Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Friday, July 24, 2020

MAFARKIN ABDOUL COMPLETE HAUSA NOVEL

adsense here
MAFARKIN ABDOUL COMPLETE HAUSA NOVEL

COPY N COMPILED BY
ESHAAT SMILER 
HOME OF HAUSA NOVLS DOCUMNTS
WASAPP 08066360176 FOR MORE


Mafarkin Abdoul
[31/08 12:19] Ummu Abdoul🖋: MAFARKIN
ABDOUL
Alkalamin Safiyyah Ummu Abdoul
WANNAN NA KU NE
Labarin nan kirkirrarre ne don kaunarku gare ni,
na sadaukar da labarinnan ga Ɗaukacin
masoyana da ke 'Kasar Nijar. Ubangiji Allah ya
Haskaka rayuwarku ya barmu tare
2010

Zaune take gaban fannin kimiyya (Faculté des
Sciences) ta jami'ar Abdoul moumouni
(Université Abdoul Moumouni Dioffo) da ke
Niamey a jamhoriyar Nijar. Sun fito lectures
kenan kasancewarsa ɗaliba yar aji uku a fannin
tsirrai (plant biology),
Yarinya ce 'yar kimanin shekaru ashirin a
duniya, tana da matsakaici tsawo, Albarkan
mazaunen da ke gareta da kumatunta yasa
akan mata kallon mai jiki kasancewar ta ma'
aboki yar sa hijab. Kalarta mai tsada ne, baka
ce ba wuluk ba ma'abociyar fararen idanu kalar
madara.
Wasu na mata kallon mai girman kai yayin da
dayawa kan so ta saboda hakurin ta da
yalwataccen fara'an da ake samu a fuskanta.
A zahirance kallon wayarta takeyi fuskarta ba
yabo ba fallasa, amma tunaninta ya tafi chan
wani duniyar. Ko a aji yau ba zata ce ga abinda
akayi musu ba.
Kiran da ya shigo wayarta yasa ta sakin ajiyar
zuciyar da ya sa kawarta da ke zaune gefenta
kallonta.
"Sweetyna kana lafiya, duk hankalina ya gaza
kwanciya, ina ka shige" Ta faɗi a marairaice
kamar zatayi kuka.
"barci na tashi ya kike ya makaranta?"
"Alhamdulillah, ka ci abinci" Ta sake
tambaya cikin yanayin kula
"Bana jin cin abincin ne, ga de ni nan Haj na
min favorite ɗina" Ya faɗi yana dariya. Itama
dariyan tayi.
Haka suka cigaba da hira cike shaukin juna.
Har wajen mintuna ashirin sannan suka rabu cike
da kewan juna.
"Halima fisabillillahi bazakiyi ma kanki faɗa
ba, wallahi Hammad ba aurenki zeyi ba. Ki
natsu ki roki Allah ya baki nagari, kada so ya
rufe miki ido" faɗin kawarta da ke zaune a
gefenta.
"Faɗima wallahi muna son juna da Hammad,
kun kasa fahimtarmu ne, kuyi mana fatan
alkhairi kawai"
"ina guje miki halin mazan zamanin nan ne,
basu da alkawari musamman in son da mace ke
musu ya zarce misali, duk abin sa kar ki yarda
ayi gwajin takalmi da ke" Faɗima ta ce cikin
halin ko in kula.
"in ma gwajin riga zai yi ba komai bane mu dai
muna son junanmu kuma za muyi aure" Ta faɗi
a kufule duk ranta ya ɓaci. Fuuuu ta tashi
kamar mai shirin tashi sama.
[01/09 08:48] Ummu Abdoul🖋: MAFARKIN
ABDOUL
©Safiyyah Ummu Abdoul
Da kyar ta iya isa gidan baffanta da take zama
wanda ke bayan Homeland Hotel, da ke
Off Ave du General de
Gaulle, a wahalance ta yi sallama, ta iske matar
baffanta haj Mas'uda a zaune tana kallon tashar
Sunna TV.
"Momma barka da gida" Ta faɗi tana mai
samun wajen zama a kusa da kafanta. Kallo
ɗaya tayi ma ta ta fahimci bata cikin natsuwa.
"Halimatus sa'adiya taje makah da madina ta
sha miya mai daɗi har da kadangare soyayye"
Ta shiga rera mata tana tafi. Dariya Halima ta
farayi yayinda ranta ya fara sanyi.
"faɗa min waya taɓa ki" Ta tambayeta tana
mai tsareta da idanu.
"Faɗima ce na rasa mai na tsare mata,
tsakani da Allah nake zaune da ita amma sai ta
yi ta min bakin ciki da hassada" Ta faɗa ido
cike da kwalla, zuciyar ta na mai jin an ci
amanar kauna.
"tohhhh fa, me ta yi miki, kwata kwata ba
tayi kalan mai wannan halin ba" Ta amsa mata
fuska cike da alhini.
"Momma a 'yan kwanakin nan sai tayi ta ce
min in rabu da Hammad ba aure na zaiyi ba, ki
duba fa ko haushin yafi mijinta kyau da kuɗi
take yi ko mai yasa ni ban sani ba" Ta karasa
tana kukan da yafi jini ciwo don a duniya bata da
kawar da take kauna sama da Faɗima duk da
kasancewarta kanwa a wajen kishiyar uwarta.
"Na rasa me ke damun mutanen zamanin
nan. Sam bama son gyara, da ga an nuna
mana kuskurenmu maimakon mu gyara sai mu
ce ana mana bakin ciki ko hassada.
Mai sonka ke gyara maka, nasan son da
Faɗima ke miki ba za ta bari ki cutu ba.
Hammad dai iyayen ki ba sonsa suke ba,
asali ma cewa su ka yi ki rabu da shi, ina mai
shawartanki da ki roki zaɓi Allah in Hammad ne
alkhairi Allah ya tabbatar in ko ba shi bane
Allah ya kawo wanda ya fi shi a komai"
"Momma ko ba Alkhairi bane Allah ya sa mu
mallaki juna, ina sonsa da yawa Momma" Ta
katse ta gudun yan aameen su amsa ma
addu'ar ta,.
"Halima ko dai Hammad ya sanki a ɗiya mace
ne, in ba haka ba wannan irin nacin son da kike
masa ya zarce hankali, dama mamanki ta faɗi
na karyata gashi kina neman gaskata
maganarsu". Ba ta jira amsarta ta ba barta
zaune tana gunjin kuka.
Kiran sallar la'asar da akayi ne ya tashe ta
daga barcin wahalan da ya kwashe ta a wajen.
Tashi tayi ta sallace la'asar da azahar ɗin da
ake bin ta bashi.
Tare da Momma da babbar yar momma Amina
da suke kira Amna suka kammala girkin dare.
Suka shirya, karfe shida duk suka haɗu gaba
ɗaya suka ci abincin, don ka'ida ne a gidan cin
abincin dare karfe shida don ya zazzage kafin ayi
barci, sannan abincin safe baya wuce karfe
takwas ɗin safe duk don samun ingantacciyar
lafiya.
Bayan kammala sallah isha'i ta koma ɗaki da
nufin barci. Shafin Facebook ta shiga don duba
abubuwan da ke kai, har zata sauka sai sakon
gayyata ya shigo ta buɗe sai taga "ABDOULLAH
ABOUBAKAR (ABDOUL ABOU)" Sai da ta duba
shafinsa ganin bai bada wasu bayanansa masu
mahimmanci ba iyaka dai taga shima ɗan Zindar
ne. Har zata goge sai ta tuna da tobashinta
Abdoul Abou sai tayi tunanin Shine. Tsaki ta ja
kafin ta amince. Haka ta cigaba da shige
shigenta tana hira da kawarta da suka haɗu a
Facebook ɗin Tiddar Azzoubir.
Da ta gama ta kalli agogo ganin goma saura
na dare ta sa ma ranta tabbas Hammad ya
gama kallon kwallo. Waya ta ɗauka ta kira shi
sai da ya kusan tsinkewa sannan ya ɗaga.
Yanayin yanda ya amsa mata yasa ta
tambayeshi ko ya fara barci ne
"ke dai bari hajiyata, wallahi na ɗanyi aron
hannu ne kinsan gajiya yake sawa" Ya faɗi cikin
halin ko in kula
Bakin ciki ya cikata amma haka nan ta ɗaure ba
tare da nuna ta damu ba tace
"sweetyna yaushe zaka daina zuwa rage
ruwan nan ne, lokaci yayi da ya kamata mu san
mai muke ciki"
"anya in munyi auren nan baza'a samu
matsala ba, kishin ki na neman kaiki ga zargi
na, gaskiya da sake toh" Ya katse ta a fusace.
Nan take ta fara bashi hakuri da kalaman
soyayya da tasan yafi so. Haka suka shirya
suka cigaba da soyayya har sha ɗaya da rabi
sannan sukayi sallama suna masu begen
junansu .
[02/09 17:05] Ummu Abdoul🖋: MAFARKIN
ABDOUL
©Safiyyah Ummu Abdoul
٣
Juyi ta ke yi hannunta rungume da filo Mafarki
take amma na ido biyu (day dreaming) ga ta da
Hammad ɗin ta sunyi aure. Auno su take irin
soyayyar da zasu kwasa, kamar an mintsile ta
tashi tayi ta lalubo kananan kayan da ta siya
don kaiwa gidan aurenta. Murmushi ta saki gani
take an ɗaura aurensu da Hammad an gama.
"Toh in ya cigaba da Aron hannu fa?" wannan
sashi na zuciyar mutum da ba'a taɓa yaudara ya
tunatar da ita, bata ɓata lokaci ba tayi fatali
dashi kana ta faɗin "ai na san zai daina da
munyi aure".
Kwanciya tayi don tayi barci amma ko gezau
barcin ya gagare ta, sai ma tunani da ke neman
kar da ita, bata bari ya hargitsa ta ba ta dauki
wayarta ta hau Facebook
"Assalamu Alaikum yan mata" Ta iske na
Abdoullah Aboubakar, ita sam ta manta wani
Abdoul.
Amsa sallamar tayi , ashe yana kusa nan yayi
ta janta da hira, tun tana sharewa har ta fara
bashi amsa.
***
TUSHEN SU
Alhaji mousa uomarou ɗan asalin garin Zindar
ne, duk da tarihi ya nuna fatauci ya kawo
kakanninsa Kasar Nijar daga Kano, har
auratayya da chakuɗeɗeniya ya sa sun zama
yan kasa.
Yara biyu Allah ya mallaka masa wato Idrisa
da Abbas. Gidansa sannan nan gida ne da a
unguwar yadakwandage kasancewar yafi sauran
rufin asiri. Yayi kokari wajen ganin yaransa sun
samu yalwataccen ilimin zamani, haka ma na
addini.
A rana ɗaya sukayi aure inda Idrissa ya auri
Mas'ouda balarabiyar Kasar Aljeriya amma
mazauna Kasar Nijar shi kuma Abbass ya auri
yar gwoggonsu khadija.
Wata goma sha ɗaya bayan aurensu khadija ta
haifi yar ta mace wacce aka sa ma suna
Halima. Mas'ouda kuma sai bayan shekaru
haɗu Allah ya buɗe mata kofar haihuwa. Lokacin
Idrissa ya sami aiki a fannin kuɗi da tattalin
arzikin yammaci Afirka wato Union Économique
et Monétaire Ouest Africaine
(UEMOA). Don har sun koma garin Niamey da
zama.
Halima ta taso cikin gata da kula, sannan ta
sami ingantaccen ilimi tun daga na addini har
zuwa na zamani. Rashin haihuwar mahaifiyarta
tun bayan haihuwanta yasa Abbass kara aure,
inda ya auro Sauda.
Tun da ya auri Sauda kuma haihuwa ta sake
buɗe wa a gidan. Sai ya zama kamar ana gasar
haihuwa ne a gidan tsakanin khadija da Sauda.
Bayan Halima ta kammala sakandarenta a
LYCÉE AMADU KURAN DAGA (LAKD) ta samu
gurbi karatu a université Abdoul Moumouni
Dioffo, dalilin haka ta koma gidan baffanta
Iddrissa.
A shekaran Halima ta haɗu da Hammad wata
rana ta dawo daga registration dai dai kwanar da
ya raba su da homeland hotel shi kuma ya fito
daga otel ɗin. Hammad Touareg(Buzu) ne ɗan
asalin Agadez ne. Fari ne kyakkyawa kamar shi
ya kera kansa. Ba shi da hayaniya don magana
wahala take bashi
Yana da son kyale kyalen duniya amma mace
da kuɗi sune kan gaba. Bai sha wuya wajen
zulmiyar da Halima zuwa ga sonshi ba amma
bai taɓa yunkurin taɓa ta ba yanda bai yi
yunkurin zuwa neman aurenta wajen iyayenta
ba.
A dalilin haka iyayenta suka raba ta da shi
amma fir ta ki don a tunaninta bata fara sonsa
don ta daina ba haka kuma a shirye take da ta
jira shi duk lokacin da ya shirya suyi auren.


Mafarkin Abdoul 2nd post
MAFARKIN ABDOUL
© Safiyyah Ummu Abdoul
BAN HAKURI
Ina mai baku hakuri rashin ji na da kukayi kwana
biyu. Ina fama da rashin lafiyan ido shi yasa.
Thnx for ur luv
Keep reading, voting and commenting...
Ummu Abdoul luvs u wujiga wujiga😘😘😘😍
٤
Babu abinda ya fi faranta ran Halima kamar ta
zauna tana MAFARKIN ido biyu.
Zaune take da Hammad suna ciyar da
junansu abinci a baki, suna yi suna jifan juna da
kallo mai cike da kauna.
Yaransu suka shigo suna kwala mata kira cike
da murnan dawowasu....
Ire-iren mafarkan nan Halima keyi sai ta ji duk
duniya babu macen da ta kai ta dacewa da
samun masoyi. A haka har ta kai aji uku ana
saura mata shekara ɗaya ta kammala karatunta
hakan ya tada hankalin iyayenta don sun so ta
kasance a ɗakinta a wannan shekaran
kasancewar ta cika shekaru ashirin a duniya.
Nan dai Halima ta kekashe ta ce ita bata da
masoyi sai Hammad....
WANNAN KENAN
***
Washegari kamar kullum ta Shirya ta isa
makaranta, faɗi ma bata ga wani fara'anta ba,
ba yabo ba fallasa suka kasance tare har aka
tashi. A hanyar ta na komawa gida ta shiga
Faba-faba (wata yar bus da ake motar haya
dashi a Nijar) nan ta iske wasu yan mata biyu a
ciki.
"Kin san Allah Faɗima, ko da tonton oumar ya
ce an tsaida ranar auren mu da Hammad ban
yarda ba, tsoro na kar in ya ce ya fasa" faɗin
ɗaya daga cikinsu. Wacce da gani ta fi rawan
kai.
"ke ma kinsan yana sonki kawai don ya fiye
ka'idoji ne amma kawai ki kiyaye shike nan.
Allahu ya nuna mana" faɗin wacce aka kira da
faɗima.
Hankalin Halima ya kasu kashi kashi sai take ji
kamar Hammad ɗin ta ne, wani zuciyar na faɗi
mata ai Hammad ba ɗaya bane a duniya.
Bata san sanda bakinta ya fara furta
"kar dai a ce ke ce amaryan grand frère (yaya
namiji)". Nan duk suka juyo suna kallonta.
Murmushi ta sakar musu sai ta ɗauko littafin da
ahlin ɗinsu Hammad sukayi wai barka da sallah
ta ce
"ko ba wannan bane angon naki grande
soeur (yaya mace)" Nan ma fuskarta cike yake
da murmushi yayin da ranta ke rokon Allah kar
ya kasance Hammad ɗin ta.
"kinga irinta ko Sadiya, da rashin mutunci
mukayi da kin kwan ciki, yi hakuri kanwarmu .
Ya gida ya su mama"
"Lafiya lau, gashi har na zo in da zan sauka,
zan faɗa masa mun haɗu da pretty damsel
ɗinsa" Ta faɗi tana dariyan da yafi kuka ciwo.
Tana sauka ta hau kabu-kabu wanda shi ya
karasa da ita gida. Jinta take kamar
mahaukaciya, haukan ma sabon shiga.
Ko da ta isa ɗaki ta shiga Direct, sai da ta
tuɓe ya rage daga ita sai breziya da siket
sannan ta kira shi a waya.
"Akan me zaki je kina min bincike Halima, ko
an ce miki sadiya bata san duk yan gidanmu
bane" Ya tare ta da shi kafin ya amsa
gaisuwanta.
"Ai ban san cewa gidanku ɗaya ba sai yanzu.
Yanzu Hammad sakayar da zaka min ke nan"
Ta faɗi a raunane, idanunta na fitar da kwalla.
Zuciyarta kamar ta fitar dashi saboda azaba
kunan da yake mata.
"ki fahimce ni Halima, ban taɓa miki
Alkawarin zan aure ki ba, ina sonki mais (but)
kin san hali na, hakan yasa kike zargi na kuma
kike bincike na, bafa muyi aure ba kenan. Kuma
kinga sadiya shekarunta goma sha shida ne
kawai, zan iya zama in tsara ta yanda nake so"
Ya karasa yana dariya.
Halima da jikinta ke karkarwa burinta ta tashi
daga muguwar MAFARKIN da take tayi kokarin
faɗin
"Amma Hammad.... " bata kai aya ba ya katse
ta da ban hakuri.
" Don Allah Halima kiyi min rai s'il vous plaît
(please) kada wannan ya taɓa soyayyar mu kinji
Don Allah " bata karasa jinsa ba tayi hurgi da
wayar ta kara rushewa da kuka wanda ya fi jini
ciwo.


Mafarkin Abdoul 3rd
MAFARKIN ABDOUL
©Safiyyah Ummu Abdoul
0
Tsabagen kukan da tayi ya haifar mata da
matsanancin ciwon kai. Tun da ta shige ɗaki ba
ta fito ba sai faɗi ma mommansu zazzaɓi take
yi.
Washe gari ma haka ta yini sukuku, mamaki
ya cika ta rashin ganin kiran Hammad, zuciyar
ta guda na ingiza ta kan cewa ta kira taji ko
lafiya yayin da ɓangaren zuciyarta mafi gaskiya
na faɗi mata ta kyale shi.
Waya ta ɗauka ta kira Abdoul saboda amincin
da ke tsakanin su yasa basa kyashin faɗi ma
junansu sirrin rayuwarsu.
Saurarenta yayi cikin natsuwa da fahimta.
Sannan ya ce
"ki ɗaure ki fitar da shi a ranki tun a yau, kar
ki saurare shi, zafin da zaki ji kaɗan ne akan sai
gaba ki sami ɓacin ran da yafi wannan. Ina
office yanzu za muyi magana in na koma gida"
Ta gode masa kana ta ɗan yunkura don cire
damuwa a ranta.
Haj. Mas'ouda na ankare da duk wani take
takenta amma ta basar. Cikin lokaci kankani ta
zabge ta rame, fara'anta ya zama ragagge ga
yawan tunani. A lallaɓe ta kammala jarabawan
zangonnan ta tafi Zindar.
Abdoul kaɗai yasan matsalarta hakan ya sa
shakuwa fiye da farkon haɗuwansu. Bakin
cikinsa ɗaya sanda suka haɗu tana tare da
Hammad da babu abinda zai hana masa
aurenta. Ga shi saura wata bakwai a ɗaura
aurensu da Agaysha.
Kaifin basiranta da hankalinta yasa yake saka
ta kan gaba a dukkan lamuransa don duk
shawarar da zata bashi matukar zai yi amfani
da ita toh akwai nasara.
***
Tana Zindar aka ɗaura auren Abdoul da
Agaysha. Duk wani shiri na biki akan shawaran
Halima akayi. Halartan bikin ne kawai batayi ba
amma ko a ranar sunyi waya yafi sau goma,
yana lallaɓata da ban hakuri akan matsalarta da
Hammad.
Amarya Agaysha ta tare a gidanta da ke
Jeune cadre wanda ya sha gyara kasancewarta
yar gidan masu kuɗi..
Agaysha Iggalher fara ce mai jiki, tana da
tsawo bata da wani diri amma baza'a kira ta a
chushe ba, yar asalin agadez ce buzuwa ce,
amma ta taso a Dosso, iyayenta masu kuɗi ne
kuma yan boko. Sun haɗu da Abdoul ta hannun
yayanta sidi inda da farko ta ki amincewa da
shi kasancewarsa talaka, amma tunda ya samu
aiki ta makale masa.
Aurensa bai sa shakuwarsu ta ragu ba sai ma
a ce ta karu don duk wanda yake tare da ita ya
san alakarta da Abdoul, wanda bai san danginsu
ba takan ce masa yayanta ne, walau uwa ɗaya
ko tubashinta. Tayi samari kala kala amma ba
wanda ta yi soyayyar wata uku da shi ba gani
take duk mayaudara ne.
"Na rasa me ke damun matan adarawa
(hausawa) da buzaye sam basu san wani abu
kula da miji ba, duk soyayyar da za'a maka
kafin ayi aure ne sama they are not caring😡"
Abdoul Ya turo ma Halima ta bbm ɗin da suka
maida hanyar hiran su, hakan yasa suka rage
2go.
Ɗan Aljani dariya haɗe da ɗaga hannun ba
ruwa na ta tura masa
"Allah ba wasa ba, kin san aboki na bayarben
nan da wannan inyamurin wallahi har ban son
zuwa gidansu, kinga dai ba Kasar su suke ba
amma matan basu yi kyashin kula da su ba" Ya
sake tura mata, bata so ta shiga harkan
iyalinsa, don bata so ayi mata. Amma ta dake
ta amsa da
"Allah GF (grand frere) matanmu na kokari
wajen kula sai dai abinda ba'a rasa ba, aure
ɗan hakuri ne" Ta tura haɗe da aljani mai
murmushi
"Ni wallahi har danasanin aure yanzu nake,
kai aure dama haka yake, mace bazata natsu ta
kula da kai ba wai kar ka raina ta, na yaushe
kuma. Shi yasa mazan Hausawa da buzaye
suka gwanance a Aron hannu "
Sai da tayi dariya ma'ishi kasancewa ta san
ya tsani kalmar nan ta aron hannu da gayu ke
amfani dashi mai makon zina.
"dariya ta kike wai, kin san dai a nahiyar mu
anan ba Kasashen fa suke da Al'ada iri ɗaya
kamar Nijar da arewacin Nijeriya. Toh kina isa
arewacin Nijeriya zaki ga korafin iri ɗaya ne,
matan banda rashin kula har da da rashin
biyayya suna tunanin gyaran gado ne kawai
aure, mstwww " Nan ma dai dariyar ta sake bin
shi da shi, tana mamakin sa. Toh ai ba duka
aka taru aka zama ɗaya ba. Don kuwa yanda ta
tsara rayuwar Aurenta bata tsammanin za'a
samu matsala da ita a wannan fannin. Burinta
kullum rayuwar aurenta ya zama sanadin shigar
ta Aljanna mai babban daraja.
Ganin ba ta niyyar bashi haɗin kai balle har
ya c faɗa mata matsalarta yasa ya juye hiran
zuwa tambayar ta ya zancen karatunta da take
shirin kammalawa. Karfe goma na dare yai
mata sallama ta sa masa tsiya faɗi take
"wajen buzuwa fa zaka kake sallama, ashe suna
da rana haka" dariya sukai gaba ɗaya sannan
sukai sallama.
MAFARKIN ABDOUL
©Safiyyah Ummu Abdoul
٦ .
MAFARIN MAFARKIN
2012
Zaune take tana kintsa kayanta saboda zata
kai ma Haj Mas'ouda ziyara kasancewar ta
kammala karatunta na licence na shekaru 3,
(kwatankwacin kwalin degree inji yan 9ja)
sakamako fito yayi kyau. Wannan zuwan ma
baffanta ya sa ta nemi gurbin karatun masters a
cewarsa tunda taki aure.
Wayarta ce ta fara kuka, kallon number ta yi
don ko mutuwa take bazata manta numb nan
ba. Kamar bazata ɗaga ba chan dai yana gab
da tsinkewa ta ɗaga haɗe da sallama.
"meye duniyar ne Halima, ace zaki iya share
ni haka. Shekara biyu kenan fa, haba Halima
alkawari bai ce haka ba" Ya faɗi yana mai
kwantar da murya.
" qui est sur la ligne (wanene akan layi) ta
faɗi a ɗan fusace duk da ta fahimci muryan.
Dariya yayi mai isarsa sannan yace " mon
nom est Hammad de agadez (sunana Hammad
daga agadez)" Ya faɗi yana dariya.
"Au wai kai ne, ni ban gane muryan ba." Nan
suka gaisa.
"ina takwarata" Ta tambaya
"hmmmn hajiyata kinsan mun rabu kuwa"
Ya faɗi cikin halin ko in kula.
"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun! Me yayi zafi
haka Master" Ta faɗi tana mai dafe kirji kamar
yana ganinta
"Wallahi bazan iya ba, idanunta sun buɗe da
yawa, duk wani hanyar rage ruwa ta san shi,
wai yarinyar nan ce ke faɗa min don bana
laguda ta toh tana shakkar son da nake ikrarin
ina mata"
"haba Hammad, yarinya ce fa karama, hakuri
zakayi, amma dai da aka tsaida rana sannan
zaka ce ka fasa, ka yi hakuri"
"yarinya ce karama amma ko ke da kika gama
jami'a ba za ki yi abubuwan da take ba, har
ɗaga wuya fa ance tana yi."
" Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, ni ko ta ɓata
wayonta kuma ta kunyata ku, Allah raba mu da
zaɓen tumun dare." Ta faɗi tana mai kashe
wayar.
Cigaba da shirya kayanta tayi sannan ta ɗauki
hanyar Niamey
Sai chan cikin dare sannan ta labarta ma Abdoul
duk inda hankalinsa ya kai a yawa duk sun
tashi. Ya rasa meyasa lamuran Halima ke
tsayar masa a rai, ko dan tana mutunta shi ne
ko menene shi kan shi ya rasa ganewa.
Tun daga ranar Halima da Hammad suka fi
tif da taya mannewa kafin a ankara shakuwarsu
tafi na da.
***
Ziyara suka kai birnin Paris na Kasar Faransa.
Sun sauka a ɗaya daga cikin otel da suka fi
tsada watau RITZ Paris da ke lamba ta 15
Place Vendôme, 75001 Paris.
Sunyi wanka, sun rama sallolinsu sannan
suka zauna cin abinci. Daga nan kuma suka
Lula duniyar da su kaɗai suka san da shi don
kawar da gajiya.
Basu kai ga isarwa ba yaji saukan ruwa a
fuskarsa. A firgice ya farka yana lalube ko
idanunsa zai kai ga Halima amma ina sai ta kai
ga Agaysha tana huce kamar mai shirin dambe.
"Zina kake min a kan gadonmu na sunna"
Ta faɗi hawaye na kwarara daga idanunta.
"Zina kuma Agaysha" Ya faɗi a ruɗe, ko dai
abinda ya ke tunanin a mafarki ne a gaske abin
ya faru, amsar da ta bada ya dawo da shi daga
tunani.
"Ya zaka kwanta kana numfarfashi a cikin
barci, Allah ya isa tsakanina da Aljannar da ke
shiga gona ta. Don taga bana ganin ta, kai
kuma sai jin daɗi kake" Ta karasa tana gunjin
kuka.
Rungumo ta yayi yana tura mata sakonni
masu wuyan fassarawa, "mafarki nayi kina
shayar dani zumanki nefa ma femme (matata)"
da haka ya rufe bakinta. Bata sake ɗaga zancen
ba yayin da shi kuma ya gagara cire shi a
ransa.
Ina muku barka da sallah.
ﺗﻘﺒﻞ ﺍﻟﻠﻪ ﻣﻨﺎ ﻭﻣﻨﻜﻢ ﺻﺎﻟﺢ ﺍﻷﻋﻤﺎﻝ


Mafarkin Abdoul 4th
MAFARKIN ABDOUL
©Safiyyah Ummu Abdoul
٧ .
Zaune take tana kwalliya, murna ne fal a cikinta
don grand frère ɗinta Abdoul zai kawo mata
ziyara. Sanye take da riga da skirt na material
mai kaloli, ɗinkin ya fito da surarta ya bayyana
asirtaccen kyawun da Allah ya mata.
Feshe jikinta tayi da turaruka fin kala biyar,
duk da kasancewarsu masu saukin kuɗi sun
fitar da kamshi mai daɗi da kwantar da hankali.
Karfe biyu ya iso, kiranta yayi a waya cewan
ya iso, yayin da ita kuma ta zura hijabinta
purple kasancewar shine kala mafi karanci a
kayan.
Falon su tayi masa iso, wanda ke fitar da
sassanyar kamshin freshener irin na Larabawa.
Lumshe ido yayi sanda ya sa ka fara guda a
cikin falon. Kamshin da ya daki hancinsa ya sa
masa nishaɗi, se da ta kawo masa abin tarba
sannan ta samu waje ta zauna.
"yan mata" Ya faɗi fuskarsa yalwace da
murmushi.
"yayan yan mata" Ta faɗi tana maida masa
da murmushi.
Tsare ta yayi da ido yana neman abinda zai
bambamta ta da halimar da ke zuwa masa a
mafarki, mafarkinsa na jiya ya dawo masa inda
yayi Wai Halima ta haihu an samu Abubakar
suna ce masa saadik . Hure masa fuska tayi.
Nan da nan yayi farka daga duniyar tunanin da
ya shiga.
"lafiya grand frère" Ta faɗi cikin yanayin
damuwa.
"Babu komi je pense à ton avenir (ina
tunanin future ɗinki ne) " Ya faɗi yana
murmushi wanda kallo ɗaya zaka masa kasan
iyakarsa fatan baki ne.
"wani abun ya faru ne?" Ta faɗa a ɗan
firgice, kallonsa take cikin kwayar idonsa ko
zata fahimci wani abun. Ganin bata fahimci
komi ba yasa ta saukar da idonta.
"abinda da Hammad ya miki mana, aka ce
miki baya damuna ne. Addu'a ta kullum Allah
baki miji na gari, shekaru ashirin da biyu ai ba a
ce da ke yarinya ba" Ya faɗi ya na basar da
damuwar da ta shiga kamar bai san tayi ba.
"Au da ma Shine, ai mun shirya kasan na
faɗa maka wancan yarinyar bacin biyan maza da
take har da ɗaga wuya tana taɓa wa, wai
karamar yarinyar da aka rabu da ni yar jami'a
saboda ita kenan" Ta faɗi tana dariya kasa
kasa.
"don ta sha giya Shine me? Ba hakan ya
ganta ya ce yana so ba, in ita giya tasha ke
anya beyi gwajin takalmi da ke ba, wani irin
zuciya gare ki, kina tunanin zai chanza
ra'ayinsa ya aureki ne bayan tun farko ya nuna
miki shi ba mijin aure bane, haba Halima da
hankalinki da komi kina bari so na sarrafa miki
rayuwa, oh ku ne masu bin na turawa da suke
cewa 'everything is fair in love and war' Ko? Toh
ki sa ma ranki cewa rien est juste dans l'amour
et la guerre (nothing is fair in love and war)" Ya
faɗi a fusace, tabbas ta san gaskiya ya faɗi
amma ya zatayi da son Hammad. Kuka take
mai hana sukuni ido ya sa mata duk da yana jin
kukan har kahon zuciyar sa. Sai da tayi mai
isarta sannan ya fara lallashinta.
"Kinsan rayuwarki na da mahimmanci a
tattare dani, kiyi hakuri kiyi tunani kinfi karfin
Hammad in aka dubi halayya da kamala, ki
hakura tun yanzu kafin ya kara miki wani
takaicin gaba. Ki kuma cigaba da addu'a Shine
maganin komi" haka yayi ta bata kalaman karfin
gwiwa har ta sake.
"Ana fa fama da zazzaɓin cizon sauro, da
typhoid ga tattalin arzikin duniya na cikin
ha'ula'" Ta faɗi tana mai sauya hiran.
"Eh wallahi, ko ina har fa Nijeriya kuma
rashin tsaftar muhalli duk ke kawo hakan fa"
Ya faɗi cikin halin ko in kula.
"Ta ya kenan?" Ta tambayeshi don bata
fahimce shi ba.
"sakacin mu yayi yawa, ba ma gyara gwata a
anguwanni, bola ko ina, ciyayi sun fito jikin
gidaje, amma son kai irin na mutanen mu yanzu
ba'a gyarawa. Sauraye sun samu mafaka, in
ka gyara cikin gidan ka ai zaka fira waje, kinga
dole zazzɓin cizon sauro yayi yawa.
Typhoid kuwa yanzu kinga damina ne, muna
tara ruwan sama muna sha ba tare da an tafasa
shi ba. Tsakanin sama da inda ka tara ruwa ai
akwai germs da zasu shiga. Ko rijiyoyi da suka
cicciko kinga ai ko alam mutum yasa dattin zai
kwanta kafin a sha."
"wai yaushe ka fara aiki da asibiti ban sani
ba. Tunaninka sak abinda ya ke faruwa. Allah
dai ya kare mu da lafiya".
"Aameen ya rabbi"
Haka suka cigaba da hira yaje yai sallan
la'asar ya dawo, sai wajajen biyar na yamma
yai musu sallama suka rabu.
MAFARKIN ABDOUL
©Safiyyah Ummu Abdoul
٨ .
Yanda Abdoul ya tafi haka shawaran da ya bata
ya bi ta gefen kunnen ta don kuwa sabon
soyayya suka fara da Hammad, duk tayi masa
zancen aure yakan ba ta amsa da cewa "ai
kawancenmu yafi soyayya mahimmanci kar ki
bari zugin kewaye ya zama katangar biyan
bukatar zukatanmu" a haka yake binta da daɗin
baki har ta saduda.
Ana cikin haka sai ya sauya salon soyayyar su
ya zama hiran da suke na batsa ne, tun bata
sakin jiki har ta kware a sarrafa kamai da kan
motsa sha'awar su wanda hakan yasa yakan
bata kula na musamman. Sukan kashe awanni
suna waya har sai sun kai ga samun natsuwa,
wata rana suna cikin irin wayar se ya ce mata
"Baby ina so in na zo Niamey zaki ɗan min
wasu abubuwan da kike kwaɗaita min a waya"
Ya faɗi cikin sigar rarrashi.
"Anya sweetyna kana so na kuwa, kasan
dai bazan taɓa yin zina in saɓa ma Mahalicci na
ba don faranta ranka" Ta ce a fusace
"wa ya ce miki zina za muyi ai kin wuce ayi
aron hannu da ke, wallahi iyakarmu romance,
ba zan taɓa keta haddinki ba." haka yai ta faɗa
mata kalamai masu nuna aminci da yarda har ta
amince.
Washegari kuwa sai gashi, ta shirya da
sunan zata shiga makaranta kamar yanda ya
raɗa mata ta faɗi sai ga Abdoul ya iso gidan
babu sanarwa ya zo mata sallama za shi karatu
Kasar Faransa.
"haka ba ko ɗan notice" Ta faɗi a
zolayance
"Na duba ne naga tabbas in ba wani
kwakkwaran abu zai kaiki skul ba toh kina gida,
shi yasa kawai na ga gara in zo yau tunda
tafiyanmu ta nuna zuwa France"
"aiko da ka taka zero, yanzu take shirin
shiga makarantar wai an kira ta" faɗin haj
Mas'ouda da ke shigowa falon.
Kallonta Abdoul yayi alamun rashin yarda,
murmushin yake ta sakar masa wanda ya
tabbatar masa da zarginsa.
"shin ina zata je tayi karya da makaranta" Ya
samu kansa da tambayar kansa hakan.
"Sai muje mu dawo kawai momma" Ya faɗi
ma Haj Mas'ouda yana murmushi
"Toh a dawo lfy, kaga sai kayi mata faɗan
rashin tsaida miji, ta lake ma Hammad wanda
sam ba aurenta a rayuwarsa." Ta ce fuskanta
na nuna alamun takaici.
"Momma lokaci ne..." gwaɓe mata baki da
akayi ne yasa ta yin shiru. Se dai a ranta tai ta
surutun an sa mata idanu.
Fita sukayi tana tunanin yanda zasuyi da
Abdoul don ya sauke ta a inda Hammad ke jiran
ta. Sake-sake kawai takeyi don har sun kai ga
gate ɗin makarantar su sai wayarta ta ɗau
kara. Kafin ta ɗauka yai saurin ɗauka ya amsa
wayar kana ya sa wayar a handsfree
"baby ina jiran ki tun ɗazu, na matsu naji
ɗumin jikinki" aka faɗi a ɗayan ɓangaren. Da
ace zata iya nutsewa a kasa da tayi don kunyar
da ta shige.
"se dai kaji azaban wuta don ubanka, kai
rayuwar da ka zaɓa ma kanka kenan lalata
yaran mutane toh Halima tafi karfin ka kuma ka
fita hanyar ta ko in wulakanta maka rayuwa"
bai jira amsar Hammad ba ya figi motar zuwa
gida.
Haj Mas'ouda ya zayyana ma komi nan ta
fara kuka tana salalami
"Halima me yasa zaki ɓata rayuwar ki haba
nayi mamakin abin da yasa kika kasa rabuwa
dashi ashe, ancen mahaifiyarki gsky ne da tace
an gama kwakule ki. Tir wallahi da halinki" Ta
faɗi tana shirin tsallaketa ta wuce.
Kafafunta ta riko tana rokon ta, rantsuwa
take mata akan ba abinda ya shiga tsakanin su
asali ma wannan ne na farko nan dai ta kwashe
yanda sukayi ta fada musu.
"Toh da kika tashi zuwa ki isko shi aka ce
miki haka ne zai sa ya aureki? Sai ma ya kara
tsanar aurenki. Kinga dai ni namiji ne, duk
macen da na lagudata ta yarda ta aure ni
wahala zata sha, kuma haka duk wani namiji
yake, uwa uba ya sa ki a ɗiya mace to babu
sauran mutunci tsakani.
Zama ayi ta wayar batsa shi ke kai matasa
ga aikata, zina, kuma da yake ce miki turmi da
taɓarya ne kawai zina ina ya bar ayar Allah da
yace kada mu kusanci zina, kinga kenan hatta
karatun batsa, zantuttukan batsa, kallon batsa
ana iya danganta su da kananun zina, kuma
abin nisantarwa. Halima ki ji tsoron Allah ki
tsoraci kwanciyar kabari, wuta gsky ne kuma
azaban Allah gaskiya ne. Momma na wuce sai
in na dawo" Ya karasa zancen yana mai da
akalar zancen zuwa ga haj Mas'ouda.
Godiya ta bishi dashi da albarka da tayi ta
sanya masa. Nan ta bar Halima da bakin ciki da
kunya.
Mafarkin Abdoul 5th
MAFARKIN ABDOUL
©Safiyyah Ummu Abdoul
٨ .
Yanda Abdoul ya tafi haka shawaran da ya bata
ya bi ta gefen kunnen ta don kuwa sabon
soyayya suka fara da Hammad, duk tayi masa
zancen aure yakan ba ta amsa da cewa "ai
kawancenmu yafi soyayya mahimmanci kar ki
bari zugin kewaye ya zama katangar biyan
bukatar zukatanmu" a haka yake binta da daɗin
baki har ta saduda.
Ana cikin haka sai ya sauya salon soyayyar su
ya zama hiran da suke na batsa ne, tun bata
sakin jiki har ta kware a sarrafa kamai da kan
motsa sha'awar su wanda hakan yasa yakan
bata kula na musamman. Sukan kashe awanni
suna waya har sai sun kai ga samun natsuwa,
wata rana suna cikin irin wayar se ya ce mata
"Baby ina so in na zo Niamey zaki ɗan min
wasu abubuwan da kike kwaɗaita min a waya"
Ya faɗi cikin sigar rarrashi.
"Anya sweetyna kana so na kuwa, kasan
dai bazan taɓa yin zina in saɓa ma Mahalicci na
ba don faranta ranka" Ta ce a fusace
"wa ya ce miki zina za muyi ai kin wuce ayi
aron hannu da ke, wallahi iyakarmu romance,
ba zan taɓa keta haddinki ba." haka yai ta faɗa
mata kalamai masu nuna aminci da yarda har ta
amince.
Washegari kuwa sai gashi, ta shirya da
sunan zata shiga makaranta kamar yanda ya
raɗa mata ta faɗi sai ga Abdoul ya iso gidan
babu sanarwa ya zo mata sallama za shi karatu
Kasar Faransa.
"haka ba ko ɗan notice" Ta faɗi a
zolayance
"Na duba ne naga tabbas in ba wani
kwakkwaran abu zai kaiki skul ba toh kina gida,
shi yasa kawai na ga gara in zo yau tunda
tafiyanmu ta nuna zuwa France"
"aiko da ka taka zero, yanzu take shirin
shiga makarantar wai an kira ta" faɗin haj
Mas'ouda da ke shigowa falon.
Kallonta Abdoul yayi alamun rashin yarda,
murmushin yake ta sakar masa wanda ya
tabbatar masa da zarginsa.
"shin ina zata je tayi karya da makaranta" Ya
samu kansa da tambayar kansa hakan.
"Sai muje mu dawo kawai momma" Ya faɗi
ma Haj Mas'ouda yana murmushi
"Toh a dawo lfy, kaga sai kayi mata faɗan
rashin tsaida miji, ta lake ma Hammad wanda
sam ba aurenta a rayuwarsa." Ta ce fuskanta
na nuna alamun takaici.
"Momma lokaci ne..." gwaɓe mata baki da
akayi ne yasa ta yin shiru. Se dai a ranta tai ta
surutun an sa mata idanu.
Fita sukayi tana tunanin yanda zasuyi da
Abdoul don ya sauke ta a inda Hammad ke jiran
ta. Sake-sake kawai takeyi don har sun kai ga
gate ɗin makarantar su sai wayarta ta ɗau
kara. Kafin ta ɗauka yai saurin ɗauka ya amsa
wayar kana ya sa wayar a handsfree
"baby ina jiran ki tun ɗazu, na matsu naji
ɗumin jikinki" aka faɗi a ɗayan ɓangaren. Da
ace zata iya nutsewa a kasa da tayi don kunyar
da ta shige.
"se dai kaji azaban wuta don ubanka, kai
rayuwar da ka zaɓa ma kanka kenan lalata
yaran mutane toh Halima tafi karfin ka kuma ka
fita hanyar ta ko in wulakanta maka rayuwa"
bai jira amsar Hammad ba ya figi motar zuwa
gida.
Haj Mas'ouda ya zayyana ma komi nan ta
fara kuka tana salalami
"Halima me yasa zaki ɓata rayuwar ki haba
nayi mamakin abin da yasa kika kasa rabuwa
dashi ashe, ancen mahaifiyarki gsky ne da tace
an gama kwakule ki. Tir wallahi da halinki" Ta
faɗi tana shirin tsallaketa ta wuce.
Kafafunta ta riko tana rokon ta, rantsuwa
take mata akan ba abinda ya shiga tsakanin su
asali ma wannan ne na farko nan dai ta kwashe
yanda sukayi ta fada musu.
"Toh da kika tashi zuwa ki isko shi aka ce
miki haka ne zai sa ya aureki? Sai ma ya kara
tsanar aurenki. Kinga dai ni namiji ne, duk
macen da na lagudata ta yarda ta aure ni
wahala zata sha, kuma haka duk wani namiji
yake, uwa uba ya sa ki a ɗiya mace to babu
sauran mutunci tsakani.
Zama ayi ta wayar batsa shi ke kai matasa
ga aikata, zina, kuma da yake ce miki turmi da
taɓarya ne kawai zina ina ya bar ayar Allah da
yace kada mu kusanci zina, kinga kenan hatta
karatun batsa, zantuttukan batsa, kallon batsa
ana iya danganta su da kananun zina, kuma
abin nisantarwa. Halima ki ji tsoron Allah ki
tsoraci kwanciyar kabari, wuta gsky ne kuma
azaban Allah gaskiya ne. Momma na wuce sai
in na dawo" Ya karasa zancen yana mai da
akalar zancen zuwa ga haj Mas'ouda.
Godiya ta bishi dashi da albarka da tayi ta
sanya masa. Nan ta bar Halima da bakin ciki da
kunya.
MAFARKIN ABDOUL
©Safiyyah Ummu Abdoul
٩ .
Da kyar ta iya tashi ta sallaci magriba da isha'i
sannan ta sa tuwon shinkafa da fakku (malohia
murzazza) don taci. Jinsa take kamar maɗaci
haka tai ta tutturawa har ta cinye kaɗan ɗin da
ta ci. Har zata kwanta ta yi tunanin ta ba
Abdoul hakuri don ta san da wuya ya sake
amincewa da ita.
Nan ta iske missed calls ɗin Hammad fiye da
talatin. Bayan ta tura sakon ban hakuri ga
Abdoul ta kwanta tana wasikar jaki nan sai ga
kiran Hammad ya sake shigowa, kamar bazata
ɗaga ba don yana gab da tsinkewa ta ɗaga da
sallamanta
"Ni zaki wulakanta Halima? Nasan hana ki
zuwa akayi amma ya akayi baki tsara su yanda
mukayi planing ba, kin ban mamaki kuma ki
rusa mana budget don wallahi zancen aurenmu
yasa naso haɗuwar mu ba komi ba wallahi"
Yayi shiru yana huci a tunaninsa zata ce wani
abu sai tayi shiru wanda hakan ya kara harzuka
shi.
"kin ma maida ni mahaukaci ne ko, haka
Allah ke abunsa, ya bani daman mallakar ki a
matsayin mata nai wasa da wannan daman
yanzu gashi kuma soyayyar ta dawo min kina
min wulakanci" Ya faɗi kamar zeyi kuka.
"tsaya! tsaya! Hotel ne zakayi zancen aure
dani, ina in har haka ne gidanmu yafi dacewa da
muyi, ban taɓa haɗa makwanci da namiji ba
kuma bazan fara akanka don kana min
barazanar aure na zaka yi ba. Na kara gode ma
Allah da ban saɓa masa saboda kai ba, wallahi
kunyar da naji yau yafi min sau dubu akan
wanda zanji ranar kiyama inda na cikata
umurninka." Ta karasa tana mai shessheka.
"haba Mon amour (masoyiyata) kin san
Allah ɗaya ko to Je t'aime de tout mon Coeur
(ina sonki da dukkan zuciyata. Kiyi min rai ki
sake bani lokaci mu tattauna wallahi duk abinda
zamu tattauna mai mahimmanci ne, akan
zancen aurenmu ne. Ki taimaka min ba son ni
ba" Ya faɗi cikin sigar lallashi da ban hakuri.
"Na ji gobe ina gida kazo kawai" Ta faɗa a
takaice.
"wani irin kina gida, haba sweetyna kar kiyi
min haka, in zaki samu fitowa ki same ni a hotel
din. Don Allah ba don ni ba" abinda ya samu
kansa da faɗi kenan bayan ya tattara
natsuwarsa zuwa yanda bazai bayyana fushinsa.
"bafa zan saɓa ma Mahalicci na don faranta
ma abinda ya halitta ba. Kayi hakuri kawai
kazo gida" itama ta faɗi kai tsaye ba tare da
shakka ko tsoro ba.
"lallai duniya juyi juyi yanzu duk son da ake
min an dena ne, sai ni kuma da Allah ya
jarabta da sonki. Wai ba kiyi mamaki ba
Halima, anya zan iya rayuwa babu ke, ki
taimaka. Mana don Allah" Ya karasa da
sumbatar iska, wanda yasan Halima na so
kwarai da gaske koda ranta a ɓace yake da ya
mata takan manta inda kanta yake. A
mamakinsa sai yaji tace
"Ni in bazaka zo ba muyi maganar anan shike
nan, banyi mamakin chanzawarka ba don kana
son gani na komi zaka iya"
"shike nan kin zaɓi rabuwarmu akan ki zo,
kin san dai babu abinda zan miki, just
tattaunawa zamuyi akan mafitanmu" Ya nace
akan son yardar da ita akan ra'ayin shi.
"se da safe don na ga baka da niyyar gane
annabi ya faku. Bazan saɓa ma Mahalicci na
bafa" bata jira cewarsa ba ta kashe wayar.
Buɗe kofar da akayi yasa tayi saurin share
hawayen da ya gangaro mata. Har ga Allah tana
son Hammad amma ya ta iya. Rungumarta Haj
Mas'ouda tayi tana share mata hawayen.
"kin cika yar hallak Halima, ubangiji ya dubi
hakurin ki ya baki mijin marainiya, kar ki sa
damuwa a ranki, wani baya auren matar wani
haka wata ba ta auren mijin wata. Don haka
mata masu cewa zasu bada kansu don a auresu
babban kuskure ne da suke tafkawa, in Allah
beyi shine mijin ba sai dai bakin ciki ya kashe su
don bayan asaran mutuncin su har da asaran
masoyi. Kuma duk saurayin da kika ba shi kanki
walau karami ko babban zina wallahi ranar da
aka ɗaura aure duk son kan koma kiyayya,
hantara da wulakanci zaki kwasa maimakon
soyayya da tattali.
Halima bakya mamakin meyasa auren yanzu
babu karko wallahi maimakon mata su gina
soyayya a zukatan masoyan su sukan gina
sha'awa ne, tura ma samari kalamai da hotonan
batsa wai da sunan su rike su har su aure su.
Daga ranar da akayi auren kuma ya kashe kishin
shaawarsa se ya fara gasa ta. Ki cigaba da
addu'ar zaɓin Allah ki aje son rai. Gara ki so
mijin da kika aura da ki auri mijin da kika so.
Kar kiyi gaggawa a aure, Allah ne mafi sani a
dukkan Al'amura, Allah ya miki Albarka " Ta
karasa tana lallashi ta, sannu a hankali ranta ya
fara haske ta nemi bakin cikin ta rasa.
Hamdala tayi ta nanatawa a zuciyarta akan
gatan da Allah ya mata na samun mai ɗaura ta
a hanya.

Mafarkin Abdoul 6th
MAFARKIN ABDOUL
©Safiyyah Ummu Abdoul
١٠
Sannu a hankali ta fara farfaɗowa daga cutar da
ke addabarta, tun tana tuna Hammad sau ba
adadi har ya zama takan kidaya su, tafiya
tafiya har bai wuce ya faɗo mata sau biyu ko
uku a rana ba.
Kwatsam wata ɗaya da faruwa wannan
Al'amarin suna kallon tashar Dounia TV (Radio
Télévision Dounia) su duka har da baffa, bayan
Ummitr Bingel sa Gimbiya Zuby sun gama
shirin da sukanyi na mu shakata sai aka sako
tallan auren Hammad da wata Amina. Shiru ya
ratsa su a falon har aka sa wani shirin. Se chan
ne baffa ya nisa ya musu nasiha mai ratsa
zuciya, ya nuna musu illar yaudara da kuma
mata su zubar da mutuncinsu. Tun daga ranar
ta tattara lamuran Hammad ta sa a bola sannan
ta kona.
Ta samu aiki a makarantar da ta gama wato
Université Abdou Moumouni bayan ta kammala
masters ɗin ta. Ba laifi tayi kiba tayi kyau
abinta yayinda maza suka sa ta gaba, ita kuma
bata basu uzuri daga sun nemi raina hankalinta
zata kora su, tsoranta zuciyarta ta kamu da son
wani ta kara wahala.
***
2014 ...
Gari na wayewa dare na yi kwanaki na tafiya
har su isko watanni. An wayi gari Halima kan
manta Hammad in ba taji an kira sunan shi ba
ko taganshi kasancewar yakan kawo matarsa
makarantar da take aiki. Bata da wani abokin
ɗebe kewa da ya wuce Abdoul sun shaku sosai,
komi ta samu in na yara ne takan siya ma
yaransa ne safiyyah da ta ci sunan mahaifiyarsa
hakan yasa suke ce mata Ummu abiha ,sai biyun
Halima kuma a hakan suke kiranta.
Agaysha ta san da zaman Halima kuma tana
kishi da ita amma bata ɗauka da gaske bane
don a cewarsa Halima kawarshi ce kawai da ya
ɗauka kanwarsa uwa ɗaya. Hakan ya kwantar
mata da hankali don duniya in dai kawance
kawai Abdoul ɗin ta zeyi da koma wacece ba
soyayya ba toh babu abinda ya shafe ta. Kalmar
budurwa ne dai ta tsana don ko da wasa kace
mata "ga budurwan Abdoul" toh zaka shiga cikin
jerin makiyanta da bata da kamar su.
***
Wata rana cikin ranaku, Halima na zaune a
ofishinta da ke cikin Faculté des Sciences, kira
ya shigo wayarta wanda daga amon kiɗan ta
san yayanta ne. Da sallama ta amsa wani farin
ciki na ratsa ta, lumshe ido duk sukayi a yayin
da suka ji muryoyin junansu, shiru sukayi na
yan dakikai, su kaɗai suka san mai zukatansu
ke raya musu.
"yan mata jiya nayi mafarki da ke wanda naga
ya chanchanci in isar miki shi ta hanyar labarta
miki". Ya katse masu shirun.
"wow! Allah sa alkhairi ne MAFARKIN
ABDOUL ɗin" Ta faɗi tana dariya. Shima cikin
dariyar ya caɓe
"Au wai har kin sa mai suna ne, tun kafin kiji"
tun kan ya dire tace
"kasan da ace ina da fikrar rubutu babu abinda
zai hana in mai da shi littafi har in sa mai sunan
MAFARKIN ABDOUL" Ta faɗi cike da alamun
iyakan gaskiyarta kenan.
"wai tsaya, in kuma mafarki nayi ana
nakaɗa miki duka, shima alfahari zakiyi dashi"
Ya faɗi yana mai cigaba da dariya, wanda ta
kasa bambantashi da na keta.
Cikin Alamun gundura da dariyarta tace "Ni ba
abinda ke cikin mafarkin ya sani murna ba balle
ka samu abin tsokanata da shi, wanda yayi
mafarkin ne ke da mahimmanci Alaranma"
dariyan ya cigaba da yi ba tare da ya damu da
fushin da ta fara ba.
" Toh hajiya halimatu ai ba yau ne farau ba,
ina ga ba'a cike sati. Banyi sau biyu ba, wannan
dai kawai ya tafi da hankali na sannan ya
magance min matsalar da nayi shekaru biyu ina
fama. Shiyasa zan faɗa miki in ba haka ba ai se
kin biya. Ya sake kara sawa yana dariya.
"yanzu kana da matsala shi ne baka taɓa
faɗa min ba, kuɗi ne ko ciwo ko har yanzu
mamansu Ummu abiha ba ta dena tozarta ka
bane." Ta faɗi kamar zatai kuka. Wannan na
ɗaya daga cikin dalilin da yasa take da
mahimmanci a gareshi. Takan nuna damuwa ko
farin ciki yayinda ɗaya ya same shi.
"ba ko ɗaya, wato ke hajiya ko. Kina kwasan.
Albashi, toh cepa miliyan ɗari nake so,
karkaɗa kunni ki sha labari" Ya faɗi. Yana
dariya, itama ta tayashi
MAFARKIN ABDOUL
©Safiyyah Ummu Abdoul
١١ & ١٢
MAFARKI...
"Na ganni ne a wani lambu mai ban sha'awa,
bayan kayan marmari da ya yalwatu a cikin
lambun har da wasu furanni masu fitar da
daddaɗar kamshi wanda ya sa na kara
kishingiɗa a resting chair ɗin da nake zaune a
kai. Lumshe idanu nake farin ciki na yalwatuwa a
zuciyata.
Sallaman da kikayi ne yasa na buɗe idanu ina
mai sakin murmushi. Farantin hannunki kika aje
a gefe sannan kika fara shayar dani salad ɗin
kayan marmarin da kika zo da shi. Wanda
daɗin sa bai sa na ankara da ya kusan karewa
ba har se da kika daga Yankar karshe na abarba
sai na na riko hannunki haɗe da spoon ɗin da ke
baki na. Hakan yasa kikai saurin ɗago idanu
kika kalle ni, idanunmu na haduwa kika kasa
ɗauke idanu na wasu dakiku. Muna cikin haka
sai ga yara biyu sun zo a guje suna kiran
"Abbu! Ummu!" kallo ɗaya nayi musu na san
yan biyu ne kuma daga tsatsonki suka fito
saboda tsabagen kaman da sukayi da ke. Sun
faɗo jiki na kenan suna haki kiran sallah ya tada
ni daga barci, faɗa min me kika karanto a ido na
da kika tsare ni da kallo" Ya karasa yana mai
tsokanarta,
"ka bari sai mun sake haduwa a dreamland
sai ka min tambayar, kasan me?" Ta dakata ko
zai amsa
"A'a se kin faɗi" Ya bata amsa
Se da tayi dariya son ranta sannan tace
"za ka yi kyau da rubuta labarin soyayya fa.
Wannan iya tsara lbr haka" ba ta dena dariyar ba
shi kuma kansa duk ya ɗaure,
"yanzu ba za ta ba MAFARKIN mahimmanci
ba bare ta kai ga fahimtar abinda ya ke damuna
game da ita b" Ya faɗi a ranshi yayin da a
bayyane shiru yayi mata kawai. Jin ya kyale ta
yasa T faɗin "hello!" dariya kawai ya bi ta dashi
kana sukai sallama.
Shiru tayi tana tariyo labarin da ta sanya ma
MAFARKIN ABDOUL, bata san me ke shiganta ba
ta dai tsinci kanta cikin wani yanayi daga tafin
kafarta har Kirjinta wanda salon bugun zuciyarta
ya chanza nan take.
Amon muryar Abdoul take ji a kunninta
sa'ilin da yake bata labarin. Nan take wani farin
ciki ya mamaye ranta yayinda tsoro kuma ya
shige ta sanda ɓari guda na zuciyarta yace da
ita "in baya sonki fa". Nan take sai ta shiga
damuwa.
Sai sa su ka yi sati biyu babu wani
kwakkwaran magana da ta shiga tsakanin su,
iyaka sukan gaisa da ɗan hira sama sama.
"Amarya a gidan Abdoul barka da yini" Ya
shigo WhatsApp ɗinta daga lambar aminin
Abdoul Yahai.
Aljani mai dariya kawai ta tura masa sannan
suka gaisa a mutunce.
"kina gara ɗan uwa na fa Halima shi
tsoransa ki yankuna shi wanda hakan zai taba
zumuntarku amma wallahi nasan duk kuna
sonjunanku, meye amfanin cutar da kai, in shi
ya kasa buɗe hanya ke baza kiyi ba? Ya tura
mata haɗe da aljani mai jan kai.
Bata ce komi ba sai aljani mai dariya da
hawaye ta tura masa, ganin bata da niyyar
bashi haɗin kai yasa ya kyale ta.
Daren ranar ta tsawaita hirarsu da Abdoul
har yake faɗi mata mafarkan da ya keyi kusan
kullum inda yake kara hura mata wutan sonshi a
ranta. Chan dai ta ɗaure ta tura "inaama!
Inaama!" Yana gani ya tashi zaune, sannan ya
kira ta. Ringing biyu ta ɗaya da sallama.
"me kike cewa ne Halima ɗazu" addu'a yake
ta faɗi abinda ranshi ke son ji.
" cewa nayi inaama! Inaama MAFARKIN
ABDOUL zai tabbata. Da an samu maaurata
gwanaye da zasu sadaukar da rayuwar su
wajen faranta ma juna" Ta faɗa bil hakki abinda
ke ranta kenan. Ya daɗe da sanin Halima irin
mutanen da masana psychology kan kirasu da
extrovert ne, sam bata ɓoye ra'ayinta akan abu,
ya daɗe yana jinjina mata ɓoye soyayyar sa
dake zuciyarta, ko da yake matantakanta ya
taimaka mata ainun wajen ɓoyewa.
"Halima kina da matukar mahimmanci a
rayuwata, in na koma zindar karshen sati, zanyi
magana da mama da Maman Ummu akan auren
mu, fata na kar su kawo matsala, shekara mai
kamawa zamu tabbatar da MAFARKIN ABDOUL,
sai in kama miki gida a nan Niamey ko ya kika
ce" mamaki ya cikata, wannan sai kace jira
yake ta furta.
"Amma wannan assurance ɗin da kayi min
anya beyi wuri ba, bana son abinda zai taɓa
alakarmu fa, kasan ban iya son abu ba, ina
sonka da yawa Abdoul" Ta furta a sanyaye
wanda hakan yasa yaji tausayin ta ya mamaye
shi.
" kar ki damu ina tare da ke insha Allah ba
gudu ba ja da baya" da haka suka dulmiya
duniyar soyayya ba ji ba gani. Wasu kalaman in
ya furta mata har mamaki takeyi da ma chan
yana sonta ne. Da kyar sukayi sallama bayan
sun tsara yanda zai nemi aurenta da kuma
yanda aurensu zai kasance.
Cikin watanni biyu sun shaku sosai fiye da
wanda sukayi a baya. Kulan da suke ba junansu
abin ba'a magana, ko da yaushe suna nane da
juna walau a Chat ko a waya.
Cikin tsarinsu ne bazata faɗa ma kowa ba har
se yaje yayi magana da iyayensa in sun tashi
zuwa neman aurenta. Duk yanda yaso zuwa aiki
ya hana shi motsi kasancewar ya fara aiki da
Ministère des Affaires Étrangères et de la
Coopération ( Nigerien Ministry of Foreign Affairs
and Cooperation) hakan yasa ya kan bi tawagar
da ke zuwa duba République Niger ambassade
na sauran kasashe. Yanayin rashin zama yasa
bai tafi da Agaysha ba amma wani sa'in
musamman in yara na hutu sukan je a tare.


Mafarkin Abdoul 7th
MAFARKIN ABDOUL
©Safiyyah Ummu Abdoul
١٣.
Soyayya suke mai cike da tsafta, har yanda
aurensu zai kasance sunyi, wani zuwansu
Abuja a tarayyan Nigeria ya siya yadin
material ya bada a Hanifa boutique ya ba da a
ɗinka bridal gown a Hanifa creations & couture
da ke lamba ta 10, Gimbiya Street area 11, garki
Abuja. Tun da ya kai yake manta santin ɗinkin.
Don sai da ya ba mai wajen haj. Hadiza shawara
in da hali ta buɗe musu a Nijar ko suma zasu ci
romon ɗinki hadaddu. Dariya tayi tace " me zai
hana, Nijar da Nijeriya ai duk ɗaya suke, zamu
duba se a buɗe a Niamey in de zaku kawo
ɗinki".
Yini yayi yana faɗa ma Halima karamcin su
tun daga siyan material har ɗinki fatansa su
cika masa alkawari. Halima bata tabbatar da
haɗuwan dinkin su ba sai da ta leka shafinsu
na Instagram, rudewa tayi tana nuna ma
momma haj mas'uda, faɗi take "momma anya
bazamu aika sauran ɗinku nan ba, ɗinki sunyi
kyau" itama dai haj mas'uda ta yaba da kyawun
dinkin har tayi shaawar aika ma kawarta haj.
Maijidda dake birnin Kano in za'a samu wanda
ze kai tunda suna home delivery a Nijeriya.
Hakan kuwa sukayi sanda Abdoul ya tabbatar
masu da cika alkawarin su. Sai akayi da Abdoul
ya karbo tunda za'a kammala kafin su dawo
Nijar.
Bata tsaya ba sai da tayi booking kwalliyar da
za'a mata wajen ramat makeover, sannan ta
bada aikin waka wajen mai zazzakar murya da
amon muryarta yafi zuma daɗi wato sa'a Vocal.
"wai ke iyayensa basu zo ba duk kun gama
shiri ko dai ku zaku aurar da kanku ne," faɗin
haj mas'uda da ta fada mata ta yi booking
wakar sa'a Vocal, da irin karamcin da sa'a tayi
mata da ta kira ta a waya.
"momma kinsan yace January yake so ayi,
da sunzo za'a yi komi gaba ɗaya" Ta faɗi tana
rufe ido.
"Au! Wai dama kina da kunya, bayan ina
ganin kosawa a tare da ke." itama ta faɗi tana
dariya.
"momma shekaru na fa ashirin da biyar,
kinga kenan ai na tsufa, ko" dukan da aka kai
ma cinyarta yasa ta yin shiru.
"Toh shi ɗin kin tabbatar da ya isa da
iyalinsa? Kuma baza'a samu matsala ba, kin
san maza in har basu isa da matansu ba
aurensu matsala ne. Ki cigaba da addu'a de, in
Alkhairi ne Allah ya tabbatar, in babu ya zaɓa
miki abinda yafi alkhairi"
Jikinta yayi sanyi, yaushe rabon da tayi
addu'a, a ganinta ai shi ne alkhairi tunda ya zo
bayan rabuwanta da Hammad. Haka dai ta fara
istigfari tun daga zaune. Ranar itace har da
tsayuwar dare.
Dawowannan Abdoul ya sa ta farin ciki da
annashuwa, gani kawai aurensu ya zo. Bayan
ya aje musu sakon ɗinki ya dauki hutu ya wuce
zindar. Nan ma ya samu tarbo mai kyau daga
Agaysha.
Sai da ya kwana biyu sannan ya fara mata
Maganar wata rana suna hira
"Madam aure nake son yi, ba don bana sonki
ba sai don gazawarki wajen kula dani, ina sonki,
banda niyyar kara aure amma yanda kike tafiyar
dani yasa har shakuwar mu tayi karfi da Halima
tace tana so na, kuma nayi niyyar aurenta" Ya
faɗi kai tsaye. Kuka sosai ta fara, ganin yayi
shiru yasa ta cakume masa wuyar rigarsa tana
ihu tana kuka
"kaci amanata, Halima ta munafunce ni, tayi
ta ban shawara ashe sonka takeyi toh wallahi
baka isa ba, zan kai karanka wajen baba don
wallahi bazan yarda ba, ka gama zubar min da
mutunci a idonta sannan kace zaka aure ta"
rungumar ta yayi yana bata hakuri.
Rigima taki ci taki cinyewa, kuka Agaysha
takeyi ta ki cin wani abinci, tayi baki ta rame,
yaranta ko wanka bata musu, ya bada hakurin
taki, har sai da ta tsare shi ya kira Halima.
Ringing yake Halima na kallo taki dagawa
don takaicin tunda ya koma ko WhatsApp yaki
hawa, bai dauki wayarta ba haka bai kira ta ba..
Sai da yayi kira uku sannan ta ɗauka da
fara'arta ta gaisheshi, a dakile ya amsa sannan
yace
"Na kira ki ne in baki hakuri, sannan in faɗa
miki bazan iya aurenki ba, tunda na faɗa ma
Maman Ummu abiha zancen auren gida na ya
koma sansanin rigima, matsalar gida na yasa
nayi tunanin kara aure kuma ta min alqawarin
canzawa, kiyi hakuri ki jingine zancen soyayya
tsakaninmu".
Saurin tare shi tayi tana mai kuka "kar ka
min haka, ina sonka zan jira ka har zuwa sanda
zaka shirya amma don Allah kada ka rabu da ni"
kuka take Bil hakki.
"kinga Halima matata ta ishe ni bazan iya ba
nace, ko ana dole, mtswww" Ya karashe da
jan tsaki kana ya kashe wayar.
Tun daga ranar bai sake ɗaga wayar Halima
ba, Agaysha kuwa hadiye shi ne batayi ba
saboda kula. Tarairayan da yasa ya manta wata
Halima a doran duniya.
A ɓangaren Halima tun tana ganin abin
wasa, taga har anyi sati ba kiranshi ba alamun
shi yasa ta kira amininsa Yahai
Bayan sun gaisa ta faɗa masa duk abinda
ya faru ta kara da faɗin
"ka bashi hakuri in laifi na masa, duk Dokan
da zai sa min na yarda in dai zai aure ni, don
Allah ka taimaka min."
"shike nan Halima, yanzu haka yana hanya
munyi alkawari zamu haɗu, zan kira ki yayinda
nake masa maganar don ki ji komi daga
gareshi" godiya tayi ta zuba masa kamar yai
mata bishara da Aljanna.
Ba'a yi awa ɗaya ba kuwa sai ga kiran
Yahai, da saurinta ta ɗaga tayi shiru tana ji
Yahai yace
"wai ni Abdoul ina Halima ne ya zancenku ya
kwana"
"mtsw! Tana chan, ni bazan kara aure ba ina
son zaman lafiyan gida na, tunda na faɗa mata
ban sake neman ta ba"
" ko dai ka gano wani mugun halinta ne,
yanzu kake neman rabuwa da ita? " Yahai ya
sake tambaya
"kasan in da banyi aure ba babu abinda zai
hana aje Halima a matsayin mata, rigima ce dai
banso. In kana so kuma Allah sanya Alkhairi".
Mamaki da takaici ya cika Halima, ta yi saurin
katse wayar kafin taji abinda zai ɓata mata rai.
Tsam ta tashi ta je ta faɗa ma momma
abinda ke faruwa, mamaki ya cika ta kwarai
amma ta bata hakuri haɗe da nasiha akan
addu'ar su ya karɓu Abdoul ba Alkhairi bane a
gare ta.
***
A kwana a tashi Halima ta zama wata mara
fara'a, kallon ko wani namiji a matsayin
mayaudari take in akai mata magana tace tunda
Abdoul yayi kowa ma zeyi.
Wata rana kawarta faɗima ta zo gidan
momma kamar yanda ta saba kawo mata ziyara.
Suna cikin hira tace
"wai dama Agaysha Iggalher ce matar
Abdoul?"
"Eh! Ina kika Santa?" itama ta tambaya.
"kin san kanwar miji na ke auren babanta, da
kyar uwar ta yarda akayi, jiya muka haɗu a
gidan da yake ita ayshatou din ta haihu, Shine
fa take nuna hotonki wai kin nace ma mijinta
kina son shi har tana muyi kafa kafa da
mazajenmu kwacen miji ki keyi " kukan da
Halima ta fara yasa yin shiru. Ta fara bata baki
tana cewa
" bafa na faɗa miki don ki bata ranki bane, ina
so dai ki yi aurenki ki huta sa surutunta, don ta
ɗauki alwashin sai ta hukunta ki"
"Ta ya zata hukunta ni, asiri ko tsafi bazai
taɓa kama ni ba don na rike addu'ar da manzo
SAW yace mu rike ma kariya. Manta da ita kinji
yar uwa, jiya na dawo daga zindar fa" haliman
ta karasa tana mai chanza hiran.
Bayan magriba ta dauki waya ta kira Abdoul,
sun gaisa kamar da ya tambaye ta mutan gida,
itama haka. Chan ta ce
"Na kira ka ne in ce ka ja ma matar ka kunni,
babu abinda zanyi da mijinta, tun tana kira na
tana zagi na ban tanka mata ba, har ya kai zata
dinga yawo da hoto na da guntuwar wasikar da
ban san da zamansa ba wai na rubuto maka, ai
laifin ba nawa bane naka ne mijinta. Don Allah
ku fita harkata nima daga yau na fita naku"
"kinga bazaki zo ki ma mata na sharri ba,
kuma Allah ya saka mata, aure ne dai nace
banyi ko dole ne" Ya katse ta a fusace,
"in da ina bin ta da sharri kasan da tuni na
barka ka saketa ko, ko ka manta sirrin gidan ka
yayi zama hannuna, Allah bamu Alkhairi" Ta
kashe wayar gaba daya ta sallaci isha'i wani
farin ciki take ji ta rasa na menene, hatta yan
gidan sun kula don sai da baffa ya ce mata
"Halima Albishir ɗin Aljanna akai miki?"
Tayi dariya tace
"kusan haka ne fa, kasan an ce budurwa in bata
taɓa zina ba ta rasu tayi shahada da ladan
jihadul Nafs. Ko dai zancen mutane ne baffa? "
Ta tambayeshi tana dariya.
" se kinga auren jikokinki Halima, Allah sa
jinkirinki alkhairi ne " momma ta katse musu.
" Allah dai yasa in tafi a sa'a, momma bata so
in tafi, se hakuri in lokaci yayi" Ta faɗi tana
dariya
Haka sukai hira har goma da rabi sannan tai
musu sallama ta je kwanciya
Kwanciyar ta ke da wuya ta fara ciwon ciki,
da kyar ta daga waya ta kira momma, a ruɗe ta
shigo ta iske ta cikin amai cikin na murɗa mata.
Cirko Cirko sukai akanta, bayan cikin ya lafa,
faɗi take "ku yafe min, kuce su mama su yafe
min, na yafe ma kowa"
"ciwo ba mutuwa ba ai kinji sauki, sannu
halima" kawai suke cewa.
Huɗu da minti arba'in cikin ya sake
motsawa, wannan karan tana wani irin mika in
ya rike ta. Ɗaukan ta sukai zuwa mota don kaita
asibiti basu san sun kai ta ga ajalinta bane.
Daidai kwanar fita anguwansu tayi wani mika
haɗe da salati, shike nan ta amsa kiran
ubangiji.
"Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun" kawai baffa
ke faɗi. Hajiya mas'uda kuwa mutuwar zaune
tayi. Hawaye na gasar tsere a fuskarta.
MAFARKIN ABDOUL
©Safiyyah Ummu Abdoul
١٥ .
NADAMA....
Tunda ya sauke wayar jikinsa yai masa sanyi.
Anya ya kyauta mata kuwa, yarinyar da ke
ɗaukan shi mai babban daraja ya yankuna
haka. Shiru yayi kalamanta na dawo masa ɗaya
bayan ɗaya.
"wai me yasa ake ɗaukan maza masu mata
mayaudara ne, duk wanda nace ma kai zan aura
sai sun ce Allah sa kar kayi min halin, in dai aje
wani spare, tunda soyayya ba mota bace meye
amfanin tara samari" Ta faɗa masa wata rana
suna waya.
"Ni dai ba yaudaranki zanyi ba. In kinga ba
mu yi auren nan ba mutuwa ce, kece fa mafarki
na kece tunani na a farke" sai da yaji kunyar
kansa da ya tuna alwashinsa gare ta.
"momma cewa tayi ba komi ya sa maza masu
aure iya yaudara ba sai ganin suna da matan su
a gida, ba su da halin karin aure amma su je
suna kwadayin soyayya da wasu, basa ko
la'akari da suna da yaya mata ana iya musu
suma. Wasu kuma ba laifinsu bane matan su ke
hana su aure, su ma basa tunanin mazajensu
na iya mutuwa ko su rabu wani mara matan ne
zai aure su, ai aure kanta wa'adi gareta ban ga
abin tashin hankali akai ba"
"lafiya ka zauna kana tunanu" Agaysha ta katse
masa tunaninsa nan de ya zauna sukuku har
lokacin barci yayi ya kwanta.
***
Sanye take cikin shiga mai kyau, kyallin da tufan
jikinta ke fitarwa kaɗai abin kashe ido ne, babu
wani al'auranta da ke waje, fuskarta cike yake
da murmushi.
"Abdoul kaga ɗaukakan da Allah yai min ko,
ka gafarce ni in na saɓa maka amma na tafi
bazan sake damunka ba" Ta na faɗin haka ta
fara tafiya, taurari sun kewaye ta, haske ya
bayyana, kamshi ta ko ina.
"Halima! Halimaaaa! Halimaaaa!" yake faɗi
iya karfinsa wanda ya tada Halima daga barci.
Kallon agogo yayi karfe biyar na asuba ya tashi
ya ɗauro alwala nan ya fara jero nafilfili
kasancewa biyar da rabi ake kiran sallah.
Tunani yake dole ya je Niamey su sasanta
kansu bazai ma Halima haka ba, bata
chanchanci abinda yai mata ba, ai Halima
matar alfahari ce, wacce Burinta tayi aure tayi
Ibadan da zai zama sanadin shigar ta Aljanna.
Yana fita Agaysha ta kira kawarta da ke
mata rakiya zuwa gidan malamin da ke mata
aiki akan zasu je, Abdoul ya tashi cikin dare
yana kiran sunan Halima.
Ko da ya dawo sallah yayi mamaki da bata
tsare shi da masifa ba, illa hillatarsa da tayi ta
yi har ya shagala. In bayan sun samu nutsuwa
take faɗa ma sa zai kai ta gidan kawarta zasu je
ta'aziyya, ba gardama ya amince.
Karfe goma sha biyu suka bar gida ya sauke
ta sannan ya karasa Mirriah don ya samu sallar
Jumma'a a Grande Mosque de Zinder. Bayan an
iddar da sallah ne aka bada sanarwan za'ayi
sallan jana'iza, na wata baiwar Allah da ta
rasu. Haka kawai yaji tsoro ya shige shi. Bai
gama jawo natsuwa ba idonsa ya kai ga baffa,
da mahaifin Halima suna share kwalla. Kallon
zanin da aka rufe ta yayi in bai manta ba yana
daya daga cikin ɗinkunan da ya amso masu har
yana mata tsiyar tayi zani plane.
Se da ya sa ma zuciyar sa mahaifiyarta ce ta
rasu sannan ya samu natsuwar tashi ayi sallan
da shi. An idar haka yabi tawagar farko, ya kula
da yanda mahaifinta ya rushe da kuka sanda
suka yi ido hudu dashi. A harabar masallacin
aka shigo da hillux aka shimfiɗe gawar. Yana
ta kallon mutane ɗai ɗai, ga yan uwanta mata
daga sashin mata na masallacin. Da kyar ya
shiga motarsa, inda wasu yan anguwan su
haliman suka cika motar. A hankali akai ta tuka
motar har makabarta inda an riga an gine mata
lahda ɗinta. Ko a nan sai da mahaifin Halima
ya jawo shi, yayin da ake maida kasan da zai
rufe ta.
Suna nan tsaye bayan an rufe ba ma kusan
minti arba'in suna mata addu'a kamar yanda
manzo SAW ya umurce mu kar muyi saurin barin
makabarta yayinda muka rufe wani namu.
Har suka fito babu wanda yace uffan, ya kula
da Muguwar kallon da baffa ke jifan shi da shi,
yayin da mahaifin Halima ke masa kallon
tausayi. Sun fito gate din makabarta kenan
mahaifin Halima yace
"Abdoul ya hakurin mu, Halima kuma wa'adi
ya cika. Sai mu" be kai aya ba sai ganinsa
sukai a zube sumamme. Shafa masa ruwa akai
sannan aka sa shi a mota, baffa ne ya ja motar
suka dunguma zuwa gida. Banda ajiyar zuciya
babu abinda Abdoul ke yi, ina ma zai farka daga
barcin nan.
Nasiha sosai suka haɗu sukai masa har
baffa da ke cike da jin haushin sa. Ya shiga
cikin gida yai musu ta'aziyya sannan ya koma
wajen maza. Shi dai zai kira kan shi da mutum
mutumi don motsin kirki gagaransa yayi. Ya
kasa yarda Halima ta rasu.
***
Can su Agaysha sun gurfana gaban malaminta,
bayan duk surutanshi da shafe shafensa yace
"Halima anyi ta ne kawai don ta kawata
MAFARKIN ABDOUL, sai de akwai wasu yara a
gaba da nake hange, kuma bana tsammanin
naki ne amma tabbas na Abdoul ne, yanzu de
za'a yanka bakin bunsuru ayi rubutu dashi ki
sha, kishiya sai ta abin hawa ba dai mutum ba,
" yana gama faɗi ta aje masa cepa dubu talatin
sannan suka juya.
Ko da ta isa gida bata iske shi ba, nan tsoro
ya cika ta kardai ya je wajen Halima ne.
Karfe tara da rabi ya shigo gidan da sallama,
a cikin ta amsa amma ganin idanunsa jawur
gashi yana jan kafafu wanda shi ne abin da yafi
tsana a rayuwa.
"lafiya abban ummu" Ta faɗi a firgice tana
taro shi, a zuciyarta fata take Ace an ɗaura ma
Halima aure amma se taji yace
"Allah yayi ma Halima rasuwa jiya da dare"
"Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun, Allah ya
jikanta yasa ta huta. Wai hankali na yanzu zai
kwanta babu mai takurawa miji na" dukan da ya
fara mata ta ko ina ya sa tayi shiru haɗe da
shekawa ɗaki ta rufo kofa don gani take
mutuwar ta taɓa kwakwalwar sa.
Nan shima ya zube yana mai sakin kuka,
abubuwa da dama yai ta dawo masa dangane
da soyayyar su da Halima.
Mafarkin Abdoul 8th
MAFARKIN ABDOUL
©Safiyyah Ummu Abdoul
١٦ .
Dashi akayi zaman makoki aka gama, Agaysha
ko a kwalar riganta don tunanin ta Abdoul nata
ne ita kaɗai. Duk da walwalarsa ya zama tarihi
ba don son da yake ma Halima ko kuma don ya
gagara ɗaukan kaddara, A'a, ya kasa yafe ma
kansa rabuwa da Halima da yayi. Shin dama bai
shirya aure bane yaje ya fara neman ta. Shi ma
yana cikin jerin maza masu yaudara kenan. Me
yasa ya gaskata ma Halima zancen da ake
cewa maza masu aure sun fi yaudara.
Mafi yawan lokutta ba laifinsu bane tsoron
fitina yake sawa su hakura, amma ai Allah ya
basu ikon yi me yasa ya biye ma Agaysha har
ya saɓa ma Halima, ya ci amanar yardan da ta
mishi, ya sa kafa ya ci mata mutunci duk da
girmama shi da take yi. Me yasa tun farko ya
amince zai aure ta bayan yasan bai shirya kari
ba. Anya Halima ta yafe masa kuwa.
Da irin wannan tunanin ya shirya ya je gidan
baffa. Cikin sa'a ya same shi a gida. Bayan
sun gaisa sunyi ma juna ta'aziyya sai kawai ya
sa musu kuka, tun suna takaici har ya dan
soma basu tausayi. Basu hana shi ba har sai da
yayi mai isarwa sannan ya ce
"Halima ba ta yafe min ba ta tafi ta barni. Na
ɓata mata da yawa ban san da hakan ba sai da
lokaci ya kure min, fitinar Agaysha ya sa na ki
zuwa, ni kadai na san abinda na fuskanta." Ya
karasa yana sakin wani kukan mai tsuma zuciyar
mai saurare.
"Da ma chan ba sonta kake ba Abdoul mu
barshi a hakan kawai" faɗin momma don ita da
tana da hali zata murkushe shi take ji.
"mu dai barshi a yana sonta ɗin, babu
sauran abinda za'a iyayi se dai hakuri. Halima
kafin ta rasu sai da ta furta yafiya ga kowa.
Muyi fatan inda take tafi nan da ta bari, in da
rabo ai ss ku kasance a Aljanna," kuka dai
Abdoul ya cigaba, nan Baffa ya zauna yayi ta
bashi baki, nasiha yake masa mai shiga jiki
sannan ya rufe da addu'a.
***
2016...
A kwana a tashi ba wuya wajen Allah,
shekaran Halima ɗaya da rasuwa. Kullum
kwanan duniya sai Abdoul ya bi ta da addu'a
wani zubin har da sadaka da azumin nafila da
niyyar Allah ya kai ladan zuwa gareta.
Agaysha tun da ta buɗe idanu ta tabbatar da
gaske Halima ta rasu ta chanza salon rayuwar
aurenta duk wani nau'i na kula da take ma
Abdoul ta janye. Bata kyashin zaginsa ko ci
masa mutunci ko a gaban wanene. Ta kanyi
amfani da kuɗin da dangin mahaifiyarta ke
dashi tayi ma danginsa gorin arziki.
Irin haka ne ya faru yau, ya shigo ya iske
tana hira da kanninshi. Duk suka gaisa da shi
ita kuma ta yi kamar bata ganshi ba. Har ya
shiga ɗaki ganin minti goma bata biyo shi ba
yasa ya dawo falon ya same su.
"Madam me kika girka, zanyi baki wasu
Diplomate yan Nijeriya zasu zo" Ya faɗi
zuciyarsa na bugawa ɓat! ɓat! Kar ta kwaye
masa baya.
Ilai kuwa buɗan bakinta sai cewa tayi " Au
nom de Dieu il partir au restaurant le plus près
pour nous acheter à manger (kasan Allah ka je
Restaurant mafi kusa ka sayo muku abinci) ,
don ko naka na ba kanninka, ni na gaji ba
abinda zanyi tun safe nake aikin girki Haba!" ta
karasa tana murguɗa bakin ta.
Kallonta yake yanda ta jinɓire waje ɗaya.
Rigar sa mai tambarin wajen aikin su ne ta
sanya da zaninta. Shike nan don tana da ciki ba
zata yi ma kanta faɗa ta dinga kwaliya ba, ko
yaya ne ta yi shiga mai kyau.
"kin san Allah babu abinda zai hanaki girkin
nan in ba so kike rayuka su ɓaci ba" Ya faɗi
yana haɗa fuska ko Allah zai sa yayi mata
kwarjini amma ina don tsaki tayi tace
"banga uban da ya isa ya sa nayi girki ba,
dilla kalle ka wai kai har namiji ne anan.
Mtsww! An dai rako maza wallahi, banda ba
makwanci wahala ba abinda mutum zai buga
kirji ya ce ya iya. Ka gayyato Halima daga inda
take tayi maka" Ta faɗi tana barin shi zaune a
inda yake. Kaninsa dama tun da ta fara masa
masifa suka fice daga wajen. Dafe kansa yayi
da hannu biyu yana tunanin wani irin hukunci zai
mata. Ashe dai haka take. Wasu siraran
hawaye ne suka fara zubo masa, yana tausayin
kansa. A haka ya fara tunanin rayuwar sa,
wanda ya sani da wanda aka bashi labari.
ABDOULLAHI ABOUBAKAR
Asalin kakanninsa yan jihar Borno ne a gabashin
Nijeriya, sana'ar siyar da citta da tafarnuwa ya
kawo su Nijar inda suka sauka a zindar.
Mahaifinsa Aboubakar ya taso ɗan dangi
kasancewarsa auta cikin yaran kakansu talatin
da shida. Yayi karatu zuwa sakandire kafin ya
faɗa harkan kasuwanci, tun yana karkashin
ubangidansa mommadou har ya samu kantin
kansa.
Amanarsa da gaskiyarsa yasa ubangidansa
masa tallar yarsa mafi soyuwa a gareshi
Safiyyah . Nan take kuwa don shi ma ya daɗe
yana sha'awar mallakarta a matsayin mata sai
dai tsoro ya hana masa tunkararta.
Anyi biki amarya ta tare a nan cikin gidansu
tare da sauran yan uwansa maza. Shekarar su
ta farko ta haifi yarsu Aisha, daga nan sai
Abdoul wanda tsakanin sa da Aisha shekara uku
ne, daga nan kuma Safiyyah tayi haihuwa
bakwai wanda ya cika su tara gaba ɗaya.
Duk abinda Alh Aboubakar ya tara akan
karatun Yaransu yake karewa, makaranta mai
kyau yake tura su, duk da kasancewar daga shi
har safiyyah ba suyi wani karatun zamani ba
hakan bai hana Yaransu samun sakamako mai
kyau ba don kullum suna musu addu'ar samun
nasara.
Abdoul na da rauni ɗaya 'yan uwansa, baya
son abinda zai ɓata musu, burinsa farin cikinsu
sannan yana hakuri da duk wani mai son su.
Wannan raunin da kuma kalaman Halima ya
hana shi ɗaukan muguwar mataki akan Agaysha
don duk abinta bata wulakanta su sai da in shi
ta zage su a gabanshi ko tayi amfani da kissa ta
hana masa yi musu wani abin arziki.
Karar da wayarsa tayi yasa ya dawo daga
duniyar tunanin da yake. Share hawayen da ya
gangaro masa yayi sannan ya ɗaga wayar.
"kun iso? Toh gani nan" Ya faɗi yana
ɗaukan mukullin mota.
Fita yayi dasu zuwa Assemblée, Auberge
Mourna ya tsaya inda ya kasance gidan abinci
mai lamba ɗaya.
" wannan rowan abinci har ina, salon kada
mu gaisa da Madam ne ko" faɗin Ɗahiru ɗan
jihar Kano. Dariya Abdoul yayi yace
"kun san tayi nauyi. Muna gama waya ɗazu
sai ga kiranta. Wallahi oder nayi ɗazu na kai
masu" Ya karasa yana istigfari a zuciyar sa.
Ya kashe musu kuɗi sun ci sun yi kat
sannan suka koma gidansa gaban sa na faɗi.
Ba laifi ta karɓe su da kyau kuma ta chanza
kaya zuwa shiga na kamala. Har cikin ransa ya
ji daɗi don har lemun abarba da kankana ta
basu mai sanyi.
MAFARKIN ABDOUL
©Safiyyah Ummu Abdoul
١٧ ..
Hira sosai sukayi da abokansa, sai da akayi
magariba sannan sukayi sallama. Ranar duk sai
ta wanke laifukanta saboda lafiyayyar abinci
tuwo da fakku (malohia murzazza) ta kawo
musu karfe shida na maraice.
"Ga fa fakku ku ci ku ba Yan Nijeriya labarin
daɗinsa" Ta faɗi tana dariya. Kasancewar ta
gwana a fannin girki yasa basu so ya kare ba,
tas suka tashi da shi suna ci suna santi. Kudi
suka aje mata dubu hamsin na kuɗin Nijeriya,
zo Kuga murna wajen Agaysha saboda sanin da
tayi in ta juya su zuwa cepa zata samu kusan
dubu ɗari don ma darajar cepa ya faɗi. Da naira
dubu daya za'a baka cepa dubu uku, Yanzu
kuwa dubu da dari shida zaka samu.
Ko da ya dawo daga rakiyansu ya iske har
ta gyara wajen ta baɗe gidan da kamshi. Har
cikin ransa ya ji daɗi. Nan suka baje hira bayan
ya ja musu limancin isha'i.
***
"Yanzu Agaysha haka zamu dinga kallon su
Ummu Abieha da sadiya, shekarun Sadiya and
kusan talatin fa balle ayi maganar Ummu. Wai
bakya jin wani iri ganin su a gida ba aure" faɗin
Abdoul ransa ya kai kololuwa a ɓaci. Ace
Yaransu mata babu wanda ya fito da niyyar
aure.
"wallahi kuwa babansu, duk masu zuwa
kuma da matan su, da anyi maganar aure
matayensu su tada rigima, nima fa abin na
damu na." Ta faɗi tana gyara zama.
"kin san har Halima ta mutu bata yafe min
ba, kar ya zo alhakin ta ne ya ke kama mu.
Allah ka yafe mana yaranmu su samu mazajen
aure" Ya faɗi yana kwalla.
"Aameen ni ko na hudu ne in dai za'a so
su ba komi, " faɗin Agaysha
"Amma ke bakya son kishiya, kike fatan ayi
ma wasu don a auri yaranki. Lallai son kai ya
miki yawa" Ya faɗi yana mikewa, don ya fara jin
kiran sallah.
Kiran sallan ya ki karewa, tun yana Jinsa
daga nesa har yaji na bayan gidansu an kira.
Leman da ya ji yasa ya taɓa gadon da yake
kwance. Jike yake da zufa, da ma ana mafarki
mai tsawo ne haka, shi dai har ga Allah bai
taɓa ko jin labarin mafarki a bayyane kuma mai
tsawo hakaba, tun da ya samu natsuwa da
Agaysha, kalaci kawai yayi barci ya kwashe shi
kafin ya kai ga wanka. Kallon agogo yayi karfe
huɗu da minti biyar, tabbas la'asar aka kira,
shi kuwa wani irin barci ne wannan tun karfe
tara na safe.
Abinda bai sani ba haka kawai Agaysha taji
bata aminta da shi ba, ta sa masa maganin
barcin da take ɗura ma yaranta in suka ishe shi.
Don kar ma ya nemo Halima kafin ta dawo daga
wajen bakanta. Abin tambaya anan shin dama
ana mafarki a barcin da ba na Allah ba ko kuwa
MAFARKIN ABDOUL daban ne. Amsar na
wajenku masu karatu😜
Tashi yayi jiki babu kwari, yunwa yake ji
amma bayi ya fara isa yayi wanka, gami da
alwala. A zaune yayi sallah sannan ya shiga
kitchen ya iske tayi tuwo kafin ta fita. A nan ya
zauna ci hannu baka hannu akushi. Sannan ya
samu karfin gwiwan fita. Gidan Yahai yaje don
ya samu rakiyansa, nan ma ba wani zama yayi
ba suka ɗauki jiki zuwa gidan iyayen Halima.
Bayan an musu iso, sun gaisa da mahaifinta
wanda murna ya hana shi ɓoyewa. Baffa ya
faɗa masa komi dangane da alakar Halima da
Abdoul banda rabuwansu.
Nasiha sosai yayi musu musamman akan aje
mace fiye da ɗaya a gida, mahimmancin hakuri
da adalci. Sunyi murna kwarai da karamcin
dattijan arziki.
Tsoron Abdoul ɗaya yanda Halima zata amshi
Zancensa, hakan ya sa Yahai ya bashi shawara
da ya bi ta hannun iyaye kawai. Yasan dai yana
da fada a wajen iyayenta maza shi yasa ya fara
da mahaifinta.
Bayan tafiyar su Abdoul ya ɗaga waya ya kira
Baffa. Nan ya ke faɗa musu zuwan Abdoul da
kuma yanda suka kwashe.
"shi Abdoul ɗin ne yazo wajenka?" Ya
tambaya cike da mamaki. Dariya yayi sannan ya
bashi amsa da cewa
"shi fa, ko minti uku basu yi da fita ba. Ga
ma tsarabar da ya kawo ma yara nan. Yace
zuwa Asabar kaga jibi kenan zai shigo wajenku".
"Allah ya kaimu, yanzu muka dawo asibiti
Halima har oxygen aka sa mata da muka isa,
mun aza ma rai yayi halinsa sai mommansu ta
nace akan Halima bata rasu ba. Amma
Alhamdulillah har drip ɗin da akasa an cire kafin
in dawo. Ban kira ku ba don bana son hankalin
ku ya tashi ne" hawayen da suka zubo masa ya
goge don ya san da Ace Halima ta rasu ko
iyayenta baza su kai shi rashin ta ba, in bai yi
karya ba ai cewa zaiyi ya fisu sanin wacece
Halima da darajan da Allah ya bata. Samun
irinta sai an tona.
"Allah ya bata lafiya, gobe bayan Jummu@
zamu zo mu duba ta, in kuma an sallame ku
shike nan" Ya faɗi bayan ya gama tunanin anya
a duniya akwai sauran masu riko da zumunci irin
yayansa.
"Toh shike nan, Allah ya baku iko, ya sanya
Alkhairi tsakanin ta Abdoul in babu ya musanya
mana" "kai baffa ba bu ko yar kunyar nan.
Yar farin ku ce fa kar ka bari a ji kana kwararo
addu'a fa" mahaifin Halima ya tare shi da
tsokana, nan sukayi dariya.
***
Ko da su Abdoul suka isa gida Agaysha ta dawo
tayi yan birne birnenta wanda aka tabbatar
mata da in har Abdoul ya shigo gidan toh sai
yanda tayi dashi. Suna gab da shiga gidan
Yahai ya ja shi gefe yace
"karanta addu'ar shiga gida haɗe da suratul
ahad, ba wani jinsi na shaiɗan da zai kasance
tare da kai. Kayi sallama kuma tun daga bakin
kofa kar ma Ace sun rako ka zuwa bakin falo.
Ire iren sakacin nan ke sa tsafi yai tasiri a gidan
mutum. Rashin yin addu'ar fita gida da shigowa
"
Ba musu ya karanta, suka shiga da sallama.
A ciki ta amsa tana yatsine fuskanta kamar taga
kashi. Cikin tsawa ta ce
" Daga ina kake na dawo baka nan" Ta
tambaya kamar wani ɗan ta da take shirin
mazga.
"Gida na ya zo fa gashi na kawo miki shi har
gida, dafatan banyi laifi ba" Yahai yai saurin
amsa mata don ya san kaidinta, Allah kaɗai
yasan tsafin da tayi.
"Auho! Kasan akwai wata karuwa da take
neman rusa mana zaman lafiya a gidanmu,
wallahi na aza wurinta ya je don yau da asuba
sunanta ya tashi da shi a baki, tsoron zuwansa
wajenta na bashi maganin barci a tea, kasan
abinda ya ban mamaki" Ta karasa tana jefa ma
Yahai tambaya, dama ita haka take da son nuna
isa, in tayi abu gani take wayonta ne ya kaita
ga hakan.
"Sai kin faɗa madam"
"ko da na fita kuka yake yana kiran Halima ta
rasu, tsakanin ka da Allah ko a littafi ka taɓa
karanta mutum na barci yana mafarki Alhali
barcin magani ne, nayi Alkawari sai na hukunta
yarinyar nan, duk tsafinta sai na hukunta ta"
Ta karasa tana kara yamutsa fuska kamar
Halima ne a wajen.
"gaskiya shi yasa na gagara yarda da ita, a
sani na ke kaɗai ce aboki na ke so, kwatsam ya
zo min da zancen wata Halima. Allah raba
nagari da mugu, mtsw! Mata basa kyautawa
wai takan namiji su siya wuta da hannunsu, sai
ki ji suna malam malam yoh ko da ayar Kur'ani
akai lakani dashi ai bazai tashi da ga shirka ba.
Annabi ya faɗi su zasu fi yawa a wuta. Kuma
ba komi bane zai kai matan zamanin nan wuta
sai son mallake ɗa namiji. Allah ya shirye ta da
sauran masu yi "
Fuuuuu! Ta shige ɗaki ba tare da ta amsa
aameen din ba. Nan ya ja Abdoul kofar gida
suka tsara yanda komi zai kasance. Ya kara
nanata masa kar ya yarda tasan aikinta bai ci
ba, tunda hutun sa ma ya kare, ya lallaɓa ta
kafin ya wuce.Mafarkin Abdoul 9th
MAFARKIN ABDOUL
©Safiyyah Ummu Abdoul
١٨ .
Ranar Asabar tun da safe Abdoul ya shirya ma
tafiya. Karfe tara Yahai ya iso suka ɗauki hanyar
Niamey. Duk kayan marmarin da suka gitta
mawa sai sun tsaya sun siya. Sannu a hankali
suka isa, hiran da ya ɗau hankalinsu yasa basu
ga wani nisan tafiyar ba.
Sun isa sun taradda an sallame Halima har ta
dan warware. A falon Baffa aka sauke su inda
shi ya fara tarbonsu kafin kowa. Bayan sun
gaisa ne ya kalle su yace
"ko zan san me ke tafe da ku?"
Duk da sunyi mamakin tarbon arziki da suka
samu, amma basu yi tunanin zai jefe su da
wannan tambayar ba. Sunkuyar da ka Abdoul
yayi sai Yahai ne ma da yayi karfin halin tattaro
natsuwarsa ya ce
"Baffa mun zo neman izinin ka ne, don neman
auren Halima"
Shiru ya sake ratsa wajen. Zukatansu nai
musu ki ɗan lugude don basu san ko zai amince
ba.
"Ba zan ce komi ba sai Halima ta faɗi ra'ayin
ta, in ka samu ta amince ka gaggauta turo min
waliyanka, in kuwa bata amince ba ina rokon ka
arziki kar ka sake zuwa min gida, na barku
lafiya" yana kai aya ya tashi ya shige gida.
Sun zauna ma kamar minti goma sai ga
Halima ta shigo da kawarta Shamsiyya Ummu
A, fuskarta a sake, amma ko kallon ɓarayin
Abdoul bata yi ba. Hankalinta gaba ɗaya ta ba
Yahai. Sun gaishe shi, sai shamsiyya ta kalli
Abdoul ta ce
"ɗa na! Fatan dai kana lafiya" da murmushi
mai nuna tsantsan farin cikin an san da zamansa
ya ce
"Mommy ina fa lafiya, nayi zunubi mai girma,
don Allah ki sa baki a yafe min kinji" Ya faɗi
yana marairaice fuska.
Jin duk sunyi shiru ya sa ya fara basu labarin
duk abinda ya faru da ya koma gida har zuwa
mafarkansa da yayi masu ban al'ajabi.
Shamsiyya dai da ka kalle ta kasan ta na cike da
tausayin sa yayin da Halima tayi ko oho, ganin
sun tsare ta da kallo ne alamun suna son ji daga
gareta ne ta muskuta ta ce
"Abdoul mafarki ba gaskiya bane, Allah ne yake
aikowa bawa wasu lamarika daga cikin
buwayarsa, domin ya haskaka masa wata baiwa
tashi wadda zai gane rayuwa da abinda yake
cikinta....
Idan bawa yayi mafarki mai dadi kona ra'ayinsa
sai yayi Sadaka kamar yadda yazo a hadisi
Majma'ul Bahraini cewar "Annabi yace kunemi
yayewar bakin ciki, da bacin rai wajan yin
Sadaka " hardai zuwa karshen hadisin, shiyasa
akeso bawa ya kasance mai yawan addu'a aduk
lokacin dazai kwanta barci, sbd yanayin mafarkin
dazai iyayi, idan mai dadine sai yafadama mafi
kusanci dashi kuma abokin sirri agareshi amin
domin yatayashi rokon Allah nake alheri akan
mafarkin.
Idan kuma mafarkin abin tsorone kokuma tashin
hankali wanda zai haifar da bacin rai, ana so
kana farkawa ka nemi tsari ka tofa ɓarayin hagu
sannan ka chanza kwanciya, shima dai mutum
sai yayi Sadaka yanemi tsari akan abinda yagani
acikinsa, yanemi kuma zabin Allah na alheri akan
mafarkin, yazama mai sirri akansa wajan barwa
cikinsa sirrin mafarkin, tosai Allah yaji
tausayinsa kuma yayi imani tare da tawassali da
Annabi wajan zabin alherinsa.
Wannan bayani kadan kenan daga cikin
abubuwan da Mafarki yakunsa, Allah yasa
mudace da rabo mai amfani adukkan rayuwarmu
Amin. " tana kaiwa nan ta tashi tsam sai zuwa
cikin gida. Dukkansu ba wanda kansa bai ɗaure
ba don a zahiri sun ga tsantsan rashin bawa
lamarin mahimmanci.
Sunyi zugum na wasu yan mintoci chan
shamsiyya tayi karfin halin magana inda ta ce
"Kun san ba lafiya ta cika ba, jiya aka sallamo
ta daga asibiti, mu ɗan ɗaga mata kafa. Ɗa na
kasan dai kai me laifi ne sai ka san yanda zakayi
ka wanke kanka" Duk sukai dariya sannan suka
tambaye ta jikin Halima inda ta amsa musu da
taji sauki sosai. Sun ɗan taɓa hira kafin daga
bisani sukai sallama suka tafi.
Wasa wasa se da akayi wata biyu Abdoul na
zaryan neman sulhu amma Halima ta kafe akan
ba'a haifi namijin da zai wulakanta ta ba, nan ta
maida hankali a aikinta ba ta saurari zancen ba.
Yanzu ma zaune take ya zo, momma ta kora
ta dole taje gare shi, tsayuwa tayi a kan shi,
bata ce masa komi ba. Kiran da taga ya shigo
wayarta ne ya hana mata cewa komi don niyyar
ta kwance masa rashin mutunci . Ɗaga wayar
tayi da sallama. Maimakon a amsa sallama sai
saukar ashar taji, neman tsari take da ga
sheɗan. Faɗin da tayi "Abdoul yafi karfin ki
jaka" nan ta fahimci wacece kuma.
MAFARKIN ABDOUL
©Safiyyah Ummu Abdoul
١٩
Shiru tayi ma wasu dakiku sannan ta ce
"kin kira a sa'a ma, tun ɗazu ya ke jira na
fitowar kenan se ga kiranki, gashi ku gaisa" Ta
karasa tana mai mika masa wayar fuskarta cike
da murmushi.
"macuci, azzalumi, annamimi, wallahi in
baka tuba ba wutan Allah sai ya ci ka" Ta faɗi
tana haki bayan muryarsa ya sauka a dodon
kunninta.
Murmushi kawai ya saki ya katse kiran tare
da kashe wayar gaba ɗaya.
"bani wayata, meye nufin ka na kashe min
wayar gaba ɗaya" Ta faɗi a tsiwace, kallonta
yake yana so idanuwar su su haɗu amma fir ta
ki.
"Ki zauna, magana nake so mu yi" Ya ce
yana nuna mata kujera. Zama tayi babu
gardama.
"Halima, L'erreur est humaine, (ko wani
mutum na tare da kuskure) ki yi hakuri s'il vous
plaît Il faut me pardonner. (don Allah ki yafe
min)" Ya faɗi yana rusunawa. Ganin tayi shiru
ya sa ya cigaba
"Nasan ba a son rai mafi yawa daga cikin
mata ke auren mijin aure ba, burin kowacce
mace ta kasance uwar gida, amma ina zamu kai
kaddarar rayukanmu. Allah ya faɗi a cikin littafi
mai tsarki LIKULLI AJALIN KITAAB, wato ko
wani kaddara a rubuce ta ke.
Ba wai zan aure ki don in cikata giɓin da nake
da shi a gida na ba, kin san dai ina son matata,
toh ba wai zan aure ki don son nata ya ragu
bane, sonki da kaunarki yasa nai sha'awar
aurenki, don in yi bautan Allah in nemi
yardansa. Bayan wannan banda wani dalili.
Bana so in miki karya shiyasa kika ga nayi
shiru akan zancen laifin da nayi Il faut me
pardonner." tsare ta yayi da idanu, burinsa su
haɗa ido amma fir ta ki yarda.
Shiru sukayi na kusan minti biyar, zuciyar ta
na rawa kamar pendulum, chan dai ta tuna isa
da mulki da Agaysha ke Gwadawa akan Abdoul
na ta ne ita kaɗai yasa ta tsaida zuciyarta ta ce
kamar bazata magantu ba
"ka turo ayi magana" Ta na faɗi ta shige cikin
gida. Murna a tare da shi ba'a magana, sai da
ya kira baffanunsa suka tsaida masa da ranar da
zasu je sannan ya bar falon da aka sauke sa.
Itama da ta shiga ciki ta faɗa ma momma
abinda ta yanke ta ji daɗi sosai. Nan suka yi
addu'ar Alkhairi amma kowannensu zuciyar sa
kal da murna.
***
Kamar yanda suka yi alkawari haka suka zo da
zancen neman aurenta. Iyayensa sun yaba da
karamci da halin girma iri na iyayen Halima. An
tsaida auren bayan wata uku kamar yanda
Halima ta roka sanda momma ta tambaye ta.
Tun da lokacin wani sabon shaukin kaunar
juna ya shiga tsakaninsu. In baya gari ko Kasar
suna manne da juna a waya. Agaysha tayi
asirin, tayi tsafin amma kullum lokacin bikin
matsuwa yake duk da bokanta ya tabbatar mata
baza'a taɓa auren ba.
Yau ma ta shirya zuwa maraɗi don ganin
wani boka, sarkarta da ammbasadan Nijar a
Saudiyya ya ba Abdoul ne ta siyar, tayi karyan
zuwa ta'aziyya ta ɗau hanyar maraɗi.
Sanda layi ya kai kanta ta shiga don ganin
sa. Kallo ɗaya yayi mata ya kwaɗaitu da ita.
Nan ya ce mata
"Halima ba ko mi bace face abin da zai
kawata MAFARKIN ABDOUL, yanzu dai ɗan
tsatsuba ya na son ya ji kalan ruwanki, da shi
zai halaka Halima"
" Ruwa kuma ya mai biyan bukatu" Ta
tambaya cikin rashin fahimta.
"eh! Kwaye min wannan zanin in ɗiba" ba
musu ta Kwaye, ta tsorata da ya cire zanin da
ya ɗaura a kugu amma zuciyar ta da ta tuna
mata shike nan kafin ta koma an hallaka Halima
da auren saura mako ɗaya ya sa ta sakin jiki.
A wahale ta fito runbun boka ta sa mu abin
hawa, Gidan kawarta Taghayshuwane ta je, nan
ta huta washe gari ta koma zindar.
Shiru! Shiru tana jiran a ce mata an fasa aure
amma sai shirye shirye ake, ta kira boka yace
shi dai yasan baza'a yi auren nan ba, ta
kwantar da hankalinta ko an taru za'a fasa.
Hakan yasa ta ji sakayau fatanta a fasa ranar
ɗaurin aure don zai fi musu zafi.
BIKI BIDIRI ....
Karfe goma na safen 13 ga watan febweru 2016
a Nijar, Nijeriya, Kamaru da Chadi aka ɗaura
Auren Abdoullah da Halima bisa ga sadaki mafi
karanci.
Anyi shagulgula sosai inda mawakiya Sa'a
Vocal ta wake ango da amarya. Hanifa creations
and couture suka fito da amarya da ango da
zafafan ɗinkuna inda mutane sukai ta santi.
Ranar Lahadi da safe aka yi walima a gidan
ta da ya kama mata a nan Niamey. Agaysha
bata yarda da an ɗaura auren ba sai da aka kai
amarya gidan iyayen mijinsu da maraice sannan
taga sun dau hanyar Niamey. Nan ta ɗau waya
ta aika ma Abdoul sako kamar haka
"Ango mijin Amarya, ina maka murna, na ba
ka wata uku kyauta kasha amarci lafiya"
ko da ya karanta sai da yai dariya a ransa cewa
yake "wannan bata san abinda ke damunta ba"
nuna ma Yahai wayar yayi ya karanta.
"mtswww ! Wasu matan fa na kwafsawa,
akan wani dalili zaki bar ma wata mijinki wata
kawai don ya auro ta da yaudaran kai zata
ginshe shi. In kaga an ginshi juna amaryar bata
iya takunta bane. Ai ta baku daman fahimtar
juna a ne amarya kuma ta kafa gwamnatin ta da
kyau. Aminina kasha amarci lafiya" Ya karasa
suna masu tafawa.
Mafarkin Abdoul 10th
MAFARKIN ABDOUL
©Safiyyah Ummu Abdoul
٢٠
An watse taro Lafiya yan Uwa sun koma
gidajensu lafiya lau sai addu'an zaman lafiya da
aka bi maauratan dashi. Ɓangaren Agaysha kuwa
kawayenta na nuna mata gara da tayi hakan
kafin wata ukun ya wuce za'a tura mata warin
jaɓa da ɓallewan jini. Haka dai sukayi ta
shawara har dare ya tsaga.
Washe gari ma haka sukai ta bata shawaran
da suke ganin zai fishe su, kafin suka watse aka
barta da kunan zuciya. Mafarkin ido biyu ta yini
tana yi, idonta na hasko mata Abdoul ɗinta da
Halima. Tayi kuka kashi kashi, ta yini tana tsine
ma bokayen da sukayi mata aiki, barinma
wanda ta ba jikinta.
Kamar an muntsile ta, wayarta ta ɗauko ta
kira shi don ta ci masa mutunci. Ringing biyu
ya ɗaga.
"mace mai garɗi Uwargidan Abdoul kina
lafiya" Ya faɗa yana kasa da murya, hakan bai
hana ta jin kaurin muryar kamar saukar aradu.
"kasan kuwa an ɗaura auren" abinda bakinta
ya iya furtawa kenan.
"Kinsa kokwanto, baki bada gaskiya akan zan
iya hana auren ba. Aiki da kokonto ai ba zai
taɓa karɓa ba." Ya faɗi daga chan ɓarayin.
"Kokwanto kuma?" Ta tambaya tana zare
idanu kamar yana ganin ta.
"Eh! Ai da kin mika gaskiya, kin amince
zan iya yin komi duk da ba haka ba. Amma bai
yi latti ba, ki samu ki zo sai a tura mata cuta
wanda zai kar da ita har lahira." jin hakan ya
saukar mata da wani farin ciki da bata san daga
ina ya fito ba. Haka dai yai shawo kanta da
zantuka na karfin gwiwa da tabbatar mata da
Halima mai karan kwana ce.
Tunani da kukan da ta yini tana yi ya saukar
mata da zazzaɓi, wasa wasa tana zata ji sauki
ta samu ta leqa maraɗi amma ina sai da tayi
sati kwance. Kullum Abdoul kan kira su sau biyu
ko uku a rana don ya ji lafiyansu, amma tana
ɗauka zata mika ma su Ummu Abeyha wayar su
yi masa magana.
Auren na da sati biyu ya samu zuwa duba
su, nan ya iske duk ta rame tayi baki, da ya
tambayi dalili ne yaji ta yi ciwo, bai tambayi
dalilin ta na kin sanar da shi ba. Dare na yi ta
wuce ɗakin Yaransu ta kwanta abin ya ɓata
masa rai har ya tunkare ta da zancen, buɗan
bakinta kuwa sai cewa tayi
"Ni fa sai munje anyi maka gwaji zan kara
amincewa da kai, ba zaka auro min raguwan
sida sannan in amince maka ba" tana faɗin
haka ta juya baya. Bakin cikinsa ya ninku amma
sai bai nuna ba. A daddafe ya karaci kwanakin
da ya ɗiba zai yi on yazo yayi ya kara gaba.
***
A Ɓangaren amarya da ango kuwa soyayya suke
gudanarwa mai tsafta. Tun da ya amfana da
sadakinsa ya kara jinjina ma Halima, ya san ba
karamin jihadi tayi ba na tsare mutuncin ta. Ace
mace yar shekara ashirin da shida ai dole tana
da sha'awa, zata bukaci abokin ɗebe kewa
tunda dai mutum ce ba dutse ba. Amma yana da
ga cikin jihadi (jihadul nafs) wanda yafi kowane
nau'i na jihadi daraja fin karfin zuciya. Yayinda
mutum yai hakuri, ya danne sha'awarsa har
zuwa lokacin da ba ma sha'awa hakkinsa zai kai
ka ga aljanna ne ba wuta ba shima babban nau'i
ne na jihadi mai babban daraja (ni safiyyah
Ummu Abdoul nace Allah ya kare mu da
zuriarmu daga aikata zina da sauran Alkaba'ir,
Aameen ya rabbi ).
Tun lokacin yake bata wani daraja na
musamman don ta karyata masu bahagon
tunanin duk yar da ta je jami'a har ta kammala
to lallai ta siyar da yan matancinta. Wasu ma
har kauɗin kiransu karuwai suke yi, su kan
manta babu tsattsauran sheda a musulunci
kamar shedan zina.
"banga kaddarar da zai kaini ga auren yar
jami'a ba, balle a ce ta gama har tana aiki, ai
duk ba budurwa cikinsu sai dai budur-budur"
faɗin wani abokin aikinsa. Tsakin da ya ja ne ya
dawo da hankalin Halima wajen shi.
"Sweetyna! Lafiya kake tsaki" Ta tambaya
fuskanta cike da damuwa.
Kallon cikin idonta yake zuciyarsa na ayyana
masa tsarkin da ke tattare da dukkan lamuran
ta,chan dai ya ce
"Ina mamaki ne, yanda wasu mazajen
musamman namu na Hausa Fulani ke jifan
matan da suka yi karatun boko da rashin
tsarki... " nan dai ya bata labarin yanda sukayi
da abokin aikinsa mai wancan tunanin.
"ka ji ka dai sweetyna, wai me yasa mazan
hausa fulanin kuma suke ganin nasu kalar
tsarkin a matsayin ado. Amma fa laifin matan
ne, sakarkaru, su bari ko wani gardi ya taso sai
ya ba gaɓɓai huɗu wahala, kuma su garadan
ganin kansu suke a tsarkaka yayin da matan
najasa.
Duk namijin da kaji yana kiran matan jami'a
ko wa'inda suka Gama a Yan iska toh Allah
sweetyna ya san inda yake haɗuwa da su. Sai
ka ga namiji ya gama sheke ayarsa wai shi a
dole zai ma Allah wayau se ya koma ma auren
karamar yarinya. Hukuncin mace da namiji a
fagen shari'a dai ɗaya ne, duk namijin da yayi
saɓon Allah toh saɓo ne dai dai da na mace,
hukuncin su ɗaya sweetyna" Ta karasa tana
sakar masa wasu sakonni mai gamsar da mai
amsa.
"Allah ya bar min ke Amaryar Abdoul" Ya
faɗi yana sumbatarta a goshi.
***
June 2016
Raywarsu na tafiya gunin ban sha'awa,
Abdoul yayi kiba sosai, haskensa ya fito sosai.
Da gani hankalinsa a kwance ne. Duk sati biyu
yana zuwa zindar yayi kwana biyar, matukar
yana kasan. Agaysha dai kiri kiri ta ki amincewa
da shi, akan sai an masa gwajin sida, yayinda
sai chushe chushe takeyi a jikinta da birne birne
duk don Halima ta mutu.
Sau biyu yaranta na zuwa hutu wajen Halima,
duk suka dawo takan lura da chanjin da take
gani tattare da su, nan ta fara rigimar baya
adalci Halima daɗi ta ke ci.
"Halima aiki takeyi ba ta jira sai na ɓata
kafin ta yi" Ya iya ce mata ya barta nan.
Kwatsam! Wata rana ta je fitsari sai ta ga
kyankyaso a cikin masan, kasancewar ta
matsoraciyar kyankyaso yasa ta tsuguna tayi a
kasa, ta tsorata ainun ganin kalar Fitsarin
kamar jini ga wasu fararen ababenan a ciki
wanda da ta kalla da kyau sai ta ga ashe
tsutsotsi ne.
Ta firgita ainun, kasancewa ya fi sati take jin
azaba yayin fitsari, kuma bata taɓa tunanin in
tayi ta duba ba, tana tsarki take matsa wajen
da zai flushing.
"kar dai Halima ce ta turo mata" wani sashi
na zuciyarta ya faɗa mata.
"ko kuma naki ne dawo miki ba" ɗayan sa
shin mai faɗin ya ce hakan. Shiru tayi duk a
tsorace. Wa za ta kira, gashi ana azumi balle
ta je wajen boka.
Wasa wasa ciwo ya cin magani, tsutsotsin
har fitowa suke, tunda aka je asibiti likita ya ce
sanadiyyar chushe chushe ne ko kuma jima'i da
mai ciwon ko duka ya jawo hakan Abdoul ya sa
ma ransa chushe chushe ne, ya haɗa kan
yaransa sai Niamey, sai de ya turo mata kuɗin
magani in ya samu sarari ya leqo ta don cewa
yake
"kinga ranar zuwa wajen boka"
Sai da su Halima suka je Zindar da sallah
sannan ta iske laluran Agaysha, kwarai ta
tausaya mata nan ta ɗauki alwashin taimaka
mata. Bata yi shawara da kowa ba ta shirya
komawa har da Agaysha kasancewa Abdoul ya
riga su komawa. Da fari taki yarda su tafi tare
sai da ta tambayi kawayenta nan suka zuga ta
akan taje sai ta haɗa mata tuggun da zai fitar
da ita.
Ko da Abdoul ya gansu bai ce uffan ba, don
yana shirin zuwa wani course a Spain. Ba zai
dawo ba sai Satumba.
Nan Halima tayi ta haɗa ta da likitocin mata
gwanaye masana makamin aiki, sannan ita ce
har sako tayi aka haɗa mata magunguna daga
Egypt duk ta haɗe ma Agaysha.
Basa ko zaman hira, iyakansu gaisuwa sai
bayani akan magani in an kawo. Duk bidirin nan
daga aljihun Halima ne hakan ya kara mata
daraja a idon Abdoul.
September 2016....
Fari da kyawun Agaysha ya fito sosai, lafiya
ya samu tana son ta nemi gafaran Halima amma
sam bata ba ta fuska ba, don ko aikin gida bata
yarda ta sa mata hannu ba. Ranar da Abdoul
zai dawo ta ga abin mamaki don shirin da tayi
don tarbansa ko ita da ya yi shekara a France
bata yi masa ba a lokacin.
Da ya shigo gidan kuwa taga abin mamaki,
ita da yara suka tarbo shi tun daga gate,
Agaysha na kallon su ta window, yaran nan fa
ba na Halima ba amma bata yi son kan raba su
da uban su ba. Nan tayi mamakin kyawun hali
irin na Halima.
Sai da ya kintsa ya zauna cin abinci sannan
ta fito tayi masa sannu da dawowa. Ya amsa a
hankali ya dago ya kalle ta, ya girgiza da kyan
da tayi. Sai ka ce kafin suyi aure. Fitowan
Halima ya kalle ta yace
"me kike ba my dear da ta chanza haka"
dariya Halima tayi ta ce
"kace kawai na fita iya kula, ai se Ka biya
kawai"
"Ai gidanki na nan a Aljanna mai babban
daraja" inji Agaysha. Duk sunyi mamaki don
Halima bata taɓa mata abu don ta ce ta gode ba
ma.
Nan ta dage ta roke su gafara, inda ta ke
faɗin ta ga illar boka da bokanci, ta ga illar
zalunci da mugunta. Nan duk suka yafe mata
tare da kara mata nasiha akan tsoron Allah,
wuta gaskiya ce haka Aljanna ma gaskiya ce.
8th October, 2016
Tun a hanyarsu na dawowa asibiti Halima ke
tsokanar su
"Ya kamata ku je honeymoon fa, wata 9
kenan fa rabonku da juna, tab ni dai na yafe har
sai na haihu nayi arba'in" Ta faɗi tana kallon
Abdoul da ke harararta. Asibiti suka je aka
tabbatar da lafiyan Agaysha.
"wai ido kika sa mana ne haka, mu de tsofai
tsofai damu ina zamu kai honeymoon" Ya faɗi
yana kashe ma Agaysha ido.
"meye na kashe mata ido " Halima ta faɗi
tana dariya.
"Halima ba fa rayuwar Abdoul kawai kika
haska ba, har na wa da yaranki. Allah ya sauke
ki lfy ya kara mana kaunar juna"
"Aaameeeen!" suka faɗi su duka...
And they live happily ever after....
Et il vécurent heureux pour l'éternité....
Godiya ta musamman ga Haj. Mas'ouda
Moulaye.
Thank you all for sticking around, MAFARKIN
ABDOUL is neva complete without u. I Luv u all
fisabillillahi.
Contact me via
Wattpad
Ummu-Abdoul
Www.soufjay.wordpress.com


adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *