Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Monday, September 7, 2020

SANADIN KIDNAPPING COMPLETE HAUSA NOVEL

adsense here

SANADIN KIDNAPPING COMPLETE HAUSA NOVEL


🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*SANADIN KIDNAPPING*

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*ZAHRA SURBAJO*


*بسم الله الرحمن الرحيم*


*Kirkirarren labarine,banyishi dan wani ko wataba,dan haka akiyayi juyamin shi ta kowacce siga,duk wanda yayi na barshi da Allah*


*Gani Allah ya nufa nazo muku da wani sabon karatun,littafine daya kunshi abun tausayi,Yaudara,Nishadi,fadakarwa,uwa uba zazzafar soyayya,kubiyoni cikinshi kusha mamaki,dan da yardar ubangiji,babu kamarsa ajerin littattafaina,takowacce siga,comnents dinku shi ze bani kwarin guiwar yinshi akan lokaci,kubiyo yarnufawa domin jin wainar da zaa toya,#nice de dinnan Surbajo for life*


*1-2*


"Who is he?"ya tambaya cikin kakkausar muryar dake nuna tsananin tashin hankali da bacin ran da yake ciki.


jiki na bari,wanda aka tambaya ya matsa kusa dashi ya duka yace.


"Sir,He is a contract killer,he can do anything for Morney"


"Oh God,how can we find him now"ya fadi yana yamutsa gashin kansa.


"Sir the solution is,we have to be very smart first ,dan mutum ne shi me hatsari in aka nuna masa karfin mulki ze iya kashe Sanaya kuma ya gudu batare da anganshi ba"


Se a lokacin matar dake zaune a gefe tana ta shirgan kuka,tace cikin kukan.


"Alhaji,ni ba komai nakejiba,se Sanaya,nawane milyan dari,kayiwa girman Allah kabasu su sakomin yata,kana ganin Yadda hankalin Munaya yatashi sabida rashin yaruwarta"


Shuru yayi yana kallonta,zuwacan yace.


"Ba naki bada kudin bane,kawai inaso naji muryarta ne,to kuma sunki bata wayar tai mgn,amma tunda hakane zan basu,hajiya ki kwantar da hankalinki"


Dubansa yakai gurin me tsaron lafiyarsa yace cikin kakkausar murya.


"After given them the Ransom Morney,you guys i want you to find the person who was behind this kidnapping,if you find him chop him in to tiny pieces,so that no one can recognize him,this is an order"ya fadi cikin kakkausar murya.yana kaiwa nan ya fice Daga falon kamar kububuwa.


Da sauri me tsaron lafiyar tashi ya bishi a baya.


Ita kuma hajiya mikewa tayi ta nufi dakin Munaya domin ta rarrasheta ta samu taci abinci.


*DAJIN KUDARU*


Wani babban dajine me manyan dutsuna,da bishiyoyi,ga duhu,kwata kwata dajin beda kyan gani ko a ido ne,dajin na kan hanyar pambegua zuwa Saminaka.


Wasu gungun matasa ne zaune cikin wani kogon dutse,sunkai su ashirin dukansu babu alamar imani atattare dasu,inka cire daya daga cikinsu wanda ke zaune can gefe rike da bindiga ya takure,


Wata kyakkyawar budurwace zaune a tsakiyarsu sun daureta se kuka takeyi,ko suturar jikinta kawai ka kalla kasan yar manyan masu kudice.


Wani bakin mutum ne mummuna rike da kwalbar giya ya nufeta yana tangadi,sharab ya zube agabanta yana dariya,Hannu yakai ya shafo fuskarta yace.


"kaga wata jar fulawa,gaskiya ko babanki ya bada kudin bazan sakekiba,sena huta ajikinki"yayi maganar cikin muryar maye,


Hannu yasa yana kokarin shafo boobs dinta,ayko a zafafe wannan matashin yataso ya iso gabanshi ya ture yarinyar daga kusa dashi yace cikin bacin rai.


"haba oga ya zaka bata mana ayki,bafa daukota mukayi dan haka ba,kawai mun ɗaukotane dan kudi,to meyasa kakeso kaci mutuncinta?"


Dariya ogan yayi sannan yace.


"kaga shegen yaro,Wlh wannan fulawar se na mata ban ruwa koda so biyune kan ta bar gurinnan,"


Gabadaya sauran dariya suka kwashe da ita,shiko matashin shuru yayi yana binsu da ido,yayinda ita kuma yarinyar ta tsananta kukanta jin abun da ogan yace.


"Wannan ba daidai bane,kuma wlh hakan bame yiwuwa bane,babu wanda ya isa cikinku ya taba mutuncin wannan yariyar matukar ina numfashi"cewar saurayin cikin kakkausar murya.


Wani ne daga cikin sauran yataso da sauri yazo gurin saurayin yace.


"Haba Safwan kasha kwayane,ka tunafa taimako ka nema agurina na kawoka gurin oga,dan kasamu kudin biyawa mahaifiyarka kudin operation din da zaa yimata,shine dan rainin wayo har oga na fadi kana fadi wlh kashiga hankalinka"yafadi yana me nunashi da yatsa.


Cikin matsanancin fushi,yace.


"Don't point your fingers at me or else i will cut them,ina danasanin haduwa dakai hafizu,kar ka kara fushina kasa na saukeshi akanka"


Sanin halin safwan na bakar zuciyane yasa hafiz jan bakinshi yayi shuru.


Sauran dayake abuge suke ba wanda yay mgn,guri safwan yasamu yana huci.


Jan duwawu yarinyar ta dunga yi har tazo kusa da safwan din,Bayanshi taje ta lafe,tana hawaye.


Waigowa yayi yana kallonta,sosai tabashi tausayi,hannu yasa yacire mata plasta din da suka rufe mata bakin.


Muje zuwa.


Surbajo for life.


🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*SANADIN KIDNAPPING*

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*ZAHRA SURBAJO*


*Fatima Abubakar Radda,kina da guri na musamman a zuciyata,ina sonki ina kaunarki,Allah ya dauwamarmin dake cikin farinciki har iya karshen rayuwarki,ya raya mana zuria,Wannan littaffin gaba dayanshi sadaukarwane gareki*


*Auta Inna ibrahim kime😝,ina gaisuwa*


*3-4*


Lumshe ido tayi tana ci gaba da kallonshi hawaye nabin fuskarta.


Daure fuska yayi dan shifa beson raini kuma karma wataran su hadu ta tona masa asiri,dan kallon yayi yawa.


Hannu yasa yaja rawanin dake kan wuyanshi ya rufefuskarsa,Tsab Sanaya ta fahimci manufarsa,ita ko bakomai yasa take kallonsaba,sedan ganin gashi dan iska amman yasan daraja da mutuncin yamace.


Haka suka zauna zugum zugum,har dare yayi,da yake Safwan beyi bacci ba yana gadin sanaya shiyasa da dare yayi yakwanta tunda sauran sun tashi daga baccin buguwar da sukayi.


Oga Jagan shine sunan shugaban kungiyartasu,Jagan mutumne mara imani,beda tausayi ko kadan,inyamurine daga Delta state,


Ya gagari akamashine sabida tsabar asirin dake tattare dashi,amman babu wani state da jagan beje yayi barna ba,contract killer ne shi na sosai,kuma gwanine gurin yin kidnapping,


Haduwarshi da Safwan tasamo asaline daga abokin safwan din Hafiz,wanda ya kasance yaron jagan dinne kuma unguwarsu daya da Safwan.


Mahaifin Safwan ya rasu da jimawa,dagashi se kanwarsa kawai iyayensu suka haifa,suna zaune a unguwar tudun wada dake kaduna.to kwatsam se Allah ya dorawa mahaifiyarsu,ciwon cancer ta nono,


Sun kashe kudi sosai gameda ciwon har mashin dinshi ya siyar amman suk da haka abun ya faskara.


Safwan yayi karatu tundaga primary har zuwa matakin degree akarkashin jagorancin mahaifiyarshi shiyasa yashiga damuwa dan yakasa taimaka mata shima,dan ko ayki bedashi.


Alhaji Khabeer Umar, shine Mahaifin Sanaya,wanda ya kasance kuma shine zababben gomnan jihar Kaduna na wannan lokaci.


Mutum ne shi da beda tausayin na kasa dashi ko kadan,kanshi kawai yasani da iyalinshi.


Cikin ikon Allah se Safwan yasamu Aykin share office din gomna,da taimakon takardunshi,shima yasha wuya kan yasamu,


Sede Alhaji Khabeer irin mugayen gomnonin nanne masu kin biyan albashi akan lokaci,wani sain ma har na wata biyar rikewa yake be biyaba.


Matsalar da Safwan ya fara fuskanta kenan dan ga mahaifiyarshi kwance a gida ba kudin zuwa koda ganin likitane,


Hakannw yasa ya yanke shawarar tuntubar gomnan aduk sanda ya ganshi.


Yau monday da wuri gomna ya iso office dinshi,sabida akwai wasu yan kwangila daze sawa hannu,


Safwan yana sane yaki yin aykinsa da sauri dan so yake yaga gomnan dan inde yasake yafita kan ya shigo to bazaa barshi yashigo gurinsa ba.


Shigowar gomnan keda wuya shida mukarrabansa,Safwan ya nufeshi,da Sauri masu tsaron lafiyarshi suka dakatar dashi.


Cikin kuka safwan yadaga murya yana rokon gomna.


"Don girman Allah ranka yadade kayi mana albashi haka,wlh mahaifiyatace ke gida zata mutu sabida ciwon cancer gashi babu kudin zuwa Asibiti"


Tasowa gomna yayi cike da izza yazo gaban safwan din,yasa hannu ya kifeshi da mari,sannan yace.


"in uwarka ta mutu ba damuwata bace,tunda ba tawa uwar bace,da rayuwar uwarka da mutuwarta ni agurina bata da bambanci da ta karen dake gararamba a titi,bazan biyaka albashi ba,baya ga haka ma na sallameka a ayki,wawa dan matsiyata kawai"


Safwan akwai zuciya,haka yashiga dambe da masu gadin gomnan,har yasamu ya isa gareshi,janshi yayi da karfi ta yadda suka hada goshi,a haka safwan yace.


"Kare irinka,be isa ya ambaci sunan mahaifiyataba,dan haka ko tanzu daka ambata nasan da taka kake ba tawa ba,kuma albashina dole ka biya ni dan bana yiwa karnuka ayki abanza"yana kaiwa nan yasakeshi taga taga gomna yayi kamar ze fadi daga bisani ya tsaya kam.


Tsananin mamakin karfin hali da jarumtar safwan ce tasa gomna kasa bada umarnin a kamashi,koda securities suka bi bayanshi zasu kama,da Sauri gomnan ya tsaida su.


"Ku barshi,zamu gana watarana"cewar gomna yana murmushin mugunta,shide safwan ko kallonsu beyiba,yasa kai yafice daga office din zuciyarshi na tafasa.


Ba komai yasa gomna yace akyale safwan ba,sedan tausayinshi da yaji,dan yasan bakin talaucine ya rufe masa ido har yaci mutuncinsa haka,


Bayan sati guda da faruwar lamarin,jikin mahaifiyarshi ya tsananta dan zuwa yanzu har tsutsotsi ke fita a nonon.


Haka zasu sata agaba shida kanwarshi rahama suna kuka,ga wani arnen wari dake fita ajikinta.


Haka suke kula da ita,kwatsam se Safwan ya hadu da hafixu,inda ya karanta masa damuwarsa ya bukaci daya ranta masa kudin daze kai ummanshi Asibiti.


"karka damu safwan,munada kungiya me kawo mana kudi shafshaf,in kanaso zan kaika gurin oganmu ya taimaka maka,sede da sharadi baa fita acikin kungiyar dan in kace zaka fita kasheka oga zesa ayi"


Da yake soyayyar mahaifiyarshi ta rufe masa ido,kai tsaye ya amince da sharadin,ayko hafizu yasadashi da ogansu jagan.


Hannu bibbiyu suka karbeshi,dan lokacin suna gab da fita wani opretion ne,dubu dari oga jagan yaba safwan,akan yaje yakai ummansa asibitin yazo su fita operation din.


Dan dadi har kuka safwan yayi haka yazo yadauki,Umman da Rahama zuwa asibitin Barau Dikko dake unguwar rimi kaduna.


Be baro gurinba seda yaga ummansa ta samu kulawar data dace,dan likitocin sun shaida masa sede yakaita shika dake zaria,su zasu kula da ira na iya yaune kawai.


Bayan Safwan ya koma gurinsu oga jafan,da.misalin karfe hudu na yamma,suka fita operation din,


Airport suka nufa,domin Ranar ne yaran me girma gomna,twins munayada sanaya ke dawowa daga kasar England .


Sunyi shiri na musamman,dan haka tawagar masu dauko yaran na zuwa,sukuma suka bude musu wuta,kan wani lokaci sega gawarwakin yansanda akasa.


Da gudu twins din suka fice daga mota,kasancewar dare yafarayi dan magribane lokacin kuma gurin ba haske.


Sanaya gudu take ko waige batayi,seji tayi taci karo da mutum,Safwan ne tsaye agurin,dan duk kashe kashen da akayi babu shi agurin,oga jafanne yace yatsaya agurin in wani yazo guduwa ya kamashi,


Sanaya na ganin safwan da gudu tayi bayanshi tana kuka tana fadin.


"Don Allah kataimakeni zasu kasheni"


Murmushi yayi gamida jan hannunta ba musu tabishi,wata mota yasata aciki sannan shima yashiga yatada motar ta fice da gudu daga airport din,yana fita dakarun sojoji na isowa,


Su jagan dakyar suka sha,sojojin basu rutsasu ba,jin jiniya na tashine yasa munaya fitowa daga inda ta boye,tana neman sanaya amman bata ganta ba.


Shiko safwan ko motar ɗayasa sanaya ciki ta oga jagan ce shi yabashi for emmergency,danhaka daita tay amfani gurin guduwa da sanaya.


Ganin bebi hanyar gida da ita bane yasa tafara ihu,ayko parking yayi kamin yakai marabar jos ya fita yasa igiya ya daureta ya manna mata plasta abaki.


Da yake kan akai maraba akwai checking point na sojojine yasa yadanna kan motar ta cikin daji,yadunga tafiya cikin duhun dajin har yafado kan titin daze kaika pambegua,tafiya yake aguje sosai dan haka be jimaba yazo pambeguan dauke kan motar yayi yafara bin daji dan can gaba akwai checking point,da taimakon wayar da sukeyi dasu oga jagan ya isa mahadar tasu lafiya dansu tuni sun jima da isa.


Ba karamin jin dadi sukayiba sanda suka ganshi da sanaya,dan da sun dauka sunyi fitar banza ne.


Acan kaduna ko tuni ankai munaya gida,ansa matakan tsaro akoina dan neman sanaya,hankalin gomna in yayi dubu ya tashi dana iyalinshi,sabida ba abinda yakeso arayuwarshi kamar sanaya itace farincikinshi.


A wannan yanayinne yasamu kira daga oga jagan akan cewa yarsa na hannunsu se ya bada ransom morney milyan dari.


Wannan shine abinda ya faru abaya,labarin ze dora


muje zuwa


surbajo for life.

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*SANADIN KIDNAPPING*

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*ZAHRA SURBAJO*


*Autah Inna ibrahim kime🤣😜wlh dadin kiran sunanki nakeyi me babies face😝*


*Dedicated to Fatima Abubakar Radda*


*5-6*


Safwan baccinshi yake cikin kwanciyar hankali.


Sanaya lallabowa tayi ta matso inda yake kwance,ta dora kanta agadon bayanshi,tana feeling much comfortable in yana kusa da ita duk wani tsoro na kaucewa,dan ita fyade ne bataso ta gwammace ta mutu da hakan ta faru da ita,to ta fahimci baze bari ayi mata ba.


tana kwantar da kanta wani bacci yayi awon gaba da ita.


Oga jagan duk abinda ke faruwa akan idonshine,ganin tayi baccine yasa ya mike yanufi inda take,


daukarta yayi cak,se wani lungu acikin kogon dutsen,ya ajiyeta,yana ajiyeta ta farka,zatayi kuka ya rufe mata baki da plasta.


Nanfa yafara rabata da kayanta,da yake sanaya akwai manyan boobs to sune sukafi daukar hankalin oga jagan,jikinshi har bari yakai gurin son fito dasu daga cikin bra din jikinta.


Sanaya naji na gani bata da ikon hanashi domin adaure take,


Bayyanar boobs dinta awajene yasake dagawa jagan hankali,da sauri ya nutsa fuskarshi a tsakankaninsu,wata sassanyar ajiyar zuciya yasaki sanda yaji laushinsu.


Safwan nacan kwance kamar wanda aka tsikara ya farka,,waige waige yafara yana neman sanaya.


Ganin bata agurinne yasa yamike zumbur ya dauki bindigarshi yafara zagaye cikin kogon dutsen,duk sauran matasan se dariya suke masa.


Yana cikin zagaye gurinne ya iso inda oga jagan yake shida sanaya.zuwa lokacin har ya fara cire kayan jikinshi.


Itako boobs dinta sunyi jajawur sabida matsasu da oga jagan yadunga yi,se zafi suke mata.


Idon safwan na sauka kan boobs dinta da suri ya runtse ido,ya furta.


"Noooooooooooooooooo¡!!!!!!!!!!!"wanda sabida karajinshi har kogon dutsen seda ya dauka duka.


Da gudu ya nufi oga jagan sede kan yakarasa sauran matasan sun taso sun rikeshi.


Duk yadda yaso subarshi sun hana shi,gashi yana kallon yadda boobs din sanaya keshan tsotsoagurin oga jagan yana imagining ace Kanwarsace Rahama awannan yanayin yazeyi.


Wani kukan kura yayi ya kwace daga rukon da suka masa,nanfa yashiga kaimusu duka ta koina,


Fada ake bana wasaba,safwan dukansu yake suna ramawa amman dayake azuciye yake ko ji baya yi.


kan wani lokaci tuni,ya musu likis,wani irin tsalle yayi wanda har se da yayi tambul asama sannan ya dira akan gadon oga jagan.


Hannu yasa ya kamo hannayen dake matsa boobs di ya banƙaresu baya jikake kas,sun karye🤣


Dagashi yayi ya mikar ashi ya rike kanshi yadunga bugawa ajikin dutsen seda ya tabbatar da babu wani sauran hakori da yayi saura abakin sannan ya kyaleshi.


Hannu yasa ya kinkimi sanaya yasata akan kafadarshi,ya dauki bindigarshi,yayi nufin ficewa daga kogon da ita


oga jaganne wanda yake cikin mawuyacin hali dakyar ya iya furta.


"Don't let him go free"Ayko nanfa sauran yaran suka mike suka dauki bindigoginsu,suka mara masa baya.


Gudu yake da Sanaya akafadarshi,yayinda yaran oga jagan keta harbi da bindiga,tsananin karar harbinne ya haddasawa sanaya sumewa,


hak yake gudu da ita,hannunshi daya yana harbi dashi,


Duk wanda yasan dajin kudaru yasan dajine da har yanzu akwai ragowar mugayennamun daji dasukai saura aciki.


Safwan bedamu da kallon gabanshiba bayanshi kawai yake kallo yana harbi.


cikin saa wani daga cikin yaran oga jagan yasameshi da harsashi akafa,


Dagashi har sanayan wanwar sukai akasa,azabar da yaji bazata misaltuba,kwance yake rike da kafarshi,daidai lokacin akayi wata walkiya.


Idonshine ya hango masa sanaya kwance kasan wata shirgegiyar kasa,ta fasa kai tana shirin yin kalaci da sanaya,wacce alokacin tafarka daga suman datayi ganin macijitarne yasa tasake komawa suman,a raina nace tokode irin abunnan na kanawa tayi damacan wato likimo🤣😝.


Wayyo safwa,waigawa yayi ya hango yaran oga jagan sunkusa tarad dasu,wanda yasan in suka zo kasheshi zasuyi su tafi da sanaya,suyi abunda suka ga dama da ita


Tofa,ga sanaya kasan macijiya kasa,ga harbi a kafar safwan ga yaran jagan sunkusa cinmusu,koya zata kasance?


Muje zuwa


Surbajo for life.


🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*SANADIN KIDNAPPING*

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*ZAHRA SURBAJO*


*Ruqayya Hassan gaskiya kinsani nishadi,narasa bakin gode miki,Allah yasakamiki da alkhairi yasa kifi haka,Allah ya bani ikon kwatanta abunda kikamin,ngd ngd ngd,ilove you so much more my sis,just keep burning the light,the sky is your limit,#me laya kiyayi me zamani♥♥♥♥♥*


*Dedicated to Fatima Abubakar Radda*


*7-8*


Waige waige kawai yakeyi yama rasa abunyi,hannunshine ya sauka kan wani dutse kato,ay beyi kasa aguiwaba ya dauki dutsen


Be saukeshiba se akan macijiyar,take kan macijiyar ya fashe,jini ya zuba jikin sanaya,wanda yasanya ta farfado.


Ganin gawar macijiyar ajikintane yas ta kwalla wata kara wacce ta sanya yaran oga jagan fahimtar inda su sanayan suke,


Ganin sun nufo gurinne yasanya Safwan yamike da kafa daya yana dingisa dayar ya dauki sanaya wacce gaba daya afirgice take,yaci gaba da gudu da ita.


Tuni yaran jagan suka hange shi,dan haka mara musu baya sukayi,


Haka sukai ta gudu cikin dajin Allah,har suka iso bakin wani  kogon dutsen,ayko safwan wuf yayi ya fada ciki,batare da tunanin koma meye aciki ba.


Suna shiga ya sauke sanaya suka labe ajikin dutsen,yaran jaganne suka karaso gurin,daidai bakin kofar shiga kogon suka tsaya,suna nemansu.


Sanaya jin wani tayi me sanyi yana bi mata kafa,ayko azabure tafara diddire kafar,gamida daka wani uban tsalle ta makale kafadar safwan ta kankameshi jikinta na bari.


Hannu yasa ya gyara mata zama ajikinshi gamida tallafe mazaunanta gudun karta fado🙊.


Sanaya sake shigewa jikinshi tayi dan sanyin dake gurin yayi yawa harma yafi na waje,hakanne yasa ta dora kanta akan kafadarshi gamida sakala hannunta awuyanshi.


Hakanne yabawa kirjinsu damar haduwa irinta no gab,Safwan jin da yayi abu me laushi na taba kirjinshine yasa yakai hannu danjin komeye,an be zaci boobs din Sanaya bane.


Yana kai hannu da sauri yasaki,sabida fahimtar ko meye da yayi,itako sarkin tsoro batamasan yayiba,addua kawai take akan Allah yafiddasu.


Yaran jagan sunkusa awa guda agurin,sannan suka wuce,jin motsin wucewarsune yasa Safwan fitowa daga ramin koramar da ya shiga batare da yasani ba,wanda da yayi gaba ba makawa cikin ruwa zasu fada.shiyasa sanyi yayi yawa agurin.


Cikin sanda yake tafiya,dauke da sarkin tsoro dake kankame ajikinshi,Sannu a hankali yake tafiya zuwa lokacin jiri yafara daukarsa sabida raunin kafarsa,jinine kawai ke fita,har yafara barin cikin duhuwar dajin,yafara zuwa gurin gonaki.


wani ginin daki guda daya ya gani a cikin wata gona wadda yasan na masu gonarne suka gina sabida in sunzo aykin gonar.


mukulli yagani ajikin kofar sanda ya isa bakin dakin,so yayi yasauke sanaya dan ya samu damar balla mukullin amman inna kankamo🤣 fafur taki sauka,karshema kuka tasa tana fadin.


"wlh bazan sauka ba,nide bazan saukaba"


Harda kara makalkalewa,kyaleta yayi ahaka yayi iya dabararsa ya bude kofar,suka shige.


maida kofar yayi ya kulle,sannan yafara laluben abinda ke cikin dakin.


Wayarshice tai kara,wanda dagashi har sanaya seda suka firgita,wanda shi sam bema dauka wayar n jikinshi ba,dakyar yaciro wayar,yaga rahama ce ke kira.


Dakyar ya dauka,yana dauka yaji ta rushe da kuka tana fadin.


"Yaya safwan kazo umma zata mutu,wayyo Allah na shifa uku don Allah kazo"


Tashin hankali baasa maka rana,zaman dabaro safwan yayi,wasu hawaye na biyo fuskarsa,cikin kuka yace.


"Rahama,bazan iya zuwa ba wlh yanzu haka harbine na bindiga a kafata,gashi ina guri me hatsarin gaske,don Allah kisawa umma wayar akunnanta nai mgn da ita bazata mutu ba da yardar Allah"


Umma dake cikin mawuyacin hali,dama tunda taji Rahama ta ambaci sunanshi take mata alama data bata wayar.


Samata wayar tayi akunne tana kuka,


Dakyar umman ta furta


"Safwanullah kana ina?"


cikin kuka Safwan yafara yimata bayani,br boye mata komaiba ya sanar da ita duk abinda ya aykata.


Cike da tausayin halin da ya jefa kanshi sabida soyayyarta tace masa.


"Karka damu safwan,ni Allah yayi ba rayayyibace,yar mutane daka dauko lfy kayi kokarin sadata da iyayanta lfy,karka bari acutar musu da ya,na yafe maka dana,Allah yayi maka albarka,ka kula da rahama,safwan daka aykata mummunan ayki dan sama muku abinci gwanda kabari yunwa ta kasheku,kamin alkawarin maida yarinyar nan gida"ta karasa mgn cikin haki daya taso mata.


Tunda ta fara mgn safwan ke kuka sanaya na tayashi dan tanajin duk abinda umman ke fadi.


"Umma naimiki alkawarin maidata gida cikin koshin lfy,karki mutu umma da safe zanzi nakaiki asibitin shikan don Allah umna ki rayu damu karki tafi ki barmu"


"Allah yay muku albarka"itacr kalmar data fito abakin umman,safwan najin sanda take kalmar shahada,zuwacan yaji sautin ihun rahama na kiran doctor ko baa fada masa ba yasan umma ta amsa kiran Allah.


Sharaf ya zube ajikin sanaya dake nanike da jikinshi wacce inbanda kukan tausayinshi babu abinda takeyi,koda ta tabashi babu numfashi atattare dashi.


Muje zuwa


Surbajo for life.


🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*SANADIN KIDNAPPING*

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*ZAHRA SURBAJO*


*Aisha Yar'aduwa natayaki murnar kammala book dinki me suna matar babana,Allah yakara basira sis naji dadin sadaukarmin dashi da kikayi ba kadanba,Allah yasaka da alkhairi yasa kifi haka,banji dadin cewa kindena book da kikayiba,pls sisto aduba kokenmu aci gaba😭😭😭*


*marubuciyar kawalli surbajo da marubuciyar beautiful zahra,naga books dinku ngd Allah yasaka da alkhairi yasa zumuncinmu ya dore,ngd sosai,ana mugun tare*


*Dedicated to Fatima Abubakar Radda*


*9-10*


Ihu sanaya tayi tashiga jijjigashi,amman ko motsi bayayi,wayarshi ta dauka ta kunna fitila ta haska dakin ba ruwa babu alamarsa.


Kuka take kashirban harda majina,tsoronta kar ya mutu ya barta,tunanine ya fado mata na cewa itafa doctor ce,hakanne yasa da sauri ta duka ta hade bakinsu guri guda ta shiga hura masa iska.


Sannu a hankali iskar ke shiga huhunsa ba jimawa yafara numfashi sama sama har numfashin ya daidaita,sam sanaya bata lura ya fara numfashi fa,ta dukufa gurin hura masa iska,jin taki dainawane yasa shima data hura ya huro mata,saurarawa tayi taji daga ina aka huro mata,sake yi yayi danta kauda tantama,


Dagowa tayi tana kallonshi gamida gyara gashin kanta me uban yawan daya musu rumfa sanda ta dukar da kanta.


Da sauri ta mike cike dajin kunya,shiko ya kasa koda mikewar halin rasuwar mahaifiyarshi shi ke damunsa,ga ciwon kafarsa dake damunsa.


Yana kwance inbanda hawaye ba abinda yakeyi,tabbas rayuwarsu nacikin wani hali na rashin ummansu,


Sanaya shuru tayi itama tana tayashi kukan,idonta ne ya sauka kan kirjinta,wata wawiyar kara ta saki gamida sa hannu ta kare.


Duk bidirin da akeyi se yanzu ta lura da babu riga ajikinta,gaba daya kunyace ta kamata,ashe haka ya daukota daga gurin oga jagan batare daya dauko mata rigar taba.


Safwan kallo ya bita dashi gamida mikewa dakyar ya zare rigar jikinshi ya mika mata.


Da sauri ta amsa ta saka,har lokacin bata dena jin kunyarba.


Haka suka kwana dashi da ita adakin,a takure,yayinda ita tasha baccinta,shiko yana zaune kafa tasashi agaba


Da garin Allah ya wayene,sanaya ta lura da wukake masu kama da aska dake rataye ajikin bangon dakin,da sauri ta saukosu,dukda bata da garanti gameda tsabtarsu amman yazama dole ta taimaka masa dan yasamu sassauci.


Alokacin bacci ya fara daukarshi,matsawa tayi kusa dashi ta kafa kafar dake ciwo,tashiga kokarin ciro masa bulƙet din da aka harbeshi,


Azabar data ratsashine yasashi yatashi afirgice,da sauri ta dago tana dubanshi,fahintar abunda takeyi yasa ya koma ya kwanta ya runtse idonshi ita kuma taci gaba.


Wayyo azaba haka safwan ya daure,ita sanayan dake cirowan itace ke kukan,ahaka tasamu ta ciro masa da kyar.


jini ne yafara zubowa da sauri ta yagi kasan rigar data saka,ta daure masa kafar,


wani zazzafan zazzabine ya rufeshi,rasa yadda sanaya zatayi tayi,gashi tana tsoron bude kofar,karta bude taci karo da wani abun.


Dataga de ba sarki se Allah dole ta bude,safiyace itatuwa se kadawa sukeyi, ahankali tasa kanta waje.


Ganin ba kowane yasa ta fice daga dakin gamida jawo kofar.


ta fara tafiya kenan taji sautin tahowar mota,da sauri ta boye bayan wata bishiya,


Bin mitar tayi da kallo se taga tayi parking,ba jimawa se taga na ciki sun fito sun bude bayan boot sun fito da ghana must go guda biyu sun ajiye agurin,gamida kiran waya dataga dayan yayi.


"Hello,ga kudin fansar sanayan nan ankawo,dan haka kuyi hanzarin sakota don Allah muna bakin titi muna jiranta"yana kaiwa nan ya kashe wayar,suka juya suka nufi mota.


Da gudu sanaya ta fito zata bisu,se kuma ta tuno da Safwan,tsayawa tayi chak,tana kallonsu har suka bace.


Jikinta na bari ta isa gurin kudin,da kyar ta iya daukar jakunkunan,ta ruga zuwa dakin da safwan yake.


A firgice ta shiga dakin ta maida kofar ta rufe se zare ido,take.


Dagowa yayi da kyar yana kallonta,gamida mikewa da kyar.


A rude tai masa bayanin komai,shuru kawai yayi yana tunanin abinda ya hanata binsu bayan tasan ita suke nema.


Haka suka wuni gurin bame cewa kowa komai,har yamma tayi hankalin safwan nagurin gawar ummanshi,da rahama,ga yunwa da sukeji shida sanaya.


wani buhu yagani cikin dakin da sauri yasata ta bude srga dankalin hausa aciki.


ay daga shi har ita haka suka haushi da ci ba kakkautawa.


Suna tsaka  Da cinr suka fara jiyo karar harbi gamida karar helikwafta a sama a firgice sanaya ke kallon safwan wanda shi ko ajikinshi.


Tawagar gomnane dama yacr in jamian tsaro sukaji shuru baa sakotaba subude wuta,


Kamin wani lokaci tuni ankamo yaran jagan dashi kanshi,koda aka nemi sanaya,cewa sukai safwan yamata fyade kuma ya gudu da ita.


Afkawa jamian tsaron sukayi cikin dajin nemansu kokadan basu kawo suna cikin wancan dakin da suke hangowa ba


Acan daki ko fada akeyi tsakanin sanaya da safwan.


"kifita kibi yan uwanki"cewar safwan cikin fushi.


"don Allah ka kyaleni,wlg bazan ita tafiya na barka ba,kana bukatar taimako,pls kabarni tare dakai"


"bana bukatar taimakon ki ki fice kawai nace"


Kuka tasa masa tana rokonsa yabarta amman fafur yaki yarda,daga karshema wurgata waje yayi da kudin uban nata ya kulle kofar.


Komawa yayi ya kwanta yana cigaba da kukan rashin ummansa,hadarine ya taso me karfi iska se kadawa takeyi,ba jimawa ruwa ya tsuge kamar da bakin kwarya.


Wundon dakin a bude yake dan haka feshin ruwa na shigowa,yayi iyayinsa ya kulleshi tacikin dakin avbun ya gagar dan haka bude kofar yayi da nufin kulle wundon.Sanaya yagani t

saye cikin ruwa ya mata shegen duka se kuka takeyi.


Sosai ta bashi mamaki,kulle wundon yayi sannan yasa hannu ta janyota zuwa cikin dakin ita da kudin.


muje zuwa.


Surbajo for life.


🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*SANADIN KIDNAPPING*

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*ZAHRA SURBAJO*


*My Humy luv ga gaisuwarki,ina sonki irin sosai dinnan,ina yinki sisto Allah yabarmin ke kijima ki karko,Allah yakara basira Surbajonkice for life♥♥♥pls kimana typing🙏😝😝in yaso ni nayi me wuyar wato posting😜*


*Dedicated to Fatima Abubakar Radda*


*11-12*


Sumi sumi ta shige dakin se digar ruwa takeyi,guri ta samu ta tsuguna.


Haka kawai ran safwan yadunga masa daci sabida dukanta da ruwan yayi.


"Baki da hankaline zaki tsaya awaje ruwa na dukanki?"ya tambaya rai abace.


Jikinta har bari yake ta duka agabansa tace.


"Don Allah kayi hakuri,kaine ka koreni ni kuma bazan iya tafiya na barka ba,kuma alkawari kayiwa umma cewa har gida zaka maidani lfy,"tayi mgnr hawaye nabin fuskarta.


Shuru yayi yana kallonta,wato ya fahimci yarinyar irin tabani kaga sarkinnance,wato shagwababbiya ta ajin farko,dan ya lura kuka ba wani abu bane me wuya agurinta.


Maganartace ta dawo dashi daga tunanin da ya tafi.


"In har ka yarda bazan cutar dakai ba kabani aron wayarka inyi kiradon Allah"


Ba tare dayayidogon tunani ba yamiko mata wayar.


jikinta na bari,ta amsa tasaka number  munaya,ta jima tana ringing kamin munaya ta dauka.


"karki kira sunana ko kiyi ihun murna,sanaya ce"cewar sanaya.


Zumbur munaya tamike zaune,ji take kamar amafarki,sanaya na kiranta,cikin kuka da zakuwa tace.


"My Sweetheart kina inane don Allah?"


"Ba shi zaki tambaya ba,yanzude nan da awa biyu inason ganinki a cikin dajin kudaru,kitahomin da abinci da kayan sawa both maza da mata,sannan kitahomin da first aid box da drip da da da da😊"


"are you mad sanaya how can i do so,ni na kawo kaina halaka,,pls tell me ina kike ina kuma gayen da ya miki fyaden?"


Sosai batun yaba Sanaya mamaki,amman setace mata.


"in har da gaske kina sona,kizo kisameni kamar yadda nace,inkuma kika bari wani yasan munyi mgn nidake babu yafiya har abada"kit ta kashe wayar tana share hawaye.


Munaya tuntsurowa tayi daga kan gado ba shiri,da yake doguwar rigace ajikinta takalmi kawai ta zira,ta dauki key din motarta,cikin sanda ta nufi dakin sanaya,ta dauki kayanta tasa ajaka,sannan ta fito ta nufi part din yan ayki,abinci tasa suka hada mata me rai da lfy,a kuloli.


Daki ta koma ta dauko first aid box din sannan ta nufi parking space,bude motar tayi ta zuba kayan aciki sannan ta shiga ta tada.


Masu tsaron lafiyartane suka nufoto da gudu,da sauri ta dakatar dasu da cewa.


"gidan naigbours dinmu zan shiga,no need ku biyoni"tana kaiwa nan taja ta fice a gidan da mahaukacin gudu.


Lekawa sukayi sukaga tadau wata hanyar dabam,da gudu suka kira dad dinta suka sanar dashi,


Ayko gurin sakkowa daga stairs har gangarowa yayi sabida tsabar kidima,tsawa yadunga dakawa masu tsarin gidan,inda yabasu umarnin binta abaya.


Munaya gudu take bana wasa ba,dan tuni ta tsaya awani pharmacy tasai sauran kayan,gamuda kayan mazan da sanaya ta bukata.


Tafiyar awa daya da rabice ta sadata da dajin,da yake yamma ce yasa tashiga cike dajin tsoro.


Wayar da sanaya ta kiratata shiga kira,nanfa sukaita mata kwatance,tasha wuya kan ta gano wannan daki.


parking tayi ta fito taje ta fara kwankwasa kofar gamida kiran sunan sanaya.


Da gudu sanaya ta bude kofar ta rungumeta tana kuka.


cikin dakin suka shiga inda safwan ke kwance kafa ta kumbura tayi suntum😭


Cike da mamaki munaya ke kallonsu.


"sanaya waye shi,me kukeyi anan?"


"Shine wanda ya ceceni daga halaka,nan shine inda muka fake"daga haka ta kwashe komai daya faru ta shaida mata.


Sosai munaya take kuka na tausayin safwan,shide kallonsu kawai yakw,yana mamakin tsananin kamanninsu.


 

Abincin sanaya ta fito dashi,ta taimakawa safwan yatashi,ta shiga bashi abaki,tana hawaye,cin abincin yake ayunwace,har seda ya koshi.


Munaya dakw gefe tuni ta fara kukan tausayin yaruwartata,dan duba daya taimata ta gane ta fada tarkon son wanda bedace tasoba.


seda yaci ya koshi,sannan suka hadu su biyu sukai masa dressing kafar tasa yasha azaba,dan har ihu seda yayi,munaya ce karfin aykin dan sanaya inbanda kuka ba abinda takeyi.


Allurar bacci munaya tai masa,sannan ta daura masa drip,tuni ya bingire agurin yana bacci.


da sauri munaya ta kama hannun sanaya tace 


"to taso mu tafi gida,sanaya nan gurin bedace dame matsayi irin naki ba"


"wlh sis bazan fito adajinnanba hat se ranar da hero yaji sauki,da kanshi ze kawoni gida dan haka kitafi kawai ngd da taimakonsa da kikayi"


Duk yadda munaya taso tafiya da sanaya dole ta hakura ta tafi ta barsu,


A hanya taci karo da wanda aka turo nemanta dan haka rankayawa sukai zuwa gida tare.


Muje zuwa


surbajo for life.


🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*SANADIN KIDNAPPING*

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀




*ZAHRA SURBAJO*



*Where are you my other half🗣Hauwau Muhammad Danjuma N,B,S,?here is your page,thanks for the visit,i hope you arrived home safely,Surbajo love you so much,always remember this my sweetheart,Don"t cry in Love coz 4 whom u r crying does not deserve ur tears & the person who deserves it will never let u cry!!!ana uhibbuki hubban shadidan,my suruka(Amaryar yusuf)♥♥♥♥♥♥♥♥♥🤝*


*Dedicated to Fatima Abubakar Radda*



*13-14*



Haka sanaya taci gaba da kulawa da safwan,tare da taimakon munaya dake kawo mata ziyara a boye.


ko kadan kulawar sanaya bata burge safwan,shi burinshi yasamu sauki ya maida ita gaban iyayenta kamar yadda yayiwa mahaifiyarshi alkawari.


Kimanin sati guda kenan,jamian tsaro kullum cikin neman safwan suke da sanaya,amman koda wasa basu gansu ba.



Zuwa lokacin kafar safwan tayi sauki,dingishi kawai yakeyi shima ba sosai bane.



Sanaya ce zaune ta takure agefe tana kallan safwan yana waya da rahama,sosai yake burgeta,musamman dan karamin bakinshi,kamar ba namiji ba.



Batai auneba har ya kamata tana kallonshi,da sauri ta dauke ido ta fara soshe soshe alamun jin kunya.


Mikewa yayi ya dauki jakunkunan kudin,ya fitar dasu waje sannan ya leko yace mata batare daya kalleta ba.


"uwar yan kallon kwaf,seki fito mutafi"


Mikewa tayi jiki asanyaye dan ko be fada mata ba tasan gida ze maida ita.


fitowa tayi tana turobaki gaba,tana shirin yin kuka,


shiko ko ajikinsa haka ya dauki kudin suka kama hanyar da zata sadasu da bakin titi,


sundan jima suna tafiya kan suzo bakin titin,shatar mota ya daukar musu zuwa kaduna,har lokacin sanaya bakinta a ture yake.



Sun iso kaduna lfy,inda kai tsaye unguwar rimi suka nufa inda anan gidan nasu da sukafi rayuwa aciki yake.



isarsu tayi daidai da fitowar gomna zashi gidan gomnati dake kashim ibrahim house.


Sanaya ce ta fito sannan safwan,akan idon mahaifinta hakan ta faru,a gigice,yacewa direba ya faka.


Tun kan agama tsaida motar ya fice,dama tuni masu tsaron gidan sun kama safwan,


da gudu sanaya tayi jikin mahaifinta tana kuka,runfumeta yayi kam kamar zaa kwace masa ita.



Janta yayi zuwa cikin gida,yayinda yabada umarnin a shigo da safwan.


Nanfa hayaniya ta kaure,dan safwan ware kwanji yayi ya kwace daga rukon da aka masa.


takawa yayi yaje gaban gomnan,ya finciki hannun sanaya,ya kamo na gomnan yasa aciki yace afusace.


"Banyi fatan,sake saka a idona ba firauna,ga yarka nan nadawo maka da ita cikin aminci,ashawarce kadunga adana duk abinka dakasan yanada muhimmanci,dan nan gaba in na dauka bazan dawo dashi ba" 


Daukeshi da mari gomnan yayi,sannan yace cikin fushi.



"dama kaine karen daya ketawa yata mutunci?kaine karen,daya hana iyalina sukuni?dole na hukuntaka daidai da abinda ka aykata"



"karnukan zasu kara yawa,da zaran nazo gidanka akaro na biyu na kara yin haushi"cewar safwan,ya juya a fusace ze bar gurin.


"hey dakata dan samari,ay ban sallamekaba,zaka bar gurinnan ne kawai idan nai maka umarni"cewar gomna.


Batare daya waigoba ya bashi amsa.


"sanda nazo ba umarninka nabiba,dan haka zan koma vatare dana jira umarninkaba,in kuma akwai wanda kake tunanin ze tsaidani inason ganinshi"



Nuni gomna yayi da hannu kawai,ay kan kace kwabo tuni sojoji sunyi kan safwan.


Da wata razananniyar kara sanaya tace musu.


"ku dakata!!!!!"


Cak suka tsaya,takawa tayi taje gurin safwan din,tana zubar hawaye,ta duka agabansa tace.


"kai namijine safwan,kayi rawar gani a rayuwata,bazan taba mancewa dakaiba,don Allah ka manta da abinda ya faru,sabida kar ko nan gaba in nemi alfarma agurinka ka kasa yimin sabida laifin babana,katafi cikin aminci babu me tabaka"



Shuru yayi yana kallonta,daga karshe yasa kai ya fice daga gidan batare da kowa ya tankashi ba.


mikewa tayi da gudu ta nufi jikin mahaifinta tana kuka,rungumeta yayi,ya nufi cikin gidan da ita,mahaifiyartace ra taso da gudu ta rungumeta,tana hawayen farinciki.



Kamin wani lokaci tuni gida ya cika da yan uwa da abokan arziki sunzo tayasu murna,ba abinda yafi va gomna mamaki kamar ganin kudin da aka dawo masa dasu baa taba ba.



Acikin masu zuwa murna harda Shaheed yaron abokin daddy,wanda aka tsaida mgnr aure tsakaninshi da sanaya,sabida son juna da sukeyi.


Ada un akace ga shaheed,sanaya rasa inda zata sa kanta takeyi dan murna,dan so tari kan yafito daga mota,tuni ta isa gareshi.


Sabanin yau,da tanajin muryarshi ta lumshe ido alamun bacci takeyi.


Shigowa yayi cike da murna,gaba daya yayi baki ya fada sabida rashin sanaya,ko yanzu ma doguwar rigace kawai ajikinshi ya nƴfo gidan.


Kusa da ita yaje ya zauna yana kallon yadda ta dan rame gamida yin duhu,jiyayi ranshi ya baci,gamida tausayinta daya kamashi.


hannu yasa ya shafo kanta,ya furta a hankali.


"i miss you my pretty,nagodewa Allah da kika dawo cikin koshin lfy"


duk abinda yake sanaya najinshi Tade yi shuru ne,dan ita yanzu ko kallonshi bata son yi🤔



muje zuwa



kuyi hakuri na rashin jina tsawon lokaci, nayi bakine daga gida,so na basu dukka lokutanane,yanzu zaku ci gaba da ganina akan kari ngd



Surbajo for life


🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*SANADIN KIDNAPPING*

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*ZAHRA SURBAJO*


*Gaida me gaisheka ko baze amsa ba,my Bilyn shantali,wannan shafin nakine,ngd sosai da yadda kike bin rubutuna kuma kike fahimtar bambacin dake tsakanin nawa dana saura,ina sonki bily Allah yabarmu tare*


*Dedicated to Fatima Abubakar Radda*


*15-16*


Haka ya gaji da zaman jiran ta farka ya tafi,amman badan ransa yasoba.


Yana fita ta farka,tabi bayanshi da kallo,runtse ido tayi hawaye nabiyo fuskarta,na tausayinshi,dan tasan yana sonta,ita kuma yanxu ba sonshi aranta.


Safwan yana barin gidan gidansu ya nufa,inda yasamu kawunnans na kauye sune sukazo suka sallaci gawar ummansa suka mata sutura.


Yau sadakar bakwai shiyasa yasamesu a kofar gidan,suna ganinshi sukayo kanshi da tambayoyi.


"safwanu ina ka shiga tsawon wannan lokacin?"cewar kawunsa.


Kasa mgn yayi kawai se yasa kuka,nanfa sukayo kanshi da rarrashi,dan sosi ya basu tausyi.


Rahama na ganinshi da gudu tajeta rungumeshi,tana kuka,ranar mutuwar sbuwa ta dawo.


Koda aka rkashi kabarin umman be baro gurinba se da magrib,yana ta kuka gamida yi mata addua.


Haka rayuwa taita tafiya har akayi sadakar arbain din ummansa,yana fita yayi aykin karfi dan yakawowa rahama abinci ko kadan be barinta da yunwa.


A nashi  bangaren kuma gomna yasha alwashin se yaga bayan safwan,dan beci bulus ba,yanajin tsanar safwan a zuciyarshi kamar yadda bawa ya tsni mutuwa.


Sanaya rabuwarta da safwan yasa ta koma so silent,in banda tunaninshi ba abinda takeyi,a nsu tunanin iyayenta da gaske ne safwan yamata fyade,shiyas mummyn ta ta maida hankali gurin dirka mata magunguna domin rufuwar asirinsu


Sanaya ce rike da wayarta,ta buga uban tagumi,tanaso ta tuno wani abu.


zuwa can naga tayi saurin fara danna numbobi a wayar tata,ba number kowa tasa ba seta safwan.


wacce ta jima da haddaceta tun suna daji.


bugu daya biyu ya daga.


"slm wa ke mgn"ya fada batare da damuwar komaiba.


Jin muryarshi ne ya haddasa mata bugun zuciya,da kyar ta iya cewa.


"Hero sanaya ce"ta fada a tsorace.


Mamakine ya kamashi,na inda ta samu number shi.


batare da mamakin komai ba yace.


"oh sanaya,sannunki ykk"


Tunda sanaya take bata taba jin bakin da ya kira sunanta daidai ba kamar safwan,runtse ido tayi wani farinciki na ratsa ta.


"lfy launake,ya dadin hakurun umma?"


"mun gode Allah"


"Allah yajikanta"


"Amin"


Shuru ne yabiyo bayan hakan.


zuwa can de ta sake cewa.


"ina rahama?"


"Tana gida"ya bata amsa.


sake rage murya tayi sannan tacd.


"kai kuma kana ina?"


"ina gurin kasuwanci na"


"wanne irin kasuwanci"ta tambaya .


Tambayoyinta sun fara isarshi dan haka cemata yayi.


"ngd ko sanaya,se anjima"kan tayi mgn ya kashe wayarshi.


kifewa tayi akan gado tana share hawaye,tabbas tasan safwan baya sonta,amman ita kuma shine rayuwarta,zatayi duk me yiwuwa wajen ganin ta mallakeshi🤔


Tana kwance tana kukanne kuran shaheed ya shigo wayarta,a fusace ta dauki wayar tace.


"To uban yan naci,me kake nema kuma?"


ita kanta batasan sanda mgnr ta fita a bakinta bs,shiko shaheed wayarcr ta kusa faduwa a hannunsa sabida tsabar kudima da jin sunan data kira shi.


"Sanaya nine uban yannacin?"ya tambaya.


"Eh"ta bashi amsa gamida kashe wayarta.


Jirine ya soma dibar shaheed da sauri ya nemi guri ya zauna,tashin hankalin daya shiga baze faduba


dama shi ya lura tunda sanaya ta dawo gaba daya ta sauya masa,dan haka ze yiwa dad dinshi mgn ayi saurin yi musu aure,dan yana tsoron rasata.


Ba comments a whatsapp,but Facebook abun se godiyar Allah

su sunayi sosai.


muje zuwa 


surbajo for life


🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*SANADIN KIDNAPPING*

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀




*ZAHRA SURBAJO*




*AUNTY RUMAISA LAGOS,MACE ME FARAR ZUCIYA DA KYAWUN NIYA,A MASOYANA INNACE DAYA TO TABBAS ZAN AMBACEKI A BIYU,SHAWARWARINKI GARENI SUNAMIN DADI,KUMA IN NABI SUNA MIN RANA,INA SONKI SOSAI AUNTY NA,ALLAH YA RAYA MANA ZURIA,YABAR MU TARE DA MAZAJENMU CIKIN SO DA AMINCI,LOVE YOU SIS WITH ALL MY HEART♥♥♥♥♥♥♥♥♥*



*Dedicated to Fatima Abubakar Radda*



*17-18*



Sanaya ranar wuni tayi kulle adakinta tana kuka dan safwan ya kashe mata waya.


Shaheed ko Allah Allah yake dad dinshi ya dawoya sanar dashi aje nema masa auran snaya cikin satinnan,tunda sun kwashi tsawon shekaru uku suna soyayya.



Mahaifin shaheed na dawowa ya tare shi da maganar,murmushi kawai yayi yace.


"son ba ko kunya wai aure yakeso,to karka damu bari zuwa gobe se in shiga gurin dad dinta muyi maganar "


Murnace ta kama shaheed rungume dad din nas yayi,yana masa godiya,dan shi dama yafiso ayi auran inma laifi yay mata ya rarrashi abarsa sanda ya dorata akan cinyarshi.


Washe gari da safe,dad din shaheed yaje gurin gomna,sun tattauna gameda auran tunda dama kowa yasan suna soyayya.


Kamar yadda shaheed ya bukata,haka aka saka wato nan da sati guda.


Bayan sun rabu ne gomna ya shiga bangaren mtarshi inda yasmeta zaune dasu sanaya suna hira.


Be damuba yafara maganar data kawoshi.


"hajiya kinji mutananki ko,sanaya da shaheed yanzu sun fara mgnr auransu,dan yanzu mahaifinsa yabar gidannan shaheed ya matsa akan a daura auranshi da sanaya cikin satin nan to nasan da amincewarta shiyasa na amince a daura din"


"WHAT!!!!"cewar sanaya da taji maganar kamar saukar aradu.


azabure ta mike tana kuka tana faɗin.


"no daddy bazan aureshi ba,ko na aureshi ze sakenine,kafa tuna dad safwan yarigadaya batamin rayuwa,wlh ba namijin dazega mutuncina mtukar bashidin daya yimin fyaden ba,dan haka wlh banason shaheed inkuma kamin dole wlh sena kashe kaina"tana kaiwa nan ta juya ta shige dakinta tana kuka me tsuma zuciya.


wani gumine yashiga karyowa gomna,safwan ya cuce shi,cuta tahar abada taya ze iya yafe masa.


"Alhaji batun sanaya abun adubane fa,kasan fa budurcin mace shine mutuncinta dana iyayenta agurin miji da danginsa,pls kayi nazri sosai kar muzo muna dana sani"cewar mummy.


Shide yakasa mgn gumi kawai yakeyi dan ko giyar wake yasha baze bari sanaya ta auri safwan ba,inde shine ubanta.


Alamura sun cabe gaba daya dan yanzu sanaya kwananta biyu kenan kwance adakinta tarufe kofar baci basha,gaba daya ta fita hayyacinta.


Hankalin iyayenta duk yatashi ba ma kamar gomna tsoronshi kar yunwa da damuwa ta kashemishi sanayarsa.


Masu balla kofa ya kira suka balla kofar, a kwance suka hangota ko numfashi batayi,dagudu dad ya sungumeta,zuwamota mummy da munaya nabinshi.


Da sauri excorde dinshi suka bude musu motar,tuni jiniya ta fara tashi,suka fice a dari,zuwa asibitin Garden City.


Duk abun da ya dace shi aka mata,inda binciken farko yabada tabbacin jininta ya hau,sosai snnan damuwa tayi yawa a zuciyarta wanda gab take dahatsarin kamuwa da ciwon zuciya.


Kukane kawai gomna beyiba,amma mummy da munaya sunyi kuka har sun gaji.


Safwan ya gama cutar dasu,cuta ta har abada haka kawai suke maimaitawa.



Shaheed besan wainar da ake toyawa ba se yau dayaje gidan aka sanar dashi ay mutan gidan na Asibiti.



kai tsaye asibitin ya nufa,inda ya samu kowa jugum jugum ana jiran farkowar sanaya.

Ayko suna zaune ta farka.


"wlh banason shaheed bazan aureshiba,inko aka takuramin sena kashe kaina,na tsaneshi bana kaunarshi"itace kalmar dasanaya ta farka da ita akan bakinta.


A gigice shaheed ya mike yana ja da baya yana fadin


"No,no, no, sanaya kina sona duniya ma tasan hakan........"ji kake sharab ya yanke jiki ya fadi kasa sumamme,



wayyo tashin hankali baa sa maka rana gomna ko takalmi babu akafarsa 🤣haka yake daba kafar akasa,


Emmergency aka shiga da shaheed rai a hannun Allah,itako sanaya bata masan anayi ba dan ci gaba tayi da fadin batasonshin cikin mayen ciwo.




muje zuwa 



Surbajo for life


🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*SANADIN KIDNAPPING*

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀




*ZAHRA SURBAJO*




*Sometimes I forget 2 say hi, sometimes I forget to reply,sometimes my msg doesn reach u, but it doesn"t mean I forget u. I"m just giving u time to Miss me😊 AUNTY ASMAU ABDULLAHI SHAREEF YAKO AND AUNTY ALIYA SHAREEF GAMBO YAKO,YOU GUYS I LOVE YOU IRIN SOSAI DINNAN♥♥♥♥♥♥♥🙈*



*Dedicated to fatima Abubakar Radda*



*19-20*


Kan kace me an dukufa gurin ceto ran shaheed,dakyar akasamu numfashinshi yadawo shima seda taimakon oxygen. 


Do kyar security din dad suka lallabeshi yasa takalmi,se masifa yake tayi.


Sanaya ko allurar bacci aka mata dan ta daina cewa batason shaheed.


tuni labari ya isarwa iyayensa tuni suka garzayo asibitin domin kawo masa agaji.


Sun kidima da ganin halin da dan nasu yake ciki,mumynshi in banda kuka ba abinda takeyi.


Munaya ko tausayin shaheed yafi komai sata kuka,dan tasan irin son da yakewa sanaya ba na wasa bane.


Bayan kwana biyu dukansu sun dan murmure,hakanne yasa daddy sawa asallamesu in yaso doctor yaje gida yaci gaba da duba su.


Batan an sallamesunne yasa aje azo masa dasafwan in yayitaurin kai,su babballasa su kawo shi.


Allah sarki bawan Allah yanacan gurin da yake faskare,yaga motoci kamar ana yaki dan harda igwa🤣.


"ka bimu muje cikin aminci inba haka ba wlh se mun harbeka,me girma gomna ne keson ganinka"cewar daya daga cikin wainda aka turo.


Ba musu safwan yabisu dan dama yanaso yamasa warning na karshe😳


Har cikin falon gidan suka shigar dashi,yayi mamakin ganin kowa zaune yana kallonsa.


Sanaya na ganinshi ta rushe da kuka,sabida tuno sharrin data mushi.



"meyasa kayiwa sanaya fyade?"


jin tambayar  yayi kamar daga sama da sauri ya waiga yana kallon gomnan.


"tambayarka nake ko baka ji vane?"ya maimaita.


"katambayeta ni ban yi mata fyade ba,ay gatanan tana jinmu"cewar safwan.


"Sanaya,waye ya miki fyade?"gomna ya tambayeta batare da wasa ba.


kukanta ne ya karu inda cikin kukan tace.


"Daddy safwan ne yamin,wlh har so goma yana maimaitawa"t karasa maganar cikinkuka inda taci gaba da cewa.


"ka cuceni safwan,ka lalatamin rayuwa,kasa nida shaheed mun haramta ga juna dan ko na aureshi baze ga mutuncina ba,dan haka yazamemaka dole ka aureni tunda kaine ka fara Sanina"ta karasa maganar cikin gunji kuka.


A zabure safwan ya mike,ya nunata da dan yatsa yacr cikin fushi.


"naga alamun kamar yadda tsohonki yake dan giya kema kin fara korawa,agidan ubankine ni safwan nai miki fyade,wlh ki shiga taitayinki ni ba saan wasanki bane"


"wlh kaine,kuma dole ka aureni a hakan,in banda kaddara ma ni mezanti dakai kazamima irinka"cewar sanaya cikin kuka.


wata cafka yakai mata inda ya shako wuyan rigarta sega sanaya a sama ya ruketa da hannun daya,dan masifa hancinshi har budewa yake,yace.


"kin gama rabarwa atiti ne yasa kikeso ni na kwashi saura ko,to bari kiji ni nafi karfin ragowar wani,kuma wlh ko na aureki sanaya,senasa kin mance da waye ubanki,karuwa kawai"cillar da ita yayi,sanaya fitsari ne kawai batayiba dan tsananin tsoro.


"Nan gidanane dan samari ba naka ba,kuranka nayi dan na baka umarni,yazama dole kayi daya aciki,ko ka auri yata daka lalata ko kuma nasa atsareka anan na tura karti guda goma gidanku su yagalgalamin kanwarka kamar yadda kayi wa tawa yar,wlh ba wasa nakeba"cewar gomna yana huci.




kuyi hakuri da wannan abubuwanne se ahankali



surbajo for life.


🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*SANADIN KIDNAPPING*

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*ZAHRA SURBAJO*


🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏

*Don Allah kuyi hakuri na jina shuru da kukayi,wlh inada babban uzurine,daya sha kaina,ina fatan zakumin uzurin*


*Dedicated to Fatima Abubakar Radda♥*


*21-22*


Shuru safwan yayi yana kallon sanaya,cikin matsanancin mamakin sharrin da ta masa.


Se yanzu yayi danasanin saninta a rayuwarshi,wasu hawayene masu dumikebin fuskarsa,dan yasan sabida kansa baze so ya tarwatsa rayuwar kanwarsa ba,uwa uba anashi ganin,da yakai rahama gidan miji ba cikakkiyar budurwa ba to gwamma shi yadauki second hand din koda hakan zeyi sanadin salwantar numfashinshi.


Zubewa yayi akan guiwowinsa yana kuka ya rike kafafun gomnan,yace.


"zan auri yarka domin kare mutuncin kanwata,bana son yarka bana kaunarta,na fada maka ne dan ka tabbatar da cewa kiyayya ba abunda bata sawa,dan haka in har ni kakeson na aureta to ka daura mana auran yanzu,dan wlh ya wuce yanzu bazan aureta ba,koda kuwa da naman jikina zaa dunga yin miya a gidanka kullum"ya karasa maganar cikin dakewar murya.


"kai dalla malam dakata,ubanwaye saanka anan,kabar ganin fa ina kyaleka,wlh ba tsoronka nake jiba,akwai lokacin da zakayi nadamaraykata min duk abinda kayi,kasan duk wanda ya rigaka dakwana dole ze rigaka tashi,yata ni nake da ikon saka ranar auranta ba kaiba dan haka bazan daura auran yanzu ba"


mikewa safwan yayi yace


"to naji,sede ka manta da cewa,sanayace yarka ba niba,kana daiko akanta amman banda ni,dan mulkin naka ba inda aka rubuta se gomnan jihaya amince dan jihar zeyi aure,kamar yaɗdana fada da farkoin na fita yanzu wlh bazan aureta Ba"yana kaiwa nan ya juya Ze bar falon.


Dawani mahaukacin gudu sanaya tazo tasha gabanshi har tana haki,sabida adan zamanta dashi ta fahimci shi kaifi dayane,inde ya fadi abu ti tabbas seya aykata,


ruko shi tayi tana kuka tace.


"Don Allah kar ka tafi,ka bari adaura auran yanzu"da sauri ta waiga gurin dad dinta tace cikin kuka.


"dad inde da gaske kana son farincikina  toka Daura aure na  yanzu anan gurin,"


"Sanaya..."cewar dad


"dad"ta katse shi da hanzari.


shiko safwan ko ajikinshi,so yake ta bashi guri kawai yawuce.


Ganinfa da  gaske sanaya take ne yasa dad  Yin abinda ta bukata badan shi yasobane.


Shide shaheed dake zaune kamar gawa inbanda  kuka ba abinda yake.


Haka  abban shaheed yayiwa sanaya wakilci sannan gomna yayiwa safwan aka daura kan sadaki dubu dari dahamsin .


an daura aure lfy,sanaya se murna take,ana gama daura auren taje gaban daddynta tace cikin kuka.


"daddy kuyi hakuri,zan sanar daku gaskiya,wlhsafwan beyimin fyade ba,kawai sonshine ya kama zuciyata ta yadda bazan iya hakuri dashi ba,ina son safwan dad fiye da raina,shaheed kayi hakuri,wlh nakasa jurewa ne"


Azabure kowa ya mike yana kallonta,cikin fushi dad yasa hannu ya dauketada mari,sannan cikin fushi yanufi safwan.


"nasan kunnenka yaji maka,cewa ba gaskiya bane sharrin data maka,dan haka yi hanzarin sakarmin ita yanzu dan baku dace da ita va"


Murmushi safwan yayi,ya mika hannu ya kamo sanaya suka tsaya gaban dad yadubeta yace


"Kina sona da gaske ko?"


kai kamar na kadangarw haka tashiga gyada shi.


murmushi yasakeyi Sannan yakai dubansa gun gomna yace.


"Baba a tayamu da addua dan nima.gaskiya ina son matata"yana kaiw nan yaja hannunta suka fice daga falon.


"sanaya in kika bi karen nan na tsmeki acikin yyana,bani bake har abada"cewar gomna kamr zeyi kuka.


Sanaya ko hawaye kawai takeyi dan tasan yanzu safwan yafi iyayenta iko da ita,dan haka ko waigowa bata yiba,tabi safwan suka fice daga gidan.


tofa

adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *