hade rai mama tai tana cigaba da kallan hafsatu
"Banasan iskanci, ki wuce kije kiyi Alwala"
Zumburo bak'i tai ta juya ta kalli Sulthana dak'e tsaye kanta a kasa tayi kwaffa tabar wajan..

Mama ta maida dubanta ga Sulthana
"Ga ruwan maza jekiyi Alwala kamin Baffanku ya dawo"
Amsa tayi ta shiga bayi ta kama ruwa ta fito tai Alwalan, dai dai itama mama ta gama nata Alwalan
"Sulthana shigo dak'ina kiyi Sallan kafin Baffanku ya dawo maza ki hanzarta"

dasauri sauri ta sauya kayan jikinta zuwa wata kod'adiyar Atampha dogon riga, Hijabin mama ta sanya ta tada Sallah. Tana Cikin sallan taji sallaman Baffa, Hanjin Cikinta neh ya k'ada dakyar ta k'arasa idar da Sallan ko Addua bata tsaya yi bah ta fito daga dak'in. Hangoshi tai a Bukkan tumakin shi yana zuba musu Abinci, dagowan da zaiyi yaga ta fito daga dakinshi tana yan Rabe Rab'e kanta a k'asa..

"Sulthana! Daga wani dak'i naga kin fito yanzu"
Inda Inda ta soma yi chan sai mama ta fito sanye da hijabi da Alama Sallah ta idar
"Sallah nace tazo tayi"
Mugun kallo Baffa yabi mama dashi
"Sau nawa Saratu zan fada miki ki fita harkar Yarinyan nan anma Kink'i"
Sakin Bak'i mama tai da mamaki tana cigaba da k'allan Baffa
"Haba Mallan sai kace bakai ka haifeta bah, baka tsoron hakki. Yarinyan nan Amanace fah a Wurinka mai yasa Kake ha.."

"Dallah rufemin baki"
Maida Dubanshi yayi ga Sulthana dake tsaye har lokacin kanta a Kasa da Alama kuka take
"Keh kuma tsayuwa kikai kina Karemin Kallo bazakije kiyi aikinda Yakamata bah"
Dasauri tabar wajan ta Nufi kicin dinsu, kwanonin datti ta soma fitowa dasu tana kaiwa bak'in Rijiya tana Ajewa, lokaci lokacin takan share hawayen dak'e gangaro mata a fuska...

*Shin anya kuwa Baffa mahaifin Sulthana neh?"*
    Ku biyoni dan jin Cigaban Labarin

*Ummy AbduAbduol✍🏻

πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
         πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
                 *SULTHANA*
          πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

By *Ummy Abduol*

              *Page 6 to 10*

Lokaci lokaci takan share hawayen dake gangaro mata a fuska. Saida ta wanke kwanukan tas sannan ta share tsakar gidan tareda daura abin kari. Bayin gidan ta wanke ta Fito tadau Tsintsiya ta nufi dak'insu Hafsatu. A Kwance ta sameta tana barci gefenta kuma ameena ce zaune kan sallaya tana karatun alkur'ani, dan Rusunawa tai
"Ina kwana yaya Ameena"
Saida ta kamalla sannan ta juyo ta k'alleta da murmushi akan fuskanta
"Lapia lau Amal, kin Tashi Lapia"
Kanta na K'asa ta amsa da Lapia Lau.

Shiru ne ya biyo baya na wasu mintina, dakyar amal ta bude baki tace
"Dan Allah Yaya Amina ki tayani tashin yaya hafsatu inaso nai shara"
Batare da tace komai bah ta shiga tashin hafsatu, dakyar ta tashi suka bata waje ta gyara musu dak'in tsaf. Bata gama ayukanta bah sai wuraren karfe bakwai da rabi na safe, baffa ko sai masifa yak'e tak'i ta gama abin karyawa ga yara naso suje makaranta. Koko ta dama ta dafa musu dankalin Hausa, saida ta zubama kowa ta kaimai Sannan ta dau nata ta nufi zaure dashi.

Hafsatu da Amina suk'a leko dak'insu baffa bayan sun gama karyawa
"Mama, Baffa mun tafi"
Da Fara'a yak'e kallansu Tareda sa hannu cikin Aljihunshi, kudi ya Ciro naira Dari biyu
"Gashi ku raba"
Amsa sukai tareda mai godiya Suka wuce. Mama ta Kalleshi Fuskanta bah Walwala
"Mallan Idan nace inajin Dadin Abinda Kakeyi nayi K'arya"
Kallanta yayi da Mamaki
"Meh kuma nayi?"

Shiru tai dan Tasan Halin baffa Yanzu ya zazzage ta dah Masifa
"Keh nake sauraro"
Ta maza tai ta Kalleshi
"Haba Mallan, Baka gudun surutun mutane?? Koda yake surutu ni nake shanta bah Kai bah"
Kallanta yayi da Alamar mamaki
"Ki fito fili kiyi magana bah kwana kwana bah"
Akan Maganan Sulthana mana Mallan, Yarinyan nan batakai shekarunda zata Rink'a wadan nan Aikin bah, Sannan kuma ka hanata zuwa makaranta. Haba Mallan sai kace bakai ka haifeta bah"

Dogon tsaki yaja tareda mik'ewa
"Ina K'ara gaya miki ki fita Akan harkan Yarinyan nan Bah ruwanki"
Itama Mik'ewan tai tana kallanshi da damuwa
"Haba mallan wanne irin bah ruwana, yarinyan nan fah y'arka ce, jininka ce duk inda na zaga kallona ake ana nunani ana zagina akan ina cizgunama yarinyan nan, kowa laifina yake gani"

Gidon tsaki yaja yabar dakin a fusace, a tsakar gida yayi kicibus da Sulthana shigowanta kenan cikin gidan tana tattara kwanukan da aka ci abinci. Dasauri tabar wajan dan k'aramin aikinshi ne ya duketa batamai komai bah. Kwafa yayi ya fita daga cikin gidan a fusace..

         Wanene Baffa?

Dan Asalin jahar kano ne a kauyen karaye. Cikakken Sunanshi Mallan Jamilu dan Mallan, mahaifinshi Mallami neh mai tara Almajirai. Shi kadai mahaifinshi ya haifa, bayan rasuwan mahaifinshi ya cigaba da kula da Almajiran mahaifinshi kasancewar shima yanada Ilimi sosai. Ya gaji gado mai tarin yawa wanda idan ana lissafin masu kudin kauyen zai zo saahu na biyu ko na uku.
A Haka Allah ya hadashi da Rabiatu yarinyar wani buzu da sukazo Cirani nigeria, Shida Rabi sunyi auren soyaiya da Kaunar juna. Sun shafe shekaru masu tarin Yawa har Mallan Jamilu ya sak'e Aure inda ya auri saratu, aurenta da shekara daya ta haifo Amina, bayan Shekara biyu ta K'ara Haifo Hafsatu. Rabiatu da Saratu sunyi zaman lapia sosai wanda ba wanda kejin Kansu duk da kuwa bah Gida daya suke zaune bah. Hafsatu nada Shekara biyar Rabiatu ta Samu Ciki, Cikin Ikon Allah ta Haifi Yarta Ranar Suna Ita da Kanta tasa mata suna Sulthana wato (Sarauniya)

Sam Mallan baiyi Farinciki da Haihuwan nan bah, Tun a Sannan Rabiatu ta fara Fuskantan Wulakanci da Cin Mutumci gurin Mallan, Sulthana nada shekara Sha Biyu mahaifiyarta Allah ya mata Rasuwa ta sanadin Ciwon zuciya wanda Mallan Yak'i kula da ita har Allah ya dauki rayuwarta. Bayan Rasuwan mahaifiyarta Mallan ya dawo da ita gidan d'ayar matarshi Saratu, inda Ya hana sauran yayanshi kowane aiki sai Sulthana, mama wato Saratu na matukar tausayama halinda take ciki itada Aminatu. Mallan Ya cireta a makaranta wanda dama ummanta ce ta sata, ya hanata Hulda da kawayenta, Gashi yan uwan mahaifiyarta bah a kasan suk'e bah..
Wannan knan.....

*Ummy Abduol✍🏻*
[28/08, 01:12] Friend Hussaini: πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
           πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
          *SULTHANA*
           πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

By *Ummy Abduol*

            *Page 11 to 15*

Wannan knan..

Kwanaki sunja Sosai, Kullum Sulthana Fuskantar Wahala wajan Baffanta tak'e, sai in baya gida tak'an danji dadi wajan Mama ko Ameenatu.
Zaune Tak'e tana tsince Shinkafa lokaci lokaci takan sah bayan Hannunta tana share hawayen dak'e Gangaro mata, Baffa neh ya fito daga daki yana K'allanta
"Bah Rashin Lafiya bah Allah Yasa mutuwa zakiyi sai kinyi Aikin nan, Dan tsabar iskanci harni zaki duba kice bakida lapia"
Ameena ce ta fito daga bayi hannunta rik'e da buta
"Baffa dan Allah kai Hakuri, na Yarda ni zan mata aikin na yau"
Kini kini yayi darai
"Ban yardah bah kuma ban lamunta bah, Karna Sak'e na ganki kindau Tsinke a cikin Gidan nan. Anfaninta knan Ki Barta tayi"
Bai kara cewa komai bah yayi shigewansh dak'i..

Hafsatu ce ta fito tana dariya mai sauti harda rik'e ciki
"Yaya Ameena knan, menene na takura kanki kan Wannan Kuchakan Yarinyan, Nifa Wallahi na Tsaneta Shegiya sai kyau kamar Aljanna"
Dogon Tsaki Ameena taja batace Komai bah Ta wuce dakinsu, Binta da Kallo Hafsatu tai Sannan ta maida dubanta ga Sulthana
"Yarinya Koh kukan jini zakiyi sai kinyi Aikin nan, kima gama kizo ki wankemin Uniform"
Batace Komai bah ta Cigaba da Tsintar shinkafanta..

Dafa Dukan shinkafa ta dafa Musu, Saida ta zubama Kowa Sannan Ta kankare K'anzon ta juye a Leda Dan Ko kwanukan Gidan Baffa ya hanata Anfani dasu, Zaure ta nufa wanda a yanzu ta maidashi kamar dak'inta, Muryan Baffa taji yana Kiran Sunanta
Dasauri ta Sak'i ledan K'anzon ta nufi wajanshi tareda Durkusawa
Kwano ya ajiye mata a gabanta cike da Gyada Danye
"Maza ki Wanke shi ki daura a Wuta dan Yau zaki fara min Talla"
Dasauri ta Dago ta K'alleshi da Mamaki
A ranta ta maimaita "Talla"
Mama ta Fito Dasauri jin Abinda Ya Ambata
"Haba Mallan, Wallahi kaji Tsoron Allah bai kamata kana irin Wannan bah, dur Arzikin dah Allah ya maka kace kuma zaka Rinka daurama Yarka Talla"
Baice Komai bah Ya Kalli Sulthana
"Zaki dau gyadan ko saina B'aballaki a nan"

Da Sauri jiki na Rawa tadau Gyadan ta Nufi Bakin Rijiya Hawaye na Gangara a Idonta, Runtse ido tai jin Kanta Na Sara mata, Dakyar ta Wanke Gyadan ta Hada wuta ta daura ta koma Gefe tana Dubawa, Jin Zazzabi na neman Rufeta Yasa ta Mik'e dakyar ta shiga dak'insu Ameena gabanta na Faduwa
Tako ci Sa'a Hafsatu Bata Dakin
"Dan Allah Yaya Ameena ki taimakeni da Maganin Ciwon Kai"
Kallanta Ameena tai cikeda Tausayawa
"Kiyi Hakuri Sulthana, Duk Tsanani Sauk'i na nan Zuwa Kinji"
Kai Kawai ta Gyada batare da Tace Komai bah. Maganin Ameena ta bata Da Ruwa Tasha Sannan tai mata Godiya tabar dakin..

Saida ta dafa Gyadan ta Juye Sannan Tayi Sallama dak'in Baffa, Fitowa Yayi
"Yauwa Kin Gama?"
Kai ta Gyada Kanta a Kasa
"Maza ki juye a Faranti ki dauka ki Shiga Gari, Kuma Wallahi idan Kika Dad'e Nida Keh neh, Sannan gwangwani naira Goma"
   "Tho" Kawai tace tabar Wajan, Gyadan ta Dauka ta Dau Hijabinta daya Sha Miya da kura tasa Kafanta ko Takalmi babu tabar Gidan. Tafiya kawai take batareda Tasan Inda zata nufa bah dan Talla Bakon Al amari neh a wajanta, Kicibus sukai da K'awarta Sadiya Tana Dawowa Daga Islamiya, Turus tai da Mamaki tana K'allan Sulthana

"Yau Kuma meh idona keh Gani Sulthana, Talla??" cewar Sadiya
Dan Murmushi Kawai Sulthana tai Tana Kokarin Wucewa, Hijabinta Sadiya taja Hakan Yasa Ta Tsaya batare da ta juyo bah, Gabanta Sadiya taje ta Tsaya tana K'allanta
"Sulthana Nice Fah Sadiya yau kuma Hanaki Magana da Kowa akai"
Dakyar ta Iya bude Bak'i Tace
"Dan Allah Sadiya kiyi hakuri ki bani hanya na Wuce, Wallahi Ance idan na dade sai an Dukeni"
Nan da Nan idonta ya cik'o da kwalla..

Jan Hannunta Sadiya tai duka koma Gefe
"Kiyi Hakuri Sulthana, Banajin Dadin Yanda Nak'e Ganinki, Inasan Zuwa wajanki Anma ina tsoron Kar Baffa yamin Fada koya Dak'eni, Kinsan meh?"
Kai Sulthana ta Girgiza Alamar Aa
Kullum da Daddare Zan Rinka kawo Miki abinci a zaure ko in Rinka turo Sani yana kawo miki
Murmushi Sulthana tai Wanda Saida Dimple dinta Masu K'ara mata kyau suka Bayyana
"Nagode Sadiya"
Itama Murmushin Tai, A Haka Suka Rabu Cikeda Kewar Juna.
Rasa Inda Zata Nufa Tai, Yanke Shawara tai ta Nufi Bakin Kasuwa da Gyadar, Cikin Ikon Allah Nan da Nan koh aka siye ta dawo gida. Baffa ta mik'a mah kudin Yanata Washe bak'i
"Yauwa haka Akeso, Gobe mah zak'i sake dafawa"
Mama na gefenshi sai K'allanshi tak'e Cikeda Takaici.
Koh hutawa batai bah Ta daura Aikin da yakamata tai na yanma, Bata Gamaba Saida Aka Fara Kiraye kirayen Sallan Isha'i. Alwala tai Ta koma zaure tai Sallanta tana zaune Hafsatu ta shigo Gidan Tana Wani Girgiza tana Waka
Mama dake tsakar Gida Ta K'alleta da Alamar Mamaki
"Hafsatu daga ina Kike? Tunda Akai Sallan Azahar kika Fita Gidan nan sai yanzu kike gadaman Dawowa"
Turo Bak'i tai ta Turo dan kwalli Gaban Goshi
"Haba Mama ni shiknan banida Yancin Kaina Duk inda Naje Sai aita Tambaya nah"
Ameenatu ta Fito daga dakinsu Sanye da Hijabi da Alama Sallah ta Idar
"Hafsatu Ashe Bakida Hankali, Yanzu Mama kike gayama Irin Wannan Maganan??"
Batace Komai Bah Tadau Buta Tayi Shigewanta Bayi tana Magana K'asa K'asa

*Ummy Abduol*✍🏻
[28/08, 01:12] Friend Hussaini: πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
           πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
          *SULTHANA*
           πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

By *Ummy Abduol*

            *Page 16 to 20*

Batace Komai bah tadau buta tayi shigewanta bayi tana Magana Kasa kasa. Girgiza kai kawai mama tai batareda tace Komai bah, Wuraren Karfe tara na safe Lokacin Baffa ya shiga gida Sadiya ta shigo zauren dauke da kwanon Abinci. Da fara'a Sulthana ta tareda suna dan hira K'asa kasa Tanacin Abincin
"Sulthana kin daina zuwa makaranta, bah Islamiya bah Boko Kullum sai Mallamai sun tambayeni keh"
Dan murmushin takaici Sulthana tai
"Baffa ya hanani zuwa makaranta, ko dah chan dama umma ce keh biya min"

Hawaye ta share tana cigaba da kallan Sadiya
"Bansan menai ma baffa bah, Ni kadai a Garin nan nake shan wuya bansan menai bah"
Kuka neh yaci karfinta, Sadiya ta rungumota K'irjinta ta shiga Lallashinta
"Kiyi Hakuri Sulthana, ko kin manta Karatun dah Mallan Dauda ya mana, Innallaha Ma'a Sabirin, Allah yana Tareda masu hakuri"
Shiru Sulthana tai tana cigaba da kukan K'asa kasa
"Ki daina kuka kinji, Kinsan menene?"
Kai Sulthana ta girgiza Alamar Aa
"Gobe idan Kikaje Gaida Baffa ki kara mai magana akan Makarantan ki, idan Allah ya dauraki a kanshi zai yarda"
Kai Kawai Sulthana ta daga batare da tace komai bah..

Mikewa Sadiya tai,
"Zan tafi gida kinga dare yayi gobe ma zan dawo kinji"
Kai Sulthana ta daga mata tana murmushi, Sauran Abincin da ta rage ta juye a kwano ta mik'a mata kwanon
"Nagode Sadiya ki gaida Goggo"
Zataji cewar Sadiya ta Fita daga zauren Cikeda Tausayin Kawar nata..

Washe Gari ana Sallan Asubah tahau Aikin Gida, Baffa na dawowa ta Karasa kusa dashi ta gaidashi, Bai amsa bah saima tsaki dah yayi ya bar wajan ya shige dakinshi. Komawa tai ta cigaba da Aikinta kamar yanda ta saba, da wuri Ta gama ayukan tah tana zaune bak'in murhu dan lokacin ana dan sanyi
Hafsatu ce ta fiti daga daki tana mik'a
"Keh Sulthana, Maza dauramin Ruwan wanka"
Tho tace ta mik'e dan Daurawa jin Muryan Amina tai tana cewa
"Karki sakeki daura wani ruwa, Idan bazata daura da kanta bah tah bari"
Da Mamaki Hafsatu ta Kalli Ameena
"Haba Yaya Ameena, Makaranta fah zani ki kyalleta ta daura min mana"
Murnushin takaici Ameena
"Hafsatu ki tausaya mah yarinyan nan mana, duk aikin gidan nan ita tak'eyi yakamata ki tausaya mata"
Tsaki Hafsatu taja
"To ni ina Ruwana, Ai bani kesata aikin bah, Baffa neh dan haka ni bah ruwana"
Jin Hayaniya a tsakar Gidan Yasa Baffa ya fito
"Lapia meke faruwa neh naketa jin hayaniya"

Shiru Ameena tai tana Muzurai, nan da nan Hafsatu ta maida bayani. Baffa ya Kalli Ameenatu da Mamaki
"Lallai Ameenatu, Wuyanki ya Isa yanka, Tho bari kiji Baki isa ki chanzamin Abinda nai niya bah. Wallahi Ameenatu ki fita idona in rufe"

Bataco komai bah kanta na Kasa, Sulthana tun fitowan baffa ta hau kiciniyar Daura ruwan, yana waigowa yaga ta daura yayi kwafa ya koma daki abinshi. Mama najin ya shiga dakinshi Ta fito tana kallan Ameenatu
"Ameenatu kisa ido kamar yanda nasa, Allah bah Azzalumin Bayinsa baneh"
Kai Ameenatu ta gyada batace komai bah
"Keh bazaki makarantan baneh" cewar Mama
"Aini jiya muka zana jarabawanmu na k'arshe"
Dafe Goshi Mama tai tana Murmushi
"Oh na manta, Tho Allah yasa An gama Makarantan a sa'a"
Ameen Ameenatu tace ta wuce dakinsu Cikeda Takaicin Abinda Baffa yakeyi..

Ruwan nayi ta sauke ta surka mata takai mata bandak'i sannan taje ta Sanar da Ita. Tana fitowa ta tsaya bak'in Kofar dakin Baffa Gabanta na bugawa cikeda Tsoro, Daurewa tayi tai sallama a bakin Kofar dakin, Fitowa Baffa Yayi yana k'allanta
"Menene"
Dan Jim Tai Jikinta na rawa
"Keh nake Saurare"
Duk'ar dakai tai sannan tace
"Dan Allah Baffa inaso na cigaba da Zuwa makaranta"
Bude Baki Baffa yayi da mamaki yana K'allanta
"Lallai na Yarda Bak'ida Kunya Sulthana, Ki Kalli tsabar Idona Kice Makaranta Kikeso ki Koma"
Jin Daga Muryan Baffa Yasa Mama dasu Ameena suka Fito
Kara Kallanta yayi rai bace
"Ki Sani Kin Gama zuwa makaranta, keda makaranta har Abada kisan wannan"
Kuka sosai Sulthana tahau yi
"Zakimin Shiru koh sainq zaneki a nan wajan"
Nan da nan ta hadiye Kukan sai hawaye datake fitarwa

Mama ta Kalli Baffa itama Rantq Bace
"Wallahi Mallan Karinka jin Tsoron Allah, Bai Kamata Masani kamarka yana irin wannan bah, Ya Za'ayi ka hanata Zuwa makaranta kuma gasu Hafsatu na zuwa"
   "Saboda su yadace suje makaranta bah ita bah" cewar Baffa
Tsaki Hafsatu tai tadau kwandon Soson Wanka tai shigewanta bayi.
Murnushin takaici kawai Ameenatu tai itama ta koma dak'i, Yarone cikin Almajiran Baffa ya shigo cikin gidan dah Sallama Saida Ya Russuna Sannan yace
"Wai ana Sallama da......

*Ummy Abduol*✍🏻
[28/08, 01:12] Friend Hussaini: πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
           πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
          *SULTHANA*
           πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

By *Ummy Abduol*

           *Page 21 to 25*

"Wai ana Sallama da Hafsatu"
Dah mamaki Mama ta K'alli dan Aiken
"Dah Sassafen nan"
Tsaki Baffa yayi
"Ina Ruwanki, Kai jekace tana zuwa"
Hafsatu naji ta fito dasauri ta dire bokitin a Tsakar gida ta shige dak'i, A Gurguje ta shirya koh karyawa bata tsaya yi bah tayima Mama sallama Ta fice, Binta da K'allo Sulthana tai tareda girgiza kai dan Tasan bai wuce Ahmad Mayan matan nan..

Tsaye ta Sameshi a Kofar Gida sai k'ara kallan kayan jikinshi yak'e, da Fara'a ta k'arasa inda Yak'e tace
"Barka da Zuwa Habibyna"
Dan Murmushi yayi yana Cigaba da K'allanta
"Haba Hafsy nah, nifah na Lura bah sona kike bah"
Waigawa Zaure tai Sukayi ido hudu da Sulthana dake Zaune sai Kallansu tak'e, Hararanta tai Sannan ta juyo ta K'alleshi
"Mubar nan dan Gadon Gulma da munafinci na Sauraronmu"
Baice komai bah suka jera suna Tafe suna Hira har kusa da Makarantan su
"Kaima Kasan Ina Sanka Habiby, Bani dah Tamkar kah duk duniyan nan"
Murmushi yayi tareda shafa sumar kanshi dake Cike dam Bakyan Gani
"Banga Alamar Haka bah Hafsy, Dah kina sona dah kin bini Partyn dana gaya miki a Birni, Anma kin ki"
Marairaice Fuska tai Tana K'allanshi K'asa kasa
"Bah Laifi nah Baneh habiby kai kanka Kasan Halin Baffa, Mai zai hana tho ka turo gidanmu ai mana aure kaga Shiknan sai ka kaini Birni mu rinka zuwa Partyn tare koh"

Gintse dariya yayi ya gyada kai kawai
"Kaji" cewar Hafsatu data Marairaice
"Naji Hafsy but inaso na sauyaki, Ki waye ki zama yar birni Sosai, Ki koma sah kaya irin na yan birni ki fita daban cikin matan Kauyen nan. Bt Kudi neh yamin Cikas, Anma karki damu danaje birni na dawo komai zai daidaita"
murmushi jin dadi Hafsatu tai tana cigaba da K'allanshi, Harga Allah tana Matukar san Ahmad, musamman yanda ya fita daban Cikin Mazan Kauyen, Gashi dan Gayu mai zuwa birni, Gashi Kyakyawa san kowa kin Wanda Ya rasa..

Bell din makaranta Aka kada ta K'alleshi tana Yar Murnushi
"Habiby Mu hadu Anjima da Magriba a dandali"
Bata jira mai zaice bah ta shiga makaranta dasauri. Murmushin cin nasara yayi a ranshi Fadi yak'e
"Keh kina tunanin ni Ahmad Aurenki zanyi, Baridai na Samu abinda nake nema bak'i kara ganina a garin nan"..

Yauma kamar jiya Baffa dakansh ya diban mata Gyadan ta Dafa ta Fito Talla, Mutane sai kallanta suke da Mamaki dan basu taba ganin yayan Mallan jamilu da Talla bah, Bakin Kasuwa taje Yauma Anma Tai Rashin Sa'a Baifi Gwangwani hudu aka siya bah Har Gaf da Magriba, Ganin Dare na Neman Yi yasa ta dawo Gida cikeda Fargaban Abinda Baffa Zaiyi mata, Bata sameshi a gida bah Yana Wajan Almajiransa, a Kofar dakinshi ta aje Gyadar ta Shiga aikinta na Yanma..

Sai Bayan Isha'i ya Shigo Gidan dasauri, Gyadan da ta ajemai a kofar dak'i ya K'alla yayi kwafa ya Shiga Cikin Daki, Baifi Minti Goma Bah Ya Fito Dasauri Ya Shiga Dakin Mama
"Saratu! Saratu!!"
Mama data Sallame Sallah ta K'alleshi da Mamaki
"Lapia Mallan Kake Kwalamin Kira haka??"
Kin Shiga dakina neh kin dauki Kudi"
Kallanshi tai da Alamar Mamaki, "Ban ganeh Kudi bah, na Taba daukan kudinka ban fadama bah"
Bai kara cewa komai bah Ya fita daga Dak'in, Sulthana ya soma Kwalama Kira, Ta Shigo Tsakar Gidan Dasauri tareda Rusunawa
"Na'am Baffa"
Ido Ya zazzaro yana Kallanta
"Kudina Zaki bani da Kika dauka"
Mama ta Kalla dasauri sannan ta maida dubanta ga Baffan dake Tsafe ya Kafeta da Ido
"Wallahi Baffa ban dau Maka Kudi bah"
Ameenatu Dake Dak'i ita da K'awarta habiba ta fito dasauri
"Baffa Lapia"
Kudi na Ajiye a daki ko kin Gani?"
Girgiza kai tai dasauri
"Aa banga kudi bah"
Ina Hafsatu? Cewar Mama
Dan Jim Ameenatu tai Sannan Tace
"Tunda Akai Magriba ta fita Bata Dawo bah"

Dak'i Baffa Ya shiga Chan sai Gashi da Dorina katuwa mai Baki dayawa, Mama ta Kalleshi
"Meh Zakayi Mallan"
Keh! Nan da nan Jikin Sulthana yadau Rawa
"Wallahi Baffa Bandau maka kudi bah, Dan Allah kai Hakuri Karka dakeni"
Daka Mata Tsawa Yayi
"Ki Fito Min da Kudina, Oho! Wato dan nace bazan saki a makaranta bah shine kika satan min kudi dan ki koma makaranta koh"
Kuka sosai Sulthana take
"Wallahi Baffa ban dau maka kudi bah, Dan Allah Karka Dakeni."
Hakuri Ameenatu ta soma bah Baffa anma ko Kallanta Beyi bah, Bulalan dake Hannunshi ya soma dukanta Dashi ta koina, ihu Sulthana take Tana Rokonshi Anma ina. Rike bulalan Mama tai a Fusace
"Haba Mallan, Wannan Wane irin rashin imani neh, wanne tabbaci kake dashi na cewa ita tadau maka kudi"
Huci sosai Baffa Yake
"Sakar min Bulalan nan Saratu, Yayana basa Sata, Saida Wannan Yar Iskan Yarinyan ki sakar min Bulala nace"
Bazan Saki bah, mallan Kaji Tsoron Allah"
Wani Tsawa ya saki tareda Fizge bulalan Daga Hannun Mama, Rusunawa Ameenatu tai tana Kuka tareda Rokon Baffa, Anma Ko Kallanta Beyi bah, Saida Ya duketa San Ranshi Sannan Ya Kyaleta. Kuka Sosai Sulthana take, Duk Jikinta ya Farfashe. Dakyar ta Mike Tsaye, ya Kalleta a Harzuk'e Ficemin Daga Gida Karna K'ara Ganinki a Gidan nan..

Kuka Sosai ta k'ara Fashewa dashi tana bashi Hakuri, Binta yayi da Bulalan ta Falla a guje tabar Gidan ya koma Ciki ya rufe Kofa, Yana Shiga Yaga Mama ta fito Sanye da Hijabi, Ya kalleta da Mamaki, Ina Zaki?
"Gaskiya Mallan bazan cigaba da zama a gidan nan kana Azabtar da Yarinyan nan bah Na gaji Gaskiya"
Kafada Ya daga Tareda Cewa
"Idan Har kika fita kofar gidan nan tho ki sani a bakin Aurenki"
Ameenatu da har lokacin tak'e Tsugunne a Kasa tana Kuka ta dago ta Kalleshi da Mamaki...

*Ummy Abduol*✍🏻
[28/08, 01:12] Friend Hussaini: πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
           πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
          *SULTHANA*
           πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

By *Ummy Abduol*

           *Page 26 to 30*

Ameenatu da har lokacin tak'e tsugunne a kasa tana kuka ta dago ta kalleshi da mamaki
"Mallan Yanzu dah bakinka kake Fadin irin wannan maganan" cewar Mama Tsaki yayi batare da yace komai bah yayi shigewarshi dak'i
Dosar kofan fita Mama tai Ameenatu ta mik'e dasauri ta kamota tana cigaba da kuka
"Mama dan Allah karki tafi, kiyi Hakuri"
Hawaye ne ya gangaro a idon mama

"Na gaji da zama ana Azabtar da Yarinya ina kallo banida halin magana, Duk inda naji sai aita nunani ana gulmana mutane sai suyita tunanin ni nake wahalar da Sulthana"
Hawayen idonta Ameenatu ta Share
"Mama karki manta idan har kika fita kin saku, Dan Allah Mama karki fita kiyi Hakuri, Idan Kika fita Zamu Shiga wani hali"
Murmushin takaici Mama tai
"Ameenatu duba ki gani yanda ya Kori yarinyan nan da Daren nan, Ina Yake tunanin Zata? Yanda Kauyen nan Yakeda Hatsari kuma gata K'arama"
Shiru Ameenatu Tai nadan wani lokaci.

Sallaman Hafsatu sukaji ta shigo Gidan Rik'e da Bak'ar leda ganinsu Mama a tsaitsaye Yasa Ta K'araso kusa dasu
"Mama lapia meya Faru?"
Ameenatu ce ta shiga zaiyana mata duk abinda ya faru, Dan Murmushi tai tareda Girgiza Kai Sannan ta Kalli Mama
"Tho Mama mu ina ruwanmu, tunda ya koreta ai shiknan mun munma huta wallahi"
Tsaki Ameenatu taja
"Hafsatu kinada Matsala, Bansan Keh inda kikasa gaba a rayuwarki bah"
Turo baki tai ta kauda kai..

Mama ta dafa Kafadar Ameenatu
"Ameenatu kuje ku nemo Sulthana dan Allah, Kunga Dare neh Akwai hatsari"
Kara turo baki hafsatu tai tana Gungunai
"Ni Mama na Gaji Wallahi"
Tsawa mama ta daka Mata, Hijab Ameenatu ta koma ta dauko suka fito itada Kawarta Habiba suka Fita Hafsatu na Binsu a Baya, Sallama Habiba tama Ameenatu ta wuce gida, Ameenatu ta juya ta Kalli Hafsatu dake tafiya kamar wacce kwai ya fashema a ciki
"Haba Hafsatu ki dago kafa Mana Wai meye Haka"

Dogon Tsaki Hafsatu taja nifa Gaskiya Ya Ameenatu kun Takura min, Allah badan Mama ta matsaba bah Abinda zai kara fito dani da Dadaren nan. Girgiza kai Kawai Ameenatu tai ta cigaba da Tafiya tana haske hasken Hanya da Torch light..

Sulthana kuwa tana Fitowa Gudu kawai take  batareda tasan inda ta nufa bah, Saida tai mai isarsa Sannan ta Samu guri ta zauna Tana kuka sosai mai Sauti, Kuka take kamar ranta zai Fita
"Umma meyasa kika tafi kika barni? Meyasa baki bari mun tafi tare bah. Ina sanki Umma, ina Kewanki"
Kuka ta cigaba dayi gwanin ban tausayi, duk ilahirin Jikinta zugi yake mata bin jikinta tai da K'allo taga duk Baffa ya fafasa mata jiki. Nan da nan jikinta yayi zafi, Idanunta suka fara Lumshewa. Kangon Ginin Kasan dak'e Gefenta Ta mik'e dakyar tana Ganin Jiri ta k'arasa ta Shiga Cikin Kangon ta zauna, Jin Jirin tai na K'aruwa ta lumshe ido da k'arfi ta Bude tareda Girgiza kai. A hankali ta Sulale a Wajan..

Bah Indah su Ameenatu basu jeh bah, Tun daga Gidan Kawayen Sulthana Har Wuraren dah suk'e zaton Zata Iya boyema, Anma bata bah Alamarta. Hankalin Ameenatu Yakai Kololuwa Wajan Tashi, Ganin Dare Yayi sosai Yasa Suka Koma Gida. A tsakar gida Suka samu Mama sai kaiwa da komowa take, Tana ganinsu ta K'araso dasauri
"Yaya kun Ganta?"
Kasa magana Ameenatu tai, Hafsatu ce ta Yatsine Fuska
"Duk inda Muke tunanin Za'a sameta munje bamu ganta bah"
Bata jirah mai Mama zatace bah ta Wuce dakinsu..

Kuka Ameenatu tahau yi a hankali Kanta a K'asa, Mama ta dafata itama hankali tashe,
"Kiyi Hakuri Ameenatu, Insha Allahu Za'a ganta jeki kwanta kinji"
Kai kawai tai k'arfin Halin Dagawa ta Nufi dakinsu jiki a Sanyaye...

Hasken daya Haska mata Fuska neh Yasa ta Bude ido dak'ar, Ganin Gari ya Waye Tangaran da Alamar Rana mah ta Farayi Yasa ta Mik'e Zaune Dakyar tana Yatsine Fuska. Wanne Irin Mugun Ciwo Kanta keh mata da duk ilahirin Jikinta, dakyar ta mik'e tsaye Ganin Har yanzu tana Jin Jiri Yasa ta koma ta Zauna Tana Hawaye a Hankali. Abubuwan da Suka Faru jiya suka Dawo mata, Kuka ta Fara Sosai Tareda Daura Hannayenta Biyu akai
"Umma Ki Dawo dan Allah, Ina Sanki meyasa zaki tafi ki Barni, Wallahi Baffa naso ya Kasheni. Dan Allah Umma ki dawo mu zauna tare, Kin Barni Cikin..."
Kukan neh Yaci Karfinta, Sulalewa tai ta kwanta Tana Shafa Ciyayin Dake Kasan wajan tana Cigaba da Kuka..

Ta dade a haka Sannan Ta daure ta Mik'e ta Fito daga kangon Tana tafiya Saboda Yanda Takejin Jikinta yana mata Ciwo. Duk inda Ta Wuce K'allanta ake, Sai Yanzu ta Tuna Koh Dan kwalli babu a kanta. Runtse ido tai wasu Sabbin Hawaye suka gangaro Mata, Direct Gidansu Sadiya Ta Wuce dan Duk Kauyen nan ita kadaice Tasan Zata iya Taimaka mata da Wani abun...

*Ummy Abduol*✍🏻
[28/08, 01:12] Friend Hussaini: πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
           πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
            *SULTHANA*
             πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

By *Ummy Abduol*

          *Page 31 to 35*

   _kuyi min afuwa jina shiru da kukai, Hakan ya faru neh bisa Rashin Lapia danai. Anma Alhamdulillah naji sauqi, Nagode Sosai da Kulawarku a Kaina_


   Dis page x 4 uh besty *Ayoosh Gidado Yar'adua "My Gidos"*

Direct Gidansu Sadiya ta wuce dan duk kauyen nan ita kadai tasan zata iya taimaka mata da wani abun. Dakyar ta karasa gidan ta Shiga da Sallama, A Tsakar gida ta Samu Sadiya tanayi ma Mamanta Sallama Zata tafi makaranta.
Juyowa tai ta K'alleta da Mamaki
"Sulthana! Daga ina kike? Jiya su Yaya Ameenatu nata nemanki"
Waje ta samu ta zauna a tsakar gidan tareda tafe kai, Dasauri Sadiya ta karaso inda take
"Mama! Mama!! Fito kiga Sulthana"
Mama da Baba suka fito a Tare dasauri,
"Lapia Sulthana meke Faruwa" cewar Mama
Kuka ta Fashe dashi Kanta a Kasa, Baban Sadiya neh ya K'alleta Cikeda tausaya wah
"Sulthana, Yi Magana Mana"
Kasa magana tai sai kukan data K'ara Fashewa dashi, Mama ta K'alli Baba tana nunamai Sulthana Hankali Tashe
"Mallan Kalli jikin Yarinyan nan, Duk yanda akai Duka Akai mata"
Sai a Sannan Baba ya lura da Raunukan dake Jikinta.

Girgiza kai yayi
"Hajjo dau Yarinyan nan ki kaita Ciki, Taci abinci tai wanka. Idan ta huta sai muji Koma menene"
Rungumeta Sadiya tai itama tana Kukan
"Kiyi Hakuri Sulthana, Mallan meh koh?"
Kasa cewa komai Tai sai kanta kawai tada Gyada. Da taimakon Sadiya da Mama ta Mik'e Mama ta kaita Dak'inta Ta zaunar da Ita, Dumamen tuwon dayaji man Shanu Mama ta kawo mata
"Sulthana ci abinci nasan Bakici Komai bah"
Kallan Abincin tai Sannan ta maida dubanta ga Mama
"Dagaske inci"
Gyada mata kai Mama tai Cikeda tausayawa wah, Hannu tasa Cikin Abincin ta soma ci tana Lumshe ido, Ganin Yanda takecin Abincin Hannu baka Hannu Kwarya Yasa Hawaye ya Gangaro ma Mama, Dasauri ta Mik'e tabar dakin Tana sharan Kwalla..

A tsakar Gida tai Kicibus da Sadiya tanata Safa da Marwa
"Keh Sadiya, Makarantan fah"
Turo baki tai tareda Kauda Kai
"Ni Mama bazanje makaranta bah, Kinga fah Sulthana batada lapia"
Sakin Baki Mama tai da Mamaki, A Ranta Fadi take
Lallai Sadiya Nasan Sulthana. Batace Komai bah Sai Girgiza kai datai tabar wajan, Sadiya na Ganin Tabar wajan ta Shiga Dakin Dah Sultanan keh Ciki. Zaune ata sameta Tana Cin Abinci, Kusa da Ita ta Zauna Tana Kallanta

"Sulthana Baffa neh koh?"
Nan da Nan hawaye suka cika Idonta, Sheshekan kuka ta Fara kanta a kasa
Matsowa kusa da Ita Sadiya tai ta Dafata
"Kiyi Hakuri kinji, Zancema Baba ya dawo dake nan gidan mucigaba da zama tare muna zuwa makaranta"

Dagowa Sulthana tai Da Fara'a
"Dagaske Sadiya"
Kai Sadiya ta Gyada itama da Fara'a kwance a Fuskanta.
Saida ta Cinye Tuwon Tas Sannan ta Dago ta Kalli Sadiya dake zaune kusa da ita
"Sadiya Kaina na Ciwo tun Jiya"
Dasauri Sadiya ta mik'e batare datace komai bah ta fita daga dakin, Chan Sai gata dauke da Wani jikon Magani
"Gashi Mama tace Kisha, Sai kizo kiyi wanka"

Jim tai tana K'allan Sadiya, A Sanyaye Tasa Hannu ta K'arba Maganin Tasa Sannan Ta Mik'e, Zani Sadiya ta mik'a mata ta Amsa sannan tabar dakin. Kayan jikinta ta cire ta daura zanin Sannan ta Fito, A tsakar Gida tasamu Mama Bakin Murhu Tana Iza Wuta
"Sulthana kin Fito?"
Kai Ta gyada kanta a kasa
Murmushi Mama tai
"Maza kije ga Ruwa chan a kewaye kiyi Wanka"
Tho Tace ta Nufi Bandakin Idonta Cike da kwala, Zama Tai a Bayin Ta Fashe da Kuka a Hankali, Kuka take Sosai mara Sauti
"Umma meyasa zaki tafi ki barni, Dan Allah ki dawo nima kirinka sona kamar yanda Maman Sadiya ke santa"
Jin Muryan Mama a Wajan Yasa tai Saurin Goge hawayenta ta Fara wankan..

Tana Gamawa ta Fito tasamu Mama ta fito mata da Kayan da Zatasa, Saida ta kimtsa Sannan Baba Ya shigo dakin shida Mama, Tana Ganinshi ta Zame ta Zauna a Kasa. Kallanta yayi cikeda kulawa
"Sulthana fadamin meya Faru"
Hawaye neh ya Gangaro a Idonta, Duk abinda ya faru  ta Sanarmusu.

Shiru Dukai Mama ta Kalli Baba
"Mallan Abinda Mallan Jamilu yake Baya Kyautawa, Sai kace Bashi Ya Haifeta bah, Niko a Mafarki Bantaba Ganin Irin Wannan bah, Abinda yakamata kishiyar mahaifiyarta tayi Sai kuma a Sameshi Wajanshi"
Shiru Baba yayi na Wasu mintina, Chan Ya dago Ya Kalli Sulthana
"Kiyi Hakuri Sulthana, A Matsayina na Aminin Mahaifinki Zanyi kokari Naga nayi mai magana ki koma Makaranta Sannan Ya daina Daura miki Talla"
Turo Baki Sulthana tai Idonta Ya kawo Kwalla
"Baba Ni bazan koma bah, ni Anan zan Zauna"
Mama neh Tai Saurin Cewa
"Mallan idan shi Mallan Jamilun Baya Santa Akwai Masu so dayawa, Wallahi da Zai amince ni Zan Iya rik'e Sulthana."
Murmushin Takaici Yayi tareda Mik'ewa
"Hmm Hajjo knan"

Ummy Abduol✍🏻
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
           πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
            *SULTHANA*
             πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

By *Ummy Abduol*

          *Page 36 to 40*

Murmushin takaici Yayi tareda mik'ewa
"Hmm Hajjo Knan"
Bai jirah mai Mama zatace bah yabar Gidan...

Harya Fita ya dawo
"Sulthana dauko Hijabinki Muje"
Narai Narai da Ido tai Tana K'allan Mama
"Mama Dan Allah Kada mu Maidani ni banasan Gidan Baffa, Kullum Dukana Yakeyi"
Sadiya ce Ta Shigo dakin Dasauri Tareda Durkusawa
"Dan Allah Baba Kada a Maida Sulthana a Batta mu Rinka zuwa makaranta"

Hade Rai Baba yayi ya Kalli Mama
"Miko mata hijabi mutafi"
Jiki a Sanyaye Mama ta mikama Sulthana Hijabin Sadiya dak'e ratayi jikin Gado mai runfan dake dakin. Karba Sulthana tai tana kuka sosai, Saida tasa Sannan suka fito daga dakin, Kuka sosai Sadiya take tana Rokon Baba, Baiko Saurareta bah ya kama Hannun Sulthana suka bar Gidan..

Gidan Mallan Suka nufa, A Runfan da Almajiranshi Suke Baba ya hangoshi, Juyawa yayi ya K'alli Sulthana daketa Sharan Kwalla
"Tsaya a nan ina zuwa"
Tho Tace Ya nufi Runfan Mallan da Sallama
"Hade Rai Mallan Yayi Ganin Tareda Sulthana Suke"
Baba ya Mik'a ma Mallan Hannu suka Gaisa
"Mallan Jamilu Wurinka Nazo" cewar Baban Sadiya
"Tho Mallan Sani ina Sauraronka"
Jim Baban Sadiya yayi tareda Girgiza Kai

"Mallan Jamliu a matsayina na amininka mai kuma baka shawara, kuma kana Dauka. Yauma nazo da Nasihar nan da nasha maka Akan Y'arka Sulthana"
Tsaki Mallan Yaja Tareda Kauda Fuska
"Mallan Sani Na fada maka ka daina sa bakinka a Wannan maganar dan Sam bazan fasa abinda nai niyya bah"

Murmushin Takaici Baban Sadiya yayi Kanshi a Kasa
"Mallan Jamilu Knan, Nasan kasha fadamin haka Anma a matsayina na Aminin kah ya kyautu na Baka shawara ka dauka. Dubah kaga yanda kaima Yarinyan nan duka, Haba Mallan Sulthana Fah Amana ce a Gurinka"
Shiru Mallan Jamilu Yayi yana Cika yana Batsewa
"Ina mai rokon arzikin Kai hakuri yarinyan nan ta koma gida, saboda bai kamata Yarinya karama kamar Sulthana na Gararanba a Gari bah. Dan Allah kai min Wannan Alfarman"
Guntun Tsaki Mallan Jamilu yaja Sannan Ya Kalli Baban Sadiya
"Taci Darajan Kah, Anma dah bah haka bah bazata zauna min a gida bah"
Murmushi Baban Sadiya yayi ya Mik'a mai Hannu sukai Musabaha Sannan sukai Sallama..

Inda Sulthana take tsaye Baban Sadiya ya Nufa
"Sulthana Maza Shiga Gida Baffanku Ya hakura"
Nan da nan Fuskanta ya Chanza
"Dan Allah Baba ka tafi dani gidanka ni banasan Gidan Baffa dukana Yakeyi shida Yaya Hafsatu"
Jim Baban Sadiya yayi na Dan Lokaci, Shi Kanshi Yana Tausaya mata Yana kuma San Rik'eta Anma sam Mallan Jamilu ya Hana. Jin Tana Kuka Yasa Ya Lallasheta Tareda Rakata Har Cikin Zauren Gidan, Hannu Yasa a Aljihu ya Ciro Naira Hamsin Ya bata
"Gashi Ki siya wani abu kinji? Anma ki daina Kuka"
Kai kawai ta Gyada Ya mata Sallama Ya Bar Zauren..

Zama Tai Ta Fashe Da Kuka, Sai datai mai isarta Sannan Ta Mik'e ta Shiga Cikin Gidan. A Bakin rijiya Ta Hango Hafsatu Gabanta DaKwanonin wanke wanke sai Yatsine Fuska take. Sallama Tai a Hankali, Ameenatu dake Bakin Murhu ta Mik'e Dasauri
"Mama! Mama!! Fito ga Sulthana Ta Dawo"
Dasauri Mama ta fito da Fara'a ta K'araso inda Sulthana tak'e Tsaye
"Sulthana kin dagamin Hankali, Jiya bah Inda Su Ameenatu basuje bah Ba'a Ganki bah"
Hawaye neh Ya Gangaro mah Sulthana tai Saurin Sharewa Sannan Ta K'alli Mama
"Mama Dan Allah Kicema Baffa Ya barni na Koma gidansu Sadiya ni nafisan Chan"

Wata Uwar Ashar Hafsatu ta daka,
"Wallahi Kinyi kaddan, Idan Kika tafi Uban wah zai rinka Aikin Gidan"
Hararanta Ameenatu tai
"Kedai Hafsatu Bakida Hali Wallahi, Jiba Tun dazu Mama tasaki Wanke Wanken nan anma Baki koh Fara bah"
Tsaki Hafsatu Taja Tareda Turo dankwalin Kanta Gaban Goshinta
"Nifah Ya Ameenatu kin Fara takuramin a Gidan nan"
Bakinta Mama ta bige rai bace
"Hafsatu Bakinda Hankali, Ameenatu Yayarki ceh fah, na Lura Abubuwanki k'ara gaba gaba Sukeyi"
Turo baki tai Tabar Wajan Tana Gungunai..

Ameenatu ta K'araso inda Sulthana take tsaye
"Sulthana Ina Kika kwana? Waya baki wannan Kayan"
Kayan Jikinta ta K'alla sannan ta Dago ta K'alli Ameenatu
"A Wanchan Kangon na Kwana, Kayan Sadiya neh Mama ta bani"
Jim Ameenatu tai Batace Komai bah. Mama ta kama mata Hannu suka Shiga Dakinta, Lallashinta ta soma yi tana Bata baki har bacci ya dauketa a Wajan...

Sai bayan Azahar Mallan ya Shigo Gidan, Har lokacin Sulthana bacci tak'e. Dakinshi Ya wuce batareda tacema Kowa komai bah, Saida Ya gama Abinda Yake Sannan Ya Daga Labulen Dakin Mama dan ya sanar da Ita zai Fita. Sulthana ya hango kan Gado tana Bacci Hankalinta kwance
"Bude baki yayi da Alamar Mamaki, Lallai Yarinyan nan Wato har lokacin Bacci tasamu a Gidan nan"
Dakinshi ya koma ya dauko dorina Ya Tsula mata, Dasauri Ta mike Tareda Sakin Kuka
"Dan Allah Baffa Kai Hakuri Bazan Sake bah"
Jin Kukan Sulthana Yasa Mama dake Bandaki ta Fito dasauri
"Haba Mallan kaji tsoron Allah, Duk dukan dakama Yarinyan nan Bai isheka Bah"

Tsaki yaja ya koma Dak'inshi Ya Dibo Gyada Ya Fito, a Gaban Sulthana Ya direshi yana K'allanta
"Kinje Kin Kai K'arana wajan Aminina, Tho ki sani bai isa yasani na Sauya abinda nai niyya bah. Maza ki dau gyad'an nan ki Dafa, Kada ki bari na dawo na Tarar baki tafi Talla Bah"
Dasauri ta Amsa da
"Tho"
Jiki na Rawa tadau gyad'an ta Nufi bakin Rijiya Dashi. Babban Rigansh Ya kakkabe Yayi yabar Gidan Rai Bace, Binshi da K'allon Takaici Mama tai Tareda Girgiza kai.

Ummy Abduol✍🏻
[28/08, 01:12] Friend Hussaini: πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
           πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
            *SULTHANA*
             πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

By *Ummy Abduol*

          *Page 41 to 45*

Babban riganshi ya kakkabe Yabar Gidan rai bace, binshi da K'allon takaici Mama tai tareda Girgiza kai. Bakin Rigiyan tah K'arasa ta taya Sulthana Wanke Gyadan suka daura a wuta, Abinci ta zubo mata Taci ta koshi. Gyadan na Dahuwa Mama ta juye mata ta daura mata ta Fita..

Kamar zata Shiga Gidansu Sadiya Sai kuma ta Fasa dan Fushi take dasu Saboda sun maidata Gida. Bakin Kasuwa ta Nufa da Gyadar, takoyi Sa'a Anata Siya. Kudi taga an Mik'o mata Naira Dari biyar, Ta zaro ido Batareda ta Dago bah, Bah Chanji.
"Kidai dubah, Gyadar tabani Saha'awa"
Muryan dataji neh yasa ta dago da Sauri sukai ido hudu da ita, Da Mamaki Ta K'alleta
"Sulthana Dama kina nan? Kullum idan na Tambaya Sadiya sai tacemin Kunyi tafiya har yanzu baku dawo bah, Meyasa kika daina zuwa makaranta Kika koma Talla"
Idon Sulthana neh ya Ciko da K'alla
"Baffa na neh ya Hanani"

Jim Matar tai tana K'allanta
"Laifi kika mai knan"
Dasauri Sulthana ta girgiza kai
"Aa malama banmai komai bah"
Kallan Gyadan tai
"Wannan Gyadan zaikai na Nawa?"
Dasauri Sulthana ta Amsa
"Nah Dari Uku ya Rage"
Murmushi malaman Tai ta Mik'a mata Dari biyar din
"Na Siya duka, Mik'e muje ki Rakani gidanku inaso nai magana da babanki"
Bah Musu ta Mik'e ta Juye mata gyadar a Leda ta mik'a mata, Turan ta daura Akai suka Kama hanyar Gida..

Da Sallama Suk'a Shiga Gidan, Mama ta amsa tana Zaune Kan Tabarma Gefenta Ameenatu Suna Shan iska, K'arasawa Mallaman Tai Ta Zauna Suk'a Gaisa da Mama. Dasauri Ameenatu ta gaidata dan ta koyar dasu a Makaranta, Gyaran Murya Mallaman tai tana Cewa
"Ni Mallama ce a G.G.S.S dake Garin nan"
Da Fara'a Mama ta k'ara Gaisheta, Mallaman Ta amsa tareda Cewa
"Mahaifin Sulthana Nake nema"

Dan Jim Mama tai Sannan Tace
"Ameenatu Yimai Magana Yana Waje Wajan Dalibai"
Tho Tace Ta mik'e tadauko hijab Ta Fita, Chan Sai Gasu Tare sun Shigo, Da Fara'a Ya Karaso
"Barka da xuwa malama"
Murnushi tai tana K'allanshi
"Barka dai Mallan"
Zama yayi Mama da Ameenatu Suka mik'e suka bar wajan, ya K'alli Sulthana dake gefe tanata Raba ido
"Keh Bazaki tashi bah sai kin Gama ji kiji dadin barbadawa Gari"
Dasauri ta mik'e Jiki na Rawa tabar Wajan. Maido da dubanshi yayi ga mallan
"Ina Fata dai Lapia Malama"

Murmushi ta kuma Yi
"Gaskiya bah Lapia bah Mallan"
K'allanta yayi da Alamar Mamaki
"Meh ya Faru Mallama"
Dago kai tai ta K'alleshi
"Zaikai Shekara daya knan dah bana ganin Sulthana Jamilu a Makaranta, nakan tambayi kawarta Sadiya Sani Kullum sai tacemin Sunyi tafiya basu dawo bah, Yau kuma Sai Gashi na Ganta a bakin Kasuwa tana Talla"
Shiru tai tana k'allanshi Ganin Yanda Ya Hade Girar Sama data K'asa
"Eh Hakaneh Sulthana ta dena zuwa makaranta"
Da Mamaki Mallama ta K'alleshi
"Saboda meh Mallan"
Kauda Fuska Yayi sannan Yace
"Saboda na Cireta, Banida Kudin dah zan Rinka biya mata Kudin Makaranta"
Mamaki neh ya kama Mallaman Saboda tasha jin Labarin Mallan Jamilu da kuma dukiyarda Mahaifinshi yabar mai..

Girgiza kai Tai
"Mallan Sulthana tana Cikin Yaranda Keda Matukar kokari a Makarantan nan, Ka daure ta cigaba da Zuwa makaranta. Ina mai tabbatar maka insha Allahu wata rana zakai Alfahari da Ita"
Tsaki Mallan Yaja Yana K'allanta a hassale
"Bazata komah bah ko dolene"
Murmushin Takaici tai
"Tho Shiknan Mallan ka Yarda ta cigaba da zuwa ni nayi Alkawarin zan cigaba da daukan Dawainiyar tah"
Mik'ewa Mallan Yayi Dasauri Rai Bace
"Ce Miki Akai Banida Kudin dazan Biya mata? Makaranta neh Kuma nace bazata Koma bah ko Yarki ce"
Ran Mallaman neh Ya Baci itama ta mik'e a Hasalle
"Anya Mallan Jamilu kai ka Haifi Sulthana Kuwa? Dan ni koh a Karance Karance da yawan Karatu danai ban taba ganin Irin Wannan bah"..

Kofa Mallan Ya nuna Mata
"Maza ki tattara kibar min Gida, Karna Kara ganinki a Gidana, Itakuma Sulthana'n zataxo ta Sameni Wato K'arana Ta kawo Miki koh"
Tsaki Mallaman Taja Tabar Gidan Rai Bace, Jin ta fita Mama ta fito daga Daki
"Haba Mallan Abinda kai ya dace? Gaskiya abinda kake Baka kyautawa, Mallan Kaji Tsoron Allah Haba sai kace bah Mallami bah"
Baice komai bah Sai Hucin Dayakeyi, Dakinshi Ya shiga ya Dauko dorina ya nufi Zaure, Duka Yama Sulthana Sosai Sannan Ya bar Gidan Cikeda Bacin Rai..

Ummy Abduol✍🏻
[28/08, 01:12] Friend Hussaini: πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
           πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
            *SULTHANA*
             πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

By *Ummy Abduol*

          *Page 46 to 50*

      Wannan Shafin naki neh *Bilkisu Jibril* Nagode Sosai Allah Yabar K'auna

Dasauri ta Mik'e tana Zaro ido, Trayn dake gefenta ta dauka ta Fara tafiya tana waigensu. Tsaki Yasir Yaja Yana Cewa
"Yara basajin Magana musamman na Kauye, Ji Wannan yarinyan dan Allah, Yanxu haka aikenta akai ta tsaya nan ruwa ya mata duka"
Shidai Masroor shiru yayi yana Bin Hanyan da Sulthana ta nufa da Kallo. Taboshi Yasit yayi Tareda Yatsine Fuska
"Yadai Shagwababe"
Dukan Wasa Masroor yakai mai
"Bansan Iskanci fah Yasir I hate dis name"
Dariya Yasir Yayi harda Kyakyatawa
"Ni kuma kaga I love the name, Shi zan Cigaba da Kiranka"
Tsaki Masroor yayi batareda Yace Komai bah yayi shigewarshi Motan Ya Zauna, Murmushi Yasir yayi shima Ya shiga motan ya Kunna suka Bar wajan..

Sauri Sulthana take Hannunta na Hago Rik'e da Tryan Gyadarta na Dama ta Dafe Kirjinta tana Numfashi Dasauri dasaur, Gajiya ta soma yi dan haka ta rage Saurin datake Ta cigaba da Tafiya. A kwanan dazai kaita gidansu tai arba da Ameenatu, Ganin Halinda take ciki yasa Ameenatu ta rik'eta Dasauri
"Sulthana Lapia? Meke Damunki"
Kasa magana Sulthana tai Sai K'irjinta datake nunama Ameenatu, kamata tai suka nufi gida. suna shiga gidan Ameenatu ta soma kwallama Mama, Mama ta fito dasauri ganin Halinda Sulthana take ciki yasa Ta K'araso inda suke ta kama Sulthanan ta nufi dakinta da Ita...

Ameenatu ta Fita dasauri ta Dauko wani Kaya ta shigo ta cire mata na jikinta ta Chanza mata, Mama ta fita ta Dibo Garwashi a kasko ta soma Gasa mata Jikinta. Lokaci Guda Sulthana ta fita Hayyacinta Numfashinta na cigaba da Fita sama sama, Hankalin Mama da Ameenatu bah K'aramin tashi Yayi bah, Duk abin nan da ake Mallan na Dakinshi kwance abinshi. Ganin halinda Sulthana take ciki yasa Mama ta nufi dakin mallan dasauri, Da Sallama ta shiga ya amsa yareda dagowa
"Lapia meke Faruwa naganki a rude"
Hankali tashe Mama tasoma magana
"Mallan Sulthana fah batada lapia Sosai gatachan Kwance bata numfashi sosai"
Tsaki Mallan Yayi ya koma ya kwanta
"Wallahi Saratu kinada Matsala, Tho ina ruwana dan batada lapia"
Da Mamaki Mama ta k'alleshi
"Haba Mallan, wai meyasa kake haka ai yarinyan nan ko tsintanta kai baka kamata irin wannan rik'on bah Balle Y'arka daka Haifa"

K'ara jan Tsaki yayi tareda juyawa
"Saratu kina damuna Ki Fita kiban Guri Barci Nakeji"
Girgixa kai Mama tai cikeda takaici ta fito daga dakin, Hafsatu ce ta fito daga bandaki Ta aje buta ta kokarin shiga dakinsu, Mama ta tareda dasauri
"Hafsatu dan Allah idan kinada Dari Uku ki ranta min Zankai Sulthana Chemist ne batada Lapia"
Tabe baki Hafsatu tai
"Ni Mama ina naga Dari uku banida ko sisi nan da kika ganni"
Mamaki ne ya cika Mama harta kasa boyewa
"Haba Hafsatu Dazu fah dasafe naji kina fadama Ameenatu saurayinki ya baki dubu daya"
Turo baki Hafsatu tai tana gungunai
"Inadashi anma gaskiya Mama bazan bada dan Akai Sulthana Wani Chemist bah"
Bata jira mai Mama Zatace bah tabar wajan tana Surutai a Hankali. Binta da Kallo Mama tai tai Cikeda Bakin Ciki..

Dakinta ta koma yanda tabar Sulthana haka ta dawo ta sameta, Ameenatu ta dago ta K'alli Mama Hankali tashe
"Mama meh Baffan yace"
Girgiza kai Kawai Mama tai batace komai bah, Ameenatu ta gane mai Ake Ciki ta Mik'e tsaye Tana Share Kwalla
"Mama barinje Gidan Baba Sani nasan Zai Taimaka"
Saurin Rikota Mama tai tana girgiza mata kai
"Aa Ameenatu karkije Kinsan idan kikaje idan ranmu yayi dubu ya baci a gidan nan saboda kinsan sai Mallan Sani yamai magana"
K'allan Sulthana Ameenatu tai ta Fashe da Kuka
"Mama haka zamu zuba ido muna K'allan Halinda Sulthana take Ciki bamuda Bakin magana. Wai meyasa Baffa yake Haka Neh"
Bata jira mai Mama zatace bah ta nufi dakin Baffa Idonta rufe Saboda bacin Rai..

Sallama tai a dakin, Baffa ya amsa tareda mata izinin ta Shigo, ta Shiga ta Samu Guri Kusa da Gadon K'arfenshi ta zauna. K'allanta Baffa Yayi Yana yar Murmushi
"Ameenatu lapia"
Dagowa tai ta K'alleshi Bako digon Tsoro a ranta
"Baffa Abinda kakeyi Babu kyau, Meyasa kake Wahalar da Sulthana. Dan Allah inaso nai Maka Wani Tambaya"
Murtuke Fuska yayi yace
"Ina Sauraronki"
Jim tai nadan wani lokaci Sannan tace
"Baffa Anya kuwa kai ka Haifi Sulthana"
Juyowa Baffa tai dasauri Cikeda Mamakin Maganan Ameenatu...

*Tho Fah*

Ummy Abduol✍🏻
[28/08, 01:12] Friend Hussaini: πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
           πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
            *SULTHANA*
             πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

By *Ummy Abduol*

          *Page 51 to 55*

           I Dedicated is Page to Uh *My Ummyn Yusrah* nagode da Soyaiyyarki Gareni

"Baffa Anya kuwa kai ka Haifi Sulthana"
Juyowa Baffa tayi dasauri Cikeda Mamakin Maganan Ameenatu. Bata ankara bah Taji Saukan kyakyawan Mari a Fuskanta, A gigice ta dago Ta K'alleshi tareda Dafe Kuncinta. Huci Yake Sosai Yana K'allanta
"Ameenatu ashe duk K'allan danake miki na Mai Hankali bah haka baneh, Ficemin a daki tun ban zaneki bah"
Dasauri tabar Dakin Tana Hawaye dafe da Kuncinta, Batabi takan Dakin Mama bah ta Fita daga Gidan rai bace..

         *Shin Suwaye Masroor da Yasir*

Alhaji Aminu Sunan Mahaifin Masroor dan Asalin Jahar Gombe neh Zama Ya kawoshi Garin Kano, Yanada Mata Hajiya Salma mace mai Hakuri da Juriya da Sanin Yakamata, Alhaji Aminu Babban dan siyasa neh Wanda a Halin Yanzu Yafito Takaran Gwamna Jahar Kano. Yanada Y'aya Biyu a Duniya Masroor shine Babba dan Shekara Ashirin da Shidda, Saurayi kyayyawa Ajin Farko, Dogo Mai Cikar Zati. Yayi K'arastunshi Na primary da Secondary a Kano daga Bisani Mahaifinshi ya turashi K'asar Turkey inda Yake Karatunshi na Architecture, Kasancewarshi Tun yana Yaro Ma'abocin Zane Zane..

A Yanzu Haka Yana shekaranshi na k'arshe a Makaranta, Satinshi Daya knan Da Dawowa K'asan Dan Sun Samu Hutu. Yanada K'anwa mai Suna Mahnoor Y'ar Shekara Sha Biyu tana Js2 yanzu. Suna Zaune Cikin Jin Dadi da Annasuwa a Familyn Kasancewar Mahaifiyarsu ta basu Tarbiya mai Kyau da Kulawa..

Yasir Ya Kasance Aboki kuma Aminin Masroor, Sun Kasance Abokanai tun Suna Yara Ta Sanadiyan Iyayensu Mata da Suk'e Kwaye. Zuwansu Kauyensu Sulthana yasano Asaline kan Project da Yasir Yake Rubutawa Akan Traditional Herbs, An Musu Kwatancen Wani Tsohon Mallami mai bada Maganin shine Sukazo ruwa Ya Tsaresu a Hanya..
   

     Cigaban Labari

Cikin Garin Yasir keh K'okarin Shiga Masroor ya juya yana K'allanshi
"Pls mu koma Gida, I'm Feeling Sick"
Da Mamaki Yasir Ya K'alleshi
"Kuma! Kaifa Shagwababen nan Tsiyata Dakai Knan"
Kauda Kai Yayi Batareda Ya bashi Amsa bah, Kan Motan Yasir Ya Juya Suka tasanma barin Garin. Saida Suk'a Bar Kauyen Sannan Masroor ya Saki Ajiyar Zuciya Mai K'arfi Har saida Yasir ya juya ya k'alleshi. Murmushin Takaici Yaja
"Abinda mukajeyi mah baka bari munyi bah, Masroor Kanada Damuwa"
Murmushin Mugunta Yamai Yana Yatsine Fuska
"Haba Mallan Ka kaini Kauye ina K'okarin Mutuwa, Allah K'ar ya K'ara Kaini K'auyen nan So Boring Wallahi"
Murtuke Fuska Yasir Yayi Bai K'ara Cewa Komai bah Yar Suka Isa Gida..

Wani Hadadden Gida Na gani na Fada Sukai Horn Masu Gadu su Wajan Uku suka Taso a Guje Suka Bude K'aton Gate din Dake Gidan, Saida Sukai Parking Sannan Yasir Ya K'alli Masroor Dake Kokarin Fita Daga motan
"Kauye Bah! Hmm Shagwababe Yanzu mah Kah Fara Zuwa Insha Allah"
Bai Jira Mai Zaice bah Ya Fita Daga motan Ya nufi Main Palourn Gidan Fuskah bah walwala. Binshi da K'allo Masroor yayi Sannan Ya Fito ya rufe Motan ya rufa mai Baya..

A Falo suka Tadda Hajiya Salma Tana Zaune Kan Lumtsatiyar Kujerun Dake Falon Sanye da Farin Medicated Glass Hannunta Rik'e da Jarida Alamar Karatu Take, Jin K'aran Bell Yasa dago. Wata mai aiki ce ta Fito Jiki ja Rawa ta Bude Kofan Tareda Duk'awa ta Gaida Yasir Sannan Tabar Wajan. Ajiye Jariymdan Hannunta Tai Tana Murmushi
"My Sons Har an Dawo"

Wajanta Ya nufa Yana Bata Fuska
"Mami Bamuyi Komai bah, Infact koh Cikin Garin bamu k'arasa bah Masroor yasa Muka Baro"
Dai dai Nan Masroor ya Shigo da Sallama Yana Hararan Yasir
"Mami Gulmana Ya Kawo koh, Karya yake dukma abinda Ya Fada"
Girgiza Kai Mami tai Tana Y'ar Murmushi, Tunasu ta Shiga Yi da Yatsa
"Ku Biyun nan Bah Abinda zance sai Allah Ya Shirya"
Mik'ewa Tai
"Bazan Tsaya Jin Shirmen nan naku bah inada abin yi"
Saman Benen Gidan Tahau Tana Yar Murmushi tareda Cewa
"If uh need any thing Call the Maids"
Bata jira mai Zasuce Bah ta Shiga Wani Kofa Ta rufe...

A Bangaren Sulthana Fah
Ameenatu na Fita Tayi Arba da sani Saurayinta Cikin Almajiran Mallan, Gaisawa Suk'ai Ya Kalleta nadan Mintina Yace
"Ameenatu K'amar kina cikin Damuwa"
Dan Murmushin Yak'e tai
"Bbu komai Saminu Dama Magani nakeso na Saya Banida K'udi kuma Baffa na Barci"
Bah T'areda bata lokaci bah Yace
"Har na Nawa"
Dan Jim Tai Sannan Tace
"Dari Uku neh Dai nake tunani"
Hannu Yasa a aljihu ya Ciro Dari Biyar Wacce Ita k'adai ta Rage mai ya mik'a Mata
"Gashi Bah Yawa Kiyi Anfani dashi"
Godiya Ta shiga yi Mai sannan Sukai Sallama Ta koma Gida...

Dakin Mama ta Shiga tana Nuna Mata Kudin, Chak ta Tsaya Ganin Mama Zaune tana Kuka Gaban Sulthana dake Kwance Warwas Bata Numfashi..

Ummy Abduol✍🏻
[28/08, 01:12] Friend Hussaini: πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
           πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
            *SULTHANA*
             πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

By *Ummy Abduol*

          *Page 56 to 60*

Dakin Mama ta shiga tana nuna mata kudin, Chak ta tsaya ganin Mama zaune tana kuka gaban Sulthana dake kwancd Warwas Bata numfashi, A Hankali ta Sulale ta Zauna a Wajan Tana K'allan Mama
"Mama Meyasa kike kuka"
Cigaba da Kukan Mama tai Dak'yar ta Iya Cewa
"Sulthana Bata Numfashi, Allah dai Yasa bah rai baneh Yayi Halinsa"
Mik'ewa Zumbur Ameenatu tai ta Fita Ta nufi Dak'in Baffa, A Rufe ta Sameshi Alamar Ya Kulle daga Ciki. Dukan Kofan ta fara tana magana cikin daga murya saboda ya jiyota
"Dan Allah Baffa ka bude kofan, Sulthana bata numfashi ka tashi dan Allah mu Kaita Chemist"
Kuka Take sosai a wajan tana cigaba da buga kofan anma a banza, Hafsatu da tunda ta fara bugawa ta leko daga dakinsu tace
"Yaya Ameenatu ku daina damuwa da Lamarin Yarinyan nan, Wanda ma ya haifeta bai damu da Itaba Balle Ku"

Mari mai rai da Lapia Amenatu ta Wankama Hafsatu tana huci
"Hafsatu na lura Iskancinki k'ara Gaba yake, Tho Wallahi ki sani idan baki sauke gigin dake Kanki bah Sai nayi maganinki a gidan nan"
Kuncinta tah Rik'e baki bude
"Dan Nafada muku gaskiya shine zaki Mareni"
Tsaki Ameenatu taja ta Shiga Dak'in Mama a Fusace.
"Mama tashi Muje Chemist, Insha Allahu bah abinda zai Sameta"
Mik'ewa Mama tai tadau Hijabinta Tasa, Ameenatu ta Mik'e Sulthana Tsaye
"Mama Samin Ita a baya na Goyata"
Taimaka mata tai tah Goyata Suka Fito Suka Fita Daga Gidan, Dare Ya soma yi dan Sahu har sun Fara daukewa. Tafiya Suke dasauri sauri Mama na Haska musu Hanya da Torch light, Akwai Tazara sosai Tsakaninsu Da Chemist din Saboda Shi Kadai Garesu duk Kauyen..

Saida Sukai Tafiya Mai Tsayi Sannan Suka K'arasawa Wajan, Koda Sukaje sun Tadda Mutane Sosai a Wajan, Sauke Sulthanan Ameenatu Tai Mama Ta Rungumeta a jikinta ita Kuma ta k'utsa Cikin Mutanen
"Dan Allah Ku Taimaka, Yarinya ce Bata Numfashi ina Likitan"
Mutanen da Suk'a bi Layi Kowa Ya Tsaya Suka Shiga da Ita Cikin Dakin Maganin, Kwantar da ita akai a irin Gadon Marasa Lapaia dake Dakin, mutumin Ya dauko Sthethoscope Yasa a K'irjinta Cikeda Fargaba, jin Zuciyarta Na Harbawa Yasa Ya Sauk'e ajiyan Zuciya. Ameenatu daketa K'allanshi Hankali Tashe Tace
"Likita ta mutu koh?"
Kai Ya Girgixa mata Sannan Yace
"Bata Mutu bah tanada rai, Anma maiya Sameta"
Itama Ajiyan Zuciyan tai Tana K'allan Sulthanan
"Ruwa neh ya mata duka dazu shine ta dawo gida tana numfashi Sama Sama"

Baice Komai bah Sai Gani datai ya Hado wasu Allurai Guda Biyu Ya mata Sannan Ya Dauko wani ya mata a Hannu. Ganin Abubuwan Dayake Yasa Ameenatu Tai Saurin Cewa
"Likita Wallahi Bamuda kudi Dari biyar ce a Hannun mu ka taba magani K'awai"
Juyowa yayi ya K'alleta tareda Murmushi
"Karki damu, ni Likita ne nazo Kauyen nan dan Taimaka ma Alumma kuma Kyauta nakeyi"
Murmushi ne Ya subuce mata har saida Fararen Haqoranta Suka Baiyana. Cigaba Yayi da Abinda Yakeyi Har drip yasa mata Sannan Ya maida dubanshi da Mama Dak'e Tsaye
"Mama Samu Guri ki Zauna Dan Bah Yanzu Zaku tafi bah Har sai Ruwan dana Sah mata ya K'are Sannan kuma ta Farfado"

Wuri yaba Mama Ta zauna tana mai Godiya, Baice komai bah Sai Murmushin dayakeyi. Ameenatu ta matso inda Mama take Zaune Ta sadda kai Kasa tana cewa
"Mama ki koma gida, Banasan Abinda zaije ya dawo, karki Damu Insha Allahu komai zai daidaita. Kada Baffa ya fito bakya nan"
Tho Mama tace Tareda Mik'ewa tai Musu Sallama Ta Wuce Gida. Har Likitan ya Gama Bah duban Mutanen Dake waje Magani Anma Sulthana Bata Farka bah, Dak'in ya Shigo Tareda Cire Lapcoat din dake Jikinshi. K'allanshi Ameenatu tai
"Likita Har yanzu bata Farka bah"
Juyowa yayi ya K'alleta Yana Y'ar Murmushi
"Karki damu Zata Farko koda xuwa Safe neh"

Ameenatu Batace Komai bah ta Maida Dubanta ga Sulthana Dak'e Kwance.
Wayoyinshi Dake kan Table ya dauka Tareda Briefcase dinshi Sannan Yace
"Yan Mata Zan Tafi Masaukina"
Key din Chemist din ya Mik'a Mata Yana cewa
"Nasan Sai nah dawo ruwan zai k'are dan Haka Ga Key ki rufe Kofan Karki bude har sai idan nine nace miki nazo"
Hannu bibiyu ta Amsa tamai Godiya, Torchlight ya Mik'a mata Sannan ya Fita Ita kuma ta Tashi ta Rufe Kofan Ta dawo ta zauna...

Bacci ne Ya kwasheta a Wajan bata farka bah Saida Dataji Ana Kiran Sallan Asubah, Mik'ewa tai dasauri Sai a Sannan ta tuna Bah Gida tak'e bah, Sulthana ta k'alla taga ta juya Kwanciya. Murmushi tai ta tabata
"Alhamdulillahi, Allah Ya baki lapia"
Dube dube ta soma yi koh zata samu ruwan Alwala, Anma bata samu bah. Haka ta zauna har Gari yayi Haske Tangaran har ta soma jin hayaniyar mutane Bakin Shagon Alamar Magani sukazo Amsa, Jin Ana dukar kofan Yasa Tace
"Waye"
Muryan Likitan Ta jiyo yana cewa
"Bude Nine"
Bah Musu ta Bude kofan Ya Shigo Yana K'allan Sulthana. Gaidashi Ameenatu tai Ya Amsa Da Y'ar Murmushi a Fuskarshi
"Ya Jikinta"
Dasauki Ameenatu Tace K'anta a K'asa, Karasawa yayi inda Sulthanan keh Kwance Ya soma Dubata, A Hankali ta bude ido ta daura su akan Kyakyawan Saurayin Dake Tsaye a Kanta
Mik'ewa Tai dasauri tana K'allanshi Shima ita Yak'e Kallo. Kauda kai tai tareda Bin dakin da K'allo, Ameenatu ta Gani zaune tana K'allanta ta mik'e Tana kokarin Sauka daga Gadon, Saurin Rikota Ameenatu tai tana cewa
"Ina zaki bayan Bakida Lapia"
Sai a sannan Taji zafi a Hannunta, Duba Takai Wajan tana Hannunta da Allura Ruwa na Bi. Tabe Baki tai Ta zauna Tana Yatsine Fuska. Tunda Ta bude ido bah Abinda Likitan nan keyi sai K'allanta Kamar zai Cinyeta. Ganin Irin Kallan Da yak'ema Sulthana Yasa Ran Ameenatu ya baci Zuciyarta Tahau Mata zafi...

*Tho!  Kunjimin Wannan Ameenatun, Tho me Take Nufi*

Ummy Abduol✍🏻
[28/08, 01:12] Friend Hussaini: πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
           πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
            *SULTHANA*
             πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

By *Ummy Abduol*

          *Page 61 to 65*

             Gareki *Hafsat Hassan* Sakonki ya Iso Gareni, ina Godiya da Soyaiyyarki Gareni. Wannan Shafin Naki neh..

Ganin irin K'allan da Yakema Sulthana Yasa Ran Ameenatu ya baci Zuciyarta tahau mata zafi, Kauda kai tai Tareda Jan Guntun Tsaki.
"Likita Yaushe Ruwan zai K'arene Inaso mutafi Gida"
Sai a Sannan Yadawo daga Duniyar Tunani ya K'alli Ameenatu yana cewa
"Nan da Y'an mintina, ai ya kusa Karewa"
Batace komai bah Ta juya fuska tana k'allan wani wajan..

Sulthana ya K'alla yana mata Murmushi
"Ya jikin naki"
Turo baki tai ta kauda kai gefe
"Ni Bah abinda ke damuna"
Murmushi Yayi yabar wajan ya koma inda Jama'a ke tsaitsaye Suna jiranshi. Sai a Sannan Ameenatu tace
"Sulthana ya Jikin"
Murmushi tai Kanta a kasa
"Dasauki"
Shiru neh yabiyo baya Har na Wasu yan Mintina, Ganin Ruwan ya k'are Yasa Ameenatu ta mik'e taje ta Gayama Likitan Fuska bah Walwala, dakanshi yazo ya Cire mats tareda Hada mata magunguna Suka amsa Tareda mai godiya...

Har zasu fita Yadan Sosa Sumar Kanshi Yana Cewa
"Ummm ji mana"
Ameenatu ta Tsaya batareda ta Juyo bah, Karasawa Yayi inda Tak'e tsaye yace
"Gashi zaku tafi bansan Sunayenku bah, n Inason idan bah damuwa mu K'ulla zumunci da Ku"
Murmushi Ameenatu har Fararen Hakoranta Suka baiyana
"Bah Damuwa Sunana Ameena, Ita kuma Sunanta Sulthana kuma muna Unguwar Taro tari gidan Mallan Jamilu mai Almajirai
Sunan Ya maimaita a Hankali tareda Lumshe ido Sannan Yace
"Ni kuma Sunana Dr Fareed, ni dan Cikin Garin Kano neh"
Murmushi Ameenatu tai
"Mun gode Sosai Dr Allah ya saka da Alheri"
Kai Ya daga mata Yana K'allanta har tah fita daga shagon, Already dama Sulthana ta fita..

A Gida Kuwa, da Asubahi Kiran Sallan Farko Baffa ya fito ya Nufi Zaure dan Tada Sulthana kamar Yanda ya saba, Ganin Bata nan Yasa ya Dawo ya buga Dakin Mama, Budewa tai tana Bata Fuska
"Dama na Fada miki, Yanzu je ki gani da Idonki Yarinyan nan Ashe ba'a gida take Kwana yawon karuwancinta take tafiya  sai asubah tayi take dawowa. Tho yanzu dai gashi yanzu tah Makara"
Tabe Baki Mama tai Tareda Kauda kai
"Tho indai Sulthana bata gidan nan tah Tafi Yawon karuwancin neh kamar yanda ka fada tho tareda Y'arka Suka Tafi"
Da Mamaki Ya K'alli Mama rai bace
"Ni kike Gayama Wannan Maganan, Yanzu na K'ara tabbatar da bakida Hankali da Tarbiya Saratu. Da bakinki Kike ai banta Y'arki"
Guntun Tsaki Mama tai dan Baffa ya mugun Kaita Mak'ura Yau

"Aibanta Y'a ai a wurinka na koya, Sannan Maganan Tarbiya Rainonka neh. Idan kuma baka Yarda bah sai kaje ka duba ka gani"
Bata jira mai zaice bah ta rufe kofan dakinta Bam!
Jiki na Rawa Baffa ya nufi dakinsu Ameenatu yana Duka, Hafsatu dake Barci ta Mik'e xaune Cikeda Masifa
"Wai Wayene"
A Harzuk'e Baffa Yace
"Budemin Kofa"
Jin muyan Baffa Yasa ta Bude dasauri ta fito, Ido yasa yana jiran Fitowa Ameenatu jin Shiru Yasa ya K'walla mata k'ira
"Keh Ameeenatu bazaki Fito bah"
Hafsatu tace
"Ai ba'a dakin tah kwana bah"
A rude Baffa Yace
"Ina Taje?"

Girgiza Kai Hafsatu tai tana cewa
"Bansan inda taje bah, bata dai kwana dakin bah"
Tamkar Mahaukaci Baffa ya koma a cikin gidan, Bai damu da Sulthana bah Burinshi Kawai Yaga Ameenatu, Fita Yayi ya nufi masallaci. Yana dawowa ya soma Kwallama Mama kira..

Fitowa tai daga daki tana cewa
"Lapia kira da Sassafen nan"
Huci yake kaman Zaki Yana k'allanta
"Ina Kika kai min Y'a tah"
Mama ta tabe baki tace
"Ina Kuwa zan Kaita nifah Rabona da ita tun jiya da Daddare"
Cikeda masifa Yace
"Idan bakisan inda taje bah ya akai kikasan bata gidan"
Sai a sannan Mama ta K'alleshi itama rai Bace
"Mallan kullum magana tah daya ce gareka ka rinka jin tsoron Allah, Duka yaran nan Y'ayanka neh. Ka daina nuna banbanci, ni tunda nake ban taba ganin Irin Wannan Abin naka bah, Haba M..."

Saurin Katseta Yayi da Cewa
"Bah Wannan Na tambayeki bah maganan Y'ata make miki"
Murnushin Takaici Mama tai
"Ameenatu takai Sulthana Chemist jiya da Daddare rai a Hannun Allah, A Chan suka kwana"
Zaro ido Mallan Yayi Yana K'allan Mama
"Da Izini Wah?"
Bata bashi amsa bah Tabar Wajan ta shiga Kicin Abinta..

Basu suka K'araso gida bah Sai Wuraren K'arfe Tara da Rabi, Da Sallama suka Shigo cikin Gidan, Baffa suka Samu zaune a bakin Kofar dakinshi da Alamar su Yake jira dan yana ganinsu ya mik'e dasauri. Ameenatu ya Kalla yana cewa
"Daga ina kike"
Cikeda tsoro tace
"Daga Chemist muke nakai Sulthana neh"
Da Izinin Wah?" cewar Baffa

Dan Dagowa Ameenatu tai ta Kalleshi sannan ta duk'ar dakai
"Bah Kowa, Anma Baffa gani nai tana cikin Wani Hali datake Bukatar Taimako"
Nuna Ameenatu Baffa yayi da Yatsa
"Idan Na K'ara gani ko naji makamancin Haka a gidan nan Wallahi saina mugun Saba miki, ki rubuta ki ajiye"
Bai jira mai zatace bah Ya fice daga gidan.. Jin ya Fita Yasa Mama ta Leko Suka shiga Dakinta, Abin karyawa ta Basu Suka ci Sannan Taba Sulthana Magani. Dakinsu Ameenatu ta Koma ta kwanta dan tadan K'ara Kwanciya, Lumshe ido tai ta Bude Dasauri a Fili tace
"Dr Fareed mai yasa kakemin Gizo a Idona, Mai yasa nake tunaninka tun Sanda muka Rabu"

Niko Ummy Abduol nace ki jira Readers su baki amsa nidai baza'aji mutuwar sarki a bakina bah...

Ummy Abduol✍🏻
[28/08, 01:12] Friend Hussaini: πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
           πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
            *SULTHANA*
             πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

By *Ummy Abduol*

          *Page 66 to 70*

       Dedicated dis page to *Summayya Danfulotie* Sakonki Ya iso Gareni, Nagoda da Addu'a Allah yabar K'auna.. da Kuma Sahiba *Aysha Zagi* I beg make uh no hug transformer uh knw I lurv uh..

Kwance Yake kan katafaren gadonshi Yana Latse latse a Waya, Bude kofan Dakin Akai koba'a fada mishi bah yasa Yasir neh dan Shi kadai ke shigo mai daki bah Tareda izini bah. Kan gadon Yasir ya zauna yana k'allan Masroor da yayi kamar bai Ganshi bah
"Morning Shagwababbe"
Hade rai Masroor yayi yana cigaba da abinda Yakeyi, fuzge Wayan Yasir yayi a aje a Bedside din dake kusa dashi
"Ina ma magana kayi banxa dani"
Tsaki Masroor Yayi tareda Mik'ewa Yana cewa
"Yasir Wallahi ka kiyayeni da kirana da Wannan Sunan"

Dariya Yasir yayi harda Rik'e ciki
"Kaga Yanda kake da baki kamar wani k'aramin Yaro"
Tsaki Masroor yayi ya kauda kai
"Pls banasan Damuwa Yasir meh kuma ya kawoka"
Tsagaitawa da Dariyan yayi Yana cewa
"Dan Allah d'an Rakani zakai"
Zaro ido Masroor yana K'allan Yasir
"Tab! Allah ya kiyaye na K'ara raka kah, Jiya da naraka kah ka Kaini kauye."
Dariya Yasir ya K'ara Fashewa dashi
"Kuma kaman Kasani Wallahi Chan nakeso muje cox Inasan nasamu wasu informations ne wajan Mallan din nan, Pls Frend"
Shiru Masroor yayi yana Yatsine Fuska
"Shiknan bah Damuwa anjima sai muje"

Murmushi Yasir Yayi
"Dats y I lv uh Friend"
Shima murmushin yayi dai dai nan aka turo kofar dakin, daga kai Masroor yayi yana k'allan kofan. Ganin Mahnoor ce yasa ya rike Kugu Yana K'allanta
"Any problem"
Itama K'ugun ta rike tana Y'ar dariya tace
"Any problem"
Kanta yayo rai bace dan ya Tsani yayi abu a kwaikwayeshi, dasauri ta ruga bayan Yasir ta Labbe tana cewa
"Pls Bro Yasir karka bari ya dakeni"
K'areta Yasir yayi yana k'aftama Masroor ido
"Meye Haka kaifa kanada Matsala"
Kwafa Masroor Yayi har zai juya ya hango tana mai dariya, Duka yakai mata ta goce sai a Fuskan Yasir. Dafe wurin yayi yana K'allan Masroor
"Nagode Dukan naka ya rasa inda zai tsaya sai a Fuska nah"

Dariya Masroor yayi
"Sorry wallahi Mistake neh"
Mahnoor na Ganin Haka ta runtuma a guje, Saida ta fita Sannan ta Lek'o tana Murguda baki
"Daddy yace ka Sameshi a Study room"
Bata jira mai zaice bah Tabar wajan dasauri dan tasan halinshi yanzu yana iya Kai mata duka. Yasir ya K'alla yana cewa
"Au b ryt back"
Gyada mai kai yayi batare dayace komae bah..

Study room din ya nufa Ya murda kofan tareda Sallama, Daddy a Amsa Yana Murmushi
"Shigo have a Seat"
Zata Masroor Yayi
"Daddy ance Kana Kirana"
Medicated glass din dake idonshi ya Cire Yana K'allan dan nashi
"Ya kamata tunda yanzu kana Final year dinka neh ace ka nemi matar aure, Kaga daka gama dai kawai ai aure"
Turo baki Masroor Yayi
"Haba Daddy Aure kuma, I'm still young Banfa isa aure bah"
Dan Murmushi Daddy yayi
"Son Look at uh, Uh a Matured Enough ace ka Aje Iyali, Na Tsufa and I Want to see my grandchildren kafin na Tafi"
K'ara Cuno baki Masroor yayi yana gungunai
"Nidai Daddy dan Allah kabar Maganan nan banaso"
Kai daddy ya gyada
"Shiknan bbu damuwa, Yanzu dai idan kagama Kasani Company na Dake Lagos Nakeso ka Rik'e Har abada Na Barmaka"
Dago kai Masroor Yayi dasauri yana K'allan Daddy
"Daddy Are you serious"

Kamin Daddy yayi Magana Mami ta shigo Da Sallama, Tana Y'ar murmushi
"Kana Mamaki neh" cewar Mami
Kasa magana Masroor yayi saboda Farinciki, Dasauri ya Rungume Daddy yana Dariya
"Thank uh! Thank uh!! Daddy, U're the best dad evr"
Dariya Mami da Daddy Sukai a tare. Barin dakin Yayi dasauri ya nufi dakinshi, Yasir dake Latse Latse a Laptop ya dago jin Yanda Ya banko Kofan dak'in, Rungume Yasir Yayi Yana Dariyar Farinciki
"Friend am now the Owner of MasMah Company"
Xaro ido Yasir yayi da Mamaki
"Are uh Serious"
Kai ya Gyada mai Yana murmushi, Rungume juna suk'a kara yi Cikeda Farin Ciki Yasir Yace
"I'm Very Happy for you Yasir"
Dagowa yayi ya K'alli Yasir din
"Friend Barinyi Wanka Na Fito Yau akwai Chilling"
Dariya Sukasa a Tare Masroor ya nufi Bathroom dasauri...

*Bayan Kwana Biyu*

Ameenatu Kullum Cikin Tunanin Likitan nan take, Duk ta Chanza ta koma Shiru shiru, Duk sanda Mama ta tambayeta sai tace bah Komai. Sulthana Ta Warke Ras ta cigaba da T'allanta Kamar yanda ta saba.

Yau Ta Dau T'allanta kamar yanda ta saba ta Fito, Yanke Shawara tai kawai ta Nufi Tashan dake garin dan a nan take tunanin Zatafi yin Ciniki, Tashan ta nufa duk da nisan dake Tsakani da Cikin Kauyen su. A haka har ta isa Tashan ta nemi guri ta zauna, Ciniki ta Fara Kadan kadan harta Siyar, da murna tadau Tray'nta Tana Fadin
"Alhamdulillah na Gode Allah yau Baffa bazai zaneni bah"
Gida ta Nufa Tana Tafiya Dak'yar saboda Yunwan dake Damunta. Layi ta Fara a Hanya tana Rik'e da Cikinta daketa Kukan Yunwa. A guje Suka taho dan Yau Masroor ne ke driving din, Bai ankara bah Yaga Mutum a Gabanshi tana Layi dasauri ya Taka burki Motar ta Tsaya Daidai Inda Sulthana Tak'e Tsaye Rik'e da Cikinta..

Jin K'arar taka Burki da K'uran daya tashi Yasa ta K'walla ihu Ta Matsa dasauri har saida ta Fadi, Kudin Dake Hannunta suka Watse iska ya soma Tafiya dasu. Masroor ne Ya fito dasauri Rai Bace Yana K'allanta
"Keh Wacce irin Dabba ce, Bakya Gani neh. So kike na bugeki ku samu abin Fada Koh"
Dafa Kafadanshi Yasir Yayi
"Haba Masroor Cool down mana Bakasan meye Dalilinta na Tsayawan bah"
Mik'ewa Tsaye Tai Dasauri Ta fashe da Kuka mai Sauti, Sai a Sannan Sukaga Fuskanta. Kudin dah suka watse ta soma bi tana kuka sosai Tana Harhadawa. Wasu Har sun Mata nisan da bazata iya daukowa bah"
Dawowa tai tadau Tray'n tana Cigaba da kuka sosai, Sai a Sannan Yasir Yayi Magana
"Friend Itace Yarinyan nan na Rannan da Mukagani a Kusada Motan mu"
Kurrrri Masroor ya mata ko Kiftawa bayayi, Yasir neh Yayi K'arfin Halin k'arasaw inda Take yana K'allanta
"Its ok Nawane kudin na biyaki"
Dago Manyan idanunta tai daya rune Zuwa ja Ta K'alleshi har ta bude baki zatai Magana wani Kukan Yazo mata Ta k'ara Fashewa da Sabon Kuka..

    *Manage dis*

Ummy Abduol✍🏻
[28/08, 01:12] Friend Hussaini: πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
           πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
            *SULTHANA*
             πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

By *Ummy Abduol*

          *Page 71 to 75*

     Alhamdulillah Nw Am One of the *Zamani Writers Association* Members.. Thank uh Once again *Aunty Fauzah*

Dago manyan idanunta tai da suka rund zuwa ja yana ta kalleshi, har ta bude baki zatai magaba wani kuka yaxo mata ta k'ara fashewa da Sabon kuka. Goshinshi ya taba
"Oh God!"
Dakyar Masroor ya k'araso Wajan Cikin Sanyayan Muryanshi yace
"Kiyi Haquri Fada nawane kudinki na Biyaki"
Cikin kuka tace
"Dari Shidda neh"
Hannu Yasa a Aljinu ya Ciro Sababbin Dubu daya Dayawa ya Mik'a mata tareda Fadin
"Pls kiyi haquri kinji"
K'allanshi Kawai Yasir yake da mamaki kaman bashi ya Gama Masifah bah Yanzu.

Zaro ido tai ganin Kudin Daya mik'a mata, ja dabaya tai dasauri tana Girgiza kai. Yasir Yace
"Ki Amsa mana"
K'ara Girgiza kai Tai
"Ni..Ni baxan Amsa bah kudin Yayi yawa, Idan nakai gida Baffa dukana zaiyi"
Tana gama magana taji muryan Hafsatu a Bayanta tana cewa
"Iyeh! Sulthana Dama abinda kikeyi knan koh, Juye ake miki. Ai Wallahi Kamar Baffa Yaji Labarin nan"

Juyawa Sulthana tai Dasauri Tana K'allan Hafsatu Tada Rik'e Kugu itada Ahmad Saurayinta, Jikinta neh ya soma rawa
"Dan Allah Yaya Hafsatu kiyi Hakuri Wallahi bah juye sukemin bah"
Tsaki Hafsatun Tai Tana K'allan Masroor da shima ita yake K'allo Cikeda Mamaki
"Haba Baiwar Allah Kyadai Tsaya ki saurara abinda yake Faruwa koh"cewar Yasir
K'allan Rainin Wayau Hafsatu tabi Yasir Dashi
"Dalla Mallah Rufema Mutane Baki, Nafasanku Mazan Birnin nan irinku ne masu Bata Yaran mutane. Itama Barin koma gidan zataci Ubanta Wallahi"
Zuciya ce ta Ciyo Masroor duk da Shi bah mai San Fada baneh balle Surutu

"Shut up ur Dirty mouth! hu du uh think you are. K'aramar Yarinya dake Kina Fitasara Irin Wannan. Ki maida Hankalinki If not Wally uh will Regret all dis"
Rikeshi Yasir Yayi Ganin Yanda Yake Daga Hannu dan Yasa Masroor da Saurin Hannu
Juyawa Hafsatu tai ta K'alli Ahmad daketa sunne kai
"Haba Habibyna Kanaji Wannan dan Rainin Wayan yana Gayamin Magana san Rai Kah Kasa magana"
Sai Sannan Masroor yakai dubanshi Ga Ahmad
K'allan Sanni Masroor yakemai Anma ya manta a inda ya sanshi. Jan Hannun Hafsatu Ahmad Yayi yana cewa
"Ki Kyale kawai mu tafi inace ai kince zaki gayama Baffan ku"
Janta ya dingayi tana cigaba da zage zage Har suka bar wajan...

Juyowa Masroor yayi anma yaga Wayam bah Sulthana, K'allan Yasir Yayi da Alamar Mamaki
"Ina Yarinyan nan Take"
Yasir ya K'alleshi
"Tah Tafi"
Naushin Iska Masroor yayi
"Oh Shit! Meyasa Zaka bari tah tafi, Ni ban lura bah"
Yasir ya Bata Fuska Tareda juyawa
"Tho ina Ruwanka dah ita, Pls Kazo mu tafi"
A Sanyaye Suka Shiga motan Suka nufi Cikin Garin Sosai
Sunsha Wahala kamin Su gane Gidan Malamin, duk abinda Yasir keh buk'ata ya samu Sun dade a K'auyen Sannan Suka Nufi Gida..

A kofar gida Sulthana taga Mallan Zaune Yana K'arantar da Almajiransa, Hawayen Idonta ta share Tareda Rusunawa ta gaidashi. Bai amsa bah ya kauda kai, Gidan ta shiga tana cigaba da matsar kwalla. Mama ta gani a tsakar gida tana shan Iska, ta K'arasa ta Tsuguna ta gaidata Sannan ta aje Trayn ta koma Zaure ta zauna. Baffa bai Shigo Gidan bah Sai da Akai Sallan Magriba, Kwala mata kira yayi ta fito daga bayi dasauri Gabanta na dukan Uku uku, Dole yau tasan sai tasha dukan tsiya. Tana xuwa ta tsuguna a gabanshi ta fashe da Kuka Hade rai Yayi
"Mai Akai miki da zaki Hau Kuka, Ina Kudin Gyadan"
K'ara Fashewa da kuka tai Daidai nan Hafsatu ta shigo gidan tana Washe Baki da Ledar Kaza a hannunta. Jin Abinda Baffa yake cewa Yasa Tai Saurin K'arasawa wajan
"Wallahi Baffa K'arya take duk abinda ta fadama, Yarinyan nan Ashe Juye ake Mata. Yaudai Allah ya toni Asirinta na gani da idona wani dan Birni na mik'a mata Bugun Abuja dayawa Wallahi"

Hannu Baffa Ya dagama Hafsatu Alamar tai Shiru Sannan ya Kwalama Mama kira, Duk abinda akeyi tanajinsu banza tai dashi ya gaji da kiranshi ya Kyalle. Rannan Dukan tsiya Sulthana Tasha Abin Tausayi duk Baffa Ya Farfasa mata jiki. Zaure ta koma tai Kukanta mai Isarta Sannan Barci ya dauketa ga yunwa dake damunta..

Bayan Isha'i Wani d'an Yaro Almajiran Baffa ya Shigo da Sallama, Tsugunawa Yayi ya Gaida Mama Yace
"Wani neh a Waje yake Sallama da Ameenatu"
Mama tace
"Kaje kace tana zuwa"
Kwalama Ameenatun Kira Tai ta Fito daga Dakinsu Fuskanta bah Annuri jin Abinda ya Faru da Sulthana bayan ta dawo daga Gidansu Habiba. Mama Da Murnushi a Fuskanta Tace
"Maza kije ana Sallama Dak'e"
Tsaki Ameenatu tai
"Mama fah bai wuce Musa mai Kifi, Nidai Gaskiya bana Sanshi"
Hade Rai Mama tai Rai Bace
"Maza ki dau mayafinki Ki Wuce Kafin Raina ya baci. So kike kita zama a gida Muna K'allanki"
Daki Ta shiga tana Gungunai tadau Hijabinta tasa Ta nufi Zaure tana Turo baki, Sulthana ta gani kwance Tana Barci. Hawaye Suka ciko idonta Ta rintse ido Ta fita dasauri..

Tsaye ta Sameshi jikin wata Hadadiyar Benz, Sanye Yake da T shirt Bak'i da Brown Trouser. Hannunshi d'aya Cikin Aljihu D'ayan Yana Latse Latse a Wayarshi K'irar Samsung Galaxy S7.

 Ummy Abduol✍🏻
[28/08, 01:12] Friend Hussaini: πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
           πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
            *SULTHANA*
             πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

By *Ummy Abduol*

          *Page 76 to 80*

Hannunshi D'aya Cikin Aljihu D'ayan Yana Latse Latse a Wayarshi K'irar Samsung Galaxy S7. K'ara Mutsitsika ido tai Tabbas Dr Fareed ne, K'arasawa tai a sanyaye fuskanta dauke da murmushi, Sallama Tamai Ya dago kai Yana K'allanta Sanna Ya amsa.

Wayan ya saka cikin aljihu tadan sauke kai ta gaidashi ya amsa fuska a sake. Shiru ne ya biyo baya nadan wasu seconds, Yadan K'alleta yana Murmushi
"Ya jikin Kanwarki"
Kanta a K'asa tace Dasauk'i. Jim yayi sannan Yace
"Wel Ameena koh?"
Kai da daga mai Alamar eh. Sannan ya cigaba da cewa
"Dalilin Xuwana Shine Gaskiya ni Naga Sisternki Inaso, and so na Gaskiya nake mata, Bansani bah ko Zaki Taimaka min"
Gaban Ameenatu ne keta faduwa jin Maganganun dake Fitowa daga bakinshi, nan da nan gumi ya feso Mata. Jin Shirun yayi yawa yasa yace
"Kina jina?"
Kai ta gyada mai batareda tace komai bah, Hawaye ne Suk'a gangaro mata tai Saurin Kauda kai Sannan Tace
"Bah Komai ai anma bah mamanmu d'aya bah ita mamanta ta rasu"
Cikeda damuwa yace
"Allah ya Jikanta"
Ameen Tace Zuciyarta na Mata zafi, Ji take Kaman ta Fashe da Kuka a Wajan.

Ganin Shirun Yayi yawa yasa Tace
"Zan Shiga Gida, Saidai kai Hakuri dan Ta riga tayi barci"
Murmushi yayi tareda Sah Hannu a Aljihun Shi
"Babu damuwa Zan dawo gobe"
Kudi ya Ciro dayawa ya mik'ama Ameenatu anma tak'i Karba, Saida Ya hadata da Allah Sannan Ta K'arba Tamai Sallama ta Shiga Gida. Kamar Yanda Tabar Sulthana haka ta dawo ta sameta Kudundune tana Barci, Batace komai bah ta Shiga Cikin gida, Dakinsu ta nufa ta fada Kan Gadonsu ta Fashe da Kuka Mai Ban Tausayi.

Damuwa Masroor ya Shiga Tunanin Sulthana ya Hanashi Sukuni, Tunanin Halinda Take Ciki yake tabbas Yasan yarinyan tana cikin Mawuyacin Hali, Duk dah baisan meke faruwa da ita bah. Koda suka isa gida yana gaida Mami ya wuce dakinshi kai tsaye, wanka yayi tareda sallan la'asar ya fada kan gado, hugging pillow yayi yana tuna abinda ya faru dazu. Mikewa yayi dasauri tareda girgixa kai yana cewa
"No bah santa nake bah, Tausayinta neh Kawai"
Wayanshi ne Yayi K'ara Ganin Sunan dake wayo yasa Ya dauka a Sanyaye
"Hello" yace Sannan Yayi Shiru. Chan Yace
"Gani nan zuwa Mami"

Mikewa yayi ya Fita zuwa Falon Ya Fita A Stirs dinda zai Kaishi xuwa part dinsu Mami yaga Mahnoor tana K'okarin Zuwa side dinshi. Murmushi tai Tana Turo baki
"Bro Masroor tunda ka dawo kah daina tayani Assignment, Kuma kah daina Wasa dani"
Hararanta Yayi da Wasa
"Ai na lura neh yanzu bakida Kunya"
Kara Turo baki Tai Sannan Tace
"Mami toh na K'iranka"
Hannunta Ya Rik'e yana cigaba da Tsokanata Har suka K'arasa Side din Mami, Falon K'asa Suka sauko inda Mami ke Zaune tana Rubuce Rubuce a Wasu Takardu. Zama Yayi Sannan Yace
"Mami gani"
Dago Kai tai ta K'alleshi
"Son Yaya dai is anything Wrong"
Yadan Girgiza kai Yana cewa
"Bbu Komai I'm Fine"
Girgiza kai tai na Rashin Fahimta tace
"Shiknan, Pls akwai Mutane a Waje da Suke bukatar temako"
Kudi ta Dauko Bandir Guda Uku Yan Dubu D'aya ta Mik'amai
"Kah Rabamusu"

Girgiza kai Masroor Yayi Yana Y'ar murnushi
"No Mami zan Basu ki Aje Wannan"
Mik'ewa Yayi ya K'alli Mahnoor data Makaleshi Yana cewa
"Tho Sakeni Naje inda aka aikeni koh"
Turo baki tai tana buga k'afa a kasa
"Nidai muje tare"
Baice mata komai bah Ya Haura sama zuwa dakinshi, Bedside drawer'n dakinshi ya bude yadauko kudi Ya fito. Tsaye ya Samu Masroor Tana jiranshi, Hannunshi ta kama suka Fito farfajiyan Gidan. Ma'aikata neh burjik kowa nata aikinshi, Daga K'ai yayi inda Wasu Maza Masu aikin Gidan Ke Wanke Motocin Daddy. Tsayawa yayi chak yana K'allansu, Su sam mah basu lura dashi bah

Hannun Mahnoor Ya saki ya K'arasa Wajan motocin Y'ana K'allan daya daga cikinsu dak'e wanke Taya Yanata Surutu. Duka Sauran Suk'a zube suna Gaidashi, wanda ke Tsugunen Ya Dago Dasauri Suka Hada Ido Nan da Nan Jikinshi Ya soma Rawa Ya duk'ar dakai yana Raba idanu

Ummy Abduol✍🏻
[28/08, 01:12] Friend Hussaini: πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
           πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
            *SULTHANA*
             πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

By *Ummy Abduol*

          *Page 81 to 85*

Duka sauran suka zube Suna Gaidashi, Wanda ke tsugunen ya dago dasauri suka hada ido nan da nan jikinshi ya soma rawa ya Duk'ar dakai yana raba idanu. Bude Baki Masroor Yayi da niyar magana ya fasa, Juyawa yayi yabar wajan dasauri Cikeda Mamakin Ganin Saurayin nan da suk'e tareda marakunyar Yarinyan datamai Fitsara dazu. Kamar yanda Mami ta Umarta haka yayi, duk dunbin Mutanen dake Wajan saida ya raba nusu dubu d'ayi D'ayi Shida Mahnoor Sannan suk'a Shigo Gida, Saurayin nan ya Y'ara bi da K'allo Sannan Ya nufi Side dinshi ta K'ofar Waje...

K'iran Sallan Asubah ne ya tada Sulthana ta Mik'e dakyar saboda yana jikinta ke mata ciwo, cikin gidan ta shiga tai alwala da sauri sauri ta dawo zaure ta shimfida buhu tai Sallah dan tasan dah Baffa ya fito bah lallai baneh ya barta tai sallah, tana idarwa taji k'aran bude kofan Baffa, Saida yayi alwala sannan ya nufo zauren..

Haskata yayi da torch light Ganinta zaune yasa ya bata fuska yace
"Kindai san bah ruwa a rijiya koh, Maza ki tashi duk inda xaki samo ruwa kije ki samo"
Mik'ewa tai da Sauri har Saida tadan saki Y'ar K'ara, nan da nan idonta ya ciko da K'walla, Jikinta duk Ciwo yak'e mata kuma a haka Baffa yace ta dibo Ruwa. Yana Fita ta koma ta zauna ta fashe da kuka a Hankali, Jikinta take Tabawa tana Kuka Sosai, K'ayanta dake Cikin Poly bag ta fara bincikawa, Wani Zani ta Ciro ta rungume ta k'ara Fashewa da kuka tana Turo Baki
"Umma meyasa Zaki tafi ki Barni, Baffa Baya sona. Nima inaso na mutu nazo inda kike"
Kuka take Sosai, sai bataji Zuwan Mama bah sai hasketa da Torchlight datai

"Sulthana Kukan meh Kike"
Mik'ewa tai dasauri ta share Hawayen Fuskanta,
"Babu komai"
Zanin ta mayar inda yake Ta nufi Cikin Gidan, Bokitin K'arfe ta dauka ta Fita. Abinda Ya daure mata kai bai Wuce K'in Amsa gaisuwanta da Ameenatu tayi bah. Haka ta Cigaba da Tafiya tana Mamaki, Duk Gidan Tasan Masu Santa daga Ameenatu sai Mama, Har ta Nufi Rijiyan Burtsasai sai ta tuna Rijiyansu Sadiya bai K'afewa. Murmushi ne Ya subuce mata ta nufi gidan dasauri..

A tsakar gida taga Maman Sadiya da ita sadiyar suna alwala, dagowa sukai tareda amsa sallaman datai cikeda mamakin ganinta a wannan lokacin. Mama na gamawa ta mik'e tace
"Yaki nan Sulthana"
Bokitin ta aje ta k'arasa inda Maman take, Hannunta ta rik'e duka biyu tana haske Jikinta da torchlight, sanin shedan duka yasa ta girgiza kai ta dago ta k'alleta
"Waya dukeki Sulthana"
Shehekan kuka ta soma tana turo baki a hankali
"Baffa neh ya dukeni jiya"
Sadiya ta k'araso wajan itama fuskanta bah walwala
"Sulthana me kika fito yi da asubah"
Bokitin data aje ta k'alla
"Koba Baffa baneh yace naje na dibo ruwa"
Girgiza kai Mama tai cikeda takaicin Hali irin nah Mallan Jamilu, Bokitin ta dauka da k'anta ta diban mata tareda daurata akai ta tafi gida. Sahu tai Yakai Goma daga Gidansu zuwa gidansu Sadiya, Duk sanda taje Mama je diban mata ta kuma Daurata ta nufo Gida. Ana K'arshen Mama ta zaunar da ita taci abinci ta Koshi sannan ta nufi gida Cik'eda murna..

Yauma gyadar ta dafa K'amar kullum, A tray ta juye Tana kici kicin dauka, Ameenatu ce ta shigo cikin gidan da sallama hannunta dauke da leda da alama daga aike take, K'allanta tai tana d'an murmushi
"Yaya Ameenatu dazu na Gaisheki baki amsa bah, Koh baki ji baneh"
Harara Ameenatu ta wurga mata tareda kauda kai, Mamaki sosai Sulthana har ta k'asa boyewa
"Yaya Ameenatu menai miki, dan Allah kiyi hakuri"
Tsaki Ameenatu tai tana nunata da D'an Yatsa
"Keh karna k'arajin kin kira. Sunanan a gidan nan idan bah haka bah wallahi zaki sani"

Bata jira mai Sulthana zatace bah ta bar wajan tana tsaki, hawaye ne masu zafi suka gangaro mata
"Shiknan Ameenatu ta daina santa, yanzu ina zata waiga taji sanyi"
Durkushewa tai ta fashe da kuka mara sauti, Jin k'amar sheshekan kuka yasa Mama ta fito dan ko ba'a fada mata bah tasan Sulthana neh. Durkushe ta sameta gaban Gyadan,
"Sulthana kedai kuka bai miki wuya, mai makon kizo ki gayamin ai dana dauraki"
Mik'ewa Sulthanan tai Mama ta daura mata gyadan tareda mata Kashedin K'arta kula maza, Sannan idan har tasan maza na mata juye tho ta daina. Tho kawai tace ta fita zuwa Bakin kasuwa inda ta daba Zama. Tana Cikin Tafiya taji ta bayanta ana Cewa
"Sulthana bako gaisuwa"
Juyawa tai dasauri, K'allanshi ta tsaya yi nadan Wasu Seconds. Ganin bata ganeshi bah yasa yayi murnushi ya k'araso inda take Tsaye
"Baki ganeni bah koh"
Kai ta gyada mai batareda tace komai bah...

Murmushi ya K'arayi yana k'allanta
"Nine likitan dana dubaki ranan a Chemist"
Sai a sannan ta tuna, idanunta ta sauk'e k'asa tace
"Ina Wuni"
Amsawa yayi yana Mata murmushi, Ganin Tana kokarin tafiya yasa yasha gabanta dasauri
"Ina zaki bamu gama magana bah"
Turo baki tai idonta ya ciko da Kwalla
"Dan Allah kaban hanya na wuce"
Ganin yanda Hawaye ke gangarowa a idonta yasa ya matsa jiki a sanyaye ta wuce, Binta da K'allo yayi harta bace ma ganinshi. Ajiyan zuciya ya sauke, Zuciyarshi ta shiga raya mishi
"Yarinyan nan tana cikin Damuwa"
Kamar zai bita ya Fasa ya shiga mota ya nufi Cikin Garin Kano...

Ummy Abduol✍🏻
[28/08, 01:12] Friend Hussaini: πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
           πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
            *SULTHANA*
             πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

By *Ummy Abduol*

          *Page 91 to 95*

Turo baki Masroor yayi ya mik'e yabar Dinning din
Girgiza kai Mami tai
"Ai kai bakasan Maganan aure"
Mik'ewa Daddy yayi
"Zan Tafi Office daga nan zanje Meeting da Party chairman"
Fatan Alheri Mami tai mai ya fito bodyguards dinshi suk'a budemai Kofan mota ya shiga, Driver yaja Sukabar Gidan Tareda Suran Bodygyards din da Suke a wata motar daban..

Kamar Jiya yauma Bakin K'asuwar Masroor yazo anma baiga Sulthana bah, yaranda ke wajan ya tambayan sukace mai bata zo bah. Hankalinshi  ne ya tashi, motarshi ya shiga ya shiga cikin kauyen, duk inda ya kutsa da mota K'allanshi ake bama kaman mata. Tsaki yayi ya kauda kai ya cigaba da driving, ya dad'e yana kewaye Garin kafin ya koma gidah ranshi babu dadi..

Sulthana kuwa tana dauk'ar tallanta tasha ta nufa dan ma k'artaga Wannan dan Birnin, Batako dad'e bah ta saida Gyadarta ta dawo gida cikeda Farinciki. Abu guda keci mata tuwo a kwarya rashin Sake fuska da Ameenatu batamata yanzu, Hakan yasa ta yanke hukuncin ta sameta taji koh wani laifin tai mata. Tana zaune Zaure Baffa ya fita wajan Almajiranshi, tana ganin ya fita ta mik'e ta shiga cikin Gidan, Dakinsu Ameenatun tai Sallama ta Shiga, Kwance ta samu Ameenatun akan Sallaya. Jin muryan Sulthana yasa ta mik'e zaune
"Keh Wacce irin Dabba ce idan anyi Sallama bah bari ake sai mutum yace a shigo bah"
Dagowa Sulthana tai dasauri tana K'allan Ameenatu da mamaki, tunda take da Ameenatu bata taba mata Fada bah sai yau. Idonta neh ya ciko da K'walla ta zauna dabar a Kasa tana k'allan Ameenan daketa cika tana batsewa
"Yaya Ameenatu mai nai miki kike fushi dani, idan namiki magana bakya amsa min"
Mik'ewa Ameenatu tai tana nuna mata k'ofa
"Fita daga dakin nan ko yanzu nai miki dukan tsiya, dah ina ganin laifin Baffa dayake azaptar dake ashe ko da Gaskiyar sa"
Kuka Sulthana ta fashe dashi

"Dan Allah yaya Ameenatu kiyi haquri idan na miki laifi bazan sake bah"
Mari mai rai da Lapia Ameenatu ta dauke Sulthana dashi
"Zaki fita koh saina babbala ki"
Dagudu ta fita ta nufi zaure tana cigaba da kuka, kukanta neh ya fitoda Mama daga daki
"Lapia meke Faruwa Sulthana"
Lekowa cikin gidan tai ta zube gaban Mama tana cigaba da Kuka, Dagota tai tsaye
"Yi Shitu fadamin menene"
Tsagaita kukan tai
"Yaya Ameenatu ne ta mareni bansan menai mata bah"
Da mamaki Mama tace
"Mari?"
Kai Sulthana ta gyada tana cigaba da kuka, Lallashinta Mama tai dakyar tai shiru ta koma zaure ta zauna tareda hade kai da Guyiwa...

Mama ta kwalama Ameenatu kira ta fito tana gungunai,
"Haba Ameenatu mai Sulthana tai miki da zaki mareta, ki tuna fah keh kadai take rab'a tanajin dadi"
Tsaki Ameenatu tai tareda kauda kai
"Mama ni yanzu kawai naji na tsani Sulthana"
Da mamaki Mama ta K'alleta baki bude
"Kinko san Abinda kike fada Ameenatu"
Gyada kai Tai tareda barin Wajan, Abin ya dad'e yanaba Mama mamaki, Tabbas akwai wani abu da Ameenatu ke boyewa..

Bayan isha'i Sulthana na Kwance Yaro ya shigo zauren harda zai shiga cikin Gidan Ya dawo inda tak'e Kwance
"Sulthana ana sallama dake a Waje"
Mik'ewa zaune tai dasauri tareda zaro ido
"Wanene?"
Girgiza kai yaron yayi
"Bansan waye bah, Wani ne dai a mota"
Zazzaro ido take cikeda tsoro, Kaje kace bana nan. D'an jim Yaran yayi sannan yace
"Jiya yazo wajan yaya Ameenatu kila sako zai baki ki kai mata"
Jin haka yasa ta mik'e tadau dankwalinta ta daura ta fito kofar gidan. Zaune yake cikin mota yana latse latse a wayanshi, k'arasawa tayi bakin Motan cikin muryanta mai Sanyi tace
"Ina Yini"
Dagowa yayi ya k'alleta da Murnushi kwance kan Fuskanshi
"Lapia lau Sulthana, Ya gida"
Lapia tace a takaice..

Fitowa yayi daga cikin motan ya tsaya, shiru ne ya biyo baya nadan mintina Sannan ya dago ya K'alleta kanta a k'asa yace
"Sulthana"
Dagowa tai tadan K'alleshi sannan ta maida kai tace
"Na'am"
Ajiyan zuciya ya sauke yace
"Shekaranki nawa?"
Dan Jim tai kamar karta fadamai sai kuma ta dan dago batareda ta kalleshi bah tace
"Sha hudu"
Jinjina kai yayi yace
"Ajinki nawa a makaranta"
K'ara dago kai tai ta K'alleshi tareda girgixa kai
"Bana zuwa makaranta"
Kallanta yayi da Mamaki
"Meyasa?"
Kauda kai tai tareda turo Baki
"Baffa ya cireni"
Kallanta ya tsaya yi, Abinda ya fahimta da Yarinyan shine tana fuskantan kiyaiya a gidan zai iya cewa wajan kishiyar mahaifiyarta kuma abinda ya burgeshi da ita sam batasan wani bare yasan halinda take ciki.

Hakan ya burgeshi sosai, Muryanta yaji tana cewa zan shiga gida kada Baffa ya fito ya ganni. Bata jira mai zaice bah tabar wajan ta shiga cikin gida. Kurri yana kofar gidan, tausayin Sulthana ke ratsa shi. Runtse ido yayi ya bude a hankali yace
"Ina sanki Sulthana, zan iyayin komai a kanki. Insha Allahu zaki fita daga k'angin da kike ciki kwanan nan"

Ummy Abduol✍🏻
[28/08, 01:12] Friend Hussaini: πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
           πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
            *SULTHANA*
             πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

By *Ummy Abduol*

          *Page 86 to 90*

"Yarinyan nan tana cikin damuwa"
Kamar zai bita ya fasa ya shiga mota ya nufi Cikin garin kano. Zama tai Bakin Bishiyan Data saba Zama, Gyadan ta soma saidawa kamar yanda ta Saba. Atika dake kusa da ita tana saida Rogo ta yafici Ladi tana nuna mata wata hadaddiyar mota datazo wucewa
"Kai Ladi ji Wachan motan, Tafdi! Ni tunda nake ban taba ganin mota mai sama a bude bah"
Kyalkyacewa da dariya ladi tai tana tafawa
"Kai Wallah Motan nan Akwai Kyau, Allah ka bamu irin wanna motan"
Jin Yanda suke zuzuta motan yasa Sulthana ta dago ta K'alli motan, Lallai kuwa motan yanada Kyau, Murmushi ta soma tanabin Motar da K'allo. Duk mutanen dake K'asuwan kowa bin motar yake da K'allo cikeda Sha'awa, Wanda ta gani Cikin motan neh yasa Fara'ar dake Fuskanta yakau, Hijabin Fuskanta ta Turo Gaba ta Rufe Fuskanta dashi..

Zagaye yake yana yatsine Fuska, Waje ya samu yayi Parking Sannan ta fito. Mata sa binshi da K'allo suke harda Mazan, Dan D'an gayu neh na K'arshe. duk gungun Yara masu talla daya gani sai ya tambaya tareda Fadin sunanta anma duk suce basu santa bah, Ganin Yana Kokarin nufosu yasa Sulthana ta mik'e tana K'okarin daukan trayn Gyadan tah k'araf suka hada ido, Dauke kai tai Ta dauki Trayn Gyadan ta Fara tafiya. Binta Yayi tateda Kiran sunanta, Juyowa tai ta Murguda mai Baki
"Kah daina kiran sunana kuma ka daina bina"
Murmushi Yayi yanda ta murguda bakin Saita k'ara mai kyau
"Meyasa zakice na daina binki"
Batareda ta juyoba tace
"Nidai Dan Allah ka daina bina kada Yaya hafsatu ta ganmu taje ta fadama Baffa, Idan ta fadama Baffa dukana zeyi, Jiyama saida ya dakeni"

Tausayi ta bashi Ya sha gabanta yana K'allanta
"Kiyi Hakuri nasan mu muka ja miki dukah koh"
Batace mai komai bah tana k'okarin tafiya, hannu ya daga mata Yana cewa
"Tsaya mana, kudinki na jiya nakeso na Baki"
Kauda kai tai gefe
"Kah barshi, nidai dan Allah ka bani Hanya na Wuce"
Matsa mata Yayi ta soma Tafiya Yana K'allanta, meya tuna ya bita da Sauri tareda shan gabanta
"Tsaya tho kiji"
Tsayawa tai hannunta d'aya a kugu
"Inaso gobe mu hadu a Inda kike saida Gyada kamar wannan lokacin kinji"
Batacemai Komai bah ta cigaba da tafiya abinta. Binta yayi da K'allan tausayi, A Ranshi Yana raya
"She's Cute n Young, She need help. No matter how Zaki Kasance Cikin Farinciki nan daba"

Motarshi ya nufa dan komawa gida, Yara ya gani Yayyabe da Motan Sunata Shafawa, K'arasawa yayi dasauri ya koresu. Ganin Sunki Tafiya yasa ya Dauko bandir din yan Hamshin ya soma Raba Musu, ai a nan yaga wawaso harda manya. Tausayama Halinda yan K'auyen suke ciki yayi. Motan ya shiga ya tada Yabar kauyen Cikeda Tausayin Sulthana...

Gida Ya nufa Kai Tsaye, Horn yayi masu Gadi Suk'a budemai kofa, Saida yayi Parking Sannan ya Fito. Bodyguards din dadd ya gani a tsakar gidan, Murmushi Yayi
"Wel daddy is back"
Main palour ya nufa tareda Danna Bell, wata mai Aiki ce ta bude Tareda Zubewata gaidashi, Bai amsa bah ya Shiga falon Yana Fara'a Baiga kowa A falon bah. Wani Corridor ya nufa wanda zai sadashi dah Dinning area, a nan ya gansu zazzaune suna Lunch. Sallama yayi ya k'arasa ya rungume Daddy Yana dariya,
"I Missed uh Daddy"
Murmushi Daddy yayi Yana Shafa Kanshi cikeda Zolaya Yace
"Sai Kace nayi shekara kwana biyu fah nai"

Turo baki Mahnoor tai tareda Rungume Hannayenta
"Daddy kacema Bro Masroor ya daina Rungumeka shi babba neh"
Zama Masroor yayi akan Kujera suka fashe da Dariya duka, Hararanta yayi
"Lallai baki isah bah, Ai daddy nane"
Idonta ne ya ciko da K'walla ta kara hade rai tace
"Daddy na dai"
K'ara Fashewa da dariya sukai duka. Ganin Sunata mata dariya yasa ta fashe da kuka ta mik'e Tabar wajan tana kuka..

Hararan Masroor Daddy yayi
"Kaga kah koranmin Baby koh, Tho Maza ka tashi ka Lallasheta ta dawo taci abinci"
Turo baki Masroor Yayi yana Kai Loman Abinci
"Daddy kah kyaleta cikin wah Bah nata bah, Karta Cin"
Lekowa Mahnoor tai Tana Share kwalla
"Baza'a kyaleni din bah."
Guntse Dariya Mami da Daddy sukai dan Yanzu sunayi zasu takalo Rigima..

Rungume Mami tai ta Baya ta shagwabe Fuska
"Mami yanzu bro Masroor baya sona, Bro Yasir ne kawai ke Sona"
Cup din Juice Masroor ya dauka ya kora Sannan ya aje Yana cewa
"Kedai kika sani"
    "Ahan ina Kaje dazo baka fadama Yasir bah,  yazo nemanka neh kuma nasan din inda zaka tare kuke zuwa"
D'an jim yayi sannan yace
"Eh wannan fitan ni kadai neh, Banda Shi"
Murmushi Daddy yayi cikeda Nishadi
"Koh anje Wajan Sirikan nawa neh"
Suman Kanshi Ya Shafa Yana Y'ar Dariya.
"Aa Daddy"

Mami Itama Dariyan tai
"Ai dama bazaka fada bah, tho bari kaji gwara fa kama fada tun yanzu coz ana gama Hayaniyar siyasan nan Zamuje neman aure"
Turo Baki Masroor Yayi ya mik'e yabar Dinning din...

Ummy Abduol✍🏻
[28/08, 01:12] Friend Hussaini: πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
           πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
            *SULTHANA*
             πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

By *Ummy Abduol*

          *Page 96 to 100*

"Ina sanki Sulthana, zan iyayin komai a kanki. Insha Allahu zaki fita daga k'angin fa kike ciki kwanan nan"
Motanshi ya shiga yabar wajan cikeda tausayin halinda Sulthana take ciki.

Da zazzabi Sulthana ta tashi da asubah, dakyar ta iya mik'ewa ta fito tsakar gidan. Alwala tai ta koma zaure tai Sallah, Tana zaune Baffa ya fito ya tafi masallaci. Kasa shiga tai aikin data saba tayi a cikin gidan har wuraren k'arfe bakwai da rabi, Ameenatu ce ta fara fitowa daga daki ganin ko'ina batsa batsa yasa ta nufi zaure a fusace. Kwance ta sameta tanata rawar sanyi, tsaki Ameenatu tai tana magana cikin daga murya
"Wato dan kin raina mutane yau bazaki je kiyi aikinki bah. Uban wa kikeso ya miki shara da wanke wanke"
d'an dagowa Sulthana tai hawaye na gangarowa a idonta
"Dan Allah yaya Ameenatu kiyi hakuri banida lapia neh"
Duka takai mata dai dai nan Hafsatu ta k'araso wajan tana Murmushin Mugunta
"A'a yaya Ameenatu yau kuma Y'ar son ake duka"

Tsaki Ameenatu ta k'arayi tana nuna Sulthana da yatsa
"Wallahi idan baki tashi kinyi aikin daya kamata bah sai na miki dukan tsiya"
Kallanta hafsatu tai da mamaki, Yau kuma Ameenatu kecewa zata duki Sulthana, Lallai abin babba neh.
Kasa tashi Sulthana tai sai kuka datake Mara sauti, dakyar ta mik'e ta zauna tana k'allan Ameenatu data hada girar sama data k'asa
"Dan Allah yaya Ameenatu kiyi Hakuri"
Ai kamar zugata take nan da nan ta rufeta da duka, Hafsatu taga bati itama ta tayata. Bah abinda Sulthana take in banda ihu. Ihunta ya fito da Mama ta K'araso wajan dasauri..

Dakyar ta kwace Sulthana a hannunsu a fusace tace
"Wannan wanne irin iskanci meh Ameenatu, wai meke daunki me? Metai muku kuke dukanta haka kamar Allah ya aiko ku"
Ameenatu ta hade rai tana huci
"Dan wulakanci tun dazu yarinyan nan batai aikin gida bah, jibi gidan nan sannan ina mata magana tana cemin wani batada lapia"
K'allan Ameenatu Mama ta tsaya yi
"Lallai Ameenatu baiwarki ce ita da zakice dole sai tamiki aiki, ai rashin lapia ya wuce komai sai kuyi mata uzuri"
Hafsatu ta chuno baki
"Haba Mama ke kullum sai ki rinka hana ana hukunta yarinyan nan, Gaskiya..
Saukan Mari Hafsatu taji a fuskanta, a fusace Mama tace
"Wallahi ki kiyayeni Hafsatu, na lura abubuwanki nema suke su wuce wuri"
Nunasu da dan Yatsa tayi tana cewa
"Tho bari kuje, daga yau Sulthana bazata k'ara aikin gidan nan bah ku zakuyi. Meye ku anfanin ku"
Baffa ne ya bankado kyauren gidan ya shigo jin hayaniya, cirko cirko ya samesu a tsaye sai Sulthana dake Zaune a kasa tana kuka duk jini a hancinta da baki..

"Lapia??" Baffa ya tambayi Mama, Hafsatu ce ta koromai bayanin duk abinda ya faru. Nan ko Baffa yahau sababi ta inda yake shiga batanan yake fita bah, Ameenatu ta kalla yana cewa
"Ku cigaba da dukanta ai wannan ma iskanci neh"
Hafsatu ce ta cigaba da dukanta Mama na tsaye tana k'allan Baffa cikeda takaici, batace komai bah ta koma dakinta ranta bace. Itama Ameenatu daki ta koma a fusace, ligi ligi Hafsatu taima Sulthana Baffa na Tsaye. Saida ta duketa san rai Sannan ta kyalleta, Sannan Baffa yasata tai duk aikin Gidan yana Tsaye. Tanayi tana kuka dakyar tai aikin ta gama ta koma zaure ta zauna ta cigaba da kukanta..

Nan da nan wani sabon Zazzabin ya rufeta. Ana Sallan Azahar Baffa ya kwalla mata kira, ta nufi Cikin gidan dasauri, gyada ya mik'a mata. Ta amsa dasauri ta hau wankewa, tana gamawa ta daura a wuta ta zauna bakin murhun ko sanyin datake ji zai ragu. Bata gama bah sai bayan La'asar sannan tadau Gyadan ta nufi bakin kasuwa. Inda ta saba zama ta aje gyadan, zama tai ta hada kanta da guiwa ta fashe da wani sabon kukan, murya taji a kusada ita mai sanyi yana cewa
"Meke damunki Sulthana whats wrong"
Dago runanun idanunta tai duk a tunaninta likitan nan neh, Ganin Masroor yasa ta maida fuskanta ta cigaba da kuka. Runtse ido Masroor yayi ya dunkule Hannayenshi, jin kukanta yake har cikin Ranshi nan da nan shima idanunshi suka chanza launi..

"Sulthana, meke damunki? Tel me pls"
Dago kai tai tana turo baki, ganin yanda take karkarwa yasa ya mik'e dasauri
"Sulthana are you sick?"
Dauke kai tai tana cigaba da turo baki, dakyar ta iya mai magana shima tanayi hakoranta na karo da juna
"Nidai ka daina zuwa inda make, idan Yaya hafsatu taganni zata fadama Baffa kuma dukana zaiyi"
Tsugunawa yayi gabanta cikeda damuwa
"Sulthana fadamin meke damunki, nasan kina cikin damuwa. Me hafsat take miki itada Baffa"
Mik'ewa tai dasauri tana k'akabe Riganta, trayn gyadan ta sunkuya zata dauka yayi saurin rik'ewa
"Please Sulthana ki tsaya ki saurareni, Am here to help uh. Taimakonki zanyi, ki fadamin ko menene nikuma na miki alkawarin zan kawo karshen koma menene"
Tsayawa tai ta tana K'allanshi da Alamar mamaki...

    Tho fah ga *Doctor Fareed* Ga *Masroor*
       Shin Fans wah kuka zabarma Sulthana ya taimaka mata?? Nidai nace......

Ummy Abduol✍🏻
[28/08, 01:12] Friend Hussaini: πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
           πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
            *SULTHANA*
             πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

By *Ummy Abduol*

          *Page 101 to 105*

Tsaya tai tana K'allanshi da Alamar mamaki. kai ya gyada mata
"I mean what I said"
Sai a Sannan ya K'alleta da kyau, a rudeyace
"Sulthana maiya sameki a fuska? Wayaji miki ciwo?"
Shafa wajan tai, batace komai bah
Trayn Gyadanta ta fuzge ta daura akai ta soma tafiya. Binta yayi yana mata magana anma ko sauraranshi batai bah tayi tafiyarta. Ranar Sulthana batai ciniki nah hakanan ta koma gida, Duka kuwa saida tasha shi Wajan Baffa. Haka tai kukanta ta gaji ta kwanta, yauma k'amar jiya Yaro ya shigo yace Ana Sallama da ita, turo baki tai tacema yaron yace bazata zo bah haka koh akai, Yaron ya koma yagayama Fareeed Sakon da Sulthana ta bashi..

Baice komai bah ya bude mota ya dauko wani k'aton leda, yaron ya mik'ama wah
"Dan Allah gashi ka kai mata kaji"
Hannu Yasa a Aljihu ya ciro dubu daya ya mik'a ma Yaran
"kai kuma ga naka"
Washe baki Almajirin yayi tareda godiya, ledan ya shiga dashi cikin zauren ya bah Sulthana, zaro ido tai tana k'allan almajirin
"Dan Allah ka maidan mai kada Baffa ya gani kace nace banaso"
Niki niki yaron yadau leda ya koma dashi, yana fita yaga wayam bah motan Dr Fareed. Dawowa yayi ya shaida mata ya aje ledan ya fita, jikinta neh ya soma rawa yanzu idan Baffa yaga ledan nan tasan duka zataci. Sadiya ce ta fado mata a rai ta dau ledan dakyar ta nufi gidansu sadiya cikeda Fargaba..

Da sallama ta shiga Allah ya taimaketa Baban Sadiya baya nan, saida ta gaida Maman Sadiya sannan ta zaiyana mata duk abinda ke Faruwa, ga mamakinta sai gani tai Maman Sadiya ta washe Baki.
"A'a Sulthana wannan ai abin farinciki neh"
Hannu ta daga ta godema Allah sannan ta k'alli Sulthanan data sake baki tana k'allan Mama
"Ina tayaki murna Sultana, insha Allahu komai ya kusa zuwa karshe. Ni nasan wannan likitan sanki yake"
Gwalalo ido Sultana tai idanunta suk'a ciko da kwalla, Mama ta cigaba da cewa
"Kinga idan kikai aure komai zai zamo tarihi, zaki fita daga cikin wannan wahalan da kike ciki"
Rufe fuska Sulthana tai tana murmushi. Rungumeta Sadiya tai tana cewa
"Iyeh! Amarya"
Dukan wasa Sulthana takai ma Sadiya, kyalkyalewa da dariya Sadiya tai cikeda farinciki.

Mik'ama Mama ledan tai tareda mik'ewa
"Mama idan Baffa yaga wannan kayan dukana zeyi"
Amsan kayan Mama tayi ta hau dubawa, Hadaddun kayane kala kala. Dogayen riguna, Atamfofi da lesuka ready maid. Sai takalma da turaruka. Sakin baki sadiya tai
"Tab ni ban taba ganin irin wannan kayan bah"
Tabe baki Sulthana tai
"Mama kiyi anfani dasu keda Sadiya"
Dago kai Mama tai tana k'allanta, girgiza mata kai tai
"A'a bazamuyi anfani dashi bah Sulthana, na miki alkawarin zan aje miki su har lokacin da kika bukata"
Girgiza kai Sulthana tai tana cewa
"A'a kiyi anfani dasu"
Tsofafin Silifas dinta wari daban daban tasa tace
"Mama na tafi kada Baffa ya fito bai ganni bah"
Sallama Mama tai mata Suka fito tareda Sadiya, kara kyalkyalewa da dariya Sadiya tai
"Amarya knan"
Duka Sulthana ta d'aka mata tana hararanta
"Banaso fah"
Murmushi Sadiya ta rik'e haba tace
"Niko inasan naga wannan saurayin d'an birni"
Turo baki Sulthana tayi tana yatsine Fuska
"Nidai bana sansa"
Sakin baki Sadiya tai batace komai bah, a haka sukai sallama Sulthana ta nufo gida dasauri...

A kofar gidansu taga Ahmad saurayin Hafsatu, K'allanshi tayi da nufin gaidashi ganin ya balla mata harara yasa sum sum ta shiga Gida, kan buhunta ta zauna tai shiru. Haskota akai da torchlight ta mik'e dasauri muryan Hafsatu taji tana cewa
"Gatanan ta dawo"
Gabanta ne ya fadi Dam! Shiknan yau tasan nata ya K'are..

Baffa ne ya kwalla mata kira ta amsa ta shiga cikin gidan jikinta na rawa, Cirko cirko ta samesu a tsakar gidan, Ameenatu sai Balla mata harara take. Tsugunawa tai Sannan tace gani.
Baffa rai bace yace
"Waye Saurayin nan da hafsatu taganku dashi Ranan"
Gaban Sulthana ne ya fadi
Daka mata tsawa Baffa yayi
"Badake nake magana bah"
Muryanta na rawa tace
"Baffa wallahi ban sanshi bah, ranan kudin gyada na zai bani"
Mari Baffa ya dauketa dashi yana huci
"Bazaki fadamin Gaskiya bah"
Kuka Sulthana ta fashe dashi ta soma Rantse rantse
"Wallahi Baffa bansanshi bah"
Ameenatu ce ta amshe da cewa
"Karya kikeyi, wato Sulthana kin Fara kula kulan maza koh? Ai dama tunda naga wannan likitan nasan dan iska neh"
Sai a sannan Sulthana ta gane inda maganansu ta dosa
Daki Baffa ya shiga ya dauko Bulala, Sulthana na ganin haka ta kwala ihu tana kuka sosai

"Dan Allah Baffa kai hakuri Wallahi bansanshi bah"
Hafsatu tace
"Rannan Ahmad yake gayamin ya ganshi, kyaleta nai kawai ban fadaba sai yau kuma ni da idona naganshi Yazo yaba wani yaro katon leda ya kawo mata, shiyasa dana tambayi Mama sulthana ta kawo mata leda tace wani leda"
Tsula mata bulala Baffa yayi ta saki ihu ta fashe da kuka. Tana kururuwa
"Dan Allah Baffa kai hakuri bazan Sake bah"
K'asa magana Mama tai ta koma daki abinda cikeda bakin ciki
Saida Baffa yaga bata numfashi Sannan ya kyalleta Sukai shigewansu daki suka barta nan warwas a tsakar gidan...

Mamace ta fito jin sun shige daki, kuka ta fashe dashi mara sauti ganin Sulthana kwance. Daki ta koma ta debo ruwa ta yayafa mata, ajiyan zuciya tai ta K'ara fashewa da kuka tana ihu
"Baffa kai hakuri, Wayyo baffa zai kasheni. Yaya Ameenatu ki taimakeni"
Saurin rufe mata baki Mama tai itama tana kukan, Dakinta ta kaita ta dawo ta hada wuta ta daura mata ruwan wanka, ruwan na zafi ta surka ta kai mata ban daki. Da taimakon Mama tai wanka, nan da nan Zazzabi ya rufeta, magani Mama ta bata tasha Barci mai nauyi ya dauketa. Sai gaf da Asubah Mama ta tasheta ta koma zaure gudun kar Baffa yazo fita massalaci bai ganta bah...

A Bangaren Masroor kuwa koda ya koma gida kasa sukuni yayi, Falon k'asa ya zauna yayi shiru, Mami ce ta sauke zuwa falon ganin Masroor zaune ya k'urama tv ido anma daga gani hankalinshi ba'a tv take bah. Zama tai kusa dashi tadan Tabashi, Razana yayi ya juya ganin Mami yasa ya saki ajiyan zuciya.
"Lapia Meke damunka son" cewar Mami
D'an Murmushi yayi yana girgiza kai
"Nothing Mom"
Kauda kai Mami tai gefe fuskanta bah Walwala
"Masroor bakada kamana, ni yakamata ka fadama damuwanka."
Sumar kanshi daketa kyalli ya shafa yana y'ar Murmushi
"Mami bah komai karki damu"
Bell aka danna, Cikin Maid din gidan ta shigo dasauri ta bude kofan, Mahnoor ce ta shigo dagudu ta wurgama Maid din jakan Makarantan tah tana Murmushi
"Mamina I'm back"
Ganin Mami yasa ta nufeta dagudu ta rungumeta tana dariya
"I Missed you Mami"
Masroor ta k'alla taga sai hararanta yake..

chuno baki tayi
"Mami wai meyasa ya Masroor sai ya rinka eyeing dina"
Sumar kanshi ya shafa
"Mami K'arya take"
Hararanshi Mami tayi
"Banasan Haka fah, ka daina hararan min Y'a"
Baice komai bah yabar Falon..

Ummy Abduol✍🏻
[28/08, 01:12] Friend Hussaini: πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
           πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
            *SULTHANA*
             πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

By *Ummy Abduol*

          *Page 106 to 110*

         *Masoya Littafin Sulthana naga sakonin ku da dama wasu ban samu na karanta bah. Abinda nikeso ku gane a nan shine* _labarin Sulthana ya faru ne dagaske_ *So duk abinda kuka gani a ciki bah k'irkira nai bah abu ne daya faru dagske. Sannan Fans din Masroor da na Dr Fareed kowacce tasa ido taga Yadda labarin zai k'arke, yanda yazo a labari hakan zan baku a rubuce insha Allah. Ina fatan zaku fahimceni*..

         Wannan Shafin Naku neh *Sulthana Fans* Allah yabar k'auna

Hararanshi Mami tayi
"Banasan haka fah, ka daina hararan min y'a"
Baice komai bah yabar falon. Bell aka k'ara dannawa Maid ta fito dasauri ta bude kofan, Yasir neh ya shigo da sallama ya karasa inda Mami ke zaune ya tsuguna har K'asa ya daidata. Da fara'a a fuskanta ta amsa tareda tambayanshi mutan gidan, ya amsa mata da lapia lau. Mutum nashi ya tambaya Mahnoor ta fadamai yana daki, mik'ewa yayi ya hau sama ya nufi side din Masroor..

Kwance ya sameshi kan Three seater cikin hadadden Falon shi yana k'allan celien, Zama yayi k'an 1seater kusa dashi tareda dafashi
"Friend its anything wrong"
K'akaro murmushi Masroor yayi yana k'allanshi
"No I'm fine"
Ajiyan zuciya Yasir ya sauke harya bude baki zaiyi magana aka danna bell din Falon, mik'ewa yayi ya bude kofan, cikin ma'aikatan gidan neh dauk'e da tray cikeda kayan ciye ciye, kan center table din falon ta aje ta fita tareda jawo kofan. Komawa Yasir yayi ya zuna yana facing Masroor da yanayinshi ya chanza..

"Friend tel me something, meke damunka coz bah haka kake bah"
Mik'ewa zaune Masroor yayi yana k'allan Yasir. Bai boyema Yasir komai game dashi kamar yanda shima Yasir din bai boyemai komai. Sumar kanshi ya shafa ya fara magana cikin sanyayar muryanshi
"Kah tuna yarinyan nan da naso bigewa ranan da mukaje kauyen nan"
Kai Yasir ya daga alamar eh, cigaba da magana Masroor yay
"I donno why I always think of her, kullum cikin tunaninta nake. Ina tausaya mata coz alamu sun nuna she need help"
Murmushi Yasir yayi mai sauti har saida Masroor ya kalleshi da mamaki
"Just tel me san yarinyan nan kake"
Saurin girgiza kai Masroor yayi yana cewa
"No friend bah santa nake bah, kawai tausayinta nake. Yarinyan taki tsayawa muyi magana just becoz of dat useless sistern nata"
Jinjina kai Yasir yay
"Nima na lura da haka anma tunda bataso y not kawai ka kyaleta"
Shiru Masroor yayi baice komai bah..

Ganin yanda Masroor din ya damu yasa Yasir ya dafashi
"Look friend uh are in love kawai kaidai bakaso ka fadane"
Mik'ewa tsaye Masroor yayi dasauri yana girgiza kai
"No Yasir kawai tausayi neh. Kamasan wani abu?"
Kai Yasir ya gigiza,
"Kasan guy din nan da yake tareda sistern tah a nan gidan yake aiki"
Yasir ya mik'e dasauri
"Kai haba"
Gyada kai Masroor yayi sannan yace
"I'm serious"
Shiru sukai nasamu mintina chan Yasir ya dago ya k'alli abokin nashi
"Ga shawara"
Dasauri Masroor ya zauna yana cewa
"Am all ears"

"Why not mu samu guy din mu biyashi ya fada mana labarin yarinyan, Coz am sure yasan komai tunda yana tareda sistern tah. Daga nan kaga sai mu nemi solution"
Shiru Masroor yayi yana cigaba da shafa sumar kanshi tareda furzar da iska
"No Friend bana tunanin haka zai yuwu, besides banasan yasan wani abu gameda wannan"
"Buh we dn't have any choice" cewar Yasir
Dago kai Masroor yayi da murmushi dauke a fuskanshi
"Yes! Nasan meh zanyi"
K'allanshi Yasir ya tsaya yi
"Meh knan"
Tasowa Masroor yayi ya dawo kusada Yasir ya zauna
"Zan Hadata da Parrot neh"
Dariya Yasir ya fashe dashi
"Do uh think it wil work"
Gyada kai Masroor yayi yana murmushin jin dadi...

Dukda irin dukan da Sulthana tasha a haka Baffa ya bata gyada ta dafa, da taimakon Mama ta dafa ta juye. Mama da kanta ta daura mata akai tai mata Fatan Alheri ta fito.. Yanke Shawaran ta tafi bakin kasuwa tai, tafiya take ahankali jikinta duk Ciwo yake mata, dakyar ta k'arasa bakin kasuwa ta samu guri inda tasaba zama ta zauna. Tagumi tai ta lula cikin tunanin Mahaifiyarta nan da nan hawaye ya soma gangaro mata, Muryan yarinya taji a kanta ta dago dasauri. Murmushi ta mata tareda
Mik'a mata Dari biyar
"Gashi ki bani gyada"
K'allam yarinyan Sulthana ta tsaya yi, kyakyawa da ita Sanye take cikin bakin dogon Riga mai kyau. Yarinyan bah K'aramin burge Sulthana tai bah, k'asa dauke idonta tai daga k'allan Yarinyan. Har saida Tace
"Bakya jina neh"
Zabura Sulthana tai ta maida dubanta ga kudin tana cewa
"Na nawa zaki siya? Banida chanji"


Saurin Girgiza kai tayi tana cewa
"Ai na duka zaki bani"
Jiki na rawa Sulthana ta soma nema ledan dan dama gyadan bazai wuce na haka nah"
Juyawa Mahnoor tai ta k'alli Masroor dake cikin mota nesa dasu, kai ya gyada mata. Ta juyo ta tsugunna tana taya Sulthana zuba gyadan a Leda
"Menene Sunanki" cewar Mahnoor
Dagowa Sulthana tai tana k'allan Mahnoor da manyan idanunta, Yarinyan ta burgeta sosai. Dan murmushi tai tace
"Sunana Sulthana"
Dariya Mahnoor tayi tareda maimaita sunan
"Woaw nice name, ni kuma sunana Mahnoor"
Kurri Sulthana ta mata itama ta maimaita sunan. Dai dai nan ta juye gyadan a Leda ta mik'ama Mahnoor.
Mik'a mata kudin tai tasa hannu biyu ta k'arba. Mahnoor tace
"Inaso ki zama k'awata"


Dan Dariya Sulthana tai dimple dinta suka lotsa
"Nima haka" cewar Sulthana
Mik'ewa tai tana cewa Shiknan zan tafi gida tunda na siyar. Mahnoor ta turo baki
"Bafa mu gama hira bah zaki tafi"
D'an zaro ido tai
"Kinga yau na saida gyadata dasauri barin tafi gida nasan Baffa idan yaga na dawo da wuri bazai dakeni bah"
D'an Shiru Mahnoor tai sanna tace
"Tho gobe zaki zo?"
Kai Sulthana ta gyada
"Ehmana, Anma inane gidanku"
Shiru Mahnoor tai ta rasa abin cewa har saida Sulthana tace
"A Birni kike ko"
Gyada kai Kawai Mahnoor tai tana y'ar murmushi. Sallama suk'ai Sulthana ta nufi gida dasauri itama Mahnoor ta shiga mota tareda fadama Masroor duk y'anda sukai. Murmushin jindadi yayi
"Dats my Lil Sis am proud of uh"
Itama Murmushin tai suka bar Cikin Kauyen.
Yinin ranar Sulthana tayishi neh cikeda tunanin k'awarta y'ar birni. Tayi murna sosai da haduwa da Mahnoor. K'ullum sai Masroor ya kawo Mahnoor wajan Sulthana idan ta taso School, shaquwa sosai ya shiga tsakaninsu duk da Har yanzu bah abinda Sulthana ta fadama Mahnoor dangane da halinda take Ciki...

*Anya kuwa Wannan Shawaran na Masroor mai bullewa ce*
 Mudaije zuwa..

Ummy Abduol✍🏻
[28/08, 01:12] Friend Hussaini: πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
          πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
         *SULTHANA*
         πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

By *Ummy Abduol*

         *Page 111 to 115*

Shaquwa sosai ya shiga tsakaninsu duk da har yanzu bah abinda Sulthana a fadama Mahnoor dangane da halinda take ciki...
Yauma kamar kullum tana dawowa daga makaranta taci lunch tai Sallah, side din Masroor ta nufa knocking tai a bakin kofan falonshi taji shiru, ta dad'e tana knocking jin shirun yayi yawa ta juyo ta koma side dinsu. Tana k'okarin Saukowa k'asa taci karo da Mami ta fito dak'i, tsaya tai tana k'allanta da Mamaki
"Wai Mahnoor na tambayeki"
Gyada kai kawai Mahnoor tai, Mami ta cigaba da cewa
"Kullum da kuke fita din nan keda Masroor ina kuke zuwa?"
Turo baki tai dan Masroor ya jamata kunne K'ar ta sake ta fadama kowa. Mami tace
"Badake nake magana bah"
Harta bude baki zatai magana sukajiyo Muryan Masroor ta bayansu yana cewa
"No mami bafa wani guri muke zuwa bah, just ina wanke lefuka na neh danai kinsan fushi take dani wai tunda na dawo bama zuwa yawo"

Gizgiza kai kawai Mami tai dan Tasan k'arya ya fada
Mahnoor ta K'alla tana cewa
"Zo ki daukomin wannan abin" ta juya ta shiga dakinta, matsowa Masroor yayi ya sassauta murya yace
"No matter now karki fada mata"
Gyada kai Mahnoor tayi ta shiga dakin Mami da sallama shikuma ya dauko k'asa..

Zaune ta samu Mami bakin Katafaren Gadonta, kusada ita mami ta nuna mata
"Zo ki zauna nan"
Bah musu taje ta zauna, Mami ta fara magana cikin sigan Lallashi
"Mahnoor ina kuke zuwa"
Chuno baki tai
"Nifah Mami bafa wani guri muke zuwa bah yawo kawai yake kaini"
Jinjina kai Mami tai
"Mahnoor bakya min k'arya meyasa yanzu kika fara, tunda bazaki fadaba Shiknan"
Ajiyan zuciya tai sannan ta cigaba
"Uh should be very careful kina jina?"
Kai ta gyada ma Mami ta mik'e tana Kakkabe skirt dinta
"Mami bye sai mun dawo"
D'an murmushin yak'e Mamin tai
"Ai bari Daddynku ya dawo zance ne Islamic Lesson teachern ki ya daina zuwa bayan isha'i ya koma zuwa bayan Asr. Sai muga yanda za'ai a rinka fitan"..

Bubbuga k'afa Ta fara ta fita daga dakin tana gungunai, a cikin Hadad'iyar doddge dinshi ta hangoshi zaune, k'arasawa tai ta shiga ya tada suka bar gidan..

Yau Masroor yaci Alwashin koma mai zai faru saidai a faru anma dole sai Sulthana ta sanar dashi halin datake ciki. suna cikin tafiya a mota Mahnoor tace
"Bro Masroor ka tsaya nasai ma friend chocolate da ice cream"
D'an murmushi yayi
"Kinada kudi neh"
Turo baki tai
"Tho bah kai kanada shi bah"
Baice komai bah ya juya k'an motan, tare suka shiga ta zabar ma Sulthana k'ayan ciye ciye k'ala kala suka fito suka nufi kauyen..

Yau abin mamaki bah Sulthana bah alamar tah, dasauri Mahnoor ta k'alli Masroor idonta cikeda k'walla
"Bro Friend bata nan"
Shiru Masroor yayi yana k'allan wajan cikeda damuwa. Kamar ance ya dago ya hangota tafe da trayn gyada akai tana matsar kwalla, dasauri ya bude motan ya fita Mahnoor tabi bayanshi..

Zama Sulthanan tai inda ta saba zama tana cigaba da matsar k'walla, mahnoor ce ta k'araso wajan ta zauna tana cewa
"Friend meyasa kike kuka"
Jin muryan k'awarta y'ar birni yasa ta dago dasauri tasa hannu tana share kwallan daya gangaro mata. Murmushi tama Mahnoor
"Bah komai k'awa"
D'an turo baki Mahnoor tai
"Nifah Friend dinki neh, kifadamin waye yake dukanki"
Murmushi Sulthana ta k'arayi
"K'awa bah kowa"

Muryan Masroor sukaji a bayansu yana cewa
"Lokaci yayi daya kamata ki fada mana abinda ke damunki, ki daina boyewa dan cutar dake zeyi"
Daga k'ai tai suka hada ido ta mik'e dasauri tana k'allanshi tareda nunashi da yatsa
"Kah daina zuwa inda nake, idan Baffa ko yaya Hafsatu taganmu dukana xasuyi"
Baiji wani d'ar bah ya kama hannunta tana turjewa mutane sai k'allansu suke bayan mota ya sakata ya rufe, Mahnoor ta dauko trayn gyadanta ta saka a booth, sannan ta shiga Masroor ya bar Kauyen a guje..

Ihu kawai Sulthana take
"Sun Saceni, Jama'a ku taimakeni"
Bah wanda yayi yunk'urin taimakonta saima bin motar da ake da K'allo
Gudu yake sosai k'amar zai tashi sama, bai tsaya ko ina bah sai Gidansu Yasir, horn yayi mai gadi ya bude ya shiga yayi parking. Itako Sulthana tunda aka bar Kauyensu tai shiru ta fara rarraba idanu dan tunda take bata taba barin kauyensu bah sai yau, bin titi take da k'allo tana shafa Glass din motan tana murmushi..

Wayanshi ya dauka ya soma neman Layin yasir, yana cikin kira ya fito daga side dinshi yana murmushi.
"Yau suprise akai min"
Karasowa yayi bakin motan, Ganin Sulthana a baya tanata Zare ido yasa yayi turus yana k'allan Masroor daya hade girar sama data k'asa. Sulthana ta dafa Mahnoor cikeda damuwa
"K'awa ina kuka kawoni? Dan Allah karku ciremin kaina ban muku komai bah"
Kyalkyalewa da dariya Mahnoor tai tana cewa
"Mu ai bama cire kai"
 Bude Murfin motan Masroor yayi ya fita tareda jan Hannun Yasir, side dinshi suka nufa a falo suka zauna, Yasir ya kada baki yace

"Masroor what do uh think uh are doing?, ka dauko yarinya hakanan kawai. Ko kasanar da Iyayenta neh"
Mikewa Tsaye Masroor yayi cikin daga murya yace
"I Cn't hold it any more Yasir, inaso na taimaka ma yarinyan nan. I donno why I always think of her, kullum sai tazomin a mafarki"
D'an Murmushi Yasir yayi ya mik'e ya dafashi
"Look at me Friend"
Dagowa Masroor yayi ya kalli Yasir, Murmushi yasir yamai
"Uh are in love Masroor, santa kakeyi. Beleive me"
Girgiza kai Masroor yayi idanunshi sun k'ada sunyi ja. Suman kanshi yaja tareda furzar da iska
"No Friend, forget abt dis lets find solution"
Kamashi Yasir yayi ya zaunar dashi yana cewa
"Abinda kayi bah daidai baneh Friend, bai kamata ka daukota bah. A hankali zakabi komai har kasamu abinda kakeso."

Masroor baice komai bah saima mik'ewa dayayi yabar falon, mota ya koma yaga Mahnoor a baya kusada Sulthana daketa kuka kamar ranta zai fita. Bude kofan yayi ya janyo hannunta. Ihu ta saki tana turjewa, daka mata tsawa yayi tai gum da bakinta, bai saketa bah saida ya shiga Falon Yasir Mahnoor na biye dasu...

Yasir na ganinsu ya mik'e tsaye
"Masroor whats all dis? Pls ka maida yarinyan mutane. Kada Mum ta dawo ta samemu a nan pls"
Baice komai bah ya zaunar da Sulthana k'an kujera shima ya zauna ana kusa da ita. Murya a sanyaye yace
"Sulthana!"
Dago jajayen idanunta tai jikinta na rawa tace
"Na'am"
Suman kanshi ya shafa Yace
"Ki fadamin meke faruwa dake karki boyemin komai"
Shiru tai nadan mintina, ganin dagaske masroor yake yasa yasir yaja hannun Mahnoor suka bar falon..

Saukowa Masroor yayi daga kan kujeran dayake ya tsugunna a gabanta, hannunshi yasa ya dago fuskanta
"Kiyi min magana Sulthana karki boyemin komai"
Sheshekan kuka ta fara ts fashe da kuka a hankali..

Ummy Abduol✍🏻
[28/08, 01:12] Friend Hussaini: πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
          πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
         *SULTHANA*
         πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

By *Ummy Abduol*

         *Page 116 to 120*

"Kiyi min magana Sulthana karki boyemin komai"
Sheshekan kuka ta fara ta fashe da kuka a hankali. Ganin yanda idonshi yayi ja ya hade rai yasa ta fara magana a hankali, labarinta tun sanda tai wayo har izuwa yanzu taba Masroor bah abinda ta boye mai. Saida ta gama sannan ta dago suka hada ido, hawaye ne tagani nabin kuncinshi..

Motsin dah Masroor yaji a bakin kofa neh yasa yasa hankie ya goge hawayen fuskanshi Sannan ya dago, Yasir ya gani idanunshi sunyi ja dah ala yaji duk labarin dah Sulthana taba Masroor, Cikin falon ya shigo ya zauna yana k'allan Masroor
"Akwai wani abu a k'asa, bt uh knw what?"
Kai Masroor ya girgiza Fuskanshi bah walwala
"Take her home"
Bah musu Masroor ya mik'e
"Tashi na maidake gida"
Juyawa yayi ya nufi hanyar fita,
Mik'ewa tai jiki a sabule tabi bayanshi, a mota suka tarar da Mahnoor tana game da wayan Masroor, dah kanshi ya bude mata kofan motan ta shiga shima ya zagaya ya shiga suk'a bar gidan..

A garinsu Sulthana fah, labari meh ya k'arada garin nah an sace Sulthana, Baffa dake kofar gida wajan almajiransa wani makocinshi ya k'araso tareda bashi hannu sukai musabaha, Mak'ocin nashin mai suna Mallan Bala yace
"Wani mummunan labari nake tafe maka dashi"
Baffa yadan zaro ido
"Tho Mallan Bala meya faru"
D'an dukar dakai Yayi sannan yace
"Dazu muna bakin kasuwa wata mota hadaddiya mai kyau, ta shigo wani saurayi neh ke tuka motar. Yana zuwa yaja y'ar wajanka Sulthana ya tura cikin motan ya tafi a guje"
Ga mamakin Mallan Bala sai ji yayi Baffa yace
"Ah! Ai na dauka Y'ayana Ameenatu da Hafsatu kake magana, yoh indai Sulthana ce bai wuce samarinta ne da suk'e fasik'anci tare"
Da Alamar Mamaki Mallan Bala ya k'alli Baffa har ya kasa boye Mamakinshi Yace
"Haba Mallan Jamilu, bai kamata wannan furucin ya fito daga bakinka bah. Na dade inajin labarin abubuwan dake.."
Saurin katseshi Baffa yayi inda yake shiga bata nan yake fita bah, ganin abin na k'ara gaba yasa Mallan Bala barin wajan sum sum...

Haka labari ya dinga zuwa kunnen Mallam jamilu anma ko a jikinshi, su Mama suma sunji barin, anma Hafsatu da Ameenatu bah wanda ya nuna alhininsa saima cigaba da safgoginsu da sukai, Mama ce kawai ta nuna damuwanta harda y'ar kwallanta. Su Maman Sadiya da sadiya duk sun shigo gidan jaje, Sadiya sai kuka take dakyar su Mama suka lallasheta ta koma gida...

Driving Masroor yake hankalinshi a tashe, gidansu ya nufa yayi horn masu gadi suk'a bude mai gate, Parking yayi nesa da inda ake parking motocin gidan, Mahnoor ya k'alla yana cewa
"Ki tafi ciki, idan Mami tah tambayeki ni just tl her bakisan inda zani bah"
Kai kawai ta gyada ta bude kofan ta fita tana d'agama Sulthana hannu wacce sam batama luraba sai Haraban gidan datakebi da kallo cikeda sha'awa..

Reverse yayi ya fita daga gidan yadau hanyan k'auyensu Sulthana, fashewa da kuka tai tana turo baki
"Dan Allah karka maidani wallahi Baffa dukana zeyi gashi ban saida gyadan bah"
Baice mata komai bah sai ma idonshi daya runtse da k'arfi ya bude, Wasu tarin Almajirai yagani a bakin titi, yayi parking yadauko trayn gyadan ya raba musu Sannan ya dawo ya cigaba da driving..

Kuka kawai Sulthana take tanabin hanya da k'allo har suka fara shiga cikin k'auyensu lokacin an fara kiraye kirayen sallan magriba, bakin kasuwan yayi parking Sannan ya juyo ya k'alleta
"Its ok Sulthana, ki daina kuka kinji"
Kai ta gyada mai tana share hawayen daya gangaro mata da bayan hannu. Ajiyan zuciya ya saki yana bin K'asuwan da kallo
"Kinga anata kiran Sallah, yimin kwatancen gidanku na kaiki coz dare ya farayi"
Girgiza kai tai dasauri tana zaro ido,
"Aa nidai kawai ka budeni na tafi idan Baffa ya ganka ni duka"
Fitowa yayi ya bude mata itama ta fito tadau traynta, Hannu yasa a aljihu ya ciro bandir din y'an hamsin guda hudu ya mik'a mata..

Zaro ido tai tana k'allan kudin
"Aa bazan amsa bah nidai kaban kudina kawai"
D'an murmushi yayi yana k'allan dimples dinta dake k'ara mata kyau
"Tho nawane kudin naki?"
Turo baki tai cikeda shagwaba tace
"Bah dari bakwai baneh"
Baice komai bah ya k'irga dari bakwai ya mik'a mata, ta amsa ta irga sannan tadago tana murmushi tace
"Nagode"

Kwaikwayan yanda tace nagoden yayi, ta d'anyi murmushi ta juya zata tafi, Hannunta yayi saurin rik'ewa ta juyo tana k'allanshi da Alamar mamaki
"Bah ko sallama sai ki wani wuce"
Batace komai bah sai turo baki datai tana k'okarin fizge hannunta, sakin Hannun yayi yana mata murmushi.
"Tho shiknan sai da safe koh, gobe ina nan ina jiranki kinji"
Batace komai bah ta juya ta fara tafiya tanayi tana waigenshi, hannu ya daga Mata tad'an saki murmushi itama ta d'aga masa hannu, bai bar wajanbah saida ya daina ganinta. Phone dinshi neh ya hau ringing, motan ya shiga ya zauna sannan yadau wayan yana cewa
"I will be on my way, na maidata ai"
Shiru yad'anyi sannan yace
"Saidai nazo kawai" ya kashe kiran. Motan ya kunna ya bar wajan dasauri direct gidansu Yasir ya nufa, motar Mum daya gani yasa yayi murmushi ya nufi side dinta, zaune ya sameta a falo tana k'allo. Ya k'arasa yana cewa
"My one and only mum"
Dagowa tai da fara'a dan bah wanda ke ce mata haka sai Masroor, hararanshi tad'anyi tana cewa
"Idonka knam Masroor"
D'an dariya yayo ya k'arasa kusada ita ya zauna yana cewa
"Zuwana na biyu fah knan yau dazu nazo bakya nan"
Gyada kai tai
"Eh tho nayau na yarda dan bana gida tun Safe"
Hira suka cigaba dayi shida mum din Yasir. Sunyi hira sosai sannan ya mata sallama ya wuce Side din Yasir

Zaune ya sameshi a falonshi yana shan lemu hannunshi rik'e da remote yana chanza tasha, dariya masroor yayi mara sauti
"Gaskiya friend kanajin dadinka"
Murmushi kawai yasir yayi ya mik'e yasauko cup ya zubama Masroor sannan ya mik'a mai..

Amsa yayi yana cewa
"Yadai kake nemana"
Cup din hannunshi ya aje yana k'allan Masroor
"Friend kayi ganganci dazu, mai zaisa kah dauko yarinyan nan a wannan halin da ake ciki. Dnt uh knw zai iya bata siyasan Daddy"
Shiru Masroor yayi yana shafa sumar kanshi
"Yes uh ryt, bt bazan k'ara haka bah"
Gyada kai Yasir yayi ya kurbi Juice din yace
"Yah kukai da mutuniyar taka"

Tashi Masroor yayi daga inda yake ya dawo kusada Yasir ya zauna yana cewa
"Friend she's Cute, friendly, nice and..."
Saurin Katseshi Yasir yayi
"Hmm I wll kip on telling uh san yarinyan nan kake, bt tunda kace Aa watarana da kanka zaka ban labari"
Yatsine fuska Masroor yayi yadau car key dinshi yace
"Nidai na tafi"
Har bakin mota ya rako shi sukai Sallama ya nufo gida cikeda fargaban tambayoyin Mami..

A bangaren Sulthana fah..

*Mu tara page na gaba dan jin yanda Sulthana zata kwashe da y'an gidan nasu*

Ummy Abduol✍🏻
[28/08, 01:12] Friend Hussaini: πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
          πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
         *SULTHANA*
         πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

By *Ummy Abduol*

         *Page 121 to 125*

Har bakin mota ya rakoshi sukai Sallama ya nufi gida cikeda fargaban tambayoyin Mami..

A bangaren Sulthana kuwa tafiya take sauri sauri duk inda ta bi k'allanta ake wasu kuma nunata. abin bah Karamin daure maka kai yayi bah, kanta a k'asa ta karasa gida. Da Sallama ta shiga ciki bah kowa a tsakar gidan dan haka ta aje trayn Sannan ta leka dakin Mama, zaune ta sameta k'an sallaya. Mama najin Sallamanta ta mik'e dasauri
"Sulthana ina kikaje? Ance anga wasu sun turaki mota"
Gabanta ne ya fadi ta fashe da kuka
"Wasu neh suka saceni"
D'an zaro ido Mama tai ta shiga jujuya Sulthanan tana dubata
"Basu dai miki komai bah koh"
Kai ta gyada tana cigaba da kuka a hankali..

Jin kamar magana daga dakin Mama yasa Hafsatu da Ameenatu fitowa daga dakinsu, dai dai nan Sulthana ta fito zata koma zaure, Hafsatu ce ta kada baki tace
"An dawo yawon dandin yawon iskanci, ai dama nasan bah wani saceki da'akai"
Tsaki Ameenatu tai tareda rik'e kugu
"Kuma bai wuce Wannan likitan nifah na tsaneshi, dan na lura dan iska neh. Koda yake ai yar uwa ya samu"
Mama tafito dasauro ta daka musu tsawa
"Kul! Ameenatu karna k'ara jin wannan maganan a bakin ki, wai meke faruwa neh? meyasa Ameenatu duk kika chanza"
Juya kawai tai ta shiga daki, itako uwar marasa kunya Hafsatu cigaba tai da Aibanta Sulthana har saida Mama tayo k'anta Sannan tabar wajan a guje..

Kuka sosai Sulthana take a inda take tsaye, karasowa Mama tai ta dafata
"Ki daina kuka kinji, wata rana sai labari"
Kai Sulthana kawai ta gyada batace komai bah
"Maza dau buta kiyi sallah kizo kici abinci" cewar Mama
Bah musu tadau butan ta dibi ruwa ta shiga bayi..

Sai Bayan isha'i Baffa ya shigo gidan, tun yana waje yaga shigowan Sulthana, baice komai bah ya shiga dakin Mama, Sannu da zuwa tamai Sannan ta kawo mai Abinci. Yanaci tanamai Fifita tace
"Sulthana ta dawo, kaji saceta akasoyi"
Tsaki Baffa yayi
"Ina ruwana, dama an saceta na huta"
Kallanshi Mama tai baki bude
"Mallan kakosan abinda kake fada"
Baice komai bah saima Sulthana daya soma kwalama Kira, tana gefen rijiya tsugunne tanacin Abinci taji kiran. Amsawa tai ta nufi dakin dasauri, Saida tai sallama Sannan ta shiga...

Hannu Baffa ya mik'a mata, tasan me yake nufi dan haka ta ciro kudin a gefen zaninta ta mik'a mai. Amsa yayi yana duba kudin tareda k'allan Mama wacce itama kudin take K'allo
"Kindai gani da idonki koh? Sababbin kudi gar haka"
Girgiza kai Mama tai ta kauda kai gefe. Tab'e baki yayi ya k'alli Sulthana wacce kanta ke kasa tana jiran hukuncin da Baffa zai yanke a kanta, ga mamaki sai taji yace
"Tashi ki bani guri, abinda zan gaya miki shine kada ki sake ki kawomin Cikin Shege gida"
Hawaye ya ciko idonta ta fita daga dakin ta nufi zaure ta fashe da kuka mai sauti.
"Haba Mallan wannan wanne irin abu neh da kanka kaita aibanta y'arka kana mata baki"
Dogon tsaki Baffa yaja ya wanke hannu cikin roban dake kusa dashi ya mik'e yabar dakin..

Kuka mai isarta tai Sannan ta sulalle a wajan ta kwanta, tunanin abinda ya faru dazu tai, Yau data fadama wani halin datake ciki har tadan samu sauki azuciyarta. Lumshe ido tayi ta bude a hankali tareda sakin Murmushi
"Yau naje birni" ta fada a hankali tana cigaba da murmushi _Lol oh bakauyiya_
Da shirmen tunane tunanen tah barci ya dauketa..

Yauma kamar kullum Bakin Kasuwa taje kamar yanda ta saba, mutane sai mata jaje suke itadai saidai tai murmushi idan sukace Allah kyauta na gaba bata amsawa a ranta kuma fadi take bah Amin bah _kujimin Sulthanan nan fah haha_
Yau da wata benz yaso bakin Kasuwan, chan bayan wajan yayi parking ya tura yaro ya kiramai ita. Tana zaune yaron yazo yace
"Wai kije ana kiranki"
D'an zaro ido tai tana k'allan yaran
"Wah?"
Girgiza kai yayi yana cewa
"Bansan sunanshi bah, wani neh a k'atuwar mota"

Bata kawo komai bah ta mik'e ta tabo Murja dake kusada ita
"Dan Allah murja ga tsaron Gyadata ina zuwa"
Tho murjan tace ita kuma Sulthana tabi hanyar da yaran ya nuna mata. Motan ta hango tayi slow ta tsaya tana k'arema motar kallo dan bah karamin burgeta yayi bah. Ta mirrow ya hangota ya fito yana mata murmushi, wajan motan ta k'arasa ta manna k'anta jikin windown tana K'allan ciki. Dagowa tai tana turo baki
"Ina K'awata"
Sumar kanshi ya shafa Yana y'ar murmushi
"Yau kam k'awarki bata nan suna biki"
Hannu ta rungume tana cigaba da turo baki.
Kurri Masroor yayi yana k'allanta, ganin hawaye cike a idonga yasa ya k'araso gabanta ya riko hannunta suka zauna bakin bishiyan dake wajan
"Karkiyi kuka kinji, gobe na miki Alkawari tare zamu zo"
K'ara tunzure baki tai ta kauda kai, d'an dariya yayi
"Dama haka kikeda rigima? Lallai akwai aiki"
Juyowa tai ta k'alleshi murya K'asa k'asa tace
"Yaya"

Juyowa yayi ya k'alleta da mamaki, har ya bude baki zaiyi magana wayanshi ya fara ringing. Hannu yasa a aljihu ya ciro ganin sunan dake jiki tasa ya dauka yana murmushi
"Old Friend, yau ka tuna dani"
Shiru yayi yana sauraren mai kiran yana murnushi Sannan yace
"Oops! Wallhi bana gida naje wani guri bt nan da 1hr I wl b on my way"
Shiru ya k'arayi Sannan yayi dariya mara sauti Yace
"Kah bata haquri ai nima zanzo"
Sallama sukai ya kashe kiran yana k'allan Sulthana da itama shi take K'allo..

Murmushi yamata itama ta maidar mai, mikewa yayi ya bude motan ya ciro wani leda ya mik'a mata.
"Gashi tsaraba nane"
Mak'e kafada tai tana k'allanshi kasa kasa
"A'a idan aka gani a gida dukana za'ayi"
Tsugunawa yayi daidai Saitin Fuskanta Yace
"Ki ansa ai bah nace kije dashi gida bneh"
Amsa tai ta soma bude ledan, Takeway neh da drink sai Icecream da cake. Takeawayn taketa Kici kicin budewa, dariya ya mata ya amsa ya bude mata, K'allan Abincin tai Sannan ta kalleshi
"Duka nawa neh"
Kai ya gyada mata yana cigaba da k'allanta da narkakun idanunshi..

Abincin ta soma ci hannu baka hannu kwarya, Kallanta yake cikeda tausayi, saida taci tai nak sannan ta dago tana mai murmushi
"Nagode Yaya"
Murmushi shima ya mata yasa yatsa ya taba Dimple dinta. Mik'ewa tai dasauri tana zare ido.
"Yaya lokaci na tafiya kuma ban saida gyada tah bah"
Hannu yasa a aljihu yace
"Nawa neh kudin gyadan?"
Girgiza mai kai tai dasauri
"A'a kah barshi wanda nakai jiya saida Baffa yamin Fada"
Kai ya jinjina kawai
"Yaya ka tafi nima zan koma, kah gaida min K'awata"
Bata jira mai zaice bah ta fara tafiya tana waigenshi tareda daga mai hannu. Binta yayi da k'allo harta bace...


    *Shin ya labarin Dr Fareed neh??*

Ummy Abduol✍🏻
[28/08, 01:12] Friend Hussaini: πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
          πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
         *SULTHANA*
         πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

By *Ummy Abduol*

         *Page 126 to 130*

Bata jira mai zaice bah ta fara tafiya tana waigenshi tareda daga mai hannu. Binta yayi da k'allo harta bace ma ganinshi, Ajiyan zuciya ya sauke sannan ya shiga motarsa yaja yabar wajan...

Saida ya shiga cikin gari sosai Sannan yadau waya ya soma kira, ana dauka yace
"Am on my way na kusa gida"
D'an murmushi yayi Sannan yace
"Ok sai kah karaso"
Ya kashe wayan ya tura a aljihun shi. Bai zame koh ina bah sai gida, a haraban gidan yaci k'aro da Mahnoor ita da wasu masu aiki tana tayasu shara, girgiza kai kawai yayi ya nufi side dinshi. Tana ganin ya wuce ta aje tsintsiyan ta bishi, wanka ya farayi sannan ya fito Cikin Threequaters dah T shirt fari kal, zaune ya samu Mahnoor a falonshi tana K'allo, jin Karan bude kofa ta shagwabe fuska ta dago tana kallanshi
"Bro Masroor shine ka tafi bakaje dani bah koh"

Zama yayi kusa da ita ya kamo hannunta
"Am sorry sis, kinga fah bakwa nan and I cnt wait har sai kun dawo, dnt uh worry wata rana nan zata dawo ku zauna tare"
Zaro ido tai ta saki murmushi
"Allah dagaske bro Masroor"
Kai ya gyada mata shima yana murmushin _kujimin wannan masroor din fah taya zata dawo gidansu_

Phone dinshi yadau ringing ya dauka Sannan yace
"Ok ganinan zuwa"
Ya kalli Mahnoor wacce itama shi take kallo
"Barinje nayi bako"
Tare suka fito ita ta nufi side dinsu shi kuma ya fita wajan gate, a kofar gidan ya ganshi zaune Cikin mota, karasawa yayi yana y'ar murmushi
"Uh welcome old friend"
Dariya yayi Sukai musabaha, Masroor yace
"Wai gidan bakonka neh dah bazaka shiga bah"
K'asumbarshi ya shafa yana y'ar murmushi
"Banasan Mami ta ganni neh dan nasan sai nasha surutu"
Dariya Masroor yayi mai sauti
"Surutu koh sai kasha shi indai mami ce, saidai kah rufe ido kah toshe kunnuwan kah"

Yasir neh yayi parking ya fito yana murmushi
"Kai wah nake gani haka?"
Hannu yabashi suka gaisa "Dama ana ganinka"
Dariya yayi
"Yasir knan dama kana nan?"
A tare suka shiga cikin gidan zuwa side din Masroor, maids din gidan suka shiga hidima dasu. Jin surutu na tashi daga side din Masroor yasa Mahnoor ta shiga side din tana rarraba ido, dagowa bakonsu yayi yadan zare ido
"Wah nake gani nan kamar Mahnoor, lallai kin zama big girl"
Murmushi tai ta k'arasa kusada shi ta zauna
"Bro Sannu da zuwa"
"Yauwa" yace yana shafa kanta yana murnushi. Zamewa tai daga jikinshi ta fita daga daga side din... batafi minti biyar da fita bah wayan Masroor ya soma ruri..

Dauka yayi yasa a kunni sannan yayi murnushi yace
"Ok gamu nan zuwa"
Dariya ya saki mai sauti yana shafa sumar kanshi,  binshi da kallo sukai da mamaki, sai dayayi mai isarshi Sannan yace
"Numbernka ya fito Mami na kiranka, kuma nasan Mahnoor ce ta fada mata"

Dariya Yasir shima yayi
"Kace mai lefi neh?"
Kai masroor ya gyada yana cigaba da dariya a hankali. Murmushi yayi ya mik'e
"Tho ku tashi muje"
Bah musu suka tashi suka nufi side din Mami, A falonta suka sameta zaune da bakuwa, kan carpet suka ya zauna su kuma Masroor da Yasir sukai d'are d'are akan kujera, sunkuyar dakai yayi sannan yace
"Ina yini Mami"

Kallanshi Mami ta tsaya yo jin shiru yasa ya dago suka hada ido ya maida kai dasauri
Murmushi tai
"Likita bokan turai Kama daga kai kawai, wato kasan bakada gaskiya shine harda zama a kasa"
Dagowa yayi yana y'ar dariya
"Mami knan kiyi hakuri, bana zama neh shiyasa"

Masroor da Yasir sai dariya suke mai yanata susunne kai, Mahnoor ce ta shigo falon ta zauna kusadashi a Kasa
"Bro fareed zakaje dani wajan Umma"
_niko Ummy Abduol zaro ido nai jin sunan da mahnoor ta fada_ wah knan take nufi?

    *manage dis banida chargi*

Ummy Abduol✍🏻
[28/08, 01:12] Friend Hussaini: πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
          πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
         *SULTHANA*
         πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

By *Ummy Abduol*

         *Page 136 to 140*

       *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION*
 
           Wannan Shafin Sadaukarwa ce gareku All *Da Bazarmu Writers Association* Members.. Allah ya bar K'auna.

Shekewa da dariya Hafsatu tayi harda tafawa
"Gaskiya neh Baffa haka yayi"

K'ara rushewa da kuka Sulthana tai jin Abinda Baffa yace, Saida tai mai isarta Sannan ta shigo cikin Gidan idanunta a kukumbure. Gyadan daya saba aje mata a kofar dakinshi ta dauka ta daura a wuta ta koma gefe tana cigaba da hawaye...

Yana dahuwa ta sauke ta zuba a tray, batayi mah Mama sallama bah ta tafi, inda suka saba zama ta hango Motar Masroor, ta k'arasa jiki asanyaye ta samu guri ta zauna batareda tamai magana bah. Sam bai lura da tazo wajan bah saida ya leko tah glass din motarshi sannan ya hangota zaune tayi tagumi, fitowa yayi dasauri ya k'araso inda take ya zauna
"Sulthana meke damunki"
Shiru tai k'anta a kasa

Ya marairaice Fuska yana cigaba da K'allanta
"Banasan ina ganinki cikin damuwa kinsan fah ina..."
Kasa k'arasa Maganan yayi ta dago jajayen idanunta tana kallanshi. Ajiyan zuciya ya sauke
"Meyasa yau kike so boyemin damuwarki? Nifah Abokinki neh kuma yayanki"
Hawaye ne ya gangaro mata, ta dago tana k'okarin Fashewa da kuka
"Baffa neh zaimin Aure"
"What?"
Fashewa da kukan tai ta duk'ar dakai K'asa

Rudu Masroor ya shiga ya mik'e ya dawo gabanta ya tsugunna
"Sulthana kin Tabbatar da abinda kike gayamin"
Batace komai bah sai kukan data cigaba
Suman kanshi yaja ranshi b'ace
"Pls Banasan kukan nan, ina jinshi har cikin raina. Just answer my question"

Ganin tak'iyin shirun yasa ya mike tsaye, k'ugunshi ya rik'e da hannu daya, dayan kuma yana cigaba da jan suman kanshi. Nan da nan idanunshi suka kad'a sukai ja
Tsugunawa yayi guiwa biyu a k'asa
"Pls stop crying, fadamin meya faru"

Cikin sheshekan kuka ta bashi labarin duk abinda ya faru
"No!!!" ya fada da k'arfi hakan jaya hankalin mutanen dake wajan suna k'allansu, bai damu da yanda ake kallansu bah saima cigaba da magana dayayi cikin D'aga murya
"No 1 can snach uh from me, u're mine."
Duk abinda yake fada bah wanda Sulthana tasan ma'anarshi idan bah no din bah, duk'ar dakai kawai tai saboda yanda mutane ke K'allansu

Gani tai ya mik'e ya shiga motarshi yaja yabar wajan da gudu. Bin motan tai da k'allo ta k'ara fashewa da matsanancin kuka, cikin muryan kuka take magana a hankali
"Shiknan yaya yayi fushi ya barni na shiga uku, meyasa Baffa baka sona? Menai maka??"
Hannu ta daura akai tana kuka wiwi
"Mama meyasa kika tafi kika barni? Kowa baya sona ki dawo dan Allah"
Mutanen dake wajan sun tausaya mata matuk'a jin kalaman datake fada..

Wasu ko basa sha'awar gyadan suna siya dan su rage mata radaddin datake ciki, haka taita bah mutane tana cigaba da kuka harta siyar. Hanyan da Masroor yasaba bi taketa k'allo tana hawaye, ganin bai dawo bah yasa ta mik'e jiki a sanyaye ta kama hanyar gida...

Gudu Masroor ke shararawa kamar zai tashi sama, Ikon Allah ne kawai ya kaishi gida, baiyi wani k'wakwaran parking bah ya fito ya nufi side din Mami idanunshi jawur. Bell ya danna aka bude mai ya shiga, masu aiki sai gaidashi suke anma baiko kallesu bah ya nufi falon Mami. Ganin bata falon sai bak'inta dake zaune suna jiranta yasa ya k'arasa dakinta, knocking yayi a kofar dakin ta amsa tareda tambayan waye
"Masroor" yace atakaice
Bashi umarni tai daya shigo

Yana shiga suka hada ido  ta mik'e dasauri ganin yanda idanushi suka rune
"Son whats wrong"
K'asan dakin ya zauna yana cigaba da ajiyan zuciya
Mami ta k'araso kusadashi tareda dafashi
"Son tell me whats wrong pls, meke damunka? Why are you like dis"
Kama hannunta yayi ya ya dago ya k'alleta idaunshi Cikeda kwalla
"Mami som1 wnts 2 snach her from me, I love her, I so much love her. Shes my happiness, I cnt do without ha"

Fashe mata da kuka yayi ya duk'ar da kanshi kasa
Rungumoshi jikinta tai itama hankalinta tashe
"Its ok son, stop crying. Cool down and tel me meya faru"

Kasa magana yayi sai kukan daya cigaba dayi, dak'yar ta ja hannunshi suka mik'e tsaye, hannunshi ta rik'e ta kaishi side dinshi. Bedroom dinshi ta shiga dashi tareda zaunar dashi kan gado, tsugunawa tai ta ciremai cover'n dake kafanshi sannan ta mik'e tana shafa suman kanshi
"Its ok son have some rest, idan kah huta sai muyi maganan kaji"
Kai kawai ya gyada mata, ta fita daga dakin cikeda damuwa...

Masu aiki tasa suka kaimai abinci, anma koh kallan abincin beyi bah..waya Mami ta d'auka ta kira Yasir bai d'au lokaci bah ya k'araso gidan a rud'e. Falon Mami ya fara zuwa saboda tace ya sameta.
Da sallama ya shiga ya sameta zaune tana y'an rubuce rubuce. Zama yayi ya gaidata, ta amsa fuska bah walwala..

Duk abinda ya faru ta zaiyanama Yasir sannan tace
"Yasir nasan kai zakafi kowa sanin wanda Masroor yakeso, baya cikin hayyacinshi dats why ban tambayeshi bah"
Yasir yayi murmushi ya gyara zama yaba Mami labarin tun sanda suka soma ganin Sulthana har zuwa daukota da Masroor yayi da labarin data basu nata. Mami ta share k'walla tace
"Yasir meyasa tuntuni baku fadamin bah? Yarinyan nan bah kalar Masroor bace anma kodan yanda yak'e santa zan hakura kuma nasan Alhaji zai yarda"

Shiru yayi baice komai bah kanshi a k'asa, Mami ta cigaba da cewa
"Ya zamuyi yanzu Yasir? Masroor na dak'i yana kuka"
Jin haka yasa Yasir mik'ewa dasauri ya nufi side din Masroor hankalinshi tashe..

Zaune ya sameshi yanda Mami ta barshi, saidai yanzu bah kukan yake bah. Ya k'arasa ya zauna kusa dashi
"Friend why all this?, uh have to be strong. Komae zai zama normal"
Masroor baice komai bah sai girgiza kanshi dayayi. Dak'yar yasir yasamu yaci abincin ya hada mai ruwan wanka yayi sannan yajashi suka tafi yawo ko hakan zaisa ya rage tunanin dayake...

Washe gari kamar yanda Fareed da Sa'ood sukayi hakan neh ya faru, karfe hudu a kauyensu Sulthana tai musu, bayan layinsu Sulthana sukai parking motarsu, yaro suka samu suka hadashi da sabuwar dari biyar ya musu k'iran Babban Almajirin mallan.

Ummy Abduol✍🏻
[28/08, 01:12] Friend Hussaini: πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
          πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
         *SULTHANA*
         πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

By *Ummy Abduol*

         *Page 131 to 135*
   

"Bro Fareed zakaje dani wajan Umma"
Rik'e baki Mami tayi tana kallan Mahnoor
"Mahnoor da yawo, sae kace taci kafan kare. Tho schl din fah"
Zumbure zaki tayi ta juya baya,
"Mami kinga fah sai bro fareed ya rink'a kaini"
Kanta fareed ya shafa yana y'ar murmushi
"Sis ki bari idan akai hutu da kaina zanzo na daukeki kinji"
Kai ta gyada ta mik'e tabar wajan tana gungunai..

"Likita bokan turai aure fah?"
Sosa kai yayi kanshi a k'asa
"Mami na kusa, kiris ya rage"
Gyada kai Mami tai tana murmushi
"Gaskiya kah kyauta kaga wadannan"
Ta nuna Yasir da Masroor
"Sunk'i aure suna nan sai gantali"
Dariya mai sauti Yasir keyi ya dafa kafadan Masroor
"Mami ai shagwababen naki ya kusa, hmm zan baki labari anjima"
Dukan wasa Masroor yakai mai
"Mami k'arya fah yake"
Tabe baki tai ta kauda kai kudai kuka sani..

Fareed ya mike yana cewa
"Mami zan tafi, dama na shigo ne mu gaisa inada patients a asibiti"
Mami itama ta mik'e da Fara'a
"Kah gaidamin dah hajiya sai nazo, wallahi duk hidimar campaign din nan neh ya hanani zuwa"
"Ai itama bata zama kullum bata nan itama dai campaign din neh" cewar Fareed
Yasir yace
"Inafa zama wajan matan governor dana duty governor"
Dariya sukasa duka, Masroor da Yasir suka raka Fareed har Bakin motarshi, sukai Sallama ya tafi...

Lokaci nata tafiya, shakuwa sosai ta shiga tsakanin Sulthana da Masroor harda Yasir, kullum a bakin tasha suk'e haduwa da Masroor suyita hiransu har tayata Saida gyadan yake taitamai dariya wai bai iya badawa bah. A bangaren Dr Fareed ma yakanzo lokaci zuwa lokaci wajanta watarana ta fita wata rana bata zuwa, santa yake bana wasa bah. Yanke hukunci yayi kawai zai samu mahaifinta da magananta ko Allah zai dace.
Tareda abokinshi Sa'ood sukaje gidansu Sulthana, a k'ofar gida suka samu Baffa xaune yana koyarda Almajiransa. Suka karasa inda yake, yana ganinsu ya soma washe baki ganin zankadediyar motar da zukayi Parking.
"Sannunku da zuwa karku zauna a wannan tabarmar yara duk sun bata" cewar Mallan

Gida ya shiga jikinshi na rawa ya dauko sabuwar tabarma ya shinfida bakin kofa sannan yace
"Bismillanku ku zauna"
Zama sukai, Mallan ya mik'a musu hannu dan suyi musbaha, mak'e hannu sukai yaxe
"Aa mu gaisa mata ya haka"
Dak'yar Fareed ya mik'a mai hannu suka gaisa
Mallan yace
"Ban shaidaku bah"
Sa'ood neh ya duk'ar dakai yace
"Sunana Sa'ood sai Abokina Fareed" ya nuna Fareed daya duk'ar dakai yana murmushi
Sulthana ta fito gida rik'e da kofin silver, slippers dinta ta cire ta tsugunna
"Ina wuninku"
Sa'ood neh ya masa yana kallanta,
D'an dagowa Fareed yayi suka hada ido tai saurin dauk'e kai ta aje Kofin tabar wajan..

Sa'ood ya cigaba da Magana
"Mu y'an cikin garin Kano neh a gwanma ja, Mahaifinshi d'an siyasa neh, shike neman mataimakin Gwamna na wannan jaha. Shi kuma cikakken likita neh"
K'ara washe baki Mallan yayi

"Aa Madallah sannunku da zuwa, ina fata dai lapia"
Sa'ood ya k'ara duk'ar dakai
"Abokina nah neh Yaga y'ar wajanka yanaso shine mukazo mu nemi izini"
Mallan ya k'ara gyara zama
"Kai Madallah nayi farinciki da jin wannan maganan, tho wacecce daga ciki hafsatu koh Ameenatu"
Murmushi Sa'ood yayi yace
"A'a Sulthana"
Nan da nan fara'ar fuskan Mallan takau ya hada girar sama data k'asa. Jin Mallan yayi shiru Yasa Fareed yad'an dago ya kalleshi, ganin yanda ya murtuke fuska yasa yasha jinin jikinshi
"Sae dai kuyi hakuri dan na riga nama Sulthana miji"
Dago kai Fareed yayi da sauri yana K'allan Mallan
Sa'ood yace
"Tho shiknan bbu damuwa mun gode Allah ya saka da Alkhairi. Allah kaimu ya basu zaman lapia"
Ameen Mallan Yace atakaice

Hannu Fareed yasa a aljihu ya ciro bandir din y'an dari biyu ya ajema Mallan.
"Gashi bah yawa"
Washe baki yayi ya taba kudin
"A'a ayi haka"
Sa'ood yayi murnushi
"Babu komai ai"
Ganin suna k'okarin tafiya yasa yace
"Nace bah"
Fareed ya dago dasauri yana k'allan Mallan, cigaba da magana mallan yayi
"Akwai yaninta su biyu da hafsatu da Ameenatu, duk wacce yakeso ai sai abashi"
Fareed ya yatsine fuska
"A'a Mallan mun gode, zamu tafi"

Mik'ewa sukai Mallan ya rakosu har bakin mota yanata godiya, sukaja mota suka bar k'ofar gidan cikeda takaici. A hanya Sa'ood ya nisa yace
"Doctor akwai wani abu danai observing"
Fareed ya juya kadan ya kalli Sa'ood sannan ya maida dubanshi ga titi,
" kamar na meh fah?"
Naga k'iyaiyar yarinyan nan a idonshi, bakaga k'allanda yake mata sanda ta kawo ruwan nan bah..

Murmushin takaici Fareed yayi
"Na dad'e da gano akwai matsala a gidan, yarinyan tak'i bani hadin kai naji damuwanta"
Sa'ood ya gyara zama
"Ga shawara"
Parking Fareed yayi ya juya yana k'allanshi
"Mai zai hana mu samu wani ya bamu labarin yarinyan?"
Lallausan Murmushi  Fareed yayi
"Yes! Uh ryt, y not gobe sunday sai mu dawo"
Sa'ood yace
"Haka za'ayi"
Haka suka kama hanyan gida suna tattauna yanda zasu bulloma Alamarin..

Rai bace Mallan ya shiga gida, baiga Sulthana a zaure bah, ya k'arasa gidan ya soma kwallama Sulthana kira da k'arfi rai bace. Jin yanda yake kiran yasa Ameenatu ta fito itada Hafsatu dan idan sukaji wannan kiran to bah lapia bah. Jiki na rawa Sulthana ta fito daga bayi ta aje butan ta k'araso wajan, Mama ta fito tana tambayan lapia. Nuna Sulthana yayi da yatsa ranshi bace Idanunshi sunyi ja..

"Indai ina raye tho ki sani bake bah aure, keh kina tunanin akwai mai abinda zai rabaki da gidan nan? Sai dai mutuwa"
Mama tace
"Lapia Mallan wai meke faruwa neh"
Zayyana musu duk abinda ya faru yayi, hankalin Ameenatu ne ya tashi, dama likita d'an babban gida neh? Hafsatu koh tabe baki tai tana cewa
"Ai Baffa duk sune suke fita da ita, dama ka kyaleta anyi auren kwana biyu neh ya sakota"
Kunnen Sulthana baffa ya kama
"Idan na K'ara jin an ganki da likitan nan, keh ko kallanshi kika karayi balle har ki gaidashi saina kasheki a gidan nan"
Gyada kai Sulthana tai hawaye nabin kuncinta,
"Tashi ki bani waje"
Mikewa tai jiki na rawa ta nufi zaure ta saki matsanancin kuka..

"Abinda kakeyi Mallan baka kyautawa, tunda bakasan ka bude ido kaga yarinyan nan a gidan nan bah saikai mata auren bah tunda ta samu wanda ya fito yana santa"
Jin haka yasa hawaye ya zuboma Ameenatu ta shige daki ta fada kan gadonsu ta fashe da kuka.
Tsaki Baffa yayi
"Likita babba, wanda mahaifinshi ke kokarin hawa babban matsayi shi zan dau wannan dabban naba? Ina! Tunda abin yazama haka cikin Almajiraina zan aura mata kuma anan zasu zauna tare dani ta cigaba damin bauta dan shi yafi dacewa da ita"
Shekewa da dariya hafsatu tai harda tafawa
"Gaskiya neh Baffa haka yayi"

Ummy Abduol✍🏻
[28/08, 01:12] Friend Hussaini: πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
          πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
         *SULTHANA*
         πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

By *Ummy Abduol*

       *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION*
   
           *Page 141 to 145*

K'arfe hudu a kauyensu Sulthana tayi musu, bayan layinsu Sulthana sukai Parking motarsu, yaro sula samu suka hadashi da sabuwar dari biyar ya musu k'iran Babban Almajirin Mallan. Sai washe baki yaron yak'e dagudu ya nufi runfar Almajiran, yakoyi Sa'a ya sameshi zaune shi kad'ai a dakinsu yana karatu. Tare suka k'araso wajan sannan yaran yabar gurin cikeda murna..

Musabaha suk'ai Sannan Sa'ood yace
"Sunana Sa'ood sai abokina Fareed, mu yan cikin garin kano neh. Munzo akan maganar wata yarinya Sulthana munasan musan labarinta dan gwamnati na buk'atar a taimaka ma yara masu irin shekarunta"

D'an jim yayi Sannan ya dago yace
"Ni sunana Sani kuma Almajiri neh ni, kuyi haquri bazan iya fadan wani abu dangane da cikin gidan Malamina nah"

Hannu Fareed yasa a Aljihu ya ciro bandir din y'an dari biyar ya mik'a mai yana cewa
"Kah taimaka, ka fada mana munaso neh mu taimaka mata"

Jim Sani yayi yana tunani Shi kanshi bayasan abinda akema Sulthana a gidan, yanke shawara yayi kawai ya fada musu dan haka yace

"Kuzo ga Bakin bishiyar chan akwai inuwa sai mu zauna"

Bah musu suka nishi suka zauna, nan Sani ya soma basu labari tiriyan tiriyan iya abinda ya sani. Kuka neh kawai Fareed beyi bah anma idanunshi sunyi jah, shi kanshi Sa'ood hankalinshi bah k'aramin tashi yayi bah. Sa'ood neh yayi k'arfin halin cewa

"Mallan Sani anya kuwa Mallan neh ya haifeta"

Dagowa yayi dasauri yana k'allanshi da Mamaki

"Shine mahaifinta mana"

Girgiza kai Fareed yayi fuskansh bah Annuri

"No bashi ya haifeta bah, dan mahaifi bazai taba muzgunama D'anshu haka bah"

Sani yayi murmushin takaici Yace

"Mallan jamilu shine ya haifi Sulthana, duk kuma wanda zaka tambaya a kauyen nan abinda zai fadama knan"

Fareed neh ya mik'e dasauri yana k'arkade rigan jikinshi, Sa'ood ma ya mik'e yana k'allan Sani

"Mungode sosai Sani, zamu tafi idan bukatar k'ara ganinka ta taso zamuzo mu sameka"

Shima mik'ewan yayi ya basu hannu sukai musabaha

"Bbu komai ai ina maraba da dawowanku matukar za'a san yanda za'ayi a taimaka ma Sulthana"

Kudin Fareed ya mik'a mai, ya nok'e yaki k'arba

"Kubar kudinku, Allah dai ya baku sa'an niyyan da kuka dauka"

Ameen sukace suk'a k'arami godiya. Kasa driving Fareed yayi Sa'ood ya amsa keyn motan suka bar wajan kowa da abinda yak'e sakawa a Ranshi..
Fareed yayi ajiyan zuciya yana k'allan Sa'ood

"No mattet how hard the situation will be, no matter how bad. Sai na fitarda Sulthana daga k'angin nan datake ciki, koda kuwa zanyi asarar dukiyana da matsayina matsawar zata kasance cikin farinciki da Annashiwa"

Girgixa kai kawai Sa'ood yayi baice komai bah har suka k'arasa gida..

Ala ala Mami tak'e Daddy ya dawo, bai dawo gidan bah sai wuraren k'arfe goma da rabi na dare. Saida yaci abinci ya huta sannan Mami ta sameshi a office dinshi dake cikin gidan, zama tai kusa dashi
"Sannu da hutawa"

Da Fara'a yadan juyo yana k'allanta

"Sannu uwargida sarautar mata"

Murmushi tayi Sannan tace

"Alhaji inaso neh muyi magana dakai kuma naga kamar kana busy"

Takardun hannunshi ya aje ya matsar da system din dake gabanshi

"Ina jinki"

Jim tai tana k'allanshi Sannan tace

"Akan Maganan Masroor neh, yana daki tun dazu yak'i cin abinci sai aikin kuka yake, saima danai ma Yasir.."

Saurin katseta Daddy yayi hankali tashe

"Meke damunshi? Meyasa yake kuka?"

Nan Mami ta kwashe duk abinda ya faru ta sanar dashi Sannan ta fadamai yanda sukai da Yasir .

Baice komai bah yadau waya ya soma neman layin Masroor, yana dauka yace

"Kah sameni a falona"

Bai jira mai zaice bah ya kashe wayan sannan ya mik'e yana k'allan Mami

"Muje falona"

Koda suk'a karasa falon sun sameshi zaune akan Carpet kanshi a k'asa. Daddy ya zauna kusada shi yana k'allanshi

"Son meke faruwa? Karka boyemin fadamin damuwanka"

Baice komai bah k'anshi na k'asa, k'ara magana Daddy yayi Sannan ya d'ago jajayen idanunshi yana k'allan Daddy

"Daddy inada wacce nakeso but.."

Shiru yayi ya kasa k'arasa maganan

Daddy yayi murmushi

"Go on ina jinka"

Masroor ya sunkuyar dakai sannan ya cigaba

"Sunanta Sulthana ina santa daddy kuma babanta yace zai aura mata almajiri"

Daddy ya k'alleshi da mamaki

"Almajiri"

Kai Masroor ya gyada, daddy ya nisa yace

"Wanene Mahaifinta a garin nan"

Gaban Masroor neh ya fadi jin abinda ya fada, Mami tai saurin amshewa

"Alhaji inace munyi wannan maganan tun achan"

Hannu Daddy ya d'aga mata alamar tai shiru yace

"Ina jinka"

K'ara sunkuyar dakai yayi

"Daddy babanta bah kowa baneh a kauye suke"

Har daddy ya bud'e baki zaiyi magana Mahnoor ta shigo falon dagudu, jikin Mami ta d'ane tana kallan Daddy tana dariya

"Daddy uh welcome"

Murmushi daddy ya mata
"Thank uh my baby, ya school?"

Ta amsa da lapia lau. Hade rai Mami tai

"Tashi min a jiki, bakiga muna magana baneh kin wani shigo bako Sallama"

Zumbure baki tayi ta mik'e zatabar wajan, daddy yace

"Kyalleta zo nan abinki babyna"

Da d'an murmushi ta k'arasa ta zauna kusada Daddy.

"Maminku ta fadamin duk yanda kukai da ita, da kuma yanda zukai da yasir. So zan fara sawa a bincika min Yarinyar da Asalinsu idan har babu matsala insha Allahu she will be ur wife"

Dago kai yayi da Fara'a yana k'allan Daddy

"Daddy dagaske?"

Murmushi Daddy yamai tareda kyada kai. Mahnoor ta k'alli Masroor

"Bro Sulthana?"

Kai ya gyada mata Cikeda farinciki

Tsalle sukaga Mahnoor tahauyi tana murna, Mami da mamaki tace

"Ina kika santa"

Tsagaitawa tai tana k'allan Masroor. Da rarrafe ya matso kusada Daddy ya zauna kusada k'afarshi yanatamai Godiya Sannan ya mik'e yana hararan Mahnoor yabar wajan. Tasan mai yake nufi, murguda baki tayi ta juya tahau bah su Mami labarin zuwanda sukeyi gurin Sulthana..

Mami ta tausaya mata sai taji tanasan yarinyan tun bata hadu da ita bah...


Kwana biyun nan da Masroor baizo bah kullum Sulthana batada aiki sai kuka. Hakan yasa takanje gidansu Sadiya idan tadau tallan dan ta debe mata kewa. Yau tana zaune bakin tasha tayi tagumi tana k'allan hanyar da Masroor ya saba biyowa. Kamar a mafarki taga motarshi ya doso wajan, dasauri ta mik'e ta karasa inda yayi parking. Fitowa yayi yana mata murmushi, zumbure baki tayi ta juya ta koma inda take zaune

Murmushi yayi yabi bayanta, kusa ita ya zauna yana k'allanta. Kauda kai tayi ya juyo da fuskanta. Hawaye ya gani na gangarowa daga idonta

"Omg! Haba Beauty meya faru? Meyasa kike kuka"

Ai kaman jira take ta fashe da kuka harda shesheka, kanshi ya dafa

"Pls stop crying banasan kukanki beauty"

Hankie ya dauko ya soma goge mata hawayen dake fuskanta yana murmushi

"Me aka miki kike kuka?"

Zumburo baki tai

"Bakai baneh ka daina zuwa bah kullum sai nazo nan ina jiranka"

Kallanta yayi da Mamaki

"Kinyi kewana neh?"

Hannu tasa ta rufe fuskanta tana murmushi, shima murmushin yake cikeda Farinciki

"Oh come on! Fadamin kinyi kewana?"

Kai ta gyada mai, murmushi yayi mai sauti

"Nima nayi kewanki beauty, idan natambayeki wani abu zaki fadamin?"

Eh tace tana kallanshi, saida yayi jim sannan yace

"Kina sona?"

Dasauri ta mik'e tabar wajan tana dariya. Shima dariyan yayi kasa kasa, dakyar ya lallabata ta dawo ta zauna yace

"I so much love uh my beauty ina sanki sosai"

Hannayenta biyu tasa ta rufe fuskanta tana murmushi...

Shakuwa mai k'arfi ya k'ara shiga tsakaninsu, har Mami da daddy sun saba da hiran Sulthana da Masroor ke musu kullum. Lokaci nata tafiya, har yanzu bah abinda ya chanza dangane da k'iyayar da Baffa kema Sulthana...

*Bayan wata d'aya*

Alhamdulillah anyi Election Allah yaba Daddy sa'a yanxu shine gwamnan Jahar Kano, Alhaji shuaibu mahaifin Fareed shine mataimakinshi. Bayan komawansu government house Masroor ya matsama Mami akan zuwa gidansu Sulthana saboda nan da sati d'aya zai koma school, Mami na samun Daddy da maganan yace

"Nima abin na raina mantawa nai ban fada miki bah, gobe in Allah ya kaimu za'aje nema mai aurenta"


    *tho fah* anya kuwa?

Ummy Abduol✍🏻
[28/08, 01:12] Friend Hussaini: πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
          πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
         *SULTHANA*
         πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

By *Ummy Abduol*


       *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION*

         *Page 146 to 150*

       *Masroor Fans* Wannan shafin naku neh... fatan Alheri gareki *Hajiya Fateema* kinfi kowa san littafin ina godiya da soyaiyarki gareni.

"Nima abin na raina mantawa nai ban fada miki bah, gode in Allah ya kaimu za'aje nema mai aurenta"
Dad'i sosai Mami taji ai dasauri ta fita ta k'ira Masroor a waya Tareda fadamai Albishir. Murna wajan Masroor ba'a magana suna gama wayan ya kira yasir ya sanar dashi lokacin shi yana hanyar zuwa wajan Fareed dan kwanakin nan da akai election tare suketa shige da fice hakan yasa suka k'ara sabawa sosai..

Yana isa Asibitin yamai waya ya sanar dashi isowarsa. Fitowa Fareed yayi yana murmushi

"Old friend na d'auka fah wasa kakemin"

D'an dariya Masroor yayi yana shafa suman kanshi

"Ai nafika zumunci"

Hannu Fareed ya mik'a mai suka tafa suna dariya

"Kaji talle kema audi gori, duk bah wannan bah friend. Naga sai annashuwa kakene fadamin meya faru?"

K'ayattacen murmushi Masroor yayi

"Gobe in Allah ya kaimu za'aje nema min aure"

"Woaw" Fareed yace cikeda farinciki

"Who is dis lucky beb"

Masroor ya girgiza kai

"Sunanta su...koda yake zaka ganta wata rana da kanta zata fadama sunanta"

Hannu Fareed ya mik'a mai

"I'm very happy 4 uh Friend, Allah ya kaimu musha biki"

"Ameen, tho kaifa yaushe ne nakan?" cewar Masroor

Ajiyan zuciya Fareed ya sauke

"Nikam bah yanzu bah"

Da mamaki Masroor ya kalleshi

"Why?"

Juyowa Fareed yayi yana fuskantan Masroor

"Wata yarinya na gani shes young n beautiful. Saidai yarinyan na cikin Matsala infact namadai je naga mahaifinta yak'i amincewa"

Gaban Masroor neh ya ya fadi. Zuciyarshi ta shiga zargin kodai shine wanda sulthana take fada mishi likitan dayaje nemanta. Dagowa yayi da Alamar damuwa

"Y'ar wacece aina take?"

Murmushin takaici Fareed yayi yana girgiza kai

"Bah y'ar kowa bace, a kauye ma suke."

Kan Masroor neh ya soma sara mai, juyawa kawai yayi fareed ya matso yace

"A'a Old friend bamu gama hiran bafa ina kuma zaka?"

Da hannu ya nunama Fareed kanshi dak'yar ya iya cewa

"Gida zani kaina ke ciwo"

Bai jira mai fareed din zaice bah ya figi mota yabar Asibitin da sauri ya nufi gida...

Hankali tashe ya k'arasa gida, side dinshi ya wuce kai tsaye bai kuma fitowa bah har washe gari...


Safiyar Ranar lahadi da wuri Abokanan daddy su biyu suka shirya Yasir ya musu jagora zuwa k'auyensu Sulthana. Kasancewar bai taba zuwa bah da kwatance Suka gane gidan, a kofar gidansu sukai Parking motarsu. Mallan na ganin Katuwar mota ya mik'e dasauri ya fito daga runfar Almajiransu..

Yasir ne ya fito ya k'arasa suka gaisa da Mallan sannan ya fada mai tareda baki suke. Nan da nan Mallan yahau washe baki ganin mutanen da suka fito daga motan daga gani bah k'ananan mutane baneh..

Tabarma ya dauko ya shimfida suka zazzauna, Mallan ya soma gaidasu suka amsa, d'aya daga cikinsu ne ya fara magana

"Sunana Alhaji ilyasu sai kuma abokina Alhaji Tanimu, daga Cikin Gari muke. Alhaji Aminu Datty gwamna maici yanzu shine ya turo mu dan mu naima ma d'anshi auren Y'arka"

Nan da nan Mallan ya rud'e,

"Anya bayin Allah ni kuwa Mallan Jamilu?"

Alhaji Tanimu yayi Murmushi ganin Yanda ya rud'e

"Kwarai kai"

Gyara zama yayi jikinshi na rawa

"Wacce daga ciki Ameenatu koh Hafsatu?"

Yasir dake gefe yace

"Sulthana"

Had'e rai Mallan yayi baice komai bah, ganin yanda ya sauya fuska yasa Alhaji ilyasu cewa

"Koh Akwai damuwa neh"

Dagowa yayi ya kallesu d'aya bayan d'aya sannan ya bud'e baki ya fara magana

"A gaskiya bazan cuceku bah, saboda d'an babban gida kaman wannan bai kamata na rufeshi bah"

Shiru yayi na wasu lokuta, Alhaji tanimu yace

"Mallan muna jinka"

Abinda Mallan ya fadane yasa ni Ummy Abduol na mik'e dasauri har saida Wayata ta fadi garin fargana

" *A Gaskiya banine uban Sulthana bah, Sulthana shegiya ce batada Ubah*"


Tabdi Jam!...

Kuyi Managing wannan

Ummy Abduol✍🏻
[28/08, 01:12] Friend Hussaini: πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
          πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
         *SULTHANA*
         πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

By *Ummy Abduol*


       *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION*

         *Page 151 to 155*

"A gaskiya banine uban Sulthana bah, Sulthana shegiya ce batada ubah"

Mikewa Yasir yayi dasauri yana nuna Mallan da Yatsa

"Mallan k'iyayar da kakema y'arka har takai haka? Kace bakai ka haifeta bah"

Alhaji tanimu ya had'e rai yana k'allan Yasir

"Wanne irin rashin hankali neh wannan? Wayasa bakinka a maganan nan"

Zama Yasir yayi yana huci ranshi bace. Alhaji tanimu ya maida dubansa ga Mallan fuskanshi bah walwala

"Tho Mallan tunda kace bakai baneh ka haifeta, tho ina mahaifinta yake"

Mallan ya yatsine fuska

"Bansan inda Mahaifinta yake bah, kawai dai ni rik'onta nake"

Mikewa Alhaji ilyasu yayi, Alhaji tanimu ma ya mik'e yana cewa

"Mun gode Mallan mu zamu tafi"

Baice musu komai bah suka kakkabe babban rigansu suka shigaa mota Yasir yajasu suka bar kauyen kowa ransh b'ace..


Yanmacin ranar Sulthana tadau gyadanta kamar yanda ta saba, Bakin tasha ta nufa ko kamin ta k'arasa ta hango motar Masroor pake a inda suka saba zama, da sauri ta k'arasa tana murmushi. Ta mirrown motan ya hangota zuwa ya fito dasauri ya nufeta yana huci

"Dama labarinda kika fadamin duk k'arya neh Sulthana? Ke ashe shegiya ce bakida uba"

Trayn kanta neh ya fadi ta k'walallo ido tana kallanshi da Mamaki, cigaba yayi da Magana cikin kakkausan Murya

"Kin cuceni Sulthana, dama duk abinda kika fadamin k'arya neh? Duk sanda nake miki? Duk lokacinda na bata akanki"

Tsugunawa Sulthana tai ta fasa ihu tareda daura hannu aka

"Yaya Masroor waya fadama wannan maganan? Wallahi k'arya neh Baffa shine Babana"

Ranshi b'ace ya juya Mata baya
"Shi Baffan zai miki Karya neh? Haba Sulthana Kinsa Mahaifina dani munji kunya, why Sulthana why?? Nasan baki sani bah Mahaifina neh Gwamna mai ci yanzu Alhaji Aminu"

Dagowa tayi da Mamaki tana K'allanshi

"Danasan Abinda zai faru knan daban bari Aminan mahaifina sunzo bah. Yanzu da wani ido zan kalli Daddy nah?"

Kuka sosai Sulthana take Hankalinta tashe

"Dan Allaha yaya Masroor karka gujeni, kai kad'ai ke sona kake tausaya min. Idan ka tafi ya zanyi"

Tsugunawa Yayi kusada ita zuciya na cinshi

"Sulthana Bazan iya bah"

Bai jira mai zatace bah ya shiga mota ya bar wajan a guje. Kuka ta k'ara fashewa dashi kamar ranta xai fita, hakanan ta d'au trayn gyadan ta nufo gida tana cigaba da kuka.

Zaure ta zauna ta cigaba da kukanta, saida tai mai tsarta Sannan ta mik'e rai bace ta shiga cikin gidan. Zaune ta samu duka y'an gidan a k'atuwar tabarma da Alama iska suk'e sha. Karasawa tai ta aje trayn a gaban Baffa ta tsugunna akan tabarman k'anta a kasa ta fara magana

"Baffa mai nai maka ka tsaneni baka sona? Idan na maka laifi neh kai hakuri. Meyasa kace bakai ka haifeni bah"

Da mamaki Mama ta k'alli Mallan Gabanta na faduwa

"Mallan Abinda Sulthana ta fada Gaskiya neh"

Tsaki yayi tareda kauda kai

"Hakaneh mana, bazai yuwu bah ace d'an gwamna guda yazo neman aurenta batareda na fadamai abinda ke faruwa bah. Tho yau ku shaida zan amayar da Abinda yake cikina"

Hafsatu ta mik'e dasauri tareda dafe k'irji

"Dan gwamna"

Daga kai Mallan yayi yana k'allan Hafsatu

"Kwarai kuwa"

Hankalin Ameenatu neh ya tashi tace

"Baffa muna jinka me kace zaka fada"

Sulthana ya nuna da Hannu yana cewa

"Sulthana bah y'ata bace, Shegiya ce batada uba. Cikin Shege uwarta tai ta haifeta"

Ihu Sulthana ta saki ta mik'e Dasauri ta daura hannu a kai ta fashe da kuka, rasa inda zatasa kanta tai ta dawo gaban Mallan ta tsugunna tana kuka sosai

"Baffa kai hakuri karka ce haka, ni yarinyanka ce haka Umma tace"

Tsaki yayi

"Karya umman naki takeyi, niba ubanki baneh"

Mutuwar Zaune Mama tai itada Ameenatu, Hafsatu ko cewa take

"Ashe gado tai, shiyasa itama take bin maza. Lallai gwara Baffa daka fadamana"

Kamar mahaukaciya Sulthana ta zama a cikin gidan, ihu kawai take tana kuka kwi kwi. Mama tai k'arfin Halin cewa

"Tunda nake ko a tarihan da mahaifana suka bani ban tabajin inda Uba yakema Y'arshi hakaba sai kai. Kaicona da aurenka Mallan"

Mik'ewa Mallan yayi yana huci

"Ni kike jifa da irin Wadannan Kalaman?"

Kauda kai Mama tai Ranta bace. Baffa ya dakama Sulthana Tsawa yanacewa

"Tunda abin naki ya zama haka maza ki tattara inaki inaki ki tafi ki nemi ubanki. Kada ki kuskura na fito daki na ganki a cikin gidan nan"

K'ara rushewa da kuka Sulthana tai ta rungume Mama tan kuka kamar ranta zai fita

"Dan Allah mama kice Baffa yayi Haquri ni y'arshi neh. Kadaya koreni dan Allah, wayyo Allah na"

Ameenatu ta rarrafo inda sulthana take rungume da Mama itama tana hawaye

"Kiyi haquri Sulthana, Baffa shine Babanki. Kada..."

Muryan Baffa dataji a kanta neh ya hanata k'arasa Maganan datai niya

"Kul! Karna k'araji Sam bah y'ata bace. Maza ki tattara ki bar min gida"

Dorinan daya fito dashi ya d'aga Sulthana na gani ta mik'e dasauri ta fice Zuwa zaure da gudu tana cigaba da kuka..

Mama ta shiga Dak'inta tadauko Mayafinta tana cewa

"Allah wadaranka Mallan, bazan iya cigaba da zama dakai a gidan nan bah"

Takalmanta tasa ta fice daga gidan tana kuka...

Gudu sosai Masroor yake yana kuka kamar K'aramin Yaro. Gidan da suk'a baro ya nufa wanda yanzu shine gidanshi, yana shiga ko k'wakwaran Parking beyi bah yahau hada kayanshi a Trolley yana cigaba da kuka. Waya yama Yasir akan su Hadu a Airport, dama Tun kwana biyu da suka wuce visan shi ya fito. Yana gamawa ya fitoda Akwatin yasa a mota ya kulle gidan ya nufi Airport..

Yana zuwa Yasir na K'arasowa, fitowa yayi daga nashi motan ya dauko Akwatinshi ya k'araso inda Yasir ke tsaye yana k'allanshi da Mamaki

"Friend meye haka?"

Hawayen idonshi ya share yana kallan Yasir

"Sulthana betrayed me, bazan iya cigaba da zama a k'asan nan bah."

Hannunshi Yasir ya kamo Cikin sigan Lallashi

"No Friend, Ni inaji a Jikina Sulthana nata yaudareka bah. She's young and batada wani ilimin da zata fadama K'arya, think of dis"

Girgiza kai Masroor yayi hawaye na gangara a idonshi

"I love her so very much Yasir, meyasa zatamin haka? Ni nasan Mutumin nan bazai mata k'arya bah"

Hannunshi Yasir yaja

"Pls Friend be strong muje gida mu tattauna"

Kai Masroor ya girgiza, duk yanda Yasir yaso Masroor ya hak'ura fafur yak'i yarda dole hakanan ya hakura ya barshi yahau jirgi zuwa lagos shi kuma ya tuk'a motar masroor din ya nufi government house jiki a sanyaye

Bayan dogon bincike Aka bari ya shiga gidan, nan ma kamin ya samu ganin Mami sai da akayi bincike Sosai Falonta datake ganin bak'i aka kaishi. Jin Yasir neh yasa batad'au wani lokaci bah ta shigo falon tana fara'a


"Idonka knan Yasir, tun bayan election ban k'ara ganinka bah"

Duk'ar dakai yayi fuskanshi bah Annuri, ganin haka yasa Mami ta zauna a sanyaye

"Yasir meke faruwa?"

Labarta mata duk yanda sukai da Masroor yayi cikeda damuwa. Mami ta girgiza kai rai bace

"Lallai Masroor ka kyalleshi ai dai ba'achan zai xauna kwatakwata bah koh? Zai dawo ya sameni"

D'agowa Yasir yayi

"Mami Masroor nasan yarinyan nan sosai, ni ina tunanin tsabar k'iyaiya ce kawai da Mahaifinta yake mata yasa yace haka"

Jim Mami tai alamar tunani Sannan tace

"Nima ina tunanin haka saidai bah yanzu zamu tunkari Alhaji da maganan bah dan yanzu yayi fushi"

Yasir ya gyada kai ya mik'e tsaye tareda mik'a mata keyn motan Masroor. Amsa tai tamai godiya yabar gidan...

Kuka sosai Sulthana take tana gudu batareda tasan inda zata bah, gashi gari ya fara duhu dan anata kiraye kirayen Sallan Magriba. Bata farga bah Ruwa ya tsuge kamar da bakin kwarya sam bata lura da hadari bah. Cigaba tai da gudun lokaci lokaci tanasa bayan hannunta na hagu tana share hawayen Fuskanta. Hasken Fitilan motane ya haskata ko kamin tai wani yunkuri tuni motar tai ciki da ita ta fadi k'asa sumammiya...

Ummy Abduol✍🏻

πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
          πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
         *SULTHANA*
         πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

By *Ummy Abduol*


    *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION*

       _Mak'i Gani Ya Kauda Idonsa_

         *Page 156 to 160*

       Dedicated dis page to *Hadiza Ya'u* best fan.. Allah ya bar zumunci


Hasken fitilan motane ya haskata ko kamin tai wani yunk'uro tuni tayi ciki da ita ta fadi K'asa sumammiya. Dasauri ya fito daga motan hankalinshi tashe, Ganin wanda ke wajan yayi baya da sauri da Alamar mamaki. Nunata ya soma y bakinshi na rawa yace

"Su..Sulthana"

A hankali ya k'arasa inda take kwance ya d'auketa yasata a mota ya figi motan xuwa babban Asibiti dake cikin garin Kano inda yake aiki. Shi da kanshi ya shiga bata taimakon gaggawa duk da yanayi jikinshi na rawa zuciyarshi na bugawa, saida numfashinta ya daidaita sannan ya fita zuwa gidanshi kamin ta farka lokacin wuraren k'arfe goma na dare..

Sallah yayi Sannan yayi wanka duk hankalinshi na wajan Sulthana, wayanshi ya jawo ya soma neman layin Sa'ood yakoyi Sa'a yana fara ringing ya d'aga

"Aboki ya Akaine?" cewar Sa'ood

Murmushi Dr Fareed yayi suka gaisa sannan ya zaiyanamai abinda ke faruwa. Shiru Sa'ood yayi nad'an wani lokaci Sannan yace

"Yanzu abinda za'ayi gobe mu hadu a asibitin da safe lokacin ta farka sai mu tattauna"

Tho Fareed yace tareda mai godiya ya kashe kiran. Keyn motanshi ya d'auka ya rufe gidan ya koma asibiti, har yanzu bacci take. kujera yaja ya zauna kusada gadon datake kwance. K'allanta yake yana murmushi, hannunta na dama ya saka cikin mashi yana murzawa a hankali, a haka barci ya d'aukeshi ya d'aura kanshi gefen gadon..

Masroor na Sauka Lagos Airport, taxi ya shiga ya kaishi hotel dinda zai kwana. Yini yayi bah walwala koh abinci ya k'asa ci. Zuciyarshi Sunan Sulthana kawai take kira, Wayanshi ya janyo ya kunna sannan yasata a Fight mode dan baisan a nemeshi. Pictures d'in wayanshi ya shiga, hoton Sulthana ya dubo wanda ita batamasan an d'auka bah tana xaune tana murmushi da alama Gyada akazo siya

Shafa hotan ya soma yi hawaye cike a idonshi

"I love uh my beauty, meyasa kikamin k'arya"

Hawayen dake mak'alle a idonshi suka gangaro ya share tareda mik'ewa ya shiga toilet don watsa ruwa..

Sulthana bata farka bah sao wuraren k'arfe bakwai da rabi na safe. Firgigita ta mik'e zaune, bin dakin da Kallo ta soma yi cikeda mamaki. Ganin kan mutum kusa da ita yasata kwace hannunta tareda sakin ihu, tana k'okarin sauka daga kan gadon..

Farkawa Fareed yayi ya mik'e yana k'allanta da Murmushi

"Meya faru? Y are you shouting"

Drip din hannunta take kici kicin Cirewa tana k'allanshi a tsorace, rik'e hannunta yayi dasauri ganin tana kokarin jima kanta ciwo

"Me kike kokarin yi, ki kwanta bakida lapia neh"

Girgiza mai kai tayo hawaye na fita a idonta dak'yar da budi baki tace

"Ni ka ciremin wannan abin na tafi, ina neh nan? Waya kawoni"

Jin tashin Magana yasa Wata nurse ta shigo dak'in ganin dr Fareed yasa ta koma dasauri tana cewa

"Sorry sir"

Baice komai bah ya maida dubanshi ga Sulthana dake kuka a hankali

"Jiya da Daddare na bigeki a mota shine na kawoki asibiti, ina zaki da daddaren nan Sulthana"

Sai a Sannan ta tuna koran da Baffa ya mata, wani sabon kukane yazo mata, ta kauda kai gefe tana kuka kamar ranta zai fita. Runtse idonshi yayi ya naushi Iska ya fice daga Dak'in, Nurse dinda ta leko yama magana akan karta bari ta fita Sannan ya fita zuwa haraban asibitin. Motarshi ya hau ya figeta yabar Asibitin

Gidanshi ya nufa saida yayi wanka sannan ya k'arya duk abinda yakeyi jikinshi a mace yake. Wayan Sa'ood ya kira yace su hadu k'arfe tara a asibiti. Yana gama wayan yad'au keyn motarshi ya fice. Gidansu ya nufa batareda dogon bincikeba saboda securitys din sun sanshi aka barshi ya shiga gidan..

Mottoci ya gani kusan guda biyar a haraban gidan cikin shiri, da wasu mata dake gefe da Alama Umma suk'e jira. Side din Umman ya nufa kai tsaye dan yasan yanzu Abba ya fita zuwa Office, Bai sameta ta falo bah sai ma'aikata daketa gyara Falon. Benen dake falon ya hau a nan suk'ai kicibus da ita cikin shiri da Alama fita zatayi

"Good Morning Umma" yace kanshi a k'asa

Tsayawa tai chak sannan tace

"Morning"

Jin tayi shiru yasa yad'an dago suka hada ido

"Fareed Meke damunka?"

Wayancewa yayi

"Babu komai me kika gani"

Hannunshi ta kama suka sauko k'asa. Ma'aikatan na ganin haka sukabar falon dasauri, zaunar dashi tai kan 1seater itama ta zauna ana kusa dashi

"Fadamin meke damunka? Bah haka ka saba zuwa bah"

D'an murmushi yayi

"Bbu komai Ummah i'm fine bah abinda ke damuna."

Bayaso ta cigaba da tambayatan shi dan haka yace

"Ummah inace ke ake jira a waje"

Mik'ewa tai dasauri

"Eh wallahi, zamuje mu hadu da Matar governor zamuje wani meeting neh"

Kai ya gyada yana y'ar murmushi

"Allah ya tsare, kice ina nan zuwa na gaidata"

Hararanshi tai cikin sigan wasa

"Ni y'ar aikenka ce?"

Dariya yayi k'asa kasa yana shafa sumar kanshi
Sallama tamai ta fita. Shima mik'ewa yayi shima yabar gidan.

Saida ya tsaya yasai mata abinci mai rai da lafiya sannan ya koma asibitin. Patient ya gani burjik sunata jiranshi, saida ya tsaya suka gaggaisa sannan ya nufi dakin da Sulthana take kai tsaye.

Zaune ya sameta kan gado ta hada kai da guiwa tayi shiru. A hankali ya k'arasa kusada gadon yaja kujera ya zauna, zabura tai ta d'ago idanunta da suka runne tana k'allanshi. Harta bud'e baki zatai magana kuka yazo mata ta k'auda kai gefe tana kukan a hankali..

Runtse ido yayi ya bud'e tareda aje mata abincin a kusada ita

"Kici abinci sai kisha magani barin duba patients"

Bai jira mai zatace bah ya bar office din. Kamar yanda suk'ai da Sa'ood k'arfe tara ya k'araso Asibitin lokacin ya gama duba patients dinshi. Fareed ne yama Sa'ood jagora zuwa dak'in, yanda ya barta haka ya dawo ya sameta bata taba abincin bah. Nunama Sa'ood kujera yayi ya zauna shi kuma ya tsaya a tsaye.

Sa'ood ya nisa yace

"Sulthana!"

Kai ta d'ago ta kalleshi shi kuma ya cigaba da cewa

"Ki kwantar da hankalinki bazamu cutar dake bah"

Fareed ya nuna da hannu yana cewa

"Nasan kinsan wannan, ki fadamin meya fito dake jiya da daddare har ya bigeki da mota"

Hawaye ya cika mata ido ta k'auda kai gefe murya chan k'asa tace

"Bah komai"

Murmushin takaici Fareed yayi tana girgiza kai. Sa'ood ya cigaba da cewa

"Karki boyemana komai Sulthana, munsan halin da kike ciki keda Baffanki so ki fada mana meke faruwa? dukanki yayi ko meh?"

D'agowa tai ta kalleshi da mamaki. Murmushi Sa'ood yayi dan ya gane k'allan datake mai

"Kina mamakin y'anda akai muka sani koh?"

Kuka ta saki tana cewa

"Baffa ne ya koreni daga gida yace bashine babana bah wai banida..."

Kukane yaci k'arfinta. Sakin baki su Fareed sukai da mamaki

"Bashi ya haifeki bah?" cewar Fareed

Kai ta gyada kanta a k'asa tana cigaba da kuka. Lallashinta Sa'ood ya soma yi dakyar tai shiru, ya mik'e ya kama hannun Fareed suka bar dakin. Wata nurse Sa'ood ya samu budurwa wacce bazata wuce shekara ashirin bah da gani y'ar practical ce yasa hannu a aljihu ya ciro kudi masu tsoka ya mik'a mata

"Inaso ki kulamin da patient din dake dakin chan"

Ya nuna dakin da Sulthana ke ciki sannan ya cigaba da cewa

"Tak'i cin abinci neh inaso kisata taci abinci pls and banaso tana kuka"

Kudin ta amsa tana washe baki

"Bbu damuwa sir za'ayi kamar yanda kace"

Office din Fareed ya shiga ya sameshi zaune yayi tagumi. Sun dad'e suna tattaunawa Sannan Sa'ood ya mik'e tareda mai Sallama yabar Office din.


Saida Sulthana tai kwana hudu a Asibiti kullum tana tareda Nurse dinda Sa'ood ya barma amanarta, Sun saba sosai dan Sulthana batada wuyan sabo har tad'an saki ranta.

Kayan sawa kala kala Fareed ya saima Sulthana, sister Aisha ita ta koya mata yanda ake saka kaya da sauransu. Randa ta cik'a kwana shidda aka sallamesu a nan neh hankalin Fareed ya tashi dan baisan inda zai nufa da Itabah..

     *wai ina labarin Masroor neh?*

Ummy Abduol✍🏻

πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
          πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
         *SULTHANA*
         πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

By *Ummy Abduol*


    *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION*

       _Mak'i Gani Ya Kauda Idonsa_

         *Page 161 to 165*

Randa ta cika kwana shidda aka sallamesu a nan neh hankalin Fareed ya tashi dan baisan inda zai nufa da itabah. Yanke shawara kawai yayi ya kaita gidanshi dan haka ya juya akalan motarshi zuwa gidanshi...

A bangaren Masroor kuwa kwanashi Biyu a Lagos sannan jirginsu ta d'aga zuwa k'asar turkey. Karatunshi ya cigaba dukda har yanzu san Sulthana na nan mak'ale a zuciyarshi. Mami da Daddy sun kirashi sun mai fada sosai akan rashin Sallamasu da baiyi bah, kullum yakan zauna yayita tunanin Sulthana gani yake kamar bai mata adalci bah daya taho ya barta batareda ya mata Sallama bah.

Yau ya kama sunday yana zaune a gidanshi bayan ya dawo daga supermarket. Waya ya d'auka ya soma neman layin Yasir, bugu d'aya ya dauka suka gaisa. Shiru Masroor yayi nad'an seconds sannan yace

"Alfarma nake nema Yasir"

Batareda bata lokaci bah Yasir yace

"Ok babu damuwa"

Ajiyan zuciya Masroor yayi sannan yace

"Dan Allah Yasir inaso neh kaje min wajan Sulthana, she's always on my mind. Kullum zuciyana bugawa yake gani nake kamar wani abu ya faru da ita"

Saurin katseshi Yasir yayi da cewa

"No stop saying that, babu komai insha Allah"

Runtse ido Masroor yayi sannan ya bud'e, Yasir ya wuce aboki a wajanshi ya wuce Amini ya zama hamimi. Bah abinda zai iya boye mai, zaiyana mai duk yanda Sukai da Fareed yayi hankalinshi tashe..

Yasir yayi murmushi yana cewa

"Oh friend wani tabbaci kake dashi akan cewa Sulthana ce"

"Naji a jikina itace Yasir, idan har Fareed santa yakeyi bansan yanda zanyi bah I cn't live witout Beauty"

"Ka kauda wannan tunanin a ranka pls"

Kai Masroor ya gyada kamar yana ganinshi

"Shiknan sai na jika"

Sallama sukai tareda kashe kiran..

A kauye kuwa Mama na fita Ameenatu ta bita a guje tana kuka bako hijabi, hannun Mama ta rik'e

"Dan Allah Mama karki tafi, idan kika tafi dawa zamu zauna"

Kuka itama Maman keyi

"Ameenatu bazan zauna bah, duba fah abinda Mallan yayi yanzu kina kallo, wannan wanne irin k'iyaiya neh?"

Ameenatu ta share hawayen idonta da bayan hannu

"Kiyi haquri Mama karki tafi dan Allah, nasan Sulthana batai nisa bah zan dubota nidai ki koma gida"

Hannunta ta kama suka koma cikin gidan, dakinsu ta shiga ta samu hafsatu zaune kan gado tana nunke kaya

"Hafsatu komenene ya faru Sulthana K'anwarmu ce, kada ki daka ta baffa dan abinda ya fada bah gaskiya bneh. Ki natsu kiyi tunani kada rud'in duniya ta kwasheki, ranar danasani nake gudan miki Hafsatu, ranar da batada wani anfani"

Dagowa Hafsatu tai tana K'allan Ameenatu fuskanta bah walwala da Alama magananta ya fara tasiri. Ameenatu ta zauna kusada ita ta rik'o hannun hafsatu tana hawaye

"Hafsatu ke k'anwata ce kamar yanda Sulthana take kanwata. Haka kema Sulthana kanwarki ce, bai kamata muk'i yar uwarmu bah jinnin mu ce ki tuna"

Hawayen idonta ta share tana jan magina

"Kinyi karatun Addini daidai gwargwado akwai hadisi da manzo Allah tsira da Aminincin Allah su tabbata a gareshi yake cewa imanin d'ayanku baya cika har sai kasowa d'an uwanka abinda kakd soma kanka. Kiyi tunani cikinmu bah wanda yakeso ya kasance cikin rayuwar da Sulthana take ciki bama muba har y'ayanmu"

Hawaye ne suka gangaro daga idon Hafsatu

"Haka neh ya Ameenatu, tho menene dalilin Baffa na cewa Sulthana bah y'arshi bace"

Girgiza kai Ameenatu tayi

"Ki cire wannan Maganan a ranki, bah gaskiya baneh wannan"

Hafsatu ta mik'e tana share hawayen Fuskanta

"Yaya Ameenatu yanzu ya zamuyi? Gashi Baffa ya koreta"

Itama ta mik'e tana cewa

"Zamu fita neh nemanta ta dawo gida mu zauna mu nunama Baffa rashin Amincewan mu akan abinda yake mata"

D'aukan Hijabi hafsatu tai suk'a fito tsakar gidan, a nan suka samu Mama zaune tayi tagumi, basuxe komai bah suka fita suka soma nemanta.

Duk inda suke tunani Sulthana zatace bah inda basu jeba anma duk maganar d'aya ce batazo bah. Hankalinsu bah k'aramin tashi yayi bah, koda Suka samu Mallan sani Aminin baffa da maganan bah K'aramin Mamaki yayi dajin abinda Baffa Yayi bah.

Sadiya sai kuka take jin k'awarta ta bata, haka ma Mamanta ta shiga Cikin tashin hankali sosai. Ganin hadarin dake garin yasa suka dawo gida duk'ansu jikinsu a sanyaye. Tun daga nesa suke hango Almajirai tsaitsaye a kofar gidansu, dasauri suk'a karasa aka matsa musu suka shiga cikin gidan. Nan ma mutane suka gani zagaye, Hafsatu ce ta k'usa ganin Baffa tayi kwance kan tabarma yana numfashi Sama sama Mama na kusa dashi tana kuka..

Hankali tashe Hafsatu ta shiga tambayan meya faru, Mama ce ta bata amsa da cewa

"Wai a bakin Masallaci ya fadi shine aka kawoshi gida"

Ameenatu ta k'araso wajan ta tsugunna kusada Baffan itama tana hawaye

"Allah gamu gareka, idan Laifi mukai maka Allah ka gafarce mu. Mun tuba, Mun tuba.."

Kuka take sosai tana k'allan Baffa dake kwance rai a hannun Allah. mutanen dake wajan kowa ya watse aka barsu su kadai sunata kuka..

Da taimakon Babban Almajirin Mallan da wasu almajirai aka shiga dashi d'akinshi saboda hadarin dake garin..

Magani aka hau yima Mallan Anma kamar ba'ayi, mallan Sani duk inda yaji Mallami sai ya nemoshi ko ya amso maganin Anma Abin dai gaba yake. Su Ameenatu da Hafsatu idan ka gansu gwanin ban tausayi, abu ya hadu musu biyu ga rashin Sulthana ga rashin Lapian Baffa...

Mallan ya koma kamar bashi bah ko magana baya iyayi, idanunshi kullum a bud'e yana k'allan sama komai saidai aimai baya iya komai... _niko Ummy Abduol cewa nai Allah ya k'ara_


Fareeda yayi Parking a haraban gidanshi ya d'an kalli sulthana daketa bin Gidan da Kallo

"Muje koh?"

Bah musu ta bud'e kofan motan kamar yanda taga yayi dazu ta fito shima ya fito suka nufi cikim gidan. Kofan main palour ya bud'e Ya shiga Sulthana na biye dashi, zama yayi kan Kujera ita kuma ta zauna k'asa kan Carpet ta makure tana bin Falon da Kallo cikeda kauyanci

"Meyasa kika zauna a k'asa tashi ki zauna kan kujera, ki saki jikinki ki rink'a min magana kinji"

Kai ta d'aga ta mik'e ta zauna k'an kujera tana cigaba da bin Falon da k'allo. D'an dariya yayi k'asa kasa yace

"Falon ya miki kyau neh?"

Murmushi tayi wanda saida dimples dinta suk'a lotsa. Kallanta ya tsaya yi ganin irin kallan dayake mata yasa ta duk'ar dakai. mik'ewa yayi yaja Trolleyn kayanta Yana cewa

"Taso na nuna miki"

Bah musu ta mik'e tabi bayanshi, wani bedroom dake hannun dama ya bud'e ya shiga juyawa yayi bai ganta bah ya lek'o ya ganta bakin kofa tsaye yace

"Shigo mana"

Zuciyanta na bugawa ta shiga dakin, wow tace a ranta dan tunda uwarta ta haifeta bata taba ganin daki mai kyau irin wannan bah. Murmushi ya mata ya kamo hannunta ya zaunar da ita kan katafaren gadon dake dakin

"Meyasa kike d'ari dari dani neh. Bazan cutar dake bah, daga yau nan neh dakinki"

Batasan lokacinda ta saki lallausan Murmushi bah har saida Fararen Hak'oranta suka baiyana

"Dagaske?"

Shima murmushin yayi dan Yaji dadin yanda tad'an saki ranta. Gani yayi kuma ta bata fuska tana k'okarin kuka, hankali tashe yace

"Menene"

Bai ankara bah ta fashe da kuka tana shesheka

"Shiknan bazan koma gidanmu bah? Meyasa Baffa baya sona. Dan Allah kaje ka bashi hakuri idan namai laifi neh, ni y'arshi ce"

Tausayi ta bashi ya zauna kusada ita tareda rik'o hannayenta

"Ki daina kuka, insha Allahu nan bada dad'ewa bah komai zai daidaita zaki koma wajan Baffanki kinji"

Kai kawai ta gyada tana cigaba da matsar k'walla. Kawar mata da damuwan yayi ta hanyar cewa

"Tashi na nuna miki yanda ake anfani da komai"

Bah musu ta mik'e tana binshi a baya, da cikin d'akin suka fara sannan suka shia toilet nan ma ya nunnuna mata suka fito zuwa sauran sauran wurare dake cikin gidan..

Ummy Abduol✍🏻

πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
          πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
         *SULTHANA*
         πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

By *Ummy Abduol*


    *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION*

       _Mak'i Gani Ya Kauda Idonsa_

         *Page 166 to 170*


Kwanan Sulthana Uku a gidan Fareed, Kullum cikin tunanin Y'an uwanta take dakuma Masoyinta Masroor, takanyi kuka idan ta tuna koranda Baffa ya mata da kuma gudunta da Masroor yayi. Har yanzu sanshi da kewanshi na mak'alle a zuciyarta, bah lefi cikin kwana ukun sun d'an saba da Fareed yakan jata da hira duk da ba wani amsan kirki take bashi bah.

Aranan na hudun Sa'ood yazo gidan suna zaune a falo suna hira Sulthana na dak'i tana barci. Sa'ood ya nisa yace

"Magana nakeso muyi dakai Fareed"

Gyara zama Fareed yayi Sannan yace

"Ina jinka"

Sa'ood ya soma magana yana k'allan Fareed

"Zamanka da mace ku biyu bah abu baneh mai kyau, shedan ake gudu."

Ajiyan zuciya Fareed yayi

"Gaskiya neh Sa'ood, saidai kasan Matsalan Ummah bazata taba yarda Sulthana ta zauna da ita ba kuma ma kagani yanzu bah zama take bah"

Shiru Sa'ood yayi yana tunani chan yace

"Dole mu nemi mafita dan wannan bah abu mai yuwuwa baneh"

Fareed ya d'ago yana cewa

"Ga shawara"

Sa'ood ya ce

"Ina jinka"

"Mezai hana nasata a boarding school har zuwa sanda zan sanar da Abba da ummah"

Murmushi Sa'ood yayi

"Yes haka ya kamata"

Sun aje akan ranar monday da Sassafe zasu kaita zaria academy dan mata registration..

Abubuwan sunma Yasir yawa gashi kullum sai Masroor ya kirashi akan Zuwa kauyensu Sulthana. Yau yana barin School kauyen ya nufa kai tsaye. Batareda wani d'ar bah yasamu Almajiri yace yamai Sallama da Sulthana. Almajirin yace

"Ai Sulthana ta b'ace ba'a ganta bah yanzu sati uku knan"

Hankali tashe Yasir yace

"Garin yaya?"

Almajirin ya tab'e baki yace

"Nima ban sani bah, andai ce Mallan ne ya koreta."

Ran Yasir ba karamin Baci yayi bah yace

"Mallan din na nan"

Yaran yace

"Ai mallan bashida lapia tun ranar data bace ya fadi a bakin Masallaci har yanzu bai warke bah"

Hannu yasa a Aljihu ya ciro d'ari biyu ya mik'ama yaran yana murmushi

"Gashi abokina nagode"

Amsa yaran yayi tareda godiya shi kuma ya shiga motanshi yabar kauyen Hankali tashe. Yanzu taya zai gayama Masroor wannan mummunan labarin.

Yini yasir yayi cikeda fargaban yanda zai fadama abokin nashi wannan labarin. Yakoyi sa'a bai kirashi bah sai washe gari, da kyar ya dauka suka gaida Masroor yayi saurin cewa

"Yasir kakoje?"

Shiru Yasir yayi har saida Masroor yace

"Kana jina kuwa?"

Ajiyan zuciya Yasir ya saki yace

"Ina jinka friend, naje anma ban samu ganinta bah"

Nan da nan Masroor ya rud'e ya shiga jeromai tambayoyi

"Meyasa baka ganta bah?? Bata nan neh? Ko taje talla?? Pls Yasir yimin magana uh sound strange"

Ta maza yasir yayi ya zaiyanema Masroor duk yanda sukai da Almajirin daya samu a kofar gidansu Sulthana. Wayan dake Hannun Masroor ne ya fadi hawaye suka cika idonshi, kuka ya saki mai sauti tana kiran sunanta da k'arfi. Neighbours dinshi suka fifito suka tsaya a bakin kofan hankalinsu tashe jin yanda yake kuka da k'arfi yana fashe fashe..

Saida yayi mai isarsa sannan ya mik'e idanunshi sunyi luhu luhu ya shiga toilet yayi alwala ya soma kai kukanshi ga ubangiji _oh Masroor I pity uh_

Washe gari da safe Fareed da Sulthana suna kan dinning suna breakfast kamar yanda suka saba y'an kwanakin. Maganan sata a makaranta ya mata. Tayi farinciki sosai daga baya kuma ta hade rai

"Yanaga kuma kin chanza meya faru?

Rau rau tayi da ido

"Yaya Fareed yanzu shiknan bazan k'ara ganin Mama da yaya Hafsatu da yaya Ameenatu bah"

Goshinshi ya dafa

"Oh God! Sulthana ki cire wadan nan mutanen a ranki su basa sanki kece kawai kika damu dasu"

Hawayen dake makalle a idonta suka zubo tana girgiza

"Ina Sansu Yaya Fareed suma suna sona"

D'an jim yayi ya mik'e yana cewa

"Shiknan yanzu dai bansan kukan, ki shirya gobe da Sassafe zamu tafi. Idan akai hutu saiki je"

Ihu ta saki tana Y'ar Murmushi

"Nagode Ya fareed"

Kai kawai ya gyada ya bar wajan a zuciyarshi yana raya. Lallai rashin kula da gata yasa Sulthana shiru shiru dan yanzu data d'an wartsake ya hango k'iriniya da shagwaba a idanunta..

Washe gari da wuri da wuri suka tashi, da kanshi ya shirya mata kayanta a trolley da duk abinda take buk'ata. Saida ya tsaya a wani babban supermarket yayi mata sayaiyya sosai sannan suka biya ta gidansu Sa'ood ya daukeshi suka nufi zaria..

Bayan gwajinda akai mata Mallaman sukace za'asata a js1 rok'onsu Sa'ood yayi asata a js3 saboda ta girma she is 15. Hakan ko akai saida akai mata komai aka kaita hostel dinsu sannan su Fareed suka dawo gida...

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya. Ta bangaren Masroor kuwa
Kullum da tunanin Sulthana yake kwana dashi yake tashi, yanzu Masroor ya koma shiru shiru bashida hayaniya. Hoton Sulthana shi yazan mai tv, lokaci lokaci yakan sa Yasir yajemai Kauyensu Sulthana ko da wani labari gameda ita anma bbu. Yasir na matuk'ar tausayama abokin nashi hakama Mami dan Yasir ya sanar da ita duk abinda ke faruwa...

Sulthana taji dad'in makarantan sosai dan a ranar datazo tai k'awa mai suna Aisha ibrahim itama y'ar jahar kano ce. Yarinyar wani senator ne a gwamnatin dakaci yanzu. Y'ar gayuce sosai ga Rashin ji da Tsiwa, tasu tazo d'aya sosai da Sulthana, wajanta take koyan Abubuwa kamar karatu da sauransu..

     *Bayan shekara d'aya*

Sulthana na hango tsaye a wajan makaranta sanye da k'ayan hostel hannunta Rik'e da trolleynta, ta k'ara tsawo da cika, fatanta ya murje tayi kyau sosai. gefenta k'awarta Ayoush itama tsaye da Alama hutu akai saboda yanda dalibai keta fitowa da jakunkunan su. Hira suk'e suna dariya chan saiga wata had'adiyar mota k'irar doddge tai parking. Fareed ne ya fito daga motan sabye da Farar yadi sai baza k'amshi yake. K'arasowa inda suke tsaye yayi yana y'ar murmushi,

"Am sorry Queen I know i'm late"

Zaumbure baki tai ta kauda kai gefe, dariya Ayoush take k'asa kasa ta gaidashi da kanta ta saka jakan Sulthana a motar sannan ta karasa inda take tsaye

"Queen kiyi haquri mana kuje kinji"

Murmushi Sulthana taima Ayoush suka rungume juna sannan Sulthana ta shiga yaja sai kano ta dabo..

Fushi Queen dinshi keyi dashi, bah yanda beyi bah daran ranar ta rakashi yanada Dinner anma taki wai ita barci take ji. Hakanan ya hak'ura ya kira Sa'ood sukaje tare..

Masroor ne xaune cikin  jirgi yau cike yake da farinciki zai dawo nigeria wajan iyayenshi. K'arfe hudu na shidda na yanma jirginsu ya dauka a kano, koda ya dauko Yasir ya gani tsaye shida Mami da Umma'n Fareed sai wasu mata dake bayanshi dukansu fuskokinsu d'auke da murmushi..

Dasauri ya k'arasa ya rungume Mami cikeda farinciki sannan ya rungume Yasir sunama Juna Dariya. D'an rusunawa k'adan yayi ya gaida Umman Fareed ta amsa fuska a sake, Mahnoor ta fito daga mota da gudu itama ta rungumeshi

"I missed uh bro"

Kanta ya shafa yana murmushi

"I missed uh too lil sis"

Yasir ya k'araso wajansu yace

"Dare yayi muje gida kwayi maganan"

Hannun Mahnoor Masroor ya kama suka shiga mottoci suka dun guma zuwa government house. A chan ma taron jama'a ya gani dan murnar dawowanshi da kuma murnar kammala karatunshi. Cikin taron harda Fareed da abokinshi Sa'ood suma sun samu halarta, anyi ciye ciye da adduo'i sannan kowa ya tafi gida..

Washe Gari dasafe Mahnoor zaune itada Masroor suna breakfast, Mahnoor tace

"Bro yaushe zamuje wajan Sulthana tunda ka dawo"

D'agowa yayi dasauri ya kalleta tareda sakin Fork din dake hannunshi..


Ummy Abduol✍🏻

πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
          πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
         *SULTHANA*
         πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

By *Ummy Abduol*


    *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION*

       _Mak'i Gani Ya Kauda Idonsa_

         *Page 171 to 175*
       Dedicated dis page to Aunty Nurse (Ayoush) Allah dawo min dake nigeria Lapia.

D'agowa yayi dasauri ya kalleta tareda sakin fork din dake hannunshi. Ta fama mai tsohon kumin daya dad'e a zuciyarshi baice mata komai bah ya mik'e yabar wajan. Mahnoor ta bishi da kallo cikeda Mamaki..

A kauye Mallan ciwonshi sai gaba yake kullum cikin magani anma babu abinda ya chanza. Rayuwa knan! Duk yan kudadenshi sun tafi wajan magani, Almajiranshi duk sun gudu sun tafi gida. Yanzu Mallan da iyalinsu sun zama abin tausayi Abinci ma dak'yar suke samu watarana ma haka suke kwanciya basuci komai bah. _niko Ummy Abduol nace dama rayuwa haka take, yau gareka gobe ga wani. Abinda ka shuka shi zaka girba in Alkhairi ka shuka shi zaka gani, in kuma sharri neh shidin dai zaka gani_
   
_Allah kasa mufi k'arfin zuciyarmu. Ka bamu ikon aikata Alkhairi ka nisantar da zuciyarmu da Aikata sharri Ameen_

Sulthana zaune a palour yana k'allo taji bud'e gate din gidan, mik'ewa tai dasauri ta fito haraban gidan dan dama shi take jira. Yana parking ta bud'e mai murfin motan tanamai Murmushi

"Ya Fareed tun dazu nake jiranka, ko ka fasa kaini yawon"

Goshinshi ya fada tareda furzar da aska

"Oh God! Queen bakya mantuwa neh?"

D'an zaro ido tayo cikeda shagwaba tace

"Yauwa nama tuna kace zaka saimin phone"

Muryan shagwaba yayi shima yace

"Tho Queen sai ki bari idan na huta"

Dariya ta kyalkyale dashi ya mik'a mata breifcase dinshi ta amsa tana tafe yaba binta a baya. Abinci mai rai da lapia ta dafamai ta jera a dinning, kallan warmers din yayi da Mamaki

"Waya kawo wadan nan abincin"

Bubuga k'afa tayi a kasa tana turo baki

"Nifah na dafa fah"

Iyeh yace cikeda mamaki

"Waya koya miki girki?"

Hannunshi ta kama ta zaunar dashi kan kujeran dinning din tana murmushi

"A school mana, ai munayin Home economics"

Gyada kai kawai yayi dai dai lokacinda ya saka loma d'aya. Ya lumshe ido ya bud'e

"Umm! Wannan ai saiya ciremin kunni"

Dariya tayi ta zauna itama ta zuba nata, saida yaci yayi nak Sannan ya mik'e yana cewa

"Bari nayi wanka na shirya sai muje"

Tsalle tayi tana dariya

"Thank uh ya Fareed dts why I love uh"

Da mamaki ya k'alleta tai saurin juyawa ta shiga dakinta tana cigaba da dariya.

Masroor neh yayi paking a kofar gidansu Yasir. Waya ya dauka ya kiranshi ya sanar dashi isowar shi, ba'adau lokaci bah ya fito yana murmushi

"Har ka gama hutawan?"

Kai kawai Masroor ya gyada ya shiga mota ya zauna, yasir na ganin haka shima ya shiga ya zauna yana k'allanshi

"Yadai friend meke faruwa?"

Batareda ya kalli yasir bah yace

"Inaso neh muje gidansu Beauty"

Yasir ya yatsine fuska

"Muje muyi meh kuma Masroor? Duk sanda naje bana samunta bata dawo bah. Pls Friend ka cire yarinyan nan a zuciyarka myb ma bata raye"

Dago jajayen idanunshi yayi ya zubama Yasir,

"Wannan wanne irin magana neh Yasir? Na cire beauty a raina fah kace??"

Runtse ido yayi ya bude

"Bazan iya bah yasir, bazan iya bah. Indai zaka rakani to idan kuma bazaka rakani bah"

Ya nunamai kofa

"Zaka iya tafiya zanje ni kadai"

Murmushin takaici Yasir yayi

"Muje"

Kunna Motan Masroor yayi suka d'au hanya..

La'asar lis suka isa kauyen, masallacin kusada gidan sukai Sallah sannan yasir yayi sallama a kofar gidan. Hafsatu ce ta fito duk tayi bak'i ta fige kamar ba ita bah, Masroor na ganinta ya had'e rai. Yasir ne yace

"Munzo neman Sulthana neh"

K'uri tama Masroor tana k'allanshi shiko gogan ya kauda kai sai cika yake yana batsewa. Sai a sannan taganesu tad'anyi Murmushin y'ake tace

"Ina wunin ku?"

Yasir ne ya amsa ita kuma ta cigaba da cewa

"Sulthana ta b'ace ba'asan inda take bah shekara d'aya knan da k'usan rabi"

Hankalin Masroor ya tashi ya juyo ya kalleta murya na rawa yace

"Dan Allah bakuji wani labarinta bah?"

Kai Hafsatu ta girgiza tana matsar kwalla

"Bah wani labari. Muma Mallan na kwance bashida lapia tun lokacin"

Yatsine fuska Masroor yayi ya juya yana cewa

"Sai anjima Allah bashi lapia"

Rufamai baya Yasir yayi suka shiga mota suka bar k'auyen..

Yawo sosai sukasha ranar itada Fareed, Sannan daga baya sukaje plazer yasai mata hadad'iyar waya k'irar iphone5. Murna wajan Sulthana ba'a magana sai tsalle take a plazern cikeda Farinciki. Biyan kudin yayi suka fito tana Murmushi mai k'ara mata kyau, saida suka shiga mota sannan ta kalleshi da fara'a

"Thank uh ya Fareed"

Kai ya gyada yace

"Keh koh Queen! Wai aina kika koyo wannan shagwaban da rashin ji haka"

Turo baki tayi ta sauke kai tana duba kwalin wayan. Baice komai bah ya tada motan suk'a d'au hanyan gida.

Masroor driving yake anma hankalinshi sam bai jikinshi, ji yake kaman ya fashe da kuka. Gabanshi ne ya soma faduwa yad'an dago ya kalli Yasir Sannan ya maida dubanshi ga Titi.  Yasir ne ya taboshi tareda nunamai Motan dake gabansu yana cewa

"Wannan bah benz din dr Fareed baneh"

Wani faduwa gaban Masroor ya k'arayi ya d'ago dasauri yana k'allan motan

"Eh itace"

Murmushi Yasir yayi

"Lallai Fareed d'an duniya neh, shine rannan yacemin baida budurwa anma ji kamar wata nake gani a motan"

Faduwan gaban Masroor neh ya tsananta, wuri ya samu yayi parking yana k'allan motan Fareed har suka b'ace. Ganin halinda yake ciki yasa Yasir ya fito ya zagayo tareda bud'e kofan wajan Driver

"Fito sai nai driving"

Bah musu ya fito ya koma inda Yasir din yake suka nufi Gida..

Kwanaki nata tafiya tunanin Sulthana ya hana masroor sukuni, abin ya soma damun Mami da Daddy, daddy baida choice hakanan ya k'ara tura mutane dan neman labarin Sulthana anma bah wani bayani..

Mahnoor tayi kuka sosai jin labarin bacewan Sulthana saboda yanda take santa. Abin Masroor sai gaba yake hankalin Mami da daddy ya tashi sosai bama kamar Mami basatan wani abu ya faru da d'an nata..

Yau Sulthana na cikin farinciki saboda yau bestynta Ayoush zatazo, har Mamaki Fareed yake yanda yaga taketa b'are b'are. Girki kala kala ta hada don taran k'awar nata. Wuraren k'arfe hudu da rabi Sulthana na dak'i kan dadduma bayan ta idar da Sallah taji horn din mota, zumbur ta mik'e ta fito a guje. Fareed ta wuce dake falo zaune yana kallan news ta fita tsakar gidan, dai dai lokacinda Ayoush ta fito d'aga motansu ta fara knocking gate din gidan..

Sulthana na bud'ewa suka rungume juna suna dariya, Ayoush ce ta fara cewa

"I missed uh besty"

Dariya Sulthana tayi tace

"I miss uh 2"

Hannun Ayoush ta kama suka shiga cikin gidan, a falo suka samu Fareed yana k'allo Ayoush tad'an rusunna ta gaidashi ya amsa fuska a sake Sannan suka shiga dakin Sulthana. Ciye ciye sukai kala kala, Sannan Suk'a barke da hira.. Ayoush ta d'ade a gidansu Sulthana, sunyi exchanging phone number Ayoush ta tafi cikeda kewan k'awar nata da kuma mamakin ganin bah kowa a gidan sai Fareed da Sulthana..


A kauye kuwa ciwon Mallan neh ya tashi gadan gadan, Hafsatu ta fito a guje ta nufi gidan Mallan sani aminin Baffa tana kuka sosai. A tsakar gida ta sameshi yana cin abincin rana, ta k'arasa inda yake zaune ta tsugunna tana sheshekan kuka

"Baba dan Allah kazo ciwon Baffa neh ya tashi"

Maman sadiya dake gefe ta tab'e baki tareda kauda kai dan ita ta tsani Baffa saboda wulakancin da yayima Sulthana. Rufe abincin Baba yayi ya mik'e ya wankr hannu yana k'okarin sa takalmi

Mama tace

"Ina zaka Mallan baka gama cin abinci bah?"

Yad'an waigo yana cewa

"Barinje na gani yanzu zan dawo"

Batace komai bah anma ranta a b'ace yake, tare suka fito da Hafsatu tana tafe yana binta a baya har gidan...

Ummy Abduol✍🏻

πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
          πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
         *SULTHANA*
         πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

By *Ummy Abduol*


    *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION*

     

         *Page 176 to 180*

           
            Na sadaukar da wannan page ga parrots din Deejatou novels grp *Deejatou, Fateema Ashemi, Meela adeel, Nafeesah Hasheer n Zee naseer*

Batace komai bah anma ranta a b'ace yake, tare suka fito da Hafsatu tana tafe yana binta a baya har gidan. Ameenatu ce a tsakar gidan tsugunne tanata kuka ganin Mallan sani yasa ta mik'e dasauri ta k'araso wajanshi tana nunamai d'akin da Baffa ke ciki. Dakin ya shiga ya tarar dashi kwance yana tari sosai idanunshi sun kakkafe, gefenshi Mamace itama kukan take..

Addu'a mallan sani ya soma tofama Baffa shima hankalinshi tashe. Ameenatu da Hafsatu na tsaye daga bak'in kofan cirko cirko suna hawaye sukaji Sallama a k'ofar gida, hafsatu ce ta fita. Wani mutumi ta gani tsaye sanye da Bak'ar jallabiya yana rik'e da qurani a hannunshi na dama, dayan hannun kuma ya rataya jakar fata..

Gaidashi tayi ya amsa yana cewa

"Naji labarin tashin lafiyan Mai gidan nan shine nazo na gwada sa'ata da wani magani ko Allah zaisa a dace"

Shigo kawai tace mai tamai jagora har cikin d'akin, har yanzu Tarin yake idanunshi a kakkafe. Zabura Mutumin yayi yana k'allan Baffa da mamaki, jikinshi ne yayi sanyi ya k'alli Mama yace wannan bah komai baneh face jinnu kuma insha Allahu zai samu lapia..

Mallan sani ya k'alla yace

"Ka rike min shi namai karatu insha Allahu za'a dace"

Rik'eshi Mallan sani yayi shi kuma mutumin ya soma karatu, nan da nan Mallan jamilu ya soma ihu tana bank'are bank'are tareda buge buge, Mama ita ta rik'eshi ana cigaba da mai karatun. Ganin su biyu bazasu iyaba yasa Mama ta kwalama su Ameenatu kira, duk suka taru suka rik'eshi Mutumin na cigaba da karatu..

Chan Mallan ya soma magana cikin wata murya da batasa bah

"Kayi hakuri karka konamu, zamu fita daga jikinshi"

Mutum ya tsagaita yace

"Meyasa kuka shiga jikin bawan Allahn nan kuna Azabtar dashi"

Wata murya ce ta soma magana tana cewa

"Mutumin nan bah Allah a ranshi, yana wulakanta ma d'an sarkin mu wacce yakeso shine mukazo mud'au fansa shima ya d'andana"

Mutumin yace

"Wacecce wace d'an sarkinki keso"

Wata muryan tace

"Sarauniya Sulthana"

Duka y'an dakin suk'a kwalalo ido suna kallan juna. Cigaba da magana sukai

"Kayi hakuri karka k'onamu zamu fita"

Mallamin yace

"Ku fita daga jikinshi kuma ta hanci nakeso ku fita. Karku k'ara dawowa idan har kuka dawo saina k'onaku"

Yana gama fadi Baffa yayi Atishawa sau uku sannan ya sulalle Barci mai nauyi ya daukeshi harda munshari. Mallamin ya share zufan daya k'aryo mai yace

"Alhamdulillah sun fita yanzu zan baku magunguna da hayaki da za'a rinka mai da kuma wasu Adduo'i"

Godiya su Mama suka hau mai baice komai bah ya bud'e jakar fatanshi ya ciro wasu magunguna ya mik'ama Mama tareda fada mata duk yanda ake anfani dasu sannan ya mik'a mata wata takarda wacce take kunshe da Adduo'i..

Godiya sukamai sosai baice komai bah ya mik'e hawaye suka gangaro mai a fuska. Mallan sani ya k'alleshi da Mamaki

"Lapia mallan meke faruwa?"

Hawayen idonshi ya share yace

"Idan yaji sauk'i inasan Magana dashi, akwai wani magana mai mahinmanci danakeso mu tattauna"

K'allan kallo suka hau yi yan dakin, mallamin ya musu Sallama ya bar gidan yana cigaba da hawaye...

Saura sati biyu su Sulthana su koma makaranta su shiga Ss1, yau Tana falo zaune tana k'allo lokacin Fareed na Asibiti. Masroor ne ya fado mata a rai ta runtse ido ta bud'e hawaye suka gangaro mata muryanta na rawa tace

"I miss uh ya Masroor"

Wayanta ne ya soma ringing ko ba'a fada mataba tasan Besty ce ta d'auka da fara'a tace

"Besty ya dai yau saura two weeks mu koma skul muma mu zama daga cikin seniors din nan"

D'an dariya Ayoush tai

"Gaskiya fah, kinsan meyasa na kiraki?"

Kai Sulthana ta girgiza sannan tace

"Aa"

Ayoush ta cigaba da magana tana cewa

"Inaso ne ki rakani muje wajan wata friend dita"

D'an jim Sulthana tai sannan tace

"Saidai ki tambayi ya Fareed anjima idan ya dawo i will flash uh sai ki kira na baki shi"

Ayoush cikeda jin dadi tace

"Ai indai ya Fareed ne banida matsala dashi"

Hira sukai k'adan daga bisani sukai Sallama. Fareed bai dawo gidan bah sai wuraren k'arfe tara na dare dan saida ya biya ya gaida Masroor dan bashi da lapia sosai...

A falo ya tarar da ita ta cika tayi fam. Yana k'allanta ya fashe da dariya hakan yasa ta k'ara kullewa ta fashe da kuka ta mik'e ta shiga daki tana cigaba da kukan, mik'ewa yayi yabi bayanta zuwa dakin, zaune ya sameta kan gado tana sheshekan kuka. Zama yayi kusada ita ya kamo hannunta ya hada da nashi cikin muryanshi mai sanyi yace

"Queen kin cika rigima, me kuma ya faru?"

Turo baki tayi ta shagwabe fuska tace

"Bah kai baneh ka fita tun safe sai yanzu ka dawo bah kuma ka barni inata jin tsoro"

Murmushi yayi har saida fararren haqoranshi suka fito yace

"I'm sorry swthrt kiyi hakuri patients ne sukamin yawa kuma na biya na gaida wani friend dina neh bashida lapia."

Gabanta ne ya fadi tad'an dago tace

"Allah ya bashi lapia"

Ameen yace sannan ya mike yana cewa

"Kin hakura?"

Kai ta gyada tana murmushin yak'e dan tunda yace abokinshi bashida lapia taji jikinta yayi sanyi ga kuma faduwar da gabanta yakeyi..

Cikinshi ya shafa yace

"I'm hungry"

Kan tai magana wayanta yad'au ringing, batareda bata lokaci bah ta d'auka ta kara a kunne sannan ta mik'a mai tace

"Besty ce zatama magana"

Amsa yayi ita kuma ta fice daga dakin a sanyaye. Tana cikin zubamai abincin ya k'araso ya zauna kan dinning din yana k'allanta

"Wato abinda kuka shirya knan koh?"

Turo baki tayo ta kauda kai. Ajiyan xuciya ya sauke yace

"Shiknan Allah ya kaimu goben Lapia, n na fada mata karku dad'e"

Murmushi tamai tareda godiya ta mik'a mai abincinshi suka cigaba da hira..


Washe gari wuraren k'arfe sha biyu na rana Sulthana ta gama shirinta tsaf, yau batasan meyasa bah bugun zuciyarta yafi na jiya. Falo ta zauna tana jiran wayan besty, batafi minti biyar da zama bah kiran besty ya shigo wayan. Ta mik'e dasauri ta rufe gidan ta fito waje, drivern ta gaishar sannan ta shiga motan suka bar kofar gidan

Sunyi nisa Ayoush ta juyo ta kalli Sulthana tana murmushi

"Kin t'aba shiga government house?"

Kai Sulthana ta girgiza, Ayoush tace

"Chan zamu"

Zaro ido Sulthana tai da mamaki

"Wah kike dashi a government house? Tho ai ma baza'a barmu mu shiga bah"

D'an dariya Ayoush tayi k'asa k'asa tace

"Bakiga motan da muke ciki bah? Na government neh so bah wani bincike zamu shiga, tho bakima sani bah y'ar governor din ce k'awata tare mukai school. Kuma Maminta k'awar mum dita neh"

Gyada kai Sulthana take da mamaki, dai dai lokacin da suk'a karaso gidan gwamnatin. Booth dinsu aka duba sannan aka bari suka shiga, tafiya sukayi mai nisa gada gate din gidan. Sulthana ko sai raba idanu take tana k'allan cikin gidan cikeda sha'awa, wani dad'i ke ratsa ta yau gata a gidan gwamna. A d'ayan bangaren bugun zuciyarta ne ya tsananta...

A bakin wani d'ank'areren gini sukai parking, Ayoush ta bud'e marfin kofan motan ta fito, itama Sulthana ta fito tana cigaba da k'arema Gidan kallo. Hannunta Ayoush ta rik'e tana mata magana a hankali

"Ki daina k'alle kallen nan kada a raina mu"

Nan da nan ko Sulthana ta d'aure, Ayoush taja hannunta suk'a nufi wani k'ofa dake gefensu. Bodyguards neh a wajan murd'adu bak'ake, hannu Ayoush tasa a jaka ta ciro wani i.d ta nuna musu, a take suka bud'e mata kofa taja hannun Sulthana da jikinta keta rawa ganin bodyguards din..

Tangamemen Falo neh mai cik'e da kayan Alatu, wata maid ce ta fito dasauri tana musu Sannu da zuwa tareda tambayanta wanda tazo gani. Noor tace atakaice, maid din tadau wayan dake falon ta soma kira, saida ta gama Sannan ta k'allesu tace

"Bata nan taje Shopping"

Ayoush ta shafa goshinta

"Oush!"

Ta k'alli sulthana wacce ta shagala da k'allan Hadad'en Falon tace

"Gashi banida numbernta I loose her contact"

Sai a sannan Sulthana ta k'alleta tace

"Mud'an jirata idan bata dawo bah sai mu tafi"

Maid din najin haka tace

"Uh can come in"

Tafe take suna binta a baya har zuwa wani had'adden falo mai kyawun gaske. Sakin Baki Sulthana tai tana k'allan Falon, Ayoush ta zungureta tana kyafta mata ido. Nan da nan saita kanta...

Waya Ayoush ta d'auka ta soma kiran mum dinta tana d'auka tace

"Mum Noor batanan wai taje Shopping, kuma kinga banga Mami bah. D'an Allah kid'an kirata a waya dan ni banasan rainin wayan Maids din nan"

Tana gama wayan ta kashe ta kalli Sulthana fuska bah Annuri,

"Zakisa a raina mu wallahi, sai kalle kalle kikeyi"

Murmushi Sulthana tai ta duk'ar da kanta k'asa. Wata Maid ce ta shigo tace

"Follow me"

A tare suk'a mik'e suna biye da ita har zuwa wani falon, shima falon ya tsaru sosai har yafi sauran da suka baro. Wuri maid din ta nuna musu suka zazzauna, chan sai ga wata ta kawo musu kayan motsa baki ta fita..

Sunkai minti sha biyar a falon a zaune sai ga Mami ta shigo falon da sallama sanye cikin kaya na Alfarma, Gaban Sulthana ya yanke ya fadi ta k'asa dagowa ta kalli Mami. Ayoush tad'an rusunna ta gaida Mami, Itama Sulthana ta Rusunna kanta a k'asa ta gaidata. Amsawa Mami tai Fuska a sake tareda tambayanta Mutan gidan, Ayoush ta amsa da Ameen..

Tunda Mami ta shiga Hankalinta na kan Sulthana haka kawai yarinyan taji ta burgeta, ta kalli Ayoush tace

"Sai kuma gashi bata nan taje Shopping kuma kindai san Halinta idan ta fita"

Murmushi Ayoush tai

"Eh haka aka fada mana, tafiya zamuyi yanzu bt zamu dawo wata rana. Muma zauje wani guri neh"

Mami ta gyada kai tace

"Ai gwara ke akanta, ita yaushe rabonda naga ta shirya da sunan zuwa gidanku"

Murmushi kawai Ayoush tayi batace komai bah. Mami ta k'alli Sulthana tace

"Wai k'awarki bata magana neh"

Ayoush ta kalli Sulthana tana Murmushi

"Hmm Queen ai haka take"

Ayoush ta mik'e tace

"Mami zamu tafi"

Sulthana itama ta mik'e har lokacin kanta a k'asa,

"Tun yanzu?" cewar Mami

Dariya Ayoushi tayi

"Ai zamu dawo"

Mami ta mik'e tana cewa

"Tho ina zuwa"

Chan sai gata dauk'e da brown envelops guda biyu, Ayoush ta mikamawa tace

"Gashi keda k'awarki tunda tak'i sakin jiki"

Itadai Sulthana nai Murmushin dole take kanta a kasa. Godiya Ayoush taima Mami itama Sulthana murya a sanyaye tace

"Mun gode"

Mami tai Murmushi tace

"Bbu komai"

Sallama Sukai mata Suka fito suka shiga motarsu suka d'au hanyan Fita..

Suna K'okarin fita Motarsu Mahnoor ta shigo gidan, sam su Ayoush bata lura da suwa ke cikin motan bah. Itama Mahnoor din k'anta na k'asa tana chating a wayanta. Kamar ance ta d'ago ta sauke idanunta kan Motarsu Ayoush, Zaro ido tayi  bakinta na rawa tana nuna motarsu Ayoush bakinta na k'okarin furta Wani abu..

Ummy Abduol✍🏻

πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
          πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
         *SULTHANA*
         πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

By *Ummy Abduol*


    *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION*


         *Page 181 to 185*

      _na Yank'e labarin neh saboda banasan nakai har bayan Sallah ban gama bah Ina fata zakumin afuwa. Fans naga sakonin ku dayawa ina godiya Sosai Allah ya barmu tare_


Kamar ance ta d'ago ta sauke idonta kan motarsu Ayoush, zaro ido tayi bakinta na rawa tana nuna motarsu Ayoush bakinta na k'okarin Furta

"Sul..Sulthana"

Kamin ta ankara motarsu Ayoush har yabar cikin gidan a guje..


Alhamdulillahi Baffa ya samu sauk'i sosai Mama dasu Ameenatu sai murna suke. Yau yana kishingide akan tabarma a tsakar gida Mama na mishi fiffita, duk abinda ya faru ta kwashe ta sanar ma Mallan ga mamakinta sai gani tai ya tab'e baki baice komai bah..

Sallama akai a kofar gidan, Mama ta kwallama Ameenatu kira taje chan sai gata itada wannan Mallamin. Tun kafin su k'araso Mama tace

"Ga Mallamin nan"

Tashi Mallan Yayi ya zauna duk da bai jin k'arfi, wuri Mallamin ya samu ya zauna suka gaisa da Baffa da Mama. Godiya Baffa ya soma mai yayi saurin dakatar dashi da hannu, daidai lokacin su Hafsatu suka zo suka zauna tareda gaidashi. Ya amsa fuskanshi bah walwala, Magana ya soma cikin rawar murya

"Dama nace idan kaji sauk'i zan dawo dan akwai wata muhimmiyar Magana danakeso mu tattauna dakai"

Baffa ya gyara zama su Ameenatu suna k'okarin tashi Mallamin ya dakatar dasu

"Aa ku zauna dan ku zama sheda"

Komawa sukai suka zauna, mallamin ya soma magana yana hawaye

"Ni d'an garin zamfara neh, iyayena duk yan chan neh. Mahaifina Mallami ne sananne a chan garin mu, Shekara goma sha biyar da suk'a wuce na kasance banajin magana duk abinda iyayena suka umarceni da nayi bana yi. Banida abokanai sai y'an isa marasa ji yan uwana"

Tsagaitawa yayi ya share hawayen fuskanshi Sannan ya cigaba

"Duk wani kayan maye da aka sani ina sha, muna farauta da abokanaina sannan mu kashe mutum a wajanmu bah wani abu baneh. Sacce sacce da fashi duk babu wanda bama yi munyi k'aurin suna sosai a garinmu. A haka har muka fara bin gari gari muna shiga gidajen mutane muna fashi"

Ya d'ago ya kalli Baffa wanda shima Mallamin yake Kallo ya cigaba da cewa

"Akwai wata rana da mukazo garin kano inda mukai wata mummunar fashi har muka kashe wani babban d'an siyasa a kofar wannan kauyen"

Zabura Baffa yayi ya gyara zama

"Dama ku kuka kashe Alhaji tijjani isiyaku?"

Kai Mallamin ya gyada kanshi a k'asa ya cigaba da cewa

"Bayan munyi fashin da kwana biyu rannan ina kewaya wannan kauyen naganka kaida wad'ansu mutane kuna cinikin gona. Tsayawa nesa daku har kuka gama cinikin aka damk'a maka kudinka a hannu, binka na somayi har xuwa gidan danaga ka shiga Sannan na juya na tafi. A ranar da daddare na  kawoma gidanka Samamme"

Duk da rashin karfin da Baffa yake dashi baisan lokacin daya mik'e tsaye bah tana nuna mallamin bakinshi na rawa

"Da..Dama kaine ka shiga gidana? Ka rusamin farincikin dake gidana??"

Kuka Mallamin ya fashe dashi yanaba Baffa yakuri, Mama tace

"Tabbas na tuna lokacin nan, a Gidan marigayiya Mahaifiyar Sulthana koh"

Girgixa kai Mallamin yayi yana cigaba da hawaye

"Bansani bah, nadai san ita wacchan kamar buxuwace"

Baffa ya rintse ido ya nunashi da Yatsa shima hawaye na fita a idonshi yace

"Kun ganshi nan shine Mahaifin Sulthana, a daren ranar aka samu cikinta"

Ameenatu ta mik'e dasauri ta dafe k'irji

"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun"

Mallamin ya d'ago da Mamaki yana k'allan Baffa

"Ban ganeh meh kake nufi bah"

Baffa ya share hawayen idonshi yace

"Bayan ka kwanta da matata ta samu ciki kuma harta haihu yanz..."

Katseshi Mallamin yayi da cewa

"Wallahi tallahi ko kurani zaka bani na dafa na rantse zan dafa ban k'wanta da Matarka bah. Nadaiyi niyya ta hadani da Allah na fasa"

Baffa ya zaro ido yace

"meh kake nufi"

"Wallahi ba abinda ya shiga tsakanina da matarka wallahi"

Kuka sosai Baffa ya fashe dashi harda d'aura hannunshi aka, Mama tace

"Mallan kamana bayani yanda zamu fahimta"

Zama baffa yayi yana cigaba da kuka ya fara magana

"Kamar yanda ya fada shekaru baya da suka wuce wani barawo ya taba shigowa gidan tsohuwar matata mahaifiyar sulthana knan, ya shigo da k'atuwar bindiga ya bukaci mu bashi kudin dana saida gona. Dama na bata ta ajemin dan haka nace taje ta d'auko mai, tasata yayi a gaba har cikin d'akin barcin mu ni kuma ina falo ya kulleni harda bakina gashi ya kulle kofan ba halin dazan fita nai ihu azo a taimakemu"

Matse kwalla Baffa yayi ya cigaba dacewa

"Ban ankara bah naji maganan d'an fashin nan nacewa riba biyu yakeso ya samu ya amsa kudin ya kuma kwanta da Matata. Bansan sanda na fashe da kuka bah ina nan zaune a falon, ihunta naji tana bashi hakuri shi kuma yana dariya. Chan sai gashi da kudin a leda ya bud'e kofa ya fita, ita kuma tazo ta kwanceni tana kuka sosai"

"Bayan sati biyu da Faruwan hakan tazomin da labarin tanada ciki, tun a lokacin na fara hantaranta dan nasan bah cikina baneh"

Baffa ya fashe da kuka ya nuna Mallamin yace

"Ka cuceni, Allah ya isa tsakanina dakai."

 Mama ta matso tana kuka itama

"Kai hakuri Mallan shima ai gafaranka yazo nema"

Kuka baffa yake wuiwui

"Bah irin rantsuwar da batayi bah akan bah abinda ya shiga tsakaninku anma ban yarda bah. Ashe dagaske ne"

Ya k'ara rushewa da kuka

"Ki yafeni Rabiatu, ban miki aldarci bah naci amanar dana dauka naki. Ki yafeni"

Kuka yake sosai yana cigaba da cewa

"Kah cuceni ka rusamin farinciki, yanzu dama Sulthana y'ata ce naketa mata wannan kiyaiyar"

Zumbur ya mik'e yana k'okarin sa takalmin shi. Mama itama ta mik'e

"Ina zaka Mallan?"

Yana kuka yana cewa

"Zanje neman Sulthana ta dawo gida, ta yafeni rashin sani neh"

Mama ta rik'eshi

"Kayi hakuri Mallan Kaga bakajin dadi, kuma Sulthana shekara d'aya fa knan da rabi rabonmu da ita. Bbu wanda yasan inda take"

Dakyar ta Lallabashi ya zauna, kowa a wajan kuka kawai yake bama kamar Baffa. Yana kuka hannunshi akai

"Allah ka yafeni, Rabi ki yafeni. Sulthana ki yafeni"

Sun d'ade a haka bah wanda yake rarrashin wani har na wasu lokuta sanna Mallamin yace

"Duk inda y'arka take indai tana raye tana rayuwa ne tareda Aljani, ma'ana akwai aljani a jikinta"

Baffa baice komai bah ya mik'e ya shiga dakinshi yana cigaba da kuka. Dakyar su Ameenatu sukaba Mallamin Hakuri ya tafi...


Mami na barin Falon d'akin da Masroor ke kwance ta nufa. Ga mamakinta sai ganinshi tayi tsaye yanasa Burtin din shirt dinshi da Alama wanka yayi

Kallo d'aya zakamai kaga ramar dayayi. Dasauri ta k'araso wajan baki bud'e

"Son idona gizo yakemin ko gaske meh? Kaine a tsaye a nan"

Juyowa yayi ya rik'e kafadanta yana Murmushi

"Nine Mami, am now fine"

Mahnoor ce ta shigo dakin a rud'e tana haki, hannun Masroor ta rik'e tana nunamai Kofar fita. Sakin Hannunta yayi yana k'allanta

"Menene? Waya biyoki?"

Haki take tayi saida yad'an tsagaita tace

"Mami wallahi yanzu naga Sulthana a wata mota sun fita d'aga nan gidan kuma a motar gidansu Aisha neh"

Tun kanta k'arasa maganan Masroor ya nufi kofar fita, Mami ta rik'eshi tana girgixa mai kai

"Ina zaka kaida Bakada lapia"

Idanunshi cik'e da kwalla yana k'okarin kwace kanshi daga rikon da Mami tamai

"Mami ki kyalleni naje dan Allah I want to see her"

Kallan Mahnoor tayi fuskanta a had'e

"how sure are you itace??"

Nan Mahnoor ta fara inda inda. Masroor sai kokarin kwace Hannunshi yake ya kasa saboda jikinshi daba k'arfi. Hannunshi taja ta zaunar dashi kan gado

"Kah kwantar da Hankalinka indai itace komai yazo k'arshe tunda tare suke da Aisha"

Baice komai bah k'anshi na k'asa baisan Mami taga hawayen dake zuba a idonshi taja hannun Mahnoor suka bar dakin..

Ummy Abduol✍🏻

πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
          πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
           *SULTHANA*
           πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

By *Ummy Abduol*

 
     DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION

           *Page 186 to 190*

Baice komai bah k'anshi na k'asa baisan Mami taga hawayen dake zuba a idonshi, taja hannun Mahnoor suka bar dakin..

Sun danyi nisa da government house, Sulthana ta rik'e kanta tana k'allan Aisha

"Ayoush ku kaini gida kawai kaina wanni irin ciwo yake"

Ayoush tamatso tareda taba goshinta

"Kuma jikinki bah zafi, kanne kawai ke ciwo?"

Kai kawai Sulthana ta gyada batace Komai bah. Gida suka kaita lokacin Fareed baya nan sukai Sallama ta tafi. Falo ta shiga ta zauna kanta na mata ciwo sosai, rintse ido tayi tareda tafe kan tun daga nan bata k'ara sanin inda kanta yake bah...


Ganin halinda ake ciki yasa Mami ta d'au waya ta soma neman layin Abba, lokacin yana tsaka da aiki ya daga tareda fada mata aiki yake. Saurin katseshi tai ta fadamai dalilin bugowanta daneman izinin fita. Bai musa bah ya amince ta kashe kiran..

Aminiyarta ta kira wato matar duty governor suka nufi gidansu Ayoush tareda rakiyan bodyguards dinsu. Masroor na ganin sun fita ya dau makulin motanshi ya mara musu baya..

Tarba sosai Mum din ayoosh tai musu, saida Suka natsa sannan suka sanar da ita dalilin zuwansu. Batareda batalokaci bah tayo kiran Aisha, tafito ta tsugunna har k'asa ta gaidasu. Mami ce tafara magana tana cewa

"Aisha menene Sunan Yarinyan da kukazo tare"

D'an dagowa Aishan tai sannan tace

"Queen!"

Mami ta girgiza kai tana y'ar murmushi tace

"Sunanta na gaskiya nake magana"

Batareda bata lokaci bah tace

"Sulthana!"

Masroor dake mak'e jikin labule ya fito dasauri ya k'araso inda Aisha ke tsugunne shima ya tsugunna

"Aisha dan Allah aina take?? Fadamin pls"

Kowa dake falon mamakin ganin masroor yayi bama kaman Mami. Aisha ta kalleshi tareda sauke ajiyan zuciya

"Classmate dita ce, a nan kano suke itada brothern tah"

Saurin girgiza kai Mami tayi tana cewa

"Wannan bah Sulthanan ka bace Masroor, kaji wannan fah y'ar kano ce kuma tanada yaya"


Hannun Aisha ya kama idanunshi cikeda da kwalla

"Pls ki kaini wajanta, ni nasan Sulthana na neh."

Kai ta gyada ta mik'e tadauko gyalenta ta fito, dukansu suka dunguma zuwa gidan..


Shigowan Fareed kenan cikin gidan tun daga haraban gidan yakejin k'aran fashewan abubuwa, dagudu ya k'arasa cikin falon. Bin falon ya somayi da kallo komai a hargitse, center table a fashe abubuwa duk a fashe. Jin wani k'aran a dakinshi yasa ya nufi dakin dasauri, ganin Sulthana yayi tsaye duk gashin kanta a barbaje hannayenta na jini sai fashe fashe take tana ihu kamar bah itaba.

Jikinshi ne ya soma rawa ya k'arasa kusada ita ta daga sauran mirrown dake hannunta za wurga mai, dasauri yaja da baya mirrown ya fadi gefenshi ya fashe...

Ihu ta saki mai k'ara ta nufeshi dagudu ta rikeshi tana dukanshi tako ina. Kallanta kawai Fareed keyi jikinshi a mace hawaye na gangara daga idonshi, dakyar ya tattaro karfinshi ya rik'eta murya na rawa yace

"Queen meya sameki? Why all this"

Dukanshi kawai take a k'irji da iya karfinta. Janyota yayi dakyar zuwa falo ya zaunar da ita k'an kujera sai kokarin tashi take tana ihu da karfi..

Motocin su Mami neh suka tsaya a kofar gidan, umman Fareed ta k'alli Aisha da Mamaki

"Nan neh gidansu Yarinyar?"

Kai Aisha ta gyada sannan tace

"Nan neh nasan tanama ciki"

Da mamaki umman Fareed ta k'alli Mami tana cewa

"Nan fah gidan Fareed neh"

Dasauri Aisha tace

"Eh sunan yayanta knan"


Umman fareed ta kwalalo ido ta fito daga motan dasauri, tuni Masroor ya fito daga tashi motar yana jiran fitowansu dan ta nunamai gidan. Aisha ce ta musu jagora zuwa bakin kofar gate din. Kofar a bud'e take dan haka suka shiga gidan kai tsaye..

Ihun da sukaji neh yasa suka tsaya chak, Masroor ya saki kuka mai sauti dagudu ya shiga falon dake gidan. Sulthanan shi ya gani rungume jikin Fareed tana kuka da ihu tana kokarin ture Fareed daga jikinta

Tsugunawa Masroor yayi ya runtse idonshi yana girgiza kai bakinshi na furta

"Noo! Noo!! Sulthana"

Juyowa Fareed yayi firgice jin murya a bayanshi, dai dai nan su Mami suka shigo falon kowa na kallansu da Mamaki. Umman Fareed ta k'araso ranta b'ace

"Fareed meh nake gani haka? Ka aje yarinya a gidanka"

Baice komai bah har yanzu kuma yana rik'e da Sulthana daketa ihu tana dukanshi, kokarinta kawai ya saketa. Hawayen dake mak'alle a idanunshi suka sauka muryanshi na Rawa yace

"Umma I'm very sorry, its not what uh think. Yanzu abinda yafi shine mukaita asibiti"

Kasa cewa komai Mami tayi ta k'arasa inda Masroor ke tsugunne yana kuka kamar yaro. D'agoshi tayi tsaye tasa hannayenta tana sharemai hawaye

"Stop crying son, karka jama kanka wani ciwo"

Muryan Fareed yaji yana cewa

"Friend help me mu kamata mu kaita Asibiti"

K'ara k'allan Sulthana yayi yaga yanda take ihu da bige bige, ya rintse ido ya bude. Daky'ar suka kamata sukasa a mota suka nufo asibiti dukansu..

batareda wani bata lokaci bah aka amsheta ganin manyan mutane kuma tare da likita. Dr Sa'ood da wasu likitoci ke kanta, aluran barci sukai mata sannan suka hau mata gwaje gwaje. Sun d'au lokaci suna dubata, Fareed na tsaye har lokacin hawaye yake ya kasayin komai..

Saida suka natsa sannan Sa'ood ya kira su Mami Office dinshi. Bayan sun zauna ya soma magana

"Ur excellency duk binciken daya kamata muyi duk munyi anma bamuga komai bah. Ni sai nake gani kamar Cutar bata asibiti baneh inaga..
"

Saurin katseshi Umman Fareed tai da cewa

"Wanne irin magana kakeyi Sa'ood, yarinyan da kowa yagani tana abu kamar mahaukaciya zakace bana asibiti baneh"

Ajiyan zuciya ya sauke sannan ya cigaba da cewa

"Umma! Bata lokaci kawai za'ayi, a shawarce shine a nemo malami dazai mata ruk'iya"

D'an Murmushi Mami tai ta mik'e

"Mun gode doctor insha Allahu hakan za'ayi"

Office din suka fito a bakin kofa sukaga Masroor tsaye kanshi a k'asa. Hannunshi Mami ta kama ya d'ago jajayen idanunshi yana k'allanta

"Son muje gida kasha magani"

Girgiza mata kai yayi dasauri

"No Mami zan zauna tareda Sulthana"

Rungumoshi jikinta tayi tana shafa bayanshi

"I know how uh feel Son, be Strong everything wil be fine. Baga Aisha bah she wil take care of her"

Dakyar ta lallabashi suka koma gida. Sai dare suka natsa Mami ta samu Abba a dakinshi ta sanar dashi duk abinda ke faruwa. Ya cika da mamaki sosai, shi kanshi yanajin son yarinyan musamman yanda yaji batada gata. Washe gari da safe shima mutanenshi sukaje gaisheta, Maman Aisha suka samu a wurinta da Fareed..

Sun gaisheta tareda mata addua coz har lokacin bata farka bah sannan suka tafi..

K'arfe 10 na safe a Asibiti tayi mah Masroor shida Yasir, direct dakin suka shiga kai tsaye. Aisha suka samu da Fareed a dakin. Masroor baice komai bah ya nufi bakin gadon yana K'allan Sulthana tareda tambayan Aisha jikinta. Ganin Masroor baimai Magana bah yasa ya mik'a mai hannu yace

"Morning Friend"

juyowa Masroor yayi ya galla mai harara ya juya ya maida Fuskanshi ga Sulthana. Daidai lokacin idanunta suka fara rawa Masroor ya kara matsowa kusada gadon yayi kneeldown yana k'allanta da hawaye cike idonshi

"Beauty open ur eyes its me Masroor"

Bud'e idonta tai dasauri tareda mik'ewa zaune ta k'uramai ido idanunta taf da hawaye. Ganin tana neman kuka yasa ya girgiza mata kai hawaye na gangara a idonshi

"Karkiyi kuka Beauty, nine dai Masroor naki"

hawayen daya gangaro mata ta share ta t'aba hannunshi taji tabbas shine, k'ara fashewa da kuka tayi ta rungumeshi. Shima kukan yake a hankali yana shafa suman kanta..

Duk yan dakin yan K'allo suka koma, Fareed ko gabanshi ne keta faduwa zuciyarshi ta shiga masa zafi ganin yana kokarin fashewa da kuka yasa yabar dakin dasauri. Direct Office dinshi ya nufa ya zauna akan kujeranshi ya daura kai kan table ya fashe da kuka mai tsuma zuciya. Kuka yake sosai anma bah mai Lallashin shi

A haka Sa'ood ya shigo Office din ya sameshi, Zama yayi yana kallan Fareed batare dayace komai bah. Saida ya bari yayi kukan mai isarsa sannan ya mik'e ya dawo kusa dashi tareda dafashi..

"Na barka kai kukan neh saboda ka samu relief, tel me whats wrong"

Idanun Fareed taf da hawaye ya d'ago yace

"Sa'ood na rasa Sulthana, na rasata."

Dasauri Sa'ood ya zagayo ya tsugunna yana facing dinshi dakyau

"Bangane kah rasa Sulthana bah Fareed"

Runtse ido Fareed yayi hawayen da suka makale suka zubo ya d'ago yana k'allan Sa'ood wanda shima shi yake kallo

"Friend dina Masroor yana san Sulthana, kuma kasan yanda muke dashi da kuma yanda iyayenmu suke."

Shiru yayi yana share kwallan dake idanunshi. Sa'ood ya nisa yace

"And so what Fareed, kanasan Sulthana?"

Dagowa yayi dasauri yana k'allan Sa'ood shekeke

"I so much love her, I cnt do witout her. And banasan abinda zai kawo matsala tsakanin wannan zumuncin dake tsakanin mu"

Sa'ood yaja dogon tsaki tareda mik'ewa

"Fareed fight and get wat uh want, karka kasa wannan a ranka. Kayi kokari ka yaki har kasamu abinda kakeso ka.."

Wayan Fareed dake ringing neh ya katse shi, ganin mai kiran yasa ya d'auka tareda Sallama Sannan ya mik'e yace

"Ganinan zuwa"

K'allan Sa'ood yayi

"Zanje gida Umma na nemana"

Gyada kai kawai Sa'ood yayi sukai Sallama yabar office din.

Ummy Abduol✍🏻

πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
          πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
          *SULTHANA*
          πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

By *Ummy Abduol*


 DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION

      *Page 191 to 195*


Fita yayi daga Office din ya nufi motarshi dasauri direct gida yayi, saida ya shiga side dinshi dake gidan yayi wanka da Sallah sannan ya shiga side din Umma gabanshi na faduwa..

Zaune ya sameta itada bak'i, zama yayi kan Carpet suka gaisa da mutanen falon. Yana nan zaune har suka gama ta sallamesu Sannan yad'an duk'ar dakai murya na rawa yace

"Ina kwana Umma"

Shiru tayi tana kallanshi, jin shirun yayi yawa yasa yad'an dago suka hada ido yayi saurin maida kai kasa. Umma ta nisa ranta b'ace ta soma magana


"Fareed ina hankalinka yaje ina iliminka? Bantaba expecting haka daga gareka bah"

A hankali ya d'ago cikin sanyin murya yace

"Dan Allah Umma kiyi hakuri nasan nayi kuskure"

Ajiyan zuciya ta sauke

"Fareed kasan matsayinda mahaifinka yake kai yanzu, bai kamata haka na bullowa bah. Bakama gudun maganganun mutane kadauko yarinya ka ajeta a gidanka har na tsawan shekara"

Hawaye cike da idanunshi ya dago

"Umma kiyi hakuri d'an Allah wallahi it was'nt my fault, gani nai kamar bazaki yarda ta zauna dake bah. And yarinyan need help babanta ne ya koreta witout any serious reason"

Umma ta girgiza kai tana murmushin takaici

"Fareed uh are stil young, bazaka ganeh abinda nake nufi bah."

Baice komai bah kanshi a kasa. Nasiha Umma ta soma mai mai ratsa jiki, Sannan tace ya tashi yaje. Godiya yayi ya mik'e ya koma side dinshi jiki a sanyaye..


A asibiti kuwa ta dad'e a jikin Masroor tana kuka mai ban tausayi daga bisani ta janye jikinta daga nashi tana kallanshi

"Ya Masroor meyasa zaka tafi ka barni, meyasa kak'i yarda dani."

Hawayen idanunshi ya share

"Kiyi hakuri Beauty nasan nayi lefi i'm sorry"

Batace komai bah ta koma kan gadon ta kwanta ta juya mai baya. Hannunshi Yasir ya kama yajashi suka fita. Aisha ta matso kusada gadon tad'an taba ta tana cewa

"Sannu Queen ya jikin"

Tashi zaune tayi tana yatsine fuska

"Ayoush meya kawoni asibiti? Bah gida kuka kaini bah"

Murmushi Aisha ta mata

"Kin tuna kince gabanki na faduwa? To shine ya Fareed da kikayi barci ya kawoki asibiti"

Tana kokarin jeho mata wani tambayan tai saurin katseta da cewa

"Yauwa Queen inaso na tambayeki"

Gyada kai tayi tana kallanta, Aisha ta cigaba da cewa

"Aina kikasan Masroor, Sannan keh wacece coz ance ya Fareed bah brodanki baneh?"

Murmushin takaici tayi

"Zakisan duk abinda baki sani bah dnt worry, yanzu ina ya Fareed"

D'an jim tayi tace

"I donno myb yana office"

Batace komai bah ta koma ta kwanta zuciyanta a jagule..

Kwanan Sulthana biyu a asibiti, tun daga ranan da aka kwantar da ita bata k'ara ganin ya Fareed dinta bah. Masroor kuwa kullum yana tare da ita shida Aisha, haka Mahnoor tazo dubata itama. Sulthana tasha Mamaki sosai jin su y'ayan gwanma neh. Ranar da Dr Sa'ood yayi discharging dinta ta tareshi da tambayan ya Fareed baice mata komai bah yabar dakin..

K'allan Aisha tayi fuskanta bah walwala

"Aisha d'an Allah ki kaini Office din ya Fareed"

Nan da nan fara'ar dake fuskan Masroor takau ya hada girar sama data k'asa. Sulthana na ganin haka tasha jinin jikinta ta koma ta zauna. Waya ya dauka ya kira Mami ya sanar da ita sallamansu da akai, batareda bata lokaci bah tace ya d'aukota suzo gida. To yace ya kashe wayan ya kalleta fuska bah walwala

"Mami tace na daukoki muje gida"

Batace komai bah ta mik'e tadau gyalanta ta yafa Aisha ta soma hada musu kayansu. Ganin suna abu slow yasa yad'au wasu kayan ya fita yana cewa

"Ku sameni a mota"

Aisha ce ta amsa. Bayan fitanshi Sulthana ta kalli Aisha idanunta cike da hawaye

"Aisha ina Ya fareed? Meyasa yak'i zuwa inda nake? Duk wanda na tambaya shi sai yayi banza dani."

Aisha batace komai bah ta k'ama hannunta suka fita daga dakin, Office dinshi suka nufa a kofar office din Aisha ta tsaya itakuma ta tura kofar ta shiga jikinta na rawa

Zaune ta sameshi yayi tagumi ga tulin folders a gabanshi, jiki a sanyaye ta k'arasa kusadashi ta dafa kujeran dayake kai

"Ya Fareed! Ya Fareed!!"

Zabura yayi ya juyo a tsorace yana kallanta. Ta shagwabe fuska

"Ya Fareed inata nemanka shine kaki zuwa ka dubani koh bayan kuma kaine ka kawoni"

Kirkiro murmushi yayi

"I'm sorry Queen ayuka neh sukaimin yawa"

Dawowa tayi ta zauna kan kujerun dake Office din tace

"Ya Fareed meyasa zanje gidansu Ya Masroor? Bah gidanmu zamu koma bah"

Mik'ewa yayi dasauri yana kallanta

"Gidansu Masroor?" ya furta da Alamar Mamaki

Kai ta gyada tace

"Eh haka yace"

Kafin yayi Magana aka banko kofan Office din aka shigo, a tsorace Sulthana ta kalli kofan ganin Ya Masroor tsaye yana huci kaman zaki yasa jikinta ya soma rawa. Karasowa wayanta yayi rai bace yace

"Fita ki wuce mota ki jirani"

A guje tabar Office har tana kokarin faduwa
A harzuk'e Fareed yace

"What do you think you are doing Masroor? Na lura san Sulthana kake to ka sani bazaka taba cin nasara bah becoz sulthana tawa ce!"

Dariya Masroor ya fashe dashi yana numa Fareed da hannu

"Kai har kana tunanin zan iya tsayawa ina musayan yawo dakai? No! Coz nagaba yayi gaba na baya sai labari"

Bai jira mai Fareed din zaice bah yabar Office din tareda bugo kofa. A mota ya samu Sulthana zaune itada Aisha sai zazzare ido take. Baice komai bah ya tada motan yabar Asibitin a guje, bah Sulthana kawai bah Har Aisha saida ta tsorata da yanda yake tukin. Government house suka nufa kai tsaye suna shiga suka tarar da Mahnoor da Maids bakin kofan Side din Mami suna tsaye suna jiran k'arasowan su. Yana parking Mahnoor ta nufo motan a juye, Sulthana na fitowa ta rungumeta tana dariya. Mahnoor tace

"Uh welcome friend"

Dariya Sulthana kawai tai mata duk hankalinta nakan ya Masroor ganin yanda yawani d'aure fuska. Mahnoor ce tai musu jagora zuwa cikin gidan, wani hadad'en daki takai Sulthana tana cewa

"Sis wannan shine d'akinki inji Mami"

Bin dakin da kallo Sulthana tayi tana Murmushi, gyallenta ta aje kan katafaren gadon dakin ta hau juyi cikeda jin dad'i sannan ta juyo da fara'a sosai akan fuskanta ta rik'e hannun Mahnoor tace

"Kicema Mami nagode Sosai, I'm so greatful"

Itama murmushi Mahnoor din tayi, Aisha tace

"Dak'in yayi kyau sosai"

Ledojin Hannunta ta aje tana cewa

"Zanje gida"

A tare suka fito duk'asuka rakata,  Mahnoor tasa driver ya kaita gida sannan Mahnoor ta shiga nunama Sulthana Cikin gidan..

Sosai Sulthana taji dad'in kasancewa gidan, ko bakomai ta kafa tarihi ta zarce su Ya ameenatu dan ita yau gata a Cikin gidan gwamnati..

Basu samu had'uwa da Mami bah ranar dan batanan sai washe gari, Mahnoor ce keta d'ebe mata k'ewa. Da safe tare suk'a sauko da Sulthana Family dinning din dake gidan, Suma neh kawai Sulthana bataiba Ganin Mutumin datake Gani a tv yau a gabanta zahiri

Kanta a k'asa suka k'araso wajan Dinning din, Mami ce zaune da Abba sai Masroor dake gefe fuskannan nashi bah walwala. A hankali ta tsugunna har k'asa ta gaida Abba, cikeda kulawa ya amsa sannan ta gaida Mami itama ta amsa mata da Fara'a.

D'an dagowa tayi ta k'alli Masroor sannan tace

"Ina kwana ya Masroor"

Kamar bazai amsa bah chan kuma yace

"Lapia"

Bah Sulthana kadai bah har Mami da Abba sunyi Mamakin yanda ya amsa mata gaisuwan. Kujera Mahnoor taja mata ta zauna Sannan ta soma serving dinta.. Ganin tak'i sakin jiki taci abincin yasa Abba ya tashi yamusu sallama yabar Wajan..

Itama Mami ta mik'e tana cewa

"Ina zuwa"

Ganin haka yasa Masroor d'aukan plate dinda ke Gabanshi yabar wajan. Sai a sannan ta kalli Mahnoor idanunta taf da hawaye tace...


Ummy Abduol✍🏻Abduol✍🏻

πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
          πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
          *SULTHANA*
          πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

By *Ummy Abduol*


 DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION

              *Page 197*


Gudu yake sosai yabi ta bayan gidan inda zai sadashi da filin basket ball. Ganin tuk'in nashi bana hankali baneh yasa Sulthana k'ara fashewa da kuka

"Dan Allah ya Masroor kayi hakuri ka daina gudu"

Wani wawan burku yaja ya juyo yana k'allanta idanunshi a rune

"Sulthana bakya sona ko? Fareed kikeso?"

Batace komai bah k'anta a kasa, fita yayi daga motan ya jingina yasa hannayenshi a aljihu ranshi a b'ace. Tana ganin haka tafito jikinta na rawa ta tsugnna gabanshi kanta a k'asa

"Kayi hakuri ya Masroor, ya fareed na d'aukeshi yayana saboda shiya taimakeni. Ban tab'a sanshi bah kuma bai tab'a cemin yana sona bah"

D'agota yayo daga tsugunnen datake ya tallafo fuskanta suna kallan juna

"Ina Sanki Beauty, ina sanki sosai. Pls ki soni kar sanki yasa na shiga wani hali"

Rungumeshi tayi ta fashe da kuka, a hankali tace

"I love uh to ya Masroor"

D'agota yayi daga jikinshi ya kura mata manyan idanunshi da Mamaki

"What do uh just say"

D'an Murmushi tayi tasa hannu tana share hawayen fuskanta. Da lebbunanta ta furta

"I lav uh"

Tsalld yayi yace

"Woaw!"

Ta kyalkyace da dariya tana kallanshi. Motar Fareed neh tazo wucewa ganinsu awajan yasa yayi parking dan yau ji yake saidai duk abinda zai faru ya faru..

Parking yayi ya fito ya karaso inda suk'e tsaye, Masroor na ganinshi ya had'e rai ya juya ya kalli Sulthana yana cewa

"Shiga mota ki jirani"

Bah musu ta bud'e kofan tana kokarin shiga Fareed yayi maza ya k'ama hannunta, a tsorace ta juyo ta kalleshi. Masroor ya fizge hannunta daga nashi yana huci

"Fareed ka kiyayi kanka, meyasa kake kokarin shiga hurumin daba naka bah"

A hasale Fareed yace

"Hurumin daba nawaba ko hurumin daba naka bah"

Ya kalli Sulthana suka hada ido yace

"Tun ranar da Yayarki ta kawoki chemist din kauyenku Allah ya d'auramin Sanki. Nayita k'okarin in sanar dake ban samu daman hakan bah. Naje neman aurenki wajan Mallan anma yacemin an miki miji. Bayan kin dawo gurina inata kokarin na sanar dake abin yacitira"

Ya d'ago yana kallanta

"Ina matuk'ar sanki Sulthana. Na dad'e ina dakon soyaiyarki a zuciyana"

Fashewa tayi da kuka ta fadi a wurin zaune tana kuka sosai, harga Allah bata tab'a zatan Ya Fareed zai Furta Mata Kalmar so bah.
K'arasowa wajan Masroor yayi yana huci

"Fareed kana b'ata lokacin ka neh a banza, karka taba tunanin Sulthana a matsayin matarka. Na fada zan kuma k'ara fada Sulthana Tawa ce!"

Bai ankara bah yaci Fareed ya kai mai wani mugun naushi a baki nan da nan bakin ya fara jini, Fadane Sosai ya kaure tsakaninsu, Sulthana ta mik'e dasauri tana kuka ta shiga tsakiyarsu

"Ku daina fada d'an Allah"

Ta juya ta kalli Fareed dashima gefen idonshi ke jini tace

"Ya fareed ku daina fada, indai saboda nine na hakura banayi"

Ai kamar k'ara zuga Fareed take ya wawuri Masroor ya soma kaimai nushi, Shiko Masroor kasa dukanshi yayi dan sam baiso hakan ta faru tsakaninsu bah. Ganin Fareed na neman halakashi yasa shima ya fara maida Martani, dukan juna suke bana wasa bah Sulthana na gefensu tana kuka da ihu dan neman agaji. Daidai nan mottocin su Mami suka k'araso wajan a guje dan tun dazu bayan fitansu Mahnoor ta sanar da Mami abinda ke faruwa. Yawo suketayi har Allah yasa suka biyo ta wajan..

Umman Fareed ce ta fara fitowa ta k'araso wajan a zuciye, lafiyayyen Mari ta wanke Fareed dashi tana huci

"Bantaba sanin bakada hankali bah sai yau Fareed, yanzu akan mace shine kuke kokarin Kashe junanku?"

Kasa ma magana Mami tayi anma kana gani kasan ranta bah k'aramin Baci yayi bah. Mahnoor ta k'araso wajan ta rik'e Sulthana daketa kuka kamar ranta zai fita tasata a mota. Motar y'an sandan dake bayan nasu Mami Umman Fareed tasa aka shigar dasu Masroor aka kaisu Asibitin dake Cikin gidan..

Daddy da Abban Fareed suma Ransu bah k'aramin baci yayi bah bama Kamar Abban fareed dan shi cewa yayi Fareed ne baida gaskiya dan koma menene bai kamata ya biyo Masroor har gidansu ya dakeshi bah. Dole hakan yasa aka hadu dan Sulhu wuraren K'arfe sha d'aya na dare a babban Falon Daddy..

Daddy da Abban Fareed a a gefe zaune sai Mami da Umman Fareed suma suna gefe. Su Masroor kuma suna k'an Carpet zaune kowa da kumburaren Fuska. Daddy neh ya soma magana fuskanshi bah walwala

"Banji dadin abinda ya faru bah, haba Masroor haba Fareed. Yanzu akan mace kuke kokarin kashe kanku"

Abban Fareed yayi saurin amshewa da cewa

"Yanzu idan abun nan yakai waje duniya zatai mana dariya akan cewa ga y'ayanmu suna fada tsakaninsu akan mace. Sam wannan abin bai dace bah"

Masroor ne ya soma d'agowa yace

"Daddy, Abba kuyi hakuri"

Abba ya nuna Fareed da yatsa

"Duk abinda ya faru ga babban mai lefi nan, haka kawai Masroor baya kamaka da dukaba dan kazo gidansu. kaida nakema Kallan mai hankali ashe bakada shi, karka manta kaifa babba neh ka girme ma Masroor anma ace haka na faruwa tsakaninku"

Daddy yace

"Ai bashi k'adai bah harda Masroor din, shima kana ganinshi bashida hakuri."

Abba ya nisa yace

"Sam baku kyauta mana bah. Banji dadi bah kun bamu kunya"

Daddy ya nunasu da yatsa

"Sannan ku sani yarinya bazata taba aurenku bah duka tuna abin haka neh"

Mami tai Saurin cewa

"Ur excellency inaga hakan kamar tauyewa neh. Yakamata ita yarinya ta fadi wanda takeso sai a bata, wanda kuma bataso saiya hakura"

Gyada kai Abba yayi

"Wannan Gaskiya neh"

Daddy yace

"Abinda za'ayi gobe in Allah ya kaimu da Sassafe dukanmu zamu dunguma muje kauyensu dan mu samu asalinta. D'an duk wannan abin da mukeyi kamar munyi tuyane mun manta da Albasa"

Umma tace

"Gaskiya neh"

Abba yace

"Hakan ma yayi, daga chan sai ayita ta k'are ta fadi wanda takeso mu nema masa aurenta kawai"

Kowa dake falon ya amince Abba yace su Fareed su tashi su tafi, duk suka mik'e suka bar falon kowa jiki a sanyaye..

A daren Mami ta samu Sulthana a dakinta kwance tana aikin kuka, karasawa tayi ta zauna kan gadon ta dagota tareda share mata hawaye.

"Wannan kukan duk na menene? Ya isa haka kinji"

Kai ta gyada kawai kanta a kasa dan yanzu kunyan yan gidan takeji. Mami tace

"Gobe dasassafe ki shirya zamuje kauyenku dan.."

Kuka Sulthana ta fashe dashi ta rik'e hannun Mami gam

"Dan Allah Mami karku maidani wajan Baffa kasheni zeyi"

Rufe mata Baki Mami tayi cikeda tausayawa

"Bah barinki zamuyi bah, zamuje neh dan yasan kina wajanmu"

Dakyar Mami ta shawo kanta ta amince, saida taga Barci ya dauketa Sannan tabar dakin..

Ranar Fareed da Masroor babu wanda ya runtsa kowa da abinda yake s'akawa a ranshi. Ganin bacin ya gagara yasa Masroor mik'ewa yayo Alwala ya soma kai kukanshi gurin Ubangiji..

Kamar yanda akayi da Sassafe Abban Fareed da Umma sai shi Fareed din suka iso gidan, Already su daddy sun shirya. Wasu motoci daban suka d'auka bana gwamnati bah suka dau hanyar kauyensu Sulthana..

Fareed ne yakema Drivern kwatance har suka kawo kofar gidan. Gaban Sulthana ne ya fadi sanda ta kalli gidan, duka suka fifito daga mota anma banda Sulthana, Mahnoor ta bud'e kofan

"Sulthana fito mana"

Dakyar ta sauko kafa ta fito tana bin kofar gidan da Kallo, bah abinda ya chanza har yanzu komai na nan yanda yake, saidai ta lura kamar yanzu bah almajirai a runfar su. Yaro su Abba suka samu yamusu Sallama da Baffa.

Ba'adau lokaciba ya fito daga gidan, Kallo d'aya zakaima Baffa kaga ramar da yayi. Duk ya fige kamar bashi bah, ganin Manyan Mutane Yasa jiki na rawa ya shiga cikin gida yasa aka shishimfida tabarma sannan ya fito yace

"Bismillah ku shigo"

Sam bai lura da Sulthana dake jikin Mami a makale bah. Tsakar gidan suka shiga Suka zazzauna, Ameenatu ta fito daga dakin Mama dauke da kwanun sha ta aje Sannan ta gaidasu, harta mik'e suka hada ido da Sulthana. Mik'ewa tayi dasauri tana nuna Sulthana bakinta na rawa

"Su..Sul...Sulthana"

Baffa ya mik'e yana kallan inda Ameenatu ke nunawa, jin kamar an kira sunan Sulthana yasa Mama fitowa daga dakinta hakama Hafsatu

K'ara shigewa jikin Mami tayi tana boye Fuska, Baffa ya soma Hawaye yana cewa

"Sulthana ki gafarceni, nasan nayi kuskure. Sharrin shedan neh da kuma rashin sani"

Jin abubuwan da Baffa yake cewa yasa ta d'ago tana kallanshi da Mamaki. Mama ta k'araso wajan itama tana hawaye

"Sulthana dama kina raye, bah inda bamuje nemanki bah. Baffanki kullum ke yake anbata"

Sai kallansu Sulthana take da Mamaki, Abban Fareed neh yace

"Mallan zauna muyi magana"

Bah musu Baffa ya zauna yana matsar kwalla. Tunkan Abba ya sake Magana Baffa ya soma zaiyane musu duk abinda ya faru yana hawaye. Kuka Sulthana take na farinciki da Allah yasa ita bah shegiya bace. Bayan ya gama Abban Fareed shima ya dora da basu labarin zaman datai tareda fareed da kuma wanda tayi a gidansu Mami..

Zabura Baffa yayi ya gyara zama yana rarraba ido

"Dama da Gwamna da Mataimakinshi nake zaune"

Ya juya ya Kalli Mama dasu Ameenatu tana mai cikeda Farinciki. Hafsatu da yanzu ta zama salaha tace

"Sulthana ki yafemin lefukan dana miki, nasan nayi kuskure"

Yau Sulthana na Cike da Farinciki yau ga yan uwanta na santa suna neman gafaranta.. batareda wani dogon tunani bah tace

"Baffa, Mama, yaya Ameenatu, yaya Hafsatu duk na yafemuku tuntuni, dama ban rikeku bah. Ina sanku sosai"

Mik'ewa tayi ta rungume Baffa, ya fashe da kuka yana cewa

"Allah ya jikan Mahaifiyarki Allah ya gafarta mata. Ke kuma Allah ya miki Albarka"

Ameen tace Sannan ta janye jikinta ta rungume Mama da sauran Y'an uwanta..

Su Daddy yan kallo suka koma kowa yana tayata Murnar sassantawa da Mahaifinta da y'an uwanta

Mama ta mik'e ta soma kici kicin d'aura girki na musamman Dan tarban manyan Bakinsu...

Saida aka natsa, Sulthana tana d'akinsu Yaya Ameenatu itada Mahnoor sunata basu labarin Birni sukuma su Daddy suna kam tabarma cikin ihuwa sunata hira da Baffa kamar sun saba. Su Masroor kuwa suna chan gefe zaune sunyi jugum jugum kowa da abinda yake sakawa a ranshi...

Ummy Abduol✍🏻

πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
          πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
          *SULTHANA*
          πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

By *Ummy Abduol*


 DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION

                *Page 198*

Su Masroor kuwa suna chan gefe zaune sunyi jugum jugum kowa da abinda yake sakawa a ranshi sannan Abba ya gyara zama yaba Baffa labarin Soyaiyar dake tsakanin Sulthana da y'ayansu sanna ya d'aura da cewa

"Dole yanzu zamu kirata neh ta zaba wanda takeso a cikinsu"

Baffa ya b'ata rai

"Haba ranka ya dad'e ai duk wannan bai taso bah, kuma fah iyayenta neh ku da kanku kawai ku zaba mata wanda zata aura"

Daddy yayi murmushi yana k'allan Baffa

"Aa baza'ayi haka bah, idan mukai haka kamar mun tauyeta neh. Tho idan kuma muka zaba mata wanda ita bai kwanta mata bafa?"

Shiru Baffa yayi baice komai bah. Abba yad'au waya ya kira Umma yace su fito duka, duk suka fito daga dakin Mama itada Mami suka zauna k'an tabarman. Baffa Yacema Mama ta kira Sulthana tace tho

Dakin ta shiga ta kirata suka taho tare, koda sukazo sun samu Fareed da Masroor xaune a wajan. Kusada Mami ta zauna k'anta a kasa, Abba ya kalleta da fara'a

"Y'ata mun kiraki neh dan muji ra'ayinki. Munaso ki fada mana tsakanin Masroor da Fareed wa kikeso"

Gabanta neh ya fadi ta d'ago ta kalli Masroor taga kanshi a kasa ta maida dubanta ga Fareed shima kanshi a kasa. Kasa magana tayi gabanta na cigaba da bugawa. Mami ta tabota

"Sulthana kiyi Magana mana karkiji Tsoro ki Fada abinda ke ranki"

Shiru tayi nad'an mintina Sannan tad'an dago bakinta na rawa tace

"Ya Fa..."

Dasauri Fareed ya d'ago ya kalleta da Alamar Mamaki, Masroor ko runtse idonshi yayi zuciyarshi na bugawa da sauri. Umman Fareed tace

"Kiyi Magana mana Sulthana keh muke jira"

Ta maza tayi ta saukar dakanta kasa tace

"Yah Masroor"

Sauke kai Fareed yayi yana girgixa kai ahankali, dasauri ta tashi tabar wajan. Abba yace

"Tho Alhamdulillah tunda yarinya ta fadi wanda takeso yanzu sai ayi maganan sadaki koh"

Su Umma najin haka suka mik'e suka bar wajan, Su Fareed suma suka mik'e suka fita waje. Fareed ya share hawayen idonshi yace

"I'm very sorry friend"

Ya mik'ama Masroor hannu yace

"Congratulations am very happy for you, Allah ya sanya Alheri"

Jikin Masroor neh yayi sanyi shima ya mik'amai hannu

"Ni yakamata nabaka hakuri, bakai bah"

Fareed ya girgixa kai ya shiga mota ya zauna ya daura kanshi jikin stering motan ranshi jagule..

Sulthana na shiga d'akinsu ta fada kan gado ta fashe da kuka, Ameenatu ce ta dafata tana cewa

"Meke faruwa Sulthana?"

Mik'ewa zaune tayi hawaye chabe chabe a idonta, tace

"Bansan da wani ido ya Fareed zai kalleni bah. Gani nake kamar namai Butulci"

Hafsatu ta dafata tana Murmushi

"Mahnoor ta mana bayanin komai, kuma bakida laifi saboda bai sanar dake bah Sannan kuma na lura bah wai sanki yake bah tausayinki neh"

Sulthana ta k'ura mata ido da Mamaki, gyada mata kai Hafsatu tayi sannan ta juya ta Kalli Ameenatu wacce itama su take kallo ta juya ta maida dubanta ga Sulthana tace

"Ya Ameenatu ta dad'e tanasan Likitan nan, tun sanda ta soma ganinshi ta fara sanshi, kullum sai tayi min maganar shi."

Mik'ewa Ameenatu tayi rai b'ace

"Baki kyautamin bah Hafsatu Ashe bazaki iya rik'emin d'an sirrin nan dana baki bah"

Murmushi Sulthana tayi ta share hawayen Fuskanta ta mik'e ta fito tsakar gidan, ganin su Fareed basa wajan yasa tasa takalmanta ta fita kofar gida. Zaune ta sameshi cikin mota shida Masroor suna hira jefi jefi, nesa dasu ta tsaya Masroor na ganinta ya fito ya karaso inda take yana murmushi

"Har na cire rai Beauty, sai gashi nine gwaninki"

Hannu yasa ta rufe fuskanta tana dariya

"Dan Allah ya Masroor inaso nayi magana da Ya Fareed"

Murmushi ya mata

"Bbu komai ki sameshi a mota"

Dariyan jindadi tayi

"Thank uh Bro Masroor"

Da Sassarfa ta k'arasa bakin motan ta bud'e ta shiga tana Kallanshi

"Ya Fareed kayi hakuri dan Allah"

Sai a Sannan ya d'ago ya kalleta tareda k'irkiro Murmushi

"Bakimin komai bah Queen, Laifina neh da ban fadamiki tun tuni bah naiyi zurfin ciki,  haka Allah yaso. Allah ya nufa ke bah Matata bace"

D'an dukar dakai tayi tana wasa da zoben dake hannunta tace

"Nagode ya Fareed, bazan t'aba mantawa dakaiba a rayuwata. Kayimin Abubuwa da dama wanda banida bakin godiya, ka taka muhimmiyar rawa a rayuwata thank uh v...."

Saurin katseta yayi ya d'aura yatsanshi a lebenshi

"Uh dn't have to thank me"

Jim tayi nad'an wani lokaci sannan tace

"Ya Fareed akwai wani abu danakeso kayimin dan Allah"

Batareda wani bata lokaci bah yace

"Menene shi Queen?"

Tacigaba da cewa

"Inaso dan Allah Ya Fareed ka auri ya Ameenatu"

Dasauri ya juyo yana kallanta da mamaki, gyada mai kai tayi tana y'ar murmushi. Kasumbar dake fuskanshi ya shafa

"Ita tace miki tana sona?"

Girgiza kai tayi alamar Aa. Ya numfasa yace

"But queen I have no feelings for ha, and zai iya yuwuwa bata sona. Kawai ki barshi nagode"

Ta turo baki ta soma gungunai

"Nidai Dan Allah Ya Fareed ka aureta, shes kind kuma batada matsala. Nasan zata soka and kuma kagani zaku saba"

Dariya yayi Mara sauti yana k'allanta kasa kasa, baisan ya musa mata kuma a ganinshi wannan karamci tamai and kuma bah lefi yarinyan tanada kyau Sam bata kamo k'afar Queen dinshi bah dukda ita b'akace.

Ya juyo da Fara'a kwamce kan Fuskanshi yace

"Shiknan Queen na Yarda"

Ihu ta saki tana dariya har saida Masroor ya K'ara sako wajan dasauri. Fitowa daga motan tayi ta shiga cikin gida da gudu. Dakyar suka shawo kan Ya Ameenatu ta fita wajan Fareed, a waya Sulthana ta fadama Masroor abinda ke faruwa, Yaji dadi sosai shima. Ameeantu da Fareed sun fahimci juna kuma har ya Amince zai aureta, su Daddy sunyi Mamaki sosai jin Maganan. Basu bar Kauyensu Sulthana bah saida aka tsaida Ranar Bikin Masroor da Sulthana sai Fareed da Ameenatu wata d'aya, Aka ba Baffa sadakinsu Dubu D'ari d'ari dan Baffa yace baison Asa Sadakin dayawa..

Mama ta rok'i Alfarman a bar mata Sulthana har zuwa ayi bikin. Baffa ya tambayi Sulthana ta amince batai Gardama bah, Masroor sam baiso haka bah bah yanda zaiyi hakanan ya hakura sukai musu Sallama suka tafi bayan Sun Cika Baffa da kudi. washe gari Mami ta turo Driver da Kayan Sawan Sulthana da Kayan Abinci dana sawa nasu Mama cike da Mota...

Kula Sosai Sulthana take samu a gidan Mahaifinta ta bangaren Mama da Baffa har takan rasa wayafi kula da ita. Kullum suna Makalle da Masroor a waya haka soyaiya Suke mai Tsafta da Shiga rai. Fareed na Xuwa wajan Ameenatu hakan yasa suka k'ara shakuwa da ita, ya sai mata waya itada Hafsatu. Shima Masroor na xuwa shida Yasir..

Mama ta zage tanata gyara Y'ayan nata daidai karfinta, Mami ma Tana aiko Mahnoor da Wasu kayan gyaran jikin anaba Mama dan tayi Musu. Yau Saura kwana biyar Biki, Yau Sulthana take expecting Mahnoor dan tace mata zatazo har a gama biki. Tana gidansu Sadiya K'awarta Wayan Sulthana yahau Ruri, ta d'auka da Fara'a tana cewa

"Kin iso neh"

Harta mik'e ta koma ta zauna tace

"Yah Hafsatu tana Nan kice ta kawoki"

Bata jira mai zatace bah ta kashe kiran. Sadiya dake gefenta tace

"Ta iso neh?"

Da Fara'a tace

"Eh wai da lefe suka zo"

Dariya Sadiya tayi ta mik'e dasauri

"Ah bari muje muga Lefe"

Tab'e baki Sulthana tayi sadiya tad'au mayafinta ta fita daga gidan dasauri. Tana fita Mahnoor ta shigo gidan itada ya Ameenatu, sulthana ta mik'e dasauri ta rungumeta tana Dariya

"Uh welcome"

Dagota Mahnoor tayi daga jikinta tana k'are mata kallo

"Friend kinga yanda kika koma? Kin K'ara kyau sosai"

Turo baki Sulthana tayi tana doka kafa a kasa. Nan suka zauna suka soma hiran yanda bikin zai kasance basu bar gidan bah sai Yanma lis lokacin sun tabbatar yan kawo lefe sun tafi..

Ummy Abduol✍🏻

πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
          πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
          *SULTHANA*
          πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

By *Ummy Abduol*


 DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION

                *Page 199*

Lefe na gani na Fada aka kawo kowaccen su akwati dozin biyu akai mata. Mutanen Kauyen sai shiga suke suna kallan kaya kowa na tofa Albarkacin bakinshi..

Ranar Alhamis Ameenatu da kawayenta Sukayi k'auye day, su kuma su Sulthana dukayi Fulani day itama itada nata k'awayen. Ranar Juma'a aka sasu Lalle da daddare. A Daren Masroor da Fareed sai d'an rakiyansu Yasir dukazo gidan, a tare amaren suka fito kowacce ta k'araso wajan angon nata. Masroor sai Kallan Sulthana yake da Murmushi

"Beauty kin k'ara kyau meye sirrin?"

Rufe fuskanta tayi da Hannayenda da sukasha had'adden kunshi. Ya rik'o hannunta yana kallo yace

"Waya miki wannan design din yayi kyau sosai"

D'an murmushi tayi ta turo baki

"Ya Masroor ka daina wannan maganan kanasa inajin kunya"

Dariya yayi yana shafa sumar kanshi

"Ki daina jin kunyana beauty, nidake yanzu mun zama d'aya karki manta gobe za'a daura mana aure ki zama tawa na xama taki"

Hannu tasa ta rufe fuskanta tana dariya K'asa kasa, daidai nan Yasir ya karaso wajan yace

"Ni kun barni chan gefe"

Ya kalli Sulthana

"Madam kinsan meye?"

Ta girgiza kai tana kallanshi, ya gyara tsayuwa ya sassauta Murya

"Nifah Sistern nan naki nakeso"

Tace "wah kenan?"

Yace "Hafasat"

Da zumud'i tace

"Dagaske?"

Kai ya gyada Mata, Masroor yayi saurin cewa

"Dallah kyalle wannan, mayaudari neh karki yarda
kadama ki fadamata"

Duka Yasir yakaimai

"Kai bansan fah iskanci i'm serious"

Sulthana tace

"Karka damu Ya Yasir zansan Yanda zanyi"

Godiya ya mata yabar wajan. Sun d'an taba hira sannan suka musu Sallama Suka tafi..

Washe Gari ya kasance ranar Sati, a ranar duban mutane suka shaida d'aurin auren Fareed da Ameenatu, sai Masroor da Sulthana. D'aurin auren daya samu hallartar Manyan Mutane tun daga kan shi kanshi shugaban k'asa, Gwamnoni, sarakuna da saurayan Manyan mutane masu fada aji a nigeria..

Har hawaye saida Baffa yayi dan bai taba tunanin zaiga irin wadannan Mutanen bah a rayuwarshi. Masroor baki yak'i rufuwa, Ana gama d'aurin aure yad'au wayanshi ya soma nemqn layin beauty. Ya dad'e yana ringing kamin a kawo mata ta d'auka tana y'ar Murnushi, cikeda Farinciki yace

"Beauty am now urs uh are mine. An d'aura"

Dariya tayi ta kashe kiran tad'au buta tayi alwala tazo ta tada nafila. Addua tayi sosai har tana hawaye musamman data tuna ana aurenta Ummanta bata raye, tayimata Addu'a sosai. Sannan ta tashi ta koma cikin k'awayenta..

Anyi d'aurin aure lapia kowa ya koma gudanshi. Wuraren k'arfe hudu na yanma aka d'au Amare dan kaisu Gidajensu, Ameenatu da Sulthana sai kuka suke bama Kamar Ameenatu, Nasiha mai ratsa jiki tayi Baffa da Mama sukai musu sai Maman Sadiya. Sannan aka d'aukesu zuwa government house..

Su kuma achan ake shagalin bikinsu Fareed da Masroor dan sun hada taron ne shi yasa gidan ya cika mak'il bah masaka tsinke. Yan kauye nan suka saki baki suna kallan Aljannar duniya, Wani had'aden Part dake gidan aka kai Sulthana, ita kuma Ameenatu sai daga baya za'a kaita. Mai make up aka kira ta d'andasa musu kwaliya sukasa had'aden golden gown dan zuwa dinner. Yau k'auye duk an basu anko sunsha sunata washe baki cikeda Murna. Kowacce Amarya tareda angonta suka tafi wajan dinnern, suma angon nan cikin Babban riga Fari tas dah aikin Golden. Sunyi kyau ainun gwanin ban sha'awa

A gurin dinner anci ansha anyi nak, su deejatou harda zuba abinci a leda lol. Bayan an gama an dawo sannan Aka kai Ameenatu gidanta. Washe Gari da safe akayi bud'an kai, shima wani buki akai na musamman Bayan an gama akasa yan kauye a mota aka maidasu bayan an cikasu da alheri sunata godiya. Aka bar Sulthana daga ita sai Mahnoor, Aisha batasamu zuwa bikin bah dan ta koma makaranta...

Mahnoor batabar Side dinbah saida sukai sallan isha. Wuraren k'arfe tara ango ya shigo sanye da fara k'ar din yadi sai zuba kamshi yake Hannunshi rike da leda, k'ara rufe fuskanta tayi cikin gyale tana wasa da zoben zinarin dake hannunta. Kan gadon ya zauna gefenta a hankali yasa hannu ya yaye gyalen ya d'ago fuskanta, runtse ido tayi tana murmushi shima murmushin yayi yace

"Open ur eyes beauty, Masroor dinki neh."

Tad'an bude ido kadan tareda janye fuskanta ta dan kauda kai. Hulan dake kanshi ya aje gefen bedside ya mik'e tsaye tareda riko Hannunta

"Tashi muyi Alwala muyi nafila dan mugodema Allah"

Bah musu ta mik'e shi ya fara shiga yayi alwalan ya fito Sannan itama ta shiga. Ko kamin ta fito ya shinfida musu Sallaya, tana fitowa ta yafa gyalenta suka tada sallah.

Bayan sun idar ya d'auko ledan daya ajiye yace

"Dauko mana plate Beauty"

Bah musu ta mik'e ta aje gyalanta akan gado ta fito daga dakin, shige shige ta soma yi dakyar ta gano kicin din. Tsayawa tayi tana k'arema wurin kallo dan kaya neh mak'il a ciki masu tsada da daukar ido, murmushi tayi dan tasan wannan aikin Mami ce. Kwalin dinner set ta d'auko dakyar ta bud'e ta ciro plate ta wanke sannan ta d'auko cups shima ta wanke ta koma dakin. A gabanshi ta ajiye tana kokarin mik'ewa, dasauri ya rike hannunta ya jata ta fado jikinshi

"Ina zaki? Ai tare zaki zauna muci"

Turo baki tayi tana kokarin fizge jikinta daga nashi

"Nifah na koshi dazu muka gama cin abinci da Mahnoor"

Yanda tayi maganan bah k'aramin burgeshi yayi bah har saida ya kwaikwayi yanda tayi. Dariya tad'anyi ta k'ara shagwabe Fuska

"Nidai ka daina"

Kazan ya saka a plate din ya bud'e fresh youghut ya zuba a cup dinda ta ajiye Sannan ya soma bata a baki. Kauda kai tayi tana yatsine fuska

"Nifah ya Masroor na koshi"

Matso da fuskanshi yayi daidai nata har numfashinsu na had'uwa

"Wai yaushe za'a chanza min suna neh daga Ya Masroor"

Batace komai bah sai murmushi datayi. Tura mata kazan ya somayi tana ci tana bata fuska kamar xatai kuka, shi kuma yana mata d'ariya. Tadanci bah lefi sannan ta mik'e ta xauna kan gado tana cigaba da yatsine fuska

"Kagani koh kasa cikina ya cika dayawa"

Mik'ewa yayi ya kamo hannunta

"Tho zo na miki doki nasan cikin zai sassauta"

Tsugunawa yayi a kasa sannan yace tahau. bako kunya ta d'ane bayanshi ya soma tafiya ita kuma sai dariya takeyi, sun dad'e suna haka sannan ta sauka tana hanma a hankali

"Bacci nakeji"

Kai ya gyada yace yana zuwa ya fita daga d'akin. Kamin ya dawo ta shiga toilet tayi wanka ta fito ta sauya kayan jikinta zuwa na barci tahau gado nan da nan barci ya d'auketa

Wanka ya shiga yayi a d'akinshi, koda ya dawo nata ta dad'e dayin bacci. Hannun jalabiyar jikinshi ya nad'e ya d'auketa chak ta bud'e ido dasauri tana kallanshi Murnushi ya mata ganin yana kokarin fita da ita daga dakin yasa ta soma zulezule, bai direta ko inaba sai lumtsatsiyar gadonshi.

Mikewa tayi ta zauna a tsorace

"Ya Masroor Bacci fah b
Nakeji"

Bako kunya yace

"Kazana da kikaci zan amsa abuna"

Bata gane me yake nufi bah tace

"Tho bah kai kace naci bah ni yanzu ina zan samu kaza na biyaka"

Tana magana cikeda shagwaba. Fitilan d'akin ya kashe ya rage na side lamp sunada haske sosai dan su kadai mah sun wadata d'akin. Kan gadon ya hau ya matso kusada ita tad'an mata, ya kara Matsowa ta k'ara Matsawa

"Beauty ni dodone? Meyasa kike matsawa"

Shagwabe fuska tayi

"Ni tho ka kwanta a gefe nima na kwanta a gefe"

Maganar tazo mai a bazata anma ya share yace

"Anma ai keh matata ce xan iya kwantawa a kusa dake ai"

Batace komai bah sai chuno baki datayi, matsowa yayi kusada ita ya rikota tareda matseta a jikinshi. Bud'e baki tayi zatai magana ya had'a bakinshi da nata. Ina ganin haka na tattara inawa inawa nabar musu gidan gaba d'aya na koma k'auyenmu..

*Bayan Wata hud'u*

Masroor ne zaune a falo yana daddana system dinshi, hankalinshi duk ya tattara ga abinda yakeyi. Sulthana ta fito cikin wani riga pink iya cibi da wani matsatsen short, kayan sun mata kyau sosai. Jikin Masroor ta fada tana maida numfashi. Dasauri ya aje system din ya k'ara matseta a jikinshi

"Beauty naji jikinki ya k'ara zafi, nifa zafin jikin nan na. Cutana gashi kinki yarda muje asibiti"

Batace komai bah saima janye jikinta datayi daga nashi ta koma chan gefe ta zauna. Kara matsowa yayi yana kokarin tabata, bai ankara bah ta soma kwararo mai Amai, Aman take sosai jikinta na rawa. Riketa yayi har saida ta gama sannan ya mik'e ya dauko ruwa ya bata ta kuskure baki ya dauketa ya kaita daki ya kwantae da ita. Masu aiki ya kira suka gyara wajan ya koma dakin

Kwance ya sameta tana juye juye jikinta bah dad'i, daukanta yayi chak ya kaita bayi ya mata wanka ya fito da ita. Da kanshi yasa mata kaya ya d'auketa yasata a mota sukad'au hanya. Tana ganin sun nufi asibiti ta soma bata fuska, baice mata komai bah. Da kanshi ya d'auketa suka gida, bah tareda wani b'ata lokaci bah aka dubata tareda mata gwaje gwaje, a nan neh aka gano cikin datake d'auke dashi na wata biyu.

murna sosai Masroor yayi, d'aukanta yayi suka nufi gidan Mami bayan an rurubuta mata magunguna tareda bata shawarwar..

Ummy Abduol✍🏻

πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
          πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
          *SULTHANA*
          πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

By *Ummy Abduol*


 DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION

                *Page 200*

     πŸ”š

Da Farinciki suka k'arasa gidan Mami bah ko kunya ya mik'a mata takardan test din itadai Sulthana na zaune k'anta a kasa. Mami na gama karantawa ta girgiza kai tana mai cikeda farinciki

"Allah ya raba lapia"

Ga Mamakin Mami da Sulthana saijin Masroor sukai yace

"Ameen Mami"

Kunya sosai Sulthana taji har ta k'ara duk'ar dakai, shiko gogan ko a jikinshi. Tun daga ranar Sulthana ta k'ara samun kula daga wajan Mami da Masroor da duk sauran yan gidan mah. Tattalinta sukeyi sosai kamar kwai hakan bah k'aramin sata farinciki yayi bah..

A bangaren Fareed da Ameenatu basuda Matsala zama suke na soyaiya da mutunta juna. Ita tana d'auke da nata cikin na wata uku, Mama da Baffa bah k'aramin farinciki sukayi bah da samun labarin cikin da y'ayansu suke d'auke dashi. Yasir da Hafsatu sun hada kansu har anma Ranar biki. Haka Sadiya k'awar Sulthana da S'aood wanda ya ganta lokacin biki ya lik'e mata.

Bayan wata shidda Ameenatu ta haifi santalelen d'anta namiji inda akasa mai suna Farhan. Bayan wata d'aya Sulthana ta xankado santaleliyar Y'arta mai kamada Masroor sak. Murna wajan su Mami ba'a magana. Inda yarinya taci sunan Mahaifiyar Sulthana wato Rabiatu anma ana kiranta da Mimi. Kula Sulthana take samu itada jaririyarta sosai daga bangarorin biyu hakan yasa ta saki jikinta tana shayar da y'arta hankali kwance..

Ban k'ara komawa government house bah sai bayan Shekara biyu. Anan nakejin Labarin Ansha bikin Hafsatu da Yasir haka na Sadiya da Sa'ood dukanninsu suna d'auke da tsohon ciki haihuwa yau ko gobe. Sai Mahnoor dake karatunta na likita a k'asar Masar

 Had'adiyar Mace mai jida kanta na gani ta fito a wata lumtsatsiyar Mercedes benz, saida na k'ara matsawa dakyau naga Ashe Sulthana ce. A gajiye ta shiga gida ta fada kan kujera tareda fadin wash. Y'ar yarinya ce fara sol kana ganinta kaga Masroor saidai tafi Masroor din haske ta taho dasauri da tafiyanta dabai gama k'wari bah ta fada jikin Sulthana. Rungumeta ta k'arayi tana y'ar Murnushi

"Mimi ina kikanar nannyn naki"

Dai dai nan nannyn ta karaso wajan a guje tana kwalla ma yarinyan kira. Ganin Sulthana yasa tayi turus ta tsugunna tana gaidata. Amsawa tayi ita kuma yarinyan sai k'ara shiga jiki Mamanta take tanama Nannyn dariya. Sulthana ta kalli Nannyn tace

"Barta kawai tunda na dawo"

Tho tace ta tashi tabar wajan ita kuma ta k'ara shigewa jikin Mamanta. Dadaddare tana kwance akan cinyar Masroor suna k'allo yace

"Beauty ya jamb din yayi sauki koh"

Murnushi tayi

"Sosai mah"

Ya janyota ya k'ara matseta jikinshi yana shakar kamshinta

"Anya baza'a bar karatun nan bah sai shekara mai xuwa? Dan ni k'ani nakeso aima Mimina"

Mikewa Sulthana tayi dasauri tana turo baki

"Gaskiya my pearl bah yanzu bah, haihuwa fa da zafi."

Yayi dariya ya kama hannunta cikeda xolaya yace

"Tho shiknan yanzu ni sai kimin cikin ni na haihu kinga sai a rinka rabawa koh"

Kyalkyalewa da dariya tayi ta mik'e tabar wajan ta biyota tana ganin ya nufo dakinta ta tura kofan ta rufe tareda sa key tace

"Gaskiya My pearl yau ka barni na huta na gaji kullum abu d'aya"

Kwafa yayi yace

"Zan kamaki neh xaki sani"

Bai jira mai zatace bah ya shige Dakinshi yana cizon Yatsa..


 A nan zance Allah ya baku Zaman lapia mai d'orewa ya k'ara muku k'aunar juna Ameen..


ALHAMDULILLAH

    A nan na kawo k'arshen littafina mai suna Sulthana.. Allah ya bamu ikon Anfani da darusan dake ciki. Kurakuren danayi Allah ya yafeni Ameen


Ina godiya ga Masoyana na nesa dana kusa. Ina alfahari daku dan da bazarku nake rawa Masoyana

*Bazan Manta daku bah*

Ayoush yusuf
Ummyn yusrah(my ruhi)
Jannart lameed'o (my zuciya)
Sumaiya d'an fulotiee (Allah yasa na fadi sunan daidai)
Members na pure moment of life writerd
Hajiya Fateema
Aisha zagi
Fati azland
Deejatou
Meela adeel
Nafeesah hasheer
Zeenaseer
Hafsatbm
Ummiey
Fatima adamu
Nana khadeejah
Maman zakiya
 Wai kumin Afuwa kunada yawa. Kuma wadanda ban anbata bah kunsan kanku ina Alfahari daku ina mik'a gaisuwata gareku

*Sadaukarwa*

Na sadaukar da wannan littafi ga late Rabiatu s suleiman (mrs usman kademi) Admin House of novels Allah ya gafarta miki yasa Aljannatul firdaussi ya zama makoma a gareki yasa kina a kyayyawan Makoma Ameen..

*Kyautarwa ga*

Mahaifiyata Allah yaja kwana Mama..

*Jinjina*

Ga Members na dabazarmu Writers Association. Kunyi neh Allah ya barmu tare..

*Godiya ta musamman*

Sulthana novel fans
Dabazarmu writers association
Musan kanmu Marubuta
Musan juna o.h.w
Deejatou novels
House of novels
Itace kaddarata fans grp
Preety queen novels
B u hamzert novels grp
Feedoh online novels
Marubuta
Marzah hausa novels
Sweerys novels fans
Duniyar novel
Mukaru da juna
Mata rahamane
Jannart lameed'os novels grp
Jinin Sarauta fans
Tamamancy novels
Facebook surbajo fans
M.kaoje novels
Fareedat novels grp
Hausa novels by surbajo
Ummyn yusrah novels
Ko ajikinmu
Maryam salisu maidala
Da duk sauran grps daban anbata bah. Ina jinjina a gareku na gode sosai.. Ummy Abduol na sanku.

    Sai kunjini a sabon littafina nan bada dad'ewa bah

Taku har kullum

Ummy Abduol✍🏻

adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *