Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Tuesday, June 23, 2020

RUKAYYA YAR ALBARKA COMPLETE LITTAFIN HAUSA

adsense here
RUKAYYA YAR ALBARKA COMPLETE LITTAFIN HAUSA

8/[6/8, 8:12 AM] Fatima 💖: RUQAYYA YAR ALBARKA
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM



Su uku ne a cikin office din likitan. Sai hadiyar yawu yake yana sake kallon akwatin kudin da yake bude akan table din da ke gabansa. A zuciyarsa kuwa sai nanatawa yake 'yan Nigeria akwai kudin banza. Abinda take so daga gareshi a ganinsa ko a kasarsu zata iya samu. Sai dai kuma bai san dalilinta na tahowa har India ba. Ya sake kallon kudin.....karbar haihuwa kawai shine ta bashi dalolin nan. Mai cikin ya kalla madam kina da wata lalura ne da tasa zaki iya kudi fiye da abinda asibiti ke bukata? Batare da ta amsa shi ba ta tashi tsaye a gabansa ta daga doguwar rigarta ta zaro wani pillow wanda ta daidaita shi sosai a jikinta kamar cikin gaske. Dr Gupta ya mike tsaye ba shiri dama ba ciki gareki ba? Duk maganar da turanci yake yinta. Daya matar wadda uwa ce ga mai cikin tace Dr Gupta ka saurareni da kyau magana zamuyi. Ba tun yau ka sanni ba ina zuwa medical check up wurinka. Wannan 'yata ce kuma ko sau daya bata taba samun ciki ba tunda take, aurenta shekara takwas kenan. Dr Gupta yayi dan murmushi ai ba matsala tazo inda zaa taimaka mata. Dattijuwar tace babu abinda zaka iya yi mata Dr. A kasar nan kawai taje asibiti ya fi biyar banda na USA, England da Egypt. Mahaifarta ce take da matsala bazata iya rike ciki ba ko da an daureta. A halin da ake ciki tayiwa mijinta karyar ciki na wata takwas kuma ya yarda saboda bata bari ya ga jikinta ba. Ta nuna masa yar tata kalleta da kyau har kiba ta kara don ta nuna alamun ciki kuma kowa a kasarmu da ya kamata ya yarda ya yarda din. yanzu mun taho haihuwa ne wata uku da suka wuce so muna bukatar baby a wurinka. Dama tunda ta fara magana Dr Gupta ya harbo jirginta.

Dr Gupta ya dan share gumi don kuwa bukatarsu babba ce. Yace Madam me ya hana ku nema a can Nigeria, nasan a can zaku sami babies da yawa wanda zasu dace da bukatarku. Dattijuwar tace kaga Dr muna bukatar sirri ne saboda mijinta babban mutum ne. Idan kuma muka nema a gidan marayu ana cike ciken takardu wanda karshe dai wata rana asiri zai iya tonuwa. Yar tata ta soma masa kuka tana rokonsa. Yace to ba komai amma dole su bashi time ya duba cikin patients din asibitin wadanda suka fito daga kasashen Africa amma bakake don abin ya fi daidai. Matar ta ce to Dr mijina fari ne sosai mai tsaho da jiki, idan dan da hali zanso da namiji wanda ka ga iyayensa sun dace da irin yanayin da na kwatanta maka ko kusa da hakan. Dr Gupta yace ba matsala. Suka tashi da akwatin kudinsu wanda aka yi masa alkawarin ya zama nashi indai bukatarsu ta biya nan da sati uku zuwa hudu.

Tana shan maganin yana mata dariya saboda yadda take yamutsa fuska. Ta hade rai tana ta hararsa. Gwalo yayi mata ya tashi daga gabanta yana ta dariya. Maryam ta turo baki Hajjaju kin ganshi ko? Hajjaju ta rike masa kunne tace kaga Mukhtar ka kiyayeni. Mutum baka da aiki sai tsokana kamar wani yaro. Maryam ta kalle shi tana masa gwalo itama. Yace Hajjaju kinga kina min fada tana dariya ko?  Ta dafe kai ni naga ta kaina. Tunda kuka taho dani kasar nan kun mayar dani mai rabon fada. Ta dan ja tsaki abin haushi ma  sai na shiga nayi dumu dumu sai ku gwaleni. Mukhtar da Maryam suka tafa suna dariya. Ta harare su kungani ko....zanyi maganinku ne fitinannun yara kawai. Sake dariyar suka yi har Hajjaju ta tashi zata shiga bandaki sai ta ga Maryam ta dan cije lebe. Da sauri ta dawo ta zauna sannu cikin ne ko? Maryam ta shafa katon cikinta yau babban mutum shurina kawai kake yi tun safe. Hajjaju tayi murmushi ita dai tana kaunar yarinyar nan. Shekara hudu da aure tayi bari yafi biyar sai wannan cikin ne ya zauna da taimakon Allah da dabarun likitoci. Sunce mahaifarta ce sam bata da kwarin rike ciki. Watansu na uku kenan a India ana kula da lafiyarta da ta abinda ke cikinta. Hajjaju kanwar babar Mukhtar sannan gidan mijinta kusa yake da gidansu Maryam. Ta dalilinta suka hadu dukkansu maabota barkwanci.

Maryam na dafe da ciki Mukhtar ma ya dafa yace ke babbar mutum bar ganin na matsu da zuwanki ba'a taba min mata. Haba duk kin hanamu sakat, ko yar soyayyar nan kin wani bake hanya. Pillow Hajjaju ta jefa masa yaran nan baku da ta ido. Ni kiyi ki haihu mu koma gida. Haka kawai zaku  bata idanun tsohuwa. Maryam da mijinta suka sake tafawa suna ta dariya. Sannan tace wai bazaka dena kiran dan nan mace ba? Yace anki din, mace zaki haifa min amma kada ta dauko tsiwarki wallahi don nasan wataran za'a doke bakin. Hajjaju tace ni dai mai albarka muke fata. Mukhtar yace matar, Maryam ta juyo naam mijin. Ya kalli gefen yatsun hannunsa da na Hajjaju yace kin tuna cewa kin auri dangin cindo ko? Duk wanda ya hada jini da babansu Hajjaju ko ta uwa ko ta uba sai an haifeshi da yatsu shida. Kai tsohon nan jininsa ba dai karfi ba. hajjaju dai rankwashi ta kai masa tace kuma kaga kune kawai masu yanke naku. Mu ai duk da abinmu muke rayuwa ta fada tana shafa karamin yatsanta na shida. Mukhtar yace haka kawai na rasa mata? Ai tana haihuwa indai akwai yadda aka cire min nawa haka zaa yanke masa. Ya taba wurin da yayi alama ya ce ahhh su sarkin noma Muhammadu Cindo ka bar mana gado har jikoki. Maryam ta rinka dariyar yadda Hajjaju ke binsa tana rankwashi.







Batul Mamman💖
[6/8, 8:35 PM] Fatima 💖: RUQAYYA YAR ALBARKA✨2




Bayan kwana biyu Maryam tana zaune akan kujera a dakinta na asibiti ita kuwa Hajjaju ta dan kwanta akan gadon marasa lafiyan Mukhtar ya shigo da sallama. Wani katon akwati yake ja da kyar. Maryam tace mijin ka dawo, sannu da zuwa. Yana murmushi yace yauwa matar. Ya dubi Hajjaju ina wuni mamanmu. Kafin ta amsa yace yanzu sai ki koro min mata ki dare gadon kamar kece mai cikin. Hajjaju ta ce to ka dawo zamu fara ko. Ta nuna shi da yatsa ka kiyayeni ni fa babarku ce ba kaka ba. Maryam ta taso ta zauna kusa da ita rabu dashi Hajjajuna. Zamu hada shi da Umma idan muka koma gida. Hajjaju ta dan ture mata hannu ba wani nan. Ke da mijin nan naki duk halinku daya. Ni ban ga na zaba ba a cikinku. Suka kalli juna suka tafa suna dariya. Hajjaju a ranta tayi murmushi tana adduar su cigaba da zaman lafiya. Duk halin tsokanarsu mutanen kirki ne duk su biyun ga rikon addini. Mukhtar lawyer ne mai zaman kansa wanda ya fara suna a kasar Nigeria saboda kwazo da hazakarsa. Ita kuwa Maryam bana ta gama karatun mass comm, wato aikin jarida. Idan ta koma zata tafi bautar kasa. Sunyi aure tun bayan ta gama secondary school. Suka zauna suna ta hirar baby don sunki yarda a fada musu jinsi bayan scanning. A cewarsu koma meye suna so. Ita Maryam tace namiji tafi so kamar mijinta shima yace mace yake so irinta.

Dr Gupta ya rasa abinda ke masa dadi. Tabbas kudin nan zai ishe shi ya karasa ginin asibitinsa a kauyensu. Matsala daya ya gama binciken bakaken mutanen dake asibitin masu haihuwa su biyar ne. Daya ce yar Nigeria, biyu yan Ghana ne, daya daga Mali sai wata yar Jamaica. Ya rasa da yadda zai bullowa lamarin gaba daya. A wannan yanayin yaga wucewar Mukhtar yana jan akwati. Kura masa idanu yayi sosai yana kallonsa. Tabbas ya dace da kwatancen matar nan. Fari, dogo mai jiki duk da ba kiba gareshi sosai ba. Bayansa yabi har dakin da suke. Ya fito ya nemi file dinsu a wurin receptionist. Duk wani bayani na Maryam ya samu dadin dadawa ma sune yan Nigerian. Neman likitan da take kula da Maryam yayi cikin hira ya samu dukkan bayanin da yake nema. Sai kuma yayi saa likitar tace ita tana son daukan hutu a sati mai zuwa zata yi tafiya amma sunyi da abokin aikinta zai yi mata nata aikin kafin ta dawo. Dr Gupta yace haba dai ina nan kike neman taimakon wani. Kinsan dai shima yan kwanakin nan aiki yayi masa yawa. Ki bani patients dinki ni ba ma sai kinyi min nawa aikin ba idan kika dawo. Ta washe baki da gaske Dr? Yace sosai ma, ai amfanin zaman tare kenan. Cikin kwanaki biyu ya zama likitan Maryam Hassan kuma suka saba sosai da Mukhtar.

Sati biyu da faruwar haka Maryam ta fara nakuda. Tun bayan asuba ta fara jin ciwo sai ta daure. Hajjaju ta kula da yanayinta ta ce ko in kira likita ne? Maryam taki yarda wai ba ciwo sosai. Haka suka zauna har Mukhtar ya shigo ya ganta a wannan yanayin. Yadda yaga tana cije lebe yasan ciwon na damunta don sararta kenan. Da gudu ya tafi neman likita. Da yake babban asibiti na wadanda suka san abinda suke yi baa dauki lokaci ba sai ga nurses da likitoci a dakin. Dr Gupta ya kira hotel din da matan suke ya sanar dasu su taho yanzu akwai wadda zata haihu.

Maryam ciwo yaci karfinta tana addua tana zubar da hawaye. Haka ta kwana ta yini tana abu daya. Jikinta duk babu kwari tana kwance hawaye na zuba daga gefen idanunta. Mukhtar ya rike mata hannu yana shafa mata kai. Kiyi hakuri kinji matar, duk ciwon nan kankarar zunubi ne a gareki. Kinsan Allah Yana da tausayin bayinSa shiyasa duk abinda ya jarabce bawa dashi Yake bashi lada. Kuma kina haifo mana santaleliyar budurwa zaki manta ma anyi. Murmushi tayi tace kaima ai kankarar zunubin ne tunda hankalinka a tashe yake amma kake hakuri. Ta dan share hawaye kukan nan ma duk na jin dadi nake kada ka dauka ni raguwa ce. Yace ai nasanki ba dai himma ba. Hajjaju tana daga gefe tana share kwalla. Gashi dai duk basu da nutsuwa amma kokarin kwantar wa juna hankali suke. Sai da Dr Gupta ya tabbatar haihuwar ta zo yasa aka shiga da Maryam dakin haihuwa. Duk yadda Mukhtar yaso binta suka hana. Ana turata ya rike mata hannu yayi dan murmushi duk da cewa hawaye na zubo masa ki daure kinji Maryam dina. Zan je nayi ta addua kema kada ki fasa. Ta ce to sannan ta ce kada ka cinye kazar nan don Allah ka jira ni. Dukkansu suka yi murmushi Hajjaju tana binsu da addua.

Jiki ba kwari ya tafi ya dauro alwala yana ta yiwa matarsa adduar haihuwa lafiya. Maryam kuwa ciwo na karuwa tana ta salati taga shigowar Dr Gupta da wasu nurses biyu. Dukkansu fuskokinsu a rufe suke da face mask. Da indianci yake magana da daya suka gama hada komai ya duba ta. Yace ta kusa haihuwa, matar ce a tsaye a kanta tana goge mata gumi da hankici. Can taji wani irin ciwo ba shiri ta kara sautin hailalarta. Matar ta rike mata hannu tana mata sannu cikin harshen turanci. Dr Gupta yana tsaye a gabanta yana cewa tayu nishi sai ga kan baby ya fito. Ya dan yiwa daya nurse din signal da ido tayi saurin hada ruwan allura ta matso. Maryam tana salati gaba daya baby din ya fito. Ai tuni ta fara hamdala tana murmushi don duk ta gama gajiya. Da zumudi tace Dr me na haifa? Bai amsa ba sau kawai ya mika baby din ga matar wadda idanunta ke hawaye..yau ita ce da baby zata kaiwa mijinta gida. Ta dan dubi maryam da tausayawa tana rokonta gafara a zuci. Tayi alkawarin biyan duk kudin asibitinsu don bata da abin saka musu. Maryam ta sake cewa me na haifa tana mika hannu alamun a miko mata. Tsikarin allura taji a hannunta nan take idanunta suka fara lumshewa. Abu daya zata iya tunawa shine sautin kukan baby da yatsu shida da ta gani a hannuwan da suka leko ta mayafin da aka lullube baby din.







Batul Mamman💖
[6/10, 1:00 AM] Fatima 💖: RUQAYYA YAR ALBARKA✨3





Matar tana ganin Maryam tayu bacci tayi saurin cire kayan nurse da ta saka. Idanunta akan baby din tana kallo tana jin dadi. Bayan ta gama shirinta tsaf ta dauko akwatin kudin ta mikawa Dr Gupta. Sannan ta bawa nurse din check. Gaba dayansu sun nuna farinciki sosai. Sai kudi mai yawa ta mikawa Dr din ga wannan nasan zai isa a biya gaba daya kudin asibitin matar nan. Daga nan ta sake musu godiya ta fice. Ko awa biyu basuyi ba ita da mahaifiyarta suka hada kayansu suka nufi airport. Cikin dan kankanin lokaci suka tashi sai Nigeria.

A hankali Maryam ta bude idanunta. Haske ne ya gauraye dakin ta dan rufe idon sannan ta sake budesu. Kyakkyawar fuskar mijinta ta gani yana mata murmushi. Ita ma murmushin tayi masa sannan ta dago hannuwanta miko min baby dina. Kukan Hajjaju taji tayi saurin juyawa tana kallonta. Hajjaju sai kawai ta fita waje tana kukan. Maryam ta kalli Mukhtar shima hawaye yake sosai kamar karamin yaro. Daga nan hankalinta ya soma tashi ta tashi zaune me ya faru? Rungume ta yayi yana kuka kiyi hakuri baby din bata zo da rai ba. Kirjinta kamar ya buga don tsoro da firgici. Itama kukan ta soma sai can tace ba komai mijin ai wannan ma ba wayon mu bane ya bamu. Allah zai bamu wani wannan dai guzurin qiyama ne. Ji yayi ya kara sonta, Maryam akwai tawakkali. Ta dago kai tana share masa hawaye to meye na kukan ashe kai rago ne ban sani ba? To ka kwantar da hankalinka ina yin arbain zan sami wani cikin. Dan murmushi yayi tace ina baby din? An kaita wani daki suna jira musa hannu a bamu mu binne. Maryam ta tashi da kyar yana rike da ita yayi mata jogara zuwa dakin. Nurse din da ta ke dakin lokacin haihuwarta  tana ganinta ta karaso ta kaita ciki. Bude musu wani abu kamar dan akwati aka yi baby din na kwance a ciki. Jikinsu duk a sanyaye Maryam ta karewa yarinyar kallo tana kuka a hankali. Har zata juya ta kula da hannun yar...a firgice tace ina daya yastsan? Mukhtar yace wanne kuma, ga su nan kina gani. Maryam ta fara daga murya tana kuka wallahi abinda na haifa yana da cindo. Yatsun hannun shida ne. Ta dubi nurse din tana fada da turanci ku bani baby dina. Mukhtar tace baby din fa bata ma zo da rai ba. Maryam tace KARYA NE tana taba kunnuwanta tace da kunnen nan naji kuka kuma da idanuna naga yatsun hannun. Ni dai ban sani ba ko mace ne ko namiji amma ka yarda dani naji kuka. Mukhtar dai da kyar ya fitar da ita daga dakin suka koma tana ta masifa. Cikin kankanin lokaci jininta ya hau ta fara zubar da jini sosai fiye da yadda ya kamata. Ba shiri likitoci suka taru a kanta. Tasha allurai da drip sannan tayi bacci.

Sai bayan kwana biyu ta dan ji saukin  jikinta. Dr Gupta da wani likitan suka sake zuwa dubata. Tana ganinsa ta soma kuka ita ya bata baby dinta. Ta tabbatar mai rai ta haifa kuma mai yatsu shida. Idan  har ya mutu a bata gawar ta gani. Dr Gupta dai yace sumbatu take saboda firgici. Shima Mukhtar ya yarda don a tunaninsa ko maganar da suka yi ne da ya fada mata duk danginsu ana haifar mai cindo shine tasa rai. Duk yadda suka yi da ita taki yarda. Da kyar suka samu tayi shiru. Dr Gupta da abokin aikinsa suka bawa Mukhtar report din gwaje gwajen da aka yiwa Maryam. A nan suka tabbatar musu Maryam da wuya ta sake samun ciki.

A razane Mukhtar ya juya don yaga yanayin da Maryam ta shiga. Bakin gado ta samu ta zauna kusa da Hajjaju. Idanunta ko digon hawaye babu sai addua take a zuci Allahumma ajirna fi musibati wa akhlifna khairan minha. Tun tana yi a zuci har muryarta tana rawa ta fito fili. Mukhtar yasan tsabar gigicewa ce sai ya zauna a bakin gadon ya riko ta. Ta fizge hannunta idanunta a kafe a kansa tace Mukhtar na yarda da kaddara na kuma godewa Allah da dukkan ni'imarSa gareni. Amma ka sani wallahi abinda na haifa mai rai ne kuma da yatsu shida a hannuwansa. Yace matar kiyi hakuri ki dena zancen nan don Allah. Idanun nan nata a soye tace har in mutu bazan dena bincike da nema ba. Idan ya mutu Allah Yasa mai ceto ne garemu idan kuwa mai rai ne wallahi kotu ce zata rabamu da kai ta nuna Dr Gupta. A wannan yanayin ta takurawa Mukhtar su koma gida ta karasa warkewa a nan. Kudin  da matar ta bayar ya biya ba tare da kowa ya sani ba aka sanar da Mukhtar wani mai tausayinsu ya dauki nauyin su.

Tun da Maryam ta fara tashin hankali akan baby dinta da rai yazo kuma mai yatsu shida hankalin Survi ya tashi. Ita ce nurse din da ta taimakawa Dr Gupta wurin nemo gawar baby da bawa wannan matar baby din Maryam. Gaba daya ta kasa nutsuwa, kudin da aka bata ma ta kasa amfani dasu. Kullum taga halin da Maryam ke ciki sai tayi kuka. Dr Gupta na ganin halin da take ciki ya ritsata a office dinsa akan cewa ta bar asibitin gaba daya don idan ta kuskura ta tona masa asiri ba ita ba hatta yan uwanta sai ya kashe su. Jin maganarsa da yadda ya nuna rashin imani wurin raba mata da baby dinta duk da ya tabbatar Maryam din da wuya ta sake haihuwa ya tsorata ta. Ba shiri ta hada kayanta da yan marayan 'ya'yanta biyu ta bar garin.

Maryam kuwa sun koma gida tasha kuka sosai a wurin mahaifiyarta Ammi. Umma babar Mukhtar ma tayi ta rarrashinta. Haka suka rinka lallabata kowa na kokarin kyautata mata. Mukhtar na kulawa da ita tare da nuna mata so sosai.  A zahiri sai ta nuna musu ta hakura har ma ta dage Mukhtar sai yayi aure tunda shi lafiyarsa kalau. Amma ta kudiri niyyar tsananta bincike game da abinda ya faru a asibitin. Ta tabbatar cikin hankalinta taji kukan baby kuma taga yatsu shida.






Batul Mamman💖
[6/10, 5:46 PM] Fatima 💖: RUQAYYA YAR ALBARKA✨4




BAYAN SHEKARU

A hankali yake saukowa daga benen jirgin yana tafiya yana waya. Bakar suite ce a jikinsa da bakin wando, sai farar shirt wadda ya bar maballai biyu na sama a bude. Kafarsa bakin takalmi ne cover shoe da bakar safa sai suka fito da haskensa. Bayansa kuwa wani siririn mutum ne dan baki yana fama da jaka. Da sauri yake bin bayan mai wayar  yana kokarin kada yayi masa nisa. Suna gama saukowa motoci biyar ne suke jiransu a kasa daga gefen jirgin duk bakake suna ta sheki. Bai dena wayar ba ya karasa gaban motar dake tsakiya wani mai sanye da bakaken kayan da bakin tubarau yayi saurin bude masa bayan motar ya shiga. Sunyi tafiya mai dan nisa sannan ya ajiye wayar ya kwantar da kansa jikin kujera tare da lumshe ido. Burinsa kawai su isa gida yaga Mom dinsa. Duk da cewa wata biyu kenan da ta kai masa ziyara Manchester inda yake karatu amma kewarta duk ta ishe shi.

Wani makeken gida suka nufa. Duk wurin yafi kowane gida kyau da tsari. Girmansa kuwa zai dauki akalla gidaje goma manya. Bangare bangare ne a gidan ga swimming pool, lambu mai dauke da kayan marmari kala kala da kayan lambu masu kyau. Daga gefe kuwa wani madaidaicin zoo ne ga dabbobi daban daban a cikin kejinsu. Sai wurin ajiye motoci wanda shima motocin ne da yawa a wurin.

Tun kafin ayi horn aka bude gate din saboda tarbar babban bako. Yan mata ne da maza sun kai ashirin duk sunyi layi an sa carpet tun daga daidai inda motar tsakiyan ta tsaya. Ana bude motar matan masu sanye da rigar atampa iri daya iya gwiwa da maza masu gajeren wando irin na atampar da bakar shirt suka hau watsa masa flower. Idanunsa kyam a kanta ya fito da hanzari ya nufo ta. Wani irin kallo tayi masa mai nuni da ya nutsu ya dena tafiya da sauri. Ba yadda zaiyi dole ya rage saurin. Sai da ya rage tazara kadan tsakaninsu ya yi gudu ya karasa ya rungumeta. A kunnenta yace I miss you Mom. Itama hawayen farinciki take tace I miss you too my son. Sauran mutanen da suke tsaye a wurin suka dauka lokaci daya welcome home Prince Richard. Ko kallo basu ishe shi ba ya juya ga kakarsa ya rungume. Grandma kin kara tsufa fa. Ta ja masa kunne Richie da tsokana ka dawo ko. Yana dariya wadda da wuya ake ganinta yace Mom ina Dad ne? Ta danyi murmushi suna da meeting ne amma nan ba da dadewa ba zai shigo. Ta ja hannun danta zasu shiga gida yarinyar gefenta wadda tasha kwalliya tayi dan gyaran murya. Sanye take da riga doguwa har kasa fitted mai siririn hannu. Gashin kanta ya sha kari anyi mata kalba kanana sai kamshi take. Mamansa tace Richie ga Princess Sophia tazo taya mu murnar dawowarka. Idanunsa suna karewa surar jikinta kallo ya kama hannunta ya kai bakinsa ya yi kissing. Yayiwa mamansa kallon tuhuma yana son karin bayani. Ta kifta masa ido sai sun shiga ciki.

Sai da suka gama meeting ya fito cikin sauri. Ba don kada fadawansa su raina shi ba shima da gudun zaiyi ya isa ga tilon dan nasa. Ana bude masa kofar hall din suka hadu shima saurin yake yaga babansa. King Edward ya rungume dansa suna ta murna. Tare suka zauna a dinning table suka ci abinci kala kala da aka jere domin murnar dawowar Prince Richard. Daren ranar sunsha hira sosai da dan nasu. Har Sarkin yana sanar dashi washegari an shirya liyafa a fada domin murnar dawowarsa. Richie kamar yadda iyayensa suke kiransa yace ni dai bana son taron nan Dad. Duk hayaniya zata cika min kunne. A shagwabe yake maganar wadda suke yinta da turanci. King Edward yace sai dai kayi hakuri amma dole alummar garin Ndam su fito domin nuna farincikin dawowarka gida lafiya da birthday dinka da ya wuce tun last week. Yarona yayi shekara ashirin da biyar dole nayi celebrating. Princess Sophia tace haba Prince kada ka hana mu nuna murnarmu mana. Yarinyar nan tana burge shi sai kawai ya daga kai. Magana bata dameshi ba, idan kaji yana faraa ko wasa to iyayensa na kusa ko kakarsa ta wajen uwa don iyayen babansa sun dade da mutuwa.
*********

Da kyar Fatima ta iya tashin yarta daga bacci. Iya Tasallah tana daga falo tana jin yadda surukarta take ta fama da autarta akan ta tashi tayi shirin Islamiyya. Ruqayya ta sake tura kanta cikin bargo haba Mami don Allah ki bari na kara baccin minti goma kacal. Fatima ta ce to kwanta amma ki sani idan na dawo ruwa zan watsa miki. Fatima na fita Ruqayya ta sauko daga kan gadonta da bismillah. Bacci ne sosai a idonta amma bata son makara saboda bulalar malam. Sai da ta sake maimaita tilawar haddar da ta hana ta kwanciya da wuri ta tashi. Daga falo taji Iya Tasallah tana cewa haba Fatima kiyiwa Allah kada ki watsa mata ruwan nan yar albarkar guda. Fatima ta yi murmushi to Iya na fasa amma yau idan aka yi mata bulalar makara sai dai tayi kukan a waje. Suna zaune a falon ta fito da uniform dinta. Riga ce doguwa light blue da hijab shima kala daya. Da yake yau asabar tun tara suke fara karatu. Har kasa ta durkusa ta gaishe da kakarta sannan ta wuce ta sha tea kadan cikin sauri ta dauki jakarta. Mami tace yau wata zata sha duka idan bata yi sauri ba. Tun dazu su Abida suka tafi. Ruqayya ta fita da sauri tana fargaba. Tara da kwata yau ita da Malam Hafiz zasu yi drama don ta tsani duka. Ko da ta fita makotansu ta shiga suka gaisa aminiyar mamanta Anti Gaji. Ta dan sunkuyar da kai a ladabce Anti don Allah Yaya Munir yana nan? Murmushi Antin tayi tace yana nan yar albarkar Mami. Yau ma anyi abin ne? Suna haka Munir ya fito yana waya. Kusan minti biyar Ruqayya duk ta gama rudewa don makarar tata tayi yawa. Kawai hango M. Hafiz take yana lafta mata bulala sai ga hawaye. Anti Gaji tace haba Munir wace irin waya ce wannan kana kallo har ta fara kuka. Kasan halin abokinka na duka. Munir ya ajiye wayar yace yi hakuri yar albarka zuwa zanyi na bashi hakuri don nasan abinda ya kawoki kenan. Shi ya isa ya doki kanwata ma. Har zasu fita yace  Mama abokina ne Richard ya dawo har ya gama karatu mu strike yasa muna level 3. Anti Gaji tace Allah sarki bai manta ka ba. Haba dai Mama shi ya isa ma. Tace ai ban taba ganin mutum mai ji da kai irinsa ba. Haduwar jininku tana bani mamaki. Kukan Ruqayya suka ji tana yi iya karfinta. Gara ta fara kukan tun a nan tunda yau ga dukkan alama Yaya Munir din ma bashi da niyar taimakonta. Anti Gaji na kiranta ko juyowa bata yi ba ta fita tana kuka.






Batul Mamman💖
[6/23, 10:10 PM] Fatima 💖: RUQAYYA YAR ALBARKA✨5




Ko da ta fito makarantarsu ta wuce. A ranta tana rayawa yau daya dai bazata yi kukan bulala ba. Tana isa bakin gate din ta hango Mal Ghali yana zuga wa wata yarinya bulala. Duk bulala daya ji take kamar a jikinta ne. Kafin a gama yi mata shida Ruqayya fuskarta ta jike da hawaye tamkar ita ake yiwa. Bata ankara ba taji muryar malamin ajinsu Hafiz yana cewa Ruqayya Muhammad. Ai tamkar ta saki fitsari don firgici ta fice daga makarantar da gudu. Ta danyi tafiya sai kuma ta fara fargabar komawa gida. Tasan Mami da kanta zata zaneta idan tayi fashi. Can wata kyakkyawar idea ta sauko mata....wani guntun murmushi tayi harda dungure kanta. Tuni ta canja hanya ta fita daga layin islamiyar. Tana tafiya sai a layi na biyu ta shiga tana tafiya tana waige waige kada ta hadu da idon sani.  Tana ganin gidan ta gane shi saboda girmansa da kyan tsarinsa. Karamar kofar kusa da makeken gate din ta wucewar mutane ta nufa. Ta tura iya karfinta kofar taki budewa sai ta sami dutse tana bugawa. Daga ciki taji ance waye? Ta ce Ruqayya ce aikoni akayi. Maigadin ya bude ya dubeta. Karamar yarinya ce da bazata wuce shekara goma sha biyu ba. Bata da haske sosai ga dan dimple a kumatunta na dama da yar wushirya. Yar kyakkyawa da ita.

Maigadin yace wa kike nema? Yadda ta ganshi gabjeje ya so ya bata tsoro sai ta dake. Tace wurin barrister nazo. Yace barrister ko matarsa? Ruqayya ta danyi turus tohhh...ita dai tasan ana cewa ga gidan barrister amma bata ma san mace bane ko namiji. Tayi saurin cewa wurin matar nazo. Za ta samowa Mamina gidan aiki ne shine ta aiko ni tambayar ko an samu. Shi dai maigadin yayi mamaki anya gidan take nema kuwa. Daya maigadin yace kaga ka korata gida kila bara tazo yi. Dama hawayenta na kusa ta soma tana rokonsu. Dole suka barta ta wuce mai shara yana aikinsa.

Wata kofa ta gani ta je tana bugawa sai ga wata budurwa tazo ta taga tana yi mata nuni da ta zagaya. Da sallama ta shiga harda gaishe da yan matan da ta gani suna ta aiki. Daya na goge falon dayar na jera plates akan dinning table. Ruqayya ta kalli wadda tafi kusa da ita don Allah mamanku tana nan? Suka dan murmusa hajiya yanzu ta gama girki ta hau sama amma bari na fada mata. Ba jimawa ta dawo tace ki jira tana shiryawa amma dawo daga nan. Wasu kujeru uku ne a dan lungu da dan table a gabansu. A tsorace ta zauna sai gashi an kawo mata karamin tray da plate wanda aka rufeshi da wani. Sai juice din kwali da cup din tea. Yarinyar ta ce mata ki ci kafin Hajiya ta sauko. Ruqayya ta fara zare idanu lokaci fa kara tafiya yake. Yau Mami kila ma yankata zata yi idan taji labarin abinda tayi, ga cin abincin gidan mutana..tabdijam. Ta tashi da sauri ni dai na tafi kawai na fasa tambayar ma. Taku taji daga benen alamun ana saukowa sai kuma taji muryar babban mutum yace  dawo ki zauna.

Hantar cikinta ta kada ta bi benen da kallo. Kasa dauke ido tayi tana kallon mutanen da ke saukowa a tare. Mijin dogo ne fari mai dan jiki kadan yana sanye da dogon wando da farar jallabiya, matar kuwa duk da bata kaishi haske ba itama ta hadu. Riga da zani ne atampa a jikinta ta daura dankwali amma gashin da ta tufke har kusan rabin bayanta. Mutane ne masu kwarjini da kamala. Suka karasa saukowa ta durkusa har kasa ta gaishesu. Yarinyar sai ta basu shaawa. Ta mike tsaye don Allah ku bari na tafi kada Mami tace nayi kwadayi. Haj Maryam ta yi mata murmushi ai tunda kika shigo nan ya zama gidanku. Mamin bata fada miki mutum baya kwadayi a gidansu ba? Ki ci abincin sai ki fada min abinda ya kawoki. Ruqayya tuni idanu sun cika da hawaye zata soma kuka don ta gama tsorata. Mijin matar ne ya durkusa a gabanta ya rike mata hannu. Haba yar albarka meye na kuka kuma? To da kaina zan kaiki gida in hana a taba ki. Hawayen na zuba ta dago kai tana kallonsa, dama kasan haka su Abba suke kirana a gida yar albarka? Haj Maryam tace mun sani mana ai mu ma iyayenki ne. Yanzu dai kici abinci kada ya huce kinji. Mu ma zamu ci namu sai muyi magana nasan aikoki akayi ko? Ruqayya ta gyada kai.

Plate din ta bude taga soyayyen dankali da kwai da sauce din nama. Gabanta ya fadi...badai abinda take jin labari bane ya zo kanta. Dama ance duk gidaje manya masu kyau na satar mutane ne. Sannan kuma sai sun bawa mutum abinci mai kyau yaci don ya kara kiba naman jikinsa ya kara yawa. Ta daga kanta taga yadda mutanen ke cin abinci suna kallonta suna murmushi. Jikinta ya suma bari so suke taci ta fara bacci. Allah Sarki Mami ashe yau  ganin karshe tayi mata, ita ma iya Tasallah kakar Abbanta ashe bazasu sake haduwa ba. Da ta tafi islamiyar da tuni dukan M. Hafiz ya dena zafi. Idan yaji dadin haddarta ma har alawa yake bata. Ta dafe kai oh ni Ruqayya shiyasa M. Hafiz yace karya ba kyau. Daga nan sai kuka hawaye wani na bin wani. Barr Mukhtar da Haj Maryam suka kalli juna hankali a tashe.







Batul Mamman💖
[6/23, 10:30 PM] Fatima 💖: RUQAYYA YAR ALBARKA✨6





Tare suka taso daga dinning table din suka dawo gabanta. Haj Maryam ta dafa mata kafada dena kukan ki fada min sunanki kinji 'yata. Da kankanuwar murya tace Ruqayya. Barr Mukhtar yace to fada min abinda ya kawoki yana mata murmushi. Tasa hannu ta share hawaye idan na fadi gaskiya zaku barni in tafi gida? Haj maryam tace me zai hana Ruqayya. Sai lokacin hankalinta ya dan kwanta tace to waye barrister mai shiga kotu a cikinku? Barr Mukhtar yayi murmushi yarinyar is so cute ina ma....sai yayi saurin kawar da tunanin. Nine barrister din. Ta ce to kara na kawo amma na fasa yanzu kawai ku barni in tafi gida. Yace da kaina zan kaiki gida amma ki fada min abinda yasa kika zo ba tare da kowa ba. Shekararki nawa ne? Ruqayya tace shadaya zanyi nan da sati biyu. Amma fa mu gidanmu Abba baya mana birthday. Sai dai yayi wa mutum addua kawai. Haj Maryam tace ai hakan yafi. Ruqayya ta cigaba karar M. Hafiz na kawo na islamiyarmu. Daga nan ta fara bada labarin yadda yake duka da dalilinta na kin zuwa yau. Ta ce ni dai so  nake ka zama lauyana ka yanke masa hukunci a kotu. Dariya sosai suke yi mata ita kuwa ko a jikinta ta cigaba da bayani. Bana so a rufe shi a gidan yan kurkuku amma ayi masa fada ya dena duka. Ita kuma Mami sai ka fada mata a hanya kaga ina kuka ka tambayeni. Ta dan zare ido, idan taji da kaina nazo sai ta zane ni. Ko Iya Tasallah tayi mata fada sai tayi. Hmmm shine abinda Maryam ke fada. Yarinyar akwai wayo. Tace to Barr aiki fa ya sameka. Yayi dariya sosai ma kuwa. Amma Ruqayya baki fadi nawa zaki biyani ba. Nan tayi tsilli tsilli da ido. Can tace ai kaga yanzu na kusa gama primary idan duk na gama na fara aiki sai na biya amma da nayi tunanin zaku ji tausayina ku yi min a kyauta. Idan kayi kyauta sai ka fi samun lada. Shi da matarsa kallon juna kawai suke suna jindadin yadda take magana. Yace to an gama Ruqayya kyauta zanyi miki. Yanzu tashi mu tafi ko. Haj Maryam ta dage sai ta bi su. Barr Mukhtar yace jira mu shirya sai mu tafi. Har suka hau sama suna dariyar shirmen Ruqayya.

Suna bakin mota Ruqayya ta hango masu gadin sai tace da Haj Maryam bari in fadi wata gaskiyar kada Allah Ya kona ni. Dazu karya nayi wa masu gadin ku shine suka barni na shigo. Barr da yake gefen su yace to mun yafe tunda kina fadin gaskiya amma ki dena karya nan gaba babu kyau. Allah Yayi miki albarka. Tace amin sannan ta shige bayan jeep din da dreba ya bude. Barr ya karbi key din motar ka zauna ba nisa zamuyi ba. Ya shige mazaunin dreba da matarsa a gefe. Ruqayya ta dan leko da kanta tsakaninsu  tace in rinka kiranki Anti? Haj Maryam hawaye take kokarin boyewa na tausayin kansu na rashin haihuwa tace a'a ki samar min wani mai dadi banda Anti. Ni ma mamanki ce fa. Ruqayya tace to sunanki Mummy irin yadda kawata take fada. Shine na yan gayu. Haj Maryam tace yanzu ni yar gayu ce? Ruqayya ta gyada kai sosai kuma wallahi kina da kyau kamar Mamina. Barr yana tuki hankalinsa duk yana kansu yace to ni kuma fa Ruqayya nima babanki ne ko? Tace eh mana. Sai ta dan yi tunani tace Abba barrister zan kiraka yadda zan ganeka da Abbana. Ya dan waigo amma sunan yayi tsayi. Haj Maryam tace to mun rage maka ka koma Abba B. Suna tafiya suna hira. Rabon da yaga Maryam cikin farinciki irin wannan tun ranar bikin Nadiya daya daga cikin 'ya'yan Hajjaju da suka rike.

Suna isa gate din makarantar hankalinta ya tashi. Jiki a sanyaye suka ce ta fito. Tare suka tafi office din shugaban makarantar tana rufe fuska da hijab dinta. Shugaban makarantar yana hango Barr Mukhtar ya taso daga office dinsa da sauri yana murmushi yace ranka ya dade yau kaine a makarantar tamu? Suka yi musabaha Barr yace Alh Saleh ya aiki? Alhamdulillah ya bashi amsa amma idonsa na kan Ruqayya. Yace koma aji tunda kin rakosu. Barr yace ai tare muke ba rakiya tayi ba. Alh Saleh yace to ku shigo ina fata lafiya dai.

Bayan sun zauna Barr yace Alh karar ku aka kawo min. Cikin Ruqayya ya bada sauti don tsoro wai wa ya aike ta ne. Ya cigaba da magana a kira min M. Hafiz don yau zan yanke masa hukunci. Kurkuku zan kai shi,yana magana yana kallon Ruqayya.  Ai kuwa ta tashi zumbur tace   Abba B na fada maka banda kurkuku. Mummy ki bashi hakuri ko in tafi gida. Kukan nan ta soma jiki na rawa. Haj Maryam ta rungumeta yi hakuri wasa yake miki. Shi dai Alh Saleh tashi yayi ya tura a kira Mal Hafiz. Ba jimawa Ruqayya taji sallamarsa. tashi tayi da gudu har tana tuntube ta buya a bayan labule. Duk suka yi mata dariya harda Alh Saleh. M. Hafiz ya gaisa da Barr Mukhtar sannan ya  tsaya jiran dalilin kira. Barr yayi gyaran murya yana kallon bayan labulen da Ruqayya ta buya. Yarinyar ta shiga ransa lokaci guda. Yace M. Hafiz an kawo kararka kuma nine lauyan mai kara. lokaci guda jikin Hafiz yayi sanyi...kara kuma? Ji yayi kamar kafarsa bazata iya daukarsa ba. Ya dubi Alh Saleh wanda ke masa kallon tuhuma yace wallahi ranka ya dade ni bansan komai ba. A waje dai ina yin taka tsantsan cikin lamurana. A nan ma haka. Yarinya daya ce ma tun kwanaki ta nuna tana so na har wasika tayi min nayi mata fada taki ji saboda bata da kunya. Har zaneta nake amma duk a banza. Saboda ita na zama mai duka a makarantar nan saboda gudun zargi da fitsarar yan mata. Amma karshe cewa tayi sai ta kulla min sharri. Ya dan kalli barrister ko sunan  mai karar Lubna Hadi? Barr Mukhtar yace a'a karar taka ta shafi dukan da kake yiwa yaran da basu ji ba basu gani ba saboda laifin wata. An sami yarinyar da abin ya isheta har ta nemi taimako na. M. Hafiz na jin haka yayi dan murmushi yallabai ko Ruqayya Muhammad ce? Daga inda ta buya ta fito tayi sharkaf da hawaye M. Hafiz don Allah  kayi hakuri kaga Mummy ce ta ganni ina kuka shine ta tambayeni na fada mata tsoron duka nake. Haj Maryam tace lahhh  Ruqayya haka zamuyi dake ba dazu aka yi miki fadan karya ba. Ita dai Ruqayya duk ta tsorata gani take zaneta zaayi tace don Allah ni dai ka yi min bulalar kawai na tafi aji. Tana rufe baki taji sallamar Yaya Munir da Maminta.





Batul Mamman💖
[6/25, 6:49 AM] Fatima 💖: RUQAYYA YAR ALBARKA✨7




A tsorace Mamin ta shigo sai mamaki ya bayyana a fuskarta ganin mutanen da ke zagaye da 'yar ta. Tayi musu sallama tare da gaisawa da du. Ita kuwa Ruqayya tana ganinta ta kara bare baki tana kuka. Yau masu dukan nata suna da yawa. Mami kuwa farinciki ya mamaye zuciyarta ta janyo Ruqayya jikinta tana share mata hawaye dena kukan mana. Tana duban Alh Saleh tace ina zaune Munir yace min ya biyo bayanta zuwa nan. Sai dai kafin ya karaso gate din yaga ta juya da sauri ya rasa layin da ta shiga. Shine muka biyo baya muji abinda ya faru. Haj Maryam tace ki kwantar da hankalinki babu abinda ya faru. Nan ta labarta mata yadda Ruqayyan taje gidanta da dalilin zuwan nata. Ana fada kanta a kasa don tasan tayi laifi.

Sai da aka gama mayar da zance Barr Mukhtar yace to Alh Saleh kaji dai yadda tsoron duka yasa yarinyar nan ta kusa shiga matsala, domin kuwa Allah ne Ya tsareta. Da ta fada mugun hannu a kokarinta na guduwa da bamu taru a wurin nan ba. Hakika babu wani ilimi da zamu bawa yaranmu sama  da na addini sai dai kuma malamanmu sun dabi'antu da yawan duka. Katon saurayi yayiwa karamar yarinya bulala goma ko sama da haka da reshen bishiya ko dorina saboda makara, fashi ko rashin rike karatu. Ni a tunani na addini ya wuce haka. Ko kadan bai kamata mu dasawa yara tsoro irin wannan ba. Nan gaba sai kaga raini ya shiga tsakanin malamai da dalibai. Akan bulalar wasu sun gwammace suki zuwa makaranta gaba daya. Wasu su koyi karya kala kala da dai sauran halaye marasa kyau. Na sha gani ko jin malamai masu duka har sai bulala ta karye. Kunga daga karshe maimakon yaran su sami tsoron Allah sai su tashi da tsoron malam. Karatun ma duk ladan da ke ciki sai suyi saboda gudun duka ba don neman yardar Allah ba. Ya zama dole mu dage wajen ganin yara sun sami ilimin islama mai yawa su zama hafizai da malamai. Amma idan suka tashi da irin  mugun dukan nan  zukatansu bushewa suke. Abinda ake nema sai a rasa shi. Ya kamata iyaye da malamai mu hada kai wurin samar da wani nau'in horon ga yara wanda ba zai zama cutarwa garesu ba. Sauran kasashe kamar na larabawa ai basa irin wannan dukan kuma gashi ana samun manyan malamai a cikinsu. Idan ma dole sai anyi to a duba ayi na hankali ba irin wanda zai sa yaro ya dawo gida da jiki a fashe ba.
Muma iyaye kuma mu dena dauke kai ga lamuran yara irin haka. Su amana ne garemu dole mu kula da hakkinsu. Misali yanzu Ruqayya na tabbatar da ta san iyayenta zasu taimaka mata akan halin da take ciki babu abinda zai sa tazo gidana. Yau da wani ta hadu tashi kila ya cutar da ita yadda mutane suke ba gaskiya yanzu.

Maganganun barrister sun shigesu gaba daya. Ya cigaba da cewa horo ga yaro ko dalibi dole ne amma farfasa jiki da duka bashi da muhalli a addini. Annabi SAW ya koya mana tausayi da rangwame ga na kasa da mu. Amma abin takaici a wurin koyar da karatu wani lokacin ma yaran suna karatu sai malami ya rinka binsu da bulala kawai don nishadi ko idan yaji muryarsu tayi kasa kasa shi a dole kada a raina shi. Ina so duk ku fahimce ni....yaro sai da horo don a tankwara shi amma idan yayi yawa zamu ragewa 'ya'yanmu tausayi da jin kai a rayuwarsu ta gaba. Allah Yasa mu dace. Gaba daya suka ce AMIN. Alh Saleh yayi godiya sosai ga Barr Mukhtar yace idan Allah Ya yarda zai tabbatar da kawo gyara a wannan fannin a makarantarsa. Mal Hafiz ya bawa Mami hakuri sannan ya dubi Ruqayya da  ke sharar hawaye yace kiyi hakuri Ruqayya ina fata zaki yafe min. Ta dan dago kanta kana nufin duk abinda nayi bazaka zaneni ba? Haj Maryam tace ai ke da duka yata sai na ruwan sama. Tashi ki tafi aji Allah Yayi miki albarka. Mami taji dadin adduar sosai tace amin Hajiya mungode sosai. Allah Yayi wa naki yaran albarka a duk inda suke. Ba Haj Maryam ba hatta mijinta sai da zuciyarsa ta yi masa zafi ba don rashin son adduar ba sai dai ta zama fami ga halin da suke ciki. Mami bata lura ba ta cigaba da magana...Abbansu yayi tafiya amma idan ya dawo har gida zamu zo sake yin godiya. Allah Ya bamu ikon zumunci mai dorewa. Haj Maryam tace amin amma fa daga yau Ruqayya ta zama mai iyaye biyu. Duk aka yi dariya sannan suka yi sallama kowa ya tafi.






Batul Mamman💖
[6/27, 6:57 AM] Fatima 💖: RUQAYYA YAR ALBARKA✨8




Washegari da yamma Engr Muhammad Hamza ya dawo daga Lagos inda yaje wani aiki da aka tura shi daga office dinsu na Kano. Shi maaikacin nepa ne kuma suna da rufin asiri daidai gwargwado. Shekarunsu goma sha shida da aure shi da Fatima suna da 'ya'ya uku duk mata. Hidaya ce babba mai shekaru sha biyar sai Abida yar shekara sha biyu sannan Ruqayya mai neman shekara ta shadaya.  Suna zaune ne tare da kakar Engr Muhammad da suke kira Iya Tasallah. Sauran yan uwansa duk mata ne shiyasa ya dauko kakar take gidansa tun bayan haihuwar Hidaya. Dukkansu yan Kano ne kuma suna zamansu lafiya.

Bayan yayi wanka yaci abinci iyalinsa sun zagaye shi Mami ta bashi labarin abinda Ruqayya tayi. Yaji dadin abinda tayi amma sai da ya fara yi mata fadan zuwa gidan mutane ba tare da izini ba. Iya Tasallah tace haba babana ai anyi mata fadan nan ku dai ku cigaba da sa musu albarka da yardar Allah rayuwarsu duniya da lahira bazasu tabe ba. Mami tace Iya ba kya son dai a rinka musu fada. Ta tauna dan guntun goronta ba haka bane Fadimatu kullum ina fada muku kada ku taba kiran yaranku fitinannu ko marasa jin magana. Indai zaku jure sa musu albarka to da ranku da lafiyarku sai kunga albarkar nan. Ta dan share hawaye ai dai kunfi kowa sanin ina sauran da mai rai da lafiya da arziki amma saboda irin bakin da nake binsa dashi na zagi da mummunan fata idan yayi ba daidai ba yau sai yayi shekara ban ga keyarsa ba. Dukiyarsa muna tare daku amma zance yana dawo mana ta haram ce da handamar dukiyar talakawa. Abba yace zamu kiyaye Iya. Mami tace gobe idan ka kara hutawa sai muje gidan baristan ko? Ruqayya tayi saurin cewa Abba don Allah nima zani. Abida ta ce kin ma isa aje dake a barmu a gida? Yaya kinji ta fa. Mami tace to zaku fara ko...ku tashi ku bar Abbanku ya huta duk zamu je daku in Sha Allah.

Da murna  Ruqayya ta kwana don zata sake ganin Mummy kamar yadda ta lakabawa Haj Maryam. Sai dai sunyi rashin sa'a suna zuwa masu gadi suka sanar dasu sun fita unguwa. Abba ya bar sakon gaisuwa a sanar dasu iyayen Ruqayya ne.

Haj Maryam da Barrister zaune gaban Umma mahaifiyarsa. Tsufa ya soma kamata tana zaune kan wani tattausan kafet tana kallonsu daya bayan daya. Kan barrister a kasa yace don Allah Umma kada ki bari taje na sha fada miki abinda zai kaita wallahi ba aiki bane bincike ne. Nasan halinta sarai duk shekarun nan bata taba hakura ba. A zahiri dai bata min zancen amma wasu lokutan cikin bacci sai naji tana cewa ita abinda ta haifa yana da rai. Tunda ya fara magana Haj Maryam ke kuka...Allah kadai Yasan ciwon da ke ranta saboda rashin sannin ainihin abinda ya faru da abinda ta haifa. Har akwai ciwon da ya wuce mace ta haihu ko ganin fuskar abinda ta haifa bata yi ba a canja mata da gawar wani? Zuciyarta kamar ta fashe duk lokacin da ta tuna yadda aka raina musu wayo a India kuma mijinta har yau ya kasa gaskata zancenta.  Umma tana ta kallon yadda tayi nisa da tunani ta kama hannunta ta rike. Hakan yasa ta dawo daga tunanin da take ta dago kai idanunta sunyi ja sosai. Ki kara hakuri da juriya Maryam shine abinda zan fada miki. Iya rabonku kenan da mijinki tunda kinga aurensa biyu bayan faruwar lamarin nan haka suke rabuwa da matan ko batan wata babu wacce ta taba yi. Sanin gaibu sai Allah amma ki dena barin abin yana damunki haka. Shekaru sama da ashirin ai an dade. Dama ni nake takura ku akan jikoki kuma na hakura da ikon Allah nagode Masa tunda kannensa duk suna da 'ya'ya. Haj Maryam tayi ajiyar  zuciya...Umma ni duk ba wannan ke damuna ba. Karo na biyar kenan da wurin aikinmu ke turani India yana hanani zuwa. Barrister ya tashi a fusace kuma bazan bari kije ba yanzun ma. So kike kije ki kara tadawa kanki hankali ku tafi tare da yan office dinku a aiko min jininki ya hau ko? Tace ba haka bane na fada maka na hakura don Allah Umma kisa baki. Umma ta ce indai na isa da kai to na bata izinin tafiya amma ku je tare kamar yadda kuka saba saboda tsare mutumcin matarka. Ko kadan ba haka Haj Maryam taso ba don a bincikenta ta gano shekarar da suka je a shekarar Dr Gupta yabar asibitin ya koma garinsu inda ya gina wani asibitin. A yanzu haka an fada mata yana daga cikin likitocin da kasar ke ji da aikinsu sosai. Har bayanai ta samu game dashi a internet tare da hotonsa. Ya kara tsufa amma bazata taba manta kamaninsa ba. Peace radio inda take aiki ne suka tura su seminar a matsayinta na babbar yar jarida shine take son amfani da damar wurin bincike sai dai kuma zuwa da barrister zai kawo mata cikas. Duk da haka tayiwa Umma godiya ta amince da tafiyar a haka.
*********

Kwance yake kansa na cinyar Mum dinsa tana sanye da glass tana karatun jarida. Shi kuwa idonsa a rufe yake yana sauraron karatun da take da karfi don ya ji. Bayi ke ta kai kawo suna kallon Queen Amelia da dan shagwabarta. A haka Princess Sophia ta same su ta fito tana ta rausaya. Yan kwanakin da tayi a gidan ta kamu da matsanancin son Prince Richard. Shima da farko yana dan kula ta sama sama amma tun ranar da babansa ya sanar dashi ita suka yanke shawarar aura masa ya fita harkarta gaba daya.  Saboda ita ya dena cin abinci tare da iyayensa a dinning table. Gani haka mahaifiyarsa ma ta dauke mata wuta. Sam bata sakar mata fuska a cewarta bata ga dalilin da za'a takurawa dan nata ba. Sai dai sarkin da abokinsa sarkin garin da ke makotaka dasu sun gama shawara aure ba fashi. Princess Sophia ta karaso ta zauna a kujerar kusa dasu tace your majesty kina kara shagwaba Richie da yawa. Jaridar ma sai kin karanta masa?...lallai bayan aurenmu ina da aiki. A hankali ya bude idanunsa yace kada ki sake kirana Richie, wannan sunan na iyayena ne kawai. Bata yi fushi ba tace to kayi hakuri na dena. Akwai sunaye masu dadi da zan rinka kiranka dasu daga yanzu. Queen Amelia ta ce Sophia da kin hakura kunyi zumunci kawai da Richie ina guje miki ya aureki ki kasa samun kulawarsa saboda rashin so. Muryar King Edward suka ji yana cewa indai so ne a hankali zai zo. Dole ne yayi hakuri yabi umarni na idan har ya damu da sarautar garin nan. Queen Amelia da Sophia duk suka tashi tsaye saboda girmamawa ga sarki har ya zauna. Shi kuwa dan shagwabar jira yayi mum dinsa ta koma mazauninta ya sake dora kansa a cinyarta. Sarki yace duk kayi ka gama likewa jikin mamanta aure ya zama dole. Ke Sophia kama shi ku tafi dakinsa ya kwanta a can. Ba kunya ta tashi  tana mika hannu ya doke shi ya tashi a fusace...Dad na fada maka bazanyi aure nan kusa ba sannan ko zanyi, to zan nemo matar da kaina. Haba shekaruna 25 fa amma duk kun matsa min. Har na fara dana sanin dawowa. King Edward yace idan baka dawo da kafarka ba zansa a dauko min kai ne. Har ka manta nan da karshen shekara zan nada ka crowned prince..kai ne zaka gaji sarauta idan na tafi ga magabatanmu. Dole kuma ayi nadin tare da baiko. Biki kuma zamu yi shawara da babanta ya nuna Sophia.  Zai sake magana wayarsa ta soma kara kamar kada ya dauka da farko ,sai da ya ga sunan mai kiran ya dauka tare da fadada murmushinsa wanda ya kara masa kyau ya kuma kara masa masauki a zuciyar Sophia. Mutumin da ya rika a matsayin amini ne ya kiran shi.  Bakin swimming pool yaje ya amsa wayar yana ta fara'a. Ba jimawa ya koma falon ya sanar da iyayensa zai je Kano ziyartar abokinsa Munir. King Edward yace bazan hanaka zuwa ba amma dole ka tafi da guards da yawa ban cika son hulda da hausawa ba. Shima Munir din don banga ta yadda zan iya rabaku bane. Queen Amelia tace ta ina zaka raba abotar shekara shida tun suna JS1? Idan kaje dai kada ka dade kuma ku dawo tare don ya kamata nasan abokin nan naka a zahiri. Princess Sophia ta dawo kusa dashi ta tsaya tare da rike masa hannu amma tare zamu tafi ko my prince? Kaga sai mu sami fahimtar juna. Wani mugun kallo yayi mata wanda yasa ta sakar masa hannu ba shiri.






Batul Mamman💖
[6/29, 9:02 AM] Fatima 💖: RUQAYYA YAR ALBARKA✨9




Ruqayya na zaune gaban Abbanta tana tilawar surar da zata karanta ranar walimar saukar Hidaya. Saura kwana biyu gidansu ana shiri kamar masu biki. Muryarta akwai dadin sauraro saboda dadin kira'ar ta. Cikin nutsuwa take bawa kowanne harafi hakkinsa. Abbanta har wani lumshe idanu yake yaji tace SADAQAL LAHUL AZEEM. Yayi murmushi ya kalleta yar albarka kamar kada ki dena karatun nan. Allah Ya sakawa M. Hafiz da alkhairi. Tace amin sannan ta tashi ta haye cinyarsa. Abba baka manta kace zaka siya min sabon keke ba ko? Keke kuma Ruqayya ai kin girma ki yi shawara da yayyanki dai ki nemi wani abin. Bata jira taji karshen maganar ba ta tashi tana kuka. Yana ta rarrashi taki yin shiru. Mami dake kitchen tana jinsu tace ba ina fada maka ta fiye rigima ba sai kaki yarda. Gara ta gwada maka halin...maza Ruqayya cigaba da kuka kada ki yarda sai ya siyo miki keken nan. Ai kuwa taji zuga ta kara sautin murya tana kuka Abida da Hidaya suna kara tunzura ta. Abba yace na fuskanci kun hade min kai ne amma zanyi maganinku. Sallamar da suka ji ta hana shi jifan Abida da pillon kujera.

A yanayin da ta gansu sun matukar bata shaawa sannan hakan ya kara tuna mata da halin da suke ciki. Tana ji tana gani banda wurin seminar da suka je Barrister baya bari taje koina ita kadai sai ya bita. Dole ta hakura da binciken suka dawo gida. Ruqayya na jin muryarta ta gane ta. Da gudu taje ta rungumeta. Mummy kin dawo? Tayi murmushinta mai kayatarwa na dawo 'yar albarka waye ya taba min ke kike kuka? Mami ta fito tana goge hannu Hajiya sannu da zuwa...ga wuri ki zauna mana. Tana rike da hannun Ruqayya suka zauna tare sannan ta gaisa da Abba da Mami har take basu sakon gaisuwa daga barrister. Su Hidaya ma suka gaisheta. Abba ya tashi zai shige daki ya basu wuri ya kalli Ruqayya idan baki dena kuka ba muryarki zata dashe karatun ki ya zama mara dadi. A take ta hadiye kukan don banda duka babu abinda ta tsana kamar ace kararunta babu dadi. Mummy tace fada min dalilin kukan ko kun ci zalin 'yata ne ta tambayi su Abida. Yan matan sai murmushi suke mata suka ce a'a. Duk suna yanayi da juna. Da tana da nata yaran kila suma suyi kama......sai tayi saurin barin tunanin dake sata shiga yanayin damuwa idan ta biye masa. Tsarabar riga da wando irin na pakistan pink and light blue ta kawowa Ruqayya masu matukar kyau. Da jakar makaranta harda wani pink din takalmi da yar jaka ta gayu. Murna sosai Ruqayya ta yi tana ta godiya. Mami kuwa har daki ta kaiwa Abba kayan shima ya fito yayi mata godiyar. Daga nan suka gayyaceta walimar Hidaya ranar asabar. Har bakin mota Mami ta raka ta. Duk da dai Haj Maryam ta girmeta amma tana da mutumci. Ko da Iya Tasallah ta tashi daga bacci aka nuna mata kayan itama tayi godiya da addua ga wadanan bayin Allah.

Harabar makarantar babu masaka tsinke saboda makaranta ce babba  garin kano. An gayyaci mutane da dama da malamai. Karo na uku kenan da ake yaye dalibai wadanda suka yi haddar hizfi sittin da arba'una Hadith na Annawawi. Sai bayan shekaru bibbiyu ake yaye daliban. A filin da ke bayan makarantar ake taron. Bangaren mata daban na maza daban sai na dalibai maza da mata suma daban daban.

Yan sauka matan duk sun sa hijab ruwan madara dogo mai hannu har kasa mazan kuwa jallbiya suka saka farare. Ruqayya da Abida tare da sauran dalibai duk uniform suka saka duk sun sha wanki da guga.

Daga bangaren yan uwansu Ruqayya dangin mami dana abba da yawa sun sami zuwa. Sai Anti Gaji maman Munir da sauran yan uwa da abokan arziki. Ruqayya tana daga bangaren dalibai amma tana baza ido taga shigowar su Mummy da Abba B.

Kwanan prince Richard biyu da zuwa yana hotel ko fita baiyi ba wai bai gama warware gajiya ba. Munir dake zaune kan wata karamar kujera a dakin yace hutu ne yayi maka yawa ina gajiyar take kai da ka zo a jirgi? Richard ya kara rufe kansa da bargo please Munir bazaka gane bane. Na takurawa Dad ya barni na taho ni kadai sai driver da bodyguard gashi yanzu ruwan wanka ma sai na hada da kaina. Jiya har konewa nayi  a hannu. Munir kallon abokin nasa yake cike da mamaki na halinsa da bai canja ba. Ko da suna secondary school a lagos dan wani mai aikinsu aka kawo su tare a matsayin dalibai amma shi yake masa komai. Da kyar da lallabawa ya samu Richard ya tashi yayi wanka ya shirya cikin farar shirt da blue din wando. Shigar ta masa kyau. Zasu fita ya tuna da sarkar gold din da Mum dinsa ta bashi mai cross saboda kariya ya saka suka tafi wurin walimar kanwarsa Munir kamar yadda ya fadawa Richard din. A mota ma yana ta korafi shi baya son zuwa taron addinin da ba nasa ba kada a rinka kallonsa. Yana magana yana kara shigewa cikin kujerar motar a baya inda suke zaune da Munir.

Mutane da dama wadanda suke daga baya baya sai da suka juya kallon hadaddiyar motar da ta shigo wurin taron. Daga baya aka yi parking Munir ya fito. Shi kuwa Prince Richard sai da body guard dinsa ya bude masa ya fito. Can bangaren maza Munir ya ja shi suka zauna a karkashin katuwar canopy din da ke wurin. A lokacin da suka zauna hakimin karamar hukumarsu ke jawabin kara karfafawa yara gwiwa su cigaba da neman ilimi. Yana bayani Richard na kallon mutane daidai. Bai taba zuwa arewa ba sai wannan lokacin. Gaba daya ya takura saboda zafi ya tashi...munir ina zuwa bari naje mota na dawo. Yana zuwa yace da dreban ya fita daga gaban ya shiga ya kunna AC. Bai dade da tafiya ba Ruqayya ta hango shigowar  Haj Maryam da daya daga cikin masu aikinta. Ji tayi kamar ta tashi ta taro su don har ta mike ta ji muryar Mal Hafiz ta speaker yana kiran sunanta tazo tayi karatu kafin a cigaba da jawabai.

Duk dokinta na karatun sai da gabanta ya fadi saboda yawan mutanen da zata yi karatu a gabansu. Wata nutsuwa ce ta sauko mata ta tashi a hankali ta je gaban Mal Hafiz ya miko mata loudspeaker. Ganin idanu sunyi mata yawa sai kawai ta rufe idonta ta danyi gyaran murya. Wannan gyaran muryar yasa prince Richard fitowa daga mota ko kashewa baiyi ba ya dan tsaya daga baya inda zai hango mai shirin maganar saboda yaji kamar muryar yarinya.

Ido a rufe Ruqayya ta nemi tsari daga shaidan la'ananne sannan tayi Bismillah ta fara karanta Suratul Rahman. Wurin tsit yayi tamkar babu kowa saboda yadda muryarta ke tashi cikin nutsuwa da dadin kira'a. Surah ce da take bayani sosai kan kyakkyawan tanadin da Allah SWT Yayiwa yan aljannah. Kuma tana kara kwadaita mana so da neman Rahmar Mabuwayi gagara misala Allah Madaukakin Sarki. Allahu Akbar.......har ga mutanen da basa gane larabci karatun yayi tasiri a zuciyarsu. Prince Richard da ke tsaye a gefe  tunda ta fara karatu gabansa ke faduwa. Wani irin yanayi ya shiga da ya kasa ganewa tsoro ne ko jindadi. Tana yi zuciyarsa na bugawa har ta kai tsayuwa ta gagare shi. Ji yake kamar ya dade yana gudu saboda yadda kirjinsa ke bugawa. Ya samu ya rike wani karfe dake rike da canopy din. Gumi yake sosai shi kanshi sai da ya tsorata da yanayin. Ga mamakinsa tana cewa Sadakal Lahul Azeem sai kawai hawaye ya sauko masa. Wannan wane irin sihiri ne mutanen nan suke yi shine abinda ya tambayi kansa. Dole ya bar wurin kafin wani abin ya same shi.







Batul Mamman💖
[7/2, 8:38 PM] Fatima 💖: RUQAYYA YAR ALBARKA✨10





A wannan yanayin yaji an dafa masa kafada. A firgice ya juyo dama bashi da cikakkiyar nutsuwa. Munir na ganin yanayinsa hankalinsa ya tashi. Me ya same ka Richard? Bana jindadin jikina Munir, ka kaini gidanku don bazan iya zama a dakin hotel dina ni kadai ba. Da sauri Munir ya ja hannunsa suka nufi mota. Da yake makarantar a unguwarsu take basu dade ba suka isa gidan. Dakinsa ya kai shi ya kwanta a kan katuwar katifar Munir ya ja bargo ya rufa. Shi kadai yasan me yake ji a jikinsa. Tunda yake a duniya bai taba firgita kwatankwacin haka ba. Shi kuwa munir yana ganin Richard ya kwanta ya fita nemo masa maganin zazzabi tunda yaji jikinsa yayi zafi.

Bayan karatun Ruqayya an kira dalibai masu sauka sun karanta suratul Fatiha da shafin farko na Suratul Baqara sannan aka basu allonsu. Daga nan taro ya watse bayan an rarraba musu kyaututtuka. Haj Maryam dai a nan tayi musu sallama Mami bata so hakan ba. Haba Mummyn Ruqayya muje gida ki ci abinci mana. Tayi murmushi kiyi hakuri lokacin program dina har ya kusa bai fi rabin awa ya rage min ba. Ruqayya ta ce meye program kuma? Haj Maryam ta dafa mata kai program yana nufin shiri a gidan rediyo ko tv. Ai sai ta washe baki ashe ana nuna ki a tv. A'a ni a gidan rediyo nake. Mami ta kalli agogonta ta tuna shirin da take ji a wannan lokacin tace ba dai kece Maryam Hassan ba? Maryam mai yin Kyakkyawar Rayuwa a Peace Radio. Murmushinta ne kawai ya karu ganin mata sun fara kallonta. Dadi ne ya kama mami sosai ta kara ganin girman Haj Maryam saboda shirin nata a kullum yana burge mutane ga karuwa da ake yi dashi. Mami tayi mata sallama amma ta kudiri niyyar tambayarta wani abu. Domin kullum ta gama shirin sai tace abin nan dai da nake nema ku cigaba da sani a addua. Sau da yawa akan bugu waya a tambayeta abinda take nema sai tace sirri ne. Bayan sun isa gida ne Mami ta aiki Ruqayya da almajirinsu suje karbo mata meatpie da samosa da Anti Gaji zata soya wanda za'a hada tare da abinci a rabawa mutane. Ko cire uniform din islamiyar bata yi ba suka tafi.

Prince Richard jiki ba kwari ya tashi yayi abinda bai damu da yi ba ko a gida. Durkusawa yayi gwiwoyinsa a kasa ya hada hannuwansa yana addua. Duk adduar bata wuce neman tsari daga halin da zuciyarsa ta fada bayan jin karatun Ruqayya.

Anti Gaji na jera meatpie din a wata cooler tace ta kira mata Munir yazo ya fitar wa da almajirin cooler din don sauran yaran duk suna wurin sauka. Saura kuma idan kinje ki tura kai cikin dakin nasan yana ciki dai tunda naga kofar a bude. Ruqayya ta tashi tana dariya ta je kofar dakin tayi sallama. Ko da Prince Richard yaji muryar ya ganeta duk da a speaker yaji ta dazu. Kara tsorata yayi duk dakewa irin tasa ya daga sautin muryarsa yana cigaba da addua. Ita dai Ruqayya sai ji tayi ana cewa.....In Jesus name I pray...Halleluyah!!!
 Tuni ta manta da gargadin Anti Gaji ta banka kai cikin dakin. Ganin mutum a durkushe yasa ta ja da baya da sauri. Shima ja da bayan yayi yana nunata yana cewa ..The Devil is a liar. Da gaske tsoronta yake ji saboda tasirin karatun Al Qurani. A hankali ta dawo dakin tace kai arne ne? Naji kana kiran Jesus to wallahi wuta zaka shiga inji Malam. An fada mana irinku ko tsarki bakwa yi. Haka ne don Allah? Shiru yayi yana jindadin muryarta. Karamar yarinya ce kyakkyawa sai magana take masa da hausa. Shi kuwa banda sannu babu abinda ya iya. Ganin bai amsa ba sai tace you no Hausa? Ya gyada mata kai a hankali ga mamakinsa. Ta cigaba you will enter hellfire. Allah will punish you. Stop praying to gunki. Ta dan kalle shi ni na manta sunan  gunki da tarunci amma dai you will enter hellfire ni ba ruwana. Wannan yarinyar ko aljana ce ne ya tambayi kansa. Zata sake magana Anti Gaji tazo da kanta Ruqayya ban hanaki shiga dakin maza bane. Kai kuma me ya zaunar da kai Fatima fa tana jira. Turus ta tsaya kallon mutumin da bata sani ba. Ruqayya tace Anti Gaji kinga arne na gani a dakin shiyasa ban taho ba. Kasa yi musu bayani yayi sai ga Munir da ledar magani. Shi yayiwa mamansa bayanin ko waye bakon. Ta ja hannun Ruqayya haba ko da naji,ai da tunanin mu nemi taimako nake. Munir yace masa Richard ga mamana, wannan kuma kamar kanwata take yar makotanmu ce. Tasowa yayi a hankali cikin nuna isa ya zo gaban anti Gaji ya miko mata hannu nice meeting you Ajiya. Ruqayya da ke gefe ta make hannun ta kalleshi a tsiwace we are muslims no greeting with hands tana magana ta hade rai abinta. Kallonta ya rinka yi yana mamakinta, babu wanda ya isa yayi masa haka a fadar babansa. Duk da Munir yayi yunkurin hana shi mikawa mamansa hannu amma yaji kunyar abinda Ruqayya tayi masa. Ga mamakinsa Prince Richard bai nuna bacin rai ba sai ma sorry da ya ce da Antin. Sannan yace da Munir zai tafi idan akwai jirgi yau zai koma gida.







Batul Mamman💖
[7/8, 9:56 PM] Fatima 💖: RUQAYYA YAR ALBARKA✨11





A ranar Prince Richard ya koma gida don babu abinda zai sa ya sake kwana a kano. Muryar yarinyar kuwa kuwwa take masa kamar a lokacin take karatu. Da zuwansa gida bai jira an gama kashe motar ba ya fita da sauri. Bayin gidan sai gaishe shi suke yi amma bai kula ba. A kitchen ya tarar da wadda yake nema tana bawa masu girki umarni akan abinda take so su dafa. Ji tayi an kankameta ta baya har tana jin saukar hawaye a wuyanta. A firgice ta waigo Richie me ya sameka? Bai iya magana ba sai hawayen da suka cigaba da sauko masa. Queen Amelia ba karamin gigicewa tayi ba ganin yadda danta yake zubar da hawaye. Abu ne da ta dade rabon da ta gani. Da sauri taja hannunsa suka tafi dakinta. Sai da suka zauna tace me ya sameka Richie? Me aka yi maka? Kansa ya dora a kan cinyarta Mum na hadu da abin tsoro a Kano. Wani irin tsafi naji wanda ban taba jin abu mai tasiri kamarsa ba. Ya kama hannunta ya dora akan kinjinsa..kinji yadda zuciyata take bugawa tunda naji abin har yanzu. Itama kukan ta soma saboda tsananin son da take masa. Bata son ko kadan taga ransa a bace bare ta kaishi ga zubar hawaye. Yinin ranar haka ya kwana jiki a sanyaye. Washegari da King Edward ya dawo daga zuwa nemarwa Prince Richard auren Princess Sophia ya tarar da dansa a wani yanayi. Ya ce dama ni bana son zuwanka arewa ko kadan amma bana son hanaka kaga kamar wani raayina ne. na dade da sanin cewa mutanen nan ba ababen yarda bane. Queen Amelia tace amma Your Majesty me yasa ka bari yaje tun farko? Gashi ya dawo mana a birkice. Haka suka zauna suna ta tattaunawa game da addinin mutanen arewacin Nigeria. Bayan yan kwanaki Prince Richard ya kasa komawa yadda yake kafin zuwansa kano, karshe ya matsawa babansa yana son ya koma karatu. Ba haka iyayen suka so ba sai dai kwanciyar hankalinsa tafi komai. Dole suka barshi  ya tafi amma da sharadin zai yarda ya auri Princess Sophia komai daren dadewa idan ya dawo kasar. Don su barshi ya tafi ya yarda da zabin su duk da ko kadan bai sa ta a ransa ba.
*********************

Wani fili ne mai girman gaske. Babu komai a cikinsa sai yashi, a cikinsa yake tafiya da kyar yake jan kafa ga tsananin zafin rana yana ta gumi. Daga can gabansa ya hangota a tsaye karshen inuwar wata bishiya katuwa. Irin wannan karatun yaji tana yi a hankali cikin zazzakar murya. Wata irin nutsuwa ce ta saukar masa a take ya fara gudu yana son zuwa gareta sai dai da ya iso sai ya ga kamar ta kara matsawa gaba.......
Tana kallon yadda yake haki shi kadai a kwance ta dan taba shi....a firgice ya tashi kamar wanda yayi tsere duk ya jike da gumi yana dube dube a dakin. Ya dafe kansa da yake sarawa a duk lokacin da yayi mafarki da wannan yarinyar.  Sai a hankali ya tuna inda yake ma.  Debbie ta rungume shi wai me yake damunka ne Richard? Tunda muko zo hotel din nan ranaku kadan ne bana ganinka cikin wannan yanayin. Ka fada min idan akwai abinda yake damunka. Tashi yayi daga kan gadon ya nufi wani tebur ya dauki jug ya zuba ruwa ya cup ya sha. Sai da ya cika shi sau uku yana shanyewa sannan ya dawo ya zauna kusa da abokiyar aikinsa kuma sabuwar budurwarsa. Ya ja hannunta ya rike yace Debbie idan mutum yana da matsalar da ke damunsa me kike ji ya kamata yayi don ya magance ta? Kallon fuskarsa take cike da so...ta fi shekara biyu tana sonsa sai yan kwanakin nan  ta sami kanshi. Mutum ne mara son hayaniya da wuya yake shiga sabgar sauran abokan aikin nasa ma. Kamar daga sama taji yace tambayarki fa nake yi. Ta dago kanta ta dan yi masa murmushi tace idan mutum yana da matsala kokari yake ya gano silar matsalar sannan yayi ya nemi magance ta. Ya ce idan mutum ya gudu daga matsalar ai inaga shikenan ko. A'a ta bashi amsa, idan ka gudu babu inda matsalar zata je. Zama zata yi ta jira ka har ku sake haduwa kila tafi damunka ma...Richard ya dora kansa a kan pillow nagode Debbie ina jin lokaci yayi da zan fuskanci matsalata...shekara bakwai ina mafarkin abu daya. Debbie ta dan kwanto a jikinsa wane  irin mafarki ne wannan Richard? Bai bata amsa ba ya tashi ya shiga hada kayansa a wata jaka. Sai da ya gama yace ni zan koma gida Debbie daga nan zan tafi Nigeria a can zanyi hutu.  Tace amma zaka dawo ko? Yayi mata murmushinsa mai kyau ya sumbaci goshinta,yace  zan dawo saboda ke Debbie  sannan ya dauki jakarsa ya fita. A take yaji kamar an soma sauke masa wani nauyi daga kansa. Yayi dan murmushi sai na nemo ki duk inda kike yarinya, sai  kin cire min abinda kika yi min.








Batul Mamman💖
[7/11, 7:33 AM] Fatima 💖: RUQAYYA YAR ALBARKA✨12





Sallamar wadda taje jira taji daga bakin kofa ta tashi da gudu har tana tuntube da takalmi. Mami tace to sarkin garaje taji muryar mamanta zata yaga mana carpet. Haj Maryam ta shigo rungume da Ruqayya yanzu Fatima gara yar tawa ta fasa baki da carpet dinki ya yage? Lallai nasan zaman da nake yi da ke. Mami dai sai dariya tace to turota ta yaga sai ku canja min a na aurenta. Haba wane ke irin carpet din gidan 'yata. Nata ma daga waje zan shigo dashi. Mami tana dariya dai tace ya Barrister ina fata kun dawo lafiya. Lafiya kalau ta amsa mata sannan ta mikawa Ruqayya leda ga tsarabarki yar albarka. Ina can ina dawafi ina miki addua Abbanku ya kira Barrister yace kinyi ta hudu a musabaqar kasa da akayi. Allah Ya kara miki basira Yasa next time kiyi ta daya. Mami tace amin Ya Rabbi.

Sai bayan laasar Haj Maryam ta tashi tafiya Mami tace mata jibi yarki zata tafi Abuja gidan Abida. Haj Maryam tace Ruqayya zasu mayar min da ke yar shara da wanke wanke ko. Murmushi kawai tayi ta sunkuyar da kanta. Mami ta dube su tana jindadin yadda suka shaku a ranta. Shekarun da sukayi da Barrister Mukhtar da matarsa sun zama kamar yan uwa na jini. Nadiya da su Barrister suka rike yar Hajjaju ma sun saba da ita duk shaanin juna tare suke yi. Ta ce ai ba dadewa zata yi ba in sha Allah, laulayi ne da yaran nan. Kin tuna Hidaya ma duk haihuwa biyun haka muka rinka fama. To har gara ita, Abida dama ba dai raki ba. Shi kuma Munir sai ya biye mata. Jiya ma Anti Gaji tazo tana sake rokon zuwan Ruqayyan wai don ita babu sauran mata ne a gabanta ta ga kamar ja musu rai nake. Haj Maryam tayi murmushi kaji uwar miji mai shagwaba suruka. Allah Ya kaimu zan sa Malam Malam ya kaita don tukinsa yafi nutsuwa. Ni da Ruqayyan ke da ciki ai gidanta zan tare. Mami ta kwashe da dariya ashe mijin zai koro ku kuwa. Wai har ya ban tausayi tun bai zo ba. Ruqayya dai sai dariya ta raka Mummynta har gida duk da da dreba tazo.

Bayan kwana biyu Ruqayya ta shirya ta tafi Abuja. Haj Maryam har kuka tayi da ta biya yi mata sallama. Tana matukar son Ruqayya kamar jininta. A can kuwa ba Abida ba hatta Ya Munir yaji dadin zuwanta domin babu abinda Abidan take iya yi a gidan. Cikin yana matukar bata wahala bata iya girki ga yawan amai. Tunda taje komai na aikin gidan ita take yi. Idan Ya Munir ya dawo zata zauna su danyi hira kadan daga nan ta koma daki ta yi bitar haddarta ko ta duba wasu littattafan. Dama hutu suke amma tana karatu ne a College of Qur'anic Science.

Wata rana da daddare tana wanke wanke Abida tana tsinkar zogale a kitchen suna dan taba hira Ya Munir ya shigo rike da waya a hannu yana ta fara'a. Ruqayya tace Yaya wannan fara'ar kamar an maka albishir da kujerar Hajji. Bazaki gane murnar da nake yi bane...ya kalli matarsa, Abida abokin nan nawa ne ya zo kasar last week shine yace zai zo gobe mu gaisa kafin ya koma. Wai kano yake son zuwa amma zai fara zuwa nan. Tayi murmushi Yayana kana son abokin nan naka. Shima murmushin yayi yana kyautata min ne, da taimakonsa da taimakon Allah na sami aikin nan duk da baya kasar. Rabon da mu hadu an fi shekara shida. Tace Allah Ya kawo shi lafiya. Suna shirin barin kitchen din Ruqayya tace karfe nawa zai zo don nasa abinci da shi? Munir yace a nan zaiyi lunch amma bamu yi maganar inda zaiyi masauki ba sai yazo.

Amma kasan yarinyar nan ta dade tana jiranka ko Richie. Har yaushe zamu zauna da kai shekara sama da talatin baka batun aure.? Ba don ta nace sai kai ba da tuni babanta ya aurar da ita ga wasu maneman nata. Tamkar ba dashi King Edward yake magana ba Prince Richard ya cigaba da turawa Debbie email ta computer. Ran sarki ya baci sosai Queen Amelia na shigowa ya fara fada ta sangarta yaro gashi baya jin maganar kowa. Duk abinda suke yi tana ji saboda haka ta bashi hakuri tace zata yi magana da dan nata. Cikin fushi ya fita ya basu wuri ta karasa gaban table din ta riko hannun Richie suka dawo bakin gado. Richie me yake damunka ne da anyi maganar aure? Fuskarsa a sake yace Mum bana son Princess Sophia ko kadan. Na sanar da Dad Debbie nake so yace bazan auri baturiya ba. To shima bazan auri zabinsa ba. Ni sarauta bata gabana saboda haka.....kul Richie ta fada tana rufe masa baki da hannunta. Kada na sake jin kace sarauta bata gabanka. Sarauta ita ce sanadin haihuwarka, ita nake maka fata dole ka gaji ancestors din babanka. Meye aibun Sophia ne ma? Bana sonta kawai ga ta da rawar kan tsiya. Queen Amelia tace gaskiya akwai rawar kai nima ba sonta nake ba amma ka amince ka farantawa babanka rai daga nan ko bayan auren duk macen da ka bukata zaka samu. Kai fa dan sarki ne babu abinda yafi karfinka. Itama wadda kake so din kana iya barinta a UK din kana kai mata ziyara akai akai. Idan ta haihu ni zan rinka zuwa ganin jikoki na .(Wa iyazu billah). To naji Mum amma sai na dawo zanje wurin Sophian. Ina son zuwa Abuja munyi magana da  friend dina Munir zanje nayi sati biyu. Sam bai taba fada musu halin da yake ciki ba shiyasa bai sanar da ita zai wuce kano ba. Queen Amelia tace ba komai Richie sai ka dawo din.







Batul Mamman💖
[7/13, 12:59 PM] Fatima 💖: RUQAYYA YAR ALBARKA✨13





Shinkafa da vegetable soup Ruqayya ta dafa da rana wadda tasha cabbage da caras da sauran kayan lambu na miya sai tayi pepper chicken  ta markada kankana, cucumber da ayaba ta sa sugar kadan ta tace. Sai da ta gama jere komai a dinning table ta shiga wanka. Abida na fitowa falo kamshin abincin yasa ta koma daki da sauri saboda aman da ya taso mata. Ruqayya na ganin ta fara amai ta je ta taimaka mata ta gyara wurin sannan ta fara mata fada yanzu me ya kaiki falo har kika sa kanki amai. Abida tace to Baaba zaki fara fadan ne kamar wata yayata? To zuwa nayi na tayaki. Hmm kanji ki wai ki tayani. Ke dai kinje kwadayi bukata bata biya ba. Ki kyale zuba musu abincin idan har sun bukata zanyi serving dinsu kada kije ki kashe musu appetite da kakarin amai. Wani murmushin mugunta Abida tayi tana daga kwance...yarinya zakiyi bayani bari lokacinki yazo. Ke da duk wata kike cika mana gida da ihu bansan yadda zakiyi da laulayi ba.  Suna hirarsu suka ji tsayuwar motoci a waje. Ruqayya ta leka ta dawo baki bude...ni fa motoci uku na gani banda ta Ya Munir. Ta dan zaro ido, fada min  gaskiya waye bakon nan? Abida ma ta leka ta dawo wani dan sarki ne fa a can kudu kudu ni na mant sunan garin. Ko zo baya ji da Hausa a yadda Yayana ya fada min. Sun shaku sosai kuma duk da basa tare suna kokarin zumunci. Ruqayya ta dora karamin hijab kan pink din jallabiyar jikinta ta nufi kitchen tana tunanin me zata dafa da sauri a aikawa sauran mutanen motar saboda wanda tayi bazai isa ba.

Har ta fara diban kayan miya zata soya Ya Munir ya shigo yana tambayar ko abinci zai isa tace wani zata dora. Cikin yan mintuna ta dafa jallop din taliya ta juye a katon flask.

Prince Richard da Ya Munir suna cin abinci suna yar hira da Abida da ta fito su gaisa. Ruqayya ta fito daga kitchen da flask a hannu ta shigo falon da sallamarta.
A take hantar cikin Prince Richard ta kada. Ko da lokaci ya tsawaita amma bazai taba manta sautin wannan murya da ta hana shi kwanciyar hankali ba. A daidai lokacin ma ruwa yake sha, tana fitowa suka hada ido ruwan da yake kokarin hadiyewa da sauri ya kware shi. Nan da nan tari ya sarke shi su Ya Munir suka tashi suna masa sannu. Ita ma Ruqayyan kafin ta wuce waje tayi masa sannu. Ita bata ma gane shi ba ta wuce ta mikawa abokan tafiyarsa abinci.

Idanunsa a kanta ta har tazo ta sake wucewa a karo na biyu zata kai musu plates da ruwa. Nan ma kallon ya bita dashi har sai da ta tsargu. Ta dan waiwaiyo suka sake hada ido kawai sai ta murguda masa baki tayi gaba abinta. Duk da irin yanayin da zuciyarsa ta shiga da ganin wadda zai tafi nema a kano sai da yayi dan murmushi da ta murguda bakin. Dole ne ma ya san ko wace yarinyar nan. Dole ta raba shi da abinda ta saka masa ko da sihiri ne.






Batul Mamman💖
[7/13, 5:53 PM] Fatima 💖: RUQAYYA YAR ALBARKA✨14





Har bakin motocin da suka yi masa rakiya Ya Munir ya raka shi. Yace to Prince yaushe zaka tafi Kanon? Ai ya ma manta da zancen wani zuwa Kano tunda yaga wadda zashi dominta. Ya dan shafa kai ina ganin zanyi sati daya a garin nan idan ba damuwa nan zan cigaba da cin abinci. Ya Munir yaji dadin hakan sosai yace babu damuwa. Prince Richard yace amma kada ku damu da wadan can ya nuna yaransa. Ni kadai zan rinka zuwa, zan basu kudin abinci. Har zai shiga motar sai ya dan fito...Munir baka fada min kayi mata biyu ba irin yadda kuka saba Hausawa. Ido Munir ya zaro auren shekara biyun ne zan sake wani? To kanwar Abida ce wadda ka gani sunanta Ruqayya. Yayi dan murmushi kun taba haduwa a Kano a dakina. Ka tuna yarinyar da ta doke maka hannu? Prince ya kirkiro murmushin karya....lahhh ita ce? Gaskiya ta girma. A ransa yace yaushe zai manta da fuskar ko muryar. Zuwansa kano a lokacin shine mafarin rashin cikakkiyar nutsuwarshi. A haka suka rabu da alkawarin zai zo karfe tara na safe.

Ruqayya na kallon wata lecture ta Dr Zakir Naik a daki Abida ta shigo da sallama. Bayan ta amsa tace yau dai kun kawo bako mai kallon tsiya. Dazu sauran kiris nayi tuntube. Abida tayi dariya kuma sai kinyi sati kina ganinsa safe,rana da dare. Ruqayya ta bata fuska ban gane ba. Me kuma zai rinka zuwa yi? Cin abinci Abida ta bata amsa. Yace kin iya girki sosai zai dauke ki aiki a fadar babansa. Tuni Ruqayya ta kule ba aiki ba ya mayar dani baiwarsa kawai. Ni haka kawai naji mutumin ya bani haushi. Baki ga kallo ba kamar zai cinye ni. Kada ku je gaein kwashe kwashe ku debo mana maye dai. Abida sai dariya  take yi mata yadda ta dage tana mita. Kinga yadda kika bata rai kuwa? Amma seriously he is a Prince kamar yadda na fada miki a wani gari can a kudu na manta karkashin wane state ne. Ruqayya tace ko da naji kice ba musulmi bane shiyasa baya rissina ido wurin kallon mata. Ni kamar na taba ganinsa amma bazan iya tuna ko a ina ba. Kila kuma bashi bane. Abida tace kunyi waya da Hidaya kuwa? Tace idan kika koma zaki gidanta tayi PT jiya ita ma ciki gareta. Yanayin fuskar Ruqayya ne ya sake bata dariya. Ke wasa nake miki amma da gaske ciki gareta. Hankalin Ruqayya ya dan kwanta tace ku cigaba da yin ciki kuna mayar dani yar aiki dai. Nima auren nan zanyi na huta. Kamar gaske ina saurayin? Mami ta fada min banda wani mai katin waya babu wanda ke zuwa wurinki. Kukan shagwaba Ruqayya ta sa zaki ga mai kati, gobe zan koma gida. Ni mijin da zan aura ma sai ya baku mamaki In sha Allah. Kuma sai na fadawa Mummy. Abida na jin haka ta fara bata hakuri don tasan ko da wasa ta fada mata ba mamaki ta ce sai Ruqayyan ta dawo gida tunda suna matsa mata.

Washegari kafin takwas da rabi Ruqayya ta gama hada breakfast . Ya Munir yana ta kallon time saboda ya kusa makara gashi har tara da kwata Prince Richard bai zo ba. Shi kuma da kawaici baya son kiran shi yace zai makara. Karshe dai dole ya fadawa Abida idan yazo tace ya tafi sai su bashi abinci. Yana mota prince Richard ya kira yana bashi hakuri wai bai tashi da wuri bane. Munir yace ba komai  ni na fita, kaje gidan sun san da zuwan ka. Suna gama wayar Prince Richard ya yi wani dan murmushi. Yana sane dama yaki zuwa da wuri. Idan da hali yana son yin magana da Ruq....sunan da wuya amma dai yana son magana da yarinyar nan.

Kamar daga sama taji kararrawar gidan tana ce Assalamu alaikum. Lokacin har ta fara gyangyadi a falo. Abida na daki tun fitar mijinta tana bacci. Mayafinta mai kauri ta dauka ta yafa kan riga da skirt din da ke jikinta sannan ta bude kofar. Kamar jira yake tana budewa idonsa cikin nata tayi saurin kawar da kai sannan ta bashi hanya ya wuce. Ita ba don Ya Munir da kansa ya kirata yace zai zo ba ai da baccin karya zata yi taki bude kofar. Da hannu tayi masa nuni da wurin da zai zauna yace goodmorning. Kamar bazata amsa ba sai kuma dai ta dan saki fuska ta amsa masa. Farfesun kayan cikin ta dauka tace masa zata dumama da turanci sannan ta shige kitchen. Har ta bace yana bin ta da ido. Ya rasa me yake ji game da ita. Ruqayya na shiga kitchen tayi tsaki....mutumin nan yana neman kaita bango. Ita ta tsani kallo irin wannan. Ace ko kiftawa bazai yi ba. Duk sanda ta juya sai taga ita yake kallo ko idanunsa a kanta. Cikin tukunya ta juye farfesun ta fara dumamawa ta hango yar robar da ta zuba sauran attaruhun da tayi blending. Dauka tayi ta kwara a cikin tukunyar tana dariya. Idan ya kasa ci gobe bazai dawo ba ta fada tana dan murmushin keta.

Da ta fito tea taga yana sha...lallai mutumin nan kamar wani gidansa. Ina laifi ya jira tayi masa Bismillah. Ta ja wani tsakin ta ajiye masa flask ta koma gaban tv don bazata barshi shi kadai a falon ba saboda tsaro. Yana ci ta dan waiga taga ko ya zuba farfesun. Ai kuwa bakinsa yaga yana fifitawa sai ruwa yake kurba. Dariya ce ta kwace mata tana yi a hankali taji yace HELP cikin karamar murya. Sai kuma ya bata tausayi ta tashi tana tambayarsa ko lafiya.








Batul Mamman💖
[7/15, 11:54 AM] Fatima 💖: RUQAYYA YAR ALBARKA✨15





Wata harara ya watso mata wannan yajin sai kace zata kashe mutum. Yanzu ya kara tabbatar da akwai wani abu game da yarinyar nan. Kila ma makiyan babansa ke amfani da ita. Lemo mai sanyi sosai ta kawo masa tana sannu tare da murmushin mugunta. Da sauri Prince Richard ya shanye lemon ya dago idanunsa da suka yi ja cike da hawayen wahala ya kalleta. Ta dan saki fuska tace gobe ma ka dawo kwadayi gidan mutane. Shi ma murmushin yayi ta sake cewa wadannan idanun sai na tsiresu idan basu dena bi na da kallo ba. Ga tsananin mamakinta sai ji tayi yace ga fork a kusa you can use it. Ai a take ta rikice ji take kamar an watsa mata ruwan sanyi. Kunya sosai ta kamata. Kai amma Abida ta cuceta, ta ce mata ba bahaushe bane.....yanayin fuskarta kawai yake kallo. Yarinyar tana da kyau sai dai she can't be trusted. Ita dai Ruqayya a sanyaye ta bar wurin, shima tashi yayi don yajin yayi masa yawa sosai. Bakinsa yaki daina zugi. Hanyar kofa ya nufa ta dago ido ta dube shi...zaka dawo anjima ko? I hope so ya bata amsa sannan ya fice.

Numfashinta bai dawo daidai ba sai da taji karar tashin mota. Ita kuwa wane irin abin kunya ne wannan. Yi da mutum a gaban idonsa....gashi abinda tayi ba na fada bane duk wanda yaji fada zai mata. Dole taja bakinta tayi shiru. Sai wurin shabiyu ta dora abincin rana bayan tayi wanke wanke.

Abida na lura da yadda Ruqayya take yawan kallon kofar shigowa gidan. Can ta ce wai wa kike jira ne. Ko kinyi saurayi ne a Abuja...eyye kaga Ruqayya anyi kasuwa. Fuska a kwabe tace Wallahi ya isheki Abida. Mtsw ni zan je na kwanta idan Ya Munir da abokinsa zasu ci abinci ai zaki iya zuba musu ko? Abida tayi murmushi jeki idan suka dawo zan tasheki. Kinsan dai bana son harkar abincin nan. Zan sake tambayar Mami anya zan wuce stage din nan kuwa? Dazu fa da na leko kina yanka salad bakiji yadda zuciyata ta tashi ba. Sai kuma Ruqayya taji tausayinta tayi mata sannu. A da duk gidansu babu mai kaunar harkar kitchen kamar Abida sai gashi yanzu falo ma sai an bubbude windows take iya zama. Tace lallai Allah mabuwayi ne gagara misali...nan gaba kadan fa sai komai ya daidaita kamar bakiyi ba.

Har takwas da rabi na dare basu ji duriyar Prince Richard ba. Tana son tambaya tana gudun kada Ya Munir ya tambayeta dalilin damuwa da abokinsa. Tana bitar haddarta a hanlali ya Munir yake fadawa Abida bari ya sake kiran Prince yaji ko lafiya. Tun dazu ya kasa samun wayoyinsa kuma shima bai sanar dashi bazai zo ba. Kunnen Ruqayya sai ya koma sauraren wayar....Subhanallah wane asibitin ne gani nan zuwa. Haka taji ya fada da turanci ya ajiye wayar. Ta tashi a dan tsorace don tunaninta bai wuce abincin da ta bashi bane yayi affecting dinsa. Ya Munir kuwa duk ya gigice ya dauko key din mota da sauri. Ruqayya ta kasa daurewa. Me ya faru da abokin naka? Wai tun safe bayan ya koma hotel dinsa yake ciwon ciki. A tsorace ta ce ciwon me? Abida da Ya Munir suka bita da kallon mamaki tayi saurin wayancewa ...kasan mutane bare kace dan sarki ne kada su zarge mu ace abincin gidan nan ne. Ya dan saki fuska to ku zo muje asibitin tare kawai.

Ya Munir na gyara parking din mota suka ga shigowar wasu motoci har bakwai. Dukkansu bakake ne masu kyau da tsada. Kowacce an rubuta Ndam Kingdom a jiki. Maza ne suka rinka fitowa karfafa sanye da bakaken coat kowa da bindiga a hannunsa. Sai da suka tsaya a layi sannan wasu yan mata masu daurin kirji da zani iya gwiwa sun sha sarkokin jajajen duwatsu suka fito suka fara watsa flowers a kasa. Cikin kankanin lokaci idanu sun koma garesu. Ruqayya ta tabo Abida tace kudi yana inda yake a kasar nan. Ya Munir da ke jinsu yace iyayen Prince Richard ne. Cikin Ruqayya ya kada, tsoronta bai wuce ace yajin da ta zuba masa bane ya jawo kwanciyarsa a asibiti. Kamar sauran mutane a gefe suka tsaya har aka bude motar tsakiyar wani dattijo ya fito sanye da manyan kaya harda babbar riga na wani green and maroon lace. Kansa golden crown ce irin ta masu saurauta a kudancin Nigeria. Yana rike da sandar tafiya da sarkoki shima sun cika masa wuya. A rude ya fito daga motar sannan wata mata ta biyo bayanshi. Itama zani ne kawai tayu daurin kirji na lace irin nasa. Sai crown wadda aka dora a kan gashin da tayi kari dashi aka gyara mata kai. Tun daga kanta har hannuwa da wuya gwal ne ko ta ina. Banda kasancewar kuka take yi amma tayi kyau sosai. Su Ruqayya dai ana gefe ana kallo har sai da mutanen suka wuce.

Fuska cike da hawaye Queen Amelia ta shiga dakin da aka kwantar da Prince Richard. Kafin a bude kofar tuni kamshin turarenta ya sanar dashi Mum dinsa tazo. Duk da yana jin jiki haka ya daure ya tashi zaune. Ana bude kofar ta shigo da sauri suka rumgume juna. King Edward ya kalli likitan da yayi musu jagora zuwa dakin yace Dr meye yake damun dana? Shi kuwa likita sai rissina yake yaga kudi yace Your Majesty, Prince Richard yaci yaji ne fiye da yadda cikinsa zai iya dauka shine ya bata masa ciki. Queen Amelia cikin kuka tace a wane hotel ne kaci abincin Richie? Your Majesty ya kamata a rufe hotel din kuma a kama masu girkin. Ta sake rungume danta, haka kawai  zasu nemi kashe min yaro. Bari mu koma gida dole mu nemi Oracle Priest yayi magana da Goddess ta kara bawa Richie kariya. Idan na rasa dana mutuwa zanyi Your Majesty, dole kayi wani abu a kai.







Batul Mamman💖
[7/16, 9:46 AM] Fatima 💖: RUQAYYA YAR ALBARKA✨16





Ya Munir a reception yace su zauna bari ya je dakin ya gani ko za'a barsu su shiga. Bai dade da tafiya ba wasu nurses biyu suka zo ta gaban su Ruqayya suna hira. Daya tace wai ni yau dan waye a asibitin nan naga doctors wurin biyar a dakin. Yar uwarta tace hmmm dan wani sarki ne mai shegen kudi. Ai yaron ga kudi, kyau da mulki. Sai kuma ta dan matso kusa da dayar.....Ruqayya da ke gefe itama ta kara mika kunne taji me ake fada.
Ai in fada miki mum din Prince din tace za'a rufe hotel din da yayi masauki kuma a kama masu wurin abincin da ya ci. Abida har sai da ta dan juyo jin yadda cikin Ruqayya ke cewa kulululu.

Wani gumi ke Ä·eto mata. Yanzu idan ya bada sunanta ai kashinta ya bushe. Nurse mai kawo labari ta sake cewa wai fa duk abinda ake yi yaji ne yayi masa yawa. Da yake dan masu fada aji ne kinga ina ji sarkin ya kira FCT minister ya kai karar hotel din. Kuma ga dukkan alamu za'a rufe din. Yanzu ni mai abincin nake tausayi ma.

Ruqayya dai jiki ba kwari don ta tabbatar da zaa aunata jininta ya mugun hawa. Ta ce Abida bani aron wayarki idan da credit. Ke ina taki zaki ce na baki aron tawa? Pls sis ki taimaka min. Yanayin Ruqayya duk ya canja lokaci guda. Hakan yasa Abida ta mika mata wayar. Tana karba ta fice waje inda ake ajiye motoci ta rubuta numbar da ta dade da haddacewa.

Haj Maryam na sallah ta ji waya na shigowa. Kafin ta idar an kira sau hudu shiyasa tana sallama ta amsa wayar. Numbar Abida ta gani hakan ya fadar mata da gaba. Wata ajiyar zuciya Ruqayya tayi da taji an amsa wayar sai kuma ta soma kuka. Haj Maryam tace me ya sameki Ruqayya? Baki da lafiya ne ko jikin Abida ne? Nan ma shiru sai sautin kuka da take ji. Tun tana tambaya har itama dai ta soma kukan. Ruqayya tamkar gudan jininta take jinta. Duk abinda zai tadawa yarta hankali bata sonsa ko kadan. Barrister Mukhtar yana daga daki yaji muryar matarsa tana magana tana kuka. Da sauri ya fito yace me ya faru? Tace Ruqayya ce take kuka nima bansan me ya sameta ba. Dan guntun tsaki yayi amma ku mata sai abarku. Yarinya na kuka sai ki biye mata. Ya karbi wayar yar albarka me ya faru kuke kuka ke da Mummyn ki? Saboda muryarta ta dashe da kyar yake gane abinda take fada. Abba B don Allah zaka zama lauya na? Sai kawai yasa wayar a speaker, kinji yarki da ta tuna wai na zama lauyanta. Daga daya bangaren tace Abba B da gaske nake. Kulleni za'ayi ko a yanke min hukuncin kisa. Ku fadawa su Mami su yafe min wallahi banyi zaton abin zai kai haka ba. Nan ta labarta musu abinda tayi. Barr Mukhtar yace to saurareni da kyau....kada ki kuskura kice kina da lauya sai su zata da gayya kika yi. Idan har shi yaron bai sanar da iyayensa sunanki ba to ki rike bakinki. Banda ma dai an rasa me zaayi da kudi daga cin yaji sai gadon asibiti. Mummy tace a'a fa Abba B kasan nima yaji baya yi min da sauki. Ta karbi wayar...Ruqayya ki share hawayenki kinji ko. Duk abinda ya faru zuwa anjima sai ki sanar da wuri.  idan ta kama Abban ya taho gobe sai ya taho. Bazan fadawa Mami ba sai munji daga gareki. Ruqayya tace to ta ajiye wayar a sanyaye.

Ya Munir ta gani a bayanta wanda hakan ba karamin tsorata ta ya karayi ba. Fuskarsa a hade kamar bashi ba. Biyo ni ana nemanki a dakin da aka kwantar da Prince Richard. Wani fitsari taji yana barazanar digowa saboda yadda ya matseta lokaci guda don tsananin tsoro.






Batul Mamman💖
[7/16, 6:04 PM] Fatima 💖: RUQAYYA YAR ALBARKA✨17





Bakinta har yana hardewa tace Ya Munir ai ba sai munje dakin ba. Indai jikinsa da sauki mu tafi gida kawai. Ki wuce muje kawai taji yace, ta bi bayansa a sanyaye. Tun kafin su karasa take arba da wasu murdaddun maza masu siffar ban tsoro. Kowanne yasha bakar coat suna muzurai. A hankali ta soma kalmar shahadah don indai ba son zuciya ba tasan karshenta ne yazo.

Wani cikin mazan ne ya bude musu kofar dakin suka shiga su uku. A kwance yake kansa na cinyar Queen Amelia. Ruqayya na kallonsa ta kawar da kai...daga safe zuwa yanzu duk ya rame. Suka dab rissuna suka gaishe da King Edward da matarsa.  Queen Amelia ta kalli Ya Munir da dan murmushinta, kai ne babban abokin Richie ko? Yayi murmushi yace eh. Ya nuna Abida, ga matata wannan kuma kanwarta ce.  Prince Richard yace ita ce wadda take yin abincin.

Dis.. dis..dis haka Ruqayya taji fitsarin ya soma diga. Hasbunallahu wa ni'imal wakil ta ambata a zuci. Shikenan ta faru ta kare... King Edward ya dan saki fuska Richie ya fada mana yadda kuke karrama shi Mungode sosai. Amma idan ku kuke bashi abinci a ina ya sami wannan yajin? Prince Richard da Ruqayya suka hada ido. Daga kallon da take masa ya fahimci rokonsa take kada ya tona mata asiri. Sai ya kawar da kai gefe. Yau ban fito da wuri bane kuma ina jin yunwa. A hanyata ta zuwa gidan naga mai kosai a bakin hanya na siya. Me??? Iyayen suka fada tare. Kosan hanya Richie kamar baka da gata shine abinda sarkin ya fada. Ruqayya kamar ta zuba ruwa a kasa tasha don murna. Ita kuwa Queen Amelia cewa tayi ina su Sela yaran da ya taho dasu. Suna ina yake siyan abincin hanya bayan sune masu kula da rayuwarsa da lafiyarsa. Prince Richard yace Mum kada kiyi musu fada. Nine nace su zauna ina son fita ni kadai..tace sam bata yarda ba sai an sake su saboda basa kula da aikinsu sosai. Ita mai kosan a wane titi take? Ruqayya tace kai matar nan da shegen bin diddigi take. A dole sai ta kama wani da laifi. Tunda dan nata ya tashi ai sai ta hakura haka.

Sun dan jima a asibitin King Edward yana ta jan su da hira. Sai da zasu tafi Prince Richard yace Ruqayya ina jiran abincin safe daga gareki kafin takwas. Iyayensa da su Ya Munir duk sunyi mamakin jin yayi hausa. Ita kuwa Ruqayya dama yayi taji mamakinta akan abincin da ya nema ne sai kace wata baiwar gidansu. Koda yake bata  da bakin magana ita da ya rufawa asiri. Ya Munir yace yaushe ka ji Hausa? Murmushi kawai yayi. Yace ai tunda nazo kano shekarun baya na sami intrest akan yaren. Sai ya dubi Ruqayya har kin manta ni ko? Kin manta mutumin da kika dokewa hannu a gidansu Munir. Baki kawai ta bude....dama kaine wannan arnen da na gani a dakin Ya Munir. Abida ta daka mata duka a baya wai ba'a hanaki cewa arne ba? Don Allah kayi hakuri. Yayi murmushi ba komai.

Iyayensa kuwa abin ya burgesu. Dan nasu akwai kokari akan duk abinda yasa a gaba. Ji yadda yake hausa kamar wani yarensa duk da dai hausar tasa tamkar yana turanci haka take fita.

Sai a mota Ruqayya ta bawa su Abida aininhin labarin abinda ya faru da Prince Richard. Ya Munir yace ai abinda naji kina fada a waya ne ya dan bani tsoro. Yanzu gobe ki samu ki tashi da wuri ki dafa masa abincin sai na kai kafin na wuce office. Nasan kawai punishing dinki yake son yi. Kuma daga yau ku iya bakinku. Kamanin fuska ba shi yake nufin mutum baya jin yare ba.  Sai dai suna zuwa gida text din Prince ya shigo wayar Ya Munir.

(Come along with your sister inlaw in the morning)

Ya Munir ya sake karanta text din har sau uku. Zuciyarsa bata masa dadi ba gaskiya. Baya son Prince Richard ya fara shigewa Ruqayya duk da dai ya yarda da tarbiyarta amma mutum irin Prince ba abin yarda bane. Yana da kyau mai daukar hankali ga uwa uba kudi.....a take kuma yayi murmushi ya danyi magana da karfi, daga cewa nazo da ita na fara tunanin wani abu daban. Abida tana ninke kayanta tace magana kake ne? Yayi mata dariya,  A'a maman baby. Ki fadawa Ruqayya tare zamu asibitin gobe. Sai ta sake bashi hakuri ma.








Batul Mamman💖
[7/18, 9:24 AM] Fatima 💖: RUQAYYA YAR ALBARKA✨18





Bin sa take a baya kamar bata son tafiya. Har sai da ya juyo yace ko kayan sun miki nauyi ne? Ya mika hannu kawo na tayaki. Ruqayya tayi dan murmushi barshi Ya Munir babu nauyi. A haka suka karasa dakin da aka kwantar da Prince Richard. Yau ma kwance yake kan cinyar Mum dinsa tana shafa masa wani mai mai kamshi a kansa yana jin dadi har da lumshe idanu. Sallamar Ruqayya ce tasa ya bude idon. Ita ta manta dakin ba na masu amsa sallama bane tayi. Shi kuwa Ya Munir baiyi ba dama. Karasawa yayi suka gaisa da abokinsa. Prince Richard ya kalli yan matan da ke dakin masu kaya iri daya. Kallon nasa ya tabbatar musu yana son su karbi kwandon abincin da ke hannun Ruqayya. Ai kuwa cikin sauri suka karba suna musu sannu da zuwa. Ruqayya ta dan duka ta gaishe da Queen Amelia sannan shima Prince tace masa good morning. A hankali ya amsa yana binta da mayen kallonsa. Kayanta na ciki ba masu nauyi bane amma hijab din da tasa har kasa yake mai kauri. A ranta tace maye kalli iya ganinka babu abinda zaka gani. Ba wata hira suka yi ba Ya Munir yace zai mayar da ita gida ya wuce office. Queen Amelia tace nima zan tafi hotel din da Dad din Richie ya kwana naje na shirya...idan babu damuwa ka bar kanwar taka a nan saboda bana son barin shi shi kadai. Idan na dawo za'a kaita gida.

Ruqayya ta kafe Ya Munir da ido alamun kada ya barta. Zuciyarta cike take da tsoron Prince Richard da yan gidansu. Karshenta ma so suke ya tafi su kamata. Ko amsar sa bata jira ba Queen Amelia ta tashi tayi kissing goshin danta tayi wa yan matan nuni da hannu suka shiga gaba tana binsu a baya. Sai da ta tafi Ya Munir yace gara na tafi da ita gida saboda girkin rana. Prince Richard yace kada ka damu Munir nayi maka alqawari bazan cutar da ita ba. Kuma bazan taba fadin cewa ita ta bani yaji ba. Ya Munir ya bashi hakuri ya sake mata fada a gabansa sannan yace ta kula zai dawo da wuri ko da basu mayar da ita gida ba. Tana ji tana gani ya fita.....daga ita sai Prince. Ko shi mara lafiya tasan yafi ta kuzari. Tsoronsa take da gaske don tasan da ganinsa bazai yi hakuri ba, karshenta yace sai ya rama.

Yana daga kan gadon ya  dora kafa daya kan daya ya jingina bayansa da bango. Ruqayya kuwa ta dage tana kallon kasa don ma kada su hada ido. Dama can ita bata son mu'amala da wadanda basa sallah bare wannan mutumin mai ji da kai. Shirun ya katse ta hanyar cewa zuba min abincin mana. Sai a lokacin ta kalle shi lallai ma, wai an  fada masa kowa bawa ne a gidansu. Baki ji me nace bane? Naji ta amsa a dakile sannan ta nufi basket din abincin. Ta dauko flask tana kokarin hada masa tea yace bana son tea please. Bata amsa ba ta mayar ta dauko wani wanda ta soya doya da kwai da sauce. Tana budewa yace wannan ma bana so. Wata harara ta wurga masa yayi murmushi. Ta dauko wani karamin flask to wannan ne na karshe idan shima baka so sai na koma gida. Faten tsaki ne yasha alayyahu da yakuwa. Shine abincin da Abida tafi ci duk safiya saboda amai shiyasa take mata. Har zasu fito Ya Munir yace ta dibar masa kila ya sha tunda bashi da lafiya. Matso na gani ya umarceta. Hannunta mai dauke da flask din ta tura masa fuskarsa. Ya sa yatsan hannun hagunsa ya lasa. Tace meye haka kuma? Na zata dai duk duniya kowa yasan ba kyau cin abinci da hannun hagu. Ya dan tura baki ni da shi nake amfani kuma Mum dina bata taba hanani ba. Ruqayya tace ni kuma indai abincina zaka ci sai kayi amfani da damanka. Prince Richard ya dan gyara zama. I have a better idea....ki bani a baki kawai. Ba don basu tashi da wannan tarbiyar ba da yau ta yi ashar din da aka dade ba'a ji irinsa ba. Kallon banza ta bishi dashi, ka manta nasa a bakina na tauna sannan na baka. Yace am ok with it.....fuskarsa dauke da murmushi. Ranta ya kara baci, wato shi bai san gatse ba. A cikin bowl karami ta zuba faten ta sa cokali ta mika masa ya dan sha kunu...ai sai kin fara sawa a bakinki na gani. Ban manta da ke kika jawo min kwanciyar asibiti ba. Ruqayya ta gaji da magana dashi...hausar dai tana fita amma irin ta masu iyayin nan da turanci ya kamawa harshe. Don ya kyaleta tasa cokalin ta diba ta sa a bakinta. Zata canja wani yayi saurin karbar na hannunta. Gani tayi ya sa shi a baki yana wani kashe mata ido ya lashe cokalin.....dama bakinki nake son ya fara shiga kafin nayi amfani dashi. Nasan abincin  will taste better. Kanka ake ji kawai ta fada ta ja kujera ta zauna can gefe.







Batul Mamman💖
[7/18, 5:30 PM] Fatima 💖: RUQAYYA YAR ALBARKA✨19




Da hannun hagun yaci abincin yana yi yana kallonta yaga ko zata sake magana. Wayarta ta zaro a jaka tana dan dube dube. Shi kuwa Prince Richard yana gamawa ya dago plate din gashi na gama. Shiru ma magana ce inji bahaushe. Ko motsin kirki Ruqayya taki yi bare ta nuna masa taji abinda yace. Ya maimaita har sau uku sannan ta dan daga kai ta nuna shi da yatsa....kaga ka kiyayeni wallahi, ni ba baiwarku bace ko mai aiki. Dan lallabaka da nake ma its because I feel guilty.  To tunda bazaki karba ba bari na tashi na ajiye da kaina. Idan Mum dina ko Yayanki suka dawo zan sanar dasu irin wahalar da kike bani. Ya dan kalli sama alamun mai tunani, kin san Mum ta damu tasan mai kosan nan. Tana zuwa zan fada mata na tuna sunan. Kafin ya rufe baki ta tashi  ta fizge bowl din daga hannunsa. Garin sauri tayi tuntube da kafar kujera saura kadan ta fadi tayi sauri ta dafe bango tana cewa Bismillah. Ko da ta mike a tsorace don kadan ya rage tasha kasa sai taga Prince Richard a bayanta a tsaye. Hannuwansa na kokarin rike kugunta ya taimaka mata ta tashi tsaye sosai. Kada ka taba ni ta fada da sauri tana kara yin baya. Shima baya yaja...daga taimako kike wani matsawa kamar  kinga abin tsoro? Ganin ya sake miko hannun ta kuma dakatar dashi, please don't touch me. Sai ya juya ya koma gadon ya zauna cike da bacin rai. A hankali ta mike ta koma kujera ta zauna tana dingisa kafa daya da ta gurde.

Dakin yayi shiru kamar babu kowa sai Ruqayya da ke matsa kafarta. Lokaci sai gaba yake ba Ya Munir ba Queen Amelia. Bazaki bani hakuri ba? barin kafar tayi ta mayar da hankalinta gareshi jin abinda ya fada. In baka hakuri saboda me fa? Ni tunda nake komai yi min ake yi. Yau daya nayi yunkurin taimakon mace ta nuna bata so. Kamar kinga kazanta a jikina. Mata suna so na sosai har gudunsu nake amma for the first time naga macen da ke nuna kiyayya gareni.
Dariya maganarsa ta bawa Ruqayya sannan tace welcome to reality your highness. Ya kamata kasan cewa duniyar tafi karfin garinku inda kuke sawa ku hana. A fusace yace karya ne, babana yana da karfin iko a kasar nan sosai. Ki manta da sarauta yana da kudi. Kuma kudi shine mutum a duniya. Kawai gulma kike yi. Ruqayya itama ranta ya baci, gulma kuma? Yace eh...kina son na taba ki kina pretending. Ku musulmai haka kuke. Ai na dan yi bincike a kanku. Sai ku ce babu kyau namiji ya taba mace amma kun iya bin maza. Mazan ku ma ko a inda nake aiki suna da yan mata da yawa bayan suna da aure. Addininku banda mugunta da kashe mutane babu abinda yake nuna muku...

Zuciyar Ruqayya ba karamin tafasa take ba. Sai da ya taba mata addini tasan cewa dazu ba fushin gaske take ba. A fusace ta mike tsaye tsakaninta da Allah marinsa take son yi don shi ne kadai abinda zai sa ta huce, sai kuma ta tuna abinda yace game da musulunci. Yanzu duk abinda tayi masa zai dorar a matsayin halin musulmin duniya. Dole ta koma ta zauna tasa hannu ta dafe goshi saboda kanta har ciwo yake mata sannan ta rufe idanu. A hankali tayi Bismillah sai kawai ta fara karanta Suratul Mulk. Daga inda yake yana jin sautin muryarta sai dai tamkar wani maganadisu yake jin muryar na fizgarsa. Cikin nutsuwa ya tashi ya dawo gaban kujerar ya durkusa. Ita kuwa ko motsinsa bata ji ba. Sautin muryarta kawai ta kara tana yi nutsuwa na saukar mata. Tuni ta manta da wani Prince ta koma ga Allah SWT. Ba jimawa ta kammala surar. Sai a lokacin ta bude ido...nasa idanun ta gani wadanda suka yi ja saboda  kaduwa. Jikinsa yayi masa nauyi ya kasa tashi daga gabanta. Ba karatun da take ba, ita kanta Ruqayyan wani irin sonta ne yake ji yana ratsa dukkan jikinsa. A sanyaye yace mata ki sake yin wani. Yanayinsa da muryarsa yasa taji tausayinsa sosai. Babu musu ta kara yin basmalla ta soma karanta Suratul Yaseen. Wani irin yanayi suka shiga gaba daya. Hawaye ke zubar masa ba tare da ya sani ba. Ita ma Ruqayya ta tsinci kanta da hawayen da bata san dalilinsu ba. Haka suka kasance har ta kai ayar karshe. Tamkar kada ta dena haka yake ji. A take ya kara gaskata cewa ita din matsafiya ce amma babu abinda bazaiyi ba domin mallakar wannan matsafiyar. Sonta da yake ji ma bazai wuce effect din tsafin ba saidai a yadda yayi masa kamu zai so kullum ta rinka yi masa irin wannan tsafin mai matukar tasiri.

Motsin da taji daga waje ne yasa ta dawowa cikin hayyacinta. Tayi saurin kara tura kujerarta baya tana goge fuskarta. Shi kuwa Prince Richard ko motsi baiyi ba har aka bude kofar Queen Amelia da yan matan aikinta suka shigo. Ba shiri Ruqayya tayi saurin tashi daga kan kujera tana yi mata sannu da zuwa. Queen Amelia hankali yayi wajen rabin rai Richie tace me ya sameka kake zaune a kasa. Ko cikin ne? A'a ya bata amsa....Ruqya ce take koyamin wani excercise da yake maganin murdewar ciki. Queen Amelia ta washe baki ai tsoro naji ne. Amma ya naga ka jike da gumi duk sanyin dakin nan, kamar ma kayi kuka. Ta kalli Ruqayya nagode amma baa matsa masa da aikin wahala. Jikinsa baya jura. Don kece ma shiyasa zan kyaleki tunda baki gama sanin matsayinsa ba. Ta nuna mace daya cikin yan matan. Ke Ella ki wuce ki fadawa dreba ya kaita gida yanzu. Ki rakata har gida ne kiyi musu godiya. Ta taimakawa danta ya mike tsaye. Muje kayi wanka kaji.

Gaba daya hankalinsa yana tare da Ruqayya dake hada kwanukan da tazo dasu. Yace mata cikin wata sassanyar murya da shi kanshi ta zama bakuwa a gareshi...please ki sake dawowa. Bata amsa ba ta fice zuciyarta ba dadi.

Sai da ta shiga toilet a gida sannan ta saki wani irin kuka mai sauti. Wannan wane irin yanayi ne ta tsinci kanta a ciki. Wai TAUSAYIN kafiri wanda baiyi imani da manzancin Annabi Muhammad SAW ba. Muryarsa da take bata umarni ta cigaba da karatu kawai take ji. Shima hawayen da yayi mata ta kasa gane dalilin su. Meyasa yace ta kuma zuwa wurinsa? Kai bazani ba ta fada a fili. Irin mutanen nan baka rabasi da tsafi. Ace lokaci guda daga tsana da jin haushinsa sai kawai tausayi ya biyo baya. Tsaki tayi ta dauro alwalar azahar ta fito.

.





Batul Mamman💖
[7/19, 11:21 AM] Fatima 💖: RUQAYYA YAR ALBARKA✨20





Kwanaki uku kenan babu Ruqayya babu dalilinta. Baya son kowa ya gane halin da yake ciki musamman Munir amma dena zuwa da ita asibiti ba karamin cutarwa bane gareshi. Yasan ma ciwon sonta ne ya kara kwantar dashi ba ciwon ciki ba. Abin da mamaki gaskiya yadda yake jinta a ransa. Baccin kirki baya iyawa saboda mafarkin da yake da ita tana wannan karatun. Idan ya tashi kuwa a jike yake farkawa da gumi. Sai dai sabanin tsoro zuciyarsa da nutsuwa take tashi.

Ruqayya na gyarawa Abida wardrobe suna yar hira suka ji shigowar Ya Munir. Da fara'a ya shigo dakin har Abida na tsokanarsa ko wani abokin nasa ne zai zo. Ai kuwa ya bata rai cikin wasa wai ta raina shi.  Ruqayya kuwa tana dariya tace Yaya kaine ka iya kwashe kwashe. Kowa abokinka ne. Ya ce lallai yarinyar nan ko don kwana biyu kin horo da zuwan Prince Richard ne? To kwantar da hankalinki yau dinnan jirgi zai auna su gida. Sai dai kuma Hafiz yace na gaishe ki. Wallahi ki dena ja masa rai ko kiji guda idan na gaji.... gaban Ruqayya ne yayi mugun faduwa, wanda bata san dalili ba. Sauran maganar Ya Munir din ma bata gane ba sosai. A take kunci ya ziyarci zuciyarta ta fara neman tsari daga shaidan. Meye haka kuma Ruqayya ta kwabi zuciyarta.

Ya Munir yace nima tafiyar tasa tayi min dadi. Duk yadda muke dashi bana jindadin yadda yake neman ya rinka shige miki yar kanwata. Bai fada musu yadda Prince Richard ya dame shi akan ya bashi numbar wayarta ba kafin ya baro asibitin, lokacin suma suna shirin tafiya. Kememe yaki bayarwa harda karyar ta kusa aure kada ya kira mijinta ya gani, kasan mazan hausawa da kishi. A dole Prince Richard ya hakura ba don yaso ba. Ya Munir baya son wata alaqa ta hada abokin nasa da Ruqayya don ruwa ba sa'an kwando bane. Kudi kam yafi su sosai amma kanwarsa mace ce mai ibada....kai Allah ma Ya tsare ya fada a zuci. Muryar Abida yaji tana sanar dashi yau ita tayi girki su tafi ta zuba masa. Hakan ba karamin dadi yayi masa ba don yayi missing girkin matarsa.

Ita kuwa Ruqayya da kyar ta iya karasa aikin. Duk ta tsani kanta da damuwar da tayi daga jin cewa ya tafi. Yadda taga ya sauya bayan sauraron zancen Allah SWT shine babban dalilin damuwarta. Da zasu cigaba da haduwa da ta kwadaita masa addinin Islam. Ta mike kila bashi da rabo ne gara na dena damun kaina.

Ba jimawa taji alamun shigowar motoci. Da yake gidan na mutum hudu ne bata yi tunanin nasu aka zo ba sai da taji kararrawa. Ya Munir ta gani yayi saurin fitowa daga daki yace mata barshi bari naje da kaina. Princr Richard ne, kila wata sallamar yazo muyi. Ya bude kofar sai yaga Queen Amelia da Prince Richard cikin shigar alfarma. Sunyi kyau sosai musamman shi da yafi sa kananan kaya. Yau lace ne a jikisa fari har da babbar riga. Sai jar hula karama wadda akayiwa ado da ruwan gold. Wuyansa da hannaye duk sarkoki ne na jan stones yasa bakin takalmi. Ya fito a Prince Richard of Ndam Kingdom. Ya Munir yayi musu maraba suka shigo cikin gidan tare da yaran su.

Ruqayya da Abida suka fito suka gaisa dasu. Queen Amelia tana murmushi tace nazo yi muku godiya ne kafin mu wuce airport. Richie yace ka biya lokacin ina hotel ban fito ba. Sarki yace nayi muku godiya a madadinsa da masarautar Ndam gabadaya. Ya wuce gida tun shekaranjiya. Ya Munir yace ba komai ai yiwa kai ne. Ruqayya tace bari na kawo musu lemo da hausa, Abida ta ce to Allah Yasa akwai mai sanyi dai. Ta tashi ta nufi kitchen din. Zasu tashi Abida tace suyi hakuri su sha lemo. yarinyar da tafi kusa da Prince Richard ta bi bayanta da sauri, bari naje na tayata. Su Ruqayya na kitchen su kuma suna falo suna dan taba hira.

Sai da ta gama hada cups a wani tray zata dauka yarinyar ta shigo ta mika mata wata farar takarda sannan ta dauki tray din ba tare da ta tsaya yi mata wani bayani ba. Baki ta bude tana kallon karfin hali, sai kuma da maida hankalinta ga takardar. Numbar waya ta gani har kala hudu sai suna daga kasa. RICHIE!!!

Hannunta har rawa ya fara , me zai sa ya bata numbarsa? Kuma a boye kamar baya son a sani. Ji tayi Abida na cewa Ruqayya yaya ne? Da sauri ta dauki jug din ta fito. Tana shiga falon suka hada ido dashi. Dama jiran fitowarta yake. Gabadaya ya tsareta da ido yana mata wani irin kallo fuskarsa tayi yanayin tausayi. Ita kanta tayi mamaki yadda tayi saurin gane abinda kallon nasa yake nufi. So yake ta kira shi. Zata dauke kai ya sake tsareta da ido kawai sai tayi masa dan murmushi. Wani irin farinciki yaji a ransa mara misaltuwa. Kara son yarinyar nan yake a kullum. Cike  da nishadi suka cigaba da hira. Har bakin mota su Abida suka raka su. ita kuwa Ruqayya daki ta shige ko sake waigensu bata yi ba. Prince Richard yaso kwarai ta fito ya sake ganin fuskarta sai dai ya hakura. Ji yake a ransa ya shiryawa duk wani kalubale da zai iya fuskanta a dalilin sonta.







Batul Mamman💖
[7/19, 11:56 PM] Fatima 💖: RUQAYYA YAR ALBARKA✨21





Sati biyu kenan da komawar Prince garinsu amma shiru babu wayar Ruqayya. Duk wata bakuwar number sai ya dauka. Idan ta shiga missed call ma sai ya bi baya.  A hankali Queen Amelia ta fara lura da yadda Richie ya chanja tun bayan dawowarsu daga Abuja. Ta damu kwarai da rashin walwalarsa sai dai ya dage akan babu abinda ke damunsa. Ana haka kuma Dad dinsa ya bullo da maganar aurensa da Princess Sophia. Yaso ya bijire sai dai a wannan karon mai goyon bayan nasa ma ta nuna tana son yayiwa mahaifinsa biyayya. Lokaci guda abubuwa suka rikice masa. Ya rasa yadda zaiyi da ransa. Gashi ba zai iya sake tambayar Munir numbar ta ba.

Fadar Sarkin Ndam His Royal Highness King Edward ta wayi gari da shirye shiryen engagement party din Prince Richard da Princess Sophia. Bisa al'adarsu dangin mata ke zuwa gidan su mijin. Lokacin wata guda kenan da rabon da Richard yasa Ruqayya a ido ko yaji muryarta. Soyayyarta a ransa kullum kara zama sabuwa take yi. Yake kawai yake yana jira a gama engagement din ya san karyar da zaiyi ya tafi Abuja.

Saura kwana biyu gagarumin taron baikon Richie a garin Ndam. A garin Abuja kuwa Ruqayya ce ta tubure ita gida zata koma. Ko kadan bata da sukuni tun bayan tafiyar Richard. Hankalinta a tashe yake amma ta rasa wanda zata fadawa taji dadi a ranta. Tunaninta bai wuce ta sanar da Mami halin da take ciki ba ko zata taimaka mata da addua. Ranar dai Abida har haushi taji yadda Ruqayyan ta dage sai ta tafi ranar asabar. Cikin dare tana bacci tayi wani mafarki da ya kara dagula mata lissafi. A dokar daji take tafiya ba gida gaba ba gida baya. Kukan wani take ji yana yi da tattausar murya. Kana ji kasan yana cikin matsanancin hali. Yana kukan yana kiranta. A hankali ta rinka bin hanyar da take jin sautin muryar har ta tarar dashi. A durkushe yake an daddaure masa hannuwa da kafafo yana ta kokawar kwancewa ya kasa. Tayi gudu ta karasa taimaka masa sai taga Prince Richard ne. Guguwa ce ta taso tana neman dauke shi yana ta miko mata hannu. Ki taimakeni kada na halaka...ina cikin mugun hali ki taimaki rayuwata. Daga nan iskar tayi gaba dashi ta barta a wurin tana kuka.

Da kalmar Auzubillah ta tashi a firgice. Kuka ne ya kwace mata. Wai meye damuwarta da arnen mutumin nan ne da yayi sanadin kunci a rayuwarta? Tashi tayi ta dauro alwala tayi nafiloli sannan ta zauna tana addua. Kuka take sosai tana cewa Ya Allah kaine masani akan komai. Ya Allah bani da wani wayo ko dabara sai abinda Ka tsara min. Da izininKa na hadu da wannan mutumi Ya Allah kada kasa abinda nake ji game dashi ya zama so....Ya Allah kada Ka dora min son makiyinKa, kada Ka sanya ya zama sanadin gurbacewar rayuwata. Ya Allah ina tsoron azabarKa. Kada ka barni don bani da mataimaki sai Kai kadai.  Daga nan kuka yaci karfinta sosai. Da kyar ta sassauta ta kare da cewa Ya Allah idan har akwai wani alkhairi tsakanina dashi na rabon shiriyarsa Allah Ka sake hadani dashi. Idan babu ina rokonKa da sunayenka tsarkaka Ka nesantani dashi kamar yadda Ka nesanta gabas da yamma. Haka Ruqayya ta cigaba da zama akan abin sallah tana yiwa Allah tasbihi har aka kira assalatu. Sai bayan tayi sallar walha ta koma bacci.
Ko da ta tashi zuciyarta fes haka taji. Ta shiga hada kayanta don nutsuwarta bazata cika ba sai taga Maminta da Mummy. Tana zzzage jakarta ne takardar da ta manta da ita ta fado. Ta dauka ta kare mata kallo. Har zata yaga sai kawai ta fasa ta dauko wayarta. Numbar farko ta saka tayi kira. Bugu biyu taji an amsa. Muryar mace taji tana cewa da turanci  Richie darling anyi maka waya. Gabanta yana dukan uku uku taji muryarsa yana cewa idan kika sake kirana Richie ranki zai baci. Kuma waye ya baki damar daukar min waya? Ko kuwa gulma ce don ki sami damar yi min bincike. Ita dai macen sai hakuri take bayarwa. Ruqayya ta rike wayar ta kasa kashewa.

Yana ganin bakuwar number ya dauka da sauri. Yace hello har sau uku ba amsa har zuciyarsa ta karaya zai ajiye wayar yaji ance RICHIE. Tsayuwa ce ta nemi gagararsa har yayi saurin zama akan kujera mafi kusa dashi. Shi kadai yasan dadin da yaji a ransa don ya fidda rai zata kira. Ji yake kamar a mafarki. Ita kuwa Ruqayya jin yayi shiru yasa tayi nadamar kira...am sorry ta fada tayi yunkurin kashe wayar. Yayi saurin cewa please stop...a ina zan ganki? Ina son ganinki Ruqya.







Batul Mamman💖
[7/20, 10:16 AM] Fatima 💖: RUQAYYA YAR ALBARKA✨22





Jin abinda ke fitowa daga bakin Prince Richard yasa Ruqayya saurin katse wayar. Ya ganta yayi mata me? A take wayarsa ta shigo sai ta kasa dauka. Karshe ma dai kashe tata wayar tayi ta cigaba da hada 'yan kayanta. Abida ta shigo dakin tana hade rai ita a dole Ruqayya bata kyauta mata ba. To amma Mami tace su barta ta taho ai tayi kokari. Sama da wata daya abinda bata saba ba. Amma gaskiya kirkinki kadan ne yarinyar nan. Wai duk yadda nake bata rai kinki ki hakura mu tafi tare nan da sati biyu. Ni na rasa gane abinda ke damunki kamar wata mai aljanu sai kiyi ta tunani yan kwanakin nan. Ruqayya ta zuge zip din jakarta. Son kai ke damunki wallahi. Don kawai nace ina son zuwa gida kika dena kula ni. So kike duk hutun na kareshi a nan bazan zauna a gidanmu ba? Eh lallai tunda gaki a daji ko yar wulakanci. Sai kuma Abidar tayi murmushi Allah bana so ki tafi ne. Ba wai don kina tayani aiki ba ai kinga ina iya girki yanzu. Gidan sai yayi shiru kafin ya dawo daga office. Ruqayya dai ta gama yanke shawara tasan kuma yar uwartata neman karyar mata da gwiwa take tayi dariya to kiyi hakura zan kara kwana zuwa lahadi. Ai kuwa Abida taji dadi tace baki fadawa Mummy zaki taho ba ko? Kinsan ta sarai kada tace zata taso dreba yazo daukarki. Da kin hakura sai mu tafi tare. Ruqayya tace haba ai da hankalina, nima bazan so dora musu nauyi ba. Abida ta ce to yanzu dai Abba yace a kaiki tasha a biya miki kujerar mutum biyu saboda kada a matse ki. Sukayi dariya dukkansu don Ruqayya kam bata taba zuwa wani gari a motar haya ba. Duka duka za'a iya kirga wuraren da taje.

Shi kuwa Prince yana jin wayar a kashe yaji babu dadi. Hannuwan Sophia yaji ta rungume shu ta baya. A fusace ya janye jikinsa yana mata fadan da bashi da dalili. Gani yake kamar jin muryarta yasa Ruqayya kashe waya. Tamkar ya zama tsuntsu ya bar garin haka yake ji amma dole ya hakura a gama abinda za'ayi saboda kada ya kara batawa babansa rai. Ranar asabar da daddare aka yi taron kece raini a babban dakin taro da yake fada. Mutane da dama sun halarci wurin. Anci an sha abubuwa iri iri. A dole Prince Richard ke kirkirar murmushi saboda Mum dinsa. Duk ta shiga damuwa don tasan baya son auren. Amma ba yadda zata yi ta hana shiyasa take iya kokarinta wurin ganin ta kyautata masa. Bayan jawabi daga sarakunan guda biyu akayi musayar zobe tsakanin Richard da Sophia. Daga nan ta yunkura tayi kissing dinsa don taga shi bashi da niyar yi. Ai kuwa iyayensu da sauran jamaa sai murna da tafi. Kakar Richard Madam Hannah ta taba yarta....Amelia me take damun jikana ne? Hankalinsa yana wani wurin. Ki duba kiga yadda fuskarsa tayi. Queen Amelia tace Mama nayi iya yi na yace ba komai. Kawai sai ta soma hawaye....Mama bana son bacin ransa, bana son fushinsa. Ki lallaba shi ya sanar dake abinda yake so. Akwai kudin saboda haka banga abinda zai nema ya rasa ba. Madam Hannah tace yaushe rabon da ki kaishi wurin Oracle Priest? Kinsan irin makiyan da babansa yake dasu masu son ganin bayansa. Ki fada masa gobe da sassafe ya shirya muje. Yana bukatar kariya daga Goddess din garin nan.

Karfe hudu na asuba Prince Richard ya gama shirinsa tsaf. Ya hade cikin kananan kaya da suka kara masa kyau. Sai kamshi yake don gwanin barnar turare ne.  ya dauki jakarsa ya fito farfajiyar gidan. Mutane da yawa a fadar suka kwana yawanci duk sun bugu saboda giyar da aka sha. Wani yaronsa ya kira yace yazo ya kaishi airport. Ba jimawa suka isa yace masa idan ka koma gida ka sanar dasu na tafi Abuja wani babban aiki ne ya taso daga kamfanin mu na Switzerland. Ya dan kalli agogo zanyi musu waya ma amma dai don kada a nemeni ina jirgi ka fara fada musu. Yaron yace to haka zaka tafi ba guards? Kada ka damu tafiyar ce ba shiri. Idan ina bukata zan sanar. Abin da mamaki dai, Prince da bai iya yiwa kansa komai banda wanka da sa kaya shine zaiyi tafiya shi kadai. Anya lafiya kuwa? Sai dai kuma ba huruminsa bane tsawaita bincike. Daga nan suka yi sallama ya tafi.

Prince Richard yayi zaman awa daya da rabi kafin jirgin ya tashi. Dama saurin da yayi don kada kakarsa ta tsare shi sai sunje wurin Oracle Priest. Idan Goddess din ta damu da cigaban garin ta bashi kariya a duk inda yake. Shida da rabi na safe jirgin su ya sauka a Abuja. Daga airport din ya sami motar da zata kaishi cikin gari. Duk a takure yake jin kansa saboda motar bata yi masa ba duk da shi kadai ne a ciki. Wani yaron babansa ya kira kafin su isa cikin gari sosai saboda yar tazarar dake tsakanin airport din da gari ya ce ya nemi kamfanin sayar da mota yanzu ya samar masa wadda zaiyi amfani da ita mai kyau. Wurin karfe tara an gama komai ya karbi sabuwar motarsa wadda ko leda ba'a cirewa seats din ba. Yana shiga gidan Munir ya nufa cike da fariciki.  Yau fa sai dai ayi wadda za'ayi amma zai fada masa gaskiya yana son kanwar matarsa.

Yana karyo kwanar gidan ya hango motar Munir tana fita daga gate. Gabansa ya fadi ganin Ruqayya a bayan mota tana magana da Abida dake gaba. Dariya sukeyi cike da nishadi. Ganinta cikin farinciki ya kara sanyays masa zuciya. Sai kawai yabi bayan motar tasu. Basu tsaya ko'ina ba sai Jabi motor park. Ya kalli wurin da aka rubuta sunan wurin ya zaro idanu....me Ruqayyansa zata yi a tasha? Tashar ma wadda kowa yake zuwa. Akan idonsa Munir ya fito mata da jaka yasa a bayan wata motar. Sannan ya ciro kudi ya mika mata. Yana kallo suna rungume  juna da Abida sannan yaga ta shiga gaba ta zauna su kuma sun ja mota sun tafi . Zuciyarsa sai kuna take ganin yadda yan talla suka baibaye tagar inda take zaune. Tasa hijab din jikinta ta rufe fuska. Haushinsu ya kamashi, duk sun cika masa Ruqyan sa da warin jikinsu. Kashe motarsa yayi ya fito yana tafiyar kasaita. Yan kamasho suka yo kansa ya daure fuska.

Ruqayya na zaune ta dukar da kanta tana dana sanin kin zama su taho dasu Ya Munir. Hayaniyar wurin duk ta isheta ga masu talla sun hanata shan iskar kirki. Ji tayi an bude kofar ta dago kai da sauri zata yi fada.. zuciyarta ce ta kusa bugawa da ta ganshi.....taso mu tafi shine kawai abinda ya ce yana dubanta cike da so.











Batul Mamman💖
[7/20, 5:03 PM] Fatima 💖: RUQAYYA YAR ALBARKA✨23





Ruqayya ta dan zaro ido muje ina? Wai me kake yi a nan? Kuma ya akayi kasan ina nan? Muryarta dadi take masa. Nutsuwa yayi yana sauraronta tana ta watso masa tambayoyi kamar wata yar jarida. Sai da yaga tayi shiru tana kallonsa yace duk zanyi miki bayani a mota, kizo mu tafi. Tace amma wasa kake ko ta jawo kofar ta sake rufewa. Mutum na karshe da zai cika motar yazo ya shiga dreba ya gama sallamar dan kamasho ya shiga mota. Prince Richard yace please ki sauko Ruqya. Ta dan tsuke baki ni sunana Ruqayya ba Ruqya ba. Murmushi yayi zan kiraki sweetheart. Sai da taji wani abu a zuciyarta saboda yadda ya fada. Ya salam ta fada a fili...bata kaunar yadda zuciyarta ke tausasa gare shi. Ya sake bude kofar bazan bari ki tafi ba a wannan motar. Zuwa lokacin hankalin sauran fasinjojin ya dawo kansu. Dreba yace yallabai ya akayi ne? Idan tafiya zaka yi ka nemi wata motar wannan ta cika. Prince Richard yace ku bata hakuri ta sauko mu tafi. Wata babbar mata a baya tace kaga malam kana bata mana lokaci menene yake faruwa? Richard ya ce matata ce munyi fada shine zata gudu gida ta barni. Wata matar a baya tace yar nan yaji zaki yi? Ai a wannan zamanin shashasha ke yin yaji. Ya dan rage murya yace mata meye sha-sha-sha. Tayi yar dariya wai kai take nufi. Cikin hausarsa da bata gama kama harshensa ba yace wa matar ni banyi yaji ba. Bana son yaji ma, ciwo yake samin a ciki. Ruqayya sai dariya take. Wani yace hala baka jin hausa sosai. Yace eh amma ku bata hakuri tazo mu koma tare. Nan fa aka shiga bata baki ba jimawa bakin motar ya cika da yan kallo. Yan motarsu duk sun sauko. Ruqayya da taga abin da gaske ne sai tace wallahi karya....bata karasa ba babbar matar da ke tare dasu tace kul, kada na sake jin kin karyata mijinki. Daga samun sabani sai kice yana karya? Mutum irin wannan idan bakiyi da gaske ba kina ji kina gani wasu matan zasu kwace miki shi. Mamaki duk ya isheta yadda ya dage ita matarsa ce mutane suka goyi bayansa. Daga karshe ranta ya soma baci tace da dreban idan bazaka daukeni ba ka bani kudina na nemi wata motar. Prince Richard ya zaro bandir yan dari biyar biyar ya mika masa. Kaga ina da kudi, tace zata je gida ne nace sai next week shine tayi fushi ta fito. Ga motata can na dauko zamu tafi tare.

Ruqayya ta rasa yadda zata yi dashi ta dauko jakarta daga booth din motar gara ta koma gidan Ya Munir kawai. Matsalarta daya ita bata gane garin sosai. Ta juya baya taji ana lahhh, kunga, kalli mutumin can......sai ta juyo taga abinda ke faruwa.  Prince Richard ta gani durkushe akan gwiwoyinsa ya hada hannuwansa biyu yana rokonta. Sweetheart kada ki barni please. Baki kawai ta bude tana kallon ikon Allah. Yasa hannu ya share wani guntun hawaye....dama saboda pregnancy dinta ne bana son tayi doguwar tafiya. Matar cikin motarsu ta taba ta kusa da ita. Meye pregicy  kuma. Dayar tace ciki. Haba shiyasa naga tayi fayau da ita ashe rabo aka samu. Lallai Richard ya iya karya. Banda aure harda ciki kuma. Bata ankara ba taga babbar matar tazo ta kama mata hannu sannan ta kama hannun Richard ta tayar dashi. Tace don girman Allah yar albarka kice kin yafe masa kinji. Murmushi tayi saboda sunan da ta kirata dashi. Murmushin nata yasa aka fara zaton ta yafe masa. Matar tace shi aure ai zaman hakuri ne kinji ko, ki dena saurin fushi ko don lafiyar abinda ke cikinki. Ta kalle Prince kaga idan bata hakura ba wani satin kazo nan zaka sameni. Ina saro kaya ne na kawo nan. Zan baka 'yata ka aura. Yayi murmushi nagode Mama. Ta ce to bashi hakuri kema....harararsa kawai tayi matar tace ashe ban isa da ke ba. Dole tace yi hakuri a hankali. Jakar hanunta matar ta mika masa sannan ta ja hannunta har mota. Da kansa ya bude ta taimaka mata ta shiga. Ya juyo yace da mutanen nagode. Bakin motar tasa wasu suka dawo ana ta daga masa hannu har suka bar tashar.

Ruqayya ta gama hade rai suna dan yin tafiya nesa da tashar tace ka tsaya na sauka. Kamar baiji abinda tace ba ya cigaba da tuki. A daidai bakin wani kanti ya tsaya ya tambayi  mai taxi ta ina zai bi yaje Kano. Mutumin yayi masa kwatance yayi masa godiya. Ruqayya ta daga murya tace ka tsaya na fada maka. Kallonta kawai yayi ya yi mata murmushi. Ta kara kulewa idan baka tsaya ba zan maka ihun barawo. Nan ma shareta ya sake yi. Sai ta dauko wayarta...ji tayi kawai ya fizge ta tura ta wurin kofar gefensa. Indai zata dauka dole ta taba shi. Ganin haka ta shiga dukan kofa tana kuka. Dama glass din motar a dage suke sai taji yasa central lock ya rufe kofofin.

Tun tana kuka tana kokawa da kofar har ta hakura ta dena don lokacin sunyi tafiya fiye da awa daya. Idanunta duk sun kumbura sunyi ja. Duk kukan da take  tamkar tana sukar zuciyarsa ne sai dai gara ya tafi da ita akan ya barta ta zauna a motar haya. Ita kuwa tunaninta me zata cewa su Mami idan ta koma gida? Gashi ta rasa dalilin da yasa suke yawan haduwa. Ba zato taji yace I LOVE YOU....kuma I promise you bazanyi mugun abu gareki ba. Zuciyarta ce ta shiga dukan uku uku...love kuma. Ita kuma rabonta na duniya shine mutumin da ba musulmi ba yace yana sonta? Kawai sai kukanta ya tsananta. Indai suka isa Kano lafiya zata kira M. Hafiz da kanta. Gara ya turo ayi maganar aure tun wuri. Tana tsoron kada yayi mata tsafin da zai sa tace itama tana son sa.

Gefen hanya ya samu yayi parking. Ta dan daga kai taga basa tafiya. Ga ruwa anayi da karfi. Cikin kuka tace ni ka kaini gida. Tissue ya zaro ya mika mata. Ki goge fuskarki muyi magana kinji. Ba musu ta goge....yanayinsa yana karyar mata da zuciya. Ta sake satar kallonsa. Ai shikenan Ruqayya kin gama yawo tunda kika fara ganin kyaunsa. Wani kukan take yi na tausayawa kanta. Dama a hadith ance sai ya kasance tsakanin mutum da makomarsa sai ya rage zira'i sai ya fara aikata aikin da ya dace da wurin. Sai ya shiga...wa iyazu billah. Ya Allah Ka bamu kyakkyawan karshe. Amin

Hannu ya miko zai tabata ta matsa sosai jikin kofa. Richie ta kira shi a hankali. Yaji dadin yadda ta fadi sunan kamar ita ta sa masa. Yace yes. Me kake nema a tare dani? Your love, ina sonki sosai Ruqya. Ya bata labarin lokacin da ya fara ganinta da yadda muryarta tayi tasiri a zuciyarsa. Duk lokacin da kike irin wannan karatun sonki yana karuwa a zuciyata. Nasan yanzu bazaki yarda ba kuma duk iyayenmu bazasu yarda ba suma. Sai dai ina tabbatar miki nine mijinki. Zamuyi aure kuma zamu zauna lafiya. Ta dan tabe baki ko me ya sa kayi wannan tunanin? Yace saboda kina da tausayi. Kuma kema kina so na. Kuma akwai wani special bond tsakaninmu. Tayi saurin cewa Allah Ya tsari gatari da saran icce. Hausar tasa bata kai nan ba sai bai bata amsa ba. Ganin ruwan ba mai tsayawa bane da wuri sai ta dauko karamin Qur'anin ta ta bude ta fara karanta suratul Sajda.

Kirjinsa ya dafe saboda tsananin bugun da zuciyarsa take yi. Ko kalma daya bai fahimta ba amma ya shiga wannan yanayin da ya saba shiga idan tana karatu. Ji yake kamar ya rungumeta. Sai dai kuma baya son ya tsoratata. A hankali ta dan kalli shi, yau ma hawayen yake yi sosai. Wane irin mutum ne wannan ta tambayi kanta. A lokacin ta tuna mafarkin da tayi dashi. Kila wannan haduwar tasu Allah Ya nuna mata. Kuma ai tayi addua akansa. Tayi imani Allah maji rokon bayinSa ne. Hankalinta kawai sai ya kwanta dashi.  Sai da ta kai ayar karshe  tace Richie zaka karbi Islam yanzu? Da kyar yace mata ni ba addininki nake so ba ke nake so. Idanunsa a rufe suke saboda yadda yake ji kamar ana hura masa wutar sonta. Tayi masa murmushi wanda ya kara mata kyau. Maybe kana sona amma addinina ne ya kawoka gareni. Ya bude ido, Ruqya nasan kinyi min tsafi ne kuma ya kamani sosai amma bana ganin laifinki. Ki amince ki aureni don bazan taba yarda son da nake miki ya kare a waje ba. Ina da duk wani abu da zaki bukata a duniya. Yanzu kuma ai lallaba shi zata yi tunda ta yarda har ranta tasirin Al Qurani ne yake taba masa zuciya. Allah Kasa yana da rabo ta fada a fili tana dubansa. Sai yanzu taji sonsa da gaske a zuciyarta. Ta kuma amince dashi don tana ganin akwai nasara...ita ma zata shiga jerin masu jihadi.










Batul Mamman
[7/21, 10:39 AM] Fatima 💖: RUQAYYA YAR ALBARKA✨24





Yana tuki yana satar kallonta. Idanunta a rufe suke ta dafe kai da hannu daya, tunanin yadda su Abba zasu karbi lamarin take yi. Yana son yi mata magana amma baya son ya dameta. Can ta bude ido tace Richie. Yana son yadda take kiransa. Ya dan dubeta, idan kina kirana Richie sai naji kamar nayi kissing lips dinki. Taji kunyar abinda ya fada don yaga yadda ta sunkuyar da kanta kasa. Shi hakan ma ya bashi shaawa. Tace a addini na ba'a son magana da ta shafi irin wannan tsakanin mace da namijin da ba aure tsakaninsu. Yace wace magana kenan. Ta kawar da kai gefe ta kara rage murya irin wadda kayi yanzu. Ya shafa kansa...oh you mean bazan fadi gaskiya ba. Da gaske ina so, yanzu ma don ina tuki kuma nayi miki promise bazan miki komai ba amma da tun ranar nan a asibiti na.....ta daga masa hannu am serious bana son irin maganganun nan. Musulmin kwarai baya irinsu . Yace to ai ban zama ba. Sai munje Kano nake son na karanci mutanenku sannan ki fada min reasons dinki da kike ganin ya kamata na karbi addininki. Indai wannan ne kada ka damu. Ina fata kana da masauki ko? Yayi murmushi yes, dakinki zamuyi sharing. Ruqayya ta dafe kai...ba yanzu na fada maka ba'a irin wannan maganar ba? Turo baki yayi yadda ya saba yiwa Mum dinsa shagwaba, to yanzu me na ce kuma. Ke a garinku ba'a sharing ne? Nufina mu kwana a dakin amma bazan damu ba ko a kasa na kwana. Kawai dai bazan so kwana nesa dake bane. Ruqayya tace yau na dauko ruwan dafa kaina. Yayi saurin kallonta ina ruwan? Ki bari muje gida sai na daukar miki. Girgiza kai kawai tayi. Aikin nata da yawa indai akan Richie ne.

Suna tafiya yana janta da hira har suka iso Kano. Tun daga wuraren kwankwasiya city cikinta ya duri ruwa. Bata san yadda zasu kwashe iyayenta ba. Tace wai ya maganar inda zaka kwana ne? Ya fahimci duk ta damu yace ba dai akwai hotels ba. Ta gyada kai, to mu fara zuwa ki nuna min wanda yafi kyau sai na kaiki gida. Ruqayya tace tabdi ka ajiyeni dai na shiga adaidaita sahu ka kama gabanka. Cikin rashin fahimta yace kamar yaya na kama gabana? Dariya tayi kawai Richie ba hausa ta fada tana cigaba da dariya. Dagewa yayi sai da ta nuna masa hotel daya. Suna zuwa gate din yace to mu shiga na kama daki sai mu wuce. Tace wa ni??? Rufa min asiri don Allah kada ka shiga. Ya sha kunu yanzu dakin da zan kwana ne bazaki tayani zaba ba? Ganin ya tura motar hanyar gate yana shirin karbar gate pass yasa ta soma hawaye da gaske. Wai ita dama in ba hauka ba ina ita ina wani Prince Richard. Ribas yayi da motar ya ce tayi masa kwatancen gidansu. Shiru tayi kawai tana kukan bakinciki. Ji tayi yace Ruqya...cikin muryar kuka tace RU-QAYYA sunana. Yace naji Ruqqayya. Ki dena kuka kinji. Trust me, Prince Richard da dukkan abinda yake dashi naki ne daga yau. Bani da niyar cutarki ko kadan. Tsokanarki nake yi kika yi tunanin gaske ne...tsakaninmu amana ne. Ko sonki zai kasheni bazan taba saki kiyi abinda addininki baya so ba. I love so much. Jikinta duk yayi sanyi ta share fuskarta suka tafi.

Da kyar ya yarda ya ajiyeta a kan kwanar layinsu tare da bata wayarta. Sai da yaga ta shiga gida sannan ya koma hotel din. A lokacin ya tuna yana jin yunwa sosai ya kwana biyu bai ci wani abin kirki ba. Restaurant din cikin hotel din yaje ya cika cikinsa sannan yayi wanka ya kwanta. Rabonsa da tuki mai nisa ya manta.

Ita kuwa Ruqayya ranar gidansu sai murna. Iya Tasallah tace gaskiya idan kika yi aure kewarku zata yi mana yawa. Suka sha hirarsu da iyayenta. Tana idar da sallar magriba Gali almajirinsu ya rakata gidan Mummy. Haj Maryam da bata san zata zo ba tayi mamaki. Suka rungume juna cike da murna. Abba B ma yana gidan ta zauna suna hira sai karfe tara ta koma gidan. Da yake wayarta ta sa a chaji kafin  ta fita kuma da ta dawo wata hirar suka dasa sai bayan shadaya ta shiga daki. Missed calls sunfi hamsin duk na numbar da bata yi saving ba. Amma tana gani tasan kiran na waye. Ta duba dare yayi sai kawai ta tura masa text. Goodnyt Richie.
Bata ajiye wayar ba wayarsa ta sake shigowa tayi saurin dauka. Ba kya sona ko? Ita ce tambayar da yayi mata. Tace kayi hakuri nasa chaji ne. Kuma sai na fita na bar wayar a gida. Am sorry Richie. Ajiyar zuciya taji yayi, I was worried sosai. Kinji kaina har yayi zafi yana min ciwo. Tace sannu kasha magani mana. Yace no need, zai dena tunda naji muryarki. Bacci nake ji Ruqqaya. Tace to ka kwanta mana. Ai na kwanta baccin ne na kasa. A gida ana yimin tausa every night. Ta rike baki to a nan sai dai kayi wanka da ruwan zafi ka kwanta. Muryarsa can kasa yace dazu na kasa kunna ruwan zafi da mai sanyi nayi. Ruqayya tace Subhanallah, baka nemi maaikatan wurin su taimaka maka ba? Yace mata ni a gida ko da shower zanyi wanka sai an daidaita ruwan ake kirana. Kace kawai sun shagwaba ka. To kayi hakuri a hankali zaka koya. Yace kamar zanyi mura nake ji, ke kuma kika sa min damuwa. Duk bani da lafiya. Muryarsa kamar mai shirin kuka. Bata san lokacin da tace ka fiye raki da shagwaba. Kawai rufe idonsa yayi ya shige  bargo  ya rasa yadda zai kwanta yaji dadi saboda katifar bata yi masa yadda yake so ba. Kiyi min karatun nan ko na minti daya ne maybe nayi bacci. Wani dadi ne ya kamata ta kankame wayar, harda gyaran murya sannan ta karanta masa Ayatul Kursiyyu. Dadin muryarta yasa ya gyara kwanciya. Ta karanta sau bakwai sai taji yanayin numfashinsa ya chanja. Tace Richie? Shiru yana can bacci ya dauke shi. Fasa kwanciya tayi don murna taje tayi alwala tayi nafila tana rokon Allah Yasa tayi nasara akan Prince Richard.







Batul Mamman💖
[7/21, 6:10 PM] Fatima 💖: RUQAYYA YAR ALBARKA✨25





Queen Amelia ta shiga matsananciyar damuwa bayan sakon Richie ya risketa. Ko kadan bata yarda aiki ne ya kaishi Abuja ba. Zuciyarta tafi bata guduwa yake son yi daga auren Princess Sophia. To itama dai tana ganin yarinyar ta fiye naci. Da tun farko ta hakura dashi bazata ga wulakanci irin haka ba. King Edward dai yayi ta fada akan me zaiyi tafiya daga yi masa baiko. Ya kamata a fara shirye shiryen bikin gargajiya da zaayi masa da matar da zai aura. Kuma abin takaici babu wani layinsa da ake samu a waya. Hankalinsu ya kwanta ne bayan sun sami labarin tabbas yana Abuja don har mota ya siya. Queen Amelia tace ni yadda zaiyi komai shi kadai yana damuna. Dana bai iya yiwa kansa komai ba. King Edward ya harareta ai duk ke kika bata shi. Madam Hannah tace suyi hakuri ita zata koma gida. Idan ya dawo a tura mata shi tana son ganinsa.

Wayar Richie ta biyar kenan yana tambayarta yaushe zasu hadu. Ruqayya ta rasa yadda zata yi dashi. Tana tsoron kada ya zo gidansu don ba karamin aikinsa bane. Karshe dai Mami ta lallaba ta barta taje gidan Hidaya. Tana rufe gate din gidansu ta hango shi yana gyara parking din mota. Subhanallahi ta fada tana sauri ta karasa wurin shi. Sai masifa take shi kuwa farinciki yake ya hangota baya jin abinda take fada. Kamar baka da hankali zaka zo kofar gidanmu. Salon ka jawo min matsala. Nima wanda ya aikeni sauraronka. Tun jiya duk bayan yan mintuna sai nayi nadamar haduwa da kai. Kafin ta karaso wurin motar ya fito ya bude mata seat din gaba. Ta daure fuska idan ba kare kare tayi masa ba bata jin zasu zauna lafiya. Me kake yi a nan? Yasan sarai ya bata mata rai amma babu yadda ya iya da zuciyarsa. Yayi mata murmushi kiyi hakuri nayi laifi ko? I just want to see you. Idan kina so yanzu ma sai na koma. Ta harare kamar gaske. Gidan yayata zani ka sameni a can zan maka kwatance, ko kuma ka biyo bayan motar da zan hau. Tuni ya hade fuska shima. Ni kike fadawa na biyo bayanki a public transport? I am a prince ya zaayi matata ta shiga taxi. Sosai taga bacin ransa. Tace to na fasa amma ka dena zuwa nan please. Naji ya bata amsa fuskarsa a daure. Muje na ajiyeki. Zanje neman gida ne nima. Sun fara tafiya tace wane irin gida kuma? Shi fa har yanzu ransa bai gama sakewa ba, wai kamarta tace zata bi motar haya...haba sai dai idan ya mutu. Yana ci mata magani yace aure nazo yi a Kano so ina neman gidan da zan ajiye matar. Tayi dariya eyye yar gata, har an baka ita ne da zaka nemi gida? Ya kara shan kunu a dole an bata masa rai. Za'a bani ita, she belongs to me. Ruqayya tace ina tayaka fatan hakan. Tana tsoron ranar da za'a hanata aurensa ko da ya karbi musulunci.

Sun kusa zuwa gidan tace ya tsaya a gefen hanya zata sauka. Kafin nan ta hado masa litattafai kala kala na manyan malamai masu muhawara akan addini kamar su marigayi Dr Ahmad Deedat. Tace kada ka neme ni sai ka karance su duka da zuciya daya. Ya duba zasu kai shida. Anya basuyi yawa ba? Tace indai kana sona zaka karanta ka fahimta ka sanar dani. Yace to ba komai zanyi. Amma menene Islam dinnan? Ta gyara zama...Musulunci shine mika wuya ga Allah SWT. Ka kadaita Shi, ka tsarkake Shi, ka bauta maSa Shi kadai ba tare da kishiya ba. Richie yace naji wannan amma a wane dalili ne zan bautawa God daya, idan wata rana nazo ina rokonsa bai bani abinda nake nema ba fa? Kinga a irin wannan time din sai na nemi kananan su taimaka min. For example a garinmu muna da goddess. Dayake mace ce tana da tausayi. Da wahala mu tambayeta bata amsa ba.

Ruqayya na daga gefe cewa take uhmm uhmm Allah Sarki. Har ka bani tausayi. Allah SWT shi kadai ne bashi da abokin tarayya. Gyangyadi ko bacci bai taba daukarSa ba. Yana sane da dukkan wata halitta komai kankantarta. Bazaka gane waye Allah ba sai ka saurari zancen Annabi Muhammad SAW. Domin Allah Yace musan Shi kafin mu bauta Masa. To sanin Allah kuma sai wanda ya gaskata manzancin Annabin karshe. Wadannan books din zasu tabbatar maka da cewa hakika Allah SWT Ya sanar da AnnabawanSa Isah AS da Musa AS da dukkan Annabawa zuwan Muhammad SAW. Ba wani balarabe bane da ya zauna ya kirkiri magana ya kawo mana a matsayin manzo. Idan har ka yarda da cewa lallai Muhammad manzon Allah ne to daga nan sai mu fara duba sakon da ya kawo gaskiya ne ko kuwa ba abin yarda bane kamar yadda wasu suke tunani. Richie ya yi murmushi kin iya tsara zance my love. Zan karanta amma sai naga reasons masu kyau a ciki zan yarda. Tayi murmushi lallai bai san yadda malaman musulunci masu ilimin gaskiya suke bata tunanin manyan pastors da ma'abota bautar gumaka ba. Kaje ka karanta Richie, ni na yarda da kaina na yarda da addinina. Allah zai bude maka kwakwalwarka indai da gaske kana neman shiriya. Daga nan suka yi sallama ya tafi ita kuma ta karasa gidan Hidaya.






Batul Mamman💖
[7/22, 4:19 AM] Fatima 💖: RUQAYYA YAR ALBARKA✨26






Har lokacin bacci ba wayar Richie ba text. Tun Ruqayya na basarwa har dai ta shiga damuwa sosai. To ko dai ya bar garin ne? Kila ya fasa karbar addinin? Allah Yasa dai ba rashin lafiya yake ba. Wadannan tambayoyin ta rinka yiwa kanta har bacci ya soma daukarta wurin biyun dare.

Shi kuwa Richie yana zaune a tsakiyar gado ya baza littafai. Ciki akwai What is His Name? , Is the Bible  God' Word?, Christ in Islam,  What the Bible Says About Muhammad, Was Jesus Crucified? Haba Ruqayya ta gwara masa kai sosai. Karatu yake amma gani yake kamar baya sauri. Ya jike sharkaf da gumi amma ya manta da batun kunna AC ko fanka. Daga baya laptop ya dauko yana karatu yana browsing. Wuraren hudun dare ya dauki waya batare da kula da lokaci ba ya kira Ruqayya.

Ta mika hannu ta kashe a tunaninta alarm ne sai taji kidan da yake tashi alamun kira ne. Ta duba lokaci dare yayi sosai kuma wayar Richie ce. Da sauri ta dauka tasa wayar a kunne. Kafin tayi magana yace menene yasa akace babu wanda yafi wani a wurin Allah sai wanda yake tsoronSa sosai. Ruqayya ta tashi zaune sosai ta share idanu. Wai me kake yi baka yi bacci ba ta tambayeshi. Ki amsa min question dina kawai. Ina da karatu a gabana. Taji dadin amsarsa duk da ba niyarta ya kasa bacci ba. Tace Allah SWT Ya halicci mutane da yawa  duniya. Talaka, mai kudi, mai mulki da mai sarauta. Cikinsu kowa ya dogara da dayan domin rayuwa ta tafi daidai. A musulunce Annabi SAW ya fada mana babu wanda yafi wani a wurin Allah sai wanda yafi tsoronSa. Maana kada mai kudi ko mai mulki ya raina talaka saboda bashi da kudi. Shi Allah zuciyarmu yake kallo ba sutura ba. Idan Ya baka kudi jarabawa ce Yaga ko zakayi amfani dashi wurin taimakon masu bukata ka kyautata rayuwar wasu. Shi kuma talaka Allah na duba hakurinsa ne akan yanayin da ya tsinci kansa. Saboda haka kada ka taba raina mutum domin baka san abinda yake dashi a wurin Allah ba wanda baka dashi. Haihuwarka cikin arziki ba yin kanka bane. Da ana zaba kila da duk yan Nigeria sun ce Dangote ya zama babansu. Tsari ne na Allah wanda babu wanda ya isa ya canja.  Amsarta ta gamsar dashi sosai. Ya sake jefo mata wata tambayar...idan raina ya baci a musulunci me ya kamata nayi? Ruqayya tace to da farko idan a tsaye kake ana son ka zauna, idan kana zaune sai ka kwanta ka karanta wannan adduar Allahuma ajirni fi musabati wa alkhlifni khairi minha. Da Innalillahi wa inna ilaihi rajiun. Kayi ta yi har sai kaji sauki a ranka. Yace idan da beer(wani na'uin  giya) mai sanyi ai zatayi saurin cooling dina. Ko kadan inji Ruqayya, karshe ma dai hauka zata saka ka. Idan kasha giya na dan lokaci zaka manta komai kaga hauka yazo kenan. A irin wannan yanayi har dukan mutane akeyi ko ka fadi wani sirrinka da zaka yi regretting fada idan ka dawo hayyacinka. Richie yace kuma fa gaskiya kika fada. Sai yayi tunanin abu da yake ganin ba lallai bane yayi mahimmanci a addini. To idan zan sa sabon kaya fa? Ta karanto masa adduar. Tsoho fa? Nan ma ra karanta. Shiga jirgi fa? Ta karanta masa adduar tace da mota, jirji, babur da duk wani abin hawa koda dabbace duk haka zaka ce. Duka tanayi tana fassara masa da turanci. Idan zan shiga toilet fa? Ta karanta adduar tana dariya. Tasan kureta yake son yi. Haka yayi ta mata tambaya ita kuwa tunda ta haddace Husnul Muslim shi ta kure. Karshe yace yana yar dariya nasan dai bakya so amma ina son sanin ko har a nan Annabinku bai barku ba. Idan zan kwanta da matata me zan ce? Yana dan murmushinsa na keta ta karanta adduar tare da bayanin dalilin yinta. Richie yace na yarda Muhammad ba karyar Prophethood yayi ba. Amma har yanzu ina bukatar abinda zai kara tabbatar min da gaskiyarsa. Ruqayya tayi Hamdala a zuciyarta tace idan ka gama da books din lokaci yayi da zan gabatar maka da Al-Quranil Karim.

Daga wannan daren bata sake ji daga gareshi ba itama kuma bata bi bayansa ba. Bazai wuce yana ta bincike ba. Adduarta Allah Yasa a dace. A kwana takwas din da bai nemeta ba wani mai shara ya samu a hotel din ya tambaya ko akwai malami mai rikon addini da gaskiya. Yaron tace akwai su da yawa. Daga nan ya nuna masa wani masallaci inda Dr Abdallah Saraki (Meye Dalilinka) yake tafsir. Kullum bayan karfe goma Richie zai shirya ya tafi masallacin. Ya yanke shawarar dena neman Ruqayya har sai ya nemi gaskiya da kansa. Baya so soyayyarta ta rufe masa ido yaje ya karbi tsafi ko wani mugun addini. So yake ya gano gaskiya da kansa don yanzu ya damu yasan dalilin zuwansa duniya. Kullum yana zama idan zasuyi sallah sai ya fita. Lokacin tafsir kuma ya dawo ayi dashi. Anan ya lura da dan dako da Alhaji kowa shiga sahun sallah yake a hada kafafu wuri daya. A rana ta bakwai  ne yana waje a zaune suna sallar magriba bayan an idar yaji an taba masa kafada. Dama dai wasu kan miko masa hannu su gaisa amma yau ji yayi an taba shi. Ya mike tsaye yana kade bayan wandonsa. Suna hada ido gaban kowannensu ya fadi. Jikinsu ya danyi sanyi. Suka dan dauki lokaci suna duban juna sannan Barrister Mukhtar yace bawan Allah me kake yi a nan? Na lura kana zuwa masallacin nan kusan kwanaki uku ina kula baka sallah tare damu. Richie ya sake kallon mutumin. Haka kawai yaji wani abu a ransa. Yace masa ni ba musulmi bane. Barrister Mukhtar yayi mamaki amma sai yace ina fata ka sami amsar da kazo nema a nan. A dan firgice Richie yace wa ya fada maka abinda nazo yi? Barr ya dafa masa kafada ya ja shi har cikin masallacin. Zuciyata ce ta bani ba da mugun nufi kazo ba. Ka dena bata lokaci ka rungumi gaskiya shine kawai kwanciyar hankalinka.

Gaban Dr Abdallah suka je bayan sun gaisa irin gausuwar abokai, Dr Abdallah yace Barrister yaron nan yana yanayi da kai musamman tafiyarku. Murmushi kawai Barr Mukhtar yayi yace da Richie ka gabatar da kanka. Sunansa kawai ya fada musu sannan ya basu labari tun farkon haduwarsa da Ruqayya. Duk su biyun da mutanen dake tare dasu kowa ya kadu da jin ikon Allah. Dr Abdallah yace idan ka amince ba bisa tursasawa ko tsoro ba zan baka maganin duk wata fargaba da rashin nutsuwar da kake fuskanta a rayuwarka. Kana cikin mutanen da muke kyautatawa zaton rahmar Allah na tare dasu shiyasa kazo neman gaskiya. Prince Richard yace a tsaya yana da tambayoyi. Nan ya rinka yi ana bashi gamsassun amsoshi. Yace da Barr Mukhtar ko zaka karanta min wani abu a cikin Quran. Bismillah yayi ya fara karanta suratul Fatiha. Kafin ya kai karshen ayar farko sauran yan masallacin harda Dr Abdallah suka kama. Prince Richard yaji wani sanyi da rahma a ransa. Sunayi yana kuka har suka kai karshe. Yace I want to be a muslim. Da masu jin turanci da marasa ji suka hau kabbara. A take Dr Abdallah ya karanta masa kalmar shahada yana maimatawa.
ASHHADU ANLA'ILAHA ILALLAH WA ASHHADU ANNA MUHAMMADAR RASULULLAH. Ya karanta masa ya fassara masa da turanci don ya fuskanci hausar tasa da saura. Sai ga maza harda wasu daga waje da suka ji yadda masallacin ya kaure da kabbara suka shigo suna rungume shi. Sai yau sai yanzu Prince Richard yaji zuciyarsa ta koma sakayau kamar an zare masa kibiya. Dr Abdallah yace wane suna kake so? Richie ya kalli Barrister Mukhtar yace kaine BABANA a musulunci ka samin  suna. Hawayen farinciki suka saukowa Barrister yace idan ka amince sunanka UMAR FAROUQ. Farouq yana nufin mai banbance karya da gaskiya. Shine khalifa na biyu a musulunci. Prince Richard dadi ya kamashi mara misaltuwa sai kawai ya rungume Barrister Mukhtar yana kuka sosai.

Ruqayya na daki tana karatu taji wani sanyi a ranta. Sujjada tayi tana mai kara rokon Allah Ya azurta Prince Richard da samun haske a rayuwarsa ko da ba aurensa zata yi ba.





Batul Mamman(Mrs)💖
[7/22, 11:15 AM] Fatima 💖: RUQAYYA YAR ALBARKA✨27





Bai bar masallacin ba sai da Dr Abdallah ya hadashi da wasu dalibansa su biyu kusan sa'aninsa wadanda zasu rinka koya masa al'amuran addini. Sannan ya bashi shawarar shiga makaranta. Umar Farouq jin kansa yake kamar wani jariri. Mutanen wurin kowa na son kusanci dashi. Wani da gidansa yake kusa mai suna Mujahid yace lokacin sallar Isha ya kusa ya kamata yayi wanka da alwala ko? Kowa ya amince da haka. Suka tafi tare da wasu yayi wanka kamar yadda suka koya masa. Sannan yana kallo ana alwala yana bi har suka gama. Kaya masu kyau mutumin ya bashi sai kamshi suke ya saka ba tare da jin kyankyami ba. Kodayake wannan ba Richie din da bane.

Ya bisu sallah kamar yadda yaga sunayi a yan kwanakin da yake zuwa masallacin. Bayan yayi sallama da mutane Barr Mukhtar yace masa daga wane gari kake ne? Ya amsa da cewa daga kudancin kasar nan yake wani gari Ndam. To idan baka da masauki zanso ka dawo gidana. Richie.....au Umar Farouq yace ina da masauki. Amma ka bani address dinka don nazo. Kamar yadda na fada kaine Babana a nan. Da taimakonka na zama sabon mutum yau. Barr yaji dadi sai yace bari na baka numbar wayata dai. Matata tayi tafiya ne zuwa kyauye sai next week zata dawo. Nasan zatayi farincikin haduwa da kai. Itama zata mayar da kai danta. Idan ta dawo kayi min alkawarin zaka zo. Murmushi kawai yake na jindadi yace zan zo. Barr Mukhtar yace kace In sha Allah. Ya maimaita sannan suka yi sallama.

Murna yake sosai har ya isa kofar gidansu Ruqayya. Lokacin tara na dare ta wuce. Yayi ta kiran wayarta a kashe. Dole ya hakura ya koma hotel dinsa yana dokin gari ya waye yayi mata kyakkyawan albishir.

Bayan ta idar da sallar asuba ta dauko wayarta da ta kwana jikin socket ko da zaa kawo wuta tana bacci. Sun yini ba wuta ga injinsu ya lalace. Ta kunna ba laifi ta kusa cika. Sai kawai ta kira Richie don ta tabbatar ba guduwa yayi ba . A lokacin bacci yake maidadi, mafarkinsa yau ya nuna masa suna zaune karkashin inuwar wata bishiya shi da Ruqayyansa suna karatu. Karar wayar ce ta tashe shi ya dauka yana murmushi ganin sunan mai kiran. Salam alakum taji ya fada cikin murya mai nuni da mutum ya kwana cikin kyakkyawan yanayi. Tace Assalam alaikum wa rahmatullah wa barakatuhu ake cewa Richie. Yace ke baki iya koyarwa ba. Da kadan kadan ya kamata ki fada yadda zan rike. Wane Richie kike kira? Wato har kin manta dani kike kiran wani old boyfriend dinki ko? Wayar ta cire daga kunnenta ta sake duba numbar tunda bata sa masa suna ba. Tabbas haka take numbarsa ce. Kana neman confusing dina. Ba confusing dinki zanyi ba my love, ina son kiji wani abu mai dadi ne yanzu. Kalmar shahada taji yayi duk da larabcin akwai gyara sosai. Sai kuma ya maimaita da turanci. Sannan ya bata labarin abinda ya faru kwanakin da baya nemanta. Da ya gama shiru yaji bata ce komai ba. Ruqqayya nayi miki laifi ne? Sautin kukanta yaji tanayi tana cewa Alhamdulillah. Sai da tayi kukanta na murna cike da kunya tace I LOVE YOU Prince Richard, dama alkawarin da ta daukarwa kanta kenan. Ranar da ya musulunta zata tabbatar masa da yadda take ji game dashi. Yayi shiru yana jinta. A rana daya Allah Ya bashi sabuwar rayuwa kuma ya sami soyayyar yarinyar da yake matukar so. Halin da zuciyarsa take ciki abu ne da bazai iya kwatantawa ba. Yaushe zamuyi aure Ruqqayya? Tambayar tayi mata nauyi wata kunya ta kara dirar mata. Da ace munyi aure yau da na nuna miki irin yadda sonki yayi yawa a raina. Kece dalilin da zuciyata ta fara son neman purpose din rayuwa. Bazan taba iya rabuwa dake ba don Allah kema ki zauna tare dani. Babu abinda bazan iya yi miki ba don nasa ki farinciki. Allah Yayi miki albarka. Tace Allah Yayi min tunda Ya amsa adduata. Fada min sabon sunan mijina naji ko da dadi. Ba don yadda ya wargaza dakinsa ba saboda rashin iya gyara da ya zuba ruwa a kasa yasha. Wai shi Ruqayya ke kira mijinta. Yace sabon baban da nayi yasa min Umar Farouq. Ji yayi tace ina sonka Umar Farouq. A zuciyarta tana kara godiya ga Allah da Yasa alkhairi a saurarensa da tayi ba sharri ba. Don kullum adduarta kada Richie ya zama silar lalacewar rayuwarta. To amma Umar Farouq suna biyu ne na mutum daya. Ka amince matarka ta kiraka Farouq kawai? Na amince ya bata amsa. Sun fi rabin awa suna hira tare da jaddadawa juna soyayya. Cikin hirar ne tace wai kayi sallar asuba kuwa? Yayi saurin ture bargo banyi ba. Ita guda nawa ce? Ta ce biyu ce. Haka yayi alwala iya yadda ya iya tunawa yayi sallar ba karatu sai kabbara. Har kunya sai da yaji don yasan ba haka ake yi ba.

Bayan ya idar ya sake kiranta yace ta bashi izini yazo gidansu. Tace yau zata koma makaranta idan ta dawo zata fada masa lokacin da zai zo. Karfe tara yayi wanka ya sauka yaci abinci ya koma masallacin nan neman masu koya masa addini. Sallah ce tafi damunsa ma. Bai bar wurin ba sai bayan da suka idar da sallar azahar. Da tambaya ya nemi College of Quranic Studies inda Ruqayya taje registration don bazai iya jiran har sai can yamma ya ganta ba. Kwanakin da basu hadu ba da kewarta yake kwana amma dole tasa ya hakura.

Mami na dan bacci taji an dira a kanta. Ta mike da sauri tana cewa Ruqayya yaushe zaki girma ne? Ga mamakinta sai taga Abida. Suka rungume juna cike da murnar ganin juna. Mami tace saukar yaushe? Jiya muka zo Mami wurin shadayan dare shine yace mu wuce gidan Umma kada mu tada muku hankali. Amma ba wani satin kika ce zaku zo ba? Eh da sai wani satin to jiya bayan azahar ya  dawo yace an basu hutun sati daya shine yace mu taho kawai. Mami tayi mata fadan tafiyar dare da suka yi. Ina Munir din? Ya tafi makarantar su Ruqayya wurin Malam Hafiz. Jaje zaiyi masa an sace masa mota shekaranjiya a kofar gidansu. Mami tace barawo ba imani. Yaro ya dade yana tari motar duka duka bata jima ba. Ni bani da labari ai da nayiwa mamansa jaje.

Ya Munir na shigowa gate din makarantar yabi hanyar office din abokinsa. Ruqayya ya gani tana tafiya zuwa wurin da dalibai ke parking abin hawansu. Fuskarta dauke da murmushi. Duk da hijab ta saka amma tayi kyau. Yace hmm kanwata ko ina zuwa? Har zai wuce idan ya fito ya nemeta su gaisa ko su tafi gida idan ta gama ya hango wata dalleliyar mota mai kyau. Daga mazaunin dreba yaga an fito kuma ga dukkan alamu nan Ruqayyan ta nufa. Zuciyarsa ta kusa bugawa ganin wanda ya fito daga motar. Shakka babu kallon soyayya suke yiwa juna ita da Prince Richard. Ransa yayi mummunan baci saboda irin mugun tunanin da yazo kansa. Me suke yi tare? Ya akayi ya biyota kano? Ko rufe motarsa baiyi ba ya fito daga ciki a fusace yayi kansu.





Batul Mamman(Mrs)💖
[7/22, 3:02 PM] Fatima 💖: RUQAYYA YAR ALBARKA✨28





Babu wanda ya ga tahowar Ya Munir cikinsu. Wayarta tayi kara ta dauka...Farouq ne yake kira. Har tana hango shi yana mata nuni da ta amsa wayar. Tana sawa a kunne yace da ke matata ce zuwa zanyi na daukeki na sakaki a mota. It seems kin gaji da yawa ba kya son tafiya. Hmmm wai yaushe aka koya maka sani jin kunya? Bata kai ga jin abinda zai fada ba taji an kwace wayar daga bayanta. Tana juyowa aka dauketa da marin da yayi matukar gigita mata lissafi. Tuni idanunta suka kawo ruwa ta soma kuka bayan ta gane waye mai marin. Farouq ma saurin karasowa yayi wurinsu ganin Ya Munir zai kuma marin ya rike masa hannu. Da turanci Ya Munir ke masa magana sanin cewa idan yayi da hausa wasu kalmomin da zai fada ba lallai Prince Richard ya gane. Idanunsa jazur kamar gauta don tsananin bacin rai. Ashe kai dan iska ne ban sani ba?  Na daukeka abokina ka zo kana cin amanata. Me ya hadaka da Ruqayya? Yaushe ka biyota har kuka kulla alaqar da tasa take zuwa gareka? Farouq yace kayi hakuri Munir dalili ne yasa muka boye muku. Amma komai ya daidaita yanzu babu dalilin da zaisa ku hanani auren Ruqayya. Ya Munir ya kalle shi a wulakance. Kai har ka isa ka auri Ruqayya? Wulakantacce, manemin mata, kafiri kamarka. Ya juya ya kalli Ruqayya wadda ta dafe kumatunta tana kuka...ke kuma da kika biyewa son zuciya ki wuce mu tafi. Richard bashi da kirki ko kadan, bai dauki mace a bakin komai ba. Nasan ya gama bata miki rayuwa. Haba Ruqayya har nawa ya baki kika sayar masa da mutumcinki. Ran Farouq ya baci sosai jin yadda Munir ya jefeta da kalma mara dadi irin wannan. Ga mutane sun fara taruwa amma duk da haka sai da ya cakumi wuyan rigar Munir. Kada ka sake zagar min mata. Munir yace babu ruwanka da abinda zan kirata don kanwata ce. Na fada din ka mayar min da kanwa karamar karuwa. Tassss yaji saukar mari a kumatunsa shima. Farouq yace bazan yafewa duk wanda zai fadi mummunar kalma ga matata ba. Shi kuwa Munir kalmar matar ne ya kara tunzura shi suka rike juna suna fada sosai. Munir bakincikinsa bai wuce ya dauko wanda ya gurbatawa su Mami yarsu ba. Me zaice da iyayen yarinyar nan? Shi kuwa Farouq bacin ransa akan rashin kwakkwaran bincike daga abokinsa har yake furta masa kalamai marasa dadi.

Ruqayya dai sai kuka takeyi tana cewa su bari jikinta sai rawa yake saboda yadda ta tsorata. Mazan wurin suka taru ana kokarin rabasu kowanne yaki cika dan uwansa. Har security sai da suka zo su biyu abu yaki karewa sai ga jiniyar 'yan sanda. Mota guda ce ta shigo dayake akwai station a kusa dasu. Security daya ne yaje ya kira su. Gabadaya su ukun aka saka su a bayan mota suka tafi.

Sergent Bako ya tura Munir da Farouq cikin cell ya rufe bayan ya karbe wayoyinsu ya dauki jawabinsu wanda shima suna fada masa suna yiwa juna masifa. Yace bari DPO ya shigo. Ita kuma Ruqayya aka bata kujera ta zauna tana ta sharar hawaye. Ta tambayi sergent din ko zata iya buga waya ya bata izini. Abbanta ta kira tana kuka ta fada masa station din da suke tace ya taho.

Engr Muhammad cikin meeting wayar ta shigo. Ganin tana kira yana katsewa amma bata dena kiran ba dole ya nemi izini ya fita ya amsa wayar. Abinda ta fada yayi matukar razana shi, saboda tsoro ya kira Mami yana tambayarta me ya hada Ruqayya da Munir a Abuja har suka kare a police station. Itama ta kadu ta jefa tambayar ga Abida mai cin abinci. Ita kwarewa ma tayi sannan tayi rantsuwar babu abinda ta sani. Anti Gaji mahaifiyar Munir itama sun sanar da ita  suka dunguma gaba daya zuwa ofishin yan sanda. A can suka tarar da Abba ya rigasu isowa yana rungume da Ruqayya tana ta kuka. Mami ta karasa da gudu tana tambayarta me ya hadasu ita da ta tafi makaranta. Abida ma kuka take don kan kowa a kulle yake. DPO Bala ya bukaci kowa yayi shiru sannan ya kirasu zuwa office dinsa. Daga nan yace sergent Bako ya fito da masu laifin. Kayan jikinsu duk sun yamutse kowanne yaji jiki a wurin dan uwansa. Umma wato Anti Gaji tace Munir me nake gani haka? Abida kuwa banda mijinta idonta ya gane mata ko waye dayan. Ta dafe kirji tace Prince Richard??? Me kake yi a Kano, me ya hadaku fada Ya Munir? DPO yace su natsu ayi bayani. Ya Munir ya nuna abokinsa yace ga wadanda basu san shi ba wannan aminina ne tun secondary school. Zama ne na amana tsakaninmu dashi duk da bambancin addini da yare. Sunansa Prince Richard Edward. Babansa yana da kudi sosai kuma sarki a wani gari Ndam. Aikin da nake ma taimakon babansa ne Umma da Abida sun sani. Zuwan Ruqayya hutun nan yazo har suka dan sami sabani karshe ya kaishi ga kwanciya a asibiti. Daga baya ya nuna komai ya wuce sai ranar da zai tafi ya bukaci numbarta na hana. Kawai yanzu na gansu tare a makaranta. Richard ya iya canja yan mata kamar mai canjin hula. Karshenta yaudararta yazo yi ta fada tarkonsa har yana fadamin aurenta zaiyi. Abba ya dubeta cike da bacin rai abinda yayanki ya fada gaskiya ne? Ruqayya tace eh Abba amma jiya ya musulunta. Yace kenan da gaske soyayya kike dashi? Sai ta sunkuyar da kanta kasa. Kowa yayi mamaki. Ruqayya da Richard kamar a mafarki. Mami ta yunkura zata daoketa kawai sai ta fadi kasa a sume. Wannan wane irin tashin hankaline ace yar cikinta mai riko da addini tana muamala da kafiri.






Batul Mamman(Mrs)💖
[7/24, 12:26 AM] Fatima 💖: RUQAYYA YAR ALBARKA✨29





Ruqayya tayi kanta da sauri tana kuka. Mami don Allah ki tashi kiyi hakuri. Abida ta dage ta ture ta gefe ta dora kan Mami a cinyarta. Ruwa suka shafa mata ta farfado ta cigaba da kuka. Jikin Farouq duk yayi sanyi yadda suke nuna tsantsar kyama a gareshi. Ya Munir yace nasan ko da gaske ne ka musulunta kayi ne kawai don ka yaudari Ruqayya. Ina baka shawara ka tattara ka koma garinku tun kafin ka hadu da bacin rai fiye da wannan.

DPO yace kai samari ko kana da kwakkwarar shaida akan karbar musuluncinka? Farouq yace a wani mosque ne bansan unguwar ba amma zan iya zuwa daku. Mutanen wurin har wanka suka sa nayi muka yi wata sallah Eshiya dasu. Sergent Bako yace Isha dai ko?. Farouq ya nemi a bashi izinin kiran shaidarsa daya da sukayi exchanging number. Da kyar DPO ya yarda.

Barr Mukhtar yana ta bawa Haj Maryam labarin yaron da ya musulunta a masallacinsu daren jiya. Tana ciro kaya daga akwati tace gaskiya na dade banga kana farinciki irin wannan ba. Tamkar an maka bushara da kujerar makkah. Murmushi kawai yayi. Bazaki taba fahimta bane, irin wannan labarin yafi dadi ka gani da idonka. Ko kinsan ni ya bawa damar saka masa suna. Tayi dariya anya namiji ne kuwa ba mace ba? Duk ya sace min zuciyar miji daga yin tafiya. Kafin ya bata amsa waya ta shigo. Umar Farouq ya gani. Da sauri ya nuna mata kinga abinda nake fada miki, dan halak ya iya kira. Tana kallon yadda fuskar mijinta ta canja lokaci guda bayan ya gama wayar.  Yana ajiyewa drebansa ya kira yace zasu police station. Haj Maryam tace me ya faru zaka police station kuma. Yana sa takalmi yana bata labari a takaice kamar yadda Faruoq din yayi masa. Tace muje na raka ka na nuna kusu kuskurensu na tozarta bako a musulunci. Wannan inda raunin imani sai yayi ridda ai. Yace ki zauna ko awa bakiyi da dawowa daga tafiya ba. Ta dage yace muje.

Minti shabiyar ya kaisu station din. Duk suna ofishin dpo har yanzu. Ruqayya na can gefe tana kuka don babu mai kulata. Farouq ke kokarin su hada ido amma ta tura kanta cikin gwiwoyinta taki daga kan. Suna haka suka ji sallamar Barr da matarsa. Mami ta mike da sauri tana kuka tace Mummy kinji masifar da Ruqayya take neman jawo mana ko? Tace masifa kamar yaya, ina Ruqayyan take? Jin muryar mummynta yasa tayi saurin  tashi taje ta rungumeta. Nan aka sake bada labarin komai. Barr yayi murmushi yace da Abba Engineer kwantar da hankalinka. Nine shaidar da ya kira a waya. Wallahi jiya da kaga da yadda ya karbi addini kila kayi kuka kamar yadda nayi. Labarinsa ya abin al'ajabi ne sosai. Ya kalli Ruqayya hakika kin nuna min ke cikakkiyar yarinya ce wadda albarke ke binta. Ai ina ga a kashe case din nan mu karasa gida. Abba da Barr suka yi yan cike ciken takardu aka sake su suka wuce gidansu Ruqayya. Ita da Farouq suka yiwa juna murmushi.

A falo duk suka taru Barr Mukhtar yace hakika naji dadin yadda wannan al'amari ya kasance. Ruqayya kinyi matukar kokari wurin kare mutumcinki dana addininki. Wasu matan idan mutumin da ba musulmi ba ya nuna yana sonsu sai kaga ya rinjayesu sun bar nasu addinin. Nasan naki lamarin ma kariya ce daga Allah. Alhamdulillah. In sha Allah kamar yadda Dr Abdallah ya hadaka da masu koya maka addini muma nan duk zamu sa ido duk abinda baka gane ba kada ka yi nauyin baki. Farouq yace ai bakina ba nauyi. Hakan yasa su  murmushi sannan Mami tace ana nufin kada kaki tambaya, naga hausar taka bata fita sosai. Munir dai ba karamin kunyar abokin nasa yaji ba yace don Allah kayi hakuri.  Farouq ya taba lebensa na kasa da ya fashe yace ka bari na rama kawai sai na hakura. Nan ma dariyar suka sake yi. Farouq ya kalli Ruqayya abinka da rainon can haka gashi bai gama fahimtar addini ba, my love zaki aureni yanzu? Kunya mai tsanani ta kamata ta rasa yadda zata yi. Shi kuwa ya cigaba da magana da Abbanta a dalilin Ruqqayya nasan Islam amma ba saboda ita na canja addini ba. Ina fata zaka bani aurenta..... Nan fa Abba yayi dan shiru.. sai yayi gyaran murya yace tunda Barrister yayi maka shaida to dole na yarda ka karbi musulunci kuma muna tayaka murna da samun wannan arzikin na rayuwa. Ya dafa kan Ruqayya kaga yarinyar nan Allah Ya gani bazan iya bawa tubabbe aurenta ba. Kowa sai da maganar ta ya girgiza shi saboda firgicin da ya bayyana a fuskar masoyan.
Ina tsoron kada wata rana iyayenka su zo su nemi a raba auren ko kuma ka tafi da ita garinku a cutar da ita ko asa ta canja addininta. Daga jiya zuwa yau baici ace kasan komai a musulunci da zaka rike min yarinya ba. Kayi hakuri ka nemi wata. Barrister yace haba haba Engineer wannan wace irin magana ce? Ya kalli fuskokinsu ba Ruqayya ba shi kanshi Farouq hawaye yake. Sai yanzu ya san meye so sosai kuma yake yinsa da gaskiya ga yarinyar da tayi sanadin haska rayuwarsa. Kuyi hakuri, kai ku bamu wuri muyi magana in sha Allah aure za'ayi shi nan ba da dadewa ba. Abba yace kada kasa musu rai a banza kuyi zamanku. wallahi  bazan hada dangi da mutanen kudu ba. Tsafe tsafensu yayi yawa ga iya mugunta. Musuluntar yaron dai har ga Allah ina murna amma ba a gidana ba. Barrister Mukhtar yace yanzu baka tunanin  hakan yasa yayi tunanin bamu da kirki yayi ridda. Abba yace idan yayi wannan kuma dama don bada zuciya daya ya karbi addinin bane. Hankalin kowa ya tashi yadda Abba ya rufe ido yace babu maganar aure. Su Mummy suna ta bashi baki yace suyi hakuri. Ya Munir ma sai da yayi nasa rokon duk a banza. Barrister yace tunda ka rantse bazaka aura masa ba ni zan zama waliyinta na daura auren. Abba yace wallahi bada yawuna ba Barrister. Ko don ba yarka bace shine zaka hadata da mutumin da bamu san asalinsa ba. Maganar tayiwa Barr da Mummy zafi sosai. Don Mummy mikewa tayi tace kazo mu tafi kawai. Ban taba tunanin magana irin haka zata shiga tsakaninmu ba. Mami ta rinka bata hakuri. Barrister cikin zafin rai yace da ina da yar wallahi bazamu tashi ba sai an daura musu aure a wurin nan. Nagode ka tabbatar min bani da nawa na kaina. Kai Farouq tashi mu tafi, akwai yan matan danginmu da zan iya aura maka. Ke kuma Ruqayya Allah Ya biyaki abinda kikayi na alkhairi Ya baki miji nagari. Suna kallo suka fita Barrister na jan hannun Farouq, Mami tana cewa kuyi hakuri, Abba don Allah ka basu hakuri. Dakinsa kawai ya shige ya barsu a wurin. Wani irin kuka Ruqayya take yi mai raunana zuciya wanda har suka shiga mota suna jin sautinsa. Munir har bakin motar yazo yana basu hakuri Mummy wadda itama kukan take tace ba komai kaje ka bawa Ruqayya hakuri. Ka rarrasheta don nasanta da barin abu a rai. Allah zai mana magani.









Batul Mamman(Mrs)💖
[7/24, 3:51 PM] Fatima 💖: RUQAYYA YAR ALBARKA✨30





Tsaye suke gaban Chera babban bokan garin. Daga shi sai wani jan kyalli da ya daure kwankwasonsa dashi. Duk jikinsa anyi dige dige da wani farin abu. Ga layoyi daure a kowacce gabar jikinsa. Gashin kansa kuwa ya cukurkude ko mahaukaci albarka. Yana ta yan surkullensa Queen Amelia na daga gefe tana kuka mijinta yana rarrashinta. Chera yace your Highness na gano danku. Yana nan da ransa amma ban san inda yake ba. Queen Amelia tace ni dai ka juyo min da hankalinsa ta dawo gida kawai. Fiye da sati daya ko wayarsa babu. Ta dubi mijinta aurensa da Princess Sophia ba dole bane, nasan saboda ita ya gudu. Kasan abinda zaka fadawa mahaifinta amma bazan rasa dana ba saboda son zuciyarku. King Edward bai kula ta ba yace the great Chera babu abinda zaka iya yi domin taimakawa ka gano a inda yake? Chera ya tsugunna gaban katon gunkin dake gabansa yayi ta surutai wanda suma kansu basa ganewa. Ya jima a haka sannan suka ji ya kwala ihu mai razanarwa. Ya tashi tsaye da sauri, your Highness danka yana cikin wani haske wanda ya hanani dogon bincike na gane a wane wuri yake. Hasken tamkar kariya ne a gareshi. King Edward yace bangane haske ba. Da a duhu yake ko me? Chera yace ni dai abinda na gani kenan. Goddess tace ku kwantar da hankalinku zai dawo gida nan ba da dadewa ba.

Haj Maryam tayi magiyar ta kuma fada karshe ta koma rarrashi duk akan Farouq yaci abinci amma yaki. Shi ya dage ma su barshi ya koma hotel din da yayi masauki. Barrister Mukhtar yace ni bazan bari ka tafi ka kwana kai kadai ba. Na daukeka a matsayin dan cikina saboda haka zan kula da kai bisa amana. Ka daure kaci abinci ko kadan ne. Kaga ka sa min mata kuka ya nuna Mummy da ke aikin share hawaye. Har ranta take tausayin yaron. Jinsa take kamar jininta, yadda ya shiga ranta tamkar farkon haduwarta da Ruqayya. Sai dai shi wannan ta rasa dalilin  da yasa take jinsa kamar jininta. Kirar jikinsa kamar Barrister sai dai yafi shi tsaho da kadan. Kila saboda kuruciya. Da sauri ta kawar da tunanin saboda yadda zuciyarta ta fara tuno mata wannan ciwon nata. Murmushi yayi ya kalleta kinga Babana bai damu naci abinci ba,  so yake naci kawai don ki dena kuka. Itama murmushi tayi kyale shi kaji. Ka daure kaci ko kadan ne. Kadan din kuwa yaci yace ya koshi. Dole suka barshi haka. Amma suka matsa masa lallai sai ya kwana a gidan saboda basu san halin da zai shiga ba idan ya tafi shi kadai. Ba yadda zaiyi da mutanen nan masu kirki da iya jan mutum ajiki. Haka ya hakura aka bashi daki daya. Da zai je dauko kayansa a hotel ma tare suka je da Barr ya dubi kayan daidai a tsakar daki. To bari in fada maka tun wuri ka koyi gyara kayanka saboda kada ku rinka fada da matata, nima haka muka yi da ita har dai na dan koya kadan. Farouq yana jindadin yadda mutanen ke da barkwanci yace matarka ko Mummyn mu ni da Ruqqayyata. Tafi son mu shiyasa har muka taho take kuka. Barrister sai dariya yace Umar Farouq don Allah ko ka koma gida kada ka bar addini kuma kada ka manta da iyayenka na Kano. A ransa yana mamakin yadda idan yayi murmushi yake masa kama da Haj Maryam. Shima kamar yadda tayi saurin kawar da tunanin yayi.

Sati biyu kenan da rigimar da ta raba Ruqayya da Farouq dinta. Duk ta rame ko makaranta bata zuwa. Hidaya da Abida ne masu bata hakuri kullum. Mami kuwa cewa tayi ta dena kuka ta fawwala wa Allah lamarin. Duk abinda mahaifinki ya fada gaskiya ne game da yaron nan. Komai na iya faruwa idan ya tafi dake garinsu. Suna iya cutar dake a matsayin wadda tayi sanadin raba dansu da addininsa. Ki kuma yi kokarin sassautawa zuciyarki son da kike masa ki rinka istikhara. Idan mijinki ne bamu da zabin da ya wuce aura miki shi. Idan kuwa babu alkhairi tsakaninku to dole kuyi hakuri da juna. Bayan ta tafi Abida tace banda abinki ma Ruqayya duk masoyanki ki rasa wanda zaki zaba sai Richard? Kai ta dago da idanu a rine sunyi ja tace sunan Umar Farouq. Abida tace to kiyi hakuri matar Umaru. Abba zamu danne da addua har sai ya sauko. Ni dama bana kinsa, rashin addini ne yasa. Amma yanzu ai zanso ace wannan dan kyakkyawan mutumin ya zama kanina. Ko ba komai yadda kike da muni kya haifo mana 'ya'yan da zasu ganu. Dama ta fada ne don ta bawa kanwarta dariya kuma tayi din har ta dauko hijab tana binta wai sai ta zaneta. Don kinga ina raga miki saboda ciki ko, kinsan dai ko da kuruciya nafiki karfi . Abida tace to tuwon da kike narka ai ba a banza ba yarinya.






Batul Mamman(Mrs)💖
[7/24, 6:07 PM] Fatima 💖: RUQAYYA YAR ALBARKA✨31




In ka dauke tsabar so da kewar Ruqayya Farouq bashi da wata matsala da su Mummy. Sosai suke kula dashi yana jindadin hakan. Ko sau daya baiyi tunanin neman Mum dinsa ba duk da yadda ya damu da rashinta. Ta shagwabashi da yawa kuma ga Haj Maryam ma tana nata kokarin. Yana tsoron komawa gida bayan bai gama sannin addininsa sosai ba su raba shi dashi. Ba karamin aikin Dad dinsa bane yasa Oracle Priest dinsu Chera yayi masa tsafin da zai iya manta komai. Shiyasa ya yanke shawarar sai yayi akalla wata biyu zashi gida shima ba don ya zauna ba. Wata rana yana ta juya waya a hannunsa yana tunanin Ruqayya. Wayarta sam bata shiga sai dai Munir yana fada masa halin da take ciki don sun shirya da abokin nasa duk da ya koma Abuja. Barrister ne ya shigo ya ganshi a haka sai tausayinsa ya kara kamashi. Yaron ya bar komai na gatan rayuwarsa saboda addini da soyayya amma Abba yaki gani. Yace Umar Farouq ko na sama maka wata matar ne? Dago kai yayi don baiji sallamar sa ba saboda tunani. Ina jiran Abban Ruqqayya yayi hakuri ne nasan zai yarda aureta In sha Allah. Kullum ina yin addua kuma na yarda Allah zai amsa min. Da kyau haka nake so ka karfafi zuciyarka. Jiya kace zaka yi min magana bamu sami lokaci ba. Farouq yace dama ina son zuwa UK ne. Wurin aikinmu sati biyu suka bani gashi dade. Ina son zuwa neman transfer ne zuwa kasar nan. Idan bazan samu ba zan ajiye aikin na dawo kawai. Barr yace kana ganin ya kamata ka ajiye aikin? Its better that way, bana son abinda zai dauke min hankali daga barin koyon ibada. A can ina da wata girlfriend da nayiwa alkawarin aure. Itama ya kamata naje na bata hakuri ta dena jira ko. Jiya Malam yace min alamar munafuki harda wanda baya cika promise dinsa. Barr Mukhtar yace haka ne Allah Yayi maka albarka kaji. Yaushe ne tafiyar yace nan da kwana biyu. Ranar da zai tafi Mummy harda wani kukan. sun saba dashi sosai kamar wadanda suka shekara tare.

Ruqayya tana zaune tana rokon Iya Tasallah yar tsohuwa mai ran karfe ta sa baki Abba ya bata wayarta. A gidan yayi musu gargadi kada wanda ya bata aron tasa. Iya tace bazan masa magana ba haka kawai kin nacewa kedari. Ni wallahi yayi min daidai abinda yayi gara da ya toshe kunnuwansa. Kin bi kin dorawa kanki soyayya kamar kinga autan maza. Sai dai banji dadin yadda kuma abin ya shafi su Haj Maryam ba. Yarinyar akwai mutumci ba ita ba ba mijin nata ba. Ruqayya ta share hawaye Iya ni kuka na ba na son Farouq bane kawai. Ina bakin cikin yadda kuka kasa fahimtar mutane irinsa suna bukatar tarairaya daga garemu don addinin ya sake shiga zuciyarsu. Ina amfanin ya musulunta bayan dan lokaci yace ya bar addinin saboda mabiyansa basu da halin kirki. Iya ki tuna duk manyan sahabban Annabi SAW da duniyar musulunci take tutiya dasu tubabbu ne tunda suna da addininsu aka kawo wani, sai gashi su suka gina musuluncin . Wadansu ma sai da suka tsufa aka yi wahayi kuma suka karbi addinin suka zauna lafiya. Akwai wata sahabiya Rumaisa wadda ake yiwa lakabi da  Ummusulaim babar Anas ibn Malik RA. Ita da zata sake aure manemin nata Abu Dalha RA cewa tayi dashi musuluntarsa shine sadakin aurenta. A take yaje gaban Annabi SAW ya karbi shahada. Kuma ya zama gwarzo cikin sahabbansa a sauran rayuwarsa har yana cikin mutum goman da akayiwa bushara da aljanna.. Iya da hakan akwai kuskure ai Manzonmu SAW bazai yarda da auren ba. Nana Safiya RA uwar muminai bayahudiya ce da farko aka kamasu a yaki. Annabi SAW yace ta karbi musulunci ya yantata ya aureta ta karba kuma ta shiga jerin iyayen muminai. Da ana gudun baki a addini bazamu gansu tare da Annabi SAW ba. Hakika da babu mai karbar sabon addinin sai jarirai. Ina son Umar Farouq sosai Iya. Amma nafi damuwa da Abba yayi kyakkyawar muamala dashi domin ya sami lada. Kin mutum kawai don yana bako a addini yana daga abinda ke hana wasu musulunta. Saboda muna nuna kyama a garesu. Dukkanmu fa ba yin kanmu bane aka haifemu cikin addinin. Da Allah Yaso da yanzu kece Queen Elizabeth ta ingila ita kuma tana nan tana sallah. Iya Tasallah ta zuba mata rankwashi amma baki da kirki yar nan. Ruqayya tace gaskiya ne tana murmushi mai ciwo. Kila Mami ita ce Mariah Carey mai waka, Abida  ta zama Rihanna, Hidaya Kim Kardashian, Abba kuma Micheal Jac......... yi hakuri taji muryar Abban daga bakin kofa  ya katse mata magana kafin kuma ya karasa shigowa dakin shi da Mami. Naji na fahimce ki ba sai kin hadani da wani kasurgumin kafirin ba. Ita tsoro ma taji da ta ganshi don ya dena sakar mata fuska. Yace Ruqayya Allah Yayi miki albarka. Tabbas bayananki sun tuna min da abinda naso mantawa saboda son zuciya. Fatima muje daki ki karbo mata wayarta. Ki bani da kaina zan kira Umar Farouq nayi masa albishir zai zama mijin Ruqayya. da gudu Ruqayya ta rungume shi tana zubar da hawayen farin ciki. Mami tace don shakiyanci da mai waka nayi miki kama ko?sannan ta dubi Abba, idan kayi wayar kuma sai muje mu kwashi kunya gaban iyayen yarinyar nan. Ko waya na kasa yiwa Haj Maryam saboda kunya. Abba yace shaidan ne ya kusa galaba a kaina. Allah Ya shige mana gaba.

Suna fita daga dakin Ruqayya ta fada kan Iya tana hamdala. Iya Tasallah taji nauyi tayi kara. Dagani don girman Allah kada ki karasa kashin tsufa. Nida nake son yi miki wankan jego in kin haihu da dan kedarinki. Ruqayya tace wallahi Iya bana so. Don baki ganshi bane ranar da yazo. Kamar bafillatani fa yake.  Zubinsu kusan daya  da Abba B ni har yanayi suke min.




Batul Mamman(Mrs)💖
[7/25, 1:41 AM] Fatima 💖: RUQAYYA YAR ALBARKA✨32





Sau uku kenan Abba yana gwada numbar taki shiga. Ita kuma Ruqayya wannan kawai take da a waya. Yar takardar da ya taba bata ma bata san  inda take ba. Yake kawai take don kada iyayenta su gane amma hankalinta ya tashi sosai. Shikenan karshenta ya koma garinsu. Abba yana lura da ita, ta bashi tausayi. Ruqayya duk rigimarta yanzu ba'a jin kanta a gidan. Yace kinga yar albarka kwantar da hankalinki. Ba dai ni na korar miki shi ba? In sha Allah da kaina zan dawo dashi. Ko don kada na batawa musulmai suna wurin son kansu da kin bare. Mami tace su Mummy kila zasu san inda yake tunda ranar tare suka fita. Allah Yasa baiyi nisa ba dai.

Shiru Ruqayya na zuba ido taga matakin da Abba zai dauka bata ji komai ba. Ga Abida ta tafi gidansu Munir gaishe da Ummansa babu abokin shawara. Ita kadai ta shiga daki ta sa dankwalinta ta toshe baki tana kuka mai tsuma zuciya. Ashe haka take son wannan dan sarkin? Ji take kamar an rabata da wani sashe na jikinta. Sai da tayi mai isarta ta fito bayan Isha ta tarar Abba da Mami sun fita. Iya Tasallah tace ina kika shiga suna ta kira zasu fita. Ruqayya da kanta yake sarawa saboda ciwo tace bacci nayi. Iya Tasallah tace dole kiyi bacci mana tunda sun tafi nemo labarin autan maza. Hanyar dakin da ta nufa tayi saurin dawowa. Iya me kika ce? Ina suka tafi? Gidan Mummy? Bari na bisu a kafa ai ba nisa. Iya ta jawota haba ke kuwa a ja aji mana. Sai kuyita abu mu tsofaffi ma ko ada bamuyi ba. Kiyi addua dai su sane shi idan sun je.

Sai kallon kallo ake tsakanin su Mami dasu Mummy. Abba yace don Allah Barrister ka dena min wannan kallon wallahi kunyarka nake ji sosai. Barrister Mukhtar ya ce ai bazan dena ba sai naji dalilin zuwanka yanzu. Dalilin 'yarku ne ya bashi amsa. Mummy tace rabu dashi ku zauna Mami. Bayan sun zauna aka  gaisa sannan Abba yayi musu bayanin abinda ya kawosu. Barrister yace kai kuwa me yayi saurin chanja maka raayi? 'Yarku dai ita tayi wannan aikin. Mami ta basu labarin abinda suka ji tana fada. Sai gashi iyayen sun koma dariya. Duk da haka Abba ya sake basu hakuri. Barrister yace to Micheal Jackson ai dole na hakura tunda 'yata ta rama min. Suna dariya Abba yace ai da ban katseta ba nasan kanku zata dawo tunda mun kare. Wa yasan da wa kayi mata kama? Mami tace rabu da yarinyar nan ai muna tafiya naji tana cewa Iya wai Farouq yana mata yanayi da Abba B. Dariya aka sake yi sai dai maganar ta tsayawa Barrister da Haj Maryam. Sunyiwa su Mami bayanin dalilin tafiyarsa tare da basu sabuwar numbarsa. Abba yace bari na kira nayi masa albishir. Sai Abba B yace kyaleshi. Daga shi har Ruqayyan ina da yar idea da zamuyi surprising dinsu.

Ruqayya bata wuce minti biyar bata kalli agogo ba. Sai shadaya saura taji shigowar Abba yana gyara parking. Ta fito da sauri sai kuma ta basar tana tambayarsu ya suka baro Mummy. Mami tace tana nan lafiya. Tace jibi ranar jumaa  kije zaki rakata biki. Ruqayya tace to gobe ma zani ai nayi missing dinta da yawa. Mami tace nima goben naso kije to akwai inda zata da sassafe shiyasa tace ki bari sai juma'ar. Ruqayya bata ji dadi ba amma tunda an daidaita gobe ma zata yi mata waya su sha hira. Sai kuma ta jira bayani game da Farouq wanda shine dalilin fitowarta. Daga Mami har Abban babu wanda yace mata komai suka shige daki. Zuciyarta ta kara tsinkewa karshenta basu same shi ba shine suka yi shiru kada su daga mata hankali. Addua kawai ta sawa ranta zata cigaba. Haka ta cinye daren cikin kuka da sallah tana rokon Allah Ya cire mata sonsa in har ba mijinta bane.

Gari na wayewa Hidaya tazo da yaranta aka taru ana hira wai duk zasu kwantar mata da hankali. Ruqayya ta dauki Sameer yaron Hidaya dan shekara daya ta shige daki. Su har suna iya hira suna dariya. Inama ita ce su haka take rayawa. Abida ta kira mai kunshi tazo tayi musu wai na komawa Abuja take yi. Yarinyar tayi musu baki da ja amma na Ruqayya duk yafi kyau duk da da kyar suka samu ta yarda zata yi. Bayan an gama da laasar Hidaya ta cire mata dankwali bari muga abinda kike tamkewa da dankwali tun dazu kamar wata me gashin kirki. Kai meye haka a kanki kamar yar dambe. Mami kinga kan yarki ta zama kazama. Ruqayya ta sa ihu ita a bata abinta. Ba ruwansu da kanta. Mami ta shiga daki ta dauko dubu biyar ta bata Hidaya taimaka ki kai min ita salon kinji. Ruqayya tace ita bata so. Au haka zamuyi dake ki bani kunya, haba yar albarkan Mami da Mummy. Abida tace itama zata ana ware su don sun bar gidan an dena basu kudin gyaran kai. Da yake ba nisa a motar Hidaya yar koyo suka tafi. Gashin Ruqayya kam yasha gyara sai gashi fuskarta ta kara fitowa.

Washegari ta tashi taga gidan nasu da baki maza da mata yan uwan Abba da Mami. Tana gaishesu Mami tace ta fita ta tafi gidan Mummy yau suna da baki kada a hanata fita da wuri. Ita sai mamakin bakin take yi amma ta kasa tambayar kowa don bata kawo komai a ranta ba. Tunda asabar ce kila yini suka zo. Tana cikin tafiya taji horn din mota a bayanta. Ga mamakinta Ya Munir ta gani. Tayi saurin zuwa gaban motar yace ina zuwa? Gidan Mummy ta bashi amsa. To zo na rage miki hanya rana ta dena dukan kanwata. Suna tafiya tace Yaya yaushe kazo? Jirgin bakwai na biyo na zo dazu kewar yayarki nake yi. Ranar lahadi zan tafi da ita in sha Allah. Sai kuma yace Ruqayya don Allah kiyi hakuri akan abinda ta faru. Haba Yaya wallahi ya wuce har abada. A kofar gidan ya ajiyeta ya koma gidansu wurin su Abba.

Da gudu ta shiga gidan don tayi kewar masu shi. A falo ta tarar da Nadiya yar Hajjaju. Suka rungume juna tace Anti Nadis kema zaki bikin da zan raka Mummy ne? Tace eh kannenki na sama suna bata fuska wai su nan kwalliya. Ruqayya tace ina Mummy na? Gani nan Ruqayyatu yar albarka. Murna sosai tayi ganin Mummynta. Suka rungume juna har Nadiya na tsokanarsu ko Ruqayya zata shiga ciki ne a sake haifarta. Ruqayya tace Mummyna kinyi kyau sosai wallahi bari na daukeki hoto. Haj Maryam ta gyara tsayuwa ta dauketa. Anti Nadis ungo ki daukemu tare. Mummy tace ai sai kin yi kwalliya. Ruqayya ta bata fuska ni Mummy na dena kwalliya gaskiya. Tace ta yau dai saboda na roka kiyi min kinji. Muje daki har sabon kaya na ajiye miki na zuwa bikin. Biki ne na 'yan karya in bakiyi bani waje. Ruqayya ta hau murna suka hau sama da Mummy bayan Mummyn tayiwa Nadiya signal da ido.





Batul Mamman(Mrs)💖
[7/25, 12:37 PM] Fatima 💖: RUQAYYA YAR ALBARKA✨33






Ashe ba karamin kewar Barrister da matarsa yayi ba abinda Farouq ke fada kenan a ransa lokacin da ya hango Barrister Mukhtar yana dago masa hannu. Sauri yayi yaja trolley dinsa ya karasa jikin motar. Murmushi suke yiwa juna tun kafin ya karaso. Umar Farouq daga yin sati  har kayi kiba? Ka manta da iyayenka ko Barrister ya zolaye shi. To ya hanya? Murmushi  yayi ya mika masa hannu suka gaisa sai dai ga mamakinsa ji yayi Baban nasa kamar yadda yake kiransa ya rungume shi. Suka shiga mota dreba na jansu. Basu tsaya ko ina ba sai gida. Barr Mukhtar yace kayi hakuri zan dan takura maka muna zuwa gida kaci abinci kayi wanka zaka rakani daurin aure. Hankalin Farouq yana ga tunanin Ruqayyansa bai ji me ya fada ba sai da ya maimaita. Ya kalli agogon hannunsa ai lokacin sallah ya kusa a ina zaa yi auren? Dama ina son ganin yadda akeyi a garin hausawa irin na musulmai. Ai kuwa yau zaka gani har ka bada labari. A masallaci ne bayan an idar da sallar jumaa. Haka suka tafi suna ta hira, farouq yaso tambayar Ruqayya amma sai ya hakura ganin baban nasa yana cikin nishadi. Baya son bata masa rai saboda abinda ya faru a gidansu Ruqayya.

Suna shigowa dakin da ya zama nasa ya wuce yayi wanka. Wata shadda ruwan madara wadda akayiwa aiki da dark brown din zare Barrister ya ajiye masa a dakin. Harda babbar riga kayan sunyi kyau sosai. Hula da cover shoe  dinsa da safa ma duk dark brown. Hatta agogonsa na fata mai tsada duk dark brown ne. Sai a lokacin yace wato saboda haka jiya  Mummy ta tambayeshi size din takalmi siya zasu yi. kaya kuwa bai san yadda suka iya dinka masa sabbabi ba. Bayan ya shirya ya fito da babbar riga a hannu sai kamshi yake. Yayi kyau sosai kamar ba Prince Richard ba. Anti Nadiya tana kallon bene tace maza ka fita yana jiranka a waje kada ku rasa sallah. Yace bamu gaisa ba Anti zaki koreni don itama ya dan saba da ita yan kwanakin da yayi a gidan. Tace jeka ka dawo yau har tukwici zaka bani. Tuku... me ya maimaita yana yamutsa fuska. Wasu words din naku wahala garesu. Tana jin motsi daga sama tace oya oya fita don Mummy na ganinka zata bata muku lokaci. Ya ce ni gaskiya sai ta ganni zan fita. So nake tace kayan sunyi min kyau. Muryar Barrister yaji yana cewa Umar Farouq kada mu makara fa. Dole yayi saurin fita ba don yaso ba. Gaskiya yaso ganin Mummy. Ita ke rage masa kewar Mum dinsa. Ko ya take ji baya nan? Next week zaiyi kokarin kai musu ziyara don yasan ya dauki alhakinta da yawa.

A bakin gate din gidan motocin suka yi parking daya daga cikin guards din ya fita ya tambayi maigadi ko Munir yana nan aka sanar dashi da sassafe ya tafi Kano. Queen Amelia ranta ya kara baci da jin bayanin da guard din yayi mata. Ni banyi tunanin karbar numbarsa ba da na kira ta fada tana mita. Shi kadai ne abokin Richie a nan, ina fata yasan inda yaron nan yake. Ta ce da yar budurwar dake zaune a gaba jeki ki fada musu mu tafi office dinsu Munir din nasan maaikatar. Bazasu kasa sanin address dinsa na kano ba. Daga nan mu wuce  airport Kanon zani. Idan na tabbatar baya nan Dad dinsa zai wuce Manchester kila ya koma aiki. Duk akan wannan banzar Princess Sophian Sarki ke neman rabani da dana. Sunyi saa an sami wani dan Kano wanda ya bada cikakken kwatancen gidansu Munir. Sai dai kuma babu sauran jirgi mai zuwa Kano a ranar sai washegari. Ai kuwa Queen Amelia tace su ja motocin a wuce don bata ga ta zama ba bata san inda danta yake ba.

A masallacin Dr Abdallah suka yi sallah tare da mutane da dama harda Abban Ruqayya. Yayi mamakin yadda Abba ya jashi a jiki har yana tambayarsa ya hanya. Daga nan yace wa Barrister ya shigo cikin masallacin zasuyi magana. A gaban sauran mutanen dake ciki da su Ya Munir aka daura auren Umar Farouq Edward da Ruqayya Muhammad Hamza batare da daya daga cikinsu ya sani ba. Iyayen sun fito suna ta gaisawa da jama'a ana ina angon. Shi dai Farouq yaga ana gaisawa dashi amma shima neman angon yake har yana mamakin wai har an gama auren babu amarya. Yana daga waje ana hayaniya duk baiji me ake fada ba. Basu bar masallacin ba sai uku saura. Farouq yace Babana ni ban ga komai a auren ba. Idan zaayi wani ka shiga dani ciki na gani da kyau. Yace to kayi hakuri zan kiyaye next time.

Ruqayya tasha kwalliya sosai wadda Anti Nadiya tayi mata da kanta. Dama ita gwanar abin ce don mijinta yaki bari taso ta rinka yin na amare. Shadda ce dinkin doguwar riga mai dogon hannu Mummy ta bata ta saka. Itama ruwan madara ce da komai dark brown harda takalmi. Sai fashion suma ruwan madarar masu tsada da kyau. Dankunne, sarka, abin hannu da zobe. Daya hannun agogo ne kalar adon kayan. Anti Nadiya tayi mata dauri mai kyau ta zubo mata gashi ta tsakiya da wani a gaban fuskarta. Ruqayya ta ce Anti bazan iya fita haka ba wallahi. Tace ke na hoton da zan muku da Mummy ne. Ko so kike babar taki ta fiki iya gayu. Nima nan wurinta na koya. Bayan ta gama ta fesheta da turaruka har kala uku. Ruqayya tace ai wallahi bazan fita a haka ba Anti Nadis. Kinji kamshi kuwa? Tace yau daya dai kiyi ado a gida. Bikin ma sai bayan laasar kila zamu tafi kinga har yabi iska turaren. Kai anya kuwa Anti ai turaren irinmu ne mai bin iska ba na Mummy ba. Idan kamshin bai tafi ba sai na mayar da kayana. Zasu sauka kasa ta fara neman mayafi. Nadiya tace kai yarinyar nan ki bari azo tafiya sai kisa mayafin. Ruqayya tace to ta bi bayanta.

Suna saukowa Mummy ta zuba mata ido. Yar albarka kinyi kyau Masha Allah. Har dan hawaye tayi na tsananin farinciki tayi saurin sharewa. Jeki dakin can akwai gift da zamu tafi dashi ki duba min. Ko a wardrobe ko a karkashin gado. Saura ki fito kice baki gani ba. Ruqayya tayi dariya don ta iya zuwa aike tace babu. Sai ta koma kamar sau biyu sai ta dawo da abinda aka aiketa nema. Tace Mummy nagode da kayan amma banga mayafin ba. Tana turo baki Mummy tace jeki ki dawo bari na duba yana cikin kayana. Zata shiga dakin taji shigowar mota tayi saurin shigewa dakin kada Abba B ya ganta ko lullubi babu.

Dakin a gyare yake ga kamshin turaren wuta da air freshner ga sanyin AC. Ruqayya da har wasa takeyi a ciki yanzu kuwa an kara gyara shi. A kan centre table card ne taga an rubuta HAPPY MARRIED LIFE...from Anti Nadiya. Ta dauka tana juya shi waye kuma yayi aure. Ta nufi wardrobe da katin a hannu  sai taji kamar ana taba kofa. Hantar cikinta ta kada waye kuma zai shigo ya ganta kamar yar tsana ba mayafi. Ta nufo bakin kofar tace waye kawai sai taji an bude an jefeta da wani abu mai kamshi. Farouq ya tsaya tunanin waye a dakinsa bayan ya jefa babbar rigar da ta ishe shi da nauyi. Ya dan juya sai ya ga falon babu kowa. Rigarsa yayi kokarin cirewa daga jikin da ya jefa sai yaji an riketa gam. Yaushe zata bari wani ya ganta a haka. Idan ta fita a kawo musu ko ta waye. Ya sake ja itama ta rike iya karfinta. Sai yayi dan tunani ko sata aka shigo yi a gidan. Kamar mace don yaga ba tsaho kila ma cikin masu aikin Mummy ne. Yayi murmushi ya kama barawo yace wayyo lizard a jikin rigar. Da gudu Ruqayya ta jefar da ita zata kwala ihu. Suka hada ido....

Kallon kallo suka tsaya yi don basu taba tsammanin haduwa a nan ba. Ruqayyansa tayi masa kyau sosai kamar ba ita ba. Rigarta tayi daidai da jikinta sosai. Wani irin sonta yaji ya kara shigarsa. Itama kallonsa take yi saidai ta kasa hada ido dashi don kunya. Yayi kyau ya kara jiki da haske. A hankali yace my love kece ko idona ne. Ganinki nake yi a gabana kinyi kwalliya yau ko hijab babu....sai a lokacin ta tuna ta fara kokarin fita. masu aikin Mummy su biyu ta gani da tray din abinci da na lemo da ruwa. Dayar tace Mummy tace kada ki fito sai kin bawa mijinki abinci. Ruqayya ta rike mata hannu tana shirin fita ke tsaya, miji kika ce fa? Yarinyar tayi murmushi Anti Ruqayya ance dazu aka daura miki aure da Uncle Farouq. Yarinyar na fita yasa kafa ya tura kofar ya rufe dakin. Har zuciyarta taji karar duk da a hankali ya tura. Yau gata ga Farouq a matsayin mata da miji. Kai anya da gaske ne kuwa? Sai a lokacin ta fara tunanin abubuwan da suka faru daga jiya zuwa yau. Kayan jikinsu ma iri daya da shi. Ko dai gaske ne. Wani yanayi ta tsinci kanta a lokacin da Farouq ya kama hannuta ya kaita bakin gado ya zaunar da ita sannan ya ja wata karamar kujera gabanta ya zauna. Kanta ta sauke kasa tana me jin kunyarsa. Shi kuwa kallonta yake yana kara godewa Allah da Ya bashi ita. Yasa hannuwansa biyu ya dago fuskarta kawai sai ta rufe ido. Ki bude idonki ki ga mijinki my love. Ta girgiza kai alamun bazatayi ba. Yace kunyata kike ji kuma? Nan ma bata bashi amsa ba sai murmushi a saman fuskarta mai fitar da dimple din kumatunta na dama. Ba zato taji bakinsa a kumatun. Tayi saurin tashi ita bazata iya da wannan bakon yanayin ba. Tana tashi shima tashin yayi ya rungumeta sosai a jikinsa. Hawayensa taji suna sauka gefen fuskarta. Cikin sassanyar murya yace nagodewa Allah da Ya bani ke kuma nagodewa su Mummy. Kema nagode miki da son da kike min my love. Ban san inda zan sa sonki a zuciyata ba . Ya fara kokarin hada bakinsa da nata  rasa yadda zatayi gashi kunyarsa take ji sosai. Sai kawai tace a garin nan fa ba'a shiga dakin amarya sai an siyo mata kaza gasashshiya. Kai ko ruwa baka taho dashi ba. Yace kin tabbata ba don kina kunyar kada nayi kissing din lips dinki bane? Wata kunyar ya sake bata tace eh da gaske nake. Yace to ai kece baki koya min yadda akeyi idan anyi aure ba. Da me kuma zan shigo? Tace kazar ma ta isa. So take ta sami damar gudu kawai.Å«  tana kallo ya bude wata karamar drawer ya dauko key din motarsa ya nufi kofa. Tace ina zaka je? ke dai ina dawowa yanzu.. Har zai fita ya dawo yace I love you Ruqqayya. Sai da ya juya tace I love you too Umar Farouq. Yana fita ta kai goshinta kasa tayi sujjadar godiya ga Allah.






Batul Mamman(Mrs)💖
[7/26, 2:39 PM] Fatima 💖: RUQAYYA YAR ALBARKA✨34






Farouq na fitowa daga dakin ya hadu da Mummy da Abba B suna hira da Anti Nadiya. Barrister ya tashi yace ango ina zuwa kuma? Bai bashi amsa ba sai rungumeshi da yayi yana kuka. Su Mummy sukayi murmushi. Farouq yace yau na tabbatar ko kaine mahaifina iyakar abinda zakayi min kenan. Nagode! nagode ! nagode Babana. Allah Ya samu a jannah. Duka suka amsa da Amin. Anti Nadiya tace kai dai Farouq ba dai iya kuka ba, da ganinka nasan kayi kukan banza. Mummy tana dariya tace ai ba kansa farau ba. Kema halinki kenan ga shagwabar tsiya. Anti Nadiya tana kallon benen tace yi a hankali kada su Amira su ji su sami na tseguntawa babansu . ta kalli Farouq a jikin yayanta kuma babanta tunda shi ya riketa. Basa kama sosai a fuska sai dai wasu abubuwan nasu kamar uba da dansa. Musamman kirar jikinsu, tayi ajiyar zuciya to tace ai gara nawa amma shi wannan dan naku mai dalili yake yi. Dan sarki jikan sarki, kuna kallo yadda har yau ko zuba abinci a plate bai iya ba. Ni har tausayin Ruqayya nake ji an hada ta da ajebo. Tana cewa Ruqayya kuwa Farouq yace kada na bata lokaci bari naje na dawo. Mummy tace ina zuwa daga daura maka aure? Yayi dan murmushi yana kallon kofar dakin. Ruqqayyata ta iya rigima sosai, wai sai na siyo kaza zan shiga dakin. Kuma fa nasan saboda tana jin kunyata ne. Yana duban Anti Nadiya yace dama haka hausa girls suke da kunya? Ko kallona ta kasa yi, Seriously Anti Nadiya ina son yarinyar nan, so beautiful. Bakintan nan kamar in.......Barrister ne ya toshe masa baki da hannunsa su Mummy kuwa sai dariya. Tunda ya fara magana suma kunyar ta kama su. Idan ba'a tsayar dashi ba kila sai yasa duk sun bar falon ba shiri. Barr Mukhtar yace ai ba tarewa zata yi yanzu ba sai iyayenku mata sun gama daidaitawa zaayi biki a kaita. Farouq yace a kaita ina Babana? Gidanka mana ango anti Nadiya ta bashi amsa. Yayi murmushi don an kusa gama gininsa a  nan cikin unguwar tasu. Abinka da wanda kudi suka zauna masa. Wani gida ya siya da ya dage wa Barrister yana son siyan nasa. yasa akayi yan rushe rushe a wasu bangaren ake gyara masa shi. Gabanin tafiyarsa aka fara aikin yanzu kuwa suna tunanin gamawa a wata daya zuwa biyu. Nadiya tace a takaice yau ba ka bukatar kaza sai ranar da zata gidan so maza ka koma ciki. Yace gaskiya ko ice cream sai na siyo mata. Duk yadda nake sonta babu abinda na taba bata saboda yanayin da muke ciki. Ita take yi min komai. Barrister yace bari na bawa dreba ya siyo Umar Farouq ka gaji da yawa yau, kuma har yaushe ka gama gane gari. Ya daga keys din motarsa kagani yanzu zan dawo akwai wani shop da na gani kusa yake. Daga haka ya fice yana cewa Mummy kinyi kyau ko amaryar Babana kika zama ?. Zaka dawo ka sameni ta fada tana dariya.

Yana fitowa daga shagon da ledarsa a hannu fuskarsa dauke da murmushi ta hango shi. Wurin babu mutane sosai saboda yayyafin da aka soma. Dan babur suka sa a gaba zai kaisu unguwarsu Munir sai gashi ta hango shi yana shiga mota. Dadi da farinciki suka mamaye mata zuciya cikin daga murya tace da dreban ya tsayar da mota. Duka motocin hudu a hankali sukayi parking a gefen titi, kafin guards din su fito Queen Amelia ta fito da gudu tana cewa my Richie. A firgice ya waigo yana tare ruwa da hannunsa kafin kuma ya soma murna. Jefa ice cream din yayi seat din gaba ya nufota shima da gudu. Tabi fuskarsa tana ta kissing tana kuka. Ina ka shiga kabar mahaifiyarka? Ya sake kankameta i miss you Mum. Ta  kalle shi da kyau gashi duk guards sun zagaye su ana saka musu lema. Richie kayi kyau sosai waye yake kular min da kai haka? Yace Mummy ce kizo muje gidan kiga sabuwar rayuwar da na samu da sabon family. Queen Amelia tayi turus....Mummy kuma? Wata uwar ka sake bayan ni? Yayi murmushi ba haka nake nufi ba amma yadda take kula dani tamkar dan cikinta. Nima ji nake kamar ku biyu kuka haife ni. Ita da mijinta suna da kirki sosai. Ya rike hannun Mum dinsa muje kiga babban surprise da na ajiye miki,  sannan na fada miki komai game da dalilin tahowata. Allah Ya kawo min chanji a rayuwata. Queen Amelia ji take dan nata yana wata magana kamar shirme. Har akwai wadda zata amsa sunan uwa a wurinsa bayan ita? Sai ta tuna taji yace ALLAH shikenan tsafin yan Kano ya kama shi. Guards tayi wa alama ta bayansa bai ankara ba yaji sun daga shi su uku suka tura shi a mota. Yana cewa su sauke shi ya bar matarsa a gida. Kuka Queen Amelia ta saka tace gashi garin gudu daga auren Princess Sophia ya haukace a Kano. Yaushe ya baro garin da har zai yi aure bata sani ba. Abu ne da ta tabbatar Richie dinta bazai taba yi ba. Farouq hankalinsa bai kara tashi a motar ba sai da yaji Mum dinsa tace su kama hanyar garinsu komai dare sai an kai Richie wurin Priest Chera yayi masa magani. Dama ya fada mata Richie yana cikin wani haske mai bashi kariya. Koma menene yana son rabata da danta dole ta dauki mataki. Ya nutsu ganin motar da suke ciki ta soma gudu akan titi yace Mum kada kiyi min haka. Ina da family a nan kuma dazu aka yi min aure. Yarinyar nan ce kanwar Munir. Queen Amelia ta kara harzuka in har gaske ne Munir ya cuceta. Tace may the gods strike him....a wane dalili zai aura maka kanwarsa. Nasan bazai wuce son kudi ba. Shiyasa ya rinka kawota asibiti ko? To daga yau sai su manta sun taba ganin Prince Richard. Zai sake magana ta dauko wani kulli da Priest Chera ya bata ko da zata ga dan nata amma yaki biyota. Tana hura masa garin ya fada jikinta ko motsin kirki baya yi. Tayi murmushi idan kuna tsafi kunzo gidansa. Dana yafi karfin auren irinku.

Sau uku Anti Nadiya tana kwankwasawa Ruqayya kofa akan ta fito falo amma kunya ta hana. Da wane ido zata kalli su Mummy. Karshe su Amira ne suka bita dakin suna mata hira. Hankalinta gaba daya baya wurinsu don an kwashi awa da fitar Farouq. Gashi wayarta  tana falo ballantana ta kira shi.

Ita ma Mummy abinda ke damunta kenan. Wayar Ruqayya tayi ringing ta tura Rahma yar Nadiya ta biyu ta kai mata daki tunda yau kunyarsu take ji. Abida ce ta gama tsokanarta tace ina angon naki. Ruqayya tace ya fita siyo min kayan dadi zaki ci ne hajiya kwalama? Abida tayi dariya su Laila Majnu nasan bakinki har keya yau. To ki dai rage min yan kayan dadin kinsan masu ciki. Suna gama hirar Ruqayya ta gwada kiran Farouq ashe ba kudi a wayar. Tace Amira aro min wayar Anti don Allah. Amira taje ta dauko waya, Nadiya tace dawo min da ita sarakan game. Amira tace Anti Ruqayya ce ta ce na aro mata zata yi waya. Mummy tace Allah sarki kila ko don taji Farouq shiru ne. Anti Nadiya tace bari na kira na tsokane shi kafin na bata. Ringing biyu taji an dauka tace ango zan mayar da amaryar wallahi. Ji tayi ance sai dai ku tsananta addua amma wallahi an sace shi. Anti Nadiya tace wayar aka sace ko me? Mutumin yace muna cikin shago saboda ruwa ya fito zai shiga mota sai ga wasu bakaken motoci har uku. To da farko munyi tunanin yasan mutanen sai dai bamu ankara ba muka ga sun tura shi a mota yana tirjewa. Kafin mu fito wallahi sunyi nisa don da yar tazara tsakaninmu. Ni na tsinci wayar dama kasa amfani mukayi da ita muke jiran ruwa ya tsagaita mu nemi yan sanda. Anti Nadiya ta soma zubar hawaye tace a ina ne? Ya fada mata wurin ga motarsa ma a bude ya barta. Mummy na ganin halin da take ciki tace ke me nene duk da gabanta sai faduwa yake. Nadiya tace yan yankan kai sun  sace Farouq. Mummy tayi matukar razana ta hau sama da sauri ta sanar da Barrister. Ita kuma Amira da akayi abin a gabanta itama ta tafi da gudunta ta ce Anti Ruqayya yan yankan kai sun sace Uncle Farouq. Tayi dariya bakinki suka sace dai. Amira ta na hawaye tace muje falo kiga wallahi su Ummanmu kuka suke. Ita duk tunaninta ko wasa ne tabi bayan yarinyar. Abba B ta gani yana ta juya jallabiyarsa ya kasa daidaita ta ya saka. Cewa yake Innalillahi wa inna ilaihi rajiun. Me yayi musu zasu sace shi? Ya Allah Ka kare yaron nan duk inda yake. Ji tayi kunnuwanta kamar sun dena ji saboda tsabar kaduwa. Kada ku fadawa Ruqayya ya ce da su Mummy, bari naje wurin na gani. Sai dai muryarta kaeai suka ji tana Salati sai ta fadi kasa sumammiya.









Batul Mamman(Mrs)💖
[7/26, 11:18 PM] Fatima 💖: RUQAYYA YAR ALBARKA✨35





Mummy tana kokarin daga Ruqayya Anti Nadiya tace ta kyaleta. Dukkansu kuka suke yi shi Barrister ya kasa basu hakuri. Dankwalin Rahma Nadiya ta cire ta jika shi da ruwa a kitchen ta matse ta dawo tana shafa mata. Mummy cikin kuka tace ka tafi ka duba Farouq din sannan ka kira Abbanta. Idan bata farfado ba zamu tafi asibiti. Da kyar ya iya jan kafarsa ya fita. Lokacin ruwan yayi karfi sosai, zuciyarsa zai zafi take masa saboda yadda lokaci guda al'amura suka baci. Innalillahi wa inna ilaihi rajiun kawai yake fada har ya shiga mota. Sai da ya tada motar ya kira Abba ya sanar dashi komai.

Haka Barr Mukhtar ya ja motar zuciyarsa na ta sake sake. Su waye suka dauki Umar Farouq? Dama haka iyaye suke ji idan dansu ya bata? Lallai Maryam tayi dauriya tunda ta sawa ranta abinda ta haifa yana da rai amma yaki gaskata zancenta. Yanzu idan bai sake ganin Umar ba zaiji dadin rayuwa? Wani irin haske ya gani a gabansa daga nan motar ta kwace yayi karo  da transformer.

Da takalma duk hagu Abba ya fito daga dakinsa ya fada falon baki babu ko sallama inda Abida da Munir suke zaune suna hira. A gigice yake, su kuwa zumbur suka mike tsaye yace Munir tashi mu tafi. Munir yace Abba ina zamu? Mami da ta hango shigarsa falon ta biyo baya tace lafiya kuwa Abban Hidaya? Allah kadai Yasan  yadda zuciyarsa take masa yace ku tafi gidan Barrister yanzu. Hidaya ta daure ta ja ku a hankali kai kuma muje BM mall Barrister na jiranmu a can. Ita dai Mami jikinta duk yayi sanyi suka tafi kowa na tsoron abinda zasu tarar. Suna tafiya a mota ne Abba ya sanar da Munir abinda yake faruwa. Shima ya kadu sosai. Ga duhun gari dana hadari amma hakan bai hana shi ganin motar dake hayaki a gabansu ba. Ga mutane suna kokarin ciro mutum daga ciki. Abba ma ya lura yace tsaya kamar motar gidan Barrister. Da gudu suka karasa suka tarar dashi a sume jikinsa duk jini. Duk dauriyar maza ba karamin gigita Abba yayi ba. Shi kuwa Munir kuka yake yana cewa hannu aka sa musu. Daga wannan sai wannan masifar. Abba ya daka masa tsawa kada kayi sabo mana. Da taimakon mutanen wurin suka sashi a mota suka wuce asibiti. A hanya suka tsaya Munir ya karbi wayar Farouq da mukullin motarsa.

Da salati Ruqayya ta farka taga iyayenta da yan uwa a tsatstsayi a kanta. Idanuwansu duk sunyi ja saboda kuka. Duk da hawayen da ke sauko mata kamar ruwan zafi sai cewa tayi ba'a ganshi ba ko? Hidaya ta gyada kai....tayi murmushin da yafi kuka ciwo nasan zai dawo In Sha Allah. Idan bai dawo ba haka kaddararmu take zanyi hakuri har Allah Yasa naji sassauci a zuciyata. Tasa hannu ta share hawayenta bari naje nayi sallah ta tafi toilet. Babu wanda ya tsayar da ita ta shiga tana rufe kofar ta zauna a kasa ta dafe zuciyarta dake yi mata zafi ta saki kuka sosai har suna jin sautin kukanta. Mami tayi hanyar toilet din sai Mummy ta riketa kyaleta tayi Fatima sai ta sami sassauci a zuciyarta. A lokacin babu mai rarrashin wani duk kukan suke yi suna jin tausayinta. Sai da ta gaji da kukan ta fito tayi  sallar magriba da ishai. Anti Gaji ce ta shigo suna jajantawa juna tace musu ya kamata su kai Ruqayya asibiti a dubata. Munir ne ya sanar da ita komai har hatsarin Barrister. Da dabara tasa suka tafi da Ruqayya duk da ta dage ita lafiyarta kalau. Dama ita so take su je su ga Barrister bs tare da ta sake daga musu hankali ba. Bus din gidan Anti Gajin ce ta daukesu suka tafi kowa shiru. Sunyi mamakin ganin motar Munir a waje sai kuma jinin da suka gani a jikinsu Abba ya kara tada kusu hankali, Mummy tace an tsinci Farouq din ne? Ina Barrister ta fada tana neman wayarta bari na kira shi. Abba ya kalleta cike da tausayi yace mata ki kwantar da hankalinki in sha Allah komai zai zo da sauki. Barrister yana cikin theatre ana masa aiki. Kusan dukkansu kowa yace Me? Aiki? Me ya same shi?  Abba ya numfasa yace hatsari yayi kafin yaje inda aka ga motar Farouq. Mummy tace La'ilahaillah Muhammadur rasullullah. Ni Maryam Allah nagode maKa. Sai wani sabon kukan ya tashi. Ruqayya ta rungumeta suna yi babu mai bada hakuri sai Abba mai cewa suyi masa addua ba kuka ba. Anti Nadiya ce ta iya kiran Hajjaju mamanta da Umma babar Barrister a waya ta sanar dasu.




Batul Mamman(Mrs)💖
[7/27, 6:41 PM] Fatima 💖: RUQAYYA YAR ALBARKA✨36





Kwanaki biyu kenan Farouq yana kwance tun ranar  jumaa da Queen Amelia ta fesa masa maganin da Priest Chera ya bata har yanzu bai farka ba. Suna tsaye gefen gadonsa ita da King Edward harda Princess Sophia. King Edward ya dubi matarsa da ke zubar da hawaye yace wai yaushe kika koma wurin Oracle Priest har ya baki wannan maganin? Yaron nan zai iya rasa rayuwarsa idan bai farfado ba. Ita da kuka takeyi kamar ranta zai fita ta zauna gefen gadon ta rike masa hannu. A hankali take magana...kin amincewa yayi ya biyoni har yana cewa wai yayi aure. Sophia ta dafe kirji aure fa kika ce? Queen Amelia bata kula ta ba ta cigaba da maganarta. Maganganunsa kamar wanda ya sami tabin kwakwalwa haka naji suna fita shiyasa nayi amfani da maganin. Idan Priest Chera bai zo ba har dana ya mutu nima kashe kaina zanyi. Bazan taba iya rayuwa babu Richie ba. Sai a lokacin ta bawa King Edward tausayi ya janyota jikinsa yana rarrashi.

Dakin da aka kwantar da Barrister Mukhtar kullum cike yake da yan uwa da abokan arziki. Ba laifi ya soma samun sauki duk da yaji jiki sosai. Karaya biyu ya samu a hannunsa na hagu sai yankan da glass yayi masa a kafada wanda aka dinke. Ga ciwon da jikinsa yake yi saboda buguwa. Mummy duk ta rame a 'yan kwanakin nan. Ruqayya kullum tana tare da ita a asibiti. Duk wanda ya gansu sai ya tausaya musu. Maganar batan Farouq har wurin 'yan sanda amma shiru babu wani kwakkwaran zance. A gaban mutane Ruqayya nuna dauriya take yi sosai sai ta shiga daki tayi kuka mai isarta.

Ranar da Barrister yayi kwana uku a asibiti duk yawancin mutane sun tafi sai Mummy da su Abba da Hajjaju. Yana daga kwance ya dubi Mummy yace wai yar kwalliyar nan ma kin dena yi min don kinga ina kwance ko? Abba yayi murmushi Barrister ka fiye zolaya. Hajjaju tace rabu dashi, yanzu da zatayi sai yace bata damu dashi bane. Girma yazo amma basa fasa hali. Ta dubi Mummy da tausayi yar tawa ce ma naga bakin ya dan mutu. Ruqayya ta danyi murmushi tana kallon su. Fuskarta ko kwalli babu wanka kawai take yi ta zura kaya. Barrister ya kalleta kiyi hakuri yar albarka da yardar Allah zan nemo mijinki indai yana raye. Allah bazai sa naji kunya ba na hada aurenku. Abba yace haba ka dena irin maganar nan. Idan ka sami lafiya sai mu koma kan batunsa. Jiya Munir ke cewa zaije garinsu ya duba yana iya kasancewa daga gida aka zo aka dauke shi. Idan barayi ne ya kamata ace sun hada da motar. Wata ajiyar zuciya Ruqayya tayi don sai a lokacin suka yi wannan tunanin. Ita indai yana nan lafiya ko da a gaban iyayensa ne hankalinta zai kwanta.  Barrister yace wato Engineer ina mamakin yadda Allah Ya dora min son yaron nan. Sai yanzu nake jin abinda mutanen da aka sacewa yara sukeji a ransu. Lokacin da Maryam ta haihu ta dage an canza mata baby a asibiti kin yarda nayi. Batan Umar Farouq yasa na kara tausayin halin da ta shiga. Yana kallon fuskarta yace in sha Allah idan aka gama da case din amarya Ruqayya zamuje India domin a warware mana komai yadda zamu sami nutsuwa. Shekaru talatin da biyu kina ta kwana da zulumi kullum. Mami tace dama kin taba haihuwa? Ko wannan ne abinda kike cewa a tayaki addua kullum a shirinki na rediyo? kuka kawai Mummuy take yi tana basu labarin abinda ya faru da ita shekarun baya. Mami tana tayata kukan tana kuma bata hakuri. Ruqayya ta rinka kallonta cike da tausayi itama tana kukan. Ba karamin juriya Mummy tayi ba. Dole ta rinka sata a addua Allah Ya tabbatar musu da alkhairi game da abinda suka haifa.

A can garin Ndam kuwa Priest Chera ne tsaye kan Farouq yana ta surutansu na bokaye yana turnuka masa hayaki. Su Queen Amelia suna gefe suna jiran farkawarsa. Kwanaki har sun kai biyar bai tashi ba. jinsu take kamar shekaru tayi ba Richie. Can suka ga ya motsa kafarsa. King Edward ya zauna a gefen gadon ya rike masa hannu. Richie bude idanunka ka ganni babanka ne. Queen Amelia ma ta zauna ta dora kansa a cinyarta yadda ta saba yi masa. Ka tausayawa mamanka Richie ka tashi. A hankali ya bude idanunsa yana cewa Lailaha illallah Muhammadur Rasullullah. Priest Chera ji yayi kamar sandar tsafinsa ta zama itacen wuta yayi saurin yar da ita a kasa. Ya dubi Farouq a razane...your majesty me ka fada yanzu? Farouq ya tashi yana dafe kai yace salati nayi. Baka sanshi ba amma na ambaci sunan ubangijin dukkan halittu ne Allah SWT. King Edward ya mike a zabure Richie kada ka ce min kayi doguwar muamala da musulmai a Kano. Queen Amelia tace kada ka soma yi masa fada daga tashinsa. Yayi murmushi Dad abinda ya hadani da yan Kano ya wuce muamala. Daga yau sunana Umar Farouq, na karbi musulunci kuma dazu aka daura min aure da Ruqayya. King Edward ya kalli Priest Chera ka taimaka min yaron nan ya haukace. Shi da ya kwana biyar a kwance amma yake cewa dazu yayi aure. Wani tsalle Farouq yayi ya sauko daga kan gadon. Mum da gaske nayi kwana biyar a kwance? Tace eh Richie abinda na fesa maka ne yaki sakinka da wuri, duk mun tsorata. Takalmansa ya soma dubawa a gefen gado. Ya kalli guard din da yake tsaye kusa da gadon yace kai samo kin takalmi. Kano zan tafi yanzu nasan su Ruqayya hankalinta da nasu Mummy ya gama tashi. Ina wayata na kira su? Queen Amelia ta fara kuka tana tsalle da gaske danta ya haukace. Sai kiran wata yake da Mummy. Wannan wace shegiyar ce take son rabani da dana? King Edward yace sauran guards din su rike masa Richie kada a bari ya fita zai nemo likitoci. Shima Priest akace yayi nasa tsafin ya kwance nasu kullin. Priest Chera yace ai na fada muku danku ya sami haske. Ya durkusa gaban Prince Richard, your Majesty nima ina son irin haskenka. Zan dawo ka taimaka min, abinda ka fada dazu yasa har yanzu jikina yana rawa. Farouq yayi murmushi yace sai ka dawo Chera. King Edward yayi ta kiransa ya fice abinsa ko waige. Guards din da suka zo rike Farouq kuwa tsawa ya daka musu yace kada su taba shi. Queen Amelia ta cigaba da kuka ya rike kafadunta. Mum kiyi hakuri ba haukacewa nayi ba. Musulunta nayi kuma na auri yarinyar da tayi sanadin haduwata da musulunci na aureta da izinin iyayenta. Duk inda naje zan dawo gareki ki barni na tafi na gansu. Ta rike masa hannu kam bazaka tafi ka barni ba Richie. Muje naga abinda suka yi maka. Sunyi hanyar kofa king Edward yace idan ka fita daga nan Richie kada ka dawo don na yafeka a matsayin dana. Ya dubi babansa cike da takaici ba komai Dad zan dawo kuma yadda naga haske a rayuwata kaima zaka gani. Daga nan ya rike hannun Mum dinsa suka fito waje. Sai lokacin yaga duhun dare ya tambayeta karfe nawa tace hudu da rabi na dare. Yace to sai da safe zamu tafi yanzu bari naje nayi sallolin dake kaina.




Batul Mamman(Mrs)💖
[7/28, 1:43 PM] Fatima 💖: RUQAYYA YAR ALBARKA✨37




Batul Mamman(Mrs)💖





Kafin bakwai na safe Farouq ya gama shirinsa tsaf cikin kaya na alfarma.  Yanayin shigarsa tamkar prince Richard na da. Sai dai wannan karon yafi nuna kwarjini da kamala saboda sunansa Umar Farouq. Queen Amelia itama shigarta ta matar sarki tayi. Ga mahaifiyarta Madam Hannah a gefenta.Ya zama wajibi a gareta taje taga mutanen da suka sauya mata danta har yake kiransu iyayensa. Sai kuma tayi murmushi da ta tuna yace yayi aure. Tabbas idan har ya auri irin matar da yake so zata ji dadi. Bata son takurar da ake neman yi masa. Sai da suka fito ana shirye shiryen shiga motocin da aka jere a waje suka ga wata mota ta shigo. Princess Sophia ce tare da dreba. Bayan ta durkusa har kasa ta gaishe da Queen Amelia ta mike zata rungume Farouq. My Prince nayi kewarka da yawa, ya jikin naka? Ya ja  baya da sauri. Tayi dan murmushi nasan baka sona Richie kuma na riga na fadawa zuciyata ta hakura da abinda bazata samu ba. Duk tsahon shekarun nan ban sami soyayyarka ba nasan bazan samu yanzu ba. So nake kawai mu zauna a matsayin abokai. Sakin fuska yayi da jin maganarta. Nagode da kika fahimceni amma wa ya fada miki na farfado? Nine nan yaji muryar babansa. Shima a shirye ya fito. Zamu je Kano tare daku na duba irin mutanen da ka zauna dasu da matar da suka baka. ko zan hakura da kai a matsayin dana sai na tabbatar da wurin da ka koma. Hakan yayiwa Farouq dadi har yana tunanin ko adduarsa ta shiriyar iyayensa ce ta soma cinsu. Haka suka shirya motoci takwas a jere suka kama hanyar Kano. Basu iso gari ba sai goma na dare shima don suna tsayawa Farouq yayi sallah.

Abba yana ta mitar su Mami su tashi su tafi dare yayi amma ba ita ba ba yaran ba kowa yaki tashi. Ruqayya dama tana zaune tsakiyar Mummy da Anti Nadiya. Anti Nadiya tace nima tun dazu nake son Hajjaju ta tashi taki Kawu. Idan zaki kwana da dan naki ne ki fada min na tafi kada maigida ya kullenmin kofa. Hajjaju ta daka mata duka a cinya. Zama da Maryam da Mukhtar yasa kema kika mayar dani kakarki. Kuma yau sai shadaya zamu tafi idan kuma zaki barni ne sai naji. Na kira mijin naki komai dare yazo ya kaini. Ana ta dariya Ya Munir yace Abba dan kyalesu mu dan sake zama ko don saboda Abba B tunda hakan nayi masa dadi. Nan kuwa kwatancen asibiti yayiwa Farouq yake jira su iso. Shi kadai yayi murnarsa a waje amma yaja bakinsa yayi shiru. Yafi son ya shigo kowa ya ganshi da idonsa. Farouq kuwa har kuka yayi jin Barrister yayi hatsari.

Dr Yahya shine zai karbi likitan da ya wuni a asibitin. Ya dawo daga hutun da ya dauka na karshen shekara wanda a lokacin ne yayi aure. Likitan na nuna masa files din patients da yan bayanai game dasu yana cewa ya gane. Nan kuwa text amarya tayi masa yake ta karantawa yana murmushi. Ana gama bayanin ya kwashe files din ya kira nurse suka tafi zai duba su.

Maigadin asibiti ganin irin motocin da ke shigowa ya saki baki yana kallo. Dole ya barsu suka shiga ganin fuskokin mazan da ke gadin mutanen cikin motar. Kafin motar ta gama tsayawa Farouq ya bude ya fito da sauri. Queen Amelia tana cewa ya kula kada ya fadi. Ya Munir ya sake kira ya fito daga dakin ya sauko kasa suka rungume juna. Farouq yace ina matata? Dama nasan duk baka damu da mu ba. Muje wancan dakin ne ya nuna masa. Ko jiransa baiyi ba ya haye saman. Da sallama ya tura kofar dakin. A cike ya gan shi amma hakan bai hana shi fara hada ido da abar sonsa ba. Zuciyar Ruqayya ta shiga bugawa da sauri. Sai tasa kuka kawai. Kowa yayi mamakin ganinsa a wannan lokaci. Lokaci guda hawaye ya sauko masa ya karasa ciki ya rungume Barrister Mukhtar yana kuka. Babana kayi hakuri kwana na biyar a kwance bansan inda nake ba. Wani sanyi da farinciki ne ya cikawa  Barrister zuciya. Sai Hamdala yake kawai. Farouq ya dago ya rungume Abba shima. Hajjaju tace wannan dan naku shine sarkin runguma. Sai da ya gama gaisawa da kowa harda Mummy wadda itama kuka takeyi sannan ya janyo hannun Ruqayya daga inda take zaune. I miss you so much my love. Ta rasa yadda zata yi da shi. Tana murnar ganinsa tana kunyar idon mutane. Itama rungumetan yaso yi a wurin abinsa don ba ruwansa da yawan mutane . Hidaya da Abida suka ce masa yaja ta su tafi  waje. Mami dai kasa daga ido tayi don kunya. ko a jikinsa kuwa yayi niyar fita rike da hannunta Dr Yahya ya turo kofar tare da nurse. bayan sun gaisa yace lallai bawan Allah kana da yan uwa da yawa. Allah Ya kara sauki. Suka amsa da Amin .To wane ne dan nasa ya tambaya. Farouq yace nine. Mummy da Abba B sunji dadin amsarsa. Dr Yahya yace da nurse din ta debi jininsu su biyun. Abba yace me zaayi da jini kuma? Yaron nan dansa ne amma ba na jini ba. Likita yana laluben wayarsa da ya sake jin shigowar text bai sami damar bada amsa ba saboda baiji me Abba ya fada ba. Suna gama diba yace ku jira a kawo result  sannan suka fice yana karanta text yana dariya.

Farouq ya ja hannun Ruqayya suka fice. Mummy tace yau dai Fatima siriki ya hanata motsi. Sai a hankali zai gane al'adunmu. Shi kuwa a wajen da suka fito tambayarta yayi ko akwai dakin da babu patient ta nuna masa sannan tace me zakayi dashi? Ya dan lumshe ido yana jindadin kallonta. Nima kwanciya zanyi ki duba ni bani da lafiya. Tayi yar dariya  Suna shiga dakin ya janyota jikinsa. A kunnenta yake rada mata yadda yayi missing dinta. Idonta fal hawaye yace kiyi hakuri in sha Allah bazan kara tafiya na barki ba. Ya dago kanta cikin tafukan hannunsa. Ta fara sunne kai kasa. Not today my love, please kada ki hanani kallon fuskar Ruqayyata. Ta kalle shi da mamaki yaushe ka iya fadin sunana sosai. Yayi murmushi ladan iyawa nake so. Ya kara matso da ita jikinsa. Ta juya baya zata gudu ya sake kamota tana kallon kofa. Da yasan yadda take ji don kunyarsa da ya barta ta tafi. Gaba daya ya rufeta ta baya dama gashi da tsayi. Ya saita bakinsa  a kunnenta yana magana a hankali.  Yau na taho miki da kazar amma tana mota. Ai zan iya kissing dinki ko.....wani murmushi tayi kafin tace a dakin asibitin? Ya juyo da ita ganin tana shirin gudu. Ki dena yi min yanga Ruqayya kada na ce zan rama fa. Kwankwasa kofar da akayi ne yasa dole ya hakura ya bude kofar.

Ya Munir ne ya bude to sarkin soyayya kasan ka bar su Sarki a kasa ko. Sun ce sai kaje zasu hawo tare da kai sannan an kawo result din test din ka fito. Kafin ya fita Ruqayya tayi waje da gudu. Ya Munir yana dariya yace ka bita dai a hankali Babanta lauya ne ta iya kai karar mutane. Farouq yace ni da ita ba kai kara baban Yaya.  amma jinin me aka dibar  mana ne ko zaayi masa karin jini ne? Ya Munir yace nima ban sani ba.
[7/30, 7:21 PM] Fatima 💖: RUQAYYA YAR ALBARKA✨38





Batul Mamman(Mrs)💖





Da suka fito daga dakin Farouq yayi hanyar benen bari na sauka na kirawo su kada su kara cewa su Mummy suna son rabani da su. Ya Munir ya jira shi ya sauka suka taho tare da iyayensa da Madam Hannah.

Jikin bango ya hango Ruqayya kanta a kasa kada ma su hada ido. Murmushi kawai yayi sai yayi maganin wannan kunyar. Ya dakatar da iyayensa daga bakin kofa amma ya barta a bude..naga akwai likita a ciki bari ya gama sai mu shiga. Dr Yahya rike da wayarsa ya dubi su Barrister yace Alhamdulillah komai na jinika da dan naka yayi daidai saboda haka gobe da karfe uku in sha Allah za'a shiga theatre ayi aikin. Allah Ya kara sauki yanzu daga nan har ayi kada ku sake bashi komai sai da izinina ko wani likitan. Abba cikin rashin fahimta yace wai wane aiki za'ayi masa ne doctor? Dr Yahya yace aikin kidney transpant(dashen koda) mana. Kowa cike da mamaki suka rinka tambayar likitan me ya sami kodar tasa. Shi kanshi Barrister Mukhtar tashi yayi zaune saboda jin wannan maganar ta likita. Farouq da yake tsaye da su King Edward shima karasa shigowa yayi a razane. Yace Babana dama kana da matsalar kidney? Barrister yace nima sai yau nake ji. Abba ya dubi Dr Yahya da yake kokarin rubuta text a waya cikin nutsuwa yace kaga likita ka dan taimaka ka ajiye wayar nan taka a aljihu. Dr Yahya ya dan bata rai sannan ya zurata a aljihun wandonsa. Abba yace Madallah, yanzu ina so kayi mana bayanin yadda akayi mutumin da yayi hatsari ya karye a hannu ya kamu da ciwon koda lokaci guda har ake shirin dasa masa wata. Watan ma ta yaron da babu wata alaqa ta jini tsakaninsu. Dr Yahya yace bangane ba, yallabai kana son cewa ban iya aikina bane ko me? Ya mika hannu ga nurse din da suke tare. Ke bani file dinnan, ta miko ya karba yana dubawa. Ya dago kai a fusace yana kallon Abba mara lafiyan naku ba shine Tanko Namata ba? Hajjaju tace Alhamdulillah ba shi bane. dana sunansa Muntari. Dr Yahya ya rude, what? Sai ya karbi sauran files din yana dubawa. A kunyace bayan yaga wanda yake nema yace kaine Barrister Mukhtar? Abba yace yanzu naji magana, shine. Mu da aka cewa nan da kwana biyu zaa sallame shi sai kazo kana maganar dasa koda. Queen Amelia ta taba mijinta da turance ta tambayeshi me suke fada yace shima bai sani ba.

Dr Yahya yaji kunya sosai ya shiga basu hakuri. Abba yace ai wayar nan zaka ajiye idan kana aiki. Aikinku yana bukatar nutsuwa saboda rayuwar dan Adam ba abin wasa bace. Dr Yahya yace hakane don Allah ayi hakuri dai. Har ya fita su King Edward sun gama shigowa dakin ya dawo da sauri. Ya dubi Abba da suke yiwa juna barka yace yallabai kace jinin yaron da muka diba basu da alakar jini da patient din. Farouq yayi dan murmushi yace eh amma tamkar babana na dauke shi. Dr Yahya yace kai, kai, kai idan ni nayi kuskure wanda yayi gwajin nan bazaiyi ba. Saboda yadda sakamako ya nuna mara lafiyan na jin jiki muka yi gwaje gwajen nan da wuri cikin nutsuwa. Mutum biyu ne suka yi suka bamu sakamako iri daya fa. Abba yace kaga likita kaje kawai babu komai. Dr Yahya ya tsaya ya kalli Barrister ya kalli Farouq yace kai wallahi kada abin ya koma rainin hankali. Ke Amina tafi lab ki karbo min robobin da aka saka jinin mutanen nan mu gani. Su kadai akayiwa irin test din nan a yau. Nurse Amina ta tafi cikin sauri. Su Abba kuwa sai jiran sake bawa likita kunya. Hajjaju tace anya yaron nan kasan abinda kake yi kuwa? Sau daya matar Muntari ta taba haihuwa yarinyar bata zo da rai ba. Sai kawai ka kalli yaro ga iyayensa a baya kace wai gwajinku ya nuna dansu ne. Mummy dai gabanta sai faduwa yake. Ta rasa dalilin wannan firgici da ya kamata lokaci guda.

Bai fi minti biyar da tafiyarta ba Nurse Amina ta dawo da kananan robobin har da ainihin takardar gwajin guda biyu da aka saka sunayensu. Dr Yahya ya duba ya kuma nunawa Abba da Farouq har ma da Munir. Kun gani ko...ga shi dai sunayensu ne a jikin takardar da kuma robar da aka zuba jinin. Su kada ne a wurin da akayi ballantana ace an hada na wani da na wani. Wanda yayi test din ma sai gashi ya shigo shima ya sake tabbatar da hakan.
 Dr Yahya ya kalli King Edward a ransa yace da gani baya jin hausa. Da turanci yace masa ka tabbatar yaron nan danka ne? Ya nuna Farouq. King Edward yaji tambayar wani iri yace kai ka kiyayeni ko nasa a karbe lasisinka na aiki. Queen Amelia tace wace irin tambayace wannan zaka ce ko dansa ne. Amma zuciyarta ba karamin firgita tayi da jin maganar ba. Dr Yahya yace ni yau bazan bar wurin nan ba sai an warware min wannan kullin. Queen Amelia ta karasa shigowa tace kaga Richie ka nuna min matar taka kawai na ganta mu tafi. Gobe idan sun daidaita matsalarsu sai mu dawo. Farouq ya nuna mata Ruqayya a sanyaye duk maganar Dr Yahya ta tsaya masa a rai. Queen Amelia  tace ina mamanki take mu gaisa. Mummy ta mike tsaye, gani ta matsa kusa da Ruqayya.

Da za'a gwada jinin Queen Amelia ba karamin hawa yayi a lokacin ba saboda tsananin rudani. Ko kadan bata wani kalli fuskokin matan dakin sosai  ba sai yanzu. Yaushe zata manta wannan fuskar da ta dade tana mata yawo a ka. Fuskar da take yawan tashinta daga bacci a firgice. Jiri ne ya debata ta kusa faduwa. Farouq ya riketa da sauri. Ta daga hannunta da yake rawa ta nuna Ruqayya kin tabbatar yar..yar...yarki ce ta cikinki? Mummy ta dan sha kunu meye matar take neman kure su tace 'yata ce mana. Queen Amelia ta durkushe a kasa tasa kuka da karfi. Madam Hannah  ta rike ta tace Amelia me ya faru? Shima King Edward ya rude yazo yana kokarin tashinta tsaye shi da Farouq. Queen Amelia tace laifinmu na shekarun baya ya tarar damu Mama. Gashi saboda son zuciyarmu wa ya auri kanwarsa ta ciki daya. Nan da nan kowa hankalinsu ya dawo garesu King Edward kuwa sakinta yayi saboda bai fahimci furucinta ba. Princess Sophia da aka manta tana tsaye a bakin kofa tace your Majesty me kike nufi? Queen Amelia tana cigaba da kuka ta dubi Mummy, ranar wanka ba'a boyon cibi...ko kin tuna zuwanki India haihuwa shekarun baya da suka wuce???
[8/1, 9:57 PM] Fatima 💖: RUQAYYA YAR ALBARKA✨39



Batul Mamman(Mrs)💖




Mummy na jin haka gabanta yayi mugun faduwa.  Ji take kamar zuciyarta zata fasa mata kirji ta fito. Queen Amelia ta cigaba da cewa Richie danki ne gashi ya auri kanwarsa. Wannan wace irin mummunar rana ce gareni. Mummy jiki a sanyaye da kyar ta iya jan kafa ta karasa gaban Farouq ko tunanin bawa Queen Amelia amsa batayi ba. Hannuwansa biyu ta kama kowa a dakin yayi tsit yana kallonsu. Ta juya hannuwan daidai saitin kananan yatsunsa. Gabanta ya sake faduwa ganin abinda take nema. Cikin kankanuwar murya tana mai kare masa kallo ta tambaye shi da turanci yadda kowa zai fahimta Umar Farouq meye wannan a hannuwanka.? Zuciyarsa duk ta gama tsinkewa ya bata amsa Mum tace da yatsu shida aka haifeni, shine aka cire min wurin yayi wannan tabon. Daki sai salati ake yi da sautin kukan Queen Amelia. Mummy na jin abinda ya fada ta ja shi gaban Barrister Mukhtar. Shima hannunsa ta kama ta juyasu yadda mutanen dakin zasu ga tabon inda aka cire masa yatsansa na shida tace wannan shine mijina kuma mahaifinka. Ta matsa kusa da Hajjaju ta juya mata hannuwa. Ita kuma wannan kanwar kakarka ce kaga nata yatsun ko. Farouq ya gyada kai kamar kurma. Wai me yake shirin faruwa a wajen nan ne, me Mum dinsa take nufi? Ta kama hannuwan Anti Nadiya ta sake nuna musu wannan yar Hajjaju ce kaga ta zama kanwa ga mahaifinka. Sai a lokacin ta soma kuka sosai. Allah nagode maKa da Ka nuna min wannan rana da raina da lafiyata. Ya Allah Ka karawa Annabi Muhammad SAW daraja da daukaka. Su Mami cewa suke amin amin suna tayata kukan. Barrister Mukhtar ya rungume dansa ya kasa daurewa duka kuka sukeyi mai ban tausayi. Babu wanda ya taba tunanin faruwar wannan al'amari.

King Edward fadawa yayi jikin Ya Munir batare da ya sani ba saboda gigitar da yayi. Bashi kuma da ikon karyatawa tunda Queen Amelia da bakinta tace Richie ba danta bane. Madam Hannah kuwa cewa tayi Amelia kin cucemu kin tona mana asiri. Ita dai kukanta takeyi kawai bata kula maman tata ba. Ana wannan kukan Mummy ta saki Farouq, shi gabadaya kansa ya daure da abinda yake faruwa. Gaban Queen Amelia ta tsaya sai ji akayi ta shara mata mari. Queen Amelia ta rike kumatu zatayi magana Mummy ta sake marinta a daya kumatun. Duk dakin babu wanda yayi tunanin hanata hatta Farouq da akeyi dominsa. Ya rasa a wane mazauni zai saka Mum din tasa da yake so kuma yake tunanin itama tana sonsa.

Mummy ta kalli Queen Amelia dukkansu idanuwansu kamar garwashi murya na rawa tana girgiza kai tace shekara talatin da biyu! Shekara talatin da biyu mijina da yan uwana suna min kallon wadda son haihuwa ya tabawa kai. A tsahon lokacin nan babu wanda ya taba yarda da zancena. Ni kadai nake kukana a boye nake adduata saboda kada na tabbata mara hankali a gaban mutane. Shekara talatin da biyu ina kukan batan dan da bansan wane iri bane amma bazan iya yi a bayyane ko na fadawa mijina ba saboda bani da hujja. Kinsan sau  nawa nake farkawa cikin dare ko rana saboda mafarkin kukan jariri da naji da yatsun da na gani da idona amma likitoci sun karyata ni. Ni kaina har tunani na fara yi ko da gaske tsabar son 'ya'ya ya taba min kai. Ko kinsan shekarata nawa ban sami cikin da ya zauna min ba sai nasa. Kina ina nake shan wahala sosai duk domin cikin ya zauna??? Me nayi miki kika cutar dani kika sace min da? Farouq ya kasa jure kukan mahaifiyar da baisan yana da ita ba sai yau yaje ya rungumeta.  Abba yayi yar gyaran murya kiyi hakuri Haj Maryam. Kunga yadda Allah Ya nuna ikonSa. An sace shi a wata kasar amma Allah Ya nufa kasa daya zai rayu da iyayensa. Kuma Allah Ya wadata shi da fahimtar musulunci ya karbi addinin iyayensa da kakanni. Daku dashi babu wanda yayi tunanin za'a wayi gari abu makamancin wannan ya faru sai gashi wani abin mamaki wadda ta dauke shi ba'a ma santa ba amma da kafarta ta kawo kanta kuma ta tonawa kanta asiri. Lallai Allah Mabuwayi ne gagara misali. Hakika Shi kadai Ya cancanta a bautawa batare da kishiya ba. Barrister yace hakane Engineer. Ka duba kaga yadda Ya tsara komai tun daga abotar Umar farouq da Munir zuwa ranar da malam Hafiz ya kusa dukan Ruqayya har tazo gidana. Da ace bamu saurareta ba ai da bamuga rana irin ta yau ba.

Queen Amelia ta rarrafa gaban mijinta tana rokon shi ya yafe  mata. King Edward tureta yayi ya hade fuskarsa kamar bai taba fara'a ba. Ba don abinda ya faru yau ba nasan har abada bazaki taba fada min gaskiya ba. Babu wani abu da zakiyi min wanda zai wanke laifinki saboda haka kada ki kuskura ki dawo min gida. Zan turo lauyana da takardar saki kisa hannu. Queen Amelia sai kuka tace your highness kada kayi min haka. Na tuba ka yafe min....ta matsa ta rike kafar Farouq, shima tureta yayi babu wani abu da zaki samu na yafiya a tare dani. Duk 'ya'yan duniya ki rasa wanda zaki dauka sai ni. Ta mike tsaye ta ce haba Richie kada ka yada ni a lokacin da nafi bukatarka. Tabbas ban haifeka ba amma na raineka Richie. Ni na shayar da kai ba wata ba. Matsayin babanka bai taba sawa na bar kula da kai ba. Bani da sauran jindadin rayuwa idan har baka tare dani. Ka yafe min dana albarkacin shekarun da mukayi kana kirana mahaifiyarka. Tana ji King Edward da Princess Sophia suka fita. Ta durkusa a gabansu tana rokonsu gafara. Madam Hannah ma durkusawar tayi tana kuka. Farouq sai ya kallesu ya kalli su Mummy. Barrister Mukhtar yace gatan da Allah Yayi mana ba wayonmu bane ko dabara saboda haka kuje mun yafe muku. Mummy tana share hawaye  ta gyada kai. Queen Amelia ta kama hannuwanta ta rike tana ta godiya. Idanu suka dawo kan Farouq ana jiran yace ya yafe musu sai kawai ya koma kan gado kusa da mahaifinsa ya zauna. Su Madam Hannah kuwa sun bawa Ruqayya tausayi. Ta kalli Farouq ta dan bata rai tana masa nuni dasu a durkushe a kasa, sarai ya gane  abinda take so sai ya ji akayi yace anki din. Mami tace kai da wa kuma? Ya dan tura baki Ruqayya ce sai zare min ido take wai na yafewa Mum. Abba yace da kai bazaka yafe ba? To Abba duk abinda ya faru ai kawai su tafi su da Allah. Ruqayya ta harare shi sannan ta daga Queen Amelia tsaye tana share mata hawaye. Ki dena kuka ya yafe miki. Queen Amelia ta ce kinga ko kallona baya yi fa. A yadda yake sonki gashi ku yan uwa ne ai dole yaki yafe min. Hidaya tace kinga Madam Queen wannan ita ce  maman Ruqayya ga kuma babanta ta nuna Mami da Abba. Farinciki ya bayyana a fuskar Queen Amelia tace Mama ashe dai bamu da rabon azaba daga wurin goddess. Amma meyasa kika ce yarki ce ta tambayi Mummy. Barrister yace saboda mu hausawa muna da kara da kawaici. Kai kuma Umar idan baka ce ka yafe mata ba babu mai baka Ruqayya. Tana jin haka ta sunkuyar da kanta kasa tana murmushi. Shima dama jan aji ne amma yaushe zai manta da mum dinsa. Rungumeta yayi yace na yafe miki amma albarkacin Ruqayya. Duk akayi dariya Queen Amelia dai murna ta isheta ta kama hannunsa ta riko na Ruqayyan ta hada....duk da na rasa komai na rayuwata a yau amma ina tayaka murnar haduwa da iyayenka da auren da kayi.

Daga bakin kofa aka ji wata ajiyar zuciya. Dr Yahya ne yace koda naji ace yau duk asibitin nan kowa ana zarginsa da yin kuskure a aikinsa. Yallabai idan kun gama murnar don girman Allah kada maganar nan taje gun Director wallahi yana iya sawa a dakatar dani. Barrister yayi murmushi a madadina Baban Farouq da sauran mutane dakin nan muna masu tabbatar maka zance zai kai kunnnen director. Dr Yahya ya zaro idanu. Barrister yace amma yabo ne da godiya gareka.
[8/2, 4:58 PM] Fatima 💖: RUQAYYA YAR ALBARKA✨40




Batul Mamman(Mrs)💖





Katuwar tsakar gida ce cike da yan uwan Barrister Mukhtar da na Haj Maryam. Gwaggonni ne da kawunnai da 'ya'yansu. Hira ake yi cikin nishadi da farinciki. Suna ta gabatar da kawunansu ga Farouq.  Tun yana faraa har ya soma yake. Mummy ta kalle shi yana ta turo baki. Ta lura hakan ya zame masa jiki idan abu baya masa dadi ko ya gaji. Sati guda kenan ana ta yawon ganin dangi dashi. Gashi daga ita har baristan ba dai 'yan uwa ba. Har wurin yan uwansu na kauye duk an kaishi. Yau lahadi aka zaba a matsayin ranar da za'ayi yar karamar walima a gidan su Barrister Mukhtar da yan uwansu na kusa. Mummy ta ce Baban Farouq kaga danka yau tun safe ransa a bace. Barrister yayi murmushi yana son sunan nan da ya radawa kansa. Kinsan akwai gajiya yawon nan da muke yi dashi. Duk gidan da baka je ba ya zama abin surutu. Haka zai hakura komai mai wucewa ne. Gobe da jibi hutawa zamuyi don nima na gaji ga hannun nan yana damuna tun dazu da na bige. Sun cigaba da hirarsu Farouq ya taso daga inda yake zaune yana hira da cousins dinsa yazo ya kwanta akan tabarma ya dora kansa a cinyar Mummy. Ai wuri sai ya kaure da sowa ana ta yi masa dariya. Mummy ma dai taji kunya amma dan nata ko a jikinsa. Umma mahaifiyar Barrister ta taba Hajiyan su Mummy tace wannan jika naki ba dai son jiki ba kamar mage. Baki ji yadda kafata ta sage ba jiya da ya kwanta a  kai. Hajiya Kulu ta kwashe da dariya. Dama Umma ba lafiyar kafa ba...nima haka na sha wahala da Maryam yadda kika san bata da kashi haka take da. Umma tace a'a ya kawai don nace jikanki na son jiki zaki ce 'yata ma haka take? Umma tasa mafice ta dan taba shi kai taso ka koma wannan cinyar tafi kwari kada ka danne min 'ya. Ana ta dariyar yadda Farouq ke noke kafada yana dada kwanciya jikin Mummy. Bakin Barrister ya kasa rufuwa saboda komai dan nasa yayi dadi yake ji. Yace Umma don Allah ki dena matsa masa kara'i yake yi. Aka sake yin dariya Farouq yace Mummy ta kalle shi....ance hausawa idan suna son abu shiru suke yi su jira a basu. Hajjaju ce ta  bashi amsa. Ba komai ake yiwa haka ba amma ana son kunya da kara dai. Yace to ni nayi ta yin kunyar da karar duk baku gane ba. I miss my Ruqayya,  kwana takwas ban ganta ba ina ta yin kunyar amma anki a gane. Yan uwansa suka shiga tsokanarsa ya share su Mummy Allah zanyi kuka idan ban ganta ba yau. Anti Nadiya tace dama na fada miki ina jin dalilin turo bakin nan nasa kenan tun safe. Allah sarki Romeo yau dole kaje kaga matarka. Ya mike zaune yana murmushi yauwa Anti Nadiya.  kullum sai can dare muke komawa gida idan nace zani a ce dare yayi. Sau uku kuma duk a wani gidan muke kwana. Wayar da muke yi ma bata isa saboda duk inda muka je ana surutu. Bana iya bacci sosai saboda tunaninta ko nayi mafar...Mummy ta toshe masa baki da sauri don tana kallon yadda su Umma suke ta kawar da kai don kunya. Yanzu sai ya baro maganar da zata sa kowa jin kunya. Yana kokarin cire hannunta ta rada masa a kunne kayi hakuri yau ana yin sallar Magriba zamu tafi gida. Ya rungumeta harda kiss a kumatu. Hajjaju tayi dariya to gizo gizo sarkin runguma. Mummy kuwa kawar da kai tayi ai idan baka bani kunya ba sai a canja maka suna. Shi kuwa Baban Farouq ya rasa inda zaisa ransa don dadi. Ganinsu yake kamar Maryam dinsa da dan jaririn dansu. Umma tana kallonsu ta share kwalla Ya Allah mungode maka amma Maryam tayi hakuri sosai. Ba kiga yadda suke bani shaawa ba. Hajiya Kulu tace Allah baya bacci. Komai naSa da tsari da hikima. Mu mutane ne kawai masu gazawa da gajen hakuri.

Ruqayya tana zaune a kan kafet tana yankewa Iya Tasallah farce suna hira. Iya tace wai ina kedarin mijinki ne kwana biyu shiru. Ruqayya ta ce lallai Iya bakya son yatsunki. Ina miki yankan farce kina kiran sweetheart dina kedari? Ko yanzu kika zama kuturwa ai  zaki iya bara. Mami ta shigo falon ta  sakar mata rankwashi kakar tawa zaki yiwa danyen aiki? Ruqayya na susar kai tace ce wallahi da zafi sai na fadawa Mummy. Iya ta yi dariya kinga an rama min. Amma na dena tsokanarsa dama don naga yau ba kya faraa sosai ne. Gaskiya na jiyewa su Haj Maryam dadin ganin dansu. Mutanen kirki Allah Ya dubi hakurinsu. Ita dai Ruqayya sai shafa kanta take yi suka ji sallamar Mummy. Gabanta taji ya fadi Mummy ta zama surikarta. Ta soma kokarin tashi ta gudu daki don ko dankwali babu a kanta. Mummy ta shigo kana ganinta kasan tana cike da farinciki ...dawo dawo ta tsayar da Ruqayya yau ni kike gudu haka. Mami tace ai zamu ganku a rana. Dazu nace mata yaushe rabon da ta kiraki tace  wai ita kunyarki take ji. Mummy ta janyota jikinta haba yar albarka. Ni da ke ai babu surukuta. Ita dai Ruqayya sunkuyar da kanta kawai tayi tana dariya. Muryar Farouq suka ji daga bakin kofa. Sallama yayi ko jira a amsa baiyi ba ya ce Mummy kince zaki turo min ita kuma naji shiru. In shigo? Iya Tasallah tace shigo dan albarka. Mummy tana uhmm uhmm Iya barshi a waje taje ta same shi. Iya ta mike zancen banza kun hana yara ganin juna sai an ja musu rai. Kai karaso ga matarka nan. Ya shigo falon ya kaure da kamshin turarensa mai dadi. Ruqayya ta dan saci kallonsa yayi kyau sosai. Anyi masa aski da gyaran fuska ya fito a hausa fulaninsa. Wurin Mummy ya nufo hankali kwance saboda yaga Ruqayya sai kuma ya dan nutsu ganin  Mami har da durkusawa ya gaisheta yana sunne kai. Mummy ta bude baki ai dama iya shege ne baka jin kunyar kowa. Yau kaga suruka ka wani sauke kai kasa kamar mutumin kirki. Mami tayi murmushi rabu da ita kaji ni nan mamanka ce ba suruka ba. Mummy tace bakiga abinda yake yi bane yaron nan. Ta soma bata labari har dai ya kosa da jira ya tashi tsaye ya dan karkace kai shi a dole zaiyi maganar hankali hmmm Mummy bari muje dakin Ruqayyata mu gaisa kafin ku gama hirar ko. Mami ta dora hannu a ka ita kuwa Mummy rufe ido tayi. Iya Tasallah ta ce Allah Ya kara kun tsaya kuna batawa bawan Allah lokaci. Kaga Faruku ni bazaka burgeni ba sai sunga Ruqayya da juna biyu a gidan nan. Ya washe baki Allah ko Iya. Shi kuma junan a ina ake samun shi?   Ya koma kallon Ruqayya da ta ruga daki da gudu. Kina ganin zaiyi mata kyau? Iya ma dai ba amsa ta shige dakinta tana dogara sanda. Mummy tace kinga Fatima muje ciki muyi maganar bikin nan.

Farouq ya juya cike da mamakin dalilin tafiyarsu gabadaya. Sai kawai ya sami wuri ya zauna akan kujera. Yau kuma me na fada ba daidai ba ya tambayi kansa.
[8/2, 6:34 PM] Fatima 💖: RUQAYYA YAR ALBARKA✨41




Batul Mamman(Mrs)💖





Shirye shiryen biki ya kankama daga gidajen biyu. Soyayyar Farouq da Ruqayya kuwa kullum kara gaba take yi. Farouq ya matsa a kai masa amaryarsa ko kuma a gyara masa daki a gidan Mummy su zauna a nan. Mummy kuwa tace sam bazasu zauna mata a gida ba. A haka ma idan yayi wani abin su yake bari da kunya ina ga an kawo ta cikin gidan. Ta bakin Mummyn tace daga nesa nesa dai. Saura sati biyu a fara biki aka kawo lefe. Ko kwandala babu ta ango. Babansa ne yayi komai. A cewarsa a auren Umar Farouq ne zai dan fanshe rashin kasancewa yare da dansa. Akwati seti biyu aka kawo guda shida shida. Harda sarkar gwal guda biyu da awarwaro. Iyaye mata sai san barka. Abban Ruqayya kuwa har gida yaje ya nunawa barrister rashin jindadinsa. Suna zaune a falo yace tsakani da Allah Baban Farouq wannan abu ai ya zama bidia. Lefen nan fa don ya zama al'ada  ne idan ba haka ba tsakaninmu ai babu irin wannan. Barrister yace Engineer baka san yaya mutum yake ji ba idan ya zama uba bayan shekara talatin da shida da aure. Babu abinda bazan iya yi ba domin kyautatawa Umar Farouq. Ba wai ina sonsa bane kawai don dana ne. Idan da kana wurin lokacin da yazo karbar musulunci zaka fi fahimta ta. Abba yayi murmushi nasan haka to Allah Ya zaunar mana dasu lafiya Baban Farouq. Suka tafa suna dariya.

Ranar da zaa fara jere kuwa gidansu Ruqayya cika yayi da yan uwa. Suna shirin tafiya Mummy ta shigo tare da su Anti Nadiya. Mami tace kada kice min kema zuwa zakiyi jeren. Anti Nadiya tace wallahi nayi nayi tace ai tana da niyar zuwa jere gidan Ruqayya ko ba danta zata aura ba. Mami ta rike hannun Mummy tace su tafi Allah babu inda zaki. Duk ga yan uwa suna mana kara me zaki yi a can. Idan da gaske zaki taimaka cire mayafi mu shiga kitchen a samar musu abinda zasu ci idan sun dawo. Dole Mummy ta hakura suka tafi tana ta mita. Bayan dan lokaci Hidaya ta bugo wa Mami waya wai an kawo wani gadon da kujeru banda wandanda suka tafi dasu. Mami tace kila batan kai ne kice musu ba gidan bane. Mummy najin haka ta karbe wayar. Ke Hdaya ku nuna musu wuri su ajiye muku kayan. Na 'yata ne da na siya tun kafin ta sami mijin. Mami kawai sai ta soma hawaye. Me zan ce daku Mummyn Ruqayya da Farouq? Duk wata kyautatawa kunyi mana. Mummy tace inaaa Fatima kune kuka kyautata mana. Sanda bani da dan da zan kira nawa kin kawar da kai kin bar min taki. A dalilinta dana ya sami shiriya har ya hadu da iyayensa na asali. Iya Tasallah ta leko kitchen din to ya isa kafin ku fara min kuka. Suka yi murmushi ganin tana share hawaye.

Farouq da Ya Munir suna zaune a fadar King Edward. Ga sarkin a zaune sai Madam Hannah da Queen Amelia. Gefe kuma manyan fadawa ne da oracle priest Chera. Farouq yace nasan a yanzu duk kun san matsayina a garin nan. Ni ba danku bane, ba dan garinku bane kuma ba addininmu daya ba. Ya rike hannun Queen Amelia. Nazo ne rokarwa Mum dina ku yafe mata laifin da tayi na ha'intarku ta kawo muku dan da ba naku ba. Your highness kayi hakuri ka mayar da matarka domin bana tunanin zaka taba samun wadda zata soka kamarta. Ku ma manyan garin nan ina rokon ku wannan alfarmar. King Edward yace ka dena batawa kanka lokaci Richie. Ko kasan tana shirin karbar addininka daga ita har Priest Chera!!! Farouq da Ya Munir sai hamdala suke. Yace indai haka ne ba sai ka mayar da ita domin babu aure tsakanin mace musulma da namijin da ba musulmi ba. King Edward yace ko da kuwa namijin sunansa Abubakar? Farouq ya mike da sauri. Dad me kake nufi? Priest Chera yace yana nufin jiya mun karbi addininku our Prince. Nayi nazari sosai na gane bautar goddess da mukeyi da Jesus da wani lokacin su sarki keyi duk babu inda zai kaima. Lamarinka yana da ban mamaki dole mai hankali yayi nazari akai sosai. Queen Amelia sai murna tace your highness nima ka bani suna na musulunci. Farouq zai bude baki King Edward ko muce Abubakar yace sunanki Aisha. Dukkaninmu masu kuskure ne amma zamu gyara da yardar Allah. Richie wannan aikin na tabbatar da sabon addini a garin Ndam yana wuyanka. Sannan abu na biyu bazamu dena daukarka a matsayin danmu ba. Ka dauki kanka a matsayin mai iyaye biyu. Madam Hannah tace nima ina son addinin a sake min suna. Farouq yayi dariya Allah Yasa ba don sabon suna kike son addinin ba. Sunanki sananne a musulunci Hannatu. Dan murmushin dake fuskarta ya dauke. Nufinka bazaka canja min ba. Ya Munir yace ki zaba Hannatu ko Hanne duk yayi. Tayi dariya to nafi son Hanne din. Yafi kama da na gayu.
[8/3, 12:33 AM] Fatima 💖: RUQAYYA YAR ALBARKA✨42




Batul Mamman(Mrs)💖





Bayan dawowar Farouq da Ya Munir daga Ndam da sati daya aka fara biki. Barrister Mukhtar da Haj Maryam sunyi rawar gani sosai. Sun kashe kudi an gayyaci mutane da dama. Kamu aka fara yi Ya Munir aminin ango shine yake masa bayanin me ake yi ranar kamu a garin Kano don ma yanzu abin yazo da zamani. Abin ya burge Farouq yace yanzu bazasu jira sai munje wurin ba nima a saka min turaren? Ya Munir yayi dariya ai an dena kamun ango yanzu. Daga nan suka cigaba da shirinsu. Anyi Kamu an gama lafiya ango ya shigo da yan uwa da abokansa anyi hotuna. Ya Munir bai bari sun dade ba duk da ba haka angon yaso ba amma dole su tafi tarar bakinsu dake airport a lokacin.

Washegari dinner zaayi, Ruqayya na zaune a daki Anti Nadiya tana tsara mata kwalliya. Duk jiki yasha gyara ga kunshi mai kyau ja da baki. Wayarta tayi kara ta mika hannu zata dauka Abida ta riga ta. To tsuntsayen soyayya ai dai yayi hakuri ku hadu anjima. Jiya ina kallo kamar ya cinyeki. Ta kalli katon cikinta ni wallahi kun cuceni. Da kun jira sai na haihu hancin nan ya koma sai ayi bikin. Anti Nadiya tace tabdi ashe da zaku wayi gari ku nemeta ku rasa. Kinsan yadda Farouq yake son yarinyar nan kuwa? Allah Ya baku zaman lafiya. Yan matan dakin suka ce amin. Farin lace ta saka rigar anyi mata dinkin buba. Sai gwaggaro da mayafinsa harda sarkar da dankunne, takalmi da jaka duk lemon green. Kayan sunyi mata kyau sosai. Amarya duk yadda take kara kyau take da bikinta. Tana fitowa sai Masha Allah ake cewa. Motoci suka fara daukar mutane Ya Munir ya shigo yace a fito da amarya. Hidaya ta tsokani Abida. kaga Munir abar matarka a gida kada ta bata taro da ciki. Wata yar uwarsu tace dadin abin kema da naki kike tsokanarta. Ya Munir yace rabu da ita ma. Ke ba don cikin nan ba ai da masu bikin basu hadu ba. Dan albarka ake fada miki. Yaro mai hada soyayya. Daga nan suka fito aka kai Ruqayya wata mota a tsakiya.

Farouq ne kadai a zaune a mazaunin dreba. Ruqayya na zama ya riko hannunta yana murmushi. My love kamar daga nan mu tafi gidanmu kawai kinyi kyau sosai. Ta sunkuyar da kai shima farar shadda yasa rigar tasha aiki amma ba mai yawa ba. Shima lemon green ne a jikin aikin da hularsa. Tace kaima kayi kyau mijin Ruqayya. Ya kwantar da kai a jikin sitiyari....ki min izini mu fasa zuwa dinner dinnan. Ta girgiza kai me zamu cewa su Mummy? Mun tafi honeymoon mana. Nayi aure wata guda amma ko dan....tace yi hakuri zaka fara ko. Yayi dariya ai ban fara ba My love sai kin dawo gidan Umar Farouq. Daga nan suka wuce wurin dinner da ya kawatu sosai. Su Mummy sunyi mamakin ganin Queen Aisha da Mama Hanne sun halarci taron. Anyi hotuna da yawa tare da ango da amarya. Anci an sha an tashi taro lafiya. Washegari akayi yini da yake gidan a unguwar ne sai da aka idar da isha karfe takwas aka tashi kai amarya. Nan fa Ruqayya ta rinka kuka sosai. Tana yi Mami na tayata. Hidaya tace Mami wannan kukan har yafi namu gashi ita ba nisa zata yi ba. Mami tace banyi zaton aurenta zaizo nan kusa ba. Ki rike Allah da ManzonSa Ruqayya shine kawai nasihar da zan miki. Iya Tasallah ma tayi nata kukan aka wuce da Ruqayya yar albarka gidan mijinta.

Kowa ya watse sai kawayenta biyu aka bari. Farouq da su Ya Munir suka rako shi har su hudu ya na ta mamakin  ganin sun biyoshi har cikin gidan. A falo suka tarar da su Ruqayya. Farouq ya kalli kawayenta da su Ya Munir ya dan bata rai. Munir kana nufin wannan ma al'adar hausawa ce a wurin aure? Cousin din Farouq mai suna Aliyu yace kwarai kuwa. Shi ake kira siyan baki. Farouq yace siyan me? Wallahi bazan sayar muku ba. Ni duk a al'adun ma wannan batayi min ba. Nasan ko a addini ba ta sami karbuwa ba. Ku biyoni har cikin falo kuma zaku sayi bakin matata. To ni me zaku bar min? Suna masa dariya Ya Munir yace kaga kwantar da hankalinka addua zamuyi muku mu fita. Farouq yace ai kune baku yi bayani yadda zan gane ba. Ana shafa addua ya matsa kusa da Ruqayya yace my love yau ban manta kazar ba. Akwai wani abin ko shikenan? Ji tayi kamar ta nutse a kasa. Ya Munir kuwa  yace da kawayenta kai ku tashi suma abokan ya tattara su suka fice suna dariya. Suna fita ya rufe kofar ya dawo kusa da ita. Mayafin ya cire ya jefa a saman kujera. Ya kare mata kallo kinci sunanki Ruqayya yar albarka.

Zama suke cike da soyayya da kyautatawa juna. Malamai har biyu aka tura garin Ndam kuma anyi saa mutane da yawa suna ta karbar addini. Tsakanin Farouq daviyayensa kuwa shagwaba yake zuba musu son rai. Itama Ruqayan yi mata yake yi. Watanta biyar cikinta shima wataninsa kenan. Wata rana ya dawo daga karatu ya sameta ta kwaye ciki wai yana mata kaikayi. Mummy ya kira a waya. Tana amsawa yace Mummy cikin Ruqayyata yana mata kaikayi sosa mata zan rinka yi ko akwai magani? Mummy tayi murmushi don yanzu ta saba da maganarsa sai dai yayi aji kunya. Tace kada ta sosa anjima kazo ka karbi zaitun ta rinka shafawa. Yace haba Mummy ta shafa da kanta taji wahala.  ai  kwanciya za tayi na shafa....Ruqayya ta karbe wayar ta kwala masa a ka. Ya sosa wurin yanzu kuma me nace ba daidai ba. Ta ja masa hanci Mummyn kake cewa zan kwanta ka shafa min ciki? Ya ce to zan mata karya ne? Ruqayya tace a'a dan rufawa zaka yi saboda kunya. aikinki kenan kunya kunya ga katon ciki kuma a gabanki duk kunyar taki. Murmushi kawai tayi ina sonka Umar Farouq. Ya rungumeta nima ina sonki Ruqayyan Farouq.

Bayan wata hudu Ruqayya ta haifo yan biyu mace da namiji. Murna wurin iyayensu baa cewa komai. Hatta King Abubakar da Queen Aisha sunzo ganin jikokinsu. Farouq ya dage Ruqayya bazata gida wanka ba dole Mummy tasa aka gyara musu dakinsa ta koma nan saboda a kula da ita. Ranar suna ya sawa yaran sunan iyayensa bisa shawarar da yayi da Abba. Aka sami Mukhtar(Annur) da Maryam (Noorie). Farouq an zama baba ya na kula da iyalinsa da karatunsa sosai. Gashi ya sami aiki a wani company. Haka rayuwarsu ta cigaba da kasancewa cikin ALBARKA.


ALHAMDULILLAH
Godiya ta tabbata ga Allah SWT da Ya bani ikon rubuta littafin nan. Allah Yasa a amfana da sakon da yake ciki. Yayi mana ALBARKA baki daya.

Sadaukarwa
Ga yar uwata Ruqayya. Allah Ya jikanta Ya gafarta mata da sauran musulmi baki daya. Allah Ya raya mana(abinda ta bari) baby Ruqayya Yayi mata albarka Ya bamu ikon kulawa da ita. Ya Allah Kayi mana albarka da 'ya'yanmu da iyayenmu da sauran musulmi. Amin

Fatan alkhairi gareki a duk inda kike MARYAM NOOR baturiyar da ta karbi musulunci tana da shekaru sittin a duniya. Labarinta ne ya taba min zuciya har nayi wannan dan labarin.

Nagode muku dukkan masoya Ruqayya yar albarka. Allah Ya bar zumunci Ya bamu rayuwa mai albarka[truncated by WhatsApp]

adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *