[6/21, 6:34 PM] Zahra✍🏻: ^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^
🌻♣🌻♣🌻♣🌻
🌹♣🌹♣🌹
☘♣☘
🌹
*♡YAR ALMAJIRA♡*
☘♣☘♣☘♣☘♣☘♣☘
🌹♣🌹♣🌹♣🌹♣🌹
🌻♣🌻♣🌻♣🌻
☘♣☘♣☘
🌹♣🌹
🌻
©🔥ĔL̆ŎQ̆ŬĔN̆C̆Ĕ W̆R̆ĬT̆ĔR̆S̆ ĂS̆S̆ŎC̆ĬĂT̆ĬŎN̆ ✍🏻
*ʂɬơγყ & щγıɬɬɛŋ ცყ:*
🌹Zαняα α.α (Dι∂єєуℓσν)✍🏻
*🌻тнιѕ вσσк ιѕ ∂є∂ι¢αтє∂ ιи нσиσυя σf му ∂єαяєѕт fяιєи∂ѕ gєитℓє, яєαℓѕмαѕнєя, нυввєєу, αυfαиα & ℓιρтσи😘*
_______________________________☘
_Aѕѕαℓαмυ αℓαιкυм ωαяαнмαтυℓℓαнι тααℓα ωαвαяαкαтυн, вαякαи мυ ∂α ѕαкє кαѕαи¢єωα тαяє α¢ιкιи ѕαвσи ℓιттαfιиα мє тαкєи *'yar αℓмαʝιяα* ℓιттαfιиє ωαи∂α кє ¢ιкє ∂α ∂αяυѕѕα мαѕυ уαωα ωαи∂α zαмυ ιℓιмαитυ zαмυ иιѕнα∂αитυ, ℓιттαfιиє мє ¢ιкє ∂α αвυвυωαи вαи вαи мαмαкι ∂α αℓαʝαвι, кυ ¢ιgαвα ∂α кαѕαи¢єωα ∂αиι zαняα у'αя αυтα (∂ι∂єєуℓσν)♠_
*🌹ωαииαи ραʝιи иαкυ иє αℓкαℓι'ѕ, αℓℓαн уα кαяα ωα αииαвι ∂αяαʝα, αℓℓαн уα αℓвαякα¢ι яαуυωαя мυ, αℓℓαн уα ѕαкαωα ιуαуєимυ ∂α gι∂αи αℓʝαииαтυℓ fιя∂αυѕ😘*
_☘ вιуαууαи ιуαує ѕнιиє gαвα ∂α кσмαι вαуαи кιуαує ∂σкσкιи υвαиgιʝι, ¢ιи яιвαи zαмαи ∂υиιуα ∂α ѕαмυи ℓαнιяα уαиα кαякαѕнιи αℓвαякαи ιуαує, αℓℓαн кαвα мυ ιкσи zαмα 'уα'уα мαѕυ вιуαууα gα ιуαуєимυ_
_______________________________🌻
♠ *Bismillahir Rahmanir Raheem*♠
*🌹1▶5🌹*
*🌻вσяиσ ѕтαтє*
*♣вαмα ℓ/g*
Umma! umma!! umma!!! "kitashi karki mutu kibarmu a cikin wannan rayuwa me cike da tarin bakinciki da kuncin zuciya dan Allah umma kiyi hakuri ki bude idanunki" kuka sosai takeyi me cin zuciya, tana jijjiga ummanta dake kwanta akan wani tsamurarren katifa, ganin dai har yanzu umman taki motsawa yasa ta fita waje dan neman agaji, abun mamaki tana fitowa naga wani hadadden gida agefe me cike da abubuwan ban mamaki da al-ajabi, sake kallon ta nayi sannan na kalli d'akin data fito aciki, tunani nafarayi kodai 6angaren yan aiki ne ko kuma d'akin matar me gadi ne toh koma dai miye bari zan binciko mana daga baya.
Wani me adaidaita ta tsayar sannan ta rokeshi akan ya taimaka mata su d'auko mahaifiyarta daga ciki, dafarko yak'i yarda saboda tsoron irin hali na d'an adam awannan zamanin daga baya kuma ya amince suka shiga suka fito da ita, basu tsaya ko inaba se government hospital dake cikin garin bama, kasancewar weekend ne asibitin shuru ba hayaniya ba kuma mutane dayawa, bayan anshigar da ita ta biya kudin me adaidaita sannan ta shiga dan biyan kudin ganin likita, wani kudi naga tafito dashi kamar tsumma duk ya kod'e ya sha lik'i kallon kudin ta tsayayi tana hawaye kamar bazata mik'a ba, ganin haka yasa account din taji tausayinta tace tabari zata biya ai dari biyar ne ba komai insha Allahu baze gagara ba, godiya tayi mata bayan ta karb'i reciept sannan takoma gefen emergency inda aka kwantar da umma, tana zuwa likitan yafito yana share zufa kallonta yayi kafin yace "kibiyoni office dina".
Bayan sun shiga ya nuna mata gurin zama sannan ya bukaci reciept kafin ya fara magana kamar haka "agaskiya mahaifiyarki tana shan wahala, shawara daya ce kufitar da Ita waje ko kuma ku rasata domin tana bukatar wannan aikin da gaggawa".
Kallonshi tayi tana hawaye kafin tace "likita banida yanda zanyi domin banda wanda ze taimakamin ni nake bara nake aikin dako nake ciyarda mu dani da kannena biyar da kuma mahaifiyarmu, da ace inada hanyar da zan iya taimakon mahaifiyata afitar da ita danayi, ko kuma da ace inada kudin biyan aikin dana bada nawa ansanya mata domin bamuda kowa se ita" takare maganan tana kara sautin kukanta.
♣🌹♣☘♣🌻♣
Agida kuwa Amina,Habiba da Nusaiba sunata sharban kuka domin sun tausaya wa umma sosai ayanayin datake ciki, tabbas suna ganin rayuwa da jarabobi kala kala, umma itace gatansu yanzu kuma tana cikin halin rayuwa ko mutuwa domin kuwa indai bawani ikon Allah ba sunsan ayanda aka fitar da umma daker tadawo musu, suna cikin haka hauwa'u da Khadija suka dawo daga kasuwa gurin da Fateemah take wanke wanke awata me saida abinci kasancewar ciwon umma ya tashi da dare shiyasa sukaje domin ta basu ranchen kudi sukai umma asibiti, suna dawowa sukaji abunda ke faruwa nan suna suka bud'e shafin kuka kamar ance musu ta mutun.
Umma wato (Maheeda) d'iya ce ga marigayi alhaji aliyu bomoi, mahaifinta shahararren malamine kuma hamshak'in mai kudi, mahaifiyarta ta rasu tun aranar da aka haifeta, umma yar gata ce gaba da baya kuma yar sarauta domin mahaifiyarta d'iyar sarki ce mahaifinta kuwa na rike da mukamin hakimin gari, umma su biyar ne a gun mahaifinsu, hud'un yaran yadikkon ta ne wato matar babanta, mahaifiyarta itace ta biyu agun mahaifinta, kasancewar ta me sunan mahaifiyar babanta yasa take samun soyayya fiye da sauran yaran sannan kuma gata marainiya tausayin ta ya karu azuciyar mahaifinta, hakan yasa yadikkonta salame ta tsaneta kuma take kishi da ita domin tasan yanda mai gidan ke son marigayiya, gashi kuma son ya shafi d'iyarta har ake nuna banbanci tsakanin ta da yaranta injita da fada, haka rayuwa ya cigaba da tafiya musu har tayi aure tabar musu gidan inda matar babanta tayi sanadiyar mutuwar mahaifita dan taci gado sannan kuma ta raba ta da danginta aka manta da ita kuma tayi sanadin rushewar rayuwar aurenta....
*_INA BAWA MAKARANTA HAK'URI BISA CANJIN SUNAN LITTAFIN DA SUKA GA NAYI HAKAN YA FARU NE SAKAMAKON WA 'YAN SU 'YAN DALILAI INA FATAN HAKAN BA ZAI B'ATA MUKU RAI BA NAGODE_*
♠ *∂ι∂єєуℓσν тαкυ¢є* 🤝🏻✍🏻 http://didi98dotblog.wordpress.com ♠
[6/22, 5:33 AM] Zahra✍🏻: ^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^
🌻♣🌻♣🌻♣🌻
🌹♣🌹♣🌹
☘♣☘
🌹
*♡YAR ALMAJIRA♡*
☘♣☘♣☘♣☘♣☘♣☘
🌹♣🌹♣🌹♣🌹♣🌹
🌻♣🌻♣🌻♣🌻
☘♣☘♣☘
🌹♣🌹
🌻
©🔥ĔL̆ŎQ̆ŬĔN̆C̆Ĕ W̆R̆ĬT̆ĔR̆S̆ ĂS̆S̆ŎC̆ĬĂT̆ĬŎN̆ ✍🏻
*ʂɬơγყ & щγıɬɬɛŋ ცყ:*
🌹Zαняα α.α (Dι∂єєуℓσν)✍🏻
*🌻тнιѕ вσσк ιѕ ∂є∂ι¢αтє∂ ιи нσиσυя σf му ∂єαяєѕт fяιєи∂ѕ gєитℓє, яєαℓѕмαѕнєя, нυввєєу, αυfαиα & ℓιρтσи😘*
_______________________________☘
_A αѕѕαℓαмυ αℓαιкυм ωαяαнмαтυℓℓαнι тααℓα ωαвαяαкαтυн, ιиαуιωα ∂υккαиιи мυѕυℓмαι вαякα ∂α ѕнαи яυωα вαякα ∂α ѕαℓℓα, αℓℓαн уα вαмυ ιкσи gαиιи ωαиι ωαтα мє αℓвαякα ωαтσ *яαмα∂αи* ♠_
*🌹 ωαииαи ραʝιи иαкυ иє вσмσι'ѕ, αℓℓαн уα кαяα ωα αииαвι ∂αяαʝα, αℓℓαн уα αℓвαякα¢ι яαуυωαя мυ уα нα∂α кαимυ gαвα ∂αуα, αℓℓαн уα ѕαкαωα ιуαуєимυ ∂α gι∂αи αℓʝαииαтυℓ fιя∂αυѕ😘*
_☘ α∂∂υα мαкαмιи мυмιиι,∂υк ωαи∂α уα яιкι αℓℓαн вαzє тα6α тα6єωα вα, ιℓιмιи α∂∂ιиι нαѕкєи яαуυωα_
_______________________________🌻
♠ *Bismillahir Rahmanir Raheem*♠
*🌹6▶10🌹*
*🌻вσяиσ ѕтαтє*
*♣вαмα ℓ/g*
Ni sunana fateemah ana kirana da Noor kasancewar naci sunan kakarmu ta wajen uwa, mun tashi cikin gata irin wanda ko wani 'dan adam ke son kasancewa aciki, mahaifin mu babban attajirine wato Dr muhammad Nura, mu shida ne agun iyayenmu, nice babba shekarata goma sha-shida se Nusaibah me shekara goma sha-hudu sannan Hawwau me goma sha biyu, Habeeba nada shekara goma, Aminatu yar shekara takwas da autarmu khadijah mimi me shekara bakwai wacce taci sunan mahaifiyar babanmu, kuma tsakanin su da Aminatu ba nisa mun kasance yan gata kowa nason mu kota wani 6angare kwasam se wani abu yafaru wanda yasan yamu cikin wani haki na kuncin rayuwa mun rasa mahaifin mu alhali yana raye mun rasa dangin mu na kowani 6angare alhali suna raye sannan gashi wacce muke gani muji dadi tana cikin wani hali .
♣🌹♣☘♣🌻♣
Se guraren karfe biyu umma ta farfado daga doguwar sumar da tayi, farinciki ne ya cika zuciyar Noor, zuwa tayi ta rungumi umma tanayi mata sannu sannan taje ta d'auko ruwa da roba ta wanke mata baki bayan ta gama ta bata abinci seda taga ta koshi kafin ta bata ruwan da likita ya sayo musu sannan ta gyara gurin tafita waje dan wanke kular.
Bata dade da fita ba ta dawo tana sauri sauri dan kar umma ta bukaci wani abu, office din likita ta fara shiga ta ajiye mishi kular ta sake yi mishi godiya sannan ta koma dak'i gurin umma, se da suka kara awa daya sannan likita ya sallame su tare da basu magunguna kyauta da kuma kudin adaidaita, albarka kam likita yasha agurin umma dan se godiya suke mishi mara adadi suna fitowa harabar asibitin suka samu napep, kwatancen unguwar suka mishi sannan suka shiga, suna isa suka bashi kudinshi kafin suka shiga ciki.
"oyoyo umma oyoyo umma, wayyo Allah mun gode daka dawo mana da umman mu lafiya cikin koshin lafiya" shine abunda yaran ke fad'a da sukaga umman tashigo da kafafunta batare da taimakon wani ba, haka suka zauna suka zagaye ta suna hira suna mata adduar samun lafiya me d'orewa da kuma kudin da za'ayi mata aiki.
Horn din da sukaji ne yasa duk duka tashi suka nufi gurin taga, kod'add'en labulen tagar suka d'aga suka kallon me shigowa, atare naga duk suna share hawaye ashe kuka suke ni banma sani ba, kallon umma nayi naga tayi saurin goge nata hawayen tana cewa "hayya alal salah, duk muje muyi alwala gashi ankira sallah" tafada tana janyo Mimi daga jikin tagar, itama Noor ta rike hannun sauran kannenta suka kama hanyar waje dan yin alwala.
Komawa nayi waje dan ganin abunda ya sanya su kuka gaba dayansu harda umma amma kash na makara dan kuwa banga kowa ba se motocin dake ajiye a haraban gidan da kuma karnuka dake ta kaiwa da komowa.
*_INA BAWA MAKARANTA HAK'URI BISA CANJIN SUNAN LITTAFIN DA SUKA GA NAYI HAKAN YA FARU NE SAKAMAKON WA 'YAN SU 'YAN DALILAI INA FATAN HAKAN BA ZAI B'ATA MUKU RAI BA NAGODE_*
♠ *∂ι∂єєуℓσν тαкυ¢є* 🤝🏻✍🏻 http://didi98dotblog.wordpress.com ♠
[6/23, 9:04 AM] Zahra✍🏻: ^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^
🌻♣🌻♣🌻♣🌻
🌹♣🌹♣🌹
☘♣☘
🌹
*♡YAR ALMAJIRA♡*
☘♣☘♣☘♣☘♣☘♣☘
🌹♣🌹♣🌹♣🌹♣🌹
🌻♣🌻♣🌻♣🌻
☘♣☘♣☘
🌹♣🌹
🌻
©🔥ĔL̆ŎQ̆ŬĔN̆C̆Ĕ W̆R̆ĬT̆ĔR̆S̆ ĂS̆S̆ŎC̆ĬĂT̆ĬŎN̆ ✍🏻
*ʂɬơγყ & щγıɬɬɛŋ ცყ:*
🌹Zαняα α.α (Dι∂єєуℓσν)✍🏻
*🌻тнιѕ вσσк ιѕ ∂є∂ι¢αтє∂ ιи нσиσυя σf му ∂єαяєѕт fяιєи∂ѕ gєитℓє, яєαℓѕмαѕнєя, нυввєєу, αυfαиα & ℓιρтσи😘*
_______________________________☘ _Aαѕѕαℓαмυ αℓαιкυм ωαяαнмαтυℓℓαнι тααℓα ωαвαяαкαтυн, ιиαуιωα ∂υккαиιи мαѕσуαиα fαтαи αℓкαιяι ωα∂αи∂α иαѕαиι ∂α ωαи∂α вαиѕαиι вα ∂υк кυѕα αяαикυ кυиα яαιиα_🤝🏻♠
*🌹 ωαииαи ραʝιи иαкυ иє shdg Novella, αℓℓαн уα кαяα ωα αииαвι ∂αяαʝα, αℓℓαн уα αℓвαякα¢ι яαуυωαя мυ уα нα∂α кαимυ gαвα ∂αуα, αℓℓαн уα ѕαкαωα ιуαуєимυ ∂α gι∂αи αℓʝαииαтυℓ fιя∂αυѕ😘*
_☘ нαкυяι яιвαя zαмαи ∂υиιуα, αвυи∂α нαкυяι вє нαιfαя вα яαѕнιи ѕα мα вєzє вαуαя вα, мυ ¢ιgαвα ∂α кαѕαи¢єωα мαѕυ нαкυяι ∂σмιи αℓℓαн ѕωт уαиαѕσи мαѕυ нαкυяι_
_______________________________🌻
♠ *Bismillahir Rahmanir Raheem*♠
*🌹11▶15🌹*
*🌻∂υвαι*
*♣αℓ-qυσχ*
Wata yarinya nagani wacce baza ta wuce 16 years ba tafito daga Credence High School wanda ke cikin al-quox a hanyar da ake kira sheikh Zayed road tana tafiya tana wakar ta da turanci Yasmin!!! shine abunda naji ankira ta dashi, juyawa tayi taga wanda ke mata irin wannan kiran, tsaki taja ganin dreban ta acikin motar domin yau batada niyar zuwa gida da mota tafi sha'awar tafiya da kafa amma tunda har moses ya riga yazo toh dole ta bishi dan akwai shi da naci, shi kuwa moses dariya ta bashi ganin yanda tawani 6ata rai kamar za tayi kuka seya tuna farkon haduwar su a supermarket lokacin taje sayan kayan zak'i mistakely ya buge ta kafin ya bata hakuri harta kwashe shi da mari takara gaba ,k'aran buga kofar motar yasa ya dawo daga duniyar tunanin daya shiga sannan yaja mota suka nufi gida.
Kwantar da kanta tayi ajikin kujeran tana hawaye saboda ya 6ata mata budget in banda haka ba da yanzu har tayi nisa atafiyar ta amma ba komai tasan maganinshi murmushi tayi da ta tuna da irin muguntar da zata mishi, moses kuwa duk abunda takeyi yana kallonta ta mirrow shima murmushi yayi irin wanda tayi saboda yasan in har tayi haka toh akwai abunda take shiryawa shina kuma yasan tarkon daze d'ana mata.
Sake baki nayi ina kallon kofar gate din da suka tsaya lailai aljannar duniya kenan inbaka mutuba zaka sha kallo, gidan ya hadu iya haduwa domin tsarin ya zarce tunaninku, shiba tsarin ginin villa ba shiba whitehouse ba shiba gidan sarauta ba narasa awani 6angare zan ajiyeshi, garin kallo ashe har sun shige sun barni sedai wani lokaci dan Aufana tace kar in dira ta katanga.
♣🌹♣☘♣🌻♣
*🌻вσяиσ ѕтαтє*
*♣вαмα ℓ/g*
Dafe kirji tayi tana cewa "Wayyo Allah na umma aman jini? Zaro ido tayi tana kallon umman nata dake nishi sama-sama, dagudu sauran yaran suka fito jin irin ihun da yayar tasu ta buga, suna zuwa su kayi turus suna kallon abunda ke faruwa kowacce tafara hawaye tana ambator Allah aranta dakyer Noor ta iya daga kafarta ta isa gurin umma tana kuka tana mata sannu ganin dai hakan ba shine maslaha ba yasa tayi sauri ta fita waje dan neman abun hawa, batare da 6ata lokaci ba tasa mu wani dan tsoho wanda ya taimaka musu suka shigar da umma sannan suka d'auki hanyar asibiti.
Suna isa aka fito da gadon sanya marasa lafiya aka d'auki umma wanda har zuwa wannan lokacin aman jini bai tsaya ba, yaran na kuka sukabi bayan ta ita kuma noor ta tsaya ta sallami me adaidaita kafin ta bi bayan su.
Likitoci dayawa suka taru akan umma dan ceto rayuwarta amma Allah beyi zatayi surviving ba, sedai muce Allah ya jikanta yabawa yaran hakurin rashinta, ahaka suka fito ajere kowannen su na tausayawa yaran musanman likitansu wato dr affan wanda ya dade yana jimamin abun yama yarasa ta inda sefara tunkaran su da batun gashi babu wanda yasani nasu balle ya sanar dashi ko zesan yanda zeyi, hawaye yaji yana zuba a idanunshi, seda ya daidaita kanshi sannan ya fita ya kira noor, kallonta yayi sannan yace ta zauna.
Jiki asanyaye ta zauna tana jiran taji yau kuma menene jawabin likita Fateemah!!! "inaso ki bani hankalinki muyi magana ta fahimtar juna, kece babba kuma duk kin fisu sanin rayuwa saboda haka ki natsu ki saurareni".
Jin yanda yau yakira sunanta yasa ta bada hankalinta domin tasan bawasa acikin maganar tasa kuma duk abunda ze fada me mahinmanci ne, gyara zamanta tayi ta Tsura mishi ido kamar me kallon film, d'auke idonshi yayi daga cikin nata dan karta karya mishi zuciya sannan yace "Fateema zaman duniya 'yar hakuri ce domin kuwa abune me karewa, idan yau mune gobe ba lallai yazama muba sedai wasu kuma daban, idan yau ana damawa dakai gobe ze zama da waninka, mutuwa kuwa rigar kowace kuma dukkanin mai rai mamacine, Allah yana d'auke abunda kafiso badan ya musguna maka ba se dai dan ya jaraba imaninka, haka zalika yana baka abunda kakeso bawai dan ya faranta maka ba sedai dan ya jaraba imaninka inaso ki kasance me yarda da kaddara aduk yanda yazo miki kuma inafatan zakiyi kokarin cinye wannan jarabawa dake gabanki, ina mik'a ta'aziyya ta gareki Fateema ina bawa zuciyarki hakuri ina tayaki kukan wannan rashi da ku kayi Fateemah Allah yayi wa umma rasuwa wanda ya fimu sonta ya d'auki abunsa Fateema bsbu yanda zamuyi sedai muyi mata adduar samun dacewa" yakareshe maganar yana kuka mecin zuciya baze iya rikewa ba tabbas ya tsasaya wa wadannan bayin Allah.
*_INA BAWA MAKARANTA HAK'URI BISA CANJIN SUNAN LITTAFIN DA SUKA GA NAYI HAKAN YA FARU NE SAKAMAKON WA 'YAN SU 'YAN DALILAI INA FATAN HAKAN BA ZAI B'ATA MUKU RAI BA NAGODE_*
♠ *∂ι∂єєуℓσν тαкυ¢є* 🤝🏻✍🏻 http://didi98dotblog.wordpress.com ♠
[6/23, 9:17 AM] Zahra✍🏻: ^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^
🌻♣🌻♣🌻♣🌻
🌹♣🌹♣🌹
☘♣☘
🌹
*♡YAR ALMAJIRA♡*
☘♣☘♣☘♣☘♣☘♣☘
🌹♣🌹♣🌹♣🌹♣🌹
🌻♣🌻♣🌻♣🌻
☘♣☘♣☘
🌹♣🌹
🌻
©🔥ĔL̆ŎQ̆ŬĔN̆C̆Ĕ W̆R̆ĬT̆ĔR̆S̆ ĂS̆S̆ŎC̆ĬĂT̆ĬŎN̆ ✍🏻
*ʂɬơγყ & щγıɬɬɛŋ ცყ:*
🌹Zαняα α.α (Dι∂єєуℓσν)✍🏻
*🌻тнιѕ вσσк ιѕ ∂є∂ι¢αтє∂ ιи нσиσυя σf му ∂єαяєѕт fяιєи∂ѕ gєитℓє, яєαℓѕмαѕнєя, нυввєєу, αυfαиα & ℓιρтσи😘*
_______________________________☘ _Aѕѕαℓαмυ αℓαιкυм ωαяαнмαтυℓℓαнι тααℓα ωαвαяαкαтυн, ιиαуιωα ∂υккαиιи мαѕσуαи ωαииαи ℓιттαfι fαтαи кαѕαи¢єωα ¢ιкιи кσѕнιи ℓαfιуα ∂α кωαи¢ιуαя нαикαℓι_🤝🏻♠
*🌹 ωαииαи ραʝιи иαкυ иє ѕмαѕнєя & нυввєєу иσνєℓѕ 1/2, αℓℓαн уα кαяα ωα αииαвι ∂αяαʝα, αℓℓαн уα αℓвαякα¢ι яαуυωαя мυ уα нα∂α кαимυ gαвα ∂αуα, αℓℓαн уα ѕαкαωα ιуαуєимυ ∂α gι∂αи αℓʝαииαтυℓ fιя∂αυѕ😘*
_☘ zυмυи¢ι αвυиє мє gιямα gαяємυ уαи α∂αм, ∂υк ωαи∂α вє яιкє zυмυи¢ι вα уαиα∂α αιкι αgαвαиѕα, мαиzσи αℓℓαн уα нσяємυ αкαи мυ кαѕαи¢є мαѕυ zυмυи¢ι ∂σмιи zυмυи¢ι αвυиє ωαи∂α zє ιуα ѕα∂α вαωα ∂α αℓʝαииα кυмα яαѕнιиѕα уαѕα∂αѕнι ∂α ωυтα_
_______________________________🌻
♠ *Bismillahir Rahmanir Raheem*♠
*🌹16▶20🌹*
*🌻вσяиσ ѕтαтє*
*♣вαмα ℓ/g*
Wani irin zabura tayi ta fita a office din da gudu ta nufi d'akin da aka kwantar da umma, ganin haka yasa kannen nata suka bi bayanta, atare suka isa jikin gadon da aka kwantar da umma, hannu na rawa Noor ta bud'e abunda aka rufe umman tasu dashi, wani irin kuka ne yazo mata da sauri ta fita waje seda ta isa haraban asibitin ta samu kasan wani bishiya ta zauna tana kuka me cin zuciya, duk wanda yazo wucewa ta gurin seya tausaya mata, a 6angaren kannenta kuwa kwanciya sukayi ajikin umma suna jijjigata suna kuka anrasa me rarrashin wani, tausayin kansu ne ya kama su lailai duniya ba komai bane dazu fa suka gama wasa da dariya suna murnar cewa tasamu lafiya ashe duk na bankwana ne.
Likita kuwa tana fita yabi bayanta, seda yaga tayi kuka me isarta ta fara ajiyar zuciya sannan ya nufi inda take, dutsen dake kusa da ita yaja ya zauna sannan yafara mata nasiha me ratsa zuciya, seda yaga jikinta yayi sanyi sannan ya jata suka nufi d'akin da aka kwantar da umman, zuwa tayi ta rungumi umman tana hawaye tana mata addua sannan taja k'annenta suka fita waje dan akai ta gida ayi mata sutura, batare da 6ata lokaci ba likita da abokansa suka sanya gawar a mota suka nufi gidansu Dr da ita amma seda suka biya ta unguwar su Noor aka sanar da mutanen unguwar kafin suka wuce, likita yayi mamakin ganin gidan su Noor wanda ba boyayye bani a garin bama amma dai se komai ya lafa ze tambaye su dangantakar su da wannan hamshakin mai kudin ko kuma dai saboda rud'ewa ne yasa basu lura da gidan da suka nuna mishi ba koma dai menene zeji daga baya, bayan anyi mata wanka aka kirasu suzo suyi mata adduar bankwana kafin a tafi da ita, kuka sukeyi suna manne ajikinta, dakyer suka iya yi mata addua sannan hajiyar affan tajasu zuwa falo dan afitar da umma, kowa agurin ya tausaya musu, bayan an mata salla aka kaita makwancinta sannan akafara zaman makoki, likita ke kar6an gaisuwa a waje ita kuma hajiya a cikin gida tare da yaran.
♣🌹♣☘♣🌻♣
*🌻∂υвαι*
*♣αℓ-qυσχ*
Wani wawan ajiyar zuciya nayi danaga gate din gidan abud'e yanzu kam zaku sha labari dan daganin wannan Yasmin din akwai daru, sad'af-sad'af na shiga cikin gidan kamar 6arauniya, ji nayi an rufe kafar gate din da karfi sannan an sanya key ta ciki ashe baba me gadi ne ya dan zaga waje shine yabar kofar a bud'e, da gudu nayi hanyar shiga gidan inayi ina duban bayana, ina zuwa narasa ta hanyar da ake shiga dan kuwa kofar me lock ne se an rubuta numbers, tsaki nayi sannan na juya zan koma inda na fito se naji Hubbeey tace ta gwada zagaye gidan kila insamu kofar shiga, ai kuwa hakan nayi inata bin gidan lungu da sako, chan na hango wasu mata biyu suna fitowa ta wani kofa da alamu dai masu aikin gidanne dan harda wani uniform pink da fari,6oyewa nayi seda suka wuce sannan na fito na shiga cikin gidan ta wannan kofar, ashe kitchen ne komai na ciki pink da fari gurin ya matukar burgeni, kutsawa nayi ta wani kofa dana gani amma miye se naga lock na alphabet, haushine ya kamani amma da na tuna da wani abu senayi murmushi nafara danne danne ai kuwa se gashi inasa enter ya bude ai da sauri nayi shigewata ina kwasan shokiii.
Wasu yan biyu nagani maza wanda baza su wuce ishirin da uku ba suna buga game din kwallon kafa, kowanne sanye da rigar jesse me red colour gasu farare tas kamar larabawa iya had'uwa sun had'u harse da Lipton lipty ta kyasa su.
Bayan nagama dasu na haura sama zuwa dayan falon shima irin wancan lock din nasa ya bud'e wani kya'yataccen falo nagani purple & pink sa6anin nak'asan me golden da ratsin bak'i lallai an narka kudi a cikin gidannan, wasu matan nagani yan biyu da baza su haura sha uku ba suna karatun al Qurani gwanin ban sha'awa seka rasa muryan wanda yafi dadin sauraro, ga k'yau kamar su sukayi kansu nikam gashin ne ma yafi d'aukan hankalina.
Bayan nagama kallonsu na haura dayan stairs din anan naci karo da falon daya chasa wancan dan kuwa wannan mutuwar tsaye nayi kalarsa ja da ratsin ruwan toka yaji royal chairs, wata mata nagani zaune akan sofa tana danne-danne a laptop da glasses a idanunta tanayi tana kur6an shayin larabawa ni inagama balarabiya ce ai fa shiyasa yaran suka gadota, bayan nagama na sake hango wani stairs din wannan karan abokiyar tawa nagani tana dansewa Yasmeen kenan yar gayu akwai ji dakai sedai akwaita da tausayi sosai, earpiece ne akunnenta tasha wando swagger bak'i da top purple kyakyawace domin ta d'ara kowa agidan ita ta fito sak mahaifiyarta da hasken da karamin ruwan.
Komawa nayi kasa inda na baro masu game anan naga wani handsome din wanda dagani yayansu ne domin yafisu girman jiki, yana zaune yana danna waya ya daura kafa daya akan daya yana murmushi da bansan Ko na miye ba, bari dai in leko almajirata inga me suke ciki Allah sarki bayin Allah abun tausayi.
*_INA BAWA MAKARANTA HAK'URI BISA CANJIN SUNAN LITTAFIN DA SUKA GA NAYI HAKAN YA FARU NE SAKAMAKON WA 'YAN SU 'YAN DALILAI INA FATAN HAKAN BA ZAI B'ATA MUKU RAI BA NAGODE_*
♠ *∂ι∂єєуℓσν тαкυ¢є* 🤝🏻✍🏻 http://didi98dotblog.wordpress.com ♠
[6/23, 12:26 PM] Zahra✍🏻: ^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^
🌻♣🌻♣🌻♣🌻
🌹♣🌹♣🌹
☘♣☘
🌹
*♡YAR ALMAJIRA♡*
☘♣☘♣☘♣☘♣☘♣☘
🌹♣🌹♣🌹♣🌹♣🌹
🌻♣🌻♣🌻♣🌻
☘♣☘♣☘
🌹♣🌹
🌻
©🔥ĔL̆ŎQ̆ŬĔN̆C̆Ĕ W̆R̆ĬT̆ĔR̆S̆ ĂS̆S̆ŎC̆ĬĂT̆ĬŎN̆ ✍🏻
*ʂɬơγყ & щγıɬɬɛŋ ცყ:*
🌹Zαняα α.α (Dι∂єєуℓσν)✍🏻
*🌻тнιѕ вσσк ιѕ ∂є∂ι¢αтє∂ ιи нσиσυя σf му ∂єαяєѕт fяιєи∂ѕ gєитℓє, яєαℓѕмαѕнєя, нυввєєу, αυfαиα & ℓιρтσи😘*
_______________________________☘ _Aѕѕαℓαмυ αℓαιкυм ωαяαнмαтυℓℓαнι тααℓα ωαвαяαкαтυн,ιиα вαωα ∂υккαиιи мαѕσуαи ωαииαи ℓιттαfι нαкυяι вιѕα ¢нαиʝιи ∂α αкα ѕαмυ иα ѕυиαи ωαииαи ℓιттαfι вιѕα gα ωαѕυ ∂αℓιℓαι ∂αfαтαи zαкυ fαнιм¢єиι_🤝🏻♠
*🌹 ωαииαи ραʝιи иαкυ иє єℓσqυєи¢є ωяιтєяѕ, gσ∂ιуα ∂α ʝιиʝιиα gαяєкυ мα'αвσтαя куα'ωαωαи ∂αвιυ, αℓℓαн уα кαяα ωα αииαвι ∂αяαʝα, αℓℓαн уα αℓвαякα¢ι яαуυωαя мυ уα нα∂α кαимυ gαвα ∂αуα, αℓℓαн уα ѕαкαωα ιуαуєимυ ∂α gι∂αи αℓʝαииαтυℓ fιя∂αυѕ😘*
_☘ яιкσи αмαиα αвυиє мє мαтυкαя мαнιимαи¢ι, ∂υк ωαи∂α уα¢ι αмαиαя ωαиι тαввαѕ zє ѕнιgα нαℓαкα, яιкσ ∂α gαѕкιуα αвυиє мє ∂'αgα ∂αяαʝαя мυтυи α ι∂σи мυтαиє кαяуα gιиѕнιкιиє мє ℓαℓαтα ∂αиgαитαкα_
_______________________________🌻
♠ *Bismillahir Rahmanir Raheem*♠
*🌹21▶25🌹*
*🌻вσяиσ ѕтαтє*
*♣вαмα ℓ/g*
Allah sarki Noor duk ta fige ta zama wani iri dama ba auki gareta ba gashi kuma ta sake lalacewa, rashin uwa babban cuta ne da bashida magani sedai fatan Allah ya jikan iyayen mu ya saka musu da gidan Aljanna.
Yau anyi sadakar uku kowa ya watse daga su se hajiyar affan, affan da kuma kanwarshi suhaila, kullun a cikin rarrashin su hajiya take kamar kullun yauma suna falo suna zaune ko wacce ta buga tagumi tana tunanin rayuwar duniya dadin dake cikinta da wahalhalun dake cikinta sukam sunga rayuwa domin sun d'and'ana kowani fanni na rayuwa, sunyi rayuwar jindadi na alfarma sun kuma shiga rayuwar ha'ulai sedai godiyar Allah kawai.
Hawayen dake mak'ale a idonta ta share sannan tace "hajiya mun gode da irin d'awainiyar da kukayi damu kuma mun gode da karamcinku agaremu bamuda kalmar da zamuyi amfani dashi domin godiya agareku sedai muce Allah ya saka muku da gidan Aljanna, sannan munaso mu koma gidanmu yau dan Allah" tayi maganar cikin girmamawa.
Kallonta hajiya tayi tana me yaba halayyar yarinyar gata da natsuwa ga hankali da sanin ya kamata "kar ki damu noor ai hakan yiwa kaine kuma ni ina ganinku ne kamar yaranda na haifa, maganar komawarku gida kuma zansa affan ya kaiku zuwa anjima, amma zamanku ku kadai ai baze yiyu ba inaga gwara ku zauna agidannan idan baza ku takuru ba tunda bakuda kowa agarinnan.
Murmushi dole ta yarfa wa fuskar ta sannan azuciyarta tace "mu kuwa muke da yan uwa agarin bama kuma mu mukeda abunda zamuyi tunkaho mu nuna isa ga koma waye amma ayanzu bamuda maraba da shara, umma kin tafi kin barmu acikin rayuwa me cike da kunci".
Azahiri kuwa cewa tayi "hajiya zamufi kowa farincikin kasancewa cikin zuri'arki amma sedai muna masu baki hakuri bisa hakan dan baza mu iya zama anan ba zamufi jin dadi idan muna rayuwa a inda zamu ringa gani kamar umma tana kewaye damu, sedai zamu rika zuwa miki akai-akai".
♣🌹♣☘♣🌻♣
*🌻∂υвαι*
*♣αℓ-qυσχ*
"Mammy! Mammy!! ana jau'anun very very hungry (mammy! mammy!! Inajin yunwa sosai sosai) kwanciya tayi ajikin mammy tana zuba shagwaba,Yasmeen kenan sarkin daru.
Kallonta mammy tayi tana nazarinta Kafin ta maida hankalin ta akan aikin da takeyi a computer tana cewa "if the food is in my stomach then take it out and eat (idan abincin acikina yake seki cire kici) i dont know why you are always lazy (bansan meyesa kike da ganda ba) you better leave here before i decend on you (gwara ki tashi kibar nan kafin inji miki ciwo.
Tashi tayi tana bubbuga kafa ta sauka zuwa kasa, tana zuwa ta samu yan biyu as usual suna karatun al qurani hararansu tayi sannan tace "ai ko kune yaran sarkin makka se hakan, haba kullun aikin kenan sekace ance muku ku kad'aine musulmai" tsaki taja ta sauka zuwa dayan falon.
Anan kuma taga yayan su a falo yana barci tsaki ta sake ja tana cewa "mutun bashida aiki se barcin tsiya da chating Allah dai yasa amishi aure ya bar musu gidansu su huta da zalinci".
Har zata shiga kitchen kuma ta hango yan biyu suna buga game kallon su tayi daya bayan daya kafin tace "aikin kenan dai daga sarakan musulunci se sarkin barci se sarakan buga game kowa da nashi salon se kace gidan haya.
*_INA BAWA MAKARANTA HAK'URI BISA CANJIN SUNAN LITTAFIN DA SUKA GA NAYI HAKAN YA FARU NE SAKAMAKON WA 'YAN SU 'YAN DALILAI INA FATAN HAKAN BA ZAI B'ATA MUKU RAI BA NAGODE_*
♠ *∂ι∂єєуℓσν тαкυ¢є* 🤝🏻✍🏻 http://didi98dotblog.wordpress.com ♠
[6/25, 11:50 AM] Zahra✍🏻: ^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^
🌻♣🌻♣🌻♣🌻
🌹♣🌹♣🌹
☘♣☘
🌹
*♡YAR ALMAJIRA♡*
☘♣☘♣☘♣☘♣☘♣☘
🌹♣🌹♣🌹♣🌹♣🌹
🌻♣🌻♣🌻♣🌻
☘♣☘♣☘
🌹♣🌹
🌻
©🔥ĔL̆ŎQ̆ŬĔN̆C̆Ĕ W̆R̆ĬT̆ĔR̆S̆ ĂS̆S̆ŎC̆ĬĂT̆ĬŎN̆ ✍🏻
*ʂɬơγყ & щγıɬɬɛŋ ცყ:*
🌹Zαняα α.α (Dι∂єєуℓσν)✍🏻
*🌻тнιѕ вσσк ιѕ ∂є∂ι¢αтє∂ ιи нσиσυя σf му ∂єαяєѕт fяιєи∂ѕ gєитℓє, яєαℓѕмαѕнєя, нυввєєу, αυfαиα & ℓιρтσи😘*
_______________________________☘ _Aѕѕαℓαмυ αℓαιкυм ωαяαнмαтυℓℓαнι тααℓα ωαвαяαкαтυн,ιиα тαуα уαууιимυ αиту нαѕѕαиα & αиту нυѕѕαιиα м.υ мυяиαя zαgαуσωαя нαιнυωαяѕυ αℓℓαн уα кαяα яαуυωα мє αℓвαякα, ιиα мιкα gαιѕυωαтα zυωαgα му ℓσνℓу нυввєєу αℓℓαн уα вαкι ℓαfιуα уαѕα zαккαя ʝιкιиє_🤝🏻♠
*🌹 ωαииαи ραʝιи иαкυ иє уσвє/ρσтιѕкυм ωяιтєяѕ αѕѕσ¢ιαтισи, αℓℓαн уα кαяα ωα αииαвι ∂αяαʝα, αℓℓαн уα αℓвαякα¢ι яαуυωαя мυ уα нα∂α кαимυ gαвα ∂αуα, αℓℓαн уα ѕαкαωα ιуαуєимυ ∂α gι∂αи αℓʝαииαтυℓ fιя∂αυѕ😘*
_☘тαявιууα ωαиι gιиѕнιкιиє иα ¢ιкαя α∂∂ιиι, мє тαявιууα zαкα ѕαмєѕнι αвυи ѕσ ∂α ѕнααωα αgυяιи ʝαмαα мαяα тαявιууα кυωα zαкα ѕαмєѕнι αвυи к'ι αgυяιи ʝαмαα, ιуαує мυуι кσкαяι gυяιи тαявιуαитαя ∂α уαяαимυ кσ zαмυ ѕαмυ ∂ανєωα ∂υиιуα ∂α ℓαнιяα_
_______________________________🌻
♠ *Bismillahir Rahmanir Raheem*♠
*🌹26▶30🌹*
*🌻вσяиσ ѕтαтє*
*♣вαмα ℓ/g*
Dr affan ne ya shirya domin mai dasu gidansu, hajiya ma ta shirya domin rakasu gida, batare da 6ata lokaci ba suka dunguma se babban housing estate dake cikin garin bama ayanda yaran sukayi kwatance hakanne dai yasake kasancewa Ita kanta hajiya tayi mamakin ganin unguwar da suka shiga amma daga baya seta alakanta da cewa kila ko aiki su keyi agidan ko kuma mahaifinsu megadi ne agidan.
Suna isa kofar gidan a
Dr yayi parking duk suka fito atare, karamin kofar suka bude suka shiga zuwa part din da aka ajiyesu, kasancewar masu gadin gidan sunsan da zaman su shiyasa babu wanda ya kula da shigowarsu ko wanne harkar gabansa yakeyi, bayan sun shiga sun zauna akan tabarman da aka shinfid'a musu hajiya tace "ashe gidan alhaji muhammad Nura kuke da zama?" ta fada tana karewa d'akin kallo cike da tausayin su.
Noor ce tayi saurin cewa "eh agidan muke da zama muna taya matar sa aiki amma yanzu basa nan sunyi tafiya basu masan da rasuwar umma ba sedai idan sun dawo" tafadi hakanne dan kar wata acikin kannenta tafara zuba kuma kar hajiya tasake yi musu wani tambayar.
Tausayin su ne ya sake cika zuciyar hajiya musanman ganin irin gurin da suke zama acikin irin wannan gida na alfarma wanda tasancewa ai masu aiki sunfi karfin irin wannan gurin amma dai batasani ba ko awaje ne yakeda kyawawan halayya acikin gidan sa kuma mace ke juyi da kujeran sa "shikenan Noor mu zamu tafi ki kula da kannenki kuma ki kasance me yawan ibada da neman tsari insha Allahu babu abunda ze sameku zan ringa zuwa idan na samu time shima affan ze ringa zuwa duba min ku, gawannan kuyi anfani dashi kafin insake muku aike" kud'i ta m'ika musu sannan ta tashi ta gyara mayafinta tayi musu sallama.
Godiya sukayi mata sannan suka mata rakiya har waje kafin suka dawo ciki suka zauna suka dasa wani dandalin kukan saboda kewar ummansu daya addabi rayuwarsu, Noor ce tace bari tashiga kasuwa gurin madam dinta tasanar mata da rasuwar kasancewar karta jita shuru dayawa kuma babu wani labari, dukkan su kowcce tace zata bita, haka suka dunguma zuwa cikin kasuwa inda madam tayi musu rashin mutunci ta kuma koreta wai saboda ta raina mata hankali shine zataki zuwa har wajen kwana biyar kuma bazata sanar da ita dalili ba ko tayi aiken kannenta kota wayar ummansu tabarta da asara saboda babu me wanke mata plate din da zata bada abinci, yanzu kuma jiya tasamu wata saboda haka ta kore ta taje gaba ko zata samu wani guri, haka su kayita kuka suna rokonta amma tayi kunnin uwar shegu dasu, ahaka suka dawo gida suna jimamin abunda ya faru.
♣🌹♣☘♣🌻♣
*🌻∂υвαι*
*♣αℓ-qυσχ*
Tana shiga kitchen ta hadu da Iya zata kwashi abincin masu aiki takai musu, tsayar da ita Yasmeen tayi sannan tace taje sama takawo mata wayarta yanzu yanzunnan.
Haushine ya kama Iya amma yazatayi ai dolenta tayi tunda 'yar gaban goshin alhaji tayi aike inba haka ba zata iya rasa aikinta intayi wasa, ajiye ksysn abincin tayi sannan ta nufi cikin gida.
Tana tafiya Yasmeen ta d'auki abincin Moses ta zuba mishi dakekken maganin barcin data daka da yaji ta juya dakyau yanda babu wanda ze gane musanman kasancewar abincin jollof rice sannan ta dauki lemonshi na zobo ta zuba tablet ta jijjigashi harse da ya narke sannan ta ajiye su amazaunin su ta goge gurin ta wanke hannunta tana dariyar mugunta.
Tana gamawa Iya ta sauko ta rutsina ta m'ika mata wayarta kafin tace da ita akwai wani abun ko zata iya tafiya, batare da Yasmeen ta kalleta ba ta amsa da cewar ba komai taje kawai sannan ta koma ciki ta nufi dinning dan cika cikinta tunda kowa da abunda yake aikatawa ita kam bazata iya jiraba Allah ya gani tanajin yunwa sosai sedai su had'e a breakfast din gobe ko kuma idan ta dawo k'ari zuwa anjima.
*_INA BAWA MAKARANTA HAK'URI BISA CANJIN SUNAN LITTAFIN DA SUKA GA NAYI HAKAN YA FARU NE SAKAMAKON WA 'YAN SU 'YAN DALILAI INA FATAN HAKAN BA ZAI B'ATA MUKU RAI BA NAGODE_*
♠ *∂ι∂єєуℓσν тαкυ¢є* 🤝🏻✍🏻 http://didi98dotblog.wordpress.com ♠