Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Monday, September 7, 2020

SO MUGUN WASA COMPLETE HAUSA NOVELS

adsense here

SO MUGUN WASA COMPLETE HAUSA NOVELS

 Copied By

HAYATU BABA ZUBAIRU(YAYA HAYAT) 

(ADMIN OF ADMINS)

        (admin 

   Hayat hausa novels

Hausa novels and fashion

Cool novel, makeup and kitchen1⃣

Cool novel, makeup and kitchen2⃣

                   AND 

Cool novel, makeup and kitchen3⃣) 

      WHATSAPP NO:

        09030159301


[05/04 4:44 pm] Washa: ⚜ *BRILLIANT WRITER'S ASSO* 🖊




                   *SO*

       *MUGUN WASA*




     { *Love is a bad game* }




*JAMEELA MUSA* { meelat musa }



*BISSIMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*



*Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama su ne na fiyayyen halitta, shugan Annabawa kuma jagoran Manzanni Annabi Muhammad, { S. A. W } da iyalinsa da sahabbansa baki ɗaya*


*Wannan labari da zan rubuta banyi dan wani ko wata ba,, duk wanda yaga labarin yayi daidai da labarin rayuwarsa to yayi hakuri, dan haka a guji zargi* 🤷🏻‍♀



*Story, Writing & Editing*

                  *by*

          *Meelat Musa*


                  *SO*

      *MUGUN WASA*




*1-3*



Amana ce aka bashi amma saboda tsabagen rashin tsoron Allah da rashin sanin matsayi irin na amana yasa ma amanar kuli da mai ya yankama ta albasa da tumatari ya kwadata ya cinye ta cikin cikinsa,,


ya gurbata mata rayuwa ya cuci rayuwarta, baya barinta da abokiya ko daya sannan kuma baya barinta tayi mashi nisa, saboda kada wasu su hure mata kunnuwa ta daina nema masa kudi, babbar sana'ar daya dora ta akai itace *Sata*  tunda ta tashi bata san wata rayuwa ba sai sata, bata san mai kyau ba kuma bata san marar kyau ba tunda bata da wanda zai koya mata, kyakkyawa ko akasin haka,


 Yayi mata horo da sata sosai saboda haka itama ta kware wurin iya sata, kana tsaye zata { sane } ka wato sacewa ba tare daka sani ba, idan ta shafa jikinki baka taba sanin an taba ka,,


Shi kuma saboda san duniya da tsabagen san kudi wannan dalilin ya hanashi aure bare ya aihu "ya"ya suci gajiyarsa, baya da aiki sai caca, shaye shaye, amma baya neman mata,


Itama haka ya horata da nuna mata cewa babu maza a rayuwarta, kuma ya nuna mata maza abin tsoro ne, da kalamai masu muni ya ai bata maza sosai a wurinta sai labarin karya dana wofi da yake bata akan soyayya shine yasa ta dauki wuka ta cakawa *SO* bata kaunar ayi maganar *SO* bare kuma ayi maganar maza a gabanta,,


A cikin horonsa ya koyar da ita jarumta sosai ya koya mata fada kuma ya koya mata kafiyar zuciya, ya koya mata daukar wa rai, tana masa biyayya sosai dan bata san kowa a duniya ba saishi, idan tayi mashi maganar iyayenta sai yace saita tara masa miliyoyin kudi zai fada mata inda suke, dan yasan idan ta tafi bazata sake dawowa gareshi ba, wannan dalilin yasa ta dage wurin kwamashe aljihun koma waye,


Banda samha yana tare da "ya"yan dan uwansa suma dukansu mata ne, bayan rasuwar yayanshi ya tattara yaran ya dawo dasu wurinshi kuma ya tattara gadonsu wato abinda mahaifinsu ya bari ya rike a hannunshi,


Suma dai haka ya horasu da suyi sata, kamar yanda ya hora samha, amma duk cikinsu babu mai rashin tsoron samha da kuma jarumta irin tata,,


shi kanshi yana alfahari da samha sosai, shi yasa kullum yake kokorin munanta kalamar *SO* da *mugun wasa* saboda kada soyayya tasa samha gudunshi wata rana,


muje dai cikin labarin , { *so mugun wasa* }



****



Dukan kofar dakin yake babu ji babu gani kuma babu kakkautawa tare da fadin baza ki bude ba? Yaci gaba da cewa bakyajin ina magana ko? Ke samha dake nake fa, 


Daga cikin dakin kuma samha ce tayi tsaki tare da kara jan bargo ta lullube jikinta ba tare data ce komai ba,,,,


Ci gaba yayi da dukan kofar tare da jijjigata cincin karfinsa, tsaki samha tayi sannan ta sauko daga saman katifar ta tayo bakin kofa, bude kofar tayi tare dayin mika tana hamma,,,,,


Hasken rana ta fara karewa da hannunta sannan tace wai kawu ya akayi ne? Tsaki yayi tare da juya mata baya , cikin daga murya yace wane lafiya?" bayan kin tura su yusra aiki gasu can an samu matsala memory card din an kwace shi,,,


Da sauri samha ta fito daga cikin dakin tare da komawa gaban kawu tana cewa kawu mi kace?" cikin nuna fushi yace nace taje tayi sakaci an kwace m. Card din,,,



Wani irin ihu samha tayi tare da cewa ina yusra?" ina kausar din?" kawu yace gasu can kina ganinsu,, juyawa samha tayi inda kawu yake nuna mata,, 


Yusra ce tsaye ita da kausar, kowa ya dukar da kansa kasa, cikin tsananin bacin rai samha tayi wurin, tana zuwa babu wani bata lokaci ta daga hannunta tare da kwararama ko wannensu mari,,, sannan itama samha ta kashe kanta da mari, tana kuka,


Cikin kuka samha tace Yusra kun cuceni kun zalinci rayuwata, garin ya akayi har kukayi sakaci rayuwata tayi wani wurin? Cikin kuka yusra tace samha kiyi hakuri wallahi faduwa yayi kafin in dauka wani ya dauka sannan yace inje in turo duk wanda ya tsaya man ya ganshi,,,


Samha cikin kuka tace shi waye ya tsaya masa ne?"" kausar tace bamu sani ba ranki ya dade,, cikin kuka samha ta juya tana kallon kausar sannan tace haka zan fada cewa baku sani ba?"" cikin kuka samha tace mutane sun bani aiki amma kun mayar min da aiki baya,,,, yusra tace samha kiyi hakuri don Allah, cikin daga murya sosai samha tace inyi hakurin banza?",,, wane gwallon dan iskane ya kwace m. Card din nan ne?" ta karasa maganar cikin karaji kamar makoshinta zai fashe""",,,,,



Babu wanda ya sake magana,, samha ta dago kanta ta kallesu da jajayen idanuwanta sannan ta dafa kanta da hannunta tace,


Na rantse da babana, hawaye ya sake gangarowa daga cikin idonta,,, sannan tace na rantse da mahaifiyata,,, ta dafa daidai zuciyarta, sannan tace ina zuwa wurin lamari ya lalace domin duk jakinda m card din nan yake hannunsa saina cire masa hannu daya,,,


Da sauri Yusra tace A, a samha ki sauke rantsuwarki, cikin tsananin bacin rai samha ta daga ma yusra hannu, tare da cewa naje nace ko waye, ni kan banza ma zan cire,,,


Cikin fushi ta juya zata shige daki kawu yace ke zo nan, tsayawa samha tayi ba tare data juyo ba, kawu ya matsa kusa da ita sosai sannan ya mike mata hannunshi tare da cewa bani na shan sigari?


Cikin daga murya sosai samha tace wane nashan sigari kuma?" kullum sigari kullum sigari ni shikenan rayuwata a kudin sigari da kudin caca shaye da sakarci zasu kare? Jiya bana baka ba?" dukan abinda na samo shine na kundume gaba daya na baka, jijjiga jikinta tayi tare da rike gaban rigarta tana cewa to ai saika daukeni kaje a baka sigarin dani, shikenan ko?" taci gaba da cewa ko ba haka kake so kaji nace ba?


Tsaki tayi sannan tayi gaba, tana kokarin shiga daki kawu yace to naji idan baza'a bani kudin sigarin ba ai sai a biyani kudin hayar gidana, cikin kuka samha tace kayi hakuri kawu wallahi banda ko sisi a hannuna wa'ancan banzayen kuma sun daukar man, m card din daka bani da niyar su gani, kuma sunje wurin haukansu wani dan iska ya kwace shi, ta karasa maganar cikin yanayin a tausaya mata, tana kara goge hawayen idonta da bayan hannunta,


Kawu yace to gaskiya aje a samo man kudi, cikin yanayin lallashi samha tace haba kawu waikai baka gajiya da kudi don Allah , ka mayar dani A T M mashing dinka, kullum saidai in baka kudi?"" Kawu yace to kada ki bani kudin idan na gudu naga wanda zai nuna miki babanki da mamanki, murmushin karfin hali samha tayi mai cike da kunar rai sannan tace to swry bara in fito,


Tsaki kawu yayi ita kuma samha ba tare da ta sake magana ba tayi ciki,, su Yusra kuma jiki a sabule suka yi bayan samha,


Babu wani bata lokaci samha tayi wanka, a gaggauce ta shirya cikin shiga mai boye suffar jikinta, tasa katuwar hijabinta, sannan ta dauki nikaf ta rufe fuskarta dashi, kallon Kausar tayi sannan tace idan kunga dama kuna iya tashi mu wuce,


Kowa ya dauki nikaf ya rufe fuskarshi, sannan suka fito daga daki, kawu na zaune saman kujera plastic chair yana murza shalisha, samha ce kadai tayi mashi sai sun dawo, hannu ya daga mata yana murmushi,


Gaba dayansu suka fita daga gidan, napep suka tare sannan suka fada mashi inda zai kaisu, shiga sukayi sannan suka tafi,,


Fitar su samha kawu ya ciro wayarshi daga aljihunsa yayi dan danne dannen sa sannan ya kara a kunne, bayan wani lokaci ya kecewa da dariya, sannan yace na tura ta aiki, shiru yayi na wani lokaci sannan kuma yace kada ka damu da hannunta zansa ta kasheshi, dariya kawu yayi sosai sannan yace duk barsu dani suka zance, shiru yayi na wani lokaci sannan yace ka manta samha bata sauraren maza?"",,, murmushi kawu yayi sannan yace barta ai ina tare da ita dai, murmushi kawu yayi sannan yace kada ka samu damuwa, kashe wayarsa yayi sannan ya tashi daga wurin yana dariyar mugunta,


Su kuma su samha suna isa bayan sun sallami mai napep, suka ware gefe daya suna karewa wurin kallo sannan kuma suna karantar mutanen wurin,


Murmushi samha tayi sannan tace Yusra, ki fara shiga wurin nan da gudu sosai, ke kuma kausar kibi bayanta, ni kuma lokacin da zan shigo ku tabbatar kun gama kwamashi whylet din kowa, ke ki cire kudin sai ki bawa kausar ita kuma zata bani in matar dashi aljihun duk wanda kuka dauka,


kamar yanda samha ta tsara musu haka sukayi, dan haka tana gama magana babu wani bata lokaci suka fara kutsawa cikin mutanen suna shiga da gudu kamar wanda bala'i ya biyo su,


Haka suke wucewa da gudu suna kara kutsawa cikin mutane, duk mutumin da suka wuce sai sun dauke mishi kudi idan yusra ta zare tana mikawa kausar whylet ita kuma samha tana mayarwa,,,


Su kuma tafiya sukeyi, amma dayan yana waiwayen su samha, sannan ya maida dubansa wurin wanda yake bin bayan sa tare da cewa "yar labai kalli yarancan da gani basu da hankali mahaukata ne,, wanda aka kira da "yar labai  murmushi yayi tare da cewa ai kaine mahaucin, cikin mamaki ya kalli kansa tare da cewa ya akayi na zama mahaukaci "yar labai?"" murmushi yayi cikin izza sannan yace su can daka gansu wai wayau garesu "yan sane ne,,, miye sane ranka ya dade?" ba tare daya kalleshi ba yace sata sukeyi wa mutane,


kaima sun sane ka,,, da sauri yakai hannunsa a aljihu ya lalaubo whylet dinsa sannan ya fiddo yana dubawa yaga babu ko sisi,,, kallon shi yayi tare da cewa wallahi babu,, towai yaushe ma suka dauka ban sani ba?""


A daidai lokacin da yusra ta sake dawowa wurin ogan nashi tasa hannuta a aljihunshi da sauri ya rike hannun yusra sannan ya zagayo da ita gabanshi, nikaf din fuskarta ya yaye dukanshi sannan ya kashe da wani irin firgitaccen mari wanda ya gigita ta, marin da yayi mata yasa ta sakin fitarin tsaye,,


Tsoro ya kama Yusra da sauri ta rufe idonta, sannan ta fara kiran sunan samha,, ita kuma samha ta riga tayi mata nisa, dan haka kausar tana jin yusra na kiran samha sai tayi wurin da takejin sautin muryar yusra take fitowa,


A daidai lokacin da yake cewa an gaya miki ni mace tana taba min jiki ne?",,, gaban Yusra yayi wata irin mummunar faduwa, yaci gaba da cewa duk macen data tabamin jiki saina cire hannun banza, faduwar gaban yusra ya kara karuwa, murmushi yayi da gefen bakinsa sannan yace kinji tsoro ko?" yusra tayi shiru sai kyafta idanuwa take kamar munafika,,,,


Hannun Yusra ya saita sosai sannan yasa hannunshi cincin karfin sa ya karya hannun kat,, wani irin ihu yusra saki tare da faduwa kasa somammiya,,, jin ihun yusra yasa samha tayo wurin da gudu,,,,,



Suuuuuuu , take tafiya saboda sulbin wurin wanda idan kayi sakarci zaka iya faduwa,, tana isowa a gaban kausar tayi tirjiya a ta durkushe saman guyawunta sannan ta rike hannun kausar tare da cewa miye?"",,,,


Cikin kuka kausar tace ya karya hannun yusra, cikin masifa samha tace wane tattarin kwallon dan iskan ne?"",,, da hannu kausar ta nuna mata hanyar da suka bi,,, da sauri samha ta mike tare da cewa saina ga bayanka,,,,,,,,,,,,,,, ta karasa maganar cikin daga murya tana kuka,,, da gudu tabi su, amma ina kafin ta isa har an bude mashi mota ya shige har sun tafi, bayanshi kawai ta gani amma bata ga fuskarshi ba,


Da sauri samha ta tare mai mashin tare da cewa bimin banyan wancan banzayen motocin, mai mashin yace hajiya in baki shawara?"",,,, cikin daga murya samha tace naci uwar shawarka shawarar kan banza, to aiki na saka ka, kuma biyanka zanyi ba kyauta zakamin , mai mashin ya fara tafiya tare da kara jaddawa samha ta kiyayi kanta da wanda take kokarin bi, dan binshi tamkar daukar rayuwarta ne zuwa cikin kabari,


Wuta suke sosai a titi, tsakanin mai mashin din samha da kuma motar wanda ya karya hannun yusra,,,, ita bama tasan motarshi ba, saboda comeboy ne akayi ma motar, 


Cikin motocin da suke bin bayan motarne,  wani daga cikinsu ya dauki wayarshi tare da shedawa mai gida masu nikaf suna bin bayansu fa,,,, magana yayi cike da izza cewa duk jakin daya sake binsu ayi mishi barazana ta hanyar harbi da bindiga,,,


bayan ya gama wayar ne, ya ciro bindiga daga inda suke ajiye bindiga dan cika umarni mai gida,, ta window din motar ya leko da kansa tare da fara barin harsashe ji kake tata ta tata,


mai mashin yana ganin an fara harbi hannunsa ya fara rawa,,, dolensa ya fadi kasa da mashin,,,, samha tanaji tana gani motocin suka bace mata,  bata da yanda zatayi dolenta ta hakura suka dawo inda yusra take, sallamar mai mashin tayi sannan ta shiga wurin,


Da ita da kausar suka kama yusra sukayi gida,,, bayan sunje gidane, samha tasa aka kira mai gyaran hannu ya gyara hannun yusra, amma har aka gama gyaran yusra bata farfado ba,


Samha kuwa sai zungura zagi takeyi tare da daukar alkawari, itama saita karya hannun ko wane dan iska ne kamar yanda ya karya hannu yusra,


Har gari ya waye Yusra bata farfado ba, wannan abu ya kara konawa samha rai, dan haka ta samo bulalarta taci gaba da dukan yusra, kausar ce tace haba samha da wane zataji don Allah?"" da karayar da ya mata a hannu ko da dukan da kike mata?"


Cikin fushi samha tace duk uwar da zataji taji babu abinda ya dameni🤷🏻‍♀, saboda tana banza jaka da ita, sai taje tayi satata da baki namiji ya karya mata hannu?"",,,,


Kawu ne ya shigo dakin tare da cewa wai miye ne?",,,, da sauri kausar tace kawu samha ce take dukan yusra, kallon samha yayi tare da cewa samha miye haka ne?"",,, murmushi 😬 samha tayi tare da cewa so nake ta tashi ne, cikin sanyi kawu yace to ai ba haka ake tashin mutum ba, wanda bata da lafiya ya zaki tasheta a haka?"",,,,,



nishin da Yusra takeyi shine yasa suka mayar da hankalinsu inda yusra take, ganin tana motsa baki yasa sukayi wurinta a hanzarce,


Samha ta dagota tare da cewa yusra waye ya miki haka?", cikin kuka yusra tace samha shine ya kwace m card dinki, kuma yace da kanki zakije ki ansa idan kina so,,,,,


Tsaki samha tayi tare da jinjina kanta alamar gamsuwa murmushi tayi sannan tace to dani zaiyi fada?"",,, murmushi samha ta sakeyi tare da goge hawayen idon ta da bayan hannunta sannan tace hmm wato m card dina ya kwace yace saina zo?"",,,, mikewa tsaye tayi tare da yin wani irin ihu ta buga kafarta kasa, sannan tace idan har ka bari na sameka sai nayi maka lullusar fitar hayyaci,


Yusra tace samha ki kiyayi kanki, kuma ki nisanta rayuwarki dashi saboda mutum ne shi mai hadari, wayau gareshi sosai kada ki kuskura ya ganki dan idan harya ganki hakika yanda yake nemanki nayi imani saiya kasheki,


Dariya samha tayi tare da bude hannuwanta tace karya ne, ni nan kadaina na ishi banza, ina yake zamane?""


Wata katuwar wuka kawu ya mikawa samha mai kaifi sosai sai sheki take tana walkiya har kallon fuskarka kake a cikinta saboda sabintar ta da kaifinta, abinda yasa kawu yayi haka saboda yaji yusra tace wani yace sai taje da kanta zai bayar da m card, ansar wukar samha tayi tare da cewa da wannan wukar zan aika ka lahira banza in kasheka kayi mutuwa irinta karnuka,,


Kawu yayi ta zuga samha, murmushi tayi tare da cewa waishi mace bata taba shi?"",,, amma ni ya taba man m card dina?" wanda shine rayuwata ,, hmmm duk abinda kike yusra gobe muje ki hadani dashi, yusra tace tom, juyawa kawu yayi yabar dakin tare da jin dadi a ransa,



Samha ta sake kallon yusra tare da cewa zaki iya siffanto man yanayinsa?" Yusra ta girgiza kanta alamar A, a, murmushi samha tayi da gefen bakin tare da cewa ya akayi kika gane shine ya anshi m card din?" Yusra tace wallahi shine kuma ya fadi min da bakinshi yace idan ya kamaki saiya kasheki, kuma jiya ma kafin ya karya hannuna ya sake fadin haka, gyara zama samha tayi tare da cewa mi nayi mishi yake san ganin ya kasheni?"",,, Yusra tace ban sani ba,



 Samha tace kefa kausar?", zaki iya fada min kamanin sa?" kausar tace nida ba ruwana, dariya samha tayi sosai bayan ta tsagaita tace nikam da ruwana, kuma gobe zanje saina farke cikin banza, ina zuwa zan kashe shi da mari, sannan in fito da wannan wukar in dora bisa wuyansa, sai ince bani m card dina, idan ya bani , sai ince ya fita daga harkata, idan yace bazai fita ba sai ince mishi to lallai idan har bai fita ba nima nice zan kashe shi,


Daga kausar har yusra kallon samha suke, haka tayi ta nuna musu irin azabar da zatayi mishi,


 Su kuma suna isa gida, bayan ya shiga dakinshi wanka yayi bayan ya gama wankan ne ya fito, rigar wanka ce a jikinsa sai towel a hannunsa yana goge gashin kansa, lokaci lokaci yana murmushi, wayarshi ya dauka tare da kiran wani abokinsa, bayan ya dauka suka gaisa, yace duk abinda kake gobe idan Allah ya kaimu ina san ganika, bayan ya gama wayar ne, ya kashe wayarsa tare da ajiyewa, inda ya ajiye m card din ya nufa ya dauko shi, yana jujjuyashi a hannunsa, murmushi yayi sannan ya fada saman lallausar katifar dake saman gadonsa,


*Meelat Musa*




⚜ *B . W .A* 🖊

[05/04 4:44 pm] Washa: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊



                 *SO*

     *MUGUN WASA*



       *{ Love is a bad game }*




*JAMEELA MUSA* { meelat musa }




*Story, Writing & Editing*

                   *by*

         *Meelat Musa*



                  *SO*

      *MUGUN WASA*



*Gaisuwa ta musamman jinjinar ban girma fatan alkairi da addu'ar samun lafiya mai dorewa, amanata, zuciyata wato REAL MAI DANBU ubangiji ya baki lafiya "yar uwata Allah yasa zakkar jikine,*




*4-7*



Tunda samha tayi sallah da asuba har yanxun ta gagara ta koma bacci saboda tsabar bacin rai da kuma damuwa,


Zaune take ta zabga tagumi saman abin sallah, cikin tsananin bacin rai take kallon kawu dake tsaye, dan gajeran tsaki tayi tare da kauda kanta gefe guda,


Cikin fushi da kunar zuciya tace haba kawu, haba don Allah yanxun abinda kayi ka kauta kenan? Shima cikin daga murya yace naje nayi ai gidan nawa ne ba ubanki ya siya ba!


Samha cikin lallashi tace ai dama bance babana ya siya ba, kawai dai kace yau kwayarka a  kaina kake so ta kare daga magana sai gori kamar kana jirana? Kawu yace jirankin nakeyi idan ma bakiyi hankali ba hada duka zan hada miki, samha tace duk mi yayi zafi? Yusra dake kwance tana fama da hannunta tace samha kiyi shiru don Allah,


Murmushin takaici samha tayi da gefen bakin ta, tare da murza idanuwanta ta sake kallon yusra sosai tace wane inyi shiru kuma? Magana zanci gaba dayi  bani kadai ba kowa da kowa sai yayi magana, dan damuwar ba tawa bace ni daya kowa da kowa ta shafa, baki dayanmu muyi magana dan musan miye mafita, idan banda san kai irin na kawu domin Allah sai yaje ya dauki gidan nan yasa shi a caca? Yanxun an cinye gidan ki fada min a ina zamu koma da zama?


Cikin fushi kawu yace kaji munafikar yarinya nine nayi san kai ko ke? Ya nuna samha da hannunsa sannan yaci gaba da cewa aisai da nace kuyi kokori ku rika sato kudin da yawa, amma saboda kun daukeni shashasha kullum rana da wata dubu ishirin din banza kuke dawo min wata ranar ma basu kai hakan, waye ma ya sani ko boyewa kukeyi,


Tsaki yayi sannan ya matsa ya jingina bayan sa da bango kafarsa ta dama ya dora jikin bango ta baya, sannan yaci gaba da cewa yanxun ku fadamin miye mafita? Kowa yayi shiru, kawu yace to kada Allah yasa kuyi maganar ke samha idan na gudu sai naga ubanda zai nuna miki babanki, 


Da sauri samha ta mike tare da daga hannunta alamar kawu ya saurara, dariyar keta yayi tare dayi ma samha wani irin kallo wanda shi kansa baisan dalilinsa nayin hakan ba, kusa dashi samha ta matsa tare da cewa kawu fadamin mafitar da kake ganin itace ta dace muyi,


Murmushi kawu yayi sannan yace abinda zakuyi yanxun shine, ku fita aiki tun yanxun ku fara da tashar mota kasuwa gidan kallon kwallo shagunan mutane gidanjen mutane kai ko a masallaci ya kama idan har kuna ganin zaku sami kudi ku shiga kawai ku kwamaso min kudaden mutane kai harma chochie ban cire mata hula ba dan inyamiran nan kudade ne dasu kamar hauka, yusra tace kawu ai tunda kace hada masallaci ai zance chochi duk aikin banza ne, kawu yace rufe min baki munafika bada ke nake magana ba, sakara da kikaje namiji ya karya miki hannu, shiru tayi ba tare data sake cewa komai ba,


Gefen hijabi samha tasa ta goge zufar goshin tare da cewa haba kawu? Abun kuma ya tashi daga sane wa mazaje zamu koma fashi? Kawu yace to ai wannan hanyarce kadai zata kawo kudi da sauri, samha tace amma kuma kawu hada masallaci? Kawu yace hmm yarinya kina wasa da lamarina, jinjina kai samha tayi tare da cewa hmm itama,


Juyawa tayi ta kalli kausar sannan tace tashi mu tafi, kawu yace itama mai karyayyen hannun ta tashi ta biku, wani iri samha tayi da fuska kamar taji warin tusa, sannan tace haba kawu da wane zataji ne? Kawu yace can matsalarta yayi maganar ne tare da daga kafadarshi, sannan yaci gaba da cewa kinga gobe idan ya kama hannun zai karya saita karya nashi itama, ai da haka ake koyon jarumta, matsoraci bazai taba zama gwani ba, ku tashi da Allah ku tafi kafin wasu su rigaku ya karasa maganar cikin daga murya,


Babu musu Yusra ta tashi tabi bayan su samha suka fita daga gidan, suna fita samha tace yawwa Yusra a ina zan samu wannan dan iskan yaron ne? In rama miki abinda yayi miki kafin iskancinsa yazo kaina? Yusra ta tallabe hannunta mai ciwo sannan tace mu fara zuwa dai aikin idan muka samo kudin sai muje ta wurin shi, Samha tace haka nake so, to muje,


haka sukaci gaba da tafiya, suna sane mutane , saida suka gama da cikin gari sannan suka nufi wurin, wurin training ne kuma wurin an kayata shi da abubuwan burgewa sosai wurine bana wasan yara ba, an tanaji wurin dan manyan masu kudi suzo suci ma kudin su uwa, duk wanda ka gani a wurin hakika kasa tasan da zamanshi, ga abubuwan motsa jiki nan masu burgewa, kowa ka gani harkar gabansa yakeyi, 


Tun daga nesa yusra ta hangoshi idanuwa ta zaro sosai tare da cema samha yawwa gashi can, ta nuna wurin da hannunta, hmmm shi kuma basu san yafi su bariki ba, tun shigowarsu ya gansu, dan haka yau yayi alkawarin sai ya kama samha da hannunshi kuma sai yayi mata dukan rabani da yaro,


Amma matsalar da take damunshi shi baima san waye samhar ba, amma lallai idan ya kamata sai taci ubanta da kyau da kyau, wai kamarshi zatayi mashi sane? Tsaki yayi a bayyane sannan ya ciro wayarshi daga cikin aljihu ya duba lokaci, murmushi yayi da gefen bakinsa sannan ya sake wurin tsayuwa,


Samha tace yawwa wancan dan iskan ne ko? Ta nuna wurin da hannunta Yusra tace Eh shine, ita samha bata sanshi ba, ita kuma yusra lokacin data nunashi hankalin samha ba wurin yake ba, dan haka ba tare data tabbatar da shine ko bashine ba samha tace to kuyi maza ku fita dan ina zuwa zan sara mishi wukar nan bisa keyar shi, sai naga yakai yanayin mutuwa sannan ince ya bani m card din, Yusra tace kedai kada kiyi hukunci da wuka danshi da bindiga yake harbi,


Samha tace da Allah gafara can banza wanda kika rako mata bindigar shin banza, yusra tace to keda baki rako mata ba Allah ya bada sa'a tana fadin haka tayi gaba, kausar kuma tabi bayan samha suka matsa wurin,


Mutumin da yusra ta nuna mata tana zuwa kusa dashi ta daga rigarta ta ciro wukarta, daf dashi ta matsa a hankali tanayi tana waige waige , shi kuma ganin sun shigo cikin mutane sosai yasa shi fitowa daga inda ya boye, bodyguard dinsa ya  nunawa kausar ba tare da sanin ba itace samha ba, yace ya dauko mishi banzan yarinyar can yaci gaba da cewa yau din nan sai nayi mata lullusar fitar hayyaci, a daidai lokacin da samha ta yanki bayan wanda yusra ta nuna mata da wuka,


Lokaci guda yayi wani irin ihu wanda ya jawo hankalin duk mutumin da yake wurin, ba tare da jin tsoro ba ko fargaba samha ta basar kamar ba itace tayi yankan ba, da gudu mutane suka iso wurin tare da tambayar lafiya? Cikin kuka yake nuna bayansa tare da cewa wata kauranya ce ta yankesa a bayansa, 


Ita kuma samha wannan taron da mutane sukayi ya bata damar ci gaba da saka hannunta cikin aljihunsu tana ci gaba da sane masu kudade, saida ta gama tattara kudin kaf sannan tayi waje, nan ta barshi yana ta kururuwa kamar mace mai nakuda,


Tana fita inda yusra take tsaye taje, tana bata labari yaufa ta yanke banzan yaron nan taci gaba da nuna mata yanda yake kuka, tana buda bakinta tana gwadawa tace sakaran banza, gyara tsayuwarta tayi tare da daga kanta sama ta dora hannunta saman bakinta tana girgiza kanta tace amma fa bai wani yanku sosai ba, sauko kanta tayi tana kallon yusra sannan tace kiyi hakuri gobe zanzo in karya mishi hannu kamar yanda ya karya hannunki amma fa kiyi hakuri, sai kuma maganar m card dina, dan gajeran tsaki tayi tare da cewa bari in koma,


Tana juyawa da niyar komawa taga kausa ta fito a guje ga wani murdeden kato yana bin bayanta da gudu, da sauri samha tayo baya, ita kuma kausar tayo bayan samha ta boye, kallo daya yusra tayi mishi ta zungura da gudu saboda kalar ban tsoro gareshi, cikin tashin hankali samha tace ya akayi ne? Ka wani zo a gabana kayi min tsaye sai huci kake kamar ka kada giwa? 


Cikin daga murya mai kalar bada tsoro yace cire wannan munafinci da kika rufe fuskarki dashi, cikin rashin tsoro samha tace idan kuma ban cire ba fa? Yace yanxun nan kici ubanki, girgiza kai samha tayi tare da cewa mudaici uban juna, cikin fushi yayo kan samha tare da niyar kamo mata wuyan hijabi da sauri ta zaro wukarta ta yanki hannunshi, 


Cikin sauri yaja da baya tare da rike inda samha ta yanke shi, sannan yace dama kece samha? Rike kugu samha tayi itama tace kaine dan iskan daka anshi m card dina? Wata irin dariya yayi tare da cewa zaki ci ubanki bari in kira mai gida, daure fuskarshi yayi sosai sannan yaci gaba da cewa yau idan ya kamaki duk ubanda ya tsaya miki a garin nan sai yaci uwaki barauniyar banza, yana fadin haka ya juya da sauri dan komawa ciki,


wannan kalma daya fadi ma samha ta barauniya ta tsaya mata a rai kuma tayi mata ciwo sosai, dan haka ta daga muryarta sosai tare da cewa kai!  Ji nan mana, juyowa yayi ba tare da yayi magana ba, samha tace idan kaje kace ma mai gidan naka inji samha , nima idan na kama shi sainaci kutumar duma du,


Tana fadin haka tace ma su kausar mu tafi, juyawa sukayi sukayi tafiyarsu, napep suka samu suka shiga, har suka isa gida samha zuciyarta tana mata zafi saboda kalmar barauniya da aka kirata dashi,


Shi kuma da gudu ya isa wurin yana cewa ranka ya dade ga mai memory card can a waje, ba tare daya kalleshi ba yace tana ina?  Daga saman benan ya leko dan hango inda yabar su samha ya  nuna mishi samha, amma babu kowa a wurin, cikin girmamawa yace ranka ya dade sun tafi, 


Kanshi ya jinjina alamar gamsuwa sannan yace ashe wuka tazo ta kasheni dashi, Allah ya tsareni, duk ranar dana sake ganinsu wurin nan saina ci mata mutunci,,, tsaki yayi sannan ya dauki robar ruwan dake gabanshi ya fara sha, saida ya gama shan ruwan  sannan yaron sa yace ranka ya dade kaga inda ta yankeni da wuka, ba tare daya kalli wurin ba, yace wato kauranyace, ga sane ga yanka,


Wanda samha ta yanka da wuka kuma an kaishi asibiti ba wani yanka bane sosai gaskiya, dan kadan ne ta mishibai wani yanku sosai ba dressing akayi masa kawai suka tafi gida,


Tunda su samha suka koma gida, kawu sai raba idanuwa yake yana kara irga kudin, saida ya gama sannan yayi tsaki tare da kashe yusra da mari kuma ya mari kausar amma bai mari samha ba, sannan yace wannan dan kudin shine kudin siyen gida? To wallahi ko giya basu isana sha, idanuwa samha ta zaro tare da cewa haba kawu? Kudi masu yawa haka duk zaka tattara kasha giya dasu? Kallon samha yayi sannan yace samha insha giya insha sigari inyi caca kona kodin da benalin ban samu ba, a hakan ma wai maleji zanyi, ya watse kudin kasa tare da cewa fadamin taya zasuyi su isheni?


Kallon yusra yayi tare da cewa daukomin giya a frij, yusra ta tashi a hankali tana rike hannun ta mai ciwo, taje ta bude frij ta fiddo mishi giya ta kawo mishi, haka ya balle murfin ya fara sha, tashi yayi ya fita daga dakin yana ci gaba da shan giyarsa,


Kawu yana fita kausar ta matso kusa da samha tare da cewa samha Allah ya rufa miki asiri, samha tace miye? Kausar tace wallahi mu rufa ma kanmu asiri mu sake wurin sane, dan kinsan Allah wannan mutumin ya kamaki saiyaji miki ciwo, kausar taci gaba da cewa wasu katti ukku yasa su rikeni, Allah ya taimakeni na cire nikaf dina ina ta bashi hakuri nace ba nice samha ba, samha nidai shawara daya kiyi hakuri mu daina zuwa wurin nan,


Samha tace ga inda muke samun kudinmu? Miyasa zamu daina zuwa wurin? Yusra tace wallahi wannan mutumin idan ya kamaki saikin kwammace kida da karatu, kausar tace da harbina zaiyi da bindiga nayi ta bashi hakuri ina ce mishi ba suna na samha ba wallahi na bashi hakuri sosai amma saida ya mareni yana kokarin harboni in fado daga saman bene in mutu,


Samha tace barshi ni zan harboshi ya fado daga saman benan ya mutu kowa ya huta,  can kuma tayi nazari sannan tace yawwa ku barni nasan maganin dan iska, yusra tace miye zaki mishi? Samha tace sunan sa kawai nake so ku nemo min, tsaki yusra tayi tare da cewa mi zakiyi da sunan sa? Samha tace muyi kokarin samun sunansa, ni matsalar ma bazan ganeshi ba, tunda gashi naje caka mishi wuka na yanki wani daban, kausar tace idan dan suna baki da matsala, samha tace Allah ya kaimu gobe lafiya, gaba dayansu suka amsa da ameen,


Samha tace ma kausar da Allah dan tashi kice ma kawu ya bamu abinda zamuci danni wallahi yunwa nakeji, daga waje kawu yace ga abinci nan kuxo ku dauka, kausar taje ta dauko abincin sannan dawo daki,


Saida dare yayi sosai sannan kawu ya shigo gida yana kiran sunan samha, tanajinshi amma tayi mishi shiru, dukan kofar dakinsu ya farayi tare da cewa samha yayi maganar ne cikin muryar "yan kwaya, cikin bacci kausar taji dukan kofa dan haka ta tashi a hankali tare da cewa samha kawu yana magana fa,


Samha tace naji shi kada ki sake magana barshi yayi ta haukansa, saida ya gaji da iskancinsa sannan ya wuce dakinsa ya kwanta,


Haka dai samha da yusra da kausar sukayi ta bige bigensu suna sace kudaden mutane , duk da ciwon da yusra take fama dashi kawu yace dole sai taje anyo aiki da ita a haka dai suka samu suka hada kudin gida da kawu yaje yasa shi a caca, suka biya kudin,


Yusra tayi kokarin yin binciken sa kamar yanda tayi alkawari, kuma ta samu ta samo sunan sa, Hydar Naseer Hamza, yanda ta binciki sunan sa haka tayi kokarin sanin waye shi, amma hakan dai bata samu ba, andai fada mata cewa mamanshi da babanshi sun rasu sanadiyar hadarin jirgin sama da suka samu, dan gajeran tsaki yusra tayi tare da cewa amma fa gaskiya bana tunanin daidai aka fadamin,



Yusra ta kara da cewa amma gaskiya samha ki fita harkar mutumin nan kima daina wani maganar m card dinki, ki barshi da Allah, dan wallahi yayi rantsuwa idan harya kamaki sai ya tilloki daga saman bene, kuma kindai ga benan wurin nan hawa biyar dan kafin ki kawo kasa inajin rai yayi halinsa, samha ina shawartarki kiyi hakuri ki fitar harkasa wallahi, murmushi samha tayi sannan tace na ranste da girma Allah saiya bani memory card dina, banda kike mahaukaci inma barmishi da m card lallai ma yusra banma taba samun dan iskan daya raina min hankali irinki ba, ashe haka nan nake kokarin ma wannan dan iskan rashin mutunci ga babbar "yar iska a gida ina tare da ita, shin a hannunwa ma ya anshi m card din idan ba'a hannunki ba? To idan har kika bari na zare hannuna a lamarin saiki anso shi da kanki, yusra tace Allah ya baki hakuri,


Saida sukayi kalaci sannan suka fita daga gida, dan yau sunyi sati biyu basuje wurin ba, lokacin da suka isa wurin babu mutane sosai, yusra ce ta fara hango yaransa suna shawagi a wurin, dan haka tace ma samha taho muje,,


Shi kuma yana zaune saman wani abu amma idan ka ganshi zakayi tunanin tsugunne yake, wani karfe yake dagawa da hannu daya yana kallon su samha da sukeyowa wurinshi amma idan ba shiba babu wanda ya isa ya  gane cewa su yake kalloba, ganin sun kusa isowa wurinsa yasashi yin,


Murmushi yayi sannan ya mike ya fara tafiya cike da izza yabi wata hanya ya shige, kausar tace samha ya gudu tana nuna mata inda yayi da hannu,  itama a hanzarce samha tayi wurin dan bin bayansa, shi kuma yana shiga a aljihunsa ya ciro marX ya rufe fuskarsa ko miya sa yayi ? Oho 🤷🏻‍♀


Yana sakawa ya boye a bayan kofa, samha a guje ta shiga wurin tare da rike kofar tana dan kalle kalle ta nasu kamar wanda za'a cakawa allura so kawai take taji ta ina zata jiyo motsin sa? Hannuta kuma dayan yana saman kugunta daidai inda ta soke wukarta, su yusra ganin samha ta shiga a guje yasa suka fita daga wurin suka koma waje suka tsaya,


Ganin tsayuwar bata fishshesu yasa yusra ta fara kiran wayar samha, samha dake tsaye ta rike kofa jin shigowar wayarta yasa ta maida hankalinta wurin wayar, ganin yusra ce yasa ta dauki wayar sannan tasa earpies a kunne ta mayar da wayar cikin aljihun wandonta dan wannan itace sana'arsu idan sukaje sata haka sukeyi sai suyi ta magana a haka, bayan ta mayar da wayar a aljihu ta fara magana cewa yusra ya akayi ne?


Ajiyar zuciya yusra tayi tare da cewa samha kin ganshi samha tace A, a, yusra tace to kada ki kashe waya don Allah ina ganin a haka hankalina zaifi kwanciya samha tace to babu damuwa,


A hankali samha ta fara tafi tana shiga cikin wurin sadaf sadaf kamar tana tafiya saman wuta harta shiga ciki gaba dayanta, tana shiga ta fara dube dube,  jin an rufe kofa yasa samha juyowa da sauri tace Ah kamar wanda aka watsa ma ruwan zafi,


 



*By meelat musa*





⚜ *B. W. A* 🖊

[05/04 4:44 pm] Washa: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊



                 *SO*

     *MUGUN WASA*



       *{ Love is a bad game }*




*JAMEELA MUSA* { meelat musa }




*Story, Writing & Editing*

                   *by*

         *Meelat Musa*



                  *SO*

      *MUGUN WASA*


Dedicated to, Real Mai dambu,


Gaisuwa,

*Asmeenat Xeeyan*

*Ayush Iliyasu*

*Na'ikke*

*Maman Arfat*



*8-10*



Da sauri ta fizgo wukarta daga cikin kugunta tayi mata rikon kirki, rikon da tayi ma wukar yana nuni da idan ya masto kusa da ita tou pha lallai sai tunbinsa yasha iska,


A hankali hydar ya fara tafiya dan ya isa kusa da samha, samha ganin yana tun karota yasa ta jefa mashi wuka, da sauri ya goce wukar ta wuceshi ta soki bango,


Juyawa yayi ya kalli wukar lallai fa a bango ta shige, jinjina kansa yayi tare da maida dubansa wurin samha a ranshi yace dafa ban goce ba shikenan data sameni,


Dauke fuskarsa yayi daga duban samha sannan ya juya inda wukar ta soke, ya zarota yayi kan samha da ita, idanuwa samha ta zaro tare da cewa idan ka sokamin nima saina caccaka maka ita harsa naji baka lumfashi,


Baiyi magana ba ya fara matsawa saida ya kusa isa kusa da samha sannan shima yayi jifa da wukar kamar yanda tayi mishi, a tsautsayi kuwa wukar ta soki gefen kafadar samha, wata irin kururuwa samha tayi tare da cewa nika soka da wuka? Saina kasheka ta karasa maganar cikin disashewar murya saboda zugin da takeji a wurin, 


Yusra dake waje tasa earpies a kunnenta suna magana da samha, jin samha ta ambaci wuka yasa tayo ciki a guje tare da cewa jama'a ku kawo dauki, shi kuwa baibar samha a haka ba wata wayar wuta dake bayanshi ya dauka yaci gaba da dukan samha, tare da cewa ni sa'arki ne zaki zo kina  min sane? Bakaji ina magana? Idan kika kuskura kika sake tabani kina man sata saina gundile mike hannu,


Yana dukanta yana tambayarta kamar uwa tana dukan danta, rike wayar wutar samha tayi gam, sannan tace nika caka da wuka ko? Ta jinjina kanta alamar tambaya, samha taci gaba da cewa da wukar ta soki zuciyata fa a maimakon gefen kafada ta fa? Hawayen azaba ne suka gangaro mata daga idonta, samha taci gaba da cewa to lallai idan har kaga na cire wannan wukar daga inda ka cakamin shi tou pha lallai na tabbatar an gitta gawarka a mankara  za'ayi maka sallah dan kaika kabari,


Samha taci gaba da cewa saina kasheka, da kaina zan kashe ka kayi mutuwa irin ta karnuka, jin samha tace saita kashi shi yasa hydar ya fara kokarin yaye mata nikaf din data rufe fuskarta dashi dan yaga fuskarta, amma ya gagara, yusra kuwa cikin waya sai cewa take samha wai miye? Kiyi magana mana, samha tayi shiru, su kuma mutanen da suka taru a bakin kofa ganin baza a bude ba yasa suka fara harbin kofar da karfi dan jiyo muryar samha tana saita kashe hydar,


Shake mata wuya hydar yayi tare da cewa nine zaki kashe? To kasheni gani a gabanki maza maza, maza kasheni da Allah rike kanta yayi sosai yana kokarin fara buga mata shi a bango, jikinta na rawa takai hannunta cikin aljihun wandonta ta ciro wata "yar karamar wuka dakel tana cirota ta cakawa hydar a hannu tare da cewa an fada maka maza suna tabamin jiki ne? Wato maganar daya fadawa Yusra cewa waye ya fada miki mace tana taba min jikinshi? Shine samha ta fada mishi itama,


Jin samha ta soka mishi wuka a hannu yasa ya rufe samha da duka babu ji babu gani yana dukanta yana halbina yana tattakata, amma duk bala'in da yake mata baisa samha ta cire wukar daya soka mata a kafada ba,


Haka yayi ta dukan samha har aka bude kofar, bodyguard dinsa ne a gaba wurin shigowa suna shigowa sukayi  wurin da yake dukan samha da sauri suna rikeshi amma sai kara kaiwa samha harbi yakeyi yana kokarin kwacewa daga rikon da sukayi mishi,


Sai nuna samha yake da hannu amma ya kasa magana, su kuma su yusra suna shigowa suka kama samha dan tafiya da ita, amma samha sai kara jaddadawa hydar takeyi saita kasheshi, da ido kawai yake bin bayan samha da kallo a zuciyarshi kuwa shine kadai yasan abinda yake burin yi akan samha, su samha suna fita ya cire abinda ya rufe fuskarsa sannan yayi kyakkyaean murmushi,


Ranka ya dade wannan ai ba aikinka bane, saboda waccan "yar yarinyar ka tsaya kana bata ranka?  Bodyguards dinsa sunfi su goma a gabanshi suna bashi hakuri tare dayi mishi alkarin zasuyi mishi maganin samha, murmushi yayi tare da cewa kada wanda ya taba ta, su barta dashi, yana fadin haka yayi gaba da sauri suka bi bayanshi cikin girmamawa,


Lokacin da su samha suka isa gida har masassara ta rufeta saboda wukar dake cikin jikinta, kawu kuwa yayi masifa yayi babbar bala'i saboda an cakawa samha wuka, kuma yayi alkawari sai ya rama abinda akayi wa samha, 


Juyin duniya babu wanda kawu baiyi ba aje asibiti a cire wukar ayi mata dressing amma fur samha tayi rantsuwa sai gobe za'a cireta kuma sai taje da safe wurin da suke training din taci mutuncin hydar sannan taje asibiti a cire mata wukar,


Babu yanda kawu ya iya haka ya hakura ya fita daga dakin tare dayi ma samha alkawarin sai yasa hydar bakin ciki tunda har yasa samha kunci,


Saida kawu ya fita daga dakin sannan samha tayi murmushi tare da karkatawa ta fiddo wayar hydar daga aljihunta da hannun haggunta mikawa kausar wayar tare da cewa ya kwace min m card dina da karfin sa, ni kuma na kwace wayar banza da hikimata da kwarewata wurin iya sane { sata },


Gaba dayansu suka sheke da dariyar mugunta, yusra tace kai amma samha baki da dama, murmushi samha tayi tare da cewa a to, ai nafishi rashin kunya kuma ni nafishi taurin kai, saima gobe zai tantance haka, kinga yau sai ya kwana da bakin ciki a zuciyar sa rashin wayarsa a kusa dashi, haka dai taci gaba da kudiri a ranta,


Daren ranar nan samha bacci ya gagareta, banda nishi babu abinda takeyi , sai kwalla dake diga daga cikin idonta a hankali ta tashi zaune ta jingina bayanta da bango, ta dukar da kanta kasa, tana sauke ajiyar zuciya, kausar ce ta farka tare da cewa samha sannu, ba tare da samha tayi magana ba ta jinjina kanta alamar yawwa,


Kusa da ita kausar ta matso sosai tare da cewa tun da daddare ake kiran wayar nan amma ban dauka ba, dana gaji ni kuma kawai saina kashe wayar baki daya,  sahma tace to, 


Da safe kuwa tunda samha ta gama sallah asuba take zaune ta tsurawa agogo ido tana jiran lokaci yayi, tana nan zaune har lokaci yayi tace ma su yusra suje, 


Gaba dayansu suka tashi suka fita ko kalaci basu tsaya sunyi ba, suna fita suka samu napep ciniki sukayi dashi sannan suka shiga suka tafi,


Suna zuwa suka sallami mai napep sannan suka shiga cikin wurin gaba dayansu, haka suka gaji da dube dubensu amma basu ga hydar ba, samha ta kyalkyale da dariya tare da cewa dan iska yaji tsoro kenan, Yusra tace to mu tafi tunda baizo ba muje asibitin don Allah ko munyi mun gama da wuri danni wallahi banajin dadin jikina so kawai nake in kwanta,


Juyawa sukayi suka fita har suna kokarin shiga napep motocin hydar suka fara shigowa wurin, tunda hydar ya hango su samha yayi sauri ya rufe fuskarshi kamar yanda yayi jiya, bayan motocin sun gama parking ne aka bude ma hydar dan ya fito, a hankali ya ziro kafarshi daya amma har yanxun bai fito daga motar ba,


Ganin yana raina musu hankali yaki fitowa yasa samha tayi wurin cike da masifa, tun kafin ta isa bodyguards dinshi sukayi kanta, hydar yace su barta tazo, matsawa sukayi suka bata wuri ta wuce har kusa dashi sannan ta rike murfin motar, ba tare daya kalleta ba yace ya akayi ne? Tace magana ta farko ka kalleni ka gani,


Yace bana bukatar kallonki fadamin abinda kuma kike nema a wurina? Samha tace zuwa nayi in nuna maka wukar daka sokamin jiya gata a jikina, murmushi hydar yayi wanda baizo cikin bakinshi ba iyakar murmushi a zuciyarsa, sannan yace naji, sai kuma mi? Samha tace dama dan in fada maka yanda nabar wukar nan ta kwana a jikina saina kasheka, 


Hydar yace tou, daga nan kuma sai mi? Samha tace sai ka bani m card dina, hannunsa yasa a aljihunshi ya ciro m card din, nan nade a tissue ya mika ma samha, kafin samha ta amsa yace to yanxun dai babu wani abu tsakani na dake, dan haka idan na sake ganinki a wurin nan kinsan Allah duk wanda ya tsaya miki a garin nan saina lalata miki fata da duka, yaci gaba da cewa maganar wayata kuma itama ki dauka na bar miki amma ki cire layikan ki kayarsu, yana gama fadin haka ya fito daga motar ya raba ta gaban samha ya wuce,


Yana wucewa samha ta daga muryar ta tare da cewa anje anzo kuma bazan fasa zuwa ba idan gidan baban mutum ne sai in gani idan ya isa ya hana inxo, shidai baiyi magana ba kuma bai waiwayo samha ba kuma baiyi magana ba ya wuce abinsa, mabiya bayansa kuma suka bishi dan take masa baya,


Tsaki samha tayi tare dayin magana kasa kasa cewa ai tunda ka bata ma samha rai to lallai sai samha tasa ka kunci harsai ka bar garin nan, Kausar da Yusra a tare suka iso wurin tare da  tambayar samha abinda yake faruwa tsakaninta da hydar, tabe baki tayi tare da cewa muje kawai,


Haka suka dunguma zuwa asibiti, likitan da zaiyi ma samha dressing ya fara fada wai tabar karfe yakai wani lokaci a jikinta, cikin masifa samha tace kai da Allah malam rufe ma mutane baki kai nan har wani kokari gareka? Namiji da aikin allura idan so kake ka nuna gwaninta kaje ayi yaki dakai ko ka tafi aikin soja, kainan har wani ji kake kai wani ne? Tsaki tayi tare da cewa bari a caka wukar a jikinka muga kai idan kana iya yini da ita? Shidai baiyi magana ba, samha taci gaba da kwaikwayon maganarsa miya sa kika bari karfe yakai wani lokaci a jikinki? Kaza kaza, dan rainin hankali kawai dakai,


Dan gajeran tsaki samha tayi sannan taci gaba da cewa nawa ne kudin ka? Yace ni bazanyi miki aiki ba, samha tace ka huta nima matsamin akayi saina cireta banda haka ai ina da aikin yi da bazan ma saurari lamarin wata wukar banza ba bare har inyi kokarin rabata da jikina, mikewa tsaye tayi tare da cema su yusra muje da Allah,


Ganin samha tana kokarin fita yace zo, juyowa tayi tace miye? Yace zo in cire miki, dariya samha tayi sannan tace ashe dai ana so ake kaiwa kasuwa, a daidai lokacin data zama sannan taci gaba da cewa mahaukaci da bafullata yace mai nono kawo, bayan tazo mahaukaci yace sauke, ta sauke yace samin na ishirin ta zuwa nashi sai mahauci yace shanye,


Ba fulatana ta daga ta shanye, mahaukaci yace karo na ishirin, ta kara mishi ya sake cewa shanye, haka yayi ta sawa tana zuba nono tana shanyewa har saida nono ya kare, sannan mahaukaci yayi dariya yace munafika ashe dai anaso ake kaiwa kasuwa, doctor kaima fa irin abun kayi, dariya yayi bamai yawa ba sannan yace ni ba kudinki nake so ba kawai tausaya miki ne,


Samha tace to godiya nake likita bokan turai, saida ya gama dressing ya rubuta mata magunguna, samha tayi godiya, doctor yace bayan kwana biyu ta dawo dan a kara duba mata hannun, godiya samha tayi sosai, sannan suka tafi,


su samha na fita doctor yayi murmushi a bayyane yace kai yarinyar nan kangararrace, Allah ka kara shirya mana zuri'a niko nace amin,


Haka dai samha taci gaba da kula da hannunta, kuma tana zuwa wurin doctor dressing kamar yanda yace, kuma doctor yayi juyin duniya samha ta bashi number su rika gaisawa sai tace mishi kawunta ya hanata magana da maza, daya matsa mata tace to saidai ta bashi number kawun, doctor yace baisan na kawu, kuma yayi ta fada gidansu amma taki, haka dai samha tayi jinyar hannunta har ta warke,


Tunda hydar yayi ma samha kashedi da wurin training nasu ita dai ta daina zuwa kwata kwata amma su yusra suna zuwa, 


A kofar dakinsu samha kawu tsaye sai kwarara sallama, yakeyi, daga cikin daki samha ta ansa sallamar, kawu yace samha mi kikeyi ne yanxun? Tace ba komai kawu yace to fito, samha tace to, tashi tayi ta saka hijabi sannan ta fito tsakar gida,


Kawu yace maza maza kiyi wanka zaki rakani anguwa kuma ba wannan zundumemiyar hijabin zaki saka ba, kallonshi samha tayi sannan tace idan ban saka hijabi ba mi zan saka? Ledar hannunshi ya mika mata ba tare da yayi magana ba, ansa samha tayi ta fara dubawa, kaya ne a ciki, fiddo kayan tayi ta fara dubawa riga da skart ne da gyale sai takalmi da jaka masu kyau,


Sake maida dubanta tayi wurin kawu sannan tace kawu a ina ka samu kudi? Murmushi yayi sannan yace kedai ki shirya muje, itama murmushi tayi sannan ta juya ta koma daki,


Babu wani bata lokaci samha ta fito cikin shiga mai kyau da kama hankali, shima kawu zugewa yayi cikin kananan kaya sannan ya kawo glass mai kyau ya dora a fuskarshi yayi kyau sosai, ba tare daya kalli samha ba yace muje,


A cikin mota kawu ya dauki samha, samha an wani kashe a gidan gaba, duk wanda ya kalli samha sai ya sake kallonta, tafiya yake da motar cikin natsuwa har suka isa inda zasuje kawu baiyi magana ba, bayan yayi parking ne ya fiddo wani glass ya mika ma samha,


Ansa samha tayi ba tare da ta tambayi kawu glass din miye ba? Kallonta kawu yayi sannan yace saka, sakawa tayi ba tare da tayi gaddama ba ko tambayar kawu glass din miye ba,  kawu yace kinga wannan glass din na fuskarki? Samha tace Ey, kawu yace to zai rika hango miki numbobi na jikin catin cacarmu idan kin gani saiki fadamin,  anshi wannan ya sake mika mata tare da cewa saka a kunnanki, samha ta ansa ta saka shima batayi musu ba, bayan ta saka kawu yace kinga wannan abun na kunnenki? Samha tace Ey kawu yace to ko ina da nisa dake zakiji maganata sannan kuma nima idan nayi magana zaki ji, samha ta daga kanta alamar gamsuwa,


Kawu yace fita muje, bude mota samha tayi ta fita, shima kawu fita yayi sannan ya rufe motar yace ma samha muje, jerawa sukayi suna tafiya har suka isa cikin wurin,,,,


Suna shiga gaba daya kallo ya dawo kansu, kawu kuwa aka wani fiddo sigari aka kunna mata wuta ya kaita ga bakinshi ya fara ibar hayaki yana wani daddaga kansa sama yana fiddashi cikin iskanci, abokan kawu yan duniya suka fara ihu ganin abokinsu yazo da mai zafi,


Bayan sun isa wurin mutane kawu ya fara gaisawa da abokansa, sannan ya matsa inda ake siyar da giya, dan wurine na tantiran "yan iska, ga karuwai nan iri iri, masu caca sunayi masu lalubar mata sunayi masha nashan giya , to shima kawu saida yasha yayi tatul saida ya gama sannan yace ma samha suje,


Bin bayanshi tayi har ya isa inda ake wasan caca, kujera kawu yaja ya zauna, sannan ya nunawa samha wurin zama kusa dashi, bayan sun zauna ne, kawu ya gabatar da samha a wurin abokan wasan cacarshi fadin sunanta daga karshe kuma ya rufe musu da cewa amanarshi ce, wani dan duniyar abokin kawu ne irin "yan iskan nan yace wowww samha is gud ai da kyau da kyau  da kyau yana wani iskanci da idanshi , hannu kawu ya daga mishi sannan yace ku saurara,


Gaba daya sukayi shiru amma hankalin kowa yana kan samha, kamar yanda suka saba idan zasu fara wasan caca, yauma hakan ta kasance, mai gabatar da shirin caca ya mike tare da cewa kowa da kowa ya saurara, gabaki daya wuri yayi shiru kamar irin abun nan da yara suke cewa wai mutuwa ta ratsa , to haka wurin yayi shiru bakajin karar komai sai karar fanka,


Bayan kowa da kowa yayi shiru, ya fara da cewa yau wasa ne tsakanin kalifa Abbas, wato kawu,  sai kuma abokin wasan nasa wato kamal dan cinna, dan haka kamal ya saka naira na gugar naira har naira dai dai dai har naira miliyan daya sannan ya daga jakar kudin, gabaki daya wurin ya dauki ihu da sowa, bayan an tsagai yace shi kuma yau kalifa Abbas da wani sabon salon yazo, dan Allah kalifa miko naka, kawu ya tashi tare da kama hannun samha suka isa wurin,


Mai gabatar da shiri yace dan Allah jama'a ku saurara ina san kowa da kowa ya bani aron hankalinsa, bayan kowa yayi shiru kuma kowa ya zubo idanuwa yana kallon sa, yaci gaba da cewa kunga wannan zukekiyar yarinyar? Gatanan dai san kowa kin wanda ya rasa gata da kyakkyawar fuska, kuma gata mai dirin gaske ga kyakkyawan hanci sannan kuma ga ta da kyakkyawan gashi wanda yake kwarara a tsakiyar gadon bayan ta kamar kunfar teku, kunga duk kyawun yarinyar nan da tsaruwarta da haduwarta, da manyan idanuwanta masu firgita mai kallonta wai kalifa yace idan har akaci shi a caca tofa lallai ya badata a maimakon kudi, gaba daya wurin ya dauki ihu mutane suna kururuwa kamar karnuka sunga karya, yayin da wasu suke cewa sunayin cacar kowa yaci gaba da sako kudade masu yawan gaske, dan kowa yana san ya ciyo samha a natsayin kautar caca,


Murmushi kawu yayi sannan yaja hannun samha suka sauko daga inda kowa da kowa yake kallonsu, dawowa sukayi suka zauna a tebirin cacar yayin da mutane suka zagaye tebirin da ake gabatar da shirin wasan caca dan kallo, kowa ya zuba ido dan ganin waye zai ciwo samha a shirin wasan caca, bayan kowa ya natsu shirin wasan caca ya fara,,



*Meelat Musa ce*

[05/04 4:44 pm] Washa: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊



                 *SO*

     *MUGUN WASA*



       *{ Love is a bad game }*




*JAMEELA MUSA* { meelat musa }




*Story, Writing & Editing*

                   *by*

         *Meelat Musa*


*Albishirin ku daukancin masoyan brilliant writers association, ina kuke? Tou ku marmatso domin shararrin marubutan nan na brilliant association sun sake dawo muku da wani sabon salo mai burgewa bugu da kari  shahararin marubutan sunxo muku da tsaraba mai shiga zukatan masu karatu,*


*Ita dai ummu sayyid tazo muku da tsarabar littafinta mai suna FURUCI,  ita kuwa saleehat tazo muku da littafi mai suna DACE DA JUNA, ku daddage ku durawa wayayonku carji domin kada a barku a baya sai kunji, daga taskar tsakar gidan brilliant writer association ni meelat musa nake cewa asha karatu lafiya*



                  *SO*

      *MUGUN WASA*


Dedicated to, *Real mai dambu*



*11-13*


Kamar yanda kawu ya fadawa samha haka taci gaba da fadawa kawu nombobin da take gani,


Haka akaci gaba da buga wasan caca, kawu saida ya lashe duka kudaden da aka dora mishi, lokacin da wasa ya tashi wurin ya kideme wanda basu samu samha ba sunyi bakin ciki sosai,


Kawu kuwa ya tattara kudadensa ya dauki wasu samha ta dauka wasu suka wuce abunsu, dama haka wasan caca ya gaji asara, dan duk mutumin dayece caca tou pha lallai yana tare da asara, wata rana kaci wata rana a cika,


A mota kawu kuwa saidai yace wuhuuuu,,, kai samha lallai nayi dace, Allah ya cikamin burina akan, yana maganar yana dariya, ganin kawu yana farin ciki yasa samha itama tayi murmushi tare da cewa,


Kawu don Allah yaushe zaka hadani da iyayena? Murmushi kawu yayi sannan ya mika hannunsa ya kamo hannun samha ya rike a cikin nasa a hankali yake dan murza hannunta, sannan yace kada ki samu damuwa kasancewa dani yafi miki dadi akan ki kasance da kowa!


Murmushi karfin hali samha tayi sannan tace haba kawu, nayi maka kokari fa kuma nayi maka hallaci na tara maka kudi sosai, gashi yanxun har ka fara sakani a wasan caca yanxun da, da tsotsayi idan wani ya cika a caca kawai zaka bashi ni, ya tafi dani, shikenan haka rayuwata zata lalace nazo duniya ban wani san dadinta ba, kowa ya rayu da iyayenshi amma ni bani dasu,


Kawu ka tausayamin ka hadani da iyayena domin gaskiya ka gurbata min rayuwata, idan har na mutu a wannan halin lallai ban dace da rayuwa ba, parkig kawu yayi da mota a gefen titi, kallon samha yayi sannan yace,


Sahma nine na gurbata miki rayuwa? Samha tace Eh mana ai idan akwai babban wanda ya gurbata min rayuwa ba kowa bane kaine, kullum cewa kakeyi zaka hadani da iyayena inyi maka sata kullum sata kullum sata ko beranya bai kaini sata ba, haba kawu kaji tsoron Allah,


Murmushi kawu yayi mai shiga zuciya sannan ya riko kafadar samha cikin kyakkyawan murya kawu mai tattare da daukan hankali yace kiyi hakuri, ki daina cewa na gurbata miki rayuwa zaki gane abinda nake nufi sai nan gaba,


Cikin damuwa samha tace kawu miyasa sai nan gaba? Ka fadamin don Allah dan in samu natsuwa a raina, wani irin kallo kawu yayi mata wanda yasa ta jin wani bakon al'amari, murmushi kawu yayi tare da dan bude idanuwanshi gaba daya yanda yayi abun yasa samha tayi saurin rufe idonta gabanta na faduwa, murmushi kawu yayi sannan yace kiyi hakuri samha duk wannan abun saboda ke nakeyi da zarar na tara kudade masu yawa zan daukeki in tafi dake in canja miki sabowar rayuwa,


Samha tace amma miyasa ka zabi wannan sana'ar ne kawu? Murmushi kawu ya sakeyi sannan ya shafa gefen fuskar samha, ba tare da yayi magana ba yaja motar suka ci gaba da tafiya, har suka isa gida babu ya sake magana, 


Lokacin da suka isa gida har su yusra sunyi bacci, samha tana kokarin shiga daki ne, kawu yace samha, juyowa tayi ba tare da tayi magana ba, kusa da ita kawu ya matsa sannan yace samha 3 3 2, cikin rashin fahimtar abinda kawu yake nufi samha tayi yake 😬, sannan ta shige dakinsu,


Shima kawu dakinsa ya shige, saida yayi wanka bayan ya gama ya shirya, inda kattin kaladun hotunan samha suke ya matsa, duk hoto daya ya cinye bango daya, a jikin kalanda daya hotunan samha ne sun kasu kashi hudu, duka bangunan daki kalanda ce daga farko bango har karshe,


Hotunan samha sunyi kyau sosai wasu tayi murmushi wani kuma tayi kalar sakata, murmushi kawu yayi sannan ya dauko jan baki kamar yanda ya saba,  yabi hotunan yana shafa musu rigar jikinshi ya cire, sannan ya matsa jikin mirrow, daidai inda ya darkaka sunan samha yakai hannunshi ya shafa, an karta fatarsa an rubuta *SAMHA* murmushi kawu, sannan ya matsa wurin hotunan samha, yace Allah ka dorawa samha kaunata Allah kasa samha ta soni , 


Haka yaci gaba da sabbatu a jikin hotunan samha saida ya gaji sannan yazo ya kwanta yana kallon hotunan samha, murmushi yayi sannan ya kalli wani hoton samha tanayin fushi murmushi kawu yayi sannan yace miye kike fushi? Kallon wani hotonta yayi wanda tayi dariya murmushi kawu yayi sannan ya tashi saida yaje yayi kissing din hoton sannan yazo ya dauki wani dan karamin hotonta ya rungume dashi yayi bacci a jikinshi,


Da safe bayan samha tayi kalaci, tace ma kausar ta dauko mata m card din data bata ajiya, bayan an dauko m card din ne, ta saka a waya dan dubawa amma a mamaki babu komai a m card din komai ya goge, sake dubawa tayi sosai amma fa ba komai har yanxun, samha tace yusra bafa komai a m card din nan, kausar tace kamar ya babu komai? Cikin sanyi samha tace dan iskan hydar din nan ne ya goge komai, wani irin lukeken zagi samha ta dirkakawa hydar sannan tace yanda ya goge komai na cikin m card din saina goga mashi bakin ciki da harya mutu bazai manta dani ba,


Yusra tace wai miye a m card din ne samha? A sanyaye samha tace bansan ko miye a ciki ba tunda ban gani ba amma koma miye nasan sakone mai mahimci tunda daga hannun a halina ya fito, ku tashi muje mu sami hydar saina ci mashi mutunci,


Haka suka tashi suka dinguma baki dayansu suka fito, suna fita napep suka hau suka nufi wurin, rabon samha da taje wurin tafi wata biyu sai yau,


Suna zuwa, bayan sun sallami mai napep, suka shiga, suna shiga suka fara dubawa babu hydar babu dalilinsa, a gefe kuma mutane ne sun cika sosai ga kuma "yan jarida suna ta daukar rahotanni komi akayi ne oho?


Cikin sauri samha ta isa wurin tare da tambayar lafiya? Wani dan jarida ne ya juyo wurinta tare da cewa ko kema kina da abin cewa ne? Cire nikaf din fuskarta tayi sannan tace idan har na fadi sakona zai isa inda nake so yaje ne? Dan jaridar yace mi zai hana kuwa? Murmushi samha tayi sannan tace kasan *Hydar Naseer Hamza* ne? Yace sosai ma , na sansa,


Murmushi samha tayi sannan tace to gaskiya ya shiga rayuwata sosai, ya matsamin kace mishi nace ya fita hanyana idan ba haka ba na kamashi sai na lahira yafishi jin dadi, murmushi dan jaridar yayi sannan yace anya  kina iya karawa dashi? Bakiji kirarin sunan Aliyu ba? Bakiji hausawa suna cewa Ali zaki ba?  Samha tace ni babu wani ruwana Allah ma yasa giwane ba zaki ba, kuma idan kai Ali zakin ne idan har sakona ya iso a gareka ka nunamin kai jarumine gwarzo a cikin gwarazan maza idan har ka samu sakona nasan sai kaji faduwar gaba, dan rainin hankali ka dawomin da m card dina idan ba haka ba kasan halina, irin abinda nayi maka kwanakin baya irinshi zan maka, 


Dan jarida yace to ya kike dashi ne? Dan uwa ne ko soyayya, murmushi samha tayi tana tunanin abinda zata fada akan hydar dan ranshi ya baci, murmushi tayi sannan tace ma dan jarida Eh to dama maganar *SO* ne shine yake so na, kuma sosai kullum sai yazo gidanmu zance, tabe baki samha tayi sannan taci gaba da cewa kuma nace mishi bana sansa amma ya wani matsamin danni gaskiya babu soyayya a tsarin rayuwata kai hydar kayi hakuri kaji,


Dan jaridar yace to miya sa bakyasan kiyi soyayya dashi ne? Turo baki samha tayi sannan tace bashi kadai ne bana so ba, duk duniya babu abinda na tsana irin maza, bana san maza kuma bana san soyayya na tsani masu soyayya, dan jaridar yace miya sa kika sani kalmar *SO*? Samha tace kawun su waccan ne! Ta nuna inda su yusra suke tsaye, dan jaradir yace mi kawun nasu yace game da soyayya murmushi samha tayi sannan tace kawu yace *SO MUGUN WASA* ne, kuma yana fadamin wanda so ya wahalar a rayuwa wannan dalilin ne yasa na tsani kalmar *SO* da ma masu soyayyar ma maza da kuma mata baki daya amma fa banda babana,


Murmushi dan jaridar yayi sannan yace to hajiya samha nagode da wannan dan gajeran bayanin naki kuma na gamsu, miye sakonki na karshe wurin hydar naseer hamza? Samha tace sakona na karshe a wurinshi shine saina kafa maka babban tarihi a duniya sannan kuma sai kayi nadamar sani na, saboda gogemin komai da komai na cikin m card dina idan na kamaka kaima kasan sauran, 


Murmushi dan jaridar yayi sannan sukaci gaba da daukar rahotan ninsu bayan sun gama suka kama gabansu, suma su samha sun danyi sane sannan suka wuce gida,


Lokacin da su samha suka isa gida kawu baya nan, dan haka suna zuwa daki suka shige, bayan dukansu sunyi wanka sunyi sallah azahar ne, suna zaune zasu fara cin abinci yusra tace nikam samha in tambayeki ne?


Samha tace Allah yasa na sani, yusra tace mi yasa kikayi abinda kikayi ne a gaban "yan jarida? Dan gajeren tsaki samha tayi sannan tace nama sha maganar arziki ne, daga haka bata sake magana, kausar tace gaskiya da bakiyi haka ba, samha tace ke da Allah naje nayi ya dade baisa an kasheni ba sai wani daddaga murya kikeyi sai kace dan gidanku mtswww,  ganin yanda samha ta zakalkalo yasa sukayi shiru dukansu har suka gama cin abinci babu wanda ya sake magana,


Lokacin da jarida taje hannun hydar ba karamin baci ransa yayi ba, ga abokansa "yan gayu masuji da kansu sai bugo mishi waya sukeyi suna tambayar sa maganar samha, kowa yana so yaji karin bayani daga baki hydar,


Cikin tsananin bacin rai yake basu ansa cewa shi baima san yarinyar ba wallahi a idonshi bai taba ganinta ba, saike daukar jaridar yayi da take ajiye a  gefenshi ya sake duba hoton samha, iyakar sanin sa a duniya bai taba ganin wannan fuskar ba, amma dayaji maganar m card lallai ya yadda samha ce, sannan kuma tace zai gane kurensa da irin wannan maganganun hydar ya tabbatarwa da zuciyar sa ba kowa bane "yar sane ce,  { barauniya } dan gajeran murmushi hydar yayi sannan ya daga wayarshi ya kira wanda ya kawo mishi jaridar,


Bayan yazo hydar yace a ina ka samu jaridar nan ne? Cikin girmamawa yace ranka ya dade a wurin training na gani shine na taho maka da ita dan ka gani, tsadajjen murmushi hydar yayi sannan yace in kaso jeka abinka, juyawa yayi ya tafi,


Bayan fitar bodyguard nasa, kiran wani abokin hydar ne ya sake shigowa wayarsa, hydar ya dauka suka gaisa bayan sun gaisa, abokinsa faruk yace wai abokina ya akayi haka ne? Dan gajeran tsaki hydar yayi sannan yace nima ban sani ba, amma ka barni da ita zan koya mata hankali, faruk yace gaskiya kaci ubanta sosai ka nuna mata kai ba sa'an yara bane, manyan matanma koda da kudin gidansu tarayya da hydar saida rabonsu, daga ganinta "yar gidan bani Oho ce, hydar tace miye miye bani Oho? Faruk yace talaka mana alere dangin jakai banzar ta mutu gobe ma wasu zasu kawo maka hari, bare kai da tsadaddun mata suke so amma baka da lokacinsu har diyar gidan bani oho ta kawo maka raini? 


Dan gajeran tsaki hydar yayi sannan yace faruk ni matsalar ma wallahi yarinyar kauranyace yanka mutane takeyi da wuka, kuma ta iya salon mugunta iri iri, mutumin da yake nemanka da sharri sai kayi hankali dashi, kanaji abinda ta fadawa "yan jarida cewa bata san soyayya kuma ta tsani maza kaga dama ta fadamin da bakinta cewa itace ajalina, 


Faruk yace kasa a rufe maka banza ka manta da  lamarin diyar talakawa, dan gajeran murmushi hydar yayi sannan yace wannan ba mafita bace, barta dani ni zan ladabtar da ita, faruk har ka manta da wane hydar? Ai tama yi sa'a "yan manza sunyi laushi amma har yanxun ruwa yana maganin dauda, barni da ita saina sata jinyar zuciyarta badai tace ta tsanani maza ba? Barta hydar shine mai maganin kangararun mata, haka dai sukaci gaba da firansu daga baya sukayi sallama da juna kowa ya kashe wayarsa,


Daren ranar nan kirikiri bacci ya gagari hydar, yana tunanin irin hukuncin da zaiyi ma samha, ajiyar zuciya yayi sannan ya tashi ya zauna a gefen gado, kallon agogo dake makale a jikin bangon dakinsa yayi karfe 2:04am, 


A hankali ya koma ya kwantar da bayansa saman gadon sa fuskarsa tana kallon silin din dakin, murmushi yayi sannan ya shafa lallausan gashin kansa, a bayyane yayi magana cewa, "yar sane, kin hana hydar bacci,


Lallai hydar saiya kacaccala miki rayuwa, saina dasa miki baban tambarin da sai yasa kinyi a man zuciyarki, wanda so yayi ma mugun kamu ciwon zuciya sukeyi amma ke saboda kince kene ajalina shi yasa zan hukuntaki ta hanya mafi saukin mutuwa,  bazaki gane maganar  kawunki gaskiya bace saina doraki a babar cuta, wai *so mugun wasa*? Lallai  ne ke bazaki magane so ya zama mugu ba sai abun ya tattabata a kanki,


Nine mutum na farko da zan share zuciyarki in tada katangar sona a zuciyarki, kuma in koya miki so na, daga baya kuma in  rusa ta , sai na saka kin zama abin tausayi, duk kan gararki da jarumtarki bazaki iya control zuciyarki ba, saina mayar dake abin tausayi  sannan hydar zai zuke yabarki da babbar cuta a ranar zaki fadawa duniya cewa lallai *SO MUGUN WASA* dariyar mugunta hydar yayi sannan yace idan ni baki kasheni ba ni zan mayar dake dan bitin bitimi, kara shekewa yayi dariya sannan ya mike ya nufi toile, tare da kara kudirin azzatuwa da zaisa zuciyar samha,


Alwalla yayo sannan yaxo ya haye abin sallah dan ibadar dare wanda dama wannan aikin sa ne duk daren duniya baya bacci sai ya raya wannan daren,


Su samha cikin shirinsu na tafiya aikin sane, suna tsaye a gaban kawu shi kuma yana masu ban kwana zaiyi tafiyane, bayan ya gama musu ban kwana ne yace  yusra da kausar su tashi tashi sukayi dukansu amma sai yace samha ta zauna, ba musu ta dawo ta zauna,


Cikin wata irin murya kawu yace samha, ba tare data dago kanta ba tace na'am kawu yace kallarni, daga kanta tayi sannan ta kalli idon kawu cikin idonta, dararan idanuwan kawu , kawu ya fara wasa dasu cikin wani irin yanayi wanda yasa samha taji sanyi ya kamata, cikin rawar baki samha tace kawu miye? Murmushi mai narkar da zuciya kawu yayi ma samha, dan lumshe idanuwanta samha tayi sannan ta bude su,  tana ci gaba da kallon kawu, kawu yace abu na farko dazan fada miki shine ki kula da kanki babu so da kowa, mutane mugaye ne, mazan karni basa jin tsoron Allah duk wanda yace yana sanki kice a, a *SO MUGUN WASA*ne kinji ko? Kai kawai samha ta iya dagawa alamar gamsu dan kawu ya gama kashe ta murus , 


Kawu yaci gaba da cewa kuma idan ma soyayya zakiyi nine zan sama miki miji mai hankali mai sanki da yawa inyi miki aure kinji ko? Samha tace Tou , kawu yace tou 3 3 2, yake samha tayi dan bata san abinda hakan take nufi ba, dan kawu yana yawan gaya mata kalmar 3 3 2, 


Har kawu ya mike samha tace to kawu sai kuma maganar ahalina banji kanayin maganar gidanmu ba, murmushi kawu yayi sannan ya kama hannun samha ya mikar da ita tsaye, yace gidanku? Samha ta daga kanta alamar Eh, kawu yace ai nanne gidanku yana nunawa da hannunshi, sannan yace ahalinki kuma ai nine ahalinki, wata dakikar dariya samha tayi 😬 wanda yasa kawu shima yayi murmushi, 


Sannan yace muje, bin bayanshi samha tayi suna fitowa daga dakin su samha su yusra suka taso gaba dayansu suka bi bayan kawu danyi mishi rakiya, saida ya tafi sannan suma suka fita daga gidan,


Hydar yau baizo da boduguards nashi ba, shi daya ne yazo kuma tunda yazo yana cikin mota bai fito ba, kai hydar yayi wanka ya wanku sosai saboda hutu ya zauna a jikinshi, yayi gayu shi gayun da kansa zai nuna cewa hydar shine babban dan gaye, kyakkyawan gaske ga kamshi kuma kamshin maisa zuciyar mata saduda, kai hydar fa ya gama hadewa ga kudi ga mulki ga kyau ga asali , duk kangarar zuciyar mace idan taga hydar saitayi fatan ta sameshi matsayi mijin aurenta,


Lafiyayun gargasar jikinsa lulluluf sunyi kyau da jikin sa kamar ya kamasu ya jerasu a jikinshi yanda suka yi kyau, hydar yana da kyawawan idanuwa masu firgita duk wanda ya kalleshi wannan dalilin ne yasa baka iya ido cikin ido dashi, yana da hanci mai kyau wanda ya dace da kyakkywar fuskarsa, yana da girare masu kyau, idan kuma hydar yayi murmushi baka gajiya da kallonsa dan murmushi yana kara bayyana da aihanin kyauwunsa, yana da beauty point shi yasa mata suke kai masa hari, da wannan kyakkyawan surar da Allah yayi mishi shine yayi kudirin ladabtar da zuciyar samha, dan haka yau ya bude ainayin hydar din babu rufe fuska yau a bude yake,


Su samha suna isowa wurin suka sallami mai napep, hydar yana ganinsu yayi murmushi dagefen bakinsa, jan motarsa yayi tare da nufa inda su samha suke tsaye, glass din motarshi a sauke yake, dan haka yana isowa wurin ba tare daya bude motar ba yayi musu sallama fuskarshi na dauke da murmushi,


Da sauri yusra da kausar suka saukar da kansu kasa saboda hydar yayi musu kwarjini, gaishe shi sukayi ba tare da sun dago kansu ba, ya ansa sannan yace ina samha? 


Cike da tsiwa ta rike gudunta tare da cewa ya akayi ne? Tana magana tana murguda baki a zuciyar yayi dariya tare da cewa zaki ubanki ni nafi rashin kunya, amma a fili sai yace haba keko? Zuwa nayi in baki hakurin abinda ya faru a baya, yayi maganar ne cikin sigar lallashi,


Hydar yaci gaba da cewa bayan dogon nazari da nayi naga abinda nayi miki ban kyauta ba, amma kiyi hakuri ki daina rikeni a ranki kinji ko? Murmushi samha tayi sannan tace ashe dai kaji tsoro, hydar yace naji mana inani ina karawa da babar giwa, karo dake ai faduwar gabana, masalaha da zaman lafiya shine kwanciya hankali na, bara ma kiga shedar komai ya wuce, 


A daidai lokacin da su yusra sukayi ciki, shi kuma ya dage glass din motar abinda idon samha ya gani shine *I LOVE YOU SAMHA* haka hydar ya rubata a jikin glass din motar sa, 


Sannan ya sauke glass din, sanyayyan kallo hydar yayi ma samha tare da cewa i love u, yanda ya fadi kalmar yasa samha taji faduwar gaba, dan tunda take a duniya babu namijin daya taba furta mata yana san ta, bude mota hydar yayi sannan ya fito, kusa da samha ya matsa cikin disasshiyar murya hydar yace don Allah ki tausaya min ki so ni, ko yane kawai kidance kina so na so daya tak nake so ki fada,


samha tayi shiru, daf da ita hydar ya matsa sannan ya yaye nikaf din fuskarta, da sauri samha ta rufe idonta, hydar ya tabbatar lallai itace samha dan hotonta ne ya gani a jikin jarida murmushi yayi tare da cewa samha saina kafa miki babban tarihi a rayuwarki, sai kinyi alfahari dani , saki nikaf din yayi , sannan ya nufi wurin motarsa, bude motar yayi wata katuwar leda ya fiddo ya sannan ya rufe motar a gaban samha yaxo ya ajiye, sannan yace samha na tafi, zamuyi waya dake anjima, batace komai ba, har yaje ya shiga motarsa yaja yayi tafiyar sa,


Saida hydar tafiya sannan yace munafika, zaki gane kuskurenki, dan gajeran tsaki yayi sannan ya dauki glass dinshi ya saka a idonshi,


Samha jiki a sanyaye ta duka gaban ledar da hydar ya ajiye, budewa tayi, abinda idonta ya gani yasa ta mikewa da sauri tanabin inda yabi ya wuce da kallo,



*Brilliant writers asso*

[05/04 4:44 pm] Washa: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊



                 *SO*

     *MUGUN WASA*



       *{ Love is a bad game }*




*JAMEELA MUSA* { meelat musa }




*Story, Writing & Editing*

                   *by*

         *Meelat Musa*



                  *SO*

      *MUGUN WASA*



*Dedicated to Real mai dambu*



*14-16*



Saidai taga motan hydar ya bace daga wurin bat sannan ta koma ta tsuguna a gaban ledar daya ajiye mata,


A hankali ta fara dan budewa tana lekawa dan ganin abinda yake ciki, yusra da kausar ne suka fito da gudu tare da fadin samha tashi taso mu gudu, da sauri samha ta mike tsaye,


Kallonsu samha tayi tare da fadin ina kuka jijjibo wannan katon akwatin ne? Yusra tace kudai ku tsayar mana da napep kafin a cimma mana,


Samha tace nifa babu inda zamu je da wannan akwatin sai an bude shi naga abinda yake ciki, kausar tace aike matsalarki kenan zumudi ki wuce mu tafi idan muka je gidan sai a bude baki daya, yusra ta taka akwatin da kafarta tana dan bubbugawa tana cewa mun warke talauci kawu yaga kudin nan ai babu mu ba kara sane,


Kedai muje, a daidai lokacin da suka dauki akwatin sukayi gaba, ganin sun dauki akwatin yasa samha ta dauki ledarta tabi bayansu, napep suka tsaida sannan suka saka akwatin bayan napep dakel suka shigar dashi sannan suka shiga baki dayansu,


Kausar ce ta juya ta dora hannunta saman akwatin tare da fadin samha a akwatin nan kudin america ne, lallai idan kawu yaji irin kokarinmu tou pha lallai sai ya yaba ma gwazonmu, dariya tayi sannan ta kalli samha tace kema nasan zakiji dadi dan gajeran tsaki samha tayi tare da cewa kuna da matsala gaskiya,


Yusra tace gaki katotuwar mai matsala, ke samhar nan na lura dan kinga ana wani lallabaki sai kiyi ta rainawa mutane hankali an fada miki tsoronki mukeyi ne? Baki samha ta tabe tare da ware idanuwanta dukan su tana kallon yusra,


Yusra tace kallarni da kyau, na lura tunda kikaga akwatin nan keke mana bakin ciki saboda ba kece kika sane shi ba { sata } ,


Murmushi samha tayi daga shi bata sake cewa komai ba, har suka isa gida yusra sai masifa takeyi, dan haka suna tsayawa a kofar gida suka sallami mai napep suka shige ba tare da sunce samha ta taho ba,


Suna shiga gida suka ajiye akwatin a kofar daki , ita kuma samha tana shigowa ba tare data kalli inda suke ba ta wuce ciki, anan ta barsu suna shawarar yanda zasu yi su bude akwatin,


Samha tana shiga daki, ledar da hydar ya bata ta zazzage, abinda yake ciki daga waya sai manyan hijabai gudu biyar sai nikaf sabbi suma biyar sai kuma zunzurutun kudi wanda samha ta kasa irgawa, tattara kudin tayi ta kwashesu ta mayar a cikin ledar,


Murmushi samha tayi sannan ta dauki wayar tana kallo, irin wayarshi ce data sane mishi kwanakin baya, murmushi samha ta sakeyi sannan tace a bayyane wannan waya tana kyau,


Bayan ta gama jujjuya wayan ne, ta latsa ta hoton hydar ne ya bayyana a gaban wayar, hoton yayi kyau sosai, kuma daga gani ya dauki hoton ne yana cikin farin ciki, kurawa hoton ido tayi tana kallon hoton ajiyar zuciya tayi tare da cewa mai kyau da kyau yake inji bakin jaki daya ga magon doki,


Lallai kayi kyau sosai, amma abinda na lura dakai gaskiya kai mugu ne, kuma ba'a banza kazo kana so na ba, ajiyar zuciya sannan ta ajiye wayan,


Matsawa tayi ta jingina bayanta da bango, tayi tagumi, ko nazarinmi takeyi Oho mata,


Gaskiya yusra bai kamata kiyi wa samha haka ba, kausar ce takewa yusra magana, tsaki yusra tayi tare da cewa Allah haushi ta bani ne, kausar tace kiyi hakuri muje mu bata hakuri itace kadai zata iya bude akwatin nan,


Gaba dayansu suka shiga dakin, samha tana zaune tayi tagumi ta kurawa wuri daya ido tana kallonshi kamar mai kararren kwana, da sauri yusra ta isa wurinta tare da cewa samha miye? Murmushi dauke da fuskarta ta kalli yusra tare da cewa miye kika gani ne? Tayi maganar ne tana kankance idanuwanta,


Yusra tace kiyi hakuri don Allah abinda nayi miki dazu ya wuce kiyi hakuri ki taso muje a bude akwatin nan kudadene masu yawan gaske a ciki,, samha tace ba kudi bane a ciki, yusra tace kudi ne mana, ya zaki ce ba kudi bane,


Samha tace ke waye yace miki kudi ne? Yusra tace a wurin training da mukaje ne naji masu akwatin suna cewa kudine a ciki na america, dan gajeran murmushi samha tayi tare da dauke kanta daga duban yusra,


Ganin samha batayi magana yasa yusra cewa kice wani abu mana? Dan gajeran tsaki samha tayi tare da cewa ai bazaki gane ba, ke aikinki sane, { sata }  saboda haka ba komai zaki rika gani kina dauka ba idan ba haka ba wata rana sai kin dauko ajalinki,


Gaban yusra ya fadi da jin maganar samha , samha taci gaba da cewa muje mu gani, tashi sukayi gaba dayansu suka fita, suna fitowa a gaban akwatin samha ta tsaya ta karewa akwatin kallo sosai, murmushi tayi da gefen bakinta sannan tace nidai shawara daya zan baku idan kun yadda akwatin nan kuyi hanzarin rabashi da gidan nan, idan kuma kunki ji to nidai babu ruwana, kausar tace miyasa kika ce haka ne? Samha tace nayi imani idan har kudinne gaskiya ne a ciki kuma kunce kudi ma na america babu wanda zaiyi sakaci dashi harya rasa shi,


Kila mutane sun gaji da muna musu sata ne zasu kashemu, dan haka ina shawartarku da ku hanzarta daukar akwatin nan ku mayar dashi a inda kuka dauko shi, tana fadin haka ta juya ta koma daki,


Tsaki yusra tayi tare da cewa kada mu mayar so take idan muka mayar ita taje ta dauke ta kawo ma kawu bakiga dama shi yasa kawu yafi santa ba saboda tana kawo mishi kudi, ki lura mu har dukanmu yakeyi amma ita baya dukanta kullum magana mai dadi yake fada mata,


Haka suka fara kokarin bude akwatin, ita kuma samha tana komawa daki wayarta dake ringing tayi saurin isa wurin wayar ta dauka,


Hydar? Haka ta fada domin hakan ta gani a rubuta, dan gajeran tsaki tayi sannan ta dauki wayar tare da cewa Assalamu alaikum, ansa sallamar yayi ita kuma a daidai lokacin data zauna a gefen katifa,


Samha tace hydar kake kenan ko? A gadarance yace umm , umm din wanda bai kawo a bakinshi ba, samha tace to da kyau, am malam hydar kasan abinda nake so dakai? Yace saikin fada, samha tace yawwa kanaji na ? Abinda nake so dakai shine ka fita daga harkata idan ba haka saina wulakanta maka rayuwa,  samha taci gaba da cewa shin wai jira ma anya idonka ya taba ganin *SAMHA*?  Lallai banma san rainin naka har yakai haka ba da har kamarni wai zaka tun kareni kace kana so na,


Kai yaro ka kiyayi samha dan wallahi samha ba wasan yara bace ba, nafi karfinka, wato kana da wata manufa akaina ko? Shi yasa zaka shigo min rayuwata ba? Murmushi samha tayi sannan tace tunda nake a duniya ban taba samun mutumin da banso irinka ba, baka taba birgeni ba, haushi ma kake bani da wasu munafikan idonka kamar na mujiya, kai bari kaji in fada maka idan aka taka min muyanka saina yanka ka da wuka, idiot


Hydar yace nine nake da idon mujiya? Nine idiot? Samha tace kaji ma ashe kake sake tambayata? Banza shashasha sakarai ma irinka, mtswww , hydar yace ke "yar iska ce? Nine  kike min tsaki? Idan na kama sai naci ubanki munafika, dariya samha tayi tare da cewa dan iska ashe dama soyayyar baika zuciyarka ba a haka zanso ka?, Munafi mai sigar "yan dambe, nima idan na kamaka sai naci kutumar duma du, hydar yace zan kamaki zaki fada min wanda kike cewa zaici kutumar duma du, kuma idan na sake ganinki wurin training dinmu wallahi saina zaneki, samha tace ai ba wurin babanku bane ko babanka ya ginashi ne? Kai dan karamin kwaro baka isa ka hanani inje inda raina yake so ba, sai nazo idan kai kaci dan rashin kunya ka tabani kaga yanda zan farke maka ciki da wuka,  tana fadin haka ta kashe wayarta tana kara dirkakawa uwar hydar zagi,


Ajiyar zuciya hydar yayi tare da yin dan gajeran murmushi, a bayyane yace lallai yarinya kinci abinci, amma saina koya miki hankali dan tunda nake a duniya ban taba samun tantiriyar "yar iska number daya irinki ba, amma nine maganinki saina mayar dake abin tausayi da kwatanci a rayuwarki, dan gajeran tsaki yayi sannan ya mike ya fita daga dakin, dan dama fita zaiyi,


Samha jin ihunsu yusra yasa ta fito da gudu tana tambayar lafiya? Jaririya ta gani a akwatin dasu kausar suka bude sai kuka takeyi inya inya inya inya kamar zata sike diyar, salati samha tayi tare da mafidin munshiga ukkunmu, subahanallah wannan masifa da mi yayi kama? 


Yusra da kausar kuwa sai kuka sukeyi, samha tace kunga abinda nake gudu ko? Da yake ku daƙiminalniƙi ne allazi ɗifɗif saida nace kada ku bude ku mayar a inda kuka dauka amma kunkiji,


Cikin kuka yusra tace samha daukarta mana, zaro idanuwa samha tayi tare da cewa indauki uwar me? Wallahi hijabina kawai zan dauka in karawa bujena iska dan bazan zauna cikin masifa ba, tana fadin haka ta shiga daki ta dauko hijabi tana fitowa tsakar gida taga "yan sanda, innalillahi wa'inna ilaihir raji'un samha ta fada, tare da cewa malamai yane? Kun fado mana gida haka sai kace kunxo gidan giya,? Dan sanda yayo kan samha tare da kwarara mata mari a gigice samha ta daga hannunta itama ta sharara mashi mari,


Haka sukayi ta mare mare, saida sukayi biyar sannan dan sanda ya sauke ajiyar zuciya, kallon samha yayi sosai sannan yace samha! Dan gajeran tsaki samha tayi tare da cewa dan sanda abokin kowa, kallon samha ya sakeyi sosai sannan yace ya akayi wannan akwatin yazo wurinku? Saida samha ta sake dan gajeran tsaki sannan tayi magana cikin rashin jin tsoro cewa,


Kasan gaskiya mu bamu da aike sai sace sace, ko kai yanxun idan naga dama ina iya sace komai na jikinka ba tare daka sani ba, amma maganar gaskiya wannan jaririyar shine bamu da masaniya akanta,


Kai ku kamasu dan naga zasu raina mana hankali idan munje office sunyi bayani, dan sandan ne yayi magana, gaba daya sauran yan sanda sukayi kansu samha, aka kama yusra da kausar amma kirikiri samha ta kasa kamuwa, haka tayi ta zugewa kuma sunyi barazanar harbi amma samha ta fece daga gidan da gudu,


Haka aka tattara yusra da kausar da akwatin jaririya aka tafi dasu police station dan gabatar da bincike,


Ita kuwa samha tana fita abin hawa ta samu ba tare data san inda zataje ba, a napep sai mita takeyi wai bataci nanin ba babu wanda zaisa taje zaman wakafi, saida ta basu shawara amma da yake su wawaye ne sunke su gane karatun, dan gajeran tsaki tayi tare da fara sunno kanta waje, ta sunno kanta sai  leke leke takeyi, tana cikin leke leken ne ta hango motocin hydar tayi anyi parking dinsu a wani  wurin cin abinci shima dai wurin na "yan gayu ne, ga kuma bodyguards nashi sai shawagi sukeyi a wurin, hydar ta gango tsaye da wani yaro a gabanshi,


Da sauri tace ma mai napep, malam dakata nan yayi tsaya, tsayawa mai napep yayi bayan samha ta sallameshi ne, ta sauka a hankali ta fara bin bayan motacin cikin sando harta shige ciki,


Tana shiga yaron data gani tsaye da hydar a waje , ta gani ya kame bisa tebirin cin abinci, cikin sauri sahma ta isa wurin yaron ta zauna, murmushi tayi ma yaron tare da daga mishi hannu cewa sannu ko? 


Yaron yace yawwa, samha tace da Allah wanda na ganka dashi a waje waye dinka? Yaron yace ba kowa na bane kawai dai nace ya taimaka ya siya min abinci, samha tace to dami dami za'a baka ne?


Yaron yace kawai tuwo nake so, murmushi samha tayi sannna tace kam lallai kawai sai ka zauna kaci tuwo? Ga shikafa ga naman kaji ga farfesun yan ciki ga komai mai dadi sai kawai ka wani zauna a baka tuwo sai kace mara gata? Yaron yace ai ba kudi na bane, taimakamin a kayi , dan gakeran tsaki samha tayi sannan tace ina wanda yace a baka abincin ne? 


Yaron yace yana ta bayan can yana waya, yana nunawa da hannunshi, a daidai lokacin da ma'aikacin wurin yazo yana tambayar mi za'a kawo mashi? Yaron yace tuwo, samha tace kai ba tuwo zaka kawo mishi ba, shinkafa da rabin kaza lemun gwangwani guda daya ruwan roba daya sai sai a bashi sai farfesun "yan ciki a hado mishi da wainar kwai sai a kawo shayi kofi biyu,


Kallonta mutumin yayi tare da cewa hajiya a ina zaikai abincin nan ne? Ni cewa akayi tuwo zan bashi inji "yar labai, Cike da masifa samha tace ina ruwanka? Ba biyanka kudin ka za'ayi ba?  Ai yanxun ya canja shawara bazaici tuwon ba, shin wai kake ta magana haka ba kudinka za'a biyaka ba? Yace Eh tace yi sauri ka kawo kana bata mana lokaci, juyawa yayi dan kawo abincin,


Yana tafiya samha ta kara matsawa kusa da yaron tace kai almajiri ne? Yaron yace Eh, samha tace ya akayi ne yace a baka tuwo? Yaron yace nine nace ya taimakamin na yini banci komai ba gashi har dare ya fara, samha tace Allah sarki baka da abokai ne? Yaron yace ina dasu mana, samha tace maza kaje ka tattarosu kuci abinci,,,


Da gudu yaron ya fita babu dadewa kuwa yaro ya dawo da abokansa almajirai sunfi su talatin kowa ya kama kujera ya zauna, haka samha tasa duk aka basu abinci kamar yanda akayi ma yaron, almajirai kuwa sukaci gaba da shagalinsu,


Lokacin da hydar ya dawo dan biyan kudi, bill na kudi ya gani masu yawan gaske da mamaki ya tambayi yanda akayi, nuna mishi samha akayi ita kuma ta wani hade kafa daya saman daya tana shan lemu, mutumin yace itace tace a bawa kowa yaci kuma itace ta fadi abinda za'a bawa kowa, jinjina kai hydar yayi sannan ya cire kudin ya bada yayi tafiyarsa,


Lokacin da yaxo zai wuce ta kusa da samha tasa kafarta dan ta kadashi amma saiya matsa daga gefe ya wuce abinsa, ganin baiyi magana ba kuma ita tayi hakan danta bata mishi rai taga kuma baiji haushi ba dan haka ta tashi ta wuce shi da gudu har tana tuntube,


Tana fita wurin motar sa ta nufa, taje ta duka kusa da tayar motar ta sacemata iska fiiiyyyy iskan ta fita gaba daya, a daidai lokacin da hydar ya iso wurin ana kokarin budewa hydar ya shiga, 


Samha ta tashi daga inda take tsugunne data sace tayar motar ta tashi tana dariya kusa da hydar ta matso sannan tace wani yaro yau zaici gidansu, tana fadin haka ta kwalkwala da gudu tana mishi gwalo,


Murmushi hydar yayi tare da cewa zaki gani kurenki, wata mota aka canjawa hydar aka tafi dashi gida, zuciyarshi cike da kudirin ciwa samha uwa,


Saida dare yayi sosai sannan samha ta sidada ta koma gida, tana shiga ta rufe kofa, da gudu ta shige daki saboda tsoro tana shiga ta kulle kofa, saida ta kwanta saman katifarta sannan ta dauki wayarta ta fara kiran number hydar,


Haka wayar ta gaji da ringing bai dauka ba, dariya samha tayi sosai sannan tace yechh tare da yarfa hannunsa tace yawwa ya fara shaka, yaji haushi sosai,


Lokacin da hydar yaga wayar samha ji yayi kamar ya mika hannunshi ya kamo samha ya shaketa sai yaji tayi amai ya saketa, ita kuwa samha da taga bai dauka ba hakuri tayi, tayi kwanciyarta bacci mai dadi ya dauketa zuciyarta cike da farin ciki hydar yayi fushi,


Su yusra kuwa sunci ubansu sosai anyi musu lullusar fitar hayyaci sunsha kuka tare da kiran samha ta kawo musu dauki amma a banza, dan samha batajin su,


Bayan wasu "yan kwanaki samha idan ta kira hydar ya daina dauka kuma kullum sai taje ta sace mishi tayar mota, amma yanxun kwana biyu bata ga hydar ba, ita kuma a tunaninta saboda fitinar ta hydar ya daina zuwa training,


Shi kuwa hydar yayi alkawarin sai yasa samha tayi aman zuciyarta ba ciwo yake so zuciyar tayi ba A, a, so yake zuciyar gaba daya samha ta amayo ta, dan haka yaje kasar waje yasa akayi mashi fuska ta daban wanda zai rika sakawa a saman fuskarshi dan kawai yasa samha shiga mummunan yanayi wannan dalilin ne yasa ta daina ganinsa kwana ki da dama,


Watansu yusra biyu ana cin bara'ubasu police station sudai maganarsu daya wannan jariri basu sanshi ba, kuma sunfada cewa samha banda ita aka dauko shi kuma tace su mayar dashi amma sunki, sunci uwarsu sosai fa, sannan aka sanya bilen su da kudi masu yawa, 


Haka suka bada number kawu aka kirashi a waya, aka fada mishi kudin don haka dolen kawu ya dawo dan ansarsu yusra,


Uhum su yusra fa an canja kamanni dan idan ka gansu sai sun baka tausayi, gaba daya sun fita a hayyacinsu, lokacin da suka dawo gida sunyi kuka sosai, tare da alkwarin basu kara sane,

dan haka aiki ya koma na samha ita daya,


Hydar tsaye a gaban mirrow yana murmushi, saida ya gama shirin sa tsaf sannan ya dauki fuskar da akayo mishi a india ya dora, kallon kanshi yayi sosai a madubi sannan yayi dariya tare da cewa Allah ya jikanki samha,


Ita kuwa banda dube dube babu abinda samha takeyi a wurin training ganin babu hydar yasa ta hakura ta juyo dan tafiya gida, shi kuma lokacin daya iso yaga samha tana kokarin fitowa da sauri yayi parking ko rufe motar baiyi ba ya taho da dan gudunsa dan ya bige samha yana san yayi magana da ita, 


Itama samha da sauri ta taho, shima ya tafi gaba dayanshi, samha ta bigeshi wayarshi ta fadi kasa, da sauri samha ta duka ta dauki wayar tare da cewa don Allah kayi hakuri wallahi ban gani ba, wani irin kallo hydar yayi mata tare da cewa miye sunan ki? Samha tace suna Hafsat amma samha ake cemin,


Tabe baki hydar yayi tare da daga giraranshi yace ni kuma suna na,




Meelat Musa ce,

[05/04 4:44 pm] Washa: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊



                 *SO*

     *MUGUN WASA*



       *{ Love is a bad game }*




*JAMEELA MUSA* { meelat musa }




*Story, Writing & Editing*

                   *by*

         *Meelat Musa*


*REAL MAI DAMBU ina sanki! Ina sanki!! Ina sanki!!! Gaskiya ina kaunarki kuma ina tare da dumbin masoyanki a duk inda suke a fadin duniyar nan, abinda nake so dake shine don Allah ki daina biyewa wasu jakuna suna bata miki rai, kada ki kuskura ki bari a koya miki halin da ba naki ba don Allah tawa, dan wallahi mutane da dama basa gane meelat musa basa gane real mai dambu, lokacin da abin nan ya faru wallahi mutane da dama sun samu number na sunyi min magana cewa don Allah in daina biyewa wawayen mutane suna batamin rai in daina fada da kowa, nace ni bana fada da kowa sai aka rika turomin novel naki na gani,  a lokacin na fahimta dan haka sai saida na rika ce musu to na gode sosai da shawara kuma zan gyara, to tawa gaskiya abinda nake so dake shine nidai na haneki don Allah ki daina, dan duk wanda ya tabominke nine ya taba ba dake yake ba da ni yake, kiyi hakuri kiyi hakuri kiyi hakuri kinji zuciyar meelat musa? Kuma masoyanmu muna baku hakuri don Allah akan abinda ya faru kunsan ita zuciya tsokace yayin da mutum yake cikin fushi baya iya control nata amma duka hakuri shine yafi cancanta to kowa da kowa yayi hakuri ina bawa masoyan mai dambu tawa hakuri kuma nima ina cewa kuyi hakuri don girman Allah dan duk mu "yan adam ajizainai, Allah ya kara mana hakuri baki dayanmu ubangiji ya yafe mana zunubanmu baki dayanmu*


Masoyan brilliant writer's association kudai kara kasancewa da Asmeenat Xeeyan domin ta sake zo muku da sabon labarinta mai cike da abun mamakiyos kada ku bari a barku a baya kuma bana so a baku labari shi yasa na sanar daku tun yanxun ku dai ku nemi labarin ta mai suna *NAMIJI* idan har kika bari aka baki labarin namiji gaskiya anyi miki wayau karanta da kanki dan kema kiji abinda kowa yakeji,,


*Surayya ina tayaki murnar kammala littafinki mai suna MAKAUNIYAR HANYA masoya har yanxun littafin baiyi muku nisa ba kuyi kokarin neman sa gaskiya domin marubuciyar ARNE itace ta dawo muku da wannan sabon salo , ku nemi makauniyar hanya kafin mu tsunduma cikin sabon novel nata, surayya ce kada ku bari a baroku a baya*


Hhhhhh baiwar Allah kenan, nikinma bani dariya 😂 ni bana fada bana habaici bana zagin kowa dan wallahi babu ruwana da rayuwar kowa abunda yake gabana shi nakeyi ni baki isa ki koyamin abinda ban iya ba, kiyi tayi duk zagin da kikemin babu inda ya fito min ajikina, meelat musa dai tai miki yawa saida a nemi wata 😜



                  *SO*

      *MUGUN WASA*


*Dedicated to* zuciyar meelat musa, mai dambu tawa ceeeeeeeeeeee,



*17-19*


Kama hannun samha yayi yajata suka shige ciki, wuri ya samar mata ya zaunar da ita sannan shi kuma ya haye saman mashing din excercise,


Tana zaune ita kuma tana kallonshi, agogon wayarta ta duba taga 8:30am dan haka ta mike ta matsa kusa dashi cikin natsuwa tace don Allah kayi hakuri wallahi ba'a san raina hakan ya faru ba, amma idan baza ka damu zaka iya bani wayar idan na gyara maka zan dawo maka dashi,


Saukowa yayi daga inda yake yake motsa jikinsa  inda ya ajiye wayar ya dauka yaxo ya bata, tare da cewa kuma idan bata gyaru ba sai kin biya mai wayan na fada miki, cikin damuwa samha tace kada ka wani damu zata gyaru ma insha Allah,


Harta juya ta fara tafiya ta juyo tare da cewa idan na dawo ban ganka ba sunan wa zan tambaya? Ba tare daya kalleta ba yace ki kaima hydar wayarshi ce dama, murmushi samha tayi sannan tace kai kuma ya sunan ka? Yace sunana sahib, Samha tace to zan bawa hydar din amma ka bashi hakuri kafin inje,


Yace kema idan kinje zaki bashi hakurin da kanki, ajiyar zuciya samha tayi sannan ta fita daga cikin katon holl din tana tunanin kudin da zata biya a gyara wayarnan, tashin hankalinta na gaba shine yama zatayi ta tinkari hydar da wayarshi bayan abinda tayi mishi? Wata zuciyar tace kedai gyara wayar sannan ki samu mafita,


jiki a sanyaye samha ta tsaida mai napep dan tafiya gida, shi kuwa fitar ta dariya yayi tare da kwaykwayon maganar samha, yana maganar yana wani tabe baki, idan nazo waye zance sunanka? Jinjina kansa yayi sannan yace zaki xo ki sameni, yana fadin haka yaci gaba da abinda ya kawoshi,


Napep nayin parking samha taga "yan sanda a kofar gidansu sun wani yi ciccirokai ciccirokai, a hankali ta zura kafarta ta fita, tana kokarin shiga gida taga an fito da kawu rirrike dashi,


Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un samha ta fada sannan ta matsa wurin inda ake kokarin saka kawu a mota, samha tace kawu mi ya faru ne? Murmushi kawai yayi ma samha amma baiyi magana ba, samha na kokarin matsawa wurin kawu har anshigar dashi mota sunja sun tafi,


Jiki a sanyaye ta nufi cikin gida, tana shiga ta samu su yusra sun hada kayansu wuri daya, samha tace kausar ina zakuje ne? Yusra tace zamu tafi gida dangin mamana sunzo tafiya damu tunda dangin uba sun kasa, murmushin karfin hali samha tayi sannan ta matsa kusa da yusra ta riketa sosai sannan tace,


Haba yusra, haba kausar ya kuma zakuyi min haka don Allah? Plz kada ku tafi kuyi hakuri muyi zamanmu tare, idan nayi maku wani abu wanda bai muku dadi ba insha Allah bazan sake ba, kuyi hakuri mu zauna tare,


Yusra tace tafiya kam ta zama dole samha saidai kiyi hakuri, kema Allah ya bayyana ma iyayenki gaskiya suxo su tafi dake ga kawu kuma an kama, samha tace shi kuma mi yayi? Yusra tace can shida abokan caca ne, a daidai lokacin da wani mutum ya shigo gidan yana cewa kausar ku taho ku kadai muke jira,


Samha tanaji tana gani kausar da yusra suka dauki kayansu, suka fita daga cikin gidan, ganin sun fita da gaske yasa samha ta bisu da sauri tana kallo haka aka dauki kayansu aka jibgasu a motar cikin farin ciki suka shige mota akaja suka tafi suna dagawa samha hannu,


Ajiyar zuciya samha tayi sannan ta kulle kofar gidan ta nufi cikin gida, tana shiga daki ta wuce shima ta rufe kofar, 


Samha bata sake fitowa ba saida safe, dan haka da shirinta ta fito gaba daya, tana fitowa ta rufe dakinsu sannan ta fice daga gidan, shima gidan rufewa tayi sannan ta nufi wurin mai gyaran waya, 


Mai gyaran waya haka ya cakallali waya yayi mata daidai shida kawai akace glass din waya zai canja amma ya kama waya ya kwance ta kuma yayi, yayi ya hada waya ya kasa, haka dai ya hakura ya tattarawa samha wayar ya bata tare da cewa ta gama aiki,


Cike da tsiwa samha tace to idan ta gama aiki sai ka mayar yanda na baka mana, mai gyaran waya yace gaskiya hajiya kiyi hakuri amma bari in baki kudi ki matsa can gaba akwai ogana kila zai iya, haka yayi ma samha magana mai dadi ta hakura ta anshi waya da kudin ta tafi,


Haka taje ta kai inda ya nuna mata shima dai a banza amma ya hada wayar saida bata kawo haske, haka samha ta hakura ta koma gida, 


Washe gari ma bataje ba, kuma bata sake fita gyaran waya ba, hydar kuwa ya zuba ido yaga samha amma shiru bai ganta ba kuma baiji ta ba, saida samha tayi kwana ukku sannan ta hakura ta dauki waya dan kaiwa hydar,


Da marece taje wurin da mayar da waya ta bada hakuri, lokacin da samha taje wurin gaba daya wurin cike yake da mutane maza da mata "yan gayu masu kudi masu aji wanda suka san abinda sukeyi,


Banda faduwa babu abinda gaban samha yakeyi, mutane ta gani zageye da hydar kuma yau ba kayan training bane jikinsa, kananan kaya ne ya saka kuma hakika kayan sunyi matukar bartaba jikinsa, yayi kyau sosai,


Cikin dakiya samha tayi wurin, amma kana ganinta kasan bata da gaskiya, ita matsalarta kawai kada ya dizgata cikin mutane dan abinda ta lura hydar tantirin dan iska ne saboda kwata kwata baisan darajar mutane ba, kuma ta lura yana da wulakanci sosai,


Dan haka ta daura damarar idan har yayi mata iskanci sai ta rama wallahi saida a tsireta, tana isa wurin a daidai lokacin da hydar ya ba wani abokinshi hannu suka kashe, cikin dariyar rainin hankali suke fira,


Sallama samha tayi a daidai lokacin data iso wurinsu, babu wanda ya ansa sallamar daga cikinsu, itama bata damu ba dan haka kusa da hydar ta matsa sosai sannan tace ga wayarka kayi hakuri, sahib ne yace in baka, ba tare daya kalli samha ba ya anshi wayar,


Ganin wayar yayi duk an birkita mata tsari dan haka cikin zafin rai ya juyo tare da dauke samha da wani irin gigitaccen mari wanda yasa ta yin dimuwa, duk mutumin dake wurin jin karar marin yasa shi juyowa dan ganin wanda ake duka, hydar kuwa cewa yake lallai dan babanki wayana zaki ma rashin kunya?


Ita kuma samha tana can tana lalabu hankalinta ya dawo jikinta, hydar yaci gaba da cewa bakyaji ina magana ne? Yana kokarin kara kai mata dukan wani abokinshi ya rikeshi tare da cewa haba hydar yi hakuri mana, a daidai lokacin da samha ta dauko wani katon dutse zata rosa mishi kai,


Wata budurwace ta fito daga mota da gudu tayo kan samha tana zuwa takai wa samha mari tare da cewa dan ubanki hydar zaki jefa? Ai bata gama rufe bakinta ba samha tayi sama da ita ta darkakata da kasa, sannan tayi kan hydar da sauri aka rike samha amma sai ihu takeyi tare da cewa saita rama marinta idan kuwa ba haka ba wallahi yasan sauran,


Hydar yace su barta su bari tazo, sakin samha akayi kafin ta isa kusa da hydar ya fiddo wani abu daga aljihun wandonshi ya fesawa samha a ido, wani irin ihu samha tayi dan abun bata san da wane irin suna zata kirashi ba, shidai ba jayi ba kuma ba attaruhu ba, gaba daya ji tayi kamar idanuwanta basa cikin gurbin idonta,


Dukewa tayi tana kuka, kusa da ita hydar ya matsa ya ajiye wayar tare da cewa jaka sai kin biyata idan ba haka ba anan wurin zansa bodyguards dina su kacallala miki rayuwa, idan ma baki zo ba, zansa a dauko minke anan filin zansa su daya bayan daya kowa sai yayi miki abinda bakya tunani,


Hawaye kadai yake diga daga cikin idon samha, hydar da kanshi yaje ya daga wanda samha ta fadar da ita kasa, har suka tafi samha tana duke wurin tana kuka cikin tsananin kunar rai,


Saida abin ya saketa sannan ta tashi ta dauki wayar da hydar ya ajiye ta nufi gida, tare da gudirin zata biya waya sabuwa sannan kuma itama tayi alkawarin saita rama abinda hydar yayi mata,


Kalma daya ta tsayawa samha a rai, anan filin zansa bodyguards dina daya bayan daya suyi miki abinda bakya tunani, ajiyar zuciyar samha tayi sannan tace a bayyane wai nice jaka? Sannan kuma nine za'ayi ma abinda bana tunani, waini za'a kacaccalawa rayuwa,


Ajiyar zuciya samha tayi ta saukewa babu kakkyautawa, gaba daya tsoro ya kamata, cikin rawar baki samha tace toni inama zan samu wasu kudin siyen waya, kuma idan nace inyi sata yanxun kowa yasa min ido saboda sace sace na gara akwai in rufawa kaina asiri in gudu in bar garin nan,


Wata zuciya tacewa samha ki gudu kije ina? Ga kawu nan kuma bai fadaki da iyayenki ba, kedai kawai ki bawa hydar hakuri tunda kece kikayi mishi laifi ko kuma ki nemi sahib din, lallai sahib zan nema dan na lura kamar yafi hydar mutunci, haka ta hakura ta ajiye waya ta kwanta bacci,


Tunda asuba police station ta nufa, tana so a hadata da kawu tayi magana dashi, saida akayi mata tambayoyi kamar tazo kabari sannan aka fito da kawu, bayan sun gaisa ne samha tace kawu wai ya kayai ne haka ta faru?


Kawu yayi murmushi amma baiyi magana ba, samha tace bazaka fadamin ba? Kuma gida babu kowa su kausar an tafi dasu basu saini daya gashi banda kudi ga yunwa inaji ga ido ansa min gari kowa so yake ya kamani da wani laifi yayi man hukunci mai tsanani, ka rufamin asiri kawu don Allah ka hadani da iyayena,


Kallonta kawai kawu yakeyi, haka samha taci gaba da magiya amma saboda kawu digirarran dan iska ne yayi mata shiru har akazo akace lokaci yayi ya koma, saida aka fara tafiya dashi dan mayar dashi ciki sannan ya juyo ya kalli samha yace wato bakiy maraicina ba da bana nan sai in hadaki da iyayenki ko? To ai sai kije ki ganosu, yana fadin haka aka shige dashi ciki,


Haka samha ta hakura ta tafi dan kawai sahib wayar hydar, tadan jima sannan sahib ya iso saman mashin rover rover, tun kafin ya tsaya samha ta mike ta nufi wurinshi tana mishi sannu da zuwa, tsayawa yayi amma bai sauko daga saman mashing din ba, gabanshi samha taje ta gaishe shi ya ansa,


Sannan ta ciro wayar daga cikin jakarta ta mikawa sahib, cikin sigar lallashi tace don Allah yaya sahib kayi hakuri ka taimakeni yanda Allah ya taimakeka ka bawa hydar hakuri ka bashi wayarshi wallahi banda kudin gyaran waya bansan ina zan samu ba, kaga tun jiya nake neman kudin nan amma ban samu ba kuma ga kawu na "yan sanda sun kamashi abokanan aikina suma iyayensu sun tafi dasu kayi hakuri ka bashi da kanka,


Murmushi hydar yayi amma yanda samha tayi maganar ne ta bashi tausayi, amma sai ya basar cewa to nidai samha kiyi hakuri gaskiya kije ki samu hydar kiyi magana dashi kinga nima a karkashin sa nake ko kina so ya koreni daga aiki ne? Ga mamana bata da lafiya kuma ance za'ayi mata aiki dubu dari ukku nake nema yanxun a ina zan samu? Cikin tausayawa samha tace wayyo Allah ya bata lafiya, sahib yace amin, amma kije ki bawa hydar din wayarshi, a daidai lokacin da yake kokarin saukowa daga saman mashin,


Samha tace sahib kana da mutunci kana da kirki sosai nikam a halin yanxun bazan iya tunkarar hydar ba, dan bakaji abinda yace min ba, kyakkyawan kallo hydar yayi ma samha, sannan yace miye hydar yace? Samha tace cewa yayi sai kuma tayi shiru, murmushi hydar yayi sannan yace to idan kin shirya maganar saiki fadamin yana fadin haka ya fara tafiya, da sauri samha tace don Allah ka tsaya, tsayawa yayi ba tare daya juyo ba, zatayi magana kuma saidai tace babu damuwa kawai zanga hydar din kamar yanda kace,


Juyawa tayi ta fara tafiya, hydar ya juyo yana kallon bayan samha har ta bace, dan gajeran tsaki yayi sannan ya cire fuskar daya dora saman fuskarshi yana sauke ajiyar zuciya, saman mashin dinsa ya koma ya zauna,


Samha da ta dawo gida ta duba kudin da hydar ya bata lokacin daya ce yana santa ta, amma fa babu kudin babu wayar babu hajiban kuma babu nikaf din komai an dauke,


Haka rayuwa taci gaba da tafiya tsakanin samha da sahib, abu kullum kara kullewa yake, samha dai tana jin sahib a ranta amma dan kadan, dan yanxun ta daina zuwa wani wurin tana gida kuma a gida yake zuwa ya sameta suyi fira sosai, idan tana aiki yana tayata, abinda ta kula shi sahib basu da wani hali dan haka tana tausaya mishi kuma tanajin haushin hydar daya kore sahib daga aiki dan shi sahib din cewa yyai ma samha wau hydar ya koreshi daga aiki saboda ita,


Ita kuwa samha haushin hydar takeji sosai, kullum sai ta zagi hydar a gaban sahib, yauma haka ta kasance sahib yazo ya samu samha ta tattaro kayanta tana wanki ya zauna yana tayata,


Duk ya jika jikinshi, sai zufa yakeyi saboda bai saba ba, hannunshi kuwa gashi yayi ja sosai sai zafi yake mishi, saboda dan gurza kayan da yakeyi, samha tayi juyin duniya ya ajiye amma yace zaiyi,


Bayan sun gama wankin ne, sahib ya samu wuri ya zauna yana sauke nunfashin wahala, samha taje kicin ta kawo mishi abinci kallo daya hydar yayi ma abinci yaji yana kokarin yin amai, kallon samha yayi yace nidai na koshi banajin yunwa, kije ki ajiye, samha tace to daukar abincin tayi ta tafi,


Dan gajeran tsaki hydar yayi sannan ya kalli jikinshi yace kai nafa sha wahala ai yanxun nasan yarinyar nan ta fara so na haka nan danni na fara gajiya wallahi, ganin samha ta taho yasa hydar mikewa tsaye yana cewa nifa tafiya zanyi,


Samha tace haba yaya sahib tun yanxun? Murmushin karfin hali yayi sannan yace kinsan jibi zan tafi kauye jikin mamana yayi tsanani sosai zanje in siyar da gonar gadonmu a nemar mata magani, ajiyar zuciya samha tayi sannan tace miya sa zaka siyar da gadonka? Hydar ya tabe baki tare da cewa samha ya zamar min dole sai nayi hakan idan har ina san ceto rayuwar mahaifiyata,


Samha tace to babu damuwa komi kenan zamuyi waya zuwa gobe insha Allah, hydar to sai najiki, samha tayi ma sahib rakiya har ya hau napep sannan ta dawo gida,


Dan gajeran tsaki hydar yayi sannan yace mai napep ajiye ni anan, ajiyeshi yayi ya sallameshi da kudi masu yawan gaske, bayan ya sauka yayi waya akazo ka daukeshi,


Hydar yana zuwa gida wanka yayi bayan ya gama wankan ne ya fito a gaban madubi ya tsaya yana kallon kanshi, daidai zuciyar ya taba sannan yace wallahi na horeki da kiyayyar samha, duk abinda nakeyi a wasa nakeyi kada ki kuskura ki zo min da tsarin da bashi na saka ki ba! 


Hydar yaci gaba da cewa bana san samha ko daya ban tabajin digon santa a cikin ki ba, dan haka idan kika kawo min sakarci saina cire ki na canja sabuwar zuciya, dan haka ki rufawa kanki asiri kada ki kuskura ki samha idan dai kina san kasancewa a cikin jikin hydar,


Ita kuwa samha tafiyar sahib gidan kawu da yake makotanta taje ta samu dillai akayi mishi kudi naira miliyan daya da dubu dari daya, dan haka ta sallama shi tare da cewa gobe take san kudin idan Allah ya kaimu, 


Washe garin safiyar sai misalin 11:03pm aka kawo ma samha kudin gidan, dan haka a daren tayiwa sahib waya, hydar dake kwance yana hutawa jin wayar daya ware dan samha tana ringing yasa shi juyawa a hankali ya dauki wayar, murmushi yayi sannan ya kara wayar a kunnenshi,


Sahib barka da dare, murmushi hydar yayi sannan yace ya kike? Lafiya qalau kayi hakuri na tasheka daga bacci nasan ka fara bacci yanxun, murmushi hydar ya sakeyi sannan yace banda abinki samha waye yace miki talaka yana bacci? Samha tace to don Allah kazo yanxun ina nemanka,


Da sauri hydar ya kalli agogo sannan yace yanxun a tsohon daren nan samha? Samha tace nidai kam yanxun nake san ganinka don Allah kazo sahib, ajiyar zuciya hydar yayi sannan yace to gani nan zuwa insha Allah, samha tace yawwa sai kazo, 


Hydar yana kashe wayar ya tashi inda yake ajiye fuskar da yake dorawa yaje ya dauka sanna ya saka, bayan ya saka fuskar ne ya canja kaya, waya yayi cewa a fiddo motoci zai fita,


Yana gamawa ya fice daga dakin, lokacin daya fita an hada motoci shi kawai ake jira, yana fita aka fude mishi mota ya shige babu wani bata lokaci suka bar gidan, bayan sunje a nesa da gidan su samha sosai hydar ya sauka, ya tafi da kafafuwanshi,


Saida yaje kofar gidan sannan yayi ma samha waya cewa yazo, tace to tana zuwa, kudin ta dauka dukansu sannan ta fita daga gidan, yana nan tsaye har samha ta fito, bayan ta fito ta gaishe shi, ta bashi hakuri akan ta tashe shi daga bacci, murmushi yayi sannan yace nifa banyi bacci ba kawai ina can ina neman hydar ya taimakamin ya maida ni aiki samha, 


Kinsan tunda kika lalata mishi waya ya koreni waisai kin biya shi wayarshi, murmushi samha tayi sannan tace kayi hakuri ya sahib nasan duk nine sila amma insha Allah gobe zan biya hydar wayarshi,


Bude jakar data zuba kudin tayi ta daukosu duka ta bawa sahib tace ka canjawa hydar wayarshi ka bashi, sannan kuma ka daukin kudin da zaka siyawa mamanka magani, sauran kudin kuma ka samu sana'a ka dagora da kanka bana san ka kara dogara da hydar dan na tsani hydar a rayuwata ban taba samun mutumin da bana kauna irin hydar ba, idan har aka ajiye min hydar aka taka min wuyanshi saina yanka banza da wuka ya mutu dan iska kowa ya huta,


Ajiyar zuciya hydar yayi sannan yace haba samha miyasa bakya san hydar? Cike da bacin rai samha tace wallahi tunda ya salwantar min da m card dina na tsani rayuwarshi bansan sa, cikin sanyi murya cike da salon yaudara hydar yace kiyi hakuri samha kada ki dauki hydar da zafi a ranki ki sassauta mishi, samha tace wallahi bazan sassauta ba ko zan mutu akan hydar saina dasawa hydar bakin cikin dasai yayi nadamar zuwansa duniya da har yasan samha,


Ya sahib kawai kaje ka siya mishi waya kace inji samha, murmushi yayi sannan ya ciro kudin yace to ke a ina kika samu kudin nan ne? Samha tace gidan kawu ne na siyar, hydar yace to miyasa kika siyar mishi? Samha tace da ban siyar ba, kaine zaka siyar da gonar gadon ka kuma bana so ka sake kasancewa a karkashin hydar jeka da sauri dare yanayi,


Ajiyar zuciya hydar yayi sannan yace to kinga yanxun ban tare da hydar amma ki cire kudin wayarshi sai ki siya mishi da kanki, ki kai mashi, samha tace to kudin ya bata tare da tsareta da ido yana kallonta a ranshi yace yanxun saboda ta tsaneni yasa ta siyar da gidan da ba nata ba dan kada sahib ya kasance a kasana, a daidai lokacin da samha ta dago kanta tace na dauka, murmushi karfin hali hydar yayi sannan ya anshi kudin jiki a sanyaye  ya fara tafiya,


Yana tafiya yana waiwayen samha ita kuma tana daga mishi hannu, har ta daina ganinshi sannan ta koma gida ta rufe,


Tun kafin hydar ya isa idan motocinsa suke ya cire fuskar, tare da tunanin maganar samha, kawai kaje ka siya mishi waya kace inji samha, kanshi ya juya, maganar samha ta sake dawo mishi, kuma bana so ka sake kasancewa a karkashin hydar, ajiyar zuciya hydar ya sauke sannan wannan kalmar tafi tsaya mishi a rai, na tsani hydar bana kaunarsa idan har aka taka min wuyan hydar saina yankashi da wuka, a daidai lokacin da hydar ya iso wurin daya bar motocinsa,


Bude mishi mota akayi ya shiga jiki a sabule, kalaman samha masu muni akanshi suna tayi mishi yawo a kwalwa, har suka isa gida hydar tunanin maganganun samha yakeyi,


Kudin data bashi ne ya ajiye a saman mirrow, ciro wayarshi dake ringing yayi daga aljihunsa sunan samha ya gani, dan haka ya dauka samha tace fatan kaje gida lafiya? Murmushi hydar yayi sannan yace lafiya qalau, samha tace to sai da safe hydar yace mu kwana lafiya, haka sukayi sallama,


Da safe samha bayan ta gama abinda takeyi ta shirya ta nufi kasuwa, haka taje ta siyo sabuwar wa dal dan yiwa hydar ramuwa,



 ⚜ *B. W. A* 🖊

[05/04 4:45 pm] Washa: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊



                 *SO*

     *MUGUN WASA*



       *{ Love is a bad game }*




*JAMEELA MUSA* { meelat musa }




*Story, Writing & Editing*

                   *by*

         *Meelat Musa*



                  *SO*

      *MUGUN WASA*



*Dedicated*

             Real mai dambu


*20-22*



Kai tsaye gida ta wuce da wayar, tana komawa wanka tayi bayan ta gama ta shirya ta fice daga gida,


Wurin wani dan daba taje kana ganin sa kaga tantirin dan iska, dan haka bayan taje suka gaisa tace don Allah illo maciji nake so,


Illo ya zaro idanuwa cikin maganar daba yace maciji kuma samha? Samha tace Eh, dariya illo yayi sosai sannan yace mi zakiyi da maciji ne? Samha tace wani dan iska nakeso ya sassare min,


Dariya illo ya sakeyi sosai sannan yace banda maciji amma zuwa yaushe kike san macijin ne? Samha tace daga nan zuwa marece, illo yace baki da damuwa zan samo miki insha Allah kije gida kawai ki jirani,


Samha tace tou amma idan ka samo min macijin ka cire mishi hakora da harshe kada ya cijeni, illo yace to kada ki damu insha Allah,


Cikin farin ciki samha ta nufi gida, tana zuwa gida ta dauki wayarta ta kira sahib, bayan ya dauka suka gaisa tace mishi albishirinka? Da sauri hydar ya tashi zaune daga kwanciyar da yayi sannan yace goro, cikin farin ciki samha tace ka kasance anjima wurin training zakayi kallon yanda zan wulakanta hydar,


Hydar yace wane irin wulakanci kuma samha? Dariya tayi sosai sannan tace kaidai kasance da samha kada ka bari hydar ya baka labari dan sai nashi gudu da gajeran wando cikin damuwa hydar ya sauka daga saman gado tare da cewa gani nan zuwa gidanku yanxun, samha tace sai kazo,


Hydar yana kashe wayar yace kaji shigeyar yarinya nine zata sa inyi gudu da gajeran wando? Kai amma lallai yarinyar nan, to ko ya zatayi da kayan jikina? Dan gajeran tsaki yayi sannan yace nafa jawo ma kaina bala'i, 


A gaggauce hydar yayi wanka zuciyarshi cike da damuwa, lallai fa idan baiyi da gaske ba samha tana iya kasheshi kamar yanda take fada, saida ya gama shirinsa tsaf sannan ya saka fuskar sahib, ya fita daga dakin,


Yana fitowa drivernsa Alale ya taso hydar yace ya barshi ba tare zasu fita ba, da sauri hydar yabar gidan, yana fita napep ya hau sai gidansu samha,


Bayan yaje yayi mata waya cewa ya iso, tace ya shigo, yana kokarin shiga yaga illo ya fito daga gidan, tsayawa hydar yayi yabi illo da kallo harya bace sannan ya juya ya shiga cikin gidan, 


Da sallama ya shiga gidan, samha najin sallama hydar ta fito da gudu daga daki tana dariya, hannuwanta boye a bayanta, murmushi mai kashe jiki hydar yayi ma samha sannan yace miye kike dariya?


Fiddo hannuwanta tayi ta nunawa hydar idanuwa ya zaro sosai tare da ja baya, yace miya hadaki da maciji? Dan bata rai samha tayi sannan ta juya ta nufi daki,


Da sauri hydar yabi bayanta yana cewa bakiji ina miki magana ne? Samha tayi mishi shiru, hydar yace amma macijin baya da rai ko samha? Yaci gaba da cewa lallai yau zamuci uban hydar a garin nan,


Dariya samha tayi sannan tace yana da rai cewa nayi a cire hakoranshi da harshenshi yana jin wahala ne shi yasa kaga baya cizo jira ka gani kaima bazai cijeka ba, dago macijin tayi tana nuna wai ga sahib yazo ya gashe shi,


Dora macijin tayi saman jikin hydar wani irin kallo hydar yayiwa samha a ranshi yace zakici ubanki Allah ya kaimu anjima, ashe ma macijin naki na karya babu hakori babu harshe ni idan ni banyi gudu da gajeran wando ba ke zakiyi mai dalili,


Ajiyar zuciya samha tayi sannan tace kaji baya cizo ko? Kai kawai hydar ya jinjina mata, alamar Eh, samha tace to wannan macijin zanje in sakawa hydar a jiki, zaiyi tunanin macijin gaskene sai ya gudu kaga yaji kunya, hydar ya kakalo murmushin karfin hali sannan yace gaskiya yau wani yaro zaici gidansu, 


Samha tace zaisha gudu dai tunda maciji babu harshe babu hakori, hydar yace to miyasa baki samo mai cizo ba? Zaro idanuwa samha tayi sosai sannan tace idan mai cijo ne kafin ya kashe hydar ai nine zai kashe, haka dai samha tayi tama hydar shirme tare da kara jaddawa sahib itafa bata san hydar,


Sahib yace nima bana sanshi tunda bakya sansa, haka dai sukaci gaba da fira hydar ya dade sosai suna fira da samha, daga baya yace mata zai tafi dan yaga lokacin tafiya training din hydar yayi taje ta shirya takai mishi wayarshi, saida ta raka hydar ya hau napep sannan ta dawo ta fara shiri,


Tun a napep hydar yake kullawa yana kwancewa yau yayi kudirin cima samha uwa, Allah ya hadasu a filin training lafiya, bayan yaje gida yasa aka samo mishi macijin roba mai maganadiso, saida aka kawo mishi macijin sannan yasa kayan training suka nufi wurin,


Lokacin daya isa wurin tuni samha ta dade da zuwa, tana ganin motocin hydar ta mike da sauri ta nufi wurin, shi kuma hydar a daidai lokacin yake kokarin fitowa daga mota, kallo daya yayi samha ya dauke kanshi, samha tace malam wayarka na kawo maka, dan tabe baki hydar yayi sannan yace sai yau kika ga dama? Samha tace Eh yanxun na samu hali,


Ci gaba da tafiya hydar yayi samha tana bin bayanshi, hydar yace amma mina gaya miki game da wayana? Samha tace kace kwana daya ka bani in kawo maka? Hydar tace to yau kwana nawa kenan? A daidai lokacin da yake duba agogon hannushi, samha tace ban sani ba?


Ka tsaya ka anshi wayarka dan ina da abunyi idan har ka bari na sake tafiya bazan sake dawowa ba, juyo hydar yayi yana kallonta a hankali ta sauke kanta kansa, shi kuma a daidai lokacin daya jingina da wata mota, hannunshi ya mika cewa bani, wayar ta mika mishi da wayar da hannunta ya hada ya rike, sannan yace amma kinsa nace idan baki kawo min ba? Kin tuna abinda na fada? Samha tayi shiru, 


Murmushi hydar yayi sannan ya kara jawo samha kusa dashi a jikin hijabinta ya makala mata maganadison macijin sannan ya saki hannun samha yana dariya keta,


Dan idan maganadison tana jikin mutum shine macijin robar zaiyi ta bi yana makalewa a jikin mutum, a hankali ta fiddo macijinta daga cikin hijabi tare da mikawa hydar tace anshi wannan tsaraba ce inji samha, kafin ya ansa mutane suka fara ke yarinya maciji maciji a kusa dake, 


A gigice samha ta juya wani irin katon maciji ta gani ya tun karota da gudun bala'i yana bude baki, sai wani zazzaro harshe yakeyi, da sauri ta kalli macijin hannunta dan a tunaninta shine ya fadi a kasa zai cijeta, da sauri ta yada macijin hannunta sannan ta fara gudu,


Murmushi hydar yayi sannan ya gyara tsayuwarshi tare da rungume hannayensa, yana kallon samha tana gudu, duk inda ta tunkari gungun mutane saida su fashe, saboda ganin maciji, ihu samha ta farayi tare da cewa a taimaketa,


Kuka takeyi sosai tana karawa ganin maciji yaki ya daina binta yasa ta tsaya da a tunaninta idan ta tsaya zai tsaya shima ya daina binta, gani tayi ya fasa kai yana kokarin hayewa jikinta, da sauri ta tunkari hanyar bene zata haye, hankalin hydar ya tashi dan kada taje ta hau sama wurin gudu ta fado, da sauri ya koma mota ya dauki fuska as sahib ya saka ya nufi wurin da gudu,  daidai yana isa samha tana kokarin dirowa, da sauri ya rikota ya cire maganadison a jikinta,


Ganin sahib yasa samha yin a jiyar zuciya jiki a mace ta fada saman jikin hydar tana sauke nunfashin wahala, dariya yayi a ranshi amma a fili cikin yanayin damuwa yace zakije ki fada ki kashe kanki a banza,


Gaki baki kashe hydar ba hydar zai kasheki, cikin kuka samha tace saina kasheshi, murmushi hydar yayi sannan ya saketa daga jikinshi yana kallonta, ita kuma a hankali ta dago kanta ta fara dubawa ko zataga macijin hydar yace ya tafi , wuce ki tafi gida,


Rike hydar samha tayi cikin kuka tace bazan taba yafewa hydar ba ko kabarinsa zaici da wuta balbal da sauri hydar ya rufe mata baki da hannunshi yace banasan kina irin wannan abun idan ba haka ba zan bata dake, ko kina so in bata dake ne? Girgiza kai samha tayi alamar A, a, hydar yace to yafe mishi, ajiyar zuciya tayi sannan tace kawai dai barshi da Allah, hydar yace A, a, kiyi hakuri kiyafe mishi kinji samha, yayi maganar ne cikin rarrashi ,dan gajeran tsaki samah tayi ba tare da tace komai ba, kallonta hydar yayi sannan yace nifa bana san inji ana tsoki bana so, ba tare da tayi magana ba ta janye hannunta daga cikin nashi,


A hankali samha ta fara tafiya ba tare data kalli hydar ba, yana nan tsaye harta sauka, yana saman bene yana hangota har ta hau napep, samha saida ta shiga napep sannan hankalinta ya dawo lallai kayan jikin hydar sune ta gani jikin sahib, ya haka kuma? Da sauri tace ma mai napep koma baya,


Da sauri yayo rivers yana dawowa da gudu samha ta sauko a napep hydar na hangota ranshi ya bashi akwai wani abu dan haka da sauri ya cire fuskar a daidai lokacin da take hawowa shi kuma ya tilla fuskar kasa yaransa suka dauke,


Da gudu samha tahau sama, hydar yana tsaye yana kallonta, dube dube ta farayi wai tana nema sahib, haka ta gama dubawa amma bata ganshi ba, kallon hydar tayi kasa da sama sannan tace idiot, 


Hydar yace ubanki ne idot noncesess, kusa dashi ta matsa ta dauki robar ruwan daya ajiye a gabanshi ta dauka saida ta cika bakinta dashi sanannan ta watsa mishi a fuska, wani irin kallo hydar yayi mata amma baiyi yunkurin yi mata komai ba yana kallonta, samha tace sakarai mai idon mujiya, shidai baiyi magana ba yana kallonta kawai, ganin ta juya zata tafi yace ke zo nan, samha tace anki azo azzalimi sakarai mai fada mace ta ruga, daga muryarshi yayi sannan yace zakici ubanki idan na kamaki,


Daga can samha tace andai ji kunya katon banza,  yana kallonta harta fita tahau napep murmushi yayi sannan ya goge fuskarshi data watsa mishi ruwa, ajiyar zuciya hydar yayi sannan yace kada fa wasa ya zama gaske? Dan gajeran tsaki yayi sannan yace karya ne, babu wani gaske wasa ne daidai zuciyarsa ya taba sannan yace wasa ne ai kema kin sani ko? Wai zuciyarsa yake tambaya,


A hankali ya fara tafiya harya ya sauka daga saman benen lokacin har an fara kiran sallah magrib, cikin damuwa hydar ya isa gida, saida yayi wanka sannan ya nufi masallacin dake cikin gidanshi,


Samha kuwa tana zuwa gida saida tayi alwallah sannan ta shiga daki, tayi sallah magirib saida tayi isha'i sannan ta tashi, wanka tayi bayan ta gama shirinta tsaf ta dauko wayarta ta fara kiran sahib,


Hydar yana kallon wayar tana ringing amma yaki dauka, haka samha taci gaba da kiranshi amma saboda tattirancin iskanci hydar bai dauki wayar ba, ajiyar zuciya samha tayi sannan tace ko yayi fushine saboda na zagi hydar? Haka nan taji babu dadi a ranta, zuciyarta tayi mata wani iri, text ta fara rubuta mishi,


Sahib don Allah kayi hakuri abinda ya faru daxu ka dauki waya zanyi magana dakai, lokacin da hydar yaga sakon tsaki yayi sannan ya mike canja kayan jikinshi zaiyi bakuwa, kaji wani hauka wai mace zatazo zanje wurin namiji,


A hankali samha ta tashi daga kwanciyar data yi jin anki a dauki wayar kuma lokaci mai tsayi sahib bai maido reply ba na sakon data tura, taci gaba da kiran wayar, hydar dake tsaye yana feshe jikinshi da turare yayi murmushi tare da cewa yarinya ta fara fadawa tarko, kusa da wayar ya matsa sannan ya dauki wayar ya kasheta gaba daya,


Lokacin da samha ta sake kiran sahib taji wayar a kashe hankalinta ya tashi sosai, haka nan kawai taji ta hawaye na diga daga idonta, a hankali ta koma ta kwanta, tare da tunani barkatai a zuciyarta,


Shi kuwa hydar bayan ya gama gayunshi das dashi ya fito farlo ya kashe saman kujera ya dauki kafa daya ya dora saman daya, kallo daya zakayi wa hydar ka tsaida idonka akanshi dan gaskiya hydar ba karamin kyau gareshi ba, yana da kyau mai kyau, sannan kuma yana da aji bai cika dariya ba amma yana fara'a, itama fara'ar  ba kowa da kowa akeyi ma wa ba, yana da gwarjini sosai wanda baka iya saka idonka cikin nasa,


Hydar saida yasha zancenshi dashi da Asma'u ansha soyayya sosai Asma'u sai kuka takeyi ma hydar wai ya rufa mata asiri ya aureta, kallonta kawai hydar yakeyi haka ta gama surutunta shidai bai bata amsa ba, dan haka ta gaji da magana babu mai tayata ta mike tacewa hydar zata tafiya, hydar ya tashi ya shuga ciki dubu dari biyar ya bata, godiya tayi mishi sannan ta tafi,



Samha kuwa a daren ranar nan kasa bacci tayi, tace hakika kawu yayi gaskiya daya ce *so mugun wasa* ne, a lokacin da bana soyayya babu abinda yake bata min rai, amma yau ga sahib ya hanani bacci, kuma nasan yana ganin wayar amma ya basar dani, wata zuciyar tace mata A, a, samha kila baya da chargy, dan gajeran tsaki samha tayi a bayyane tace gaskiya yana gani, wannan shine gaskiyar magana,


Haka tayi ta juyi amma kirikiri bacci ya gagari samha, agogon wayarta ta duba taga 10:03pm samha tace lallai yau da nasan gidan sahib dasai naje inga ko lafiya? Amma ba komai nasashi ya nunamin saboda wata rana, haka dai ta hakura ta kwanta amma bacci dan yana barawo da batayi ba,


Hydar kuwa baccinsa yasha abinshi hankali sa kwance kamar ya hau jirgi mai ya kare, da safe bayan yayi sallah asuba ya dawo dan yaune tafiyarsa ta kama zuwa Switzerland, amma sai yacewa samha zaije kauye wurin mamanshi,


Saida ya gama shirin tafiyarsa sannan ya bude wayar da yake kiran samha dashi ya kirata, ringing daya tayi samha ta dauka kamar jira take sahib ya kirata, cike da masifa tace wannan ai daukar alhakine tun jiya inyi ta kiranka shine bazaka dauki waya ba miye haka don Allah, sassauta muryarta tayi cikin lallashi tace ko dan na zagi hydar ne? Don Allah kayi hakuri insha Allah haka bazai sake faruwa ba,


Hydar yace to babu damuwa, kuma ma ai ba kin daukar wayar nayi ba, kinsan wayarmu sai a hankali nayi nayi in dauka amma saboda ta lalace bata daukuwa, daga baya ma kawai chargy ya kare, cikin yanayin damuwa samha tace to ka canja waya mana, dan zaro idanuwa yayi kamar samha tana ganinsa sannan yace haba samha? Ke yanzun idan nace miki zan canja waya ai kinyi min fada, shin a ina ma naga wani kudin canjawa? Amma bara zanma hydar magana idan zai canja min, tun kafin ya karasa maganar samha ta tari numfashinsa cewa,


Allah ya sawake maka hydar ya canja maka waya, baga ni ba? Kayi hakuri zan canja maka insha Allah, murmushi hydar yayi sannan ya shafa gashin kanshi yace to a ina zaki samu kudi ne? Samha tace insha Allah zan samu, hydar yace to kada ki wani wahalar da kanki insha Allah zan canja bara sai na dawo daga kauye, 


Samha tace bazaka zo min bankwana ba? Kallon kanshi yayi sannan yace kiyi hakuri samha ina nan tasha kuma har motar ta cika, ajiyar zuciya samha tayi sannan tace amma banji dadi ba wallahi hydar yace kada ki damu ina dawowa kawai gidanku zan sauka, murmushi tayi sannan tace to Allah ya dawo dakai lafiya yace amin, amma zaki ga bana kiranki kauyenmu babu services samha tace har wannan dadewar bazanyi waya dakai ba? Hydar yace kiyi hakuri, haka dai sukayi fira sosai, daga baya sukayi sallama da juna,


Hydar yana gama waya da samha ya kashe wayar da yake kiranta ya ajiye, dan gajeran tsaki yayi gaskiya ace zaiyi wata ukku har ya dawo baiyi waya da samha bai kyauta mata ba, to amma lallai dole haka zaiyi dan idan har ya kirata da number waje zata iya ganewa, baidai ji dadin hakan ba, tashi yayi lallai bazai iya tafiya baiyi ma samha sallama ba,


Ajiyar zuciya yayi sannan ya fita ba tare daya saka fuskar da yake cewa sahib ba, ya tafi as hydar dinshi, yana fitowa ya shige moto akayi comeboy kamar yanda ya saba idan zai fita haka aka dauki hanya sai gidansu samha dan daga can bazai dawo ba, wucewa zaiyi dan haka suka tafi,


Lokacin da motocin hydar suka isa kofar gidansu samha ita kuma tana tsaye kofar gida ita da illo, tsaki hydar yayi sannan ya fita daga motar a zuciye dama jiya ya ganshi ya fito daga gidan yau kuma tunda safe tana tsaye dashi tana ta wani bude baki tana dariya, ko inda hydar yake samha bata kalla ba, taci gaba da firanta, shi kuma illo bai san motocin waye ba, saida hydar ya fito sannan ya gane ko waye da sauri ya sake kallon hydar lallai shine wallahi ba mafarki yakeyi ba, illo saida ya kalli samha ya kalli hydar, ganin ya iso kusa dasu ne yasa illo dukawa da sauri ya gaishe shi, ba tare daya kalli inda yake ba ya isa wurin samha,


Yana zuwa kusa da ita ya daga hannushi ya shararata mata mari, ya sake marinta ya kara narka mata mari ya kara dardarka mata shi sosai cikin tsananin bacin rai yaja hannunta ya shiga gida da ita, a tsorace samha take jikinta har kyarma yake saboda azaba dan gaskiya marin hydar yana mata ciwo sosai, zatayi magana yace idan kika sake kice min wani abu saina shakeki har naji baya nunfashi, samha tayi shiru ta sadda kanta tana kallon kasa,


Tsaki yayi sannan yace ina sahib yake? Cikin rawar murya samha tace baizo ba, hydar yace karya kikeyi ya zo mana a ina kika boyeshi? Samha tace wallahi baizo ba yanda tayi maganar ne hydar yaji ta bashi tausayi dan gaba daya bata cikin hayyacinta, kallon samha yayi sosai sannan yace shi kuma wancan waye shi? Samha tayi shiru hydar yace bakiji ina magana ne? Goge hawayen idonta tayi sannan tace abokina ne, aboki? Dama mace tanayin aboki da namiji?


Samha tayi shiru, jinjina kai hydar yayi sannan yace munafika ji yanda take wani kwantar dakai kamar ta kirki, ganin yana gyara tsayuwa yasa samha ta ruge ta shige daki ta rufe, sannan ta leko ta window tace kaima munafiki da wasu munafikan idonka kamar na mujiya, waikai nan kamshi kakeyi kana shigo naji gidan ya fara tsamin dauda, oyo oyo tayi mishi gwalo , murmushi hydar yayi sannan ya fita daga gidan yana dariya,


Saida ya fita sannan samha tayi ajiyar zuciya gaban mirrow ta matsa tana kallon yanda hydar yaci ma fuskarta mutunci ga sahun hannunshi duk ya fito, sake fashewa tayi da kuka sannan tace wallahi bazan yadda ba saina rama tana maganar tana kuka, 


Hydar ko a motar murmushi yakeyi yana tunanin daya mareta yanda ta wani zazzaro ido kamar an shaketa, idan ta fiddo idanuwanta yana san ganinta a yanayin saboda shi kadai yasan yanda yakeji wannan dalilin yasa yake tsorata idan ta fiddo idanuwa baya so ya daina kallonta dan yanda take abun yana mishi dadi, murmushi ya sakeyi sannan yayi wasa da idanuwanshi, wai nine nake da idon muji ajiyar zuciya yayi sannan yace tana san idanuwana tunda tana yawan maganarsu,


Saida ta tabbatar hydar ya tafi sannan ta fito tsakar gida ta zauna jikin bishiyar mangwaron gidan tana kuka bazata yadda ba, da sahib ya gani shine zaiyi mishi duka lallai da sahib ya daka wallahi saina ci ubanshi, haka tayi ta kukanta tana jawo ma hydar Allah ya isa,


Tana nan zaune tana kuka illo ya shigo gidan da gudu, tare da cewa samha shima sane shi kikayi yazo ya dakeki? Cikin kuka samha tace wallahi bazan yadda ba saina rama marina, idanuwa illo ya zaro tare da cewa ke samha? Kin kuwa san waye hydar? Wallahi ki rufama kanki asiri dan yafi karfinki dan duk inda baki tunanin hydar ya wuce wurin,


Illo yaci gaba da cewa wallahi matashin yaro ne Allah yabai sa'ar rayuwa, mamanshi da babanshi shi kadai suka haifa daga shi basu sake haihuwar kowa ba, yanajin dadin rayuwarshi mutuwa tayi ma iyayenshi gaggawa amma wasu sunce hada kai akayi aka kashesu sai akace wai jirgi yayi hadari dasu sun mutu, gaskiya baban hydar baban mutum ne ya rike mukamai da yawa a cikin siyasa ya tara kudi kamar hauka, yana cikin jin dadinshi ya ansa kiran mahalicci dashi da matarsa,


Ke ina kika san hydar? Samha tace wurin training, illo yace to ai wurin training dinma nashi ne, zaman kadaici ne yasa yake zuwa, amma wallahi ki kiyayi hydar idan ba haka ba yana iya batar dake babu wanda zai karajin labarinki,


Cikin gamsu samha tace to dama shine yake jana, illo yace da kin ganshi wallahi ki rika boyewa, hydar baya da wasa baya san raini, samha tace ni banma san waye ya nuna mishi gidan nan ba, haka dai illo ya saki baki yayi ta tsorata samha da maganganu masu firgitarwa akan hydar,


Saida suka gama fira da illo sannan ta shiga ta shirya dan tafiya wurin kawu, lokacin da taje saida ta bada kudi aka fiddo mata kawu, bayan ya fito suka gaisa kawu yace haba samha sai yau zan ganki? Samha tayi shiru kawu yace samha kiji tsoron Allah dan kinga bana nan shine kika fada harkar soyayya ko? Da sauri samha ta dago kanta ta kalli kawu sannan tace waye yace maka soyayya nake? Kawu yace duk halin da kike ciki na sani kuma inaji a jikina, murmushi samha tayi sannan tace,


Ba haka bane, kawu yace karya zan miki ne? Samha tayi shiru, kawu yaci gaba da cewa kalli nan ki gani, kallonshi samha tayi shi kuma ya bude gaban rigarsa, sunanta ta gani an rubuta *SAMHA* kara bude idanuwa samha tayi ta kara kallon wurin, kawu yace samha na dade ina sanki ina dakon kaunarki a zuciyata ina sanki fiye da tuannainki samha ki soni koda girgijen san da nake miki ki taimaki zuciyata, idan kuma baki yadda ba kije dakina shine zai nuna miki shedar ina sanki, 3 3 2 da nake cewa samha, 3 tana nufin *Ina* 3 tana nufin *San* 2 tana ki *Ki* idan kika hada shine zai baki { ina san ki, } 


Ajiyar zuciya samha tayi sannan tace nima ina sanka kawu sosai, so wanda ban tabayi ma wani irinshi ba, zuciyata dakai ta fara kuma dakai zata rufe, kawu yace karyane,  baki wani sona gashi saboda namiji kin siyar min da gida kin bashi kudin danshi yaji dadi, murmushi samha tayi sannan tace kai kuma dan kaji dadi kasa ni nayi ta sace sace saboda kai kawu kaga maganar siyar da gida wannan ba damuwar ka bane nice na nema kuma nice zanci gaba da nema harsai na sake mayar maka da wani,


Gyara rigarshi kawu yayi sannan yace to naji, idan Allah ya kaimu karshen wata akwai wasan caca dan haka ki shirya kije ki wakilce ni, zunzurutun kudi naira milayn biyar aka saka, idan har kika ciwo min kudin nan zan hadaki da ahalinki, 


Sahma tace haba kawu? Nifa ban iya caca ba, kawu yace babu wani abinda ya dameni shawara ta rage taki yana fadin haka ya juya harya fara tafiya sannan ya juyo yace kudinki sune iyayenki, idan kuma kin fadi babu ke babu  ganinsu har abadan duniya ina fitowa kuma daga nan zansa a daura min aure dake daga nan sai mu bude sabuwar rayuwa, yawwa samha na manta don Allah ki dan kawo min giya kwana da yawa bansha ba, tsaki samha tayi sannan ta fice daga wurin cikin fushi, dariya kawu yayi sannan yace bazata canja ba,


Hankalin samha yayi matukar tashi dan batama san abinda kawu ya mayar da ita ba, wannan ai iskanci ne, zama tayi tana nazari murmushi tayi sosai sannan tace hakika na gano sharrin kawu akaina, yana kurkuku ni kuma ina rayuwa a waje, yana so na ina soyayya da wani daban bashi ba, a wasan caca aka kamashi inje inyi mishi wasan caca, idan naje wurin wasan za'a kamani sai inje inyi rayuwa dashi a gidan yari, wata zuciyar tace ba haka bane samha, murmushi samha tayi sanna tace wannan shine gaskiyar magana, amma nasa mafita,


Zanje wurin wasan caca acan zanji sirrin kawu insha Allah a nan zan gano a ina iyayena suke, lokacin da samha ta fara zuwa gidan caca labari yakai kunne hydar kuma hankalinsa ya tashi sosai dan dama dazai tafi yasa a sakawa samha ido sosai to duk wani motsi nata yana kan tafin hannunsa, dan haka wanda yayi mishi wayar cewa yaga samha a gidan caca yace zai turo mishi number wani abaokinsa daya kara ganinta ya kirashi a kama samha harsai ya dawo,


Itama samha kwalwarta kar take dan haka saita canja lokacin zuwa, Ita kuma haka da tayi tana basaja ne saboda kada kawu ya turo a kamata, dan haka wani lokaci tana gama sallar asuba zata tafi ta zauna a wurin, 


shi kuma wanda hydar yasa gadin samha ganin ya daina ganinta kwana biyu yasa shi cewa hydar yama daina ganin samha kwata kwata kila yana jin tayi tafiya, 


Haka samha taci gaba da shirin wasan caca kuma ta koya ta iya dan haka, Dan tayi kudirin kawu zaiyi mamakinta,


Hydar zaune dashi da abokinsa suna fira, faruk ya lura hydar ya cika yawan maganar samha, dan haka faruk yace mishi waikai yaushe ka fara harkar mata ne? Murmushi hydar yayi sannan tace ba harkar mata nakeyi ba, yarinyar ce tana da taurin kai ni kuma nayi alkawarin sanya ta jinyar zuciyarta saina koya mata hankali, duk abinda ka gani faruk ba gaskiya bane wasa ne, faruk yayi dariya sannan yace amma hydar kayi babban kuskure dan lallai zaka kashe kanka a banza a wofi banda ganganci da rayuwa waye yace maka ana so a wasa? Hydar yace ban sani ba nidai nayi kuma zaka tausayawa rayuwar samha dan tuni ta fada san sahib nan bada dadewa ba zaka ga hukuncin da zanyi,


Faruk yace hydar ka rufawa kanka asiri ka fita harkar yarinyar nan, idan hukuncin abinda tayi maka zakayi to kawai kasa a hukunta ko kuma kayi mata hukunci amma wannan wallahi ba shawara bace da zata taimaka maka ba, hydar yace da Allah kada ka daukeni karamin yaro mana nafa san ban santa kuma zuciyata ta sani ita shedace, Allah na tuba faruk mata kirki ma basu dameni ba bare samha kayan banza, 


Furuk yace Allah dai ya sawake amma lallai kana san yarinyar nan, hydar yace karya ne, faruk yace karya kake yi kana santa daure fuska hydar yayi yace kada ka saki ka sake karyata ni gaskiya ne duk abinda na fada gaskiya ne, murmushi faruk yayi tare da cewa Allah ya bada sa'a,


Yau ya kama wasan cacansu samha dan haka wurin cike yake da mutane maza da mata "yan tasha wanda basu da ilimin addini bare kuma na zamani, wanda zasu yi wasa da samha yasa miliyan biyar shi kuma kudin da kawu ya bayar shine miliyan goma, gabaki daya wuri ya cakude banda warin abubuwan maye babu abinda kakeji wurin, sai kuma mata karuwai gasunan saman jikin mazaje kamar kadangaru sun samu bango sai watsewa akeyi,


Kwalben giya ne akazo aka jera a saman tebirin su samha da kofina, haka aka fara zuba giyar a kofinan sannan aka dauka aka fara basu daya bayan daya,



*Meelat Musa* ce

[05/04 4:45 pm] Washa: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊



                 *SO*

     *MUGUN WASA*



       *{ Love is a bad game }*




*JAMEELA MUSA* { meelat musa }




*Story, Writing & Editing*

                   *by*

         *Meelat Musa*


_Na'ikke marubuciyar farar tafiya { sa'a } wallahi meelat musa & ramlat Abdulrahman { mai dambu } muna sanki muna kaunarki munayinki sosai Allah ubangiji ya kara basira da hazaka Allah yasa ki zarce haka a fadin duniyar marubutu Allah ya kara hazaka da basira Albarkacin na'ikke REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM daukacin marubutan BRILLIANT WRITER'S ASSOCIATION suna muku fatan Alkairi na'ikke meelat musa & ramlat abdulrahma { mai dambu } muke miki fatan alkairi Alkairin Allah ya isoki har cikin bargon baccinki_


_Ina masoyan mai dambu? Ku marmatso ku bani aron kunnuwanku don Allah, zan fada muku ainahin sunan masoyiyarku, ku daina tambayata yaudai zan fada muku kowa yaji, wato ai nahin sunan real mai dambu shine, RAMLAT ABDULHAMAN MANGA itace kuma REAL MAI DAMBU masoyan mai dambu kunji sunan masoyiyar taku fa marubuciyar_


_Wani Al'amari_

_Yaro ma namiji ne_

_Jameela tawa ce_

_Kishiyata jahadi na_


_Kuyi ta kasancewa da Ramlat Abdulrahman, Real mai dambu ce_


_Asmeenat Xeeyan gaskiya bansan da wane irin baki zan miki godiya ba Asmeenat ki tawa ce kuma ni taki ce ina tare dake sosai ina alfahari dake dan kema din maudi'in meelat musa ce_


_Raheema maruciyar littafin uwar miji gaskiya inayinki sosai kuma ina alfahari dake ina jinki har cikin babban birni zuciyata_❤



                  *SO*

      *MUGUN WASA*


*Dedicated to* 👇🏻

_Ramlat Abdulrahman real mai dambu_



*23-25*



Kofin giya aka mikawa samha dan gajeran murmushi tayi sannan ta girgiza kanta alamar A, a,


Abokin cacar nata ne yace bazai yuwu ba tunda yasha dole itama sai tasha kuma a ka'idar wasansu haka ne ba'a fara wasa dole sai an shawu sannan ake fara gabatar da wasa,


Gyara zama samha tayi sannan tace nikam gaskiya bana maye, wani ne ya iso wurin da waya a hannunsa cewa ga kalifa nan yana waya, wato kawu,


Mikawa samha waya akayi ana cewa ga kawunki zaiyi magana dake, murmushi samha tayi da gefen bakinta sannan tace kace mishi ya kirani a wayata,


Cikin daga murya mutumin yace kada ki dauki mutane "yan iska mana? Zaki ansa ko bazaki an sa ba? Dago kai samha tayi sannan tace bazan ansa ba,


Kara daga murya yayi cewa idan bazaki ansa ba saiki tashi ki wuce ki bawa mutane wuri, murmushi samha tayi sannan tace a sauki kenan ba tare da ta sake magana ba ta mike,


Ke ina zakije ne? Samha batayi magana ba dan ta lura a wurin akwai babbar harkalla, glass din idon ta saka sannan tayi gaba, ana magana amma ta basar ta wuce abunta,


Samha tana fita ba gida ta nufa ba a napep tasa akayi ta shawagi da ita a gari, wai kada wani ya biyota ya gidanta ya kasheta a banza,


Saida samha ta gaji sannan tasa aka sauketa a napep ta sallameshi, da kafarta ta fara tafiya, haka tayi ta kutsawa wurare tana tafiya tana dan kalle kalle,


Wurin wani cin abinci ta gani da mutane wurin sosai dan gajeran tsaki tayi sannan ta duba agogon wayarta taga 9:45pm shiga tayi wurin da zumar cin abinci wani abokin kawu ta gani dan haka da sauri ta shiga wurin tana fadada murmushinta,


Kujera taja ta zauna mai fuskantar shi sannan tace sannu, yawwa yace, samha tace ya kokari? Lafiya qalau samha, murmushi samha tayi sannan tace ashe kasan suna na?


Shima murmushi yayi sannan yace har kun gama wasan cacar ne? bata fuska samha tayi sannan tace gaskiya kuduwa nayi! Gyara zama yayi sannan yace miyasa kika gudu ne? Samha tace gaskiya na lura kamar so ake a salwantar min da rayuwa,


Murmushi yayi sannan ya gyara zamanshi yace ya akayi kikayi wannan babban karatun ne? Samha tace ba karatu bane fahimta ce, murmushi yayi sannan yace gaskiya kalifa baida amana,


Samha tace wannan matsalarshi ne, a kawo mana tea mana, tayi haka ne dan kauda maganar, kawo musu tea akayi suka sha samha ta biya kudin sannan tayi ma abokin kawu sallama,


Tana fita tahau mashin a nesa da gida ta sauka sannan tabi lunguna harta isa gida, bayan taje gida ta kwanta ta fara tunani lallai akwai babbar matsala, shin ni ta ina ma zan faro ma abun nan?


Da wannan tunanin tayi bacci sai kuma sahib daya makale mata a saman zuciyarta,


Haka rayuwa taci gaba da tafiya samha sam bata sake gigin zuwa gidan caca ba, haka kuma bata sake zuwa wurin kawu ba, tsaye take saman kafafuwanta sosai tana bincike ta ina zata nemo iyayen ta? Shin suna ma raye ko suna mace? 


Kukan wayarta ne ya dawo da ita tunanin da takeyi da sauri ta isa inda wayarta ta dauka, ajiyar zuciya tayi ganin sunan sahib, da sauri ta dauki wayar tare dayin sallama ta kara wayar kunnenta,


Ansa sallamar hydar yayi sannan yace samha nafa dade da dawowa, samha tace to ya za'ayi in san ka dawo banda abinka? Hydar yace ashe ma baki sona? Murmushi samha tayi tare da dan zaro ido kamar hydar yana ganinta tace ina sanka mana sosai ma, Hydar yace ai nayi tunanin zakiyi ta kiran wayana ne har ki sameni,


Murmushi tayi sannan tace to yanxun dai Allah ya baka hakuri kayi hakuri gaskiya ban kyauta ba, amma tunda ka gyara min zan gyara nan gaba insha Allah, sannu da zuwa fatanka dawo lafiya yamai jiki? 


Hydar yace mai jiki da sauki sosai, samha tace to Allah ya kara sawake, hydar yace amin, samha tace to yaushe zaka zo ne? Dan shiru yayi sannan yace A, a saidai ke kizo gaskiya mu hadu wurin training mana, murmushi samha tayi sannan tace to sai nazo insha Allah hydar yace yawwa ina saurarenki,


Cikin rawar jiki samha ta shige daki tana shiga ta cire kayan jikinta ta fada toilet a gaggauce tayi wanka tana fitowa tayi shafa, mai da powder da kwalli kadai ta saka sai girarta data gyara,


Kaya masu kyan gaske ta dauka ta kakuba riga da sikat ne, sunyi mata kyau sosai ta daura dankwalinta dauri mai kyau sannan tabi jikin ta fara mishi anbali da ruwan turare, bayan ta gama ta dauki takalmi da jakarta da gyale masu kyau da tsada sannan ta saka,


Kusa da madubi ta matsa ta kalli kanta murmushi tayi sannan ta kara kimtsa bakinta ta fara nuna yanda zatayi magana da sahib idan sun hadu, a bayyane tace kai gaskiya nayi kyau sosai lallai sahib zaiji dadin gani na a haka,


Tana gamawa ta dauki wayarta ta fice daga dakin, tana fita ta kulle gidan sannan ta samu napep ta hau, sai wurin training,


Tana isa wurin ta sallami mai napep dan ba'a barin masu napep suna shiga a wurin, dan haka haikan ta tasar ma wurin zuciyarta cike da shaukin ganin sahib, tana kokarin shiga ne mai gadi ya dakatar da ita, 


Samha ta tsaya tare da gyara zaman glass din idonta tace malam yadai? Tana maganar tana yatsina fuska, mai gadi yace ina zakije ne? Samha tace zanje wurin sahib ne, mai gadi yace waye sahib ne? Murmushi samha tayi sannan tace kaga malam bani hanya in wuce,


Tunda nake zuwa baka taba tambayana wurin wa zanje ba sai yau? Mai gadi yace mai wurin ne yace kada a barki ki sake zuwa, samha tace wane dan iska ne? A daidai lokacin da hydar ya iso wurin yace nine nan dan uwarki juya ki koma inda kika fito,


Da sauri samha ta cire glass din idonta sannan tace waikai hydar miya sa dan iska ne? Idanuwa hydar ya zaro sannan yace ke ? Nine kike kallon idona kike cewa dan iska? Samha ta rike kugu sosai sannan tace nace banza sakarai kawai dakai,


Matsawa kusa da ita hydar yayi sannan yasa hannunsa a aljihu ya fiddo abinda yake shafawa samha a ido ya fesa mata,


Wani irin ihu samha ta farayi tana dire dire saboda azaba, da hannunta take laluben hydar amma yaja baya yana dariya dashi da abokanshi, sai kuka samha takeyi tana murza idonta, haka su hydar sukayi ta dariya daga baya yaja tawagar abokansa suka tafi,


Saida samha ta gama kukanta a hankali ta fara bude idonta, hydar ta hango suna tahowa a mota da alama gida zai tafi, jinjina kai samha tayi sannan ta matsa bakin titi ta samu wani lafiyayen dutsenta ta rike,


Motarshi tana fitowa ta saita glass din baya ta bareshi ji kake tatsatatsa, gaba daya glass din ya zube da sauri Alale yayi parking zai fita hydar yayi dariya cewa kyaleta wai nan taji haushi ta rama,


Kallon samha hydar yayi sannan yayi mata kyakkyawan murmushi mai kashe jiki yana mata wani irin kallo mai sauke gajiya, yanda yayi abun yasa samha taji kafafuwanta baya daukarta, hydar ya kula da haka murmushi yayi sannan ya dauke kanshi yayi yana dariya a ranshi,


Saida motar hydar ta bace sannan samha ta samu napep ta hau ta nufi gida, tana shiga gida wayarta ta fara ringing, sahib ta gani murmushi tayi sannan ta dauki wayar,


Cikin rawar murya ta irin wanda yasha kuka ya gaji samha ta fara magana, hydar yace mi akayi miki kuma? Kin wani barni a wurin training nayi ta jiranki shine kika wani basar dani baki zo ba? Samha tace kayi hakuri hydar ne ya hana a barni na shiga samha taci gaba da cewa kuma nayi maka gayu mai kyau kuma yau ban saka nikaf ba, murmushi hydar yayi sannan yace to mi hydar din yayi miki ne? Samha tace ba komai barshi kawai, abinda hydar ya kula samha bata cika san idan wani abu ya hadata dashi daban ta fada mishi a matsayin shi sahib,


Murmushi yayi sannan yace gani nan zuwa yanxun ki sake yin wani gayun zanzo in ganki, samha tace to tana kashe wayar ta tashi da sauri taje tayi wanka,


Shima hydar wanka yayi bayan ya fito ya shirya cikin shiga mai kyau da kama hankali, fuskarshi ya dauka ya saka, sannan ya dauki ledar kayan daya siyo ma samha switzerland, ya fita daga dakin,


Yana fita Alale driver ya anshi ledar har mota ya budewa hydar ya shiga sannan ya ajiye mishi ledar yayi mishi fatan dawowa lafiya, hydar da kanshi yaja motar yayi gidansu samha,


Yana zuwa bayan yayi parking yayi mata waya yazo, kuma shigowa zaiyi samha tace to, bayan ya gama waya da ita ya fita daga motar ya shiga gidansu samha, tana zaune a tsakar gida saman plastic chair,


Da sauri ta taso ta taho wurinshi tana mishi sannu da zuwa, hydar ya ansa, zama yayi sanan ya ajiye ledar hannushi, kallonshi samha tayi sannan tace kayi kyau fa, tana maganar tana dan wasa da ido, murmushi yayi amma baiyi magana ba,


Itama zama tayi tana kallonshi hydar yace dauka wannan kije ki saka unguwa zamu, idanuwa samha ta zaro sannan tace unguwa kuma? Da kanshi ya bata amsa alamar Eh, bude kayan samha tayi sannan tace a ina ka samo su? Murmushi hydar yayi sannan yace hydar ne ya bani yace in bawa budurwata, yanzu ma aikena yayi shine na biyo in tafi dake,


Babu wani damuwa samha ta dauki kayan ta shige ciki da sauri, kayane masu kyau da tsada kana ganin kayan kasan ba sayen yara bane ko masu dan karamin kudi,


Ga turaruka masu tsadar gaske agogo zobuna da sarka da "yan kunne duk na zinari murmushi samha tayi sannan ta dauki kayan ta saka, ta kara gyara fuska sannan ta fito,


Tana fitowa da wata irin tafiya mai jan hankali tazo gaban hydar ta tsaya sannan ta danyi wani dan gaba kadan tayi baya kadan yanda tayi abun ne yayi mashi kyau sosai yabi samha da kallo yana murmushi,


Dan daga hannuwanta tayi sama tana wani dan juyi mai jan hankali sannan ta juyowo ta kalli hydar ta daga mishi gira tare da kashe mishi ido daya sannan tace ya kaga samha? Jinjina kai kawai hydar yayi sannan yace samha tayi kyau sosai, samha tace to muje tayi gaba da dan sauri kamar zatayi fareti tana tafiya tana wurga hannuwanta, ajiyar zuciya hydar yayi yanda samha takeyin abun yayi mishi kyau sosai  tashi yayi yabi bayanta harsun kusa fita yace samha, uhmm tace tare da juyowa,


Hydar yace miyasa baki saka "yan kunnen ba? cikin sakata da shagwaba tace ni basai na wani saka ba, kaidai kawai muje a haka, dan gajeran tsaki hydar yayi sannan yace don Allah ki saka ni ina san inga mace tanayin gayu sosai nidai ina san mace ma'aboci gayu da kamshi una san tsabtatticiyar mace, nidai kije ki saka,


Batayi magana ba ta juya da sauri ta koma ta saka sarka da dan kunne zobe da agogo, saida ta kara fesa turare sannan ta fito, lokacin hydar harya fita dan haka itama da sauri ta fita sannan ta rufe gidan, a mota ta sameshi dan haka tana zuwa ta bude ta shige hydar yaja suka tafi,


Haka suke tafiyar babu mai magana, sai samha lokaci lokaci tana danyin magana hydar saidai yace umm , uumm, hmm, iyya, iyakar maganarsa kenan, har suka isa wurin da zasuje, bayan sun isa hydar ya barta a mota ya fita,


Saida ya dade sannan ya dawo yace ma samha ta fito, bude motar tayi ta fita sannan tabi bayanshi, ƙayataccen wurine da aka ƙawatashi da fitilu masu daukar hankali aka gyara shi aka tsarashi da abubuwan more rayuwa, maza da mata ne masu aji kowa harkar gabansa yake yi babu wani ruwan kowa da kowa, kowa ka gani a wurin harkar gabansa yake, 


Suna zuwa wani office suka shiga, bayan sun shiga ne hydar ya nunawa samha wurin zama ta zauna, hydar ya gabatar da samha wurin faruk abokinsa, samha ta gaishe shi, bayan sun gama gaisawa ne hydar yace a kawo ma samha lemu ai zakisha ko? Hydar ne yake tamayarta,


Murmushi tayi amma batayi magana ba, faruk ya fita hydar ya zauna kusa da samha sannan yace wai ina kawayenki da kuke zuwa dasu wurin training da? Cikin nuna rashin jin dadi samha tace iyayensu sun tafi dasu, hydar yace ba mamanku daya dasu ba? Samha tace Eh "ya"yan yayan wanda yake rikeni ne, 


Hydar yace shi din waye dinki ne? Samha tace shi ba kowa na bane bansan shi ba bansan yanda nake dashi, tabe baki samha tayi sannan taci gaba da cewa kawai dai inajin ya sace ni ne daga cikin ahalina ya zaunar dani a wurinsa, ya mayar dani injin dinsa saida in sama mishi kudi kawai,


Cikin rashin fahimta hydar yace ban gane ba? Samha tace ai baza ka gane karatun ba, murmushi hydar yayi sannan yace idan ki koyar dani zan fahimta dan babu wanda aka haifa da iyawa, gyara zama samha tayi tare da sauke ajiyar zuciya sannan tace, a tunanina babana da mamana basa raye, shi kuma kawu yace an bashi rikona ne zuwa wani lokaci, kuma wanda suka bada ajiya ta basu dawo ba har yanxun, sannan kuma yace iyayena an kashe su ya bani wani memory card yace babana yabar wasiya cewa kada a bani saina shiga 17years za'a bani idan na gani yayi imani zan rama masa kuma zan bi masa hakkinsa, 


Cikin kuka tace a ranar da aka bani m card din a ranar dan iskan hydar ya kwace daga hannun su yusra kuma ya salwantar min da labarin a halina, jingina bayanta tayi da kujera sannan tace bazan taba yafewa ba, sahib kaga hydar ya dilmiyar dani bazan ga iyayena ba ko insan labarinsu har abada haka zan dawwama ina sace sace ina caca,


A daidai lokacin da faruk ya shigo da lemo a hannunsa, baiyi magana ba kawai ya ajiye ya fita, hydar ya dauki lemon ya zuba a glasscup sannan ya bawa samha a baki tasha kadan sannan ta janye kanta, shine ya shanye sauran sannan yace amma samha miyasa kika zabi sanar sane ne?


Samha tace wallahi sahib bani na zaba ba, shi kawu ne, hydar yace to miyasa kike caca? Murmushi tayi sannan tace shima horon kawu ne, shiru hydar yayi ya fara nazari a ranar daya anshi m card daga hannun yusra, lallai ya tuna tazo ta bayanshi tana waya tana kiran sunan samha, tana kokarin saka mishi hannu a aljihune ya juyo yasa aka rike mishi ita yayi mata duka, yana dukanta ne ta fadar da m card ya dauka,


Lallai lokacin daya dauki m card ta fada mishi cewa samha zata zo da wuka, haka kawai ta fada ta gudu, kuma wannan dalilin ne yasa shi neman samha ido rufe, taurin kanta yasa shi zaiyi horonta ta hanyar dawwara mata zuciya a wasan so, to lallai m card baya hannunsa kuma ba m card din gaskiyar bane ita yusra ta yada, lallai akwai abinda yake faruwa akan maganar m card,


Juyawa yayi ya kalli samha dake bacci, agogon hannunsa ya kalla yaga 11:07pm, dan gajeran tsaki yayi sannan ya fara tashin samha, a gigice ta bude idanuwanta cikin yanayin da yake san ganinta, dan ta kara mishi abun yace tashi ga hydar nan, kara zaro idanuwa tayi sosai hydar ya kalleta yana murmushi,


Wayarsa ya fiddo ya kira faruk cewa zasu tafi, faruk yace ai yana wajen, hydar ya kama hannun samha suka fita daga office din,


Saida ya bude mota da kanshi ya saka samha ya rufe sannan ya koma wurin faruk dan sunyi bankwana, yana zuwa kusa da faruk, faruk yace hydar ka rufawa kanka asiri nayi imani da Allah ka kashe kanka ka gama, murmushi hydar yayi sannan yace karya ne ban wani mutu ba gani ina rayuwata gani a gabanka ina numafashi na gani ina kallonka ka saka shet da wando, kayi aski saisaye kuma har sai kace na kashe kaina na gama waye ya fada maka matacce yana magana ne? Duk hydar yake wannan magana yana maganar yana wa faruk murmushi,


Gyara tsayuwa faruk yayi sannan yace kadai san yarinyar can bata sanka bata kaunar duk ranar data gane kaine hydar ta gama dakai har abadan duniya bayan kai kuma ka gama koyawa zuciyarka santa ka fadamin wace matsala zaka fuskanta ne?


Hydar yace karya ne wane dan iska yace maka ina santa ne? Bana santa bana santa bana santa na tsaneta, kuma ka zuba ido ka gani kwanan nan zan sallemeta kaga sai ta tafi jinyar zuciya, dariya faruk yayi sannan yace kudai tafi jinyar zuciya tare wallahi, dan ita gara ma ita tunda har abada bata san da lamarin wani hydar ba kai kuwa ka sani kaine hydar kaine sahib ita kuma itace samha,


Idan kace ka daina santa shikenan dama kai ka kawo kanka kuma kaine ka tafi, tsaki hydar yayi sannan yace kadai kasance tare dani zaka ga yanda zan wulakanta samha a gabanka zaka ga irin kukan da zatayi dan nasan horon da nayi wa zuciyarta ba na wasa bane, yana fadin haka yayi gaba,


Faruk yabi bayan hydar da kallo cikin tausayawa dan lallai hydar yayi babban kuskure, ya rasa wanda zaiso a wasa sai waccan yarinyar ga mata cikakkan mata wanda sugar yaji amma yazo ya likewa waccan "yar karamar yarinyar wanda idan aka rufe mishi daki da ita saiya kashe har lahira wai itace yake wasan so da ita, 


"Yan matan hydar da suke mishi so na hauka faruk ya fara tunani gasu "yan gayu ma'abota gayu da kamshi tsaftatacci cikakkin mata masu komai yaji "ya"yan manyan mutane, amma hydar baya soyayya baya zuwa fira saidai mace ta sameshi gida amma yau shine yake daukar mace a mota hada wani riko mata hannu Oho🤔?  Tsaki faruk yayi sannan yace itama waccan din tana da kyau da siga amma kwata kwata ba abokiyar rayuwar hydar bace,


A hankali hydar yake tuki yana kallon samha ta wutsiyar idonshi ita kuma hankalinta yana kan wayarta saboda kirane yake ta shigowa da bakuwar number a wayar,


Gajiya tayi da kiran ta dauki wayar, muryar kawu taji murmushi tayi sannan tace Allah yaja da ran kawu, tsaki kawu yayi sannan yace wani Allah yaja da raina bayan kin manta dani kina can kin shiga harkar soyayya wato samha duk kashedin da nayi miki ya tashi a banza ko? Yabi ta bayan kunnenki ya wuce? Baza ki gane illar *SO* ba sai ranar da namiji yaja miki ziyarta asibiti dan jinyar zuciya, duk abinda zan fada miki ina fada miki a kan gaskiya ta ne,


Samha tayi shiru kawu yaci gaba da cewa banda kin dauke ni dan iska bansan abinda nakeyi ba na tura ki wasan caca shine kikace ke baki shan giya kikayi tafiyar ki!? Samha ta sakeyin shiru kawu yace to gobe idan Allah ya kaimu akwai wasa dan haka duk abinda kikeyi kije kuma kisha giya kamar yanda kowa yake sha, samha tace to, kawu yace sai maganar m card lallai yana hannuna, gaban samha ya fadi, kawu yace sosai kuma na siyar dashi akan farashin kudi masu tsada idan har kika dawo min da kudina to ni kuma zan baki, wani irin ihu samha tayi wanda yasa hydar taka burki cikin sauri,


A gigice hydar ya kalli samha ita kuma tana cewa karyane kawu ni nan saina hallaka da hannun sai samha ta kashe ka idan har ana mutuwa fiye da daya hakika sai samha ta kashe ka so adadin kwanakin da kayi a duniya, tana kokarin bude mota ta fita hydar ya riketa tare da cewa ina zakije? Fizge hannunta samha tayi ta fita daga motar da gudu tana gudu sosai hydar yana zaune yana kallonta, mashin yaga ta tsaida tahau,


Tabe bakin hydar yayi a bayyane yace ita kuma ina zataje? Duba lokaci yayi yaga 11:49pm, a hankali yaja motarshi yabi bayan samha, hydar yana biye da bayanta har ta isa wurin,


Subahanallah hydar ya fada cewa miye kuma ya kawo samha nan? Bai gama tunani ba yaga ta sauka daga saman mashing din tayi ciki da gudu, tana shiga kudi "yan sanda suka gani na tashin hankali wannan dalilin yasa suka fito ma samha da kawu,


Tun kafin a ida isowa da kawu kusa da samha, samha tayi tsalle ta dira ciki, hydar ganin samha bata fito ba yasa shi cire fuskar daya dore dan idan yaje wurin da fuksar sahib babu wanda yasanshi, yana cire fuskar ya fita daga mota ya shiga ciki da sauri a daidai lokaci da samha ta shake wuyan kawu tana fadin saita kashe shi, ga maza duk sun rirrike ta, amma sun kasa cire samha daga jikin kawu dan ji takeyi tana sakin kawu lallai ta saki iyayenta,


Yanda maza suke dakuna samha da sunan raba fada abin yayi wa hydar ciwo a zuciya ya isa wurin yana zuwa fizga daya yayi mata ta juyo, daga hannunshi yayi ya kasheta da mari kafin ya ajiye hannunshi ta daga nata da niyar ramawa amma sai hydar ya murde hannu saida ya karya hannu sannan ya saki hannun samha ta duke a wurin tana kuka mai tada hankali saboda azaba,


Lokacin hankalin kowa da kowa ya dawo wurin mamakin ganin hydar kawai akeyi yayin da ranka ya dade da kanka? Haka surutai yaci gaba da tashi aka fara gaishe da hydar yayin da wasu suke mamakin abinda ya kawoshi gidan yari da kuma irin wannan daren, hydar babu wanda yayi ma magana yaja hannun samha kuma mai ciwon yaja ta dashi sai wani irin gurnani samha takeyi saboda azaba, gaskiya hydar yana da bakar zuciya sosai wannan dalilin yasa baya kula harkar mata, dan shi baya da hakuri kuma baya daukar raini, ga dai samha an bari da karyayyen hannu a banza,


Ganin hydar yana jan hannunta yasa samha cewa dan iska sakarmin hannu ina kuma zakaje dani? Bayan du saboda kai na shiga wannan masifar ban sanka wallahi idan har na samu wuka kafin in fara kashe waccan dan iskan tsohon kai zan fara kashe, 


Murmushi hydar yayi sannan ya saka hannunshi a aljihu da sauri samha tace A, a, tana daga hannunta mai lafiya cewa yi hakuri don Allah, hydar yace to idan baki so in miki shiga mota da sauri ta bude da hannunta mai lafiya ta shiga, a ranta tace to kuma miya kawo hydar anan? Kardai yayi ma sahib wulakanci tunda shine ya aikeshi yaga yayi dare bai koma ba ya biyoshi yayi mishi wulakanci, kuka samha ta farayi lallai batayiwa sahib adalci ba yana can ta barshi a hanya wayyo Allah sahib duk sai taji babu dadi, a ranta tace bawan Allah har cewa yayi ina zanje?


Hydar ya kalli samha sannan yace yarinya kinyi babban kuskure, a gaban hukuma kike cewa zaki kashe wani?  Waye waccan da kike cewa zaki kashe shi? Cikin kuka samha tace baka sanshi ba, parking hydar yayi abinda yake fesawa samha a ido yana hannunsa dan haka fesa mata yayi a cikin ido samha ta gigice gaba daya ta fita hayyacinta hydar yace zaki fada ko saina kara miki ne? hannu ta daga da sauri sannan ta fara cewa shine, hydar yace shine waye? Samha tace ya rabani da ahalina ta karasa maganar cikin wani irin yanayi wanda shi kanshi hydar bai san dalilin da yasa samha tayi hakan ba,


A hankali hydar ya fara tafiya da motar amma a zuciyarshi ya kasa samun natsuwa lallai wanna mutumin ko waye shi zai iya sawa a kashe samha, tunani dai barkatai hydar yakeyi kallon samha yayi dake ta faman murza ido saboda azabar abinda ya saka mata a ido sannan yace gida zaki koma ne? Samha tace A, a, hydar yace miyasa bazaki koma ba? Samha tace saboda nayi fada damai gidan hydar yace yanxun ina kika nufa? Cikin matsananciyar damuwa samha tace gudan sahib zanje,


Waya hydar ya dauka ya fara kiran number faruk bayan ya dauka hydar yace sahib ka samu mai gyaran hannu gani nan zan kawo maka wannan jakar yarinya sakarar nan wanda ta raina mutane, nace dai ka fita harkar yarinyar nan dai baza ka fita ba ko? idanuwan samha a rufe tace uhum? Hydar yace Ey samha tace gaka baban jaki bata karasa magana ya sake fesa mata abun ta fara wayyo Allahna wallahi ban yafe maka ba, murmushi hydar yayi sanan yace dama nace ki yafe min?


Faruk yana jin wannan karatun ya gane inda maganar ta nufa, dan haka yace ku iso lafiya, har suka isa gidan faruk hydar bai sake magana ba sai samha dake kuka,


Suna zuwa hydar ya fita da sauri tare da daga inda ya saka fuskar ya dauka, da sauri ya shiga farlon faruk sannan ya saka fuksar ya fito da gudu, mota ya dawo yana cewa wayyo Allahna swry my samha, waye yaji miki ciwo? Yayi magana cikin rarrashi, cikin shashshekar kuka samha tace abokin gaba ne, murmushi hydar yayi sannan yace kiyi hakuri dana tafi don Allah hydar ya kirani a lokacin ya turo ni nan gidan yace inzo inyi mishi wani aiki saida nazo nake fada mishi zanje in dauko ki shine ya tafi da kanshi ya dauko ki,


Amma waye _ABOKIN GABA_  samha tace yo waye fa banda hydar azzalimi mugu wallahi bazan taba yafewa hydar ba, murmushi hydar yayi sannan ya fita daga motar ya zagaya ya fiddo samha dan bata iya bude idanuwanta, janta yakeyi a hankali kamar makauniya ana mata jagora yanda take tafiyar tana laluben hanya da hannunta yasa hydar ya saketa da sauri, wayarshi ya fiddo ya fara daukarta hoto , bayan ya dauki hoton ya fara mata vidio yanda take tafiya, saida ya gama sannan ya mayar da wayarshi a aljihu ya dan juya yaga ko akwai mai kallonsa ajiyar zuciya yayi ganin babu kowa, faruk dake labe a window yana kallon hydar duk abinda yake lallai ya tausayawa hydar dan ya gama dilmiyar da kanshi, hannun samha hydar yaja da sauri suka shiga ciki,


Suna shiga dakin da faruk ya nunawa hydar samha zata kwana a dakin ya kaita da kanshi sannan ya bata hakuri wai saida safe za'a gyara mata hannunta, saida yayi mata maganganu masu dadi da sa natsuwa a zuciyar masoya sannan yayi mata saida safe, 


Kwanciya samha tayi shi kuma hydar yana fitowa yayi ma faruk saida safe, da gudu ya isa wurin mota, yana zuwa ya shiga ya yaja ya nufi gida, lokacin daya je gida 2:01am dan haka wanka yayi ya fito da alwalla yana fito bakar jallabiya ya zura ya haye abin sallah don gabatar da iba,


Bayan tafiyar su samha kawu yayi kururuwar sosai , yanda samha taci mishi mutunci yana so ya rama amma zuciyarshi tana san samha, kudirin da yayi akanta bazai taba yadda ya rusa ba murmushi yayi tare da addu'ar Allah yasa ya fita lafiya,


Hydar kuwa saida yayi asuba ya kwanta, yanaso yayi bacci amma kirikiri bacci ya gagareshi, hotunan samha suka fara dawo mishi a zuciyar shi, lokacin daya saka mata maganadison maciji da gudun da takeyi da lokacin daya riketa a jikinshi, ajiyar zuciyar data yi ya tsaya mishi a rai, murmushi yayi sannan ya gyara kwanciyarsa,


Ranar da yaje gidan su as hydar, tsaki yayi daya tono lokacin da takeyin magana da illo, hannunta daya ja da marin da yayi mata zaro idanuwan da tayi hydar yayi ajiyar zuciyar a bayyane yace _SAMHA_ a wurin training ya tuno,


_Waye yace kada in shiga? Nine nan, kallonshi tayi sannan tace kaifa hydar dan iska ne,_ murmushi hydar yayi hoton samha ya dawo mishi lokacin da yayi mata mugunta, dariya yayi sosai ya kallo yanda ta kideme gaba daya ta fita hayyacinta, dariya yakeyi sosai harsai daya tashi zaune, dan gajeran tsaki hydar yayi sannan yace bari inzo in ganki inja fada, tashi yayi yana cewa,


Gani nan zuwa gareki, dariya yayi sannan yace ta wani zazzaro idanuwa tana yin kyau sosai idan tayi haka, shafa kanshi yayi sannan yace baiwar Allah na kare mata hannu a banza, a daidai lokacin daya shige toilet wanka yayo ya fiti, yazo ya fara shiri shiga mai kyau da daukar hankali hydar yayi yasha gayu sosai yayi kyau gaskiya ya gyara gashin kansa bayan ya gama, Alale driver yayi ma waya cewa zai fita,


Yana gama wayar ya matsa jikin mirrow ya sake kallon kanshi murmushi yayi sannan yadanyi wasa da idon shi, yace wai samha tace idona irin idon mujiya ne, tanajin dadi idan ta kallesu shi yasa tafi yaba musu, wanka da turaruka masu kyau da tsada masu dadin kamshin ya shiga ambaliya dasu a jikinshi, gaskiya hydar dan gayun karshen zamani ne kuma Allah yayi wa hydar kyau, bayan ya gama ya fice daga dakin,


Yana fita shi kadai ake jira, dan haka cikin girmamawa aka bude mishi mota ya shige, suka kama hanya sai gidan faruk,


A waje sukayi parking saboda motocin dukansu basa shiga ciki, bayan sunyi parking hydar ya fita ya shiga gidan, a parlour ya samu samha zaune tana hawaye, ga mai gyaran hannu a gefe faruk ya kawo, da sallama ya shiga suka ansa ya samu wuri ya zauna, kowa ya gaishe shi amma banda samha dake ta aika mishi da sakon harara da kallo mai nuna da zakaci ubanka,


Gyara zama hydar yayi sannan yace kada a gyara hannu a bari sai bayan sati daya, faruk ya kalli hydar sannan yace miyasa sai bayan sati daya? Daure fuska hydar yayi sannan yace ai jarumarce tace haka saboda tana so ta karyamin hannu nima, dan kwanaki da dama da suka wuce na soketa da a wuka a tsautsayi cewa tayi bazata cire ba harsai ta kashe ni, dan haka nayi imani shima hannu saita karya min nawa zata bari ayi mata ɗori,


Idanuwa samha ta zaro sosai tana kallon hydar wani munafikin murmushi yayi ma samha wanda yasa taji tsikar jikinta gaba daya ta tashi yarrr hydar ya kalli mai gyaran hannu yace zaka iya tafiya,


Samha tace a, a malam kada ka tafi don Allah kamin, hydar yace idan kika sake magana kinsan sauran tabe baki samha tayi ta bata fuska kamar zatayi kuka, hydar yace jeka, tashi mai gyaran hannun yayi ya fita faruk yabi bayanshi,


Cike da tsiwa samha ta tashi daga inda take ta matsa kusa da hydar ta fara nunashi da yatsa wani irin kallo hydar yayi mata wanda yasa ja da baya taje ta zauna, hydar yace bari kiji in fada miki ni ba'a nunani da hannu sai ki kiyaye, 


Samha tayi shiru hydar ya dauki kafa daya ya dora saman daya sannan ya fiddo abinda yake yi mata mugunta dashi yana juyashi zuciyarshi cike da mugunta, kallon samha yayi ta saman ido sannan yace zo nan,




*Meelat Musa*

[05/04 4:45 pm] Washa: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊



                 *SO*

     *MUGUN WASA*



       *{ Love is a bad game }*




*JAMEELA MUSA* { meelat musa }




*Story, Writing & Editing*

                   *by*

         *Meelat Musa*



                  *SO*

      *MUGUN WASA*


*Dedicated to* 👇🏻

_Ramlat Abdulrahman real mai dambu_



*26-28*



Murguda baki samha tayi amma bata yi magana ba, hydar yace ke bakiji ina magana ne? Ba nace kizo kusa dani ba?


Dan gunguni samha tayi wanda hydar baisan abinda tace ba sannan ta kalle shi tayi mishi kallon kasa da sama ta turo baki tana kara harararsa,


Hydar yace Eye🤔? Lallai yarinya nunawa hydar kin girma, kwantar da kansa yayi saman kafadarshi sannan yace ke? Wai nine kike harara? Jinjina kansa yayi sannan yace zaki ci uwarki keda sahib din,


Samha tace badai uwar sahib ba, hydar yace sai uwar hydar ko? Samha tace oho, Jinjina kai hydar yayi sosai sannan yace idan na kori dan iska daga karkashina sai inga wanda kuma zakiyi ma rashin kunya,


Dariya samha tayi har beauty point nata ya fito, sannan ta kalli hydar tace dan Allah korarshi yi maza maza wai mi kake jirane har yanxun banji ka koreshi ba? Tana maganar tana nuna hydar da hannu,


Samha taci gaba da cewa idan ka koreshi sai akace maka ya daina rayuwa ne? Ko kuwa zama dakai shine zaisa ya zama rayayye? Ko kuma ya kasance a mace? Ko ka manta cewa arziki da talauci duk na Allah samu da rashi ma nasa ne, dan gajeran tsaki tayi sannan tace da Allah dubeshi da wani idonshi can kamar na sadaka,


Murmushi hydar yayi sannan yayi wasa da idonshi  yanda yayi abun yayi mishi kyau sosai kuma ya soki zuciyar samha, hydar yace yarinya kwalelenki har abada wannan idon yafi karfinki, bake ba ahalinku gaba daya hydar yafi karfinsu,


Tsaki samha tayi sannan tace Allah ya ansa addu'ar ka danni ko sadakar mai irin sunanka aka bani bana so bare kuma har inyi fatan kasancewa dakai a inuwa daya, dubeka da Allah ta nunashi da hannu sama da kasa sannan taci gaba da cewa waikai ji kake kai waye?


Hydar yace harma sai kinyi tambaya? Bayan gani a gabanki, tsaki samha tayi sannan tace na lura dakai ka cika jinkai bakaji abinda hausawa suka ce ba? _jaki shike da girman kai matsiyaci kuma shike da kankanba_ sai wani kankamba kakeyi wai kai hydar mtsww,


Da sauri hydar yayi kan samha kafin ya kai mata duka faruk ya shigo a lokacin har hydar ya rike hannun samha mai ciwo yana murza shi cikin keta da zalinki, faruk da sauri ya rike hydar saboda ihun sa samha takeyi, yana cewa haba don Allah wai miye haka?


Dunkule hannu hydar yayi tare da kaiwa faruk wani irin gigitaccen naushi da sauri faruk ya rike wurin ya duke kasa, ganin faruk ya duke yana dafe inda hydar yayi mishi duka samha ta zaro idanuwa sosai tana cewa haba haba yi hakuri don girman Allah kada kamin duka kayi hakuri dan Allah ka sake min hannuna wallahi akwai zafi sosai nikam bana fada ma, kayi hakuri kasa a gyara min hannuna don Allah dan zan fita anjima,


Hydar yace bake kinajin baki da kunya ba? Da sauri samha tace kayi hakuri insha Allah ina da kunya, hydar yace to anki a gyara hannun sai yayi sati daya ba kince ke jaruma ba ne?


Murmushi samha tayi sannan tace Allah ya baka hakuri maganin tauri kadai nasha shi yasa kaga na kwana da wuka a jikina, amma bansha maganin ciwon karaya ba, don Allah ka sakemin hannu hydar,


Tsaki yayi sannan ya saki hannu ya fita, faruk ya tashi yabi bayanshi, ba tare da hydar kalli faruk ba yace kira mai gyaran hannu a gyara ma muguwa, dariya faruk yayi amma baiyi magana ba,


Samha tayi murje murje wurin gyaran hannu dan yayi tsami saboda ya kwana samha tayi "yan hawayenta, bayan an gama gyaran hannun faruk suka fita dashi da mai gyaran,


Faruk suna fita samha ta dauki wayarta ta kira sahib, bayan ya dauka ta gaishe shi, sannan ta kara da cewa sai in kwana da ciwo amma ko kazo ka ganni? Sahib yace swry samha bana nan ne hydar ya aikeni amma insha Allah idan na dawo zanzo, samha tace to ka dawo lafiya, hydar yace amin insha Allah dana dawo zanzo, samha tace anjima zan fita,


Hydar yace ina zakije? Sassauta murya samha tayi cikin yanayin damuwa tace zanje wurin wasa ne, hydar yace wane irin wasa kuma? Samha tace wasan caca mana kawu yace idan ina san sanin labarin ahalina sai naje nayi wasan caca inji kawu kuma naci sannan zai fadamin, dan gajeran tsaki hydar yayi sannan yace gaskiya kada kije, kada ya nemo ahalin naki mana, 


Cikin yanayin sahib ya tausaya mata samha tace gidanmu fa? A halina? Murmushi hydar yayi sannan yace gidanku gashi kina cikin sa, ahalinki kuma ai nine ahalinki samha ko bakyasan _SAHIB_ ne? Samha tace ina sanka sosai, murmushi hydar yayi da gefen bakin sa sannan yace to kiyi hakuri gani nan zuwa yanxun insha Allah kinji, samha tace to sai kazo, sallama sukayi sannan kowa ya kashe wayarsa,


Hydar kasuwa yasa akaje aka siyo ma samha kayan da zata rika canjawa kaya masu yawan gaske aka jibgo mata, duk abinda zata bukata hydar yasa aka siyowa samha sannan yasa faruk yakai mata,


Bayan ankai kaya samha tayi mamakin ganin kayan nan, tasan sahib baida karfin siyen kwatankwacin wannan kayan, amma faruk yace mata wai sahib ne ya roki hydar shine ya siya mata,


Haka samha ta tashi taje tayi wanka da hannu daya ta saka kayan da aka kawo mata, tayi kyau sosai dan sahib yace mata yana san mace mai tsafta da gayu tana kokarin tayi dan duk abinda zatayi sahib yaji dadi tana kamantawa, bayan ta gama faruk ya shigo mata da abinci shima sako daga hydar ne, amma samha ta kifa kanta kasa tace bazataci abincin ba anyi juyin duniya tace bazataci ba, faruk ya tambayeta dalili  tace ita bazata ci abincin hydar ba kila ma yaje ya zuba mata guba a ciki taci ta mutu,


Da faruk ya fadawa hydar dariya yayi sannan yace barta zanzo anjima ina meeting yanxun, faruk yace to, yinin ranar haka samha ta yini da yunwa, taki yarda taci komai ko ruwa bata sha ba,


Lokacin da hydar yazo as sahib abincin daya aiko dashi shine ya dauka, a gaban samha ya ajiye sannan yace tashi kici abinci, bata fuska samha tayi kamar zatayi kuka sannan tace nifa bana cin abincin hydar, sahib yace nine nace kici, samha tace idan na mutu fa? Murmushi hydar yayi sannan yace bazaki mutu ba ki yadda dani ki ci, murmushi samha tayi sannan ta dauki abinci ta fara ci, hydar yana zaune a gefenta yana kallonta, gaskiya samha tayi mishi sosai amma matsalarta daya rashin kunya, tsaki yayi a bayyane sannan yayi magana a zuciyarshi cewa lallai fa ta gano ni yarinyar nan akwai bala'i, dan na lura bata kaunata kwata kwata,


Haka rayuwar samha taci gaba da tafiya a gidan faruk, da ita da sahib da hydar zuwa wannan lokaci samha ta gama yadda zuciyarta tana tsananin san sahib sosai, saboda sahib ya iya kula da mace, kuma yana tattalinta sosai shi yasa zuciyarta take matsanancin san sahib kuma take addu'a Allah ya mallaka mata shi a matsayin mijin aurenta, lallai duk wanda yayi gigin rabata dashi tou pha ko waye tana iya yanka shi da wuka gida biyu,


Dan tuni zuciyar samha ta gama imani da sahib, dan so take mishi bana wasa ba, sahib ya iya soyayya sosai kuma yana kulawa da ita sosai, kuma gashi dan gaye ta ko ina dai tana san sahib,


Hydar ne tsaye a tsakiyar katon farlonshi wanda aka kayatashi da kattin kujeri na alfarma farlon dai ya gama hadewa sosai dan idan kana cikinsa zaka rantse cewa a kasashen waje kake, kuma tsarin farlon yafi kama da a kirashi da tsarin farlon idiyawa,


A gefe daya kuma faruk ne ya lutse cikin lutsestiyar daya daga cikin gujerin farlon, yana kallon hydar da yake dariya ga kofin coffie a hannunsa dayan hannun kuma wata takarda rike a hannun,


Tafiya hydar yayi harya isa wurin da faruk yake zaune sannan ya zauna kusa da faruk yace jiya ma mikakece? Faruk yayi shiru, murmushi hydar yayi sannan yace kake cewa bana iya rabuwa da samha ko? Faruk yace Eh, hydar yace wai kace na kamu da santa a zuciyata ko? Faruk ya sake cewa Ey, hydar yace to karya ne, ansa nan ka gani, ya mikawa faruk takardar ansa faruk yayi a daidai lokacin da hydar yakai kofin hannusa a bakinsa,


Dubawa faruk yayi sannan ya kalli hydar, murmushi hydar yayi sannan yace ya ka gani? Faruk ya jinjina kansa, hydar yace yau nawa ga wata ne? Faruk ya fadawa hydar , hydar yace ya ka gani a jikin rubutun nawa? Faruk yace yayi daidai da kwanakin watan yau,


Gyara zama hydar yayi sannan yadan daure fuskarshi yace yau shine kwanakin tarayyata mu da samha dana iba, dan haka yau kwanaki suncika cifcif saboda haka a daidai inda muka hadu a daidai wurin zan rusa ginin soyayya dana dasa a cikin zuciya banza, saika fara lissafin kwanakin mutuwarta daga yau,


Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un abinda faruk ya fada kenan, sannan yace hydar kaji tsoron Allah kada kayi haka hakika idan har kayi haka ka cuci rayuwar samha, faruk yaci gaba da cewa wallahi danayi maka maganarta a jiya banyi dan in rabaka da ita ba kawai nayi ne saboda nishadi shi yasa nace nasan yanxun baza ka iya rabuwa da samha ba amma Allah yaga zuciyana badan ka rabu da ita na fadi hakan ba, kayi hakuri kada ka rabu da samha ta dalilin maganar da nayi dan bana so inyi dakon zunibin da kake kokarin azawa akan,


Hydar bai kalli inda faruk yake ba kuma baiyi magana ba, ya dauki wayarsa ya fara kiran wayar samha, a daidai lokacin ta fito daga wanka da saurin ta, ta isa inda wayarta take, murmushi tayi zuciyarta cike da farin cikin ganin kiran sahib, dan haka samha tana dauka ta fara kwantar da murya tana waya da wani sashe na zuciyarta wato sahib,


Hydar yace hajiyata ya kike? Samha tace lafiya qalau ya kake? Hydar qalau, shiru na wani lokaci hydar ya yanke shirun ta hanyar cewa samha anjima ki sameni wurin training, cike da zakuwa samha tace to ai naga lokacin tafiyarka yayi ko? Sahib yace Ey, samha tace to sai nazo hydar yace yawwa sannan ya kashe wayarsa,


Tashi yayi daga saman kujerar yabi hanyar benen da zata sadashi da bedroom nashi faruk yana bin bayansa da gudu cewa hydar dan darajar iyayenka kada kacewa samha da wasa kake santa kayi hakuri don Allah, ka tausaywa zuciyarta,


Idan bango yayi magana to hydar yayi magana da faruk, har bedroom faruk yabi hydar amma kafin ya shiga har hydar ya shige toile ya rufe, faruk baida yanda zaiyi dole ya hakura ya dawo farlo yana jiran fitowar sa,


Saida hydar ya gama shirinsa tsaf ya fito cikin kayan training wanda sukayi matukar karbar jikinsa sunyi mishi kyau sosai, tun kafin ya iso farlo kamshi turarensa yayo gaba, faruk yana jin tahowar hydar ya tashi ya tareshi tun kafin ya iso inda take zaune,


Faruk ya kalli hydar sannan yace sahib, hydar yace yadai? Faruk yace ba komai, ba tare da hydar ya sake magana ba, ya fice daga farlon faruk yabi bayansa da sauri,


Tunda samha taje wurin gabanta yake faduwa bata san dalilin daya sa takejin faduwar gaba ba, haka nan kawai taji zuciyarta bata natsu da wurin ba, tuni zuciyarta ta farayi mata sake sake, wani bangare na zuciyarta ya fada mata wani abu da sauri samha ta mike tare da cewa Allah ya kyauta a daidai lokacin da hydar ya iso wurin,


Samha na hango sahib tayi wurin da sauri tana kara fadada murmushinta, lokacin da ta isa wurin zatayi ma sahib magana sai taga ya dauke kanshi ya bada rai kamar bai taba ganin samha ba,


Murmushi karfin hali samha tayi sannan ta kalli jikinta tare da sinsinawa wai ko batayi kyau ba ko kuma bata saka turare ba shi yasa sahib ya dauke kansa? Wata zuciyar tace ba haka bane, ajiyar zuciya samha tayi sannan tabi bayan hydar cikin sauri a daidai lokacin suna kokarin shiga holl din,


Samha tace kaiiiiiiiiiiiiiii ta ruga da gudu tayi wurinsu, jin maganar da samha tayi cikin karaji shine dalilin daya sa suka tsaya tare da juyowa baki dayansu, da gudu samha ta iso wurin kusa da sahib ta matsa sosai kamar zata shige cikin jikinsa, sannan tace sahib miye? Kace inzo nan kuma na zo shine zaka wulakantani a idon duniya mi nayi maka? Idan wani abu nayi maka ka fadamin sai in baka hakuri amma bazan iya dauka wannan hukuncin ba kana gani na kana basarwa,


Murmushi sahib yayi sannan ya saki wayar hannunshi da sauri samha ta duka da niyar dauko wayar shima dukawa yayi dan daukar wayar amma samha ta dauki wayar sannan suka taso a tare samha tace yi hakuri ban gani ba, a tunaninta itace ta fadar da wayar,


Ansar wayar hydar yayi sannan yace kin tuna ranar da muka fara haduwa? Murmushi samha tayi sannan tace na tuna a daidai nan ne, hydar yace to kuma anan zamu rabu, cikin rashin fahimtar abinda yake nufi tace ban gane ba, sahib yace gaskiya samha kiyi hakuri nidai gaskiya dama ba sanki nakeyi ba da wasa nake yi?


Idanuwa samha ta zaro sosai sannan ta kara matsawa kusa da hydar tace da wasa ne ko gaske kalamanka? Hydar yace ba wasa nake ba gaskiya na fada miki kiyi hakuri, murmushi samha tayi mai cin zuciya cikin sassanyar murya tace haba sahib? A ina ka taba ganin anyi wasa da zuciya,? Shin baka san zuciya itace mutum ba? Mi nayi maka wanda har yasa kake kokarin ganin ka hallakani ta hanyar horani da wasan so? 


Tabe baki yayi sannan yace nima ban sani ba, kawai dai an taba fadamin cewa wai *SO MUGUN WASA* ne shi yasa na gwada in gani wai maganar gaske ne? Cikin rawar murya samha tace amma ka rasa a wanda zaka gwada sai akaina? Hydar yace Eh saboda maganar daga bakinki ta fito, murmushi hydar yayi sannan yace da gaske so mugun wasa ne samha? Wato maganar da samha ta taba fada mishi kenan ya fada, yana maganar yana dariya mai cin rai, dakel samha tace sahib tsakaninka da Allah baka so na? Tabe baki yayi tare da daga girarensa gaba daya sannan yace gaskiya bana sanki bana sanki bana sanki,


Murmushi samha tayi sannan tace ikon Allah sahib yau kaine kalmar kiyayya take fitowa daga bakinka, ni ? Ta nuna kanta da hannu sannan tace ni kake cewa baka so na? Dan bude idanuwanshi yayi sannan yace shakka babu kuma da nace miki zan aureki gaskiya wasa ne 🤷🏻‍♂ amma yau kam na fada miki tsurar gaskiyar abinda yake cikin zuciyata,


A hankali samha ta dago idonta tana kallon sahib kakkyawan murmushi daya tayi wanda hydar yajishi har cikin zuciyar sa,  sannan samha tace _ni ina sanka, ina sanka, ina sanka_,lokaci guda taji wani hada hadari ya wuce ta gaban idonta, ji tayi duniyar tana juyawa da ita sosai,  murmushi dauke a fuskarta a hankali ta dafe daidai zuciyarta sannan ta durkusa kasa a hankali saman kafafuwan hydar ta dora fuskarta tana zubar da hawaye masu bala'in zafi daga haka samha bata sake sanin abinda duniya take ciki ba,


Jin samha tana hawaye yasa hydar yayi dariya sannan yace ashe dai baki kai jaruma ba, tunda har kika bari zuciyarki tafi karfinki, dukawa yayi ya dago samha da niyar ya fada mata shine hydar ya cire fuskar daya dora idanma zuciyarta zatayi bindiga tayi babu abinda ya dameshi, amma sai yaji samha bata lumfashi,


Idanuwa hydar ya zaro ya fara girgiza samha, ke ke keee miye haka? Baki san wasa ba? Samha bude idonki mana bude, bude don Allah bude idonki ki ganni ina sanka kada ki mutu wai miye haka yana maganar ya jijjjiga samha, jin hydar yana magana kamar ya haukace yasa hankalin su faruk ya dawo wurin gaba daya yaran hydar sukayo wurin da gudu ganin hydar ya fadi kasa yana wani irin ihu mai tada hankali,



Da gudu faruk yayo kanshi yana rikeshi amma hydar sai wani zukewa yake yana kara sulalewa kasa, inda samha take kwance yake kallo yana cewa kada ki mutu fa, yana daga hannunshi kamar zai jawota amma baya iyawa tun yana ganin samha sama sama har hotonta ya dauke daga idonshi, wani irin ihu hydar yayi wanda gaba daya holl din ya ansa tare da kiran sunan samha cikin wata irin murya daga haka hydar bai sake motsi ba,


Kawu ne ya shigo cikin holl din da gudu a sulale ya taho suuuuuuu, saboda ya shigo wurin da gudu kuma sulbi ke kawai sosai, inda samha take kwance kawu yayi turjiya tare da sakin wani irin ihu wuka ya daga rigarsa ya zaro tare da cewa ina hydar din yake dan kutumar ubansa?


Kafin kawu ya rufe bakinsa tuni anyi mashi lullusar futar hayyaci gajagaja akayi wa kawu sannan yaran hydar suka fara tambayarshi waye yake zagi dan kutumar ubansa? Sai yanxun hankalin kawu ya dawo jikinsa ya tsaya yana kallonsu daya bayan daya, lallai idan dai hydar nasir hamza ne babu ma abinda zai tsaya ya saurara wurin samha, to badaishi bane,


Bakaji ana maka magana dan uwarka,? Kawu yayi shiru, faruk yakai mishi halbi tare da cewa idiot, daukar hydar su faruk sukayi a lokacin har Alale ya matso da mota a bakin kofar holl din suka fita dashi a mota suka saka shi sannan sukayo ciki da gudu dan daukar samha amma suka nemi samha ko kasa suka rasa,


Cikin tashin hankali faruk yace kai maza maza kuyi da hanzari ku nemo wannan dan iskan tsohon lallai shine ya dauki samha, haka suka barbazu suna neman samha babu samha babu kawu, cikin tashin hankali faruk yace kai lallai ku nemo samha idan ba haka ba hydar zaiyi tashin hankali idan har samha tayi mishi nisa ku nemota ya karasa maganar cikin daga murya sosai,


Fitarsu faruk kawu ya dauki samha dashi da wata mace suka fice daga holl din ta baya inda suka ajiye motarsu suka sakata suka gudu,


Ganin baza'a ga samha ba yasa faruk hakura suka tafi da hydar asibiti,  taimakon gaggawa aka bawa hydar dan ganin an farfado dashi amma a banza, haka likitoci suka taru kan hydar amma duk abinda suke tunanin zai farko da hydar dai anyi amma har yanxun yana cikin yanayin da aka kawoshi,


Bayan kawu sunkai inda zasuje aka fito da samha kamar gawa haka suka shiga da ita cikin dakin da suka ware da ajiyeta, bayan an ajiye samha suka dawo tsakar gidan gaba dayansu suka fara tattaunawa,


Kowa da abinda yake fadi akan samha wasu na cewa gaskiya saida a kasheta wannan shine kadai mafita, yayin da wasu suke cewa ba kasheta za'ayi ba mu haukatar da banza, wasu kuma cewa suke ku bata m card din idan ta gani abinda yake ciki danginta bazasu bada kudin ba sai sunga samha idan aka anshi abinda mahifinta ya bari lallai sai mu sheke banza, kawu kuma cewa yayi gaskiya nidai kada ku kashe samha ina santa kuma aurenta zanyi, wata mace kuma cewa tayi wallahi babu dalilin da yarinyar nan zata rayu sai ta binneta da ranta dan ajaline yakaita ta fada soyayya da hydar,


Gaba daya wurin ya rikice kowa da abinda yake fada akan samha, sai yanxun hankalin kawu ya dawo jikinshi wane ganganci ma yasa ya yadda aka hada kai dashi aka dauko samha, masu san samha ta kasance a raye ta basu abinda suke so sune suka bada shawara a kawo likita ya dubata sannan asan abinyi,



Kwararran likita aka dauko dan duba samha, bayan likita yayi "yan gwaje gwajensa ya rubutawa samha magunguna akaje aka siyo da karin ruwa sannan yace a kula da ita sosai idan ba haka ba lallai zata iya samun babbar matsala a zuciyarta dan idan ba'ayi hankali ba sai anyi mata dashin zuciya, likita yaja musu kunne sosai dan haka yace su kula kyau,


Kwanan hydar biyu a asibiti amma babu wani abu daya canja dan haka aka daukeshi akayi kasar waje dan ceton rayuwarsa,


Lokacin da samha ta farfadowa maganar sahib ne na karshe yayi tayi mata yawo a kwakwalwa, _ban sanki, bana sanki, bana sanki, bana sanki_ wani irin ihu samha tayi wanda ya farkar da wanda aka saka suyi gadinta daga bacci, cikin kuka samha ta fara cewa,


_Haba sahib ka rufa min asiri mi nayi maka zakace baka so na? Bayan kasan da soyayyar ka nake kwana da ita nake tashi ka taimakeni ka sakani a ranka ko a bayan zuciyarka ne ka ajiyeni ka tausayamin bayan ka saba furta min kalaman soyayya miyasa kalmar kiyayya zata fito daga bakinka?_


_ka saba da furta min soyayya dana duba a fuskarka da labarin zuciyarka tawa ta yadda banaso ka barni, idan ka ƙini zansha wuya daka furta kalmar kiyayya saida zuciyata ta bugu, bazan so ba idan ka guji ni zan mutu rayuwata bata da wani amfani ta karasa maganar tana kuka mai jijjjiga jiki_


Haka tayi ta kuka tana surutai kamar wata warwararra, tsaki sukayi sannan suka koma baccinsu,,


Lokacin da hydar ya farfado wani irin kuka ya farayi danshi a tunaninsa samha ta mutu, faruk ya gani zaune saman kujera kusa da gadonsa ya dora kanshi saman gadon yana bacci, murmushin karfin hali hydar yayi sannan ya dafe daidai zuciyarsa dake kokarin fitowa daga mazauninta,

a hankali yayi lumfashi kamar ransa zai fita, 


Murmushin da samha tayi yake kallo, sannan ya tuno maganarta data ce mishi _ni ina sanka, ina sanka, ina sanka_ ajiyar zuciya ya sauke dakel sannan yace _innalillahi wa'inna ilaihir raji'un_ lallai na dabka babban hauka tunda nake a duniya ban tabajin labarin babban mahauci kamarni ba, hawaye sukaci gaba da safa wal marwa a fuskar hydar, sai yanxun yake tambayar zuciyarsa ce,


_Haka nayi dake? Wannan wane irin haukace? Ke baki san wasan ba? Kafin inyi hakan saida na gargade ki cewa babu samha amma a cikinki bama samha ba mata duka babu su amma shine saboda kangara iri taki kika koyawa kanki santa to yanxun ta mutu bata fadin duniyar nan fadamin cewa ni zaman mi zanyi a duniya? Ya karasa maganar yana wani irin kuka wanda ya farkar da faruk daga bacci_


Hydar yaci gaba da cewa _samha ke nayi wa tanadin zama tare dani kuma dake na tsara rayuwata ke nayi alkawarin aure a matsayin mata ta, dan kece kadai zaki kwantar min da hankali, banda kowa a duniya saike miyasa zaki min haka? Kece rabin jikina ke wani sashe ne na zuciyata na kasa boye sanki cikin raina saida dai ya fito fili, yabonki idan akayi a gabana sai naji dadi ganinki cikin farin ciki shine yake sa inji dadi a raina soyayya ta gaskiya data karya akwai banbanci ina sanki samha da gaske_


Da sauri faruk ya rike hydar dake wani irin tari mai tada hankali jini faruk ya gani yana fitowa daga bakin hydar a gigice faruk yace hydar kwantar da hankalinka samha tana raye, murmushi hydar yayi sannan yace rayuwata bata da wani amfanin da zatayi a wurin samha, kada ka manta babu wanda samha ta tsana duk duniya irin hydar idan har na rayu zanga masifar data fi wannan, kaga bansa samha tayi aman zuciyarta ba ni tawa zuciyarta zata fito,


Kara dafe zuciyarshi hydar yayi sosai sannan ya kalli faruk murmushi hydar yayi sannan yace ka fadawa samha, hydar yana santa, cikin tausayawa faruk yace hydar bazaka mutu ba kayi hakuri don Allah ka daina saka damuwa kayi hakuri idan har ka warke wallahi sai ka auri samha, wani irin murmushi hydar yayi sannan ya dagawa faruk hannun dama haggunsa kuma yana bisa zuciyarsa yana ci gaba da tari mai bada tsoro da gudu faruk ya fita babu dadewa ya dawo da likitoci,




*Meelat Musa ce*

[05/04 4:45 pm] Washa: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊



                 *SO*

     *MUGUN WASA*



       *{ Love is a bad game }*




*JAMEELA MUSA* { meelat musa }




*Story, Writing & Editing*

                   *by*

         *Meelat Musa*



                  *SO*

      *MUGUN WASA*



*Dedicated to* 👇🏻

_Ramlat Abdulrahman real mai dambu_



*29-31*



Faruk banda kuka babu abinda yakeyi tunanin hydar ya farayi ranar da sukaje Office dinshi shida samha,


Bayan yaje ya saka samha a mota ya dawo gaban faruk ya tsaya donyi mishi bankwana, abinda faruk yacewa hydar shine,


_Gaskiya hydar kayi ganganci kuma ka cuci rayuwarka ka kashe kanka da kanka, nidai shawarar da nake baka hydar ka fita harkar yarinyar can, dan duk ranar data gane kaine hydar lallai fa akwai matsala tunda kai kasan bata sanka, kuma na lura kai ka fada san samha_


Faruk ya goge hawayen idonsa sannan ya tuno murmushin da hydar yayi masa ya bashi amsa cewa,


_Karyane ban wani mutu ba gani ina rayuwata ina nunfashi na ina kallonka ka saka shet da wando kayi aski saisaye kuma har kace na kashe kaina waye yace maka matacce yana magana ne?_


_Wane dan iska yace maka ina santa ne ma bare har in kashe kaina saboda itane? Bana santa, bana santa, bana santa, na tsaneta yarinyar can kwanan nan zan sallameta ta tafi jinyar zuciyarta_


Ajiyar zuciya faruk yayi sannan ya tuno ansa daya bawa hydar, abinda yacewa hydar a lokacin shine,


_Lallai zadai ku tafi jinyar zuciya tare_


Yana cikin tunanin ne yaji an taba shi, da sauri ya dago kanshi dan ganin waye ya tabashi? doctor da yake kula da hydar ne ya gani tsaye dan haka da sauri faruk ya mike yana cewa doctor yamai jikin ne?


Murmishi dauke a fuskar doctor ya dafa kafadar faruk sannan yace mai jiki da sauki, murmushi faruk yayi tare da cewa Allah ya bashi lafiya doctor ya ansa da amin,


Samha na zaune ta zabga tagumi tunani barkatai a zuciyarta, banda tunanin sahib babu abinda takeyi, lallai tana san sahib amma miyasa kalma mafi muni ta fito daga bakinshi har ya fada mata itane?


Lallai babu munafikin da yayi wannan hadin fitanar ba kowa bane sai hydar, ajiyar zuciya samha tayi tare da yin magana da karfi cewa saina kasheka da sauri samha ta mike wani kwalbar giya data gani a gefenta shi ta dauka tayo waje da gudu saina kashe itace kalmar da take fada a bakinta,


Ku rike min banza karku bari ta fita mana "yan iska kattin banza baku ajiye komai ba saida kuci kuyi bacci, da sauri suka tashi sukayi kan samha suna rikonta amma a banza dan samha gaba daya ta girgirjesu gurinta kawai taga hydar ta kashe shi,


Rikon samha akeyi amma wani balagaggen karfi takeji yanda take barar da musu rikonta ne kowa abin yake bashi mamaki, dan haka da sauri budurwar hydar ta koma mota ta dauko koken tana zuwa ta shakawa samha, lokaci guda samha ta dauke diff, sannan tace ku mayar min da banza,


Haka aka dauki samha aka mayar da ita inda ake ajiyeta, ajiyar zuciya farida tayi sannan ta dauki wayarta ta fara kiran Asma'u , bayan Asma'u ta dauka farida tace mata kinga mai gonar motocin ne? Wai hydar shine cegadu mai gonar motoci haka "yan mata suke kiranshi da mai gonar moto,


Asma'u tace ban ganshi ba, amma bisa binciken da nayi ance min baya nigeria, farida tace to gadai yar iskar yarinyar nan na kama banza, Asma'u tace to kada ki damu sai nazo, farida tace to, sallama sukayi da juna sannan kowa ya kashe wayarsa,


Da farida ta tashi tafiya saida ta sake jawa masu gadin samha kunne sosai sannan ta tafi, haka suka saka ido sosai akan samha duk lokacin da farida tazo sai tasa anyi wa samha lullusar futar hayyaci sannan ace mata ina hydar?


Magana daya samha  kecewa shine itama neman hydar din takeyi ta kashe dan iska dan duk duniya babu jakan data tsana irin hydar kallon farida samha tayi sannan tace kiyi waya da hydar din kice mishi samha tace saita ga bayanshi,


Kallon kasa da sama samha tayiwa farida sannan tace amma kinji kunya wallahi duk saboda wannan jakin mai idanuwan mujiya zakizo kisa a kawoni nan ayi ta azabtar dani? Mtsww da Allah ni bani hanya in wuce,


Farida tace bari in kira Alale sannan, wato driver hydar bayan ya dauka suka gaisa farida tace Alale ga yarinyar nan a gabana shin itace samhar da takeyin soyayya da hydar? Murmushi yayi sannan yace ai samha bata san mai gida kowa ya sani kuma kema kinsan hakan, itama samha tasan bata san hydar amma tana san sahib,


Kallon samha farida tayi sannan tace waye sahib? Samha tace ki tambayi wanda kike magana dashi mana, hello Alale waye sahib ne? Alale yace yaron hydar ne, mi yakeyi wa hydar bayan nasan duka yaransa,


Alale yace kawai ake ake yakeyi wa hydar ne, dariya farida tayi sannan ta kashe waya tare da cewa shegiya Allah ya rufa miki asiri da ance min kece kike soyayya dashi yau dasai na binne ki da ranki, tana fadin haka tayi gaba abin ta,


Alale bayan ya gama waya da farida saida ya kira faruk ya fada mishi yanda sukayi da farida, faruk yace to yanxun ina ita samhar takene? Alale yace ban sani ba, faruk yace maza maza ka bugawa farida kace kayi waya da hydar yace ta tafi da samha gidanta zaizo sai suyi magana, Alale yace to, bayan sun gama waya da faruk ya kira farida yayi mata bayani,


Komawa farida tayi amma fur aka hanata tafiya da samha, saboda akwai sauran da suke jiran kawu ya kawo m card sannan su sallameta, farida tayi alkawari cewa duk lokacin da suka bukaci samha suyi mata magana tana tare da ita domin hydar zaizo ne,


Dakel dai aka bari ta tafi da samha tare da sharadi mai girma, bayan sunje gidan farida faruk da kanshi ya kira farida bayan sun gaisa ne yace wurin Alale ya anshi number nata,


Faruk yace hydar yace a fada miki cewa kada ki kuskura samha tayi miki nisa dan idan ya dawo zai dauki hukunci mai muni akanta saboda karyar da takeyi cewa hydar yana santa, dan haka ki bata kulawa sosai data bace hydar yace soyayyarki ta rushe dan yasan idan har baki tsare samha ba lallai bazaki iya kular masa da zuciyarsa ba, farida tace babu damuwa,


Faruk yacewa farida ta bashi samha, bayan an bawa samha waya tanajin maganar faruk tace faruk ina sahib yake? Ajiyar zuciya faruk yayi sannan yace bara in baki shi, murmushi samha tayi sannan tace yawwa,


Da sauri faruk ya mikawa hydar waya cewa samha zatayi magana dashi, murmushi hydar yayi sannan ya dafe daidai zuciyarsa yana kallon faruk, faruk ya sakawa hydar wayar a kunnen sa a hankali hydar yace samha,


Dariya samha tayi sosai sannan tace sahib ya kake? Ina fatan dai kana lafiya, kayi hakuri don Allah idan nayi maka wani abu nasan babu wanda ya hada munafuncin nan sai hydar kada ka wani samu damuwa ni dakaina zan kashe banza, yanxun haka ma ina nan gidan wata jakar budurwarsa wai zaizo yayi min duka ni kuma inanan na samu wuka yana zuwa zan cakawa banza ya mutu kaga daga nan sai mu gudu abinmu sai ka tayani gano ahalina daga nan sai muyi aurenmu shikenan mun kauda matsala ko ya kace? Duk maganar nan da samha takeyi babu inda ta lumfasa haka tayi ta surutu kamar ansa karatun dicshinari ance kada ta huta,


Hawaye ya gangaro daga idon hydar a hankali ya daga idonsa sannan ya kalli faruk, murmushi faruk yayi mishi sannan ya matsa kusa dashi ya dafa kafadarshi, amma baiyi magana ba,


Samha tace kayi shiru ko har yanxun kanajin tsoron hydar ne? Murmushi hydar yayi sannan yace banajin tsoronsa, amma idan har kina san sahib da gaskiya ki janye kudirin cakawa hydar wuka kada ki manta samha hydar shine gatana kuma kema shine sinadarin rayuwarki,


Tuf inji samha sannan tace maza sahib ka tofar da bakin yawu, Allah ya sawake Allah ya tsareni hydar ya zama sinadarin rayuwata, ba gara in mutu in huta ba, mi kakeji hydar yana dashi? Ka rabu da hydar nayi alkawari zan gina mana rayuwa mai inganci kace kana sona kace bakaine ka fadamin kalmar baka so na ba, fadamin inji dadi ko zan samu yau inyi bacci mai dadi sahib,


Da sauri hydar ya kara danne daidai zuciyarsa sannan yace ma samha ina sanki, ina sanki, ina sanki, kuma nayi alkawarin aurenki samha ina fatan zaki zama marufar asiri na, murmushi samha tayi sannan tace wallahi kuwa kuma duk wanda yayi gigin rabani dakai saina kashe banza, nima ina sanka sosai amma don Allah kada ka bari a sake rabamu sahib,


Goge hawaye idonshi hydar yayi sannan yace kalmar kashe wani samha ta fita daga bakinki, dole ki koyawa zuciyarki san hydar idan har kina san ganina a raye idan kuwa ba haka ba kawai zan mutu dan rayuwata bata da wani amfani, tsaki samha tayi sannan tace A, a, ka taba ganin an hada gaskiya da karya? Ko ka taba ganin wanda yace zunibi da lada daya ne? Yanda bana san zunibi haka na tsani rayuwar hydar na tsaneshi bana sansa, yanda nake san tarin lada haka nake sanka sahib sosai kuma nake fatan kasancewa dakai a matsayin mijina,


A hankali hydar ya gyara kwanciyarsa sannan yace to na gode sosai ki zama lafiya, zansa Alale ya kawo miki waya insha Allah, murmushi samha tayi sannan tace na gode, hydar yace yawwa sannan ya kashe wayarsa,


Bayan hydar ya kashe wayar ya kalli faruk sosai sannan yace lallai ina da babban aiki a gabana, murmushi faruk yayi yana so ya gayawa hydar magana amma yana tausayawa hydar a halin da yake dan haka sai yace ka kwantar da hankalinka komai zaizo da sauki insha Allah,


Murmushin karfin hali hydar yayi har yanxun hannunsa yana daidai saitin zuciyarsa yace haba faruk wane komai zaizo da sauki? Ni shikenan haka zanyi ta zama a gaban samha a matsayin sahib? Haba ai kaima kasan wannan ba mafita bane,


Faruk dai haka yayi ta kwantarwa hydar da halinki tare da kara mishi kwarin gwiwa sosai a akan zai samu nasara wurin samha,


Samha kuwa bayan ta gama waya da sahib sai murna takeyi tana jin dadi, dan yau tana cikin farin ciki yanxun ta kauda babbar matsalarta da sahib saura matsalarta da kawu da kuma maganar ahalinta,


Alale ya kawowa samha waya mai kyau da tsada kamar yanda sahib yayi mata alkawari babban farin ciki samha tayi sosai sannan Alale ya sakawa samha number hydar tare da ce mata ga number sahib din nan yace ki kirawo shi, kuma an saka miki kudi a wayar,


Samha tayi godiya sosai, bayan Alale ya tafi ne, samha ta nunawa farida wayar da sahib ya kawo mata sosai tayi farin ciki kuma wayar tayi mata kyau, ta kara kallon wayar da kuma kudin data gani a cikin wayar, amma wannan ba abin mamaki bane ba dan duk wanda yake tare da hydar shima kanshi moloniya ne dan hydar baya da bakin ciki kuma baisan darajar kudi ba shi yasa duk macen duniya take fatan hydar ya kasance miji a gareta, uwa uba ga ibada dan lallai namiji mai ibada abin so ne ga duk macen data san kanta suma ga mazan haka ne suna san mata masu ibada,


Mikawa samha wayar tayi tare da cewa Allah yasa alkairi samha tace amin nagode, tashi farida tayi ta nufi ciki tabar samha a farlo, farida tana tashi samha ta fara kiran sahib, haka sukasha firarsu sosai samha tana cikin jin dadi da annashuwa amma hydar yana cikin damuwa  yayi yunkurin bayyanar da kanshi a wurin samha amma yana tsoron abunda zai biyo baya dan haka dole ya hakura, yaci gaba da fira da samha yana kwantar mata da hankali yana sakata farin ciki ita kuma tanajin dadi,


Haka rayuwar samha da sahib taci gaba da tafiya samha tana rayuwa a gidan farida hydar kuma yana can yana jinya amma Alhamdulillah da sauki sosai gaskiya dan sahib ya shedawa samha cikin satin nan zai dawo insha Allah, samha tana cikin farin ciki sosai danji take kamar ta jawo satin ya dawo yanxun,


Dukan da akeyiwa kofar gidan farida ya farkar da samha daga bacci da sauri ta tashi tana kallon agogo, 3:05am samha tace to lafiya ne? A daidai lokacin da farida ta fito daga dakinta,


Farida tace samha maza maza tashi kiyi ta kanki idan har mutanen suka kamaki lallai kasheki zasuyi, saboda haka ki boye danni bazan tona miki asiri ba, nayiwa hydar Alkawari cewa bazan taba barin wani abu ya sameki ba, dan hydar yace idan har wani abu ya sami samha hakika soyayyata zata rushe daga zuciyarsa,


Samha tace hydar kuma?  Farida tace to sosai, samha tace badai hydar ba idan har saboda hydar zan boye wallahi bazan boye ba dan duk duniya babu abinda na tsana irin hydar da kuma mai irin sunan sa, farida tace yanxun ba lokacin nuna kiyayya bane kiyi hakuri ko badan hydar ba kiyi danni, kiyi hakuri kada ki kawo aikin gaba a yanxun,


Ci gaba da dukan gidan akayi kamar za'a zazzage kofar, farida da kanta taja samha ta bayan gidanta taje ta boyeta cikin shukokin gidan sannan ta dawo da sauri ta nufi kofar gidanta,


Tana isa ta bude kofar ba tare data ce waye ba, tana budewa tayi magana cikin yanayin bacci cewa ya akayi ne? Ina samha? Farida tace samha kuma? Eh, farida tace kada ku dauki mutane "yan iska mana ba jiya da daddare kuka turo akazo aka tafi da ita ba? Daga cikin motar ogan nasu yace ke kada ki dauki mutane "yan iska uban waye yazo ya tafi da ita ne? Farida tace yoni ya za'ayi in sani tunda masu san ganin samhar suna da yawa,


Fitowa ogan yayi daga mota sannan yazo ya shaki farida ya fara dukanta babu ji babu gani saida ya tabbatar ta bugu sosai sannan yace ina samhar take dan kutumar ubanki? Farida tace bata tare dani, 


Kara dukanta yayi sosai yana halbinta sannan yace ina samha? Murmushi farida tayi sannan tace samha bata tare dani, rike kan farida yayi sosai sannan ya bugashi a bango farida ta dafe kanta sosai sannan tace nace maka samha bata tare dani,


Ku daukomin fetir a mota da sauri aka dauko fetir a mota Oga ya zazzagashi akan farida sannan yace ki fadamin inda samha take kafin in kunna miki wuta, dariya farida tayi sannan tace samha bata tare dani, wani ne yace oga lallai bata tare da samha ka barta kada ka konata amma mu tafi da ita,


Haka sukaja farida suka tafi da ita, bayan sun tafi samha ta fito daga maboyarta komawa ciki tayi katuwar hijabi da nikaf ta saka sannan ta dauki wayarta ta fita daga,


Kai tsaye samha gidan kawu ta nufa, akwai tafiya sosai amma a kafa samha ta daɓeta, tana zuwa ta fara dukan kofar gidan amma da mamaki taji kofar a bude, dan haka da sauri ta shiga cikin gidan, kawu ta gani yashe a tsakar gidan cikin yanayin maye, da sauri samha ta isa kusa dashi sannan ta fara kiran kawu kawu kawu,


Uhum kawu yace da sauri samha tace tashi kawu tashi don girman Allah bude idonka samha ce, dariya kawu yayi sosai sannan yace haba samha kin wani tafi kin barni sai tunaninki nakeyi, samha tace ai yanxun na dawo kuma bazan sake guduwa ba, fadamin su waye suke nemana su kasheni? 


Cikin maye kawu yace kin yadda zaki aureni ne? Samha tace sosai ma, zan aureka mana bada min inji, a hankali kawu ya tashi zaune sannan yace to mubar gidan nan dan nayi imani zaki iya ganinsu anan yanxun,


Da sauri samha ta mike kawu kuma dakinshi ya shiga bai wani dade ba ya fito da wata jaka a hannunshi sannan yaja hannun samha suka fita daga gidan,


Suna fita ta bayan layi suka shiga, basu dade da shan kwana ba motarsu tayi parking a kofar gidan kawu, gaba dayansu suka fita da gudu suka shiga cikin gidan, sukayi ta dube dube har suka shiga dakin kawu,


Kattin kaladun hotunan samha suka gani, duk bangon dakin anbi an rubutashi da samha , i love u samha, duk an wani bi anyi kissing din bangon dakin kamar na wata budurwa sabuwar balaga, Wawu ya jinjina kansa sannan yace dakyau kalifa wato soyayya ko? Kun gani soyayya yakeyi da yarinyar nan shi yasa ya daukemu wasu ajawu,


Wawu ya kara kallon hotunan samha sannan yayi dariya yace kaga shegiyar yarinyar nan da uwarta take kama sosai, murmushi wawu yayi sannan yace shege kawu wato yaga jar fata da manyan idanuwa karamar yarinya ta tafi da imaninsa, shi yasa ya makale mata, wawu yace wallahi karyane babu ubanda ya isa ya tonamin asiri a idon duniya dan na tabbata idan har yarinyar nan ta anshi m card din nan lallai akwai bala'i a kasarnan,


Haka sukaci gaba da zagayawa suna ma gidan binciken tashin hankali amma babu komai kuma babu kowa kuma babu m card din kwata kwata, wawu ya ciro wayarsa daga aljihunsa yayi dan latse latse sannan ya karata a kunnensa,


Bayan wani lokaci ya fara magana cewa ranka ya dade bamu samu samha ba kuma bamu samu kalifa ba haka kuma maganar m card shima babu shi, wanda ake wayar dashi yace babu ruwana da maganar m card kawai a kashe min samha kuma a kashe min kalifa tunda sune suka san inda m card yake danni babu wanda ya isa ya batani a idon jama'a, wawu yace an gama ranka ya dade,


Bayan sun gama wayarne suka fita daga gidan da sauri dan bin bayan kawu da samha ko zasu gansu, suna shiga motar suka fitar da farida suka jefar da ita a ganinsu bata da sauran amfani a wurinsu,


Farida tanaji tana gani sukaja motarsu sukayi tafiyarsu, murmushi tayi sannan ta tunkari hanyar gidanta,


Kawu da samha kuwa wani daji suka nufa wanda illo yayi musu jagoranci, bayan sunje sun natsu ne, kawu ya kalli samha sannan yace gaskiya samha na cutar da rayuwarki sosai amma don girman Allah kiyi hakuri ki yafemin, samha tace ba komai kawu, kawu yaci gaba da cewa m card baya hannun kowa yana hannuna, dan haka gobe idan Allah ya kaimu zan baki sai kiyi kokari ki cika burin mahaifinki, ajiyar zuciya samha tayi sannan tace to kawu,


Ganin illo ya tashi daga wurin ne yasa samha cewa kawu mu sake wuri domin mutum ba abin yadda bane hakika illo zai iya tona mana asiri,  mu tashi daga nan mu koma cikin mutane, kawu yace to,


Lallai kam mutum babu amana domin dai illo ya kirasu wawu ya sanar dasu abinda ake ciki, dan haka kawu ya dauki samha a mota suka bar wurin,


Suna shigowa cikin gari samha tace da kawu mu koma gidan farida bazasu sake nemanmu a can ba, mu zauna can kafin komai ya gama zama daidai, babu musu suka tafi gidan farida,


Bayan sunje ne suka zauna aka fara maida yanda akayi farida ta bawa kawu labarin yanda sukayi dasu wawu, kawu yace to Allah dai ya sawake, abinci farida ta kawo sukaci sannan akaci gaba da maida yanda akayi,


Wayar samha dake ringing samha ta jawota daga inda ta boyeta a jikinta, ganin number sahib ne yasata dauka da sauri, bayan sun gaisa ne sahib yace mata ya dawo, samha tayi murna sosai sannan tace yaushe ka dawo ne? Sahib yace jiya na dawo, fatan alkairi samha tayi mishi sannan tace zasuyi waya idan Allah ya kaimu, sahib yace to babu damuwa, bayan ta gama wayarne kawu yace keda waye kike waya ne, samha tace wani ne baka sanshi ba, shine yake taimaka mana, daga haka bata sake magana ba shima kawu bai sake cewa komai ba,


Wawu bayan sunje basu samu su kawu ba, sunciwa illo bira'uba sosai sannan sukace ya kikayi yi musu karya saboda gaba, 


Da daddare kawu ya shirya yayi tafiyarsa wurin wasan cacarshi, acan yaje yayi mayenshi yayi tatul sannan yayo gidan farida, kawu bai sani ba akwai wanda yake bin bayansa har gidan farida, bayan yazo yaga gidan da kawu ya shiga ya koma, saida yaje gidan sannan ya fadawa su wawu yaga kawu kuma lallai yaga gidan daya shiga, wawu yace to kasa tsaro sosai bana nan amma insha Allah gobe zanzo da safe, yace to ba damuwa,


Tunda safe hydar ya kirawo samha suka gaisa, sannan tace mishi yaushe zan ganka ne? Hydar yace yanxun dai zanje wurin training idan na dawo zanzo insha Allah, samha tace to kila inzo dan gaskiya bazan jira harsai ka dawo ba, murmushi hydar yari sanna yace to, bayan sun gama wayar ne samha ta tashi taje tayi wanka, babu dadewa ta fito ta shirya cikin shiri mai kyau sannan ta fito farlo,


Zama samha tayi a gefen kujera sannan tace kawu zanje in dawo yanxun don Allah kawu yace to, amma kada ki dade, samha batayi magana ba, ba aka bankado kofa da karfin tsiya, ganin su wawu yasa kawu tashi da sauri ya zauna, sannan ya kalli samha,


Dariya wawu yayi sosai sannan yace dan iskan tsoho, kai amma duk duniya babu babban jibgegen marar rabo iri ka, wato ka bari zuciyarka ta rudeka na fadawa soyayyar dakasan bata da magani bare mafita, ka fada soyayyar yarinyar daka gama reno kayi mata horo da zalinci da kafiyar zuciya, yarinya daka koya mata rashin tausayi bare taji ƙan wani, wai ita kake so?


Ka guji miliyan hamsin saboda san rai ko? To sannu baban soyayya wawu yace to wannan ma dai duk ba shine mafita ba, ina m card din yake ne? Murmushi kawu yayi sannan ya saka hannunsa a aljihu m card ya fiddo sannan yayi murmushi ya daga m cars din sama sannan ya kalli wawu yayi murmushi, wawu ya matsa kusa da kawu yace bani, kawu yace zan baka amma duk sai kun ajiye makaman hannunku, da sauri kowa ya ajiye, murmushi kawu yayi sannan ya tashi daga saman kujera ya matsa kusa da samha,


Wawu yace kai kada fa ka daukemu kananan yara kaji bamu, kawu baiyi magana ba ya mikawa samha m card sannan yace ki rike shi da kyau maza ki gudu murmushi kawu yayi sannan yace nima zan biyoki a baya, bai gama rufe bakinsa ba wawu ya dirma mishi bindiga a kafada ta baya, samha tace wayyo Allah kawu kada ka mutu ka rufa min asiri dan Allah kawu, murmushin karfin hali kawu yayi cikin wata irin murya yace ki gudu bazan mutu ba samha harsai na sadaki da farin ciki a rayuwar ki tsira da m card din nan hakan zaisa inyi alfahari dake, wuce yana fadin haka ya fadi kasa,


Da gudu su wawu sukayi kan samha, wani irin ihu samha tayi tare da wata irin jijjiga, da kafarta ta taka wata katuwar wuka, wukar tayi sama samha ta tara hannunta wukar ta dawo a hannunta sannan ta rike ta gam, kallon su wawu tayi sannan tace ina mai kararren kwana? 


Wawu ne ya fara tattaki yana niyar matsawa kusa da samha, kafin ya matso samha ta jefa shi da wukar, da gudu sukayo kan samha, ganin haka yasa samha tayi waje da gudu, suma suka fita ɓarke,


Gudu samha take kamar zata kashe kanta, amma ji takeyi kamar ana maidota baya, da sauri ta cire hijabin jikinta dan gani takeyi kamar itace ta riketa, wurin training tayi ma tsinke dan tasan tana haduwa da sahib shine kadai zaiyi mata maganin wannan matsalar,


Hydar ganin samha bata zo ba kuma ya biga wayarta bata dauka yasa kawai zai tafi gida, dan haka ya fito dan tafiya, yana shiga mota Alale yace ranka ya dade ga samha nan, da sauri hydar ya juya amma sai ya hango samha da wasu jijjjiga jijjigan katti suna bin bayanta,


Samha babu dan kwali a kanta babu hijabi ba takalmi hydar yace subahanalla, kallon kanshi yayi a madubi ya ganshi yana mazaunin sahib dan haka ya kalli Alale cewa maza ka kiramin su Shamsu, yaransa, saboda idan zaizo a matsayin sahib baya tafiya da kowa,


Kafin hydar ya gama magana har samha ta shige cikin holl din da gudu dan a tunaninta anan zata samu sahib, da gudu hydar ya fita daga mota, kafin ya shiga cikin holl din yajiyo maganar samha daga saman bene tana kwala mishi kira, sahibbbbbbbbbbbbbb, ka taimakeni, da sauri hydar yayi wata irin tirjiya sannan ya juyo inda yakeji sautin muryar samha tana fitowa,


Hangota yayi saman bene hawa na ukku tana dago mishi hannu ga wasu irin katti sun zagayeta, wasu da wuka wasu da bindigu, wanda yafi girma hydar yaga yana tunkarar samha da wuka daga murya hydar yayi sosai sannan yace kaiiiiiiiii, ka kiyayeni kada ka kuskura ka tabamin zuciyata idan har wani abu ya sameta saina tsiyaye maka idanuwa babu tausayawa,


Wawu yace Uhum wato soyayya ko? Nine zaka siyayewa idanuwa, wawu marin samha yayi sannan yace waye waccan shi kuma? Lallai abun akwai firgici wato ga kawu ga sahib uhum to bari in tunkudaki ki fada kasa idan yana sanki saiya rike mu gani,


Wato shima yaga abunda kawu ya gani lallai dukanku zan hadaku in kasheku baki daya sannan in dauki m card din, lekawa wawu yayi sosai sannan yace ka shirya ga zuciyar taka nan zuwa, idan har kana santa saika shirya tarbarta, hydar yace kai wallahi kada ka jefota idan har ka fadar da ita daga saman bene ni kuma saina hau jirgi zan jefo banza dakai, 


Dariya wawu yayi sannan ya halbo samha da kafarsa yana cewa ga zuciyarka nan ta taho, tawani irin ihu hydar yayi sannan ya matsa da gudu yana bin saitin inda samha zata fado yana mika hannuwansa, su kuma su wawu sai dariya sukeyi suna nuna yanda hydar yakeyi, a saman hannun hydar samha ta fado hydar ya riketa sosai sannan ya durkusa saman guyawunsa yace samha tashi tashi fadamin su din su waye ne? Mi kikayi musu ne? Hannunta da yake rike da m card ta daga ma hydar har yanxun tana rike a jikinshi cikin kuka tace sahib sun yankamin wuka a hannuna tayi maganar cikin kuka, hannun mai jini samha ta taba fuskar hydar dashi cikin kuka hydar yace kiyi hakuri babu wani abu dazai sameki ina tare dake kiyi shiru ki daina kuka kin manta ke jarumace? Tashi ki gani a gaban idonki zan kashe wanda ya yankamin hannuki, m card din ta mikawa hydar sannan tace ka rikemin wannan kada ka bari kowa ya ansa, a daidai lokacin da su wawu suka sauko daga sama, yana zuwa kusa dasu samha wani irin halbi ya kaiwa samha wanda yasa ta kamewa ƙam kamar waya tayi hucing,


Da sauri hydar ya sauke samha daga jikinsa ya ajiyeta kasa sannan yace wane dan iskane ya yanka mata hannu? Wawu yace nine nan, murmushi hydar yayi da gefen bakin sannan yace jirani ina zuwa, saida yayi nisa sosai sannan ya taho da wani irin gudu yana zuwa yayi tsalle ya taka saman motarshi sannan yayi wani irin suka ya dire saman jikin wawu yakai mishi wani irin harbi, halbi daya hydar yayi ma wawu ya some, dukawa hydar yayi ya kama hannu wawu sannan ya karyashi kamar yanda ya karya hannun yusra dana samha,


Gaba daya yaran sukayo kan hydar murmushi hydar yayi sannan yace duk zanzo kanku wane dan iska ne ya takawa samha ciki? Da sauri hydar ya juya ya rike hannun wanda yake kokarin sokarshi da wuka ta baya, rike hannun yayi sannan ya murdeshi saida hydar ya tabbatar hannun ya kare sannan ya sakeshi, da sauri wani ya ciro bindiga yana saita hydar,



*Meelat Musa ce*

[05/04 4:45 pm] Washa: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊



                 *SO*

     *MUGUN WASA*



       *{ Love is a bad game }*




*JAMEELA MUSA* { meelat musa }




*Story, Writing & Editing*

                   *by*

         *Meelat Musa*


*Gaisu ta musamman fatan alkairi a gareku inayinku ina sanku, ina sanku, ina sanku, meelat musa tana kaunarku, kuma tana tare daku ina jinku har ciki babban birni ruhi na,*



*FA'IZA ANFA*  _marubuciyar_ { *DAN FASHI* }


*NA'IKKA*   _marubuciyar_  { *FARAR TAFIYA* }


*AISHA ILIYASU*  _marubuciyar_  { *MATAR SARKI* }


*SUMMY S DOGARI*  _maribuciyar_      { *DOCTOR ZAHRAH* }



*Aha manyan marubutan zamani,👍🏻 jinjinar bangirma fatan alkairi samun nasara addu'ar daukaka a gareku Allah ya kara basira da hazaka ubangiji ya kara lafiyar idanuwa Allah yasa ku zarce haka a fadin duniyar marubuta, Allah ubangiji ya barmu tare Allah ya tsaremu da sharrin mahassada, ubangiji ya kauda idanuwan mahassada akanmu, muyita hakuri da juna dan babu abinda yakai hakuri dadi a duniya, gaku nan* 👇🏻


*ASMEENAT XEEYAN*

{ _NAMIJI_ }



*MAI DANBU*

{ _KISHIYATA JIHADI NA_ }


*SURAYYA*

{ _ANFA_ }


*RAHEEMA*

{ _UWAR MIJI_ }


*MARYAM MUHAMMAD*

{ _RAMLAT_ }


*UMMU SAYEED*

{ _FURUCI_ }


*LEEMA*

{ _KURUCIYAR JUMMAI_ }


*UMMUHARNY NERSERLLERH*

{ _RAYUWAR UMMERHERNY_ }


*SALIHAT*

{ _DACE DA JUNA_ }


*HALIMA YAHYA tweety*

{ _RAINON ZUCIYA_}


*FEEDORH*

{ _SAI NAGA RUKKY_ }



*Gaishe da mai gaishe, so mai sanka a duk inda yake a fadin duniya, wannan dalilin yasa na babbako da gudu nayi zamiya a gabanku masoyana, Allah ya barmu tare gaskiya fa ina sanku sosai kuma kuna raina bazan manta daku ba,*


*SAFFA ONE*


*AISHA ABUBAKAR LOLO*


*BRILLIANT FANS GROUP*


*MEELAT MUSA FANS GROUP*


Inajinku har cikin babban birni zuciyata ❤💔



                  *SO*

      *MUGUN WASA*


*Dedicated to* 👇🏻

_Ramlat Abdulrahman real mai dambu_



*32-34*


Tun fitar su wawu daga gidan farida, cikin tashin hankali farida ta kama kawu taje ta sakashi a mota ta nufi asibiti dashi dan ceton rayuwarsa,


Juyowa hydar yayi yana kallon wanda ya saita shi da bindiga, murmushi yayi da gefen bakinsa sannan yace nine zaka harba?


To bada himma gani harbarni, har yanxun kara saita hydar yakeyi da bindigar, hydar yace idan harka harbeni cikin tsotsayi ko ganganci yasa ka harbine saina kare kaff ahalinku wallahi,


A daidai lokacin da su shamsu suka shigo wurin motoci sunfi goma, tun kafin motocin su gama tsayawa gwarazan maza kattin maza majiya karfi kosasshi masu kama da "yan rastilin sukayi ta dorowa,


Wanda yake saita hydar da bindiga suka fara ci masa kan bura'uba sosai, saida suka tabbatar yaci gidansu dakyau yana fitar da nunfashin wahala sannan suka barshi,


Saida hydar yaje ya daga samha daga inda take ya jawo hannunta kamar wani dan jagora, sannan yazo wurin dasu shamsu suke yace kuje da banzaye saina nemesu,


Alale ne ya bishi da gudu cikin girmamawa harararsa hydar yayi sannan yace bani makulin motar zanje in kai samha asibiti, Alale yace ka bari in kaita mana, hydar yace so kake sai mai gida hydar ya ganka da motarsa kuma yayi min fada?


Murmushi Alale yayi sannan ya bawa hydar makullin, samha ta kalli sahib tace muje a napep mana, kallonta yayi sannan yace A, a, a mota zamuje, a daidai lokacin daya bude mata gaban mota ta shiga saida ya rufe mata sannan ya zagaya ya shiga yaja motar suka bar wurin,


Tafiyar hydar aka tattara "yan iska ka tafi dasu kamar yanda hydar yace, wawu kuwa har yanxun bai farfado ba tun harbin da hydar yayi masa, saboda shine ya jefo mishi samharshi daga saman bene,


Saida hydar yakai samha asibiti akayi mata dressing sannan ya wuce da ita gidanshi, tunda suka tunkaro gidan samha take cewa sahib ina kuma zamuje ne?


Tabe baki yayi sannan yace hydar ne yace wai muje gidanshi ki huta kiyi wanka kici abinci, kuma bakiga yanda ya tausaya miki ba akan abinda ya faru dake,


Samha tace karya yake munafiki nasan yana can yanajin dadi yace dama na mutu, sassauta muryarta tayi sannan tace ni wallahi sahib bana san wannan hydar din banzar wallahi haushi yake bani,


Hydar yace haba samha ki rika kyautatawa hydar zato don Allah wallahi yana sanki sosai, samha tace babu wani nan kai ya rainawa wayau kada ka sake ka yadda dashi dan bakin ciki wanda baya san ganin farin cikin masoya,


Murmushi hydar yayi amma bai sake magana ba, samha taci gaba da cewa aini tunda nasan baya san tarayyarmu dakai tun lokacin daya hana ni zuwa wurin training dinsa, waishi mai wurin training, dan gajeran tsaki tayi sannan tace, da wasu banzayen idanuwansa kamar mage tana atini, dariya sahib yayi sannan ya daki sitiyarin motarsa amma baiyi magana ba,


A bakin katon get din gidan hydar ya tsaya da motarsa, sannan ya fiddo remot ya latsa get din ya bude, a hankali ya fara silalawa da motarsa ciki, idanuwa samha ta zaro tana kallon sahib, cikin kyauyanci ta taba remote sannan tace sahib waye ya koya maka? Hydar baiyi magana ba, dan haka itama bata sake magana ba,


Idanuwa ta sake zarowa ganin tafiya mai nisa ce sosai tsakanin get na farko zuwa wani, cike da tsoro tace sahib don girman Allah ka tsaya, ba tare daya kalleta ba yace miye ne?


Samha tace don Allah kada muje nidai bana san gidan nan wallahi kwata kwata, hydar yace ni kuma ina sanshi kiyi hakuri kada hydar yace ban kyauta ba ko kina so yayi min fada ne?


Gyara baki kawai samha tayi amma batayi magana ba, shima bai sake magana ba, har suka isa bakin farlon shi anan yayi parking sannan ya fita, zagayowa yayi ya budewa samha kofa yana cewa barka da zuwa ranki ya dade, dariya samha tayi saboda yanda yayi abun ya bata dariya har wani jinjinawa yakeyi yana sara mata kamar yanda akeyiwa sarakuna,


Fita samha tayi sannan ya rufe kofar tare da nuna mata da hannunsa cikin girmamawa yana dan rusunawa ya nunawa samha hanya, murmushi tayi sannan tace to muje, shine a gaba tana bin bayansa,


A hankali suke tafiya, samha tana dan kalle kalle dan gaskiya gidan ba karamin haduwa yayi ba, idan kana ciki zaka ranste ba'a nigeria kake ba,


Suna shiga parlo samha ta ida gigicewa, wuri ya nuna mata ta zauna, shi kuma ya shige ciki, samha tace sahib ina zakaje? Juyowa hydar yayi sannan ya nuna da hannunsa cewa ina zuwa👌🏻, 


Shigewa yayi ya barta a wurin, sai kalle kalle takeyi, yana shiga ya kirata a waya, bayan ta dauka yace kiyi hakuri hydar yasani zanyi masa wani abu ina zuwa, samha tace to babu damuwa bayan ya gama wayarne ya cire fuskar daya dora sannan ya dauki towel ya shige toilet,


Wanka yayi bayan ya fito ne ya shirya cikin kana nan kaya masu kyau da daukar hankali kuma sunyi masa kyau sosai, aman ruwan turare ya fara yi ma jikinsa, bayan ya gama kallon kansa yayi a madubi sannan yayi murmushi, a bayyane yace wai ido na ne mai kama dana mage tana atini, dariya yayi sannan ya daure fuskarsa yayo parlor,


Tunda samha ta hango hydar yana saukowa daga saman bene gabanta ya fara faduwa dan haka da sauri ta sauka daga saman kujera ta zauna kasa,


Dariya yayi a ransa yana jin dadi idan yaga samha tana cikin tsoro tafi mishi kyau a haka, burgeshi takeyi sosai, murmushi yayi a daidai lokacin da yake zama saman kujera,


Cikin rawar baki tace ina kwana, be kalleta ba kuma bai ansa gaisuwar ba, mikewa tayi tana nema hanyar fita, hydar yace ina zakije ne?, ba tare daya kalli inda take ba, harararsa samha tayi sannan ta murguda baki, a tunaninta baya ganinta,


Juyowa hydar yayi ya kalleta da manyan idanuwanshi masu saka mutum yaji dimuwa, sannan yace ni kike harara? Samha tace nifa ba dakai nake ba, kawai zanje waje ne in zauna,


Hydar yace zo nan, a hankali ta juya ta koma inda ta tashi ta koma zata zauna hydar yace nan zaki zo, ya nuna kusa dashi da hannunshi, a hankali ta matsa taje ta durkusa saman guyawunta inda ya nuna mata,


Hydar yace ke kalleni ki saka idonki a nawa ki fadamin ina wasa dake ne? Dukar da kanta tayi kasa tana gunguni, hydar yace ke ni kike zagi ne? Shiru samha tayi hydar yace ke miyasa kin raina mutane ne? Samha tayi shiru, hydar yace kindai san na haifeki ko? Dariya samha tayi sannan tace Allah ya sawake ka zama babana, hydar yace nima Allah ya sawake in haifeki baki ganni mai kyau ba, ga idanuwana masu kama da mage tana atini, maganar data fadawa sahib a mota, 


A hankali samha ta daga kanta ta kalli hydar bude idanuwansa yayi dukansu sannan yayi wani iri dasu da sauri samha ta zauna saman duwawunta ta ajiye kanta kasa, a ranta tace kai hydar fa dan iska ne,


Murmushi hydar yayi sannan yace ya kikaga idon hydar ne? Nasan ya miki kyau sosai, kinga sahib baida irin wannan idon amma hydar yana dashi, kina son idanuwana ne?, samha tayi shiru, hydar yace to shikenan kina so zanyi ta miki wasa dasu kinajin dadi kallar ni inyi miki, samha tayi shiru, dariya hydar yayi sannan ya mike yana cewa tunda baki so kin huta yana fadin haka yayi tafiyarsa,


Yana komawa daki kaya ya canja sannan ya saka fuskar sahib, a bayyane yace ya Allah kasawa zuciyar samha so na, Allah ka cire mata kiyayya ta goge hawayen idonsa yayi dan wayarsa dake ringing ya dauka,


Murmushi yayi sannan ya dauki wayar, bayan sun gaisa ne hydar yace faruk inanan da samha fa, faruk yace da gaske,? Hydar yace wallahi kasan daga asibiti gida na taho da ita, yanxun zan fita insa tayi wanka taci abinci sannan muyi maganar m card din data bani,


Faruk yace to Allah ya taimaka, hydar yace amin, hydar ya bawa faruk labarin abinda yayi wa samha, dariya sukayi dukansu, hydar yace wallahi na lura da yarinyar nan haushi nake bata ni banma san yanda zan bullumo lamarin ba, faruk yace gaskiya akwai aiki sosai murmushi hydar yayi sannan yace kada ka damu zan koyama zuciyarta so na insha Allah, faruk yace Allahu yasha, bayan sun gama waya da faruk hydar ya fito da sauri dan yasan yanxun samha taci kuda,


Tunda ta hango sahib take ta yashe baki tana mishi dariya har yazo kusa da ita, saida yazo kusa da ita sannan tace Allah ka batamin rai, murmushi yayi sannan yace kiyi hakuri don Allah yadan yamutsa fuska sannan yace keko dangoge goge nayi sai yanxun na gama kiyi hakuri kinji,? Samha tace ai ba hakuri zaka bani ba laifin daka yi zaka fara tambaya,


Gyara tsayuwa hydar yayi sannan yace to fadamin miye laifin sahib? Yana maganar yana mata wani irin kallo, dan gajeran tsaki samha tayi sannan tace kai daga magana shine sai kawai kaje ka kwashe ka fadawa hydar?


Idanuwa ya zaro sosai 😳 sannan yace da gaske? Samha tace ban gane ba kuma? Ni ina tambayarka kaima kana tambayana, murmushi yayi sannan yace hydar yace kije kiyi wanka, ya fadi haka dan kauda maganar,


Cikin sakata samha tace itadai baza tayi wanka gidan da babu mata ba, hydar yace kiyi hakuri samha don Allah kije kiyi magana zamuyi dake, wani irin kallo tayi wa sahib sannan tace wato kaji ina tsami tsami ko? Cikin tsiwa tace to ai kafin in fito gida saida nayi wanka sai kawai kace sai nayi wakan a gidan nan sai kace wata "yar iska?, cikin sauri hydar yace Allah ya baki hakuri ni bance ke "yar iska bane, juyin duniya hydar yayi amma samha tace bazatayi wanka ba, sahib yace miyasa to? Samha tace wannan katon gidan kila ma an makala "yar camera mai daukar hoton mutum, wai { *C C T V camera* } inje inyi wanka ana kallona, murmushi sahib yayi sannan ya juya ya sake kallon farlon, maido dubansa ga samha sannan yace to mu zauna,


Zama samha tayi hydar ya koma sama da sauri, babu dadewa ya fito da system a hannunsa, kusa da samha ya zauna a jikin flash ya saka m card in sannan yasashi a jikin loptop in, ya fara loading, bayan ya gama ne hydar ya fara neman abinda yake cikin m card din,


kurawa laptop din ido yayi tare da rike habarsa, baicewa samha tazo ta gani ba ita kuma samha bata leka ba ya dan dade sosai yana gani sannan juyowa yayi ya kalli samha, yace zo ki gani, matsawa tayi kusa da hydar sosai nuna mata wata mace yayi da hannunsa sannan yace ita wannan wace ce? Samha tace ban sani ba wallahi, jinjina kai hydar tare da ceje lebonsa na kasa yadan kankance idonsa, murmushi yayi sannan yayi copied abinda yake a m card bayan ya gama ya cire m card din, sannan ya dauki lapton din ya koma sama, ya dade sosai sannan ya dawo,


Da sauri zai wuce samha, mikewa tayi da sauri tare da cewa sahib ina zakaje? baiyi magana ba ya fice daga farlon cikin sauri, da gudu samha ta fita amma kafin ta fito hydar harya shiga mota yabar wurin, cikin mamaki tace toko lafiya? To miyasa ya tafi yabarni anan? Tambayoyi sosai takeyiwa kanta amma babu mai bata amsa, dan haka hakura tayi ta zauna a wurin ba tare data koma farlo ba, dan bata so hydar ya sake fitowa yayi mata irin abinda yayi mata dazu,


Hydar yana fita daga gidan ya cire fuskar daya saka, waya ya dauka ya kira farida bayan ta dauka suka gaisa, hydar yace kina ta ina ne? Farida tace ina ta gidana, hydar yace ina wannan mutumin da samha take wurin sa ne? Farida tace lafiya? Hydar yace bana bukatar tambaya ina tambaya kina dawo mun da magana baya,


Farida tace yana gidana an harbeshi da bindiga ne nakaishi asibiti aka cire harsashin gamu na dawo dashi gidana yanzu, hydar yace to ganinan zuwa gareku, farida tace Alkairin Allah ya kawoka lafiya, hydar ya kashe wayar, tare da cewa amin,


Hydar yana zuwa gidan farida a kofar gida yayi parking sannan ya shiga ciki, a bakin kofar parlour n yayi sallama da sauri farida ta fito tare da cewa barka da zuwa ranka ya dade, cike da izza yace yawwa,


Farida tace kai daya? Uhm hydar yace farida tace to shigo, farida tayi gaba hydar yana bin bayanta, a farlo kawu yake kwance kana ganinsa kasan yanajin azaba a jikinsa,


A hankali hydar ya samu wuri saman kujera mai kallon kawu ya zauna, a hankali kawu ya tashi zaune yana kallon hydar, shima hydar kurawa kawu ido yayi yana kallonsa kamar kura taga akuya, hydar yace ka gane ni ne? Da sauri kawu ya jinjina kansa, alamar Eh,


Hydar yace kaine kake rike samha? Kawu yace Eh nine ranka ya dade, hydar yace wace ce samha? Kawu yayi shiru, hydar yace dakai nake magana kana min kallo sai kace baka sanni ba, cikin rawar baki kawu yace don Allah kayi hakuri ranka ya dade, tashi hydar yayi daga inda yake zaune kusa da kawu yaje yana zuwa babu bata lokaci ya daga kafarsa yakai mishi wani irin gigitaccen halbi wanda yasa kawu yayi wata irin wahalalliyar gyatsa,


Dukawa hydar yayi kusa kawu sannan yaci kwalarsa yace zaka fadamin a gidan daka satota ko kuwa saina saka an kware min fatar jikinka? Kawu yace ba sato samha nayi ba ranka ya dade, hydar yace to fadamin inji, yaudin nan ina san insan labari akan mai girma samha,


Ajiyar zuciya kawu yayi sannan ya goge hawayen idonsa yace don girman Allah kada ka rabani da samha, saboda ina santa bazan iya rayuwa babu samha ba rabani da samha tamkar rabani da duniya ne baki daya, murmushi hydar yayi lokaci guda idanuwansa suka rikeda suka canja kala zuwa launin ja, wani irin kallo yayi ma kawu wanda yasa kawu dukar da kansa cikin sauri,


Hydar yace soyayya kenan ko? Kanshi ya jinjina sannan yace ni babu wani abinda ya dameni da kana santa ko baka santa kawai so nake inji daga ina ta fito? A hankali kawu ya kara gyara zaman sa sannan ya fara cewa,


Mahaifin samha babban mutum ne kuma mutumne mai mutumci da karamci da sanin darajar dan adam baya da kyamar al'umma kuma mutumne mai cikakken arziki, ni bani da dangantakar komai dashi bansan sa bai sanni ba,


Mahaifin samha dan jarida ne, kuma babbane sosai a aikin jarida, ni kuma neman taimako naje a wurinsa, lokacin ina fama da ciwon kafa wanda har likitocin nigeria suka ce kafar tawa saidai a cireta wato a yanketa gaba daya, haka na hakura na bawa raina za'a ciremin kafa,


Ana cikin haka ne, wani mutum ya bani labarin mahaifin samha wato Alhaji Yusuf Usman mutumcin sa da kuma irin taimakon da yakeyiwa al'umma, dan haka naje wurinsa nayi masa bayanin duk abinda yake damuna,


Hakika ya tausayamin sosai kuma yayi jimami kamar yasanni dan haka Alhaji ya dauki nauhina ya fitar dani kasar waje domin nema min lafiya, haka aka tafi dani kasar waje naje nasha jinya kuma cikin hukunci Allah na samu sauki sosai,


Bayan na dawo ya tambayeni inda iyayena suke amma sai nace masa banda kowa a duniya wannan dalilinne yasa na zauna tare da Alhaji, kuma ba aiki nake masa ba, ya bani wane bangare a cikin gidansa, babu abinda na nema na rasa yana kula dani kamar dan daya haifa, 


Alhaji shine ya siya min mota mai tsada sannan kuma yace in samu mata yayi min aure, nace mishi yayi min hakuri ba yanxun ba, haka dai ya matsa amma daya ga bazanyi aurenba ya hakura ya kawo ido ya zubamin,


Alhaji yana da mata daya da yarinya daya wato samha, samha ta taso cikin jindadi kuma iyayenta suna santa suna nuna mata kauna kasancewar itace diya daya rak a wurinsu, hafsat shine sunan samha sunan kakarta aka saka mata,


Zaman lafiya Alhaji yakeyi da iyalinsa kuma suna nunawa juna soyayya sosai, Alhaji bai hada iyalinsa da kowa ba, kuma itama zainab tana masa biyayya sosai, wato maman samha,


Wata rana tsakar dare, mukayi baki a gidan namu, mu a zatonmu barayi ne kuma Alhaji bayanan yayi tafiya zuwa Abuja, Ashe ba barayi bane, haka sukayi ta dirowa ta saman katanga sukayi ta fadowa tare da fara barin ruwa harsashe,


Da gudu hajiya ta fito daga sashenta tare da cewa khalifa lafiya? Ta fito cikin kidimewa tare da kiran sunana babu kyakkyautawa, kafin in fito naji wani daga cikinsu yana cewa wow shege yusuf ashe haka yake da zukekiyar mata, jibi gashin kanta yanda yake kwarara a gadon bayan ta, kalli dirin jikinta dariya yayi tare da lashe bakinsa, a daiaai lokacin daya matsa kusa da hajiya,


Lokaci guda jikinta ya dauki kyarma cikin rawar baki tace bayin Allah miye? Kecewa yayi da wata irin firgitacciyar dariya wanda ta sake firgita hajiya, bayan ya tsagaita ne yace wato mijinki duk kashedin danayi masa bazai fita harkana ba ko? Dan nayi fyade shikenan hada wani sawa aka dauki rahoto shi kuma ya wani je ya yayadani a duniya, jinjina kansa yayi sannan yace ku daukarmin banza kukamin ita a tsakiyar gadon mijinta,


Jin haka yasa hajiya ta juya tare da ruguwa da gudu, da gudu suma sukabi bayan hajiya nikam daga haka bansan abinda ya sake faruwa ba, amma naga dai sun fito da sauri suka bar gidan,


Tun a daren Alhaji ya samu labari bansan wanda ya fada masa ba, dan haka a daren ya bugo hanya ya dawo gida,


Saida Alhaji ya dawo sannan na samu na fita, a tare dashi muka shiga ciki har a farlon ta, hajiya kwance a sakiyar farlo jini yana fita ta karkashin ta, bayan bincike da likitoci sukayi cewa hajiya tana da ciki ne, shine ya zube dalilin wani babban buguwa da tayi, Alhaji yayi kuka sosai babu hajiya babu abinda yake cikinta,


Alhaji yayi bakin cikin mutuwar matarsa haka aka shiryata dan kaita gidan gaskiya, cikin wanda suka zo cikinsu ne wani yayi vidion duk abinda ya faru, kuma da kansa ne ya kawo ma Alhaji sannan yace ya mika kansa yayi masa hukuncin daya dace dashi, wannan kuma dama al'adarsu ne duk gidan da sukaje ko kuma macen da sukayiwa fyade suna dauka ne sai sun koma gida suke gani a tsanake, 


Alhaji yace kawai yaje shida Allah, to da abokan nasu suka gane cewa ya bada wannan m card asirinsu zai tonu shine suka kashe wancan sannan suka zo sukace Alhaji ya basu m card yace baya hannunsa sukace karya yakeyi sunyi ya fiddo shi amma yaki ya fiddo, dan haka suka harbi Alhaji da bindiga , a tunaninsu Alhaji ya mutu suka tafi,


Bayan tafiyarsu ne Alhaji ya kirawoni a waya ina dauka naji shi cikin wani irin yanayi cikin damuwa naje , bayan naje na sameshi a dakinshi dafe da inda aka harbeshi, yace min kalifa ka dauki ga samha nan na baka ita bisa amana, kaga ban sanka ba baka sanni ba ban taba ganinka ba kuma bansan zan hadu dakai ba,


Kaji tsoron Allah ka kularmin da rayuwar diyata kwatankwacin yanda na kula da taka rayuwar, ka hadata da,  dangina, dan nasan kafin suzo bazasu sameni a raye ba, wata katuwar jaka ya miko min kudine a ciki kuma ba kudin nigeria bane, takarda ce ya bani sai kuma wannan m card din dana bawa samha,


A zuciye hydar ya tashi yayi kan kawu yana dukan shi babu ji babu gani tare da cewa haka ake rike amana ka mayar da rayuwar yarinya haka? Ka gina mata rayuwa cikin zalinci ka koya mata sace sace da wasan caca? Haka ake amana dan uwarka, duka harbi hydar bayajin tausayin kawu,


Da gudu su shamsu suka shigo cikin farlon wanda farida tayi musu waya tun zuwan hydar dakel suka cire hydar daga jikin kawu hydar sai kuka yakeyi tare da kokarin ya kwace kansa ya kara cima kawu uwa, harbi yaci gaba da kawai kawu tare da cewa ina takardar da baban samha ya bayar? M card din yana hannuna saika nuna su uban waye suka kashe maman samha, sanan kuma a ina "yan uwanta suke? Ina kudin ta da babanta ya baka? Wato yace kaje kakai samha wurin danginshi kai ido a kudi shine ka gudu da ita ko?


Girgije su shamsu hydar yayi daga jikinsa sannan ya gyara rigar jikinsa yana cewa kuje ku hadamin shi da sauran "yan iskannan, haka aka ja kawu aka tafi dashi sannan hydar ya fice daga gidan ,


Saida hydar yaje bakin get sannan ya saka fuskar sahib wani irin ihu hydar yayi tare da dafe daidai zuciyarsa tambayar kansa yakeyi miyasa tun farko baizo wa samha a matsayin hydar ba? Ya za'ayi samha ta anshe shi a matsayin hydar? Idan har samha tayi yunkurin fita daga rayuwarsa hakika mutuwa itace tafi cancanta dashi, idan har samha ta gane shi hydar ne wallahi bazata yadda ta aureshi ba, saida hydar yasha kukansa sosai sannan yaja motar a hankali ya shiga ciki,


Samha na hango mota ta taso da gudu cike da bacin rai ta fara magana,



*Meelat Musa ce*

[05/04 4:45 pm] Washa: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊



                 *SO*

     *MUGUN WASA*



       *{ Love is a bad game }*




*JAMEELA MUSA* { meelat musa }




*Story, Writing & Editing*

                   *by*

         *Meelat Musa*


*Ina masoyan ANFA? wato marubuciyar DAN FASHI, ku garzaya jikin soket domin ku dirkakawa wayoyinku chargy tsaraba mai dadi ANFA tazo muku da ita, masoyan ANFA karku sake ku bari a baroki ku baya karku kuskusara ku bari meelat musa ta baku labari, shin Hajiyata ko kinsan MAHIMMANCIN BUDURCHI?  Kinsan darajar budurchin ki? Kinsan ƙima da daukaka da buducinki yake nema miki a gidan aurenki? Wannan daliline yasa ANFA tayi dogon nazari tare yin kundunbala ta kutsatsa tasa kwalwarta dogon nazari don bamu babban labarin akan MUHIMMANCHIN BUDURCI ku kasance da ANFA ku nemi wayoyinku a kusa daku kowa ta zurawa wayarta ido domin ganin wannan kayataccen labari mai taken MUHINMANCHI BUDURCHI ni meelat musa nake cewa asha karatu lafiya, ANFA daukacin BRILIANT WRITER'S ASSOCIATION a madadin kowa da kowa na kungiyar brilliant ni meelat musa nake cewa Allah yasa a fara a sa'a,*



                  *SO*

      *MUGUN WASA*


*Dedicated to*👇🏻

_Ramlat Abdulrahman real mai dambu_



*35-37*



Shekenan saika wani kama kayi tafiyarka abinka ka barni anan? To anan nayi zamana ta nuna wurin da hannunta, sannan taci gaba da cewa kada ka sake min irin haka daga yau kaji na fada maka!


Murmushin karfin hali hydar yayi sannan yace to insha Allah bazan sake ba Allah ya baki hakuri, yana fadin haka yayi gaba dan ya kagara ya shiga ciki ya huta danji yake kamar zuciyarsa zata fado kasa,


Samha tace to ina kuma zakaje? Kazo ka mayar dani gida mana, ba tare daya juyo ba yace wane gidan? Samha tace gidanmu mana, bai sake magana ba ya shige cikin farlon samha tabi bayansa tana kara cewa idan bazakaje ba ka fada man mana, sai ka kawoni ka wani kama ka ajiyeni?


Murmushi yayi sannan yace mai gida yace anan zaki kwana! Zaro idanuwa samha tayi sannan tace in kwana? In kwana anan gidan? Kawai sai in wani kama in kwana gidan katti sai kace wata "yar iska, tunda nazo a gidan nan banga mace ba maza kawai suke shawagi kamar kifi a cikin ruwa,


Sahib yace daga yau kada in sake ji kince ke kamar wata "yar iska, idan har kika sake fadar haka zansa hydar yayi miki dukan rabani da yaro, murmushi samha tayi kadan sannan tace komai hydar komai hydar to ai sai kaje ka fada ko an gaya maka ina tsoron sa, ni wallahi ina iya fasa masa baki mtsww dama baisan dazu ya bani haushi ba, wallahi ai shima hydar din dan iska ne,


Sahib yace samha kina da hankali kuwa? Ubangidan nawa ne dan iska? Samha tace ai ba babanka nace ba, zaka wani bi ka tada hankali sai kace an tsine maka albarka, ni wallahi bana san kana zama da wannan hydar din banzan dan wallahi na lura ka fara koyan dabi'un sa, idan har kana dabi'un hydar tsakani da Allah gaskiya nidai saidai ince Allah ya kara mana hakuri baki dayanmu,


Gaban hydar ya fadi das das, da sauri yace tsaya kiji wane dabi'u nakeyi irin na hydar samha? Samha tace Oho kaima ka sani danni wallahi idan har bana san kasuwa ko sautu bana bayarwa, murmushi karfin hali yayi wanda bai kawo a bakinsa ba sannan yace duk dan na tafi na barki kike so muyi fada ko? To Allah ya baki hakuri nikam bazanyi fada dake,


Tsaki samha tayi sannan tace mu tafi ka mayar dani gida, sahib ya matsa kusa da ita sosai, sannan yace kiyi hakuri don Allah mu kwana anan da safe sai muje training kuma zan kaiki kiyi yawo sosai daga nan sai mu dawo muyi zamanmu anan zan miki labari mai dadi ya karasa maganar yana murmushi, dan bayasan samha ta tafi dan lallai idan har taga farida zata iya fadawa samha komai shi kuma bayasan a wargaza masa shiri,


Samha tayi shiru sahib yace ko kin daina so na ne? Kallonsa samha tayi sannan tace A, a, ina sanka mana murmushi hydar yayi sannan yace zo muje sama to, idanuwa samha ta zaro sannan tace sama fa kace? Hydar yace Ey mana hydar bayanan yayi tafiya ne tun lokacin daya fito ina shara kuka gaisa? Ai yana komawa yayi fitarsa,


Samha tace ta ina ya fita ne? Hydar yace muje in nuna miki wurin ki gani, yana fadin haka yayi gaba samha tana bin bayansa cikin tsoro, tana cewa ai dazu daka tafi wallahi duk tsoro ya kamani shi yasa na zauna a waje, sahib yace tsoronmi? Samha tace kada hydar yazo, sahib yace tsoron hydar kikeji ne? Samha tace A, a, tsoron irin barin jinin da zanyi a gidan nan dan naso yazo yamin zance banza in sauke kansa kasa, kalli nan kaga ikon Allah ta daga gefen rigarta, wukace daure a kugunta cikin kubenta,


Sahib yace waike bana hanaki yawo da wuka ba bazaki daina ba ko? Murmushi samha tayi sannan ta kalleshi tace haba sahib, ina da abokin gaba zanyi sakaci? Kasan abokin gaba kullum cikin shiri yake so kake a mameni? Ai yana marina ko zagina kafin ya rufe bakin ko ya sauke hannu daya mareni saidai yaji wuka ta shige cikin bakin tabi ta makoshin sa, ko kuma in  sauke hannun daya mareni dashi, tana maganar tana nunawa, da hannunta yanda zatayiwa hydar,


Murmushi yayi sannan yace bani wukar, samha tace gaskiya bazan bayar ba tana boye wukar a bayanta, sahib yace ba nace ki bani wukar nan ba? Yayi maganar cikin kakkausar murya, samha tayi shiru hydar yace idan kika bari na sake magana wallahi saina mareki, yanda yayi maganar ne yasa ta mika mishi wukar tare dayin gunguni tana murguda bakinta tana hararar sahib, tsareta yayi da idanuwanshi duk sai taji tsoro ya kamata dan haka ta dukar da kanta kasa, sahib yace wato zaki kashe hydar ko? Wai dan Allah miyasa kika rainani ne?


Samha tace nifa bakai na raina ba, sahib yace to wa kika raina idan ba ni ba? Samha tace nifa ba dakai nake fada ba, sahib yace dani kikeyi fada mana tunda kina fada da ubangida na, da baki rainani ba idan nace ki daina abu saiki daina amma da yake kin dauke wani lusari sai maganar tabi ta bayan kunnenki ta wuce ko? Turo baki samha tayi amma batayi magana, tsoki hydar yayi sannan yace wuce muje, samha tace nima daga yau bana san ana min tsoki, murmushi sahib yayi amma baiyi magana ba, yayi gaba samha tana bin bayansa,


Ya salam abinda samha ta fada kenan, tana kara waiwaye waiwaye tana kallon dakin gaskiya dakin ya hadu, haka tayi ta kyauyanci tana kalle kalle, shi kuma hydar yana gaban wedrof yana kashe wayarsa dan kada ayi ta kiransa gaban samha, juyawa samha tayi ta nufi wurin, da sauri ya rufe yayo wurinta kafin ta iso, murmushi samha tayi sannan tace sahib insha Allah saina gina mana irin wannan dakin,


Sahib yace kiyi addu'a ni inyi mana wanda yafi wannan insha Allah, samha tace a haka zaka gina mana gida mai kyau kullum kazo kayi tsugunne kasan hydar? Taci gaba da cewa kawu yace babana ya bashi kudi masu yawa ya bani amma wai kudin sun bata kaga idan aka gano kudin ya bani sai inyi mana ginin gida mai kyau sauran kudin kuma sai kayi kasuwanci kaga daga nan sai mu dauko mama mu dawo da ita wurinmu ni zanci gaba da kula da ita insha Allah, wai lokacin da hydar zaiyi tafi zuwa *switzerland* ai cewa yayi ma samha zaije kauye ganin mamansa bata da lafiya ita kuma ta siyar da gidan kawu ta bashi kudin, towai idan sunyi aure maman za'a dauko a dawo da ita wurinta ita tana kula da ita,


Murmushi hydar yayi cikin kwantar da murya yace kai amma nagode sosai samha, kuma nasan mama zatayi farin cikin kasancewa dake insha Allah, samha tace in Allah ya yadda,


Hydar yace jeki kiyi wanka, samha tace tom, nuna mata toilet yayi ita kuma tana cewa ta ina hydar ya fitane? Sahib yace gama wanka zan nuna miki, samha tace to wane kaya zan saka? Hydar yace zan baki cikin lefen da hydar ya hadawa matarsa, dariya samha tayi sannan tace fasa auren tayi ko? Ai babu mai iya zama dashi ga zuciya ga nuna shi wani ne, sakarai ai wallahi saina rama abinda yake min yana shafamin wani abu a ido sahib kasan inda yake ajiyewa? Sahib yace A, a, ya za'ayi in sani tunda ba dakina bane? Samha tace wallahi abun nan zafi gareshi don Allah kayi mishi wayau ka gano min abun in lallaba in saka mishi a ido yaji yanda nakeji,


Hydar yace to zan gano miki amma idan ya gane nashi ne ya zance mishi? Murmushi samha tayi sannan tace barni dashi nine zan sane a jikinsa, murmushi sahib yayi sannan yace ni kuma idan har kikayi sata a jikin hydar ba tare daya sani ba, wallahi zan baki naira miliyan daya, idanuwa samha ta zaro tare da cewa a ina zaka samu? Sai yanxun hydar ya dawo hayyacinsa ya gane shi ba hydar bane, yace swry i mean zan baki 1k,


Tsaki samha tayi tare da cewa kaima an fara koya maka wannan karyar, adaidai lokacin data shige toilet, tana shiga hydar yayi dariya tare da zama gefen gado, lallai bari yaga idan har samha zata iya daukar wani abu a jikinsa, idan kuwa har tayi sane a jikinshi lallai samha ta shahara kuma ta kware wurin iya sata,


Samha bayan ta gama wanka towel ta dauro sai ta saka hijabinta sannan ta fito, hydar ya nuna mata kusa dashi ta zauna, inda ya ajiye kayan da zata saka ya nuna cewa gasu nan, naje masallaci sai nayi isha'i zan dawo, samha tace a dawo lafiya, yace yawwa sannan ya fita,


Hydar na fita samha ta tashi ta matsa jikin mirrow a bayyane tace sakarai ji don Allah saikace wata mace mtswww, mai ta shafa da powder tana cewa saina fesa turarenka munafiki turare ta dauka tayi ta fesawa saida taji ya kare sannan ta ajiye ta dauki wani ta daga shi sama tana fesawa tana fadin nasan zakaji bakin ciki idan kazo kaga kadan daga cikin aikin samha saida ya kare sannan ta ajiye ta dauki na ukku, ta fara feshewa sahib ya fado mata a rai tace kada kuma fa yazo ya wulakantashi, da sauri ta maida ta ajiye, inda hydar ya ajiye kayan taje ta dauka ta saka sannan ta fara sallah,


Hydar kuwa a masallacin cikin gidanshi yaje yayi sallah saida akayi isha'i bayan sun gama sallah yace su shamsu suje su kawo mishi kawu yanxun,


Ranka ya dade mutumin nan fa aure za'a daura mishi da samha, idanuwa hydar ya zaro tare da dafe daidai zuciyarsa ya maimata aure? Eh ranka ya dade, hydar yace waye zaiyi musu auren? A wurin dangin babansu shamsu ya fada,


Innalillahi wa'inna ilaihir raj'un hydar ya fada yana kokarin mikewa amma ya kasa tashi, a hankali ya koma ya zauna sannan yace a ina ahalin samhar suke ne? Kuma kai waye ma ya fada maka zaiyi aure da samha ne? Cikin ladabi shamsu ya fiddo i.v din bikin kawu da samha ya mikawa hydar tare da cewa Allah ya huci zuciyarka mai gida, dan idan hydar yana cikin zuciya abun babu kyau,


Ansar i.v din hydar yayi ya duba, lallai da gaske aurene zasuyi nan da sati daya, wasu aljannun hawayene suka zubo daga idon hydar, ya kalli Alale yace kalli, lallai wuri fa ya kuremin, Alale yace wuri bai kure maka ba mai gida,


Gyara zama hydar yayi sannan yace Alale kada ka manta samha bata san hydar bata kaunar hydar ka fadamin taya zata amince da bukata kafin kwana bakwai? Abinda na lura samha tana da zuciya idan ta tsani abu ta tsaneshi kuma idan tace abu ta tsaya akanshi tana da tsatstsaun ra'ayi, kuma ka taba ganin inda aka hada kiyayya da soyayya? Cin tausayi Alale ya duka kusa da hydar sannan yace mai gida kayi hakuri ka fadawa samha cewa hydar yana santa kaji abinda zata ce maka,


Murmushin karfin hali hydar yayi sannan yace wallahi bazata so hydar ba tana ganin sahib, shamsu yace mai gida kawai kaje a daura maka aure da ita daga nan saiyi bala'in da za'ayi, kallonshi hydar yayi sannan yace so kake tabi dare ta kasheni?


Haka dai yaransa sukayi ta fada mishi mafita domin gaskiya suna tausawa hydar halin da yake ciki, kamar akan samha ya fara soyayya gaba daya duk ya wani bi ya haukace,


A hankali hydar ya dafa bango ya tashi Alale yana cewa ranka ya dade a dauko kawun ne? Hydar yace bana bukatar ganin sa kawai ya fadamin inda zanga dangin samha, kuma wane ma jakine zai daura musu aure idan banda suke mahaukata? Ya gudu musu da diyar dan uwa kuma sai yaje a daura musu aure su kuma su biye masa suyi musu aure ba tare da sunga samha ba?


Wannan jakancin ne da rashin sanin darajar dan dan'uwa, ace diyar dan uwanka an gudu da ita tarin shekaru masu dama, amma kuma aje maka da bukatar aurenta sai kuma kawai su anshi bukatar kawu?


Tsoki hydar yayi ba tare daya sake cewa komai ba ya nufi ciki, da tafiya mai sauri ya shiga cikin farlon ya fara hawa tsep din benen farlon da gudu harya isa dakin daya bar samha,


Yanda ya shiga dakin yasa samha mikewa da sauri tare da cewa lafiya?  Ajiyar zuciya hydar yayi sannan yace samha zo kiji wata magana, da sauri samha ta matso bakin kofar dan hydar bai shiga cikin dakin dukansa ba hannunsa daya yana rike da handile din kofar, cikin tsoro ta matso kusa dashi sannan tace miye?


Rike hannunta hydar yayi sannan yadan matse shi kadan ya daga hannu sama daidai kirjinsa ya dora hannunta da nashi daya rike hannunta, sannan yace samha,


Cikin zakuwa samha tace wai miye don Allah? Hydar yace kinsan abinda nake so dake? Samha tace A,a, jan hannunta yayi suka shiga cikin dakin a gefen gado suka zauna har yanxun yana rike da hannun samha a nashi,


Samha tace wai miye kasa gabana sai faduwa yake yi, ko m card din kuma ya bata? Da dayan hannunsa ya dago habarta tana kallon fuskarsa sosai sannan yace samha wata alfarma zan roka Allah yasa zan samu,


Murmushi samha tayi sannan tace haba sahib ai duk abinda kake so daga gareni kada ka wani tsaya jin shakku ko fargaba kawai ka fada kanka tsaye ni kuma zan maka koma miye matsawar bai sabawa Allah ba, ajiyar zuciya hydar yayi sannan yace kinyi al kawari ko? Jinjina kai samha tayi sannan tace nayi maka alkawari ta karasa maganar tare da sassauta kallon ta ma'ana ta rage girman idanuwanta tayi kallon have corent ta zuge idanuwan, yanda tayi abun yayi mata kyau sosai,


Murmushi hydar yayi sannan yace samha kin yadda sahib yana sanki sosai ko? Murmushi tayi sannan tace shakka babu, hydar yace idan nace miki hydar yanamiki fiye da san da nake miki zaki yadda? Murmushi samha tayi sannan tace inajinka, hydar yaci gaba da cewa inajin fa hydar yana sanki ne samha, murmushin karfin hali samha tayi sannan tace,


Sannan tace nawa hydar ya baka harka manta dani a cikin zuciyarka? Wato kudi ya rudeka har zaka manta da soyayyarmu ko?  Dan tsabagen hauka shine zaka tunkareni kana min maganar hydar? Shi yasa tun wuri nace maka mubar gidan sa, duk duniya babu abinda na tsana irin hydar bana san hydar bana kaunar hydar Allah ya tsinewa hydar albark... bata karasa ba sahib yayi mata wani irin azababben mari da sauri samha ta mike tana rike da wurin da hydar ya mareta hawaye na zubowa da idonta kallon sahib tayi sosai sanan tayi murmushin takaici tace sahib nika mara saboda hydar? Sahib yace naje na mareki bana ce kidai na zagin hydar ba?


Samha tace yanxun hydar yafini matsayi a wurinka? Hydar yayi shiru,  samha tace dakai nake magana kayi wani kamar bakajina, hydar yayi shiru yana kallon samha cikin wani irin yanayi, goge hawayen idonta tayi da bayan hannunta sannan ta juya ta dauki kayanta data cire ta nufi toilet, ajiyar zuciya hydar yayi sannan ya shafa kansa, ya saka dan yatsansa a bakin sa yadan ciza shi kadan, a zuciyarsa yake magana, shifa ya kawo samha gidan nanne dan ya koya wa zuciyarta san hydar ya kuma zatayi mashi haka ne? Dama ya sani tun farko baizo a matsayin sahib ba, yanxun da komai ya zama labari Yana tunanin ne samha ta fito daga toilet,


Ta mayar da kayanta data cire wanda ta saka suna a hannunta ta linkesu, tana goge hawayen idonta, hydar yace ke miye haka ne? Waike samha baki san wasa ba? Batayi magana ba, ta ajiye kayan data cire a gefen gado sannan ta dauki nikaf dinta tayo hanyar fita, a gigice hydar ya riketa yace samha miye haka? Ina zakije ne? Nifa wasa nake miki kiyi hakuri don Allah,


Kara goge hawayen idonta tayi sannan tace dan nazo gidan nan zakai min wulakanci ne? Saboda ina sanka shi yasa kake min yawo da hankali ko? Hydar ya jawo samha jikinsa sosai sannan yace kiyi hakuri insha Allah bazan sake ba, gyara baki samha tayi amma batayi magana ba, hydar yayi ta bata hakuri tare da tayata zagin hydar tunda yaga hakan yana mata dadi, murmushi samha tayi sannan tace nayi,


Jan hannunta yayi har bakin gado sannan yace ta kwanta, kwanciya tayi yaja bargo ya lulubeta sannan ya durkusa saman guyawunsa a bakin gadon daidai fuskar samha yace samha, ina sanki sosai, murmushi samha tayi sosai sannan tace nima ina sanka sosai sahib, 


Daidai zuciyarta ta taba sannan tace, nagode miki zuciyata kinmin adalci da kika sani na yadda naso mai inganci kuma so guda daya wanda babu hadi kuma so mai "yanci na tabbata gamona dakai alkairine sahib, ka rabani a gidanka anan kadai nakejin zan samu natsuwa, sahib dan Allah  kada ka barni wallahi ina sanka kuma duk abinda hydar zai baka kada ka yadda ya rabamu nayi maka alkawari ni zan sama maka babban farin ciki a rayuwarka, murmushi hydar yayi cikin karfin hali sannan yace,


Haduwarmu nida dake silarta soyayya ce, na dade ina neman na samu burinki duk wanda yaso aka soshi yai babbar nasara tunda kin soni da gaske nima bani barinki, samha bazan iya kwatanta miki yanda nakejinki a raina ba,


Dan kin zamo min wani sashe na rayuwata idan har ina cikin farin cikin inajin nishadi sosai idan inayin fushi akamin maganarki inajin natsuwa samha, dan kin zamar min sinadirin rayuwata, tunda nake samha ban taba soyayya ba sai akanki, amma bance miki banda "yan mata ba, ina dasu sosai amma kwata kwata babu maganar aure yanxun a rayuwata, amma idan kin yadda kina so na, insa a daura mana aure dake nan da sati daya?


Murmushi samha tayi sannan tace na yadda zan aureka, amma kamin alkawari zaka samanin ahalina, murmushi hydar yayi sannan yace kada ki damu insha Allah zan hadaki da farin ciki sosai samha, murmushi samha tayi sannan tace na gode, mikewa hydar yayi sannan yace saida safe, samha tace saida safe, da sauri hydar ya fita daga dakin yana fita ya rufe kofar,


A farlo ya zauna saman kujera sannan ya kirawo faruk a waya bayan ya dauka suka gaisa yace faruk kaji yanda mukayi da samha kuma? Faruk yace A, a, hydar yace kaga nazo da ita gidan nan ne kawai dan in samu in koya ma zuciyarta so na, amma sai naji wani bakon labari wai zatayi aure da kawu,


Na sameta kai tsaye nace mata inajin hydar yana santa, kaji yanda take tsinemin albarka? Dariya faruk yayi sosai sannan yace lallai abun mai girma ne, shima hydar dariya yayi sannan yace amma kasan yanda nace mata? Faruk yace A, a, hydar yace nace mata ta yanda inyi aure da ita nanda sati daya?


Faruk yace toya tace ne? Hydar yace cewa tayi ta yadda, amma in sama mata ahalinta, faruk yace lallai akwai daru sosai ya za'ayi ayi zaman auren nan hydar? Dariya hydar yayi sosai sannan yace yanda na koyawa zuciyarta san sahib haka zan koya mata san hydar, faruk yace kada ka manta zaman aure daban lokacin ba'ayi aure ba daban, hydar yace kada ka samu damuwa, sai Allah ya kaimu gobe zamu hadu, faruk yace Allah ya bamu aron rayuwar,


Yau duka zuciyoyi biyu na masoyan sunyi bacci ne cikin jin dadi, samha tana jin dadi zatayi aure ta samu mai kula da rayuwarta ta huta da sace sace da gogayya da maza, hydar kuma yanajin dadi zai daura aure da samha bata isa ta gudu mishi ba, tunda aurenta akanshi babu idan zataje idan kuma akayi auren to lallai yasan dolenta zata hakura,


Da safe bayan hydar yayo sallah ya dawo a farlo ya zauna yayi karatun Qur'ani sai 7:04am ya ta tashi yaje ya ajiye Al'Qur'anin inda yake ajiyewa, sannan ya nufi dakin da samha take, tana kwance tana bacci, kusa da gadon ya matsa sannan ya tasheta yace tayi wanka zasu fita,


Da sauri ta sauko daga saman gado tana cewa kai? Na kwana a gidan mutane, halan da hydar yazo ya yace ne? Tabe baki hydar yayi sannan yace dadi yaji ya ganki kina bacci a gadonsa, murmushi samha tayi sannan tace nasan yaji bakin ciki a ransa, hydar bai sake magana ba, 


Yace ni yanxun dai hydar ya aikeni ne, dan haka faruk zaizo ya tafi dake kije wurin trainging idan na dawo zanzo in taho dake, samha tace to saika dawo hydar yace yawwa, yana fadin haka ya fice, hydar yasa a tafi da samha ne tunda ta saba fita kullum kullum dan tayi nishadi hydar yace taje tare da faruk,


Daga saman benen yabi wata hanya ya sauka kasa, sannan a sake hawan wani ya nufi wani dakin bacci, shima dai dakin an kayatashi sosai yafi wanda samha ta kwana a ciki kyau da kuma tsaruwa, yana shiga jallabiyar jikinsa ya cire ya nufi toilet, wanka yayo ya fito da rigar wanka a jikinsa karamin towel a hannusa yana goge jikinsa, da sauri ya isa wurin wayarsa dake ringing, faruk ne, dauka yayi tare da sallama, faruk yace gamu fa munzo, hydar yace nima yanxun nan na fito wanka bani samha,


Faruk ya mikawa samha wayar ta ansa, yace albishirinki? Samha tace goro kuma fari ƙaƙal sahib yace naga hydar ya fita da abinda yake miki zalinci dashi dariya samha tayi sannan tace zan sane shi, dariya hydar yayi sannan yace to saina dawo, samha tace yawwa, kashe wayar yayi sannan yace dani dake yau zanga kwarararre, 


A bangaren samha kuma hangowa takeyi ga hydar nan da zugarsa yana gaba suna binsa, tunani ta farayi ta ina zata fara? Wata zuciyar tace mata ta bayansa zaki zagaya hannuwanki biyu duk ki saka a aljihunsa, wata zuciyar tace idan kuma ba a aljihun wando ya saka ba fa? Kallon faruk tayi tare da cewa kiramin sahib don Allah,


Bayan ya kira hydar ya fada mishi cewa samha zatayi magana dakai, hydar yace bata, tashi tayi daga kusa da faruk sannan tace sahib wane irin kaya hydar ya saka ne? Murmushi yayi sannan yace bazaki gane shi ba? Samha tace ina ganeshi mana kawai dai inji idan masu aljihu da yawa ne ya saka, jinjina kai yayi sannan yace kayan training ne a jikinsa, samha tace suna da aljihu ne? Yace Eh aljihu biyu ne daya a gefen haggu daya a gefen dama, samha tace to kayi sauri kazo kada kuma ya ganeni yayi min duka, yace to, kashe wayar samha tayi sannan ta mayar wa da faruk ta zauna tana jiran zuwan hydar,


Bata dade da zama ba sosai motocin hydar suka fara shigowa ji tayi gabanta yana faduwa cikin tsoro ta kalli faruk sannan tace sahib ya taho ne? Murmushi faruk yayi sannan ya dauke kanshi tare da cewa nima ban sani ba, tashi yayi ya nufi inda hydar yake fitowa daga mota, 


Hydar na fitowa ya fara gaisawa da mutane, da wutsiyar idonsa yake hango samha, fuskarsa dauke da murmushi yayi inda take zaune, tana ganin hydar ya taho ta mike da sauri lokacin daya iso wurin tare da cewa ina kwana, hydar yace lafiya qalau gani nazo kince zaki sace abinda nake saka miki a ido kina iyawa ko? Gaban samha ya fadi a ranta tace shi wallahi sahib baida rufin asiri komai saiya kwashe ya fadawa hydar? Hydar ya tsinke tunaninta ta hanyar cewa kinyi shiru ko har kin karaya ne?


Cikin dakiya samha tace Eh nace zan sace idan baka daina sakamin a ido ba, fiddo abun yayi sannan yace kin ganshi ko? Kalli a inda zan mayar dashi anan na ajiye kin gani ko? To zoki dauka? Murmushi samha tayi sannan tace idan na tashi dauka ai ba shawara zanyi dakai ba amma tunda naga inda ka ajiye zaka iya tafiya abinka,


Ba tare da hydar yayi magana ba ya juya yayi tafiyarsa abinsa, yana tafi samha tayi dariya tare da kallon abun a hannunta, tace jaki harna dauka bai sani ba, lokacin daya matso kusa da ita yace ya saka a aljihu, a lokacin da take bashi amsa a lokacin ta saka hannunta a aljihunsa tana magana tana kallonshi harta dauka hydar bai sani ba,


Bayan hydar sun gama abinda suke sun fito, ko inda samha take bai kalla ba ya shige mota suka tafi, saida faruk ya tabbatar sunkai gida sannan ya dauki samha suka tafi,


Lokacin da faruk sukaje hydar har yayi wanka ya canja kaya ya fito sahib yazo farlo ya kashe saman kujera 2seater yayi kwanciyarsa, a bakin farlo faruk ya tsaya samha ta fice daga motar shi kuma faruk ya wuce da motar danyi parking,


Da sallama samha ta shiga cikin parlourn sahib ya amsa tare da cewa na rigaki dawowa, dariya samha tayi sannan ta isa inda yake kwance, tashi yayi zaune yadan jirge saman kujerar kafarsa daya saman hannun kujera yana kalon samha cewa wallahi na gaji sosai, zama samha tayi kusa dashi sannan yace ni kuma yau nayi sane a aljihun ubangidan ka, fiddowa tayi ta nunawa sahib ya kalleta tare da bude idanuwansa yace ya akayi kika daukeshi?


Samha tace bana fada maka ba saina dauka, murmushi yayi sannan yace na tabbata a lokacin da kika dauka hydar ya jiki kyaleki yayi, samha tace wane shi? Idan ina sane a jikin mutum baya taba sani saida idan ya tafi yayi ta wasiwasi, hydar yace A,a yajiki dan naji yana fadawa faruk wai a lokacin da kika matsa kusa dashi a lokacin kika saka hannunki a aljihunsa shi kuma dayafi kwarewa sai yayi miki vidio kalli ki gani adaidai lokacin da yake nunawa samha,


Idanuwa samha ta zaro sosai sannan tace kai wannan mutumin shegen wayau ne dashi sahib yace ai kema kinajin kina da wayau ko? Samha tace waye ya turo maka kai kuma? Jingina bayansa yayi da kujera sannan yace yanxun ya turo min a whatsapp yace wai in kalli matar da zan aura har yanxun baki daina sane ba,


Samha tace don Allah kayi hakuri tunda ai na fada maka, kawai dan ka bashi kunya sai kace mishi naje nayi, sahib yace babu ruwana, kema kin fadamishi da kanki, samha tace aiko ban fada kaima saika fada ni kana bani mamaki duk maganar da nayi dakai sai ka wani zagaye kaje kana fadawa hydar haka zamuyi aure kullum kana tona mana asiri?


Murmushi yayi sannan yace aida hydar din za'ayi zaman aure, samha tace ban gane ba? Hydar yace umm zaki gane bari ayi auren, samha bata kawo ma kanta komai ba, dan haka tayi diff bata sake cewa komai ba, wayar hydar tana hannunta tana lallatsawa, shi kuma hydar ya gyara kwanciyarsa ya fara bacci,


Bikin samha da hydar ya rage saura kwana biyu kuma hydar yaje ya kutsa yaci uwar kawu ya tusa keyarsa gaba yaje yakai hydar wurin ahalin samha, hydar yayi ma ahalin samha well peryar na kudi yayi barin kudi hydar baisan darajar money ba, su kuma banzaye anga kudi an rikece babu mai maganar a kawo samha, saboda rashin adalci dan anga mahifinta baya raye basa binciken hydar suga ya kamata su aurar da samha a gareshi ko bai dace a bashi samha ba, babu wanda yace hydar daga ina yake, sudai kawai kudi hydar ya lura da hakan dan haka ya balle bakin banki yayi tayi musu dukan rashin mutunci da kudi ya firgitasu ya gigitasu ya haukata su su kuma sukayi ta ihu sai hydar, haka suka yankawa hydar sadaki wai naira miliyan daya a haka hydar ya bada sadakin samha, tun a gaban hydar aka raba kudin sadakin aka bawa kowa kasansa, da hydar ya tafi saida yayi kuka tare da tirr da hali irin na ahalin samha,


 Samha kuwa bata san abinda ake kullawa ba, itadai tasan kawai zatayi aure da sahib, kuma ya fada mata baida halin wani farty ko lefe, samha tace ita babu komai, dan burin samha kawai ta wayi gari ta ganta a gidan sahib a matsayin matar aure,


Kawu ya bawa hydar wasikar da haifin samha ya bashi amma ya rantse cewa babu kudin nan da babanta ya bayar kuma duk sace sacen da yasa su samha da yusra da kausar babu ko sisi, 


Hydar yace tou idan dai samha ta yafe mishi shikenan idan kuma bata yafe mishi ba tou wallahi ya shirya biyan ta hakkinta, yanxun dai hydar kokari daya shine wanda suka kashe maman samha kadai yake nema, kuma yasa anyi azabawa su wawu amma magana dayace basu san inda suke ba, amma suna waya dasu kuma sune suke kiransu kullum da sabon layi idan har suka kira hydar zasuyi magana dasu,


Kam cakwakiya kenan lallai samha zatayi wa hydar rashin mutunci,  yau ake daura aurenta da hydar wannan wane irin rainin hankaline? Shin wai yama za'ayi zaman auren? Bayan samha bata san hydar tou pha, bari inji in zungurawa wayana chargy kafin a shafa fatiha mu gani,


Kam lallai yanxun aka fara muguntar so dan hydar yayi alkawari yanda zuciyarsa ta horu da san samha shima saiya koya ma zuciyarta, niko nace anya zaka iya hydar? 🤔 muje zuwa,




*Meelat Musa ce*

[05/04 4:45 pm] Washa: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊



                 *SO*

     *MUGUN WASA*



       *{ Love is a bad game }*




*JAMEELA MUSA* { meelat musa }




*Story, Writing & Editing*

                   *by*

         *Meelat Musa*


*Allah sarki fadeela lamiɗo na gode sosai da kulawarki a gareni Allah ya kara basira da hazaka ubangiji yasa a kammala DAUKAN FANSA lafiya, nagode sosai na gode, na gode, na gode, sai munyi waya insha Allah, masoyan littafin DAUKAN FANSA ina muku fatan alkairi ni meelat musa nake cewa asha karatun lafiya,* 🤝🏻


*Gaisuwa gareku*👇🏻


*Saffa One*

*Asma'u Abubakar lolo*

*Ayush Munka'ill Akash*



                  *SO*

      *MUGUN WASA*


*Dedicated to* 👇🏻

_Ramlat Abdulrahman real mai dambu_



*38-40*


Samha yaune daurin aurenmu har yanxun kina so na ko kin canja ra'ayinki akaina ne? Sahib ne tsaye a gaban samha yake mata magana,


Murmushi samha tayi sannan tace ina sanka har yanxun kuma ban tunanin akwai ranar da zan canja zuciyata daga sanka da takeyi, ina sanka sosai kuma na godewa zuciyata sosai ta karasa maganar tana murmushi,


Murmushi sahib yayi sannan ya zauna kusa da samha, yana cewa amma fa ni ban fadawa "yan uwana ko daya ba, babu wanda yasan zanyi aure tunda kinga mamana bata da lafiya idan har mutane sukaji zanyi aure zasuyi ta surutu sosai akaina,


Kuma nasan duk wanda yaji zanyi aure babu wanda zasufi jin haushi irin dangin mamana, murmushi samha tayi sannan tace miyasa zasuji haushi ne? Hydar yace zaki gane sai nan gaba ya karasa maganar yana murmushi,


Samha tace miyasa bazan sani yanxun ba? Tabe bakinsa yayi sannan yace yanxun wurin yayi sauri ne, amma kiyi hakuri insha Allah zaki fahimcenki, kamar yanda kika fada cewa kinaji a jikinki gamonki dani alkairi, samha alkairi ne,


Ki saka natsuwa a jikinki, ki fahimceni duk runtsi duk wahala kiyi min alkawarin bazaki taba guduna ba, zuciyarki ta zamo mai adalci kuma ki zama mai tuna alkairi komai kankantar sa ki nisanta sharrin da wani yayi miki a zuciyarki kinji ko?


Murmushi samha tayi tare da jinjina kanta alamar gamsu, sannan tace sahib rainon dakamin ka koyawa zuciyata sanka karka canja halinka tunda ka sani zuciyata da ruhina na baka, bani da burin daya zarce inga harokaranka ma'ana farin ciki da annuri a fuskarka,


Murmushi hydar yayi mai ƙayatar da zuciyar samha, amma baiyi magana ba, yana kallonta, yadan dade idanuwansa na kan kyakkyawar fuskar samha, sannan yace samha sai magana na gaba, amma bansan yanda zaki dauki abun ba,


Samha tace miye? Murmushi hydar yayi da gefen bakinsa sannan yace kinga ban gama gyaran gidana ba, kuma banda kudi amma nayi wa hydar magana ya taimaka mana da wurin zama sai yace tunda bai cika zama gidan nan ba zamu iya zama kafin Allah ya bani iko inyi, dan Allah kiyi hakuri mu zauna anan kinji samha? Samha tace to sahib babu damuwa ubangiji ya baka iko hydar yace Amin,


Tashi yayi cikin farin ciki wata "yar rawa yayi tare yin wani dan tsalle yayi kasa a hankali tare da kwaso shoki, yanda yayi abun yayi mishi kyau sosai da yake yana da tsawo dan shoki tafi ma mai tsawo kyau, dariya samha tayi sosai, shi kuma da sauri yayi sama tare da cewa munje daurin aure sai mun dawo daga can zan wuce bazan dawo ta nan ba, samha tace to Allah ya tsare daga can hydar yace amin a daidai lokacin da yake sauka daga saman benen farlon da samha take yana hawa saman wanda zai sadashi da dakin dadyn sa,


Samha kuwa a hankali ta silale ta kwanta saman kujera tare da kara tuno rawar sahib dan abun ya burgeta sosai dariya tayi mai sauti sosai sannan tace wallahi sahib baijin magana murmushi tayi, sannan tace ikon Allah yau gani zanyi aure babu wani tsalle ko amarya ma babu mai kawo ni har na riga nazo gidan mijin dakai na, Allah sarki duniya, ko ina kawu bawan Allah shima fa yana sona kamar yanda sahib yake so na, hada rubuta suna na a kirjinsa, wayyo Allah kawu tun ina karama kake cemin 3 3 2, ni lokacin bana gane yaren,


Allah sarki kawu amma nasan idan kaji labarin aurena zakaji bakin ciki, dan gajeran tsaki samha tayi sannan tace canma kai ka sani munafikin Allah, ai ka cucuni kawu amma na yafe maka tunda ni na samu mijina zanyi aurena in huta abuna,


Hydar kuwa cikin farin ciki ya shiga daki jikin mirrow ya matsa da sauri ya cire fuskar ya dora a saman mirrow tare da cewa sahib zauna anan muje daurin aure mu dawo, cikin zumudi ya shige toilet babu dadewa yayo wanka ya fito, yana fitowa ya kira faruk tare da cewa kun tafi ne? Faruk yace Eh mana hydar yace to nima gani ina zuwa insha Allah, faruk yace kazo lafiya, da sauri hydar ya kashe wayarsa tare da ajiyewa a gefen gado,


Dariya kawai hydar yakeyi wani bangare na zuciyarsa kuma yana gargadinsa da lallai ya gama murnar da zumudin zaici uwarsa wurin samha, da sauri ya matsa jikin madubi ya kalli kansa murmushi yayi tare dayin magana a bayane yace haba da Allah babu wani damuwa insha Allah,


Saida ya gama shirinsa tsaf cikin manyan kaya ya hadu sosai yayi kyau na bada mamakiyos, masu karatu kuma basai na fada muku irin gayun hydar ba kawai ku tayani hango sa, 


Bayan ya gama yayi murmushi a hankali tare da fara rerero wakar Aashiqui2 mashup, jikin madubi ya matsa tare da murza hularsa sosai, niko nace zakaci gidanku duk ka gama wake waken,


Yana gamawa ta baya ya fice abinsa inda motoci suke jiransa, yana fita yaransa suka fara kirarasa tare da kara bashi kwarin gwuiwa, budewa hydar mota akayi ya tattara babbar rigarsa ya shige aka rufe,


Suma saura shiga motoci sukayi gaba daya motocin suka fice daga gidan sai wurin taron daurin aure, tun zuwa motocin hydar kallo ya koma sama wai shaho ya dauki giwa, nan fa wanda suka san hydar suka fara kokarin matsawa kusa dashi tare da mika hannu dan su gaisa,  kowa kokarinsa ya taba hydar yace ya gana dashi, masu fiddo waya suna daukar hotuna da hydar suna yi dan suje suce sun ganshi ido da ido suna yi, yaukam yaran hydar basuyi kokarin hana kowa ya rabi hydar ba saboda rana ce ta farin ciki a wurin sa,


Haka aka fara gabatar da taron daurin aure, tare da shedawa al'umma hydar ya biya sadakin auren sa da samha lakadan ba ajalan ba, bayan an gama gabatar da taron daurin auren hydar naseer hamza, da amaryarsa hafsat yusuf usman, an gama daura aure lafiya wuri ya cakume da hayani yayin da addu'ar zaman lafiya tare da masu addu'ar samun zuri'a dayyaba ya fara tashi a bakin al'umma,


Yayin da wasu mutane kuma suke ganin hydar yayi musu fadawa toti ruwa daya auri samha, wasu kuma suna ganin samha tayi babban nasara, kowa dai da abinda yake fada a bakinsa, bayan an kammala komai hydar da zugarsa suka nufo gida amma zuciyar hydar tana cikin fargaba dan baisan yanda zaman nasu zai kasance da samha ba,


Bayan su hydar sun dawo gida anan sukayi shagalinsu sosai shidai hydar baya ciki, yana can ya shige daki yana nemawa kansa mafita, yana kwance saman gado tunani barkatai a zuciyarsa wayarsa ta fara ringing,


Dubawa yayi ganin kanin dadynsa ne yake kiransa yasa shi tashi da sauri, daukar wayar yayi cikin girmamawa, tare da sallama suka gaisawa bayan gaisuwa yacewa hydar lallai ka nuna mana kai mai tarin dukiyane tunda ubanka ya mutu ya bar maka kaburin kudi yasa kayi aure ba tare da saninmu ba tunda kana ganin baka bukatar komai a wurinmu shi yasa kayi aure ba tare da saninmu ba,


Ajiyar zuciya hydar yayi sannan ya goge zufar data keto mishi a goshi sannan yace dady waye yace maka nayi aurene? Yace duniya ta fada ko kana tunanin yanda aka sanka zakayi abu a boyene? Murmushi hydar yayi sannan yace naje daurin aurene yau daya daga cikin yarana ne yayi aure shine ake ganin kamar nine, dady bayan nasan ka bani Asma'u ta za'ayi inyi aure?


Haka dai hydar yayi ta tsara dady shima dadyn da yake dabbal arab ne sai ya yadda tare da cewa haba ai nayi mamaki wallahi hydar dama nace gaskiya badai kaine ba, hydar yace gaskiya ne, haka dai sukaci gaba da fira daga baya sukayi sallama,


Bayan hydar ya gama waya da kanin dadynsa ya tashi tare da fara rage kayan jikinsa, babbar riga ya cire sannan ya cire takalmin kafarsa ya saka silipers ya nufi dakin samha,


Da sallama ya shiga dakin samha ta ansa tare da maido dubanta inda ake sallamar ganin hydar tayi dan haka ta jawo hijabi da sauri ta saka, fuskarsa a daure ya fara shiga cikin dakin a hankali harya isa bakin gadonta,


Zama yayi a gefen gado da sauri samha ta sauka kasa tare da gaishe shi cikin girmamawa ya ansa babu yabo ba fallasa, kallon samha yayi sannan yace zuwa nayi in miki Allah yasa alkairi, kan samha a kasa tace to mun gode sosai, hydar yace Allah ya baku zaman lafiya tace amin, 


Mikewa hydar yayi jiki a sabule zuciyarsa sai suya takeyi mishi cikin wani irin yanayi, dan yaso ace dagashi har samha yau duk suna cikin farin ciki baki dayansu, amma baida yanda zaiyi dole yayi a hankali,


Yana fita daga dakin tabi bayansa da kallo tana cewa shege munafiki, ta fara yatsina fuska tare da fara kwaikwayon maganar hydar tana tabe baki, _zowa nayi inyi miki Allah yasa alkairi, Allah ya baku zaman lafiya_ tsaki tayi sannan tace Ai Allah zai zaunar damu lafiya insha Allah,


Kuma bari sahib yazo in fada masa kada ka sake shigo mana dakinmu, ko kuma ka ware mana inda zamu rika zama mtswww,


Hydar yana komawa daki duk jinsa yayi wani haggunce, murmushi yayi sannan yace wai tana gani na ta saka hijabi, komi take boyewa? Ya karasa maganar yana dariya, kayan jikinsa ya cire bayan ya gama ya haye gado yayi kwanciyarsa,


Ita kuwa samha bayan ta gama iskancinta na kwaikwayon maganar hydar tashi tayi taje tayi wanka bayan ta gama ta shirya cikin kayan da sahib ya bata ta saka,


Bayan ta gama shirinta tsaff ta kalli kanta cikin madubi tace Allah sarki samha ke kuma taki rayuwar haka tazo? Kowace "yar gata idan tayi aure kawota akeyi gidan miji cikin farin ciki "yan uwa da abokan arziki suna murna tare da masu addu'ar zaman lafiya, amarya tana kuka ana bata hakuri ana lallashinta cikin so da kauna, hawaye ya gangaro daga idon samha, sannan tace niko ban samu hakan ba,


Matsawa tayi kusa da wayarta ta dauka sannan ta fara kiran sahib, cikin bacci hydar yaji ringing din wayarsa dan haka a gajiye ya mika hannunsa ya dauka cikin muryar bacci yayi magana cewa, samha? Cikin kuka samha tace sahib kana ina ne? Da sauri hydar ya tashi zaune tare da cewa miye kike kuka? Goge hawaye samha tayi sannan tace nidai na fasa auren nan don Allah, hydar yace miyasa kika fasa ne? Samha tayi shiru tare da kashe wayarta,


Jin samha ta kashe wayarta yasa hydar saukowa daga saman gado da sauri, yana cewa ke yarinya wallahi karya kike yi nine zaki yi ma wasa da zuciya? Tsaki yayi sannan ya shiga toilet yayo wanka yana fitowa ya shirya, yasa kananan kaya, bayan ya gama ya dauki fuska ya saka tare da cewa aiki fa ya sameni,


Dan gajeran tsaki yayi sannan ya fita ya nufi dakin samha, ita kuma tana zaune a gefen gado sai kuka tayi, da sauri sahib ya shiga cikin dakin tare da cewa waye yace miki amarya tana kuka ne? Samha tayi shiru murmushi yayi a daidai lokacin da yake zama kusa da ita, jawota cikin jikinsa yayi sosai, sannan yace wai miye kike kuka ne?


Samha tace nidai gaskiya na fasa auren nan, dariya yayi sannan yace har kin karaya ne? Yaci gaba da cewa haba keko? Ina ke ina rabuwa da sahib? Ai kinzo kenan babu koma matacce ya tafi lahira, ko anyi miki wani abu ne? Girgiza kai samha tayi alamar A, a, hydar yace to kiyi hakuri don Allah ki daina kuka kinji samha?


Cikin kuka samha tace to gaskiya mu tashi daga gidan nan, hydar yace miyasa zamu tashi? A daidai lokacin da yake daga samha daga jikinsa, hydar yaci gaba da cewa kinga ki rufamin asiri muyi zamanmu anan samha da kudin da zan kama mana haya kinga sai in kara in siyawa mamana magani tunda Allah ya taimakemu an bamu aron gida,


Cikin tausayawa hydar samha tace to, amma tana san ta fadawa sahib yace ma hydar ya daina zuwa mata daki kai tsaye gaskiya amma kuma bata san yanda sahib zai fassara abin ba,


Haka dai yayi ta rarrashin samha yana kwantar mata da hankalinta, saida yaga ta samu natsuwa sannan yace ta tashi suje farlo, amma samha tace a, a, yayi juyin duniya amma samha tace A, a, ita kuma saboda hydar taki fita,


Ganin bazata fita ba yasa shi kwanciya a hankali ya dora bayansa saman gado kafafawunsa yana kasa ya jawo samha kusa dashi ya riketa yana sauke ajiyar zuciya, wanda shi kadai yasan abinda yakeji a zuciyarsa, 


Samha tace har yanxun baka ga ahalina ba? Yace Umm samha tace to ina kawu? Hydar yayi banza bai bata amsa ba, samha taci gaba da cewa bawan Allah nasan yana can yana nemana yanxu, hydar baiyi magana ba, samha taci gaba da cewa sahib a kirjinsa ya rubuta suna na, da sauri hydar ya rufe idonsa, samha tace kaji sahib, hydar yace da Allah shiru mtsww, tabe baki samha tayi, hydar yace,


Waike baki san akwai babanci da lokacin da baki da aure da yanxun da kike da aure? Samha tayi shiru hydar yace to bakinki ya rufe akan maganar ko wane namiji na fada miki, batayi magana ba amma tana kallonsa, yace ke yanxun idan nazo ina miki maganar yan mata na zakiji dadi ne? Ko kuma idan nace su rike zuwa gidan nan fa, samha tace Allah ya baka hakuri, 


Dan gajeran tsaki yayi sannan ya mike, yana cewa ni jibi tafiya zanyi zanje kauye ganin mama, kuma idan na tafi zan dade ban dawo ba, da sauri samha ta mike tare da cewa ai sai muje tare ko? Hydar yace kinmanta babu wanda yasan na aureki ne? A haka kike so inje dake ince musu ke wace ce ta?


Gyara baki samha tayi amma bata ce komai ba, hydar yaci gaba da cewa to kinga hydar yayi mana babbar halacci a rayuwarmu samha kada ki kuskura kiyi masa rashin kunya kada ki batawa hydar rai dan wallahi ban hada hydar da kowa ba, idan har kika kuskusra na dawo yace min kin masa wani abu lallai zakiga fushi na, kinsan bacin raina? Ya tambayi samha,


Samha tace bansan bacin ranka ba kuma bana so in sani har karsen rayuwata, hydar yace yawwa sannan kuma kije ki rika share masa dakinsa duk abinda yace yana so kiyi masa kuma kada ki kuskura ki sabawa duk bukatarsa akanki, kinji ni ko?


Cikin hayani samha tace wannan ai haukane, inace yanxun nan ka gama fadamin cewa akwai banbanci tsakanin da, da kuma yanxun da nake da aure, in banda hauka taya za'ayi kace inje dakin katon banza dan iska inyi masa shara? Sai kace wata karuwa? Hydar yace bazaki gyara kalamanki akan hydar ba ko? Samha tace wallahi bazan gyara ba, kullum saina bata dan iska katon banza harnan dakina ya shigo saboda jahiline harda zamarmin a bakin gado,


Cikin daga murya sahib yace yaje ya zauna ai gadonsa ne ba naki bane? Ko kece kika siya masa ne? Itama cikin tsananin bacin rai tace gadonsan banza idan yana san gadon yazo ya cire banzan abinsa ko ance mishi idan ban kwana a gado ba zan mutune? To ko a gidan kawu a saman katifa nake kwana da sauri ta cire hijabinta tare da cewa kalli jikina nunamin a ina jikina ya lalace ko akwai banbanci kyau din jiki tsakanin mai kwana saman gado da wanda yake kwanciya a katifa Mtswww,


Sahib yace wannan can matsalarki ne ba tawa ba, nidai na fada miki kuma wallahi idan har a dakin nan zai kwana zanga idan kin isa ki hanashi ya kwana shida gidansa, cikin kuka samha tace to wallahi ajali zai kawoshi dan zaka kaga yanda zanci ubans......bata karasa ba sahib ya kasheta da mari ya kara marinta saida yayi mata ukku sannan ya barta, cike da zafin zuciya itama ta daga hannunta ta watsa mishi mari cikin bacin rai hydar ya rike hannunta sannan ya sake faffaska mata mari yana cewa ke baki da kunya kamarni zaki daga hannu ki mara? Cikin kuka samha tace kamar kaidi mi? Ni ina ruwana da girmanka, hydar yace ke ni zakimin rashin kunya?


Cikin kuka samha tace kai bakasan ko ni wace ce ba? Ko jin kunyar marina bakayi ba?  Ina matsayin matarka? Sahib yace ni ba mijinki bane amma dan rashin kunya kika daga hannu kika mareni? Yau kina cikin fushin Allah yarinya kin mari mijinki, goge hawayen idonta tayi sannan tace to idan nace bazan zauna dakai ba ai sai a goge zununbin hydar yace yanxun ma kin kara wani zunubin,


Tsaki yayi sannan ya fice daga dakin, yana fita samha taci gaba da masifa cewa in banda iskanci ansan gaskiya amma ana boye saboda san zuciya da tsabagen san abun duniya, komai hydar komai hydar sai kace wani babanka mtsww,


Cikin fushi hydar ya isa dakin shi, lallai samha ta raina shi, amma zaiyi maganin rashin kunyarta, Allah ya kaimu jibin lafiya, 


Tunda daga ranar da samha tayi fada da sahib bai sake zuwa ba, kuma idan ta buga mishi waya baya dauka, ta tura sako babu reply, kuma ta nemi shi a gidan bata ganshi ba, tayi "yan koke kokenta ta gaji, Ranar da sahib zaiyi tafiya kamar yanda ya fada mata, text kawai ya tura mata cewa,


_Samha kiyi hakuri da rashin daukar wayarki da nakeyi, kuma bana reply sakonki, kinsan ina da matsar ciwon zuciya maimakon ki kwantar min hankali shine kike so ki kasheni ko? To idan baki sona ina da masu kauna na, wannan dalilin yasa nayi nesa dake dan ni ina san farin cikinki tunda ke baza ki iyamin biyayya akan abinda nake so, kuma ga hydar nan amana idan kika mishi ko kallon banza na dawo ya fadamin wallahi zakiyi mamaki yanda zanmiki, na tafi saina dawo idan kinga dama kimin addu'a idan kuma kinga haggu kada kiyi,_


Lokacin da samha taga sakon da sauri ta fara kiran sahib amma sai taji "yar inyamura ta cikin waya tace ayi hakuri wannan waya a kashe take, tashi tayi ta fito da gudu cikin 360 ta sauko daga saman benen ta saukowa parlo taga hydar zaune a farlon saman kujera, wani irin kallo yayi mata sannan yace "yan mata ina zakije ne? Ko inda yake zaune bata kalla ba tayi harya fita, tana taba kofar tajita a rufe ta jijjigata amma taji bata budewa, a hankali ta dawo zata wuce hydar yace ke zonan, samha tayi kamar bataji shi ba, tana kokarin hawa sama ya tashi ya nufi wurin da sauri,


Tsayuwa samha tayi tare da daure fuska sosai sannan tace bazan yafe maka ba, dan iska kaine kasa mijina yayi fushi dani ta karasa maganar hawaye yana digowa daga idonta, murmushi hydar yayi sannan yakai hannunsa saman lips din samha yace kai bakin nan naki ya iya tsiwa,


Bige hannunsa samha tayi tare da cewa kadai ji kunya kuma kayi asara wallahi tana kokarin juyawa hydar ya fizgota ya riketa a jikinsa sannan yayi mata wani irin kallo, yace niba sahib bane danni bana daukar iskanci ninan dakika ganni dokewa nakeyi inyi wa yarinya duka da  bulala harsai tayi fitsarin wahala,


Samha tayi shiru hydar yace "yar rainin hankalu dan baki da kunya inajinki kina durawa uwata zagi dan babu manya a gidanku, daga yau idan na sake jin kin zageni saina lashe bakinki marar kunya kawai da Allah ni wuce muje ki mammatsa min jikina, ya karasa maganar cikin wata irin murya mai sa tsikar jiki ta tashi,


Yanda yakeyi mata wani irin kallo yasa ta sauke kanta kasa tana gunguni, hydar yace wuce muje, samha tace ni gaskiya ba "yar iska bace sai kace wata jaka inje in taba jikinki? Hydar yace ni babu wani ruwana ko kina iskanci ko bakyayi nidai jikina nake so kwai a shashsha famin, samha ta fizge hannunta daga hannu hydar da sauri ya rikota tare da cewa ke ki kiyayeni wallahi,


Shi dan iskan dazai tafi bai fada miki ba? Samha tace kaine dan iska ba mijina ba, dariya hydar yayi sosai sannan yace naji ni dan iskane ai kema sahib dan iska ne, samha tace gaka jibgegin dan iska, daure fuska hydar yayi sannan yace koni dan iska ne ko ba dan iska bane bai dameni ba muje, yaja hannunta yana sauka da ita daga saman benen,


Samha tana kwacewa amma ta kasa, ta fara tirjewa tana kuka daukarta hydar yayi sama har saman kujera sannan ya sauketa, gefen fuskarta yadan shafa sannan yace kina da kyau gaskiya lallai mijinki ya more, ga kyakkywar fata ya karasa maganar yana kashe mata ido,


Zama yayi sannan yace bari kiga inda zaki dan matsamin yana kokarin cire riga, da sauri samha ta mike tayi hanyar bene har tana faduwa dogon kallo hydar yayi mata wanda tana gudu amma yana zooming nata a idonsa harta shige daki ta rufe kofa da karfi, a hankali hydar ya kwanta saman kujera yana dariya,


Samha kuwa tana shiga daki ta fara kuka da gudu ta isa wurin wayarta ta dauka ta fara kiran wayar sahib dan ta fada mishi abinda hydar yayi mata wakar dai dayace ake rera mata cewa kiyi hakuri wayar a kashe take,


Saida samha tasha kukanta ta gaji, sannan ta ajiye wayar ta kwanta, bata dade da kwanciya ba bacci ya dauketa,


Saida samha tasha baccinta ta gaji sannan ta tashi tayi wanka, har yanxun bata daina kuka ba, harta shirya tasa kayanta kuka takeyi, saida tayi sallah isha'i sannan ta fita dan taci abinci tasan hydar yana masallaci,


Taje ta zauna saman dirning table ta fara cin abinci tana ci tana kuka, hydar ya shigo a haka ya sameta da wutsiyar idonshi ya kalleta ya wuce abinshi, 


Itama batayi magana ba taci gaba da cin abincinta, saida ta gama sannan ta tashi ta nufi dakinta, tana zuwa ta rufe,


Hydar kuwa yana zuwa ruwa ya watsa sannan yasa jallabiyarsa yayi kwanciyarsa abinsa, 


To kullum dai haka kowa yake rayuwarsa samha ta fito ta shige kicin ta dafa abinci taci ta koma daki shidai yana kallonta,  babu gaisuwa tsakaninsu idan ta fito dai yana kallonta da wutsiyar idonshi,


Yauma kamar kullum hydar yana kwance farlo saman kujera 3seater samha ta sauko, tazo zata wuce taji yana waya cewa kai sahib ka kiyayeni idan ba haka ba zan wulakanta ka, kaidin banza waye kai? Ni ka daina wani bani hakuri dan banaji kuma bazanyi ba, nasan dai nayi maka halacci amma ka zama butulu, kamarni kazo ka ajiye min yarinya karama a gidan dan ta raina min hankali bazata iya gaisheni ba? Ta sameni a wurin bazatamin sallama ba? Yau kwananka nawa da tafiya dakina yayi datti dakaina kake so na share ne?


Hydar ya lunfasa zuwa wani lokaci yace to ni babu wani abinda ya dameni ka kirata ka fada mata da kanka idan kuma ba haka saidai kasan inda zaka koma kuma na koreka daga aiki daga yau na fada maka, yana fadin haka ya kashe wayarsa sannan ya tashi yayi dakinsa,


Samha dake zaune tana cin abinci dakel ta hadiye lomar bakinta da sauri ta ajiye cokalin hannunta, ta tashi ta nufi daki da gudu, tana shiga taji wayarta na ringing, cikin tashin hankali ta nufi wurinta da sauri gabanta yana faduwa, tana daukar wayar ta fara cewa sahib don girman Allah kayi hakuri kada kawani bata ranka munji ma dadi daya koremu sai muyi tafiyarmu mu samu gidan zama, gidan banza gareshi gidan wofi don Allah ka rufa min asiri kada ka bari ya rabamu da makircin sa,


Sahib yace da Allah rufe min baki wannan ai daukar alhakine, samha tace wane irin daukar alhaki kuma? Sahib yace saiki bar mutum ya zauna dakinsa da datti duk abinda kikeyi kije ki share masa na fada miki, sannan kuma yana so kiyi masa tausa to kiyi masa duk yana cikin aikin da nake masa idan ba haka ba zaki hadu da fushin zuciyata, cikin sanyi samha tace kayi hakuri ai bansan dakin ba, maganar masach kuma sahib bai kamata ba,


Sahib yace nine nake aurenki ko kuwa? Samha tace kayi hakuri, tsaki yayi sannan yace tashi tsaye, tashi samha tayi babu musu, sahib yace jeki jikin kofa, tafiya tayi har takai bakin kofa, sahib yace bude, budewa samha tayi sannan yace taho idan kin tafi sai ki shigo ta haggu, shiga samha tayi sahib yace yi dama samha ta shiga ya sake cewa kara shiga dama, shiga tayi sannan yace sauko daga saman bene,


Sauka samha tayi sannan yace kinga wata kofa mai golding ko? Tace Eh yace bude zaki ga bene tana budewa sahib yace hawo, hawa samha tayi sannan yace kiyi ta tafi zaki ga wata glass kofa har dakin hydar, idan kinje ki bashi hakuri sannan kuma ki gyara mashi dakinsa kinji ko? Samha tace to sannan sahib ya akashe wayarsa,


Tunda samha ta tunkari wurin takejin kamshin "yan gayu harta shiga, da sallama ta shiga, hydar yana kwance saman gado daga shi sai gejeran wando, da sauri samha ta juya a zuciyarta tace lallai hydar kwallon dan iska ne,


Daga saman gado yace ya akayi ne? Ba tare data juyaba tace mijina yace inzo inyi maka shara kuma naga dakin baiyi datti ba, hydar yace ai basai yayi datti ake sharewa ba, samha tace to kuma yace in baka hakuri, hydar yace ai idan mijinki yamin laifi ba haka yake bani hakuri ba, zo nan, samha tace ai naga babu kaya a jikinka ne, hydar yace ina ruwanki da kayana ko rashin kayana? Kedai ba hakuri aka ce ki bani ba? Gidana ne nan dole in zauna yanda nake so, kema ban hanaki ki fito da daurin gaba ba,


Samha tace aini ba "yar iska bace, hydar yace niko kinga dan iska ne ni shi yasa ma nake zama da gajeran wando abuna, samha tace to Allah ya shiryeka, hydar yace kai ba amin ba a barni da iskancina nafi jin dadi, nidai bani hakuri kafin zuciyata ta fara tsimama,





*Meelat Musa ce*

[05/04 4:45 pm] Washa: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊



                 *SO*

     *MUGUN WASA*



       *{ Love is a bad game }*




*JAMEELA MUSA* { meelat musa }




*Story, Writing & Editing*

                   *by*

         *Meelat Musa*


*Jinjina gareki ummu farhana marubuciyar littafin "YAR HIJIRA gaskiya aikinki na kyau, masoya brilliant kada ku bari a baku labarin littafin yar hijara nemeshi da kanki domin kisha karatunki abunki kada ku kuskura REAL MAI DAMBU ta baku labari*


                  *SO*

      *MUGUN WASA*


*Dedicated to* 👇🏻

_Ramlat Abdulrahman real mai dambu_



*41-43*


Daga inda samha take tsaye tace shiru da Allah can, bayan ta lumfasa taci gaba da cewa dan uban zuciyar ta dade bata kumbura ba karewar tsimama, kaini harka fada min tsimamar zuciya da kangara?


To lallai ya kamata kasan labari akan mai girma samha, danni bana daukar shashanci kuma bana daukar iskanci, ka tashi kasa kayanka wallahi idan ba haka ba zan dauke ka hoto a haka in tona maka asiri na fada maka,


Dariya hydar yayi sosai sannan ya sauko daga saman gadon yayo tattaki zuwa gaban samha, da sauri ta rufe idanuwanta, hydar yace waike mai girma samha? A ina wani girma, bayan kuna kasana dake da mijinki duk a karkashin iko na kuke, baku da wani "yanci bare gata, baki ga saboda girmana da isa irin tawa ba yasa mijinki ya barmin ke dan in rike morewa abuna? Duk dama bakimin ba gaskiya naga idanuwanki irin na "yan chaina ne, basu da saurin daukar hankalin namiji ko kuwa kece baki iya sarrafasu ba?


Dakel samha ta hadiye miyan bakinta saboda bacin rai amma har yanxun idonta a rufe yake, hydar yaci gaba da cewa waike har kike wani cewa zaki daukeni hoto a haka dan ki tonamin asiri to daukarni mtsww, kawai dai nasan ba asirina kike so ki tona ba zakije ki ajiye a wayarki kina kallona kinajin dadi dan nayi imani sahib baida irin wannan kyakkyawan surar,


Cikin kuka samha tace tirr, tirr da hali irin naka kaiko baka dace da rayuwa ba, kaci baya kuma kayi asara, hydar yace waye yace miki naci baya? Kuma waye yace miki ni nayi asara? Ai duk abinda babbar giwa take dashi karama ma tana dashi duk kayan da babban jaki ya dauka karami ma zai dauka saboda dama dukansu dan wahala akayosu, kinga kamarke mijinki yarona ne tunda yana kasana dake dashi duk kuna a karkashi ikona, kimin shara ki dafamin abinci kuma ki bani a baki idan naga dama har wanka sai ince kimin kuma idan dare yayi a shinfida daya zan rika kwana dake ni kuma idan wata yayi inba sahib albashi mai yawa kinga daga nan idan ya gaji da samun kudin kuma ya gaji da ina hutawa dake sai ya gina gida ya tashi ya bani wuri,


Maza maza a cire hijabi a fara gyaramin gado, cikin kuka samha tayi bakin gado ba tare data cire hijabinta ba kuma batayi magana ba ta fara aiki, hydar yace ke wallahi baza kimin aiki da hijabi ba sai kin cire, tsaki samha tayi cikin daga murya tace bazan cire ba dan isk,........hydar yace wallahi duk ranar da gigi yasa kika zageni saina cire miki kaya nafada miki, idanuwa samha ta zaro sosai amma batace komai ba,


Matsawa hydar yayi kusa da samha sannan ya fara kokarin cire mata hijabi, jin hydar yace zai zindireta yasa batayi magana ba ta cire hijabinta da kanta, ta ajiye a gefe, taci gaba da aiki tana gyara gado tana tsinewa sahib albarka a ranta, shi dama hydar haka yake so yaga ya cusa kiyayyar sahib a ran samha, ita kuwa samha gani takeyi kwata kwata baiyi mata adalci ba taya za'ayi tana matsayin matarsa amma ya barta a gidan hydar saboda san abun duniya, sai kuka samha takeyi tana aiki shi kuma hydar ya jingina da mirrow sai dariya yakeyi a ransa,


Saida samha ta gyara dakin fes ta goge shi, sannan hydar yace saura farlo har yanxun gajeran wando ne a jikinsa, shine a gaba yana wata tafiyar iskanci, kan samha a kasa har suka isa farlo hydar yace duk kujerun nan sai an daga su an share an goge, batayi magana ba ta fara, shi kuma yana daga dirning area yana hangenta yana dariya a ransa,


Haka samha tayi ta jijjibar kujeru tana daga su kamar wata katafila saita dage ta share ta goge sannan ta mayar, haka tayi ta yi harta gama gyarawa, wurin hydar taje cikin girmamawa ta durkusa har kasa sannan tace na gama,


Yace maza a dafo abinci ba tare daya kalli inda take ba, a hankali samha ta mike ta nufi kicin saida ta gyara kicin din sannan ta dora girki, tana kicin tana aiki hydar yace a dafo min tea, samha tace to,


Ruwan zafin dake cikin flarks ta dauka ta juye a tukunya ta dafa shi, sannan ta juye a kofi takai ma hydar, kallonta yayi fuska a daure yace wannan tea din? Samha tace Eh, hydar yace har ya tafasa kenan ko? Samha tace ai na dazu ne na dimama, cikin daga murya hydar yace waye yace miki a dumama tea? Idan har aka dumama tea ya zama guba wato kasheni zakiyi ko?


Yi yayi kamar zai watsa mata ruwan zafin da sauri ta rufe idonta tare da kauda kanta gefe ta dora hannunta saman fuskarta, murmushi yayi sannan yace daukarshi ki shanye, cikin kuka samha tace ai yanxun nan kace idan an dunduma tea ya zama guba so kakeyi insha in mutu?


Hydar yace baki san mutu ne? Cikin kuka samha tace kayi hakuri don girman Allah, hydar yace kina so inyi hakuri ko? Samha tace Eh hydar yace to sai kinmin kiss saiki zaba ko kiss ko shanye tea sauri sauri saurii,


Tsaki samha tayi sannan ta mike ta dauki tea din ta kafa kanta duk zafinsa saida ta shanyeshi sannan ta daga kofin ta saddashi kasa alamar babu komai a ciki, dan zaro idanuwa hydar yayi a ransa yace wato yarinyar nan bazata canja ba, tabe bakinsa yayi a ransa yace wato gara ta mutu da ta taba wanda ba maharraminta ba, murmushi yayi a bayyane ita kuma samha tuni ta koma kicin taci gaba da aikinta,


Saida ta gama dafa abincin ta sake dafa tea din sannan ta juyo komai tazo ta ajiye a gaban hydar ta koma ta gyara inda ta bata a kicin, sannan tazo zata wuce hydar yace ina kuma zakije? Tace zanje in huta ne, hydar yace inake ina hutawa yarinya? Saura aikinki ukku bani abinci wanke min motoci sai kuma kiyimin wanka,


Da sauri samha ta duka saman gwuyawunta tace don girman Allah ka soke maganar wanka ka rufamin asiri don Allah, hydar yace wallahi bazan rufa ba, ni in rufa miki asiri sai kace wani banza? Nifa ba laifina bane laifin sahib ne shine ya hadani dake, cikin kuka samha ta matsa kusa da hydar ta rike kafafuwansa tana kuka mai tada hankali tana bawa hydar hakuri,


Amma da yake hydar tantirin dan iskane ko kallonta baiyi ba, ita kuma sai kare yage baki takeyi kamar anyi wa kura wurgi da nama, da wutsiyar idon sa ya kalleta sannan yace tashi, jikinta na rawa ta tashi yace jeki ki wanko hannunki, da sauri ta matsa ta wanke hannunta ta dawo, kallonta yayi sannan yace zauna, zama tayi babu musu hydar yace kince bazakimin wanka ba ko? Samha tace Eh, hydar yace to bani abincin inci da sauri ta dauki cokali girgiza kansa yayi alamar A,a, sannan yace da hannu zaki bani,


Hannunta tasa ta fara ibar abinci tana bashi a baki cikin iskanci yake hada hannun da lips dinshi yana dan rike hannun cikin kware ma iskanci yanda yakeyin abun yasa samha taji jikinta yana rawa, shi kuma sai kara daddagewa yakeyi yana yi cikin salon iskanci,


Haka dai samha taci gaba da bashi abincin yana ci, harya gama, sannan yace to jeki, jiki a sanyaye samha ta mike hydar ya gyara zaman sannan yace kullum haka zaki rika min kinjinko? Samha tace to, tana fadin haka ta wuce da gudu ta nufi daki, hydar kuwa dariya yayi mai isarsa sannan shima ya tashi ya nufi nasa dakin,


Samha kuwa tana zuwa daki wayrta ta dauka ta fara kiran sahib, dariya hydar yayi sannan ya dauka, cikin kuka samha tace wallahi sahib ka bani mamaki, banji dadin abinda kamin ba, cikin lallashi hydar yace samha kiyi hakuri kiyi biyayya wa mijinki ba'a sabawa idan ba haka ba zakici da wuta balbal,


Cike da masifa samha tace da Allah rufemin baki kaima sai Allah ya babbaka da wutar mai zafi koda ban zuwa  isilimiya naji mai wa,azi yana cewa babu biyayya wa miji a cikin sabon Allah sai ka dauki dirjejen kato ka hadani zama,


Sahib yace kiyi hakuri samha ki kwantar da hankalinki kudi kawai zamu tara muyi hafiyarmu, samha tace innalillahi wa'inna ilaihir raji,un amma sahib baka tsoron Allah duk yanda hydar ya yadda dakai zakayi mishi butulci, kuma shine dani zaka nemi kudin? Sahib yace to miye a ciki? Kawai ki rika wanka kina saka matsatstsun kaya kina fitowa kije dakin hydar ki gaisheshi ki mishi duk abinda yake so shima zaiji dadi kinga daga haka sai ya kara mana kudi masu yawa, in taimakawa mahaifiyata in taimaki rayuwarmu samha kuma tunda kin iya sata hydar yana da kudade na tashin hankali kuma yanayin wawiyar ajiye ki rika sace mana kina tara mana, 


Samha tace Allah ya sawake aini da nasan zanci gaba da sata da bazan aureka ba, amma tunda abin yazo da haka kaima baka san baka iya rikeni ba saida ka aureni abinda nake so dakai ni bazan iya zunubi biyu ba kayi hakuri ka sawwake min aurenka akaina,


Sahib yace to sai mi? Ni dama an fada miki sanki nakeyi ne? Dan naga kina nemin mutuwa akaina na taimaki zuciyarki amma zakimin butulci banza sakara wanda bata san arziki ba, samha ta ciko bakinta ta dirkakawa uwar sahib zagi amma sai taji ya kashe wayarsa,


Samha tace lallai namiji dan iskane, amma sahib dan iskane amma zanyi maganinsa, insha Allah, hydar kuwa kashe wayar yayi baki daya sannan yaje yayi wanka yayi alwallah yana fitowa kaya ya saka ya nufi masallaci,


Bayan hydar ya dawo masallaci dakinsa ya wuce abunsa dan duk yaransa babu ko daya yace suje sai ya gama da samha zai nemesu dan bazai yuwu ba kamar shi aji mace tana mishi rashin mutunci duk da sunsan komai su kuma a tunaninsu mai gida zai more amarcinsa ne,


Da safe samha kasa tashi tayi saboda wahalar da hydar ya bata ta share share, duk gabobin jikinta ciwo suke mata tana kwance cikin wahala idanuwanta sai digar hawaye sukeyi tun ba'aje ko ina ba, sahib ya fara mata wulakanci hada yi mata gori, sai yanxun ta tuna da maganarsa cewa samha nifa da wasa nake sanki, kara goge hawayen idonta tayi sannan ta sauka a hankali daga saman gado ta nufi toilet, sai yanxun tayi nadamar sanin sahib,


Saida ta gama wanka ta fito ta saka bakar riga mai kyau ta yafa gyalen tayi kyau sosai, dan hydar yace ta daina zuwa mishi da hijabi idan ba haka ba zata ga yanda zaiyi mata, dan yace duk ranar daya sake ganinta da hijabi sai yasa ta tayi mishi wanka kuma ya rantse idan ba wanka ba kwanciya a gado daya, samha dai tana cikin damuwa,


Dakin hydar ta nufa, a bakin kofa ta tsaya sannan tayi sallama hydar ya amsa tare da cewa shigo, a hankali samha ta shiga saida takai bakin gadonsa sannan ta zube saman gwuyawunta ta gaishe shi, ansawa hydar yayi sannan yace mi akayi miki jiya kike zage zage? Murmushin karfin hali samha tayi kanta a kasa sannan tace ba komai, hydar yace sahib ya bata miki raine? Samha tace kai haba a,a, babu wani abinda yamin, kallonta hydar yayi sosai duk ta bashi tausayi kana ganin samha kasan tana tare da damuwa, cikin sigar lallashi hydar yace ko inkai wurin training ne? Samha tace A, a, hydar yace to kina san wani abu ne? Hawayen da take boyewa ya zubo mata daga idonta cikin kuka tace nidai sahib zaka taimakamin kace ya dawo don Allah,


Cikin tausayawa hydar yace mi zaiyi miki ne? Samha tace kawai ina san ganin sa ne, hydar yace ke kice mishi ya dawo da kanki mana, samha tace A, a nidai ka taimakamin don Allah, hydar yace to zan taimaka miki amma bisa sharadi daya samha tace tom,


Hydar yace to matso, a hankali samha ta matsa gyara kwanciya hydar yayi sannan yasa hannunsa biyu ya tallabo fuskar samha daidai bakin ya matsa da nashi yana kokarin hada bakinta da nashi da sauri samha tace A'uzubillahi, dariya hydar yayi sannan yace nine kike cewa A'uzubillahi? Kamar kinga shaidani, to naji  shikenan tunda kince muje ki bani abinci,


Saukowa yayi daga saman gadon itama samha mikewa tayi itace a gaba hydar yana bayanta suna tafiya, hydar yace haba samha ke ko "yar yangar nan ta mata bazakiyi ba? Shiru samha tayi dan tasan tana iyayin magana hydar ya taba mata jiki,


Hydar yace bakiji ina magana ne? Cikin girmamawa ta juyo tace kayi hakuri ni ban iya ba, hydar yace shi yasa sahib yake miki wulakanci baki san yanda ake kula da miji ba kina tafiya kina tada kura, samha tace ai ko ruwa ka watsa sai makiyi yace ka tasar masa da kura, hydar yace nine makiyin ki samha? Tace Eh mana in banda kiyayyar anan ina wani kura yake zakace ina tafiya ina baza kura?,


Hydar yace to badai zaki gyara kalaminki ba a kaina ko? Hakuri samha ta bashi baiyi magana ba ya wuce ya sauka kasa, itama bin bayanshi tayi ta sauka, shi ya zauna ita kuma ta wuce kicin danyin girki,


Hydar kwanciya yayi yana jiran samha ta gama abinci yaci, wayarsa ya dauka ya kira faruk suka gaisa, faruk yace ina amarya? Dariya hydar yayi sannan yace wace amarya tana nan ta ɓaddamin lissafi ni nama fara gajiya wallahi,


Faruk yace kada ka gaji kayi hakuri, dan gajeran tsaki hydar yayi sannan yace ni bana san wani abu ya shiga tsakanina da samha harsai ta yadda tana sona, kuma ko naje a matsayin sahib babu abinda zan mata saina tsaida mata hankali wuri daya sannan dan idan na birkice mata kwalwa nima burkutamin zuciya zatayi wallahi dan tana iya gudu kuma kasan bazan iya gano ta ba wallahi,


Faruk yace to Allah dai ya taimaka hydar yace amin , ganin samha tana tahowa yasa hydar cewa sahib ka dawo hakanan matar ka tana sanin ganinka, dariya faruk yayi sannan ya kashe wayarsa dan ya gane inda zance hydar ya nufa,


Samha ta matso gaban hydar ta tsugunna ta dafa kujerar da yake kwance kallonta yayi sannan yace miye? Kallonshi samha tayi amma itama taki tayi magana,


Tsawa hydar ya daka mata tare da cewa miye zaki wani zo kiyi ta kallona kamar wani sa'arki? Bata fuska samha tayi kamar zatayi kuka, hydar yace miye wai? Samha tace nidai gaskiya bana san girki, harararta hydar yayi sannan yace nine zan rika dafa miki abinci dan gayu?


Da Allah tashi ni inajin yunwa zaki zo ki wani ce wai bazaki dafa abinci ba, tsaki samha tayi sannan ta tashi ta nufi kicin cikin sauri tana gunguni, hydar yace ki zageni dakyau zan kamaki wallahi, tana zuwa kicin din indomie ta dafa sai mita takeyi,


Bayan ta gama ta zuba a filet ta taho saida tazo gaban hydar ta dangwarar da abinci tana cewa ni wallahi na gaji da dafa ma kato abinci, hydar yace ni kuma ban gaji ba, wanko hannu kizo ki bani da sauri,


Da fushi tayi kicin taje ta wanke hannunta ta dawo zama tayi kusa da hydar sannan ta dauki filet din ta ajiye a tsakiyarsu ta fara bashi kamar dai yanda ya saba haka yauma yakeyi mata, saida ta gama bashi hydar ya rike hannun yana lasarshi cikin kwarewa yanda yakeyin abun yasa samha taji tsikar jikinta yana tashi ga wani irin kallo da yakeyi mata, murmushi hydar yayi gani samha tana cikin wani hali a hankali ya matsa kusa da ita ya kara jawota kusa dashi hannun daya lasa ya saka a bakin samha yace mata kema kiyi a bakinki kiji hannunki akwai dadi yanda yayi maganar ne yasa jikin samha mutu murus kamar an watsa ma wuta ruwan sanyi,


Ba musu samha ta farayi kamar yanda hydar yayi mata shi kuma ya kara riketa sosai a jikinsa yana yin wani irin nunfashi mai tada hankali, jikin samha ya fara karma murmushi hydar yayi sannan yace miye? Daidai kunnenta yayi maganar cikin yanayin gajiya yayi da wata irin murya a hankali samha ta sauke ajiyar zuciya, hydar yace mi yasa kike san sahib ya dawo? Ba gani ba, zan miki duk abinda kike so ki daina tunanin sahib a ranki bazai dawo ba har abada,


Samha tana san tayi magana amma ta kasa, kwanciya hydar yayi sannan ya dagota ya dorata saman kirjinsa yayi mata kyakyawan riko yaci gaba da jagwalgwalata amma samha ta kasa magana kuma ta kasa hana hydar, murmushi yayi sannan yace bude idonki, a hankali samha ta bude idonta tana kallon hydar wasa ya farayi da idonsa cikin wani irin yanayi wanda ba samha ba ni kaina bansan shi ba, tunda yasan idonshi yana daukar hankalin samha, yana mata kallon yana murmushi da gefen bakinsa, a hankali ta sake rufe idonta hydar yace bude ki kalleni bude idonta tayi tana kallon hydar bude bakinsa yayi da niyar hada bakinsa da nata innalillihi wa"ina ilaihir raji'un samha tace da sauri ta sauka daga saman jikin hydar da sauri,


Dariya hydar yayi sannan ya tashi dakel ya zauna saman kujera, samha tana kokarin guduwa ya riko hannunta, wayarshi ya mike mata sannan yace kallarki da Allah, idanuwa samha ta zaro lallai hydar dan iskane wato duk abin nan daukarsu yayi, cikin kuka samha tace din girman Allah ka goge, hydar ya anshi wayar sannan ya mike yace ba kince zaki daukeni da gajeran wando ba? Ni kuma zan watsashi a whatsapp facebuk da Instagram duk in balbada ki kowa dakowa ya gani kuma ince matar aurece ke kike neman ubangidan mijinki, ya karasa maganar yana bude idanuwansa, cikin kuka samha tace don girman Allah kayi hakuri ka goge,


Hydar yace wallahi bazan goge ba bake kinajin mai wayau bace? Samha tace dan girman Allah ka rufamin asiri, hydar yace kina so in rufa miki asiri? Cikin kuka samha tace Eh, daga hannunwansa sama yayi sannan yace to zoki rungumeni, cikin kuka samha ta matsa kusa da hydar ta rungumeshi hydar yace sosai zaki rikeni ba kadan ba, ta kara rikeshi sosai hydar yace to kice kina so na, cikin kuka samha tace ina sanka, hydar yace kice har abada zaki daina san sahib samha tayi shiru hydar yace uhum ke nake jira idan baki fada ba zan fara posting fa, cikin kuka samha tace gaskiya nidai ina san sahib sosai kuma ina kewarsa,


Hydar yace to sakarmin jiki bari ki gani a gaban idonki zan fara turawa cikin kuka mai yawa samha tace don Allah ka rufamin asiri hydar yace to muje dakina ki bani hakuri, sakin hydar tayi yayi gaba tabi bayanshi tana kuka shi kuma sai dariya yakeyi a ransa,


A dakin hydar wanka yasa samha tayi bayan tayi wanka ya bata kaya ta saka, shima wanka yayi bayan ya fito ya saka bakar jallabiya kuma tayi mishi kyau sosai kallon samha yayi sannan yace kiyi sallah zanje masallaci yanxun nan zan dawo, samha tace to fita hydar yayi daga dakin da sauri ya sauka bene yana farin ciki sai iskanci yakeyi, ita kuwa samha tana sallah tana kuka tana tsinewa sahib albarka duk shine yaja mata wannan bala'i,


Bayan hydar ya dawo saida ya kwanta saman gado sannan yace ma samha tazo su kwanta, cikin shashekar kuka tace nidai zanje dakina ne, hydar yace okey muje tare to, samha tace nidai bazan kwana wuri daya dakai ba, hydar yace miyasa? Nifa ba dan iska bane gajeran wando kadai nake sakawa babu wani abunda zan miki wallahi kawai rike zanyi inji dadi, ya karasa maganar yana rungume hannuwansa yana dariya tare da daga kafafuwansa sama yana ma samha gwalo,


Tashi samha tayi zata fita daga dakin hydar yace wallahi idan kika fita zan miki Allah ya isa, a bayyane samha ta maimata Allah ya isa? Ba tare data waiwayo ba, Hydar yace sosai kuma wallahi bazan yafe miki ba zakiyi bacci da tsinuwar mala'iku akan zonan samha, tsaki tayi sannan tayi haryar fita da sauri hydar ya sauko daga saman gado yaje ya rikota, 


Samha zatayi magana hydar ya dora dan yatsansa saman bakinshi yace shittttt yana dan bude idonshi hawaye kwance a idonsa, samha ta kara kallon hydar sosai amma batayi magana ba, hydar yace nifa na bawa sahib kudi masu yawa dan haka ya yadda dani yace ya barmin ke inyi yanda nake so dake amma tunda ni bana neman mata kawai zandan rikeki muyi bacci don Allah,


Taho taho taho yana maganar yana dan girgiza jikinsa, tsaki samha tayi sannan tace sai kayi ta abu kamar karamin yaro, hydar yace idan ina gabanki ni jaririne nidai zo mu kwanta, agogo ya kalla sannan yace lokacin baccina yana wucewa nidai taho,


Cire hijabin jikin samha yayi ya yadar a tsakar dakin yajata har saman gado, saida ta fara hawa sannan hydar ya hau jikinsa sai kyarma yakeyi, kuji iskanci bargo yaja ya lullubesu sannan ya rungumeta sosai ya dora kafarsa saman jikinta yana cewa yawwa muyi baccinmu za'ayi ta rubuta miki lada har safiya ta waye, cikin kuka samha tace ina dai ja ana dirkakamin zunubi hydar yace danma baki bari na taba nan ba, yakai hannunsa daidai kirjinta yace dasai kinfi samun zumubin da yawa, janye hannunsa samha tayi murmushi yayi sannan yace a hakanma na gode Allah yayi miki albarka,


Samha sai kuka takeyi shi kuwa hydar baccinsa yakeyi cikin kwanciyar hankali da natsuwa baima san samha tana kuka ba, bude bargon samha tayi tana kallon kyakyawar fuskar hydar gaskiya hydar yana da kyau gashi dan gayu kuma sai yayi tayin abu mai kyau da shiga rai, murmushi tayi sannan ta rufe idonta, a ranta tace duk macen data auri hydar ta more dan hydar komai nasa yana daukar hankalin mace, murmushi tayi zuciyarta na hasko mata idan hydar yana shagwaba yanamai kyau, goge hawayen idonta tayi a bayyane tace sahib bakayi wa zuciyata adalci ba, murmushi hydar yayi dan duk abinda samha take yanaji kuma yana kallonta dan tunda ta yaye bargo idonsa biyu budewar datayi ne yasa ya farka amma bai bude idonsa ba,


Dayaji samha tace sahib bakayi wa zuciyata adalci ba, bayan hydar yayi murmushi yace waye yace baiyi miki adalci ba amma har yanxun idansa a rufe, cikin kuka samha tace don Allah kace ya dawo hakanan hydar yace zai dawo sai kinyi ciki amma, cikin tashi hankali samha ta zaro idanuwa har yanxun idon hydar a rufe yake, amma sai yace ki gama zazzaro idon cikin zan rirkaka miki nasan idan sahib ya dawo zaice nayi kokari ya kara maganar yana murmushi,


Samha tace aika dan iska ne, hydar yace Ey wallahi kuma nima shi yasa nake sanki, samha tace to an fada maka nima "yar iskane kamar ka? Hydar yace ko daya wallahi keba "yar iska bane amma ni zan koya miki, daga haka hydar bai sake magana ba, haka samha ta gaji da tunani barkatai har bacci ya dauketa,


Karfe 1:02am hydar ya farka saida ya gyarawa samha kwanciyarta ya dire daga saman gado toilet ya nufa alwalla yayo sannan yazo ya fara sallah kamar yanda ya saba, saida aka kira sallah asuba ya tashi samha tayi sallah shi kuma ya wuce masallaci,


Bayan samha ta gama sallah tana zaune saman abin sallah hannunta a sama 🙏🏻 tana addu'a Allah ya dawo mata da sahib lafiya Allah ya fidda shedan daga zuciyarta a daidai lokacin da hydar ya shigo yana cewa ba amin ba,


Juyowa samha tayi ta kalli hydar sannan tace ina ruwanka da addu'a ta ne? Hydar yace niko nake da ruwa da addu'ar ai idan har naga hannunki a sama kina addu'a ne Allah ya tsinewa hydar Albarka kuma idan har na tsine na lalace saikinfi kowa bakin ciki da tashin hankali wallahi tunda hydar bai da mama baida baba banda yaya banda kani banda budurwar banda ɗa banda jiki, ke kuwa hydar shine ginshikin rayuwarki wallahi idan na lalace saikinfi kowa shiga matsala, samha tace toni ina ruwana da kirkinki?  Ka hydar yace to kici gaba dayi a daidai lokacin daya ke kwanciya saman gado,


Saida samha ta gama addu'u'oin ta sannan ta tashi ta nufi toilet da sauri hydar ya tashi shima ya bita, tana shiga toilet taga hydar ya shigo, samha tace yi hakuri bara in fita, hydar yace A, a ni wanka zanyi ma kema kawai kiyi abinda zakiyi kowa yayi hidimarsa babu ruwan kowa da kowa, samha tace to aini na fasa abinda zanyi hydar yace bazai yuwu ba, tunda kin shigo sai kinyi,


Samha tace nikam na gaji gaskiya hydar yace niko ban gaji a daidai lokacin daya kara matsawa kusa da ita ya matseta jikin bango yace sahib fa ya raina miki hankali yana can yayi aure kuma karya yake miki baida wata mama, ashe har kudi kika bashi yayi ma maman sa magani? Da kudin yaje yayi aure ya barki anan a matsayin baiwa jira kiji abinda yace, jiya mukayi waya dashi nayi miki recording, samha tace sahib din? Hydar yace da kansa mana bakiga ya raina miki hankali ba kullum idan yayi tafiya yana ce miki wai baya da network a garin karya fa yakeyi kashe wayarsa yakeyi saboda kada ki kirashi a gaban matarsa, baki ga kullum sai nayi waya dashi ba?


Shiru samha tayi tana nazari lallai fa haka ne, amma sahib yakai dan iska shine yayi aure bai gaya mata ba? Ita zai dauka mahaukaciya? Shi yasa daya tashi aurensu yace bazai fadawa kowa ba? Hawaye ya zubo daga idon samha, hydar yace ki daina kuka samha nidai nasan baki so na, shi yasa zakiga duk abinda nake fada karya ne ga reacord in kiji ko kuma ki kirawo sahib da kanki, cikin fushi samha ta wuce daga kusa da hydar tayi dakinta da gudu tana kuka,


Dariya hydar yayi sannan yaje ya dauki wayar ya kunna ta da sauri, yana budewa kiran samha yana shigowa, samha tace sahib miyasa yanxun ka daina so na? Ko nayi maka wani abune? Kwanciya hydar yayi sannan yace gaskiya samha kiyi hakuri saida na aureki naga nayi hauka sosai amma kiyi hakuri, samha ta sassauta muryarta sannan tace to sahib mi nayi maka don Allah hydar yace to naga kina so kimin wasa da zuciya shine dalilin daya sa na hakura dake, zaki iya kama gabanki ni gaskiya bana sanki,


Samha tace haba sahib wannan kalmar baza ka daina fadinta a bakin ba? Da Allah kayi hakuri idan na tafi yanxun ina zanje? Bayan kamin alkawari zaka nemo min ahalina kace kaine zaka sama min farin ciki, kuma kasan mutane suna jirana a waje su kasheni saboda m card a gaban idonka mutuwa tayi wasan kura da raina aka jefoni daga saman bene sahib ka taimakeni don Allah don annabi kayi hakuri ka zauna dani,


Murmushi hydar yayi sannan yace gaskiya kiyi hakuri banda kudin dazan iya rikeki ba, amma idan zakiyi kokari ki sato mana a wurin hydar to, samha tace gaskiya bazan iya ma hydar sata ba, amma zan tambayeshi idan ya yadda ina mishi wanki da guga da wanki motoci sai in tara kudin, hydar yace miyasa bazakiyi ma hydar sata ba?


Samha tace ya bani tausayi yace min baida kowa a duniya shi daya ne, sahib yace kenan kin fara san hydar ko? To koshi zaki aura ne? Samha tace ai gara in fada daga saman bene in mutu da in auri hydar, hydar yace ai tausayi yana cikin so kinga kin fara kamuwa da san hydar samha tace hydar din banza, murmushi yayi sannan yace to kodai ma bana banza bane idan ya daukeki aikin to idan bai daukeki ba kina iya kama gabanki sai anjima yana fadin haka ya kashe wayar gaba daya sannan yaje ya ajiye a inda yake boyewa,


Samha kuwa tana tsaye har yanxun tana jin tashin hankali a zuciyarta sai wani barazar fitowa takeyi daga mazauninta, kuka takeyi sosai tare da cewa lallai na yadda sahib ba da gaske yake so na ba, wani irin ihu samha tayi tare da faduwa kasa somammiya, hydar jin ihun samha yasa shi tashi da gudu ya nufi dakinta,


Cikin kuka hydar ya shige cikin dakin gaba daya, inda samha take kwance a kasa ya dagota fuskarta ga  hawaye dake fita daga gefen idonta, daga ta yayi ya dorata saman gado a gigice ya dauko ruwa a frig ya fara yayyafa mata, ajiyar zuciya samha tayi tare da bude idonta, cikin kuka samha ta kalli hydar sannan tace hydar mutuwa zanyi, hydar yana kuka yace ki rufa min asiri samha kada ki mutu kafin ki mutu nine zan fara mutu,


Samha tace kai baka da budurwa kaga ka huta da bacin rai ni a yanxun na zabi mutuwa akan rayuwa, cikin kuka hydar yace samha bazaki mutu ba, fadamin duk abinda kike so a duniya zan miki wallahi, murmushir karfin hali samha tayi sannan tace sahib nake so, hydar yace idan sahib yazo zaki yi farin ciki? samha tace Eh, hydar yace to sahib zai dawo insha Allah yaushe kike san ganin sa? samha tace gobe goben nan, hydar yace gobe batayi miki nisa ba? Samha tace idan ma zaizo yanxun yanxun ina so, murmushi hydar yayi sannan ya kwantar da kansa a kirjin samha yana kuka mai tada hankali lallai idan ya sake zama a matsayin sahib babu ranar da samha zata so shi, kodai ya fada mata shine sahib? amma yanda samha take haka idan tasan shine sahib zuciyarta zata tarwatse,


Hydar kuka samha kuka babu mai ba wani hakuri, ita tana kukan sahib shi kuma yana kukan haukan dayayi tun farko yazo a matsayin sahib, saida hydar yayi kuka har kansa yayi ciwo sannan ya sauke kansa daga jikin samha yace taje tayi wanka zaiyi wanka shima,


Dukansu wanka sukayi hydar ya zuge cikin kananan kaya masu kyau sai kamshi yakeyi, kayan da samha zata sa ya taho dasu ya kawo mata yace ta saka ta sameshi waje, fita yayi ya fita waje,


Yana fita ta saka kayan ta fita da sauri, a waje ta sami hydar tsaye a jikin mota sai murmushi yakeyi wayarsa ya ciro yana cewa bara in miki hoto kinga yanda kika hadu? Yanda yayi abunne yasa samha tayi murmushi tare da gyara gyalen jikinta tace kayi mai kyau don Allah ka turawa sahib, murmushi hydar yayi sannan ya fara daukarta sai canja style takeyi, hydar yace to cire gyalen ki gani nasan zaifi ji dadi idan ya ganki babu gyale, cire gyale tayi ta bawa hydar ya rike, wallahi hydar dan iska ne, sai sawa yake samha tana ta wani murgudewa yana mata hoto,


Bayan ya gama daukarta ya matsa kusa da ita ya dan rungumeta yana cewa muyi tare kinga idan ya gani zaiji dadi yace muna zaman lafiya ko? Samha tace to, kallonta hydar yayi sannan yace matso nan ki gani a jikinsa ya nuna mata yace ta dan kwanto, haka yayi ta sawa tana hayewa jikinsa da sunan hoto, saida ya gama ya nuna mata hotunan sunyi kyau sosai sannan hydar tace to rungumeni sannan in turawa sahib,


Daga hannayensa yayi sama, samha ta rungumeshi tana sauke ajiyar zuciya hydar yace rikeni sosai, kara rikeshi samha tayi hydar yace saifa kinyi da gaske kara rikeni da kyau, samha tace na gaji, sauko hannuwansa yayi sannan yace toni bari in miki kiji, a hankali ya jawota jikinsa ya riketa sosai yana sauke ajiyar zuciya hawaye na diga daga idonshi lallai idan har samha ta fita daga rayuwarsa mutuwa zaiyi wallahi dan baiga abinda zai zauna yayi a duniya ba, wayarsa dake ringing yasa ya saki samha daga rikon da yayi mata amma tana kwance saman kirjinsa,


Tsaki yayi sannan yace gani nan zuwa, bayan ya gama wayarne yace muje samha, shigewa sukayi gaba dayansu a mota hydar yaja suka bar gidan,



*Jameela Musa ce*

[05/04 4:45 pm] Washa: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊



                 *SO*

     *MUGUN WASA*



       *{ Love is a bad game }*




*JAMEELA MUSA* { meelat musa }




*Story, Writing & Editing*

                   *by*

         *Meelat Musa*



                  *SO*

      *MUGUN WASA*



*Dedicated to* 👇🏻

_Ramlat Abdulrahman real mai dambu_



*44-46*




Suna fita hydar yace samha in kunna miki waka ne? Turo baki samha tayi sannan tace bana, so murmushi hydar yayi sannan yace,


 Naga "yan mata suna san waƙa a mota wai sunce tafiyar tafi dadi ana tafiya ana nishadi,


Samha tace niko bana san nishaɗi, hydar yace nikam ina so inyi nishaɗi kuma ina so inji dadi a rayuwata, kamar ke yanzun idan kika kwantar da jikinki a jikina dadi nake ji,


Samha tayi shiru hydar yace don Allah idan kika rungumeni bakyajin dadi? Ki fadamin gaskiya bana san ki boyemin komai,


Samha tace ni babu wani abinda nakeji, murmushi yayi sannan yace niko nasan jikina yana da dadi shi yasa nake so ki shigo cikinsa dan kiji dadi sosai nake dage miki hannuwana sama, amma tunda bakya so na daina,


Samha tayi shiru, hydar yace to ni in riƙa rungumeki? Samha bata bawa hydar amsa ba,


Murmushi hydar yayi sannan yace yi hakuri dan Allah ki dan kwanta a jikina, ni inasan inji mace tana shashshafa min jikina daɗi nakeji,


Kallon hydar samha tayi murmushi yayi tare da ɗaga mata gira yana kashe mata ido ɗaya, da sauri samha ta rufe idonta a ranta tace gaskiya hydar dan iska ne, kamar yaji abinda tace yayi dariya, sannan yace keko idan nayi miki saiki karɓa amma saiki wani rufe ido? Taya zan rika birgeki mana?


Tsoki samha tayi sannan ta juya kanta gefe bata sake magana ba, har suka isa inda zasuje hydar shima bai sake magana ba,


Parking hydar yayi sannan yace ki zauna anan kada ki fita kinji zanyi meeting idan na gama zamuje wurin training daga nan kuma sai mu wuce gida,


Gobe kuma kamar yanxun sahib yana nan kusa dake, murmushi samha tayi sannan tace na gode maka hydar, 


Murmushi yayi sannan ya mika mata hannu suka hade hannuwansu🤝🏻 hydar yana kallon samha yana murmushi,


Ya dade rike da hannunta sannan ya sake mata hannunta tare daɗan shafa gefen fuskarta yana cewa saina dawo,


Murmushi samha tayi ba tare da tayi magana ba, shi kuma hydar ya fice abinsa, tana zaune a motar har hydar ya gama meeting ya dawo,


Da zugar yaran sa hydar ya dawo dukansu suka fara gaishe da samha cikin girmamawa, suna mata fatan alkairi tare da   addu'ar Allah ya basu zaman lafiya,


Cikin rashin fahimta ta kallesu sannan kuma ta kalli hydar murmushi yayi tare da daga mata dira ɗaya yana dan kwantar da kansa gefe daya,


Itama yaƙe tayi mishi wanda yafi kuka ciwo, yanda tayi abun ne ya bawa hydar dariya sosai, amma baiyi ba sai ya basar,


Alale yace ranka ya dade tafiya zamuyi ne? Hydar yace Eh amma ni zandan kai samha wani wuri kuma kuna iya tafiya kawai,


Fatan alkairi sukayi wa hydar sannan ya shiga mota yaja yabar wurin,


Nan su shamsu suka tsaya suna ta sheganta wai mai gida yana soyayya haka sukayi ta iskancinsu daga baya suma kowa ya kama gabanshi,


Samha sai so takeyi ta tambayi hydar game da Allah yasa alkairin mi akeyi musu amma yanda hydar ya hade ransa kamar zaiyi mata duka yasa batayi magana ba,


Saida yaje wurin training amma ba wani abu yayi ba kawai fita yayi yaɗan gaisa da mutane dan ya dade baizo ba tun bayan aurensu da samha,


Bayan ya gama gaisawa da mutane ne, ya dawo yaja motarshi sukayi tafiya gida, haka dai yadanyi yawo da ita tare da mata fira wai dan hankalinta ya kwanta dan yana so ta canje maganar sahib ne a ranta,


Sai dare suka dawo gida, ta baya suka shiga suka sauka dakin hydar a gajiye samha ta haye gado dan hutawa tunda sundan shana a gari, bata dade da kwanciya ba bacci ya dauketa, shi kuma hydar alwallah yayi yaci gaba da sallah,


Da safe kuwa samha koda ta tashi bata ga hydar ba, dan haka dakinta ta tafi tayi wanka ta taci gayunta,


Bayan ta gama ta sauko parlour nanma bata ga hydar ba, kicin ta nufa dan samawa cikinta mafita, tana shiga ta window in kicin ta hango hydar baya yana kwallo shi kadai,


Murmushi tayi sannan ta matsa jikin window tace ashe kaima ka iya boll? Ba tare daya kalli inda samha take ba yace kema kin iya ne? 


Cikin zumudi samha tace na iya wallahi har yanxun wasan sa yake da boll din kuma bai kalli samha ba, yace to zo mu gani idan kin iya, dariya tayi sannan ta fita kicin din da sauri,


Da gudu ta isa wurin hydar sannan tace to muyi, rike kwallon yayi a hannunsa sannan yace kije dakina, a cikin wedrof idan kika bude daga kasa zaki ga kaya ki dauka ki saka,


Cikin sakata samha tace muyi da wannan mana, kusa da ita hydar ya matso sannan yace ai wannan baza suyi miki dadi ba, wancan riga da wando ne kiyi sauri kije ki saka,


Dariya samha tayi sannan ta ruga da gudu murmushi hydar yayi sannan yaci gaba da wasansa, babu dadewa samha ta dawo,


Amma da hijabi a jikinta ba tare da hydar ya kalli inda take ba yayi murmushi har yanxun wasan sa yake da kwallo bai daina ba,


Samha tace na saka kayan, hydar yace ai naga baki shirya ba, samha tace na shirya mana, hydar yace to idan kin shirya ki cire hijabin mana,


Dariya tayi sannan ta saka kanta cikin hijabi tana kallon kayan jikinta, duk halittun jikinta sun nuna fa, murmushi hydar yayi dan ya gane abinda take nufi,


Fiddo kanta tayi sannan ta kalli hydar da sauri ya dauke kanshi daga kallon da yakeyiwa samha, amma yana kallonta da wutsiyar idonsa,


Samha tace kayannan sunmin kadan fa, hydar yace ai zasuyi miki daidai,  ni nama gaji tunda bazaki yi ba, da sauri samha tace A, a yi hakuri don Allah muyi tare,


Taka kwallon yayi da ƙafarsa sannan yace to cire hijabin, cirewa tayi ta mikawa hydar kanta babu kallabi gashin kanta ya sauka a gadon bayanta duk data daureshi sai lilo yakeyi a jikinta,  tana mika mishi hijabin ya riketa yadan shafata kadan sannan ya saketa, yana mata wani mayataccen kallon a ransa yace samha akwai diri, ci gaba da kallon ta yayi wanda har samha taji babu dadi, 


Murmushi hydar yayi sannan yace to taho, da sauri samha tayi wurin inda yake kafarsa tana kan boll din, tana matsowa suka fara wasa, haka hydar yayi ta gyarata yana dariya, saidai ta bishi da gudu data zo zata kama boll din saiya juyata ya turata wani wuri,


Abin yayi ma samha dadi dan haka ta saki jikinta tanajin farin ciki a ranta sosai, saida suka gama kwallon ne, ne hydar yace to zo ki simbaceni, {kiss} samha tace kai wai miye haka? So kake sahib ya shigo ya ganmu a haka ne? 


Daga kai sama hydar yayi tare da bude hannuwansa yana cewa taho taho taho,,,,,,,, murmushi samha tayi sannan ta matsa wurin hydar cikin sauri, rungumeta hydar yayi sosai yanajin dadi naratsa masa tun daga cikin kwakwalwar sa har ƙarƙashin tafin ƙafarsa,


 A hankali ya sauko kanshi, a gajiye ya lalubo bakin samha ya shigar da nasa a ciki ya fara aikawa samha da sabon sakon da bata taba jin irin taken ba tunda Allah ya kawota duniya,


Samha ji tayi kafafuwanta basa daukatar jikinta sai kyarma yake dan ita kadai tasan abinda takeji, dan tunda take duniya babu namijin daya taba mata irin wannan abun, sai hydar, dan haka batayi yunkurin hanasa ba, saida ya gaji dan kanshi sannan ya saki samha,


Hannunta yaja dayan hannunsa kuma yana rike da boll din da suka gama wasa, haka yajata sukayi farlo, bayan sun shiga ya zaunar da ita saman kujera sannan ya wuce kicin yana halba kwallon a hannunsa yana buga ta kasa tana dawowa sama yana rike ta a hannunsa,


A daidai bakin kicin ya yada kwallon sannan ya shiga ciki, samha kuwa tana zaune kamar wata gunkiya niko nace ina ruwan ba sabanba,? An wani jingina da kujera sai wani tunanin abinda hydar yayi mata takeyi,


Abin ya tsaya mata a rai, murmushi tayi sannan ta dora kanta saman hannun kujera ta rufe idonta, tun farkon haduwarta da hydar ya fara dawo mata tsaff a cikin ƙoƙon kanta,


Saidai tayi murmushi tare da gyara kwanciyarta, haka tayi ta juyi tana murmushi tare da mammatse ido sai kace hydar ya kamata a gado,


Hydar dake tsaye gabanta binta da kallo yayi tare da tambayar kansa ko miyasa takeyin haka? Murmushi yayi lallaima ya gano abinda take tunani, a bayyane yace sahib, da sauri ta bude idonta tana kallon hydar, murmushi yayi sannan yace sahib ko?


Itama murmushi tayi sannan ta tashi zaune, zama hydar yayi kusa da ita sannan ya jawo samha a jikinsa, yace kada ki wani damu babu dadewa sahib zaizo insha Allah,


Samha tace kai amma wallahi na gode maka sosai hydar, murmushi hydar yayi a ransa yace zaki gode min dai, amma bari inzo miki as sahib din zaki ci gidanku wallahi,


Mikewa hydar yayi sannan yace yau inaji dake hau bayana inyi miki goyo, dariya samha tayi sannan tace haba wannan ai abin kunya ne, hydar yace kai haba babu wani abin kunya don Allah ki hau bayana muje,


Murmushi samha tayi sannan tace nifa gaskiya na wuce goyo, hydar yace inji waye ya fada miki ne? Samha tace ni na gani dakaina baka ga na zama katuwar mata ba? Hydar yace kai ni inaganinki kamar wata jaririya, hawo hawo hawo my samha, ya karasa maganar cikin sakata dariya samha tayi sosai, dan yanda hydar yayi abun taji tana san ta hau bayan nashi, kallonshi tayi sosai a ranta tace wallahi hydar hadadɗene sosai komai yana mishi kyau,


Saman kujerar ta mike tsaye hydar ya matsa da bayansa samha ta haye, tana jin kunya sai boye fuskarta takeyi a bayan hydar kamar yana ganinta, murmushi yayi sannan ya fara tafiya, kwantar da kanta tayi sosai a bayanshi tanajin dadi sosai,


Saida yakaita daki a saman gado ya kwantar da ita, shima gadon ya hau, ya kwanta saman jikin samha, cikin jin kunya ta rufe idonta da hannunta, murmushi hydar yayi sannan yace ina da nauhi ne? Murmushi samha tayi amma bata bude idonta ba kuma bata bawa hydar amsa ba,


Haɗa hannuwanta yayi ya rike duka biyun sannan yace don Allah idan kina tare dani ki daina rufe idonki, idan kina kallona inajin dadi, ina sanki sosai idanuwanki suna min kyau idan kina jin tsoro samha, zaro idanuwan tayi cikin yanayin tsoro kamar yanda hydar yake so, murmushi hydar yayi sannan yace na gode sosai, dora goshinsa yayi saman fuskarta,


Ya dade a haka sannan ya daga samha, yace to samha zan tafi bazaki sake gani na ba, samha tace miyasa? Murmushi hydar yayi sannan yace zan barki da sahib nasan yana zumudi yazo wannan lafiyayyar fatar nasan yau sahib zai more abinsa ya karasa maganar cikin sigar a tausaya masa,


Da sauri samha ta tashi ta sauko daga saman gado tayi wurin da hydar yake tsaye sannan tace miyasa kakeyin kuka ne? Murmushin karfin halin hydar yayi sannan yace ba dole inyi kuka ba, tunda ina sanki amma bakya so na? Kina ta murna sahib zai dawo,


Murmushi samha tayi sannan tace kayi hakuri ka daina kuka kuma ma ai sahib bazaice maka komai ba, tunda shine da kanshi yace ya yadda dakai to miye zakayi damuwa ne?


Cikin kuka hydar yace sahib ya yadda dani amma kefa kin yadda dani ne? Murmushi tayi sosai sannan tace na yadda dakai mana, hydar yace to idan kin yadda dani ina so ki cire kayan jikinki duka, idanuwa samha ta zaro sosai sannan tace kai dan iska ne? Hydar yace Eh kuma ina so inyi iskanci dake ke bazakiyi dani ba? 


Da sauri samha taja baya hydar ya bita, wayyo Allah tace, sannan tace hydar miye haka? Daure fuska hydar yayi yana tunkarar samha cikin tashin hankali samha tace don girman Allah kayi hakuri,


Wani irin kallo hydar yayi mata sannan yace zan baki miliyan goma, samha tace Eye? Hydar yace Eyy, girgiza kai samha tayi cikin kuka tace bana so, hydar yace miliyan ishirin samha tace bana so, yace talatin tace A, a, haka yayi ta fadar miliyans of naira samha tace bata so,


Hydar yace to wallahi idan baki cire kayanki kikamin abinda nake so ba zan kashe ki, da sauri samha takai hannunta ta fasa glass din madubi ta ciroshi sannan tace dakaina zan kashe kaina kafin ka kasheni tana kokarin cakawa cikinta hannunta sai jini yake zuba saboda kwalaben daya shiga a cikin hannunta, da gudu hydar ya matsa ya rike hannunta,


Samha tace sakemin hannu, hydar yace waye yasa kika fasan mirrow? Kinsan ko nawa na siya? Kudi da yawa amma kikamin asara? Lallai yanda kika fasa min haka nima zan farfasa miki fata, tsoki yayi sannan yace bara sahib din yazo zaki bashi labari yana fadin haka yayi waje,


Yana fita samha ta zauna kasa tana kuka, shi kuma hydar da farin cikin sa ya isa dakinsa, samha baza tayi mishi sata ba, sannan baza tayi iskanci dashi ba, dadi yaji sosai tun kafin ya isa dakinsa ya cire rigar jikinsa, amma yanxun yasan wannan abun dayayi ma samha ta kara tsanarsa a ranta , to duk dai da haka ya wuce da wannan wurin samha babu sata babu fasiƙanci, saura ya koyawa zuciyarta sanshi,


Wanka yayi yaci uban gayenshi sannan ya dauki fuskar sahib ya saka, wayar da yake kiran samha ya dauka ya kunna sannan ya kashe tashi ya boye, fita yayi ta baya, ya zagayo ta inda suke shiga, yana shigowa ya wuce kicin ya da sauri ya shiga, yana shiga ya bude lokar,


Inda ya boye goruba da taura da magarya irin dai kayan kauye, dauka yayi ya fita daga kicin din yana fita daga kicin din ya fara kwarara sallama, samha dake zaune tana kuka taji muryar sahib tashi tayi ta fito da gudu,


Tana fitowa ta hangoshi tsaye a tsakiyar parlour rike da ledoji, murmushi tayi sannan ta goge hawayen idonta da bayan hannunta ta babbako da gudu kutumar babban burodi da boter ta rungumeshi tana dariya, ajiyar zuciya hydar yayi sannan yadan matse hawayen idonshi, 


Cikin kuka mai sautin dariya tace kai amma ka iya bazata wallahi, ansar ledar hannunsa tayi sannan tayi gaba hydar yabi bayanta yanajin bakin ciki a ransa, samha tace sahib naji ledar nan da nauhi da alama kayomin tsaraba ko? Murmushin karfin hali ya ƙago sannan yace Ey,


Surutu tayi ta mishi har suka isa daki, a gefen gado hydar ya zauna, sannan ya kalli samha yace mi akayi miki kike kuka? Murmushi tayi tare da boye hannunta a baya tace ba komai mi ka gani ne? Faduwar gaba taji dan lallai bata san taya zata fadawa sahib ba abun ba,


Murmushi yayi dan yana so ya fara matsa mata a matsyin sahib dan ta fitar   dan ta fara tsanar sahib a zuciyarta, saboda yace dan ubanki bakiji ina magana ne? Cikin tashin hankali samha tace ubana kuma? Yace Ey dama ubana zan zaga? Dariya samha tayi sannan tace nidai bazan zagi ubanka ba,


A fusace ya mike tsaye yana cewa nine kike cewa ubana? Da sauri samha ta mike cikin sigar lallashi tace kayi hakuri daga dawowa kuma sai fada don Allah? Kwantar da hankalinka nayi maka girki kayi wanka ka huta sai a fara fadan ko? Sahib yace au fadan za'ayi ma ko? Tace Eh tunda kana so ayi aisai in kama maka,


To dan ubanki kiyi fadan yanxun mana, samha tace kai bafa tsoranka nake ji ba, ko an fada maka ni banzace zan zauna kayi ta zungurawa iyayena zagi ne?


Sahib yace an zaga, naje na zagesu, banza jaka dake, cikin fushi samha tace akwai babban banza jaki ma irinka? Dan iska da baka san darajar matar aure ba, kazo ka ajiyeni a gida dani da wani dirjejen kato shima dayan dan iskan kamar kai, 


Sahib yace kai kai kai? Cikin mamaki ya kalli samha sannan yace dan uwarki hydar ne dirjejen ƙato? Ya akayi kikasan dirjeje kato ne shi? Cikin duk abinda zai faru ya faru samha tace ai kasa shi ya dirdirjeni, to daya cire kayansa naga ashe kato ne,


Wani irin mari hydar yakai wa samha harsai data fadi kasa, da sauri ta tashi itama ta kashe shi da mari, sannan tace dan ina aurenka zaka mayar dani kamar fulawa kayi ta dukana? sakarni yau duk wanda ya tsaya maka a gidan nan saika bani takardar sakina, bansanka na tsaneka wallahi yau ina iya kashe ka ta karasa maganar tana ƙara fashewa da kuka,


Sahib yace to? Yayi maganar ne cikin mamaki, sannan yace nine zaki kashe? To anki a sakeki kuma tunda har kikayi zagi wa hydar gidan nan kin bani dani wallahi sai kin zama abin tausayi dama an fada miki sanki nakeyi? Banza barauniya,


Samha tace naji ni sata nakeyi kaifa? Wanda baka kishin iyalinka, dan iskan hydar din nan har lallashemin baki yayi dan ubanshi hada kwanciya dani a gado daya munafiki sai yayi ta rungumeni katon banza wanda baya tsoron Allah,


Sahib yace ke tsoron Allah yasa kika biye mishi kikayi? Samha tace duk ba kaine kaja ba? Kaine kace inyi masa komai a matsayin mijina kamar yanda zanyi maka, Allah ya sawake ma daya ciny....... Nushin da sahib yakai mata shi ya hanata karasa maganar, a hankali ta zauna gefen gado tana kuka,


Sahib yace wallahi zanyi shedar hydar bazayi iskanci dake ba, kice yau duk kin zage uwarsa? Cike da bacin rai samha tace baƙin cikina daya ma bai bari na zagi uwarsa ba ya fita, ta karasa maganar tana kuka, tsoki sahib yayi sannan yace nikam bazan iya kwana dake ba, yau din nan zanyi tafiyata, ga tsaraba nan, idan kin gama haukan na dawo,


Cikin rarrashi samha tace yi hakuri kaine wallahi duk ka ɓatamin rai daga magana sai zagi sai kace kana jirana ne? Tashi tayi tare da cewa bara in haɗo kayana mu tafi, yace to kiyi sauri, cike da zumuɗi ta matsa ta fara tattara kayanta, hydar yana ganin hankalinta ya koma wurin haɗa kaya yasa shi sulalawe yabar dakin samha,


Da gudu ya isa dakinsa, ya canja kaya tare da cire fuskar ya haye gado yayi kwanciyarsa, samha kuwa bayan ta gama hada kayanta ta dauko da niyar tafiya taga babu sahib, da sauri ta fito ta fara dubashi amma babu shi, da gudu ta fita daga farlo, ganin wasu jibga jibgan karnuka tayi masu kama da kuraye a kofar farlon, suna ganin fitowarta da gudu suka fara, wan wan wan wan hab hab hab, da gudu samha tayo ciki suka biyota, 


Da gudu ta haye bene amma binta sukeyi, ganin kada ta shiga dakinta su cinyeta babu wanda yaji ya gani yasa tayi dakin hydar da gudu, yana jin ihuta shi kuma minafikin Allah yana cikin bargo sai dariya yakeyi, da gudun tashin hankali ta shiga dakin tabi takan hydar ta wuce bayansa tana kuka, 


Banza yayi da ita kamar baisan ta shigo ba, su kuma karnukan a bakin kofa suka tsaya sai wani zalzalo harshe sukeyi suna kallon samha, sai shashshekar kuka takeyi tana tsugunne saman gado bayan hydar, banda dariya babu abinda hydar yakeyi cikin bargo harda hawaye,


Samha ganin bargon na motsi yasa ta yaye bargon hydar ta gani ya daure girar sama data kasa yana harararta, murmushin karfin hali samha tayi sannan tace kaine? Kallonta yayi sannan yace nine ya akayine?


Samha tace dama daki zanje ne, hydar yace ba dakin kika wuce ba kika zo nan? Ajiyar zuciya samha tayi sannan tace don Allah ka rakani, jan bargonshi yayi ya lulluɓe tare da cewa wallahi babu wani inda zanje, haka ta gaji da tsugunni ta zauna, ganin zaman bazai fisheta ba, ta hakura ta kwanta, tare da dafe hannunta dataji ciwo,


Shashshekar kuka tayi,  tayi har ta gaji tayi bacci, saida hydar ya tabbatar tayi bacci sannan ya tashi yayi mata dressing a hannuta dataji ciwo ya cire mata hijabin jikinta ya lullubeta da bargo,


Koda asuba da hydar zai tafi masallaci bai tashi samha ba, saida yaje yayo sallah ya dawo sannan ya tasheta, tana tashi yace tashi ki tafi kiba mutane wuri, da sauri samha ta tashi a hankali ta sauko daga saman gadon, ta fara tafiya hydar yace idan kin gama abinda kikeyi zaki dafa abinci dan yau duk wani ma'aikaci da yake gidan nan zai dawo,


Samha tace ai tafiya zanyi saika samu wanda zai dafa musu danni bazan zauna inyi ta wahala ba sai kace wanda bata da Nci, hydar yace to a sauka lafiya, kuma idan har kare ya sake biyoki kika zo min daki wallahi sai nayi miki abinda baki tunani, kinji kuma nayi rantsuwa wallahi a saman gadon nan zan miki kacha kacha na fada miki,


Samha batayi magana ba ta fice daga dakin tana kuka, da sauri ta sauka kasa, saida taje daidai kofa ta leka taga karnukan nan suna nan, tsoki tayi sannan tace "yan iska duk saina kasheku guba zan zuba muku "yan iska duk kuci ku mutu,..juyawa tayi ta koma,


Da sauri ta nufi dakinta tana zuwa toilet ta nufa tayi alwalla sannan tazo tayi sallah, tana gamawa ta koma gado tayi kwanciyarta,


Hydar kuwa fitar samha a hankali ya kwanta, fadansu na jiya as sahib ya fara tunani murmushi yayi sannan yace Allah ya sawake, lallai ina da jibgegen aiki a gabana ya za'ayi samha ta fara san hydar? Tsaki yayi sannan yace Allah ya dorani kanki samha,


Saida tasha bacci ta tashi dan kanta, wanka tayi bayan ta gama ta shirya ta koma gefen gado ta zauna, hannunta ta kalla da aka nannaɗe da bandej sannan tace in banda rashin galihu haka zanyi wani girki babu wani mai sona, kawu yana can yana jira in dawo yaci gaba da sakani sace sace, shi kuma hydar sai wani daure fuska yakeyi, "yar dariyar ma ya daina min dana bashi hakuri kuma yanxun idan ina san ganin sahib ya zanyi? Gashi gidan ba'a fita yazo ya ajiye karnuka,


Haka dai hydar yaci gaba da horar da samha da wahala, kullum haushinsa takeji, shi kuma sahib ko ankira ma ba'a samu,


Kuma tana san ta tambayi hydar amma babu fuska, kuma idan ya fita daga gida sai tayi bacci yake dawowa, dan haka duk abubuwa sun dami samha, gashi daga farlo bata zuwa ko ina saboda da karnukan daya a bakin farlo,


Haka take dafa abinci mai yawa, tun bata saba ba harta saba, kuma hydar bayacin abincin samha yanda ta zuba haka zata zo ta dauka zamane dai na samha tanajin haushin hydar shi kuma yana jin dadin zaman kuma yana kara santa, amma ita batashi takeyi ba,


Hydar ne zaune a farlo, yana zaune saman kujera 2seater ya jingina bayansa da hannun kujerar kafafuwansa yana saman dayan hannun, yana karatun Al- qur'ani amma hankalinsa yana kan samha, dan tunda safe yakejin kamar zaginsa takeyi, yana so ya tantancene idan zaginsa takeyi,


Ita kuma da mita ta fito daga kicin da katuwar kula a hannunta tana gunguni saida ta ajiye a saman dirning sannan tace nifa gaskiya na gaji da girkin abinci wa katti dan wallahi hakurina ya kare a daidai lokacin da taja kujerar dirning ta zauna, hydar yi yayi kamar baiji abinda take cewa ba,


Samha taci gaba da cewa kuma wallahi bazan sake share farlon nan ba tunda ni ba jaka bace, kullum sai inyita sharewa wani lokaci ma sai ace min baiyi ba saina sake, nanma basarwa yayi bai mata magana ba,


Tsaki tayi sannan tace to wallahi saidai a raba farlon nan biyu, kowa ya rika sharewa shima abincin kowa ya rika dafawa dan wallahi kowa yana san ya huta ni sai a ƙaƙuba min rankatakaf aikin gidan nan gani "yar yarinya aisai wahala tasa bazan girma ba, da wutsiyar idonshi ya kalleta amma baiyi magana ba,


Tashi tayi da gudu ta nufi sama, bata dade ba ta dawo da jan baki guda biyar a hannunta, hydar dai yana kallonta, bude jan bakin tayi ta duka ƙasa sannan ta fara darkakashi a saman farin teryils din, jan janbaki biyar saida ta ƙarar dashi wurin raba farlon, saida ta gama rabawa sannan tace yawwa gashi nan an raba, ga wurinka can ga nawa nan idan kabi min ta wurina wallahi mutum zaiga yanda zan mishi kaca kaca a wurin, wai maganar da hydar yayi mata cewa idan ya sake ganinta dakinshi, shine itama ta rama, murmushi hydar yayi sannan ya mayar da kanshi yaci gaba da karatun alqur'anin sa,


Ita kuma zama tayi daga saman tsef din bene tana ci gaba da gunguninta, wanda hydar baisan abinda take cewa ba, harya gama karatunsa ya rufe qur'anin ya tashi, 


Ta gefenta ya raba ya wuce, kuma bai taka inda tace ba wurinsa bane ba, ganin ya wuce yasa ta tashi ta bishi tana ci gaba da mita sai tsiwa take mishi, shidai baiyi mata magana ba, har kofar dakinsa ta tsaya tana jaraba, bata iya shiga cikin dakinshi dan yace duk ranar data shigo dakinshi na lahira sai yafita jin dadi, wannan dalilin yasa bata shiga ba tana tsaye a bakin kofa ta rike kugu tana masifa,


Ganin ya shiga wanka yasa ta hakura ta koma parlour ta zauna tana jiran fitowarsa, shi kuma yana gama abinda yakeyi ta can ya fice, yabar samha da hauka,


Ganin bazai fito ba yasata ta hakura ta koma dakinta, da daddare kuwa hydar saida ya tabbatar samha tayi bacci ya dawo, ta farlon ya shigo, inda samha tace wurinsa ne ya gani wurin kaca kaca duk ta yayyaga takaddu da ledoji ta zubar a wurin, ita kuma wurinta ta share ta goge fes, tsaki yayi saida ya share wurin ya gogoshi sannan ya dauki biro da paper ya rubuta mata,


_Na rantse da Allah na sake samun kin ɓata min wuri nima saina ɓata miki naki,_


Saida ya gama sannan ya aje a saman kujera, bayan ya ajiye ya haura sama, dakin samha ya fara shiga tana kwance tana bacci, shiga cikin dakin yayi a gaban gado ya tsaya yana kallon samha,


Kallon hannunta yayi data runtse dukawa yayi sannan ya kama hannun ya bude, murmushi yayi ganin abinda ta rubuta, wai _i love sahib_ biro ya ciro daga gaban aljihunsa sannan ya bude hannun, ya rubuta _i love hydar_ yana gama rubutawa saida ya sumbaci samha sannan ya fice daga dakin,


Da safe yana zaune a farlo yana break samha ta fito, dan kowa shi yake girka abinda zaici, bata kalleshe ba, kuma bata gaishe shi ba, saida tazo ta wuce ta kusa dashi harta kusa shiga kicin yace ke zo nan, 


Da baya baya ta dawo batayi magana ba, tazo gabanshi ta rike ƙugu, daure fuska hydar yayi sannan yace zo nan mana, kusa dashi ta matsa, kallon idonta yayi sannan yace keni abokin wasanki ne? Samha tace mi nayi maka kuma? Cikin daga murya hydar yace kamarni zaki rika rubutawa a hannunki wai kina so na?


Samha tace waye yace na rubuta, hydar yace zan miki karya ne? Yana maganar yana zaro ido, samha tace ni wallahi ban wani rubuta ba, hydar yace idan aka duba kin rubuta mi zan miki? Samha tace komai ma kamin, tunda tasan bata rubuta ba,


Wani irin kallo hydar yayi mata sannan yayi murmushi yace to bude hannuwan mu gani, kusa dashi ta kara matsawa tana bude hannun, kallonta hydar yayi sannan yace kindai ce komai in miki ko? Samha tace Eh, jinjina kansa yayi sannan yace karantomin duk abinda kika rubutu a hannun,


Daga hannuwan tayi tana kallon su, sannan tace _I love sahib_ hydar yace uhum, idanuwa samha ta zaro tare da cewa aaaaa, hydar yace inajinki, shiru samha tayi, murmushi hydar yayi sannan yace karanta fa, samha ta fara wallahi ban rubuta ba, hydar yace miye baki rubuta ba? Samha tayi shiru, murmushi mugunta yayi sannan yace jeki ki zauna a can ki jirani in gama, yana nuna mata wurin da hannunshi,


Samha tace kayi hakuri don Allah, tsawa hydar ya daka mata wanda yasa ta sauka daga wurin da sauri taje ta zauna inda hydar ya nuna mata, shi kuma sai sauri yake ya gama break ɗin dan yasan yau ko banza sai yadan rage zafi,


Yana gamawa ya sauko sannan ya nufi inda samha take zaune, yace tashi, tashi samha tayi tana kallon hydar,


Zama yayi saman kujerar ya kwantar da kanshi saman hannun kujera ya bude kafafauwanshi kana ganin kwanciyar kasan hydar kwallon dan iskane, wani irin kallo yakeyi ma samha wanda yasa taji duk tsikar jikinta ta tashi, yana mata kallon cikin wani irin yanayi yana murmushi da gefen bakin sa,


A hankali samha ta kalli kasa tana wasa da yatsunta, murmushi hydar yayi sannan yace kallarni mana, daga kanta tayi ta kalleshi shi, bude daradaran idanuwansa yayi masu firgita samha sannan yace zoki kwanta a jikina ki bani hakuri, samha tace ai basai na kwanta ba kayi hakuri don Allah, hydar yace wallahi bazanyi ba, maza kizo ki kwanta idan ba haka ba kuma zanje dake dakina, samha tayi shiru tana kallon hydar, shima ita yake kallo yana cewa bazaki zo ba?



*Jameela Musa ce*

[05/04 4:45 pm] Washa: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊



                 *SO*

     *MUGUN WASA*



       *{ Love is a bad game }*




*JAMEELA MUSA* { meelat musa }




*Story, Writing & Editing*

                   *by*

         *Meelat Musa*


*Ummu Affan ina miki sannu da jiki ubangiji ya baki lafiya Allah kuma yasa kaffarane kuma ina miko sakon gaisuwa a gareku Allah ubangiji ya bada hakuri Allah ya jikanta Allah yasa ta huta ku kuma Allah ya baku hakurin rashinta, annabi ya karbi bakuncinta, mu kuma Allah ya kyautata namu karshen idan ajalinmu yazo,*


*Assalamu Alaikum masoyana na fili da baɗili ina muku fatan Alkairi ga sakon gaisuwa na a gareku duk inda kuke a fadin duniyar nan dan kune maudu'i na, masu kirana a waya na gode sosai kuma kunsan ina amsa muku, masu min magana a chat kuma ina kokarin ganin na nayi magana, idan har kuka tura min sako ban duba ba, ko kuma banyi reply ba abubuwane sunyi min yawa kuma ko yakai yaushe ne zan duba kuma zanyi magana, kuma kunsan ina baku amsa masu cahrt dani, amma don Allah ku rika kyautata min zato, waye yace muku meelat musa tana da wulaƙanci? Masu cewa ina da girman kai ina wulaƙanta mutane to waye ya fada muku? Waye yace muku haka nake? Toni ba haka nake ba, kuma ba halina bane, ban iya ba kuma bazan iya ba, haka kuma bazan koya ba, don Allah ku riƙa kyautata mana zato, wannan ai san kaine, kuyi hakuri nasan wanda suka san halina zasu faɗi hakan to ni kowa da kowa nawa ne, kuma banda wulakanci saboda ni nasan darajar dan adam, don haka baiwar Allah ki daina yada halina akan abinda baki sani ba,*



*Baban sako zuwa gareki MOMYN MUSADDIQ 😊 ina miki fatan Alkairi kuma naga sakonki nagode sosai, gani na dawo ina tare dake kuma inayinki ina kaunarki inajinki har cikin babban birnin zuciyata, Albarkacin momyn musaddiq gaisuwa da jinjina gareku REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS ni MEELAT MUSA nake cewa Alkairin Allah ya isko ku har tsakar gidan ASSOCIATION naku*


*Sakon gaisuwa na zuwa gareki* 👇🏻


*FATIMA MUHAMMAD*




                  *SO*

      *MUGUN WASA*


*Dedicated to* 👇🏻

_Ramlat Abdulrahman real mai dambu_



*47-49*



Baza kizo ba?

Samha tayi shiru, hydar yace idan fa na tashi abun bayayin kyau kizo kawai dan rungumeni zakiyi sai kice inyi hakuri,


Samha tayi shiru, hydar yace ni kuwa da nine? Da yanxun har nayi miki yanda kike so,


Kallonshi samha tayi ba tare da tayi magana ba, shi kuma murmushi yayi sannan ya daga mata gira ɗaya, yana cewa keko zo mana! Ya karasa maganar yana kashe mata ido daya,


Matsawa tayi kusa dashi, hannunta ya riko yana jawota a hankali harya matso da ita kusa dashi, sannan ya kwantar da ita a jikinshi yana sauke ajiyar zuciya,


Yanda yake fitar da numfashin yasa jikin samha ya mutu ta kasa motsi, murmushi hydar yayi sannan yace kinasan hydar ne? Girgiza kanta tayi alamar A, a, hydar yace baki so na, amma kina rubutawa a jikinki miyasa?


Samha tayi shiru, duk maganar da hydar yake yiwa samha ta kasa magana, ganin bazatayi magana ba yasashi ya dan fara shashshafa ta, yana tambayarta miyasa ta rubuta tana sanshi? Bata bashi amsa ba, ganin bazatayi magana ba yasa hydar yaci gaba da jagwalgwala samha san ransa,


Cikin kuka samha tace don Allah ka barni bana san kana min haka, kallonta hydar yayi sannan yace ai yanxun na fara idan dai bazaki fadamin abinda yasa kika rubuta kina so na ba, dakina ma zan tafi dake tunda kina so na, sai muje in baki hydar gaba dayanshi,


Yarinya kina san hydar ne? Samha tayi shiru, ɗagata yayi daga jikinshi sannan yace sauka, sauka tayi daga jikinsa a hankali sannan ta durkusa kasa, hydar yace tashi tsaye, mikewa samha tayi tana kallon kasa, kallonta hydar yayi sosai a ranshi yace lallai jikin samha bai anshi sakona ko daya ba, to kodai taji karfin hali takeyi dan kada in gane? Kallon samha yayi sosai lallai bataji komai ba tunda har ta iya tsayawa saman kafafuwanta, tsaki yayi sannan ya gyara kwanciyarsa yace kezo nan, yana nuna mata inda zata sake kwanciya a jikinshi,


Cikin kuka samha tace don Allah ka daina wannan abun, dani dakai dukanmu muna cikin fushin ubangiji, kuma ya tsine mana albarka saboda muna aikaita saɓo, da sauri hydar yace kai nikam Allah bai tsinemin ba kuma kema bai tsine miki ba, waye yace miki Allah yana tsinewa miji da mata? Shiru samha tayi dan bata gane inda maganar hydar ta nufa,


Cikin shagwaɓa yace nidai kizo nan nace, yanda yayi abunne yasa samha taji wani yarrrrrr, a jikinta, amma saita goge hawayen idonta ta juya tayi tafiyarta, duk maganar da hydar yakeyi ma samha a banza, dan samha bata saurareshi ba,


Tsoki hydar yayi sannan yace wannan ai daukar alhakine, ni wallahi na gaji da wannan iskanci, kullum saidai kizo ki wani wuce ta gabana kina murza ƙugu, kina tafiya kina tada min hankali ke kuma hankalinki kwance ni kuma ki barni da tashin hankali, duk wasu ma'aurata suna cikin nishadi amma banda ni mtswww,


Tashi yayi ya dauki tarkacen sa yayi sama, a gajiye ya isa dakinshi, zama yayi a gefen gado sannan ya fara dogon nazari, shawara ta farko data fara zuwa ma hydar shine, kodai ya saki samha a matsayin sahib sai yaje a matsayin hydar ya aurota? A hankali ya kwanta saman gado, fuskarsa tana kallon sama, zuciyarsa tace kadai sake mafita,


Dan idan har samha ta fita daga rayuwar sahib ta tafi bata sake dawowa, murmushi hydar yayi, wata zuciyar tace masa karya ne, dan kayi ma samha babban horon da bazata iya rabuwa dakai ba, wayarshi dake ringing ta dawo mishi da tunanin sa, juyawa yayi ya dauki wayar, bayan gaisuwa yace faruk kazo gida yanzun ina san ganinka, faruk yace tom, hydar ya kashe wayarsa,


Samha kuwa tana shiga daki da gudu ta haye saman gado tana kuka, lallai sahib ya cuci rayuwarta daya hadata zama da hydar, dan ita a ganinta duk duniya babu ɗirkeken ɗan iska kamar hydar, dan idan har aka aiketa neman jibgegen dan iska tana ganin hydar zata tsaya dan hydar babban dan iskane na bugawa a jarida gashi baida kunya ko kadan, amma sahib yasan halinsa ya hadata zama dashi wannan ai haukace da rashin sanin darajar addini hade da rashin sanin mahimmanci iyali,


Samha tana kwance saman gado sai kuka takeyi, lallai sahib mahaukacine, amma lallai ya dawo tunda baya santa ya saketa dan da zama da aurensa gara tasan bata dashi saboda zunibin ya mata yawa, lallai tana san ta kasance a jikin hydar dan ita kadai tasan yanda takeji, komai tanaji amma tana jin tsoron azabar Allah tunda akwai auren sahib a kanta, tunanin abubuwan da hydar yayi mata takeyi lallai hydar ya iya taɓa mace komai yanayi cikin natsuwa da nuna kwarewa, murmushi tayi a bayyane tace Allah ka shirya sahib shima ya gyara halinsa, yafi hydar iya komai,


Bayan faruk yazo yayi ma hydar waya yazo, hydar yace ina zuwa ka jirani, faruk yace to, saida hydar yayi wanka sannan ya nufi inda faruk yake jiransa, yau sahib ne ba hydar ba, 


Ta baya ya fita, yaje inda faruk yake jiransa, bayan sun gaisa hydar yace faruk saifa ka taimaka min, faruk yace taimakon mi hydar? Gyara tsayuwarsa yayi sannan yace idan ina gaban samha a matsiyin hydar zan rika kiranka in hadaku kuyi magana da ita a matsayin sahib, idanuwa faruk ya zaro sannan yace wallahi bazanyi ba,


Hydar yace miyasa baza kamin ba? Faruk yace kai ba wasa da so yaja maka ba? Nima kana so ka dilmiyar dani? kamar yanda kayi? Hydar yace insha Allah babu abinda zai faru wallahi, faruk yace gaskiya hydar bazan iya ba, dan bazan yadda ka koyamin abinda ba halima ba,


Hydar yace to kayi hakuri ka zauna ma zauni na, zan bata numberka a matsayin hydar, faruk yace wallahi babu wanda zai ɗanɗanamin inyi abinda nasan zan cuci kaina, ajiyar zuciya hydar yayi sannan yace to gaskiya zan hakura da samha tunda bansan mafita ba,


Faruk yace kaji tsoron Allah hydar zaka cuci diyar mutane wallahi, hydar yace ai nima cuceni tayi ta wani lallai ta shige a zuciyata ba tare dana ankara ba, daga wasa sai abun ya zama gaskiya, danni ban yadda ina san samha ba sai ranar danaga ta suma, faruk yace da kasan zaka rabu da ita da baka koya mata zama a jikinka ba,


Hydar yace to ai kowa ya rama kenan, ta rikemin zuciya ni kuma na rama dan nasan ko bata nemi sahib ba dole saita nemi hydar, faruk yace kada ka kawo aikin gaba a yanxu, waye yace maka ana wasa da zuciya? Tunda kaima Allah ya dora maka kaji yanda matan daka zalinta suke ji, kaji tsoron Allah hydar yarinyar nan bata san ko waye kai ba, kace kana santa ta yadda ta soka, kai kuma kaso kayi mata mugunta, amma Allah ya rike maka zuciya ya hanaka zalinci wa samha hydar wannan halinka ne ka sani, da jikinka kake yaudarar zuciyoyin mata, suma matan basu da hankali basu san ba ko wane jikin namiji ake shiga a fita haka nan ba, kaji tsoron Allah hydar idan har kacuci samha wallahi sai Allah yayi mata sakayya,


Zalinci biyu kayi ma samha, kazo mata a matsayin sahib ka hora mata zuciyarta da san sahib, kaje a matsayin hydar ka koya mata shiga jikinka, danni da naga ka ɗagawa mace hannu ta rike ina tausaya ma rayuwarta kaji tsoron Allah hydar,


Hydar yace ai danna yadda da kaina na mata hakan amma ita bata san inayi ba, batajin komai idan tana jikina, yadda da jikin nawa yasa na fara koya mata zama a jikina wannan dalilin yasa nayi mata wannan horon amma na lura samha tana da daskarariyar zuciya, faruk yace to irin abinda kakeyi ne Allah yasa akayi maka, sai kaje ka nemi mafita Allah ya sawake, faruk yana fadin haka ya nufi wurin motarsa yaja yabar gidan,


Murmushin karfin hali hydar yayi sannan ya tashi ya nufi dakinsa, yana shiga a jikin madubi ya matsa ya kalli kanshi sosai sannan yace sahib din banza mtsww, fita yayi daga dakin ya nufi dakin samha,


Samha dake kwance saman gado tana kuka taga sahib da sauri ta tashi zaune tana cewa dan rainin hankali sai yau kaga damar dawowa ne? Daure fuska sahib yayi sosai sannan ya shiga zazzagawa samha ruwan rashin mutunci tare dayi mata fada tasa hydar yayi sharar farlo kamar wani sa'arta, ikon Allah samha ta fada cikin yanayin mamaki, sannan tace lallai sahib amma wallahi baka da adalci matsawa kusa da ita yayi ya daddaga mata hannunshi a saman hancin ta, sannan yace bazanyi adalcin ba, kuma maza maza ki tashi kije ki goge wancan iskanci da kika zana a farlo,


Samha zatayi magana sahib ya daka mata tsawa tare da cewa tashi kada ki daukeni sakarai, ganin babu alamar wasa a tattare da sahib yasa samha tashi da sauri ta shiga toilet ta dauko hypor da klin ta fito,


Sahib yace kuma minti ukku na baki ki gogeshi idan ya wuce haka na dawo zakiji a jikinki, da sauri samha ta fita daga dakin tana gunguni, dariya hydar yayi sannan ya biyo bayanta yana cewa ni kike ma rashin kunya ko?


Samha tace ni bada kai nake ba, sahib yace to da wa kike ne? Samha tace da hydar nake a duk shine munafikinmu yana hadamu fada amma baka ganewa, cikin daga murya sahib yace da Allah rufe min baki,  magana samha tayi kasa kasa wanda sahib baisan abinda tace ba, fasa hypor tayi ta zuba a wurin data zana jan bakin ta zuba klin ta duka ta fara goge, haka sahib yayi ta dakawa samha tsawa yana hantararta,


Sai turo baki takeyi tana gunguni, amma hydar bayajin abinda take cewa, saida ta goge wurin tass sannan sahib yace kuma daga yau babu maganar hydar ya sake shara na fada miki, turo baki samha tayi amma batayi magana ba, sahib yace maza kije ki dafa abinci, har wani cewa kikeyi waike kin gaji da dafa abinci wa mutane da yawa, to ki gaji din in gani, Allah yasa inji kin kara wani abu wanda bai min ba kiga yanda zanzo in miki dukan lullusar fitar hayyaci a gidan nan,


Yana fadin haka ya sauko zai wuce sulbin klin yaɗan jashi zuuuuuu, amma baikai kasa ba, samha ta kyalkyale da dariya tace dama ka fadi wallahi sai naga wanda zai tasheka, juyowa sahib yayi yana harararta, gwalo tayi mishi sannan tayi ciki da gudu tana dariya, shima hydar dariya sannan ya fita daga farlo,


Saida samha ta tabbatar sahib ya tafi sannan ta fito, da saurin ta nufi kicin tana zuwa babu bata lokaci ta daura girki, bayan ta dora ne ta fito dan ta dauki towel din data goge wurin ta mayar toilet, tana fitowa taga hydar zaune yana kallo,


Dariya tayi sannan ta matsa kusa da hydar tace bari in baka labari, kallonta hydar yayi amma baiyi magana ba, samha tace ko baka san labarin ne? Murmushi yayi tare da jinjina kanshi alamar yana so, zama samha tayi sannan ta bashi labarin kaf yanda sukayi da sahib, dariya hydar yayi sannan ya ba samha hannu suka kashe, 


Hydar ya kara da cewa dama ya fadi da munga yanda zaiyi, samha tace kuma wallahi da bazan tada mugu ba, dariya hydar yayi sosai sannan ya rungumo samha a jikinshi yana cewa miyasa bazaki tada sahib ba? Samha tace yayi girma da yawa, murmushi hydar yayi sannan yace dani dashi waye yafi wani girma samha tace ya za'ayi in sani ne? Dogon kallo hydar yayi mata sannan ya kalli kanshi yana kara rike samha a jikinshi, murmushi samha tayi sannan ta zare jikinta daga jikin hydar a hankali, a ranta tace shidai yana san ya rikeni a jikinshi, da saurin ta tashi tayi sama,


Hydar yabita da kallo yana murmushi, bayan ta fito daga daki zata sauko tace ma hydar kalli ka gani, kallonta yayi ita kuma ta tsaya daidai inda sahib ya tsaya tana cewa hydar kalli kaga yanda yayi, ta dafa karfen benan ta fara kwaikwaiyon maganar sahib da yanda yayi tsayuwar da yanda ya kusa faduwar duk samha ta nuna hydar ya sake shekewa da dariya sosai dan wallahi duk yanda yayi haka samha ta nuna, shi kuma yanda tayi abin ya mishi kyau, murmushi hydar yayi sannan yace ke kuma ya kikayi ne?


Murmushi samha tayi sannan ta fara nunawa hydar yanda tayi da tsugunni datayi tana goge wurin da gungunin da takeyiwa sahib da gwalon da tayi mishi da gudu datayi, murmushi hydar yayi yana kallon samha,


Tahowa tayi a hankali saida tazo tsakiyar farlon sannan ta nuna mishi yanda sahib ya harareta hydar ya sake kyalkyalewa da dariya itama dariya tayi sannan tayi kicin da dan sauri, murmushi hydar yayi sannan ya tashi yabi bayan samha,


Shine ya tayata girkin sunayi suna fira, har suka gama, shine ya fito da abincin ya ajiye a dirning, sannan ya koma suka gyara kicin tare shi yayi shara ita kuma ta goge,


Bayan sun fito daga kicin hydar yace tazo suci abinci samha tace ita batajin yunwa, hydar yace mi kikaci ne? Tabe baki samha tayi sannan tace kawai na koshine, zanje inyi wanka saida safe, hydar yace to Allah ya kaimu, samha tace amin,


Shima ba wani abincin yaci ba, shamsu yayi ma waya suka zo sukaci abinci sun dade suna fira, saida suka gama suka fita sannan hydar ya tashi ya nufi dakinshi shima,


Tou lamarin jiki da jini sai a hankali, yau kam samha an tashi babu lafiya, ta tashi da wani irin matsananci ciwon ciki, tana daki ta ƙudundune sai kuka takeyi, tayi goho saman gado saboda azaba sai juye juye takeyi saida ta kwanta ta tashi dan tana shan wahala sosai,


Shi kuma hydar ya dade a farlo yana jiran fitowar samha, amma bata fito ba, daya gaji da jiran ta bata fito ba tashi yayi ya koma dakinshi yayi wanka yabar gidan,


Samha kuwa ciwon cikin yana lafawa dakel ta matsa kusa da wayarta ta dauka ta fara kiran sahib, saida ta kira har sau ukku bai dauka ba, a na hudun ne ya dauka yace miye? Cikin kuka samha tace banda lafiya miya sameki ne? Ciwon ciki nakeyi, to ki fadawa hydar danni ina da abinda nakeyi banda lokacinki, a hankali samha tace banda number hydar ai, tsaki yayi sanna yace zan turo miki yanxun, yana fadin haka ya kashe wayar,


Samha bin wayar tayi da kallo a ranta kuma tunanin halin sahib takeyi gaba daya ya burkuce mata, sai wani tashen zalinci da yake mata da rashin tausayi, hmmm lallai namiji ƙanin ajaline, niko sai nake gani wadda bata dace ba itace take cewa namiji kanin ajali samha,


Tana cikin tunani sakon ya shigo, number ta gani an rubuta hydar, saida ta sake dafe cikinta sannan ta fara kiran number hydar, babu ɓata lokaci hydar ya dauka bata bari yayi magana ba, cikin kuka samha tace hydar zan mutu, hydar yace subahanallah miye yasa zaki mutu? Kuma wace ce take magana ne? 


Wani irin nishi samha tayi sannan tace nice, hydar yace kece wa? Ni samha! Hydar yace wayyo samha sannu ganin zuwa bana gida ne na fita amma ina hanya kiyi hakuri kinji, cikin shashshekar kuka samha tace to ka taho dakai da sahib, gaban hydar ya fadi sosai,


Amma saiya basar yace ki zaɓi daya, ni zanzo ko sahib? Dogon nazari samha tayi sannan tace kasa sahib yazo, hydar yace to babu damuwa zansa yazo kiyi hakuri,


Godiya samha tayi sannan ta kashe wayar, hydar kuwa yana isowa gida, dakinshi ya wuce ya shigo sahib, ya taho dakin samha tun kafin ya shigo dakin ya fara masifa, samha dake kwance ta bishi da kallo, masifa sahib yakeyi yana karawa kamar zai daki samha, wai yana uzirinsa taje ta matsa ya taho shi ina ruwanshi da ciwon cikinta, samha tace kayi hakuri, sahib yace anƙi ayi hakurin ciwon cikinkin banza? Kin wani bi kinsa an tadoni daga wuri mai nisa to ba sannu ba, kuma bazance sannu ba, zan tafi bari ki sake sa a kirani kiga yanda zan miki lullusar futar hayyaci a gidan nan yana fadin haka ya fice daga dakin,


Ajiyar zuciya samha tayi sannan ta sake jawo wayarta ta fara kiran number hydar, cikin kuka samha tace hydar don Allah kayi hakuri kazo, hydar yace au sahib din baizo ba? Samha tayi shiru, hydar yace swry my samha, ina zuwa insha Allah, samha tace to hydar ya kashe wayarshi,


Samha kuwa addu'a take Allah ya bata lafiya duk bala'in sahib saita kakkaɓe aurensa, dama ashe baida mutunci, shida Allah, tarayyarta da sahib ta fara tunowa, a ranta tace kuma fa sahib yamin babban taimako banda sahib da yanxun na fado daga bene na mutu, shigowar hydar ya dawo da ita tunanin da takeyi,


Da sauri ya shigo cikin dakin yana cewa wayyo sannu samha, duk yayi wani kalar tausayi yanda yayi abun kamar a jikinsa ciwon yake, zama yayi a gefen gado da sauri samha taja jikinta ta dora kanta saman jikin hydar tana kuka, shafa gashin kanta yayi tare da cewa sannu,


Cikin kuka samha tace hydar sahib ya daina so na, kamishi magana banajin dadin abinda yakemin don Allah, bayan yasan banda kowa a duniyar nan saishi, miyasa zaimin haka? Hydar yace kiyi hakuri ba gani ba? Duk abinda sahib zai miki zan miki wanda yafi nashi ki kwantar da hankalinki kisa a ranki hydar mai adalci ne, danni a zuciyata kin zauna kuma bazan iya cireki ba samha, samha tayi shiru dan ita bata gane yaren hydar, murmushi hydar yayi sannan yace miyasa kike ciwon ciki ne?


Samha tayi shiru dan bazata iya fadawa hydar ba, hydar yace kinyi shiru, samha bata da yadda zatayi tace aina samu samu sauki, kwanciya hydar yayi ƙafafuwanshi na kasa ya dora kan samha saman cikinsa hannunshi yana saman cikinta, yana mata sannu,


Banda ajiyar zuciya babu abinda samha takeyi, hydar yace ko inkaiki asibiti ne? Ita kunya takeji a gaban hydar a fadamishi abinda yasa take ciwon ciki, itadai period ne amma batasan ya sani da dai sahib ne zata iya fada mishi, hydar yace kinyi shiru, murmushin karfin hali samha tayi sannan tace aina samu sauki ma,


Hydar yace to kiyi bacci, samha tace to, rufe idanuwanta tayi, a ranta tace dama hydar ne mijina ba sahib ba, shi yayi tafiyarshi ya barni saboda wani aikin banzarshi amma hydar ya baro nashi yazo ya kula dani, a fili tace Allah ka shirya min mijina ya daina halin da ba nashi ba, hydar yace amin, nima Allah yasa matata ta so ni, 


Ajiyar zuciya samha tayi sannan tace hydar dama kana da mata ne? Gyarawa samha kwanciya yayi ya juyo da ita tana kallonshi hannunsa yasa ya goge mata hawayen idonta sannan yace ina da mata samha, amma bata sona kwata kwata, ta tsaneni kullum sai tace zata iya kasheni kamar dai yanda kike fadamin a da,


Samha tace Allah ya shiryeta, hydar yace amin, amma bana tunani zata so ni har abada samha, murmushi samha tayi sannan tace mi zai hana ta soka mana?, hydar yace bazaki gane ba, samha tace zan gane mana saidai idan baka fada min ba, murmushi hydar yayi sannan yace manta da wannan maganar kinji ko? Samha tace to,


Sauketa yayi daga jikinshi yana cewa bara in kawo miki magani kisha, samha tace to kai malamin asibiti ne? Hydar yace sosai ma, hada allura duk na iya, kuma allurata dadi gareta ko kina so in miki ne? Murmushi samha tayi sannan tace dama allura akwai mai dadi ne? Hydar yace sosai ma sahib bai taba fada miki ba? Samha tace Eh, hydar yace da kina so da nayi miki yarinya dasai kinso kullum kinyi rashin lafiya, don doctor hydar ya dubaki, yana faɗin haka yayi waje,


Dariya samha tayi, tare da rufe idonta, a hankali ta fara tuno tun ranar data fara haduwa da hydar yasa maX ya rufe fuskarshi, da lokacin daya jefeta da wuka, da lokacin data dawo wurin sahib ta tadda hydar da ruwan data watsa mishi a fuska murmushi tayi, sannan ta tuno abinda yake saka mata a ido, ajiyar zuciya tayi sannan tace amma matar hydar mahaukaciya ce, duk wanda ta samu hydar a matsayin miji ai ya more a rayuwarshi, to yaushe yayi auren bayan sahib yace matar ta fasa aure dashi?


Kiran da hydar yake mata ya hanata karasa tunanin da takeyi, a hankali ta sauka daga saman gado tana tafiya a hankali har ta fito, hannunta yaja suka sauka farlo, saman kujera ya zaunar da ita sannan yaje kicin ya hado mata tea  ya dawo da kanshi ya bata tasha sannan ya bata magani tasha, 


Bayan ta gama yace in maidaki daki ko kuwa? Samha tace kai ina zakaje? Hydar yace ina da meeting yanxun, ɓata fuska samha tayi tana cewa shikenan ni bani da mai so na? Tana maganar tana daga hannunta na haggu tana kwantar da kanta gefe daya kamar zatayi kuka, murmushi hydar yayi sannan yace waye yace miki bana sanki? Samha tace nifa bakai nace baka so na ba, kawai nace banida mai sona ne, hydar yace to aini ina sanki, samha tace to ka zauna kayi jinyata tunda sahib ya tafi,


Ajiyar zuciya hydar yayi sannan ya kalli agogon hannunshi durƙusawa yayi saman guyawunshi ya dafa cinyoyin samha dake kan kujera zaune yana kallon fuskarta yace kiyi hakuri dana gama zan dawo don Allah, insha Allah bazan wuce 30minutes ba 👌🏻,


Samha tace nidai kayi hakuri kaga banda wanda zaiyi aiki so kake sahib yazo yayi min rashin mutunci? Murmushi hydar yayi sannan yace nima inmishi rashin mutunci, kuma idan na dawo zan miki komai har wanka ma kina so ko? Yanda yayi abin yasa samha taji gajiya ta lulluɓeta, ga wayar hydar sai tsuwa takeyi amma sai hakuri yake bawa samha, yace kiyi hakuri kinji yanxun zan dawo insha Allah a daidai lokacin da yake kwantar da ita saman kujera, yana kwantar da ita ya fita farlon da sauri,


Haka dai zaman samha da hydar yaci gaba da tafiya hydar yana bawa samha kulawa sosai sunayin wasa tare hydar yanayin kwallo tare da samha dan ya lura tana san wasan tsalle tsalle dan haka duk wani abu da yasan zai motsa jiki tare sukeyi, samha ta fara fahimtar hydar baida matsala, sahib kuwa kullum tsakaninsu sai masifa da bala'i da jaraba, wani lokaci ta bawa hydar labari wani lokaci kuma ta basar,


Da gudu ta fito daga daki tana cewa bazaka cemin ka fara ba inzo in fara irgawa? hydar ne duƙe a tsakiyar farlo yana press up, da sauri ta sauko tace tsaya tsaya, tsayawa hydar yayi amma har yanxun kanshi yana kasa, power💪🏻 shi ta taba tace lallai wallahi kai kato ne sosai, murmushi hydar yayi sannan ya daga guyawunsa kasa kamar yaro yana rairafe, amma har yanxun kanshi yana kallon kasa,


Samha tace hydar don Allah bari inhau bayanka inga zaka iyayi dani? Murmushi yayi da gefen bakinsa amma baiyi magana ba, kusa da fuskarshi ta matsa ta durkusa a gabanshi ta kamo fuskar shi yana kallonta sannan tace in hau, murmushi hydar yayi ita kuma ta saka ɗan yatsanta cikin beauty  point nashi saida tsagar hannunta ta shige daidai inda kunshi yake tsayawa, rike mata hannu yayi yace bana ce bana so ba,


Dariya samha tayi sannan ta tashi da sauri taje ta kwanta saman bayan hydar tace muje mazaje, ruf da ciki tayi ta saƙala hannunta a wuyanshi, hydar yace to ai kin shaken wuya, ki sake hannunki kawai, samha tace ai bana so ka faɗar dani ne, yace bazaki fadi ba, sakin wuyanshi tayi ta maida hannunwan ta a bayanta ta taɓa bayanta dasu ta lafe sosai a bayanshi, sannan tace muje muje mujeeeee mazaje, hydar yaci gaba dayi samha tana irgawa shidai baiyi magana, saida yayi sosai sannan yace nafa gaji, samha tace don Allah ɗan ƙaramin mana, hydar yace ai yanxun kece zaki min,


Da sauri ta sauko daga bayanshi tana cewa wallahi bana iyawa, tana kokarin guduwa hydar ya tashi da sauri ya rikota yace saifa kinmin na fada miki, turo baki samha tayi sannan tace ni wallahi bana iya daukarka kayi babba, hydar yace karyane waye yace baki iya dauka na ne?, Dan gajeran tsaki yayi sannan yace maza duka a gwada ki gani, cikin sakata samha tace nidai bana so ka daina, hydar yace to ba komai Allah ya kaimu anjima naga wanda zai goyaki a mashin dinshin shi,


Murmushi samha tayi sannan tace bari ma inje in mishi wanka, bai sake magana ya wuce abinshi ita kuma da gudu ta nufi kicin dan ta zubo ruwa ta wanke mashin, wani mashin din tseral ne samha ta ganshi a wurin faruk ya goyo budurwarshi sunzo wurin hydar mashin din ya burge samha bayan sunyo ma faruk rakiyane samha tace hydar mashin din nan yamin kyau dan Allah kadan ɗanani akai,


Hydar yace miyasa? Samha tace kawai faruk ya birge nin....bata ƙarasa maganar ba hydar ya bigar mata baki, sannan yace mi kika ce? Samha tayi shiru, hydar yace ke bakijin wani iri kice wani ya birgeki? Ni bana birgeki ne? Samha tayi shiru, ita kuma abinda zatace faruk ya birgeta daya goyo budurwarsa akai dan mashin din idan ka hau saika kwanta saman bayan mai tukawa, ansar makulin hydar yayi ya ɗana samha a cikin gida, shine fa dalilin daya sa ya siyi mashin din kuma dan jaraba duk marecen duniya sai hydar ya goya samha a mashin din,


Da sauri samha ta fito daga kicin da bokitin ruwa a hannunta zata fita daga farlon hydar dake saukowa yace ke ina zakije ne? Da sauri tace zan wanke mashin ne, hydar yace kina hauka zaki fita haka baki ga kayan da yake jikinki ba?, sai yanxun ta kalli kanta, wandone wanda dakel ya wuce gwuwa sai top kanta babu kallabi tsaki hydar yayi sannan yace ni bana san wanke manshin idan ba haka ba zan badashi,


Samha tace yi hakuri, hydar yace na hana wanke mashin daga yau, samha tace tom, yace zo ki wuce kije kiyi wanka, da sauri ta wuce ta gaban hydar tayi daki, tana zuwa babu abinda ta tsaya yi wanka tayi, bayan ta fito ne ta dauki wayarta ta fara kiran sahib, bayan ya dauka suka gaisa sannan tace mishi nifa banda kayan shafa komai ya kare, tsaki yayi sannan yace to ina ruwana? Mutum ba kyau ba sai kilbibin yayi kwaliya mtswww ya kashe wayarshi, 


Wannan abu yayi ma samha ciwo cikin kuka ta fito da gudu tayo farlo, tunda ta fito hydar yake dariya a ranshi, tana zuwa ta fada jikin hydar tana kuka da sauri ya tashi yana cewa subahanallah? Miye? Nifa wasa nake bazan bayar da mashin ba, harma nasa an wanke miki yau hada turare zan fesa mishi dan kiji dadi, jeki ki saka kaya ki taho dan yau idan aka fara ɗani sai dare yayi,


Cikin kuka samha tace hydar don Allah wai banda kyau? Ta karasa maganar tana ɓata fuskarta, hydar yace inji waye? Samha tace sahib, ta karasa maganar tana ƙara fashewa da kuka, goge mata hawayen idonta yayi sannan yace ƙarya ne, kina dakyau, gaki fara mai hanci ga gashi ga girare masu kyau idanuwanki irin na hydar ne, kinsan haka matata take cewa wai idanuwana kamar na mage na atini, maganar da samha take fadawa sahib, wannan banzan hydar ɗin da idanuwanshi kamar na mage yana atini,


Samha tace kaima kana fada da matar kane? Hydar yace A, a, kawai dai bata so nane, mi kikayi ma sahib yace baki da kyau?, yayi maganar ne dan ɓatar da maganar matarshi, gyara bakinta tayi amma batayi magana ba, hydar yasan dai samha baza ta faɗa mishi saboda kayan shafa sahib yace haka ba, dan haka murmushi hydar yayi sannan yace kema samha da kinayin kwalliya mai kyau da daukar hankali bazace miki haka ba, da sauri samha tace ai na fada mishi banda kayan shafa ne sai yace wai ni banda kyau kwalliya bazata min kyau ba,, hydar yace to kiyi hakuri ni zan siya miki duk abinda kike so ki daina fadawa sahib tunda ya daina sanki, samha tace to, hydar yace maza kije ki saka kayanki kizo muje muhau mashin dinmu, da gudu ta tashi tayi ciki,




*Jameela musa* ce 



💋

[05/04 4:45 pm] Washa: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊



                 *SO*

     *MUGUN WASA*



       *{ Love is a bad game }*




*JAMEELA MUSA* { meelat musa }




*Story, Writing & Editing*

                   *by*

         *Meelat Musa*


*_FATIMA MUHAMMAND wannan sakon ta aiko zuwa gareku masoyan labarin SO MUGUN WASA  kamar yanda nayi alkawarin zaizo gareku gashi na kawo muku shi,_*👇🏻


*_Meelat kin burgeni da wannan bayani kinsan dayawammu karatun kawai sukeyi suji nishadi ba tare da sanin ainihin labarin ba balle ginshikinsa. Idan har samha zata gane hydar a yanzu dole ta gujeshi saboda bb sonsa ko na sisi azuciyarta yanzu kuma hydar yake kokarin dasa kiyayyar sahib a zuciyarta sannan ya kafa tasa gwamnatin ta yadda ko tazo ta ganeshi already takamu da sansa. Meelat don Allah kiyi hakuri da mutun babu mai iyamar sai Allahn sa muna tare da ke kuma alherin Allah ya kyewayeki ta yadda zaki gagari mahassada. Wallahi ina jinki araina_*



*_Ita kuma sabeera sabeer cewa tayi_*👇🏻


*_Aunty meelat tunda sun matsu dajin lbrn samha tagane hydar to sai kibarmu typing din muga yanda zasu hadasu ko ba sunan wnnn littafin love is a bad game ba yakamata mu masu karantawa mu auna mugani haryanzun samha tana son sahib so bana wasa sbd kuduba kuga rashin mutuncin dayakemata amma addu,a takemai allah ya shiryesa kuma idan kunyi hkr ai samha tafara tunani hydar kunga dazarar tagama yadda dashi shi kenan bazai sha wahala dan allah writers din brilliant kuyi hkr daga masu yimuku hassada abin ba dadi amma hakuri za kuyi mai kaunarki ce Aunty meelat sabeeran sabeer_*



*_Ni kuma Meelat Musa cewa nayi don Allah kuyi min hakuri ku bini sannu dan Allah, ku bini sannu, dan kafin in fara rubuta novel din na tsara shi saida na gama kaff sannan na fara typing nasa a online, kuyi hakuri ku kasance tare dani,_*


                *SO*

    *MUGUN WASA*


*_Dedicated to_*👇🏻

   *_Ramlat Abdulrahman real mai dambu_*



*50-52*



Da gudu ta tashi tayi ciki,


Murmushi hydar yayi a bayyane yace ashe kinji haushi nace miki babu wani kyau sai kilbibin kiyi kwalliya, dariya yayi tare da tafa hannuwanshi yace shege ni hydar ni daya na burkuta mata kwalwa, inzo sahib inje hydar, lallai fa akwai babbar cakwakiya idan samha ta ganoni, ganin samha ta fito yasashi yayi tsitt,


Da saurinta ta sauko daga saman benen tana cewa tashi muje, kallonta hydar yayi sannan yace gaskiya bazan daukeki a mashin ina yau ba, samha tace miyasa? A daidai lokacin da take zama kusa da hydar, murmushi yayi sannan yace kullum abinda kike so nake miki amma ni bakyamin? Tsoki samha tayi sannan tace kai komai a rungumeka a sunbace ka?,


Hydar yace wallahi kuwa kamar kin shiga zuciyana, kawai so nake kiɗan lashe min bakina, sai kiɗan rungumeni, sai kice min kina so na, shikenan ni kuma sai in goyaki a mashin kiji dadinki murmushi, sannan ya ƙarasa maganar yana lumshe idanuwanshi,


Samha tace gaskiya bazanyi ba, hydar yace ashe kuwa yau babu hawa mashin a daidai lokacin da yake kwaciyar a kujera, tsaki samha tayi tare da cewa kada Allah yasa ka goya, ta miƙe tayi tafiyarta, hydar yace zo samha, tayi kamar bataji shi ba, da sauri ya tashi ya bita amma kafin yakai harta shige ɗaki ta rufe kofarta da makulli,


Dukan kofar ya farayi yana kiran samha! Samha!! Don Allah bude kofa mana, wallahi wasa nake miki bama sai kinmin ba, samha tayi shiru, cikin sigar lallashi hydar yace samha don Allah kiyi hakuri ki fito kinji, ni wallahi bana san kina fushi,


Tasowa samha tayi tazo ta bude kofar, tana budewa ta koma ciki, da sauri hydar yabi bayanta, yana cewa samha don Allah ki daina fushi, wallahi idan kina zuciya dani Allah ya sani inajin kamar zuciyata zata fito waje, saboda kwata kwata wallahi banajin dadi,


Kallon shi samha tayi sannan tace miyasa zuciyarka zata fito waje akaina? Murmushin karfin hali hydar yayi wanda idanuwanshi sunyi jawur kamar zaiyi kuka, sannan yace saboda ke amana na ne, nima fa amanar ni aka baki ya nuna kanshi da hannu, sannan yaci gaba da cewa ki daina haka wallahi babu kyau wulaƙanci samha, ya karasa maganar kamar zaiyi kuka yana wani kwantar da kansa gefe, duk yayi wani kalar tausayi, hannunta ya riƙo tare da ƙago murmushi mai kartar masa zuciya, yace muje in goyaki a mashin din, samha tace gaskiya bana so yaudai kam bana so, kila saidai ko gobe idan Allah ya kaimu,


Hydar yace to muje in siyo miki kayan shafa da kaina ma zan kaiki saboda inaji dake bana san sahib ya sake ce miki bakya kwalliya, murmushi samha tayi, sannan tace to muje, hijabinta ta dauko, hydar yana so yace kada ta saka hijabi tasa gyale amma yana tsoro kada ta sakeyin fushi,


Saida ta saka hijabin sannan ta biyo bayan hydar murmushi yayi sannan ya tare kofar daki tare da cewa kawo in rike miki hannu, waidan kada ta koma ciki ya tare wurin, murmushi samha tayi sannan ta miƙa mishi hannunta, shima hydar murmushi yayi sannan ya anshi hannun yayi mashi kyakkyawan riko, yana dan murzashi a hankali, ta yadda samha zata rika jin wani baƙon lamari yana shigar duk wasu kofifi na jikinta,


Haka sukayi tafiyar, hydar shine yake tuƙa motar samha kuma tana gefenshi ita kuma ta kwantar da kanta a jikin kofar mota, ba tare da hydar ya kalleta ba, yace samha zoki kwanta anan, yana nuna mata kafadarshi, ajiyar zuciya tayi sannan ta tashi ta kwanta inda hydar ya nuna mata, bayan ta kwanta ne, hydar yace miye? Tunanin mi kikeyi ne? Samha kamar zatayi kuka tace sahib, hydar yace da Allah manta dashi tunda baya sanki ni ina sanki aikema nasan zaki so hydar ko? Dan gajeran tsaki tayi ba tare data bashi amsa ba, murmushin karfin hali hydar yayi sannan yace Allah ya baki hakuri, daga haka bai sake magana ba, amma har yanzun tana kwance a jikinsa,


Kayan shafa turaruka masu tsada na tashin hankali da daddan kamshi, da duk abinda yasan samha tana so yace ta dauka, haka samha tayi ta daukar kaya kamar hauka, saida ta gama tace ma hydar sunyi haka, hydar yace basuyi ba, ki ƙara, samha tace wallahi haka yamin, haka aka kwashi kayan aka jibga musu a mota, hydar ya biya kudi masu yawan gaske, wanda shi baisan sun fita daga cikin asusun kuɗinshi ba, yayin da samha taji hydar ya bata tausayi ya kashe kudinshi masu yawa saboda ita, duk dan ta kyautatawa mijinta, wanda shi tace ya siya mata yace bazai siya ba,


Tun a mota samha take ma hydar godiya, tare da mishi addu'a Allah ya daidai tsakaninshi da matarshi, yace amin, har suka dawo gida samha bata daina godiya wa hydar ba, bayan sunzo ne  yasa aka shigar da kayan dakin samha, bayan ankai ne hydar yayi mata saida safe, itama fatan alkairi tayi mishi,


Samha bayan tafiyar hydar ta fara kiran wayan sahib ta fada mishi abinda hydar yayi mata amma ta doka wayar yafi sau adadin yawan ledan pure water amma sahib bai dauka ba, haka ta hakura ta ajiye wayan sannan ta tattara kayan komai ta ajiyeshi a wurin daya dace, sannan ta haye gado tana cewa sahib dai ya canja hali, yana can da "yar matarsa ya manta da lamarin wata samhar banza can, hmm shida Allah, hydar ne yace mata sahib yayi aure da kudin data siyar da gida ta bashi,


Da safe bayan samha ta gama sallah ta fara kiran sahib, saida yaga dama ya dauka, cikin masifa da hayani yace wai miyene? Nikam bana san jaraba, bana san kwanata, bana san mayata, bana san kwakwa, bana san naci, nace na daina sanki, amma da yake zuciya babu sai wani kirana kikeyi fadi inajinki miye?


Cikin natsuwa samha tace dama zance maka hydar ya siyomin kayan shafa, kada ka siyo idan ka samu hali, cike da bala'i yace dama nace miki zan siya ne? Ai bazan siya ba, kuma ina da kudina ko nace miki bani dashine? Sai kuma mi? Samha tace to maganar m card dina da kuma ahalina yaushe zaka sadani dasu? Mtswwwww yayi sannan yace can keta matsewa mawa, ahalinkin banza ni ina wani ruwana da ahalinki? Ko ahalinki ahalin sahib ne?  M card kuma nayar da banza a toilet nayi filoshin, sai mi? Samha tayi shiru, tsaki yayi tare da cewa noncess sannan ya kashe wayanshi,


Dakel samha ta haɗiye miyau saboda tsananin ɓacin rai tare da maimata kalmar noncess? Tou pha, Allah ya sawake, dogon nazari tayi tare da goge ɗan kwallan daya ɗigo mata daga cikin idonta,


Jiki a sanyaye samha ta miƙe, ta nufi ɗakin hydar, tana isa a bakin kofa ta tsaya bata shiga ba, dan hydar yace wallahi idan kare ya sake biyota tazo mishi daki zaiyi mata kaca kaca a saman gadonshi, wannan dalilin yasa samha ta tsaya a bakin kofa tana kuka, tare da kiran sunan hydar,


Hydar dake kwance yace samha miye? Cikin kuka tace kazo ina san ganinka, hydar yace gani ki shigo mana, gyara bakinta tayi batace komai ba, hydar yace samha zo, cikin shashshekar kuka tace ai kace in daina zuwa maka ɗaki zakaman abinda bana zato, hydar yace Ey amma ai cewa nayi sai idan kare ya biyoki, yanxun kuma nine nace kazo dakaina, don haka shigo,


A hankali samha ta shiga ciki tana ci gaba da kuka, shi kuma har yanzun yana kwance yana kallonta har ta iso kusa da gadon tahau saman gadon a hankali harta matsa daf da hydar sannan ta kwanta, ba tare da hydar ya sake kallanta ba yace ya akayi? Samha tace zowa nayi, zowa kikayi mi? Tayi shiru, hydar yace wani abu kike so ne? Samha tace A,a, kawai zanyi bacci anan ne, hydar yace niko da fita zanyi yanzun nan ina da abinyi,


Amma tunda kina san kiyi bacci, bari in jiraki ki gama sai in tafi, gyara kwanciyarsa yayi ya juyo yana kallon samha, jawota yayi kusa dashi yaɗan riƙeta a ƙirjinsa, fuskarshi a saman goshinta yana cewa to kiyi baccin,


Cikin muryar kuka samha tace hydar kayima sahib magana, ya daina abinda yakeyi, cikin yanayi na damuwa tattare da sigar lallashi hydar yace mi sahib ya miki kuma?,, cikin shashshekar kuka samha tace daga nace mishi ka siyomin kayan shafa idan ya samu kudi kada ya siyamin, sai yace min yana kuɗi nine bazai ma abinda nake so ba,


Murmushi hydar yayi wanda bai kawo fuskarshi ba sannan yace ba nace ki daina kiranshi ba? Tunda ya daina sanki kiyi hakuri samha ya kamata ki fuskanci rayuwa ki bude idanuwanki da kyau ki gane mai sanki, tunda sahib ya aureki kullum abubu ƙara burkucewa sukeyi bai damu dake ba ta matarsa yakeyi ko jiya na gansu suna tafi a mota bakiga yanda ya wani bi duk ya rungumeta ba, yana kissing nata bari kiga yanda yayi mata,


A hankali ya daga kanshi daga saman goshin samha ya ɗago mata fuska cikin natsuwa da kwarewa ya haɗa bakinshi da nata, yana mata wani irin salon iskanci a bakinta, wai duk a cikin nunawa yanda sahib yake ma matarshi, haka hydar ya samu yayi ta shashshafe jikin samha yana sauke wani irin lumfashi wanda samha bazata iya gane karatun ba, haka hydar yayi ta iskanci yana jagula samha san ran ranshi, saida ya tabbatar sakonshi yaje inda yake buƙata a  jikinshi samha sannan ya saketa, amma badan yaso ba, dan kada samha tace mishi wani abu,


Cikin kuka samha tace saina kasheta, da gudu ta sauka daga saman gado ta fice daga dakin, shidai hydar yana kwance katon banza ya kasa tashi, da gudu samha ta isa dakinta tana kuka, tana zuwa toilet ta shiga tayi wanka, a gaggauce ta fito ta shirya cikin wata haɗaɗɗiyar baƙar riga, ta yana gyale a saman kanta,


Tayi matukar kyau sosai, jaka da takalmi goldcoulour ne, dan shine kwalliyar jikin bakin rigar, saida ta gama shirinta tsaff sannan tayi kicin da gudu, wata shareriyar wuka ta ɗauka tana cewa yau saina ci uwarki da kika kwacemin mijina, niko nace waye yace da wuka ake kishi?


Da gudu ta fita daga farlon da shamsu ta fara cin karo, yace hajiya ina zakije ne? Samha tace kasan gidan da sahib ya ajiye matarsa ne? Abin dariya yaso ya bawa shamsu amma saiya basar yace a,a ranki ya dade, kallon Alale tayi sannan tace yawwa kai abokin sahib ne don Allah a ina yake zama da matarshi? Dariya Alale yayi sosai sannan yace nikam ban sani ba, amma mai gida ya san gidan dan ko shekaran jiya yaje,


Samha tace to ai kaima ka sani tunda kaine kake kaishi duk inda zaije, Alale yace gaskiya kam haka ne, amma ranar baije dani ba, dashi da matarshi sukaje gidan, samha tace ina karnukan suke ne? Alale yace suna baya an dauresu ai dama da daddare ake sakinsu, samha tace yawwa ngd, tana faɗin haka tayi gaba,


Tafiya mai nisa sosai tsakanin get na farko bare taje wanda zai sadata da get din da zai fitar da ita gidan gaba daya, tana fara tafiya shamsu ya kira hydar ya faɗamishi, da sauri ya tashi ya matsa jikin window ya fara kiran sunanta, amma samha tayi kamar bataji yana magana ba,


Hydar yace samha bakiji ina miki magana ko? Ba nace kizo ina kiranki ba? Nanma ƙara basarwa tayi, hydar yace to shikenan kije ɗin kuma duk abinda yayi miki kada ki kara faɗamin tunda banda amfani ashe kinsan zaki iya daukan hukunci da hannunki amma kika faɗamin ba komai yayi miki kyau duk abinda kikayi daidai dakene wallahi,


Daga inda take tsaye cikin kuka zatayi magana hydar yace bana san kiyi magana anan zoki fadamin inji miye yake damunki? Tahowa samha tayi tazo ta wuce ta gabansu shamsu tayi ciki, kafin ta shiga har hydar ya fito daga dakinshi ya sauko farlo,


A sukwane hydar ya isa kusa da samha yaja hannuta suka zauna saman kujera, bayan sun zauna ne hydar yace ya akayi ne? Cikin yanayi na ɓacin rai samha tace zuwa zanyi kawai in kashe matar sahib, idanuwa hydar ya zaro sosai sannan yace kinyi hauka ne?


Cikin kuka samha tace ko daya banyi hauka ba, hasalima nafi da hankali, dan ban hada soyayyar sahib da kowa ba a zuciyata, zan iyayin komai akan sahib, hydar yace nasan irin yanda kikeji a zuciyarki samha, taɓe bakinsa yayi sannan yaci gaba da cewa nima irin abinda kikeji haka nakeji harma nawa yafi naki, amma abinda nakeso dake shine kiyi ma sahib uziri harya gama amarcinsa da matarsa, zai nemeki ne kinji?


Samha tace to, ansar wukar hannunta yayi yana cewa ki daina faɗa da wuƙa wannan halin mutane banza ne kinji? Samha tace tom, hydar yayi ta mata nasiha, tare da nuna mata girma irin na hakuri samha tace to zan kwatanta amma gaskiya na rike so sosai, murmushi hydar yayi tare da cewa kuma kina da kalar hakuri don Allah mantar da maganar sahib,


Samha tace haba hydar kada ka manta shi sirrin zuciya yarda ce, harshe ya furta kalamar so kauna ce bana tunanin sahib zai gujeni amma tunda kace in mishi uziri na mishi, sahib ya riga ya zauna sosai a zuciyana, kaga ya kamata ya rike na rike ko? Duk sai muyiwa junanmu adalci, hydar yace gaskiya, samha tace amma yana neman saɓa alkawari bayan yasan ruhi, raina, jikina duk sun laminta dashi, zani faɗa sanshi ya harbi zuciyata ya hana zuciyana ta huta, tunda ya yadda a da naji dadi, amma yanxun ya daina so na,


Shiru hydar yayi dan baisan amsar da zai bawa samha ba, haka tayi ta kwatantawa hydar girma da darajar sahib a cikin babban birnin zuciyarta, shidai shiru yayi bai sake magana ba, ita ta gaji da surutun ta tashi tabar farlon, da kallo hydar ya bita harta haye sama yana kallonta saida ya daina hangota  sannan yayi ajiyar zuciya tare da lumshe idanuwanshi,


Da marece hydar yayi ma samha waya tayi wanka yana zuwa, shima wanka yayi yasa kayan wasan kerket a jikinsa, ya dauki na samha, irin dayane da nashi, ya nufi dakin samha, a daidai lokacin data fito daga wanka, sallama hydar tare da shiga ciki, da sauri samha ta nufi inda hijabinta take zata dauka hydar ya matsa da sauri ya riƙe hijabin,


Samha tace bani mana, hydar yace bazan baki ba, miya sa baza ka bani ba? Jin dadi ina san kawai basai kin wani saka hijabi ba, maza maza ki shirya kinga kayankin iri daya da nawa ne, sandar wasan kerket a hannunsa, ya ajiye kayan a gefen gado sannan shima ya zauna yana ma samha wani irin kallo mai wahalar fassarawa,


Turo baki samha tayi sannan ta fara shafa mai, duk abinda takeyi hydar yayi mata ƙuri da idanuwa yana kallonta, harta gama, hydar yace shafa kwalli, samha tace ni bana san kwalli yace ni kuma ina so saboda haka sai an shafashi wallahi, murmushi samha tayi sannan tace nidai zafi yake min a ido, hydar yace kawo kwallin in miki addu,a idan na shafa miki zakiji babu wani zafi,


Babu gardama ta dauka takai mishi, zaro tsinken kwallin yayi yana motsa baki, sannan ya saka abin kwallin a bakinshi yana cewa matso ki gani, tsigunnawa tayi kasa a gabanshi ta dora hannunta saman jikinshi ta ɗaga fuskarta tana kallon hydar shi kuma ya dora hannunshi saman kanta ya shafa mata kwallin, murmushi yayi bayan ya gama sannan yace kinga yanda kikayi kyau? Ya karasa maganar yana kashe mata idanuwanshi, yana lumshesu yana wani bude su, 


Tashi hydar yayi ya kama hannun samha yana cewa taso ki gani, tashi samha tayi hydar ya matsa da ita a jikin mirrow yace hajiyata ya kika ganki ne? Murmushi samha tayi sannan tace kuma wallahi yamin kyau kuma babu wani zafi ta karasa maganar tana kallon kwayar idon hydar,


Hydar yace yarinya an gaya miki niɗin na wasa ne? Samha tace gaskiya kai babbane, hydar yace sosai ma, saka kayan muje, samha tace to juya, murmushi hydar yayi sannan ya juya, yanda yayi juyin yasa samha tayi dariya sosai, sannan tace waika auta ne a gidanku? Ba tare daya juyo ba yace mi kika gani ne? Samha tace kai sakataccene na lura, hydar yace bakisan ma na iya sakata ba dan bama kwana wuri daya da kinga yanda ake sakata, yanda yayi maganar yasa samha tsikar jikinta tayi wani yam,


Shiru tayi, hydar kuma dariya yayi sannan yace kinyi shiru, bata ƙara magana ba, murmushi hydar yayi sannan yace kin gama ne in juyo? Samha tace Ey, juyowa yayi yana kallon samha sannan yace yarinya ki bari mu kwana a daki ɗaya kiga yanda nakeyi bacci da matata,


Samha tace A, a, bana bukata, murmushi yayi sannan ya dauki fesincap ya saka mata a kanta yana mata wani irin kallo, murmushi samha tayi data ga kanta a madubi tace kai gaskiya ina da kyau sosai gaskiya na haɗu da yawa, kallon hydar tayi sannan tace nayi kyau? Hydar yace sosai ma, aike din haɗaɗɗiya ne, sandar wasan kerket ya mika mata ansa tayi ta rike sannan yace muje,


Shine a gaba samha tana baya sai rawa takeyi tana tsalle, saida ta kara kallonta a madubi sannan ta fita da gudu, a waje babu kowa, da sauri take bin bayan hydar cikin nishaɗi da jin ta kamar wata sabuwa, wasa hydar yakeyi da kwallon kerket a hannunsa,


A filin wasan hydar ya nunawa samha wurinta yace anan zaki tsaya nine zan rika tullo miki kwallon, kinga anan ramin zaki jefa ta, samha  sai murmushi takeyi, tace tom,


Gyara riƙon sandar tayi sosai tana ɗan duƙawa kamar yanda hydar ya nuna mata, sannan tace muje na shirya, hydar yace Aha, sai yaja baya yake tillo kwallon samha saita halbata da sandar hannunta tana dariya sai tsalle takeyi tana yar rawa, haka suke wasansu cikin nishaɗi da jin daɗi, saida samha tace ta gaji dan kanta, sannan hydar yace to, zama tayi a wurin tana maida nunfashi,


Hydar yace bara a dauko mashin shima muɗan ɗana ko? Ya ƙarasa maganar yana ɗaga ma samha gira, murmushi samha tayi hydar ya wuce daga wurin dan dauko mashin, tunda samha ta hangoshi ya taho da mashin ɗin ta tashi tsaye, a ranta tace wallahi hydar yana da kyau sosai, gashi dan gayu kuma mashin ɗin ya masa kyau sosai, murmushi samha tayi sannan ta lumshe idanuwanta ta fara ayyano sahib a saman mashin ɗin, idonta ya kawo hawaye tace ni dama da sahib ne a wannan sansayan marencen nasan nishaɗin daya fi haka,


Har hydar ya iso wurin samha bata san yazo ba, haka yayi ta zagayata da mashin din amma ina samha ta lula duniyar bege, tsayuwa hydar yayi da mashin ɗin sannan ya murzashi da ƙarfi buuuuuuu, bunbunbunn, shine yasa samha ta dawo daga tunani, murmushi hydar yayi sannan yace taho mana, yana miƙa hannunshi,


Jiki babu kwari tayi wurin hydar yana dan tafiya da mashin ɗin a hankali samha tayi wurin ta taka zata haye baya, hydar ya jawota da hannu ɗaya ya zagayo da ita gaba, taba kan mashin ɗin baya bayanta kuma yana kan gaban mashin ɗin baya, kwaciya saman jikinta hydar yayi yana cewa kukanmi kikeyi ne? Zatayi magana hydar yakai bakinshi wurin nata ya sun bace ta, tare da cewa ki daina yawan kuka kinji? Samha tace tom,


Tafiya da mashin din hydar ya farayi samha tace ni zan koma baya, hydar yace A, a, yau a haka zamuyi, samha tace nidai nafisan baya, hydar yace to sauka kije bayan, sauka samha tayi ta koma baya tahau, miƙewa tsaye tayi saman mashin ɗin ta dafa kafaɗar hydar, haka yayi ta zagayawa, shima saida tace to yayi haka muje gida, hydar yace to


A bakin kofar farlo yaci burki da mashin din sannan samha ta dire, kallon hydar tayi tana cewa to faɗamin me zamuci ne? Hydar yace nikam banajin yunwa a daidai lokacin da yake saukowa daga saman mashin din, yaci gaba da cewa ke kuma mi zakici ne? Samha tace umm nima dai kam bana jin yunwa, hydar yace to babu damuwa muje,


Suna shiga samha tace saida safe, hydar yace Allah ya kaimu, tana zuwa daki samha ta kulle kofarta kamar yanda ta saba, wanka ta farayi tare ɗauro alwallah, tana fitowa kayanta ta saka ta fara sallah magirib, tana zaune a wurin har aka kira isha'i tayi tare da addu'oi sannan ta tashi a wurin,


Bakin gado taje ta zauna tare da jawo filo ta ɗora saman cinyarta, ta dora hannuwanta saman pillow ɗin ta zabga tagumi, tunanin halin sahib takeyi,


_Fadawa hydar danni ina da abinda nakeyi banda lokacinki,_


_Banda number hydar ai_


_Mtsww zan turo miki yanzun_


Ajiyar zuciya samha tayi tare da kwantawa saman gadon a hankali,


_Hydar zan mutu_


_Subahanallah miye yasa zaki mutu? Kuma wace ce take magana ne?_


_Nice, kece wa? Ni samha! Wayyo samha sannu ganinan zuwa bana gida ne na fita amma ina hanya kiyi hakuri kinji?_


Gyara kwanciya samha tayi tare da sauke ajiyar zuciya,


_Ka taho da sahib, ki zaɓi ɗaya ni zanzo ko sahib? Sahib yazo,_


_ina uzirina kinje kin wani matsa na taho ni ina wani ruwana da ciwon cikin ki?  Anƙi ayi hakurin, ciwon cikinkin banza! kin wani bi kinsa an tadoni daga wuri mai nisa to ba sannu ba, kuma zan tafi bari ki sake sa a kirani kiga yanda zan miki lullusar fitar hayyaci,_


Lallai sahib ka zama ɗan iska wallahi, tayi kwafa,


_Wayyo sannu samha, Hydar sahib ya daina so na, kamishi magana banajin dadin abinda yakemin don Allah_


Lallai sahib ƙiriƙiri ya canja hali to Allah ya shirye ka, 


_Ahalinkin banza, ahalinki ahalina ne? M card na yarda banza a toilet nayi puloshin_


Haka dai tayi ta tunane tunane, har bacci ya dauketa, 


Hydar kuwa tafiyar samha fita yayi ya nufi masallaci, saida sukayi isha'i sannan ya dawo, shima bai zauna farlon ba yayi ɗakinsa dan hutama rayuwarsa,


Da safe saida samha tayi break sannan ta koma ɗaki tayi wanka, ta shirya cikin riga da sikat na atamfa, tayi kyau sosai, wayarta ta ɗauka tare da cewa yau alo tsiya alo danja a gidan nan, koni ko sahib dan yau duk abinda zai faru saidai ya faru dan yau ɗin nan sai an sadani da kawu, idan kuwa ba haka ba babu zaman lafiya a gidan nan dashi da munafukar matarsa, niko nace ina ruwan matarsa? 🤔


Kiran wayar ta farayi, hydar daya fito wanka jin wayar sahib yana ringing yasashi cewa tou pha Allah dai ya sawake wannan fitina, saidai ta kira kusan sau takwas sannan ya dauka ya fara magana cikin yanayin bacci, ya fara da cewa mayasatu ya akayi ne?


Samha tace nine mayasatu sahib? Tou akwai wata bayan ke? Banda shirme da sakarci kin tasar min madam daga bacci bakisan idan muna bacci ba'a kiran waya ba? Swry my wife mayasatu ce "yar anace kinsan bata da zuciya ne, yayi kamar yana magana da mace a kusa dashi,


Hydar yaci gaba da cewa swry don Allah kada ki wani damu bakiga nafi ji dake ba shi yasa kullum nake kwana a wurinki? Kai haba kada ki wani damu barni zanyi maganinta, don Allah kiyi hakuri muah 💋  samha tace na ci uwar matar dan ubanta ta karasa maganar tana kuka, sahib yace ke ahir ɗinki akan matata ta ina iya somar dake mtsww ya kashe wayan shi,


Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un samha tace, tare da faɗar an yanka ta tashi, lallai yau a gidan akwai kutumar babban biredi da botar, nice mayasatu? Nice "yar anace? Wani irin ihu samha tayi tare da cewa idan na yadda Allah ya babbakani, nice ba'aso itace ake so ake kwana a gidanta to bazan yadda ba,


Don Allah kuyi hakuri da wannan wallahi banda chargy ne,



*Jameela Musa* _Meelat Musa ce_

[05/04 4:46 pm] Washa: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊



                 *SO*

     *MUGUN WASA*



       *{ Love is a bad game }*




*JAMEELA MUSA* { meelat musa }




*Story, Writing & Editing*

                   *by*

         *Meelat Musa*


*_Kowa kukan gidansu yakeji, dan haka nima na gidanmu nake ji, jinjina gareku fatan alkairi addu'ar samun nasara ci gaba, hazaka lafiya da basira, alkairin Allah an daddanku BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION, mutane masu mutunci masu kara masu bartaba junansu da sanin darajar wanda suke tare dashi, hakika nikam naji daɗi kuma nayi dace daku Allah ubangiji ya barmu tare Allah ya kara haɗa kanmu ubangiji ya kara kwararo ruwan basira acikin ƙoƙon kawunamu baki ɗaya_*



                   *SO*

      *MUGUN WASA*


_Dedicated to_👇🏻

_Ramlat Abdurahman real mai dambu_



*53-55*


Miye banda shi miye namiji yake bukata a jikin mace wanda banda shi? Jikin mirow ta matsa tare da gogen hawayen idonta, sannan ta ƙarayiwa kanta kyakkyawan kallo,


Kwafa tayi sannan tace lallai wai kamarni sahib zai wulaƙanta? A gabana yake wa wata jaka kiss ko tsoron Allah bayayi, karshe ma jakar matar bata kaini kyau ba,


Da sauri ta fita daga ɗakin tayi kasa, a farlo taje tayi zaune sai kuka takeyi tana jiran fitowar hydar,


Hydar da sauri ya fito dan yabar gida tun kafin samha ta fito,


Yana ƙoƙarin saukowa yaga samha zaune, da sauri yaja da baya ya koma ta baya da gudu ya fice,


Saida ya kusa fita ya tsaya ya sauke ajiyar zuciya ya saita kanshi tare da tattaro ajinshi sannan ya ida fita,


Kallon Alale yayi tare da cewa kaje ka ɗauki samha kace mata kasan gidan sahib, kuje gidan Al' ameen da ita nayi ma matar sa bayanin komai, kaje maza kace ta shirya ku tafi,


Alale yace to, da sauri Alale yabar wurin ya nufo farlo, da sallama ya shiga, samha ta ansa ba tare data kalli inda Alale yake ba,


Cikin girmamawa Alale yace ranki ya dade mai gida yace inkaiki gidan sahib,


Samha tace ina yake hydar din ne? Alale yace zai fita ne, samha tace kaje kace mishi ina san ganinsa,


Alale yace gaskiya kiyi hakuri mai gida yau zaiyi tafiya ne, idanuwa samha ta zaro sosai sannan tace ina zaije ne?


Alale yace zaije *_Germany_* ne ganin likita, da sauri samha ta tashi tsaye tace da gaske? Alale yace wallahi kuwa, samha tace amma miyasa bai faɗamin ba?


Alale yace nima ban sani ba, bata sake magana ba, ta fita daga farlon da gudu, lokacin data isa wurin saidai mota ta baya ta gani domin duka motocin sun gama fita daga get din farko,


Ƙara rugawa tayi da gudu, tana kiran sunan hydar amma hydar bayajin samha, tsayuwa tayi a wurin tana kara fashewa da kuka,


Tambayar kanta takeyi mi tayi ma hydar zaiyi tafiya bazai mata bankwana ba? Ko shima yanzun ya daina tausayinta ne? Ƙara fashewa tayi da kuka sosai,


Alale dai yana tsaye daga nesa da ita yana kallonta, cikin kuka samha ta taho, ba tare da tayi ma Alale magana ba ta wuce ta shige ciki,


Da gudu mai dawo da mutum baya samha ta haye sama, tana zuwa dakinta da gudu ta isa inda wayarta take ta dauka ta fara kiran wayan hydar, amma a kashe wayar,


Samha tace hydar miyasa zaka min haka ne? Bayan kasan kai kaɗai nake gani inji daɗi kaine kake kwantar min da hankali saika tafi ka barni kuma babu sallama mi nayi maka wanda yayi zafi haka?


Cikin kuka samha ta tashi tayi ɗakin hydar, tana zuwa ɗakin tunda ta shiga taga wata zungureriyar farar takarda saman gadon,


Da sauri ta isa wurin gadon, takai hannunta ta ɗauki zungureriyar takardar ta fara dubawa,



_Samha barka da safiya, da fatan kin tashi lafiya? Ya hakuri da hydar & sahib? Sannu kinafa kokari sosai, lallai sai yanzun na yadda ke babbar jarumace 👍🏻, da banda kike jaruma da yanzun sahib yasa miki ciwon zuciya kema, nikam kinga tawa zuciyar rauni ne da ita, kuma ta dalilin san danake ma matata na kamu da ciwon zuciya, lallai kina da zuciya mai kafiya samha, zuciyar hydar kuma rauni gareta, zuciyar sahib kuma tana da san kai, to idan aka haɗa, kafiya, rauni + sankai kai, ƙarshe zai haifar da mi? Ki fiddo min wannan ansar kafin in dawo,_


_Ga Alale nan na bar miki  duk inda zakije zai kaiki, idan kina san kuɗi ki rika dauka a inda kika ga ina ɗaukan kuɗi kinji? Naje ganin likita bazan dawo ba sai bayan wata ukku, fatan zaki zama lafiya,_


A hankali samha ta kwanta saman gado, tare cewa, mi hydar yake nufi? Ƙanƙance idanuwanta tayi tare da cije leɓonta na ƙasa, 


_Zuciyar samha tana da kafiya_


_Zuciyar hydar kuma tana da rauni_


_Sahib kuma zuciyarsa tana san kai_


Ajiyar zuciya samha tayi tare da cewa lallai akwai alamar tambaya a maganar hydar,


_Kafiya, rauni + san kai, ki fiddo ansa kafin in dawo_


Lallai,


_Kafiya_

_Rauni_   =  _{ Nadama, ko rashin adalci }_

_Sankai_


Tashi tayi zauna tare da cewa lallai ƙarshen kafiya, nadama ne, karshen san kai shima nadama ne, karshen rauni ma zai iya zama kayi nadama idan har kayi rauni akan abinda kasan bazai yuwu ba,


To lallai dai, wannan amsa itace, nadama,


_Kafiya_

_Rauni_  = _{ Nadama }_

_San kai_ 


To waye zaiyi nadama tsakanin sahib samha & hydar? 


Dogon nazari samha tayi tare da cewa lallai a cikinmu ina ganin wanda zaiyi nadama,


Nine dani da sahib, saboda ina da kafiya shi kuma sahib yana da san kai, to miye zai faru wanda zamuyi nadama? Me hydar yake nufi ne?


Lallai ya zamar min dole in gano dalilin dazaisa inyi nadama, tashi tayi ta shiga toilet ɗin hydar tayi wanka, harta fito nazarin abinda zaisa ta tayi nadama takeyi,


Saida ta shirya sannan ta ɗauko kaya a inda hydar yake ɗauko mata ta saka, tare da cewa Allah ya kaimu gobe lafiya, maganar Alale ta fara tunowa,


_Ranki ya dade mai gida yace inkaiki gidan sahib_


To a gidan sahib zanyi nadama ne? Kai bazai yuwuba nikam bana nadama saidai hydar da sahib zaiyi nadama, dan idan wani abu ya sameni a gidan sahib hukuma zata hukunta su,


Lallai koma miye a gidan sahib zanji, Allah ya kaimu gobe, murmushi samha tayi tare da cewa ƙalubale gareki matar sahib, 


Amma gaskiya sankai rashin adalci ne,  hmm mu hadu dai in gani da idona,


Yinin ranar nan samha wasi wasi tayi, tayi a zuciyarta, da kuma marecen jiya yanda ta kasance tsakaninta da hydar yayi ta mata yawo a rai, yaukam samha ta kasa tabuka komai ko abincin data girka kasa ci tayi dan ta saba ita da hydar yana bata a baki, tayi zaune a dirning area ta dora kanta saman dirning sai kuka takeyi,


Shi kuwa hydar bayan tafiyan Alale babu abinda suka tsaya yi sai shiga moto, suka fara fita daga gidan, shine fa samha tana fitowa ƙallin motar ɗaya ta gani, su hydar kuma suka ibi hanya sai birnin tarayya Abuja,


Yaukam samha bacci babu wani daɗi tayi shi har gari ya waye, tana tashi bayan tayi sallah ta kara koma ta kwanta,


Saida ta gaji dan kanta ta farka, tana farkawa toilet ta shiga ta wanke fuskarta da bakinta sannan ta fito, ta nufi BQ a kofar dakin Alale ta tsaya tana cewa zan shirya yanzun, saika shirya kafin in fito,


Alale yace ranki ya dade da kanki? Samha tace Ey, kuma kayi sauri, yace an gama matar Oga, da sauri ya kama bakinshi tare da cewa Oga sahib ikon Allah,


Ba tare da samha tayi magana ba ta wuce, Alale yanajin fitarta ya fara kiran wayar Al' Ameen ya fada mishi cewa gasunan zuwa yanzun insha Allah,


Al' Ameen yace Allah yasa kuzo lafiya, Alale ya amsa da Amin tare da kashe wayanshi,


Samha kuwa saida tayi break sannan taje tayi wanka, ta shirya cikin wani lafiyayyan material mai kyau da tsada, gyale da jaka da takalmi wasu kyau wanda suka dace da material ɗin data saka, tayi matukar kyau sosai,


Tana gamawa ta sauko, kicin ta nufa ta ɗauki lafiyayar wuƙarta, harta ɗaga rigarta zata soka ta, ta tuno,


_Ki daina faɗa da wuƙa wannan haline na mutanen banza_


Maganar hydar, sai kuma sakonsa na cikin wasiƙar daya bar mata,


_Zuciyar samha tana da kafiya_


Ajiyan zuciya samha tayi tare da ajiye wuƙan, da sauri ta fita daga kching in ta fice waje,


Tana fitowa da sauri Alale ya buɗe mata mota, umm su samha aka wani kashe a gidan baya, Alale ya rufe mata sannan ya zagaya mazaunin driver ya shiga yaja suka ɓace daga wurin kamar walƙiya,


Tafiya sukeyi babu mai magana, dama ina ruwanka da driver, saida sukayi tafiya mai nisa sosai sannan samha tace am Alale don Allah ka biya dani ta gidan kawu,


Alale yace gaskiya kiyi hakuri mai gida baice min inje wani wuri ba, gidan sahib kaɗai yace, samha tace ina ruwana da mai gida baice ba,


Kayi yanda nace mana, Alale yace kiyi hakuri wallahi hakan bazai yuwu ba,


Dan hydar yajawa Alale kunne sosai akan daga ba gidan Al' Ameen ba kada yaje da ita ko ina idan kuwa ba haka akwai babban matsala, 


Samha tace zamuje ko kuwa? Alale yace don Allah kiyi hakuri wallahi idan ba haka ba zaki yanke min abincina, samha tace to aini duk abinda nake so shine hydar yakemin kai miyasa bazakamin yanda ya saba ba?


Alale yace saboda ni ba hydar bane, ni yaronsa ne a ƙasansa nake kuma kinsan saɓawa ubangidanka rashin amana ne tunda baya nan kiyi hakuri,


Kwafa samha tayi daga haka bata sake magana ba, har suka isa gidan Al' Ameen, 


A bakin get Alale ya tsaya tare dayin horn, da sauri mai gadi ya buɗe musu ganin motar hydar ne, dan shine ubangidan Al' Ameen, ya fara kai gaisuwa, Alale yace malam sani ya aiki?


Malam sani yace Alhamdulillah yau ina mai gidan namu ne? Alale yace yaje ganin likita ne, malam sani yace Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana Alale yace Amin, malam sani yace wannan itace Amaryar mai gida ne?


Murmushi Alale yayi tare da jan motar yana cewa um, dan kada Malam sani ya ɓallo aiki, banda jinjina kai babu abinda samha takeyi tare da karewa gidan sahib kallo lallai namiji munafiki ne,


Wannan ƙatoton gidan ya gina? Ga wasu jibga jibgan motoci mai lumfashi na tashin hankali a daidai lokacin da Alale ya fito ya buɗewa samha mota,


Kallon Alale samha tayi tare da cewa wannan ƙattin gwangwanayen na waye? Wai motocin sune gwangwani, Alale yace to na sahib ne gidanma nashi ne,


Haka samha ta ƙara riƙe jakarta sosai tana karewa gidan kallo ya haɗu ta ko ina, wato da sahib yace mata saiya gama gina gidansa zasu dawo shine yana gamawa yayi aure abunshi, wani baƙin ciki taji ta tokare mata zuciya kamar magunar ruwa ta toshe, Murmushi samha tayi tare da tunanin,


_Zuciyar sahib tana da sankai_


Murmushin takaici samha tayi tare cewa lallai sahib akwai san kai, Alale yace muje ciki, murmushin karfin hali samha tayi sannan tabi bayan Alale suka shiga ciki,


A farlo Alale yayi ma samha mazauni saman kujera ta wani kashe tare da ɗaukan ƙafa ɗaya saman ɗaya ta ɗora tana ƙara bin ƙaton farlon da kallo, hotunan sahib ne yana cikin yanayin farin ciki, ga kuma wasu daga kusurwar farlon wanda duk ɗaya yakai tsawon samha, sahib ne da wanda take tunanin itace matarsa,


Wani irin gurnani samha tayi tare da tashi tayi ta ɓarar da hotunan, yanda takeyin abun ya bawa Alale dariya dan haka ya fita daga farlon da sauri, ya fara kiran wayar hydar,


Haka tayi ta hauka tana zubar da hotunan na sama dana ƙasa, matar Al' Ameen ta fito da sauri tare da cewa haba mayasatu? Sai kawai kizo gidana kiyi ta hauka babu ji babu gani?


Samha tace kece wace jaka ke kuma? Haba hajiya samha dani dake ai kinsan waye jaki, nan fa gidana ne, gidan aurena ne, mijina yake sona, shi yasa ya kashe makuɗan kuɗaɗe ya ƙayata mana farlonmu da kujeru na alfarma, haka ya ware zunzurutun kuɗaɗe yayi mana manyan hotuna ya ajiye a farlo dan mu riƙa ganin juna munajin nishaɗi,


Shine dan ɗanyen iskanci kika zo kika fasa ko? Samha tace na fasa dan uwarki kuma yanda na fasa hotunan nan haka zan fasa miki kwakwalwar kanki baki san ni ɗaya nake da mijina ba? Wane ɗan iska yasa kika auranmin miji? 


Zama matar tayi saman kujera tare da cewa, abinda yasa na aureshi saboda ina sansa yana so na, shi yasa ya gina gidanshi ya kawoni ya adanani a ciki, ke kuma ya ɗaukeki yakaiki gidan hydar domin kiyi mishi shara da wanke wanke,


Kuma hydar yayi miki babban halakci amma kinƙi ki gode masa, kowa gudunki yakeyi amma hydar ya raɓaki cikin rayuwarsa, sahib ya gujeki a daidai lokacin da kike gaɓar mararin namiji a kusa da ke,


Ya gaya miki maganganu masu muni da ɗaci amma da yake baki da zuciya kanki yana hayaƙin yarinta kin kasa fahimtar waye yake sanki,


Banda Allah ya baki aron dama samha ke harkinkai matsayin zama da hydar a inuwa ɗaya? Samha tace da Allah rufemin baki kada inci kutumar kan babbar biredi da bota, matar Al' Ameen tace bazanyi ba,


Tashi samha tayi taje wurinta tare da gagara mata lafiyayyin marirrika, murmushi tayi tare da dafe wurin a ranta tace kinci albarkacin hydar, a bayyane kuma cewa tayi,


Naji ba komai, nidai mijina yana so na, ke kuma baya sanki, ta kece da dariya mai cin rai tayi ma samha, tare da cewa a fitar min daga gida kuma daga yau na sake ganinki gidan nan zakiga yanda zan zazzaga miki fetir in cinna miki ashana,


Da samha da Surayya matar Al'Ameen haka suka caku kowa yana faɗawa kowa magana mai zafi, Alale ne ya shigo farlon yana cewa ranki ya dade kiyi hakuri, kizo muje ki bari sai mai gida ya dawo zaiyi miki maganinsu,


Haka dai Alale ya lallaɓa samha suka tafi, fitarsu matar Al'Ameen ta zauna tare da sauke ajiyan zuciya tace kai lallai hydar ya jajibo ma kanshi jaraba, wannan yarinya da masifa take, danaga tana da saukin hali dana warware mata komai,


Koda suka koma gida samha banda mita babu abinda take, sai tuno maganganun matar sahib takeyi, wai itace mayasatu, dan tsabagen wulaƙanci har matarsa ya faɗa mawa itane mayasatu,


Haka dai ta gaji da jarabarta tayi shiru, tunda bata da mai bata hakuri, sai yau tasan hydar yana da amfani, lallai da hydar yana nan dayaci mata uwar sahib dashi da wannan guntuwar matar banzan sa,


Tsoki samha tayi tare da cewa kuma matar itama "yar gayu ce, kana ganinta kasan hutu ya zauna mata,


Toko dan hydar yaga matar sahib yasa yace in riƙa gayu, ko nima sahib zaiso ni?


Lallai hydar yana so na, wato baya san in zauna a matsala shi yasa yake cemin in gyara,


Haka dai rayuwar samha taci gaba da tafiya a gidan hydar, addu'arta Allah ya dawo da hydar lafiya yaci mata uwar sahib,


Samha duk ta takura gaba ɗaya batajin daɗin zaman gidan, kuma har yanzu hydar yaki ya ƙirata, bare ta faɗa mishi abinda matar sahib tayi mata,


Rayuwarta bata ɗakin hydar bata ɗakinta, haka zataje tayi kwanciyarta a ɗakinshi tayi ta tunane tuna ne, lallai sabon lamari ku tsaya kuji tunanin samha,


Kwance take a saman gado idonta yana kallon sama, 


_Hydar yayi miki babban halakci amma kinƙi ki gode masa, kowa gudunki yakeyi amma hydar ya raɓaki a cikin rayuwarsa, sahib ya gujeki a daidai lokacin da kike gaɓar mararin namiji a kusa dake!_


Mi hakan yake nufi ne? Kota na nufin ni "yar iska ne? Mtswww,


_Naji ba komai nidai mijina yana so na, ke kuma baya sanki,_


_Banda Allah ya baki aron dama ke harkinkai matsayin zama da hydar a inuwa ɗaya?_


Ajiyan zuciya samha tayi tare da cewa lallai hydar ba sa'ar yara bane, tunda duk abinda mace take nema wurin namiji hydar yana dashi 100% saidai abinda baza a rasa ba, dan mutum 9 ne bai cika goma ba, suffanto hydar samha ta farayi, ta dade tana tunaninta daga baya tace lallai fa hydar ɗan gayene,


Yana da kyau mai ɗaukar hankali, kuma idanuwanshi ma suma suna da kyau, suna birgewa idan yayi kallo dasu, murmushi hydar ta tuno yanda yakeyi sai beaty point nasa ya fito,


Haka dai samha tayi ta nazari tare da tunanin hydar a ranta, dan yanzun yanda take tunanin hydar bata tunanin sahib haka, ga lokacin da hydar ya iba zaiyi a germany harya wuce shi sosai,


Ita inda zata samu number hydar tayi waya dashi take nema amma bata samu ba, kuma tayi ma Alale magana yace baida shi, kuma tace yakaita zataje wani wuri yace mota ta lalace,


Gaba ɗaya zaman gida ya isheta kullum bata ɗakin hydar bata ɗakinta bata filin wasansu, sai taje inda aka ajiye  mashin tahau ta zauna,tayi ta tunanin marencen su daren tafiyan hydar,


Yauma tsaye take a gaban Alale wai yakaita gidan matar hydar, idanuwa Alale ya zaro tare da cewa ranki ya daɗe me zakiyi a can ne? 


Murmushi samha tayi sannan tace kawai zanje ne, Alale yace to wallahi ki rufa ma kanki asiri dan bata san mai gida idan ta ganki zata miki rashin mutunci, haka dai Alale yayi ta ƙaƙuba ƙarya yana ɗirkakawa samha, akan matar hydar,


Wanda cikin natsuwa samha ta gano irin halinta ɗaya da matar hydar amma banbancinsu ita tana san sahib, amma ita matar hydar yana santa ita kuma bata san hydar, murmushi samha tayi tare da darkakawa maganar Alale ❓


Murmushi samha tayi sosai dan ta lura Alale yana da zafin surutu, kallonshi tayi sannan tace to ya sunan matar hydar? Daburcewa yayi dan baisan amsar da zai bawa samha ba,


Samha tace kayi shiru Alale yace kai gaskiya na manta sunan ta, samha tace bakaje ɗaurin aure ba? Alale yace naje mana, samha tace tuno ranar mana,


Dukan da aka kaiwa samha yasa ta saurin miƙewa tsaye, Asma'u ce ta cakume wuyan samha tare dakai mata duka summun bukumun, Alale yace ke Asma'u kinsan abinda kike kuwa?


Samha ganin zata daku da yawa yasa ta fara maida martali, haka sukaci gaba da cakuwa a gaban Alale yana kokarin rabasu amma samha tayi ma Asma'u kyakkyawan riko, dukanta kawai samha takeyi duk ina na jikinta, harsai data cirewa Asma'u haƙori ɗaya,


Asma'u ganin haƙorinta a ƙasa yasa ta yin kukan kura tare da cewa kutumar duma du, ni kika cirewa hakori ɗaya? Zakici kutumar ubanki dake da hydar ɗin zanje in faɗawa dadyna sai zakici uwarki ɓarauniyar banza,


Samha tace dadynkin banza shima idan yazo zanci uwarsa in cire haƙorin banza kamar yanda na cire naki, dadyn zaki daka dan uwarki? Samha tace yo bazan daki banza ba sakara "yar gidan mai dattin hula,


Dadyna ne mai dattin hula? Zaki raina kanki banza "yar wasan caca, samha tace naji ke kuma kwartuwa, nice kwartuwar? Tsoki samha tayi sannan tabar wurin,


Nan Asma'u ta tsaya tayi ta zungurawa uwar samha zangi, saida ta gaji dan kanta sannan tayi tafiyarta,


Tana tafiya Alale ya kira hydar tare da yi masa ya hanya? Hydar yace sun kusa ƙarasowa amma idan ya shigo yana da meeting, 


Alale yace to ranka ya dade ko in taho in tara ne? Sai mu taho gida baki ɗaya? Hydar yace A, a, fatan alkairi Alale yayi masa sannan ya kashe wayanshi,


Ita kuwa samha tana zuwa ɗaki saida tasha kukanta sosai tare da tambayar kanta ita kuma wannan wace ce ita? Kuma mi nayi mata tayi min duka? Mi dadynta zaimin dani da hydar?


Mtsww shirmen banza, tashi tayi taje tayi wankanta ta haye gado tayi kwanciyarta,


Hydar kuwa suna isowa saida yayi abinda zaiyi ya gama, sannan sukayo gida, zuciyar hydar tana harbawa, yana shauƙi zaiga nuril ƙalbinsa, tare da addu'ar Allah yasa kada samha ta yaba mishi,


Samha dake kwance tana tunanin duniya, jin shigowar motaci yasa ta tashi da sauri ta matsa jikin window lallai hydar ne, dariya tayi sosai tare da ɗora hannunta saman bakinta, ganin hydar ya fito daga mota yasa ta tabbatar lallai shine,


Wani irin juyi samha tayi tare da zungurawa da gudu irin na "yan gayu, tunda ta fito daga farlo take kiran sunan hydar, shi kuma yana tsaye a wurin mota yana magana dasu shamsu, jin muryar samha yasa hydar juyowa yana murmushi, sannan ya matso daga cikin mutane, da gudu samha ta iso ta rungume hydar, shima riƙeta yayi sosai a jikinshi, yanajin farin ciki yana ratsa shi,


Tou pha, tunfa anan samha ta shiga rattafawa hydar dukan da Asma'u tayi mata, murmushi hydar yayi tare da jan hannunta suka bar wurin,


Saida suka shiga farlo hydar ya saki hannunta yayi gaba da sauri take bin bayanshi tana ci gaba da faɗa mishi, saida sukaje ɗakin hydar samha bata daina surutu ba, kamar an ɗaura mata na'urar labarai,


Aje wayoyinsa hydar yayi a saman bedsite, sannan ya juyo wurin samha ya jawota jikinshi, cikin gajiyayyir murya yace samha wai ke mi yake damun kanki?


Cikin tsiwa samha tace ka dawo fa an fara, wani kaina yana da wani abu,  ni babu wani abinda yake damun kaina,


Kallon ta hydar yayi sannan yace hmm ke samha baki iyayiwa mutane sannu da zuwa ba? Na dawo daga tafiya babu ya hanya ba komai sai kawo ƙara an miki an miki ke kullum an miki,


Samha tace ai nasan ka dawo lafiya tunda na ganka, gaka kayi kyau ma ai,  sai kamshi kakeyi amma ka ɗan rame ne miya sameka? 


Ajiyar zuciya hydar yayi sannan ya kara riƙe samha a jikinshi ya ɗaga kanshi sama, ita kuma tana kwance saman kirjinshi, hydar sai fitar da wani irin wahalallen lunfashi yake saukewa, yau dahar samha tana cikin sanshi har ya hango yanda wannan daren zai kasance a wurinsa,


Samha tace hydar kasan abinda na gani a gidan sahib? Har yanzun samha tana kwance a jikinsa, hydar yace Uumm, samha tace hadayin hoto da jakar matarsa, hydar yace kema sai inyi dake muma musa a farlo,


Samha tace waye yace maka a farlo yasa? Sauko kanshi yayi sannan yace dan naje gidan ai na gani, ke kuma ya kikaga matar sahib? A daidai lokacin da yake sakin samha daga jikinshi yana cire kayan jikinsa danyin wanka,


Samha tace katuwace, hydar yace kinga ko idan ta zauneki bazaki iya motsin kirki ba, dariya samha tayi sannan ta matsa ta zauna saman gado taci gaba da bawa hydar labarin dukan da Asma'u tayi mata,


Kallonta hydar yayi tare da cewa wace Asma'u ce? Nandai samha ta kwashe komai ta faɗa mishi, hydar yace waya kaiki? Ɗiyar kanin dady ne, kinsan halinsa kuwa? Wallahi makircinsa yawa gareshi, dashi aka haɗa kai aka kashe min iyayena amma sai aka laƙaba abun da haɗarin jirgin sama,


Ita Asma'u ɗiyarsa ce, nine yake so na aureta ina lallaɓasu ne badan banda abinda zanyi ba ko sunfi ƙarfina ba, na barsu ne kawai ina kallonsu amma zanyi maganinsu,


Yana faɗin haka ya shige toilet, ita kuma ɗaukar wayarsa tayi tare da kwanciya saman gado tayi ta latse latse, har hydar ya fito wanka, bayan ya fito ne yace samha jeki ki dafa min lipton, tace to tashi tayi tare da ajiye wayar ta fice,


Samha tana fita hydar ya ɗauki wayanshi ya fara kiran wayar Asma'u, bayan ta ɗauka hydar ya fara magana cikin tsakanin ɓacin rai yace miya haɗaki da matata har kika zo har gidana kika daketa? Asma'u tace yaya ciremin haƙori tayi fa,


Hydar yace haƙorin kin banza, an faɗa miki na haɗa samha da wata a faɗin duniyar nan ne? To na rantse da Allah daga yau sai yau idan har kika sake zomin gida wallahi saina ƙarya ki, yana faɗin haka ya kashe wayarshi,


Hydar na kashe waya Asma'u ta fashe da kuka dan tasan zuciyar hydar idan yace zaiyi zaiyi bare har yayi rantsuwa, haka taje ta faɗawa dady lalai da gaske hydar yayi aure,


Dady yace to barni da ita zanci ubanta Allah ya kaimu gobe lafiya, Asma'u ta ansa da amin,


Ita kuma tana gama dafa  tea ɗin ta zuba a kofi ta taho dan kawo ma hydar, daidai kofar ɗakinta suka haɗu, hydar ya shige ɗakinta itama ta bishi,


A gefen gado ya zauna ta bashi tea ɗin, yace kinci abinci ne? Samha tace banajin yunwa, hydar yace wai miya sameki ne nifa naga duk kin wani burkuce, itama zama tayi kusa dashi tare da ɗora kanta a jikin hydar, itadai Allah ya sani hydar yana burgeta sosai, 


Haka dai tayi ta tunane tunanenta har bacci ya dauketa, shi kua yana gama shan tea ɗinshi ya sauke samha daga jikinshi ya gyara mata kwanciyarta, ya ɗauki kifin ya fita,


Tun cikin bacci samha takejin ala luƙaƙa zagi a farlo, da sauri ta tashi zaune tare da duba a gogo taga 7:09am da sauri ta fita daga ɗakin tayi waje,


Asma'u ce da dadynta, dadyn yake zagin, Asma'u tana ganin samha tayi inda take da gudu, ganin ta kusa zuwa wurinta yasa samha ta ruga tayi ɗakin hydar,


A bakin kofa tayi tsaye dan hydar yace idan tana shigowa ɗakinshi da gudu zataji a jikinta, samha tace hydar taho, hydar dake zaune saman abin sallah yana karatun qur'ani ya juyo, samha tace taso ka gani, juyawa yayi yaci gaba da karatunsa,


Ƙarar marin da hydar yaji yasashi ƙara juyowa, da sauri ya rufe kur'anin ya tashi yana cewa wane hannune ya marar min fuskar matata? Daga samha har dady da Asma'u kallon hydar sukeyi,


Asma'u tace nice nan, da sauri hydar ya kama hannun Asma'u ya ƙaryashi sannan yace mina faɗamiki? Saboda tsabar iskanci har kizo a gabana kina marin samha? Har yanzun samha maimata kallamar,


_Wane hannune ya marar min fuskar matata?_


Wannan tunanin samha takeyi a ranta, tare da maimata kalmar a zuciyarta, bata gama tunanin ba, taji dady yana cewa wallahi wannan ɗiyar saika saketa, da sauri samha takai dubanta wurin hydar,





*_JAMEELA MUSA - Meelat Musa_*


💋

[05/04 4:46 pm] Washa: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊



                 *SO*

     *MUGUN WASA*



       *{ Love is a bad game }*




*JAMEELA MUSA* { meelat musa }




*Story, Writing & Editing*

                   *by*

         *Meelat Musa*


*_Mai dambu_*

*_Mai dambu_* { _Zuciyar meelat  musa }_

*_Mai dambu_*


*_Asmeenat Xeeyan ina miki fatan alkairi, kuma ina ƙara bawa zuciyarki hakuri kinji aminiyata, kiyi hakuri ki manta da wannan lamarin kibar komai a hannun meelat musa ni zanji da komai, Allah ya tona asirin munafiki Allah ya hana mugunta tayi tasiri,_*


*_Gaisuwa gareku marubuntan zamani, fatan alkairi Allah ya kara basira da zahaka ubangiji yasa ku zarce haka a faɗin duniyar marubuta, jameela musa ke cewa ku sarara abunku kuyi ƙarko tare da yin shekaru irin na DABINO_*👇🏻


*_Asmeenat Xeeyan_*

*_Ramlat Abdulrahman mai dambu_*

*_Bilkisu Khalisat_*

*_Ummu Affan_*

*_Halima Tweety_*

*_Hasina Oganniya_*

*_Halima Leema_*

*_Maryam Muhammad_*

*_Raheema_*

*_Surayya_* 💔

*_Ummu Sayyed_*

*_Ummu Farhana_*

*_Saleehat_*

           *_&_*

*_Auta Ummu Harny_*



                  *SO*

      *MUGUN WASA*



_Dedicated to_👇🏻

_Ramlat Abdulrahman real mai dambu_




*56-58*



Har yanzun hannun Asma'u yana riƙe a hannun hydar sai wani ƙara murɗeshi yakeyi tare da cewa matata abokiyar wasanki ce?


Asma'u kuwa da tuni ta suma saboda azaba, shi kuwa dady cewa yake saboda wannan ɓarauniyar ka kashe min ɗiya?


To wallahi duk ubanda ya tsaya maka yau saika saketa,


Ubanka harya bar duniya yanajin magana na, kai kuwa baka isa kazo min da raini ba,


Cikin tsananin ɓacin rai hydar yace ubana daban ni daban, can zumuncinku ya haɗaku kuma shine yaji zai iya biyayya akan duk abinda kace yayi,


Dady yace kai ban isa dakai ba? Hydar yace sosai ma, ni baka isa dani ba, danni a faɗin duniyar nan maganar mutum ɗaya nakeji, kuma gatanan tsaye a gabanka, a daidai lokacin da hydar ya harba Asma'u da ƙafarshi ta faɗi ƙasa,


Hydar yaci gaba da cewa samha _ZUCIYATACE_ ya dafa daidai saitin  zuciyarsa, sannan yace ita samha _RUHI NA CE_ dan duk wanda ya taɓa samha haƙiƙa yana man wasa da rayuwata ne, duk wanda yayi min wasa da rayuwa haƙiƙa nasan baya ƙauna na, har  yanzun hannunsa yana daidai zuciyarsa,


Cikin ɗaga murya mai tada hankali hydar yaci gaba dace to kuwa kaga wasa da rayuwa ganganci ne, dan inajin samha itace _LUMFASHI NA_ kaga kuwa duk wanda naga zai gigin zare min raina, to nine zan kasheshi tun kafin ya kasheni, ya ƙarasa maganar yana dafa kirjin sa,


Dady ya ɗaga hannunsa ya darkakawa samha mari, da sauri hydar ya rumtse idanuwanshi kamar an caka mishi wuƙa, murmushin ƙarfin hali hydar yayi ya kalli dady tare da cewa kada ka ƙara, dan nayi alkawari da zuciyata duk hannun daya hau saman jikin samha bayan nawa saina gundileshi,


Kai kuwa daka tashi dukanta ma kayi? Jinjina kansa yayi tare da cewa yau da bakai bane saina tsiyaya maka idanuwa,


Dady ya saki baki cikin yanayin mamaki yake kallon hydar,


Tsoki hydar yayi sannan ya kalli samha yace wuce kije kiyi baccinki,


Dady yace idan kika shiga saina sassaraki, hydar yace shiga ya sassarakin in gani,


Ta gaban hydar samha ta raɓa ta shige ɗakinsa, shi kuma dady, ya ciro wayarsa ya fara waya,


Shima hydar wayar yakeyi tare da zagin su shamsu duk suna aikin mi suka bar dady ya shigo mishi gida?


Faɗa hydar yayi sosai tare da cewa dukansu suzo yanzun nan yana neman su,


Ita kuwa samha tsayuwa tayi a tsakiya ɗakin tana tambayar kanta, ya akayi kuma hydar yake cewa ita matar sa ce?


Shigowar hydar yasa ta juyo da sauri tana kallonshi, shima ita yake kallo tare da cewa ba nace kiyi bacci ba?


Cike da tsiwa samha tace banaji bacci, amma miyasa kace min ni matar ka ce? Hydar yace saboda ke matar tawa ne,


Samha tace ta ina na zama matarka? Cikin fushi hydar yace ke kada ki kawo min raini, kalmar mata nawa kika sani a yaren hausa?


Samha tace irin wanda ka sani nima shine na sani, hydar yace to yanda kika fahimta haka nake nufi,


Samha tace to aiko lallai idan harni matarka ce bana sanka, kuma Allah ya sani bazan iya zaman aure dakai ba,


Idanuwa hydar ya zaro tare da cewa wallahi ƙarya kike, nine mijinki, kuma maganar bazaki zauna dani ba ai kema kinsan ƙaryar banza ce,


Cikin mamaki samha tace to yaushe ma aka ɗaura min aure dakai har na zama matar ka?


Hydar yace tunani ya zama naki, ni nayi nawa tunda na faɗa miki,


Don haka a cikin abinda na rubuta miki lokacin da zan tafi *_Germany_* anan zakije kiyi dogon nazari tunda kina da wayau nan zaki gano waye hydar a wurinki,


Yana faɗin haka ya fita daga ɗakin dan su shamsu sun iso,


Shima dady bataliyar daya tara suna farlo gaba ɗaya dai gidan ya cakuɗe, hydar hankalinsa a tashe dan kaff ahalin dadynsa babu wanda yasan yayi aure,


Amma yau Asma'u ta tona masa asiri kafin ya gama abinda yakeyi, lallai yasan yau samha saita bar gidan kuma shima yasan yaune lumfashinsa na ƙarshe a duniya,


Kakar hydar wanda ta haifi mamanshi itama dady ya gayyato ta a wurin wannan babbar badaƙala, 


Samha kuwa banda kuka babu abinda takeyi tare da faɗin sahib ya cuci rayuwarta, ya saka ta cikin harƙala mi sahib yake nufi da ita?


Bayan gida ya gama haɗuwa "yan uwa da abokan arziki, an cika paff a farlo, babu abinda kakeji sai "yan ƙananan maganganu kowa da abinda yake faɗa,


Kiran hydar akeyi amma shi yana can yana riƙon samha kamar ansashi kama maciji, ita kuma sai wani zuƙewa takeyi tana kuka tare da cewa ita bata auren hydar sahib takeso,


Hydar kuka yakeyi yana cewa samha nine sahib, ina samha bata gane karatun, neman hanyar tsira da rayuwarta takeyi dan tana jin "ya"yan dady sunce zasu kasheta tunda har hydar ya ƙarya yayarsu saboda ita,


Wasu kuwa cewa suke bazai yuwu ba, yama za'ayi yaya hydar ya auri wannan jakar yarinya, 


wasu kuma tunani sukeyi yaushe hydar yayi aure basu sani ba? 


Kakar hydar ce tace wai Aliyu bazai zo ba? Tana magana da yarenta wanda bai fita,


Dady ne yake ta zazzare idanuwa tare da cewa har kashedi yamin saboda tsinaniyar yarinyar nan waida ba nine na daketa ba saiya tsiyaye min idanuwa babu tausayi,


Samha kuwa girgije hydar tayi daga riƙon dayayi mata, shi kuma ya ƙara ɗamƙota tare da ɗago mata fuska yana cewa samha ki zama mai adalci a rayuwarki, kada san zuciya yasa kiyi abinda daga baya zakiyi dana sani,


Samha tace kai Rrrr da Allah, tunda kaga har banyi dana sani a baya ba, har abadan duniya bazanyi danasani ba, wato saboda ma ka ɗaukeni daƙiƙiya kenen ma kaine sahib? Lallai bansan fushin zuciya yana sa mutum ya zama mahaukaci ba sai yau,


Hydar yace ki gyara kalamanki akaina, danni nasan abinda nakeyi banda taimakon dana ba rayuwarki da yanzun nan baki a faɗin duniyar nan, samha tace bazan gyara ba, kuma ina so ka soke duk wani taimako tsakanin ka dani kaga zan fasa rayuwa ne?


Murmushi hydar yayi tare da cewa ke "yar wasan kwaikwayo, wasan ya isa haka, ai nasan zuciyarki tana san hydar,


Tuff samha tayi sannan tace Allah ya sawaƙe ma rayuwata, zuciya na da gangar jikina su rayu da abokin gaba,


Kakar hydar ce ta shigo ɗakin tana magana da hydar cikin wani irin yare, kamar fulatanci kamar kuma yaren shuwa, yaren dai kamar labaracci ne, hydar shima cikin irin yaren yayi magana sannan suka fita daga ɗakin yana cewa ki jirani ina zuwa, yace ma samha,


Su shamsu da dady da Alale da faruk kowa yabi bayan hydar suka sauka farlon ƙasa dan acanne kowa yake jiransu,


Fitar su hydar samha ta matsa jikin bedsite ta buɗe loker ta ciro biro da joter, ta ɗora a akai ta fara rubutawa kamar haka,


_Zuwa ga hydar,_


_A rayuwa amana tayi ƙaranci, ban taɓa sanin zamba da zalinci halinka bane sai yanzu, kayi nasara wurin jinyatar da zukata guda biyu tunda har kayi ƙoƙarin raba samha da sahib_


_Kayi nasarar rabani da sahib, nikam babu abinda zance maka sai ince sannu da ƙoƙari babban ibilishi, dan duk wanda ya raba aure haƙiƙa yakai babban sheɗani,_


_Na barka da Allah, bazan taɓa yafe maka ba harƙarshen rayuwata ba, kuma saboda baka so na, yasa kasa sahib ya yadar min da m card saboda kana so rayuwata taci gaba da lalacewa a titi, babu dangin uwa ba na uba, haka na taso ban san mai kyau ba bansan mara kyau ba, tunda bani da wanda zasu koya min kyakkyawa ko mummuna, na barka lafiya, nima naje in gano ahalina, kuma daga kai har sahib kada kusha wahalar nema na, dan na riga nayi muku nisa_


_Kunso inyi ta zama a ƙarƙashin ku kamar wata karya, to Allah yaga zukantaku shi yasa ya tseratar da rayuwata daga hannun azzalimai guda biyu, Allah ya taimakeni baku tarwatsamin rayuwa ba, da mutane sun ɗauka ni karuwa ce, tunda har kukayi kokarin yin aure dani a cikin sirri, har kake min fatar kamin ciki, wato in cikin shege ko? To Allah ya fika_


_Daga samha,_

                  _Zuwa gareka_

_Babban maƙiyi na hydar_


Samha tana gamawa ta ajiye, ta ɗauki hijabi ta saka, sadaf sadaf ta fito babu kowa a sama amma kana jiyo hayani a ƙasa kamar za'a babbakawa gidan wuta saboda bala'i,


Da gudu samha tabi ta baya ta fice, da gudu ta isa bakin get na farko, ta ƙara daddagewa ta ƙara shararawa da gudu,


 Kai hydar abinda kayi ka kyauta kenan? Aminin dadyn hydar yake mishi magana, hydar yayi shiru,


Dady yace ai ɗan banzan lalataccen yaro ne nan daka ganshi, bai ajiye komai ba sai rashin kunya da girman kai wato shi kuɗi yana gaya mishi ƙarya, yanajin sa daidai da kowa, shege munafuki,


Wani irin kallo hydar yayi ma dady wanda yasashi saurin sauke kanshi ƙasa, hydar yace daga yau kada ka sake cemin lalatacce tunda kasan ni bashi bane,


Alhaji Lawal aminin dady yace hydar bakasan ba'a aure a ɓoye ba? Wannan rayuwa haka ta yuwu kuwa? Hydar yace Dady ba auren ɓoye bane na bayyane ne,


Dan nine naje wurin danginta na nemi auren samha kamar yanda addi'ni yace, kuma suka yadda suka bani auren ta,


Dady yace toni dai duk ba wannan ba, dole saika auri Asma'u dan bazai yuwu ba, munaji muna gani yaya ya kwanta ya mutu dukan abinda ya bari aka tattara aka danka maka, hada jirgin sama, saika ɗauki dukiyar gidan ɗan uwana kaje kayi ta bishasha dasu,


Ai gida bai ƙoshi ba, baza'a kawai dawa ba, ka auri Asma'u sai su zauna su biyu shikenan sai fitina ta ƙare,


Murmushi hydar yayi da gefen bakinsa sannan yace dady gaskiya kayi haƙuri wallahi kaina baya ɗaukar hayaniyar mata biyu, dady yace to aisai ka saki ita yarinyar ka auri "yar uwarka,


Hydar yace dady ka taɓa ganin gangar jikin data kasance a duniya bayan babu lumfashi ajikinta? To ita samha itace lumfashina da zaran ta ɓace a duniya nima rayuwata ta ƙare,


Dady yace sannu ba'india an gaishe ka baban soyayya, ashe da gaske har yanzun akwai soyayyar idan bana tare dake bana iya cin abinci idan bana ganin zan makance, idan bake ba sai rijiya mai kwalabe, hydar yace ko babu su nidai akwai saurana, danni da mutum ya rabani da samha gaskiya gara kawai a kaca min wuƙa in mutu,


Dady yace to wallahi duk babbar bala'i saika auri Asma'u, hydar yace to a auramin ita in gani, a fusace dady ya miƙe tare da jan hannun Asma'u da aka fesa ma ruwa ta dawo daga duniyar suma,


Tawagar shi suka bi bayanshi suka fice daga farlon, bayan fitar su Alh Lawal yace ma hydar kada ka kuskura ka auri ɗiyarsa dan wallahi idan harka auri yarinyar can sai sulaimanu yaga bayanka,


Nan dai Alh Lawal ya ƙarayi ma hydar nasiha, tare da musu addu'ar zaman lafiya, daga baya shima ya tafi,


Farlo ya rage daga kakar hydar sai faruk sai yaran hydar "yan amana wanda sun riƙe alƙawari da amana sunajin hydar har cikin ransu,


Itama kaka haka tayi ma hydar fatan alkairi tare da musu addu'a Allah ya basu zaman lafiya, tace kuma akai mata jikarta samha har gida, duk a cikin yarensu take magana, hydar yace tom, gaba ɗaya suka raka ta har inda driver yake, saida ta tafi sannan suka dawo farlo aka fara maida yanda akayi,


Ita kuwa samha da gudu ta fice daga gidan hydar tana kuka, gata babu ko asi bare asiya a hannunta, bata da kuɗin da zata hau napep haka tayi tsaye a bakin titi tayi ta raba idanuwa kamar munafika,


Ganin tsayuwan baya fishsheta yasa ta samu napep tahau ta nufi gidan kawu,


Napep na tsayawa a ƙofar gidan kawu taga illo, dan haka da sauri ta sauka taje wurinsa tace malami dan Allah ka biya kuɗin abin hawa mana,


Cikin magana irin ta "yan tasha illo yace haba matar Oga muna ganinki munga kuɗi, duk zafafan motocin gidan hydar kika ɓige da hawan "yar ƙurƙura? Hajiyata keda zamu ga an faka an ajiyeki a cikin mota mai lumfashi sauran dakaran motocin suna take miki baya amma sai kawai ki wani zo a haka harda wani cewa in biya miki kuɗin abin hawa?


Dan gajeran tsaki illo yayi tare da ci gaba da cewa gaskiya mata kin diro babbar faɗowa kikayi, waye yace miki yanzu duniya ana zama? Tsaki samha tayi tare da cewa idan kana biyamin biya min idan ko bazaka biyamin ba kada ka kawo min hauka a cikin al'amurrana, dan yau zafi gareni kaina hayaƙin rashin mutunci yakeyi,


Wata kafirar dariya illo yayi tare da cewa shiga ciki abinki ganinan zuwa, samha ta wuce simi simi ta shiga gida, illo yaje ya biya mai napep sannan shima ya nufi gidan,


Da sallama samha ta shiga, mutane sosai a gidan, amma babu wanda ya ansa mata sallamar, a gefe kuma ga kawu kwance babu lafiya yana cikin hali mai tada hankali,


Samha ta sake cewa Assalamu Alaikum, wannan ƙaro wani mutumne ya ansa mata, tare da cewa bisimillah,


A hankali samha ta isa wurin ta durƙusa ta gaishesu cikin ladabi, gaba ɗaya suka ansa, kawu kuma ya juyo da idonshi ya kalli samha yana san yayi magana amma baya yuwuwa,


Wani ne ya shigo gidan yana cewa yawwa ku fito ga mota nan tazo, mutane suka fara tashi yayin da ake ƙoƙarin kama kawu,


Samha tayi ƙarfin halin cewa ina za'a kai kawu ne? Yace zamu kaishi katsina ne, wurin danginsa domin su nema masa lafiya, samha tace miya sameshi ne?


Yace bisa bincike da likitoci sukayi yawan shaye shaye ya lalata ma kawu "yan hanji, sannan yana ɗauke da ciwon hunhun, yawan tunani da damuwa kuma ya ɗirkaka mishi ciwon zuciya,


An kashe kuɗaɗe sosai amma har yanzun babu wani abinda ya canja, tun muna da abin maganin har yanzun ya ƙare, samha tace nidai kafin ku tafi dashi katsinar kusa shi ya faɗa min ina ahalina suke? 


Mutumin yace kiyi hakuri tunda yana cikin halin rashin iya magana, idan mukaje can tunda maganin hausa za,a mishi idan ya samu sauƙi saiya miki bayanin komai, dan gaskiya yana ta maganarki wallahi,


Haka dai aka runguɗa, samha da kawu da saura mabiya bayansa, aka ɗurasu a mota, haka aka cika j5 bayan kowa ya shiga, driver yaja motar sai katsina ta dikko ɗakin ƙara kunya garesu badai tsoro ba,


Dady kuwa tafiyarsu banda zage zage babu abinda yakeyi tare da rantsuwa sai hydar ya auri Asma'u, tare da hararo irin tarin dukiyar da ɗan uwansa ya mutu ya bari, ga motoci na tashin hankali wanda duk ƙarshen shekara sai anyi sabbin zubi zafafan motoci "yan yayi masu kyau da daukar hankali ga tsada, kuma ko mutuwar yayan nasa yayi tunanin hydar zai lalace ne, shi kuma ya ɗauki dukiyar yayi ruf da ciki da ita amma hydar yaƙi ya lalace,


Kullum dady cikin ƙoƙarin tura kwaratan mata yake dan su yaudari hydar su lalata mishi rayuwa toshi harkar mata ma da bayayi, wannan dalilin ne ma yasa daya tashi neman samha dan ya jijjiga mata zuciya yasa yaje a sahib,


Tunda shi ba ɓoyayye bane bayyananne ne shi, kuma yaso ya latsa samha sosai bisa rainashi datayi, amma Allah saiya yiwa zuciyar hydar dabaibayi, Allah ya ɗora mishi san samha matsananinci so, wanda shi hydar yake ganin hakan da Allah yayi mishi babban taimako ne yayi masa, domin da babu maganar wani aure a ransa dan gani yake duk macen daya aura za'a haɗa kai da ita a kashe shi,


Bayan sun gama firarsu kowa ya tafi, hydar ya miƙe cikin farin ciki, a ransa kuwa yana kuɗirin nunawa samha lallaifa shine mijinta dan yayi alƙawari da zuciyarsa dama bazai bari wani abu ya shiga tsakaninsa da samha ba harsai tasan shine mijinta, to yau kuma tunda taji komai dan haka lallai itama yau za'a bata babban tikiti na shiga sahun mata masu aure,


Yau zata san hydar shine rayuwarta, murmushi yayi tare da tuno maganar samha, { _Sahib hydar fa dirjeje ɗan iska ne,_ } murmushi hydar a bayyane yace yau zakisan hydar babban ɗan iska ne, kamar yanda kike faɗawa sahib, a daidai lokacin daya shiga ɗakinsa,


Da sallama ya shiga yana kiran samha, amma babu samha babu labarinta, da sauri ya nufi toilet nan fa yaren irin na tsakar ɗaki ne, da sauri ya juya da nufin fita kuma saiya juyo kamar yaga wani abu a gado,


A hanzarce ya koma bakin gado ya miƙa hannunsa ya ɗauki takardar, ganin an rubuta zuwa ga hydar yasa hydar yayi murmushi mai ciwo, zufa da hawaye hydar ya goge a daidai lokacin daya gama karanta saƙon samha,


Ajiyar zuciya hydar yayi tare da furta kalmar innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, dafa gefen zuciyarsa yayi tare da zama a gefen gado a hankali don wata hajiyaya dayaji tana neman kwaɗashi da ƙasa,


Hannunsa yakai a gefensa ya buɗe lokar bedsite da sauri ya ɗauko maganinsa yasha, bayan yasha a hankali hydar ya sauko daga saman gadon ya kwanta a ƙasa danji yake kamar zai faɗi,


Tunanin samha ya farayi tun daga ranar daya fara haɗuwa da ita a rayuwarshi, tunanin rayuwarshi da ita a matsayin sahib, rayuwarshi da ita a matsayin hydar har zuwa yau da samha bata tare dashi,


Murmushin ƙarfin hali hydar yayi tare da furta ni banma san ta ina zan fara ba, ina kika shige ne? Ina zan ganki? Da hanayi sosai hydar yace ina kike keeeeeeeeeeeee, ya ƙarasa maganar cikin ƙaraji,


Su samha an iso katsina ta dikko lafiya, tunda samha suka shigo katsina takejin farin ciki yana ratsa mata babban birnin zuciyarta, tana cikin farin ciki da nishaɗi, tace ashe haka katsina take shi yasa real mai dambu ta nace saida tazo ganin jamila musa,


Kai lallai katsina tayi kuma katsina akwai kara da mutunta baƙo, lallai duk wanda ya samu ya lafe a cikin babban birnin katsina baya marmarin zuwa ko ina, 


Samha bata gama tsinkewa da lamarin mutunci irin na katsinawa ba, saida taga yusra da kausar sunji daɗin ganin samha sosai  haka sukayi ta rungume samha irin da yanda abokai sukeyi idan an daɗe ba'a haɗu ba,


Shi kuwa kawu ɗakin ɗaya aka ware mishi a cikin ƙaton gidan kakarsu su yusra wanda yake a cikin unguwar goruba road duk a nan cikin babbar birnin katsina, a ɗakin aka kaishi ya huta, dan yusra tace india za'a kai kawu dan can india sune sukafi manyan likitoci wurin ɓangaren ciki, dan duk abinda ya shafi ciki sun ƙure a wurin,


Yusra da kausar sukaja samha zuwa nasu ɗakin, saida samha tayi wanka taci abinci sannan suka ɗanyi fira, daga baya kuma samha ta kwanta bacci domin hutama rayuwarta,


Suma baccin suka kwanta, amma ƙiriƙiri bacci yace baisan idon samha ba, tashin hankali hydar yazo yayi mata tsaye a ranta, kaji jaraba tunanin hydar ya riƙa zuwa mata a yanayin da take a jikinsa,


Kuka samha ta farayi dan gaba ɗaya bata burin daya wuce tajita a jikin hydar, goge hawayen idonta tayi tare da cewa mi hakan yake nufi? 


Har gari ya waye samha bata runtsa ba, yanda taga rana haka taga dare,  daka ga samha kasan tana cikin damuwa, ko wurin kalaci samha ruwan tea kawai tasha, bayan sun gama ta koma ɗaki tayi wanka ta saka kayan yusra, ta hau gaɗo ta kwanta,


Hydar kuwa bayan ya samu jikinsa ya daidaita tashi yayi yaje ya watsa ruwa tare da ɗauro alwalla, yana fito jallabaiya ya zura ya nufi masallaci,


Bayan sun gama sallah ne hydar ya kira faruk ya faɗa mishi samha ta gudu fa, faruk yace to ya jikin naka? Hydar yace Alhamdulillah, faruk yace bari inzo muje gidan kawunta mu gani ko za'a ganta a can, hydar yace kyaleta ni nayi imani yau duk inda samha take bata iya bacci ka barta dani kawai ai nine dai ko? Faruk yace kayi hakuri hydar kada kace haka muje, hydar yace wallahi bazanje ba, zata dawo da kanta badai ta shigi hydar ba?


Faruk yace to zanzo in kwana dakai saboda dare, hydar yace kada ka samu damuwa, faruk yace wallahi saina zo, hydar yace Allah ya kawoka lafiya, bayan sun gama wayarne hydar ya tashi ya koma ciki,


Faruk shine yazo ya kwana da hydar saboda kada wani abu ya sameshi babu mai taimaka mishi,


Cikin dare ciwo yayi tsanani, gaba ɗaya hydar ya shiga tashin hankali, dan haka ya fara tashi faruk bayan faruk ya farka hydar yace tunda ni nayi rantsu bazanje ba kaje idan samha tana nan ka bata waya zanyi magana da ita,


Faruk ya kalli agogo yaga 1:55am baida yanda zaiyi ya tashi ya nufi gidan kawu, yana zuwa yaga gidan an danƙara mishi ƙaton kwaɗo,


Dare ne baida wanda zai tambaya dan haka dole ya haƙura ya dawo gida, ya faɗawa hydar, daren dai hydar a asibiti ya kwana,


Yusra ce ta shigo ɗakin tana cewa samha kizo muci abinci mana, samha dake kwance tace banajin yunwa, amma don Allah ki bani aron wayanki, yusra tace mi kikaci ne kike cewa bakyajin yunwa? A daidai lokacin data miƙa mata waya,


Ansa samha tayi ba tare data ba yusra ansar tambayar datayi mata ba, tace yusra bani biro da paper don Allah, yusra tace to, zuwa tayi ta kawo mata sannan ta fita daga ɗakin,


Tashi zaune samha tayi tare da cewa bari in gano matsayina a cikin zukatan mutum biyu, wato hydar da sahib, ta fara rubutawa kamar haka,


_Nadama_


_Hydar rauni_

_Sahib san kai_ = { _Nadama_ }

_Samha kafiya_


_Sahib yana da san kai_


Nazari, tunda sahib yana da sankai, shi kuma hydar yana da rauni, sahib talaka ne, hydar mai kuɗi ne,


Shi sahib shine hydar ya turo shi wurina tunda yaronsa ne, yazo yayi min wayau ya fara soyayya dani, bayan na kamu da sansa, saiya ɗaukeni yakaini gidan hydar tunda shi abokin gaba na ne, a gidan hydar kuma hydar yana ƙoƙarin ya koyama zuciyar samha sanshi tunda ita zuciyar samha tana da kafiya, dan idan yazo kai tsaye bazan so shi ba,


Ajiyar zuciya samha tayi, sannan ta mike tsaye, taci gaba da nazari,


Bayan sahib ya kawoni gidan hydar, sai yace zaki zauna anan saboda banda da inda zan ajiyeki, ki zauna anan kafin zuwa lokacin da zan gama gina gida,


A lokacin sai sahib yaci gaba da bani kulawa sosai a gidan hydar har ya yaudari zuciyata na amince da aurensa, saboda yaga na kamu da sansa, ni kuma na biye masa mukayi aure ba tare da sanin iyayensa ba, sai yayi min ƙarya mamanshi bata lafiya, ni kuma na amince da buƙatarsa a bisa sharaɗin zai samanin ahalina,


Zama samha tayi a gefen gado, sannan taci gaba da zurfafa tunaninta,


Bayan ɗaura aure na da sahib, sai sahib ya fara canjawa ya koma halin da ba nasa ba, sai yace idan ina san abu inyi ma hydar magana, anan sai yayi ƙoƙarin cusa alaƙa mai ƙarfi tsakanina da hydar,


Toda har sahib yana sona tsakaninsa da Allah  dole zaiyi kishina, amma saiya ware lafiyayyen ƙato ya haɗani zama dashi, daga nan sai hydar ya biya sahib kuɗi masu yawa, sai sahib ya tafi zama ya dawo tsakanin samha da hydar,


Idan samha ta kira sahib sai yayi mata wulaƙanci sosai, zaman da samha takeyi da hydar yasa take faɗa mishi damuwarta, sai hydar ya lallashi samha, shi kuma hydar tunda mace bata taɓa mishi jiki, shine dalilin daya sa ya koyawa samha zama cikin jikinshi tunda yana da wani kuɗiri akaina daban,


Ajiyar zuciya samha ta sauke lallai mutane biyun nan sun mata yawo da hankali, miye dalilin daya sa mace bata taɓawa hydar jiki?


Samha tace lallai yana da shirin duniya ne, lallai ya zamarmin dole in gano yanzun ni matar wace ce tsakanin hydar da sahib, taci gaba da rubuta,


_Sanka_

_Kafiya_

_Rauni_


_Sankai Kafiya + Rauni_

            = _Nadama_

_Sankai Kafiya Ranuni, -Sankai_ = _Nadama_


Ai sankai an fitar dashine saboda an sallami sahib hydar ya bashi kuɗi, saboda haka yanzun babu sahib a cikin wannan lissafi, yanzun lissafi ya rage tsakanin ziciyar hydar da zuciyar samha,


Hydar wurin san ganin ya wahalar da rayuwar samha yasashi ya antaya kogin ƙaunar samha, saboda yana da raunananniyar zuciya,


Bayan hydar ya tabbatar zuciyarsa tana san samha, sai kuma ya gane   lallai samha bata sansa saboda zuciyarta tana da kafiya,


Wannan dalilin yasa ya ɗauko sahib yasa ya fara soyayya dani, kam lalai sahib ka kai babban ɗan iska,


Abinda ban gane ba yaushe na zama matar hydar? Wayar ta ɗauka ta rubuta number sahib ta fara kiran wayar,


Bai ɗauka ba, dan haka ta rubuta number hydar ta fara kira, saida ta kira har ta gaji domin hydar baya ɗaukan baƙuwan number, haka ta haƙura ta fara rubuta saƙo kamar haka,


_Suna na samha_


_Hydar na gano amsar tambayar daka min, wannan ansa itace nadama, amma abinda nake so na sani dani dakai waye zaiyi nadama?_


Bayan faruk yaga saƙo ya faɗawa hydar, murmushi hydar yayi sannan yace kirawota,


Bayan an kira samha ta ɗauka, faruk yace hydar zaiyi magana dake, bayan an bawa hydar wayarne, hydar yace kina ta ina ne? Samha tace ina katsina, hydar yace duk abinda kike ki dawo kaduna yau, m card ɗinki da labarin ahalinki duk yana wurina, kuma ahalinki suna nan cikin garin kaduna, samha tace sai nayi nazari idan naji ina buƙatar ahalin nawa zan dawo idan bana buƙata zakajini shiru, ina maka fatan alkairi ka huta kaji hydar, 


Tana faɗin haka ta kashe wayar baki ɗaya, murmushi hydar yayi sannan ya kalli faruk yace samha tana iskanci da rayuwa, kaji wai in huta abuna, bayan tasan hutun yana wurinta, kuma ahalin nata ma bata sansu,


Lallai na yadda duk abinda baka so baka sansa, amma babu wanda yayi baban kuskure saini, wai miya kaini ma? Kana ganin yarinya tana min yawo da rayuwa a hannunta ko?


Faruk yace ai kayi wasa kaji daɗi, bakasan shi *SO MUGUN WASA* bane? Waye yace ana wasa da so? Kayi addu'a ma kada ka mutu dan wannan yarinya taci ta gyare, murmushin ƙarfin hali hydar yayi tare da cewa Allah ya jiƙanka hydar, kallon shi faruk yayi sannan ya kecewa da dariya, yace wato harka mutu ko?


Hydar yace Eh mana, ni kawai ma ka tara mutane kace na mutu ya ƙarasa maganar yana matse hawayen dole, dariya faruk yayi sannan yabar ɗakin,


Ita kuwa samha tana kashe wayarta, ta fara nazari,


Idan na koma kaduna, sai inje gidan hydar tunda yace yasan labarin ahalina, idan na koma gidanshi, saiya kwance karnuka su hanani fita daga gidanshi, daga nan sai ya ɗirkakamin ciki kamar yanda ya faɗa a baya,


Bayan nayi ciki saiya fara min wulaƙanci, ni kuma ina hakuri tunda ina san sanin labarin ahalina, daga nan zai riƙamin yawo da hankali akan m card, zan kasance a ƙarƙashin ikonsa daya gama biyan buƙatarsa a kaina saiya sakeni, tunda sun ɓoye sunyi aure dani dagashi har sahib, idan suka sakoni sai in dawo gari ana min Eho nayi cikin shigeya,  burin maƙiyi ya cika akaina kenan,


Murmushi samha tayi tare da cewa ƙarya kake, Allah bazai baka nasara akaina ba, ya ubangiji kada ka bari zalinci yayi tasiri,


Haka rayuwar samha taci gaba da tafiya a katsina, kullum bata da wani tunani wanda ya wuce hydar kuma tana san kasancewa a jikinshi dan zama jikin hydar yana sata nishaɗi kuma yana kauda mata duk wata damuwa, wannan dalilin yasa take maraicin sa sosai, takan tuno abubu da dama da suke kasancewa tsakaninta dashi, saida tayi murmushi, wani kuma tayi tsoki,


Yanzu bata da burin daya wuce taga sahib tayi mishi rashin mutunci, ɗan iska daya sa rayuwata ta shiga garari, wai kamar ita ya yaudara? Hmm kuma hydar hada wani cewa shine sahib, kwafa tayi sannan tace duk zakuci uwarku ku biyu ɗin,


Shima hydar an sallame shi daga asibiti, kuma yana ɗan jin sauƙi, abinda yake kwantar masa da hankali shine daya tuna akwai auren shi a kan samha saiya ji sauƙi dan yasan dai duk haukarta bazata kula kowa ba tunda tasan ita matar aure ce,


Haka dai yake "yan huɗɗoɗinsa amma badai kamar da ba, kana ganin sa kasan yana cikin damuwa,


Kawu kuwa jiki ya ƙara lugudewa gaba ɗaya jiki ya jagwalgwale babu sauƙi sai wurin Allah, samha kuwa yanda taga yanayin kawu yasa tafi kowa tashin hankali,


Haka aka ɗauki kawu aka nufi asibiti dashi, banda kuka babu abinda samha takeyi tare da faɗin kawu kaji tsoro Allah kafin ka mutu ka bani address na ahalina, kafa san ka ɗauka alhakina da yawa ka cuci rayuwata ka gurɓata min rayuwata kasa na zamo mara "yanci kowa ya rayu a cikin uwa da uba, idan babu iyaye akwai "yan uwa, amma ni miyasa kamin haka? Haka ake riƙon amana? Wai waye ma ya baka amanata?





*_Jamila Musa_*


💋

[05/04 4:46 pm] Washa: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊



                 *SO*

     *MUGUN WASA*



       *{ Love is a bad game }*




*JAMEELA MUSA* { meelat musa }




*Story, Writing & Editing*

                   *by*

         *Meelat Musa*


*_KISHIYATA, Ina kuke masoya BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION, "yar uwata maza jawo wayarki a kusa dake, idan babu chargy maza ki matsa jikin sokert domin ɗirkakawa wayarki chargy, ki narka ki ƙara darkakawa domin in kin fara karatun labarin kishiyata kada chargy ya ƙare, albishir ne a gareku domin sharariyar marubuciyar nan wato MARYAM MUHAMMAD tazo muku da wani sabon salo nata mai take KISHIYATA, shahararriyace marubuciyar ta kware wajen iya sarrafa littafi, itace maruciyar, MAI GADON ZINARI, marubuciyar RAMLAT, ita kuma taja da baya baya ta sake zuwa muku da wannan sabon labari mai suna KISHIYATA, kada ku bari a barku a baya don ta ƙayata littafinne da abubuwan ban mamaki, darasi nishaɗantarwa gami da ilimantar da masu karatu, KISHIYATA, yanan tafee,,, Jamila Musa kece asha karatu lafiya_*


                  *SO*

      *MUGUN WASA*


*_Dedicated to_* 👇🏻

_Ramlat Abdulrahman real mai dambu_


*59-61*




Wai waye ma ya baka amanata? A hankali kawu ya juyo da kanshi ya kalli samha idonshi yana ɓarin hawaye, kamar mutum ya rasa uwa da uba a lokaci ɗaya,


A hankali samha ta matsa kusa da gadon kawu ta dafa da hannunta ta tsuguna sannan tace kawu faɗamin waye ya baka amanata? Ta ƙarasa maganar cikin sigar lallashi,


Cikin ƙarfin hali kawu yace kije gidana, a ɗakina, nishi, sannan yaci gaba da cewa, zakiga wata jaka mai ruwan kayan sojoji, lunfasawa yayi sannan yaci gaba da cewa, a ciki zakiga bayanin komai akan ahalinki da address nasu,


Miƙewa samha tayi, tare da goge hawayen idonta, harta fara tafiya wata zuciya tace mata ta dawo ta tattaka kawu ko zata rage zafi,


Wani irin juyi samha tayi, tare da rugawa da gudu tana bi ta saman gadajen marasa lafiya, dan gani take kafin taje kawu ya mutu, wani irin tsalle takeyi ta dire daga wannan gado ta faɗa wannan harta isa gadon kawu, ta riƙeshi zata fara kai mishi duka,


Da sauri aka riƙe samha, cikin kuka take kwacewa daga jikin mutane tana cewa ku sakeni yau saina kashe ɗan iskan tsohon nan bana sanka bana kaunarka ka wargazamin rayuwa, bazan taɓa yafe maka ba, ta ƙarasa maganar tare dakai ma gadon kawu wani irin harbi da ƙafarta harsai da kawu ya faɗo ƙasa, da sauri mutane sukaso kan samha suka riƙeta, 


Sai ihu samha takeyi tare da ɓarar da mutane, idanuwan samha gaba ɗaya sun ɓirkice dole ta baka tausayi tana kuka tana cewa wallahi saina kasheka, riƙon samha akeyi amma sai zuƙewa takeyi tana ƙoƙarin isa wurin da kawu yake a kwance ƙasa,


Wani mutum ne yasha gaban samha tare da cewa samha kiyi hakuri don Allah, samha ta ɗaga daradaran idanuwanta ta kalleshi tare dayin wani irin la'anannen murmushi, sannan tace haƙuri? To haƙurin samha ya mutu, danni a yau haƙurina ba ƙarewa yayi ba mutuwa yayi gaba ɗaya,


Samha sai hararar kawu takeyi tare da cewa saikaci uwarka yau ɗin nan idan baka mayar dani ba a inda ka ɗaukoni ba  saina caccaka maka wuƙa na kwakwalo wannan "yan hanjin da sukayi exp,


Asibiti ta taru kan samha, mutane sai hakuri suke bata tare da nuna mata taji tausayin kawu, amma samha tace babu hakuri yaudai a cikin tsarin rayuwarta, tayi hakuri a baya, wani mutum yace ke yarinya ana baki hakuri bazakiyi ba? Murmushi samha tayi da gefen bakinta sannan ta goge hawayen idonta da bayan hannunta, tace kana da uwa da uba?


Yace sun rasu, samha tace ya kakeji idan ka tuno basa raye a faɗin duniyar nan? Mutumin yayi shiru, samha tace nasan kanajin baƙin ciki a ranka ko ba haka ba? Ta ƙarasa maganar tana nunashi da ɗan yatsanta, kallon samha yayi amma baiyi magana ba, samha taci gaba da cewa da kaine ka kasance a halin da nakeci wane irin hukunci zakayi ma wancan ɗan iskan tsohon?


Ta nuna inda kawu yake kwance, mutumin dai baiyi magana ba, samha tace kuma ɗan iska duk cutar dayayi waishi can har wani mutuwa ma zaiyi ya barni inci gaba da lalacewa ba tare da sanin ahalina ba,


Mutumin yace kiyi hakuri, samha tace dattijo kada ka sake bani hakuri, duk wanda ya sake bani hakuri yau a asibitin nan kan mai uwa dawabi ba mara lafiya babu mai lafiya haka zanyi ta cire kawuna daga saman gangar jikin duk wanda ya sake cewa swry samha,


Cike da fushi samha take ƙoƙarin tafiya wurin da kawu yake kwance amma sai taji an riƙeta ta baya gam, taja taja taji fa riƙe take sosai, juyawar da zatayi dan ganin waye taji an zazzabga mata mari mai taɓa kwalwa,


Kiciniyar kwace kanta ta farayi ganin dady, shi kuma sai ƙara kai mata duka yakeyi ta ko ina, kafin wani lokaci samha ta jigata, yana dukanta yana cewa dan uwarki saboda ke hydar yake mana iskanci ai inajin idan na kasheki baki a duniyar mun huta,


Shi kuma hydar shigowarsa katsina kenan, ya kira yusra, ya faɗa mata ya shigo, dan da samha ta kirashi da wayar yusra, bayan ya sake kirane yace ma yusra zaizo katsina amma kada ta faɗawa samha dan idan taji zaizo zata gudu, to isowarsa kenan ya kira yusra ya faɗa mata inda suke, ita kuma tahau napep dan zuwa inda hydar ya tsaya,


Yusra tana isa tayi ma hydar waya tazo, hydar yace na ganki kece mai kaya kala kaza da hijabi da niƙaf ko? Yusra tace Eh nine, hydar yace juyo bayanki, juyawa tayi, ganin hydar yasa gaban yusra faɗuwa ta nemi rugawa da gudu, domin tunda ya ƙarya mata hannu bata sake ganinsa ba sai yau,


Hydar yace ke kada ki tafi zo mana, ina yusra bata sauraren hydar, ganin bazata tsaya ba, yasa hydar yace ma shamsu maza kamo ta, da sauri shamsu yaja mota yabi yusra da gudu, gudu yusra takeyi kamar ranta zai fita, dan ita a tunaninta hydar yazo katsina ne ya ƙara ci mata mutunci,


Da gudu shamsu yasha gabanta da mota ya karce sosai tare da tayar da kura ya fita daga motar da sauri, yusra ganin bata da mafita yasata durƙusawa ta fara bawa shamsu haƙuri tana kuka, shamsu yace ke dan babarki bakiji mai gida hydar yana magana? Maza shiga mota muje banza,


Yusra jiki yana ƙyarma ta shiga mota, shima shamsu ya shiga yaja suka koma inda hydar yake, suna tsayawa hydar yaji kamar ya mareta, amma saiya fasa, yace ina samha take ne?


Yusra tace tana asibiti, hydar yace kai muje asibitin, da sauri hydar ya koma motar shamsu yaja, dan yau tafiyar sirrice daga shi sai shamsu suka zo, yusra ce take nuna musu hanya sukayi ma asibiti tsinke,


Dan uwarki yau zaki baƙunci lahira, dan na daɗe ina mafarkin ganin Asma'u a matsayin matar hydar, "yar uwarsa ce, dani da uban hydar uwarmu ɗaya ubanmu shegiya "yar gidan bani Oho zaki shigo mana ahali har wani cewa yake idan babu ke zai mutu, to bari in kasheki saiya mutu dama ai bama so ya kasance a raye, 


Kallon wani lafiyayen ƙato dady yayi tare da cewa ja mana banza muje, idan hydar yana sanki saiya bada miliyan hamsin ya anso rayuwarshi, dariya dady yayi sannan yace yanzun zaki gane irin san da yakeyi miki idan gaskiya ne, yau zamu sheda, samha jin ance hydar ne zai bada kuɗi ya ansota yasa ta kwace jikinta daga riƙon da dady yayi mata dan ita a tunaninta idan dai hydar zai ansota tasan saida ta mutu, wannan dalili yasa samha taji wani sabon ƙarfi yazo mata,


Ta kwace daga jikin dady tayi waje da gudu, dady yace kubi min banza kuna zuwa ku caka mata wuƙa, samha naji lamarin wuƙa ta ƙara fesawa da gudu kamar zata tashi sama,


Gudu takeyi sosai ga ƙatti suna binta, wai duk mutane babu wanda yayi magana kowa sai kallo yakeyi, tun shigowar su hydar a cikin asibitin yaga samha ta taho ɓarke,


Cikin tsananin tashin hankali hydar yace shamsu bimin takan banzan can da mota, dan ya wahalarmin da matata maza takamin banza da mota ko zai tafin zuwa duniyar mutuwa, sanin halin hydar yasa shamsu yayi saurinyin parking dan yasan hydar yana iya kaɗa motar ta taka mai bin samha, 


Hydar yace ba nace ka takamin banza ba? Ya ƙarasa maganar cikin fushi, tsaki yayi tare da buɗa motar ya fita da sauri,


Ganin hydar yasa samha tayi wurinsa dan tsira da rayuwarta, da gudu ta isa wurin, a daidai lokacin da yaron dady ya nufi bayanta da wuƙa dan ya soka mata, tana zuwa ta faɗa jikin hydar da hannun haggushi ya riƙe ta, hannun damarsa kuma yana riƙe da wuƙar da akazo za'a cakawa samha,


Ajiyar zuciya hydar yayi tare da cewa ya kike? Cikin kuka samha tace lafiya ƙalau, murmushi hydar yayi sannan yace, ki tausayamin samha zuciyata ta tafi mi zaki bata? Tunda ta ambaci so ban makoma, nayi alƙawari zan baki kulawa har ƙarshen rayuwarki, idan har kinso in huta samha kice nine, idan baki yanda dani ba haƙiƙa zan iya rasa rayuwata, a daidai lokacin daya halba wanda yazo cakawa samha wuƙa,


Ya riƙe samha sosai a jikinshi yana kuka, yace samha don Allah kiyi hakuri haka nan, miye matsalar hydar? Kalli hydar ki gani idan har namiji kayana kowa zai saka a jikinsa yayi gayu dashi idan kika sako hydar a jikin nasan saikinfi kowa kyau da haɗuwa domin hydar ya dace da rayuwarki,


Ɗago mata fuska yayi, yana kallonta, sai yanzun samha ta lura da jinin hannun hydar, cikin kuka samha ta riƙe hannun tace kaji ciwo, murmushi hydar yayi tare da cewa manta da maganar ciwo kawai kicemin kina so na, murmushi samha tayi tare da ƙara kwanciya a jikin hydar a daidai lokacin da dady ya iso wurin, kallonshi hydar yayi ta saman idonshi sannan ya ɗaga samha daga jikinshi, yace dady ashe saika rigani zuwa? Yayi maganar yana kwantar da kansa a gefe, taɓe bakinsa hydar yayi tare da ɗaga girarensa alamar tambaya,


Dady zai fara wani zage zagen banzarsa hydar yace wallahi dandai kada inbar abin faɗi a duniya dana juya maka kai ya koma ta ba, kuma na rabaka da bibiyar rayuwar samha daga yau, idan kuma zakaci gaba dani dakai zamu kunna whyfer kwanakin hari zasu soma daga yau,


Yana faɗin haka yayi masa wani irin kallo mai nuni da zakaci uwarka, sannan yaja hannun samha suka nufi mota, a baya suka shiga, yusra da shamsu suna gaba, shamsu yaja motar suka fita daga asibitin, samha na kwance jikin hydar sai kuka takeyi,


Hydar yace kiyi hakuri samha, insha Allah kuka daga yau ya ƙare babu ke babu ƙara kuka har ƙarshen rayuwarki, daga yau farin ciki ya soma a rayuwarki,


Cikin kuka samha tace bazan daina kuka ba harsai naga ahalina, murmushi hydar yayi tare da cewa kada ki damu ahalinki suna tare dake,


Daga haka hydar bai sake magana ba, sai samha dake kwance a jikinshi tana ta shashshekar kuka, hydar kallon hannunshi yayi daya riƙe wuƙa dashi ya yanke sosai murmushi yayi tare da kyauda hannun gefe ɗaya,


Har suka isa ƙofar gidan su yusra a ƙofar gida suka ajiyeta, hydar ya ciro kuɗi daga jikinshi ya miƙawa shamsu yace yabawa yusra, godiya yusra tayi sosai tare dayi musu addu'ar sauka, su kuma su Ibi hanyar kd sai  ɓarin wuta suke bisa titi,


Kawu kuwa bayan zuwan dady aka ɗauki munafikin Allah aka mayar dashi a gado, cikin muryar marasa lafiya ya jirge baki gefe sai kiran sunan samha yakeyi,


Dady kuwa sai addu'a yake Allah yasa hydar yayi haɗarin mota ya mutu a hanya, saida ya gama baƙar fatarsa sannan ya dawo yayi ban kwana wa ahalin kawu tare da musu alheri, sannan suma suka fito suka shige moto suka fara cin kwalta dan zuwa garin kaduna,


Su hydar na shiga kaduna zuwa yayi aka fara mishi dressing a hannunsa daya riƙe wuƙa dashi, bayan an gama ne ya dawo mota samha tace mishi a gidan kawu zata sauka,


Hydar yace kiyi hakuri muje gida kiyi wanka ki huta sannan in kawoki, samha tace nifa bazan wani je ba, kawai ka ajiyeni a inda nace, murmushi hydar yayi sannan yace shamsu kai samha inda take so,


Shamsu ya kaɗa kan mota sai gidan kawu, bayan sunje ne samha zata fita, hydar yace kiyi sauri ki gama abinda kikeyi, danayi magrib zanzo in ɗaukeki, samha tace to,


Fita tayi su kuma suka wuce, gidan da suke bayar da ajiyan makulli taje ta karɓa, bayan ta anso ne tazo ta buɗe gidan, da sallama samha ta shiga,


Kai tsaye ɗakin kawu ta wuce, bayan ta buɗe shima da sallama ta shiga, tun a farlo ta fara ganin ƙattin takardu wanda kawu ya lilliƙa masu ɗauke da hotunan samha,


Gaba ɗaya bangon ɗakin duk yabi ya rubuce shi da i love samha, wani ɓan gare kuma zanen mace da namijine, yanda shi kawu yake nufi shine dashi da samha,


Tsoki samha tayi tare da cewa banza shashasha, duk kware hotunanta tayi sannan ta fito duka ta cinna musu wuta tanayi tana mita tare da cewa mahaukacin banza, kaida kace babu so a rayuwa, so wasa ne, kuma *_SO MUGUN WASA_* ya akayi ka bari san samha ya shiga cikin zuciyarka ba tare daka dakatar dashi ba?


Bayan ta gama ƙona hotunan, ta ɗauko jakar da kawu yace mata, tana ɗauka ta fita daga ɗakin ta fito tsakar gida, zazzage jakar tayi dukanta, 


Hotuna suka bayyana sai tarkacen takaddu, ɗaukar hotunan samha tayi ta fara dubawa, lallai ko ba'a faɗa ba wannan mamanta ne, ga yarinya tana rungume da ita jaririya wanda samha ta yanke hukunci cewa itace tana jaririya, murmushi samha tayi tare da ci gaba da duba hotunan,


Haka tayi ta duba hotunan, hoto ɗaya ne tayi tsaye a kanshi, lallai wannan fuskar tasanta amma ta rasa a ina ta sani, haka dai tayi ta dogon nazari amma fuskar ta ɓace mata, tattara hotunan tayi ta ɗauki takarda ɗaya ta duba, adress ne rubuce a jiki,


Wanda ba rubutun kowa bane na kawu ne, ya rubuta ko bayan rayuwarsa ga inda zata nemi danginta, ƙarshen rubutunsa kuma ya rubuta kamar haka,


_Samha na kamu da tsananin kaunarki, ina sanki ina kaunarki har cikin ƙarƙashin zuciyata,_


_Bayan zuciyata ta tabbatarmin da haka saina fara ƙoƙarin ta ina zan farawa lamarin? Amma sai hydar ya shigo cikin rayuwarki, tun a lokacin da kika fara soyayya dashi a matsayin sahib nayi babban bincike akan insan waye sahib? Tun a lokacin da kuka zo wurina a gidan kaso,_


_Bisa dogon bincike da nayi sai na gane babu wani sahib a duniya hydar shine sahib, kuma hydar shine mijinki,_


_Bayan kin bashi m card yaga yanda akayi ma mahifiyarki kisan gilla shima bisa binke da yayi a lokacin sai ya gano cewa mahaifiyarki kanwar mahaifiyar sa,_


_Hydar ya tattara dani da wanda suka kashe miki mahaifiya su akayi musu hukunci daidai da yanda suka aikata kisan kai, ni kuma yasa aka min horo mai tsanani bisa gurɓata miki rayuwa da nayi_


_Bayan hydar ya gano ke "yar uwarsa ce, kuma shi yazo miki a matsayin sahib, tosai yaso ya nuna miki shine hydar kuma ya faɗa miki zumunci dake tsakaninki dashi, amma saiya gane idan har kika sani bazaki yadda ba, saboda bakya sansa,_


_Wannan dalilin yasa yayi ta zama a matsayin sahib a wurinki, wannan dalilin yasa hydar ya ajiyeki a wurinsa domin ya koyawa zuciyarki san hydar, dangin mahaifinki basu san hydar ba shima hydar bai sansu ba, kasancewar iyayen hydar ba mazauna nigeria bane,_


_Wannan M card shine ya bayyana wa kakar hydar ta gano hoton mahifiyarki, a lokacin data gani tayi kuka sosai domin mutuwar ɗiyarta ya dawo mata sabo, hydar kuma yayi mata bayanin komai daga haɗuwar har zuwa lokacin aurenku, kuma duk dani akaje, kuma ta ganni ta shedani tayi tirr da Allah wadai da halina, kuma tace bata yafemin ba, daga taimako amma nayi musu sakayya da tarbiyyar jika bisa mafi munin raino_


_Dan haka mukaje aka ɗaura aurenki da hydar, abinda yasa ya ɓoye aurenku saboda illa irin ta ƙanin mahifinsa, wanda abokina ne, idan kin tuna fuskarshi muna haɗuwa dashi a wurin wasan caca, yana da san zuciya sosai wannan dalilin yasa aka haɗa kai dashi aka kashe ɗan uwansa tunanin zai samu wani abu a cikin kuɗin yayansa hydar dai zai baki baki labari,_


_Na roƙeki samha ki yafemin, kuma ki nema min yafiya a wurin kakarki, ga address nata, ya rubuta daga ƙarshe kuma yace ina miki fatan alkairi kuma inama hydar farin cikin samunki a matsayin matar aure, samha duk namijin daya sameki a matsayin mata ya more domin Allah ya wadataki da wasu sirrintacciyar baiwa da ni'ima wanda ba ko wace mace take dasu ba,_


_Samun irinki ɗaya rak zaiyi wahala a cikin mata, dake da hydar kun dace, kinyi miji fatan Allah ya baku zaman lafiya_


Zufa samha ta goge tare da cewa tirƙashi, ina niyar guduwa ashe dole in tsaya? Lallai bazanje wurin dangin uba ba gareku dan dangin uwata,


Miƙewa samha tayi ta tattara komai ta mayar a jakar, tare da cewa amma hydar yakai ɗan iska, wato shine sahib? Ya akayi ya zama mutum biyu? Ko magana ba iri ɗaya bane, dogon nazari samha tayi tare da tuno maganar hydar,


_Hydar in baka labari? Kallonta yayi ba tare da yayi magana ba, samha tace idan baka so shikenan, murmushi hydar yayi tare da cewa ina so mana,_


_Yau sahib ya kusa faɗuwa, murmushi hydar yayi tare da cewa ai saiki tadashi, Allah ya sawaƙe bazan tadashi ba, miyasa? Saboda yayi girma, murmushi hydar yayi sannan yace dani da sahib waye yafi girma?_


Kam amma lallai hydar kwallon ɗan iska ne, wani tunanin tayi,


_Ki cire kayanki duka, zan baki miliyan ishirin,_


Murmushi samha tayi tare da tuno hotuna da dama da sukayi ta faruwa a tsakanin ta hydar, 


Tun farkon haɗuwarta da sahib data fasa mishi waya a bakin holl ɗin training har zuwa yau, ya dawo mata a kwanyarta, amma abinda yafi tsaya mata a kai shine rayuwarta da hydar a matsayin sahib,


_Kizo muyi hoto nasan idan har sahib ya ganmu a wannan yanayin zaiji farin ciki yace muna zaman lafiya, kwanta a jikina hakai zaifi mishi daɗi,_


_Zoki kwanta a jikina ki ɗan lashemin bakina idan har kina so in goyaki a mashin_


_Ke zo nan, ni sa'ar wasarki ne? Mi nayi maka kuma? Ke kamarni zaki riƙa rubutawa a hannunki kina so na? Ni ban rubuta ba, idan aka duba aka gani fa? Kamin komai ma, buɗe hannuwan mu gani, wallahi bani na rubuta, rufe min baki maza kije ki zauna a can ki jirani in gama_


_sahib wallahi hydar fa ɗan iska ne, da gajeran wando yake mana yawo a gidan nan, ka mishi magana_


_Sahib banda lafiya fa, cikina yakemin ciwo, kira hydar ki baɗa mishi, danni ina da abunyi, banda number hydar ai, bara zan turo miki,_


_Hydar zan mutu, subahanalla miyasa zaki mutu kuma wace ce take magana?_


_Mijina yace inzo in maka shara, kuma naga dakin baiyi datti ba, hydar yace ai basai yayi datti ba ake sharewa ba, samha tace to kuma yace in baka haƙuri, hydar yace ai idan mijinki yamin laifi ba haka yake bani haƙuri ba, zo nan, samha tace ai naga babu kaya a jikinka ne, hydar yace ina ruwanki da kayana ko rashin kayana? Kedai ba haƙuri akace ki bani ba? Gidana ne nan dole in zauna yanda nake so, kema ban hanaki ki fito da ɗaurin gaba ba,_


_Samha tace aini ba "yar iska bace, hydar yace niko kinga dan iska ne ni shiyasa ma nake zama da gajeran wando abuna, samha tace to Allah ya shiryeka, hydar yace kai ba amin ba a barni da iskancina nafi jin dadi, nidai bani hakuri tun kafin zuciyata ta fara tsimama,_


Murmushi samha tayi tare da cewa lallai hydar wayonka yayi yawa,


_Sahib yau saina sane abinda hydar yake sakamin a ido, anya zaki iya sane a jikin hydar? Eh mana, sahib kalli na ɗauko kuma hydar bai sani ba,, murmushi sahib yayi tare da cewa shi kuma hydar dayafi wayau sai yayi miki vidio kalli,_


Haka dai samha tayi ta tunano abubuwa da dama tsakanin ta da hydar & sahib, samha tace lallai hydar yafi samha basira,


Sallamar da hydar yayi yasa samha ta tsagaita da tunaninta, kallo ɗaya samha tayi mishi ta ɗauke kanta,


Wata irin munafikar dariya hydar yayi maisa mutum yaji tsikar jikin sa ta tashi, sannan yace ashe ma baki yi wanka ba? Samha tace ban sani ba,


Hydar yace kada Allah yasa ki sani wuce mu tafi gida danni bacci nakeji sosai na gaji da yawa a daidai lokacin daya matsaya kusa da ita yaɗan rungumota,


Yanda yayi mata riƙon yasa taji duk kasala ta baibaye mata jiki, ɗan murmushi hydar yayi sannan yace mu tafi ko?


Samha tayi shiru, ɗagata yayi daga jikinsa ya duka ya ɗauki jakar da take ajiye a gabanta yana cewa wannan fa?


*_Kuɗanyi haƙuri da wannan don Allah_*


*_Jamila Musa_*

[05/04 4:46 pm] Washa: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊



                 *SO*

     *MUGUN WASA*



       *{ Love is a bad game }*




*JAMEELA MUSA* { meelat musa }




*Story, Writing & Editing*

                   *by*

         *Meelat Musa*


*_Yau wannan shafin ɗungurugum nakune masoya takardar littafin SO MUGUN WASA ina muku fatan alkairi a duk inda kuke domin kune maudi'i na, fatan Alkairi da addu'ar zaman lafiya a garemu baki ɗaya_*


                  *SO*

      *MUGUN WASA*


*_Dedicated to_*👇🏻

_Ramlat Abdulrahman real mai dambu_



*62-64*


Ɗagata yayi daga jikinsa ya duƙa ya ɗauki jakar dake ajiye a gabanta yana cewa wannan fa?


Turo baki samha tayi ba tare da tayi magana ba,


Hydar yace bakiji ina magana ne? Tsoki yayi sannan yaci gaba da cewa waike dan kinga ina lallaɓaki kike min rainin hankali ko?


Cike da tsiwa samha tace to kada Allah yasa ka lallaɓa ko nace maka ina san ka lallaɓa ni? Waikai sahib kai hydar ko? Kai amma kazo da rainin hankali,


Murmushi hydar yayi tare da cewa baki ma san nazo da rainin hankali ba sai munje gida zakiji a jikinki ya ƙara maganar yana shafa gefen fuskar samha tare dayin dariyar ƙeta,


Hannunshi samha ta bige daga fuskarta, hydar yace subahanallah mijinki kike ma haka? Bakisan bige hannun miji a jikin matarsa ba wuta balbal, murmushi yayi tare da cewa amma na yafe miki muje gida,


Samha tace nifa bazanje ko inaba anan zan kwana, kaje kawai zanzo daga baya, hydar yace to bari in siyo mana maganin sauro in dawo dan nasan gidan nan zaiyi sauro kuma ni wallahi sauro hanani bacci yakeyi, ya ƙarasa maganar yana taɓe baki,


Samha tace a ina sauro zai hanaka bacci ne? Hydar yace anan gidan mana, wallahi idan har anan zaki kwana nima anan zan kwana sai mu kwana tare,


Juyawa samha tayi ta fara tafiya zuwa ɗaki cewa wallahi ai nan ba gidan mutun bane kuma sai ka tafi tunda bakaine ka siya ba, binta hydar yayi yana cewa ke ni zaki ma rashin kunya? Baki san akwai banbanci tsakanin sahib da hydar ba?


Samha tace can matsalar ka, kuma idan baka san rashin kunya saika saken..... Wani irin mari hydar yakai mata wanda yasa tayi sujjadar dole tana kuka, hydar yace nine zakice in sakeki saboda ke mahaukaciya ne?


Cikin masifa samha tace ni bana sanka kuma bazan iya zaman aure dakai ba, ko ka taɓa ganin an haɗa ƙarya da gaskiya? Tou wallahi so da ƙiyayya bazai taɓa zama wuri ɗaya ba,


Hydar yace samha nine bakya ƙauna? Nine kike ma ƙiyayya? Cike da masifa samha tace Ey, Ey, Eyyyyyyyyyy, na tsaneka dama bana sanka, kuma kazo ka ƙara daɓa wani ƙiyayyan akan wani waika sahib, kai amma wallahi ka ɗauki samha daƙiƙiya, ni bamma san jaka zan kira kaina ba ko sakara?  Ajiyar zuciya hydar yayi sannan yayi ma samha wani irin kallo wanda shi kaɗai yasan abinda yake nufi,


Murmushin ƙarfin hali hydar yayi da gefen bakinsa tare da sassauta gani idonsa, daga haka bai sake magana ba, ya juya a hankali ya fita daga gidan, jirin daya ibi hydar ya hanashi isa wurin motarshi, dan haka ya dafe bango a tsaye yana maida numfashi,


Fitar hydar samha ta taho a hankali dan taga idan hydar ya tafi, a bayan kyaure samha ta ɓoye tana leƙen hydar, shi kuma ya kwantar da kanshi a saman mota, ya bawa samha baya, amma duk abinda samha takeyi a bayanshi ya ganta, murmushi hydar yayi sannan ya buɗe motarshi shige yaja yabar wurin,


Har zuciyar samha bataji dadi ba, da sauri ta fito daga bayan kyauren ta fita da gudu waje hydar harya ɓace daga wurin kamar walƙiya,


Tsaki samha tayi sannan ta koma gida tare da rufe ƙofa, jiki a sanyaye samha ta shiga gida, saida tayi wanka sannan tayi sallah isha'i bayan ta gama ta kwanta tana tunanin hydar, macijin robar daya saka mata ta fara tunani da gudun datayi da lokacin data kwanta a jikin sahib ya cire mata ashe duk hydar ne, Yazo a matsayin hydar yasa mata cuta sahib yazo ya cire mata,


Lallai ta tuno lokacin data ga sahib da kayan hydar ta koma da sauri kuma sai taga hydar to ya akayi haka tayi ta faruwa?


Hydar kuwa da taikon ubangiji ya isa gidan kakarsu, ko parking ɗin kirki baiyi ba ya fita daga motar yayi ciki da sauri,


Da sauri ya shiga farlon baya ganin kowa kuma duk masu gaisheshi bayajin su, lokacin daya shiga bedroom ɗin baya ƙarda komai yasan dai yahau gado da kanshi ya ɗora kanshi jikin kaka daga haka hydar bai sake sanin komai ba,


Tunda hydar ya shigo a birkice kaka ta fara magana cikin yarensu nikam bana gane komai sai sunan samha nakeji tana kira a maganarta,


Wayarta ta ɗauka ta kira faruk tace yazo yanzun tana san ganinshi, babu ɓata lokaci faruk yazo bayan yazo kakata tayi ta faɗa sosai sannan tace akai hydar asibiti kuma duk inda samha take a daren nan a nemota kuma a faɗa mata cewa hydar ya mutu ta huta ɗan uwanta ya mutu saboda ita saita zo ta zuba ruwa a ƙasa tasha,


Haka aka ɗauki hydar akayi asibiti dashi, gaskiya yana jin jiki sosai banda kuka babu abinda kaka takeyi tare da faɗin saita ramawa hydar wahalar da samha tasashi yakesha dan tasan yana santa take mishi wulaƙanci,


Har gari ya waye hydar bai farfaɗo ba, ganin haka yasa kaka tace a tafi dashi waje don ganin likita,


Samha kuwa da safe ta jirayi zuwan hydar ta bashi hakuri abinda tayi mishi kuma ta faɗa mishi tana sansa, amma babu hydar babu dalilinsa, har rana ta faɗi samha bata ga zuwan hydar ba, gaba ɗaya taji babu daɗi,


Lallai batayi ma hydar adalci ba, tuno tsaunin benen wurin training tayi tare da halbowar dasu wawu sukayi mata,


_Kaiiiiii kada ka faɗo da ita na faɗa maka, kada kamin wasa da rayuwa,_


Dariyar su wawu ta tuno hhhhhhhhhh kana santa ne? Sahib yace Zuciyata ce, dariyarsu ta ƙara dawoma samha a cikin dodon kunnuwata, sannan maganar wawu,


_Bari muga idan kana santa, shirya ga zuciyarka nan zuwa gareka_


Hawaye samha ta goge tare da sauke ajiyan zuciya, lallai kuma hydar saboda yana santa bai bari takai ƙasa ba daga saman bene hawa na ukku miyasa baza tayi ma hydar adalci ba?


Tuno jiya tayi a katsina, anzo caka mata wuƙa, amma hydar ya riƙe wuƙar ta yanki hannushi, amma duk da haka ba yanka yakeji ba, saiya fara tambayarta,


_Ya kike? Samha ki tausayamin zuciyata ta tafi akanki mi zaki bata? Tunda ta ambaci so ban makoma, nayi alƙawari zan baki kulawa har tsawon rayuwarki idan har kinso in huta kice nine_


Ajiyar zuciya samha tayi tare da cewa bawan Allah kuma har a lokacin wuƙan yana hannunshi, goge hawayen idonta tayi,


_Kiyi haƙuri samha insha Allah kuka daga yau ya ƙare babu ke babu ƙara kuka har ƙarshen rayuwanki, daga yau farin ciki ya fara a rayuwarki,_


Sallamar da akeyi ya dawo da ita daga tunanin da takeyi, ansa sallamar tayi tare da cewa waye? Faruk yace nine faruk,


Da sauri samha ta fito daga ɗaki tana cewa ka shigo mana, murmushin ƙarfin hali faruk yayi tare da cewa kaka tace inzo inje dake gida yanzun yanzun babu lafiya, samha tace lafiya dai? Faruk yace dama hydar ne ya mut............kafin faruk ya ƙarasa samha ta faɗi kasa tare da tafi duniyar suma,


Salati faruk ya farayi don baiyi tunanin haka samha zatayi ba, danshi dama kaka cewa tayi idan yazo ya faɗawa samha hydar ya mutu,


Da sauri ya ciro wayanshi ya fara kiran kaka babu daɗewa ta ɗauka cikin kiɗima faruk ya faɗawa kaka samha ta mutu, cike da tashin hankali kaka ta fara salati, tare da tambayar faruk ina ne inda suke?


Faruk ya faɗawa kaka tace gata nan zuwa, kaka tana kashe waya sai salati takeyi tare da cewa wannan wane irin masifa ne? Abu daga wannan sai wannan? Shi Aliyu yana ciwon zuciya saboda samha, ita kuma ta mutu saboda hydar?


Waya tayi da drivern ta yazo, bayan yazo ta kira faruk ya faɗa mishi inda suke, driver yace ya gane wurin, bayan sun gama wayarne suka tafi, a hanzarce suka isa wurin mota babu ɓata lokaci kaka ta shiga suka nufi gidan kawu,


Suna isa bayan driver yayi parking kaka ta fita da saurinta ta shiga gidan kawu, faruk yana ganin kaka ya fara wallahi wallahi kaka bata bari yayi magana ba, tace ya kawo ruwa,


Da sauri ya kawo ruwa kaka ta fara yayyafawa samha, ajiyar zuciya samha tayi tare da furta inalillahi wa'inna ilaihir raji'un hawaye yana tsiyaya daga cikin gurbin idanuwanta,


Kallonta kaka takeyi cike da tausayi tare dajin ƙaunar "yar jikarta har cikin zuciyarta, lallai kawu ya cuci rayuwar yarinyar nan, amma haka Allah ya ƙaddara mata dan ko wane bawa da ƙaddararsa, kenan itama tana san hydar? Tunda harta suma saboda shi?


Faruk ne yace hajiya mu tafi a kaita asibiti, kaka tace ba asibiti ba gida, dan bata da cikakiyar hausa sosai, kallon samha tayi tare da kamata alamar ta tashi cikin yarenta take cewa su tafi,


Ɓata fuska samha tayi tare da ci gaba da kuka, kaka take tambayrta kukanmi takeyi? Samha dai ta bita da kallo dan bata san abinda take cewa ba, shima faruk bayajin yaren kaka, wata maganar takeyi da hausa wani kuma baya faɗuwa dan haka suka koma yaren bebaye,


Haka dai samha ta haƙura ta tashi ta koma ɗaki ta ɗauko jakar data ɗauko a ɗakin kawu sannan ta fito tsakar gida suka fita daga gidan baki ɗayansu,


Gidan da suke bayar da ajiyan makulli taje ta bada bayan ta bayar ne, ta fito ta nufi inda kaka take jiranta suka shiga mota suka nufi gidan kaka, tun a mota kake take magana daga gani dai faɗa takeyi kuma da samha takeyi, ga banza tunda dai tunda samha batajin karatun,


Itadai sai kuka takeyi tana ƙarawa, tana so ta tambaya da gaske hydar ya rasu? Amma bata da wanda zata tambaya tunda bata iya maganar kaka ba,


Ganin bata iya haƙuri yasa ta anshi wayar kaka, ta shiga gallery ta fara dubawa, hotunan duk kaka da hydar babu wanda yake shi ɗaya, itama babu ita, ita ɗaya, dan haka ta kalli kaka tare da nuna mata hoton hydar da yaren kurame tace mata yana ina?


Kaka tace mutuwa, idanuwa samha ta zaro sosai tare da cewa waye ya kashe shi? kaka bata sake magana ba, ita kuma samha buɗe jakar kawu tayi ta fiddo hotunan tana dubawa, harsai data zo wurin hoton kaka sannan ta tsaya ta kalli hoton ta kalli kaka, a daidai lokacin da suka iso gida,


Bayan driver yayi parking kaka ta fita, itama samha fita tayi, tana bin bayan kaka tana kuka har suka shiga ciki, ganin samha bataga wasu masu zaman gaisuwa ba yasa ta fara tunani kilama kunnenta baiji mata daidai ba, itama kaka datace mutuwa kila ma batasan abinda ita samha ta tambayeta ba shi yasa tace mutuwa,


Tunda suka shiga farlo samha ta bi hotunan hydar da kallo lallai ko ba'a faɗa ba kana gani kasan hydar anaji dashi, bin bayan kaka samha taci gaba dayi simi simi har bedroom,


Zama samha tayi a gefen gado tana ta kallon hoton hannunta kuma tana ƙarewa kaka kallo, to lallai wannan itace kawu yake cewa itace ta aifi mamanta? Lallai wannan tsohuwa tana kama da momyna babu banbanci,


Towel kaka ta miƙawa samha tare da cewa kiyi wanka wanka, dariya samha tayi sosai jin maganar kaka, har ta fito daga wanka samha dariya takeyi tana maimaita kiyi wanka,


Bayan samha ta fito wanka kaka ta bata kaya ta saka, sannan tace kici abinci, wai taje tace abinci, yanda kaka take maganar ne yake sa samha dariya sosai na farko dai bata iya hausar ba idan kuma zatayi magana da hausa kamar zatayi kuka kana gani dai kasan hausa tana mata wahalar furtawa,


Tou haka dai rayuwar samha tayi ta tafiya a gidan kaka, kwanaki masu yawa anyisu, satittika anyi sun shuɗe, watanni kuma suna ta ƙara hayewa amma babu labarin hydar, saidai lokaci lokaci samha tanajin kaka tana waya kuma tanajin ana kiranta sunanta haka ya tabbatar mata da hydar ne,


Dan haka yauma kaka ta gama wayarta ta ajiye ta fita, samha ta ɗauki wayar ta shiga dialled calls, tana dubawa taga lallai da hydar ne kaka tayi waya dan haka da sauri ta shiga kiran number,


Babu daɗewa hydar ya ɗauka, bayan sallama yaci gaba da magana cikin yaren kaka dan dama basu gama magana ba kaka ta kashe wayan, gyara murya samha tayi sannan tace samha ce, hydar yace samha? Wace ce samha? Samha tace Ni, ni samha mana, hydar yace daga ina kuma? Samha tace samha fa nace maka, hafsat ta faɗi ainayin sunanta, hydar yace kai ni banwani san wata samha ba, yana faɗin haka ya kashe wayarshi,


Jin hydar ya kashe waya yasa samha ta sake kiran wayar cikin sauri, amma hydar bai ɗauka ba, da sauri ta ƙara kira saiya kashe wayan ma baki ɗaya,


Duba number tayi taga numbershi ne kenan yana ma nigeria babu inda yaje tsagwaron iskanci ya hanashi zuwa ma tunda yasan tana nan,


Shi kuwa hydar tunda ya dawo daga jinya yaji labarin samha tana gidan kaka yace bama zaizo ba bare ya ganta taci gaba da tada mishi hankali danshi ya gaji dashan wani maganin ciwon zuciya sai kace ɗan ƙwaya, amma tunda samha bata sansa zai haƙura shidai yasan yana santa kuma makahon so yake mata kuma san da yakeyi wa samha mai ɗauke lumfashi ne, dan haka zai barta ya sama mata farin ciki a rayuwarta dan bazai so yaga samha tana cikin damuwa ko tashin hankali ba, tunda dan yana santa yake san ta samu natsuwa tunda bata sanshi zai hakura kada ya takura mata itama tazo ta samu matsala irin tashi,


Jin hydar ya kashe waya gaba ɗaya yasata jin tashin hankali na karshe, dan haka da sauri ta fara kiran number faruk data gani a cikin wayan kaka, shima saida ta kusa tsinkewa ya ɗauka, bayan gaisuwa tace mishi don Allah kaje ka kaima hydar waya zanyi magana dashi, murmushi faruk yayi tare da cewa ai ina tare dashi bari in bashi,


Samha tanajin yanda faruk yake ƙaraya da hydar ya anshi waya amma yace sam, faruk ya haɗashi da Allah amma wallahi hydar yace bazaiyi waya da samha ba, a hankali samha ta silale saman gado ta kwanta hawaye na ɗiga daga cikin kwayar idonta,


Faruk taji yana cewa miyasa bazakayi waya da ita ba? Cikin tsananin ɓacin rai hydar yace haka nan, cikin sigar lallashi faruk yace dan Allah tunda harta kira tace a baka kayi hakuri ka ansa, hydar yace faruk don girman Allah ka daina min maganar yarinyar nan ni sunanta ma bana so inji ana faɗa dan haka kashe waya, faruk zaiyi magana cikin hayani hydar shiruuuuuu ya ƙarasa magana yana zaro idanuwa kamar zai kaiwa faruk duka,


Da sauri samha ta kashe waya kamar ita hydar ya dakawa tsawa, lokaci guda kuma taji gabanta yana faɗuwa jikinta gaba ɗaya ya ɗauki rawa saboda jin muryar hydar cikin fushi yasa tajita kamar ba'a duniya take ba, ashe akwai ranar da hydar zai tsananeta haka? Goge hawayen idonta tayi tare da ajiyar wayar gefe ta rufe idonta da sauri jin kaka tana zuwa,


Jin samha ta kashe waya yasa sukayi dariya dukansu, hydar yace "yar rainin hankali nima zakiji yanda nakeji, dariya faruk yayi tare da cewa ai tunda kace min ta biyoka tana leƙenka a gidan kawu nasan yarinya ta faɗo tarko, hydar yace barni da ita, nasan yanzun tana san ta ganni kuma yarinya bazaki ga hydar ba,


Faruk yace a, a, kaiko miye haka? Kada ka wani ce bazakaje ba, murmushi hydar yayi tare da jingina bayanshi da jikin gado, sannan yace kiramin farida, zan auno samha inga idan ta fara so na da gaskiya,


Kiran wayar farida faruk ya fara yi bayan ta ɗauka yace mai gida zaiyi magana dake, miƙawa hydar wayar yayi, bayan hydar ya ansa yaɗan goga farida jawabi, karshen wayarsa dai murmushi sannan ya kashe,


Samha kuwa kwance sai kuka takeyi wai ita hydar yake dakawa tsawa, amma ba komai, koda kaka ta shigo ta samu samha tana kuka data tambayi samha kukanmi takeyi, samha faɗa mata tayi hydar yayi mata wulaƙanci, abinda kai kaka ta fahimta shine sunan hydar da samha ta kiraka a cikin zancenta ita kuma kaka tasha wani abun arzikine don haka tace da kyau, tana faɗin haka ta fita,


Samha kuwa saida tasha kukanta ta gaji sannan tayi bacci,


Da safe tunda samha tayi sallah asuba bata koma bacci tana nan kwance kamar wata matacciya sai wani fiƙi fiƙi takeyi da idanuwa, tana nan kwance har 11:09am sannan samha ta tashi taje tayi wanka,


A hanzarce ta fito daga toilet tana gunguni, da sauri ta natsu danjin maganar hydar a farlo, taso ta fita amma gani takeyi kamar hydar zai watsata dan taji maganar mace, ina kuma hydar ya samo ta?


Tana tsaye tana nazari inda hydar ya samo mace, taji muryar macen tana cewa wai ina samha? Ƙasa ƙasa samha tayi da murya tare da cewa tana gidan ubanki,


Hydar yace kai mu babu wata samha a gidan nan gaskiya kaka sai yayi magana da yare, wanda samha bataji abinda yace ba, taji dai kaka tayi dariya tare da cewa samha,


Samha tace ai sai kuje kuyi tayi, in banda munafirci sai ayi ta magana da yaren da mutum bayaji, idan ba gaskiya ba a fito fili ayi magana da yaren da kowa yake fahimta mtswww,


Ganin baza ta fito ba yasa hydar ya miƙe ya nufi bedroom ɗin, fuska a ɗaure ya shiga babu alamar wasa, da sauri samha ta durƙusa ta gaishe da hydar, ya ansa a daidai lokacin da yake zama a gefen gado, yace ke zo nan, jiki a sanyaye samha ta matsa kusa da hydar tare da duƙusawa saman guyawunta cikin ladabi,


Hydar yace bakiji nazo ba? Samha tace wanka nakeyi yanzun na fito, hydar yace da kika fito kuma miye ya hana ki fita ki gaisheni? Samha tayi shiru, hydar yace saboda kin rainani ko?


Samha tace kayi hakuri, tsoki hydar yayi tare da cewa jeki gaisa da farida, samha tace miyasa ni zanje in gaisheta ne? Miƙewa hydar yayi tare da cewa ni nace ai,


Samha tace to kace tazo nan sai in gaisheta, juyowa yayi ya tsareta da idanuwa, wanda yasata ta ɗauki hijabi tabi bayan hydar, tana gunguni, juyowa hydar yayi yace badai kince baki san hydar ba? Zo kiga wanda zan aura gama I V ya ciro daga jikin aljihunshi idanuwa samha ta zaro sosai tare da ciko bakinta da magana shigowar kaka ta hana samha faɗin abinda tayi niya,


*_Jαmilα Musα_*

[05/04 4:46 pm] Washa: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊



                 *SO*

     *MUGUN WASA*



       *{ Love is a bad game }*




*JAMEELA MUSA* { meelat musa }




*Story, Writing & Editing*

                   *by*

         *Meelat Musa*


*_Bana gajiya da faɗa muku masoyan BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION, shahararrin marubutan zamani wato Tweety & Aysal sunzo muku da sabbin labarai masu ƙayatar da zukatan masu karatu, bugu da ƙari ilimantarwa darussa masu girma tare kuma da nishaɗantar da masu karatu, tweety tazo muku da, DUK ABINDA YA BAKA TAUSAYI, hausawa sukace wata rana zai baka tsoro, ita kuma Aysal tazo muku da tata shaharar littafin nata shin, BAKA NI KIYA, tou fa kunji mace ce fa baka nikiya, kada ku bari a barku, ni Jαmilα Musα nake cewa asha karatu lafiya_*


*_Gaisuwa ta a gareki, FATIMA MUHAMMAD ina miki fatan alkairi kuma ina godiya sosai wallahi da addu'arki a gareni nagode sosai Allah ubangiji yabar mutum da masoyinsa, na gode sosai wallahi,_*


                  *SO*

      *MUGUN WASA*


*_Dedicated to_* 👇🏻

_Ramlat Abdul real mai damburabos_


*65-67*



Idanuwa samha ta zaro sosai tare da ciko bakinta da magana, shigowar kaka ta hana samha faɗin abinda tayi niya,


Anshe IV ɗin samha tayi daga hannun hydar saida ta kalleshi sosai sannan tayi murmushi tare da cewa to Allah ya baku zaman lafiya ubangiji yasa ayi a sa'a,


Amma abinda nake so ka tuna shine, kace kanka baya ɗaukan hayanir mata biyu, haka ka faɗa amma yanzun zaka ƙara ko? To nima gaskiya nayi ƙarama da in zauna da kishiya nima kaina baya ɗaukar hayaniyar kishi dan haka ni nabarwa farida kai,


Tana faɗin haka ta yada IV in ta koma bedroom, kaka ta fara tambayar hydar miye? Murmushi yayi tare da duƙawa ya ɗauka iv in amma bai ba kaka ansar tambayarta ba, ya fice daga farlon farida ta tashi tabi bayanshi,


Saida hydar ya fice daga farlon, kaka ta nufi bedroom, tana tambayar samha miye? Cikin kuka samha ta fara gogawa kaka bayani ciken yaren kurame tana cewa,


Hydar, sai ta nuna ma kaka da hannunta tace mata ✌🏻dani ta nuna kanta sannan tace wannan da suka zo tare, ta nuna da hannunta a lamar zowa, taci gaba da cewa mu biyu, biyu zai haɗa ya auremu, kaka tace kai A, a, taci gaba da goga yare, tsoki samha tayi tare da cewa kimin yanda zan gane mana,


Haka kaka ta fita tana ta yare, tsoki samha tayi tare da kwanciya saman gado taci gaba da kuka,


Hydar kuma suna fita, farida tace ranka ya daɗe sai kuma yaushe? Hydar yace idan ina nemanki zanma faruk magana ya turoki, yana faɗin haka ya wuce itama ta tafi inda ta ajiye motarta ta shiga taja tabar gidan,


Yinin ranar nan samha kuka ta yini yi, wannan kuka yasa kan samha ya ansa, lokaci guda taji kanta yana wani irin ciwo kamar zai faɗo ƙasa, daga nan masassara tace salama alaikum,


Koda hydar ya dawo da daddare baiga samha ba, abinci kawai yaci yayi tafiyarshi, dan harya zo yaci abinci itama kaka bata san yazo ba,


Samha kuwa, yaukam haka ta kwana da masassarar ta da ciwon kanta, sai kuka takeyi wai hydar zaiyi aure, da kaka ta shigo ɗakin saidai tayi shiru ta goge hawaye da sauri dan idan kaka ta tambayeta bata san ta yanda zata fara gaya mata ba lamarin ba,


Tun jiya samha taƙi taci abinci tana ɗaki nannaɗe a gado kamar wata misaka, ita kuma kaka bata san samha babu lafiya ba, dan haka huɗɗoɗin gabanta kawai takeyi,


Jin maganar farida a farlo yasa samha ta lallaɓa ta tashi zaune ta jingina jikinta da gado, tunda farida ta gaishe da kaka bata sake magana ba, danma ko tayi kaka bata gane abinda take cewa,


Murmushin ƙarfin hali samha tayi sannan ta sauko daga saman gado ta nufi toilet, wanka tayo tare da wanko bakinta ta fito, tana fitowa tajiyo maganar hydar yana cewa ga kayan yarinyar nan,


Wasu muryoyi da batasan ko su waye ba taji suna ma hydar addu'ar a dawo lafiya, tambayar kanta tayi da ina hydar zaije? Wani irin haushi samha taji ya kamata, dama yau kusan kwana nawa idan hydar yazo ya daina nemanta wannan ai wulaƙanci ne,


Da sauri ta jawo kayanta ta saka, ta fito farlo, tana fitowa abinda idanuwanta suka fara gani akwatinan kayanta da yake ɗauko mata kaya cikinsu a gidanshi, kallon inda kayan suke tayi sosai daga sama ga wayarta nan, tsaki tayi sannan ta mayar da dubanta inda su hydar suke zaune shida da farida suna break,


Daƙel samha ta haɗiye yawun bakinta wanda taji kamar ta haɗiyi kunama saboda tsantsagwaren ɓacin rai, murmushin ƙarfin hali samha tayi sannan ta nufi wurin, tana zuwa taja kujera ta zauna tare da cewa ina kwana, tana gaisuwar ne tana kallon cikin kwayar idon hydar,


Lafiya qalau yace a taƙaice, samha tace banda lafiya, hydar yace Allah ya baki, gyara zama tayi tare da ci gaba da cewa asibiti zaka kaini, baiyi magana ba ya miƙe tare da kwashe tarkacen wayoyinsa, da sauri farida ta miƙe tabi bayan hydar suka fita daga farlon,


Tsaki samha tayi tare cewa can kai ta matse mawa, waini za'a bugarwa zuciya, kwafa tayi tare da tashi ta koma ɗaki,


Tun daga ranar samha bata sake ganin hydar ba, haka farida bata sake zuwa ba, saboda hydar baya nan yayi tafiya, dan haka itama samha huɗɗoɗin gabanta takeyi babu abinda ya dameta, dan babu waya tsakaninta da hydar harya dawo daga tafiya, kuma koda ya dawo bata ganin sa,


Dan haka fitarta takeyi san ranta, tayi tafiyarta biɗinta, idan ta dawo taji kaka tana faɗa da yarenta ma bata bi ta kanta dan bataji abinda take cewa bare tasan faɗa ake mata ko lallashi,


Yauma ta ɗauki uban ƙaton wankanta taci gwalabonta, taci nanaye sosai ta ɗaurayu iya ɗaurayuwa, shahararen wanka tayi na nunawa a filin gasa, ta fito tana tako ɗai ɗaya,


Kaka na ganinta tace ina? Samha tace biki, bikin wata ce zanje, kaka tace A, a, samha tace hakuri zakiyi bazan wani daɗe ba zan dawo, kaka tana magana amma samha tayi gaba tare da cewa yanzun nan zan dawo, tana faɗin haka ta fece daga farlon, da sauri kaka ta tashi tabi samha amma kafin taje har tayi waje,


Dawowa ciki kaka tayi ta ɗauki wayarta ta fara kiran hydar bayan ya ɗauka ta rattafa mishi samha bata zama yanzun kullum yawo yauma bata nan taje biki,


Hydar yace wane biki ne akeyi? Kaka tace itama bata sani ba, tsaki hydar yayi tare da kashe wayar,


Ita kuma samha tana fita napep ta haye tayi gidansu illo, ƙanwarshi ake ma biki ita kuma taje ma illo ƙara, tana zuwa ga motoci nan barjak an ajera dan safarar mutane zuwa wurin farty, dan haka samha ta samu zuƙeƙiyan mota ta shige,


Tana shiga illo yace ta fito ta fara shiga ta gaisa dasu mamanshi, tana ƙoƙarin fitane tace malam don Allah kada fa ka tafi ka barni ga jakana nan da wayana ka ajiye min in dawo na saka layi, mutumi yace okey,


Samha ta fita, tana fita mutumin yana cewa ana waya amma hankalin samha baya wurin saboda hayaniyar mutane, har wayar ta tsinke, ƙara kira hydar yayi saida ya kira da yawa mutumin ya ɗauka tare da cewa dan Allah taɗan shiga ciki idan ta fito zata kiraka,


Hydar yace inane ciki? Yace cikin gida, hydar yace ya akayi wayanta yazo hannunka? Faɗawa hydar yayi, hydar yace wane anguwa ne wurin partyn? Yace basu tafi ba amma yanzun za'a fara tafiya, hydar yace yanzun kuna ta ina ne? Ya faɗa ma hydar inda suke, kashe wayar hydar ba tare daya sake cewa komai ba,


Da sauri hydar ya tashi ya ɗauki makullin motarshi ya nufi unguwar  kawu, a ƙofar gidan kawu hydar yayi parking sannan ya fita daga motar, illo na ganinsa ya ruga da gudu yana faɗawa samha yaga hydar,


Samha tace a ina ka ganshi? Yace yana ƙofar gida, da sauri samha ta tashi tace muje, da sauri suka fito ƙofar gida, samha na hango hydar ta tafi wurin shi da sauri, tana zuwa ta fara cewa waye yace ina nan?


Hydar yace ina wayarki take? Samha tace tana moter na bari, hydar yace ina zakije? Samha tace party, jinjina kanshi yayi tare da cewa to muje in kaiki ɗauko jakarki mu tafi,


Da sauri ta nufi wurin motar data baro wayanta a ciki, tana zuwa ta buɗe tare da cewa ɗan uwa na gode sosai ga yayana zai tafi dani, kallonta yayi sannan yace waye yayan naki? Samha tace gashi a can yana jirana,


Yace ke ƙanwar hydar ce? Samha tace Eh, yace amma ba mamanku da baba ɗaya ba ko? Jawo jakarta da wayarta tayi tana cewa Eh, yace to don Allah haɗani dashi zanyi magana dashi naga kamar nasanki ne,


Samha tace kaini baka wani sanni ba, idan zakayi magana dashi kuma harsai na wani haɗaku? Sai kace wata wayar salula gaka gashi ka fito kawai kayi magana dashi,


Tana faɗin haka ta nufi inda hydar yake dan harya kusa isa wurin moter, da sauri ta isa wurinsa tana cewa ga wani can wai zaiyi magana dakai, baiyi mata magana ba ya buɗe moter ya shige, ganin bazaiyi magana ba yasa itama ta haƙura ta buɗe ta shiga tana ci gaba da cewa, yana magana fa, naga kamar munayin kama dashi,


Hydar dai baiyi magana ba yaja motershi ya fara tafiya, samha tace ina ta magana kayi shiru wannan ai babu adalci, dama naga kwanan nan wani neman fitina kayi dani, hydar dai baiyi magana ba, samha taci gaba da cewa nan har rashin lafiya nayi amma baka kaini asibiti ba, saboda kanaso in mutu, ganin hydar bazaiyi magana ba yasa ta daddage taci gaba da aibata farida,


Har tayi ta gama hydar bai ko kalli inda take ba, kallanshi tayi tare da cewa yana ga kanayin hanyar gida? Bayan kasan wurin party zanje? To tunda baza ka kaini wurin partyn ba ka mayar dani gida ni bazanje gidanka ba,


To ka tsaya in fita mana, hydar yace ai zaki iya fita a haka basai na tsaya ba, samha tace wannan wane irin abune? Ya za'ayi in fice daga moter alhalin tana cikin yanayin gudu sosai, so kake inje in faɗi a ƙasa inji ciwo?


Shidai bai sake magana ba har suka isa gida, bayan yayi parking ya fita, ba tare da yayi ma samha magana ba, samha tace sai ka kawoni nan so kakeyi kaka tace na gudu nazo wurinka?


Tace aiko bazan fito ba anan zan kwana, hydar yace to Allah ya baki sa'a, zauniyarta tayi a moter hydar ya wuce ciki abunshi, bayan ya shiga ya kira kaka cewa ya taho da samha gida kada tayi ta jiranta, kaka tace to,


Samha ta daɗe a moter zaune, tun tana zaman marmari harta fara na dole, saidai tayi tsaki ta turo baki, dan tasan da, da ne da yanzun hydar yazo yana lallashinta kilama yanzu ya daina santa, tunda har zai ƙara aure,


Daga wannan tunanin sai kuka, haka samha tayi ta kuka ita ɗaya a moter babu mai bata haƙuri, saida tasha kukanta ta gaji sannan tayi shiru dan kanta, wata zuciya tace ta fita ta shiga ciki wata kuma tace kada kije idan dai har hydar baizo ya tafi dake ba, nuna mishi kema mai zuciyace,


Shi kuma hydar yana gama waya da kaka ɗakinshi ya nufa, yana zuwa yayi wanka yana fitowa ya gama ɗan abinda zaiyi ya haye gado yayi kwanciyarsa,


Wani baƙin ciki ya ƙara turnuƙe zuciyar samha ganin har 10:30pm hydar bai dawo ba, ita kuma ta ɗaukanma ranta yau saidai ta kwana a moter, amma bazata fita ba,


Ganin har 12:04am hydar bai fito ba yasa samha ta ƙara fashewa da kuka saboda tsabar baƙin ciki, ga bacci takeji sosai ta kasa bacci a moter ga karnuka an wani saki sai wani wan wan wan sukeyi, gaba ɗaya sun firgita gidan da kuka, kukan ya hanata ta samu tayi bacci baƙin ciki ya gama ciki zuciyar samha taf, dan haka ta fara kiran wayar kaka,


Saida ta kirata sosai kaka bata ɗauka ba, haka samha tayi ta kiran kaka harsai data farka daga nannauhorn baccin daya daɗe da ɗauketa, cikin muryan bacci kaka ta fara, cikin kuka samha ta fara magana, sai kuka takeyi tana kiran sunan hydar,


Dan bata san ta yanda zata faɗawa kaka hydar ya barta a moter ba, dan haka tayi ta kiran sunan hydar tana kuka, kaka ta kashe waya ta kira hydar, bayan ya ɗauka tace mishi mi yayi ma samha?


Taɓe baki hydar yayi tare da cewa ba komai, kaka tace naji tanayin kuka ne, hydar yace ai samha tayi bacci tun dazu, kaka tace batayi bacci tana kuka, hydar yace to wallahi bai sani ba, kaka tace yaje ya gani, kashe wayan yayi sannan ya tashi ya nufi ɗakin samha,


Bayan yazo ɗakinta gaya bata nan, sai yanzun ya tuno tace zata kwana a moter, tsaki hydar yayi sannan ya sauko ya fito waje, yana fitowa kukan karnuka ya ƙaru,


Sai bin bayan hydar sukeyi suna wan wan wannnn, harya isa wurin moter, samha ganin hydar yasa ta ƙara fashewa da kuka,


Buɗe motar yayi tare da cewa fito, da sauri samha ta fito tana ci gaba da kuka, rufe moter yayi bayan ta fito, yace muje samha tayi tsaye tana turo baki,


Kallonta yayi tare da cewa kada ki sake kiran wani daga yau kina faɗa mashi wani abu tsakani na dake, samha tace ummm ummm tana turo baki gunguni kenan, 


Hydar yace ni kike ma rashin kunya ko? To kiyi idan na gaji zansa karnukan nan su cinye minke kowa ma ya huta, gyara bakinta tayi ba tare da tayi magana ba, miƙa mata hannunshi yayi alamar ta taho, itama miƙa hannunta tayi hydar ya riƙe hannun tare da jawota jikinsa a hankali ya rungumeta, wata irin wahalalliyar ajiyar zuciya samha ta sauke mai ɗauke lunfashi na wani lokaci, da sauri ta ƙara kwanciya a jikin hydar sosai,


Hydar yace kiyi hakuri ina tunanin kin taho bansan kina nan ba, cikin kuka samha tace ai kasan ka barni a moter kayi tafiyarka tunda ka daina so na yanzu, hydar yace waye yace miki? Ai san da nake miki har abada bazai goge a zuciyata ba, dake zuciyata ta fara kuma dake zata rufe insha Allah, samha tace ba wani gashi zakayi aure,


Murmushi hydar yayi sannan ya ɗago samha daga jikinshi, ɗago mata fuskarta yayi tana kallon idonshi, ɗan buɗe idanuwanshi yayi sannan ya lumshesu a hankali tare da kashe ido ɗaya, bai bata amsa ba ya dafa kafaɗarta suka fara tafiya,


Samha taci gaba da cewa wai da gaske aure zakayi? Hydar yace umm, samha tace ni ka daina sona ne? Hydar yace A, a, samha tace itama kana santa? Hydar yayi shiru, samha tace bazakaji wani iri ba mata biyu? Nan ma shiru yayi,


Itama bata sake magana ba har suka shiga, saida yakaita ɗaki ya kwantar da ita a gado sannan yace saida safe, zai wuce samha ta riƙe mishi "yan yatsu, juyowa hydar yayi ya kalleta amma baiyi magana ba, cikin shashshekar kuka samha tace sanyi nakeji, idanuwa hydar ya zaro tare da cewa sanyi kuma samha? Ɓata fuska tayi kamar zata ƙarayin kuka sannan tace Ey, dogon kallo hydar yayi ma samha sosai, sannan ta cire hannunshi daga jikin nata,


Matsawa yayi jikin wedrof ya buɗe ya ɗauko ƙaton bargo yazo ya lulleɓeta, bayan ya lulluɓeta zai tafi ta sake riƙe hannunsa, kallonta hydar yayi sannan yace miye? Samha tace na gode, murmushi yayi ba tare da yayi magana ba ya zame hannushi yayi tafiyarsa,


Ajiyar zuciya samha tayi tare da gyara kwanciyarta ta fara bacci,



Don Allah kuyi haƙuri da wannan, bana zaune ne abubuwa sunsha min kai da yawa da yawa, jiya kuma naji ƙorafinku wasu na cewa ina musu short typing, kuyi hakuri nafiku so inyi da yawa dan na ƙosa labarin ya ƙare haka nan,


*_Jαmilα Musα_*

[05/04 4:46 pm] Washa: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊



                 *SO*

     *MUGUN WASA*



       *{ Love is a bad game }*




*JAMEELA MUSA* { meelat musa }




*Story, Writing & Editing*

                   *by*

         *Meelat Musa*


```Tir qashi ayau ne shararren masani akan novel ɗin hausa ke tunawa da ranar zagayowan aihuwar sa admins of admins yaya hayatu baba zubairu, haƙiƙa muna farinciki da tayaka murna akan zagawar  wannan rana mafi haske da ɗumbin tarihi a cikin rayuwar ka! Lallai aihuwa tayi rana ka amsa sunan ka na admins of admins domin kai haziƙi ne da kuma sanin buƙatun masu karatu. Babu shakka yabon gwani ya zama dolw musamman yadda kake ilmantarwa da koyar da kwalliya irinta zamani Allah yaja kwana da shekaru masu yawa da hikima baseera a cikin jininka! Barka da wannan rana hayatu baba zubairu !Cool Novel's Make up & Kitchen! Jαmila Musα  &  Ramlat Mai dambu, 4rom BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION````,


                  *SO*

      *MUGUN WASA*


*_Dedicated to_* 👇🏻

_Ramlat Abdulrahman real mai dambu_



*68-70*


Ajiyan zuciya samha tayi tare da gyara kwanciyanta ta fara bacci,


A gajiye hydar ya isa ɗakinshi zuciyanshi cike da tunani barkatai, murmushi yayi da gefen bakinsa a daidai lokacin da yake zama a gefen gado,


Ayijan zuciya yayi tare da tambayan kanshi miye yasa samha tace mishi tanajin sanyi? A hankali ya kwanta saman gado tare da rufe idanuwansa, hoton samha ya dawo mishi akai, tare da tuno maganarta,


_Sanyi nakeji_


Murmushi hydar yayi tare da sauki ajiyan zuciya, lallai wani abu yana faru, mi samha take nufi da hakan?


Tunani sosai hydar yayi daga baya ya tashi ya nufi toilet ya ɗauro alwallah bayan ya fito ya fara sallah kamar yanda ya saba,


Samha kuwa bancinta tasha abunta hankalinta kwance kamar tahau jirgi mai ya ƙare,


Da safe bayan hydar ya dawo daga masallaci bai shiga ɗakin samha ba wucewa yayi ɗakinsa abinsa,


Ita kuma bayan tayi sallah asuba, komawa tayi bacci bata farka ba sai wurin 9:55am, toilet ta shiga tayi wanka bayan ta fito taci gayenta sosai, ta saka kaya masu kyau sannan ta fito dan zuwa ɗakin hydar,


Tunda samha ta fito ɗakinta takeji magana ƙasa ƙasa, kuma muryan mace takeji,


Da saurinta tayo ribos kamar wata urban tayo ƙasa, tunda ta sauko ta hango farida sai wani yashe baki takeyi tana dariya, tana ma hydar magana,


Shi kuma ya ɗan duƙar da kanshi yana kallon waya, gaba ɗaya hankalinsa yana kan wayarshi sai wani shashshafata yakeyi ya riƙeta a mutunce da hannuwansa biyu,


Samha bata gama saukowa ba, ta tsaya saman step ɗin ta dafa ƙarfen benen tare da cewa hydar ina magana,


Ba tare daya ɗago kansa ba daga kallon wayar yaɗan taɓe bakinsa tare da cewa zo nan mana kiyi magana dani,


Samha tace ba zanzo anan ba nace kawai kazo, murmushi hydar yayi ba tare da yayi magana ba ko ya kalli inda samha take ba,


Zama tayi a wurin tana ci gaba da cewa hydar an ɗaura aurenka da farida ko kuwa? Yace wani abu? Samha tace kawai na tambayeka ne,


Hydar yace ba'a ɗaura ba, samha tace to gaskiya daga yau sai yau kada farida ta sake zuwa gidan nan, hydar yace dalili?


Samha tace dalili kake so kaji kenan ko? Baiyi magana ba, sai farida dake ta dariya irin mai cin rai ɗin nan,


Tsoki samha tayi amma bata sake magana ba, shima hydar baiyi magana ba, yana dai ta dandanna wayarsa, ita kuma farida tashi tayi ta nufi kching, 


Samha taci gaba da gunguni tare da tutturo baki tana harar hydar, shidai baiyi mata magana ba,


Tana nan zaune har farida ta fito daga kching da flet a hannunta tana ta ƙara faɗaɗa murmushinta, ta nufi inda hydar yake zaune ta ajiye a gabanshi cikin girmamawa, da sauri samha ta sauko da gudu ta iso kusa da hydar tare da ɗaukar indomie ɗin ta zubar ƙasa,


Kallonta hydar yayi amma baiyi magana ba, lokaci mai tsayi yana kallonta ba tare da yace komai ba, farida ce tace samha miye kikayi haka?


Samha tace da Allah rufewa mutane banzan bakinki, ina ruwanki? Dani da mijina nake ko kinga tunda na fito na miki magana ne? Murmushi farida tayi tare da duƙawa inda samha ta zubar da abinci ta fara kwashewa,


Hydar yace ma farida kada ki kwashe shi itace zata kwashe kuma saita cinyeshi, samha tace Allah ya sawaƙe inci abinci ƙasa kamar wata jaka,


Hydar yace babu abinda ya dameni kinji dai abinda nace miki, tsoki samha tayi sannan ta nufi inda take zaune a ɗazu ta sake zama, hydar yace ke zo nan, duƙar da kanta tayi ƙasa tare da turo bakinta amma batayi magana ba,


Hydar yace idan na sake miki magana zakisan na miki magana kin min shiru, tashi samha tayi da gudu ta nufi ɗaki tana gunguni, murmushi hydar yayi a ransa tare da bin bayan samha da kallo harya daina hangota,


Ita kuwa farida yinin ranar nan itace ta gyara ko ina a gidan nan ta share ta goge fess, ta dafa abinci saida ta tabbatar ta kammala komai sannan tayi ma hydar saida safe itama ta tafi gida,


Farida bata dade da tafiya ba shima hydar yabar gidan,


Ita kuwa samha tana shiga ɗaki a gefen gado tayi ma kanta masauki, tana zama ta fara dogon nazari wanda ba niba ko ita kanta bata san dalilin yinsa ba,


Tsoki samha tayi a bayyane tare da cewa wallahi idan har hydar ya sake kawo da wannan banzar bazarar kaza matatta a bola bazata yadda ba, idan kuwa yayi taurin ka to lallai saidai a raba ko ina na gidan kowa ya tsaya sashen sa,


Saida ta gama nazarin yanda zata bullo ma lamarin, sannan tayi dariya dan tasan dan hydar ya ɓata mata rai yake kawo farida a gidan nan, dan haka itama tunda tasan baya san mage a rayuwarsa lallai itama saita sa yau an samo mata mage, ta yadda kowa ya ci gaba da ɓatawa kowa rai,


Dariya samha tayi a daidai lokacin da take saukowa daga saman gado, da sauri ta fita daga ɗakinta ta nufi ɗakin hydar,


A inda hydar yake ajiye kuɗi ta ɗauko, sannan ta sauko ƙasa, tana saukowa ta fara kiran wayan illo, bayan ya ɗauka tace mishi don Allah illo magenka zaka bani haya, ni kuma zan baka kuɗi mai yawa,


Illo yace baki da damuwa, zan kawo miki, samha tace yawwa, kuma kafin kazo kaje kasuwa don Allah ka siyo min jan yadi amma a yankamin shi ayi min tsawo dashi sosai, sai a min zikzza, idan kazo duka zan baka kuɗinka, illo yace to baki da damuwa saina zo, samha tace yawwa idan kazo kamin waya, yace to sannan ya kashe wayarshi,


Cikin farin ciki samha ta koma ɗakinta tana zuwa a gaggauce tayi wanka bayan ta fito sallah tayi, bayan ta gama ta shirya fess saida ta gama shirinta tsaf sannan ta ɗauki wayanta ta fara kiran illo,


Bayan ya ɗauka yace mata ya kusa isowa yanzun nan, samha tace yawwa zan jiraka a waje kafin kazo, illo yace to,


Tana gama wayan ta saka hijabinta, ta fito dan tafiya wurin illo, a bakin ƙofar farlo suka haɗe da hydar shi zai shiga ita kuma zata fita, da ɗan sauri ya raɓe ya bata hanya, ba tare daya tambayeta ina zataje ba,


Tana fita Alale ya taso da sauri tare da cewa ranki ya dade ina zakije ne? Samha tace zan anso saƙo a waje, Alale yace bara in anso miki, murmushi samha tayi tare da cewa na gode, tana faɗin haka tayi gaba abinta,


Da sauri samha take tafiya haɗi da ɗan gudu gudu, saboda akwai nisa sosai kafin ta isa inda illo yake, kafin taje har illo yazo yana jiran isowarta,


Tana isa ta bawa illo kuɗin shi kuma ya bata mage a cikin kwali sai yadin data sa ya siyo mata an mishi wiyving, godiya illo yayi sannan yayi tafiyarsa, ita kuma samha tayo ciki da magenta,


Da saurinta ta shiga farlo hydar yana zaune yana cin abinci, da sallama ta shiga farlon hydar ya ansa dakel, samha ta ajiye kwalin magenta saman kujera, sannan ta nufi sama da kyallen yadinta,


Daga jikin ƙafen bene ta fara ɗaurawa, sannan ta jawoshi ta sauko ƙasa tana janshi, saida tazo daidai saitin hydar ta fara cewa ai gara a raba farlon nan kowa yasan wurinsa, idan mutum yayi da jan baki ace saiya goge, 


To yanzun nayi da ƙalle danni bana zama sashe ɗaya da kishiya, haka tayi ta jan ƙallen har kching sannan ta ɗaure a jikin window bayan ta ɗaure ta fito,


Inda ta ajiye kwalin magenta ta ɗauka sannan ta zauna a saman kujera bayan ta zauna ta ɗauki kwalin ta ɗora a saman cinyarta, tana hango hydar an wani raba iyaka kamar tsakanin nigeria da niger,


Buɗe kwalin tayi tare da fiddo kirceciyar magen sai kuka take irin na gahurtaccin maguna miyau miyau miyauuuu, da sauri hydar ya ɗauke ƙafarshi daga ƙasa ya ɗorata saman dirning dan duk duniya babu abinda ya tsana irin yaji mage tana shafar mishi jiki,


Ɗaga magen samha tayi sama kamar tana ma jinjiri wasa, ta fara cewa kashedinki kada ki kuskura kije inda bance ba, kuma kada ki sake kibi kowa a gidan nan sai ni, kuma kada ki kuskura ki tsallaka can ta nuna inda hydar yake zaune, sannan taci gaba da cewa anja burtali { iyaka } kowa zai tsaya a wurinsa kada ki kuskura kije ki jawo min fitina, danni ban iya ɗauko samari ba,


Murmushi hydar yayi amma bai kalli samha ba, yaci gaba da cin abincisa, sake magen samha tayi ita kuma ta sauka ta zauna ƙasa saman kafet, tana ƙara ma magen kashedi wai kada taje wurin hydar ta jawo mata fitina,


Tana nan zaune a ƙasa da magen tazo zata tsallaka iyaka sai ta jawota, tace kiyi zamanki anan, dan gidan babu lafiya faɗa masu gidan sukeyi, munayin gaba dani da mai gida kowa babu mai ma kowa magana, sai ƙoƙari kowa yake yaga ya ɓatawa ɗan uwansa rai, nidai kam ina san zaman lafiya shi yasa na kawoki mu riƙayin fira tare shidai hydar budurwarsa tana zuwa masa fira kullum safiya sannan tana girka masa abinci,


Kema bara in kawo miki madara kisha kada yunwa ta kamaki, ni dan ni na ajiyeki bana so Allah ya kamani da laifin na horaki da yunwa, wani kuma ai cikinsa kawai ya sani tun safiya yakecin abinci har yanzun bai ƙoshi shi ba, ni kuma banci abinci ba duk yau ɗin nan,


Haka nan nake ta hakuri, a daidai lokacin data shiga kicin da magen a hannunta, ta haɗo mata madara a flet, sanna ta dawo farlo ta ajiye mata mage kuwa tayi ta lallashewa,


Hydar yace samha wai a ina zaki ajiye mage ne? Ba tare da samha ta kalli hydar ba, hankalinta yana kan magenta tana shafa ta tace anan mana, ai shine dalilin daya sa na raba ko ina na gidan nan magena zatayi rayuwarta cikin jin daɗi da "yan ci,


Cikin tsananin fushi hydar yace wallahi bazai yuwu ba, nine zaki zo ki ajiye mage a tare dani? Dani da mage zamuyi rayuwa a gida ɗaya?  Tun wuri ma ki mayar da ita inda kika ɗaukota idan ba haka ba wallahi zan tillata karnuka su cinyeta na faɗa miki, itama samha ciki fushi ta miƙe tsaye da magenta rungume a jikinta tace tunda kake zuwa da budurwarka ni na taɓa cewa zansa kare ya cinyeta? Hydar yace wannan ai haukane!


Kin taɓa gani kare yaci mutum ne? Samha tace ashe kuwa kare bazaici mage ba, kwafa hydar yayi tare da cewa kisan mafita dake da magennan kafin inyo wanka in dawo,


Samha tace wallahi bazataje ko ina ba sai wannan jakar ta daina zuwa gidan idan kuwa ba haka ba ni zan riƙa cinna maka magen saika suma, tana magana tana shafa magen, hydar yace wallahi zan miki duka na faɗa miki, samha tace ai dama ka saba, yau kuma sai ka dakeni saboda mace, tana maganar tana murguɗa mishi baki,


Tsoki hydar yayi sannan yayi gaba ba tare daya sake magana ba, samha kuwa sakin magen tayi tare da cewa sauka kije kiyi wasanki tunda kema ɗiyar masu gidan nan ce, tana sakin magen da gudu tayi sama, da sauri hydar ya raɓe gefe ɗaya tare da cewa samha bana san haka wallahi idan har magen nan ta taɓa min jikina wallahi kema yau sai kinji hydar a jiknki zo ki kamata, zama samha tayi saman kujera tare da cewa zo nan ka faɗamin, wato abinda yace mata kenan a lokacin data kirashi yana tare da farida,


Wayarshi ya ciro daga aljihu ya fara kiran shamsu, bayan ya ɗauka yace yazo ya fitar da mage ta shigo mishi bayaso ta taɓa mishi jiki, samha tana jin yace azo a fitar da mage da sauri ta tashi taje ta kama magenta ta shige ɗaki abinta,


Kwafa hydar yayi sannan ya wuce ɗakinsa, ita kuma samha tana shiga ɗaki ta kulle sannan ta saki magen tayi ta shawagi a tsakar ɗaki, ita kuma ta haye gado tayi kwanciyarta,


Hydar saida ya dawo sallah isha'i sannan ya kira samha a waya tazo taci abinchi dan duk yau bataci komai ba, amma sai tace ta ƙoshi, haka nan hydar ya gama zaman sa shima ya tashi ya nufi ɗakinsa dan hutama rayuwarsa,


Samha kuwa tunda ta gama sallah asuba ta fito, ta gyara daidai wurinta ta goge tass ta shiga kicin ta haɗa abinda zatayi kalaci, daidai nata, bayan ta gama ta koma ɗaki dan wanko bakinta tayi kalaci,


Hydar dake zaune yana karatun Qur'ani yaga samha ta wuce, rufe Qur'anin yayi ya ajiye, tashi yayi ya nufi kicin ɗin, baya fa kalaci irin wannan lokacin amma dan ya ɓatawa samha rai tunda yasan itama dan ta kwana da yunwa tayi sauko zatayi kalaci, yana shiga kicin ɗin ya kalli agogon dake maƙale a jikin bangon kicin ɗin, 7:09am, hmmm hydar yace tare ɗauko abinda samha ta haɗa dan kalaci ya dawo farlo,


Ya nufi wurin tebirin cin abinci, anan hydar ya bige aiki ya lashe kaf abinda samha ta haɗa don kalaci, ga mage kuma yasa an fitar da ita,  tunda ya dawo daga masallaci yaga samha tana shara a farlo ya fita ta baya yasa shamsu yazo ya fitar da banzar magen,


Ita kuwa samha tana zuwa ɗaki wanka ta shiga, bayan ta fito mai da powder sai kwalli ta shafa ba wani kwalliya tayi ba, tana gamawa ta saka kayanta bayan ta gama ta fara kiran magenta, amma shiru kake ji,


Ganin mage bazata fito ba, yasa ta hakura ta sauko saboda yunwa takeji sosai, bata ko kalli inda hydar yake ba tayi kicin da saurinta, tana shiga a sikwane ta isa wurin data ajiye kalacinta, tana taɓa flet ɗin data zuba dankali a ciki taji ba kamar yanda ta ajiye ba, da sauri ta ɗauke na saman dan ta gani ba komai a ciki,


Idanuwa samha ta zaro tare da ɗaga flet ɗin ta saddashi ƙasa, a daidai lokacin da hydar ya shigo kicin ɗin da sallama, ba tare da samha ta ansa sallama ba tace waye ya cinye min dankali na? Bayan yunwa nakeji wannan ai ɗaukar alhakine, kuma kaine ma kaci min abuna, hydar yace to ai nima yunwa nakeji,


Hawaye ya gangaro daga idon samha saboda ɓacin rai dan yunwa takeji ta kirki dan jikinta har kyarma yake saboda yunwa, dariya hydar yayi sosai tare da cewa saboda na cinye dankali kike kuka? Ya ƙarasa maganar yana ƙara kyalkyalwa da dariya,


A zuciye samha tayi hanyar fita, da sauri hydar ya riƙota tare da cewa zakisha tea ai ko? Har yanzun samha kuka takeyi, amma batayi magana ba, hydar yace ai laifinki ne, kinsan ni ba rodi bane dole ne zanji yunwa, sai ki wani kama kice ke ɗaya kawai zakiji daɗi an taɓa haka ne?


Cikin shashshekar kuka samha tace ai saikaci ka ragemin, hydar yace ba kinsan mu biyune zaune a gidan nan ba, kawai ina zato nawane ni kuma na wane cinye duka ai bansan banda ni ba,


Hydar yace swry bara in sauri in haɗa miki tea kiɗan fara nuna masa hanya, samha tace ni bazansha tea ba ta ƙarasa maganar tana goge hawayen idonta, murmushi hydar yayi tare da cewa don Allah bakiji kunya ba kina kuka saboda yunwa? Gyara bakinta tayi amma batace komai ba,


Dariya hydar ya sakeyi tare da cewa kinga yanda kike yi? Lallai yunwa tana aiki a wurin nan, juyo samha yayi bayanta ya koma saman jikinsa ita ta bawa hydar baya tana riƙe a jikinsa shi kuma ya ɗora kansa saman ƙafaɗarta hannunsa yana saman cikinta yana shafawa, murmushi yayi tare da cewa bara in ɗauko miki hoton bakinki kiga yanda yayi dan baici dankali ba, wayarta dake ajiye a gefe hydar ya ɗauka sannan ya juyowata tana kallonshi, daidai bakin samha ya ɗauka hoto, da hydar ya nuna ma samha taso tayi dariya yanda taga bakinta amma saita basar, kallon hoton hydar yayi tare da cewa shantu kenan samha don Allah kalli bakinki kamar yaji duka, ya karasa maganar yana dariya mai cin rai,


Saida ya gama dariyarsa sannan ya saki samha daga jikinsa yana cewa bara in dafa miki indomie, samha dai bata sake magana ba ta jingina da bango sai gunguni takeyi,


Harya gama samha bata sake magana ba, dan gaba ɗaya haushi takeji rabonta da abinci tun daren shekaran jiya, dan jiya babu abinda taci, bayan hydar ya gama ya juye a flet ya ɗauka sannan yaja hannun samha suka fito farlo,


Da kanshi yake bata tana ci yana dariya a ranshi dan yasan ya more mata sosai, saida ta gama sannan yace to ki tashi wannan abun da kika ɗaura ki cireshi kinga yanzun an fara zaman lafiya mun daina faɗa daga yau, farida bazata sake zuwa ba, tunda kina sona ko?


Samha tace kaine kaje ka ɗaukar ma mutane mage ko? Taɓe baki hydar yayi tare da cewa haba badai hydar ba, ni kam mi zai haɗani in ɗauka mage ina da hankalina, samha tace nima da hankalina tunda har yanzun ban fara dukan kowa ba, murmushi hydar yayi yana kallon samha ba tare da yace komai ba,


Tashi samha tayi ta nufi kicin ta fara kwanto kyallen data ɗaura, bayan ta fito daga kicin ta haura sama ta kwanto daga inda ta ɗaura, ta tattara kyallen ta kawo ma hydar tare da cewa na kwance gashi,


Hydar yace ta zauna, zama tayi babu gardama, hydar yace don Allah samha ki daina abinda kike, wallahi banajin daɗi inga kina abinda zai ɓatamin rai, yanzun dan na faɗa miki bana san mage ta shafamin jiki shine zakije ki samo mage? Wato idan ma zan mutu babu abinda ya dameki ko? Samha ni nasan baki so na kuma bana tunanin zaki soni kamar yanda nake sanki, nidai nasan sanki ya ginu a cikin zuciyata bana tunanin zan daina sanki, ina sanki ina kaunarki kuma inajinki sosai a zuciyata samha har ƙarshen lumfashina babu ranar da zan daina sanki a zuciyata,


Kuma duk abinda nasan bakya so bana miki, dan bana san kiji wani iri a zuciyarki, to ko bakya so na, don Allah duk abinda kikasan zaki min wanda zaisa inji banajin daɗi a raina kiyi hakuri ki daina kinji ko? Cikin sanyin jiki samha tace tom, ajiyar zuciya hydar yayi sannan yace bara inyi wanka fita zamuyi ki canja kaya, samha tace tom,


Tashi hydar yayi ya nufi ɗakinsa, itama tashi tayi ta nufi nata, tana shiga babu wani ɓata lokaci ta canja kaya, ta ƙara gyara fuskarta bayan ta gama ta nufi ɗakin hydar, shi kuma adaidai lokacin ya fito daga wanka, zama tayi a gefen gado sannan tace wai don Allah ya kakeyi kazo a matsayin sahib wurina? Kallonta hydar yayi amma baiyi magana ba, kuma har yanzun idonshi yana kanta yana mata wani irin kallo mai nunu da nazari yakeyi,


Ɗan taɓe baki hydar yayi ba tare da yace ma samha komai ba, harya gama shirinsa ya saka kayansa bai ƙara kallon inda samha take ba bare kuma tayi tunanin zaice mata wani abu ba,


Bayan ya gama yace ma samha muje yana faɗin haka yayi gaba, samha tace to ai ka jirani dai ko?  Juyowa yayi tare da cewa na jiraki, ɗaukar gyalenta tayi da jakarta dama takalminta yana ƙafarta tashi tayi tabi hydar saida suka sauko ƙasa sannan ta yafa gyalenta,


Hydar yana gaba yana waya ita kuma tana bin bayansa, har suka isa wurin motoci, Alale ne ya buɗe hydar ya shiga sannan samha ta shiga ya rufe, Alale ne yaja moter da hydar da samha suke ciki, sannan sauran motocin suka bi bayansu,


Bayan ya gama wayarne kuma kiran wayar kaka ya shigo a cikin wayarsa, samha jin sun fara yaren da bataji yasa tayi tsoki, da wutsiyar ido hydar ya kalleta a ranshi kuma murmushi yayi, sun daɗe suna waya da kaka sannan hydar ya miƙawa samha waya ansa samha tayi ba tare da tace komai ba ta kara wayar a kunneta, murmushi hydar yayi tare da jawo samha a jikinsa,


Kallon hydar tayi tare da ɗaga mata gira, hannusa yakai dan tayata riƙe wayar, samha tace ina kwana, kaka tace lafiya lo, samha tace ya gida ya kuke? Kaka tace lafiya lo, daga haka samha ta miƙawa hydar wayar,


Shima baice wani abu ba, ya kashe wayarsa, har suka iso inda zasuje babu wanda ya sake magana tsakanin hydar da samha, amma har a lokacin tana kwance a jikinsa,


Bayan anyi parking samha ta tashi daga jikin hydar, shamsu ya buɗewa hydar moter, fita hydar yayi amma samha bata fita ba, tunda bai bata izinin fitowa ba,


Samha tana zaune a moter ta jingina kanta da murfin moter tana nazarin rayuwa, hydar yaɗan daɗe sosai sannan ya dawo yace ma samha ta fito, fita samha tayi ba tare da tayi magana ba,


Tsayuwa hydar yayi har ta iso kusa dashi tace nan ɗin ina ne? Hydar yace gidan ahalinki ne, nan gidan yayun dadynki ne, kuma dukansu suna nan sun haɗu a ciki kowa yana san ganinki, 


Rungume hydar samha tayi idonta yana fitar da hawayen farin ciki, cikin muryar da bazaka iya tantancewa kukane ko farin ciki samha tace hada dadyna shima? Ɗan lumshe ido hydar yayi ba tare daya ce wani abu ba,


Jin hydar baiyi magana ba yasa samha tace uhum? Hydar yace kedai kawai muje, tare suka jera har ciki,


A tsakar gida suke zaune, gasu nan sun jera layi ringiss sai kace an musu gorin yawa, da matansu da "ya"yansu, kowa yana cikin farin ciki, hydar kuwa a ranshi cewa yayi lallai mutanen nan basu da kunya, wato yau sunga samha kowa yana ƙoƙarin tasan su mutanen kirki ne, bayan nan nazo neman aurenta babu wanda yace ina samha har aka ɗaura aurena da ita, yana wannan tunanin ne yaji ana cewa ranka ya dade ku zauna mana,


Murmushin ƙarfin hali hydar yayi sannan ya ɗan duƙa dan cire takalmin ƙafarsa, bayan ya cire yaja hannun samha suka hau saman tabarmar sannan suka zauna,


Bayan sun zauna gaishe gaishe ya fara, bayan an gama gaisuwa ne, suka ma samha Allah yasa alkairi tare da musu addu'ar zaman lafiya, hydar ne kaɗai yace amin amma samha kanta yana ƙasa,


Hydar yace to wannan itace samha gata nan na kawo kamar yanda nace zan kawota a gaban kawu, hydar yana faɗin haka ya mike tsaye tare cewa samha ina meeting anjima zan dawo in ɗaukeki,


Ƙanin dadyn samha yace A, a, ka barta ta kwana biyu mana dan wanda basu santa ba, su ganta, murmushi hydar yayi tare da cewa A, a, zanci gaba da dawo da ita kullum kullum amma gaskiya bazata kwana ba,


Matarsa ce tace don Allah kayi haƙuri ka barta kwana biyu ne fa kawai, kallonta hydar yayi tare dayin murmushi da gefen bakinsa, dogon kallo yayi mata sosai wanda yasa ta sunkuyar da kanta ƙasa,


Samha tace ka barni zan kwana bayan kwana biyu saika dawo, kallonta hydar yayi tare da cewa tom, zan dawo anjima in kawo miki kayanki, murmushi samha tayi tare da cewa saika dawo,


Tashi sukayi danyi ma hydar rakiya, amma banda samha, yayu da ƙannen dady suka tafi danyi mishi rakiya, wata "yar masakaiciyar jaka taf da kuɗi hydar yace shamsu yakai a ciki, wani yayan baban samha ne yace kai kawo nan shamsu ya miƙa mishi, 


Suna tsaye har motocin hydar suka ɓace daga wurin, sannan sukayo gida, bayan sun dawo gida kowa ya manta da lamarin samha suka shiga kiciniyar rabon kuɗi,


Wurin rabon kuɗi harsai da akayi faɗa, duk samha tana kallonsu sai masifa sukeyi sosai saboda tsabar san abun duniya kowa ya manta da kowa ɗan uwansa ne,


Saida suka gama rabon kuɗinsu suka dawo takan samha, dan haka suka shiga rattafawa samha surutu, tare nuna mata lallai tayi babban sa'a a rayuwa data kasance mata a wurin hydar, 


Haka sukayi ta nunawa samha girma irin na hydar a ƙasar nan, da nuna mata girma da yawa irin na kuɗinsa, ita samha kallon mahaukata take musu lallai da a wurinsu ta rayu haƙiƙa dasai rayuwata tafi shiga garari akan ta wurin kawu, dan tunda ta haɗu da hydar a matsayin sahib ya hanata sace sace, saida ta auri hydar sahib kuma yace tayi satawa hydar ashe dan ya auna ta yaga ta daina ko bata daina ba,


Anan suka faɗawa samha an kashe babanta da kisan da akayi ma mahaifiyarta da hukuncin da hydar yasa akayi musu, bayan sun gama rattafa ɗiminsu akace samha ta shiga ciki ta huta, jiki a sanyaye samha ta tashi ta nufi ɗakin wata matar ɗan yayan dadynta, tana shiga a saman gado ta kwanta, zuciyarta tana mata babu daɗi,


Hydar kuwa tunda ya tafi yakejin baƙin ciki a ransa danji yake kamar samha bazata dawo ba, harya gama meeting ransa baya masa daɗi, yinin ranar nan duk wanda yaga hydar yasan akwai abinda yake damunsa, bai koma gidansa ba gidan kaka ya wuce dan baiji yana iya zama gidan ba,


A bedroom ɗin kaka ya shige yayi kwanciyarsa saman gado, saida ya kwanta sannan ya fara kiran wayan samha, saida ya kira ta sau biyu sannan ta ɗauka, tana ɗauka hydar yace ina kika ajiye wayar ne? Samha tace bacci nakeyi ne, hydar yace da kyau wato har kina iya bacci bana kusa dake ko? 


Samha tayi shiru, hydar yace zanzo anjima da misalin 10:30pm samha tace ai dare yayi a lokacin sosai hydar yace a lokacin nakejin zan iya zuwa, sai nazo, samha zatayi magana ya kashe wayanshi,


Tsoki samha tayi tare da cewa ai sai kaje kayi ta kashewa, Rabi matar ɗanɗan yayan dady tace samha keda wa? Ɗan gajeran tsaki samha tayi tare cewa wai hydar zaizo da ƙarfe 10:30 na dare, Rabi tace sai kiyi masa tsaki? Sai kice Allah ya kawoshi lafiya ko, kam lallai da kinsan yanda samha take ma hydar ashe dasai kinci uwata,


Rabi taci gaba da cewa ke bakisan duk wani kalami da baya da kyau ba'a faɗawa mijishi ba? Mijinki sa'ar wasanki ne? Samha tayi shiru, rabi tace amma ai kinsan hydar ba yaro bane da zaki riƙa mishi rashin kunya idan kina gyarawa ki gyara idan har kina san gamawa lafiya, nan dai tayi ta ma samha faɗa, samha tayi shiru, 


Rabi tace Allah ya rufa miki asiri amma bazaki gode mishi ba, ki tarairayi mijinki ki zauna lafiya A, a, sai hauka sai shirme da kumu ƙuruciya dake mike hauka a cikin kwalwar kanki, saida tayi ma samha fess sannan ta fita daga ɗakin,


Samha kuwa tana nan kwance tana tunani daban daban a ranta, Rabi ce ta shigo ɗakin tare da cewa tashi kije kiyi wanka ga ruwa nakai miki a bayi, ba tare da samha tace komai ba ta sauko daga saman gado tabi bayan rabi takaita har toilet, tunda suka fito sauran matan gidan suke zinɗe wai ga ɗiyar karuwa can ta kama samha zata koya mata kwartanci, gidan babban gida ne, ɗakuna kashi kashi kamar ɗakunan makarantar boding, haka sukayi ta zagin Rabi wai karuwa ɗiyar karuwa, saboda karuwanci irin nata yasa bata zama da kishiya duk wanda ta shigo sai ta tafi saboda ta gama da mijinta, tou pha Allah ya sawaƙe,


_Wai da anga mace da miji suna zaman lafiya sai ace ta gama dashi, duk macen da ake ganin ta gama da namiji haƙika yana jin daɗinta, tana kyautata mishi tana mishi biyayya tana da haƙuri kuma tana da kauda kai, duk wanda yayi ma mijinsa biyayya ya zama mai haƙuri duk zafin ransa saiya ɗaga ma matarsa ƙafa saiya rage wani abun, duk tijarar namiji duk wulaƙancinsa idan kikaci maganin zama dashi sai ki zauna lafiya,_


Tou pha, bara muji wane irin karatu rabi zatayi ma samha, 


A toilet kuwa Rabi ta nunawa samha wani rober ruwa daban idan ta gama wanka zatayi amfani dashi, sannan kuma wani daban shine zatayi wanka dashi a halin yanzu, tana gama nunawa samha ta fito dan lokacin zuwan hydar ya kusa,


Saida samha ta gama wankan soso da sabulu sannan ta jawo wanda Rabi tace zatayi amfani dashi daga baya, tunda samha ta saka hannunta a bokatin taji ruwan da banbanci da wanda tayi wankan farko dashi, ruwan wani irin sirrin taccen ƙamshi yakeyi mai daɗi da burgewa,


Har samha ta gama ta fito Rabi tana tsaye a wurin, da wani kasko a hannunta samha tana fitowa ta zuwa turaren jiki a ciki tace ma samha anshi koma daga ciki ki turara jikinki,


Bayan samha ta fito Rabi tace muje, a ɗaki bayan sunje samha ta shirya, Rabi ta bata kaya ta saka, saida hydar yayo waya yazo sannan Rabi ta sake turare samha da wani turaren mai ƙamshi gaske,


Sannan ta ɗauko turaruka masu daɗin ƙamshi ta bawa samha ta feshe jikinta dashi sosai, tayi ma samha fatan dawowa lafiya, itadai samha ba dan ranta yaso ba, tunda ta fito taga shamsu tsaye, gasheta yayi ta ansa cikin kulawa sannan ta wuce,


Wurin moter ta nufa tunda hydar ya hangota ya buɗe moter tare da fiddo ƙarfarsa ɗaya har samha ta iso yana kallonta, tana isowa tayi wani ƙerere da ita kamar abun tsiya,


Murmushi hydar yayi tare da cewa inayini, samha tace lafiya qalau, murmushi hydar ya sakeyi tare da jawo hannun samha ya shigar da ita cikin motar,


Raba ƙafafuwansa yayi ya zaunar da samha a tsakiya, rungumeta yayi tare da ɗora kansa saman ƙafaɗarta, kama hannuwanta yayi ya shigar da "yan yatsunta cikin junansu sannan ya ɗaga hannun ta zuwa wurin wuyansa, yace riƙeni kada ki saki, da hannunsa ya ɗago kanta tana kallon fuskar sa, shima duƙar da fuskarshi yayi daidai tata, sannan yace a ina kika samo kamshi haka? Samha ta rumtse bakinta, sannunsa yasa ya kama leɓonta na sama dana ƙasa ya buɗe bakin sannan ya matsa da bakinsa daidai nata ya saka harshensa a ciki yana wasa dashi, tare daci gaba cewa bakiji ina magana ba?


Samha tayi shiru, cire hannunsa yayi daga riƙe lips nata da yayi, ya riƙo haɓarta da hannu ɗaya sosai yana mata wani irin salo mai wahalar fassarawa a bakinta,


Ɗayan hannunsa kuma yana cikin rigarta yaƙi ya ajiyesa wuri ɗaya ɗaya, ringing ɗin da wayan samha takeyi yasa hydar ya saketa, kafin ma ta ɗauka wayar ya tsinke, ƙara riƙota yayi tare da kwantota a jikinsa, leɓonta na ƙasa ya kama da yatsunsa ya buɗe sannan ya ɗan lasa da harshensa, ɗan latsa gefen cikinta yayi tare da shafa wurin samha taji wani tsarrrrrr hydar yace mi kikaci ne?


Cikin dakusashshiyar murya samha tace tuwo naci, ɓata fuska hydar yayi kamar yaga abin ƙanƙami yace tuwo da daddare? Samha tace yo shi kowa yaci, murmushi hydar yayi tare da ƙara yima samha kyakkyawan riƙo a jikinsa, yace waye yake kiranki a waya? Samha tace kausar ne, hydar yace mi zaki mata ne? Saha tace nia ban sani ba, 


Taɓe baki hydar yayi tare da ɗan ɗage girarensa duka ya jinjina kansa alamar gamsu, amma baiyi magana ba, samha dai har yanzun tana kwance a jikinsa, itama bata ƙara cewa komai ba,


Haka sukayi jigum kamar wasu masu zaman ta'aziyya, samha ce ta gaji da zaman tace zan tafi, shi hydar ma ya mata da a moter suke dan har ya fara bacci daga zaune,


Ɗan gajeran tsaki hydar yayi sannan ya saki samha daga jikinsa yace muje kada ma ayi tunanin na tafi dake wani wuri, fita samha tayi sannan shima hydar ya fito,


Saida ya rakata har bakin ƙofa, da sauri zata shige hydar ya riƙo hannunta tare da cewa sunbaceni mana, samha tace kai kada wani ya ganmu, tana maganar tana zaro ido kamar wanda dambu ya shaƙe, hydar yace to a ganmu mana sai mi, yimin mana, murmushi samha tayi sannan tace to matso saika sake min hannu, murmushi hydar yayi dan yasan tana so ta gudune, sakin hannun yayi samha tayi ciki da sauri ba tare da tayi abinda hydar yace ba,


Murmushi hydar yayi sannan ya juyo, saida yazo inda shamsu yake zaune ba tare daya kalli wurin ba yace muje, tashi shamsu yayi da sauri kafin ya isa har hydar ya shiga moter shima yana zuwa ya shiga yaja suka ɓace da wirin,



*_Jαmila Musα ce_*

[05/04 4:46 pm] Washa: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊



                 *SO*

     *MUGUN WASA*



       *{ Love is a bad game }*




*JAMEELA MUSA* { meelat musa }




*Story, Writing & Editing*

                   *by*

         *Meelat Musa*


*_Marubuta! Marubuta!! Marubuta!!!, Yake "yar uwata marubuciya, kisa natsuwa, kisa hankali, kisa tunani, kisa Allah a cikin lamuranki, ki zuba ido da kyau kiyi karatun ta natsu ki duba abinda yake tafiya yana dawo a duniya, rubuta alkairi ki yaɗashi domin ya zamar miki alkairi a rayuwarki, rubuta abinda kika san zai amfani al'umma, rubuta rayuwar da muke kai a yanzun ki rubuta abinda zai amfani al'umma ko bayan bakya raye, ki rubuta abinda zai ƙara miki martaba da daraja a idon mutane, yake "yar uwata, zaki iya faɗamin adadin yawan mutane da suke a social media? Zaki iya faɗamin adadin yawan mutanen da suke karanta novel naki? Zaki iya faɗa min writers nawa ne a online?  Kafin ki fara rubutu ko ni na fara anyi wasu sun rubuta nasu zamanin ya wuce, kada kice min sun mutu a, a, suna raye, kuma suna gani, to haka rayuwa take a lokacin da kike rubutu a lokacin hankalin masu karatu da natsuwarsu duka ya tattara a kanki, a lokacin kece ake ihunki a social media, littafinki ake bada labarinsa, kowa zaiyi ƙoƙarin ya sameshi, idan kina rubutu mai natsuwa babu batsa a ciki babu wanda zaibi ta kanki dan baki iya faɗar abinda zaisa mutum yaji yana sha'awar karatun novel naki ba, idan kika buɗe tsagwaron iskanci da tashanci yanzun nan kin zama super star lokacin naki ne, zaki samu fans sosai kullum kina hawa online da sabuwar number da zata miki magana, nice wancen wancen daga gari kaza na karanta novel naki yamin daɗi dakel na samu number naki ina sanki ni mai ƙaunarki ce, Allah ya ƙara basira ubangiji ya ƙara hazaƙa, ke kuma ana hura miki kai kinajin kinkai babba an samu number naki daƙel, kinsan abinda yasa kika zama masoyiyarta ne? Hmmm ki saki mutum ki kama Allah kada ki kuskura ruɗin duniya da barazanar zamani yasa ki faɗawa a cikin fushin ubangiji, ki rubuta abinda kika san zai amfani al'umma zai kuma amfani rayuwarsu, rubutu ne dai kin rubuta bazai gogewa ba har abadan duniya yana nan a cikin wayoyin al'umma, idan babu a wayarki a akwai a wayar ɗan uwanki ko yayanki ƙaninki ko wani daga cikin danginki, zaku iya tuno adadin marubutun da sukayi rubutu amma yanzun babu maganarsu a online, sun gama amfani ga madu karatun sun rubuta su kuma sun karance, kin gama baki da sauran amfani a wurinsu sai wata da take yayi ita zasu kama, kai ya kamata musan abinda muke, yau ana yayin real mai dambu, kawata kinga real mai dambu ta fara rubuta sabon novel nida yaya muh'd gaba ɗaya a lokacin mutane suna kan mai danbu ne, tana gamawa gobe kuma sai Asmeenat xeeyan, kai kawata nemi littafin namiji Asmeenat Zeeyan ta iya rubuta novel kaza kaza, daga nan saiki tashi k fara nema kinga nan an baro mai dambu, Asmee tana gamawa jibi kuma sai a nemi leema, wayyo Halimatu leema ta fara rubuta Ƙuruciyar jummai, hankalin masu karatu ya koma wurin leema an baro mai dambu da Asmee, gata kuma sai surayya, ta fara rubuta novel mai suna Anfa, wata rana kuma ummu affan, tana rubuta makoma, sai zamani ya juya ya dawo kan jamila musa, kai ƙawata meelat musa tazo da zafinta ai kinsan ta ƙware wurin iya sarrafa littafi to ta sake dawowa da ƙarfinta yanzun ta fara sabon novel nata mai taken so mugun wasa,shikenan sai hankalin kowa ya dawo kaine saboda an wasa littafi na, sai ta fara nema, tana nemansa yanda ta damu wata na ganin tana cigiyarsa sai ta fara ya haɗu, Eh ya haɗu sosai to don Allah idan kin samo nima ina so, to yake "yar uwata ya kamata musan abinda mukeyi mu rubuta abinda mukasan zamu iya faɗarshi mu kuma mai maitashi a gaban kowa, dan nayi imani da Allah wata abinda take rubutawa aka tsareta cikin ɗunɓin mutane ta faɗa wallahi bazata iya maimaitashi ba, to yake "yar uwata dani dake da su duk muji tsoron Allah muyi amfani da dama mai kyau kafin rubutun online ya direki kamar yanda ya dire su Oh Oh da Oh Oh, kada kiga fans suna binki suna ƙauanarki da zamaninki ya wuce wallahi ajiyeki zasuyi su kama wata, kyautata mu'amularki da kowa, zamo mai haƙuri zama mai bada shawara ta kwarai yanda ko bayan rayuwarki al'umma zasuyi alfahari dake, Allah yasa mu dace, Jαmilα Musα ce 4rom BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION nake ma kowa da kowa fatan Alkairi ubangiji yasa mu dace Allah yasa mufi ƙarfin zukatanmu Allah ubangiji ya bamu rayuwa mai albarka da amfani Allah ubangiji ya jiƙan iyayenmu da kakanninmu da dukkan musulmi baki ɗaya wanda suka rigamu gidan gaskiya Allah ya jiƙansu, marasa lafiya na gida dana asibiti ubangiji ya basu lafiya, mu da muke da lafiya Allah ya ƙara mana lafiya yasa mu gama da duniya lafiya, idan ajalinmu yazo ubangiji yasa mu cika da kyau da imani, Allah yasa mu dace duniya da lahira Am33n_*


*_Don Allah masu numberna kuyi haƙuri ku daina adding ina a groups wallahi group chat yamin yawa, idan kuma na fita sai kuce na fita to don Allah ku daina sakani bare in fita har kuji babu daɗi, bana so, bana so, bana so, don Allah ku daina sakani,_*



                  *SO*

      *MUGUN WASA*


*_Dedicated to_*👇🏻

_Ramlat Abdulrahman real mai dambu_



*71-73*



A sikwane samha ta shiga cikin gida, a lokacin har Rabi tayi bacci, 


A gajiye samha ta isa ɗakin Rabi, da sallama ta shiga, babu mai amsawa saboda babu wanda idonsa yake biyu,


A hankali samha ta tsallake Rabi dake kwance ƙasa a kan hanya, ta wuce saman gado ta hau ta kwanta,


Samha saida ta kwanta sannan ta miƙa hannunta ta bayanta ta jawo fillow ta ɗora kanta sama,


Tar abinda ya faru tsakaninta da hydar ya fara dowa mata gall a cikin kwakwalwar ƙoƙon kanta,


Murmushi samha tayi tare da rufe idanuwanta alamar jin kunya kamar tana gaban hydar,


Ajiyar zuciya samha tayi tare da gyara kwanciyarta ta rumtse idonta ƙam tana jiran zuwan bacci,


Hydar kuwa tunda ya taho ransa yana wurin samha, zuciyarsa da tunaninsa duk suna cikin mararinta, gangar jikinsa kuma tana matsananinci maraicin jikin samha,


Wannan dare hydar yaji baƙin ciki da bai kasance a makwanci ɗaya da samha ba, saidai yayi tsoki ya juya, yaso ace samha tana maƙale a jikinsa amma dan iskanci an wani kama yarinya an riƙe wai dangi zasu ganta mtswwww,


Ganin bacci bazai zo ba yasa hydar ya haƙura ya sauko dan fara ibadarsa, dan yaso yaɗanyi bacci zuwa lokacin da yake tashi amma hakan ya fassakara,


A ɓangaren samha kuwa wannan rana bacci kaɗan taɗanyi dan tunaninta gaba ɗaya ya tafi a wurin hydar ne,


Ko da safe samha suku suku takeyi, gaba ɗaya wata natsuwa tazo mata wanda itama kanta bata san dalilin ta ba na hakan, bayan sun gama abinda sukeyi ne suka raɓe ita da Rabi a ɗaki,


Rabi zaune a gefen gado, samha kuma tana kwance, Rabi tace samha  kin kira hydar kun gaisa? Turo baki samha tayi ba tare da tace komai ba,


Rabi tace magana nake miki amma kin wani basar dani, samha tace ni ban wani kirasa ba, ai shine ya kamata ya kirani yace min ya nake? 


Rabi tace ke yarinya zo a faɗa miki, kina ƙarƙashin mijinki? Kece a ƙasansa ke ya kamata ki bishi ba shine zai biki ba, 


Ɗauki waya maza ki kira mijinki ki gaisheshi, samha tace gaskiya bazan kirasa ba idan ina damuwa dashi ai sai ya rainani,


Idanuwa Rabi ta zaro tare da cewa mijinkin ne zai rainaki? Shi baice zaki raina sa ba sai ke? Kanta ta jinjina tare da cewa lallai yarinya kinzo da ruɗu fa,


Anya ma kina biyayya wa mijinki samha? Biyayya kuma? Inji samha, Rabi tace Eh, samha tace haba ai mazan yanzu dasu da matayensu "ya"yan agwagwi ne, basu bin uwarsu saida uwarsu ta bisu,


Rabi tace yanzun kina nufi ke bazaki bi mijinki ba saidai shi ya biki kenan ko? Samha tayi shiru, Rabi tace to ki kiyayi kanki da jiran namiji ya biki alhalin ke baki bisa ba,


Kin ganni nan a gidan nan kullum cikin tsangwama da jarabar kishin sauri nake sha, da gore gore, amma duk na kanne na manta da lamarin banzanye,


Samha kin ganni nan da kika ganni ni banda baba haka nan na faɗo a duniya nazo a matsayin ɗiyar gaba da fatiha, idanusa samha ta zaro tana kallon Rabi tare da mata kallon taɓaɓɓiya dan haɗuwarsu baikai ta faɗa mata hakan ba, kuma ko sun shaƙu sosai saida taji a wani wuri amma ba'a bakinta ba,


Murmushi Rabi tayi tare da cewa kina ganin kamar na haukace ko? Samha tayi shiri, Rabi tace samha nasan kona faɗa miki ko ban faɗa miki ba dole sai kinji an faɗa miki ni banda baba a duniya, za'a nufoni da kalamai mafi muni a wurinki don a aibatani bayan nasan ni bani nayi kaina ba,


Samha mahaifiyata ta shiga ruɗin duniya da biyewa san zuciya, wannan dalili yasa ta dilmiya kanta a harkar bariki bata samu natsuwa da kwanciyar hankali ba saida ta aifoni,


Samha mahaifiya ta kasance tantiriyar "yar tasha, ta kware kuma ta shahara wurin iya bariki, haka ta kware wurin bin malamai da sirkulle da biye ma canfefe malamai da bokaye,


Yanda labarin mahaifiyata yazo min samha, mahaifiyata ita balbela ne bata bin mai kare saima shanu, abinda nufi anan ita bata bin talaka sai masu kuɗi,


Lokacin data dulmiya kanta a harkar bari kanci mahaifiyarta tayi juyin duniya amma taƙi saurarenta, dalilin faɗawarta bariki kuwa shine,


A kawai wani matashin saurayi a lokacin baya da suka shuɗe, yana san mamana kamar ya mutu, amma mama a lokacin idonta ya rufe da tsabar tsagwaran san abun duniya,.


Duk wata hidima a lokacin shine yakeyi ma mamana, mama bata da aiki sai yaudare maza tare da kwakwale duk wani abu da suka ajiye a cikin aljihunsa,


Bayan mama ta gama yaudare shi ta gama dashi ta nuna masa bata sansa, kuma bazata aureshi, wannan dalilin ne yasashi yayi fushin zuciya tare da ɗaukar alƙawali saiya saka mamana cikin baƙin ci kamar yanda tasashi a baƙin ciki a rayuwarsa,


Ganin mama tana da san kuɗi yasan kuma yasan ita alashe money ce, to da wannan damar yayi amfani yaje ya turo maza masu ji da kansu haka ya ware zunzurutun kuɗaɗe ya basu dan kawai su ɗirkakawa mamana ciki,


To tunda ta fara harkar barinkancin ta mamanta tayi mata faɗa ta nuna mata ta daina amma sai take ganin kaka bata waye ba, to dama dai ƙarshen taurin kai nadama,


Haka rayuwarta taci gaba da tafiya ƙarshe dai saida aka dirkakawa mama ciki taje ta samoni ga wanda bata san shine babana ba, sannan ta tsugunna gida, ranar data haifeni a ranar ta mutu saboda tsagoron baƙin ciki da damuwa wannan shine dalilin mutuwar mahaifiyata,


Duk abinda zanyi a gidan nan samha sai gori sai wulaƙanci sai cin zarafi, bani da damar yin wanka inyi gayu sai ace ai da yake ni ɗiyar karuwace, 


Mata kuma da yake aure yana saki wannan kuma tsakaninsu dashi ne, nidai samha ina baki shawara don Allah ki rufawa kanki asiri kibi mijinki sau da ƙafa, ki zama mai haƙuri da biyayya,


Idan kika zamo mai ɓatawa mijinki rai kina mishi wulaƙanci da rashin ragowa yau da gobe zaki fita a kansa, nan dai Rabi tayiwa samha nasiha tare da ƙara nuna mata matsayin miji a wurin matarsa,


Bayan dai sun gama firansu Rabi tacewa samha taje tayi wanka fita zasuyi, tashi samha tayi taje tasha wankanta,


Bayan ta fito ta zuge cikin riga da zani na atamfa, itama Rabi ta shirya bayan ta gama shirinta tace ma samha muje,


Tashi samha tayi ta saka hijabinta, suka fito, suna fitowa tsakar gida suka fara, samha kada ki kuskura a koya miki bari kanci a koya miki kwartanci nan da kika ganta shegiya ce, sannan kuma tana da aure take karuwanci,


Murmushi Rabi tayi tare da cewa to samha taji kuma zamu fita ne sai mun dawo, samha kallon Rabi tayi cikin yanayin tausayawa, anyi mata wulaƙanci amma ta kasa ɗaukar hukunci,


Rabi taja hannun samha tare da cewa muje rana yanayi, fita sukayi daga gidan, su kuma matan gidan sukaci gaba da zagin Rabi tare da ci gaba ɗaɗɗake mata albarka,


Yinin ranar haka Rabi ta yini tana yawo da samha tana kaita gidajen "yan uwa kamar dai yanda mijinta yace mata, sai yamma liss suka dawo gida, a gajiye suka shigo gidan gaba ɗayansu,


Kai tsaye ɗaki suka wuce anan suka baje suna hutawa, tare da ɗan maida yanda akayi, wayar samha dake ta ihu tana neman a bata a gaji samha ta juya tare da miƙa hannunta ta jawo wayarta,


Sunan Yusra ne ya bayyana a screen in wayan samha, murmushi tayi bayan ta ɗauka wayar ta kara a kunnenta tare da cewa Assalamu Alaikum,


Yusra tace haba hajiyata tun jiya muna ta kiranki amma baki ɗauka ba, samha tace wallahi kuwa na ga kiran kausar kuma ban kira ba kuyi hakuri, yusra tace ba komai ya kike ya gida?


Samha tace lafiya qalau, Yusra tace dama na kiraki ne mu gaisa, samha tace Allah sarki aiko nagode sosai, yusra tace yawwa ngd sosai ki huta lafiya, samha tace yawwa ngd ta kashe wayanta,


Bayan sun gama wayarne Rabi tace ki kirawo hydar samha, murmushi samha tayi ba tare da tayi magana ba ta fara neman number hydar,


Babu daɗewa ya ɗauka, tare da cewa sannu samha sai yanzun kika tunani? Dama saka ido nayi inga zaki nemeni? Samha tace to ai gashi na nemeka, murmushi hydar yayi tare da cewa inzo ne? Samha tace Eh, hydar yace gani zanzo bada daɗewa ba, samha tace tom, sannan ta kashe wayarta,


Bayan ta gama wayarne ta faɗawa Rabi hydar zaizo, Rabi tace to tashi maza kije kiyi wanka bara in kai miki ruwa, a ɗan hanzarce rabi ta miƙe ta nufi wurin da suke ajiye tarkacen ruwansu, ta haɗa ruwan wanka takai toilet,


Tun kafin samha ta fito wanka hydar yake kiran waya, rabi dai bata ɗauka har samha ta fito,


Da sallama ta shiga cikin ɗakin, rabi tace yawwa ga mijinki yana kiranki kila yazo, samha ta matsa ta ɗauki wayar a lokacin harta tsinke, dan haka ta fara kiran wayar shi,


Bayan ya ɗauka yace ina kika ɓoye ne? Samha tace babu ko ina, hydar yace to fito nazo fa tun ɗazu, samha tace dama da mukayi waya dakai ka kusa zuwa ko? Yace Ey dama zowa zanyi in ganki, samha tace to gani nan fitowa, yawwa a fito lafiya, samha tace tam tare da kashe wayanta,


A ɗan gaggauce samha ta shirya dan Rabi sai azalzalarta takeyi sai cewa takeyi tayi sauri, tana gama shirinta ta saka hijabi tayi gaba,


A motar ta samu hydar kuma shi ɗayane baizo da kowa ba dan shine ya tuƙo kansa, dan haka samha tana zuwa ta saitin hydar ta zagaya shi kuma yana ganin tazo ta wurinsa ya sauke glass tare da cewa ki zagayo ki shigo mana,


Dan juyawa samha tayi taba hydar baya tare da cewa nifa bazan wani shigo ba, hydar yace miyasa? Samha tace saboda sauri nakeyi inje in huta dan na gaji sosai,


Gyara zama hydar yayi tare da ɗan kwantar da kansa saman sitiyarin motar yace to muje gida in miki tausa { masach } samha tace sai muje gida kuma mu dawo? Hydar yace Ey mana kedai shigo kawai tawa,


Murmushi samha tayi tare da zagayowa da sauri ta buɗe motar ta shige, murmushi hydar yayi da gefen bakinsa sannan ya tashi kallon samha yayi amma baiyi magana ba ya fara tafiya da moter,


Samha tace yau nayi waya dasu yusra, hydar yace da gaske? Samha tace wallahi kuwa, hydar yace mi tace miki ne? Samha tace kawai tace ta kirani zamu gaisa ne, jinjina kansa yayi alamar gamsuwa, ba tare da ya sake cewa komai ba,


Hydar yawo yayi tayi da samha ba tare daya nufi gida ba kamar yanda yace, samha tace ka gani dare ya farayi kawai ka mayar dani bana so kuma ace wani abu, hydar yace ai yanzun zamu tafi ki ɗanyi hakuri kawai zan anshi saƙo acan muje,


Haka ya sake ci gaba da shawagi shi bai nufi gida ba kuma bai wani je inda yace zai anshi saƙon ba, samha tace nifa gaskiya na gaji kawai ka mayar dani hydar yace to zan mayar dake muje gida ko? Samha tace wane muje gida kuma bayan kasan dare yayi sosai so kake ace kuma na tafi su gani kamar wani abu?


Hydar yace a gani mana sai miye idan na tafi dake? Fitina ce kawai irin nasu sunce sai kin kwana biyu ni kuma gaskiya bazan iya ba zaman gidan nan yana da hatsari, duk yanda na kyafta miki ido kada ki kwana sai kika wani basar dani kika wani ce ke sai kin kwana bana so in nunaki kamar ba wani komai bace a wurina a gaban mutane wannan dalilin yasa da kikayi magana na hakura amma badan raina yaso ba, dan haka gaskiya bazan mayar dake ba wallahi,


Samha ta hayayyaƙo ma hydar ciki masifa tace wannan ai babban wulaƙanci ne in banda iskanc......... burki hydar ya taka ƙuwuuuu,cikin tsananin ɓacin rai ya taɗaga hannunsa ya kwararawa samha wani irin firgitaccen mari maisa mutum ya fitar da ɗan autan fitsarin wahala,


Cikin yanayin na ɓacin rai  tattare da sigar fushi hydar yace na gaji da iskancinki haka nan ya isheni, dan kinga ina lallaɓaki zaki ɗaukeni kamar wani sakarai, cikin sa'oi 24 ko wace daƙiƙa ina ƙoƙarine inga kinyi bacci cikin natsuwa da kwanciyar hankali,


Duk abinda zaisa ki fushi ko kuka a bayyane ko a baɗinacce ina ƙoƙari ne inga na narkar dashi koma miye, ina ƙoƙarin sakaki farin ciki da baki kulawa a rayuwa amma ke bakya gani, na lura ke babu kunya bare ganin girmana duk kalamin daya zo a bakinki shi zaki faɗamin, duk abinda kika san zaisa nayi fushi neman sa kikeyi ina zaki bi ki ɓatamin rai rashin kunya tare da rashin saita kalamanki akaina, kwafa yayi tare da cewa zanyi maganin rashin kunya tare da kashe  bakin tsiwa, zakisan akwai banbanci tsakanin ni dake, duk ranar kika zo hannuna zaki gane nine nake aurenki bake ce kike aurena ba, yana faɗin haka yaja motar yaci gaba da tafiya samha kuma taci gaba da kuka har yanzun hannunta yana saman kuncinta inda hydar ya mareta,


Har suka isa gida samha kuka takeyi hydar kuwa bai bata hakuri ba, bayan yayi parking ne yayi mata magana cikin tsawa cewa fita kije ki kwashe wannan kayan ki tafi dasu ciki,


Fita tayi jiki sukuku taje ta buɗe but ta kwashe kayanta dayaje mata dasu jiya bata ɗauka ba, simi simi tayi ciki tana shashshekar kuka, bayan samha ta kwashe kayan hydar yaja motar ya bayar gidan,


Samha kuwa a farlo ta ajiye kayan sannan tayi sama da sauri, tana shiga ɗaki da gudu ta isa jikin mirrow tana duba inda hydar ya mareta, tare da ci gaba da shashshekar kuka, lallai ta maru dan wurin sahun hannun hydar ya fita fess a saman kuncinta,


Nan tayi tsaye jikin madubi tana ci gaba da kallon kanta tare da ƙara ɓarkewa da kuka mai yawa, saida ta gaji sannan ta cire hijabin jikinta ta ajiye a gefen gado da guda guda ta cire kayan jikinta tare da ɗaukar towel ta shige toilet, 


Har tayo wanka ta fito kuka takeyi, bayan ta fito mai taɗan shafa sama sama tare da ɗan murza powder, kayan bacci ta saka tare da hayewa gado ta kwanta,


Bata daɗe da kwanciya ba ɗan bacci mai daɗi ya fizgeta, cikin bacci taji ƙugin wayarta, a hankali ta buɗe idonta tare da kai hannunta wurin wayar ta ɗauko, kallon wayar tayi sunan mai gida hydar ya bayyana, ɗan gajeran tsaki samha tayi ba tare data ɗauki wayar ba,


Tsoki hydar yayi tare da gyara kwanciyarsa, riƙon wayarsa ya gyara tare da turawa samha saƙo,


_Kizo_


Bayan samha ta karanta saƙon hydar ta ajiye wayarta, wata zuciya tace mata taje wata zuciya kuma tace kada kije ba ɗazun nan ba ya gama kikkifa miki mari, sai kuma ya wani raina miki hankali cewa kije, 


Tana wannan nazarin taji shigowar wani saƙon, 


_Cewa nayi kizo ba nace ki tashi kiyi nazari ba,_


Da sauri samha ta ɗaga kanta sama tare da kalle kalle ta ko ina, a ranta tace to ya akayi hydar yasan na tashi zaune ne? Shigowar wani saƙon,


_Mi kike kallo ne a sama?_


Da sauri samha ta miƙe tsaye bayan ta gama karanta saƙon hydar, nazari tayi sosai sannan ta fita daga ɗakinta ta nufi ɗakinsa,


Da sallama ta shiga hydar ya ansa ciki ciki, shiga tayi ciki gaba ɗayanta, ta matsa daidai bakin gado sannan ta durƙusa saman guyawunta ta dafa hannunta a kan gadon tace gani,


Ba tare daya kalleta ba, yace hukunci zansa kiyi, kin iya shari'a ne? Cikin girmamawa samha tace ai ban karanci low ba, hydar yace ai ba karatu bane abun, bara in karanta miki kiji yanda karatun yake,


Kallon hydar samha tayi amma batayi magana ba, shima kallonta yayi ba tare dayace komai ba, matsawa baya yayi tare da cewa zoki kwanta a nan ya nuna da hannunsa, a hankali samha ta tashi tahau saman gadon ta zauna a gefen gadon,


Ta baya hydar ya ɗan riƙo samha hannunsa a cikin rigarta, idanuwa samha ta zaro tare da juyawa ta kalli hydar, ɗaure fuska hydar yayi tare da cewa kinajin karatun ko? Samha tayi shiru,


Da hannunsa daya riƙeta ya ɗan kwanto da ita ya kwantar da ita saman gado, samha zatayi magana hydar ya zare mata idanuwa tare da cewa ba nace karatu zan koya miki ba?


Cikin rawar murya samha tace karatu ai a makaranta ake koyawa, hydar yace waye yace miki a makaranta suna koya irin babban darasin da zan koya miki ne? Nine na iya karatun kuma nine zan ci gaba da baki darasi harsai kin iya, kedai riƙe hydar kisha karatu yarinya,


Samha zatayi magana hydar ya ɗora hannusa a saman bakinta tare da cewa shittt, yanda yayi abun ne yasa na lallaɓa na bar ɗakin domin nima kaina wannan karatu na hydar yafi karfin tunanin kwalwata, dan haka naɗan dawo daga ƙofar ɗakin na zauna,


Nikam wannan karatu na samha da hydar bansan yanda ya ƙare ba, ina nan dai zaune najiyo kukan samha, sai kuka takeyi tana ƙarawa, tashi nayi na koma ɗakin, hydar dai baiyi magana ba, tashi yayi ya nufi toilet samha tana kwance sai kuka takeyi hannunta a saman ido tana goge hawaye,


Har hydar ya fito samha bata daina kuka ba, rigar wanka ce a jikinsa hannunsa da ƙaramin towel yana goge kansa, ganin samha tana kuka yasa ya matsa bakin gadon ya duƙa, idon samha rufe yake, ruwan dake cikin gashin kansa ne ya riƙa ɗigar mata a fuska, da sauri ta buɗe idonta, murmushin ƙeta hydar yayi tare da cewa ya kikaji darasin yau? Samha ta sake rufe idonta ba tare data ce komai ba,


Hydar yace akwai idan baki gane ba? Juyawa samha tayi ta bashi baya, zama yayi tare da juyota tana fuskantarsa, fuuuuu samha ta kwace jikinta daga jikin hydar ta sauko daga saman gadon tayo waje,


Dariya hydar yayi tare dabin bayan samha da kallo harta fita daga ɗakin tana gunguni, dariya hydar yayi sosai tare da taɓa hannunsa yayi wata "yar rawa ta rashin kunya, da sauri ya yaye zanin gadon tare da canja wani, yana gamawa yayi kundunbala saman gado tare da cewa bacci mai daɗi, yana hayewa saman gadon ya rufe idonsa tare da jan bargo ya lulluɓe,


Samha kuwa tana zuwa ɗaki toilet ta shiga, tayo wankan tsarki, bayan ta fito tayi tsugunne a gaban gaɗo ta ɗora kanta saman gadon tana ci gaba da kuka,


Shi kuwa hydar yau ranar tasa ce, baccinsa yakeyi hankalinsa a kwance kamar yahau jirgi mai ya ƙare,


Samha kuwa tasha kukanta ta gaji ta haƙura tahau saman gado tayi kwanciyarta, lallai yau hydar yakai baban mai mugunta a wurin samha,


Koda safe samha bata fito parlour ba, dan bata san ta haɗa ido da hydar, shi kuma yana gama abinda zaiyi yayi wankansa ya kama gabansa,


Saida samha ta tabbatar hydar yabar gidan sannan ta fito, tayi dan abinda zatayi ta gyara gida sannan ta ɗora girki, saida ta gama abinci sannan ta zuba a food flasks taje ta ajiye a tebirin cin abinci,


Saida ta gama komai sannan ta koma ɗaki tayi wanka bayan ta gama shirinta ta fito taci abinci, tana nan zaune hydar ya shigo, ko inda yake bata kalla ba kuma batayi mishi magana ba,


Shima bai kalli inda take ba ya wuce abinsa, yaje yayo wanka ya shiryo sannan yazo yaci abinci, harya gama cin abinci sa babu wanda yayi ma wani magana,


Miƙewa samha tayi zata bar farlon, hydar yace idan kin gama zuciyar anjima akwai karatu, samha batayi magana ba ta wuce, ɗaga murya hydar yayi cewa ai dama haka akeyi tsakanin malami da dalibi, yayi duka wa dalibi gobe ma ya ƙara bashi karatu,


Murmushi hydar yayi tare da cewa waike? Waike dani zaki zuciya ko? Gyara zamansa yayi tare da cewa ga banza anma jaki wanka, Allah ya kaimu anjimar lafiya,


Ita kuwa samha tana zuwa ɗaki rufe ƙofarta tayi da makulli tare da cewa aisai inga ta inda zaka bi ka shigo, 


Haka dai rayuwar samha taci gaba da tafiya dan tundaga wannan ranar samha bata yadda sun sake haɗuwa da hydar ba, zadai ta fito tayi girki ta gyara ko ina da ina, data daidaici dawowarsa zata gudu ta kulle ƙofa, babu gaisuwa ba komai, 


Shima ya tattarata ya zubar da lamarinta ya ci gaba da huɗɗoɗin gabansa, 


Yau kusan kwana biyar kenan duk sanda samha ta ajiye abinci a tebirin cin abinci haka take zuwa ta samu, ba'a taɓashi kwata kwata, wannan abu ya dameta,


Yauma ta ajiye mishi kalacin safe ba'a taɓa ba, haka na rana shima ba'a taɓa ba, gana dare shima, duk ya taddasu, buɗewa samha tayi ta duba haka nan taji babu daɗi a ranta,


Rufewa tayi tare da saukowa daga wurin tazo ta zauna saman kujera tana jiran dawowar hydar,


Har 12:09am babu hydar ba labarinsa, jiki a sanyaye samha ta tashi ta nufi ɗakin hydar koya shigo ta baya, nan ma babu hydar ba labarinsa, tashin hankali kenan, da sauri ta fito ta koma ɗakinta ta ɗauki wayarta ta fara kiran wayarsa, amma dai zance ɗayane a kashe,


Haka tayi ta gwada wayar hydar amma a kashe, daren nan samha ta kasa bacci, tana tunanin kiran kaka amma idan ta kirata bata san yanda zatace mata ba dan haka dole ta haƙura da kiran kaka, haka samha tayi ta safa da marwa tsakanin ɗakinta ɗakin hydar parlour,


Kallon agogo tayi taga 12:45am, tunanin fita takeyi amma kukan karnuka ya hanata, ta kasa tsaye ta kasa zaune, Allah dai yasa lafiya innalillahi wa'inna"ilaihir raji"un, to mi tayi ma hydar wanda yasa yayi yaji haka? Idan yayi tafiya ma ai ya faɗa mata, ko bashi da lafiya yana asibiti ne? Kuka samha ta farayi tare da ayyano abubuwa da dama a ranta,


Ƙara kiran wayar hydar tayi taji ta shiga, ajiyar zuciya tayi tare da goge hawayen idonta da bayan hannunta jikinta har kyarma yakeyi taji hydar yayi magana amma bai ɗauki waya ba harta tsinke,


Saƙo ta tura mishi cewa kana ina ne? Ina meeting ya rubuto a taƙaice, samha ta tura meeting da daddare haka hydar? Ya rubuto cewe, Eh wannan lokacin na wanda matansu basa sansu ne duk wanda matarsa bata kwana ɗaki ɗaya dashi sai yaje meeting irin wannan lokacin dan ɗebe kewa tare da rage dare,


Samha ta rubuta kayi haƙuri wallahi na kasa bacci tun dazu ina jiranka, murmushi hydar yayi tare da rubutawa, zaki zo ɗaukar darasi ne? Dan kinsan malami bayasan gani daliba a gabansa ba tare daya bata karatu ba,


Samha ta rubuta A, a, kawai dai naga na daina ganinka ne, hydar ya rubuto, ai duk dalibin da kika ga ya nemi malami haƙiƙa yana neman ilimi, ko a class idan kikaga moniter ta kirawo malami ta kirasa ne dan ya koyar da ita, dan haka kema kina san ɗaukar karatu shi yasa kike neman hydar, kina san hydar ya koyar dake darasi mai wahalar karatu, tunda har kin kwana da yawa baki ganni ba gashi nan kina nema na, gani nan zuwa dan ina ganin yau karantun namu zai kai safe,


Da samha ta gama karatantawa ajiyar zuciya tayi, dan ita ta kasa gane wane karatu ne hydar yake magana, tana nan zaune tana nazari tajiyo maganar hydar daga sama yana cewa taso,


Tashi samha tayi ta nufi inda hydar yake tsaye, tana zuwa ta fara cewa mi yasa ka daina cin abinci idan na dafa? Jan hannunta yayi ba tare daya bata amsa ba, samha taci gaba da cewa kuma wane irin meeting kakeyi a daren nan ne? 


Hydar yace na marasa galihu ne, da marasa aure, samha tace kai ba gani ba? Hydar yace da kike nan wani abu kike iya tsinanawa? Samha tace ba ina girka maka abinci ba, hydar yace ance miki abinci kaɗai nake da buƙata? A daidai lokacin da suka shiga ɗakinsa,


Samha tace to dami dami kake so wanda kake ganin ni bazan iya ba? Jawota yayi zuwa cikin jikinsa, ya rungumeta tare da lumshe idanuwansa ya ɗaga kansa sama har yanzun idonsa a rufe, ya fara cewa da farko dai, idan zan fita babu Allah yasa in dawo lafiya, bare idan na dawo insa ran zaki min sannu da zuwa,


Samha tace to kayi haƙuri insha Allah na daina daga yau, hydar yace kinsan laifinki na gaba? Samha tace A, a, sauko kansa yayi ya kalli samha tare da cewa muje mu kwanta, 


Jan hannunta yayi suka matsa bakin gado,  zaunar da ita yayi a gefen gado sannan shima ya zauna yace kinayin karatu yau? Samha tace wai wane irin karatu? Hydar yace kedai kawai kice kina so, samha tayi shiru murmushi hydar yayi tare da kwanciya ya jawo samha zuwa saman jikinsa ya kwantar da ita, samha tace baka faɗa min laifina na gaba ba, hydar yace rashin ɗaukar karatu na ya ƙarasa maganar yana kashe ma samha ido ɗaya,


Ajiyar zuciya samha tayi tare da ƙara kwantar da kanta sama jikin hydar, murmushi hydar yayi tare da miƙa hannunsa ya jawo bargo ya lulluɓesu dan gabatar da karatun dare, 


Lallai darasin hydar babba ne, dan karatu mai girma yake koyawa samha, wani tana ɗauka wani kuma yafi ƙarfin kwalwarta bare kanta ya ɗauka, wani tana ƙoƙarin ansa, wani kuma baya karantuwa bare ta biyashi, samha fa ta yadda hydar shine ector itace boss, dan karatun ba iri ɗaya bane, ector dai ya kashe boss,


Saida hydar ya tabbatar samha ta ibi darasi sosai sannan ya barta dan kwalwarta ta huta, nima bari inbar tawa ta huta tun kafin kan nawa ya fara aman wuta dan tunda rana ya fara fitar da hayaƙi, kuma masu karatu ku bar naku ya huta,




*_Jαmilα Musα ce_*


💅🏻

[05/04 4:46 pm] Washa: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊



                 *SO*

     *MUGUN WASA*



       *{ Love is a bad game }*




*JAMEELA MUSA* { meelat musa }




*Story, Writing & Editing*

                   *by*

         *Meelat Musa*


*_Ina baku haƙuri don Allah naji na shiru kwana biyu wallahi abubuwane sun shamin kai da yawa da yawa, to ina dai baku haƙuri do Allah, masu turamin saƙo duk na gode sosai masu kirana ma kuma duk na gode domin fatan alkairi kukemin na gode sosai wallahi, insha Allah zaku ci gaba da jina, ina ma kowa fatan alkairi ina gaisheku a cikin wannan rana mai albarka, alkairan dake cikin wannan rana ubangiji ya sadamu dashi, sharrin dake ciki ubangiji ya nisantamu dashi ya tsare kullihin musulmi ubangiji ya sadamu da alkairi duniya wa lahira,_*


*_Duniya makaranta: Idan kaga mutane basa nemanka sai lokacin da amfanin ka yazo, to kada ka damu kawai kayi murmushi saboda ka zame musu fitilane ida sun shiga duhu, al'amurran rayuwa sun rikice musu sai a gaggauta nemanka, abokin ka na kwarai shine mai faɗa maka gaskiya, ba mai lulluɓe maka ita ba, don kada ku ɓata, ya ubangiji ka barmu da masu sanmu da gaskiya, ina muku fatan alkairi ni jamila musa nake cewa Allah yasa muyi juma'a, lafiya_*



                  *SO*

      *MUGUN WASA*


*_Dedicated 2_* 👇🏻

_Real mai damburabos_



*74-76*



Saida hydar ya tabbatar samha ta ibi karatu sosai sannan ya barta dan idan karatu yayi yawa tun kana fahimta zaka dawo baka gane komai,


Bayan hydar ya gama dirkakawa samha babban darasin da yake koyar da ita ta fara ƙoƙarin sauka daga saman gadon,


Riƙeta hydar yayi tare da cewa ina zakije ne? Samha tace zanje ɗaki ne, tsareta yayi da idanuwansa masu tada mata hankali, wanda take siffantasu da kamar an bashi sadaka,


Ɗauke kanta tayi a gefe, ba tare datayi magana ba, hydar yace anjima idan Allah ya kaimu zaki gane inda muka tsaya ko? Samha tace ya za'ayi in fahimta tunda ba'a littafi kake rubutawa ba?


Hydar yace ai inda nake rubuta saƙon yafi inda kike tunanin a rubutashi, nan dana rubuta nasan zan samu maki mai girma, idan babban result ɗin ya fito kema zakiyi alfahari dashi daga ranar zaki tabbatar hydar yakai babban malami, 


Tashi samha tayi ba tare data sake kallon hydar ba, ta fara tafiya abunta, murmushi hydar yayi a daidai lokacin da yake saukowa daga saman gado yace dalibata saida safe, 


Yi tayi kamar bataji abinda yace ba tayi waje, murmushi hydar yayi tare da shigewa toilet,


Samha tana shigowa ɗaki toilet ta shige dan tsarkake jikinta, bayan ta fito ta lallaɓa ta zuge ƙanta cikin kayan bacci, a sikwane ta lallaɓa ta haye gado abunta,


Bayan ta kwanta ne ta lulluɓe kanta da bargo, tashin farko murmushi ta farayi ko tunanin mi tayi? Oho ta dai gyara kwanciya tare cewa hydar kenan, wai shine malami wannan shine darasin? Result ɗin kuma yana nufin idan nayi ciki? Farin cikin da zanfi shi yinsa shine na aihuwa,


Uhum lallai hydar karatun nasa mai girma ne, ajiyar zuciya samha tayi tare da lumshe idanuwanta, ta fara yin bacci,


        ""Tunda samha ta kwanta babu wani isashshen juyi data yi bare ta farka wani fitsarin dare, dan gaba ɗaya jikinta ciwo yake mata dan saida hydar yayi mata jijjigar futar hayyaci ya barta,


Da safe kuwa tunda samha tayi sallah asuba ta koma bacci, shi kuma hydar daga masallaci gidan kaka ya nufa domin yi mata bankwana zaije *_Solvenia_* 


A gidan kaka kuwa hydar yace ma kaka da samha zai tafi, amma ta murza ma idanuwanta kwalli tace wallahi bazaije da ita ba, hydar yace miyasa? Kaka tace kana ganin ba wani sanka takeyi ba kaje da ita tafiya tun yanzu kana buɗe mata idanuwa wata rana zata maka ɓacewar malƙiya,


      Ajiyar zuciya hydar yayi tare da kai hannunsa da sauri saitin zuciyarsa, ya dafe, kallon kaka yayi tare da cewa A, a, bana tunanin samha zata tafi kwata kwata,


   """Kaka tace to kaje ka tafi da ita, duk abinda ya faru kada ka nemini na faɗa maka!,


Murmushi hydar yayi tare da sauke gajiyayyen numfashi, ya jingina bayansa da kujera, kansa ya ɗaga sama tare da lumshe kyawawan idanuwansa,


Hannunsa yakai a aljihunsa, ya lalubo wayarsa, saida ya fiddo ta daga aljihunsa sannan ya sauko kansa yana kallon wayar, number samha ya fara nema,


Haka yayi ta ringing ya ƙare samha bata ɗauka ba, murmushi hydar yayi tare da bin wayar da kallo, a ransa kuwa cewa yayi samha kina ji da rainin hankali,


             """Miƙewa yayi yana cewa na wuce, kaka tace yaushe zaka dawo ne? Hydar yace inajin zanyi wata biyu, kaka tace Allah ya tsare, hydar yace amin a daidai lokacin da yake ficewa daga bedroom,


A ɗan hanzarce ya fito ya nufi inda ya ajiye moter sa, harya shiga yana ci gaba da kiran wayar samha, amma samha tana ji tana gani hydar yana kiranta amma ta basar dashi,


Kwafa hydar yayi ya ajiye wayarsa a gefe ya maida hankalinsa wurin driving, harya isa gida hydar yanajin baƙin cikin rashin ɗaukan wayar da samha tayi tasa,


Saida yayi parking sannan yaji wani baƙin ciki yazo ya tokare mishi ƙirji, duk matan abokansa ba haka sukeyi ba, kowa yana san kowa sakamakon shi, shidai kaɗai yake san samha amma ita bata sansa,


A hankali hydar ya zuro ƙafarsa ya fito da ita daga cikin moter, a hankali ya fita ya rufe moter zuciyarsa tana ayyana masa abubuwa da dama, wata zuciyar tana cewa ya kama samha yayi mata dukan rabani da yaro,


Wata zuciyar kuma tace sauƙi hydar fita harkarta, haka dai ya nufo farlo da tunani barkatai a zuciyarsa, bai ƙara jin haushi ba saida ya shigo parlo yaga samha zaune a saman kujera da wayarta a hannunta tana latse latse,


Saida yazo ta kusa da ita sannan yace ke dan tsabagen iskanci baki ga ina kiranki ba? Turo baki tayi tare da ɗaga girarenta tare da girgiza ƙafarta taci gaba da murza wayarta ba tare datayi magana ba, tana  irin dai yanayin nan na mutum yanajin iskanci,


Hydar yace bakiji ne? Har yanzun hankalinta yana kan wayarta tana murza abinta, tayi mata kyakkyawan riƙo hannu bibbiyu, fizge wayar hydar daga hannunta ya kwaɗata da ƙasa, har yanzun bata kalli hydar ba bare yasa ran zatayi magana,


Sun ɗan ɗauki lokaci a hanka, hydar yana tsaye samha kuwa tana zaune, murmushi tayi tare da saukowa daga saman kujera ta matsa inda wayar ta take ta tsugunna ta fara tattarata,


Ɗaga kafarshi yayi ya taka hannun samha da ƙarfi saida hannun yayi ƙat, hummmm kuka, ta durƙusa a wurin sai kuka takeyi, duƙawa hydar yayi tare da riƙo rigarta ta baya ya ɗagota,


Sai ɓata fuska samha takeyi tana kuka, ansar wayar yayi daga hannunta, yana ansa yayi gaba abinshi, binshi tayi da kallo saida ta daina hangoshi sannan ta maida dubanta ga hannunta dake fitar da zufar wahala,


A hankali taja jikinta zuwa saman kujera ta zauna, ta ƙara rungume hannun sai wani riritashi takeyi kamar an tsamo jariri daga cikin ruwan zafi,


Hydar kuwa yana zuwa ɗakinsa, wanka yayi bayan ya fito ya shirya cikin shiga ta kamala da mutunchi, bayan ya gama ya tattara ɗan abinda zai ɗauka, biro da takarda ya ɗauka yayi rubutu a jiki, bayan ya gama ya sauko ƙasa har yanzun samha tana zaune tana kuka,


Saida yazo daidai samha sannan ya nannaɗe takarda tare da cewa ansa, ki tattara duk abinda kika san yana da alaka dake yanzun nan ki kama gabanki, 


Wani dabur dabur samha tayi lokaci ɗaya kuma idonta ya kawo hawaye, cikin sansanyar murya mai tattare da sigar lallashi tace ban gane ba, taɓe baki hydar yayi cewa ganewar da bayanin duk yana cikin takardar nan, yi sauri dan zanyi tafiya,


Zatayi magana hydar ya ɗaga mata hannu, tare da daka mata tsawa cewa ki tafi nace, a razane samha ta miƙe cikin yanayin tsoro da far gaba tace idan na tafi ina zanje? Hydar yace wannan kuma ya rage naki,


Cikin kuka samha tace wannan wane irin bala"i ne? Ni zaka wulaƙanta hydar? Ni zakaci wa mutunchi? Ka nuna min kai kana da gida ko? To ni ban wani san ina zanje ba, dan bani da kowa a faɗin duniyar nan sai kai, ban san kowa ba kuma banda kowa idan bakai ba, miyasa zakace in tafi? Ta ƙarasa maganar cikin yanayin tausayawa,


Hydar yace ƙarya kike! Kafin ki sanni a ina kike yin rayuwa? Samuna kuma baisa komai ya canja ba, dan haka nidai kawai nace ki kama gabanki, 


Gyara tsayuwa samha tayi tare da riƙe ƙugunta gam kamar mai shirin kai hydar ƙasa, tace to bazanje ba, ko bana aurenka ina da haƙƙin zama a gidanka, hydar yace ai da bake matata bace da kuɗi aka baki kizo zuwa kusa da hydar bazata zuwantu ba,


Murmushin ƙarfin hali samha tayi tare da juyawa ta nufi ɗakinta, ajiye takardar yayi a saman kujera sannan ya fice daga farlon,


         Samha tana zuwa ɗakinta saman gado ta faɗa sai kuka takeyi, saida tayi kuka sosai sannan ta sassauta, mi hydar yake nufi da takardar daya bata? Kodai sakinta yayi?


Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un hawaye ya ƙara gangarowa daga cikin kwarin idonuwanta, ji tayi cikinta yayi wani zuuu ƙuyyyy, da sauri ta dafeshi ta tashi tayi toilet a hanzarce,


Tashin hankali gudawa samha takeyi, tana kuka, cikinta sai ƙara ya mitsewa yakeyi, saida ta gama abinda takeyi sannan ta fito tana ci gaba da kuka, a zuciyarta tace ashe haka takardar sakin aure take? 


La"ilaha illallahu Muhammadu rasulillahi Sallahu Alaihai Wasallama, zufa samha ta goge tare da ci gaba da maimata innalillahi wa"inna ilaihir raji"un,


A hankali samha ta zauna gefen gado tare da dafe kanta da hannu bibbiyu, fuskarta tana kallon ƙasa, banda ajiyar zuciya babu abinda samha takeyi sai hawayen da suke kwararowa daga idonta irin dai na wanda yaci kuka ya gaji,


Hydar kuwa ciki fushi mai fushi  ya fita daga farlon ransa na ƙara ɓaci zuciyar na ƙara harzuƙa kansa yana ƙara ɗaukar zafi kwakwalwarsa tana fitar da haƙi, idanuwansa gaba ɗaya sun janza kala zuwa launin ja, kallo ɗaya zakayi masa kasan yana cikin fushi, yana fita a hanzarce ya isa wurin moter, Alale yana hangosa da sauri ya buɗe moter tun kafin ya iso,


A gadarance hydar ya shige moter Alale ya rufe, sannan ya koma mazaunin tuƙi yaja, sauran motocin suka bi bayan motar hydar wasu a gaba wasu a bayan su moter hydar daice a tsakiya haka su ibi hanya sukaci gaba da tafiya dan zuwa Abuja,


Samha saidai a goge hawaye a kwanta a tashi a zauna, yinin ranar haka ta ƙare tsakanin toilet da saman gado, ita bataci abinci ba ita batayi wanka ba saidai tayi sallah ta koma ta kwanta,


Samha batayi bacci ba saida sanyi asubahi ya fara tahowa, a lokacin wani bacci mai daɗi ya ɗauketa, tana busar baccinta cikin kwanciyar hankali da nishaɗi amma idan ka ganta a zahirance, amma a baɗinance dole tasa samha baccin nan,


Cikin bacci tayi mafarki,


Hydar ne tsaye ya fito daga wanka, fuskarsa ɗauke da kyakkyawan murmushinsa mai narkar mata da zuciya, wanda duk cikin yanayin da take wannan murmushi yana ƙara sakata nishaɗi,


Itama murmushin tayi tare da matsawa inda yake tsaye, tana zuwa ta kwantar da kanta saman ƙirjinsa, ɗan jan lumfashi yayi tare da sauke gahurtacciyar ajiyar zuciya, hannunsa ɗaya yaɗan riƙo kugunta, ita kuma ta riƙe ɗayan hannunsa da hannunta,


Cikin wata irin murya maisa mutum yaji kasala hydar yace kinzo ɗaukar darasi ne? Murmushi samha tayi tare da cewa A, a, shima murmushi yayi tare da janyeta daga jikinsa, yana tafi zuwa wurin gado yace nima idan kinzo yau banda lokaci, ya ajiye towel ɗin hannunsa a saman bed site ya ci gaba da tafiya zuwa wurin wedrof,


Bin bayansa samha tayi itama tana cewa miyasa? Hydar yace saboda baki sako uniform ba, kinsan ba'a zuwa makaranta da kayan gida, a lokacin daya matsa jikin wedrof, itama binsa wurin tayi tana cewa wane iri ne kayan makarantar naka? Ta ƙarasa maganar tana kallon cikin kwayar idon hydar,


Kusa da samha ya ƙara matsawa sosai sannan yaɗan fizgota jikinsa tace Ahhh, murmushi hydar yayi sannan yace ni a tsarin dokar koyar da karatuna a cikin babbar makaranta shine, dokokina sun haɗa da zuwa aji cikin lokaci, sako kayan makaranta ya zama wajibi ga dalibata, idan kinzo aji hawa saman tebirin ɗaukar darasi dole ne,


Samha tace ina ne tebirin naka yake? Hydar yace gadona mana, to miye uniform ɗin? Hydar yace kayan bacci masu ɗaukar hankali kinga kina zuwa cikin wannan shigar kika hau saman tebiri lallai nasan a shirye kike da ansar karatu, ni kuma daga nan zan buɗe wuta inyi ta dirkaka miki darasi harsai kin gaji, idan na tabbatar kin ilimantu sai a tashi makar........


Da sauri ta buɗe idonta jin kamar mutum a kusa da ita, tashi tayi zaune tare da wawwaigawa amma bata ga kowa ba, tsoki tayi sannan ta sauko daga saman gado ta nufi toilet, saida tayo wanka sannan ta ɗauro alwallah,


Bayan ta fito ta gabatar da sallah asubu da batayi ba, bayan ta gama sallah ta shirya ta saka kaya sannan ta fita ta nufi parlo,


Saida tayi break sannan tazo ta zauna inda hydar ya ajiye takardar, kallon takardar tayi haka nan taji hawaye yana gangarowa daga idonta,  ɗaukar takardar tayi ta jujjuyata amma ta kasa buɗewa,


Riƙe takardar tayi gam a hannunta tana kuka, tambayar kanta ta farayi saki nawa hydar yayi mata ne? Matsalar babu waya ma a hannunta data kira hydar ta bashi haƙuri, haka nan ta gaji da "yan koke kokenta ta kwanta a wurin har bacci ya ɗauketa,


Saida tasha baccinta ta gaji sannan ta farka, ɗaki ta koma tayi sallah azahar, bayan ta gama ta sauko, waje ta fita wurin su Alale bayan sun gaisa tace don Allah ya kira mata hydar zatayi magana dashi wayarta ta samu matsala,


Miƙa mata wayar yayi tare da nuna mata number da zata samu hydar ɗin, ansa tayi ta koma farlo, bayan ta shiga ta zauna a kujera sannan ta fara kiran wayar hydar,


Babu wani ɓata lokaci ya ɗauka, samha tace ina yini, lafiya qalau waye ya haɗaki da wayar Alale kuma? Cikin girmamawa samha tace arowa nayi in kiraka in baka haƙuri, cikin hayani hydar yace wannan ai haukace banda shashanci sai kije ki anso wayar yarana ki kirani saboda wawanci?


Cikin kuka samha tace kayi hakuri don Allah wallahi ba wawanci bane kawai dai ina san inji muryarka ne, murmushi hydar yayi a ransa kuma yaji daɗi, amma sai yace ma samha to ai kinji ta isheki ko in ƙara miki ne? Murmushi samha tayi tare da sauke ajiyar zuciya tace naji muryarka tafi jiya daɗi,


Hydar yace da gaske? Samha tace da gaskiya nake mana, cikin gajiyayyiyar murya mai saukar da kasala hydar yace kinji babu daɗi bana nan ko? Samha tace Ey mana, to yaushe zaka dawo? Murmushi hydar yayi tare da cewa kina so in dawo ne? Samha tace Eh wallahi gidan duk bayamin daɗi yauma saida nayi mafarkin ka wallahi,


Gyara kwanciya hydar yayi tare da cewa bara in kiraki ki bani labarin abinda kika gani a cikin bacci, kashe wayar hydar yayi sannan ya kirata dan itace ta kira da wayar Alale,


Samha ta ɗauka, bayan ta ɗauka ta kara a kunenta, hydar yace to bani labarin mafarki! Samha tace ka bari saika dawo zan faɗa maka, hydar a ni gaskiya ban yadda ba kawai ki faɗamin yanzun zanji daɗine idan kika faɗa, faɗamin don Allah ko bakya so inji daɗi?


Samha tace ina so mana, sassauta murya hydar yayi tare da cewa to faɗamin, cikin ko oho samha ta kwashe kaf labari ta rattafawa hydar,


Dariya hydar yayi sosai sannan yace lallai kice dawowa ta sameni tunda yarinya tana buƙatar karatu, samha tace bawai haka nake nufi ba kawai dai na kwanta inajin babu daɗi a raina na ɓata maka rai,


Murmushi hydar yayi tare  da cewa shima rashin karatun ya dameki tunda a baccin ba haƙuri kika bani ganinki kikayi kinzo ɗaukan darasi, kada ki damu zan dawo cikin satin nan in taho dake,


Samha tace nikam bazanje ba, kaima ka bari saika gama abinda kakeyi ka dawo, hydar yace ina ina ina???? Hakan bazai taɓa yuwuwa ba daliba tana buƙatar malami suyi karatu ai dole hydar ya dawo tunda dai na samu kina gane karatun? Haka dai suka sha firansu irin tasu ta ma'aurata, daga baya sukayi sallama da juna kowa ya kashe wayarsa, bayan sun gama,


Samha taje ta mayar da Alale wayarsa, sannan ta dawo ta wuce ɗakinta, hydar kuwa yana cikin farin ciki sosai domin yaji daɗi a ransa samha tayi mafarki dashi hakan ya nuna mishi samha tana sanshi tunda har take mafarki dashi,


Haka dai rayuwar samha taci gaba da tafiya a gidan hydar ita kaɗai takeyin rayuwarta, amma kullum suna waya da hydar cikin jin daɗi da kulawar juna, yana so ya dawo amma abubuwa ya mishi yawa, yana missing samha sosai da bata kusa dashi itama a wurinta hakan take,


Dan a yanzun samha tafi hydar damuwa da rashinsa, kullum batajin daɗi ita dai tafi shi san ya dawo kuma ta faɗa mishi amma ya kasa banbarowa daga solvenia, yanda samha take nunawa hydar tayi missing nashi yasa shi shiga tashin hankali amma ya yadda da samha 100% kullum yana kwantar mata da hankali da magana mai daɗi,


Yauma tana kwance farlo duk abin duniya ya dameta, ga batajin daɗi yau da lafiya gobe babu, wayarta dake gefenta da hydar yasa faruk ya kawo mata ta fara ringing, jawo wayar tayi hydar ne yake kiranta,


Ɗaukar wayar tayi ta kara a kunneta cikin natsuwa ta fara magana, bayan gaisuwa hydar yace mata wai miya sameki ne? Samha tace ba komai, hydar yace da komai mana kullum rana baki da aiki sai cin zogala yakuwa rama, samha tace waye yace maka? Kaka tace kene kike ce a kawo miki kullum kullum,


Samha tace na gaji da abinci ne bakina bayamin daɗi wallahi bana iya cin komai, hydar yace kinyi rashin lafiya ne? Samha tace A, a, hydar yace to ya kikeji ne? Samha tace banajin komai gaskiya kwai dai ina yawan jin gajiya ne, hydar yace bari zansa faruk yazo ya kaiki asibiti, turo baki samha tayi sannan tace ni gaskiya lafiyata qalau basai naje ba,


Haka dai suka gama wayarsu amma samha kam tace bazaje asibiti ba, shidai hydar ɗan tambayoyin da yayi ma samha ya gano kamar tana da ciki ne kuma ya faɗa mata tace ita babu wani ciki kawai dai dan baya nan ne,


Kaka tazo taga samha kuma tace zata tafi da ita gidanta, amma hydar yace a,a, shidai kada aje masa da mata ko ina saidai idan zata zauna nan ta zauna, ganin samha batajin daɗi sosai yasa kaka ta haƙura ta zauna a gidan,


Zama ne dai sukeyi mai daɗi samha najin daɗin zama da kaka sosai domin tana ririta ta sosai, amma babu mai ma wani magana domin kowa baya gane yaren kowa,


Kaka ganin samha batajin daɗi sosai yasa tasa hydar yasa aka samo masu aiki domin samha bata iya komai daga kwanciya sai kwanciya, kuma kaka ta matsa suje asibiti amma saita ce wai dan hydar baya nan ne yasa batajin daɗin gidan,


Yanzun ma samha ce kwance a jikin kaka tana bacci, ita kuma kaka tana waya hannunta kuma yana saman kan samha tana ɗan shafa mata, saida kaka ta tabbatar bacci mai nisa ya ɗauki samha ta lallaɓa ta sauketa daga jikinta domin fita zatayi,


Cikin bacci samha taji wayarta tana ringing, dan haka idonta a rufe ta kai hannunta a inda takejin ƙarar wayar ta dauko ba tare data duba ba ta kara wayar a kunnenta, muryar Rabi taji da sauri ta buɗe idonta tana murmushi,


Rabi tace gani nan a gidanki fa, samha tace da gaske? Rabi tace da gaske mana samha tace wayyo sannu da zuwa don Allah gani nan fitowa, Rabi tace ba damuwa a fito lafiya,


Suna gama wayan ne samha ta tashi ta shiga toilet ta wanke bakinta da fuskarta, bayan ta fito ta saka hijabinta dan tunda ta lura cikinta yaɗan turo bata zama babu hijabi, dan kunya takeji zuwa yanzun ita ta tabbatar ma kanta tana da ciki,


Cikin jin kunya samha ta sauko tana murmushi tare da ma Rabi sannu da zuwa, a kusa da rabi samha ta zauna, suka gaisa,


Bayan gaisuwa rabi tace shikenan daga kije ki dawo sai hydar ya taho dake, murmushi samha tayi tare da cewa kaka ce take nemana, rabi tace ba tasan kina gidanmu ba, samha tace to nikam dai ban sani ba haka dai kawai saƙon yazo min,


Rabi tace to a ranar ina kika kwana ne? Samha tace duk ya mutanen gidan? Tayi wannan maganar dan kauda waccan maganar da rabi takeyi, murmushi rabi tayi dan ta gane samha bata san maganar ne, dan haka suka canja fira,


Haka suka sha firansu rabin firar dai rabi tana bawa samha shawara ne, saidai samha tace tom, dan hydar ya koya mata tsoron mutanen ƙarni, zulai mai aiki itace ta kawo ma rabi ɗan abun taɓawa,


Haka suka yi marecensu suna fira har kaka ta dawo daga anguwa, suka gaisa da rabi, daga gaisuwa kuma kowa ya tsaya haka nan, wucewa sama kaka tayi anan tabar samha da rabi,


Rabi bata tashi tafiya ba sai bayan magrib, dan haka samha ta haɗa mata hamsin da tara na arziki kuma tasa Alale yakaita gida, haka rabi ta tafi tana godiya sosai tare da yaba kirki irin na samha,


Bayan tafiyar rabi samha ta dawo ta buɗe kayan da rabi ta kawo mata, kayan matane ko wanne da ɗan karamin takarda an rubuta sunan sa da bayaninsa a ciki,


Tsoki samha tayi tare da cewa lallai idan hydar yaga wannan shirmen faɗa zaiyi, ni bana ma so gaskiya, ɗaukar kayan tayi ta riƙe a hannunta tama rasa a ina zata ajiye?


Hanyar kchin ta nufi da kayan a hannunta tana shiga ta shige store ta ɓoyesu, sannan ta fito ta nufi ɗaki dan gabatar da sallahr isha'i,


Saida ta gama tayi wanka sannan ta haye saman gado ta ɗora kanta saman jikin kaka dake kwance, ta fara kiran wayar hydar dan ita a gaban kaka takeyin wayarta tunda bata gane abinda take cewa,


Bayan hydar ya ɗauka suka gaisa, samha tace bacci ma kakeyi ko? Hydar yace Eh, samha tace tou wai yaushe zaka dawo? Kace wata ukku yanzun har kayi wata huɗu fa da tafiya, hydar yace nikam bansan yaushe zan dawo ba dan tuni nabar solvenia samha tace gaskiya nidai ka dawo haka nan,


Hydar yace to zan dawo insha Allah, sun ɗanyi fira sosai daga baya hydar ya tambayi samha mi rabu ta kawo mata data zo? Samha tace mi tace ta kawo min ne? Hydar yace ni mi zaihaɗani da ita har tace min tazo wurinki, kawai dai nine nake tambayarki,


Samha tace to waye yace rabi tazo? Hydar yace nine na sani, samha tace to babu abinda ta kawo min, hydar yace to bari kiji in faɗa miki idanma ta kawo miki na haneki da ci ko sha ko shafawa a jiki, samha tace miyasa? Hydar yace ba dalili nakeso ki tambayeni nace dai ki kikaye,


Samha tace don Allah faɗamin kaji, hydar yace to matso kusa dani sai in faɗa miki, samha tace abinda baka nan yace to ki bari idan na dawo zan faɗa miki, kuma idan Allah ya kaimu gobe ramlat zata zo, wace ce ramlat inji samha, hydar yace matar sahib mana,


Ɗan gajeran tsoki samha tayi sannan tace matar Al'ameen dai, hydar yace to matar Al'ameen ba kaka waya, kallon idon kaka tayi itama kakar tana kallon samha, hydar yace ko tayi bacci ne? Samha tace idonta biyu gata ma tana kallona, miƙa mata wayar samha tayi suna fara waya da hydar samha ta fita dan haushi takeji suna wannan yaren,


Samha kuwa tana fita ɗakin hydar tayi tafiyarta tayi kwanciyarta, bayan kaka ta gama waya ta jirayi zuwan samha amma shiru haka ta haƙura da jiran dawowarta har tayi bacci,


Saida safe samha da kaka suka haɗu a tebirin cin abinci, anan suka gaisa, bayan gaisuwa kuwa kowansu ya fara break, har suka gama kalaci babu wanda yayi ma wani magana,


Samha tana gamawa ta koma saman kujera tayi zamanta, itama kaka tana gama abinda zatayi tashi tayi ta koma ɗaki,


Samha kuwa sai bayan azahar taje ɗaki tayi wanka sannan tayi sallah, bata gama.abinda takeyi ba zulai mai aiki tayi sallama ta shigo cikin ɗakin,


Cikin girmamawa tace ma samha hajiya kina da baƙuwa a farlo, samha tace kice ina zuwa, tashi zulai tayi tana cewa a fito lafiya,


Kaka ta kalli samha cikin yarenta tace mi nene? Ɗan gajeran tsaki samha tayi tare da cewa idan an faɗa miki bakya ganewa amma komai sai kinji,


Kaka tace iye? Samha tace Ey, magana kaka taci gaba da yi, samha kuma taci gaba da harkar gabanta ba tare data sake cewa komai ba,


Tana gama shirinta ta saka hijabinta ta sauka inda ramlat take, bayan taje a kusa da ita ta zauna suka gaisa cikin farin ciki da mutattan juna, 


Zulai mai aiki itace ta kawo komai tun kafin fitowar samha, haka dai sukayi fira tsakanin samha da ramlat, 


A cikin firansu ne ramlat tace ina sahib? Murmushi samha tayi ba tare data kalli inda ramlat take ba tace aike zan tambaya tunda mijinki ne, itama murmushi tayi tare da cewa mijinki dai, samha tace ni ba mijina bane hydar nake aure,


To sun ɗanyi fira dai sosai, da ramlat zata tafi samha taje ta ɗauko kayan matan da rabi ta kawo mata ta bata, da kayan shafa da kuɗi dubu 100 hydar yace ta ɗauka a ɗakinsa ta bata,


Godiya ramlat tayi sosai sannan ta tambayi samha a ina ta samu kayan mata? Babu wani damuwa samha ta faɗa mata, zama ramlat tayi tare da cewa rabi? Rabi shegiya? Matar ɗan yayan babanki? Samha tace Ey Eh itace, ramlat tace chaf to Allah ya sawaƙe kinci ko kinsha ne? Samha tace na ajiyene kada mai gida ya gani yayi faɗa,


Ramlat tace to Allah ya sawaƙe amma kada kiyi amfani dasu dan nima bana so, idan hydar ya dawo zai faɗa miki dalili, domin shine ya turoni, gidan nan yace dai kawai inzo amma bansan abinda zuwan yake nufi ba amma dai nazo kawai,


Samha dai shiru tayi ramlat ta gaji da surutunta sannan tace zata wuce, a bakin ƙofar parlo samha tayi mata rakiya daga nan ta dawo,


To ranaku dai sunci gaba da tafiya, abubuwa sunci gaba da faru, yanzun hydar watansa biyar da tafiya ga cikin samha ya fito ɗaff kaka kuwa banda faɗa babu abinda takeyi domin hydar yace wata ukku zaiyi dan haka yau falfala faɗa takeyi babu ji kuma babu gani tace duk abinda hydar yakeyi ya dawo hakanan,


Kaka tace wannan ai haukane, har neman kuɗi yafi iyalinsa? Tambayarsa ma takeyi shi mi zaiyi ma da kuɗi a duniyar nan? Shidai hydar haƙuri ya bata tare da alkawarin ƙarshen wata zai dawo, kaka tace bata yadda ba wallahi duk abinda yake satin nan ya dawo,


Tou samha dai jin hydar zai dawo gaba ɗaya duk tabi ta wani burkuce, dan data tuno takardar da hydar ya bata gaban faɗuwa yakeyi,


Su kaka "yan duniya tsofi da kanta ta kira hydar wai ya faɗawa samha taje ta wanke kanta tayi kitso tayi ƙunshi, dariya hydar yayi tare da cewa ke ki faɗa mata mana,


Kaka tace na faɗa mata bata ganewa, murmushi mai aji hydar yayi sannan yace ta ba samha wayar, miƙawa samha waya kaka tayi tana cewa hydar, ansa samha tayi suka gaisa,


Hydar yace kinji wai abinda kaka tace? Samha tace A, a, murmushi hydar yana cewa kaka tace ince miki wai kije a wanke mi kai kiyi kitso kiyi ƙunshi, taɓe baki samha tayi tare da cewa kai kana so ne? Hydar yace ni duk ɗaya idan kinyi yayi idan bakiyi ba duk yayi,


Samha tace to tunda haka ne, zansa a wanke min rabin kaina ɗayan rabin a barshi da datti, zanyi ma hannu ɗaya da ƙafa ɗaya kunshi ɗayan zan barsu babu ƙunshi, ai haka yayi maka ko?


Hmmm hydar yace tare da jinjina kansa yace hakan ma yayi, samha tace to da kyau, 


Hydar yace ki zama lafiya zanyi sallah, samha tace to don Allah wai miye ka rubuta a takardar daka bani da zaka tafi, hydar yace baki duba ba? Yayi maganar ne cikin mamaki, samha tace Eyy, hydar yace ikon Allah to miyasa? Samha tace kawai haka nan, taɓe baki hydar yayi tare da jinjina kansa cewa to yayi, sai anjima yana faɗin haka ya kashe wayarsa,


Ajiye wayar samha tayi ta rufe idonta dan bacci takeji, kaka ce tayi magana cikin harshenta da bai iya hausa ba cewa ki tashi min jiki zanje in sallah, samha batayi magana ba ta sauka daga jikin kaka ta gyara kwanciyarta saman gado sosai taci gaba da baccinta,


Ɗan gyara kwanciya samha tayi fuskarta ɗauke da murmushi amma fa bacci takeyi,


Wai bana ce kada ki sake zuwamin da wannan uniform ɗin ba? Kallon kanta tayi sannan ta kalli hydar, murmushi tayi tare da cewa bafa uniform ba ne, hydar yace nan ba class bane kika zo ba? Samha tace ai naga gidan kuma ba makaranta ba ne, waye ya faɗa miki bayan gaki kinzo ajina ɗaukar darasi?


Gidan nan makarantar ki ne, ɗakina shine ajikin, karatuna shine darasinki, sakamako yana fito insha Allah bada jimawa ba, hawo gado mu fara a daidai lokacin da ya kalli agogon dake maƙale a jikin bangon ɗakinsa, yaci gaba da cewa naga lokaci yana tafiya dan period in karatu ta kusa shuɗewa ta bacci tana neman shigowa hawo hawo hawoooo,


Samha wannan miye? Inji kaka tare da ɗan taɓa samha dake neman faɗowa daga saman gado, da sauri samha ta buɗe idonta ta saukeau akan kaka,


Kaka tace ki gyara, ɗan gajeran tsoki samha tayi tare da turo baki ta harari kaka dan taji haushi ta tasheta bacci bata ga yanda mafarkinta ya ƙare ba,


Ɗaukar wayarta tayi ta fita daga ɗakin tana gunguni, ɗakin hydar ta nufa tana zuwa gado tahau ta kwanta sannan ta fara kiran wayar hydar,


Hydar yana zaune saman abin sallah yana karatun Qur'anil kareem yaga kiran wayar samha, kallo ɗaya yayi ma wayar ya maida hankalinsa yaci gaba da karatunsa,


Samha taci gaba da kiran wayar babu ji babu gani, amma hydar yana ci gaba da karatun sa bai ɗauka ba,


Haƙura tayi ta daina kira, wayar ta ajiye a gefe taci gaba da bacci, saida hydar ya gama abinda yakeyi sannan ya fara kiran samha, itama basar dashi tayi wai tayi fushi, dan cikin nan wani zuciyar banza yake sata yanzun nan zatayi fushi sosai kan abinda bai kai ya kawo ba,


Shima bai sake kira ba, dan a ƙa'idar sa idan ya kira mutum so ɗaya harya tsinke bazai sake kira ba, amma ita samha yana iya kira taƙi ɗauka har sau3, ganin hydar bai sake kira ba yasa ta kashe wayanta gaba ɗaya taci gaba da baccin ta,


Yaune ranar da hydar zai dawo amma samha bata sani ba, domin tun data kashe wayarta ranar nan har yanzun bata sake buɗeshi ba, dan haka kaka da zulai kawai suke ɗan hidindimunsu,


Ita kuwa saidai ta kwanta anan ta tashi ta koma can, sai baƙin rai takeyi wanda ita kanta bata san abinda ya assasa mata shi ba, haka su kaka suka gama komai amma samha tana zaune a farlon tana binsu da kallo,


Haka nan ta gaji da zama ta tashi ta koma ɗaki, tana zuwa wanka tayi ta saka riga da zani na atamfa, ta sako hijabinta ta sauka ƙasa taci kwaɗon zogale, tana gamawa ta koma saman kujera ta kwanta, anan kaka ta barta ta nufi ɗaki dan gabatar da sallah la'asar,


Itama zulai abincinta ta ɗauka ta nufi BQ ganin kowa ya fashe yasa samha ƙara gyara kwanciyarta taci gaba da sararawa abinta cikin bacci,




-----------------------------

*_Jαmilα Musα ce_*💅🏻

--------------------------------

[05/04 4:46 pm] Washa: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊



                 *SO*

     *MUGUN WASA*



       *{ Love is a bad game }*




*JAMEELA MUSA* { meelat musa }




*Story, Writing & Editing*

                   *by*

         *Meelat Musa*


*_Alhamdulillah_*

*_Alhamdulillah_*   🔚

*_Alhamdulillah_*


___________________________________

*_Gaisuwa a gareku_* 👇🏻

*_Hauwa'u Musa_*

*_Rabi Musa_*

*_Sa'adatu Musa { Aunty }_*

*_Halimatu Musa { Uwa }_*

*_Hafsat Nasir { maman zahra }_*

*_Maryam Umar Gara_*

*_Hafsat Umar Gara_*

*_Shamsiyya Umar Gara_*

*_Farida Galadima_*

*_Ummie Galadima_*

*_Safina Aliyu karofi_*

*_Fiddausi Abdulrahman karofi_*

*_Fatima Muhammad_*


_________________________________


*_Abdulrahman Lawal B'K_*

               _&_

*_Ja'afar Lawal B'K_*


*_Allah ubangiji yayi muku albarka, Allah ya kare muku sharri darajar manzan Allah S. A. W, Allah yasa ku gama da duniya lafiya, ina muku addu'a ubangiji yayi muku jagoranci a rayuwarku, Allah ya sadaku da farin ciki a rayuwarku duniya da lahira, Allah ya dawwama farin ciki a zukatanku, ina muku fatan alkairi tare da addu'ar samun nasara da ci gaba a rayuwarku darajar sayyadis sadati { S. A. W } Ameeen Summa amin_*

 

                  *SO*

      *MUGUN WASA*


*_Dedicated to_* 👇🏻

_Ramlat Abdulrahman real mai dambu_


*77➖🔚*



Cikin bacci samha taji ihun motocin hydar da sauri ta buɗe idonta tayi wiƙi wiƙi, tare da baza kunnuwa taji a fili ne ko kuwa a bacci?


Har yanzun motocin basu gama shigowa ba, dan haka da sauri samha ta miƙe ta matsa jikin window tana leƙawa, hydar ta hango tsaye yana waya,


Ɗan matse fuska tayi tare da rufe idanuwanta ta sake buɗe su, dan a tunaninta bacci takeyi, lallai idonta biyi kuma da gaske hydar ne,


Murmushi samha tayi irin mai fitar da lumfashin nan kamar wanda yayi gudu ya gaji, a fili tace lallai hydar ya iya bazata ta ƙarasa maganar cikin farin ciki tana ƙara faɗaɗa murmushinta,


Riƙe bakinta tayi tana jin daɗi sosai, wata "yar siririyar ƙara tayi mara sauti, sannan tayi hanyar fita da saurinta, har yanzun hydar yana tsaye a inda ta hangoshi yana waya,


Cikin gudun "yan gayu mai natsuwa tattare da ɗaukar hankali tayi wurin hydar, yana ganin ta taho shima ya fara tahowa a hankali dan ya baro cikin mutane amma har yanzun wayarshi yakeyi,


Samha tana isa wurin hydar ta rungumeshi tare da cewa lallai wallahi ka iya bazata shine bazaka faɗamin zaka dawo ba sai kawai ka wani kama kayi tahowarka abinka, ta ƙarasa maganar tana "yar dariya hannunta yana saman cikin hydar ta kwantar da kanta a saman ƙirjinsa, shi kuma yaɗan tallafeta da hannu ɗaya ɗayan kuma yana a kunnensa ya riƙe wayarshi,


Kallon samha hydar yayi tare ɗan zaro ido ya buɗe baki alamar mamaki yana kallon cikin samha, ɗan ɓata fuska samha tayi tare da ƙara gyara hijabin jikinta, murmushi hydar yayi yaɗan riƙe kafarɗarta suka fara tafi zuwa cikin farlo, samha kuwa sai kallon hydar takeyi domin ta ganshi gaba ɗaya ya canja kamar an sako mata shi, gashi ya zuge cikin ƙananan kaya sun matuƙar dace da kyakkyawar fatarsa,


Saida suka shigo ciki sannan hydar ya gama wayar, zama yayi saman kujera tare da ƙara jawo samha a jikinsa yace waike jira? Haka karatun ya koma? Yana tambayarta a daidai lokacin da yake kai hannunsa yana shafa cikinta, tsoki samha tayi tare da kai masa ɗan dukan wasa a kafaɗarsa ta tashi, dariya hydar yayi ya tashi shima yabi bayanta yana cewa da Allah zoki faɗa min inji mana,


Basu gama hawa sama ba kaka ta fito daga ɗaki, murmushi hydar yayi ya matsa kusa da ita tare da cire peniscap ɗin kansa ya duƙa daidai ƙafafuwan kaka ya dafa yana magana cikin yarensu, murmushi kaka tayi tare da dafa kansa itama tayi magana cikin yare kamar yanda hydar yayi, amma da alama addu'a take masa tunda hydar yana cewa amin, bayan ta gama addu'ar ne tayi ma hydar magana tana murmushi,


Dariya hydar yayi tare da kallon samha yace wai da gaske? Samha tace mi? Murmushi yayi tare da miƙewa tsaye yaja samha suka wuce ciki, kaka tabi bayansu da kallo, ba tare datace komai ba amma yanayin fuskarta ya nuna farin ciki takeyi,


Daƙin hydar suka nufa, saida suka shiga sannan hydar ya saki samha daga jikinsa ya matsa jikin bedsite ya ajiye wayarsa da hularsa, ita kuma samha toilet ta shiga ta wanke fuskarta da bakinta, tana cikin toilet ɗin hydar ya shigo da towel a hannusa da alama wanka zaiyi,


Dan haka da sauri ta fito ganin hydar ya fara cire kayan jikinsa, tana fitowa farlo ta dawo wurin kaka, daga kaka har samha babu wanda yayi magana tunda kowa baya fahimtar kowa, tashi kaka tayi zata koma ɗaki,


Da sauri samha ta tashi tabi bayan kaka suka tafi ɗaki tare, bayan sun shiga kaka ta fara hawa saman gado ta kwanta, itama samha hawa tayi tare da kwanciya saman jikin kaka, dan haka kakar ta koya mata,


Hydar kuwa yana fitowa daga wanka, wayarsa ya ɗauka ya kira kaka bayan ta ɗauka yace ta turo mishi samha, danshi bai ɗauka tafiya tayi ba, kaka tace to sannan ta kashe wayarta,


Kallon samha tayi tace hydar kije, haka kawai ta faɗawa samha, samha batayi magana ba ta sauka daga saman gadon ta nufi ɗakin hydar,


A bakin ƙofa suka haɗu yana fitowa, samha tace gani! Ba tare daya kalli samha ba yace ina kaka takene yana ci gaba da tafiya yana gyara agogon hannunsa, itama biyo bayansa tayi tana cewa tana ɗaki ina zakaje kuma?


Ina da meeting ne, samha tace wane irin meeting kuma? Bai bata amsa ba ya fara waya tare da nuna mata da hannu yana dawowa, da sauri ya sauka ƙasa tana nan tsaye tana hangoshi harya fita daga farlo,


Ɓata fuska samha tayi, a bayyane tace ji wani abu kuma? Mutum ya dawo daga tafiya ko abinci baici ba ya wani kama ya tafi wani meeting abinsa mtsww, saida ta ƙara tsoki sannan ta nufi ɗaki tana gunguni,


Tana zuwa ɗaki toilet ta shiga tayi wanka tare da ɗauro alwallah, bayan ta fito ta shirya sannan tayi sallah magrib, tana zaune a wurin har aka kira sallah isha'i tayi,


Hydar kuwa bai dawo gida ba 12:07am dan haka ta baya ya shigo ya shige ɗakinsa, dan a lokacin daya dawo kowa yayi bacci shima ya shige ɗakinsa dan hutama rayuwarsa,


Da safe kuwa bayan ya dawo sallah ɗakin samha shiga, kaka tana zaune saman abin sallah ta jingina jikinta da bango ta miƙe ƙafafuwanta tana gyangyaɗi, samha kuma tana kwance a saman ƙafarta tana bacci, 


Duƙawa hydar yayi, daidai idon kaka yakai hannunsa yana ɗan giccegicce dashi amma kaka bata buɗe idonta, a hankali hydar ya tsugunna daidai samha ya riƙe mata baki kamar dai yanda ake ma "yan primary idan sun ishi malamai da surutu a ce kowa ya kama bakinsa, haka yayi ma bakin samha,


Da sauri ta buɗe idonta abinda yasa kuma batayi magana ba saboda hydar ya riƙe bakin, kansa da idanuwansa yayi mata nuni da tayi shiru kada tayi magana, ɗayan hannunsa kuma yana nuni ta taso,


Girgirza kanta tayi alamar A, a, harararta yayi tare da jinjina kansa, hannunsa yasa a aljihu ya ciro wani abu da sauri samha ta ɗaga masa hannu zata tashi, miƙewa hydar yayi tare dayin magana a hankali cewa to taho muje, tashi tayi tabi bayansa, fitarsu yasa kaka ta buɗe idonta tare dayin murmushi dan tun shigowar hydar taji kawai dai ta basarne kada ganinta yasa yayi gaisuwa kawai ya koma,


A ɗakin hydar kuwa suna zuwa ya haɗa hannunsa ɗaya a cikin ɗayan kamar yana gaisawa da wani, sannan ya ɗaga hannun sama kamar yana miƙa, kallon samha yayi tare da cewa oyoo yoo, murmushi samha tayi tare da shigewa cikin jikin hydar tana riƙeshi, saida ya tabbatar ta shigo sosai sannan ya sauko hannunsa ya riƙeta,


Murmushi yayi tare da cewa kinsan kaka idonta biyu fa, samha tace da gaske? Yace da gaske naga sai wani ƙiƙƙifita ido take nima nayi kamar ban gani ba, turo baki samha tayi tana cewa kuma shine saika wani ce in taho? Murmushi yayi a daidai lokacin da yake sakinta daga riƙon da yayi mata yana cewa to ni ina ruwana?


Jan hannunta yayi suka matsa jikin gado, zama hydar yayi a gefen gado sannan ya zaunar da samha itama, yaɗan riƙe gefen kafaɗarta da hannu ɗaya ɗayan hannun kuma yana saman cikinta, idonsa kuma yana cikin kwayar idonta, murmushi hydar yayi a daidai lokacin daya kwanta ya jawo samha a jikinsa suka kwanta tare,


Yace O, har yanzun hannunsa yana saman cikin samha da gani dai al'ajabi yakeyi, samha tace wai miye? Murmushi hydar yayi ba tare daya kalli samha ba yace daɗi nakeji kinyi ciki nasan har abada samha ta zama hydar,


Murmushi samha tayi tare da kauda maganar ta hanyar cewa wai don Allah mika rubuta min a cikin takarda nan ne? Hydar yace a ina kika ajiye ne? Samha tace a ɗakina, a daidai lokacin da hydar yake ɗaukar wayarsa dake ta tsuwwa, yace ma samha jeki ki kawo min da sauri, samha tace tom saukowa tayi daga saman gadon sannan ta fita a ɗan hanzarce, shi kuma ya fara waya,


Bata wani daɗe ba ta dawo da takardar a hannunta, har yanzun hydar bai gama wayar ba, zama tayi tana jira ya gama amma wayar ma kamar yanzun aka fara, tun samha tana zama na marmari harta kwanta, a hankali hydar ya jawota jikinsa ya riƙeta yana ci gaba da wayar sa, tsoki samha ta farayi dan wayar ta fara ƙufular da ita, turo bakinta tayi tare da neman saukowa daga saman gadon dan harta shaƙa, riƙota hydar yayi ta sake kwantar da ita ya sakata a tsakiyar ƙafafuwunsa yaci gaba da wayarsa,


Kallon sa samha tayi murmushi hydar yayi tare da nuna mata tayi haƙuri da hannunsa, ita kuwa samha yanzun bata da wani wahalar hayaƙa ɗan abun kaɗan zai ɓata mata rai, haƙuri hydar ya ƙara bata dai, ganin wayarsu bazata ƙare ba yasa samha ta fara baccin dole,


Ganin tayi bacci yasa hydar ya ɗagata daga riƙon da yayi mata, ya tashi ya koma parlo yaci gaba da wayarsa, ya ɗauki lokaci mai tsayi yanayin wayar, bayan ya gama ne ya kalli agogon wayarsa, yaga 8:15am, kallon zulai yayi dake ta faman goge goge, waddata gaisheshi tun ɗazu amma bai ansa ba,


Zulai kuwa ganin hydar ya gama wayar yasa ta sake durƙusa daga inda take ta gaishe shi, da kanshi ya ansa gaisuwar tare da ƙara bin zulai da kallon mai nuni da ina ya santa? Zulai ganin hydar ya kafeta da idanuwansa masu sa mutum yaji tashin hankali yasa ta miƙe da sauri ta nufi kitch, har yanzun hydar kallonta yakeyi,


Zulai tana shiga kicin tayi ajiyar zuciya tare da goge zufar goshinta lallai tasan duk irin shigar da tayi sai hydar ya ganeta domin wayau ne dashi, goge hawayen idonta tayi tare da haɗiye yawun wahala yaukam tasan ƙashinta ya bushe,


Saida ta shige sannan hydar yayi murmushi da gefen bakinsa har haƙoransa suka fito, uhum hydar yayi tare da miƙewa tsaye ya fita daga cikin farlon,


Samha kuwa tana tashi daga bacci toilet ta shiga tayi wanka tare da tunani barkatai a zuciyar lallai hydar ya raina mata wayau, shine ma zai tashi yayi tafiyarsa ya barta lallai yayi masa kyau,


Tana fitowa daga wanka ɗakinta ta nufo dan ta shirya, kaka ta gani tsaye da jaka a hannunta da alama dai fita zatayi, kallonta samha tayi amma batayi magana ba, ta wuce jikin madubi ta fara shafa mai,


Hydar ne ya shigo ɗakin da sallama, bayan sun gaisa da kaka ne sukaci gaba da maganarsu, saida suka gama sannan hydar ya matsa kusa da samha yace kaka wai zata tafi, samha tace miyasa? Hydar yace nima ban sani ba a daidai lokacin da yake zama saman bedsite,


Samha tace ka bata haƙuri mana, murmushi hydar yayi tare da faɗawa kaka cikin yarensu cewa kinji samha tace kiyi haƙuri ki zauna wai tana san zama dake, tsoki kaka tayi cewa kai bazan zauna ba inyi ta takura muku hakanan,


Dariya hydar yayi sosai har beauty point insa ya fito, kallon samha yayi sannan yace zo kiji samha, ya ƙarasa maganar cikin dariya irin mai kware mutum tare da ɗan dafa ƙirjinsa, kallonsa samha tayi miƙa hannunsa yayi har yanzun murmushi yakeyi,


Kusa dashi samha ta matsa, ɗan taltafo mata ƙugu yayi yana kallon cikin kwayar idonta, yace samha wai haka kaka tace wai kamar ta takura mana shine yasa zata tafi,


Dafa kafaɗar hydar tayi tare da ɗan ɗora goshinta saman nasa, tace don Allah kada ta tafi muyi zamanmu tare a nan dukanmu, tunda kaga a gidanta babu kowa sai masu aiki don Allah duka mu haɗu mu zauna gaba ɗayanmu,


Cikin sanyi murya hydar yace zata zauna dama barta kada ki sake mata magana duk mu ɗin muyi mata shiru zaki ga bazata tafi ba, kaka ce tayi magana ita dama samha batajin yarenta dan haka shi hydar da yakeji baiyi mata magana ba, miƙewa yayi tare jan hannun samha suka fita daga ɗakin, duk maganar da kaka takeyi hydar bai saurareta ba bare ya bata amsa,


Ganin hydar baiyi magana ba kuma yayi fitarsa, yasa kaka ta haƙura ta cire gyalen jikinta tare da ajiye jakar hannunta tana ta tsegumi da mita,


Hydar da samha zube a saman gado banda dariya dukansu babu abinda sukeyi, hydar yace kinji abinda tace ne? Samha tace ya za'ayi in sani tunda bana jinta, murmushi hydar yyi tare da cewa bani takardar da kika ɗauko min yayi maganarne dan kauda maganar kaka,


Ɗaga pilow samha tayi ta ɗauko takardar ta miƙewa hydar, murmushi yayi tare dayi ma samha wani irin kallo wanda yasata saurin kwanciya saman jikinsa, taɓe baki yayi ya jinjina kansa a daidai lokacin daya buɗe takardar yace tashi ki karanta muji,


Ta bayanta ta miƙa hannunta ta ansa, bayan ta ansa ne ta gyara kwanciyarta a saman jikin hydar ta wani ƙara bajewa sai kace shine gadon, shi kuma kallonta yayi tare da riƙe haɓarsa yana mamakin samha data ɗan saki jiki dashi, samha tace kanaji ko? Ina jinki ya faɗa a taƙaice, murmushi tayi tare da fara karantawa,


_Zanyi tafiya, naso na tafi dake amma kaka tace A, a, naji babu daɗi a raina saboda bana so nayi nisa dake, kuma kiyi haƙuri dana taka miki hannu kinji ko? Na tafi saina dawo,_


Murmushi samha tayi bayan ta gama karantawa, har yanzu kallonta hydar yakeyi amma baiyi magana ba, murmushi samha ta sakeyi tare da cewa nayi haƙuri ai ta ƙarasa maganar tare da ɗan buɗe idanuwanta ta ɗan ɗagawa hydar gira, shima murmushi yayi da gefen bakinsa ba tare daya ce komai ba,


Ɗan ƙara ɗagota yayi ya ƙara ɗorata a saman jikinsa sosai yana cewa a karatu ina muka tsaya da zanyi tafi? Murmushi samha tayi amma batace komai, hydar yace to aini na sani bara in fara daga inda na dasa aya, to hydar ayi karatu lafiya nikam bara in koma wurin zulai mai aiki da kuma kaka,


Kaka ganin hydar ya basar da ita yasa ta haƙura ta cire gyalen jikinta, fitowa tayi daga ɗaki ta sauko ƙasa dan ta ɗan taya aikace aikace da zulai keyi,


Hydar & samha darasin nasu mai girma ne domin malam hydar yayi teaching sosai wa samha ta gane karatun akwai banbanci tsakanin karatun makaranta dana makarantar hydar,



Bayan samha ta gama  ilimantuwa ne shima hydar ya tafi period in hutu yasa samha ta sauka ta nufi toilet don tsarkake jikinta, bayan ta gama abinda take ta fito hydar ya tashi shima ya nufi toilet ɗin,


Samha kuwa mai taɗan murza tare da ɗan shafa powder kaɗan, bayan ta gama taje inda kayanta suke doguwar riga na atamfa ta saka, bayan ta gama tana ƙoƙarin fita ne daga ɗakin hydar ya fito,


Yace samha zo, ba tare da tayi magana ba ta juyo, hydar yace zanyi tafiya fa, idanuwa samha ta zaro tare da matsowa da sauri inda hydar yake tsaye yana goge jikinsa, cikin damuwa tace ina zakaje kuma? Yace zanje *_Mexico_* cikin kuka samha tace haba hydar daga dawowa jiya kuma zakayi tafiya ta ƙarasa maganar tana shigewa cikin jikinsa tare da ƙara sakin kuka sosai,


Cikin damuwa hydar ya ɗagota daga jikinsa ya ruƙe ƙafaɗarta da hannu biyu ita kuma ta kalleshi hawaye na fitowa sosai daga cikin gurbin idanuwanta, hydar yace kiyi haƙuri kinji? Duka sati ukku zanyi insha Allah, cikin kuka samha tace haba hydar wannan ai ɗaukar alhakine, taɓe bakinsa yayi tare da cewa to miye wani abun ɗaukar alhaki anan kuma? Ɗan gajeran tsaki samha tayi tare cire jikinta daga riƙon da hydar yayi mata ta bar ɗakin cikin fushi,


Murmushi hydar yayi bayan fitar samha sannan yaci gaba da shirinsa, ita kuwa samha da kuka taje ɗaki ganin kaka bata ɗakin yasa ta sauko ƙasa da sauri, tana zuwa inda kaka take zauna ta faɗa saman jikinta tana ci gaba da kuka,


Kaka ta tambayi abinda yasa samha takeyin kuka amma samha bata saurara ba haka taci gaba da kukanta gar hydar ya fito, 


Kaka ta tambayi hydar miye samha takeyin kuka? Yace wai dan zaiyi tafiya kuma duka sati ukku zaiyi ya dawo, aiko kaka kamar jira takeyi ta fara faɗa sosai tare da cewa dama saboda wannan yawan yawon yasa aka kashe iyayenka, kullum suna sama a jirgi kamar wasu tsuntsaye, yau basa nan gobe basa nan, jibi suna 👇🏻


*_Venezuela, Mexico, Denmarka, California U. S A., Switzerland_*

*_Iran, Japan, Nethrlandas, Colombia, Armenia, Germany, Turkey, Bali indonesia, lebnon_*

*_Tunisia, Dubai U. A. E, Virginia U. S. A, Jordan, Greece, Slovenia, Spain, Qatar_*

*_Gaza palestine_*

*_Ottawa, canada_*

*_Sierra leone_*

*_Khobar K.S. A_*

*_Maldives_*


Hydar yace don Allah kiyi haƙuri haka nan duk miye lissafi? Cikin faɗa kaka tace nayi lissafa, daga *_England, Texas U. S. A, Bahrain, China, Paris France_*


Kallon samha hydar yayi tare da cewa taso muje! Ɓata fuska samha ta ƙarayi sosai tana kuka tare da maƙale kafaɗa ta ƙara narkewa sosai a jikin kaka kamar ƙaramin yaro yana ƙquwya, murmushi hydar yayi tare matsawa kusa da kaka ya jawo samha da karfi,


Kaka taci gaba da faɗa tare da ci gaba da lissafo sunayen ƙasashe, amma hydar ko inda take bai sake kallo ba yaja samha suka fita daga farlon, har yanzun samha kuka takeyi,


BQ ya nufa har yanzun hannunsa yana riƙe a na samha, amma har yanzun samha tana kuka, tunda zulai ta hango hydar yana tahowa yasa ta fara kuka domin tasan tata tazo ƙarshe, cikin kuka samha ta kalli hydar tare da cewa mi zamuyi a anan kuma? Ba tare da hydar ya kalleta ba yace mi kika gani ne?


A daidai lokacin da zulai ta fito da gudu daga cikin ɗaki tana kuka da sauri tayo kan hydar tana ƙoƙarin duƙawa ta kama ƙafafuwansa, da sauri hydar ya zuƙe jikinsa yana cewa karki taɓamin jiki, durƙuwa tayi ƙasa tana ci gaba da kuka,


Hydar yace ciro haƙoran da kika saka a bakinki, jiki na rawa zulai ta ciro haƙoran ta ajiye a ƙasa, kallon samha hydar yayi tare da tambayarta kin gane ta? Samha tace A, a, ai ban santa ba, murmushi hydar yayi sannan yace ya akayi kika zo nan gdan?


Zulai tace kayi haƙuri don Allah, hydar yace nima kinzo ki kasheni kenan ko? Tace wannan karon ba aikin kisa bane, aikin miye ne? Inji hydar ya tambaya a taƙaice, tace Asma'u ta turoni, kiyi mata mi? Dama magani ne ta bayar in zuba maka a abinci tace tana sanka ka aureta, 


Shigowar kaka ya hana hydar yayi magana, kaka ta fara tambayar miye? Hydar yace waye ya kawo wannan yarinyar a gidan nan ne? Kaka tace Rabi ce, wace rabi? Inji hydar kaka tace rabin daka sani mana, to waye yace ana san mai aiki? Kaka tace nice nayi mata magana,


Gyara tsayuwa hydar yayi tare da ƙara riƙe samha sosai a jikinsa, yace duk inda naga wannan fuskar bazan manta da ita ba har abadan duniya a rayuwata, kace silar sakani cikin maraici kece kika sakani cikin damuwar da har yanzun ban fita ba, kece mutum ta farko a duniya da kika fara sakani baƙin ciki, kene kika fara sa nayi kuka da idanuwana a duniya, ko kin canja komai bazaki taba canja zuciya ba, 


Wayarsa ya ciro daga aljihunsa ya fara daddannawa, hoton zulai ya bayyana, kallon ta hydar yace kinganki ko? A lokacin da abin ya faru mahaifina kafin ya rasu yayi ƙoƙarin ɗaukar hotonki ya turo min kuma yace idan har na ganki in tambayeki laifin mi yayi miki kika kashe shi? Sannan kuma nawa aka biyaki da har kikayi ƙoƙarin turasa ya zuwa duniyar mutuwa? Cikin kuka zulai tace ba abinda yayi min wallahi, hydar yace tou faɗa man inji miye dalilinki nayin haka?


Kaka ta kalli hydar cewa wai miye? Mi zulai take ma kuka? Sannan shima miyake ce mata? Shigowarsu shamsu da Alale da dai sauran yaran hydar duka domin suna jiran fitowarsa dan zasuyi tafiya amma sunga har yanzun bai fito ba shine dalilin da yasa suka biyoshi domin suga lafiya? Hydar ya bawa kaka bayani, aiko kaka kamar jira takeyi hydar ya rufe bakinsa ta fara dukan zulai tana tsine mata albarka ta kashe mata ɗiya, dakel hydar ya riƙeta tare da cewa tayi haƙuri amma kaka sai kuka takeyi tare da goge majina,


Kowa dai yana tsaye yana kallon ikon Allah bakajin motsin komai sai kukan kaka, ita kuwa samha samun wuri tayi ta zauna domin ta gaji da tsayuwar kuma gata ba ita ɗaya bace, hydar yace miye sunnaki na gaskiya? Saida zulai ta ƙara goge hawayen idota sannan ta fara,


Ni suna nan suwaiba, ina zaune a garin kano ne kuma ni haifaffiyar garince, a takaice dai na taso cikin maraici da ƙuncin rayuwa kasancewar mahaifiyata bata raye, matar babana itace ta ɗorani zuwa turba duk wanda nake kai a yanzun, mahaifina baida ƙarfi talakane sosai kuma Allah ya jarabeshi da ciwon zuciya bamu da halin nema masa magani ne, ga ciwo kullum ƙara tubirewa yakeyi,


Wannan yasa na shiga tashin hankali da damuwa, na shiga neman taimako ta ko wane hali, muna hakane Allah ya haɗani da Rabi tazo gidanmu kasancewa mahaifiyarta aminiyar matar babana ne, bayan sunzo ita da ƙawarta Asma'u bansan abinda sukace ba tunda bana cikinsu,


Ina ɗakina kwance naji gwaggo ta fara kwala min kira na taso na taho, bayan nazo ne ta nunamin rabi da asma'u, tace min wannan ɗiyar ƙawata ce sannan kuma wannan ita ƙawarta kuma aminiyarta ce mahaifinsu yake san ayi masa wani aiki akan naira miliyan ɗaya zaki iya ne?


Cikin zaƙuwa nace zan iya, miye aikin ne? Rabi tace sai munje can zakiyi magana dashi, a ranar na shirya cikin shirina muka rantaɓa zowa garin kaduna, bayan munzo ne Asma'u ta haɗani da mahaifinta bayan mun gaisa ne ya bani wani abu a kwalɓa yace min kawai zan zuba wa iyayenka a abinci ko abun sha, haka kawai yace min,


Kuma a daren ranar ne ya kawoni gidanku dan ya nunamin su, kai kuma a lokacin zakayi tafiya zuwa daraguay dani da asma'u muka gaisheka amma dukanmu babu wanda ka ansa gaisuwar wannan ne yake bin bayanka ta nuna shamsu,


Dukan kowa da kowa ya fita donyi maka rakiya, iyayenka suna sanka sukayi ta maka addu'ar fatan alkairi, fitarku ne dady ya nunamin inda wani roba yake na zuma, a cikin zumar na zuba wannan abin na cikin kwalbar daya bayani kafin kowa ya dawo har nayi na gama,


Bayan sun dawo daga rakiyarka ne aka ƙara fira daga baya muka tafi, tou bayan kwanaki biyu muka tafi abuja dani da dady da asma'u, gidan dadynka haka dadyn asma'u ya haɗa mishi sha tara ta arziki da zuma sosai a cewarsa yana san zuma,


Tou munyi kwanaki sosai a gidan, ranar da su dady zasu wuce ne a ranar ne dady yace mu muyi gaba mu dawo kaduna zai taho, Asma'u tace itadai dukanmu tare zamu tafi, dole tasa dady ya haƙura,


A inda dady ya samu hotona momynka tace mishi ita dai bata yadda damu ba, domin ta kamani ina zuba wani abu a abinci kuma ita da kanta taimin wayau cewa muyi hoto a tare, wannan hoton shine, bayan dadynka yaga hoton ya tura maka shi ya tambayeka wace ce ni? Kai kuma ka fara bincikena, dady ganin asirinmu zai tonu yasa ya babbakawa gidan wuta bayan ya gama sace abinda yakeso, bayan mun tabbatar kowa da kowa ya mutu, muka taho kaduna tare da cewa sunyi haɗarin jirgin sama sun mutu,


Murmushin takaici hydar yayi tare da goge hawayen idonsa, wani irin halbi shamsu yakaiwa subaiwa tare daci gaba da dukanta ta sama da ƙasa yana cewa kema yau zaki baƙunci lahira, kaka kuwa batasan abinda ake cewa ba, samha kuma kallon hydar dakeyin kuka tayi cikin sanyin jiki ta tashi daga inda take zaune taje wurin da hydar yake tsaye yana kallon suwaiba, har yanzun hawaye na ɗiga daga isonsa, ganin hydar yana kuka yasa samha itama ta fara kuka, sai yanzun hydar ya maido dubansa wurin samha tare da cewa miye haka kuma? Samha sai kuka takeyi, hydar ya jawota a jikinsa yana murmushin ƙarfin hali cewa ki daina kuka shamsu daina dukanta, 


Shamsu yace saina kasheta kamar yanda suka kashe mana mai gida yana ci gaba da dukan suwaiba tare da tattakata dan suwaiba tuni har tayi laushi, hydar yace Alale ku riƙemin shamsu dan qata irin zuciya gareshi, dakel aka riƙe shamsu sai haki yakeyi tare da nuna suwaiba da ɗan yatsa amma ya kasa magana sai hawaye da yakeyi, hydar yace zaki iya tafiya, shamsu yace wallahi bazata tafi ba saina kasheta hydar yace dady yace kada ayi musu komai suje duniya ta ishesu,


Haka suwaiba ta tashi simi simi babu kunya bare tsoron Allah ta fara tafiya, shamsu yace insha Allah sai kin lalace mutuwa zakiyi irinta karnuka tunda har aka haɗa kai dake aka kashe adalin mutum mai tausayi da kuma taimakon al'umma,


Hydar kuwa ya dafo kafaɗar kaka da samha shi kuma yana tsakiyarsu suka nufo farlo, bayan sunzo ne hydar yayi ma samha faɗa cewa idan tana fita harkar Rabi ta fita harkarta bama rabi ba kowa ya rabata tarayya dashi ta kiyayi duniya da mutane cikinta, shine kaɗai abun yaddarta domin baizai cutar da ita ba har ƙarshen lumfashinsa,


Dukansu fatan alkairi yayi musu samha kaɗai tayi ma hydar rakiya amma banda kaka, saida hydar suka tafi sannan samha ta dawo ta wuce ɗaki tana ci gaba da kuka don bataji daɗin tafiyar hydar ba kwata kwata,


Haka rayuwa taci gaba da tafiya samha itace takeyin komai a gida da ita da kaka dan yanzun basu da mai aiki, samha tanajin daɗin zama da kaka sosai itama haka kaka takejin dadin kasancewa da jikarta,


Hydar kuwa har cikin samha ya shiga watan aihuwa aihuwa ko yau ko gobe amma bai dawo ba shida yace sati ukku amma har yayi wata huɗu, kullum sai yace zai dawo amma baya dawowa, yanzun ma ya daina kiran samha dan kullum idan sunyi waya kuka take mishi wannan dalilin yasa kwata kwata ma ya daina waya da ita,


Yauma zaune take sai kiran wayar hydar takeyi amma yaƙi ya ɗauka, tsoki tayi tare da ajiye wayar ta tashi taci gaba huɗɗin gabanta, shigarta cikin kching kamar jira takeyi ta shiga ta durƙushe a wurin tare da faɗar innalillahi wa'inna ilaihir raji'un da ƙarfin tsiya, da sauri kaka ta fito tare da tambayar lafiya? Ganin samha durƙushe a bakin kiching yasata fara salati, tare da matsawa da sauri ta ɗago samha!


Samha sai kuka takeyi tana riƙe mararta, da sauri kaka ta saki samha ta koma sama da sauri cikin tashin hankali ta ɗauki wayarta ta fara kiran hydar babu daɗewa ya ɗauka ta fara rattafa mishi samha babu lafiya, wayyo hydar ya faɗa tare da kashe wayarsa,


Da sauri ya kira faruk cewa maza yaje gidansa do Allah samha babu lafiya, faruk yace to, kafin faruk ya iso tuni hydar ya tada hankalin su Alale kaka ta kamota sun tazo suka shiga mota, suna shiga motar faruk yazo,


Dan haka kaka tace ya bari su dawo kawai faruk yace to, haka suka dinguma da samha zuwa asibiti aka bar faruk da sauran ma'aikata masu kula da flowers da share share da dai sauransu,


Su kaka suna zuwa asibiti babu wani ɓata lokaci aka shiga da samha labour room cikin hukunci Allah ba'a wani daɗe da shiga da ita ba ubangiji ya sauketa lafiya, ta samu santalelen yaron,


Farin ciki wurin kaka ba'a magana, shima Alale ba'a barshi a baya ba, farin ciki sosai dan haka kaka ta doka waya ta faɗawa hydar samha ta sauka lafiya ta samu baby boy, hydar yayi farin ciki sosai yace insha Allah jibi zai dawo,


Bayan likita yayi "yan gwaje gwaje sa ya tabbatar da lafiyar samha da babynta ya rubuta musu sallama, suka taho gida, bayan sun dawo kaka tayi ta waya tana faɗawa "yan uwa da abokan arziki,


Kaka itace take kula da samha takeyi ma samha wanka ita da jariri tana kula dasu sosai, 


Yau samha tana cikin farin ciki saboda a yau ne hydar zai dawo dan haka da ita da babynta anyi gayu an zuge sosai ana jiran dawowar mai gida hydar,


Shi kuwa hydar bai dawo ba sai 11:48pm ya shigo gida a lokacin har samha tayi bacci, kuma koda kaka zata tasheta hydar yace kada a tasheta a barta, jaririn ya ɗauka ya fita dashi ya nufi ɗakinsa, acan yayi masa huɗuba kamar yadda addini ya koyar,


Bayan ya gama ya dawo dashi ya ajiyeshi a kusa da samha, bayan ya ajiyeshi yayi ma kaka saida safe, tace ga abinci yace bayajin yunwa, yana faɗin haka ya fita daga ɗakin,


Da safe kuwa saida kaka tayi ma samha wanka ta wanke jariri fes ta shirya shi, itama samha ta shirya ta saka kaya masu kyau, bayan sun shiryu ne kaka tace ma samha hydar ya dawo tun jiya, samha naji an ambaci hydar ta ɗauki jariri tayi ɗakinsa ba tare da tace wani abu ba,


Da sallama samha ta shiga hydar yana kwance ya ansa sallamar cikin jin daɗi, sai kallon samha yakeyi yana murmushi da sauri ya tashi zaune yana cewa barka da zuwa maman jariri, turo baki samha tayi a daidai lokacin da zauna kusa da hydar ta ajiye jaririn a jikinsa,


Riƙe jaririn yayi tare da ɗan riƙo samha a jikinsa ya kalli jaririn sannan ya kalli samha yace sannu, murmushi samha tayi tare da ƙara shigewa jikin hydar murmushi yayi sannan ya ajiye jaririn a gefe ya ƙara riƙeta sosai yana cewa kefa yanzun kin girma kin wuce hawa jiki sai jariri, dariya samha tayi sosai shima hydar ɗin dariya yayi tare da cewa wasa nake miki ai yanzun kika fara rayuwa a jikin hydar,


Samha tace a hakan kana tafiya kana bari na? Yace kiyi haƙuri insha Allah yanzun duk inda zan tafi dake zan tafi, uhum samha tace tare da ƙara lanƙwashewa a jikin hydar, 


Tou ranar suna ansha casu sosai an girgije an molaƙe an digera an kakkafe an caskaɗe sosai yaro yaci suna muhammadu hydar kuwa ya yage aljihu yayi hauka da kuɗi sosai yayi ɓarin kuɗin duk wanda yazo suna gidan samha yasan kuɗi sunce wayyo Allah wanda hydar baima san sun fita daga cikin asusun  kuɗinsa ba, matar al'amin tazo wato ramlat rabi ma tazo brilliant fans sunzo suna meelat musa fans group suma sunsha shagalinsu, hmmm mai dambu kuwa an wani yage baki sai kwasar shagali akeyi , asmee zeeyan leema & surayya da ɗaukancin brilliant writer association manya manta kenan an wani kame a saman kujera sai cin nice sukeyi, ina kallon  leema hada wani komawa ƙarin shinkafa da miya 🤣, haka dai akasha taron suna akayi suna lafiya kowa ya koma gida lafiya, aka bar samha da kaka da jaririnta & hydar angon jego,


Tou haka dai rayuwa taci gaba da tafiya zuciyoyi biyu suna ba juna kulawa, sabuwar soyayya mai ƙarfi da shaƙuwa tsakanin samha da hydar, shi kuma hydar yana kula dasu sosai daga samha har kaka da muhammad hydar yana basu kulawa ta musamman,


Kaka dai ta haƙura da komawa gida hydar yace tayi haƙuri ta zauna cikinsu, itama hakan taso domin ta rayu cikin jikokinta biyu da suka rage mata a duniya,


A ɓangaren kawu kuma ya samu sauƙi amma ba sosai ba yana dai cikin wahala dai da takura ta rayuwa sai yanzun ya gane kuɗi da "ya"ya ba'ayi musu muguwar riƙo gashi shi baiyi aure ba bare yasa ran zai samu masujin ƙansa, saidai wani ɗan almajiri aka samu yake kula dashi, uhum nikam dai nace Allah ya rabamu da tsaka mai wuya,


Bayan shekaru goma, abubuwa sunci gaba da faru sosai a ciki harda auren yusra da shamsu, itama kausar tayi aure ta samu mijinta mai rufin asiri, suwaiba kuwa ta kamu da lalurar taɓin hankali bata da aiki sai bin bola da tsince tsince,


Samha kuwa tana da yaranta huɗu ukku maza mace ɗaya, akwai muhammad sai Abubakar wanda suke kira da sadiq, umar suna kiransa da faruk, sai macen aka saka mata sunan kaka, fatima, suna kiranta da zahra, ga samha da tsohon ciki, amma kullum hydar mita yakeyi wai yafi samha sonta sosai akan yanda take sansa domin shidai yasan kawai tana zaune dashi ne dan yana ɗan uwanta amma bata sansa kamar yanda yake santa,


Saidai samha tayi murmushi tare da basar da maganar domin itama tasan tana tsananin sansa sosai amma baya yadda, 


Kuma hydar yana kula da kawu yana mishi taimako sosai da bashi kulawa albarkacin samha, haka dangin baban samha hydar yana musu taimako sosai tunda basu da ƙarfi yana taimaka musu da duk abinda yasan zai basu taimako a rayuwarsu,


A ɓangaren dady kuwa yana nan yana fama da wahala da tashin hankali dan shi dama alhaki kwikwiyone, ka kashe mutum baiji bai gani ba, dama ya zakayi ka zauna lafiya? To shima dai dady yana cikin tsaka mai wuya ubangiji ya rabamu da tsaka mai wuya duniya da lahira,


Asma'u kuwa ta haƙura ganin bata samun hydar yasa ta haƙura ta auri Alale,


Zaune suke dukansu a farlo kaka, samha, muhammad, sadiq, faruk,  zahra, zahra kuwa tana jikin kaka sai yare sukeyi domin kaka batayi musu hausa dukansu shima hydar bayayi musu hausa wannan dalilin yasa itama samha ta zage ɗantse itama ta iya yare, dan haka suna zaune suna maganarsu wanda ni banajin abinda suke cewa, 


Samha ce ta tashi ta nufi ktching, muhammad ne yabi bayanta yana mata magana cikin yare bansan abinda yake ce mata ba,


Da sauri faruk ya shigo cikin kching yana cewa Ammi zo kiga wani ya shigo yana nemanki yana magana yana zaro ido dan nunawa samha maganar da yakeyi tana da mahimmanci,


Kallonshi samha tayi sannan tace yana ina ne? Ƙara zaro ido faruk yayi sosai tare da nunawa samha da hannunsa, leƙowa tayi daga kching taga sahib zaune a saman kujera,


Da sauri ta fito daga cikin  kiching ɗin tana cewa miye haka kuma? Sahib yace nima zuwa nayi ayi firan da ni, murmushi samha tayi tare da cewa to babu damuwa tunda haka ne nima bara in koma ciki in ɗauko wuƙata, da sauri hydar ya cire fuskar tare da cewa na kama kunne na, ya ɗora hannunsa a saman kunnensa, da gudu yara sukayi wurinsa suna cewa la dady suna riƙesa, kaka ma dariya tayi sosai domin itama tasan sahib, itama samha da sauri taje ta zauna kusa da hydar tare da kwantar da kanta saman ƙafadarsa, tana riƙe fuskar sahib a hannunta, itama kaka matsowa tayi cikin ahalinta ta zauna, ni kuma na ɗaga wayata nayi musu hoto, tare da musu fatan alkairi, 🔚


Alhamdulillah,


___________________

*_Jαmilα Musα ce_* 💅🏻

___________________

Copied By

HAYATU BABA ZUBAIRU(YAYA HAYAT) 

(ADMIN OF ADMINS)

        (admin 

   Hayat hausa novels

Hausa novels and fashion

Cool novel, makeup and kitchen1⃣


adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *