Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Friday, 20 November 2020

MA AIKACIYAR GOMNATI COMPLETE HAUSA NOVEL

adsense here
MA AIKACIYAR GOMNATI COMPLETE HAUSA NOVEL

 

COMPILED BY 

ESHATT SMILER HOM OF HAUSA NOVLS DOCUMNTS


          MA'AIKACIYAR

              GOMNATI

              ⓂⓂⓂ


                   1        By

Asmabaffa      Masoyana naga sakonku sosai na yabo da jinjina kan novel dina na maraicin rahma,ban San Kalmar da zanyi amfani da ita ba wajen gode muku,na gode kwarai Allah ya bar kauna,Allah ya biya muku dukkanin bukatunku na alkhairi.


         LONDON na nufa a 80 jirgi ya saukeni da kyar na hada kudin zuwa ma sabo da jin dadinku readers bazan bari ya wuce Ku ba,wani gida Wanda ya amsa sunansa gida ko a kasar ba duk gida ba,ko ina ya tsaru wani handsome na hango narke a 3seater yana latsa wata dankareriyar iPad ga wata computer new design itama iPad a gefe yana ta aiki ciki hade da danna waya,tun daga yatsunsa nasan kudi da Hutu hade da jin dadi sun ratsashi,don guy karshene wajen haduwa da kyau  OMAR MOHD OMAR kenan dan kimanin 35yrs sunan kakansa yaci.Baban sa mohd  Omar  Ibrahim shahararren dan boko ne kuma dan kasuwa kuma dan siyasa,shi kadai tilo iyayensa suka Haifa kafin rasuwarsu,yan asalin jahar gombe ne,fulanin gombe,babansa ya tsaya masa yayi karatu kafin rasuwarsa,yanzu kam mohd Omar sai yan uwa da suke gombe kawai suka rage masa,yana musu alheri da ziyartarsu, dattijon kirki yayi aikin gomnati kala kala,ya rike mukamai da dama ta fannin siyasa,yayi mulkin siyasa state rep sau daya,house of rep a abuja har sau uku,senator sau daya,ya rike minister sau 2,yanzu haka ambassador ne na Nigeria a Russia.ga kamfanoni da yawa,harkar business iri iri,ya Tara dukiya kadarori barkatai,a takaice dai hamshakin me kudine na gasken gaske dake zaune a abuja birnin tarayya.yana da mata biyu hajia amina itace uwar gida tana da yara uku dan Allah bai bata haihuwa da yawa ba,Omar shine na farko,sai abdullah dan 18yrs sai autarta suleim yar9yrs.matarsa ta biyu hajia rahina yaranta duk matane guda 5 sadiya 27yrs,Aisha 25yrs,zainab 23yrs,naja 21yrs sajida 15yrs autarta.hajiya amina yar kauyen gombe ce,dan haka batayi karatu ba iyakacinta secondary shima bayan mohd Omar ibrahim ya aureta ya sata tayi.ita bata aiki bata zuwa ko ina ta rike yaranta ta basu tarbiya tare da mijinta,


Rahina kuwa da yaranta uku manya duk suna aikin gomnati sunyi degree,kullum sai iyayi a hau mota fuuuuuuu ko wacce ta tafi aiki,in salary yazo ai ta gasa da juna. Baffa yayi yayi su fito da miji tunda sunyi degree amma sunki,shi yasa gidan ya Tara mata rida rida.gashi na bangaren amina sune sukafi kowa kyau,musamman Omar,shi yasa suka kara tsanarshi.


        Basa zaman lfy ko kadan, dan hajiya rahina bata kaunar hajia amina da yaranta,dan amina tana da maza ita bata dasu,ganinta zata fita cin gado,gashi alhaji mohd yafi son amina da yaranta musamman Omar,da wannan yasa rahina dagewa lallai yaranta mata baza suyi aure ba sai ko wacce tayi degree tana aikin gomnati,suma yaran nata a akidar haka suks taso kuma halinta kaf suka dauko,ga karya,rashin mutunci da nuna su wasu ne,a junansu ma basa zama lfy,daga munafunci sai fada a titi,sai gasa da junansu ko wacce naso taga tafi kowa,gasu da bin malamai uwarsu ta dorasu,ita kuwa Allah sarki haj amina mutuniyar kirki ce mace ta gari,abin duniya bai dameta ba,ga hakuri da addini.addua kawai take zabgawa kanta da yaranta musamman Omar dan sunfi kishinsa,shi kam Sam baya shiga harkar kowannensu sai iya nasu dan yaga kannen nasa ba tarbiya.


     Kyakyawa ne na karshe ko shi yayi Kansa iya yanda zaiyi kenan,omar fari ne amma ba kal ba,dan baza ace masa chocolate ba dan ya wuce yakai fari za a kirashi,dogone amma ba zankaleleba dai dai,ba ramamme ba kuma ba me kiba ba,a tsakiya yake da kirjinsa me fadi normal,hancinsa me kyau da tsari kuma baiyi tsini can da yawa ba,gashin kansa Wanda ya tarashi luf dashi baki ga santsi da laushi kamar na India,girarsa me yawa ga kyau,idanu dara dara farare kal,habarsa me dan tsayi,bakinsa das dan daidai lips dinsa su ba pink ba amma kamar light pink.baza Ku sha mamaki ba readers sai danaga yayi daria kusan sumewa zakuyi yanda hakoransa suke yar yar farare kal kal,ga wani dimple nasa,skin dinsa sumul luwai sai taushi laushi da sheki,tana sulbi,kafarsa da yatsu hannayensa duk abin kallo ne da birgewa,cinyarsa da kaurinsa gashi kwance masu kyau,kirjinsa kuwa da sauran jikinsa das suke ba komai luwai luwai.duk inda kuke kallon da tunanin kyau na Omar ya wuce nan.kowa sai ya kalleshi,hattana fararen fata dake London yaba masa sukeyi wajen tsaruwa da kyau,


    Ta bangaren halaye kuwa Omar kusan 95% yake,baya shan komai,baya ko saurarar mata duk yanda suke rubibinshi, yama tsani yan mata shi,basa gabansa,baya shiga harkar kowa,bai damu da matsalar wani ba,sai in ka nemi taimako wajensa zai baka,matsalarsa akwai zucia da saurin fushi,ga girman kai,da rashin fara'a dan baya daria ba komai ke sashi murmushi ba.yana da tausayi in yaganka cikin masifa amma shi baya shiga rayuwar wani bare ya kai masa agaji sai ka nema zai maka,baya son surutu da hayaniya.yayi karatunsa na degree a London ya karanta economics,yanzu yayi masters tuni.bangaren addini kuwa ba a cewa komai yana da haddar ya kai izu 40,banda sauran wasu littafai na addini daya haddace,kuma ba laifi yana aiki da ilminsa,yana kuma addini sosai,baffa ne ya matsa masa kan lallai sai yayi aure,yana 30yrs ya nemo masa auren yar gidan wani governor wato sahar,yar boko ce itama dan medicine ta karanta tana aiki a wani babban hospital dake abj,tana da private nata guda biyu..


   Sahar kyakyawace ba laifi chocolate ce amma tsabar body cream ta dawo fara tas,ga daukan wanka ammafa in zataje aiki.bata ganin kowa da mutunci ganin tana juya naira,motocinta 4 laba laba,duk ma'aikantan gidansu tsoronta sukeyi,sabo da cin mutunci,bata da tarbiya,ba kamun kai,dan a wurin aiki har tafawa take da maza,give me five saleem bam kaji sun kashe.


Haka maza suyi ta yaban kyanta da turarenta gaskia kin hadu,mijinki ya more,tayi ta zancen batsa da mazan aiki.wasu kamilallun matan ma'aikata sunsha bata shawara amma taci musu mutunci,


   Tsiyar sahar bata tsaya nan ba har kan mijinta Omar bata ganinsa da gashi ko kadan,bai San mene aure ba,bai San dadinsa ba,bai San love ba bai tabayi ba,dama baffa ne ya lika masa dole,


     Sahar addini bai dameta ba,ita kawai kudi da aikin gomnati,ga kawaye marasa tarbiyya,a rana sai ta fita sau biyar kullum bata gida,da anyi magana tace aikinta.


Taki yarda ta haihu Sam tace ina bata shirya ba,bataso ta lalace,Omar ma sabo da kudinsu ta yarda ta aureshi,dan ita burinta kudi.Omar gajiya yayi da bakin cikin halinta ya tafi London ya huta,ita kuwa ko a jikinta,ya mata fada da nasiha taki ji,bata bari ya kusanceta sai in bukatarta ce,ko tana son karbar kudi wajensa,shi kuwa baya sonta bashi da feeling a kanta yanayi ne don sauke hakkin dake kansa,shi yasa ma yake tunanin anya yana da lafiya kuwa danshi bai taba jin sha'awar matarsa ba Sam,mata kuma ko inda suke baya kalla bare ya gano matsalarsa.    Amma babban abokinsa sultan yace dan baya son matarsa ne shi yasa,duk ranar daya hadu da real love dinsa zatayi busting dinsa sanannan zai tabbatar lfy yake.Omar kuwa gani yakeyi karyane kawai.yaki yarda kwata kwata,yaje hospital da dama a turai sunce lfy lau yake. Wannan kenan kadan daga the most handsome and sexy OMAR.     Ku biyoni readers yanzu akafara Taku har kullum 


Asmahbaffa.

[5:06PM, 3/10/2018] ‪+234 808 522 6395‬: ⓂⓂⓂ

        MA'AIKACIYAR

            GOMNATI

             ⓂⓂⓂ


                    2


By

Asmabaffa          Nigeria na dawo abuja garin da ake ji da naira.wajen gari na fita gidajen masu rangwamen gata,wanda suke kaiwa da kyar suna yar sana'a,da suke haya a wajen abuja Kafin a karasa cikin garin abuja,dai dai gefen titi na hango wata yarinya tana saida apple da dafaffen kwai,a titi take bi tana mikawa ta window na mota,apple and egg tana bi mota mota a round tana dagawa masu mota domin su siya,


Kallonta nayi sosai yarinya ce yar kimanin 15yrs ta hada gumi sakamakon ranar da ake zabgawa,sanye take da wata yar doguwar Riga ja da kadan ta wuce gwiwarta,rigar taji jiki ta kode ta jeme,ta fita daga hayyacinta da dankwalinta baki,amma kana kallon yarinyar fes da ita rigar kar kar ba dirty,da gani gidansu da tsabta,


       Yarinyar na kurawa ido na kasa dauke idona  sabo da tsananin kyau da tsarin sura na wannan yarinya,kerarriyar yarinyace me cikar zati,dan kana kallonta Kazan ta hada jinsi da larabawa basai an fada ma ba,da gani nan gaba za ayi mashahuriyar budurwa,duk motar data wuce sai ta kalleta wasu har tsayawa sukeyi suce suna sonta,


  Santala santalan kafafunta na kalla na jinjina kai,sama nayo naci karo da makeken hips dinta da tudun mazaune wasu das dasu,nan nace to fa yarinya karama kenan nan gaba fa za asha kallo,ina yin gaba naga idon garin wato boobs dinta suma dai basu girma ba kananu yanzu suke tasowa nan gaba suma uhmmm...wuyanta na kalla naga wasu yan digo digo baki sun kai biyar Wanda ake Kira tawadan Allah, wuyanta mul dashi kadan ake ganin kashi,


       Fuskarta na tafi sawa ido,bakin nan na hango light pink dan cut,lips masu matukar kyau,hakora kanana tas farare,hancinta na kalla me kyau da tsayi gami da tsini amma ba mai yawa ba,da digon baki dis a kan hancin Wanda ya kara kawata fuskarta,idanu dai dai ba manya ba ba kanana ba farare tas kamar madara,


    Gashin kanta Wanda yayi luf har gaban goshinta ga saje kadan yala yala baki sidik,bata da girman goshi lol,gashinta ta tubke jelarsa har ya wuce tsakiyar bayanta,


Sa idona bai tsaya nan ba readers sai Dana kai kallona wajen kunnenta kanana masu kyau,fara ce kar,rana da wahala ma yasa ta danyi duhu a hakan.tallanta kawai takeyi a titi bata sauraran kowa,wasu dan kyanta suke siya,wasu dan ta kulasu su sami damar lalata mata rayuwa,shi yasa bata kulasu sam,dan haka tana zuwa talla take siyarwa,


      Wata yar yarinya na gani baza ta wuce 9yrs ba me kama da me tallan apple da egg ita amma sai dai a kirata da light chocolate dan ba fara kar bace,hannun me saida apple ta kamo tana anty IKLAS kizo inji ummi tallan ya isa,wai yunwa mukeji ki dafa mana abinci,


   Hannun yarinyar iklas ta rike tana murmushi ok suhaila dama yanzu zan dawo gida,ya schl?normal anty,ance ban biya kudin books din da akace mu siya ba,ranar Friday za a rufe.


     Sorry baby akwai kudin zan baki gobe never mind,botikinta ta dauka dan tuni egg ya kare apple saura Leda biyu,gida suka wuce ita da kanwarta,nima na rufa musu baya,tafiya sukayi ba wani nisa da titi wani gida suka shiga Wanda zai iya zuwa na 3 a lalacewa kaf gidajen dake unguwar suna cikin mafi rangwamen gata.


      Gidane na bilon siminti amma kamar kango tsabar lalacewa,daki biyu ne,sai toilet Wanda rabin katangar toilet din na karfen langa langa ne,sai kitchen dinsu suma na langa langa ne,gidan ko ina da simintinsa a dabe yake,dakinsu kuwa duka ledar tsakar dakice kusan sabuwace ma,abin mamaki wani bed na gani na gaske kalar na kasar waje yasha katuwar katifa,ga wata spare katifa jingine a bango,gefe guda wasu kayan kitchen ne dana cin abinci na gaske masu tsada a katon kwali har biyu,gefe can wata sip ce itama kalar bed din da gani ansha wuya wajen shigarta dakin,rabin sip din kayan sawarsu rabi kuma suke boye kayan abincincinsu da sauran tarkace,Duk a daki daya,daya dakin kuwa Leda ce da center carpet me kyau kuma da gani me tsadar gaske ne,nayi mamaki,wasu kujeru na gani na alfarma 3 seater 2 seated da 1seater,da badan ginin marar kyau ba da palon yafi haka kyau,wata TV na gani katuwa me kyau kamar plasma tsarinta girke a kan wani glass TV stand,


     Gidan ko ina kal kal yake sai kamshin turaren wuta ke tashi,wata dattijuwa na hango a zaune tsakiyar tabarma tana fere doya,na kare mata kallo wannan sai dai a kirata kakarsu amma ba ummi ba da naji sun fada,jikinta suka zube wash ummi tsohuwa me ran karfe,mun gaji,ko wacce tana ta dakuna tsohuwa tace dalla Ku dagani zaku karasani,sai warin rana kuke,ke faratu tashi ki mana girki,kiyi wanka ki huta,gashi na rage miki hanya.na fere doya,na miki jajjage,to ummi na gode,bari nayi sallah tukun.


Sallah tayi ta shiga kitchen.faten doya ta yi musu sannan sukaci,wanka tayi ta shirya kanwarta suhaila ta rike hannunta sukawa ummi sallama ummi mun tafi islamiyya daga can zamuje kasuwa domin saro apple zamuje ma gidan gona siyo kwai sabo da siyarwa gobe,addua ta musu suka wuce.


      Wai wace IKLAS NE


      Babansu abdurrahman saddiq dan asalin kasar libiya ne,balaraben libiya a can wani kauye a yankinsu,ruwan sama aka musu mai matukar yawa Wanda ya haddasa ambaliyar ruwa a yankin,da kyar aka samu aka ceci mutane ba Sufi 10 ba,wasu kuma mutum biyar suka taimakawa Kansu da rakuminsu suka yo hanyar Nigeria,su kwana su tashi a sahara har Allah ya kawosu Nigeria,har suka sauka a jigawa state da rakumansu,maza ne su biyar,haka suke fadi tashi a kauyukan jigawa,ciki harda abdurrahman saddiq babansu iklas kenan,ana haka har mutum biyu suka rasu suka rage saura 3,sauran biyu suka koma libiyansu suka bar abdurrahman a Nigeria,yasha wuya yasha talauci a kauyuka,har ya fara Aron gona yana noma,da haka yaci gaba har ya fara samun kudi,ya mallaki gonaki, a wani kauye dake cikin roni nan ya hadu da abu bafulatana wato Babar su iklas,kishiyar babar abu ce ke gallaza mata kasancewar kafin Baban abu ya rasu sun rabu da babarta,shi yasa ya kwace yarsa abu ya bawa matarsa riko,


      Nan abdurrahman ya fada sonta ya tausaya mata,da haka ya dage saida aka aura masa abu,bayan aurensu arzikin abdurrahma ya shahara ga kauyen ana masa sharri dan mafiya,haka abu ta haifi iklas wacce sak babanta ta kwaso,daga nan ya kwashesu suka koma abuja da zama tare da Babar abu wato hajia asmau,wacce yanzu suke hannunta kenan,suke kiranta da ummi tun tasowarsu sukaji mamansu da abbansu suna kiranta ummi shi yasa suka saba suma.har yau suke ce mata ummi,


      Abdurrahman sai da ya mallaki gida a abuja ga har noma ta haka ya biya musu aikin hajji sannan ya ziyarci kasarsa ya nunawa matarsa yan uwansa maza guda biyu da suka rage a duniya,haka gaj asmai ummi kenan,duk ya hada musu hanyar da ko sabo da halin rayuwa zasu iya Neman yan uwansa,


      Bayan suhaila Nada shekara 7 da haihuwa abu maman su iklas da mijinta abdurrahman Baban su iklas suna hanyar dawowarsu daga jigawa zuwa abuja suka tafka hatsari inda Allah yayi musu rasuwa,dukansu,anyi jaje da jimami,yayinda kakarsu ummi ta kira yan uwansa ta sanar musu,har Nigeria sunzo,kuma sun bawa su iklas nasu gudunmuwar,dan suma ba yan uwansa na jini bane,dangi ne kawai sama sama shi yasa basu dauki su iklas ba suka koma kasarsu,


       Ummi kakarsu iklas ce taci gaba da kula dasu,tana sana'ar saida kayan miya,irin su citta,maggi,manja,wake,barkono etc,har abincinsu ya kare,kudin hannunsu ya kare,komai nasu ya kare kat hattana kudin makarantar su babu,lokacin iklas tana ss1,suhaila na primary 2,da haka suka yanke shawarar saida gidan da suke ciki,haka suka siyar da gidan Ganin matane yasa aka cucesu sosai aka siyi gidan arahar banza,


Da haka suka tashi suka koma wajen abuja gidajen dake kusa da garin abuja kafin a karasa cikin city,anan suka sayi wannan gidan da suke ciki,an musu tsada sosai anan kudin ya kusa karewa,shi yasa suka ebo wasu kayan na gidansu da suka siyar Wanda zasu iya amfani dasu suka zuba a gidan da suka siya,


Sun biyawa suhaila kudin makaranta tun daga primary 2 zuwa jss3 gudun kar a sami matsala,abinci suka jibge  komai da suke bukata sai da sukayi dai dai kudinsu,har da jarin kwai da apple,ita kuma ummi takeyin sana'ar siyar da kayan miyarta a gida,


     Islamiyya ma sun biya kudinta na shekaru,iklas ma an canja schl me saukin kudi,ta biya daga jss2 har zuwa ss3.ga saida apple da egg,tana dawowa daga schl zata wuce tallanta, zuwa 4 su tafi islamiyya,haka suke rayuwa har yanzu sun kwashe 2yrs.


    Yanzu komai ya dagule musu,da tallan da iklas ke zuwa da sana'ar kakarsu ummi suke ci suna sha,da sauran abubuwan rayuwa Wanda ya zama dole.


     Iklas bata da burin da ya wuce tayi karatu me zurfi tayi aikin gomnati dan ta tallafawa kanwarta da ummi,bata da burin da ya wuce tayi aikin goMnati,gashi aikin gomnati na burgeta, ita ko me aikin gomnati ta gani a titi to birgeta takeyi,ko ji tayi ma'aikata na labarin wajen aikinsu to sai ta tsaya ta saurara.


     In tana tuno aikin gomnati ita kadai zaka ga tana daria,idan kana so kaga dariarta ko jin dadinta to ka mata adduar Allah sa ki zama ma'aikaciyar gomnati ko ta company,dan haka duk layinsu in ta wuce ko abokanan tallanta zakaji ana gomnati gomnati wasu suce ma'aikaciya,arnan ko gwarawa da marasa jin Hausa da suka Santa sai kaji suna kiranta the manager.murmushi take musu sosai,


Indai kana so a nuna ma gidan su iklas to kace gidan su gomnati ko ma'aikaciya,ko gidansu  manager.


  Ya halayen iklas sukeneAsmabaffa

[5:06PM, 3/10/2018] ‪+234 808 522 6395‬: ⓂⓂⓂ

       MA'AIKACIYAR

            GOMNATI

             ⓂⓂⓂ


                    3


By

Asmabaffa
     Readers kar Ku gaji da hakuri da typing error sometimes ba time na editing.tnx
         IKLAS nutsatsiyar yarinya ce kamila,ga addini hankali da sanin ya kamata,ga kamun kai,tsabta da son kwalliya,bata so ace taci baya sai gashi talauci yasa ta zama sai a hankali,gata da kokari ita da suhaila,gaskia iyayensu sun iya tarbiya kuma Allah ya amsa adduarsu ya basu yara nutsatsu,ga yarda da kaddara,Sam basu dau duniya da zafi ba.


     Iklas bata da tsoro,tana da hakuri amma indai ka tsokaneta ko ka rainata to fa ba mutunci,bata kyalewa,gata tana da surutu amma ba me yawa ba,itama akwai zucia,gata da fara'a da mutunci da karrama dan Adam shi yasa kaf yankin da suke kowa ya Santa kuma ana sonta maza da mata,komai nata a nutse,ita sam bata son raini,Suhaila ita bata fiye son surutu da hayaniya ba. In dai kaje unguwar su iklas baka isa ka nunata da yatsa ba yanzu matasa yan unguwar zasu hada ma jini da majina,shi yasa suke zaune gidansu lfy.


      Ummi ma tana fitowa za kaga ana kwasar gaisuwa sabo da iklas ta siyo musu mutunci.wannan ne asalin da tarihin iklas .          Ci gaban labari


      Baffan su Omar ne ya kirashi a waya,Omar na daga wayar baffa ya fara fada haba Omar kasan ina Russia na bar ma komai na business dina a hannunka ga iyalinka can na jiranka amma ka tare a London kaki dawowa,bayan Kaine babba wa zai kula da harkata in ba kai ba,kasan kannenka basu da hankalin da zan dorasu kan harkata,pls ka koma gida nan da 3days.cike da ladabi yace alright baffa insha'allah zan koma yanda kace,dadi baffa yaji that's my son,yana son Omar sosai.


     Omar kuwa nazari ya shiga yana tunanin yanda zai je ya hadu da mahaukaciyar matarsa wacce take bata masa kullum wato sahar.amma ba yanda zaiyi dole yabi umarnin baffansa ya koma Nigeria,


      Yana cikin wannan tunani sahar ta mako masa kira,tsaki yayi hade da daga wayar dan yasan kudi zata roka ko wani shirmen,ba ko gaisuwa kawai ya London tace sannan tace baby wlh kudin da ka bani sun kare kuma gashi za muyi bikin wata yar wajen aikin mu,


   A hankali yace yace OK zan miki transfer,yanzu ke sahar baza kiyi hankali ba,yanzu haka ake kula da miji.ganinki kinyi dai dai,tunda na bar gida ko kirana bakiyi ba,kiji tsoron Allah sahar,kiyi amfani da damarki kafin ta wuceki,kunkuni ta fara yanzu ya kake so na maka,kullum bani da time fa busy nake,kasan aikin mu ba daga kafa,ke kullum Aiki aiki baki da wani abu sai aikin gomnati.


      To ni kaga karka dameni dan ka samu na kiraka,da bukatarki ta taso ba,ae hakkinkane ai taja tsaki hade da kashe wayar.omar sarkin zucia har zucia ta kawoshi wuya,take idonsa ya canja,sai bacin rai da huci yakeyi.


       Mama ya kira a waya suka sha hira ta hadashi da kannensa suleim da abdullah sun sha labari.yau ne ranar da omar zai dira a Nigeria,karfe 4:30pm mama,suleim da abdullah suka dauko handsome daga airport,sai murna sukeyi cike da kasaita ya bisu suka wuce gidansu na alfarma.tunda yaran hajia rahina wato umma sukaji labarin saukar Omar suka fara gulmace gulmace,hassada da bakin ciki,ko wacce part dinta daban amma su umma wato rahina sun dami rayuwarsu sabo da mugun halinsu.


    Sadiya ce ta parker motarta kuuuuuuuu ta fito dawowarta daga wajen aiki kenan,direct part dinsu ta wuce,duka yan matan kannen nata da umma suna zaune suna gulma da zage zage,sadiya ma zama tayi dabar kasancewar ita ce ba,umma kice tsinanne ya dawo kasar,Aisha tace na tsani yaya omar wlh waishi dole me kyau,me kudi,umma tace duk Ku saurara shi din banza wlh sai nayi maganinsu gaba daya har uwar tasu,


      Zainab tace wlh umma karki daga musu kafa,naja tace har mu zai nunawa kudi aikin banza wai wannan sahar din matarsa har ta isa ta ganni tamin kallon banza,yanda take ji ita me kudi ce muma haka,domin aikin gomnati ne muma shi mukeyi,


      Sadiya tace hmmm umma zatayi maganin ogan nasu ai,haka suka kai har dare suna zage zage,a karshe suka yanke zasu je masa sannu da zuwa don sugano kwakwaf,


    Ita kuwa baiwar Allah mama tasa danta gaba yaci ya koshi dan tasan matarsa ba matar kirki bace,addua take Allah masa canjin alkhairi,amma ita kam wulakancin sahar ya isheta,nasiha ta masa sosai tare da Jan kunne wajen dagewa da addini,sannan ta turashi kan dole yaje ya gaida hajiya rahina umma,


Badan yaso ba bayan sallar isha ya isa part din,da zuwansa ya gansu a Palo rida rida a kwance ko wacce na latsa waya,umma na gefe,suna ganinsa dukkansu gabansu sai daya fadi dan mugun tsoronsa sukeyi,ga kwar jini da yake musu, Sam baya musu ko murmushi,dama duk zaginsu a bayan ido sukeyi,risunawa yayi ya gaida umma,da kyar ta amsa tana masa kallon harara,su kuwa yan matan kowacce yaya sannu da zuwa ka dawo lfy,lfy kawai yace ya ficewarsa cike da kasaita 

    Yana fita suka dasa gulmarsu kunga maye yanda ya kara kyau ga iya daukan wanka,ko wanne kaya yasa kyau suke masa.wurin mama ya wuce ya roketa kan ta barshi ya kwana gobe sai ya tafi gidansa,kyaleshi tayi dan tasan matarsa ba kula take dashi ba,


       Suleim tana manne a jikinsa sai bacci takeyi,washe gari da safe uban yan daukan wanka omar sakkowa yayi daga sama yana zuba kamshi,sanye yake da wani yadi fari Sol ya matukar masa kyau,hattana takalminsa fari ne,ba hula a kansa sai gashi kwance luf.sallama yawa mum bayan ya cika tumbinsa ya basu tsaraba,wucewa yayi gidansa dake zone 11princess suit,gidan ya tsaru,


     Driver ne ke tukashi har gidansa,tun daga compound yake jiyo hayaniya sama sama,a nutse ya shiga palon da sallama,frnds din sahar ya hango arna da musulmai maza da mata suna jin kida hade da hira,ga kayan ciye ciye nan,


    Ran omar ne yayi mugun baci suna masa magana amma ko kallon su baiyi ba ya wuce room dinsa,ita kuwa sahar baki ta tabe hade da Jan tsaki,


    Saida wata kawarta zuby tace sahar kije wajen mijinki kinga kamar ransa ya baci,tsaki sahar ta ja to sai me yanzu akansa zaku tafi haba mana frnds,next time zamu dawo yanzu kije wajen mijinki cewar wani saleem abokin aikinsu,bata so ba suka tafi ,yar aikinta ta bugawa tsawa kan tazo ta gyara wajen,direct dakin Omar ta nufa tana cika tana batsewa,sanye sahar take da T-shirt baka da skert din atamfa sun kamata kam,kanta ko dan kwali babu,


     Tana shiga ta ganshi kwance kan gado yana latsa waya,baki ta turo ta kare masa kallo gaskia mijinta me kyau ne,ga iya wanka,a nan take sha'awar Omar ta motsa mata ba abinda takeso sama da ya biyaa mata bukatarta,gashi tasan fushi yake yi yanzu bare ya mata abinda take so,


       A gefen gadon ta zauna sannu da zuwa baby ya hanya?tunda yaji haka yasan tabbas sahar wani abun take so ya mata,dan bata aikin banza sai da dalili,ko kallonta baiyi ba,sha'awace ta kuma lullubeta tace baby kayi hakuri nasan na ma laifi,kallonta Omar yayi tabbas yasan da dalili,sahar baza ta taba bashi hakuri ba tare da kudirin wani abu ba,a hankali yace ya wuce,in mutum yayi da kyau shima ya sani in ya bata ma ya sani,kisani ke baki isa ki sani bacin rai ba,Wanda ka damu dashi shi ne in ya bata ma rai kake damua,sahar taji haushin kalamansa amma sabo da tana neman wani abu tayi shuru ta kara cewa am sorry hade da hayewa kan bed din,yana kallonta  ya gano me take nema,sha'awa ya hango zalla a idonta,kwancia tayi a kirjinsa,dan sahar ita bata da kunya ko kadan.


       Shafashi ta fara tana wani shagwaba,babyna I missed u alot,tabe baki yayi yana kallonta ta fara cire masa Riga,baya son ya wulakantata,kuma yasan hakkinta a kansa musamman da ya tafi London ya Dade bai dawo ba,sabo da wannan  dalilin ya biye mata yayi manage ya biyamata bukatarta,sahar tana jinta zam zam dan Omar gwarzon maza ne ya tsaya ya biya mata bukatarta sosai taji dadi har jinjina iya sex na Omar takeyi,guy ya hadu ta fannin romance da sex,ni kuwa nace danma ba zabinsa bace ke,bashi da feeling akanki.


      Sahar tana jin zam zam ta mike tayi ficewarta,shi kuwa Omar baiji wani dadinta da yawa ba dan sahar ko dan gyaran da mata keyi na shan tsumi bata yi Sam,ita fa indai ba aikin gomnati ba to bata ganewa komai.washe gari Omar ya shirya tsab cikin suit baka yayi kyau yana baza kamshi ya sakko cike da takama da kasaita,dakin sahar ya shiga tunda ya tashi bai ganta a bed dinsa ba,room dinta ma wayam bata nan,Palo ya zo ba kowa sai hindatu me aikinta,ina sahar take cewar Omar,har kasa hindatu ta duka ta gaisheshi da sakin fuska ya amsa,yanlabai ta tafi wajen aiki tun 6am wai tana da tiyata,


   Tsaki yaja ya fice gaba daya daga gidan ko dining bai kalla ba,yana mamakin yanda sahar ta rainashi ace matarka ta fita ko fada ma baza tayi ba,tsaki yaja hade da ci gaba da karanta jaridarsa yayinda ya kame a bayan wata luntsumemiyar motarsa Wanda takai milyan 40,driver ke gaba yana tukashi,shi Omar Sam bai damu da driving ba yafi so a tukashi kaji manya fa readers.


    Hadadden gidansu yace a kaishi direct wajen mama ya nufa,a Palo ya sameta tana turaren wuta rungumeta yayi hade da gaisar da ita,mama kintashi lfy?lfy babanmu ya gida,great mama,to alhmdllh.mama breakfast fa?juyowa tayi da alamar tambaya gidanka ba a baka ba,wlh mama kin San dai komai,yan aiki keyi ni kuma kin San bana son kazanta,kuma yau mama inaso naje na duba gidan gonarki da kike kiwon kaji,kinga an Dade ba a duba ma'aikatanba da sauran abubuwa,murmushi tayi yawwa babana Allah maka albarka,da har na yanke shawarar zuwa da kaina,haba mama da raina da lafiyata na barki ki wahala.to Allah maka albarka.su abdallah suna schl ae ai ka sani.OK.


     Haj amina tana da shahararren gidan kiwon kaji dake wajen garin abuja,baffan su Omar ne ya gina mata ya bata kyauta ganin haj rahina na aikin gomnati shi yasa ya bata wannan kyauta.

Haj rahina umma ta tafka bala'i akan wannan kyautar ta baffa,haka ta hakura.


    abinci yaci ya koshi yawa mama sallama ya wuce office,karfe 2pm ya bar office ya wuce gidan kajin mama.


   Asmabaffa

[5:06PM, 3/10/2018] ‪+234 808 522 6395‬: ⓂⓂⓂ

      MA'AIKACIYAR

           GOMNATI

            ⓂⓂⓂ


                   4


By

Asmabaffa      1:30pm iklas ta shigo gida ta dawo daga tallanta,domin schl din da ta koma 8to12 ce ta irin manyan mutane ce Wanda basuyi karatu da wuri ba,irinta ta koma sabo da tallan da take zuwa domin da shi suka dogara,dan haka 12 tana dawowa zata tafi talla kan titin kwalta,1-1:30pm ta dawo,tana cin abinci zata shirya ta tafi saro apple da egg,tana dawowa sannan suhaila ta dawo sai su shirya su tafi islamiyya,Saturday Sunday kuwa da safe take zuwa talla zuwa 3 to 4pm ta dawo,haka take rayuwa kullum ba Hutu,gashi watarana har girkin gida ummi take sata dan bata so iklas tayi aure bata iya girki da sauran ayyuka ba,dan haka take sata dole,shi yasa ta iya komai dama gata jaruma,


     Wanka tayi ta shirya cikin wata yar rigarta doguwa itama wata Igbo ce ta bata ita,light blue ce me ratsin ja ja da digo digon baki,daga sama ta dan matseta kasa ta bude amma itama da kadan ta wuce gwiwarta,basu da kayan kirki,dan ma waiyayenamure na taimakawa su basu kayan da suka musu kadan,wasu kuma har sabo suke basu,ita ma suhaila tana samun na yaransu,wasu kuma iklas na kokarin sai musu gwanjo,shi yasa kusan kayansu gaba daya English wears ne,tsangalallu ne badan suna sa dankwali ba sai ka dauka arnane suma saboda rashin wadata.to daya suke samun na ci ma.


     Bakin gyale siriri ta yana kanta,batayi kwalliya ba powder ta shafa kawai sai Vaseline da ta shafa a lips dinta,tayi kyau dama me kyau ko ba kwalliya me kyau ne,wani takalmin roba me igiya baki ta saka,shima wani ne da yake siyarwa ya bata kyautarsa yaga tana da hankali,ga babu ta zauna musu.tayi kyau sosai a nutse ta dauki botikin saro kwai da ledar siyo apple ta yiwa ummi sallama ta wuce,a kofar gida suka hadu da suhaila ta dawo daga schl,anty har kin shirya?yeah iklas ki jirani muje tare mana,no je kici abinci ki huta ki shirya zuwa islamiyya kafin na dawo OK.OK anty sai kin dawo,Allah tsare shafa kanta tayi ameen suhaila,tana matukar kaunar kanwarta.


      Tafiya tayi da dan nisa ta isa gidan kaji domin siyo kwai da apple,mutane da motoci birjik sunzo sarin kwai da apple suma,gaskia kowa ya kalli gidan gonar yasan an kashe dukiya,part part ne wurin kaji da kwai daban,part din fruits daban,kifi daban,ga sauran tsuntsaye da abubuwa kala kala.


    Da araha suke bada sarin shi yasa ake cika gidan gonar,shi yasa iklas ke saro nata can dan ba karamin riba take ci ba,ratsa ciki tayi ta shige,ma'aikatan ciki sai fara'a suke mata suna gaisawa,dan sun saba da ita,gashi sun karanci nutsatsiya ce me mutunci da kamin kai,suna tausaya mata mace kamar ta tana sa'a irin wannan,da gani suna cikin talauci,shi yasa suke Mata arha fiye da kowa.


          Tana tsaye tana jiran a sallami Wanda suka rigata, wata arniyar mota ta shigo cikin wurin,kowa bin motar yake da kallo,babu Wanda ya taba ganin kalar motar,har jira ake aga waye me motar,


    Ita kanta iklas duk tsaiwarta a titi bata taba ganin mota irin wannan ba,su kuwa ma'aikatan gidan sun San bazai wuce Omar ko mama ba.sun San irin wannan babbar harka sai iyayen gidansu Wanda suke jin dadin aiki karkashinsu,shi kuwa Omar tun shigowarsu kansa na kasa yana duba jarida,driver ne ya fito da sauri ya bude masa kofa,subhanallah shine abinda iklas ta furta a ranta ganin takalmi da kafafuwan Wanda ke fitowa,


     Basu gama sumewa ba sai da Omar ya fito gaba dayansa daga mota,wani daddadan kamshi ne ya mamayesu gaba daya,iklas tana kallonsa gabanta ya fadi ji kake daram dam,sunga zallar baiwar kyau da kwarjini da cikar zati,iklas tace tab yau ga Wanda ya takeni a kyau,ido ta lumshe hade da bude kafafen hanci tana shakar ni'imantaccen kamshin Omar, shi kuwa Omar iklas ya fara hangowa da tsangalalliyar rigarta,kasancewar fara ce kar sai ta haske gidan. Gonar gaba daya,kallo daya ya watsa mata shima gabansa yayi mugun bugawa,bai taba ganin dan Adam me kyanta ba,duk kyansa sai yaga ga wata yarinya ta fishi,shi bai taba jin faduwar gaba ba sai akan wannan tatsitsiyar yarinya,


     Fuska ya yatsina kamar yaga kashi yayi mata kallon kaskanci ya wuce ta gabanta,da mutanen wajen maza ya gaisa ya mika musu hannu,sannan suka dan kebe da babban me kula da wajen suna magana.


   Iklas kuwa ta cika fam sabo da irin kallon banzan da ya mata,bata son raini,dan suna talakawa shine zai yatsina mata fuska,hmm duniyace a ranta take wannan magana,ana haka har akazo wajenta aka cika mata botikinta ta mika kudi,lokacin Omar ya gama da wajen kwai ya wuce wajen fruits,da kyar take daga bokitin ta karasa wajen fruits itama ta mika kudi aka cika mata katuwar ledarta da apple,ta juya zata wuce sukayi karo da  da botikin kwanta tayi karo da mutum gwaraf,amma batafi saman cikinsa ba,botikin kwai ya tuntsire wajen guda ashirin sun fashe,shi kuwa take yaji wani mugun shock a jikinsa zirrrrrrrrrrr wanda bai taba ji ba,sakamakon haduwar jikinsu,daurewa yayi ya dawo hankalinsa,tsaki yaja ya furta psycho kawai,haushi ta karaji ya mata abu maimakon hakuri sai zagi,ledar hannunta ta apple ta ajiye gefe,gabansa ta sha ta rike kugu hade da harara,malam kamin laifi da barna ka kasa bani hakuri sannan ka zageni,da nayi niyyar yafe ma amma wlh tunda ka zageni ka kasa bani hakuri to ba kira ba abinda zaici gawayi,sai ka biyani each and every egg da ya fashe,dan akanka bazan dauki asaraba,


      Daria yace ta kamashi ya danneta,bai taba haduwa da funny girl haka ba sai yau,yar yarinya da Karin magana haka,ga masifa har wani jijjiga takeyi gaban katon namiji kamarsa.


      Allah ya taimakesu ba wasu mutane wurin sai masu shirya fruits,tasowa sukayi daya daga ciki yace haba gomnati basai kinyi fada ba za a biyaki,shine me wajen,a fusace tace dama haushinsa nakeji ni time din daya shigo yamin kallon Tara saura kwata,dan haka wlh sai ya biyani,tofa wannan yarinya da kuruciya sosai kanta ga tsiwa cewar Omar aransa. Wasu ma'aikatanne suka zo wajen suna haba gomnati ikon allah bamu sanki da haka ba,wani ciki yace the manager wannan oganmune fa,murmushi ta saki jin an kirata da sunan da tafi  so wato gomnati, Wanda ya tafi da imanin Omar, tace to na yafe masa sabo da Ku


      Gefe ta matsa tana gyara bokitin kwanta hade da kunkuni kawai an cuci mutum,wannan days fashe ni haushina ma daya asararsa da akayi,yanzu wannan ya ishemu mu soya muci da su ummi har na 5days,ko mu soya doya da kwai ta kwana biyu,ai kuwa da munci dadinmu.duk surutun nan da takeyi Omar na jinta,sai daria yakeyi a zuciyarsa,yarinyar so funny,ya dade rabon da yayi nishadi irin na yau,kwai aka kawo mata guda 100 a Leda,kallon mutumin tayi laaaa ai nace na yafe masa wlh,ai oga ne yace a baki gashi guda 100 ma aka baki kinci riba...no na yafe ai,fafur iklas taki karban kwan nan,,sunyi sunyi taki karba,Omar ne ya karba hade da daka mata tsawa karba ban son shirme,tsoro ne ya kamata,taf aka cika botikinta da kwai,aka kara mata apples da yawa sannan aka mika mata kudinta,mamaki tayi sosai ta kalli Omar a tsorace na gode oga Allah kara arziki,sosai yaji dadin adduar ta matarsa bata taba masa ba,sai wata a titi,it's OK zaki iya tafiya, uhm....uhm.....dama oga dazu kaga fadan Dana ma,nayi ta masifa rainane ya baci kanwata na aika taki zuwa,shine raina ya baci,amma maganar gaskia bada kai nake ba,da kanwata nake.


    Murmushi Omar yayi Wanda yasa iklas sandarewa ganin kyau da dimple na Omar,shi kuwa a ransa yace yarinyar nan da wayo take.a fili hade rai yayi ya tabe mata baki ya shige mota driver ya ja suka wuce.itakam taji haushin tabe mata baki da yayi,ya rainata.anyway sun sami kudin abinci lallai yau tazo a SA'A.


     Yau taga lailatulqadari sunan da ta lakabawa Omar kenan kayanta ta dauka da kyar ta nemi taxi,kayan sun mata nauyi,ga murna an vata komai kyauta,shi yasa yau ta shiga taxi,ta matsu ta koma gida ta bawa kaka ummi labari.Asmabaffa

[11:56AM, 3/11/2018] ‪+234 803 630 0627‬: ⓂⓂⓂ

     MA'AIKACIYAR 

          GOMNATI

           ⓂⓂⓂ


                  5


By

Asmabaffa   

         Har kofar gida me taxi ya sauketa da kayanta,da sauri ta shiga da kayan ta fara kwalawa ummi kira tsohuwa kaka ummi...ummi...tsohuwa wai kina ina haka,ke lfy kike rafka min kira haka kamar kina bina bashi cewar kaka ummi,iklas ce ta rungume ummi tana ummi lailatul kadari na gani yau,kinga yau komai kyauta aka bani kwai da apples ummi sai nayi 1wk banje sari ba,duk na kyauta zan siyar,kinga kudin yanzu zamu tafi kasuwa dama abincin mu saura na kwana daya,


      Kaka ummi ce ta kalleta da murmushi tana mai cike da farin cikin kalaman iklas,to iklas wai waye lailatul kadari naga ta kaina yar nan karfa kiyi mana sabo,ummi oga ne me gidan kajin ya bani komai kyauta,nan ta kwashe labari ta fadawa ummi,ummi taji matukar farin ciki,dama basu da abinci ba kudi,


To alhmdllh iklas kece wacce ta iya tsari da lissafi sai muyi shawara,ai ummi yau baza mu islamiyya ba,dan kasuwa zamuje da suhaila,Biro da jotter ta dauko suka zauna a tabarma nan iklas ta fara planning,dama iklas akwai iya planning din rayuwa,nan ta rubuta abubuwan da suke bukata ta tsara komai,ta bawa ummi na cefane taja hannun suhaila suka wuce kasuwa.


     Omar direct gidansu ya wuce wajen mama,cike yake da tunanin yarinyar da yaji ana kira da gomnati ko manager sunan ne ya bashi daria,ya kara nanatawa a ransa bai San sanda ya saki murmushi ba,nan take ya shiga tunanin yanda take masa tsiwa a gidan gona,a haka ya karasa palon mama


    Zaune ya sameta suleim na gefenta suna game ita da abdallah,sallama ya musu ya kwanta Shana Shana cinyar mama yana shagwaba sai shafa masa gashi mama keyi tana wani lallabashi,dining ta jashi ta zaunar dashi,da kanta take bashi a baki har ya koshi,


      Mama sosai take tausayin dan nata sabo da yanda tasan halin matarsa bata da hali.adduarta kullum Allah masa chanjin alkhairi.Omar yayi aure amma kullum a gidansu yake rayuwarsa,kullum babu Wanda zaice ya taba aure,Rabin kayan sawarsa gaba daya  yana room dinsa a part dinsa bangaren mama.bashi da banbanci da gwauro.mama kuwa bata hanashi.


   Direct room dinsa ya wuce,wanka yayi hade da sallah ya kwanta sai bacci.iklas kuwa Niki Niki suka shigo gida dauke da kayan abinci dai dai kudinsu.ummi ta kawo musu farar shinkafa da miya hade da salat harda kifi,dan iklas duk talaucinsu bata yarda aci fara da yaji ba sai in suna sha'awa ko da dalili,dan gaskia tana da son cin dadi,ita ta yarda su rasa komai suci abinci me kyau,tunda suna Sana'a kuma suna samu ba laifi shi yasa take musu cefane me kyau na talaka.Rabin rayuwar gidan kaf a hannun iklas take


    Wanka sukayi suka zauna hira kafin magrib ta karasa,bayan sunyi sallar isha iklas ta shiga kitchen ta dafa musu indomie da dankalin turawa harda kifi,a baki ta bawa suhaila taci ta koshi,sannan suka ebo littatafansu sukayi karatu,nafila sukayi sannan suka haye gadonsu suka kwanta,kaka ummi kuwa dama a katifa take kwana,wai gadon ji takeyi tayi sama dogogo.suhaila da iklas a katon gadonsu,

 

     Haj rahina tana ta kulle kullen mugunta kawarta na hango suna zuba hirar mugunta a zaune a palon umma,ita da babbar kawarta hajiya  binta suna shirya tuggun da zasu kullawa Omar da mama,rahina tace binta ko wajen bokaye zan je ne?daria binta tayi tace share bokaye watarana aikin baya ci,kin San munafukar akwai addua,mufa mata ne ba irin tuggun da baza mu iya kulla musu ba Wanda zai jefa su cikin wani hali,ke in ta kama har gidan nan sai sun bari,tsabar iya tuggu da sharrinmu,haba rahina kin manta mu ne, tun muna yara kin San tsiyarmu.daria da shewa sukayi hade da tafawa, su sadiya yaran rahina sunaji sai murna suma sukeyi suna tafawa,dasu ake shirya komai.sai kara zugasu sukeyi,


Iyaye da dama na kuskure manya manya duk wani gulma,munafunci hassada sai a dingayi gaban yara,ana daria kaga wasu har tafawa sukeyi da yaransu mata ana cin naman wasu,duk iyaye masu haka su sani suna gurbata tarbiyyar yaransu,da haka zasu taso suma sunayi,kuma uwa ko yaushe batawa yaranta fada,tana wasa da daria ko yaushe da yara baza su taba jin maganarta ba,rainata zasuyi,ba a hana hira wasa da Jan yara a jiki ba amma a dinga sanin kalar Wanda za ayi,kuma wasa ba ko yaushe ba,shi yasa za kaga yara na dakawa uwarsu tsawa,ta sasu abu sukiyi, suma fada mata direct baza suyi ba,sai kaga idan ubane an masa da wuri a na rawar jiki,da yace a bari an bari,ba raini,amma mu iyaye mata mu ke zubar da kimarmu gaban yaranmu,matsala iri iri,Allah sa mu gyara.


    Omar na hango yana tafiyarsa ta takama sanye da wani blue jean pencil da red din Riga me dogon hannu,wandon irin an dan farfasashi daga gwiwa zuwa cinya,amma ba me yaga ba dan ba a ganin jikinsa,driver ne da sauri ya bude masa wata sabuwar arniyar farar mota,yana yin ribas motar sahar ta cinno kai gidan,tsadajjen gogon hannunsa ya kalla yaga almost 5pm,kawayenta ya hango biyu a cikin motar.horn ta masa hade da daga masa hannu,haushi ne ya kamashi, wurin 2days baya ganin sahar sai yau,ko yaushe tace duty dare ne da ita,kwana takeyi a hospital,yanzu kuma da rana yawo da kawaye da shirme a gari aikinta kenan.sai shewa sukeyi da frnds,wurin babban abokinsa sultan ya wuce,sultan doctor ne babba shekarunsu daya tare sukayi schl a london,har secondary,sultan babansa ya rasu daga shi sai mamansa,sun gaji dukiya ta gaske shi da mamansa,sultan baiyi aure ba amma an kai kudin aurensa gidan wata yar beauty dinsa yasmin,a asibitinsa ya sameshi zaune a office,hannu ya mika suka tafa sultan yace shegen kaya ya kk,ka dawo amma sau daya ka nemeni,omar yace bari Frnd kasan office ba Hutu,baffa ya hadani da aiki,oh na zata amarya sahar ce ta boye min kai,kana can kana Jan kaya,tsaki omar yaja kaifa dan iskane sultan,kasan komai tsakanina da ita kana min tsiya,Allah kyauta cewar sultan,kaga malam gobe around 1pm zaka rakani wani company na baffa zan duba aikin da akeyi,kasan da nisa fa sai an bar garin abuja.


    Allah kaimu cewar sultan.wai Frnd har yau baka samu wacce kake so bane,tsaki omar yaja karka dameni malam.daria sultan yayi yana ci gaba da tsokanarsa.


      Washe gari kamar kullum 1pm tana titin kwalta sai bin motoci takeyi a round tana daga apple da kwanta a ledoji ,ga yayyafi anayi ruwa ya jiketa da dangalalliyar rigarta wacce taje gidan kaji da ita,duk ruwan sama ya jikata kayan sun kara dameta a jikinta,sai boobs dinta kana kana duk sunyi caro caro,hips ya fido,gashinta ya kara kwantowa a goshinta sai digar ruwa sukeyi,


     Omar da sultan suna bayan mota a lafke driver na jansu,suka kawo dai dai danjar da iklas take,suna tsayawa ta karaso wurin motar tasu ga iska ta taso haka take daga musu,ido hudu sukayi da Omar wata uwar zabura yayi hade da nunata da yatsa yace you? Bata jin me yace saboda glass din motar a zuge yake,amma ta karanta lips dinsa ta gane me yace,murmushi tayi me kayatarwa ta daga masa hannu,itama tace oga da karfi,yaji abinda tace ai bai San sanda ya saki murmushi ba,yawa driver umarnin zuge glass kasa,kallonta yayi yanda iska ke daukanta,gashi ta falle mata gyalen da ke kanta gashi yaraf har kusan duwawunta,iska na kadashi sai ta kara kyau,driver yawa umarnin karbar apple da egg din hannunta,dubu biyar yawa driver umarnin mika mata,yana bata ta karba ta duba,hangame baki tayi ta dauki dubu daya,dama  shine kudin apple dinta da egg da suka karba,ta mikawa driver sauran,da sauri omar ya kalleta yace karba nakine na baki,daria tayi ta glass ta girgiza kai tace tnx oga amma bazan karba ba.lips dinta ya karanta ya gane me take nufi,hannu ta daga masa ta juya cikin nutsuwa ta dauko dan gyalenta ta wuce,omar kasa dauke idonsa yayi daga kanta,sultan kuwa tuni yayi suman zaune yana kallo da mamakin abokinsa tare da jinjina kyau irin na iklas.


    Danja taba da hannu amma omar sai waiwaye da kallon iklas yake,yanda take kai kawo a tsakiyar titi,yarinya irin wannan amma tana wannan sa'ar.take yaji ransa ya baci tausayinta ya mamaye zuciarsa, yar waye wannan aka barta tana garari a titi,tana da kuruciya haka,musulma.


Asmabaffa

[9:45PM, 3/21/2018] ‪+234 803 592 9495‬: ⓂⓂⓂ

    MA'AIKACIYAR 

         GOMNATI

          ⓂⓂⓂ


                6


By

Asmabaffa
      Tsaki omar yaja,a ransa yana gaskia an cuci yarinyar nan.sultan Wanda mamaki ya kasheshi shi yayi karfin halin taba kafadar omar frnd ,juyowa omar yayi lfy malam karfa ka takuramin,murmushi sultan yayi yace iyye Ashe kayi sabon kamu frnd wannan zukekiyar fa gaskia tana da kyau,amma ka bani mamaki omar duk matan  turai da yawon da kayi a duniya ban taba ganin ka kalli mace da idon rahma ba,amma gashi akan yar yarinya me talla a titi gaba daya ka haukace ka fita a hankalinka,harara omar ya balla masa,kaga halinka ko sultan,me zanyi da wannan yarinyar,tsaya malam nifa ka gama kasheni da mamaki omar kai da baka shiga shirgin wani bare har ka taimaka masa ba tare da ya nema wajenka ba,hasali ko mu maza sai mu Dade bamu ga murmushinka ba sai gashi karamar yarinya tatsitsiya kakewa murmushi haka har hakora su fito,ka bata kyautar kudi bata nema ba,tana kin karba kana tursasa ta kan ta karba,,harda siyan abun titi kai da baka cin abun kan hanya.


    Sultan wai pls mene haka what is ur problem kasan me ya hadani da ita,za kazo kana wani talk na shirme,yarinya karama zanso,me zanyi da wannan me talla a titi,tallan ma mafi muni,tausayinta naji shi yasa.


   Sultan ne ya kwashe da daria mai da wukar amma wlh wannan yarinyar ka fara sonta ko kaki ko kaso.da karfi omar yace God for bit,over my death body.daria sultan yayi ya leka fuskar omar inye anyi budurwa me kyau,gaskia ka iya zabe,dama omar ka iya murmushi haka me kyau,nima naci albarkacin new catch dinka na gani yau,tsaki omar yaja sai kayi ai.


    Driver na jinsu shima ya yarda da zancen sultan,minti kadan za kaga sultan nawa omar daria sai dayaga omar yakai wuya wajen bacin rai ya ja bakinsa ya tsuke,dan yasan halin omar kwai zucia da zafin rai,sultan ne yace idi driver miko mana apple da kwan nan muci girkin amarya,omar ko kallonsu baiyi ba,ana miko kwan da apple omar ya fisge a hannun sultan,baka isa kaci abun nan ba sultan,


    Daria sultan yayi au na manta hannun amarya ya taba abun kana kishi kar mu rigaka ci.shi dai omar shuru ya musu,har sukaje suka gama abinda zasuyi omar na fushi da sultan,a hanyarsu ta dawowa omar sai zare ido yakeyi ko zai hango iklas bai ganta ba.


    Sultan ne ya kalleshi ya kara kwashewa da daria am sorry Frnd ban San dariar zata fito ba,amaryar ta tafi gida ka daina waige waige,tsaki omar yaja ya dauki apple daya cikin Wanda ya siya wurin iklas glass ya sauke ya zura hannunsa ta window ya wanke apple dinsa fes da ruwa ya kama cin apple dinsa ji kake baras,har wani lumshe ido yakeyi,sai daya ci guda biyu,ta karfi sultan ma yaci biyu,aka bawa driver ragowar biyun,


    Can suna tafiya a mota omar ya kwance ledar kwai yaci daya ya mikawa driver duka.sultan harga Allah abin na omar ya shiga bashi tsoro kamar tsafi,omar da baya cin abun hanun yara,gashi bayacin abunda rana ta dakeshi a kan titi,yau gashi hankali kwance har dafaffen kwai na titi yaci hankali kwance lallai wannan yarinya ta masa babban kamu.


    Har gida suka kai sultan suna tsayawa omar yace dalla malam fitar min daga mota,zaka nemeni next time sannan zan rama kuma kasan ramuwata me zafi ce cewar sultan.gidansa ya wuce yau bazai biya ta wurin mama ba,yana shiga ya tadda sahar kwance a doguwar kujera tana chat,sallama ya mata ta amsa kuwa tace sannu ta ci gaba da chat dinta,shima ko kallo bata isheshi ba ya wuce room dinsa,wanka yayi sannan ya dauko take away da ya zo dashi ya dauko yaci a kyankyame sannan yayi sallar la'asar,karatun Quran yayi da sauran abubuwan lada har magriba tayi ya wuce masallaci,inda ya bar sahar haka ya dawo ya sameta ba sallah,har ya gaji da fadan.


      Dakin haj rahina sadiya ce da naja ke hirar samari suna bawa umma labarin yanda suke cin kudinsu,Aisha tace ai ni full tank nake ja,zuka nake da yawa,jane dani,sai na cika tanki na.tana tsakiyarsu suna ta hirarsu,daga nan suka mike sukayi mangaren maman omar,su uku ne suka je kamar abin kirki, yan matan ne yau cewar mama,tsaki sadiya ta ja ta mata kallon baki isa,suma sauran haka sukayi,can naja tace an wani faffake gida matsafa kawai.wlh sai mun kawo karshen makirci cewar sadiya,abdallah ne ya mike ya cakumo naja suka fara kokawa tukuri,suna ganin ya fara naushin naja,suka hadar masa abinka da namiji yana karami amma da kyar suka sha a hannunsa.part din suka bari Aisha tace sai kayi dana sani yaro.


     Mama kuwa danta ta janye tayi shigewar daki dan inda sabo ta saba,Sam bata damua.haka tasa suleim da abdallah gaba ta kira driver dinta ya tafi dasu shopping har mama,suna fita omar na zuwa gidan,yaga part din kulle dama shima yana da spare key din part din mama,room dinsa ya shige a ciki yayi sallar isha,coffee ya hada ya sha yabi lafiyar gado ya kwanta abinsa.


    Tunanin iklas ya addabi zuciyarsa,to shi mene hadinsa da ita har zan na tunata cewar omar a ransa,lallai ya kamata yasan tarihin yarinyar nan,gashi ya rasa dalilin da yasa ya damu ya sake ganin kyakyawar fuskarta, sunanta ya fada a fili GOMNATI.Da kyar ya samu bacci ya daukeshi.


     Mama batasan a gidan ya kwana ba gani tayi ya sauko daga part dinsa cikin shirinsa na office sanye yake da wani cufta me tsadar gaske brown sai kyalli yake da kamshi,mama ce ta bude baki tana kallonsa babana dama nan ka kwana,ina kabar iyalinka anya babana karfa ka shiga hakkin matarka,murmushi yayi hade da rungume ta,haba mama dutyn dare takeyi  fa,ni sai muyi 3days ma ban sata idona ba,ta fifita aikinta kan aure,nayi fadan da nasiha amma mama a banza Bata San cina da Shana ba,bata San matsala ta ba,batasan komai nawa ba bata damu dani ba,


    Zama yayi ya kwanta jikin mama yace mama kin San ba sonta nakeyi ba ko daya,baffa na yiwa biyayya,amma duk da haka nayi kokarin janta jikina ta dole dan na takurawa zuciata kan dole sai na sota,amma mama ita Sam kullum bakin ciki take tura min taya zuciata zata sota,baffa ya jona min bacin rai kullum tana bata min,bazan boye miki ba mama duk da nasan kin San komai akan abubuwan da sahar keyi wlh na tsaneta,bana sonta,bana kaunar na bude ido na ganta a matsayin matata a gidana,amma ina daurewa muna zama dan nayiwa baffa biyayya.

 

    Tausayin danta ne ya lullube mama tace kayi hakuri babana nasan komai,ka dage da addua Allah zai ma canji mafi alkhairi,Allah zai baka wacce kake so take sonka,kaci gaba da biyayya.muje kayi breakfast,bayan yayi break ya wuce office,tunani yakeyi a office ya zai yi ya kara ganin wannan yarinyar me talla.idi driver ya kira ya karbi key din motar so yakeyi yayi driving da kansa yau,bai so asan ina zaije.


    Sadiya da Aisha ne suke hirar samarinsu,Aisha tace anty sadiya ya kamata kiyi aure haka karfa ki tsufa,tsaki sadiya ta ja dalla yanzu kudi da kayan gyaran jiki basa bari ka tsufa,yanzu duk wacce ta bari ta tsufa to ta rako mata duniya,samarin nawa gaskia naga  basu da kudin danake bukata gwara ma wani alhaji Adam shi kuma yana da mata daya,bai taba haihuwa ba,Aisha tace ni  a ganina ki fito dashi guy din akwai kudi,kina aikinki kinga zaki huta,kuma gidanki ke daya zai Gina miki,ga aikin gomnatinki heeeeee suka rangada shewa suka tafa,sadiya tace haka za ayi yar gari,kefa Aisha ?tace aini kin San wa zan tsayar,yaseen zan tsayar a turai yayi rayuwarsa ga kudi ga wayewa.haka sauran matan gidan ma suka shigo sai hira sukeyi.


      Iklas kuwa dawowarta kenan daga schl,sallah tayi taci abinci daga nan ummi har ta dafa mata kwai kawai tallanta ta dauka ta tafi gefen titi.shi kuwa omar 11am yaje wurin da yaga iklas na tsayawa talla amma shuru bai ganta ba,ba jiran da baiyi ba bai ganta ba,motar sa ya parker ya kira wani yaro me talla ya kwatanta masa yanayin iklas yaron yace ohhhh gomnati kake nufi,yeah ita cewar omar,yaron yace ai yanzu tana schl sai 1to1:30 take zuwa nan tallanta,take omar ya tuno time din da suka ganta jiya,


         Kudi ya bawa yaron ya hau mota ya koma office,1pm dai dai ya sake dawowa wajen danjar da iklas ke talla,nan ma bai ganta ba,shi kadai yake Jan tsaki,can ya hangota ta fito daga wani lalataccen lungu,dakyar take daga kafarta sabo da nauyin kayan,botikin kwai a kanta ledar apple a hannun ta,Tausayinta yaji sosai kamar yayi mata hawaye,yana cikin motarsa yana kare mata kallo,yana kallonta har ta fara talla,omar ne ya daga waya ya kira wani ban San me yace ba,ba a kai 10mnt ba wani ya parker a mota dai dai wajen kayan iklas,cewa yayi yana son apples da eggs amma duka zai saye mata,juye zai mata,da murnarta ta siyar masa gaba daya,yana tafiya ta kara irga kudin sai taga ya mata Karin dubu biyar akan kudin,dubu biyar din kai ta cire ta boyesu daban,da niyar in ta kara ganinsa zata bashi abinsa in bata ganshi ba zata yi masa sadaka dasu.


     Tsalle tayi tana dariar farin ciki an siye mata du,baki har kunne tace kai ni me sa'a ce,duk abinda takeyi omar na mota a gefe yana kallonta har ta tafi gida,shima yaja motarsa ya koma office,amma ya rasa dalilin da yasa yake jin nishadi yau.tunda yaga gomnati yaji damuarsa ta gama yayewa.hajiya rahina sun shirya cewar baza su fara makirci ba sai alhaji Baban su omar ya dawo gida Nigeria.Washe gari karfe 1 na rana omar yana gefen titi a wata kalar motar tasa,yana jiran fitowar iklas daga layinsu da yaga ta fito jiya.Asmahbaffa

[9:45PM, 3/21/2018] ‪+234 803 592 9495‬: ⓂⓂⓂ

    MA'AIKACIYAR

         GOMNATI

          ⓂⓂⓂ


                7


By

Asmahbaffa       Yana zaune a motarsa yana shan a.c ta fito dauke da botikin kwanta yau yaga ba ledar apple a ransa yace to ko ta kare ne apple din tata?baki ya tabe hade da daga kafada.ta karasa danja tana tallanta,omar ya kunna motarsa ya hau kan titi yana zuwa saitin iklas ya gangare gefe yayi slow da motar,batasan waye ciki ba ta famfaro da Sauri sauri gudu gudu ta kara masa ledar kwai a glass na window side nasa,glass din ya sauke kasa wani kamshi da sanyin raba ya bigeta,ba tare da ta shirya ba ta kalli cikin motar,oga ta gani a mazaunin driver,lekawa tayi da murmushi sannu oga yau ma kazo wucewa?bai amsa mata ba kuma fuskarsa a tamke take,sai ya nuna kamar bai taba ganinta ba,kunya taji na disgata da yayi,a sanyaye ta juya zata wuce,keee cikin kakkausar murya ya kirata,juyowa tayi itama ta tamke fuska,ya akayi cewar iklas,a ransa yace wai ni zata wa tsawa haka hmm.a fili yace wai baki da wata Sana'a sai wannan?kullum kina gudu a titi cikin maza,kuma bakya sa kayan arziki na musulunci,duk maza an gama kalleki.

 

    Kallonsa tayi ta watsa masa harara to ina ruwanka,ina ruwan biri da gada,taso ta watsa masa bakaken maganganu wanda suka take wannan amma kwarjini da cikar zatinsa baza su bari ta fada masa ba oga omar ba kalar raini bane,Sam fuskarsa baya fara'a baka isa ka rainashi ba,in banda ma iklas ta goge da mutane da word daya baza ta iya furtawa gabansa ba,amma gashi har tsiwa take masa,a hankali tayi maganar amma ita wai nan a dole masifa tayi masa,sai ka zata hira me dadi sukeyi,shi omar daria ma ta bashi,a fili yace hey chill yan mata,I don't mean to hurt u,tambayarki nayi fa kuma dole ki fada min,lallai zaka Dade a tasha baka samu mota ba,murmushi yayi jin kalar Karin maganarta to naji next time zan dawo zo ki bani na siyi kwan naki,lallabata yayi don yasan gomnati akwai tsiwa,ya fahimci akwai son a girmamata,yauma duka ya siye mata kwanta tana tafiya ya bita a baya a mota ba tare da ta sani ba,har gidansu yaga gidan da ta shiga,juyawa yayi ya koma office cike da mamakin lalacewar gida irin nasu gomnati,da gani suna wani hali.


     Tun daga wannan rana iklas bata kara ganin omar yazo ba,tayi tunanin ko fushi yayi kan maganar da ta fada masa,ita da kanta ta gano bata kyauta ba,tunani ya hanata sakat kan maganar da ta fadawa oga omar,ta zama butulu ta manta halaccin da yayi mata,tun damuwarta na boyewa har ta fito fili,yau Saturday tayi jugum tana tunani kaka ummi ta leko dakin,ke yar nan ki raba kanki da wannan bakin tunani da kika dorawa kanki kwana nan,na rasa gane miki,alhmdllh muna ci muna sha,ga makaranta kunayi dai dai gwargwado Allah ya hore mana amma sai tunanin banza kikeyi,ummi wlh lailatul qadarin dana fada miki me gidan kaji?ae ina jinki iklas..to ummi shine ya tambayeni kan Sana'a ta amma na manta alkhairin da yayi min da yawa na masa rashin kunya,to har yau ban kara ganinsa ba,fatana ma ace lfy yake.ummi wlh baki ganshi ba me kyau dan gayu,ya fini kyau fa,kuma ga iya wanka ummi,sai ma kinga murmushinsa.


   Kaka ummi ce ta rafka  salati lailahaillallahu ni kam naga ta kaina,iklas karfa aljanu su shigeki,ko dai sonsa kikeyi ne,dama tunda naji kin saurareshi har ya miki kyauta kin karba nasan da wata a kasa,ke da bakya karbar kyautar namiji,kullum kice suna baki ne dan su lalata miki kuruciya, gashi wannan har murna da ihu kika dinga yi,duk ranar da kika ganshi sai kin hanamu bacci da labarinsa.akan wannan har kika damu kanki tab,ai sai ki tayi aiki ya ganki,


  Baki ta cuno kaka ba haka bane bafa,haba ummi ke bakya ganewa,nawa nake kwata kwata da zan San wani so.rankwashi ummi ta zuba mata tashi sha sha sha ki mana girkin dare wlh iklas ki kiyayeni.kara ta saki ochch haba ummi zaki sani ciwon kai.


      Shi kuwa Omar tun bayan da ya siyi kwai a titi ya tsaya ya rabawa almajirai ya dauki daya ciki yaci,tunani yakeyi ta ya zai San tarihin yarinyar nan,har yasan wanne irin taimako zai mata,baya son ya bata kudi sabo da gudun kar ta yi masa mummunar fassara, tausayinta yakeji ya rasa dalili.


      Baffan su Omar ne ya sanarwa iyalansa zai dawo nan da 2wks,su haj rahina sai murna Sukeyi burunsu ya kusa cika,kamar kullum yau omar yana gidansa a Palo yana cike ciken takaddu,sahar ce ta karaso wajensa tana zuba wani matsiyacin kamshi,ga wata Shiga da tayi ta alfarma kamar zata cin gasa.zama tayi kusa dashi,shafa fuskarsa ta Shigayi,yana dagowa ya kwadawa sahar mari lafiyayye,idonsa yayi jajir u r very stupid,me kika daukeni wawa ko me,duk abinda kikeyi ina kallonki kyaleki nakeyi sabo da biyayyar mahaifina.


     Dafe da kunci sahar tace what omar in ka sa hannu a lafiyayyar fuskata ka Mara,wlh sai kayi dana sani,sai kasan ka mari mai girma sahar, kuma bari na fada ma duk dunia babu namijin da ya isa na masa biyayya dan yana mijina,sabo da ina da komai na kudi,babu abinda zan nema wajen wani.


     Dama sallama nazo yima zan tafi kano wata seminar sai nan da 1wk zan dawo fuuuuuuu ta dauki trolley dinta tayi gaba tsaki Omar ya ja,har airport driver ya kaita ta hau jirgi sai kano.


    Omar kuwa wanka ya fesa yau Wednesday bai je office ba sabo da akwai inda yake son zuwa, cikin shigar wata rantsatsiyar farar shadda kal ya fito,dinkin zamani kamar a jikinsa aka dinka,ga sumarsa ta kara yawa luf da ita yana shining, komai fari yasa agogo ma na azurfa ne,


      Yau ma bai gayyaci driver ba,wata shegiyar farar mota ya shiga,su Kansu ma'aikatan gidan omar cewa suke oga yana kashe kala a garin abuja,oga na tsiya a kasar nan.


      Layin 1:40pm ya parker motarsa kofar gidan su iklas,kowa dake layin kallon motar akeyi,ko waye zai wuce sai yabi motar da kallo.yana cikin tunanin yaron da zai aika gidan sai ga suhaila cikin uniform ta dawo daga schl,kallon yarinyar yayi tabbas wannan kanwar gomnati ce,sunyi kama sai dai gomnati ta fita hasken fata duk da itama suhaila farar ce,motar ya bude yace pls young girl?da sauri ta juyo sai kallon dan gayu takeyi,nan ne gidan su gomnati?yeah nan ne cewar suhaila,pls ki min sallama da dadynku,daria tayi ai mu bamu da dady uncle,ok umma fa,kai uncle ba ummanmu bace tare da kakarmu muke zama mu 3.OK good girl yi min sallama da kakar taku to.OK ta shige gida da gudu,Minti kadan sai ga kaka ummi ta leko sanye da wata tsohuwar atamfarta,da wani yankwanannen gyale amma fa kar kar suke ,omar tunda yaga suhaila da kaka ya tabbatar gidan masu tsafta ne.


    Uummi ce tace samari lfy kuwa?har kasa ya duka ya kwashi gaisuwa,lfy ummi yaji sunanta wurin suhaila,ummi magana nazo muyi in ba damuwa.to shigo daga ciki cewar ummi,wani kamshin dadine ya bigi omar,kal kal yaga gidan,komai tas a tsare ga kamshi Wanda bai taba ji ba dukkan gidan nayi,Palo ummi ta kaishi mamakin kayan palon yayi,masu dan tsada  tsada danshi a wajen omar masu dan tsada zai ce, ga kamshi na gaske komai tsab,ga wata fanka ta kasa me iskar niima,ga ta sama ma.


     Numfashi yaja yace ummi dama akan maganar yarinyarku ne me tallan apple,na ganta sai naga sana'ar bata dace da ita ba,kai yaro ko Kaine lailatul qadarin da tace ta gani,me gidan kaji?daria ce ta kwacewa omar ba tare da ya shirya ba,ae ummi nine,Allahu akabar kabira,dan nan ya sunanka? Omar mohd omar Allah sarki umaru,sannu da kokari Allah ya kara budi,ameen ummi,mikewa ummi tayi ta kawo masa zobo me sanyi da dadi,yasha kayan kamshi,da ruwa pure water,shikam kodan su saba da shi zai sha, sosai yaga kalar gidan ba kyankyami,har lumshe ido yakeyi dan dadin zobon,suna zaune kaka ummi sai satar kallonsa take tana jin dadin yanda ya sha abinsu ba tare da ya ji kyankyaminsu,gashi me kudin gaske amma sam bai kyamacesu ba,kaka ummi ce tayi tunani tace kai yaro ko kai dan gidan mohd omar ibrahim ne dattijon kirki,murmushi yayi yace ummi kin sanshi dama?


Ae ai muna jinsa a radio muna ganinsa a labarai,waye bai sanshi ba,ai ya zaga duk fadin nigertia,nan kaka ummi ta karkace ta bawa omar tarihinsu kaf,har halayen iklas da yanda iklas ke tunaninsa sabo da tayi masa rashin kunya tana son bashi hakuri.


  Shuru yayi yana sauraren maganganun kaka ummi,ya tausaya musu matuka gaya,ya sa a zuciarsa zai dinga taimaka musu dan ba karamin tausayinsu yaji ba,can ummi tace ai mutuniyarka na bamu labarinka,yanzu zaka ga ta shigo,ko 5mnt ummi batayi da rufe baki ba iklas ta shigo da sallama tana kwalawa kaka kira?kaji ta ko umaru cewar kaka,shi kam omar guntun murmushi yayi,yagafa kaka ummi akwai surutu,shi kuma ba ma'abocin son surutu bane,fuskarsa tamke take dama ba wata fara'ace da shi ba,sai ka Dade dashi baka ga dariarsa ba,kaka ummi ma ta gano hakan,ga izza da takama.


    Ummi ina suhaila wai tana daki tayi bacci,yau nace baza taje islamiyya ba ta kwanta ta huta,haba ummi so kike naje nasha rana a titi ga kunya da tozarci ruwan sama,iska,sanyi,rana su kare min akai,kema kina naki wahalar mun biya kudin schl din nan duk da ba me tsada bace amma kin San asarar kudin zamuyi ko,alhmdllh ni na samu dai dai gwargwado na addini,amma ummi suhaila fa kin San yarinyace,ni gaskia bazan bari ta taso a jahilci ba.sabo da schl fa nake talla a titi.dole taje schl wlh,bari na shiryata ummi zauna Palo ki dauko min Biro da jotter lissafi za muyi,


     Ke dalla rufemin baki ni cewar ummi tare da shigewa Palo wajen omar dake zaune,duk yaji hirarsu da iklas gaskia ta birgeshi,tasan me takeyi.     Asmabaffa

[9:46PM, 3/21/2018] ‪+234 803 592 9495‬: ⓂⓂⓂ

     MA'AIKACIYAR 

          GOMNATI

           ⓂⓂⓂ


                  8


By

 Asmabaffa
      In hakane to iklas na da nutsuwa da hankali,yarinya karama,ummi ce ta katse masa tunani sannu umaru kaga shashashar can bata ma kula da bako ba ita kawai ta makaranta takeyi,yarinyar nan da jarabar son makaranta take,rai ba hutu,ummi ai yanzu ilmi shine gaba,Allah kyauta cewar omar,iklas ta yiwa suhaila wanka,ta shiryata a uniform din islamiyyarsu Wanda shi kanshi wandon ya yage ta gwiwa kayan sun tsufa tukuf,amma a wanke a goge kal,sam iklas bata kula da takalmin bako ba,kawai abinda ke ranta take tunani,har Palo taja hannun suhaila wani mahaukacin kamshi ne ya daketa,kallon palon tayi,da sauri ta zabura tana zare ido,ta zata a mafarki ne sai taga tabbas a gaske ne,idonta ta kara murzawa,


     Dan rusunawa tayi kasa sannu ina yini,lfy kawai yace yana shan kamshi,tunda taga bata samu tarba me kyau ba ta mike,ta dauki Biro da jotter tace pls tsohuwa yi sauri muyi lissafin nan ina da aikinyi,iklas ke naga dan ana ce miki gomnati kanki rawa yakeyi ke a dole jinki kike kamar wata ma'aikaciyar gomnati,wlh ki cire wannan haukan ko kunya bakyaji kin fara girma kina cin kasa,baki ta cuno haba ummi dan Allah ni ki daina cewa na girma,dan uwaki ke bakya gani makauniyace jibi fa kirjinki iklas,wata kunya ce ta rufe iklas a gaban omar,kun San tsofaffi akwai baro zance,shi kuwa omar murmushi yayi ya kara wani nutsewa hade da tabe baki,a ransa yace wai wannan ce ta girma,ina abin yake,breast kamar gudan lemon tsami.


     Kasa kallon inda yake tayi sabo da kunya,da kyar ta fara rubuce rubucenta,tana ta faman buga lissafi a paper,kudin ta ebo tana turo baki gashi nan ummi wannan kin San ranar Saturday zanje kasuwa dasu,ungo wannan ki hada Dana wajenki na cefanen gida na fada miki ummi kullum ko naman 100 a dinga girki dashi ko kifi idan bani zan dafa ba dole ki dinga dafawa dashi,bana son muna cin garau garau ina shan wahala a rana a banza,blood dina zai kare a banza,kuma ban son skin din suhailata ya lalace ko babyna ta kalli suhaila,murmushi suhaila tayi tace anty ranar Monday za muyi debate a schl fa,kuma ance mu fadawa mom and dad Wanda sukaci akwai gift,muje da masu karba mana,ok suhaila Allah kaimu zanje ai cewar iklas.


  Ummi kuwa tabe baki tayi kwaji dashi can,daria suhaila tayi,iklas kuwa cewa tayi ummi yau daga islamiyya zan wuce siyowa,a'a iklas wlh baza ki wani gidan kaji da magribaba,ban yarda ba duniya ta lalace.mutane ba tsoron allah ne dasu,suje su lalata minke,a jawo mana masifa,dan yanzu da kike ganinki karama sai samu matsala.ba musu tace to ummi nifa tunda na dan Tara na abinci zanyi hutun 1wk bazanje tallaba.


   Ina ruwana da in na ce ki huta ai kin yarda kikeyi Yanzu gashi ai kin bi shawarata.kwantawa tayi jikin ummi tsohuwa zaki ci girki me dadi na zamani har na 1wk.daria ummi tayi oh ni jikar luba ta kaiwa iklas rankwashi.


      Omar kuwa birgeshi sukeyi,baren ma acting iklas tana abu kamar namiji magidanci,ga iya planning rayuwa,kai Wanda ya aureta yaji dadi,ga yanda take kula da kanwarta.ummi ce ta katse masa tunani da umaru kayi shuru,ba komai ummi ni zan tafi sai wataran,to har zaka tafi mun gode Allah saka da alkhairi,mun gode kwarai da kulawarka,hannun suhaila ya rike zo ki rakani beautyn anty.dadi suhaila taji dan gayu yace mata beautyn anty.


      Har mota sukaje da suhaila kudi ya dauko bundle guda na dubu dubu yace gashi beauty ki bawa ummi kice suyi cefane,ya kara dauko wasu manyan kwalayen sweets masu dadi da tsada da biscuits yan gaske da wasu snacks cikin katuwar Leda gashi wannan duka nakine,har kasa tace tnx uncle tana ta murna,wata ledar ya kara daukowa katuwa wannan suhaila baza ta iya dagawa ba,yace jeki ki kai wa ummi kisha sweets dinki,sannan ki cewar antynki tayi sauri ina kiranta,kafin ya rufe baki ta fada gidan da gudu,ummi murna da dadi ya rufeta,kakarsu ta yanke saka,tsalle sukeyi da murna kaka harda rawa da juyi,Riga damammiya pink bodyhug ce jikin iklas da wani jean skert shima da kadan ya haura gwiwa,


    Kallonta yayi ya tabe baki,mika mata kayan yayi gashi nan kuyi manage kafin na dawo,godiya ta shiga jerowa,juyowa yayi cikin hade rai da kakkausar muryar dake firgitata karki sake na ganki kan titi kina talla wlh,sannan ki daina yawo tsirara ga kaya nan,daure fuska tayi har zatayi magana sai kuma taji tsoro gani tayi yayi mata kwarjini.


 Amma aranta tace kuji min iyayi da shishigi,ina ruwansa da tallana,uba nane shi,shi zai dauki nauyinmu in banje talla ba,wai ina yawo tsirara kut..yayi sa'a shi ya fada min haka ina ganin mutuncinsa da wanine wlh sai ya San wace gomnati.


     Kafin ta gama wannan zancen zucin nata tuni omar ya Dade da figar motarsa ya bar layin, bayan motar ta hango kadan.gida ta wuce itama,


     Nan fa murna sabuwa gidan su iklas, ready made dogayen riguna ne masu tsada da kyau dai dai iklass kamar an aunata kala biyar,Riga da skert kala uku readymade suma,takalma kala uku flat,da yan gyale,brst basu isa sa bra ba panties kawai ya siyo kala 10,vest da tight wando guda uku,rigar bacci na yaran gida kala uku,bai San iklas Nada kanwa ba shi yasa bai siyo da ita ba,sai ya bata sweets da snacks din,atampofi kala biyar masu tsada du iklas tace kaka ummi ta dinka nata ne.  


     Murna wurin kaka ummi ba a magana ita kuwa suhaila ta sweets kawai takeyi,omar  Kuwa wurin sultan ya tafi gaisar da mom din sultan,sannan suka je wajen wasu frnds nasu,sultan yayi yayi omar ya rakashi wurin Yasmin budurwarsa amma omar Sam yaki zuwa,sultan ne yaja tsaki wlh zan rama omar,Yasmin din da zan aurace baza kaje wajenta ba?shuru omar baice uffan ba,sau daya fa ka ganta Frnd shima a hospital office dina kuka hadu.malam karka dameni kafi kowa sanin waye omar bana zuwa rakon zance,so pls excuse me cewar omar,nasan halinka mana maramutunci,miskilanci,da rashin damuwa da matsalar wani sai in matsalar ta me tallan egg ce.headphone omar yasa a kunnensa yana jin wakar Chris brown. 


   Kallonsa sultan yayi dan iska tashi ka tafi gidanku ka bar min daki ba abinda ka iya bakin hali ba annuri a fuska,gaka da mata amma baka da maraba da gwauro,gwauron banza kawai.murmushi omar yayi ya mike tare da shigewa toilet din sultan wanka ya fesa,wani closet din sultan ya duba da yake ajiye sababbin singlet dasu boxers,3quater  dan bangaren new da ba a taba sawa ba daban suke,sultan ma kwai kyau tsabta da daukan wanka,sultan shi ba fari bane chocolate ne,ya danfi omar kiba da kadan,shi yasa size dinsu kusan daya,


       Farar singlet omar yasa da 3quater ya fesa turaruka,sultan na shan kallonsa,kayan jikinsa daya cire ya eba ya zuba a mota,ya dawo room din sultan karar ruwa yaji yasan sultan na toilet,wajen mom din sultan ya wuce yaci abinci suna ta hira a kayataccen kantamemen palonta kamar aljanar dunia,30mnt yawa mom sai da safe ya wuce room din sultan,sultan ya hango jikin mirror ya hade cikin wata arniyar gezna sai turaruka yake fesawa,


    Tabe baki omar yayi daga bisani yace malam kayi sauri ina jiranka,da wata uwar masifa sultan ya juyo ubanwa zaije dakai gidan surukai haka,kamar inyamuri,ga suma duba fa shigarka,tsaki omar yaja ya sake bude layin sababbin jallabiya,wata milk color me mugun tsada ya dauko,siririya me shape dai dai jikinsa ta manyan guys,Turare ya kara fesawa sannan suka fito,mom suka gani a Palo suka mata sallama cike da fara'a hade da jindadi gami da birgewar abotarsu ta musu adduar dawowa lfy,7:30pm suka cinna hancin motarsu cikin gidan su Yasmin,gate man ya wangale musu makeken gate din su yasmin,har katafaren palon baki aka musu iso,kafin wani lokaci an cika gabansu da kayan motsa baki,


      Karaar takalmi sukaji das das,sannan kamshinta ya iso,cikin nutsuwa ta shigo da sallama,sultan ne ya amsa,ba laifi Yasmin kyakyawace fara ba kal ba amma tafi sultan haske,sun gaisa da omar ya dan jira for 15mnt ya fice ya koma mota,karfe 9pm sultan ya kira omar har umma da abbun su Yasmin suka gaisar.omar ranar gidan su sultan ya kwana.


    Asmabaffa

[9:47PM, 3/21/2018] ‪+234 803 592 9495‬: ⓂⓂⓂ

     MA'AIKACIYAR 

          GOMNATI

           ⓂⓂⓂ

  

                  9


By

Asmabaffa    Wannan page din dominku nayi shi readers masu yabo da jinjina.       

      Da safe tare sukayi break sultan,omar da mom sultan,sannan omar ya wuce office.bayan kwana biyu da zuwan omar gidan su iklas,wasu ma'aikata suka zo da kayan gini a motoci cewar oga omar ya turosu za suyi musu kitchen a canja toilet da sauran wasu abubuwa,abin har kaka ummi ya daure mata kai amma me zasuyi,nan da nan cikin 3days anyi toilet ta zamani tasha tiles,kitchen ma haka,rooms dinsu ma daga baya ya bada umarnin a sake sababbabi,kai readers gidan dungurugum aka sake ginawa komai sabo na zamani,2room da Palo tsakiya,toilet kitchen duk a tsakar gida yanda suke kawai Palo aka kara musu,ansa kofofi da windows na zamani,gidan tiles da tiles dan dagwas dashi gwanin birgewa,sai murna ake tayasu,su kuwa sai suce dan uwansu ne ya Gina musu,Palo sun maida kayansu na da, sai ya tashi haduwa,daya room din kuwa gani sukayi ankawo bed mirror sip new yan gaske aka shirya,duk rooms din an sa musu labile na zamani,next day suka kara ganin mota guda ta kayan abinci a tsorace suka yarda suka shirya kayan a kitchen komai akwai,dama suna da fridge me kyau da girma da tsada,


      Har gas da kayan kitchen kamar amarya an kawo an shirya musu,shifa omar kawai kudi yake bayarwa da umarni,next day aka kara kawo wasu kayan a Ledoji wai inji oga,dayar kaji,kifi da naman rago,a fridge suka zuba,harda lemuka masu tsada a takaice readers komai yaji a gidan na jin dadi,


      Next day kuwa wasu kayan aka sauke,ai iklas kuka tasa kaka ummi ma haka su dai karfa ace watarana su biya,dadi ya zama wahala,duk Wanda ke musu har anfi 1wk basu ga keyarsa a gidansu ba,sun shiga uku karfa ko ba nasu bane,ko aljanune ma,


    Kayan suka bude bayan sun gama kukan,uniform suka gani na wata schl dake kusa dasu schl din me tsadace,iklas dai dai ita,itama suhaila kamar an gwadata,mamaki sukeyi wai to a ina yasan size dinsu,uniform din har kala 4-4 ya musu,ga books din kowa a schl bag kala 3-3,takalman schl ma kala 3-3,a cikin jakar iklas yasa takadda me dauke da rubutunsa,


     Da sauri ta dauko ta fara karantawa kamar haka.

      ki duba cikin wata Leda akwai envelop in kunje schl din da ita zaku tafi, ki bawa p.c din,7:30 za kuga me kaiku yazo,banda talla a titi,ki gaisar da ummi.

                  Omar


    Ai tsalle suka fara da ihu suka cika gidan,wlh ummi shine yayi mana komai,lailatul Qadari Allah maka albarka,ai duk sallah sai na ma addua cewar iklas,kaka ummi babaLola science sec schl fa ya biya mana kinga receipt har na gama an biya min,suhaila iya js3 ya biya mata,.. 

  

     Daya ledar suka jawo gaba daya kayan suhaila English wears masu kyan gaske kala 10,takalma masu kyau harda kayan baccinta kala biyu,pant itama dasu vest kala 10.kuma nan ma kamar an gwadata.


      Tsalle kawai takeyi tana murna,saura wata ledar atampopi kala biyar dinkakku diff stile,shaddoji kala 4 yan gaske suma sunsha aiki,lace kala 3 sunsha dinkin zamani,da material kala 6,suma gaba daya an dinkasu dai dai jikin iklas,lace2,shadda2 mayafai manya masu tsada kala Biyar, ba a dinka ba takadda manne jikinsu anyi rubutu kamar  haka.


     Na ummi ne ki bata ta dinka,ga kudin dinki nan cikin lace,mayafaima nata natane.karamar ledar karshe suka bude,hijabaine masu hannu kala biyar size din iklas dagwas,kala uku na suhaila,kala uku manya na ummi,mayafai suka Ciro yan madaidaita masu kyau da tsada kala 6 na iklas,sai uniform din islamiyyarsu da ya gani jikin suhaila ya canja musu new kala 2-2.


    Yau har nafila sukayi suka dinga godewa Allah tare da yiwa Omar addua da iyayensa,next day kayan kwalliya iri iri Dana gyaran gashi da turaruka aka kawo musu,3days tsakani ya turo da wasu latest takalman roba na mata da jakankuna cikin Ghana must go babba,da address din company gashi nan suyi business,su dinga siyarwa a cikin gida babu zuwa talla,ai kuwa haka akayi,iklas an kulla alaka da company nasu omar,banda jaka da takalmi har wasu abubuwan take sarowa suna saidawa a cikin gida ake zuwa ana siya,sai schl tana kaiwa.sosai suke samun kudi,ga schl me kyau,sutura me kyau,ci da sha zam zam,ga tsabta da kwalliya suna bugawa,gasu wayayyu sai suka kara kyau haske da kiba.


      Tun zuwan omar na farko bai kara zuwa gidan su iklas ba,komai da yayi musu aike yayi dasu,su kuwa sun matsu su ganshi ko godiya suyi masa,amma shuru,gashi basu da number sa bare su nemeshi dan iklas ta siyawa ummi wata karamar tecno sabuwa,ita kuma ta siyi wata Samsung me kyau touchscreen,haka kawai iklas ta ji ta shiga damuwa na rashin ganin omar,


     Kullum sai ta tunashi,shi kuwa omar a ganinsa har ga Allah ya taimaka musu badan wani abuba,me zaije gidansu yayi,me zaice dasu yayi aikin ladansa suzo suyi zarginsa ko da wata manufa yayi.shi yasa tace Sam bazai kuma lekasu ba,tunda komai yayi dai dai shike nan.amma me zuciyarsa kawai sai yaji yana son yaga lafiyarsu musamman iklas,yana so ya ganewa idonsa ya suka koma,


     Baffan  su omar yayo waya cewar bazai dawo ba sai nan da 2mnths,dan haka ya umarci daya daga cikin matansa ta bishi Russia, ai rahina wuta ta bude dole itace ta tafi Russia wurin baffa Wanda Sam baiso itace zata zo ba amma ya zaiyi.


      A can ta dage tana ta kulla makirci,hade da kiran tsofaffin bokayenta tana danna musu kudi suna sheka aikinsu,sun bata tabbacin maman omar ba abinda zai iya cinta na tsafi dole tana nan daram,kuma baffa bazai daina sonta ba,dan haka tace to danfa a koreshi ya bar gidan,nan ma sukace shi zai iya tafiya amma bazai nisa da gidan ubansa ba,kuma dole zai dawo,cewa tayi koma yane ayi mata ya bar gidan.


       Sahar kuwa tunda ta dawo yanzu tafi da fita gantali,dan yanzu tafiyar kwananki takeyi.tun omar na fada da damua ya gaji ya kyaleta.kowa harkarsa yakeyi.


    Yau watan omar 1 da zuwa gidan su iklas,ya gaji da daurewa,yau dole ne yaje ya ga lafiyansu.saturday ba islamiyya ya sani,sanye yake cikin  pencil wandon jean arsh color da farar Riga me rubutu da baki jiki,ga suma taci kudi,kai ka rantse bature ne 4:30pm ya parker wata jibgegiyar sabuwar motarsa a kofar gidan,da kyar ma ya gane gidan,dan ma ma'aikatan sun nuna masa a waya ne,knocking yayi suhaila ce ta bude sanye take da vest da wandonta iya Rabin cinya,gashinta yasha gyara,tun daga kallon suhaila yasan sunci gaba wlh.


     Baki ta washe ta daka tsalle ta daneshi,oyoyo uncle,muna ta nemanka baka zo ba,to ai gani beauty yana murmushi kadan,sama ya shilla suhaila ya sabata a kafada suka shige gidan da sallama,kaka ummi ce ta fito tana amsa sallama..turus taja birki da mamaki tabbas wannan umaru ne da suke nema ido rufe domin suyi masa godiya,ummi baki har kunne ohhh dan nan yanzu sai yau kazo,muna ta jiran ganinka shuru,abubuwan arziki sai barkowa sukeyi ta hannunka,nanfa kaka tahau zuba godiya harda kukanta,daga nan ta fara yi masa hira,shi omar a bai son labari da yawa amma haka yake amsawa a dole,


     Kuma yana jin dadin labarin da take masa domin masu amfanine sosai a wurin dan Adam,dan ita ummi bata surutun shirme a nutse take,suhaila kuwa tana cinyarsa ta lafe,


      Iklas sanye take da wando 3qutr tight fari kal da riga dark blue,siririn gyale ta daura a kanta fari,tana kitchen ta gama shirya musu abinci ta gyara kitchen,sai surutun ummi take jiyowa dan ita bata ma San anyi wasu bako ba,wanka take so tayiwa suhaila itama tayi domin ita ke yiwa suhaila wanka saboda da wai suhaila jika jika takeyi kawai.fada sukeyi da suhaila sosai kan wanka,dan suhaila tace ta iya wankanta ita.


     Da sauri ta fada  palon da sallamarta....ummi wai surutun me kikeyi hakane?ina suhaila tazo na mata wank......bata karasa ba takai kallonta kan 2seater ai cik ta tsaya ganin Wanda ko a mafarki bata zata ba,ganinsa tayi ya kara kyau da kwarjini,ai da Saudi ta durkusa sannu da zuwa sir,ina yini,ya hanya? Da kyar ya amsa da lfy yana shan kamshi,ga fuskarsa ba rahama tamke,


     Ganin yanda ya amsa mata bata samu karbuwa ba a wulakance,kamar bai Santa ba yasa ta mike tare da fadin taso suhaila na miki wankan,kafada suhaila ta make a jikin omar...ni anty na iya wankana fa zanyi da kaina,no ban yarda ba jika jikar da kikeyi,kinga baby dont waste my time ki taso na miki,ina da wurin zuwa.


      Omar a ransa mamakin iklas yakeyi yanda takeyi acting kamar babbar mace bayan ita kanta iklas din bata wuce a mata wankan ba.


     Ganin suhaila bata da niyar tashi yasa ta karasa wurin omar ta jawo hannun suhaila nan suka fara kokawa,suhaila ta tura hannun iklas da karfi ta hade hannun da kirjin omar sai kiciniya sukeyi iklas na kokarin zaro hannunta wani azabar bala'in shock ne ya shigi omar,bai San sanda yace shishsh a hankali,tana janyo hannun ta fara masa sannu da bada hakuri duk ta dauka bigeshi tayi yaji zafi,...tsawa ya buga mata get lost stupid kin takurawa yarinya,


      Kaka ummi zabura tayi Allah maka albarka Umar yarinyar nan bata da kunya wlh wani halin banza ta dakko na son girma,gashi bata jin maganata na rasa inda zanyi da iklas wlh ka ganta duk wannan haukan da takeyi sauri takeyi zata je party na makwafta.dan ta taba taimakamana shine wai dole sai taje partynta na murnar zagayowar haihuwa,


     Giya fa suke sha a wurin umaru rawa maza da mata a cure ana badala nayi nayi akan Kar taje amma takiji,bata jin maganata sai abinda ta tsarawa rayuwarta kaka ummi ta fashe da kuka wiwi.


     Asmahbaffa

[9:59PM, 3/21/2018] ‪+234 803 592 9495‬: ⓂⓂⓂ

     MA'AIKACIYAR 

          GOMNATI

            ⓂⓂⓂ


                  10


By

Asmahbaffa
Wannan shafin nakine MAMAN WALEEDA ina godiya sweet sis.
           Kiyi shurunki ummi yanzu zan kula da ita duk wani iskanci da take ji dashi zan gyara ta,cuno baki iklas tayi ta bar palon,wanka ta samu tayi ta palon ta wuce sanye da hijab,kwalliya ta tsantsara ta sa daya daga cikin  rigunan da ta siyo rannan a kasuwa wata yar gaunt me dogon hannu ta haura gwiwa da kadan,daga sama ta matse kasa ta bude,orange and black color tayi kyau ba laifi harda yafa siririn gyale orange wai ita a dole zata birge,tayi shiga me kyau,don kaya manya su atamfa nauyi suke mata,bata saba ba sam,batan me yasa take so yau tayi kyau ba.wuce su omar tayi a Palo ta koma kitchen hade da kiran suhaila,abinci suka Jere a gaban omar,kallonta omar yayi tayi kyau amma wai ita bata sa kayan kirki ne?ga bako ai kamata yayi ta suturta jikinta,wato kowa haka yake kalleta tab,ummi ce tayi magana umaru bari inje makwafta zanyi ta'aziyya anjima  kadan zan dawo ba dadewa zanyi ba ka jirani,ba matsala ummi sai kin dawo,kallon iklas ummi tayi tace sai ki zauna wajensa na dawo uwar giggiwa kullum aikinki kenan yawo da watsatsun kaya,zigidir kullum da kayanki ba babu.


     Umaru kaci abincin dan Allah kaji,ko albarka kasa mana,kar ka bari na dawo na tarar baka ci komai ba,bazan ji dadi ba.ok ummi cewar omar.

Fitar ummi keda wuya dakin yayi dif ba Wanda yayi magana ga suhaila tayi bacci,sadda kai kasa iklas tayi bata son kallon omar wani faduwar gaba take ji,


       Kallonta yayi fuskar sa daure,ke a tsawace yayi maganar wato bakyajin magana ko,tun baki tafasa ba za ki kone kamarki har kin isa zuwa wani party kuma partyn na wasu tambadaddun yare,tsohuwa na zaune daku kina bata mata rai,ki kiyayeni wlh,da na kowa ne bar ganin bamu hada dangantaka ba duk lokacin Dana kamaki,ko na ji kin yi abu rubbish sai na hukuntaki.itafa iklas mamaki ya gama kasheta irin karfin  halin omar,ina ruwansa da rayuwarsu wai,sai kace ubansu,ko wani sabawa dajuna basuyi ba amma yake wani fada haka,lallai ma,Nima asmah naga shishigin omar anan.


    Turo baki tayi to birthday din maman ola ne fa sir,kuma....shut up  ba inda zaki .to ai dama na hakura sir cewar iklas a sanyaye,karma ki hakura.shuru dakin ya kara dauka can tace sir?Ina jinki,kaci abincin mana to,jagwalgwalonki zanci an fada miki ina cin girkin irinki,dama ummi ce tayi sai na ci.shuru ta masa dan taji haushin kalamansa,ta rasa why take daga masa kafa,ita da take masifaffiya bata kyalewa amma akan omar ta kasa daukan mataki.ba komai ko dan taimakon da yayi mana zan dinga kyaleshi.bani ruwan nasha kawai s ok ma maganar omar ta katsewa iklas tunani,da sauri ta mike ta fara tsiyaya ruwa a wani glass cup me kyau da tsafta,cikin izza ya karba yasha hade da mikewa tsaye idan ummi ta dawo na wuce ni ki sanar mata


     Pls ka bari ta dawo mana ko ka tsaya na kira  ta yanzu pls,sallamar ummi sukaji ta shigo palon,yawwa ummi zai tafi wai cewar iklas kuma baici komai ba wlh,hangame baki ummi tayi haba umaru ya zaka Mana haka,mu ka taimakamana mun yarda mun karba duk da bamu sanka ba,ba dangin iya ba na baba amma mun yarda da kai,yanzu dan mun baka abinci shine baza ka ci ba,kamar mun baka guba ko wata cuta.


   In dai kana so mu shirya gaskia kaci ko kadan ne idan kuma kyankyami kakeyi bazan ma dole ba.da sauri omar ya koma ya zauna haba ummi ba wani abu kiyi hakuri bari naci.baki ummi ta washe haba ko da kaifa amma ai sai ka sa muji ba dadi ai,iklas zuba masa bari naje na karasa gyara wasu kaya.omar ji yakeyi tsohuwar na birgeshi,kallonta yakeyi kamar mama.


    Tana bude flask wani kamshi ya daki hancinsa me dadi,fried rice lafiyayya tasha hadi da su hanta etc,zuba masa tayi ta kara bude wani bowl me kyau na glass kaji ne soyayyu zuba masa tayi a gefe ga hadadden salat,mika masa tayi ta zuba masa lemon kwakwa.


    Yatsina fuska ya dauki spoon da kyar ya fara ci,wani arnen dadi yaji kamar kunnensa zai fita,sai santi yakeyi a ransa a fili kuwa yatsina fuska kawai yakeyi,iklas na kallonsa kafafunta sunyi sanyi tun a fuskarsa ta gane baiji dadin abincin ba,kamar zatayi kuka bata San ace girkinta baiyi dadi ba.


    Musamman a wajen Omar bata San me yasa take so ya yaba girkinta ba.idonta har ya Tara kwalla kadan,omar yana kallonta ya gama ganota tsab,a ransa sai daria yakeyi,ganin kaka ummi bata kusa yasa yake ta wannan yatsina fuska,tunda yaga yanayin iklas ya kara yatsine fuska dan yanzu har yi yakeyi kamar zaiyi amai,abin mamaki yaci abincin yafi Rabin plate,lemon ma yasha yaji dadi amma harda rike ciki wai a dole yaci guba.can yace kai ummi ta takura naci jagwalgwalo,babu dadi haka akeyin girki,wannan  ai sai ki kashe mutane.


     Hawaye ne ya digo dis  daga idon iklas da sauri ta goge kar sir omar ya gani Wanda ta Riga ta makaro a idonsa tayi komai.kitchen ta shiga sai gata ta fito da wata Leda me kyau a hannunta,mikawa Omar tayi ga wannan ka kaiwa mom dinka,


       Tunaninsa ne ya tsaya cak wannan yarinyar akwai mamaki acikin alamarinta,wai tana 15yrs har tasan ta bawa mamansa kyauta yaji dadi kuma ta kara birgeshi.karba yayi hade da cewa tnx kira ummi,sai gani yayi iklas ta tsaya rubutu a jotter bai San me ta rubuta sai da ta gama ta wuce kiran ummi,ita kuwa iklas ta Riga tayi lissafi wannan week din sunyi dambun naman kaza gashi basu ci ba ta bayar kyauta,shi yasa ta canja lissafinta..sallama omar ya musu ummi ma ta bashi sakonta ya ba mama,


       Gidansa yaje ya duba lafiyar sahar sabo da amanar aure dake kansa,yar aikinta ya tambaya ina sahar ?ranka Dade tayi tafiya yau tace a fada ma ta tafi kasar ghana akwai wani aiki za suyi..ok kawai yace ya koma gidan mamansa,abinda Omar bai sani ba sahar ta kara lalacewa sai matan manyan alhazawa take kulawa Wanda suke da naira,wata kawarta hajiya talatu matar wani gomnace ita ta bawa sahar shawarar tunda kullum a hanya take ga mijinta ba wani shiri sukeyi ba kuma sahar akwai tsananin sha'awa kawai tunda tana da kudi a hannu ga maza nan samari yara sai ta zaba tunda yanzu matasa sun zama kwadayayyu kudi suke nema ta ko wacce hanya komai kudi,to ta mori dukiyarta ta samu wasu suna biya mata bukatarta tana biyan kudi.amma ta daina zubar da ajinta wurin omar mijinta tunda shi baya taba nemanta itama ta daina kai kanta.wa'iyazu billah mai makon muyi kokari mu gyara halinmu sai mu kara dilmiyewa mu jefa kanmu halaka wacce  har ka mutu kana da na sani.Allah shiryamu gaba daya.dan yanzu wannan ya zama ruwan dare wurin wasu matayen musamman masu naira


       Mama na room dinta tana shafa magani a kafafunta da suke mata ciwo omar ya shigo da sallama,da fara'a ta amsa masa babanmu ina ka shiga ne haka ban ganka ba,maganin ya karba ya karasa shafa mata,ina gida mama ga office ba sauki,omar kenan na dauka ma ko suruka ta biyu ka samo min,murmushi yayi mama aure tun yanzu zan kara aure,ina zan kai matan dayar ma da za a yagemin ita so nakeyi,daria mama tayi omar sai hakuri dan kawai ba auren so aka maka bane kuma matar taka ba ayi dace ba shi yasa ka fadi haka,


    Mama kinji yanzu na dawo gida wai ta bawa yan aiki sako a fada min ta wuce Ghana,duk yawon da takeyi kasar nan bai isheta ba mama.mama ma ranta ya baci da jin abinda sahar tayi,ka bari zanwa baffanku magana a waya sai aje gidansu a sanar da iyayenta tunda ta Gagari kowa,ni ma zan kirata a waya,mama ki kyaleta pls kar tazo tana miki rashin kunya kin San bazan kyale ba.ya isa omar dole a fada mata gaskia.to mama ba matsala.ledar da iklas ta bashi ya mikawa mama,ledar kaka ummi ma ya mika mata gashi mama sunce a baki kuma suna gaisheki,murmushi tayi na gode Allah saka,amma banana wannan su waye suka bani bazan bude ba sai ka fada min,ohh mama wannan red din na kaka ummi ne wannan kuma na jikarta iklas,


    Murmushi mama tayi tana jin dadi tana fatan abinda tayi tunani ya zama gaske,a fili tace ban ganesu ba ai...uhm..uhm yana Sosa kai yace aikine ya hadamu gidan gona.kyaleshi mama tayi, tace angode kaga mutanen kirki bari mu gani mene ciki.


     Ledar iklas ta fara budewa wata katuwar farar roba ce  mai murfi shake take tam da dambun naman kaza iklas yinsa tayi musamman sabo da suhaila na sonsa ganin omar yasa ta canja idea ta juye masa duka me uban yawa ta bawa mamansa.mama taji dadi sosai,ta bude ledar ummi kayan kamshi ne da sauran abubuwan miya busassu.mama sai murna takeyi omar har mamakin murnar mama yayii,babana ya kamata ka kawo min su na gansu ko ka kaini gidansu,ba yanzu ba mama to allah kaimu koma yaushene.kasan bana cin maiko sabo da ulcer ta,kadan zan iba ni da su abdullah.dauki wannan kaje dakinka dashi..da kyar ya karbi na robar wai a dole bayacin girkin yara,amma ya dauke ya wuce room dashi yana bata rai da muzurai.


      Sadiya na hango sai masifa take zazzagawa tana dura ashar a compound din gidan,duk wani ma'aikata sunyi luf suna jinta,suleim na hango da uniform jikinta tsugune a gaban sadiya tana faman bata hakuri,anty sadiya kiyi hakuri ban San takadar tana da amfani ba shi yasa Dana gani na yaga na zuba a dustbin,


       Wani lafiyayyan mari sadiya ta kwadawa suleim Allah sarki yar yarinya sai ga shatin hannun sadiya radede a fuskarta,kuka ta tsala hade da dafe kumatunta,gashinta sadiya ta ja da karfi dan uwarki baki San darajar takarda ba,gadon tsiya ba laifinki bane uwarku ba ilmi ne da ita ba jahila ce shi yasa Baku San darajar takarda ba,tsabar masifar da sadiya keyi ko kula da motar omar wacce ta shigo har ya parker bata sani ba,hankada suleim tayi ta tintsira ta bige kanta da bakinta,wani gigitaccen kuka ta fasa,omar Wanda yana kallon abinda ke faruwa ransa ya baci,idonsa yayi jajir,zuciya ta tashi,karasowa yayi wajen ya ware hannu ya dinga zubawa sadiya mari,tun tana tsaye sai da takai kasa,belt din wandonsa ya zare ya fara zabgarta gashi ya riketa ram sai daya zaneta tas jikinta duk ya fashe,a hakan ma dan mama ta fito ta rikeshi ne,duk yan gidan suna wurin suna kallo,kafin kace me su Aisha naja sun kama zage zage suma,sannan suka kira baffa da ummansu dake Russia suka fadi karya da gaskia.


    Nanfa hajiya rahina ta haukacewa baffan su omar,wlh bazan yarda ko a dauki mataki ko na dauka da kaina,an Dade ana zalinta ni da yarana Sam bazan yarda wlh,akan haka sai dai in ka sakeni amma billahillazi bazan yarda ya kashe min yara ba.tsawa baffa ya daka mata ki saurara min shashashar banza,duka kannensa ne yana da damar hukuntasu,nasan dole omar yana da dalilinsa me karfi,yaran naki bansan halinsu bane an fada miki, marasa tarbiya omar ne wakili na yana da daman yanke komai a gidana.kuma wlh tun kafin na koma ki fada musu dukkansu su fito da miji,na gaji da zubar min da mutunci da sukeyi a unguwa..... Wai wai ai rahina kururuwa ta sa da gunjin kuka,baffa kuwa gidan ya bari.    Asmahbaffa na godiya gareku masoya readers,masu commenting idan nayi posting kunfi kowa birgeni, domin kuna bani kwarin gwiwar typing, na tabbatar kuna jin dadinsa.

ⓂⓂⓂ

    MA'AIKACIYAR

         GOMNATI

          ⓂⓂⓂ

                

             10-15


By

Asmabaffa.
      Pls readers a dinga kula ana amfani da sakon da muke isarwa me kyau,marar kyau ayi watsi dasu, bukatata kenan,kuskuren da mukayi Allah yafe mana kuma readers ayi mana afwa.Allah tsarkake mana zucuyoyinmu,a dinga rula sakonni nake isarwa ko wanne page lol na gode muku yan readers dina ina ji daku.kunyi male male araina.

      

     Tunda baffa ya fita taki daina kuka sosai take sheka kuka an Zane first daughter dinta me irin halinta sadiya,sai da ta koshi da kuka daga bisani ta jawo wayarta,ta kira haj bilki babbar kawarta tas ta kwashe zance ta fada mata,lallai yaron nan kwai tsinane tambadadde cewar haj bilki,rahina tace shi yasa na fada miki kije min wurin babban malaminki na kasar Mali ayita ta kare,na gaji da tsinannun mutanen nan,akan wannan zan iya dawowa Nigeria muje tare bilki ki rakani,duk wanda na sani nawa malaman ba kudin da ban kasheba abu shuru,nasan naki manyan shegu ne,daga bangaren haj.bilki baki ta tabe daga bisani taji dadi a ranta tana adduar insha'allah bazaiyi aiki ba,yar iska wai ke mijinki me kudi har yanga kike mana kin fimu kudi,ga yaranki masu aikin gomnati,ai sai na miki sanadiyar barin gidan alhaji mohd wlh,hauka nake na yarda ki samu daula ke kadai,Baki San yanda nake miki bakin cikin auren alhaji mohd ba,dan yafi mijina kudi...


     Haj rahinace ta katsewa bilki mugun tunanin dake ranta tana ta hello....hello....inajinki network ne wlh rahina,kina jina ki kwantar da hankalinki ni danake babbar kawarki ai dole zanje kasar Mali ko dan ke,ki bar komai hannuna,ammafa sai kin turo isassun kudi,babu matsala wannan cewar rahina,kuma dole sai mun haada da tuggunmu na mata.kin san yanzu sunfi tsafi aiki wajen maza,wasu maganganu haj bilki ta tsarawa haj rahina wanda koni banji me suke cewa ba readers.


       Suna katse wayar haj rahina tace shegiya haj bilki tasan takan duniya....banza marar wayo yar matsiyata kina taimakamin na samu abinda nake buri ko kawa  nafi karfin nayi dake,jahilar banza yaushe ma inba dole ba zan tsaya ko kusa dani ki raba,iyakarki primary schl.nan umma rahina ta kwashe da daria,a karshe tace har a bada bilki sai dai ki zama baiwata ba kawa ba.haj bilki kuwa tsaki taja tace shashasha naci banza,kudinki zan cinye na Gina kaina,ta zata shawarar Dana bata zata bulle,hhhhh lallai alhaji mohd zai saki dattijuwar banza zaki gane wace bilki.


     Kunji fa readers ko wacce cin amanar ko wacce takeyi,kuma wannan cin amanar ya zama ruwan dare tsakanin kawaye musamman mata,kowacce bata son yar uwarta taci gaba hassada,ga mugun nufi wannan ya zama ruwan dare a rayuwarmu ta yanzu,taya zamu ga dai dai wannan ya jefi wannan ,wannan ya jefi wannan.Allah ka tsarkake mana zuciyoyoyinmu.


     Bangaren su oga omar kuwa abin nasa yaci tura,da kyar mama ta janyeshi suka dauki suleim,family doctor mama ta kira yawa suleim dressing,abdallah harda kuka an jiwa kanwarsa ciwo,omar kuwa jikinsa sai rawa yake ran maza ya bacifa readers,dama can ya gaji da halin kannen nasa,sharesu kawai yakeyi amma komai da sukewa mama da kannensa ya sani kyalewa yakeyi dan a zauna lfy,amma tunda haka suka zaba zaiyi maganinsu idan basu nutsu ba.sadiya kuwa sai ihu takeyi jiki ya kumbura,sun hadu a kanta su Aisha suna ta Gasa mata jiki yayinda suke ta zage zagensu iri iri,sadiya kuwa jinsu kawai takeyi dan Allah ne kadai yasan irin matakin da zata dauka kan su omar da uwarsa,dan tayi alkawari ko zata mutu,ko zata karar da salary dinta sai ta kulla musu bala'i,yanzu ta fara ta daina jiran ummansu yanzu itama ta zauna da kafafunta daram sai taga karshen omar da wanda ya rabeshi gaba daya...ruwan zafin da Aisha ta danna mata a gefen wuya shi ya dai daita tunaninta ta saki kara da ihu hade da cewa Aisha zanci uwarki kasheni zakiyi.tana ta ciccijewa sabo da azaba..ni kuwa nace heeee..na fece daga wurin,


     Omar bakin ciki ya cunkushe masa zucia,haushin gidan yakeji gaba daya,mikewa yayi ya bar gidan gaba daya,har ya dauki hanyar office din sultan ya fasa ya canja hanya,dan yasan idan yaje wurin sultan bacin rai zai kara masa,da gudu na bishi readers na tafi gulma....lol.mayenta layin su iklas na ganshi gheto area yana Jan motar a slow yau 6days rabonsa da gidan,a tsakiyar layin gefen titi ya hangota tana magana da wasu maza igbo su biyu,sanye take cikin uniform 1:30 da alama daga schl take,


     Wani bakin ciki ne ya kara mamaye cuciyar oga omar,ya kwaso bakin ciki yaci karo da wani,haka kawai ya tsinci kansa cike da bacin rai ganin iklas da wasu kucakan maza Igbo,tana ta surutunta hankali kwance.omar na karasowa wajen ya danna wani horn da karfi wanda ya janyo hankalin kowa dake wurin suka zubawa shegiyar azababbiyar motarsa na mujiya,cikinsu harda iklas me dafaffen kwai,glass ya sauke sukayi 4 eye da iklas,alama ya mata tazo sallama tayiwa mazan Igbo bye Emma a gwarance suka ce gomnati gomnati murmushi iklas tayi tare da mikawa Emma hannu suka tafa hade da cewa  NO BE SMALL THINGS WOOO,Dayan Dennis yace,ur first salary is my share,nanfa gomnati tace,never mind A NO DEY CARRY LAST MY BRO,daria sukayi dukansu sannan ta daga hannu tana WE GO RUNNERM,U ASEY DEY NOOOOW.ta nufi motar omar kafin ta karasa wani bahaushe saleem yace gomnati sai kinci da biro hannu ta daga masa tare da bude gaban motar ta shiga,ta glass ta leko da kanta tace saleem salary na farko da kasonka ciki,fisgar motar omar yayi ji kake gwaf kan iklas ya bigi gaban motar,birki yaci kyaaaaa....ta koma da baya jagwaf...kafin ta nutsu ya kara fincikar motar ta kuma gwaraf da kanta a jikin glass,kuka ta kece dashi yanda zafi ya hadata ta ko ina.cisgar motar omar ya karayi kamar zasu kifa,ina gefe nace Allah tsare na cikinta Dana kan hanya,kuka iklas takeyi musamman da goshinta wani katon kululu ya fito,parking yayi kofar gidansu,da Sauri iklas ta fita dan ta ga mutuwa with her own koro koro eye,tana fita omar ya sauke glass ji mana....juyowa iklas tayi, u hv to be very careful banda sauki ina gargadinki ki tausayawa lafiyarki kiyi abinda ya dace kunnena yaji da wanda idona zai gani,zan dawo next time hukunci yana nan zaki karba dai dai da ke cewar omar tare da figar motarsa ya bar layin gaba daya cike da jin tsananin haushin iklas,shi kadai ya rasa ma ina zaije ya huta,wani katafaren guest house dinsa ya nufa dake gwagwalada,da ma'aikata da komai a gidan so very neat.


      Iklas kam ta Dade a tsaye tana tunanin to ita wai me tayi masa,mene hadinta dashi da haka kawai zai tsaneta,ya dauki karan tsana ya Dora mata..tsaki taja tana mulmula ciwonta ta wuce gida tana kunkuni za a kasheta a banza.


    Ummi ce ta tsare iklas da tambayar me ya sameta a goshi,fada mukayi a schl ummi Da wata,shine ta buga min kai da chair nima na fasa nata da dutse.kin kyauta iklas Allah taimaka cewar ummi,shashasha matsa ko na makeki wacce bata San ta girma ba,bari Allah ya kawo min yaron albarka umaru na fada masa tunda naga kinfi jin fadan sa.


    To wai ummi ni me nake mikine dazaki dinga hadani da wani azzalumi bare can,bamu hada dangi dashi ba amma har kinfi sonsa akanmu...ummi ce ta maketa da gudu ta mike ta wuce toilet,sallah tayi,wanka da cin abinci,mikewa tayi ta kwanta tana tunani kala kala wanda yafi yawa akan omar.tana tunaninsa kuma sai taji ranta yayi fari,ji tayi gwara tayi tunanin oga fiye Dana schl,ita kadai idan tayi tunanin schl sai tace no sai tayi na omar,sai ta saki murmushi tare da cewa kai ni kwai banza,mene abun tunashi,me ma zanyi dashi,ina Sam mijina yafi wancan ogan kyau ma,


       Maman omar ce ta kira wayar sahar sai da tayi mata 5 missed calls bata daga ba,after 40min sahar ta kira back tasan Maman mijinta ce tana da number amma sai tace hello who is on the line pls?,who am I speaking with? Shuru mama tayi tana jin sahar na turancinta ta gane me take fada amma baza ta iya mayar mata da turanci ba domin abdallah yana koya mata sosai shi yasa tana ji sai dai baza ta iya mayar da magana da turanci da tsayi ba.


    Sahar Maman omar CE...ohh mama ya gida ya aiki,lfy alhmdllh,sahar dama naji tafiyar da kikayi ne shine naga rashin dacewar hakan,bai....din din din mama taji an datse wayar,kira ta karayi ringing daya taji wata ta dauka tana ta watso turanci tabbas tasan sahar ce ta bada wayar dan a ci mata fuska.mama taji zafin abin sosai amma bata fadawa kowa ba,da kanta ta shirya driver ya kaita har gidan su sahar ta sanarwa iyayenta duk abinda ke faruwa,Maman sahar tabe baki tayi to ai sahar yarinya ce hajia,dole Ku dau hakuri,mu yarmu gaskia banga wani abu da takeyi ba,ya kuke abu kamar muna kauye,zamani ya canja balle ma sahar yar boko ce tana aiki babba dole sai tayi tafiye tafiye.


    Baban sahar kuwa gyaran murya yayi am hajiya za a mata fada kar Ku damu,yarinya kuma sai hakuri domin dole tayi aiki,kuma ita yar dangi ce dole sai da ziyarar yan uwa,aikinta kuma gaskia baza tayi wasa dashi ba dan yanzu rayuwa planning akeyi,amma tunda kunce tayi laifi kar Ku damu za a mata fada.haka mama ta dawo tana jimamin halayen iyayen sahar da sahar din kanta.ko omar bata fada masa ba.


     Sadiya tayi shige shige ta samo yan daban ta inda ta basu kwangilaar a sassara mata omar,in ta yiyuwa su hallakashi nan da 3wks,kudinta kaf da ta Tara na albashi shekara da shekaru ta basu.


     Ita kuwa hajiya rahina ta ajiye shawarar da haj. Bilki ta bata sai nan da wani lokaci zata fara hada makircinsu,yanzu wata kawarta hajia magajiya ta hada da wani shahararren malamin bokanta ta sanar masa so takeyi kawai omar ya bar gidan ubansa da kafarsa.yayinda haj bilki ta samu kudin da rahina ta tura mata na bokan kasar Mali ta bude makeken wajen saloon dinta dama ta gama ginawa rashin kudin siyen kayan ciki ya jawo ta kasa budewa,


    1wk da faruwar hakan Omar ya fara jin baya son Sam yaje gidansu,haka gidansa ma bai son zama ciki dole yake zama,mama kanta taga omar ya rage zuwa wajenta,sai ta dauka ko sahar ta gyara halinta ne sun shirya,har tana murna,omar sabo da mama yake daurewa watarana ya shiga gidan,dan in ya dauki hanyar gidan ji yake kamar za a zare masa rai,ga wani mugun bakin ciki da faduwar gaba,haka the same da gidansa,steal guest house nasa ma hakan take,ya canja gidaje da dama nasu amma hakan yakeji,hotel ya koma da zama yafi jin sauki,office kuwa bashi da ikon zuwa.duk wani harkar kula da dukiyar baffa sai wani manager su me amana ya dora akan komai ba wasa


    Kuma salisu manager ya kafa ya tsare kan komai,shi yasa baffa yake ganin komai normal,sadiya yaranta sun bazama Neman Omar.amma Sam sun kasa gane inda yake kwata kwata,yayinda Omar ya hada kayansa ya tare a hotel,hakanma kullum tsoratashi akeyi,ga muggan mafarkai,a firgice yake kullum,ya rame,kullum kwakwalwarsa a tunani take ina zai je yaji dadi,ya samu peace of mind,


    Omar gashi ya kasa fadawa kowa halin dayake ciki,yayi niyyar sanarwa sultan da mama sai yaji bakinsa yayi nauyi,ita kanta mama taga omar kwata kwata baya hayyacinsa,ko sun tambaya sai yace office ne,kuma sai su Dade basu Ganshi da idonsu ba,abin ya dami mama da sultan,mama ta sanarwa baffa yace suyi masa addua kawai ko da wani abun a ransa da yake damunsa wanda bamu sani ba,


     Yaran sadiya sai Neman omar suke su aikashi garin da ba a dawowa,amma abu ya fassakara,sadiya sai masifa takeyi an kasa cika mata burinta,yayin da omar ya kara boye kansa a hotel yana karbar masifu a jikinsa,


     Dan yanzu Sam ya bacewa ganin su mama,ya kashe wayoyinsa,an rasa inda ya shige,yanzu ko bacci baya iyayi da kyar yakeyin sallah ma,amma addua ta gagareshi,ko Quran ya dauka tofa faduwa yake ya sume,idan addua zaiyi sai bakin yaki motsawa,kawai gaba daya ya yanke shawarar barin hotel din ko garin abuja duka,


    Wani tunani yazo masa ransa take ya tattara trolley dinsa ya shiga taxi har kofar gidan su iklas,cike da izza ya tura gate din yana shiga gidan yaji mugun nutsuwa ta shigeshi,hankalinsa ya dawo jikinsa,ga wani ni'ima hade da nishadi a cikin zuciarsa,tofa readers,wani hanin ga Allah baiwa,haj rahina tsafinta yaci Ashe gata Allah yayiwa omar,domin yaran sadiya sun kara nemo wasu manyan yan daba duk Inda suka San wurin kashe naira na yan Hutu,na masu kudi sunje sunje amma Sam ba Omar ba labarinsa,shi yasa komai kaga ya sameka na kaddara Allah yafika sanin dalili,sonka yake.      Sallama yayi gidan su iklas,kaka ummi ya iske ita kadai  tana kulla citta a Leda,iklas tasha baccin rana ta mike ta fito kenan tana mika hade da yin hamma,vest ce jikinta pink da skert dogo me roba.wuf ta koma daki da sauri,ummi kuwa baki ta washe tana tarbar oga umaru,a tabarmar da ummi take nan ya zauna gefenta.

Ku kara shiri readers yanzu za a fara.
       Asmabaffa

ⓂⓂⓂ

    MA'AIKACIYAR

         GOMNATI

          ⓂⓂⓂ

      

             15-20
By 

Asmahbaffa
      Ina godiya masoyana masu karatu,ban San wanne irin farin ciki ma zan nuna ba yanda kuke kara min karfin gwiwa.tsakanina da Ku sai addua.       Tunda omar ya zauna gefen kaka ummi suka gaisa bai kara magana ba,Sam ya rasa me zai ce mata,ummi kuwa ta fuskanci umaru matsalace dashi babba,tun daga yanayinsa ta gane gashi ya dan rame ya kara haske,gashi harda trolley dinsa kamar dan gudun hijira,


    Kallonsa ummi tayi a nutse kana tace umaru iceko dai lfy?naga kamar kana da damua,omar kamar zaiyi kuka amma bazai iya fadan matsalar sa ba,uhm...uhm...ummi kawai ina cikin Matsala akan lafiyar jikina,nan ne kadai Dana shigo naji nutsuwa,ban San me ya sameni ba,kawai ki tayani da addua ummi,


   Kallon omar ummi tayi tabbas iyaka gaskiarsa yayi maganar,ta tabbatar akwai Matsala tattare da omar,gashi kowa yasan babansa a kasar nan kuma da alama suma basu San matsalar dan Nasu ba,   To umaru me kake so ayi?ina

kaje haka?ummi ko ina ya gagareni zama,nan gidan kadai naji na samu nutsuwa,jinjina lamarin ummi tayi amma har yau bata gano matsalar omar ba,dan kar ta takura masa da tambaya ta kyaleshi sai nan gaba idan ya kara samun nutsuwa,


     Umaru zaka zauna damu kafin komai ya daidai tane?cewar ummi cike da murna ya daga mata kai,murmushi ummi tayi ko ba komai gidansu zai kara armashi samun namiji tsayayye cikinsu,duk hirar nan da sukayi iklas tana labe jikin labile ta zuro kanta waje,sai da taji komai,a ranta tace to shi me ya sameshi,sai kuma ta tuno yanzu room din da take kwanciya shi za a bawa wannan ogan,


    Ta gama planning dinta an rusa mata,yanzu wajen ummi da suhaila zata koma da kwana,daki daya zasu ruguntsuma,abin haushi cewar iklas a ranta.


   Omar tunaninsa ya canja state ko ya koma wata kasar amma sabo da baffa ya ce dole ya kula da harkokinsa ba inda zaije,ummi ce ta kwalawa iklas kira,wuf ta yo waje gani ummi jeki kwashe kayanki a dakinki umaru zai zauna zuwa wani lokaci,kallonsa tayi shima kuwa ya dago da kansa sukayi 4eye,Wani sanyi iklas taji a ruhinta,idonta ta janye ta gaisar dashi,yau ya dan sakar mata ba laifi,kayanta ta kwashe tas,ta kara gyara room din sai kamshin ni'ima,daga bisani ta kai masa karamar akwatinsa ciki,alwala yayi yau a nutse yayi sallar azahar da la'asar duk a gidan,


 Suhaila kuwa murna take ta tayi dan gayu zai kwana gidansu,zasu dinga shan sweet,shi yasa ta makale kusa da omar.


     Abinci iklas iklas ta kawo masa ita tayi girkin kasancewar yau ba islamiyya,tuwon danyar shinkafa miyar egusi,da dan namansu na talaka,rabon da omar ya ci abinci a nutse haka har ya manta,iklas wani table da chair dinta ta jawo ta zauna kai ita fa bata yarda ba ma'aikaciyar gomnati ce,shi yasa in tana kai tana lissafinta wani dadi take ji,kanta kara girma yake sai ta dinga hangota kamar a office,


     Tunda omar ya fara cin abinci yake satar kallon shirmen iklas,sai yanga takeyi tana ta faman rubutu,sai da ta gama karatun schl ta jawo jotter lissafinta ta fara,har yi take tana kwankwasa tsinin Biro a dole babbar ma'aikaciyace,


     Ummi na gefe suna kallonta,har gumi ta hada  sabo da lissafi,readers duk lissafin nan da iklas keyi bai wuce kan karuwar omar da suka samu a gidan ba,dole komai yanzu na ci dashi za ayi lissafi,shi yasa take ta tarawa da ebewa,ummi ce tayi murmushi su kuruci dangin hauka,in kin gama sai ki tashi ki hadawa umaru ruwan wanka.


     Ba tare da ta dago kanta ba tace ok,sai da ta dauki lokaci me tsawo sannan ta gama ta kalli agogon dake sakale a hannunta sannan ta mike ta maida littafin palo cikin drower ta dawo,sai da omar yayi wanka sannan ya shiga dakin da aka saukeshi,gaba daya jinsa yake a takure,zafi ya dameshi,ala dole zai danyi kwanaki a gidan nan kafin ya tafiyarsa,ina Sam bazai iya rayuwa haka ba,komai a takure,dan karami kamar yana prison haka yake jinsa,dan ma akwai wuta available, Daren ranaar gaba daya ya kwashi bacci cikin nutsuwa,har makara yayi,sai 9am ya farka,su iklas yau ma Sunday ba schl,tuni har sun gama gyara gidan kawai ummi ce bata karasa musu breakfast ba,fitowa waje yayi dan toilet ma sai iya ta tsakar gida dole,brush ne a hannunsa da wani tsadajjen toothpaste, omar kwai kunyar a kallar masa jiki shi yasa da 3quater da singlet farare ya fito,harda towel dinsa,kallon yan gidan yayi yaga duk sunyi wanka kowa radau dashi,iklas ya kalla wacce ta wani hakimce a farar kujera tana latsa kuturwar wayarta,ummi ta kitchen tace umaru ka makara ni na hana a tasheka saboda naga akwai gajia jikinka,guntin murmushi yayi ya wuce toilet,kalar sabulun omarma daban suke,yana Shiga wanka iklas ta shige room dinsa zuruf ta gyareshi fes fes,aka dame masa bed,roomfreshner da turaren wutar data sa masa yafi na ko ina yawa.


     Palo suka hallara da kayan break ana jiran oga dan kwalisa ya fito,sallah yayi da addua ya shirya cikin wata jallabiyya dark brown yayi kyau,,duk gidan ya dau kamshinsa,yana fitowa ya gaisar da ummi,ta amsa tana tsokanarsa da bakunta,suhaila kuwa tsam ta mike zata je wajensa iklas ta riketa ram,zauna malama zaki je ki kama hawan masa jiki,jikinkine? Ya fada fuska tamke,ummi tace kyale iklas da iyayinta,sharesu tayi ta gaishesa ya amsa tare da jawo suhaila kusa dashi,


    Kunun gyada ne da chips girkin yayiwa omar dadi,kallon ummi yayi yace amma daga ji tsohon hanu ne yayi girkin nan ko? Daria ummi tayi sosai tasan sarai iklas yake tsokana,


     Iklas kuwa haushi taji ta katse maganar da tsohuwa yau zanje wuse market,a dawo lfy saura ki kwaso wannan yan iskan gwanjunan dangalallu da kike kwasowa,


   Baki ta turo ta Mike ta wuce room dinsu,omar kuwa har fadi yake anya kuwa iklas ba aljanu gareta ba lol,ya matsu ta tafi kasuwa ya sace book din nan da yake gani tana lissafi,so yake yaga wai me take rubutawane kullum,


     Yaso ya hanata fita amma wannan kudirin nasa yasa ya rabu da ita,fitowa tayi sanye da atamfar da omar ya dinka mata red da yellow Riga da skert,tayi kyau sosai das da ita,ansha jambaki maroon,bata daura dankwali ba,gyale siriri ta yafa a iya kanta,gata jajir da ita ta haske ko ina tal,duk suna zaune Palo ta fito,idon kaka ummi omar ya faka ya dallawa iklas harara,ya mata nuni da ido kan ta koma ta canja gyale babba,ko tasa hijab,kafada ta make cike da shagwaba ta buga kafa alamar taki din,ido ya zaro ya daure fuska yayi kamar zai mike ya kamota da gudu ta fada daki,ta dauka kamata zaiyi,tasan muguntar omar dan bata manta wahalar da Tasha ba cikin motarsa,


    Hijab tasa yellow me hannu yakai tsayin Rabin cinyarta,ummi ce ta kalleta da mamaki tace yar albarka ko kefa,Ashe kin fara hankali,a lallai shi yasa akace komai da lokacinsa,Allah miki albarka yar nan,sai kin dawo kinji jikalle,tana fita ta leko kanta taci sa'a su ummi surutu suke da suhaila,a hankali ta dan girgiza labile yanda omar zai gani,kallon wurin yayi ai kuwa suna hada ido ta murguda masa baki,shi daria ma ta bashi,a take ya saki murmushi ya nuna kansa irin ni?ido ta karkada far far ta daga kai alamar eh din,kai ya jinjina alamar zaki dawo ne.ummi ce ta juyo wuf iklas ta sake labile ta bar gidan,shi kam ogan naku wani matsewa yayi.ya dauki remote ya kunna TV,


      Kaka ummi ce tace to ni umaru na shiga zan dan matse,bacci nakeji,to ummi a fito lfy.iklas kuwa kayan ta kwashe ta maida kitchen,tana fita Omar ya sadada a dauke jotter iklas ya shige dakinsa,


    Kwancia yayi a bed ya fara dubawa,murmushi ya farayi ganin harda date take sawa,kuma kome ta rubuta sai ta zanashi,Daddawar miya ya fara gani tace ta Dari biyu for 1mnth,sannan yaga ta zana daddawa,su tattasai,da sauran kayan abinci


Yanaa ci gaba yaga irin bashin da take bi su ma gasu nan,ga wani bangaren business dinsu ne,abinda ya bashi daria kwandala in ta shiga ko ta fita sai ta rubuta,wani bangaren ma planning rayuwarsu da budged tayi na 1-2yrs,bai gama shan mamaki ba sai dayaga ko bako in akayi sai ta rubuta tayi lissafi nawa aka kashe a kansa,rufe littafin Omar yayi yana daria ganin an rubuta har dambum naman da ta bashi kwananki,komai na rayuwar gidan na lissafe a cikin littafin,gajia yayi da karantawa dan kato ne littafin,ga lissafi da rubutu kaca kaca mayar mata abinta yayi inda ya dauka,a Palo yaga suhaila na kallon cattoon, kwancia yayi a 3seater yana tunanin rayuwarsa,da mamansa halin da take ciki,


       Yana wannan tunani tare da adduar Neman agajin Allah suka tsikayo sallamar iklas ta dawo,tana shigowa ta durkusa tasan tayi laifi,sannu da hutawa oga sirAsmabaffa

ⓂⓂⓂ

    MA'AIKACIYAR 

         GOMNATI

          ⓂⓂⓂ


              20-25By

Asmabaffa

        Tana kifta ido fiki fiki  da gani bata da gaskia,sum sum ta wuce,sannu da zuwa anty cewar suhaila, tsayawa tayi ta dawo wajen suhaila,baby ya gida,kinyi karatu kuwa?anty Sai anjima zanyi, to Allah kaimu..me kikaci after break? Ba komai anty..so kike ulcer ya kamaki ko,juyawa tayi ta shiga kitchen,cake ta ebo da fresh milk ta dawo palo,a gaban suhaila ta ajiye gashi nan maza ki cinye,komawa kitchen tayi ta ebo wasu snacks ta kawowa omar harda juice yasan tabbas iklas sai ta rubuta cikin jotter dinta omar yaci cake da lemo,


     Shi Sam baya son zaki juice kawai ya sha,iklas tana kitchen tana girki Omar ya shiga kitchen din,gwagwa take ta yi wajen yanka wata kaza amma ta kasa dan ta mata tauri,sai huci takeyi tana yarfe hannu,kusa da ita ya matsa hannu yasa ya karbi wukar,tsorata tayi sosai,ido suka hada tace kash wlh har naji tsoro,kazar ya fara yanka mata,tana gefe tana mamaki yanda ya iya aikin mata,sharp sharp ya yanka mata,satar kallonsa takeyi tare da yaba kyau irin na omar,shi wai to baya daria ne,mutum kullum shuru haka,omar kuwa yaji ajikinsa tana kallonsa,yana gamawa ya wanke hanunsa da liquid soap,yana juyowa ya dungure mata kai sai da ta kusa faduwa,kina kallona kamar baki sanni ba wth ur big eye,nuna min kayan abincinku cewar omar,


nuna masa tayi yaga suna da su amma sun kusa karewa,wayarsa ya kunna ya kira wani daga cikin yaransa,kwatancen gidan ya masa ya umarceshi ya kawo kayan abinci gidan,3hrs tsakani aka cika gidan da abinci.amma basu ga omar ba domin yana dakinsa bai son a San Inda yake ma kwata kwata,su kuwa yaransa sun zata yana office ko gidansa,ummi kuwa rasa bakin godiya sukayi a wajen omar,


      Maman omar kullum addua da kuka take zabgawa,harda kannensa su abdallah,su Aisha bangaren haj rahina sai murna sukeyi yayinda labari ya riskesu,Wanda hakan Sam baiwa sadiya dadi ba,an cuceta bata dau fansa ba,ga asarar kudin da tayi,Haj.rahina kuwa sai dadi takeji tana nishadi,baffa kuwa manager ya kira ya tabbatar omar ba a San inda yake ba shi ke kula da komai.gaba daya baffa ya daina walwala da farin ciki,Sam haj rahina ta kasa gane kansa,domin ko sakar mata fuska bayayi,tattarowa yayi suka dawo Nigeria,


    Waje waje gari gari suke bincike,sultan ne a gaba kullum basa zama Neman omar sukeyi,sadiya na hango ta Tara yan dabanta su wajen shida,tace isa a.c da usy a boy ya kuke ganin za ayi,kudina zaku bani ko kuwa yaya za muyi?isa a.c ne ya saki daria yace ke hajiya karki kawo yawa mana,ya kike mana shirme ne,a boy yace dalla malama saurara yasin sai na sokeki da wuka,karki raina mana hankali mana,ji mana ke ai munci kudinmu,taimako daya za muyi miki duk ranar da muka ganshi idonmu idonsa zamu cika miki burinki,idan kuma bamu gani ba sai ki ware kawai ko ya kukace.a boy ya zuki sigari ya fesawa sadiya yace ware kawai hajia kar ki bari na canja mind dina na murde miki wuya


     Tsorata sadiya tayi jiki na rawa tace kuyi hakuri ko me kukayi dai dai ne,hakan ma is OK,motarta ta figa a 100 ta bar wajen,a boy ne ya kalli yaransa suka kwashe da daria kana yace men this girl inaaaa ey na bad girl,she stingy bad.wani ciki ashar ya kunduma yar kut...da wani dry leg nata,ko shape babu komai flat.


      Hajiya rahina tsabar yawan bokayen da tabawa aiki ba a San Wanda aikinsa ya ci omar ba,kowa kawai ta yarda kawai.ciki kuwa har karyar su HAJ bilki kawayenta.


     Dare ya tsala kishirwa ta fito daga room dinsu shan ruwa,tazo Palo ta jiyo nishi dakin omar sosai abin tsoro,lallabawa tayi ta shiga dakin omar a hankali ta murda kofar ta shiga,


     A kudundune ta Ganshi ya hada gumi yana ta karkarwa yana nishi,da gani mafarkin abin tsoro yakeyi,sai ciccijewa yake yana tirje tirje,tausayinsa iklas taji sosai karasawa jikin gadon tayi ta zauna gefen bed din hade da kura masa ido,A hankali tasa hannunta a kafadarsa kamar jira yakeyi ya juyo a sa hannu biyu ya damke hannun hade da kankamesa a kirjinsa,shuru iklas tayi tana matukar tausayawa oga,da gani matsala ce jikinsa babba,ba tare da ta zare hannunba ta Kurawa hadaddiyar sumarsa ido,tasha gyara tana kyalli yalala da ita,kamar TV haka ta kurawa surar Omar ido,ta shagala sosai sai da ta share lokaci me tsawo,farkaawar da Omar yayi ita ta dai daitawa iklas nutsuwarta,


     Zumbur ya mike zaune yana kallonta tare da mamakin rike hannunta da yayi a kirjinsa,mamakin iklas shine yana rike hannunta taga ya daina karkarwar tsoron,sannu oga sir,hannu takai zata taba wuyansa,make hannun Omar yayi ya watsa mata harara mind ur business pls,ruwa kawai zaki kawo min nasha,ni ba irin su Emma bane as u can see musulmi ne ni,so u better get ths in to ur skull, ki daina gigin taba min precious skin dina.


    Baki iklas ta tabe a fili tace sannu muslimu daga taimako,kuma hannuna kai ka kamashi zuwa jikinka anji hannun yarinya me laushi ba a sababa an wani kankameshi,wuf ta fece daga dakin,dan dai kawai ta tausaya masa ne amma da wlh baza ta kaimasa ruwan ba,


      Ruwa ta dauka faro da glass cup ta koma room din,sadaf sadaf ta ajiye can nesa dashi a tsorace take kadan take jira ta zura da gudu,kafafunsa ya daga hade da dafa cinya alamar zai mike,kararaf ta kwasa da gudu ai kuwa ta daki kofa da hancintaa garin gudu ji kake fas,wayyoooo ta furta hade da rike hanci,kara kwasa tayi da gudu zata arce,caraf omar ya riko hannunta ba tare da yayi magana ba ya cire hannun da ta rike hancin,


      Jini kadan ya gani alamar ta fara habo kadan,gashi kan tsinin hancin yayi ja ya kwarzane kadan,tissue ya dauko ya matsa jikinta sosai suna jin numfashin juna,tuni jikin Omar har ya shocking yana rawa a cikin jininsa,


     Ita kuwa iklas wani kasala kasala taji kamar ya danyi hugging dinta haka taji,daurewa kowanne yayi cikinsu,hannu yasa ya dago fuskarta ya goge mata hancin tas,yana karewa pink lips dinta kaallo,kamar ya dan.....lol


      Kije toilet ki wanke cewar omar, mika mata tissue yayi har wacce ya goge mata hancin, jeki nyt.cike da tunanin kyan dirin Omar ta fice,toilet ta shiga sannan ta koma dakinsu,


    Kaka ummi ke kuwa iklas zawo kikeyi ne?kin Dade daga cewa zaki sha ruwa sannan kiyi fitsari,ummi bigewa nayi da kofar toilet kinga habo ma nayi,sallallami kaaka tayi tana ta faman yiwa iklas saannu,harda shafa mata magani a hancin wajen da ta kwarzane,


   Ni kuwa nace su iklas badai iya karya ba.kwanciya sukayi kowannensu cike yake da tunani kala kala,iklas an kalli ceiling anyi kuri da ido ana tuno kasancewarta tare da Omar dazu,duk sonta da aikin gomnati sai taji da tayi tunanin salary ko ta gama schl ta fara aiki,ga mota tana ja,suna zaga kasashe ita da su suhailanta sai taji yanzu kamar tafi jin dadin tunanin oga omar,kawai fuskarsa in ta tuno dadi take ji,a'a juyi ta karayi taja tsaki,yanda omar ke daure fuska ta tuno sai taji sanyi,a ranta tace oh zuciyata yanzu fushin nasa ma birgeki yakeyi tab,da kyar bacci ya sace iklas,bangaren omar kuwa mugun mafarkin da yayi yake tunani,ga tunanin family dinsa musamman mama ko a wanne halin take oho,rayuwar da yake ciki yanzu ya tuno da iklas me kwai sai yaji dan sanyi a ransa,ya yanke shawarar yanda zai sa iklas ta masa wani acting yanda zaiji lafiyar mama da baffansa,hade da kwantar da hankalinsu,yasan iklas tsab zata iya,ko ya wannan abu zai kasance readers oho,za dai muji nan gaba.da wannan shima yayi bacci,


    Da safe su iklas sunyi shirin schl,omar kuwa fitowa yayi so yake yaga ya hancin iklas yayi,uniform ya gani sun mata kyau,bai taba ganin wacce uniform yawa kyau haka ba irin iklas,kallo ya kare mata suka gaisar dashi,ummi ma ya gaisheta,iklas ya kalla ya kara fakar idon ummi ya dagawa iklas gira daya,hade da nuna hancinsa yana murmushi me kayatarwa,tasan tsokanarta yakeyi ba wani dubiya,baki ta turo,ta juya masa baya tana yaba muguntar omar,ummi ta juya tana gyarawa suhaila jaka ya dan ja hijab din iklas kadan,waigowa tayi itama ta dage masa gira daya,alama yake mata da hannu kamar kurame,kaka ummi ta tarfa su,sosai sun bata daria,umaru shirmen iklas kake kulawa ko,so kake ka koyi shiriritarta naga alama,ummi kalli hancin ta fa,hmmm umaru baka da dama ai jiya a bayi ta bige da kofa,ta dade tana habo,da kyar ta samu tayi bacci,daria omar yayi sosai jin karyar da iklas ta tafka,kallonta yayi suna hada ido ta kifta masa wai ya rufa mata asiri,kafada ya rike alamar yaki din,kaka ummi na kallonsu tace ohhh yau kuma umaru kurame kuka zama haka,wlh ka daina saurarar iklas,ummi wannan jikar taki bata ji ne cewar omar. 


wani yaronsa daban Omar ya kara kira ya gwada masa gidan su iklas,dalleliyar wata motar omar ya dakko ya kai su iklas schl,sai kallon su iklas akeyi a schl.


     Shima dai Wanda ya kai su iklas schl bai San daga ina omar ya kirashi ba,gashi ko wanne da new sim yake kiransu,kuma yan amanarsa yake sawa aikin Wanda yasan duk runtsi baza su bashi matsala ba,kowanne sai ya gargadeshi kar ya fadi ya kirashi a waya.


    Iklas kam yau daga schl company ta wuce ta saro kaya,yaron omar ne ya kaisu ko ina ya dawo dasu gidansu sannan ya tafi


     Kafin su iklas su dawo omar ya fadawa ummi zai aiki iklas gidansu ta gano masa lafiyar iyayensa,umaru kai da kanwarka sai ka nemi izinina,dadi yaji sosai su iklas na dawowa ya sata ta shirya cikin doguwar Riga da mayafinta,wajensa taje yana zaune tsakar gida a kan kujera sanye da Riga armless fara,da black jean gashin kansa ya kara yawa,


       Ummi tana Palo suhaila na gefenta suna kallo da cin abinci,envelop ya mika mata nan ya Shiga tsara mata yanda zata yi acting a gidan nasu, hhhhhh iklas ta kama daria yanda taga Omar ya gwada maganar mata, kallonta ya tsaya yi,yanda daria ke matukar yi mata kyau, tsayawa tayi da dariar ganin omar ya kafeta da ido,daga bisani tace action ta fara gwada masa yanda ya koya mata har kara masa idea tayi,sosai sunji dadin moment din,iklas uwar shirme ji tayi inama suyi ta yin wannan film haka me dadi.


     Kudi ya mika mata na taxi tare da address ta tafi kuwa.yau zata ga gidan su oga da family nasa,ya za aga haduwar su cewar iklas.


    Sahar kam sai Allah ita cewa tayi Omar makaryacine yana can London munafiki za a ce ya bata kato dashi,to saceshi za ayi dan haka iyayenta suka ce ta dawo gida tayi zamanta tayi aikinta.haka kuwa akayi ta kwashe komai nata tas ta bar gidan cike da nishadi ta samu yanci.


    Tun daga waje iklas take kallon haduwar gida kamar baza a mutu ba,gate ta buga,masu gadi wajen biyar suka leko ganin tsaleliya iklas suka ce wannan da gani kawar yan gidan nan ce,suma mamakin kyan iklas sukeyi kamar larabiya,gashi da ganin rigarta ta masu kudi ce,dama a rigunan da Omar ya batane tasa daya,


    Da sauri sukace ta shiga suna ciki,tana shiga nan ta rantse a ranta da zata yi bacci ta farka ta ganta a wannan gidan to cewar zatayi ta mutu tana aljanna.


       


  Asmabaffa

ⓂⓂⓂ

    MA'AIKACIYAR 

         GOMNATI

          ⓂⓂⓂ


              25-30


By

Asmabaffa
    Page din nan naki ne DIYAR KATIBI.
    Tunani iklas tayi domin omar ya gwada mata yanda gidan nasu yake ba tare da tasha wahala ba ta gane part din maman omar,shiga tayi dakin part din tare da danna door bell din da omar ya fada mata,abdallah ne ya bude kofar,iklas dauke da hand bag a hannu an wani shanye hannu irin na wayayyun mata,kallon abdallah tayi da ganinsa kasan kanin oga omar ne,


     Kallonsa iklas tayi pls mama nake nema,OK shigo tana ciki cewar abdallah sai bin iklas yakeyi da kallo yanda yaga baby me kyau haka,shiga ciki tayi salati take maimaitawa a ranta yanda taga tsaruwan palon,a kujera ta zauna abdallah kuma ya hau sama domin kiran mama,suleim ce ta fito cikin shirin islamiyya,sannu da zuwa ina yini cewar suleim,lfy zo mana mu gaisa cewar iklas,zama tayi kusa da iklas,can iklas ta kunna video recording a wayarta tana daukan suleim,wani katon pic din omar ta gani a palon,suleim waccen yayankine?ae anty amma ya bace,an nemeshi ba a Ganshi ba,mama kullum sai ta yi kuka tana ta addua,dady ma addua yace mana mu  dinga yi,kinga su anty sadiya kuwa nurma sukeyi sosai,har kida suka kunna a gidan nan,suleim kwai surutu.


    Yanzu in suka ganmu da mama suyi ta mana daria,kuma anty sahar matar yaya omar ta gudu gidansu wai ba za ta zauna gidansa ba,gaban iklas ne ya yanke ya fadi jin an ambaci matar yaya omar,dama yana da mata? Take taji wani bakin ciki a ranta,gabaa daya jikinta yayi sanyi,cikin kankanin lokaci suleim ta bawa iklas labarin gidansu,duk da batasan su waye anty sadiya ba,suna haka mama ta fito ita da abdallah,yi tayi kamar tana latsa waya nan kuwa video take musu,tsugunawa tayi cike da ladabi ta gaisar da mama,mama kuwa me aiki tasa ta kawowa iklas kayan motsa baki,


  Ganin kalar girkin hadadde yasa iklas sauka kasa ta baje kamar gidan ubanta ta kama cin abincin cikin dabara takewa kanta video record tana cika baki da abinci,


    Mama da abdallah har suleim daria sukeyi ita kuwa iklas tana sani tayi haka dan su saba da ita,sai da taci ta koshi sannan ta kalli mama tace mama wlh har na dawo hayyacina bakuga wahalar Dana sha ba kafin na gano gidan nan,kwashe kayan mama tasa akayi,yan mata meke tafe dake ne? inji mama,sultan ne yayi sallama ya shigo palon,iklas taso ta ganeshi amma ta rasa Inda ta sanshi,shima bangaren sultan hakan take sai kare mata kallo yakeyi ya kasa ganeta,domin tun iklas na tallan kwai ya taba ganinta,yanzu kuwa ta kara haske,kiba,kyau da girma.


      Zama yayi suka gaisa da mama,iklas ma ta gaisar dashi,shi dai sultan wannan bai taba ganin me kyau irinta ba sai me tallan kwai da apple ta Frnd dinsa omar,kai har muryarma suna kama,amma wannan da gani yar masu kudi ce,waccen talakace haka Allah ke ikonsa wani ba dangi yayi kama da wani duk a ransa sultan ke wannan tunani.


      Iklas ce taga sultan na kallonta,shima sai da ta masa video record,mama iklas ta kalla tace mama dama wannan na hoton tayi nuni da yatsanta jikin pic din omar dake jikin bango ne,harrrrr su mama sukayi aka zubawa iklas ido a ji bayaninta,naje company dinsu Neman aiki da dan dadewa,shine aka turani office dinsa naje interview,shine yace bazan samu aiki a company dinsu ba,amma nayi hakuri kuma yana Neman alfarmata na kawo wa mamansa sako,


      Shi zaiyi tafiya ne,har naki karba amma ya dage,mama baki gani ba har kuka yayi kan sai nazo gida wajenki na baki sakon,Baku gani ba abin tausayi har kuka ya min cewar bashi da kowa da sukafi mama da baffa,sune farin cikinsa iklas ta karashe tana matsar kwalla,mama tace Allahu akbar da su suleim tuni hawaye na ambaliya a fuskarsu jin labarin omar,tabbas iklas ta tausaya musu amma ta dau alkawarin gano wannan lamarin dake faruwa da omar da family sa ko zata tallafa.


    Sultan ke bawa su mama baki bayan sun nutsu iklas ta zaro envelop daga jakarta ta mikawa mama,wannan yace na kawo miki,Allah bai bani iko ba sai yau,


       Mama batasan karantawa don bata so ta karantowa kanta bacin rai,sabo da wannan ta mikawa sultan takarda,sultan nutsuwa yayi yana karantawa can su mama suka ga yana daria da fara'a wannan ya nuna sakon dadi ne bana bacin rai ba.


    Kwace takar dar mama tayi taga guntun rubutu ne ma,fara karantawa tayi kamar haka:


    SALAM......MAMA NAYI MATUKAR KEWARKI BURINA KI DAGE MIN DA ADDUA INA DA MATSALA A LFYR JIKINA,KI BAWA BAFFA YA KARANTA DA KANNENA SULEIM DA ABDALLAH,NAYI KEWARKU,SULTAN MA ABASHI HAKURI,INA NAN A NIGERIA MAMA CIKIN KOSHIN LFY,BANYI NISA DAKU BA,ZAN DAWO SOON,KUNSAN BAZAN TABA YIN ABU BA KWAKWARAN DALILI BA,A SANARWA BAFFA NASAN SHIMA ZAI FAHIMTA.


    Dadi mama taji dukkansu sai murna da jin dadi sukeyi,iklas kuwa sai video take musu,mama ce ta rungumeta yata yar albarka mun gode kwarai,kowa godiya yakewa iklas,mama tace yaushe ya baki sakon?ya kai week nawa?sati dayafa kenan cewar iklas,,take kowa ya kara cika da murna,suka tabbatar da Omar yana kusa kuma lfy yake,hankalinsu ya kwanta,


       Dakin baffa mama ta nufa yana ciki ta shiga ta labarta masa komai tare da mika masa takardar,yana gamawa ya dago fuska cike da annuri,dama na fada miki ki kwantar da hankalinki yana nan ni nasan son namijin gaske ne, sai mu dage masa da addua,kira min yarinyar na ganta,


     Tare da mama suka Shiga dakin baffa,a kunyace iklas ta durkusa har kasa ta gaida shi,da fara'a ya amsa tare da yaba tarbiyarta,mama hakan take,daga bisani mama tace ki saki jikinki duk lokacin da kiga kina da lokaci ki dinga bullowa muna gaisawa,baffa ya kalli hajia baki fada min sunanta ba,oh kaga murna tasa na kasa tambayarta,yar albarka ya sunanki? UMMI kawai tace,bata San wanne suna zata ce ba.


      Palo suka dawo iklas ta mike rashe rashe kwance kan 3seater tana ta yiwa kanta selfie,taga gida me kyau,


    Suleim ta jawo da uniform tayi musu pic kala kala,abdallah ma haka,mama na gefe amma saida iklas ta dauka da ita,sultan ma kiransa tayi ya manne gefenta ta musu  kala 3.duk tayi ne sabo da ta nunawa oga omar.


       Sai daria take basu iklas ba boye boye waje ya burgeta ta yaba.sai 5pm tawa su mama sallama,an cika iklas da sha tara ta arziki,mama turaruka,atamfa kala biyu,baffa 20k ya bata,sultan ma 10k ya bata,ta fito tsakar gidan kenan iyayin iklas ya kaita ta dinga zagaya compound tana ta daukan selfie,har jikin motoci,tana haka ta kai garden,yaran haj rahina ta hango birjik a garden.


      Lallabawa tayi taji Suna ta gulmar su Omar suna zancen asiri,bata karasa ji ba sukayi karo da Aisha,kallonta Aisha tayi take taji ta tsani iklas,ga bakin cikin kyau da taga iklas ta fisu kaf,tayi imani wannan tafi omar ma kyau,


     Kwalar iklas Aisha taci ke gidan ubanwa zaki,?gidan ubanki cewar iklas,ai tuni su sadiya ma suka karaso wajen,iklas taga tabbas zaneta zasuyi,da sauri tace kuyi hakuri Ku saurareni, wajen sadiya aka aiko ni,sadiya cike da bala'i tace gani lfy,karewa sadiya kallo tayi tana tuno maganganun suleim yanda sadiya ta tsanesu ta tsani yaya Omar.a kan me za a zagi oga wlh ba a isa ba kunji iklas da karfin Halifax.


      Gajiya sadiya tayi ta dakawa iklas tsawa ke karki raina mana hankali fa,duka iklas ta makawa sadiya a kirji,ba tare da  sadiya tayi tsammani ba,,tana juyowa ta dullukawa Aisha dundu ji kake dummmmm ta arce da uban gudu, gateman sunga komai,su kansu dadi suka ji,domin su aisha sun gallabesu,tana zuwa gate cike da murna suka wangale mata kofa tace na gode da karfi ta ci gaba da gudu,saida tayi nisa da gidan sannan ta Shiga taxi sai gida.


      Su sadia kuwa sunyi suman tsaye,Aisha tace billahillazi duk ranar Dana hadu da yarinyar nan....wlh.....hmm...sai na kusa zare mata numfashi. Sadiya kasa magana tayi tsabar bacin rai,yarinya karama ta kwada mata duka haka.


           Taxi na tsayawa ta wuce gida sai daria takeyi hade da haki kamar tayi gasar tsere.oga Omar yana kwance a Palo bacci ya fara daukansa dan ya gaji da jiran dawowar iklas,dariarta ya jiyo ya fito waje sanye da wata dakakkiyar gezna milk color,yasha kyau,


       Fuska tamke kamar kullum ya kalli iklas ke lfy,kusa dashi tazo tana tuntsira daria hannunsa ta kamo,yarrrr omar yaji bai San sanda ya fisge hannunsa ba,kara sakalo hannunsa tayi ta jawoshi tsakar gidan tana murmushi ta shimfida musu tabarma,kaka ummi tana kallonsu domin fitowarta kenan zata je makwafta,murmushin manya tayi tasan iklas bata fiye tsoron maza ba ta saba da gogayya dasu,tayi talla a kwalta,ga unguwarsu hausawa kadan ne,dole mutum ya tashi haka,danma iklas kwai tarbiya,  sallama ta yi musu ta tafi gidan suna makwafta zasuyi aikin abinci sai dare zata dawo,


    Suhaila ce itama tayi sallama ta dawo daga islaamiyya,oyoyo beauty cewar omar dadi suhaila taji tace sannu da gida yaya omar,ta wucewarta dakinsu, 

 

      Iklas kuwa kalonta ta mayar gefen omar,sir dole kasha lbr yau,nan iklas ta kwashe komai ta fada masa,sannan ta nuna masa video da ta musu,omar harda kwalla ganin mama da yan uwansa abin sha'awa, yayinda iklas ta bashi daria sabo da shirmen da ta dinga yi a gidansu,kamar irin yar gida,omarma ji yayi hankalinsa ya kwanta ya kara samun nutsuwa.


      Kinyi kokari yan mata cewar omar,iklas kuwa cinyar omar ta dafa kasan me nake wa daria,zame cinyarsa omar yayi,ita kuwa iklas kallon omar takeyi kaamar jininta,kamar dan uwanta,kuma ita bada wata manufa take taba jikinsa ba,ga kuma unguwarsu sun saba da hakan sabo da yaren da suke unguwarsu,wannan ba komai bane wajensu.


      Wai pls oga sir su waye sadiya ne?kar ki kara ce min wani oga ko sir,sunana omar..sorry to ya omar,ina jinki suna ta zaginka da su mama har zance asiri sukeyi,ban gama ji ba mukayi fada.fada kuma?cewar omar,sisters dinane fa,shekewa da daria iklas tayi ta manta ta sake riko hannun omar daya,kash wannan zata kasheni wlh batasan yanayin Dana ke shiga ba a zuci yayi maganar,daya hannnun yasa ya cire hannun iklas a jikinsa,ji yayi hannunta kamar Auduga dan laushi.


Video ta kunna masa fadansu da su sadiya omar kanshi yasha dariar abin,sau 2 yana kalla,drama queen dama sun zaneki,tab ai wlh basu isa ba,wannan sadiyan me siri siri kafa kamar ta sauro,wasu zagada zagada dasu,tab Allah gidanku ya omar rida ridan tsofaffine ciki hhhh kaga wata me kwalliyar aljanu kuwa,baki ya bige mata sannan tayi shuru,kayan da ta samo ta nuna masa.


     Yana gani yace kinji dadinki,wayarta ya karba ya dinga kallon pics din iklas a cikingidansu,sai daria yakeyi,mikewa tayi zata kwace wayarta ta fara jin haushin dariar da yake mata,hanata yayi tana kokarin kwacewa ta kasa,sai haki takeyi,


   Zuwa tayi da iya karfinta zata makalkaleshi da sauri ya mike tsaye ya matsa kamar irin yaga wuta zata konashi,bai son ta haddasa masa masifar da take jawo masa da zarar ta rabi jikinsa,


    Pics yaci gaba da kalla har yazo kan nata da sultan,gani yayi kafadan sultan tana gogan ta iklas,wani takaicin iklas yakeji,zuciyansa ce yaji ta baci,ga wani kishi daya taso masa,wato ma yanda take taba shi haka takewa kowa,ai kuwa sai yayi maganinta,sai ta daina shashancin taba jikin ko wanne namiji.


     Kara kalla yayi yaga wato pics dinsu da sultan har kala 3.bai San sanda ya kwarankwatsa wayar da kasa ba,sai da tayi warka warka,tayi raga raga.tsaki yaja cike da bacin rai ya ficewarsa daga gidan baki daya.


Abinda Omar bai taba yi ba kenan,tunda ya dawo gidan su iklas bai taba gigin fita ba sabo da tsoron yanayin lafiyarsa.


   Iklas tayi matukar firgita kamar me aljanu,daga yi masa abin arziki ya zama tsiya


    Tsoro taji kar ummi ta dawo ta tadda Omar ya bar gidan,tasan yanda ummi ke kaunar omar,gashi bata San me yasa ya dawo gidansu da zama ba,,duk irin arziki da Allah ya musu,yanke shawara tayi gwara fa tabi bayansa ta dawo dashi.da gudu ta bi bayansa kamar zata tashi sama.


   Titin layinsu ta mike a 80 tunda uwarta ta kawota duniya bata taba yin gudu irin wannan ba,sai tareta matasa keyi suna gomanti gomnati,iklas amma ina Sam bata ji bata gani,


    Wani uban lungu ta shawo kwana,wata majalasa ce guda ta maza,sun hango gomanti na sheka gudu,wani cikinsu tace hey weyting?iklas tana gudu tace ba lfy ta wucesu fuuuuu...suna gani haka suma suka kwasa da gudu suka rufa mata baya.


     Tazo dai dai jikin wani shago taji an riketa caraf da mugun karfi,ido 4 sukayi da omar,da karfi tazo zata rungumeshi tana murmushi hade da Jan numfashi,gocewa yayi da sauri ya matsa ta rungumi iska,


     Kunya taji ganin namiji yafita kamewa da taka tsantsan.
Ayi min afwa idan an samu matsala readers dan Adam ajizine.Ina ji dake MAMAN SULTAN.

     


Asmabaffa

ⓂⓂⓂ

     MA'AIKACIYAR

          GOMNATI

           ⓂⓂⓂ


               30-35


By

Asmahbaffa    Masoyana masu karanta wannan novel duk inda kuke a kasar nan ga gaisuwata na sauke muku mota mota,kwando kwando.ina jinjina Allah kara nisan kwana me amfani da karfin ido.ayi min afwa kwana biyu banyi posting ba.
        Me hali baya fasawa fuskar nan kamar Wanda akace mama ta rasu! haka take a daure,tunda omar yabar gidan su iklas gabansa ya kara faduwa,gaba daya tsoro da fargarba ne ya shigeshi Wanda bai San dalili ba,tuni yaji ciwonsa ya fara dawo masa,yayi niyyar kiran driver sa domin ya gwada zuwa gida wajen mama,amma me yana fitowa daga gidan hankalinsa ya tashi,ji yake kamar ana hura masa wuta a jikinsa,gaba daya ya fita a tunaninsa,ji yayi yana neman sumewa shine ya tsaya dai dai jikin shagon da ya hango iklas na famfara gudu,cikin zafin nama ya riketa dan tabbas ya San nemansa ta fito yi,gashi magriba ma tayi,

  

    Iklas kuwa tunda taji kunyar gocewa da omar yayi dan kar ta rungumeshi, ido ta kafa masa,nan ta hango jikin omar na rawa kaf kaf kamar mazari,ga gumi na keto masa duk da cewar ba a Dade da dauke ruwan sama ba,kara kura masa ido tayi nan fa ya fara dafe kirji yana cije lips kamar zai fadi,idonsa sai wani lumshewa sukeyi,tsoro ne ya kamata,sir....ya omar wai lafiyarka kuwa?

 

      Hannu ta kai zata kama hannunsa ya boye hannun,fuska ta daure itama ta fisgo hannun nasa tare da cewa! muje gida ya omar baka da lfy,rike take dashi gam,shi kuwa ba musu ya bita,suka jera abin sha'awa kowannensu na ji da kansa wajen baiwa.

    

   Duk inda suka ratsa sai an kallesu an kara kalla,duk sun haske unguwar,kowa nuna gomnati yakeyi suna ai bro dinta ne yazo,me kudi ne,gashi nan gomnati ta daina talla,ta zama yer gayu,maganganu kala kala.


       Gida suka karaso lokacin Omar ya fara nishi ma zai fadi kasa,da sallama suka shiga,yana zura kafarsa daya cikin gidan yaji wani azababbiyar niima da kwanciyar hankali,take yaji gaba daya ciwonsa ya yaye lokaci daya...a ransa ya furta lallai wannan gidan ni'ima ne,


      Bayan sallar isha kaka ummi ta dawo daga unguwa,yanzu most of d time omar ke wa suhaila assignment, yau ma hakane shi yayi mata homework, 


misalin karfe 1 na dare iklas ta farka,hanklinta ya kasa kwanciya tana tunanin ya omar karfa ko bashi da lfy,


       Mika da hamma tayi ta kama shagwaba tana ummi fitsari ki rakani,farkawar ummi keda wuya ta fara masifa ba inda zani da tsohon Daren nan,ke kenan fitsari da zawo,dama haka iklas ke so,ficewa tayi sadaf sadaf da sanda ta murda dakin omar,a zaune ta ganshi yayi tagumi a gefen bed,dago kansa yayi yasan dama sai ita,


     A tsorace ta karasa kusa dashi sir omar bacci ka kasa yi ne?harara ya watsa mata,ki daina zuwa wajena da dare ko ba komai sabo da gudun zargi,ba kya jin magana,ki daina sani magana fa tam,baki ta turo kai ya omar Allah baka San a ma gwaninta ba,me zanyi ma ina tunanin ko baka da lfy ne that's y na leko ka,OK tnx as u can see am fine sai ki tafi.


    A shagwabe tana buga kafa to kayi bacci mana,dan ta tafi kawai sai omar ya kwanta a bed din,kafin ya mike kafarsa ta karasa ta hada leg nasa wuri daya ta mikar masa dasu,blanket taja ta rufa masa,a.c ta kara karfinta kana ta kashe masa light,ta fice zuwa dakinsu,da rarrafe ta shiga dan kar kaka taji tafiyarta, kwantawa  tayi ta  bar omar da tunaninta, yanda ta iya kula da mutum , wai bata ma auri mutum ba kenan  ina ga ta aureshi.lallai mijinta ya more,sahar dinsa ya tuno wacce ko kallon arziki bata yi masa bare ta gyara masa kwanciya,wai a haka ta waye kuma yar boko,ga me talla nayin abinda ta gagara yi.


    3days later omar yasa an kawowa suhaila sweet da snacks,wayoyinsa duka a flymode suke yana buga game a Palo,yayin da suhaila da ummi suka tafi kasuwa,iklas ta tafi kai kayan siyarwarsu makwafta,Omar bacci ne ya daukeshi a Palo,nan ya shiga mugayen mafarkansa kamar kullum,ya hada zufa,sai nishi yakeyi,iklas ce ta dawo da Sauri ta fada palon,tsugunawa tayi kasan kujerar da omar ke kwance,addua ta shiga tofa masa,falaq da nas,fatiha,ayatulkursiyyu,amanarrasulu,can taga ya daina mafarkin,dadi taji tace kai Ashe zan iya rukiyya ma in na dage,


     Omar ne ya bude idonsa cike da bacci,tashi yayi zaune, a hankali ya bude idonsa tare da aza su kan kyakyawar fuskar iklas jinjina kai yayi,a ransa yana fadin wannan yarinya tana da nacin tsiya,ruwa ta dauko masa da sauri,a ransa yace ikon Allah kaga shishigi.


       A gabansa ta tsugunaa tare da kallonsa cike da tausayawa, Jim kadan tace pls sir ka fada mana abinda ke damunka,inma baza ka fada min ba ka sanarwa ummi,in kuma baka son ummi ta sani ka fada min zan boye ma sirrinka,


   Maybe zamu iya baka shawara,bai dace ka zauna haka ba,in kuma kaki to zan fadawa ummi mafarkan danaga kanayi da kuma time din Dana ganka a bakin shago,


    Ido kawai ya zubamata yana kallonta har ta gama.Hannun iklas ya riko da hannu biyu ya zaunar da ita a kujera,kinyi alkawari in na fada miki baza ki fadawa kowa ba?da sauri  iklas tace ae wlh sai in kai kace na fada,I mean sai da yardarka.Good muje tsakar gida to sai na fada miki,cike da zumudi tayi waje.


    Farar kujera ta mika masa ya zauna itama haka,har sun dauki kusan 20mnt amma omar ya kasa bude baki yace komai,a zuciyarsa har ga Allah yana so ya fadawa wani matsalarsa ko zai bashi shawara amma ya kasa,daga lokacin da yayi niyyar sanarwa wani sai ya kasa furtawa.


     Gajia iklas tayi da zama ta kirashi cike da sanyin murya,ya omar kayi shuru,kallonta ya kara yi ba tare da yace komai ba,sunyi wurin 30mnt amma yaki magana


     Da kyar da sidin goshi ya cije ya furta bani da lfy a jikina,kamar ya?cewar iklas shuru yayi mata,haka ta hakura ta kyaleshi tunda ya kasa cewa komai,ita kuma bata gane me yake nufi ba.


     Har ta mike zata wuce  sai ta fasa ta dawo ta zauna inda ta tashi,tana zama ya zuba mata ido daga bisani yace zan fada miki next time not know,


     Zuciyar omar kuwa ko ya yi niyyar fadi sai yaji a cikin ransa ana gargadinsa,zuciyarsa na tafarfasa,bakinsa yayi nauyi sai ya kasa fada.


    Ya schl yanzu aji nawa kike?cewar omar dan kawai ya canja zance.suna hira su ummi suka dawo,ummi sai Murna takeyi ganin iklas tare da yaron kirki umaru.


     Bangaren sahar kuwa duniya take tsikara da tsinke,babu ta inda bata cokalar duniya,ta manta ma da aure a kanta.

Mama da baffa sun yanke hukuncin zuwa gidan su sahar domin yin bikonta. 


    IKLAS na gidansu yau Sunday haka kawai taji yau ta tashi da masifa,ji tayi duniyar ta mata zafi,kamar ta kunnawa kanta wuta,kowa ta tsaneshi,magana kadan sai ta balbale mutum da masifa,


   Ita kanta ta rasa dalili, mamakin kanta takeyi,omar na kallonta yanda takewa ummi da suhaila,da safe ma sai da ta Zane suhaila akan kallon film.iklas tana kwance ta baje a tabarma tsakar gida,omar na gyarawa suhaila farce yayinda ummi ke kitchen,haka kawai sukaji iklas a ta fashe da kuka wiwi. Kuka take sharba sosai tsakaninta da Allah,Har shidewa takeyi.


    Kallonta omar yayi da sauri ke kumafa?lfy kikewa mutane kuka,da ganinta yasan akwai matsala,ummi kuwa fada ta kamayi me yasa zaka saurareta umaru tunda ta zama shashasha ba sai tayi ba,yarinyar nan tun safe take bala'i! haka kawai ki dauki halayyar banza da wofi,wlh bazan laminci iskanci ba.


Omar bai so fadan kaka ummi ba sai yaji haushi danme zatayiwa iklas fada,ai ruwa baya tsami banza tunda iklas tana da juria haka kawai baza tayi kuka ba


A fili yace ummi ki kyaleta maybe tana da damua ne,pls ya fada da kalar tausayi,hmm ai dama nasan kai umaru baka ganin laifinta biye mata kakeyi shi yasa take kara shagwaba.murmushi yayi ba tare da yace komai ba,sai gomnati da ya kafe da ido wacce take ta sheshekar kuka harma da jingina kanta ki?? Jikin bango tana ta yi.


     Ranar haka ta kwana tana kunci da bakin ciki,washe gari Monday haka ma taje schl kowa cin ubansa takeyi ba mutunci...


     11:30am dai dai suna class taji kamar danshi a kasanta ita kanta ji takeyi kamar acikin ruwa ta zauna,mikewa tayi tsaye ,Ai firgita tayi sosai,tabbas shine! jini ne,wato abinda takejin lbr period, ta fara itama,abin yazo kanta.


   Kunya taji yau kam ba zaman schl dole ta tafi gida,hijab din wata Christian da bata sawa ta ara, ta daura saman rigarta ta rufe wurin daya bata mata uniform.


    Omar zaune a Palo yana danna computer sanye cikin jallabiyya yar ubansu fara sai kamshi yakeyi,sumansa tayi yawa sosai sabo da ya jima baije an rage masa ita ba,sai ya kara kyau musamman da baya fita sai ya kara haske da sheki.


     Ummi na gefensa suna ta labari,iklas ce ta shigo ko sallama babu ta wuce su ummi da omar fuuuuuuuu kamar zata tashi sama,su har sun tsoratama suna tunanin ko lfy.


    Minti 2 tsakani ta kara fitowa daga room dinsu wannan karan har gudu ta hada dashi,waje tayi kofar gida wani shago ta shiga,pad ta siyo ta kara dawowa ta wuce su ummi,sai gata ta fito da Riga,da wasu tarkace a Leda,toilet ta fada karaf...... kararaf ta rufe kofar,suna jinta tana ta kwaramniya da botiki da ruwa.

Asmabaffa

ⓂⓂⓂ

    MA'AIKACIYAR 

         GOMNATI

          ⓂⓂⓂ


             35-40By

Asmahbaffa
        Ta kai wurin 1hr a toilet sannan ta fito,mikewa omar yayi ya leka ta window ya hango iklas tana shanya kaya,daure take da zani da hijab a jikinta,


 Omar ganin iklas ta wanke uniform dinta ya sashi nazari ko lfy?amma dole sai ya tambayeta yaji meke faruwa da ita, Shanyar ta gama ta shigo palon da sallama, kaka ummi ce ta amsa tare da kallon iklas sama da kasa,ke kuma lfy?me ya sameki?


     Kunya ce ta lullube iklas sai take ganin kamar kowa ya gane halin da take ciki,sai wani matse kafafu takeyi,su ummi fa sun kasa ganewa,wai me ya sameki ne iklas?ni yar nan na shigesu,


    Umaru tayani figa uwar kishiya ta zama kaza,iklas kuwa daki tayi wucewarta ta bar ummi na sallallami,shiryawa tayi cikin dangalalliyar sabuwar doguwar rigarta fara me digon ja,rigar ma da kadan ta wuce gwiwarta,irin kayan da iklas tafi so kenan,


       Turare ta shafa yau sosai a jikinta kamshi kawai takeyi ta ko ina,batayiwa kowa magana ba ta wuce kitchen,tea ta hada me kauri ta dawo Palo kusa da omar ta zauna a 3seater da yake zaune yana danna system.


     Iklas Sam ta kasa zama,sai taji kamar period zai bata mata kayanta,shi yasa minti biyu uku sai ta mike tsaye ta waiga ta kalli bayanta,sai ta wayance kamar za tayi mika,


     Omar ta gefen ido yake kallonta,ya kasa gano matsalar iklas yau,ummi kuwa tun tana masifa har ta kyale iklas.tsakar gida ta koma ta zauna a farar kujera ita kadai,wai nufinta ko da zata baci to ita kadai zata gani,


    Ta kasa sakewa Sam ta takure waje daya yau ko akwalar wayarta ta kasa dauka bare tayi danne danne,Ummi ce ta kalli omar....umaru dan Allah jeka wurin yarinyar can kaji meke damunta,tunda naga ni baza ta fada min ba, watakil in anyi dace kai ta fada maka,


    Sai da omar ya dauki 5mnt sannan ya fito waje ya nufi inda iklas ke zaune,ta hada kai da gwiwa sai hawaye takeyi tare da kallon gabas ta daga kai sama tana addua,fadi takeyi Allah ka yayemin wannan abun daya sameni,


     Idan taji zubowar period zuuuuuu sai tace wayyyoooo Allah na,ta kara daga hannu tana ta zuba addua kan Allah ya yaye mata.tsawa omar ya daka mata! lfy kiki dami mutane,shuru tayi tana kwalla idonta yayi jajir,dake fa nake karki bari raina ya baci..


    Kallonsa tayi amma kunya ta hanata fada masa meke damunta,kujera shima ya jawo ya zauna,suna zaune kowa yayi shuru,omar sai latsa wayarsa yakeyi,sun kai kusan 2hrs iklas ta mike ta shiga daki,fitowa tayi dauke da bakar Leda da abubuwa a ciki ta shige toilet,


    Nan ma ta Dade sannan ta fito,ledace kulle a hannunta zata jefa a dustbin,fisge ledar omar yayi yana kokarin dubawa,ai iklas kukan kura tayi hade da kurma ihu ta makalkale omar,wayoo ledata dan girman Allah kar ka bude min,dan Allah kayi hakuri,gani tayi da gaske budewa zaiyi,kuka ta sa masa sosai tana rokonsa,pls ya omar karka bude min,


      Omar kam ko kulata baiyi ba sai bala'in da ta haddasa masa a cikin jikinsa sanadiyyar Makalkaleshi da iklas tayi,amma ya rantse sai ya gani me take boye musu,ledar ya bude pad din da iklas ta cire ya gani,ai da Sauri ya rufe idonsa ya jefa mata ledar da sauri,


    Iklas kam fashewa tayi da kukan takaici tare da zabgawa omar harara,4eye sukayi yaga yanda iklas ke harararsa,kallonta yayi ya saki shu'umin murmushin sa me rikita yan mata,


    Ki harareni da kyau kazamar banza dama nasan bazai wuce wannan ba,kinbi kin damu mutane da kuka da masifa,wurin da ta shanya panties ya kalla jiba duk kin baza mana wannan a gida salon wasu su shigo sugane size naki.tun dare bai miki ba ki kwashesu daga nan ki kaisu can baya.


       Omar Ya kai kofar Palo zai shiga ya juyo ! ki tabbatar kin wanke mana toilet neat kar na shiga na shaki dirtyn ki.kallon omar iklas tayi hade da sakin kuka da karfin tsiya tana shure shure,


       Kaka ummi ce ta fito da Sauri jin kukan iklas, shima Omar tsayawa yayi ya fasa shiga dakin,umaru lfy?cewar ummi,hmm ummi girma ne fa ya kama jikarki, bata da lfy period ne cewar omar ko kunya bai ji ba.


    Dogon tsaki ummi taja shine kika hanamu jin dadin rayuwa ja'ira tashi kar cikon kunzugun naki ya goce ki baci.


    Daria Omar yayi ya faki idon ummi yawa iklas gwalo,daria da kuka iklas keyi, yanda Omar yayi gwalon shi ya bata daria kamar wani tom.


     Baffa da mama ne suka kama hanyar gidan su sahar domin yin bikonta tunda yanzu sun San dansu yana nan lfy,an musu tarba ta ban girma,maman sahar tunda taji biko sukazo ta daure fuska,cika take tana batsewa,dady Baban sahar kuwa fada da masifa ya fara,ta inda yake shiga bata nan yake fita ba,gaskia alhaji mohd ka raina mana hankali,billahilazim badan kai abokina bane da sai nayi kararka,kuma dan naka ya daawo ya sakar min yata,na gaji da azabtar da ita da kukeyi,ita kadai Allah ya mallakamin sannan Ku dinga min wasa da ita,fafafafaffa maganganu marasa dadi Baban sahar ke yi, haka baffa ya Shiga bada hakuri da Neman sulhu amma Sam maman sahar ta janye mijinta suka shige room suka bar su mama zaune.haka dole suka dawo gida,cike da takaicin wulakancin da iyayen sahar suka yi musu.ba komai duniace cewar mama.        Haj rahina burinta ya kasa cika,ta kori Omar daga gida domin ta kwashi naira a wajen alhaji mohd amma hakanta ya kasa cimma ruwa,domin baffa ya daina Sakar mata fuska ma,bare ma ta samu dama,ta rasa ta wacce hanya zata bullo masa domin so take ta yashi rabonta tunda wuri.sabo da haka ta kara Neman haj bilki kawarta domin ta bata shawara.


 

    Naja na hango a kitchen ita da wata me aikinsu sai dungurewa yarinya kai takeyi tana zaginta ta uwa ta uba,duk yan uwan na kallo ba Wanda yayi magana har umman tasu haj rahina,yar aikin gajiya tayi tace dan Allah ki daina zagar min iyaye,kafin kace me naja ta ebo soyayyen man gyada akan gas ta watsawa yar aikin,tare da kunduma ashar,


    Ihu sosai takeyi tana kuka tare da Neman agaji,rankwashi sadiya ta zuba mata sannan a wulakance suka dauketa zuwa hospital daga nan suka maidata kauyensu.


      Yau kwanan iklas 1 tana period yau Sam  kasa zuwa schl tayi,omar kuwa wani new sim card yasa ya kira yaronsa hade da bashi umarnin kawo pad ,iklas na zaune taga an shigo da pad da yawan gaske,kamar Zara bude shago.


   Godiya tayiwa omar,ki daina godemin fatana ki wanke mana toilet sosai.Baki ta cuno cike da shagwaba haba sir kasan fa kai yaya nane sai kana bani kunya,ai kasan dama ni ke gyara gidan ko,?


       Kafe iklas da kallo omar yayi,in tana shagwabar nan birgeshi takeyi,shi a kanta ya San shagwaba na yiwa mata kyau sosai,lalacewa yayi wajen kallon iklas na zuba masa shagwaba.da kyar ya jawo nutsuwarsa ya mannata jikinsa tare da cewa hope kin iya wankan musuluncin dai ko?daria iklas tayi ya omar bafa a asarar kudin tara in fadama babu kalar da ban sani ba ehe,


       Lumshe ido yayi wani nishadi da dadi ya tashi a sararin samaniya a dirga a zuciarsa tsabar iya fadan OMAR da iklas tayi,a dunia yana son yaji iklas tace masa omar ji yake kamar sunansa yafi na kowa dadi a dunia,


     Ya omar kazo yau da yamma muje yawo kaga kai baka fita,kai kawai ya daga mata dan ta kara kashe masa jiki,ta tsinka masa jijiyoyin jikinsa jin  ya omar again daga bakin iklas,


     

       Karfe biyar iklas ta fito sanye da wata arniyar super atamfa dinkin riga me coler da dogon hannu Riga da skert,bata daura dankwaki ba gyale ta yada,ta sha kyau pose ta dauka pink kalar atamfar takalmi ma same color,


     Numfashinta ne ya dauke ganin omar sanye da 3quater arsh da riga T-shirt milk color sai rubutu da pink ansa defence da babban baki,yayi kyau sosai ummi sukayiwa sallama,omar na fargaba da tsoron fita sabo da lafiyarsa.


      Iklas kuwa ta nace sai ta kaishi yawo,sun fita iklas ta ga wata sabuwar mota dal arsh color,mota ta alfarma ta fita kunya ta nunawa a gari,zagawa Omar yayi ya shige mazaunin driver,itama ta shiga gaba,suka fasa gari,ko Nisa basuyi ba ciwon omar ya fara motsawa,iklas ma ta kula da hakan,to shi wannan meke damunsa haka cewar iklas a ranta,


     Ciwon karfi yakeyi sosai har driving yana nema ya gagareshi,iklas ta tausaya masa ganin yanda ya fita a hayyacinsa lokaci daya,hannunsa daya ta kamo ta rike gam cikin nata,sabo da haka ya gangare kasa da hannu daya yake driving har yayi parking gefen titi,


    Duk ac dake motar omar gumine ke keto masa,iklas du ta tsorata ta rude tausayin Omar takeji sosai,hannunsa ta kara damkewa tare da goge masa gumi da handkerchief tana tofa masa addua,


       A hankali yaji sauki amma da zarar iklas ta zare hannunta cikin nasa sai ya fara jin ciwon zai dawo,kawai sai yaja hannunta har kan sitiyarin ya hade da nasa ya ci gaba da driving,har sukaje city wani tsadajjen wurin shakatawa ya kaisu,na manyan yara kowa ka gani wajen to karshene wajen rike doller.


     Iklas yar kallo ta zama,hannunta cikin nasa ko ina birge mutane sukeyi sai kallonsu akeyi,da yawa sun zata ango da amarya ne,iklas har wani gadara da yanga takeyi ita a dole babbar yarinya,omar na kallonta ta gefen ido daria yakeyi a ransa kawai,


     Dan zagawa yayi da ita,maza kowa kallon iklas yakeyi sabo da baiwar kyanta,harma da wasu matan amma su omar yafi yi musu kyau,baya son ciwonsa ya tashi that's y kawai ya musu take away,wannan karon iklas hannunta ta gwiwar hannun omar ya sakaloshi, istigifari yayi wai a bisa lalura ya rike hannunta,


    Sunzo jikin mota zasu shiga kenan motar sultan Frnd din omar ta danno kai,omar na Jan motarsa sultan shi kuma ya parker a wurin,tabbas sultan yaga omar amma gani yakeyi kamar shi kamar ba shi ba,kai tabbas wancan omar ne  cewar sultan,amma yayi mamaki da yaga kamar yarinyar nan da taje gidan su Omar takai sakon takarda,kai sultan kansa ya kulle,to omar da mace?aure yayi?to meke faruwa da Omar haka,amma kuma kamar me tallan kwai ce tare da omar.duk sultan ke zancen zuci.


    Yasan idan ma yabi bayansu yanzu sun bace masa,da ganin kalar motar ma da tsadarta gata sabuwa yasan sai omar,shine keyin too match da kayansa da mota most of d time,kuma shi ke yawan order new cars don kawai ya hau yaji dadinsa.


    Bangaren Omar kuwa yaga shigowar sultan,yaso ya masa magana amma sai yaji ya kasa,bazai iya ba,katon shopping mall ya tsaya sukayi siyayya da yawa stl hannunsu na damke da juna,nan ma wani cikin yaran sadiya yan daba yaga omar,amma kwokwanto yakeyi kamar yanda sultan yayi,


     Suna karasawa gida sun kwashe kayan da suka siyo tas,Omar ya kira yaronsa yace ka dauke motar mutumin ya fasa amfani da ita.bazai siya ba,yaro shi ya zata Omar business sukeyi.bai San oganne da kansa ba.ya musu haka ne dan karma su San inda yake.kowanne ya Kira tsarashi yakeyi.


       Omar da iklas mamaki kowannensu keyi tare da tunani to me yasa idan Omar na gidansu su iklas baya ciwon,me yasa da suka fita ciwonsa ya tashi amma tana rikeshi ya warke,idan ya saki hannunta sai ciwo ya dawo,tofa readers koma mene zamu ji nan gaba.


   Omar kullum yana yin mugayen mafarkansa,washe gari iklas ta dawo daga schl suka shigo gidan tare da Frnd dinta dan unguwansu wato saleem,zai kai 32yrs kusan made din Omar ne,


      Ummi ya gaida tare da mikawa omar hannu,da kyar Omar ya mika masa hannun,tsakar gida suka koma shi da iklas suna ta hira suna daria,ummi ta shige room,bakin ciki omar keji a ransa ganin saleem da iklas tare,


     Kujerar dake jikin window ya dawo yana jin me suke cewar dama burinsa kenan,ruwan jarka Omar ya dauka ya bude,ta window ya zuro robar dama iklas da saleem suna saitin window,kwara musu ruwan omar yayi a Kansu,.  
       Asmabaffa 


  Godiya dubu readers.

ⓂⓂⓂ

    MA'AIKACIYAR 

         GOMNATI

          ⓂⓂⓂ


              40-45


By

Asmabaffa     

        Ruwa kawai iklas da saleem sukaji a jikinsu,kara shararo ruwan yayi tas ya juyeshi jikin saleem da iklas,da sauri suka mike tsaye,omar na jikin window yana zabga harara,ya omar ka jikamu fa da ruwa cewar iklas,so what ni nace ku zauna jikin window,nazo zan zubar da ruwa ni na kula da akwai mutane nan?


    Amma ya omar jibafa yanda ka jika saleem,sorry saleem hannu ta kai zata karkadewa saleem rigarsa,wata uwar tsawa omar ya bugawa iklas...wlh wlh if u dear touch that guy yau jikinki sai ya fada miki,saleem kallon omar kawai yakeyi yana tunanin to me yayiwa wannan mutumin? Daga zuwa wajen iklas.


   Kallonsa iklas tayi haba ya omar me nayi ma kana daga cikin room kawai ka leko ta window sai fada kake mana,ok bakiyi komai bama ko...ki taba jikinsa ki gani ke na rantse da Allah yau Indai hannunki yakai jikin wannan sai na zaneki tas  a gidan nan.


     Malam pls ka tafiyarka ka daina zuwa wajenta an mata miji a kauye,daga yau ka kiyaye...ni wlh ba wani miji da akamin cewar iklas,omar ne ya fito waje ransa bakikirin,yana fitowa iklas ta fada toilet da gudu ta banko kofar,


    Saleem takaici ya kamashi ya bar gidan yayi ficewarsa,omar kuwa jikin toilet yaje gwara ma ki fito kafi na bude toilet din ta karfi na kamoki,daria iklas tayi naki na bude kuma ka balla kofar mu gani,abinda kai baka da karfi,wani karfine da kai,amma kika gudu me yasa baki tsaya ba,ai ni wanka zanyi shi yasa kaga na shiga toilet.


         Murmushi Omar yayi,na kyaleki yarinya tunda matsoraciya ce ke,ka jira na fito ka gani mana...cewar iklas,sai da ta tabbatar omar ya shiga daki ta fito sadaf sadaf,suhaila ce tace anty kiyi min gugar kayana,ke baki isa ba bani da lokaci unguwa zanje yau.


      Kije ummi ta miki,shiryawa iklas tayi cikin tsadajjiyar shaddarta para kal da dinki light blue kalar zaren,takalmi da jaka da mayafi du light blue,fitowa tayi omar ta gani a Palo wajensa taje ya omar zanje unguwa anjima kadan zan dawo,


     Ke kullum wai in baki fita ba Sam bakya jin dadine?no sir kawai dai wannan fitar me muhimmanci ce,to muje tare mana cewar omar,ni bazani da kai ba ciwonka ya tashi haka kawai,rannan hannuna har zafi ya min tsabar rikewar da ka masa,


       Sallama tayiwa omar tayi tafiyarta,direct gidan su omar naga ta tsayar da me taxi,masu gadi suna ganinta suka su bude mata ta shige,tana shiga sukayi ido 4 da Aisha,ai Aisha tana tabbatarwa ganinta ta koma part dinsu,yau ta fasa fita sai tayiwa yatinyar nan dukan kawo wuka,


    Tana shiga ta sanarwa sauran sis nata,shegiya Allah ya kawota zata ci ubanta yau wlh,sadiya kuwa wata sandar karfe ta dakko.tana Ashe yau za ayi daukan rai,kwanan wata zai kare,naja jeki waje ki jira tana fitowa ki mana flashing.


    Ita kuwa iklas part din maman omar ta wuce,hannu bibiyu suka tarbeta,yau iklas an sami waje har kitchen ita ta taya mama girki,wajen 5:30 tayiwa mama sallama ta fito domin tafiya gida,


    Tazo tsakiyar gidan su sadiya suka zagayeta kafin kace me sun rufe ta da duka,sai da suka farfasawa iklas jiki,da kyar mama da masu gadi suka kwaceta,


   Hhhh Allah sarki iklas da kyar take motsi ko ina jini,fuskarta ce kawai take normal,hospital mama tasa driver ya kaisu ita da iklas,dressing akayi mata,mama tayi tayi iklas ta bari su kaita gida amma taki yarda,dole suka kyaleta ta shiga taxi ta tafi gida,omar da ummi hankalinsu ya tashi ganin ba iklas ba labarinta,har dare shuru,Omar sai tsaki yakeyi ya kasa zaune ya kasa tsaye,sai duba agogo yakeyi,


    Shaddar iklas ta baci da jinin dukan su sadiya,sannan gashi period din da takeyi shima garin fadan pad ta goce,duk ya bata mata jiki,tana dingishi hade da nishi ta rarrafa ta shiga gidan,su ummi ta gani tsaye a tsakar gida hankalinsu tashe,da gani ita suke jira,tana shiga da sauri suka tareta,


     Rushewa da kuka iklas tayi,tana ta kuka me ban tausayi,jikinta suka gani duk rauni,omar ne ya riko hannunta,accident kikayi? cewar omar ,cikin sheshekar kuka iklas tace wash...was...wasu suka dakeni,sai ta kara sakin kuka,


      Su waye?wanne yan iskanne suka Dakar min jikata marainiyar Allah ummi ke fadi,wasu ne ummi,idan kin sansu ki fada min cewar omar,ni ban sansu ba kawai sunce na zagesu wai,omar kuwa Sam bai yarda da zancen iklas ba.ummi kuwa yarda tayi tace Allah zai saka miki,muje kiyi wanka ki gasa jikin.


    Ruwan zafi ummi ta hada mata kana tayi wanka,tana daga cikin toilet ta kwalawa ummi kira,ummi kuwa bata kusa sai omar dake zaune a kujera,me kike so a miki ummi sallah takeyi,pls sir wata Leda zaka dauko min a room kan bed dina,dakin su iklas ya shiga ya dauko ledar wacce ba komai bane ciki face pant da pad,tsaki ya ja karbi kayan kazantarki malama,hannu ta miko ta window ta karba,omar kam hannun nata ya bi da kallo,yanda suke masu matukar kyau ga ruwa jiki sunyi fresh fari tas, shirya kanta tayi, tea omar ya hada mata ta sha,duk abinda sukeyi ummi tana sallah tana kallonsu tare da jin dadi, suhaila harda kukan tausayin iklas.


    Gomnati sai kuka takeyi tana yarfe hannu abin nata harda shagwaba ya koma,omar kuwa tausayi ta bashi har wani lallabata yakeyi duk zatonta zafin ciwo ne,kukan nata jinsa yake har ransa.


     Haka sukayi fama da iklas har ta warke,kamar kullum iklas ta fito daga schl a gefen titi wata mota dalleliya ta parker a saitin iklas,sauke glass kasa akaayi,ba kowa bane face sultan,yazo wucewa ya hango wata kamar ummi da taje wajen maman omar,wacce ya gani da omar yana kokwanto,


    Gaisawa sukayi ummi kike ko?yea ya gida ya aiki?cewar iklas dan ta San sultan,ahmmmm...kamar ke na gani da omar rannan a garden kingdom ko?da mamaki iklas ta nuna Sam bata San waye Omar ba,ta manta ma da wani omar,wanne omarfa?frnd dina mana Wanda ya baki envelop ki kaiwa mamansa.ohhhhh na tuna dama sunansa omar?ai na manta ma,pls ya koma gida kuwa,


      Au dama bake na gani tare dashi ba,gaskia ba ni bace,maybe wata ce,ok pls kin taba yin sana'ar talla?cewar sultan.mene kuma talla ban gane ba.it's OK bari naje na gode fa,sultan yaja motarsa yayi gaba abinsa.


      Da sauri iklas ta sha kwana,ko nisa batayi ba wasu Igbo suka parker sukayi mata lift,har taki shiga motar saboda yan iska ne a unguwar,sabo da kar sultan ya ganota ta shige motar ba tare da tunanin komai ba,


     Joseph ne ya dawo baya kusa da iklas India shi kuma nmandi ya ci gaba da tukinsa,ga hanya kusa amma sai suka canja suka dauki ta nesa wacce za a Dade ba a zo layin su iklas ba,


   Sai shawagi sukeyi da ita a mota,Joseph ne ya matsa jikin iklas,ta kara matsawa,har suka kai karshen bangon murfin motar,


      Iklas sai hakuri take basu tana rokon su sauketa amma ina,tuni Joseph ya fara shafa cinyoyinta,kuka ta saka musu,amma sai daria sukeyi mata tare da kara kwakwumeta,manne jikinta tayi waje daya yayinda shi kuma ya sutale hijab dinta,wow this girl fine woooo,omoh see her hair like arabs girl,


      Kirjinta ya fara kokarin shafawa ta tsala ihu, make bakinta yayi,a take ya fashe yana jini har hancinta,tafiya sukeyi har sukazo gidan su iklas basu gane cewar gidansu bane,omar ya leko kofar gida yana jiran suhaila ta kawo masa recharge card daya aiketa ta siyo masa,


      Iklas ya hango a bayan motar wasu kuma mutumin taba jikinta yakeyi,iklas kuwa tana ganin gidansu ta kwala ihu tana Neman agaji, su Joseph tabbas sun ga alama zata tona musu asiri,gashi ta makale jikinta ko kirjinta ya kasa latsowa,haushi yaji ya fesa mata mari ya taka birki kuuuuu,ta fito kuwa da gudu suka ja motarsu da gudun tsiya.

 

    Suka bar unguwar,Omar kam ya gama tsorata da lamarin iklas, ya rasa ma tantancewa me yakeji a zuciarsa, wanne kalar bakin ciki ne yake ji ya kasa ganewa.


       Hannun suhaila ya ja sukayi cikin gida, kallo daya yayiwa iklas ya dauke kai,baki duk jini da hanci,a waje ta tsaya ta goge jinin sabo da ummi,


     Wanka tayi da sallah taci abinci,sai istigifari iklas keyi a ranta, duk da tasan bata da laifi amma ai ganganci tayi tasan yan iskane amma ta shiga motarsu,


    Ba abinda ya dameta irin kallon da Omar ya mata,haka kawai taji ta shiga damua,gashi ko magana yaki yi bare ta samu damar wanke kanta,yanzu zai mata kallon yar iska.kunyarsa take ji sosai,duk tayi wani sukuku da ita,ummi har tambayarta tayi ko lfy?amma tace normal take gajia ce.


          9:30pm washe gari kowa ya tashi banda Omar, yau ba schl Saturday, ummi ce ta umarci iklas da taje ta Kira Omar suyi break,kwance ta sameshi sai marfakansa yakeyi, tashinsa ta fara yi.a tsorace ya tashi zaune daga shi sai boxers, tsoro ne ya kamashi sosai kan mafarkin da yayi,bai San sanda a rungume iklas ba,yana shakar kamshin wuyanta tare da sakin ajiyar zucia
Asmabaffa

ⓂⓂⓂ

    MA'AIKACIYAR

         GOMNATI

          ⓂⓂⓂ


              45-50


By

Asmabaffa
      Na gode  masoyana Allah karo karfin ido.  

     Kiciniyar kwace kanta takeyi amma ya mata rungumar karfi,da kyar ta fara zamewa cikin magagin bacci omar yace 2nmt pls.....tsayawa tayi cak tare da lafewa ita dama iklas ta Dade da son ta jita a kirjin omar,bata San me yasa ba kuma ta rasa dalilin da yasa jikin omar ke birgeta.sun dauki minti biyar haka omar ya dawo normal,jinsa yayi manne jikin mace ai bai San sanda fancakalar da iklas daga jikinsa ba,sai da ta fado kasa daga bed din.


       Masifa ya fara IKLAS karo na farko da Omar ya kira sunan iklas,wani zirrrrrrrr taji lokacin da omar ya furta iklas,kallonsa tayi tare da tsilli tsilli da ido tana Sosa gashi,me ya kawoki dakin nan,mikewa yayi idonsa jajir ya damki kunnenta,kara ta saki kadan,ba kyajin magana ko iklas,am I ur mate? Ke bakya banbance tsakanin maza da mata,bayan yan iskan da suka saukeki dazu kinga bance miki komai ba shine zaki sauke iskancinki kaina ko?


     Ina ina ta fara ....to wai...wai ba kaine ka janyoni jikinka ba kuma ka rokeni kan na tsaya,har hawaye kayi fa wai kar na tafi,kuma kace kai dadinka kake ji,kukan karya ta fara yi,kuma ni taimaka maka nayi,daga taimak....shut up tashi ki fita mayyata kar ki kuma zuwa min room kije kiyi raping dina,ki samin kazamin jikinki duk dazu wasu gardawa sun gama goga jikinsu a naki.


    Kuka ta saka masa harda rufe ido da hannu,dama nasan yar iska zaka na kallona,na rantse da Allah billahillazi la'ila ha illahuwa Allah daya ragemin hanya sukayi shine suke kokarin tabani sir.


   Kaga Allah kallo wurin da suka dinga marina akan naki yarda ai kaga jinin ma ko,ni ban wani gani ba ke dai kawai kin lalace jikin maza kike so,in auren kike so ayi miki mana,har kayan daki zan miki, cewar omar


Iklas tsalle tayi ta make kafada  Allah kiyaye na haihu na ragwaje,ai nasan ma yanda kake ji dani baza ka bari amin auren wuri ba,tunda kai kaka tana jin maganarka.


     Igbo za a aura miki tunda su kike biyewa suna lagudaki.hawaye ta fara, wlh sir na fada ma ni ba yar iska bace,Omar yasan gaskia kawai maganinta yake son yi sabo da ta daina ganganci.

 

    rike haba iklas tayi kamar gaske tace ohh sir wai kai wanne mai kake shafawa ne?mene kuma?hmmm jikinka Allah ya Omar kamar flour baka ji ba.daria ce ta kwacewa omar,ga iklas tayi wani zaman cin tuwo a kasa, banza omar ya mata.


    Minti 1 iklas tace yaya?kinga get out,kofa ya bude mata tare da kamo hannunta ya tankada keyarta waje ya rufe kofar,sai da ta kusa faduwa kasa,tunawa tayi bata fadi kiran da ummi tace tawa Omar ba,jikin kofar ta Dora kanta ya Omar kazo inji ummi muyi break,tsaki yaja ke kinfa isheni kije zanzo wanka zanyi...ok.


       Kamshin omar da suka ji shi ya basu tabbacin fitowarsa wani danyen yadi ne sanye jikinsa light blue,har kasa ya gaida ummi,umaru wannan kwalliya haka kamar me zuwa zance?amshe zancen iklas tayi haba ummi ke ba dama mutum yayi kwalliya sai kice zance zai je to shi ya omar wa yake da ita,ina yake fita Da har zaiyi wata budurwa, to uwar shishigi ki bari umaru ya bani amsata mana,


    Murmushi omar ya saki ummi bikon matata zanje,tayi yaji sabo da rashin ganina da batayi.sallallami ummi ta fara yanzu umaru kana da mata amma baka fada min ba,ayi hakuri ummi,yanzu ma so nake iklas ta rakani can.dole kaje ai baka kyauta ba umaru.


    Da karfi iklas tace bazanje ba kaje kai kadai ina ruwana da wata matarka,ni nasa ka aureta,zamana takeyi,kai ta shafa can kaje da wata badai ni ba.cike da masifa ta mike zata shige daki,omar kuwa daria kawai yakeyi kadan kadan wannan masifa ta iklas da takeyi,riko hannunta yayi tunda bazaki ba suhaila jeki shirya ki rakani,


      Tana zaune suhaila ta fito sanye cikin English wears Riga da wando masu kyau,ummi ta gyara mata gashinta,wuce iklas tazo yi iklas kuwa kafa tasa wa suhaila ta shatile kafarta ta fadi kasa,kuka ta fashe dashi me karfin gaske,rufe iklas da masifa ummi tayi.


    Omar da ummi ne suka lallasheta da kyar,gani tayi da gaske tafiya zasuyi,fuuuu tazo ta wuce su tare da bangaje omar,mota ta gani rantsatsiya a waje, omar na danna remote ya bude iklas ta balle murfin gaban motar ta shige,


    Shi kuwa omar murna yayi a ransa dama haka yakeso,a baya ya zaunar da suhaila shima ya shiga.yasan idan ba iklas tafiyar baza ta yiwu ba saboda definitely ciwonsa zai tashi,amma idan iklas na kusa ya riketa sai ya warke


   Tafiya sukeyi sun fara shiga abuja city iklas kawai kumburi takeyi kamar zata ce wayyo na shiga uku na lalace


     Tunda suka fara tafiya omar ciwonsa ya fara tashi kawai zufa yakeyi ya rasa inda zai sa kansa, ba shiri ya sadada hannunsa ya riko hannun iklas,da karfi cike da masifa ta fisge hannunta,naga Wanda zaka rike ai yau.


     Omar ta kansa yakeyi kawai shi yasan me yake ji,suhaila ce dake bayan mota ta mikowa omar hannu gashi ya omar ni ka rike nawa hannun ka kyale na anty.iklas juyawa tayi a fusace ta zubawa suhaila rankwashi ta make hannun wai ni sa'arki ce,ina ruwanki da shi,ba a son hannun naki to.


      Omar na nishi da kyar yake tukin motar kallon iklas yayi idonsa yayi jajir,ki daina dukanta ke iskancin da kikeyi a garin nan wa ke dukanki,kunya iklas taji tace to a kyale maganar kana fama da kanka,hannunta ta miko masa ungo gashi ka rike na taimakamaka.yatsunsu ya sarkafe wuri daya yaci gaba da driving,5mnt omar ya dawo garau dashi,yayinda iklas da shi suka shiga wani hali na shauki kowannensu ji yake jininsa na masa wani yammmm.....yammmm.


     Wani katafaren barbing saloon Wanda yake hade maza da mata omar ya parker,mata maza birjik ciki ana gyaran gashi,matan manya da yaran manya,da manyan masu kudi sune a cikinsa,turawa ne masu aiki a ciki.gurin ya hadu kamar a turai,


    Fitowa yayi sakale da hannun iklas kamar chewgum,tafiya sukeyi cike da izza,iklas ta raina kanta kyaune kadai ya ceceta,dan duk tafi matan ciki kyau nesa ba kusa ba,sai kallonsu akeyi,suhaila na kusa da ya omar.bangaren mata ya fara kaisu yana zaune,iklas ta karbe daya hannun ta mika masa daya hannun gashi rike wannan dayan ya samu ya huta.


      Kujera aka ba omar yana zaune gaban iklas hannunsa rike da nata haka akayi mata gyaran gashi aka gama,suhaila ma an mata,sunyi matukar yin kyau,su Kansu masu saloon din sunyi jinjina.


    Wurin maza suka koma wannan karan iklas aka bawa kujera ta zauna gaban omar rike da hannunsa,masifu kawai take ji a jikinta na kamar sha'awa amma ta rasa gane mene take ji.


      Omar kuwa a cikin jininsa yake jin bala'in sha'awar iklas wacce bai taba ji ba,amma haka ya daure ya cije.tunda aka fara gyarawa Omar suma iklas ta fara turbine fuska,idan ta kalli Omar sai ta tabe baki,wlh ka cuci kanka ko kyau bakayi ba,minti daya ko biyu zata kalleshi tace ko kyau,wai dole za a je bikon mata.


   Gajia Omar yayi yace tunda sahar na son kalarsa ai alhmdlh dama dan ita nayi.mutumin da ba a sonsa anyi yaji an barshi wooooooo....cewar iklas,duk rashin fara'ar Omar iklas daria take sashi.


      Haj rahina ce gaban baffan su omar,pls baffan yara 1million nake rokonka ka bani zan canja motata.hajia rigimarki ta isheni duk motocin gidan nan,omar fa baya bari motoci su shekara yake kawo sabbi,jin baffa ya ambaci omar yasa ummansu sadiya daure fuska,kaga alhaji ni ba zancen tambadadde nazo kamin ba,dan iskan yaro Wanda tsabar bin matane yasa ya bar gida.wa ya sani ma ko a waje tayo cikinsa....bata rufe baki ba taji saukar lafiyayyun mari har uku...kunci ta dafe tare da tsagewa da kuka tana kururuwa ta cukume baffa da kokawa tare da danna masa ashar,ai kuwa baffa ya sa kafa ya harbata gefensa,ta bigi center table,


    Takadda ya dauko ya rubuta mata saki daya,tare da dafe kansa da kyar ya karasa dakinsa.faduwa yayi kasa yayi sharab...mama wacce abin ya faru kan idonta da kuka ta dago baffa,sannan ta kira maza masu aiki da driver suka kwashi baffa zuwa hospital.


       Gaskia kowa ya ga yanda omar ya hadu sai ya kyasa,mata sai kallonsa sukeyi,da yawa suna so su kawo kokon bararsu na love amma yanda suka ganshi kankame da hannun iklas yasa suka ja baya, sai kallo daga nesa,


       Take away ya musu na abinci kala kala sannan ya kamo hanyar gida,dadi ne ya kama iklas sosai ganin baza a je bikon sahar ba.


      Sabo da murna sai labari takewa Omar,suna isa gida iklas ta hango saleem, da Sauri ta bude mota zata fita,Omar yaga saleem sarai,rigar iklas ya rike gam, kallonsa tayi yace muje gida waccen dan iskan zaki je wajensa ko?


  Naji ai na fasa zuwa,to sakeni muje gida mana,kayan suka shigar gida,a cikin motar omar ya bar key din iklas na kusa dashi ta kwace hannunta taje wajen saleem da gudu ta karasa, har sun fara hira akan business da aikin gomnati yanda ake cuwa cuwa kudi na shigowa, wajensu Omar ya taka yaje cike da takama ya zubawa iklas rankwashi muje gida,cike da shagwaba tace ya omar da zafi fa,gani yayi zata bata masa lokaci kawai ya sunkuceta ya sabata a kafada. mutanen layin sai daria sukeyi GOMNATI ta hadu da dai dai ita.
       Asmabaffa

ⓂⓂⓂ

    MA'AIKACIYAR

         GOMNATI

          ⓂⓂⓂ


              45-50


By

Asmabaffa
      Na gode  masoyana Allah karo karfin ido.  

     Kiciniyar kwace kanta takeyi amma ya mata rungumar karfi,da kyar ta fara zamewa cikin magagin bacci omar yace 2nmt pls.....tsayawa tayi cak tare da lafewa ita dama iklas ta Dade da son ta jita a kirjin omar,bata San me yasa ba kuma ta rasa dalilin da yasa jikin omar ke birgeta.sun dauki minti biyar haka omar ya dawo normal,jinsa yayi manne jikin mace ai bai San sanda fancakalar da iklas daga jikinsa ba,sai da ta fado kasa daga bed din.


       Masifa ya fara IKLAS karo na farko da Omar ya kira sunan iklas,wani zirrrrrrrr taji lokacin da omar ya furta iklas,kallonsa tayi tare da tsilli tsilli da ido tana Sosa gashi,me ya kawoki dakin nan,mikewa yayi idonsa jajir ya damki kunnenta,kara ta saki kadan,ba kyajin magana ko iklas,am I ur mate? Ke bakya banbance tsakanin maza da mata,bayan yan iskan da suka saukeki dazu kinga bance miki komai ba shine zaki sauke iskancinki kaina ko?


     Ina ina ta fara ....to wai...wai ba kaine ka janyoni jikinka ba kuma ka rokeni kan na tsaya,har hawaye kayi fa wai kar na tafi,kuma kace kai dadinka kake ji,kukan karya ta fara yi,kuma ni taimaka maka nayi,daga taimak....shut up tashi ki fita mayyata kar ki kuma zuwa min room kije kiyi raping dina,ki samin kazamin jikinki duk dazu wasu gardawa sun gama goga jikinsu a naki.


    Kuka ta saka masa harda rufe ido da hannu,dama nasan yar iska zaka na kallona,na rantse da Allah billahillazi la'ila ha illahuwa Allah daya ragemin hanya sukayi shine suke kokarin tabani sir.


   Kaga Allah kallo wurin da suka dinga marina akan naki yarda ai kaga jinin ma ko,ni ban wani gani ba ke dai kawai kin lalace jikin maza kike so,in auren kike so ayi miki mana,har kayan daki zan miki, cewar omar


Iklas tsalle tayi ta make kafada  Allah kiyaye na haihu na ragwaje,ai nasan ma yanda kake ji dani baza ka bari amin auren wuri ba,tunda kai kaka tana jin maganarka.


     Igbo za a aura miki tunda su kike biyewa suna lagudaki.hawaye ta fara, wlh sir na fada ma ni ba yar iska bace,Omar yasan gaskia kawai maganinta yake son yi sabo da ta daina ganganci.

 

    rike haba iklas tayi kamar gaske tace ohh sir wai kai wanne mai kake shafawa ne?mene kuma?hmmm jikinka Allah ya Omar kamar flour baka ji ba.daria ce ta kwacewa omar,ga iklas tayi wani zaman cin tuwo a kasa, banza omar ya mata.


    Minti 1 iklas tace yaya?kinga get out,kofa ya bude mata tare da kamo hannunta ya tankada keyarta waje ya rufe kofar,sai da ta kusa faduwa kasa,tunawa tayi bata fadi kiran da ummi tace tawa Omar ba,jikin kofar ta Dora kanta ya Omar kazo inji ummi muyi break,tsaki yaja ke kinfa isheni kije zanzo wanka zanyi...ok.


       Kamshin omar da suka ji shi ya basu tabbacin fitowarsa wani danyen yadi ne sanye jikinsa light blue,har kasa ya gaida ummi,umaru wannan kwalliya haka kamar me zuwa zance?amshe zancen iklas tayi haba ummi ke ba dama mutum yayi kwalliya sai kice zance zai je to shi ya omar wa yake da ita,ina yake fita Da har zaiyi wata budurwa, to uwar shishigi ki bari umaru ya bani amsata mana,


    Murmushi omar ya saki ummi bikon matata zanje,tayi yaji sabo da rashin ganina da batayi.sallallami ummi ta fara yanzu umaru kana da mata amma baka fada min ba,ayi hakuri ummi,yanzu ma so nake iklas ta rakani can.dole kaje ai baka kyauta ba umaru.


    Da karfi iklas tace bazanje ba kaje kai kadai ina ruwana da wata matarka,ni nasa ka aureta,zamana takeyi,kai ta shafa can kaje da wata badai ni ba.cike da masifa ta mike zata shige daki,omar kuwa daria kawai yakeyi kadan kadan wannan masifa ta iklas da takeyi,riko hannunta yayi tunda bazaki ba suhaila jeki shirya ki rakani,


      Tana zaune suhaila ta fito sanye cikin English wears Riga da wando masu kyau,ummi ta gyara mata gashinta,wuce iklas tazo yi iklas kuwa kafa tasa wa suhaila ta shatile kafarta ta fadi kasa,kuka ta fashe dashi me karfin gaske,rufe iklas da masifa ummi tayi.


    Omar da ummi ne suka lallasheta da kyar,gani tayi da gaske tafiya zasuyi,fuuuu tazo ta wuce su tare da bangaje omar,mota ta gani rantsatsiya a waje, omar na danna remote ya bude iklas ta balle murfin gaban motar ta shige,


    Shi kuwa omar murna yayi a ransa dama haka yakeso,a baya ya zaunar da suhaila shima ya shiga.yasan idan ba iklas tafiyar baza ta yiwu ba saboda definitely ciwonsa zai tashi,amma idan iklas na kusa ya riketa sai ya warke


   Tafiya sukeyi sun fara shiga abuja city iklas kawai kumburi takeyi kamar zata ce wayyo na shiga uku na lalace


     Tunda suka fara tafiya omar ciwonsa ya fara tashi kawai zufa yakeyi ya rasa inda zai sa kansa, ba shiri ya sadada hannunsa ya riko hannun iklas,da karfi cike da masifa ta fisge hannunta,naga Wanda zaka rike ai yau.


     Omar ta kansa yakeyi kawai shi yasan me yake ji,suhaila ce dake bayan mota ta mikowa omar hannu gashi ya omar ni ka rike nawa hannun ka kyale na anty.iklas juyawa tayi a fusace ta zubawa suhaila rankwashi ta make hannun wai ni sa'arki ce,ina ruwanki da shi,ba a son hannun naki to.


      Omar na nishi da kyar yake tukin motar kallon iklas yayi idonsa yayi jajir,ki daina dukanta ke iskancin da kikeyi a garin nan wa ke dukanki,kunya iklas taji tace to a kyale maganar kana fama da kanka,hannunta ta miko masa ungo gashi ka rike na taimakamaka.yatsunsu ya sarkafe wuri daya yaci gaba da driving,5mnt omar ya dawo garau dashi,yayinda iklas da shi suka shiga wani hali na shauki kowannensu ji yake jininsa na masa wani yammmm.....yammmm.


     Wani katafaren barbing saloon Wanda yake hade maza da mata omar ya parker,mata maza birjik ciki ana gyaran gashi,matan manya da yaran manya,da manyan masu kudi sune a cikinsa,turawa ne masu aiki a ciki.gurin ya hadu kamar a turai,


    Fitowa yayi sakale da hannun iklas kamar chewgum,tafiya sukeyi cike da izza,iklas ta raina kanta kyaune kadai ya ceceta,dan duk tafi matan ciki kyau nesa ba kusa ba,sai kallonsu akeyi,suhaila na kusa da ya omar.bangaren mata ya fara kaisu yana zaune,iklas ta karbe daya hannun ta mika masa daya hannun gashi rike wannan dayan ya samu ya huta.


      Kujera aka ba omar yana zaune gaban iklas hannunsa rike da nata haka akayi mata gyaran gashi aka gama,suhaila ma an mata,sunyi matukar yin kyau,su Kansu masu saloon din sunyi jinjina.


    Wurin maza suka koma wannan karan iklas aka bawa kujera ta zauna gaban omar rike da hannunsa,masifu kawai take ji a jikinta na kamar sha'awa amma ta rasa gane mene take ji.


      Omar kuwa a cikin jininsa yake jin bala'in sha'awar iklas wacce bai taba ji ba,amma haka ya daure ya cije.tunda aka fara gyarawa Omar suma iklas ta fara turbine fuska,idan ta kalli Omar sai ta tabe baki,wlh ka cuci kanka ko kyau bakayi ba,minti daya ko biyu zata kalleshi tace ko kyau,wai dole za a je bikon mata.


   Gajia Omar yayi yace tunda sahar na son kalarsa ai alhmdlh dama dan ita nayi.mutumin da ba a sonsa anyi yaji an barshi wooooooo....cewar iklas,duk rashin fara'ar Omar iklas daria take sashi.


      Haj rahina ce gaban baffan su omar,pls baffan yara 1million nake rokonka ka bani zan canja motata.hajia rigimarki ta isheni duk motocin gidan nan,omar fa baya bari motoci su shekara yake kawo sabbi,jin baffa ya ambaci omar yasa ummansu sadiya daure fuska,kaga alhaji ni ba zancen tambadadde nazo kamin ba,dan iskan yaro Wanda tsabar bin matane yasa ya bar gida.wa ya sani ma ko a waje tayo cikinsa....bata rufe baki ba taji saukar lafiyayyun mari har uku...kunci ta dafe tare da tsagewa da kuka tana kururuwa ta cukume baffa da kokawa tare da danna masa ashar,ai kuwa baffa ya sa kafa ya harbata gefensa,ta bigi center table,


    Takadda ya dauko ya rubuta mata saki daya,tare da dafe kansa da kyar ya karasa dakinsa.faduwa yayi kasa yayi sharab...mama wacce abin ya faru kan idonta da kuka ta dago baffa,sannan ta kira maza masu aiki da driver suka kwashi baffa zuwa hospital.


       Gaskia kowa ya ga yanda omar ya hadu sai ya kyasa,mata sai kallonsa sukeyi,da yawa suna so su kawo kokon bararsu na love amma yanda suka ganshi kankame da hannun iklas yasa suka ja baya, sai kallo daga nesa,


       Take away ya musu na abinci kala kala sannan ya kamo hanyar gida,dadi ne ya kama iklas sosai ganin baza a je bikon sahar ba.


      Sabo da murna sai labari takewa Omar,suna isa gida iklas ta hango saleem, da Sauri ta bude mota zata fita,Omar yaga saleem sarai,rigar iklas ya rike gam, kallonsa tayi yace muje gida waccen dan iskan zaki je wajensa ko?


  Naji ai na fasa zuwa,to sakeni muje gida mana,kayan suka shigar gida,a cikin motar omar ya bar key din iklas na kusa dashi ta kwace hannunta taje wajen saleem da gudu ta karasa, har sun fara hira akan business da aikin gomnati yanda ake cuwa cuwa kudi na shigowa, wajensu Omar ya taka yaje cike da takama ya zubawa iklas rankwashi muje gida,cike da shagwaba tace ya omar da zafi fa,gani yayi zata bata masa lokaci kawai ya sunkuceta ya sabata a kafada. mutanen layin sai daria sukeyi GOMNATI ta hadu da dai dai ita.
       Asmabaffa

ⓂⓂⓂ

    MA'AIKACIYAR

         GOMNATI

          ⓂⓂⓂ


             50-55


By

AsmaBaffa


          Daukan da Omar ya mata bai direta ko ina ba sai daya kaita har Palo sannan ya jefata a kujera da karfi tare da shigewa room dinsa,

  Sosai Iklas taji zafi yar kara ta saki ohhh tare da dafe hips dinta..ko juyowa baiyi ba bare ya San me take ciki.

     Lokacin da su Omar sukaje saloon daya daga cikin yaran Maman Omar tare da wani abokin Omar tabbas suma sunga Omar sun fito daga saloon hannunsa rike da na wata kyakyawar budurwa.


     Lallai sunyi mamakin Omar ashe tafiyarsa yayi yana sheke ayarsa da mata,amma ake ta nemansa ana cewa ya bata.

     Abokin Omar wato Raj  ya daukin alkawarin zuwa ya fadawa Maman Omar cewar sunga Omar a saloon da mace.


   Haj.Rahina ta dauki akwati da sauran abubuwan amfaninta kadan tare da Tara yaranta tayi musu hudubar banza sannan ta bar gidan ta koma gidan babban yayansu da ke zaune a garin Abuja shima.

     Tasha fada wurin yayanta saboda yayanta Alhaji Magaji mutumin kirki ne sosai ya nunawa Rahina kuskurenta amma Sam ko a jikinta sai ma kara kaimi da tayi wurin son daukan fansa,kuma ta sa a ranta dole sai ta koma gidan Alhaji Mohd.


     Tunda su Maman Omar suka dauki Alhj Mohd wato Baffa suka yi hospital dashi gado aka basu bayan aune aune da bincike ya tabbatar yana dauke da ciwon hawan jini kuma ya masa babban kamu,sosai ake kula dashi a hospital Mama ta tsaya tsayin daka wajen mijinta,ita ke jinyar sa,su sadiya ma suna zuwa dubiya amma kullum idan sunje sai sunci mutuncin Mama tare da habaici da zage zage.

   Mama na mamakin wai ga mahaifinka a gadon asibiti rai a hannun Allah amma su sadiya suna shirme Allah kyauta.


     Sultan ma kullum yana kan hanyar dubiya,kuma shi ke kula da Baffa kasancewarsa likita babba,abokan su Omar ma kungiya kungiya suke zuwa dubiya,kamar yau ma Raj yazo yana dakin da aka kwantar da Baffa tare da wannan yaron me yiwa Maman Omar hidima duk wani aike me nisa da wasu abubuwan wannan yaron wato Nura shi ke wa Mama kusan same age suke da Omar.kuma Nura yana da dangantaka tsakaninsu da Raj.gasu frnds ne shi da Raj,shi yasa suke yawan fita tare duk da cewa Raj me kudi ne,

   

     Raj suna zaune kusa da Mama suna hira sama sama yayin da Sultan ke gyarawa Baffa kwanciya,Raj ya kalli Mama hade da gyaran murya Mama akwai wata magana da nake son fada miki,wato yau kwana uku kenan abin na damuna,gaba daya dakin Raj aka zubawa ido har Baffa da ya samu sauki shima ba a barshi a baya ba,

    Naje kusa da saloon in da Nura mun karbi sako a hannun wani Mama wlh munga Omar ido da ido ga Nura nan ki tambayeshi kiji,har kokonto mukayi sai da muka karasa har kusa dashi amma kafin mu is a wajensa sun shiga mota sunyi mana nisa,kuma Mama abin mamaki Omar da mace budurwa zankadediya muka ganshi rike da hannunta da wata yarinya zasuyi same age da suleim dinki,

 

       Sultan kuwa an zo wajen nan ya karbe zancen da cewa haba Ashe nima ba gizo idona ya min ba don nima rannan tabbas naga Omar a garden kingdom sun fito shi da wata charkwadediyar budurwa yarinya karama,Mama kamar yarinyar da ta kawo miki sakon envelop da tace Omar ya bata,kuma kamar wata me tallan kwai a titi da Omar ke taimakawa,

   Daga Mama har Baffa Kansu ya kulle,to ko dama maganar Haj.Rahina gaskia ce da tace Omar na gari sheke ayarsa yakeyi bin mata yakeyi,yaushe Omar ya zama haka,maybe zaman London ne ya lalatashi ko kuma rashin samun kulawa daga wajen matarsa ne.

     Gaba daya su Mama da Baffa sahar suka daurawa laifi sai kuma Omar da ya biyewa son zuciya tare da zubar musu da tarbiyar gida da mutunci.


    Baffa ransa ya kara baci da jin wannan magana,yasan Raj da Sultan baza suyiwa Omar sharri ba,gaskia suka fada,lallai Omar ya bashi kunya zai kuma hadu da hukuncinsa duk ranar da suka hadu.Mama kuwa harda kukan bakin ciki Omar ya watsa musu kasa a ido,amma ya za tayi dole addua ce mafita,

     Sosai su Sultan suka Shiga kwantarwa da su Baffa hankali tare da yi musu alkawarin nemo Omar,dan sunce zasu sa ido sosai a kansa.zasu Dana masa tarkon da dole sai ya fada tare da damke wannan tsinaniyar karuwar tasa wato Iklas.


    Kwana biyu tsakani Baffan Omar har yau jiki yaki sauki sabida damuwa jinin yaki sauka wahala yake sha wanda sai da su Sultan sukayi Dana sanin fada musu cewar sunga Omar.

     Mama abin ya hade mata ga rashin lafiyar miji ga rashin Omar dinta tare da jin mugun labarin yana neman mata.


     Su Iklas anyi musu hutu daga Ta boko har islamiyya,sabo da haka Iklas ta rikewa business dinta wuta yanzu ma tace sana'ar saida danyen kifi zata fara,kudin da ta samo gidan Maman Omar su ta tattara kaf ta siyo katuwar freezer sabuwa dal ta ajiye a kitchen,saura kawai ta fara saro kifi,duk tsare tsaren Iklas Omar bai sani ba,

     Dukkansu suna zaune a tsakar gida da yamma lis,Iklas na kwance a kan katuwar tabar ma da wata Rigarta doguwa ta atamfa tayi kyau,Suhaila na kan cinyar Ummi kwance tana karanta Arba'una hadith, Omar yana kan carpet gefe tare da laptop sai nunawa Ummi wakar shata me ganga yakeyi,Ummi har gyada kai take tana Allahu akabar oh kaji mazan jiya,Allah sarki jiya ba yau ba,Umaru danno min ta Ali makaho da Dan kwairo naji..daria yakewa Ummi ganin abu ba wani Dandano amma Ummi dadinsa takeji ko dan azamaninsu ne akayi wakar,


     Iklas littafinta ta dakko tana ta buga lissafin sana'ar kifi da zata fara domin gobe take sa ran sarowa,juyowa tayi dan Allah Ummi a canja mana wakar zamani amma wannan mu bama fahimtar me suke cewa,kaka Ummi dalla mata harara tayi aike ba hankali gareki ba amma ai sune sukayi wakoki masu ma'ana,tabe baki Iklas tayi pls ya Omar kai mana wakar Timaya ko ta  Devido,

    Ai kece Timayan  see ur mouth anki a kunna miki manya na maga kina shiga ciki cewar Omar,murmushi Iklas tayi cike da shagwaba ta ajiye littafin dake hannunta kajika ya Omar da nawa ka girmeni,ai ko zaka girmen kadan ne,hmm na San da auren wuri nayi da tuni na haifi kamarki,ummi ma tace fada mata Umaru in banda rashin kuya dudu shekararki nawa saboda kinyi tsayin kafa,dadin abun dai a gaban Umaru kika fara Al'ada,ba wani iyayi da zakiyi masa ,kukan shagwaba Iklas ta fara haba Ummi wai mene haka dan Allah,kunya Iklas taji sosai,Omar kuwa masu rayuwar London ko a kwalar rigarsa,saima kafe Iklas da yayi da kallo,idonta ta dauke daga kallonsa a ranta tana kai Sir din nan dan duniya ne harda kallo na.

  Su dama Maza  munafukaine abinda suke so kenan dama taji frnds dinta suna fada a schl.


  Washe gari da wuri Iklas ta saro kifinta Carton daya  na gwajin kasuwa,Omar yana bacci bai San Iklas ta fitaba,sai fitowa yayi yaga Iklas na shirya kifi a fridge Omar ya shiga kitchen din dauko furarsa dagashi sai jallabiya fara me hula dai dai jikinsa gashi sabo da baya fita baya shiga rana ya kara haske sosai skin dinsa har wani sheki takeyi,

    Kamshinsa ne ya bigi hancin Iklas a take jikinta ya mutu murus,kasala ta sakko mata,ta gefenta ya raba zai wuce jikinsa ne ya gogi nata baisan sanda a hankali yace ushshsh shshi sabo da wani irin yanayi daya tsinci kansa ciki.furar ya ebo a glass cup tare da zuka,ke me kike yi haka,duk wannan kifin da wa zaki cinye?kallonsa Iklas tayi tare da murmushi tace au baka da labari ai kifi zan fara siyarwa danye,da kudin da Baffa ya bani na kafa jarin,kaga sana'a goma maganin me gasa,kaga kala kala nakeyi kenan,

   Jinjina son kudi irin Na Iklas yayi a ransa,idanuwansa kyawawa masu matukar haske ya zubawa Iklas Wanda yasa Iklas dimaucewa hade da jin kunya,sunkuyar da kai tayi ta tsinkayo muryar Omar ba a nan gidan za ayi wannan sana'arba,baki isa ki cika mana gida da karni ba,duk sana'ar da kikeyi bata isheki ba sai kinyi kalar wannan,haba mene aibun wannan sai da kifin,ummi ma fa da kyar ta yarda wai bata so nayi,nidai ina son siyarwa sai nayi,


    Tamke fuska yayi to baki isa ba,ba a gidan nan ba na fada miki idan kuma kinga ina wasa dake kiyi na gani,da shagwaba tace pls Sir nasan in ka fada Ummi bayanka zata bi,ke kika sani ni kam na gama magana ko ki je ki mayarwa Wanda kika siyo wajensu ko a cinye a gida,ko ki bayar kyauta,tab lallai inyi asara ba riba,sai dai ka biyani kudin Dana kashe in kuna so na daina,

   Zare ido Omar yayi ina wasa dake,tsorata tayi ta fara bin bango tana rabewa hade da tafiya kadan Kadan ta fice da gudu daga kitchen din tana ae na fada a biyani kudin Dana kashe tare da kulewa dakinsu.


    Daria Omar yayi sosai ya fita shima,washe gari da safe Omar ya fito da brush da toothpaste zai shiga toilet sai ga Iklas ma ta fito tana kallon Omar ta wuce da sauri ta rigashi shigewa toilet din.Ummi sakin baki tayi yau naga yar banzar yarinya,ke dan bantan ubanki fito Umaru ya shiga,kyaleta Ummi zanyi maganinta,daki Ummi ta koma tana cewa kunfi kusa.


      Iklas kuwa har ta fara brush Omar ya jawo rigarta kiiiiiii ya jefota waje,kafin ya rufe toilet di Iklas ta kara bankawa ciki,murmushi Omar yayi oh..yanzu na gane me kikeso Ashe wanka kike so na miki,damkota yayi kamar zai fara cire mata kaya tuni Iklas ta fara kuka tana Neman agaji,da gudu ta fito daga toilet din,Omar ya rufe kofar tare da Jan tsaki karamar yar iska da kin tsaya kin gani.

    Iklas kuwa a ranta tace kut lallai Sir cikakken dan iskane.yau Iklas shiri tayi tsab domin zuwa gidan su Omar so take ta dubo masa lafiyar su Mama,fito tayi Palo tare da yiwa su Ummi sallama,da sauri Omar yace muje tare unguwar na kaiki,batayi musu ba ya kira a take aka kawo wata new Car din.


      Tofa kunji masu karatu.


   Asmabaffa

ⓂⓂⓂ

    MA'AIKACIYAR

         GOMNATI

          ⓂⓂⓂ

            


            65-70

      


By

Asmahbaffa      

       Wangale gate din su Omar akayi tare da jera Shiga wakeken rangadeden gidan da motocin gaba daya wannan kartan sukayi,Omar Wanda ya gama galabaita gashi an kawoshi har gidan da bazai iya rayuwa ciki ba,ji yake kamar za a zare masa numfashi yayin da motar da yake ciki ta shiga cikin gidan iyayensa,kafin ka bude ido Omar ya fara shuru shure da make make,gashi an daure shi kamar wani huhun goro,mutanen da suka taru za a tarbi Omar jiran fitowarsa kawai sukeyi suna washe Baku,Abdallah da suleim sai zumudi sukeyi,yayin da kungiyar haj.Rahina suka tsaya suna zage zage da masifa,aikin banza akan wannan fasikin suka wani taru aikin banza cewar Aisha,


     Bude motar akayi wasu mutum biyu suka fito da Omar dake cikin mawuyacin hali,Mama salati ta kwada tana hawaye ganin halin da danta yake ciki,da karfi Omar ya fisge kansa tare da girgije kartin nan daga jikinsa sai gasu kasa zube,huci kawai yake yana gurnani,kara ya fasa tare da zubewa kasa a yana ta birgima daga nan ya suma gaba daya numfashinsa ya dauke,mutanen dake wajen ko wanne salati da lahaula yakeyi,Mama kuwa kan Omar ta fada tana kuka haka ma su suleim,da kyar Baffah ya janyesu,su sultan ma har hawaye suka digar tare tausayin Omar,duk wani masoyin Omar sai da ya tausaya masa,su haj.Rahina kadai ke murna tare da shigewa part dinsu suka saki sautin kida.

     Sahar dake wajen itama domin sai da aka shigo da Omar sannan tazo wajen tana ganin abinda yakeyi tabe baki tayi ta kalli Baffa ta yatsina baki a kyaishi psychiatric hospital,

     Harara Baffa ya watsa mata ya wuce wajen Omar,ita kuwa sahar glass dinta baki ta kafta a fuska ta shige dalleliyar motarta ta koma inda ta fito.

      Kwance daurin da akayiwa Omar Sultan yayi,sannan suka taru aka dauki Omar aka kaishi room dinsa Wanda yasha gyara,wasu Allurori Sultan ya masa,gaba daya kowa ya tafi gida Sultan da Raj ne kawai zaune suna jiran tashin Omar suga taya zai farka.

    Mama da Baffah harma da su Abdallah suna palon Omar sunyi jugum jugum suna jiran tsammani,Umma Rahina tana ta yiwa frnds dinta waya cike da Murna tana basu labari,haj Binta tana jin labarin haushi taji taga lallai in tayi sake nan gaba Burin Rahina zai cika,don haka tace Sam wlh bazai yiwu Rahina ta fini kudi ba dole na wargatsa shirinta,sai na karya wannan tsafin da ta yiwa Omar. su sadiya kuwa rawa kawai suke takawa.


     Hospital Iklas kwance tana bacci saurayin da ya bigeta yana kusa da ita yana jiran tsammani tare da karewa surarta kallo,

     Saleem yana jin labari a rude ya fada wajen Ummi,da sauri ta tari saleem yawwa saleem maza ka bimin bayan Iklas daga aikensu amma har dare ya kusa yi,Ummi bafa lfy Iklas wai tana asibiti mota ta bigesu,innalillahi wainnailairrajiun,Ummi sai kuka Suhaila ma hakan dannan in sun mutu Ku fadamin,Ummi ba kuka za kiyi ba zo mu tafi kawai asibitin mu San a wanne hali take,guruf guruf Ummi ta sa takalmi ko mayafima suhaila ce ta mika mata hijab a waje,saleem rike da hannun suhaila suka shiga taxi suna bulayi har Allah yasa wani ya musu kwatancen asibitin da aka kai Gomnati.

  

     Fadawa dakin sukayi sai ganin Gomnati sukayi kwance saurayin na gefe,Ummi da Suhaila sai hawaye suke sharewa,Ummi na oh mun shigesu tsautsayi yasa na aikeku da nasan haka zata faru da ban fara ba sai ta kara fashewa da kuka,saurayi kuwa sai hakuri yake basu,haushinsa ummi taji ta juyo da masifa kwalabar ubanka dan jakar uba zaka dakeni ka hanani kuka ne?


A ransa sai dariar zagin kaka yakeyi,a fili sai hakuri yake bayarwa,kai da Allah ka rufe min baki cewar Ummi.likita ne ya shigo tare da cewar Goggo a daina hayaniya pls ta kusa farkawa,bata da wata matsala Allah ya gajarta wahala.

    Likita ina daya saurayinfa?wanne fa?dama su biyu aka bige?da Sauri saurayin yace no kaka wannan kadai na bige banga namiji ba,kan kakane ya kulle to Ina Umarunsu,dole su jira farfadowar Gomnati suji ina Omar ya tafi.sosai Ummi ta damu rashin sanin inda Umarunta ya Shiga.


       Baccin 6hrs Omar yayi sannan ya farka,ciwon dai yana nan sai dai Omar jikinsa Sam ba karfi dakyar yake daga yatsansa sabida Allurar da Sultan ya masa.

     Hawaye Omar ya fara ga ciwo na cinsa ga tunanin mota ta kade masa Gomnati, Sultan ne ya lura da farkawar Omar,da Sauri shi da Raj suka nufi wajensa,Mama,Baffa dasu Abdallah duk sun banko cikin room din,Omar kuwa ido jajir,ga karkarwar jiki tare da danne saitin zuciyarsa da hannu daya,

    Sultan ya kai hannu da niyyar taba Omar amma duk halin da Omar ke ciki saida ya make hannun sultan wai kar ya tabashi,Mama ce ta matsa kusa dashi ta riko hannunsa tare da dora kan Omar a cinyarta tana hawayen tausayi,Omar na jinsa a jikin Mama yaji ciwon ya karu,kuka ya fara tare da rungume Mama yana ajiyar zuciya,Baffa ma hannu yasa ya dago Omar  jinginashi a jikinsa,


   A hankali Mama tace Babana fada min me ya sameka haka?wacce cuta ce ta sameka haka ka kasa fada mana?wai ni wanne ciwo wannan Banana?

   Baffa ma haka ya dinga lallaba Omar yana tambayarsa meke faruwa,amma Omar yaki magana,kwanciya ma yayi kan bed yana numfarfashi.


     A hankali Omar yayi magana da kyar muryarsa ke fita,Ba..bazan..iy...iya...zama....nan..Gi...dan...dan..ba,Ku fitar.....da...in....Don't...Allah.

    In..kuna... So...na...za...una...Ku can...ja... Min gida...pls

Zuciyarsa ya kara dannewa yana idan....Ku...ka...barni... Nan... Mutu....wa... Zanyi sai hawaye ya ziraro daga idonsa.suma du mutanen dakin sai da suka goge ido.

      Yaci gaba da I....na..da matsala...a....lafiyata...Ku...fahim.....ce....ni.

   Da sauri mutanen dakin suka hada baki da karfi wallahi mun fahimta mun fahimceka Omar.

    Murmushin karfin hali yayi Ku...canja...min...wa...ni gidan....ko.....Ku..nemo...min...Gomnati,

   To fa mene kuma Gomnati?cewar Mama

     Iklas...na...ke ...nu....fi.a...dubo...min...lafiyarta...mo...ta...ta...kad..e..ta....ku memo...mi...n...ita...itace.....maganina.....da karfi ya kara volume cike da zafin ciwo She IS MY MEDICINE MAMA yana fadin haka ya kara sumewa,Sultan wasu alluran ya kara makawa Omar daga suma yaci gaba da bacci,sannan ga drip ya sa masa.kowannensu ya hallara a Palo suna tattauna maganganun Omar ya za a bullowa lamarin,Sultan yace Baffa da farko dole mu koma Neman Iklas a garin nan ina ganin itace Ummi wacce yake rike hannunta,wacce ta kawo sakon envelop gidan nan,kwarai kuwa Sultan cewar Mama.sannan dole fa a canjawa Omar gida a kaishi wani guess house din cikin gidajensa,kafin a nemo wannan yarinyar,sannan ya dace ayi masa maganinsa Hausa cewar Raj.Baffa ma yace dama hakan na fara tunani kawai.haka suka kwana a palon,baccinsu kadan ne.


      Da dare misalin 11 Iklas ta farka da Kuka wiwi kamar ranta zai fita sai shure shure takeyi an sace ya Omar,Ummi wlh wasu ne suka sace oga Omar,yanzu mu yaya zamuyi mun Shiga uku wayyo sir......wayyo Omar dinmu na mutu Ummi...na mutu Ummi....naga ta kaina...mene amfanina a duniya ni kuma Ummi...tawa ta kare...saleem ne ya riketa yana lallashinta da kyar aka samu tayi shuru,taki cin abinci ma wanka kawai tayi ta fara sallah bayan ta wacce ake binta ta koma yin nafeela ba ji ba gani har sai da ta kai 4am sannan Allah ya kawo nurse suka tsira mata Allurar bacci aka shimfideta tare da sa mata drip.


      Washe gari da safe  aka sallami su Iklas,gaba daya Gomnati ta birkice,bata uhm bare uhm uhm,ta daina ma magana wai duk cikin Bacin ran sace Omar take,damuwa ta shiga sosai su Ummi sai lallashi sukeyi tare da kwantar mata da hankali,Ummi tace kin San fa Baban Umaru me kudine yana can babansa ya sa a dauko masa dansa,ke banza ce wa zai iya sace Umaru,ai ba a satar manyan mutane yara ake sacewa idan aka dafa su ance sunfi manya dadi..Iklas kuwa dadi taji wai ba a sace Omar ba,daria ta saki kuma fa hakane Ummi ko a radio cigiyar yara kadai akeyi,can mintuna kadan suna Shiga gida Iklas ta fara kuka tayi missing din Omar sai gidan yayi wani iri,


     Tunowa tayi da cutar Omar yanzu tasan ma yana can ta tashi kukanta ta kara sautinsa sannan ta ruga da gudu jikin Ummi ta jata Palo suka zauna sannan Iklas ta kwashe labarin cutar Omar ta fadawa Ummi


    Ummi ma harda kuka Allah sarki Umaru,Iklas wayon banza ne dake me yasa baki fada min da wuri ba,wannan aikin sihiri da jinnu ne da tuni munyi kokarinmu an karya abin.nan Iklas ta Kara bawa Ummi labarin gidan su Omar kaf,harda dukan da aka mata su sadiya,da sahar matar Omar.sosai Ummi taji haushin Iklas da bata sanar mata ba.

     Ke rabu dani shashashar banza gashi nan ai kin jawo matsala da kin fada tun wuri da tuni haka bata faru ba,Ummi shi yace kar na fadawa kowa,yaushe dama ababen dake jikinsa zasu bari ya fada kar a masa addua.


     Ummi gobe muje gidan su ya Omar mu gani,ban yarda ba Iklas ki bari tukun muga abinda Allah zaiyi...kawai muyi masa addua,jiki sanyaye tana kwalla tace to Ummi sai kuma kuka ya kwace mata ta rufe ido da tafin hannunta biyo tana tunowa da rayuwar da sukayi tare da Omar.

      Yanda ya taimakesu,yake hanata kula kowa,kula dasu,yanda suke fada da kuma wasa da dariya.

    Kara tunowa tayi sanda ya shafa mata ruwan naman ganda a fuska sai kuma ta  fara daria ga kuma kuka da hawaye duk ita kadai.


    Ummi kuwa tausayi Iklas take bata,Suhaila ma damuwa ta shiga babu me siyo mata kayan sawa da sweet.da Sauri Iklas ta shige dakin Omar tana shakar kamshinsa tare da kwancia a bed din tana tunanin lokacin da taga Omar a mota tana talla a kwalta,yanda take kwala masa Kira ta glass din window tana Oga tare da daga hannu,murmushin da Omar ya sakar mata a lokacin shi ta tuna.


    Mikewa tayi ta cire kayan jikinta tare da daukan singlet din omar fara tasa, sannan tasa wandonsa short fari tayi kyau dama gata fara,ga gashi har tsakiyar baya.lekowa dakin Ummi tayi taga shigar Iklas daria Ummi tayi ta koma kitchen.Iklas kuwa mayyar Omar a dakinsa ta kwana tana jin kamshi tasha bacci kuwa ji tayi kamar ta rungume Omar shi yasa tayi bacci sosai.


       Omar washe gari haka ya farka da ciwonsa yana  a nemo min Magani ta,Iklas Mama kuma a fitar dani daga gidan nan,bakwa tausayina Baffa?ba shiri Su Sultan suka sashi Mota tare da kaishi wani rantsatsen gida ga yan aiki da security ko ina.Alhmdllh  kuma Omar ya dan ji sauki sauki,har yayi wanka da kyar tare da cin abinci abincin ma saida Raj yace in bai ci ba baza a memo masa Gomnati ba.

        Wani babban malamin Izala Baffah ya fadawa matsalar Omar,malamin yace Ku nemo yarinyar da yaron naka yace Alhaji sannan nasan wacce addua zan tofa masa a ruwa yasha.dole sai naga yarinyar na mata wasu tambayoyi sannan ayi addua.


         Address din gidan su Iklas Omar ya bawa Su Sultan, gaba daya Mama,Raj,Baffa da Sultan suka rankaya zuwa jin ya lafiyar Iklas da kuma daukota a kawowa Omar maganinsa.     


Asmabaffa

ⓂⓂⓂ

    MA'AIKACIYAR 

         GOMNATI

          ⓂⓂⓂ


              70-75


By

Asmahbaffa


     

    KUNA BIRGENI MASU COMMENTING KUNE NAWA .KHADY CHAFE  ALBARKA.
        Tsala tsalan motoci har biyu suka dau hanya daya motar Mama da Baffa dayar Sultan da Raj  Yanda suka ga unguwar su Iklas ta talauci basuyi zaton zasu ga gidan su Iklas me kyau haka ba,sallama sukayi Mama ta kutsa kai cikin gidan,Ummi da Suhaila suna Palo suna kallo,Iklas kuwa tana dakin Omar sai kuka da tunaninsa takeyi gaba daya ta rame sabo da bata cin abinci,

      Kamar kullum yauma sanye take da jallabiyar Omar milk color tana kan bed din sai shinshina wata T-shirt dinsa takeyi tana lumshe ido,gaisawa Mama sukayi da Ummi dama nice mahaifiyar Omar da sauri Ummi ta zabura Umaru Dana sani yaron kirki dan mutunci? sai Ummi ta fara kuka yaron da muke ta nema an saceshi,ki kwantar da hankalinki Omar yana wajenmu bari a kira sauran Mazan ma kiji bayanin komai cewar Mama.


    Da sauri Mama ta kira su Baffa su shigo,suna shigowa kowanne ya zauna a kujera,Ummi ce tace ina zuwa bayin Allah,a sukwane cike da murna ta shiga wajen Iklas tashi anga Umaru Ashe yana wajen Mamansa,gasu can yan uwansa sunzo domin yi mana bayani ki fito ayi a gabanki,ki fara kawo musu lemo da sauran kayan dadi,

     Iklas tsalle ta dira tare da murna kamar bakinta zai yage,rawa ta farayi tana Anga ya Omar...duniya sabuwa fil a kwali,ras nake jina wlh yau bacci harda munshari kuma zuwa wajen Omar ko ba tayar mota eh....eh....eh...Omarun mu.tana juyi.daria Ummi tayi tare da komawa wajen baki suna gaisawa.


     Iklas tsabar Murna ta Manta Rigar Omar ce a jikinta ta fito palon Gaba daya bakin suka zubawa Iklas ido,Raj ya zunguri Sultan a lallai dole mutumin ya rude yarinyar ba karya,gaskia dai cewar Sultan kaga ma rigar namijice jikinta kuma wlh kamar size din Omar ce rigar,Raj yace kuma ta mata kyau wlh.

    Baffa ma sosai ya tabbatar wannan Ummi ce me kai sako gidansu me hankalin nan.

     Mama kuwa ita dai tana son ummi bata San me yasa ba.Masu karatu karku manta Iklas da suna Ummi tayi amfani a gidan su Omar lokacin da takai sakon takarda.


      Tsugunawa Iklas tayi har kasa farin cikinta yaki boyuwa haka ta gaishesu baki kamar gonar auduga,kitchen ta wuce ta kawo musu lemuka da snacks,sannan ta nemi wuri gefen Ummi a kasa ta zauna,

     Baffa ne ya fara magana tare da basu labarin gidansa da komai nasa tas har lokacin da Omar ya bar gida,haka Mama ma,sannan Iklas ta basu tun farkon haduwarta da Omar har karshen da aka daukeshi mota ta bigeta,

    Godiya sosai su Baffa suka yiwa su Ummi suma su Suka musu tasu.Mama harda bawa Iklas Hakurin ci mata fuska da sukayi da kazafi,Mama ta kalli Iklas 'Yata Ashe sunanki Iklas ko ?Murmushi Iklas tayi Tare da sunkuyar da kai kasa cike da kunya tace ayi min afwa Mama.'yar kaniya cewar Ummi.


     Baffa ne yayi gyaran Murya ya roki alfarmar Ummi ta bashi Aron Iklas za a yiwa Omar magani,ita kuma Mama shawara ta kawo akan a daura aure tsakanin Omar da Iklas kawai tunda yana rike hannunta haka kuma ba san ranar warkewarsa ba,idan kuwa matarsa ce komai zaizo da sauki,sabo da gudun shedan gwara idan da aurensu ba Wanda zai damu.

     Ummi ce tayi magana duk naji batunku gaskia sai dai na Baku Aron Iklas sabida ko sec schl bata gama ba,kuma Allah gatanmu ita ce gatanmu,sannan Ummi itama ta fara basu tarihinsu Iklas kaf.sun tausayawa su Iklas gaskia.


        Baffa ne yayi magana Kaka gaskia abin a tausaya muku ne,kuma lallai Omar yayi abin kirki, wato ni Ku koma gidana da zama ke da kanwar Iklas, zan dau nauyinku babu matsala,kome kuke so ba matsala ga part din Maman Omar ne a wajenta zaku zauna abinda kuke so shi za ayi,kuma munyi muku Alkawari baza a fadawa Omar wannan auren ba har sai shi da kansa yace yana sonta zai aureta sannan mu bayyana masa,gudun kar mu aura masa ya zalinceta ma tunda babu wanda yasan zuciyarsa itama kuma yarinya haka ya dace ace da aure tsakaninsu amma bai dace ace kamarsu suna taba jikin juna ba kuma da niyyar magani shedan ake gudu.


ummi ma ta yarda da maganar su Mama kuma idan Iklas ta auri Umaru to tayi dacen miji.Ummi tace Alhaji na yarda da zancenku amma rigimar gidanka nake tsoro,karki damu Ummi nan gidan da kuke ciki Ku zuba yan haya Ku koma gidana fatanmu ki amince a daura musu aure.

Kefa 'yata?ya kika gani kin amince cewar Baffa yana kallon Iklas,har Ga Allah Iklas bata son aure yanzu gashi ko schl bata gama ba bare ta fara aikin Gomnati burinta.ita burinta ta fara aikin Gomnati sannan tayi aure ko banza ta huce takaicin da namiji.ga kawarta Fauziya kwanan nan ta samu teaching amma sai wanka take dauka rannan ma ta siyi fili a garin Abuja,ba ruwanta fantamawa take amma ita auren wuri za a mata abin haushi.

     Mata sai ci gaba sukeyi ita kuwa mijin ma da za a bata bai San ya aureta ba,ba sonta yake ba,gashi me mata,wlh badan Omar bane da ko sama da kasa zata hade baza ta taba aurensa ba.


    Amma kunyar Baffa da tuna Alkhairin da Omar ya musu,ya maidasu mutane yasa Iklas tace ta Amince kallonta kaka tayi tana mamaki,la..la...la..kaji yar banza mara kunya shi yasa gata nan kullum kayan Omaru take sawa daria akayi gaba daya tare da zuba mata ido.

     Turo baki Iklas tayi cike da shagwaba kai Ummi komai sai disgani.yo in ba munafunci ba me ya kaiki ko kunya babu wai ae kin amince.dama na Dade da ganoki.cuno baki Iklas tayi tare da shigewa daki.Sultan ne ya kalli Raj sukayi daria yace lallai Omar dan Iskane shi yaga abinda ya gani yarinyar tayi fa.

    

      A wajen Baffa ya kira yan Uwansa 20mnt suka zo su uku,Baffa da dayan dattijon walliyan Iklas,sauran kuma sukayiwa Omar,nan take suka dan taru a masallacin Unguwar harda liman nan aka daura Auren OMAR MOHD DA IKLAS,Iklas haushi ma taji an mata aure tana karama gaskia an dauki hakkinta dan ma tana so taga Omar.


      Baffa kuwa saida ya gargadi yan uwansa na Amana kada su fadawa Omar an daura masa aure.Baffa sun shigo gidan Alhmdllh an daura Ummi yanzu Ku yi shiri kayan sawa kawai zaku dauka Sultan zasu zo a daukeku Gobe insha'Allah,lefenta da sauransu duk zan mata komai idan lokaci yayi,duk da haka yanzu Mama zata hada mata akwatuna set ko 4 ne kafin na lefe suzo. Allah sa Albarka cewar Ummi.

    Sallama sukayiwa Ummi suka tafi cike da Murna.


       Ba Wanda yasan me akayi,saleem yana wajen aiki bai San komai.Ummi da Suhaila Kadai su suka gama shirya kayan tas,Iklas na daki tana kuka an daura mata aure bata fara Aikin Gomnati ba.shike nan miji zai rainata,komai sai ta tambaya.Ummi ce ta sameta a daki ta fara fada ke wato baki San lallashi ba ko,akan an miki aure kike kuka,Gata fa akayimiki,samun miji irin Omar ai sai an tona,Allah ya rufa mana asiri kina hauka,kin fi so mu tagayyara ana kiranku goyon kaka,'yayan mace,in ma zaki daina wlh ki daina taimakonmu sukayi mune abun tausayi idan kince bakya sonsa mata Dari zasu soshi,


     Da Sauri Iklas ta shigo ai wlh ba a isa an aure Omar ba shi din banza ya Isa ma,itama matar tasa na tsaneta.daria Ummi tayi to kince ba kya sonsa kuma...to wai ke Ummi nifa aikin Gomnati nake ji kar ya hanani.


     Yau naji shashasha ke ai Hutu kika samu,to bari kiji mata masu mushen tunani su ke tunanin sai sunyi aiki Gomnati za su sayi sabulu ko Omon wanki,Idan kin cika mace ba abinda miji bazai miki ba.Aikin mace shima yana da amfani,amma ki gane ko bakiyi boko ba indai mijinki na dashi kina kyautata masa ta ko ina baki Gaza ba to ba wani matsayi da baza ki taka ba.


     Mata nawane ko A basu sani ba kuma suka zaga kasashe, sun hau motoci na Alfarma, duk wani jin dadin duniya sun gama ji duk ta silar miji, suci takaucinsu tare kuma yayi kudi ki famtama sai marasa tsoron Allah Wanda nasan Omar baya cikin irinsu.


     Haka Ummi tayi ta yiwa Iklas nasiha da koya mata dabarun aure.

   Iklas kuwa jin Ummi takeyi tasa a ranta dole fa sai tayi aikin Gomnati domin ta tsaya da kafafunta.


     Washe gari da misalin 5pm Sultan da Raj sunzo da dankara dankaran motoci guda biyu daya aka zuba kayan akwatunan su Iklas daya kuma aka kwashe su sai city.Iklas kirmishishi bata kuka ganinsu tare da su Ummi.


    Tun daga gate Ummi da Suhaila suke kallon haduwa,suna fitowa daga Mota Najja kanwar su sadiya ta fito da gudu ta koma part dinsu tare da kiran gaba daya sis dinta har Umma kallon su Iklas sukeyi ta wani window suna kus kus,Sadiya tace Ku kyale munafukai zamu gano kulla kullar da makirar tayi, wlh duk sai munci Ubansu sai sun bar gidan nan.


       Suhaila daki daya aka hadasu da Suleim,Abdallah sai wani likewa Suhaila yakeyi,Iklas kuwa cewa tayi wajen Ummi zata zauna Mama tace ki dai zauna kawai amma Mijinki Marar lfy fa bari dai tukun a kawo Omar anjima mu gani inda yuwuwar zaman zai kasance.


     Sahar kuwa tuni ta kara guduwa gidansu wai Omar yahaukace,iyayenta sukace tayi zamanta dan kar ma a kawo Mahaukaci Omar watarana ya sheke musu yarsu tilo.


       Omar a daddafe yayi Sallar isha su Sultan suka daukoshi a mota sai gida,Raj gani yayi Omar kamar zai mutu tun kafin su Karasa gate ya kira Mama a waya cewar ta turo musu Iklas waje Ita kadai zata iya shigo da Omar gidan.


       Rankatakaf Mama, Iklas, Ummi dasu Abdallah suka fito Baffa shigowarsa kenan daga masallaci shima yaci Birki wajen motar su Sultan.


        Da kyar su Raj suka fito da Omar daga mota,Kamshin Iklas Omar yaji da sauri cikin mawuyacin hali ya dago kasa ai kuwa sukayi 4eye da Iklas wacce tuni ta fara kukan tausayin Omar duk ya rame ya fita a tunaninsa, Da kyar Omar ya wara hannayensa biyu cewar Iklas tazo gareshi.Mutanen dake wurin sai kallon su sukeyi cike da tausayi. Su sadiya ma suna daga cikin gate sun leko ta wata yar kafa.


     Iklas da gudu ta karasa wajen Omar tare da fadawa jikinsa tayi lamo a kirjinsa shi kuwa ya kankameta a jikinsa,hannuwanta tasa tare da tallafo kumatunsa tana Sir sannu ya Omar ciwon nan ya baka wahala,Iklas ina ta Neman ki su Mama basa tausayina,no  ya Omar sunfi kowa tausayinka fa,riko hannunsa tayi zo muje na baka abinci juyowa sukayi sai sannan Iklas ta tuna da mutane a wurin kunya taji zata zame hannunta daga na Omar taji ya kara damkeshi rada ya mata a kunne muje ni wlh yunwa nakeji.


        Su kuwa su Mama Murna da Mamaki sukeyi ganin Omar na Rike Iklas ya warke ya dawo sumul Mutum kamar kowa.Sultan ne yayiwa Iklas Magana ya kika tsaya kuma kuje ciki gamu nan zuwa,ki kaishi part dinsa akwai komai ciki har abinci an kai.


    Asmabaffa

ⓂⓂⓂ

    MA'AIKACIYAR 

         GIMNATI

         ⓂⓂⓂ


           75-80


By

Asmabaffa
      WANNAN SHAFIN NAKUNE MASOYANA.
      

       Rike yake da hannunta har suka shiga part din Omar.Su sadiya wani uban tsaki suka ja Ashe shegiyar marar kunyar yarinyar nan ce take wannan iyayayin da shishigi, Aisha tace haba no wonder ina ganinta naji na tsaneta Ashe yar bakin gida ce wlh sai tayi dana sanin zuwa gidan nan.

     Part dinsu suka koma kowa na fadin kalar nata muguntar da zasuyiwa Iklas.har palonsa Iklas ta kaishi dole tare suka zauna kamar chewgum haka ta zuba masa abinci ya tsaya yaci sosai da yawa sai da yajishi dam sannan ya Kali Iklas ina Ummi da Suhaila yanzu zasu shigo Good yace.


       Yana son ya saki hannun Iklas Gudun kar Mama ta ganshi yana jin kunya gata ita ba matarsa ba,yana wannan tunani su Mama suka shigo gaba dayansu,suna masa sannu,mamakin Omar yaga Sam su Ummi basu damu ba da suka ganshi rike da Iklas.

    Baffa ne ya shigo tare da malamin nan kowa waje ya samu ya zauna,Malam Usman ya kalli Baffa yace Alhmdllh mun godewa Allah lallai Allah da iko yake,dama Baffa ya sanarwa Malam usman batun auren da sukayiwa Omar yaji dadi shima malamin yace dakyau kar a sanarwa kowa yanzu tukun a bari ya warke. yanzu wannan yarinyar dole ta zauna kusa dashi har ya gama shan ruwan adduarsa Wanda a kalla na 3wks ne,a dakinsa zata dinga kwana dashi har agama komai,Omar kansa ya kulle sabo da cuta za a sabawa Allah su kwana 1room da wata.

 

      Kallon Baffa yayi Baffa kwana 1room da itafa haramunne za a sabawa Allah,karka damu Umaru ba abinda zai faru mun yarda daku,ta lafiyarka mukeyi cewar Ummi.

    Shuru Omar yayi zuciyarsa cike da tsoro,kwalayen ruwan faro aka shigo dasu na addua,dama malamin yanda sukeyi Ku zaku kawo ruwan roba carton din dasu ke addua ciki su Baku abunku a tsaftace ba shan cuta,Omar ma su Baffa kwali biyu suka kai na faro,sai kudin su za a basu masu tsada domin dubu Dari da hamsin malam usman ke yi ba ragi.


      Bayanin maganin ya fara musu a bashi yasha da safe Rabin jarka ragowar Rabin kuma da dare ya zauna a kan towel a shafe masa shi a jiki gaba daya,ga wannan ya mika musu man zaitun shima an Masa addua ciki kullum a shafa masa da dare a jikinsa,yau Ku fara bashi su.kome ake ciki Alh kamin waya..Godiya sukayi Masa ya mike ya tafi.

     Sultan da Raj ma jaddadawa Iklas sukayi kan ta kular musu da abokinsu sannan suka tafi gida,tuni su Suhaila sunyi bacci,Mama yau har hira kadan sukayi da Omar ammafa har yau rike yake da hannun Iklas,hannunta yayi gumi ya gaji.


      Baffa ma jaddawa Iklas yayi cewar ta kula da Omar ta Saki jiki ba kunya.sanna suka wuce part dinsu ita da Baffa,Ummi ma tayi nata sannan ta tafi,shi kam Omar tunani yake wai meke damun su Mama zasu hadashi daki daya da balagaggiya

     Kallon Iklas yayi yaga ita Sam ko a jikinta,harkarta takeyi tana latsa waya.kina jin fa su Mama wai ki kwana Room dina,ba tare da ta kalleshi ba tace to ya na iya?me zan yi ciki lfy fa za a nema maka.muje ciki kayi wanka ,fuska ya daure in sa'ankine zaki dinga sani abu wai?ko na miki kama da yaronki?lallai ka samu lfy sir ,muje pls ni bacci nakeji gwara ma ka taso,ni dai yarinya baki isa kin hau bed dina ba wlh,ba dan iska bane ni.


    Murmushi Iklas tayi to badan tsoro ba ka sakar min hannu mana yanzu a gani,baza a saki ba din,to kaga kuwa ai Kaine babban......sai ta tuna Oga ne fa wannan da sauri ta kulle bakin ta,saukar wasu rankwashi taji kwas masu zafi a kanta Omar ya zuba mata,

     Ouchshsh.....tayi kara tana Sosa kai,shice da shagwaba tace da zafifa zaka kasa kwakwalwata ta hadu da jini.

    Mikewa yayi rike da hannunta suka shiga Room dinsa,sakin hannunta yayi ya shiga toilet da kyar yayi wanka saboda ciwon ya tashi,kafin ya fito ta dauko kayan baccinsa tana ta sauri ya fito kar ciwon yayi karfi,

   Ai kuwa a wahale ya fito da sauri ta matsa kusa dashi ta rike hannunsa sai dayaji ya dawo normal ya kwace hannun ke nifa kina yawan sani aikata sabo kin dameni fuska daure yayi maganar,

      Fushi Iklas tayi ta mike fuuu ta dauko maganinsa da malamin ya kawo,to ko shima wannan din baza ka sha ba,ae bazan sha ba kije kira min Mama, fita tayi direct part din Mama taje kofa ta kwankwasa Mama ta fito Iklas lfy? Wlh Mama Ku fada masa ni matarsa ce yaki yarda ma yasha maganin komai fada yake min wai iskanci ne,kalla inda ya rankwasheni fa Mama,


     Kuma yace kije wai, murmushi mama tayi rigimamme ke kuma in banda abinki hakuri akeyi ai da marar lfy kuma kin San bai San matarsa bace ke,ni bazanje ba babu abinda zan masa kece me yin duk abinda ya dace kuma mun koya miki komai sabo da haka kije kowa yaji da mijinsa,nauyi ne kanki kije ki kula da mijinki.


     Jeki Allah tashe mu lfy,komawa iklas tayi itafa an takura mata an lakaba mata aure.komawa tayi ta sameshi ciwo ya tashi gadon tahau ko kulashi batayi ba ta dauko addua  ruwan faro ta tsiyaya a glass cup ta mikar dashi zaune da yake ciwon na cinsa karba yayi ya sha,ta kara bashi sai da ya sha rabi kamar yanda malam yace sannan ta dauko zaitun nan ma da kyar ya bari ta shafa masa yana ta lumshe ido sabo da dadin yanda take shafa masa kamar kar ta daina,sai mamaki yakeyi yarinya karama da abun mamaki,kato dashi take iya kula dashi haka,rigar ta dakko zata sa masa ya bige hannunta kin ma isa ke wai ni danki ne?mikewa tayi ta koma wata hadaddiyar kujera ta hutu ta kwanta,badai haka zaki kwana ba? kazama kije kiyi wanka,itakam ta gaji mikewa tayi tayi wankanta ta fito sanye da kayan jikinta,kije ki dauko kaya mana,mikewa tayi ga mamakin Omar yaga ta bude sip dinsa ta dauko farar jallabiyarsa ta koma toilet ta fito sanye da ita a jikinta,tayi kyau sosai.shanya waccan kayan tayi a toilet dinsa,fresh milk ta tsiyayo ta bawa Omar a baki ta sha itama suka kora ruwa tayi kwanciyarta,shi kuwa Omar ciwonsa yakeji,sai masifu yake karba

 

    Iklas tuni tayi nisa a bacci bata San me yake ciki ba,karfe daya na dare nishin Omar ya tasheta da gudu ta haura kan bed din yau ciwon na Omar ya banbanta da Wanda yakeyi wannan nishi kawai yake fitarwa da gumi shar shar,

    Iklas sosai take tausayawa Omar halin da yake ciki,tallafoshi tayi jikinta da kyar ta iya daura kansa a cinyarta ta jingina da jikin bed sai addua take tofa masa tare da shafa kansa,Omar bai San halin da yake ciki ba kawai dai yaji ciwon ya warke nan take bacci ya kwasheshi,Iklas tun tana masa addua har itama tayi baccinta a zaune jingine da bango hannunta kan sumar Omar haka suka kusa kwana,wurin 4am ta zameshi Daga cinyarta ta kifa jikinta ana Omar gashinta me matukar tsayi ya rufesu basu ma san a yanda suke ba haka suka dinga kwasar bacci,har rana ta fito basu sani ba,9am Mama da Ummi suka nufi dakin dan ganin ko lfy anjisu shuru,


     Ummi ce ta fara murda handle din tana zura kanta ta juyo ta fito tana mu koma Hajia yaran nan yan zamani ne ,Iklas ba kunya gareta ba ,murmushi Mama tayi tace Allah dai yasa karta fadawa Babana nafiso ya fara furtawaa tukun...to ameen dai cewar Ummi.


     10:30am Omar ne ya fara farkawa ji yayi kamar an danneshi hannu yasa zai ture Iklas daga jikinsa dan shi ya manta ma akwai Iklas,bai sani ba dai dai boobs dinta hannunsa ya sauka wani lutsum yaji kamar ya sa a flour,da sauri ya cire hannuwansa ya janye jikinsa,sai sannan yaga Iklas ce, a ransa yace kan uba dama yarinyar nan a bed dina ta kwana?

      Wannan batajin magana mayyar mazace,amma koma me ya faru su Mama ne suka jawo wlh ni ba ruwana.tunanin irin laushin jikin Iklas da yaji yakeyi,shi kam gaskia yarinyar nan zata tasar masa da sha'awar da zai kasa control.


     Da wannan tunanin ya shige toilet,Iklas kuwa tun farkawar Omar ta farka kunya ce ta hanata bude ido,kai yau sunsha bacci me dadi,Iklas tace yau na shaki kamshinsa da yawa bama na rigarsa ba na jikinsa.


     Mikewa tayi tare da mika ta gantsare tana salati sai murmushi takeyi ta fice daga room din da gudu,tana zuwa Palon Mama taja birki tayi turus ganin,Baffah, Mama, Ummi, Sultan da Raj.suhaila suna room suna buga game,Abdallah na koya mata da suleim.

     Kunyace ta kama Iklas musamman da tasan da jallabiyar Omar sanye jikinta,ganinta za ace mata mayyar miji,tunda Omar bai San da auren ba.

     Komawa tayi Inda ta fito da gudu su Mama kuwa daria ma ta basu,tana shiga dakin Omar ya fito daga wanka idonsa jajir yana jin ciwon amma ba kamar na da ba,da sauki sauki,

     Kallon Iklas yayi wai nikam tare aka haifemu ko mene,kin hanani sakewa sai kallon tsaraicina kikeyi bazan dauki wannan abunba ni,to ka bari nayi wanka nayi tafiyata mana.na fita wurin Mama naga mutane su sultan da Raj,


     Masifa ya fara yanzu a haka kika je maza suka ganki,jikinki fa yayi showing,Su Raj sunganki?ae har muka gaisa haushi Omar yaji da tsananin kishi baisan dalili ba.a tsawace yace Shiga kiyi wanka ki fitar min daga room,kuma ba ruwanki da ciwona na mutu ma mene damuwarki.


     Masifa kai ya Omar wallahi kasha ruwan alwala da cikin zafin nama ya rikota yana nunata da yatsansa kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa tunawa da yayi yanda take matukar kula dashi,damuwa da damuwarsa sakinta yayi kinci sa'a,kuka tuni ya kwacewa Iklas, 

Omar kuwa ji yayi ransa ya baci yasa Iklas kuka.


      Daga shi sai guntun towel iya kugu da wani a wuyansa karami farare jikinsa sai shining yakeyi ruwa dis dis.Matsawa yayi sosai kusa da ita wani shock yakeji itama wani abu taji yana fisgarta kamar ta rungumeshi,gudun kar alwalarsa ta karye kawai sai ya koma baya yana to me namiki kike kuka,kin kula shi tayi tana kukanta,to sorry yi shuru kinji Gomnati,sai kinyi Gomnati Allah dai ya biya Gomnati ba a ja daku.....daria ce ta kama Iklas sai kuwa ta fara kyal..kyal..kyal...Omar kuwa ci gaba yayi kamota nan kamota nan sai daria sukayi gaba dayansu tuni Iklas ta share hawayenta,shi kuwa Omar shagala yayi da kallon Iklas Tana dariar birgewa.Wani kayataccen kallo yake mata da yasa ta kasa jurewa ta shige toilet.da Sauri Omar ya shirya dan kar ciwo yaci karfinsa. Sallah yayi yau har nafeela yayi.inye su Omar an fara farfadowa.

     kayanta na jiya Iklas tasa ta fito itama tayi sallah da addua.

     Kafin ta idar tuni Omar ciwo yayi karfi.


       Zama tayi kusa dashi,kafadar ta tana gugan tasa sai ga Omar ya warke.hannunsa ta kama suka fita sashen Mama. Gaba daya suna palon ana jiransu kuwa.

     Kwace hannunsa Omar yayi ya koma jikin Baffah yana gaishe da kowa tare da musu Godiya.kowa ya jiki sukayi masa,tafawa sukayi da Sultan da Raj suna masa signa da ido suna kallon Iklas.


     Duk yanda yaso dannewa sai da suka bashi daria.Iklas kuwa suna gaisawa ta tafi dakin Ummi,tsantsara kwalliya tayi ta sa wata atamfa super cikin kayan da Omar ya taba dinka mata,bata taba sawa ba sai yau.Riga da skert sun kamata das tayi kyau,tasa red jambaki in ka ganta sai ka rantse yar shugaban kasasun


       Sai kamshi takeyi ta fito kowa kallonta yakeyi ,Omar ji yake kamar ya lasheta duk da cewar ciwo ya fara cinsa,su Baffah ciwon omar daure  musu kai yakeyi.


     Gomnati na zuwa taji kunyar rike Omar gaban su Mama,Gaba daya barin palon sukayi,Sultan da Raj ne kawai  suka zauna ganin kwakwaf.

      Omar sanye da wando 3quatr marar nauyi baki da blue,rigarsa blue itama,Iklas zama tayi kusa dashi wai kunyar Raj taji sai ta sa hannunta kasan cinyarta,ta danne hannun da cinya a hankali ta dinga tura hannun ta kasanta har ta tabo cinyar Omar.bata sani ba su Sultan na kallonta ai kuwa suka kwashe da daria,Raj yace mu ki daina kunyar mu ki kularmana da Frnd.ga breakfast dinku can.

    Harara Omar ya zuba musu ya fara magana.Asmabaffa

adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *