Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Friday, November 20, 2020

RANA DAYA COMPLETE HAUSA NOVELS

adsense here

RANA DAYA COMPLETE HAUSA NOVELS

[12/08, 22:25] ‪+234 907 483 8352‬: 🎀🎀🎀                 🎀🎀🎀

                🎀❣🎀

                   ❣❣


  💦💦                      🍃🍃🍃          

           *RANA D'AYA!*

  💦💦                      🍃🍃🍃

    

     _Written by Miemiebee👄_



_Assalamu Alaikum beautiful people, it's been a while, yes I know but here I am again with a different storyline. I would first of all like to thank and appreciate our mom, sister and a friend AUNTY SIS for everything she's been through for me all these time, know that am ever grateful._

   _Then to my sister, SADNAS who's been a true ally, thank you for supporting me dearly and helping me come up with this story name, I love you_

  _Lastly, to all my fans around the globe, my whatsapp group members in particular thank you for supporting me always I love y'all fisabilillah, happy reading!_

 


   *PAGE 0⃣1⃣*



   _Prime Lodge And Apartment hotels and suits - 1 Abba Kyari Abba Kolo Street Off Circular Road GRA Maiduguri, Borno state._


       1:24pm


    Samari ne guda biyu masu jini a jik'a wanda baza su wuce k'imanin shekaru ashirin da hud'u zuwa shida (24-26) ba, (kyawawa masu ginannen jiki.) Zaune suke bisa d'aya daga cikin teburan dake cikin restaurant na cikin Prime Lodge And Appartment hotels and suits suna fuskantar juna a yayinda kowanne ke da plate na fried rice had'e da co slow da kaza a gabanshi se kuma Schweps a gefe. Abincin nasu suke ci hankali kwance babu wata damuwa tattare da su. Kallo d'aya mutum ze musu yasan cewa ma'aikatan banki ne saboda corporate dressing da suke sanye da ita. Wanda ya kasance me haske sosai, mafi kyawu da kuma k'iran jiki yana sanye ne da sky blue long sleeves shirt with a red tie a yayinda d'ayan kuma ke sanye da white long sleeves shirt da black bow tie, duka da black pantsuit a yayinda suka mak'ala suit jacket nasu a jikin kujerun da suke zaune akai. 


    D'aya daga cikin wayoyin da suke kan table d'in ne ya shiga ringing, kyakkyawan ne yayi yunk'urin motsawa nuna alamun cewa wayarsa ne kenan. Drink nasa da yake zuk'a ya ajiye gefe guda sannan ya lek'a screen d'in ringing phone d'in wanda ya kasance iphone 7 plus jet black don ganin wake kira dum! Yaji zuciyansa ya buga.  


   "F*ck!" Ya fad'a a cike da tashin hankali a murya chan k'asa-k'asa. 


   "Triple A lafiya?" Abokin nasa ya tambaya immediately, yana mey maida hankalinshi sosai wajen abokin nashi  da tashin hankali ya bayyana karara a fuskansa yana me goge hannunsa jikin wani brown multicolored hanky yayin da yake da aniyar daukar wayar. "Old man ne wallahi ya kirani d'azu da muke meeting gashi na manta shaf in kirashi bayan da muka gama" ya amsa sa da sauri gudun kar wayar ta tsinke. Swiping yayi ya d'aga tare da maqalashi a kunnenshi. 


   "Uhm uhm" yayi gyaran murya tare da fad'in "Halo Abba?" cikin sweet husky like voice nasa wanda there's no doubt duk macen data kasance tana saurara dole ne ta tsinci kanta acikin wani yanayi. Murya ne da ke kwantar da hankalin me sauraronsa a yayinda yake sa ka mance duk wani damuwan da ke tattare da kai. Murya ne da ze iya sa bugun zuciyan mutum ya har6a, duk ba don komai ba se don coolness da calmness da take d'auke dashi. 


   "Prince?" Cewar Abba daga d'ayan 6angaren. 


  "Na'am Abba am sorry wallahi kai na ne yayi zafi kuma na manta in kiraka lokacin dana fito, I was in a meeting da ka kira d'azu" yayi mai bayani cike da biyayya. 


  "Oh haka ne? Nace kana ina ne?"


  "Yanzu ina Prime Lodge ne ina cin abinci" ya amsa a takaice yana me duban rolex agogon da ke d'aure a tsintsiyar hannunsa. 


  "Alright ina buk'atan ganinka please as a matter of urgency" ya sanar dashi yana mey jaddada masa mahimmancin kiran. 


  "Sure Abba gani nan tahowa right away."


   "Toh seka zo, Allah ya kare" daga haka yayi hanging tare da miyar da wayan kan table din "Huh!" Ya sauke nauyayyar ajiyar zuciya da ta ja hankalin abokin nashi. 


   "Guy how far? You seem tensed?" Tambayar abokin. 


  "It's Abba" ya amsa sa a kasalance yana me nazari. 


  "Mai ya faru da shi?" Abokin ya kuma tambaya determinately yana kai cizo wa cinyan kazan da yake riqe dashi. 


  "Nima ban sani ba kawai de something smells not right don daga yadda yake magana mutum zesan da akwai wani abu a k'asa and I've got to find out" ya k'arasa tare da miqewa wanda hakan ya bawa mai rubutu daman k'arewa tsawonsa kallo, ba shakkka tsayayyen na miji ne don kuwa ko ba a auna ba ido ya nuna he'll be nothing less than 6ft height. Damn!


  "Abincin naka fah? Bazaka k'arisa ba?" Yayi saurin tambaya. 


  "Kiran mahaifi fa Sultan? Kuma baka san me ake nufi da urgently bane? Urgently fa yace yake nema na I have to go, here" ya tsaya tare da zaro black wallet nasa na gucci dake cikin pantsuit nasa "Pay for those" ya sanar dashi tare da ajiye N4,000 akan table d'in ta gefen Sultan. 


   "Toh se yaushe kuma?"


  "Kai dai ka k'ware a wajen tambayar silly questions" ya amsa shi yana juya ido "Of course gobe mana ko ka manta yau Wednesday ne gobe akwai office kuma ina da meeting?"


   "Whatever!" Sultan ya amsa tare da jan k'aramar tsuka. Afzal be sake yi ta kansa ba ya shiga tattara assets da gadgets nasa then lastly suit nasa dake rataye jikin kujeran, ya6awa a hannunsa yayi sannan kaman yadda ya saba tafiya a hankali cike da k'asaita ya shiga takawa har ya fice daga building d'in ya shiga nufan inda yayi parking motarsa k'irar Genesis G80 dake jet black in color wacce tasha wanki k'al. 


    Bud'e k'ofan gaba yayi ya jefa suit d'in a baya tare da miqa sauran abubuwan da yake riqe dasu a passenger's seat sannan ya tadda motar. Reverse yayi ya fita daga cikin harabar hotel d'in. Beyi nisa ba wayar sa dake jikin hanger ya shiga ringing ganin Abba ke kira again yaji gaban sa ya kuma bugawa wai me ke faruwa ne? Ya tambayi kansa. Ba tare da 6ata lokaci ba ya shiga neman car blutooth nasa wanda ke taimaka masa gun amsa waya ta hanyan sauqi ba tare da hankalinsa ya rabu ba a duk lokacin da yake tuk'i. A chan k'asar motan ya samu, be hankara ba yana d'aga kansa kawai yaga ya ma bar kan kwalta gabad'aya ya na nufan kan wata yarinyan da bazata wuce kuma baza ta gaza shekaru sha takwas (18 years) ba dake tsaye some meters away from him ta bud'e baki wide open in shock kawai tana jiran aikin gama ya gama; tsabagen yadda ta tsure ko motsawa takasa yi don ku6utar da kanta daga aukuwan wannan mumunar had'ari. Sanye take da baby pink color hijab me silky feel wanda ya mugun tafiya da golden skin color nata dake nan kaman irin na sudanese girls d'innan. Tana rik'e ne da manya-manyan ledoji da alama daga kasuwa take tayo siyayya da cefane. Ba shiri ya shiga neman inda brake nasa yake da niyyan takawa don hana aukuwan wannan had'ari dake neman afkuwa sede shima don yadda ya tsure ya ma rasa a ina brake d'in yake, ya juya sterring ma duk dabarar bata zo mai ba. 

   Kafin ya samu kan brake d'in ya taka ina aikin gama ya gama har ya buge 'yar yarinyan da tuni ta zube a k'asa sede Alhamdulillah a nan Allah ya tsaida abun, Allah beso ya hau kanta ya tattake ta ba. Bonnet d'in ne ya bugeta ta gun k'afarta wanda hakan yayi sanadiyyar sum6ulewar ledojin dake hannunta na fashewa suka fashe na zubewa suma suka zube sukayi d'ai -d'ai a k'asa. 


    Wani wawan ihu ta k'urma kasancewan wannan ne karo na farko da mota ya ta6a bugeta a tarihin rayuwarta. Wallahi duk bakin Mami ne (mahaifiyarta,) abinda ta soma cewa a ranta kenan. Saida Mami tace mata tabari se yamma yayi taje aiken amman ta dage ita inba yanzu ba bazata je ba, toh ai ga irinta nan, abinda babba ya hango yaro koda ya hau kan tudu ba lalle ne ya gani ba. 


   Ba shiri mutanen da suke kusa duk suka yo kanta. Salati kawai Afzal yakeyi acikin motar har izuwa lokacin da ya fito yayi kan yarinyan dake ta shar6an ihu har yanzu wane wacce ake zare ma rai. 


   "Wayyoo ya karya min k'afa ya kasheni Mami! Kizo ki taimakeni" se ihu take tana salati. Kanta Afzal yayi da sauri tare da tsugunawa gabanta, k'afan nata data rik'e take ta ihu a yayinda yake mata zok'i ya aza hannunsa akai don duban ko taji mummunan rauni. Hannunsa na kaiwa akan jikinta baiwar Allah tayi tsit mutum na iya rantsewa liqe mata baki akayi. Tunda take a rayuwarta, a duk tarihin rayuwarta d'a na miji banda Papi (kakanta) be ta6a ta6a wani sashi a jikinta ba inba yau ba,  idan an ta6ata toh a hannu ne wanda hakan ke faruwa a garin miqa ma wani abu ko makamancin hakan. Ko a secondary school saida akayi mata shedan hakan, har ya kaiga classmates nata suna kiranta da ustaziya suna mocking nata da sunan 'yar mallam. 

    Shikenan yau nata ya k'are zatayi ciki, dama tunda ta fara menstral flow nata Maami tace mata duk sanda ta bari wani d'a na miji ya ta6ata toh zatayi ciki ranan, yau tana cikin wani yanayi. Wani irin d'an banzan ihu fiye da wad'anda take tayi tun d'azu ta saki, Afzal besan lokacin da ya sake ta ba ya shiga toshe kunnensa. Wannan wane irin mugun ihu ne! Yayi tunanin haka a cikin zuciyarshi. 


    A rayuwa idan akwai abinda ya tsana shine hayaniya kasancewar be saba da shi ba, shi kad'ai ne d'a a gun iyayensa. Baida yaya bale k'anin da ze tak'ura wa rayuwarsa, gidansu kullum tsit daga shi se Abban shi se Umminsa da kuma masu aiki. 


   Kunnensa ya shiga murzawa a tunaninsa ma ya kurmance ne. Sleepy like eyes nasa that are surrounded by long thick eyelashes ya d'ago yana kallonta cike da mamaki shin how is it possible ma ace mutum nada irin wannan murya me uban k'ara haka? To his ultimate dismay kawai yaga itama kallon nasa take ko kyaftawa babu. 


    Ta fannin ta kuwa tana iya rantsewa tunda tasan kanta inba a TV ba bata ta6a ganin kyakkyawan na miji kaman wannan dake tsugune a gabanta ba it became impossible to even blink. Shima kallon nata ya tsaya yi badan komi ba kuwa se domin tayi mai kama da wani wanda ya sani sede ya kasa tuna a ina. Sun d'au tsawon lokaci suna kallon juna, kowa da abinda yake sakawa a cikin zuciyarshi, daga bisani yarinyar ta kawar da kanta tare da kuma k'urma wani ihun da ya tsoratar dashi har yana neman tuntu6ewa. 


     "My goodness!" Yayi exclaiming a firgice anya kuwa ba aljana ya buge ba? Ya soma tunanin hakan a ransa. 

   "Wayyo bawan Allah ya karya min k'afa! Jama'a ku taimakeni!" Tasa kuka tana ta matse 'yar k'wallan da ya ciko mata a ido. 


   "I'm sorry" ya fad'a a kid'ime don ko gabad'aya ta rud'ar dashi saidai wane k'ara yace mata. "For heaven's sake kiyi hak'uri haka kibar kukan nan!" Ya sanar da ita a tsawace. Shi kansa besan lokacin da ya fusata ba. Saboda ta fara bashi haushi matuka, gashi de ya duba k'afan nata da take ta kururuwa mai bega wani ciwon arzikin da taji ba banda 'yar k'urzine guiwanta da tayi maybe sed'an internal pain wanda baza a rasa ba. Then mesa take mai ihu tana cika mai kunne haka? Bata san cewa ya tsani hayaniya bane musamman na shirme mai k'ara da ihu irin wannan nata? 


   Shiru tayi tana kallon sa cike da mamaki na matuk'a lallai kuwa ya cika d'an halas. Ma tukuna bai da kunya tayi tunanin hakan. Na farko ya bugeta ya karya mata k'afa ya sanya mata asara kuma ya tsaya yana mata masifa? Na biyu kuwa mamakin ya za'ayi muryan na miji ya kasance da irin wannan dad'i da sanyi take. Bata ta6a jin murya irin nasa ba, tana iya rantsewa muryansa yafi na duk wani mahaluk'in data sani dad'i. Masifa yake amman yadda kalamun nasa suke slipping daga pink full inviting and perfect carved lips nasa yasa tama manta inda take da kuma inda ke mata ciwo. Ganin kallon da take mai bana k'arewa bane ya sashi feeling guilty, baida right na mata masifa, does he? 


  "Look am sorry but dan Allah ki dena mun wannan ihu haka and kibar kukan, yi hak'uri zan kai ki clinic su duba ki" kafin tayi magana wani mutum ya riga ta.


   "Mallam kayi sauri mana kayi wani abu ko se lokaci ya k'ure tukuna zakayi abinda ya kamata?" Ya tambaya yana tsaye a kansu. 


    "I can handle this please duk kuna iya tafiya, ni na bugeta nasan abinda ya dace inyi, bana buk'atar wani ya gaya mun abinda zanyi so kuna iya tafiya" ya fad'a more like a command. D'aya bayan d'aya suka shiga watsewa ya rage daga Afzal se wannan drama queen dake ta faman kukan shagwa6a tun d'azu. 


   "Ke bakiya jin hak'uri ne kam?" Ya tambaya girarsa a murtuk'e yana me dawo da kallonsa a gareta like ta fara bashi haushi. 


  "Ban sani ba" ta murgud'a mai baki cike da rashin kunya "Wallahi ni gida gun Mami na zaka kaini ba wani asibiti ba. Haka kawai kana tuk'i ba ka kallon inda kake zuwa ka bugeni don mugunta da zalunci kuma yanzu ka tsaya kana min masifa wallahi Allah yafi ka, arghhhh! k'afa na" ta cigaba da ihun. Da mamaki yake kallonta, aje a bata san iya adadin shekarunsa ba amman ai ido ma ma'auni ne. Ita kanta tasan ya girmeta, inta haihuwan dabba nekam bema san kalan ta nawa ya ajiye ba. Secondly kodan wannan gigantic body structure na cikakken d'a na miji da Allah ya basa ma ai kad'ai ya isa yasa taji fakon sa tayi using respectable tone dashi amman har take kwatanta sa da azzalumi, gaskia wuyanta ya isa yanka. Mumunan harara ya watsa mata, wani ihun ta shiga k'urmawa. Ganin tana neman tara masa sabin jama'a ninkin na farkon yasa Afzal yayyafa wa zuciyansa ruwan don su rabu lafiya, duk wani feeling da girman kan da yake ji dashi ya sauk'e ya bata hak'uri. "I'm sorry" ya fad'a can ciki-ciki sede kaman bada ita yake ba ihun nata ta cigaba da rusawa chan da abin ya ishesa yace, "Wallahi idan baki min shiru ba allura zan miki" ya gwada tsorata ta don ko ba a gaya mishi ba tayi kalan me tsoron allura, yo mutumin da be karye ba yake ikirarin hakan kam ai se a hankali. 


   Allura?! ta nanata a zuciyanta. Rabonta da allura tun tana JSS1 time da tayi wani rashin lafiyan daya kusan kaita lahira, ai ba shiri tayi shiru. 


  "Better" yayi hissing yana maida hankalinsa kan k'afarta ta da take riqe dashi har a yanzun ta gurin ankle nata. Yunk'urin ta6awa yayi aiko ta make hannunsa da d'an karen zafi wanda ko be tambaya ba yasan she's left handed (mutum me rubutu da aiki da hannun hagu) babu makawa sune hannun su keda uban zafi idan sunyi mari. Da wuri yaja hannun nasa baya yana murzawa kaman d'an yaro meanwhile yana kallonta cike da rashin yardan abinda ya faru, taya zata mareshi babba da shi? Ya tabbata bata da kunya. 


   "Ke!" Yayi exclaiming still not believing abin da ya faru "Ni kika mara?" Ya tambayeta cike da rashin yarda. 


  "Kuma ka sake yunk'urin ta6a ni na k'ara ma wani ba, ba nan kad'ai ba kuma na tara maka jama'a wallahi." Totally floored ya tsaya yana kallon ta wace irin masifa ce ya jefa kanshi aciki yau? Da ba don kar ya shiga bakin jama'a ba da ya gwada mata rashin mutunci anan, da ya nuna mata waye Afzal Ahmad Amin (Triple A.) Wurga mata kud'in asibitin dayake da niyyan kaita yayi niyyan yi yayi tafiyarsa, taso ta kai kanta ko kuwa ta cigaba da zama anan d'in, how dare she slaps him? Danne zuciyarsa kawai yayi ya miqe "Tashi in kaiki clinic su dubaki in rabu da ke for good, ina da muhimman abubuwan da yafi zama gu d'aya dake."


  "Lallai ma bawan Allah ya tabbata ba kada kunya" tayi stating tana kallon cikin idanunsa a yayinda kyawun halittar da Allah yayi masa yake sake bayyana, ba abinda yafi burgeta kaman clean shave nasa da kuma silky gashin dake kwance a fuskansa a matsayin saje, only if yana tara gemu da tuni sajen da gemun sun had'e. Dama sau dayawa tana jin ana cewa maza kyawawa basu da mutunci sun kuma iya disregarding mata saboda gani suke kowa is after their beauty sede ita bazata bari ya raina taba, yo meye amfanin bakin da Allah ya bata? Right to freedom of speech. 


   "Ka karya min k'afa kuma ka tsaya kana cemin in mik'e? A ina aka ta6a yin hakan a garinku?" Ta tambaya kanta tsaye tana watsa mai harara. 


    "Now that tears it" Ya furta a fusace, tun d'azun yana d'aga mata k'afa yana saita kansa amma yarinyar nason kure hak'urin shi, dole yayi wani abu a kai kafin ta raina sa. Tsugunawa yayi ya cafko hannunta cike da mugunta yana murgud'awa. 

   "Ka sake ni!" Ta fad'a tana me k'ok'arin k'watan kanta sede takasa. Banza da ita yayi "Da farko dai ki iya wannan fitsararren bakin naki ko kisha zana anan wajen, kinga nayi maki kama da tsaranki ne?" Ya tsaya yana mata wani matsiyacin kallo. "Abu na biyu " ya cigaba "Ni Afzal ban karya miki k'afa ba so ki daina min sharri."


    "Chan maka nide ka sake min hannu ka dena ta6ani" ganin baida niyyan saketa tace cike da tsiwa " Se ta dalilin hakan ciki ya shiga jiki na tukuna ko me?!" Subhanallah wai me ke damun kwakwalwarta ne? Kunyan abinda ta fad'a ne ya kamata ita da kanta bale shi Afzal daya kasa gane ma meh tace balle abinda hakan ke nufi. Kanta ta kawar da wuri tare da rufe idon ta tana me cizan la66enta consciously. 


   Ta fannin Afzal kuwa kaman gunki yayi tsaye gun, ciki fa tace? Ta yaya? Wai shin 'yar k'auyen ina ce wannan bala'd'add'iyar yarinyan da Allah ya had'asa da ita yau? Ba tantama 'yar gudun hijira ce, bujakancin nata yayi yawa. 


    "Wallahi zan sa ihu" ta sake fad'a da bece komi ba har yanzu be kuma sake mata hannun ba. 


  "God help me!" ya fad'a yana dafe kansa. "Good idan bakiya son in ta6a ki ciki ya shiga jikinki kamar yadda kika ce to maza tashi kan k'afafunki, ki miqe-" katse sa tayi cike da rashin hakuri. 


    "Nak'i ka sani na dole mschww!" ta ja tsuka. Yunk'urin sake ta6ata yayi wannan karan don ya tsinka mata mari, tasa ihu "Wayyo dan Allah kayi hak'uri zan miqe zan miqe."


   "Good girl now up you go."  Shiga miqewan tayi kaman yadda ya buk'ace ta amman ta kasa. "Wayyo wallahi bazan iya ba wallahi bawan Allah ka karya min k'afa" ta shiga rera kuka. 


   "Ban ce kibar min sharri ba?" Ya tambaya yana nad'e hannuwanshi akan faffad'an k'irjinshi. 


   Cike da shagwa6a tana murza idonta tace, "Ka fad'a amman wallahi ba sharri bane wayyo Mami na ni ka kaini gun Mami na."


  "Kin rantse de baza ki kulle wannan k'aton bakin naki daya cika ma mutane kunne da ihun banza da rashin kunya ba ko? Nasan yadda zanyi hakan" gano bakin zaren wato so yake ya sake ta6ata yasa tayi tsit. 


   "Ki miqe nace" ya buk'ace ta. 


  "Wai ba kada kunne ne? Ce maka akayi zan iya miqewan? Inda zan iya ai da nayi da jimawa ko jinka nid'in jin dad'in zama gu d'aya da kai ne? Dubi fa k'afa ka karya min."


  "Kika sake cewa na karya miki k'afa sena go6e wannan fitsararren bakin naki try me and see" ya fad'a threateningly. 


  "Azzalumi" ta furta can k'asa-k'asa yadda baze ji taba sede shegen nisan kunne ne dashi tsab ya jiyota. 


  "Kema 'yar gudun hijira kawai" ya mayar mata. Harara ta watsa mishi tana cigaba da zum6uro bakinta, kallo ya k'are mata sannan daga bisani ya jata da hannu tare da d'agata a sama cak ya wulla ta into a bride like style sannan ya shiga takawa da ita. Cikin motar ya sata sannan ya rufe har a yanzun tana mai ihu. 


  "Wayyo 6arawo ze gudu da ni!" ta fad'a tana bubbuga glass na windon. So take ta bud'e k'ofar ta fita amman don k'auyenci irin nata bata iya ba. Yana shiga motan ya kunna ignition d'in har nan bata bar ihun ba yanzu kuma ba na ze gudu da ita take ba na cafanin Mami ne da suka zube, akan ya tsaya ta tattara sauran abubuwan da basu sha k'asa sosai ba saidai be ko saurara mata ba. Ganin hayaniyan nata bana k'arewa bane yayi pulling headphones nasa ya cika da loud music ya sanya yadda bazata kuma daminshi ba. Don kanta tayi shiru ganin ba mahalicci se Allah, har anan kuwa k'afan nata nakan yi mata zok'i. A hankali AC'n dake tashi acikin motan ya soma shiganta wani sanyin da bazata iya tuna when last ta ji irinsa ba ta soma ji probably tun da suka je competiton Kano da take ss2. 


   Afzal be sake ce mata komai ba seda suka isa asibitin inda yayi parking a harabar asibitin sannan ya fita ya bud'e mata k'ofar yana jiran ta fito itama. 

   "Ko ka manta ka karya min k'afa ne kake jiran in fita da kaina d'in?" Tayi inquiring cike da rashin kunya. 


  "Bance karki sake fad'in na karya miki k'afa ba?" Can k'asa-k'asa tace, "Ka fad'a amman ai gaskiya ne." 


   "Kuma bana son gungunin nan bana son raini" ya fad'a a cikin tattausar murya. Ita dariya ma ya bata wa yaga Babanta da har zaice ga abinda yakeso da kuma abinda bayi so. Dariyan ta saki tana me mai kallon bakwai saura kwata cike da fitsara. Har maqora ta kai sa besan sanda ya fincikota daga cikin motar ba a fusace. Wani irin mumunar ihu ta k'urma bisa zogin da k'afan nata mai ciwo yayi mata bayan da ta taka mistakenly. Zubewa tayi take a gun a k'asa tana me raira kuka a yayinda ta rik'e gun idon sahun nata tana ihu. Ganin fa tana iya tara mishi jama'a ya jata da hannu d'aya putting her in a bride-like style kaman na d'azu ya shiga takawa da ita. 


   "Ka sauk'eni nikam bana so ka sauk'e ni nace mugu kawai shin baka san haramun ne ba ta6a wanda ba muharramin ka ba? Ka sauk'e ni!" Maida kallonsa yayi a gareta, "In sauk'eki?" ya tambayeta looking directly into her brown eyes a yayinda manly k'amshin jikinsa ya cika mata hanci, yau taji k'amshin da yafi turaren wutan Mami dad'i. 


  "Eh" ta fad'a tana me kawar da kanta a hankali, bata san me ba amman bata iya kallon cikin idanunsa na tsawon lokaci. Nodding kansa yayi sannan daga bisani ya janye hannayensa da suke riqe da ita, ai ba shiri ta zagaye hannayenta a wuyansa don maintaining balance nata da kuma hana kanta daga fad'uwa a k'asa to injure herself some more. Hak'i ta shiga yi na sosai sabida yadda zuciyarta ta mugun tsinke bata d'au rashin imanin nasa ya kai ga har zata ce ya saketa ya kuma yi hakan ba. Mak'irin murmushin da ya 6ullo da one-sided dimple nasa ya saki ganin wannan funny reaction natan ashede ba da gaske take ba "Dan Allah ka tare ni kar na fad'i" tayi rasping cike da tsoro ganin tana neman zamewa shikuwa baida niyyan preventing aukuwan hakan. 


   "In tare ki? Ina cewa kikayi in sake ki? Sai ki sakeni nima" ya fad'a in an I don't care tone. 


   "Zan fad'i ne please ka tare ni."


  "Kin san da hakan kikace in sake ki?"


  "Toh kai ma kasan zaka sakenin ka d'auke ni tun farko?" Har anan bata bari sun sake had'a ido ba. 


  "Kina magana ne?"


   "A'a nayi shiru" ta furta a hankali. Mugun kallo ya watsa mata sannan ya rik'eta firmly suka k'arisa cikin asibitin inda akayi mata duk wasu gwaje gwajen da suka kamata aka gano spraining ankle (targade kafan) nata tayi a garin fad'uwan da tayi shiyasa ta kasa taka k'afan amman ba karyewa kaman yadda take ta kururuwa ba. Miqar da k'afan nata akayi inda tayita ihu wane wacce ke labor room. Shi de Afzal dake tsaye bakin k'ofa yana tsananin mamakin wacce irin roguwar yarinya ce wannan. 


   Bayan fitowan Dr ya basa prescription na drugs nata inda ya nufi gun cashier don biyan kudi sede hakan ya gagara kasancewan besan sunanta ba kuma a k'aidan asibitin bayan ko wani payment se anyi entering sunan patient da magunan da aka biya a record book. Excusing kan sa yayi ya wuce d'akin nata inda yayi knocking kamin nan yasa kai. Zaune bisa kan gadon d'akin ya tsince ta, ta zura wa k'afan nata da aka nad'e mata shi da bandage ido tana ta shessheqa. Tausayi da dariya duka ta bashi at a time, yana iya cewa tun da ya san kan sa be ta6a ganin drama queen kalan ta ba. 


   Ba'a dauki tsawon lokaci ba kafin k'amshin turarensa na Caron designs ya bugi hancinta kai tayi saurin d'agawa don ganin waye, ganin shi ne kuwa ta dukar da kan nata sannan ta shiga share hawayenta a hankali. Cike da k'asaita ya k'arisa gefen ta ya zauna daga baya kamin tace wani cikin ze sake mata idan ya matso kusa da ita. 


   Ganin ya kusan minti biyu zaune wajen batayi yunk'urin mai magana ba yayi deciding to go first, "What is your name?" ya tambayeta amman tamkar da gunki yake magana haka ta mar ko kallonsa batayi ba. "Hey dake nake magana fa" ya fad'a bayan wani lokaci. "Tell me your name in samu inyi settling bills naki" ai kaman me jiran ya kuma cewa wani abu kawai ta sa mai kuka, abinda yafi tsana kenan, ihun nan nata. 


  "Oh! Help me God'" ya furta tare da dafe kansa "Ke wai shikenan bakida sana'ar data fi ta kuka? Kukan me kuma kike min yanzu? Ni na ja miki k'afan ne? Seki je ki samu Dr'n kimar wannan kukan and not me" ya fada dalla dalla yadda zata gane. 


  "Mugu amman ai kai ka kawo ni seda na ce maka ka kaini gun Mami na kak'i Allah ze saqa min." Dariya ne ya k'eto mar dukda cewa ta kwatantasa da  mugun, muryansa ya gyara don 6atar da dariyar there's no way ze bar 'yar yarinya haka ta gane mar dariya. 


  "Whatever tell me your name, will you?"


  "I won't okay? Stop asking me to and just take me home I don't want your drugs keep it" ta sanar dashi cike da tsiwa. Baki hangame ya bud'e yana kallonta da mamaki bil adadin. Na farko sam be kawo a ransa ma ta ta6a zuwa boko ba bale ta iya speaking fluent English haka. Na biyu taya zata kalli duk girmanshin nan ta mai masifa kaman wani d'anta ko shakkansa bata yi? Yau yana ganin wacce ta fisa taurin kai, ya lura idan yace shima ze nuna mata nasa taurin kan toh ba shakka baza su amfana da komi ba illa ma raina shi da zatayi don haka ya yayyafa wa zuciyarsa ruwan sanyi ya sauk'e duk wani tak'ama da jin kai nasa, fatansa kawai su rabu. 


   Numfasawa yayi don bata hak'uri amman ya kasa gashi har yanzun bata bar kukan da take ba. 


   "Okay I'm sorry" ya furta murya chan ciki-ciki bayan ya d'auki tsawon lokaci. "Nasan duk laifi nane kike nan but-"


   "Amal... Amal Abdallah" ta sanar dashi cikin hawaye ta hanyan katse sa ba tare da ta d'ago kai ta kallesa ba. Kallonta yayi na 'yan seconds sannan ya miqe yaje yayi settling bills d'in ya dawo ya tarar da ita still yadda ya barta. 




     *~*~*~*~*~*~*~*~*~*~*~*~*~

  So guys how was the chapter? Our very own first chapter. Was it a hit? Did you enjoy it? Are you craving for another update already? 


   RANA D'AYA 

  #RD

   Love... Miemiebee👄✨

[12/08, 22:25] ‪+234 907 483 8352‬: 🎀🎀🎀                 🎀🎀🎀

                🎀❣🎀

                   ❣❣


  💦💦                      🍃🍃🍃          

           *RANA D'AYA!*

  💦💦                      🍃🍃🍃

    

     _Written by Miemiebee👄_



   *PAGE 0⃣2⃣*





    Seda ya d'auki tsawon lokacin da ya wuce tsammanin mutum sannan yace, "Ga magunan naki, ina kyautata zaton kin iya karatu za kuma ki iya gane dosage d-" bata basa dama ya k'arisa fad'in abinda yake da niyya ba ta katse shi "Mallam ba seka zageni ba am not an illiterate."


   "Serve you well" ya fad'a ba tare da nuna damuwa ba "Then kina iya tashi in kaiki gida."


  "Nagode kar ka damu I can bring myself home" taga alaman d'an rainin wayo ne shi to ya kwantar da bokatin hankalinsa, kar yace don ya ganta a haka zey raina mata wayo dan kuwa ita ba jahila bace saboda tayi karatun ta na secondary ba kuma a kowani gajan government school ba. No private school ne me kyau wanda ake kira da Ruby springfield college wanda ya kasance one of the best schools in Maiduguri. 


  "What gibberish are you saying?" Ya tambayeta a takaice. "See kar ki 6ata min lokaci, kar kiga don tun d'azun ina danne zuciya na ina binki a hankali ki d'au hakan ba a bakin komi ba. Ina da muhimman abubuwa a gaba na wanda sukafi tsayuwa anan ina rok'anki to take you home, now get up" ya buk'aceta cike da tsiwa sede ko motsawa Amal batayi ba. "Are you deaf?"


   "I said to leave me alone!" Ta buga mai tsawan itama "Ka kama ka jawo min asara ina zaman zama na zaka wani kama kace min in tashi ka kaini gida? Me kakeson in cewa Mami bayan duk cafanin dana yo mata ka ta6ar6arar min dasu kabarni da babu? Don Allah ka barni kayi tafiyanka."


   "In ke baki san abunda ya kamata ba toh ni na sani a cewarki bazan biya ki asaran dana janyo miki bane? I'm aware of all that and zan mayar miki da komi kawai ni ki tashi in kaiki gida na bawa iyayenki hak'uri na fita hak'k'inki, I have other important things to attend to" ya sanar da ita. Kaman wacce bazata motsa ba se kuma ta shiga miqewa a hankali wanda a garin hakan ta kusa fad'i kasancewar k'afar nata da ta kasa takashi. Da sauri Afzal ya tarota, ganin bey saketa ba har yanzun kuma baida niyyan yin hakan ta shiga jan hannunta sai dai ta kasa. 


   "Don't fight it" yace da ita "Muje" bata sake yunk'urin k'watan kanta ba har suka kai haraban asibitin inda yayi parking motarsa. Sanyata yayi a kujeran gaba sannan ya zagaya ya shiga shima tare da tada motar. A circular road inda ya kad'etan suka koma inda ya buk'ace ta da ta rubuta masa list na abubuwan datayi rashin nasu. Ba gardama ta amshi paper da biron ta lisafo komi harda kud'ad'e da amount nasu. Abu d'ad'd'aiku ne be samu ba wanda yamata alk'awarin bata kud'in idan ya kaita gida. A farko yaso su jesu kasuwan domin ta siyo amman tuna besan kan kasuwan ba sabida bai ta6a shiga ba seya fasa. A karo na biyu kuwa yayi tunanin ko zasu shiga su biyu tayi leading nasu but referring to her wounded leg yaga wuya kawai hakan zai bata so se yayi sticking to first decision d'in kawai: na miyar mata da kud'in. Kwatancen gidansu ya buk'ace ta da tayi mar wanda tayi ba tare da gardama ba. Chan cikin Jiddari suka shige. Tunda Afzal yake be ta6a shiga kwamacalan unguwa ba kaman wannan se yau, yasan war haka motansa ya fita daga kamanninsa ya dawo wani abun na daban saboda potholes da kwatamin daya rink'a shiga. Sun kai wani junction ta buk'ace sa daya tsaya. 


   "Ina ne gidan naku?" Abinda ya fara tambayarta kenan. 


   "Mota baya iya shiga layin zan k'arisa daga nan nagode."


 "Acewarki kawo ki kawai nayi saboda inada ra'ayin hakan? Am here to apologize to your parents and tsaya ba sekin karya min handle na mota ba" ya buk'ace ta ganin tun d'azun take k'ok'arin bud'ewa amman ta kasa. Fitowa yayi ya zagaya sannan ya bud'e mata k'ofar tare da miqa mata hannunsa.  A cewarta gabad'aya nufi yake da ta sanya nata aciki saboda ya taimaka ya fito da ita daga motan sede wani hanzari ba gudu ba tana gwada yunk'urin sa hannunta cikin nasa kawai taga yaja hannun nasa baya da sauri yana me kad'a mata kai "Tray d'in zaki miqa min" ya sanar da ita. Wani irin kunya kaman ta tone k'asa tasa kanta aciki ta jiyo amman wallahi seta rama ba shakka da gangan ya mata hakan don ya kunyatar da ita. "Kar ka damu ina da hannu I can manage" ta fad'a rai a murtik'e tare da murgud'a mai baki. Murmusawa yayi yaja gefe tare da crossing arms nasa a faffad'ar k'irjinsa yana me kallonta. Yasani sarai bazata iya fitowa ba harta sai ya taimaka mata toh why don't he enjoy the moment? 


   Amal tafi minti biyu tana k'ok'arin fitowa amman ta gagara, ko kad'an k'afan nata baison nauyi ai kawai ta rushe da kuka har anan Afzal be motsa ba seda yabari ta sha wahala ta shiga neman taimako da kanta. Ganin ba mahalicci se Allah ta kewayo da kallonta a garesa, dagangan shiko ya shiga duban lokaci a agogon dake d'aure a hannunsa pretending as if beda masaniya game da abinda takeyi tun d'azu. 


   "Bawan Allah don Allah ka taimaka min bazan iya fita ba." Dariya ne ya k'eto mar sosai amman ya dage ya danne tare da matsowa kusa da ita. "So kin iya magana da ladabi haka dama?" Ya tambayeta yana me k'are mata kallo. 


  "Ni ba abinda na buk'ata ba kenan" ta amsa tana me kawar da kanta haka kawai bata jin dad'in had'a ido dashi, "Ni ka taimaka min in samu in fita daga wannan motar nakan please!"


  "Ohh! Rashin kunya kuma zakiyi min? Kinsan kad'an ne daga cin aiki na in barki har sekinyi tsami cikin motan nan ko? Don't you dare me young lady."


   "A'a kayi hak'uri don Allah." Cike da rashin mutunci ya taimaka mata ta samu ta fito daga motan suka shiga takawa zuwa gidan nasu wanda baida nisa daga inda Afzal yayi parking. Sede duk wani angle da suka wuce se sun zama topic and side of attraction. Surutu babu wanda basu ji ba amman duk haka suka manna musu har suka k'arisa gidansu Amal d'in. 


   Gida ne dai-dai da d'an talaka bawan Allah wanda za'a iya cewa be rasa ci da sha ba da kuma tufafi. D'akuna biyu ne gabad'aya a gidan a jere seda toilet d'aya daga other end d'in sekuma kitchen a opposite nashi, suna da famfo a tsakar gidan wanda ba sai anje ibo ruwa daga waje ba. Dai-dai Mami ta fito daga kitchen kenan su Amal suke k'arisowa tsakar gidan da Afzal riqe da ita, ai ba shiri tayi baya ta b'oye kanta cikin kitchen d'in tana me leqensu ta window. Salati kawai ta shiga yi ganin yadda mutumin dake sanye da suits ya riqo mata 'ya a cewarta gabad'aya wani masifa Amal taje ta kwaso musu sanin sharpness na bakin 'yar nata kaman razor. Tun farko dama bata goyi bayan zuwa aiken nan ba don de ba yadda ta iya ne Amal tafi k'arfinta gashi Papi (kakan Amal) da take d'an jin maganansa ma bai gida balle ya mata. Yau ina zata sa kanta Amal ta ibo musu abinda yafi k'arfinsu. Tunani kala-kala ba wanda ba tayi ba. Tunda suka shigo Afzal ke bin gidan da kallo, tabbas talakawa ne amman hakan be maida su k'azamai ba. Ko leather d'aya  be gani a k'asa ba ko ina an share tsaf ga kuma k'amshin turaren wutan dake tashi. Suna k'arisowa dai-dai tsakar gidan suka tsaya, se anan ya saketa tare da jan baya kad'an hakan ya bawa Amal daman sauk'e nauyayyiyar ajiyar zuciya. 


   "Ina Mamin naki?" Ya tambayeta ai take zuciyan Mami yawani har6a shikenan nata ya k'are yau ga Papi bayi nan yayi tafiya. 


   "Dake fa nake" Afzal ya kuma fad'i jin bata bashi amsa ba. Tsaida kewaye-kewayen da takeyi don neman Mami tayi tana me dawo da kallonta a garesa "Gani nayi tare muka shigo gidan taya kake tsammanin zan san inda take?" Ta tambayesa cike da rashin kunya. Cike da d'ambun mamaki Afzal ya tsaya yana kallonta shin wannan wacce irin fitsararriyar yarinya ce? Ace ko kunyan idonsa batayi ta rage wani abun? Sai dai ya daina mamakin hakan tuna 'yan qauye da masifaffen rashin kunya ga kuma shaidan dayayi mata na 'yar gudun hijira, tama daina basa mamakin. On the other side kuwa cikin Mami ya gama d'iban ruwa ji take kaman ta cafko Amal ta nad'a mata na jaki upon all the trouble data janyo masu still tana da bakin yima wannan security (as yadda ta ma Afzal shaida ganin sa sanye da suits) rashin kunya? Lallai kuwa tayi hak'uri ta rufa musu asiri. 


   "Mami!" Amal ta k'walla wa mahaifiyar nata kira, shiru kukeji ba amsa. "Mami don Allah ki fito daga b'uyan nan ni bance miki bala'i na kawo ba wannan mutumin gefe nan ne yazo baki hak'uri ya kad'e miki 'ya" ta sanar a fili. Se anan Mami tad'an ji sukuni but even still ta kasa fitowa gani take kamar k'arya Amal keyi saboda sau dayawa takan yi mata hakan, ta d'ibo bala'i daga waje  sannan ta fake tazo tace alkhairi ta kawo. 


    "Mami wallahi zan k'ariso in janyo ki daga kitchen d'innan" tafad'a tana kallon setin windon da Mami ke leqe daga gun ai tuni ta miyar da fuskarta ciki, ashe de Amal ta ganta. Numfasa tayi sannan ta fito alokacin kuwa Afzal ji yake idan be saki wannan dariyan daya k'eto mar ba ze iya mutuwa. Wannan wacce erin matsoraciyar uwa ce? Ai kam dole Amal tayi rashin kunya haka daga ganin mahaifiyar natan batayi kalan me tsiwa ba bale har ace zatayi discipline Amal. 


   Da k'yar d'in k'yar ya samu ya maida dariyan ciki ahaka ma seda yayi kad'an a waje wanda a sanadin haka Amal ta juya ta galla mai harara sede be ganta ba dake hankalinsa gabad'aya ya duk'ufa akan Mami yana mey mamakin yadda akayi basu kama sekace ba mahaifiyarta ba. Ashe bashi kad'ai ne bayi kama da Umminsa ba (mahaifiyar shi.)


  "Sannu da zuwa bawan Allah" Mami ta fad'a tana nufo su cike da tsoro da fargaba. 


   "Yauwa Mami" Afzal ya amsa. "Ina yini?" Ya gaisheta cike da ladabi had'e da durk'usawa kad'an. Ai gaisuwan da Mami bata amsa ba kenan ta shiga basa hak'uri. 


  "Don Allah idan wani abun Baby tayi ma kayi hak'uri bawan Allah wallahi banida abun da zan iya baka banda hak'uri" tace ba alaman kwanciyan hankali a tattare da ita. Ido Amal ta juya cike da takaicin abinda Mami keyi gaban wannan maras mutuncin bawan Allah'n, taya zata tsaya tana basa hak'uri while shi ya kamata yayi hakan?


   Afzal ya bud'e baki zeyi magana kenan Amal ta riga sa "Wai ni Mami yaushe nace miki nayi mar laifi? Dubi fa, dubi k'afa nafa" tayi maganan tana miqar da k'afanta a hankula so Mami could see "Karya min k'afa yayi."


    "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un Baby!" Mami tayi exclaiming tare da yin kan 'yar nata tana me zaunar da ita a hankali bisa wani benchin dake kusa tana mata sannu in the process. 


   "Look Mami ni ban karya wa 'yarki k'afa ba don't listen to her" Cewar Afzal. 


   "Wallahi ya karya" Amal tayi saurin fad'i tana katse Mami "Idan ba karya min k'afa yayi ba toh seya fad'i dalilin daya sa ban iya taka k'afan."


   "Yi shiru Baby na sannu ai ko baki fad'a ba gashi kumburin k'afarki ta nuna kin karye saidai kariya nawa ne?"


   "Kaman biyu ne inji likitan" ta fad'a bayan tasan sarai k'arya take. Se wani zum6uro baki take cike da shagwa6a a yayinda Mami ke ta mata sannu tana shafa k'afan a hankali. 

   Shi de Afzal ya rasa nayi, ya rasa menene yayi yau Allah ya had'a sa da dramatic people kallan wad'annan, ace ba babba ba yaro? Hmm shide gado ba gwaninta ba. Da kalan uwa me d'aura wa k'arya gindi haka ai ko hannu Amal ta d'aga ta zagi mutum a kan layi baza'a ga laifin ta ba tunda gashi ba tare da bincike ba mahaifiyar nata ta hau ta zauna akan k'aryan da 'yar nata ta shirya na cewa an karya mata k'afa. 


   "Sannu ko Baby bari Papinki ya dawo a yanka miki d'aya daga cikin kajin kiwon nan. A kariya biyun har kika iya kike taka k'afan? Sannu." Har anan bata yi ta kan Afzal dake tsaye duk mamaki yabi ya mamayesa ba. 


   "Mami?" Ya kirata ganin wannan draman nasu bana k'arewa bane gashi kuma yana da k'arancin lokaci. 


   "Tsaya tukuna bawan Allah in gama da 'yar tawa ita kad'ai Allah ya bani-"


  "Mami!" ya katse ta cike da rashin hak'uri, shi kansa besan lokacinda ya fusata har ya kira ta da tsiwa haka ba. Da mamaki both Mami da Amal suka juyo suna kallonsa, a yayinda zuciyan Amal ke raya mata itama ta miyar masa da masifan. 


   "Kinga na farko ni ban karya wa 'yarki k'afa ba I admit I wasn't watching the road attentively na gauce akan hannuna na yo kanta na kuma bugeta and am dearly sorry" ya fayyace mata. "Amman ban karya mata k'afa ba" ya k'arisa. 


  "Baka karya mata k'afa bafa kace? Ban gane ba, yo ko nufi kake kawai don ado likitan ya d'aure mata k'afar da bandeji?" Ta tambaya cike da mamaki tana kallon kumburarren k'afan Amal tare da kewayo da kallonta a gareshi, ba shakka akwai rainin hankali anan. 


   "Ni ba abinda nake nufi ba kenan amman de kam ban karya wa 'yarki k'afa ba, targad'e ne ta samu tun achan kuma Dr'n ya sanar da ita hakan bansan dalilin da yasa tace miki kariya ne ba."


  "Hakane Baby?" Ta tambaya tana maido da kallonta akan Amal dake faman raba ido. 


   "Mami har sekin tambayeta ne? Da girma na ne zan tsaya ina miki wasa da hankali? Kuma idan da har banida niyyan admitting laifin da nayi do you think zan bar duk abinda nakeyi in nemi har gidanku domin in baku hak'uri akan hak'urin dana ba ita Amal d'in? Har kuma in kaita asibiti, think please" Daga yadda yake magana za a san ransa ya soma 6aci kuma bako k'arya acikin duk abinda ya fad'a. 


  "Hak'uri? Ni de baka ban hak'uri ba" cewar Amal tana murgud'a baki. "Allah ya karya min k'afa kar ki jisa Mami."


  "Baby kallen shin bawan Allahn nan karya miki k'afa yayi ko kuwa targad'en ce kamar yadda ya fad'i?"


   Ganin fa an ganota ta soma kame-kame "Toh ni ina zan sani ko had'a baki sukayi da likitan don ya rufa mai asiri-" bugi Mami ta kai mata a cinya interrupting her, wanda a sanadin hakan ta sa ihu. 


   "Yanzu haka kawai kima bawan Allah sharri ya karya miki k'afa Baby? Shin yaushe zakiyi hankali?" Baki ta zumb'uro tana kukan munafirci a yayinda Mami ta juyo kan Afzal da yayi jugum yana kallon ikon Allah. 


   "Bawan Allah don Allah kayi hak'uri wallahi haka take gagara da rashin ji toh wane akanta akayi wahayinsa."


   "Ba sekin fad'a ba naga hakan a tattare da ita" ya fad'a yana meyi wa Amal kallon rainin hankalin dayasa ta murgud'a mai baki. "So am here to say sorry and take full responsibility" ya numfasa "Ga magunanta nan" anan ya miqa wa Mami leathern inda ta amsa "Dr yace karku tada hankalinku she's going to be alright kuma gobe idan Allah ya kaimu zan dawo in maida ta asibitin don a sake dressing ankle natan kaman yadda likitan ya buk'ata. Za a cigaba da yin hakan na sati daga nan in shaa Allah k'afan zai warware." Kafin Mami da akayi ma bayani tayi magana Amal ta hau k'orafi. 


   "Ni wallahi ban komawa asibitin" ta fad'a tana buga d'ayan k'afanta a k'asa stubbornly. 


  "Rufa min baki do Allah!" Mami ta ce da ita amman still se gunguni takeyi dake sam bata tsoron idon Mami. "Allah sarki bawan Allah lallai ka cika d'an halas mun kuma gode sosai, ina me sake baka hak'uri kuma."


   "Ba komai Mami ya wuce nine da godiya."


   "Allah yima albarka Babana."


   "Ameen" ya amsa da murmushi kad'an. 


   "Nace ba kar ka damu ba seka kuma dawowa bama anan tsallake gun wanzami zan kaita a sake duba k'afan nata gobe in shaa Allahu."


   "No Mami, I promised to take full responsibility so karki damu and here" ya fad'a yana ajiye ledojon a k'asa "Sakamakon hatsarin abubuwan da kika aiketa siya suka tarwatse so gasu I'm able to get some wad'anda ban samu ba kuma zan baku kud'in seku siya in kuka samu lokaci, I'm sorry" hannu ya zira a aljihun sa don ciro wallet nasa inda yaji wayam holy sh*t ashe ya baro sa acikin mota. "Excuse me please let me get my wallet."


    "Haba bawan Allah ai da ka bari, hakan ma mun gode wallahi ni na yafe sauran" fad'in Mami. 


  "Ni ban yafe ba" cewar Amal wane da ita aka kasa, ko ta kanta Afzal beyi ba yayi saurin katse Mami dake shirin yima Amal fad'a "No Mami please I insist, ai hak'k'in kune." 


   "Toh shikenan tunda kace haka mun gode" ta fad'a tare da kewayo da kallonta akan Amal "Ke tashi ki bi bayansa ba seya sake shigowa nan inba yayi sahu biyu tunda duk ke kika jawo komi" cewar Mami. 


   "Taya ni na jawo? Ni na kaisa kad'eni?" Ta tambaya cike da rashin kunya. 


   "Da bance kibar aiken ba se da yamma kika k'i?" Zata kuma magana Mami tayi yunk'urin gwa6e bakinta nan take tayi shiru. Afzal da yayi shiru yana kallon su ne ya nisanta yace, "Karki damu Mami, let her be."


   "A'a don Allah kar muyi haka da kai. "


  "Mami-"


   "Don Allah fa nace" hakan yasa yayi shiru. 


  "Toh shikenan" ya fad'a a hankali. 


  "Yauwa bari Baby ta bika seta amso kud'in tashi mana Baby" ta fad'a tana dawo da kallonta akan Baby dake faman zumbure-zumbure ko yunk'urin miqewa batayi ba. "Ko baki ji ni bane?"


   "Toh ai bazan iya tashi ba."


  "Uhn uhn fa Baby kin san ni."


  "Don kinga Papi bai nan ba? Allah ze dawo dashi kuma wallahi sena k'irga mai komi" ba don tana so ba ta shiga miqewa wanda k'arshe saida Mami ta taimaka mata, k'ingishi ta shigayi tana takawa a hankali. Murmushi Afzal yayi sannan ya shiga bin bayanta. 


  "Toh gashi bawan Allah zaka tafi ban san sunanka ba." Kewayo wa yayi cike da ladabi sannan yace "Afzal."


  "Afzal" ta nanata "Sunan larabawa ga me k'iran su, masha Allah" ta fad'a acikin wasa. Murmusawa yayi sannan yayi mata sallama ya fice alokacin har Amal ta isa bakin k'ofa tana tsaye tana kallon yaran dake wasa akan layi. 

   "Excuse me" yace da ita ganin tayi tsaye bakin k'ofan ba chance da ze wuce. Seda tayi muttering wasu kalamu chan k'asa iya jinta sannan taja gefe ya samu ya wuce. Bayan sa ta shiga bi sannan ta tsaya daga jikin wani bango a yayinda ya k'arisa gun motan nasa. Wallet d'in ya d'auko, dai-dai yazo bud'ewa kenan don sallamarta wayarsa dake inner aljihun suits jacket nasa ya shiga ringing. Ba tare da 6ata lokaci ba ya zaro, ganin Abba ke kira zuciyansa ya mugun har6awa yau ya shiga uku. Cike da fargaba ya d'aga sede kafin ya samu daman magana Abba ya riga sa. 


   "Yanzu Afzal in kiraka sau biyu in ce maka ina neman ka as a matter of urgency shine har yanzu ban ganka ba? Ai ko bangon duniya kake yaci ace ka dawo war haka" daga yadda yake magana mutum zaisan ransa ya 6aci matuk'a ba shakka Abban nan nashi mutum ne mai gajan hak'uri. 


   "Abba I'm so sorry-" katse sa Abba ya kuma yi  "Wallahi ban san ka da halin nan ba, bansan kuma meyasa kake hakan ba amman karka damu ba seka zo d'inba domin shi wanda yake neman ma maganan ma ya gaji da jiran ka ya tafi" daga fad'in haka ya katse wayan ba tare da ya basa daman magana ba. Hankalin Afzal ya mugun tashi, rabon shi da ya 6atawa Abba rai irin na yau ya juma, probably tunda yake yaro lokacin da bai gama gano darajan iyaye ba. Yau ina zaisa kansa? A kullum shi me ladabi ne game da umarnin Abba, a kullum Abba na alfahari dashi se gashi yau all because of wannan fitsararriya 'yar gudun hijirar ya 6atawa Abbansa rai to the extent da har Abba ya kashe waya a kansa abinda be ta6a yi ba. Yasani kafin Abba ya sauk'o ya soma mishi magana kuma se ranan da Allah ya nufa. 


   Ranshi a murtuk'e ya bud'e wallet d'in be ma san iya adadin kud'in daya d'iba ba tsabaragen all he wanted at that moment was yaga kansa a gida ya samu daman bawa Abba hak'uri tun kafin lokaci ya k'ure. 


  "Ke!" Ya daka mata tsawa wanda sanadin haka ta firgita. Tun da tasan kanta bayan wani PHE teacher'n su tun a JSS 3 ba wanda ya ta6a mata tsawa yakuma razana ta irin na yau. "Kinyi tsaye achan nine zan k'ariso miki da kud'in?" Ya jefa mata tambayar cike da tsiwa. 


    "Malam dakata fa!" ta tsorata iya tsoro amman dogon bakinta baze barta tayi shiru ba "Haka kawai bazaka sauk'e min haushin da kakeji a ka ba, a dalilin meh? Don wani ya kiraka ya 6ata maka rai se ka hau huce zafin ka a kaina kana min masifa? Da ni nace ka kad'eni kokuwa ni nace ka kawo ni gida? Ra'ayin da ya saka yin all of that shi zai sa ka tako har nan ka bani kud'in da kace zaka baiwa Mami in kai mata" ta fad'a kai a tsaye ko tsoron yadda yake kallonta cike da haushi da tsana batayi. Duban time a wrist watch dake d'aure a hannunsa yayi ganin he is running out of time yasa shi fasa aikata abinda yayi niyyan mata in ba haka ba belt nasa yayi niyyan zara ya nad'a mata na jaki a gurin tunda a gidansu ba meyi mata hakan. K'arisawa spot da take tsayen yayi sede yarinyan naku ko motsawa batayi ba dukda chan k'asan zuciyarta kuwa ta gama tsorata. A duk tunaninta mari ze kai mata setaji ya damqo hannunta, damqan da tana iya rantsewa ba a ta6a mata irin sa ba ai bata san lokacin da ta shiga ihu ba. Ji tayi k'asusuwan ta suna k'ara, wannan wani irin k'arfi yake da shi? Toh ita kam ya agaza ya rufa mata asiri kafin ya karya mata d'an hannu, ace ga kariya ga targad'e? Bazata iya ba. 


   "Naga alaman Allah ya had'aki da iyaye masu sanyin da ko tsawata miki basu iya yi as ko mey kikayi dai-dai ne a idansu kisani I'll not let you disrespect me and get away with it, bazan bar k'aramar k'waron da bata kai inyi immediate sibling da ita ba ta raina ni, ko ki iya bakinki ko na koya miki yin hakan, maras kunya kawai."


 Sosai idonta ya cika da k'walla don azaba, "Ni ka sake min hannu kuma kar ka sake sa min sunan iyaye cikin zancenka, musamman na Abba na saboda ya rasu" ta fad'a cike da k'arfin hali. Ganin fa baida niyyan sake ta tasa ihu "Mami!" A lokacin har hawayen na neman gangarowa. Se anan ya saketa cike da wulak'anci regardless of her condition, wanda da ace ba bango a kusa da ita data fad'i a k'asa. Hannunta yaja out of nowhere tare da tusa mata kud'in aciki sannan ya juya ya kama tafiya. Kafin ya isa gun mota har Amal ta zaro kud'in ta k'irga, dubu hud'u ta gani "Hey!" Ta danna mai kira amman yayi banza da ita se a karo na biyu, nan ma ba juyawa yayi ba tsayuwa kawai yayi, "Ce ma akayi Papi na ya rasa na ciyar damu ne ko na sha da zaka wani kama ka bada dubu hud'u na abinda be taka kara ya karya ba?" Se anan ya juyo yana kallonta ashe de dubu hud'u ya zara "Zan d'au dubu d'aya, ban sani ba ko canji ze rage amman idan har ya kasance hakan, I'll return your change for you ga sauran kud'in ka" nan ta zare dubu daga ciki tare da yin watsi da sauran a k'asa ta juya da k'ingishinta ta wuce layin gidansu leaving Afzal da baki wangalau a bud'e cike da mamaki, don shock k'wak'walwarsa tama kasa fahimtar dashi abinda wannan 'yar gudun hijirar ta masa. Ji yake as if ya cafko ta ya nad'a mata na jaki shin wannan ya iyayenta suka girmar da ita? Fitsara sekace 6era, besan na gida ba balle bak'o. Lallai ta guji had'uwansu, yanzu baiwa Abba hak'uri ne ke gabansa dako seta gommaci kid'a da karatu. 





*~*~*~*~*~*~*~*~*~*

    So how was the chapter? One word for Amal?😂

  In shaa Allahu bayan sallan azumi kuma semu d'aura daga inda muka tsaya. Na sako pages biyun nan ne domin mutane irinsu Meela da Sumayyah masu shegen maita da tak'uri 😜 se kuma don wasu fans d'ina da suka d'au cewa na daina rubutun hausa gabad'aya. Wishing you all a faithful Ramadan ahead xoxo. 


    RANA D'AYA  

  #RD

   Love... miemiebee👄✨

[12/08, 22:25] ‪+234 907 483 8352‬: 🎀🎀🎀                 🎀🎀🎀

                🎀❣🎀

                   ❣❣


  💦💦                      🍃🍃🍃          

           *RANA D'AYA!*

  💦💦                      🍃🍃🍃

    

     _Written by Miemiebee👄_



   *PAGE 0⃣3⃣*



   

_How can I turn you guys down when the love and devotion speaks this much??😩😍 Yanzu haka kuka k'i yarda a cigaba da posting RANA D'AYA after Ramadan😩 kaman maita harda masu cewa koda sau d'aya a sati ne 😂 nida mutane na se Allah but know that ina alfahari daku sosai sosai wallahi💖. Though my schedule is tight, I'll still manage and squeeze time to type once in a week like you guys requested before Ramadan approaches, so here is chapter three. Juma'ah zuwa juma'ah zakuna samun post in shaa Allah, happy reading!❤_




     Ta kai ga yankan lungun gidansu kenan sega Mami tafito sanye da mayafi "Ina zaki Mami?" Tayi saurin tambaya "Maggi zan siyo nan shagon Usmanu ashe ya k'are ban sani ba gashi har miya ya kusa nuna. Kiyi sauri kije ki kula min dashi dama na rage ichen seki k'ara" Mami ta sanar da ita. 


    "Toh Mami ki dawo lafiya" ta amsata, da k'ingishinta ta shiga takawa amman ta tsaya chak sanadin kiran da Mami tayi mata, hakan yasata kewayowa "Na'am?" Ta amsa. 


  "Nace nawa Afzal ya baki ne?" Nan fa oganniyan taku ta shiga kame-kame tana ta6e baki. "Ya haka? Tambaya fa nike miki, nawa ya baki?"


  "Dubu d'aya" ta fad'a chan k'asa-k'asa. 


  "Har dubu? Mu gani" ta buk'aceta, nan Amal ta d'ago ta nuna mata. "Yo shine kika tsaya kina rarraba ido kaman 6eran da aka kama yana sata?"


  "Uhnmmm ni zan wuce kar miyan ya k'one" ta fad'a tana dodging had'a ido da Mami tasan tabbas idan suka cigaba da had'a ido Mami na iya gano k'arya take, bata kai ga taka k'afanta ba Mami ta kira sunanta "Baby!" Chak ta tsaya zuciyar ta na har6awa. 

   "Na'am?"

  "Juyo ki kallen" saidai ta kasa, seda ta d'au tsawon lokaci sannan ta juyon. "Fad'a min me kikayi? Tabbas babu gaskia a tattare da ke fad'i me kikayi."


  "Mami me kuwa zanyi? Ni shikenan kullum kina cikin zargi na" ta zum6uro baki. 


   "Munafuka bazaki bar k'arerayin nan naki da kike tasowa dasu ba ko? Nace fad'a min me kikayi wallahi idan kika bari har Afzal yazo gobe na tambayesa naji gaskiya daga bakinsa jikinki zai gaya miki."


  "Wai duka na zakiyi? Ai Papi baze bar ki ba" da sauri ta buge bakinta tuna Papi bayi gida yayi tafiya. 


  "Sam bazan dake kiba amman inada wanda ze daka min ke kaman ganga, Malam Bunu na islamiyyan ku zan kai mai k'arar ki nacewa har yanzu baki daina k'aryan banzan nan ba."


  "A'a don Allah Mami kiyi hak'uri wallahi dorinan shi me baki uku ne na tuba."


   "Yauwa fad'an me kikayi toh."


  "Ki rantse baza kimin komi ba."


  "Sa'ar kice ni? Zaki gayan ne kokuwa?"


 "Mami dan Allah kiyi hak'uri."


  "D'aya" Mami ta shiga k'irge "Biyu-"


   "Zan fad'a zan fad'a" Amal ta katseta a rikice. "Dubu hud'u ya bada shine na miyar masa da sauran saboda kudin abubuwan da suka rage basu kai hakan ba."


   "Oh! Amman 'yar nan anyi wawiya wallahi shi daya k'irga kud'in ya baki besan me yakeyi bane kome? Ai da niyyan kyautatawa ya bada."


   "Toh-" ta fara magana. 


  "Rufa min baki da Allah!" Mami ta katseta cike da takaici "Yanzu fisabilillahi Allah ya kawo mana arziki har gida ki miyar da hannun kyauta baya Baby? Meye muke dashi da zaki miyar masa da d'umbun kud'i haka iyye?" Don takaici Mami ji take kaman ta mauje ta, tana gwada yunk'urin hakan kuwa Amal tasa ihu gashi ba halin gudu k'afarta baze barta ba, dan tausayi de kawai Mami ta barta. "Shin ya amshi kud'in yanzu?"


  "Eh mana tun yaushe ma."


  "K'arya kike nace k'arya kike. Fa bazan haifeki ki tsaya kina raina min hankali ba nace ya amshi kud'in da kika miyar masa ko ya?"


  "Ya kar6a..." hannu Mami ta d'aga kaman zata doketa "Nace ya kar6a ko be kar6a ba?" Zata kuma wani k'aryan Mami tayi kaman zata sauk'e mata mari, tuni ta shiga bada asalin rahoton "Wallahi be kar6a ba k'arya nakeyi."


   "Nasan za ayi hakan ai, ki kiyaye nifa Baby! Ki kiyayeni ina fad'a miki wallahi ranan da nace zan tarke ki a lungu bazaki ji dadi ba. Yanzu ina kud'in tunda kince be amsa ba?"


   Chan k'asa-k'asa tana me zum6uro baki tace "Na yasar mai a k'asa da yak'i kar6a."


  "Kud'in kika yasar?!" Tas kukejin sauqan mari a bayan Amal daya sata sakan wani irin rikicaccen ihu bawai don marin yayi zafin da zaisa ta yin kalan ihun bane sai don shagwa6a irin nata. "Amman yau na tabbata kina da ciwon hauka maza wuce muje ki ibo kud'in kuma Allah yasa muje har 'yan tsince-tsince sun d'auke kiga abinda zan gwada miki a gidan nan yau, dama gashi Papin ki bayi nan balle ya shiga miki." Kukan munafurci kaman yadda ta saba ta shiga yi tana me maquro d'an k'wallan daya ciko mata a ido. Haka Mami ta sata gaba da k'ingishin nata suka k'arisa dai-dai spot d'inda abin ya faru wanda a dai-dai lokacin wasu almajirai suke k'ok'arin d'iban kud'in wani ihu Mami tasa "Karku ta6a zaku 6ace" ai kafin tace pim ta nemi yaran ta rasa tasan sarai idan ba hakan tace ba kwashe kud'in zasuyi su gudu su barta da innalillahi. Da sauri taje ta tattara dubu ukun cus ta k'irga, wani hamdala ta saki sannan ta amshe na hannun Amal dake faman murza idonta tun d'azun. "Maza wuce gida kuma Allah yasa miyan ya k'one kiga abinda zan miki."


  "Toh ni Allah ne da zan hana miyan k'onewa?" Ta tambaya tana zum6uro baki. 


  "Zan buge bakin nan fah" da sauri ta sa hannu ta toshe bakin nata kafin hannun Mami yayi landing a kai "Maras kunya kawai wuce gida saura kuma ki tsaya hira da Azee a hanya kiga abinda zan gwada miki mutum se shegen almubazaranci." Tana kaiwa nan ta yanki kwanan shagon Usama, itama Amal a hankali ta shiga takawa da k'ingishin har ta isa gida. 


   Saidai wani hanzari ba gudu ba, takai gab da shiga ciki kenan sega k'awarta Azee wacce Mami ta ja mata kunne akanta, se ince kusan rashin jinsu d'aya saidai kawai ita Azee a gaban Babanta take hakan yasa tafi Amal jin tsoron ido da bakin mutum unlike Amal. 


  "K'awas ya na ganki da bandeji waine a k'afa?" Tayi saurin tambaya tana doso ta, idonta na akan k'afan Amal. 


   "Hmm kede K'awa bari kawai wani reckless bawan Allah yau Allah ya had'ani dashi, ina zaman zama na yayo kaina da mota ya bigeni."


  "Subhanallah shine baki sanar dani ba? Sannu ya k'afan toh?" Nan suka hau hira Amal ko gabad'aya ta mance da miyan da Mami tace ta kula dashi. 




****       *****        ******       *******


   Isan Afzal gida keda wuya as tun da ya hau tuk'in yake tunanin abinda Amal tayi masa, tafasa ransa yake sosai tabbas baze bari ta gudu unpunished for what she did ba, komin ji da dad'ewa seya rama. She wants to play games? Then she got it. Yana isa gaban wata makekiyar gida da bature ke kira da mansion ya yanki corner inda ya tsaya dai-dai gaban fancy iron gate d'in. Securities biyu ne masu uniform tsaye a bakin k'ofan suna gadi, sannu da zuwa suka mar sannan suka bud'e gate d'in. Tafiya kad'an yayi ya kuma cin karo da wani iron gate d'in nan ma securities biyu ke guarding wajen bayan sun mar sannu da zuwa suka bud'e masa giving him a safe passage. Tafiya yake through the driveway a hankali exploring the beauty of the mansion. A sannu a sannu ya k'arisa last parking lot meh glassy display sannan yasa motarsa ciki ya yi parking ya fito. Makekiyar flat da me bada labari bata san daga ina zata soma labarta saba Afzal ya wuce ciki. Sashin fari ya shiga wanda ko ba a sanar da mutum ba zai san na mai gidan ne wato Abbansa. Knocking yayi bisa entrance door d'in sannan ya bud'e tare da sa kai. Makekiyar parlour ne da aka k'ayatasa da abubuwa masu tsada masu d'aukan hankalin d'an Adam. Komi aciki white, golden and red ne banda cinema'n dake manne jikin bango, ga ko ina tsaf ko dust baka gani illa k'amshin turaren wutan dake tashi.  


   "Sannu da zuwa Prince" wani na miji dake sanye da uniform ya fad'a yana doso Afzal da yayi zaune bisa one of the various golden X red royal chairs. 


   "Thank you Abba na gida?" Ya tambayesa. 


  "Eh yana d'akinsa" ya basa amsa a takaice. 


  "Good, help me speak with him please."


  "Yes sir" ya amsa. Da fad'an haka ya juya ya shiga ciki ta wani k'ofa, yakai tsawon minti biyu sannan ya dawo. "I'm sorry amma kaman Master bai da shirin ganinka" mutumin ya sanar dashi. Dama Afzal yasan za'ayi hakan ba kowa yake blaming ba illa Amal ji yake kaman idan ya kamata karya saketa se ta daina numfashi, 'yar gudun hijira kawai ya furta a ransa. "Please tell him I'm sorry yayi hak'uri ya fito" ya fad'a da damuwa karara bayyane a fuskansa. 


  "I did amman baida niyyan fitowan ne, yak'i nakega idan Hajiya tamar magana zai sauk'o, I'm sorry excuse me" daga fad'in haka yayi kan dining table inda ya cigaba da goge-gogen da yakeyi. Ganin fa zaman da yakeyi a gun baze haifar masa da komi ba ya miqe ya fita. Side na Ummi ya nufa direct don neman taimakonta. Kaman kullum seda ya ciro hanky daga aljihunsa ya toshe hancinsa sannan ya k'arisa ciki. Ko bai tambaya ba yasan yau ma da akwai hayak'in kullum d'innan, anayin abu dai-dai amman ita Ummi idan batayi over ba bata jin dad'i. Site nata kullum yana cikin hayak'i da k'amshin turaren wuta. Had'add'en parlourn ta daya k'unshi combination na white, dark and light purple ya wuce making it to her room. Knocking yayi bayan ta amsa da 'yes' ya bud'e ya shiga, miqe akan gado da zani d'aure a k'irjinta ya tarar da ita tayi ruf da ciki a yayinda 'yan mata biyu ke mata tausa, hayaqin d'akin is indescribable ba shakka yau d'inma gyaran jiki ake mata. Shi yarasa amfanin wannan abu, shin ta gyara jikin nata takai ina? Abba deh ba saurayi bane yanzu haka zalika itama ba budurwa bace. Murmushi kad'an ya saki tuna reaction nata anytime idan yace mata ita ba yarinya bace yanzu ta tsufa. Shi de ya rasa ta ina ta zama yarinya, mutumin da ya kusan approaching 50 kam ai ya manyanta. "Waye ne?" Ta tambaya kasancewar kanta na facing opposite direction na k'ofar. Kafin Afzal ya amsa 'yan mata biyun suka rigasa "Prince ne."


  "Oyoyo My Prince" ta fad'a tana k'ok'arin zama a yayinda 'yan mata biyun dake kanta suka ja gefe "Sannu da dawowa Prince" kai kawai ya musu nodding. 


  "Toh kuma kayi tsaye gun ka k'ariso ciki mana" Ummi ta fad'a tana janyo mayafi tare da lullu6e jikinta. Kyakkyawar mace ce me uban kyawun jiki wanda idan ba wai an fad'i shekarunta bane mutum baze ta6a sanin takai hamsin ba kaman yadda Afzal ya fad'a. Irin skin nata ake kira da kalan wankan tarwad'a gashi kuwa daya samu gyara se wani glowing yake like gold, ga k'iban nan tubarkallah nama du sun nannad'u a wuya. Kallo d'ai za ayi mata asan matar alhaji ce. 


   Tana da kyau sosai haka Afzal ma amman abun mamaki sam mutum baze ce mahaifiyar sa ceba saboda rashin kaman su, sam kyawunsu be zo d'aya ba. Afzal yafita haske sosai wasu sukan ce mar fari ma, ita kuwa tafi sa dala-dalan idanu da kuma dogon hanci. Hancinsa na nan shiba dogo ba shiba gajere ba gashi nan de k'arami acikin oval shaped face nasa. 


     Da hannunsa yayi mata nuni cewa hayak'in d'akin is unconducive ya mar yawa. 


  "Kai deh da ace kanada asthma da turaren wutan gabad'aya zaka hanamu yi a gidan nan toh ya akayi?"


  "Ummi please mana! I want to talk to you" ya fad'a tare da had'e giransa, hancinsa kuwa har a yanzun na toshe da handkerchief. 


  "Toh ya kakeson inyi? Bawai kaman ina da k'arfin koran hayak'in nan a lokaci guda bane."


  "Toh kizo muje parlour concentration d'in is less a chan."


  "Halan baka ka gyaran jiki ake yimin ba."


  "Fisabilillahi kullum gyaran jiki, gyaran jiki ko amarya albarka" har anan be sauk'e hanky'n daya toshe hancinsa dashi ba. 


  "Jimin d'a!" Tayi exclaiming full of wonder. "Da meye ce inba amaryar ba? Naga da gyaran jikin ne na iya na karkato da hankalin Abbanka kaga har yau bemun kishiya ba."


  "Toh whatever ni ki fito muyi magana."


  "Wai me ne da bazaka iya fad'ansa daga bakin k'ofar ba? Aure zakayi? Kuma ka bar min k'ofa a bud'e tun d'azu ko bakasan hayak'in fita yake ba?"


  "Exactly ki fito muje parlour" ganin batada niyyan motsawa yace da 'yan matan suyi excusing nasu ba gardama suka fita suka basu waje, ita de Ummi binsa da kallo kawai take ko mey yake da shirin yi? K'arisowa cikin d'akin yayi da dogayen k'afafunsa tare da tsayuwa dab a gabanta sannan ya shiga janta. "Ummi dan Allah ki tashi kin de san kina da nauyi."


  "God help me" ta fad'a sannan ta miqe suka fito parlourn inda suka zauna akan two seater side-to-side. "What is it?" Ta tambayesa. 


  "It's Abba he's mad at me" ya fad'a a takaice. 


   "Toh kuma har wani sabon abu ne wannan? Kade san Abbanka da zafin fushi da zuciya sekace kai anan."


  "Ummi please!" Ya fad'a tare da buga k'afansa a k'asa.  


  "Okay, okay toh meh dalilin?" Labarin duk abinda ya faru ya bata be bar komi ba. Numfasa tayi bayan da ta gama sauraronsa tace, "Toh Allah kiyaye aukuwan na gaba amman meyasa ba ka sanar dashi abinda ya farun ba?"


   "Yak'i ma ya saurareni kashe wayan yayi gabad'aya kuma yanzu ma daga site nasa nake, nasa Micheal ya mar magana still yak'i fitowa."


  "Toh ni yanzu me kakeso in maka?"


  "Like what a question" ya fad'a tare da juya idanunsa da suke nan farare k'al. "Kiyi mishi magana of course, he always listens to you."


   "Nifa banason kana jawo ni cikin matsalarku haka kawai kazo kasa nima yak'i cin abincina na sati."


  "Ummi please kinsan Abba be iya yin fushi da mutum ba yanzu ba k'aramin aikin sa neba ya daina min magana for a whole week!"


   "Toh ai nima abinda nake gudu kenan kar yabar cin abincina na sati."


   "Toh yau aka fara hakan ne?" Ma ta 6ata mar rai. Ai da k'yar idan Abba ya ta6a jera watanni biyu yana cin abincin Ummi ba tare da yayi fushi ba. Haka yake da an 6ata mar rai seya d'aga k'afa wa mutum, abun takaicin kuwa shine se ya nemi abinda zai fi damun mutum sannan yayi using nasa against that person. Se kuma shi gado ba gwaninta ba, shima Afzal haka yake da shegen zuciya da fushin nan irin na Abbansa ko fad'a sukayi da Ummi seya d'aga k'afa daga cin abincinta da kuma yi mata magana in banda gaisuwa ba abinda ke had'asu har se ya sauqo, shima gaisuwan don ya zamo masa dole ne. Abinda ke bawa Ummi mamaki shine bayan shi kansa Afzal d'in ya iya ma mutane fushi meye a ciki don Abbansa yayi masa? 


   "Aww abinda zaka ce kenan? Ashe dai ba dad'i, ashe idan aka maka haka bazaka ji dad'i ba amman kake ma mutane, ai halin Abban naka da kai seku ta fama kaga barin je in k'arisa gyaran jikin nan yau Abbanka yace zamu fita date kaga ko zama be kama ni ba."


 "Ummi please talk to him ni wallahi abinda yasa hankalina ya tashi ma saboda yace akwai abinda yake son sanar dani ne kuma daga yadda yake maganar nasan magana ce me muhimmanci."


  "Oh! Dam-" se kuma tayi shiru tuna yadda Abba ya jaddada mata cewa no matter what kan kar ta kuskura ta sanar da Afzal halin da ake ciki yafi son ya mar maganan da kansa. 


  "Dama meh?" Yayi saurin tambayarta. 


  "Babu bance komai ba bari in shiga daga ciki." Kafin ta kai ga miqewa Afzal ya rik'o hannunta restricting her. "Ya haka Prince?"


  "Ummi there is something you're not telling me" ya fad'a yana mata kallon cikin ido don tabbatar da abinda ya fad'a.  


  "Kai de da assumption se a hankali ni nace wani abu ne? Sakeni du Allah."


  "Ummi please tell me mene Abba keson sanar dani?"


  "Wallahi prince seda Abbanka ya ja min kunne kar na fad'a maka don't worry he is planning on telling you himself."


  "Taya ze fad'an bayan yamin fushi?"


  "Toh ka kwantar da hankalinka zan masa magana, zan mishi bayanin komai anjima idan mun fita in shaa Allah ze sauk'o kar ka damu kaji my handsome Baby?" Ta k'are zancen tare da aza hannunta akan ha6ansa tana mai wasa sekace wani jariri. Hannun nata ya cire yana zum6uro baki ashe de shima ya iya shagwa6an shine yake ma Amal kallon bakwai saura kwata don itama tayi wa Maminta bayan gashi babba dashi shima yana yi. 


   "Oww had'a min rai zakayi? Shikenan sena fasa basa hak'urin" ta fad'a da gan-gam. 


   "A'a please don't ni ba 6ata miki rai nake ba" yasa murmushin dole. Murmushin ta mayar masa tare da pecking nasa a kumatu "An kai maka abincinka a site naka ko zakaci anan?"


  "Nah am full" yayi maganan yana aza hannunsa kan flat muscled abdomen nashi. 


  "Toh sallah fa kayi?"


 "Zanyi idan na shiga" ya fad'a tare da miqewa. 


  "Alright I love you."


  "I love you too" ya amsa sannan ya kama hanya ya fita tare da nufan site nasa wanda shi kuma kominsa is in black and white. Abinda ya kama daga parlournsa, dining table, d'aki, closet, toilet and bathroom. Kitchen ne kawai pure white. Bathroom ya fad'a yayi alwala sannan yayi sallah ya rage kayan jikinsa tare da barin shorts da singlet zalla. Akan gado ya miqe tare da k'ure AC'n d'akin, ragowan aikin daya rage mar a office yakeson k'arisawa amman ji yayi ya gaji gabad'aya ko d'aga yatsa bazai iya ba don haka ya jawo wayansa daga kan side table tare da shiga Twitter inda ya shiga bin feeds nasa, yana gamawa dashi ya shiga Instagram se Snapchat, k'arshe ya leqa whatsapp wanda daga nan bacci yayi awon gaba dashi. 


   \•\•\•\•\ A cikin City star.


    Zaune Abba da Ummi suke a filin da Abba yayi reserving musu. Ummi ansha kyau kaman ba gobe se k'amshi take. Tana sanye ne da royal blue lace me torches d'in yellow wanda ko ba'a fad'a ba mutum na sani kaya ne me bala'in tsada ga wani arnen d'inkin da akayi mishi wanda ya mugun kar6arta. "Kin ganki kuwa Baby? You're looking so takeaway" Abba dake sanye da sky blue half jamper ya sanar da ita yana mey mata murmushin sosa zuciya.  


  "Kai My Dear kai de bazaka dena flattering d'ina ba ko?" Ta fad'a cike da kunya tana blushing. 


  "Ai kema kin san gaskia nake fad'i gashi har yanzu koda wasa 'yan matan waje sun kasa kawar min da hankali daga gareki, ba don komi ba kuwa se don wannan kwalliya, gyaran jiki da son k'amshin naki, keep it up."


  "Kai My Dear toh nagode in shaa Allahu kuma zan cigaba, amman kaima bakaga yadda kayi kyau bafa ai nasha fad'a maka half jumper suna ma kyau kak'i ji na."


  "Na gano hakan nima yanzu shiyasa kika ga na sanya yau." Hira jifa-jifa suka cigaba dayi har izuwa lokacin da orders nasu suka iso. Cike da k'asaita suka shiga ci suna hirar jifa-jifan har yanzu. Sun kusa gamawa Ummi tayi gyaran murya "My Dear?"


  "Na'am?" ya amsa tare da d'ago kansa yana kallonta cike da soyayya sai kace yau ya soma sata acikin idanunsa. 


  "D'azu Prince yazo ya sameni" ta tsaya deliberately don jin mey zaice. Shi kuwa tunda yaji ta ambaci 'Prince' yaji yayi losing appetite nasa ma gabad'aya. "Ya da tura plate naka gefe kuma My Dear? Kode na fad'a wani abu ne?" Tayi saurin tambaya. 


  "Na k'oshi" ya fad'a yana kawar da kansa yana me kallon gefe. 


  "Dan Allah kayi hak'uri nayi shiru barin sake cewa komi ba amman ci abincin kasan banason kana kwana da yunwa yi hak'uri" ta hau lalashinsa, cike da dabara ta mayar masa da plate d'in gabansa da k'yar ya yarda ya cigaba da ci seda ta tabbata ya k'oshi sannan tace, "My Dear kamar hak'uri don Allah Prince yaro ne kuma fushinka a gareshi babban tashin hankali ne wallahi, baka ga yadda ya shigo site d'ina ba d'azu cike da tashin hankali bayan yayi ma Micheal magana daya maka sallama kak'i fitowa dan Allah ka sassauta masa."


   "Hmm Hajiya Mariam kenan, shin ya sanar dake abinda yayi min?" Ya tambayeta "Ya fad'a miki sau biyu ina kiransa bai d'agawa? Bayan da na samu ya d'aga kuma yace min meeting suke inyi hak'uri and I agreed saboda Prince be cika min k'arya ba sede inyi ma yaro jiran duniya da Baban yarinyan nan amman yak'i zuwa, wannan abin kunyan dame yayi kama? Haka mutumin nan ya gaji da jira ya tafi."


   "Bance yayi dai-dai ba amman da kayi mar uzuri My Dear accident yayi encountering wanda daba don Allah ya tsagaita ba da sede a kiraka ace maka kazo ka d'au gawan d'anka."


  "Haka yace miki?"


  "Yes My Dear and ba k'arya yake ba sanin kanka ne Prince bai cika k'arya ba se idan ta kama so I believed him."


  "Allah kare aukuwan na gaba" kad'ai yace. 


  "Ameen ka hak'uran?"


  "Da hak'uri na da rashinsa ai du d'aya ne."


  "Taya ya zamo d'aya kuma My Dear? Idan har ka hak'ura muna isa gida ka kirasa ka mar maganan nan da kakeson yi mar ko ze d'an samu peace of mind please." Murmusawa yayi cike da k'asaita yadda manyan alhazai keyi. 


   "Hajiya Mariam you're a blessing to this family, a da kafin in aureki ban zata zan iya sake walwala ba a duniyan nan, na d'au bayan rasuwan Fateemah bazan sake tsintan kaina a cikin kalan farin ciki da walwalan da nake ciki ba a yau saidai tun da akayi mana aure kika canza dukannin wad'annan abubuwa.  Ke ce sanadin duk wani walwala da farin ciki da nida d'a na muke ciki a yau, you mended my broken heart. Hajiya Mariam bakida burin dayafi kiga our family stays together and happy yau nasan duk inda Fateemah (asalin mahaifiyar Afzal, yar Mariam wacce suke uwa d'aya una d'aya. Ta rasu ne bayan sunan Afzal da kwana biyu sanadin breast cancer) take tana alfahari dake, kin so Prince tamkar d'an da kika haifa."


   "Dear kenan" ta murmusa cike da jin dad'in wannan kalamai daga bakin masoyinta. "Ai d'an 'yar uwata tamkar d'a na yake so kadena min godiya banida kaman ka da Prince a duniyan nan. Kuma a kullum ina godewa Allah daya bani ikon farinta maka da Prince, addu'a na kuwa baifin Allah hore mana dogon rai mai albarka in cigaba da kula daku ita kuma marigayiya Allah ya cigaba da kai Rahama kabarin ta."


   "Ameen Hajiya Mariam ta" ya amsa a yayinda memories da sukayi sharing da marigayiya suka shiga dawo masa. 


  "Zaka mar maganan idan mun koma?"


  "Queen d'ina ta sa baki ai dole na."


  "Kai amma naji dad'i a ringa ma Prince sassauci please kasan yaro ne."


  "Ke kuma ki cigaba da shagaltasa  kinji ba?" Dariya kalan na manyan mata ta saki sannan ta zuk'e cocktail drink da take rik'e dashi. Hira kad'an suka ta6a sannan driver ya dawo dasu gida. Waya Abba yama Afzal akan yazo ya samesa a site nasa yanzu, alokacin Afzal na zaune a parlour yana playing game. Take ya kashe ya mik'e tare da zira farar jallabiyansa daya rataya jikin hanger sannan ya fito. Knocking yayi aka amsa sannan ya shiga, Abba da Ummi ya tarar akan two seater suna zaune looking so takeaway da alama yanzu dawowansu. Besan ya rayuwarsa zata kasance ba without these two: they simply complete him and he loves them so much. K'arisawa yayi ya durk'usa a k'asa tare da gaishe da Abba cike da ladabi da kuma yiwa Ummi sannu da dawowa. 



   RANA D'AYA

  #RD

  Love... King_miemiebee👄✨

[12/08, 22:25] ‪+234 907 483 8352‬: 🎀🎀🎀                 🎀🎀🎀

                🎀❣🎀

                   ❣❣


  💦💦                      🍃🍃🍃          

           *RANA D'AYA!*

  💦💦                      🍃🍃🍃

  March, 2018


     _Written by Miemiebee👄_



   *PAGE 0⃣4⃣*




   "Ashe abinda ya faru kenan toh Allah kare aukuwan na gaba" fad'in Abba. 


  "Ameen Abba thank you" ya amsa a nitse. Numfashi me nauyi Abba ya fisga sannan yace, "I'm sorry for my outburst on you, yaci ace na baka dama kayi min bayanin abinda ya faru kafin in yanke hukunci."


  "Ba komai Abba ni ya kamata in baka hak'uri I'm sorry in shaa Allah hakan baze k'ara faruwa ba" ya amsa cike da girmamawa, kansa sunkuye a k'asa. 


   "Masha Allah, Dama Alhj Abdallah ne keson ganinka."

  Alhj Abdallah? Afzal ya nanata a ransa, wani Alhj Abdallah d'aya? And saboda meh?


  "Alhj Abdallah Abban Nazeefah" Abba ya sake fad'a ganin kaman ya jefa d'an nasa cikin duhu. 


  "Ohh!" yayi exclaiming se yanzu ya fahimci wa Abba ke nufi. Alhj Abdallah Abban Nazeefah wanda ya kasance aminin Abba kuma second neighbour'n su, gida d'aya ne a tsakanin su. "Abba ina fatan lafiya dai ko?" Ya tambaya a takaice. 


  "Eh toh it depends, kafin nan ina son muyi wata magana da kai Prince shin ka nada tsayayyiya kuwa?" Zuciyarsa yaji ya mugun har6a bade aure Abba ke shirin masa ba don kuwa be shirya ba, sam ba mace d'ayan da ta ta6a yimasa acikin jerin 'yan matan da Allah ke had'asa dasu. To cut the story short, shi baida ko budurwa d'aya ma balle ace ya cire tsayayyiya a cikin su. Ko da yake London karatu 'yan mata ke binsa and not the other way round, kuma koda wasa be ta6a saurara masu ba haka zalika da ya dawo Nigeria ma yanzu, kusan a kullum se 'yan mata sunzo gunshi a office bayan wanda ke binsa har gida. A sanadin hakan ya hana secretary'n shi barin kowa cikin office nasa in ba wanda ya sanar da ita da zuwan su ba. 


  "Kayi shiru ko kafi son ku tattauna da Umminka ne tukuna?" Fad'in Abba jin shirun yayi yawa. 


  "A'a Abba ba abin tattaunawa don a gaskiya banida tsayayyiya" ya basa takaicaccen amsa bayan nazarin daya samu yayi. 


  "Toh Alhamdulillah" Abba ya saki hamdala wanda ya d'aure wa Afzal kai. Meh hakan ke nufi? Kafin ya kawo wani tunanin a ransa Abba ya cigaba, "Dama Alhj Abdallah ne ke tunanin had'a ka da 'yarsa Nazeefah" wani irin mumunan buguwa zuciyan Afzal yayi wanda sanadin hakan yaji zazzafan ciwon kai na neman afka masa. 


  "Aure fa kenan Abba?" Ya tambaya cike da mamaki. 


  "Yes Prince aure kuma kaga jifa yazo dai-dai da zama kenan tunda kace baka da tsayayyiya." Holy crap! Ji yayi kaman ya kashe kansa domin haushi, meyasa bema Abba k'arya yace mar da akwai tsayayyiyar ba a farko? But he can't blame himself saboda baida masaniya akan wannan zance Abba ke shirin sanar dashi. In da kuma k'aryan yayi yace yanada tsayayyiyar and Abba ya buk'acesa da yayi introducing nata ya zeyi? Meyasa Ummi bata sanar dashi wannan ne maganar da Abba ke shirin sanar dashi ba? Nazeefah fah? Wancan fand'ararriyar yarinyan da sama da friends nasa uku sunyi dating nata. 'Yar karamar yarinya amman se shegen rawan kai da falli, idan za'a k'irga samarukan cikin Maiduguri masu ji da kansu toh d'add'aiku ne basu fita da ita ba sam batada kamun kai ga d'an banzan rainin da take ji dashi a takaice de ya tsaneta. Meyasa Abba ze yarda da k'udurin abokin nan nasa? Meyasa ze yarda ya bada only son nasa wa 'yar da batada ko kamun kai? He need answers. 


   "Prince kayi shiru" fad'in Abba sede har yanzu Afzal besan da wani bakin zai soma magana ba couple with the fact that baida ra'ayin aure ko kad'an yanzu. For crying out loud he's just 25 years old ina laifin abar shi yakai koda 30 ne. "Afzal?" Fad'in Abba for second time. 


  "Nnn... na'am Abba" yayi stuttering. 


  "Bakace komai ba" ya sake ce dashi. 


  "Abba bansan me zance ba, Abba yarinyan can batada kamun kai dan Allah kar ka amince da wannan k'udiri" ya fad'a cike da tashin hankali. 


  "Tabbas ba k'arya acikin zancen ka Prince, Nazeefah tayi zara ta fi k'arfin iyayenta kullum complain da Abbanta ke min kenan. Amman idan ka duba, rashin kamun kan nata ne dalilin da yasa Abban nata ke son aurar da ita so she can change her ways. Sanin kanka ne Alhj Abdallah d'an boko ne aurar da yaro at a very tender age sam baya d'aya daga cikin tsarinsa, dalili ne ya kawo hakan kuma kaf cikin yaran abokansa tare da ni amininsa ba wanda yaga yayi masa ya kuma yaba da hankali da tarbiyyarsa kaman kai Afzal, ka gane amincewa da wannan aure kaman yin jihadi ne. Wata k'il idan akayi mata aure zata canza wannan gur6a66iyar rayuwar data d'au wa kanta" Abba yayi concluding. 


  "Abba ni kuma fah? Ban shirya yin aure yanzu ba, ban ta6a kawo tunanin aure ba a nan kusa, Abba please don't give me out" ya fad'a a maraice. 


   "Kayi hak'uri Afzal am not trying to give you out nasan wannan babban abu nake nema daga gareka shiyasa naso muyi maganan as father and son insan meye point of view naka, idan har baka son yarinyar kuma baka tunanin ko a nan gaba zaka ita yin hakan, fine bazan yi maka auran dole ba. Kai kad'ai Allah yabani Afzal and da sani na bazan ta6a yanke hukuncin da zai cutar da kai ba, ina sonka fiye da duk wani mahaluk'i a duniyan nan. Sanin mune nan kaf yarinyan nan Nazeefah bata kai ta cutar da kai ba in kuwa har zatayi hakan toh wallahi bazan ma bari a yi nisa da zancen nan ba. Da tunda mahaifinta ya tunkare ni da maganar zan ja masa layi but we all know bata kai tayi ma wani abun ba. Afzal I've known Alhj Abdallah for a very long time, tun ina masters dina. Da nauyi Afzal in ba haka ba da zan koma in sanar dashi cewa lallai-lallai kai baka amince da wannan k'udiri ba, bazan bari a cutar min da kai ba Afzal. I'll appreciate it if you'll reconsider your decision amman idan har kai kaga you can't find it in your heart to love that girl zanyi iya k'ok'ari na in fahimtar da shi abokin nawa."


    A hankali maganganun Abba suke shiga jikin Afzal suna tasiri. Kaman yadda Abba ya nuna cewa rashin halacci ne ga abokinsa idan har bai cika masa wannan buri ba shima Afzal haka yake gani. Gani yake idan har be bawa Abbansa goyin baya ba toh rashin kyautatawa ne why because tun zaman shi da Abba wannan ne karo na farko Abba ke neman abu a gurinshi da ya kuma nuna muhimmancinsa haka. Tabbas auren Nazeefah baze kashe sa ba toh why can't he sacrifice his happiness for his father's?? 


  Ya d'au tsawon lokaci yana nazari amman ya kasa deciding akan komai, ji yayi k'wak'walwarsa ta toshe gabad'aya, a sannu a sannu ya d'ago kansa dake dafe tun d'azu ya shiga magana a hankali "Tabbas k'in amincewa da k'udurin Alhj Abdallah rashin halacci ne a gareka Abba kamar yadda nima rashin baka goyin baya yake rashin kyautatawa a matsayina na d'anka. Moreover, koda ni ne na tsinci kaina a cikin wannan halin da kake ciki I would do thesame" ya tsaya. Sosai Abba yaji dad'in kalamun nan da suke fitowa daga bakin Afzal. A kullum godiyanshi kenan ga Allah na basa d'a mai hankali mai kuma tunani kaman Afzal wanda yake gudun b'acin ransa wane aikata sa6o wa ubangijinsa. 

   A hankali Afzal ya shiga magana "sai dai-" wanda Abba yayi saurin katse sa a nitse. 


   "Karka damu Prince ba wai don ka auri yarinyan nan hakan na nufin nan a gaba idan Allah ya had'a ka da wacce kakeso bazaka iya auranta bane wallahi ni ko bayan wata d'aya da auran naku ne ka kawo min wacce kakeso I'll respect your decision in aura maka ita kuma ba abinda Nazeefah ko iyayenta suka isa suyi da hakan, you're a husband to four wives, all I'm asking is kayi hak'uri ka amince da k'udurin mahaifin 'yar nan."


  "Abba..." ido Ummi ta masa don haka yayi shiru. 


  "Ba seka amince right away ba Prince, take as long as you want to make up your mind I shall respect every decision you take fata na kawai zakayi considering wannan situation, kasani k'in amincewar ka ga auran 'yar nan kaman tozartani ne a idon amini na da kuma duk wani mutumin da labarin nan ya iske sa. Kaje na sallameka Allah yima albarka, thank you for your time."


  "Toh Abba ameen, seda safe Ummi goodnight" da haka ya miqe ya fice zuwa site nasa inda ya zube a kan gado a yayinda kansa keyi masa wani irin sara, ji yayi komi ya dena tafiya masa a duniyan. Ina ma Allah ze d'au ransa cikin wannan dare (wa iyya zubillah) don komi ya wuce. Ina ma ba a ta6a k'addaro masa da rana irin ta yau ba. Upon all the women out there Nazeefah ze aura? Yarinyar daya tsana fiye da mutuwarsa, fiye da duk wani mahaluk'i a duniyan nan kuma yake da tabbacin itama ta tsanesa as much ba don komai ba kuwa se don tsan-tsan tsana da k'yaman da yake nuna mata a fili, a bayyane a fuskan sa anytime path nasu yayi crossing. God help him. A da har ya fara gyangyad'i kafin kiran Abba amman yanzu baccin nasa ya nema gabad'aya ya rasa ba don komi ba se don tashin hankali. Ido ya zura wa ceiling yana k'ok'arin tattaro hankalinsa, ana cikin haka yajiyo knock a bakin k'ofan d'akinsa se yanzu abin ya fad'o masa ashe beyi locking main k'ofar site nasa ba. 


  "Come in" ya fad'a cikin wata irin kasalacaccen murya. K'ofan na bud'uwa sega Ummi bayyane a bayansa tana sanye da hijabi tazarce. Kallonta yayi ba tare da yace komai ba har izuwa lokacin da ta k'ariso ciki ta zauna akan gadon ta inda yake kwance. "Prince tashi ka zauna muyi magana" ta buk'ace sa. 


  "Ummi dan Allah kibari ba yau ba abinda nakeji is already enough for me to handle just leave me alone I'm sorry."


  "Haba Prince ya kake magana haka? Taya kake tsammanin zan iya barin d'ana k'walli d'aya tal acikin irin wannan yanayi? Tashi ka zauna kaji Baba na yi hak'uri" da k'yar ta samu ya zauna d'in. 


  "Gaya min what is going on in your mind me kake tunanin yi yanzu?"


  "Ummi I don't know" ya fad'a abin tausayi "Am so confused I don't even know what am feeling" ya k'arasa tamkar zeyi kuka. 


  "Shikenan ya isa ka kwantar da hankalinka in shaa Allah komai ze tafi kamar yadda kakeso it's just a matter of time."


  "Ta yaya Ummi when Abba wants me to desperately marry his friend's daughter? Sanin kanki ne Ummi na tsani Nazeefan nan ko gidan nan ta shigo gaisheki ba k'aunan hakan nake ba yarinyar she's so stubborn."


  "Zata gyara in shaa Allah Prince wannan ba komai bane."


  "Yanzu Ummi kema kin goyi bayan zancen auren nan kenan?" Ya tambayeta tamkar zeyi kuka. 


  "Prince da amincewa na da rashin sa duk d'aya ne wallahi one thing am sure is aure bazai auku ba har se idan ka amince kuma har idan baka son yarinyan nan ba wanda ya isa ya saka aurarta."


   Kai ya kad'a cike da takaici "Ummi ki dena magana as if ina da choice, kina ganin yanzu idan na ce wa Abba bazan auri yarinyan nan ba komai zai cigaba da gudana a tsakanin mu kaman yadda yake a da? Kina ganin Abba baze yi holding grudge akaina ba nak'in sake min magana har duniya ta nad'e? Kin deji da kunnenki abubuwan da ya irga a parlournsa d'azu that idan har ban amince da wannan aure ba toh kaman neman tona mar asiri nake shirin yi acikin jama'a which I'll never do so to my own father."


  "Then you have a choice to make, ka yarda da k'udirin Abban naka kawai."


  "It's not that easy Ummi bana son Nazeefah kuma bana tunanin zan ta6a iya sonta wallahi na tsaneta tsana na sosai."


  "Ya Salaam!" Tayi exclaiming "Ya kake magana haka sekace ta gaza ta wani fannin ne iyye Prince? Yarinyan nan de kyakkyawa ce masha Allah son kowa k'in wanda ya rasa gata kuma daga babban gida bugu da k'ari ga iyayenta manyan mutane masu k'ima a idon jama'a, kaf garin nan ana darajasu, what else do you need?"


   "What else do I need?" Ya tambayeta cike da mamaki "Kamun kai, tarbiyya da kuma mace mai addini which Nazeefah is clearly lacking. Sam bata d'aya daga cikin jerin 'yan matan da zan iya so, bana buk'atan kyawunta da kud'in mahaifin ta cause I have all that, I'm rich and handsome."


  Numfasa tayi, "Tabbas ba k'arya acikin maganganun ka Prince addini ma cewa yayi idan na miji zeyi aure abinda ze fara dubawa acikin qualities na matar shine addininta, k'arfin imani kenan, shi arziki da kyau duk a baya suke biyowa."


  "Exactly Ummi that's why I need you to please help me, do something wallahi ina cikin tsaka mai wuya."


  "Ya kakeson muyi Prince? Wallahi in har da akwai wani alternative da na bima don ka ku6uta daga auren wannan yarinya amman babu, hak'ura zakayi ka aureta don ka farintawa Abbanka rai."


  "Ummi ni kuma shikenan kin yarda in jefa kaina acikin k'uncin rayuwa kenan?"


   "Come on Prince" ta fad'a tare da kwanto sa a jikinta tana shafa gashin kansa a hankali. "Ba wanda yace don ka auri Nazeefah zaka jefa kanka cikin k'unci, da ikon Allah zaka koyi sonta, Nazeefah is a very loving lady kawai don baka ta6a ware lokaci ka santa bane, batun rashin kamun kai kuma idan kukayi aure zata gyara, karuwai ma akayi musu aure suka shiryu balle ita da kanta ke rawa kad'ai?" D'ago kansa yayi daga jikin nata sannan a raunane yace, "You like her don't you?"


  "Prince..."


  "Bana sonta Ummi kuma kin san ni idan na tsani abu na tsanesa kenan har abada."


  "Kul!" Tayi saurin katsesa "Kar ka kuma cewa haka, ita soyayya ba'a yimata haka, saidai idan baka bud'e mata zuciyarka ba tabbas zata shige, kai deh kawai yanzu kayi k'ok'ari ka bawa Nazeefah chance am sure zaka koyi sonta as time passes by."


  "I don't think so" ya kawar da kansa. 


  "Tell me something Prince" tayi maganan tare da sashi maido da kallonsa a gareta, "Kana da watan da kake so ko ba haka ba?" Bata basa daman yin magana ba ta cigaba "Meyasa baka sanar da Abbanka ba toh? Kaga if only you did da duk hakan bai faru ba."


  "Ummi wallahi ba wata ni banida kowa wallahi."


  "K'arya kakeyi Prince" ta fad'a tana kallon cikin idanunsa don gaskata abinda ya fad'a. 


  "Ummi ana wasa da wallahi ne? Wallahi babu" ya kuma jaddada mata. 


  "Hmmmm" taja nishi cike da k'in yarda "Duk had'add'un kwanukan da ake shigo dasu kusan kullum acikin gidan nan da sunan an kawo wa Prince abinci kace duk cikinsu babu wacce tayi maka?"


  "Hmm Ummi kennan" ya fad'a tare da murmusawa kad'an ta gefen lips nasa wanda a sanadin hakan dimple nasa ya lotsa "Har yanzu baki san waye Afzal ba, bakisan kalan macen da zata iya burgesa ba har ta iya sace zuciyansa. Mace mey kunya nakeso, wacce duniya da abinda ke cikinta basu dameta ba, mace wacce take da Haddan Qur'ani koda ace ba duka ba, wacce ta rik'e addini, wacce zataji kunyan kallon cikin idanu na tace min tana so na, wacce zata lullu6e jikinta idan zata fita waje ba wacce take yawo ba d'ankwali balle mayafi akan layi ba, ko kuwa wacce ke zuwa party tana bin maza. Bana k'aunar macen da za'ace kaf cikin lungunan garin nan ta zagaya da mota sekace BOSEPA (kamfanin kwashe bola da dotti) kokuwa wacce take bin maza here and there. Sam macen da ta fad'a acikin jerin wad'annan basa burgeni." 


  "Toh Afzal na ji ka kuma na gamsu da duk wani abinda ka fad'a kuma kamar yadda Abbanka ya fad'a maka nima hakan zan kuma nanata ma wallahi kade ji rantsuwa ko? At any moment ka bud'i baki kace min Ummi ga wannan inason ta da aure zan sa hannu inga sena cimma maka wannan buri na ganin wannan 'ya ta zamo matarka, kaide abinda nikeso da kai kawai kayi hak'uri ka amince da auren yarinyan nan ku rabu lafiya da mahaifinka."


  "Ummi idan kuma banida ra'ayin auren sama da mata biyu fa?"


  "Se kayi adapting hakan Prince kokuwa ka bawa Nazeefah chance a zuciyarka and learn to love her those are the only options you have."Dogon numfashi yaja sannan ya sake a hankali, "Thank you" kad'ai yace da ita. 


   "Zan saka a addu'a ni kuma idan har wannan aure alkhairi ne toh Allah ya tabbatar mana dashi ya bada sa'a ya kuma bada zaman lafiya idan har kuma otherwise ne toh Allah kawar da zancen."


  "Shikenan Ummi thank you."


  "Bari in baka waje ka kwanta ko? I don't want you to overthink yourself Prince ka kwanta kayi bacci kawai kabar komi a hannun Allah, kad'au wannan aure as k'addaran da Allah ya k'addaro maka don ya auna iya adadin imanin ka kaji?"


  "Toh Ummi" ya fad'a a hankali. 


  "Gobe akwai office ko?"


  "Eh" ya amsa blankly. 


 "Toh Allah ya kaimu sleep tight okay?"


  "I will, I love you."


  "I love you too" ta fad'a mar tare da pecking nasa a temple sannan ta miqe ta tashi "Ka tashi kayi locking site naka kuma."


  "Manta dashi please" ya fad'a chan k'asa-k'asa sannan a fili yace, "Toh I'll follow behind you." Tana fita ya cire jallabiyansa yaja comforter ya kwanta ko k'ofan d'akin nasa ya kasa tashi ya rufe balle na site d'in gabad'aya. Baccin da Ummi tace yayin yikeson yi amman sam ya kasa, tunanin ya cigaba dayi har...



   Washegari...


  Saboda rashin samun baccin da Afzal be samu yayi ba yasa ko masallacin dake cikin gidansu ya kasa takawa ya fita sabida se daf Asuba nauyayyen bacci ya afka masa, a d'akinsa ya idar da Sallan ya koma kan gado inda ya soma bacci wane gawa totally forgetting ya kamata ya tashi by 6 ya shirya office. 

  

  Ba shine ya tashi ba se goma da rabin safe nan ma don rurin da wayansa keyi ne akan bedside drawer. Cike da kasala idonsa a rufe ya miqa hannu ya ja wayan tare da swiping ba tare da ya duba wa ke kira ba, sauk'e wayan yayi akan kunnensa don ko rik'ewa ma baijin zai iya. 


   "Triple A?" Cewar wanda ya bugo wayan daga d'ayan 6angaren. 


    "Na'am Sultan?" Ya tambaya wai tsabaragen baccin da yakeji yama kasa tantance muryan aminin nasa. Mutumin da suka kasance tare dashi tun forever, tun kindergarten (nursery school) har ila yau. 


   "Don't tell me bacci kakeyi har yanzu" Sultan yayi exclaiming cike da mamaki jin gyangyand'in dake tattare da muryan abokin nasa. 


   "Shhh! Kayi magana a hankali please bacci nakeji" yayi chanting har anan idonsa a rufe. 


  "You better get your shitty ass up ko ka manta kuna da meeting ne a office naku yau kuma kai zaka wakilta? Yanzu secretary naka ta kirani take cemin she's been trying to reach you but all your lines seem switched off nima if not ina da private numbanka off hand da bansan ya zan iya contacting naka ba."


  "F*ck!" yayi growling cike da tashin hankalin a yayinda ya bud'e idanunsa. Gabad'aya ya mance akwai wani abu wai shi office Gosh! Ya zeyi da meeting d'in yanzu? Daman wakiltan Boss nasa zeyi kaman yadda Sultan ya fad'a kasancewar shi manager'n nasu yayi tafiya seya buk'aci Afzal dayake Assistant nasa da ya wakilce shi. 


   "K'arfe nawa ne don Allah maza?" ya tambaya a gigice, gani yake kaman idan ya tsaya neman position na agogon d'akinsan ma ze 6ata mar lokaci.


   "Thirty five minutes pass 10" Sultan yayi stating. 


   "The f*ck!" Yayi exclaiming a birkice tare da miqewa "I'm late for the meeting already!" Yayi exclaiming "Meyasa baka kirani ba tun d'azu?"


   "See you! Wato baka gode bama dana kira ka yanzun?" Ya tambayesa cike da mamaki. 


   "It makes no difference!" ya amsa a d'an fusace. 


  "Ba laifinka bane nasan maganinka, ma tsaya meyasa ka makara haka? Tun jiya fa ban sake ji daga gareka ba are you sure all is well with you?"


  "Guy alot has happened I'm telling you, yanzu call back my secretary ka tsarata kace mata ciwon ciki ya kamani jiya da daddare kaima yanzu Abba ke sanar da kai."


  "A nawa kenan?"


  "Come on!"


  "Alright se yaushe zaka fito?"


  "I dunno yet amman duk abinda akwai zan sanar da kai please call her As Soon As Possible nagode."


  "No big deal" ya fad'a tare da katse wayar. Fad'awa kan gadon yayi da bayansa yana mamakin ya akayi ya makara haka yau amman tuna ya kasa bacci daren jiya sai kusan asuba ya kawar da tunanin daga kansa. Se kuma mamakin da yake ace sa6anin kullum be je ya gaishe da Ummi da safe ba kamar yadda ya saba kafin ya fita office amma ko tazo ta duba sa ko lafiya batayi ba? Ba shakka yanzun tana baje kan gado tana bacci. Kai ya kad'a sannan ya miqe ya fad'a bathroom yayi wanka. Yana cikin karyawa a kan dining table ya soma jin hayaniyan Ummi tana magana da wasu, bada dad'ewa ba se gata nan ta shigo tana sanye da nightie nata da babban mayafi akai, da alama yanzu tashinta daga bacci. 


  "Prince?!" Tayi exclaiming cike da mamaki a iya saninta de Afzal baya wasa da aikin shin toh yau meh ya faru? Mey yakeyi har war hakan a gida yau bayan ba wani public holiday bane?

   "Prince lafiya?" Ta kuma tambaya jin be amsata ba. 


  "Toh Ummi ki shigo mana a bakin k'ofan ne zan gaisheki?" Ya tambaya yana turo light pink lips nasa. 


  "Shikenan Esther ku tafi" ta sallami masu aikin tare da jawo k'ofan sannan ta k'arisa ciki ta zauna a kujeran dake gefen damansa. "Good morning" ya gaishe ta yana sipping coffeen shi. 


   "Prince me ya hana ka zuwa office yau?" Ita ko ta kan gaisuwan ma batayi ba, kafin ya samu daman amsata ta shiga auna body tempreturensa k'ila baida lafiya ne tayi tunanin hakan a ranta. 


  "Ummi please!" Ya fad'a a tak'ure tare da sauk'o da hannunta daga fuskansa. "Am fine I just happened to overslept lokacin dana tashi kuma na makara shiyasa banje office ba" ya bata amsa. 


  "Ban san ka da haka ba fa Prince nima yanzu tashi na kenan daga bacci mai wanke mota ke sanar dani cewa baiga fitowanka ba haka mai bayin flower ma."


  "Yes like I said na makara ne" ya sake jaddada mata. 


  "Meyasa ka makaran Prince? Tunani ka tsaya yi jiya baka samu ka kwanta ba se yau da Asubah ko?"


  "Kusan hakan" ya amsa ta a takaice yana k'ok'arin kai fork daya nannad'e mar fried egg, ketchup da fries a jiki baki. 


  "Toh ya kake? Ka kira office ka sanar dasu?"


  "I did don't worry."


  "Yauwa nac-" wayanta daya shiga ringing ne ya katse ta daga fad'in abinda tayi niyya, duba screen d'in tayi taga Abba ke kira wani dad'i ne ya ziyarci zuciyarta. "Kaga Abbanka ke kira bari inyi picking kayi shiru please" ta fad'a eagerly tare da d'agawa. 


  "Hello Good morning my sunshine" ta fad'a tana kashe murya, wai tsohuwa da rangwad'a. Kad'an ya rage coffeen dake bakin Afzal be bi kansa ba don dariyar data k'eto masa, shikam soyayyan dake tsakanin Abba da Umminsa mamaki yake basa, ace sam basu gajiya da junansu? They've been married for 25 years now amman sekace newly weds a da shima yana tunanin kasancewa da everlasting lover nashi someday but not anymore yanzu da akeson yi masa auren dole da  Nazeefah.

  Hannu ta mik'a ta mintsine shi, da sauri ya kama hannun nata yana mai cigaba da dariyar da yakeji, murmushi ta saki tana mai miyar da hankalinta akan wayan a yayinda Afzal ya cigaba da wasa da yatsunta wanda ta k'ayatasu da jan lalle yadda larabawan Sudan keyi. Don tsiya irin na Afzal, zoben azurfan dake yatsansa ya zaro yana mey k'ok'arin sanyawa a nata yatsan bayan sarai yasan koda Kudu da Arewa za'a had'a ba shiga zoben zeyi ba, badon komi ba kuwa se don girman size na yatsan Ummi d'aya yana matsayin na Afzal d'aya da rabi in beyi biyu ba ma kenan. Ita de bata san yaushe Afzal ze daina mocking k'ibarta ba yabarta tasha iska bTaga bawani k'iban azo a gani take dashi, k'iba ne wanda yawancin matan alhazan nan keda, kuma koda tayi k'atuwa dayawa kaman yadda yake fad'in ma taga haka baby'n ta yake sonta like die ina ruwanshi?


   "Toh My Dear zan sanar dashi sede gashi yau ko ganin ka banyi ba tun bayan Asubah, ka kama ka fita ba tare da ka sanar dani ba."


  "Yi hak'uri My Queen bacci kike so peacefully banso in ta dake ba but I'm sorry na kusa dawowa ayimin kwalliya me kyau" Abba ya fad'a daga d'ayan 6angaren wanda hakan yasa Afzal dake ta sauraron wayan nasu tun d'azu murmusawa. 


 "An gama My Dear a dawo lafiya I love you."


  "I love you too" yace mata sannan ta katse wayan tare da ajiyewa akan table tana wani murmushin jin dad'i kamar yadda ta sabayi anytime sukayi waya da Abba. 


  "Toh murmushin ya isa haka mey Abba yace ki sanar dani?"


  "Prince fa ni ba kakar ka bace tam!" Ta fad'a tana nuna mar 'yar yatsarta wanda hakan ya sasa dariya ba shiri. 


  "Haba Queen d'in Abba na, my only Queen also."


  "Noi!" Ta fad'a tana turesa da hannunta "Ni d'ince Queen taka? A yau ka samu macen da kakeso nasan mancewa zakayi dani so ba seka min zaqin baki ba ka zolayeni."


  "LOL" ya murmusa sosai wanda hakan ya sake fiddo da kyawunsa da fararen hak'waransa da suke nan kaman shi ya jerasu. "Ummi kenan believe it or not you'll always and forever be my Queen banida kamarki Ummi I love you so much" ya k'are maganan tare da placing mata peck a hannu. 


  "I love you more my Prince so Abbanka yace in sanar da kai cewa yana son yi maka magana."


  "Again?" Ya tambaya restlessly "Bade wani auren yakeson sake yimin ba ko?" Dariya comment nasa ya bata don haka ta tsaya yi "Ko kad'an Prince ai ban bari ayi maka haka."


  "Toh meneh?"


  "Kaji Prince da wani tambaya taya kake tsammanin zan san me yake son sanar da kai?"


  "Bawani fad'i gaskiya de Ummi yau ma yace karki sanar dani ne."


  "Allah ban sani ba Prince kaji na rantse."


 "Toh shikenan Allah dawo dashi lafiya."


  "Ameen bari inje inyi wanka nima kar Abbanka yazo ya ganni ahaka."


  "Aje a sha k'amshi deh, k'amshin da baya k'arewa ba" ya fad'a cike da gatsine. 


  "Naji" ta amsa tare da tureshi da kafad'a a yayinda ta miqe. 


  "Ki turo d'aya daga cikin maids d'innan su share min site please."


  "Toh Prince" da fad'in haka ta fice. Breakfast nasa ya k'arisa ya hau latsa wayansa har izuwa lokacin da Abba ya dawo ya tura Micheal da ya kira sa. 




    RANA D'AYA 

   #RD

   Love... King Miemiebee👄✨

[12/08, 22:25] ‪+234 907 483 8352‬: 🎀🎀🎀                 🎀🎀🎀

                🎀❣🎀

                   ❣❣


  💦💦                      🍃🍃🍃          

           *RANA D'AYA!*

  💦💦                      🍃🍃🍃

  March, 2018


     _Written by Miemiebee👄_



   *PAGE 0⃣5⃣*





   "Assalamu Alaikum" ya fad'a a yayinda yake sa kai cikin parlon Abba. 


  "Wa'alaikumus salam" Abba dake zaune akan kujera ya amsa tare da ajiye newspaper'n da yake karantawa yana mey maido da kallonsa ga k'ofar. 


  "Shigo Prince bismillah" shigowan yayi inda ya nemi waje ya zauna a k'asa. "Ya zaka zauna a k'asa sekace wani bak'o?" Abba ya tambayesa da wuri "Take a seat please."


   A'a Abba I'll be fine here."


  "Non sense, take a seat please" be sake yin gardama ba ya koma kan kujeran ya zauna sannan ya gaishe sa cike da ladabi. Batare da 6ata lokaci ba Abba ya wuce straight to the point "Umminka tace ka makara yau baka samu daman fita office ba ko?"


  "Eh wallahi Abba" ya fad'a yana sosa temple nasa. 


  "Toh dama batun maganan jiya ne nakeson in baka hak'uri" ido cike da mamaki da neman k'arin bayani Afzal ya d'ago yana kallon Abba da ya cigaba da magana. "Da kace yarinyan bata da kamun kai bai kamata in sake tilasta maka cewa lallai-lallai seka aureta ba saboda ko addinin musulunci ya hane yin hakan, so kayi hak'uri na maka ba dai-dai ba yanzu haka daga nan zan wuce gidan Alhj Abdallah zan basa hak'uri akan cewa auren nan ba ze yuwu ba ka na iya tafiya nagode."


  "Abba ni bakayi offending d'ina ba saboda koda ka tinkareni da maganan jiya ba lallai-lallai cewa kayi sena auri Nazeefah ba, hasali ma baki na ka tambaya ni kuma na baka amsa bisa rashin tunani. Abba farin cikin ka yafiye min komai a duniyan nan, bazeyi ka bani komai a duniyan nan ba nikuma don for once ka tambayeni abu in hana maka shi ba saboda son rai ko makamancin hakan, Abba na amince da auran Nazeefah idan har yin hakan ze farinta maka rai." A hankali kalamun Afzal suke shiga kunnen Abba suna kwanciya a birnin zuciyansa, don farin ciki ya ma kasa believing abinda kunnansa suka jiye mar, ji yayi son d'an nan nasa na k'ara dad'uwa a birnin zuciyansa, wani sa'in har tambayan kansa yake me yayi wa Allah daya azurta shi da d'a kaman Afzal, yaron da baisan meye kalman son kai ba, yaron da seya kawo tunanin wani kafin ya kawo na kansa, tabbas yasan yayi sacrificing alot to come to this decision, yasan wannan babban hukunci ne Afzal ya yanke ma kansa irrespective of whatever the outcome might be, ya sani idan da har za'a tone zuciyan Afzal ba son auren nan yake ba ya amince ne kawai don ya farinta masa rai kamar yadda shima ya fad'a kuma hakan da yayi ba k'aramin dad'i ya sanyashi ba. 


  "Afzal?" Abba ya kirasa da asalin sunansa wanda ya juma beyi hakan ba. 


  "Na'am Abba?" ya amsa kansa a sunkuye. 


  "Afzal ka d'ago kanka ka kalleni" ya buk'acesa. Hakan yayi "Ka sake nanata abinda ka fad'a" Abba ya buk'ata. Sak abinda ya fad'an ya kuma nanatawa Abba can't help but to feel shocked, surprised and happy duka. Emotions ba wanda Afzal baisa shi feeling ba. 


  "Afzal bana son a sanadin hakan rayuwanka ya shiga wani hali idan har kasan you don't mean this and you can't find it in your heart to love that girl somday karkayi forcing kanka nasan yadda zan 6ullowa Alhj Abdallah da wannan magana I want you to consider youself  first."


  "Abba I mean it your happiness means the world to me" ya sake tabbatar mishi.


  "Alhamdulillah Alhamdulillah Afzal ban san da wani bakin zan soma maka godiya ba, tabbas bansan ya rayuwata zata kasance ba idan ba kai, mahaifiyar ka batayi k'arya ba da tace mun babban kyautan da zan iya samu a duniyan nan shine kyautan ka da tayi min, yanzu nake sake jaddada hakan. Afzal Allah yayi ma albarka, Allah cigaba da sa albarka acikin rayuwan ka kamar yadda ka farinta min yau Allah ya farinta maka haka kaima, Allah ya baka yaran da zasu maka fiye da haka kaima wataran, k'arshe kuma Allah cigaba da kai rahama kanarin marigayiya."


  "Ameen Abba."


  "Nagode, nagode sosai Allah yima albarka."


  "Abba godiyan ya isa haka please idan har akan d'an wannan kake gode min haka ni kuma da kamin komai a duniyan nan ya kakeson inji? That am an ingrate?"


  "Sam ba haka bane Prince, komin da nake maka ka cancanta ne. Prince am so proud of the man you've become. Nasan ba k'aramin sacrifice kayi ba just to make me happy and I so much appreciate it" Miqewa yayi ya matso inda Afzal yake "Come here" ya buk'ace sa tare da bud'e mar hannunsa wide open and ready for a hug. A nitse Afzal ya mik'e yayi snuggling kansa cikin arms na Abba, dad'i yaji ba don komai ba se don ya sanya Abbansa farin ciki. Ya sani wannan decision da yayi making might change his life forever amman kaman yadda ya fad'a farin cikin Abbanshi ya fiye mar komai, he is ready to deal with Nazeefah for his Abba. 


    *         *          *          *         *          *


     GIDAN ALHAJI ABDALLAH


    Fankacecen upstairs ne me kyawun k'arshe wanda ke cike dam da motoci masu tsada, fakasu akayi accoridng to modality. Kallo d'aya za'ayi ma gidan asan na masu shi ne barin flawoyin da an kayi trimming nasu mutum na iya cewa a garden yake. 


     Kyakkyawar budurwa ce wacce baza ta fi shekaru sha bakwai zuwa sha takwas ba (17-18) kwance akan wani makeken Italian bed dake d'aya daga cikin manyan d'akunan da suke saman benin, komin cikinsa ya kasance pink ne banda abubuwa kaman gado da TV stand. 

     Ruf da ciki tayi bisa kan gadon a yayinda kunnenta ke manne da headphones wanda ta k'ure music aciki  connecting it to her MacBook. Waya k'irar iphone X ne rik'e a hannunta se faman yin video take tana bin wak'a tana uploading a snapchat. Wannan budurwa itace definition na '6-4 hutu dan kuwa ba damuwa ko d'aya tattare da ita. 


   K'ofan d'akin ne aka bud'e revealing wani d'an yaro ko saurayi zance me tsananin kama da wannan budurwa saide shi fari ne tas, ita kuwa skin nata yafi chocolate ne da kad'an. Kallo d'aya mutum ze musu yasan 'yan uwa ne saidai ta girmeshi don ga dukkan alamu shi wannan ba zefi shekara sha hud'u zuwa sha biyar ba (14-15.) Harara mey rai da lafiya ya watsa mata ganin bata ma san an bud'e k'ofan d'akin nata ba har yanzu balle tasan mutum na tsaye gun kasancewar loud music data cika a headphones nata, se kad'a kai take ta tana ta faman recording kanta. 


   "Ke Nazeefah!" Yaron ya danna mata kira cike da rashin kunya sekace ba yayarsa ba amman don loud music da takejin bata ma san yanayi ba. Tsuka yaja sannan a zuciye ya k'arisa cikin d'akin tare da damk'o k'afafunta guda biyu yaja seda ta kusan fad'i daga kan gadon. Ihu ta k'urma a firgice tare da juyowa don ganin wani d'an iskan ne zey mata wannan d'anyen aikin, ganin k'anin ta ne yasa ta ma daina mamakin hakan dama tasan ba mey mata hakan se shi, fusata tayi a lokaci guda. Ji take kaman ta wanke sa da mari amman sanin idan tayi hakan shima hannu zai d'aga ya rama saboda yadda ya rainata yasa ta fasa. Headphones d'in ta zare "Kai Khaleefah baka da hankali ne? Dan gidanku ni sa'ar kace da zaka firgita ni ka jani da k'afana? Sa'ar kace ni?" Ta tambayesa cike da tsiwa tana watsa mai harara da dala-dalan idanunta da suka sha artificial lashes. 


   "Had it been baki k'ure music a headphones naki ba ai da kinsan mutum yayi joining d'akin ya kuma kiraki, aikin banza kawai."


  "Aww rashin kunya zakayi min?" Ta kuma tambayansa a yayinda ranta ke tafasa. 


  "Anyin! Kinfi k'arfin ayi miki ne? Mschww!" yaja tsuka. Miqewa tayi akan gadon a fusace da niyan dukansa nan fa karnukan suka hau haushi. Dambe suka shiga yi sekace age mates ba babba ba yaro, yak'ushinsa take da dogayen faracun data tara a yayinda yake ja mata gashin kai wane ze 6allesu.


   Mummy (mahaifiyar su) da ta san za'ayi haka yasa ta biyo sahun Khaleefah only to catch them in the act: fighting. 


  "Ya Rabb!" Tayi exclaiming a kid'ime "Ya haka? Nazeefah me nake gani? Khaleefah ka saketa ko baka san yarka bace?" tayi maganan tana approaching nasu da wuri a yayinda ta shiga rabasu wanda da k'yar ta samu ta cimma hakan. "Sai kun kashe kanku tukuna zaku huta?" Ta tambayi yaran nata da suke matuk'ar kama da ita tamkar an raba kara difference nasu kawai shine adadin shekarun da ta fisu da kuma hasken fata. Fara ce sal wane sadak'ar yallan da ake samu a Kano d'innan. Hak'i duka sukeyi a yayinda suke watsa wa juna harara suna adjusting rigunansu. 


  "What has gotten into you two iyyeh?" Ta tambayesu both. 


  "She started it-"

  "He started it-" duka suka fad'a a tare. "Kawai ina cikin zamana ya shigo min d'aki without my permission sannan ya ja min k'afa sa'ar sa ce ni?" Cewar Nazeefah tana me cigaba da galla mar harara a yayinda ta shiga kama gashinta da Khaleefah ya hargitsa gu d'aya. 


  "Liar!" Ya fad'a mata "Wallahi k'arya ne Mummy na kirata sau uku amman bata amsa ba dake ta k'ure wak'a kaman shed'aniya tana ji."


  "Ni kake cewa liar da shed'aniya?" Nazeefah ta tambaya tare da yunk'urin sake kama shi da wani fad'an wanda Mummy tayi saurin shiga tsakaninsu stopping her. "Enough Nazeefah ke bakisan kece babba ba?"


  "Toh Mummy kina ji yana cemin shed'aniya se in barsa?"


  "Khaleefah bazaka daina rashin kunya ba kai kuma ko? Ce ma akayi sa'ar kace?"


  "Ni wallahi toh karki sake turoni kiran ta tunda kullum mukayi fad'a siding da ita kikeyi" daga fad'in haka ya wucesu both ya fita ignoring kiran da Mummy ke ta yi masa, d'akinsa dake adjacent da na Nazeefah ya fad'a tare da miqewa akan gado, ran auta ya 6aci. 


   "Nazeefah ki kiyayeni shikenan ke bakida aikin dayafi dambe da k'aninki gabad'aya kin bi kinsa ya raina ki ko shakkan ki baya yi" Mummy ta shiga yi mata fad'a. 


  "Toh mutumin da fitsara yake gudu a jikinsa kaman jini daman how will I expect him to respect me? Kuma wallahi ya sake yi min haka sena tattake shi."


  "Wuce Daddy na buk'atan ganinki" shiru tayi kaman bata jita ba "Ko baki jini bane?"


  "Naji zan kashe waqan dake playing ne" ta amsa ta. Kai kawai Mummy ta kad'a ta fice tabi bayan Khaleefah dake miqe akan fankacecen gadonsa a had'add'en d'akinsa da komi aciki yake blue tsan-tsan son kalan da yakeyi. Yana ganinta ya kawar da kansa, dama tasan za'ayi haka k'ofar ta miyar sannan ta k'arasa ciki ta zauna a gefensa. 


  "Haba Autan Mummy my Mr handsome yi hak'uri ka juya ka kalleni" sede kaman bada shi take maganan ba. 


  "In baka waya na ka shiga Ali express kayi ordering 3D games?" Se anan ya juyo yana kallonta tare da gyad'a kai dama ta sansa da shegen son games. "Toh ka hak'ura?"


    "Kullum sede bamuyi fad'a da Nazeefah ba se kiyita biye mata."


  "Mummy is sorry okay? Bar had'a ran haka."


  "Toh ina wayan naki?"


  "Yana d'akina na sauk'a zan bawa Inna (me aikinsu) ta kawo maka."


  "Toh" ya fad'a simply. 


  "Yau ba zuwa playing ball ne?"


   "Se anjima tukuna."


  "Toh barin sauk'a Daddy na nema na" miqawa tayi tare da pecking nasa sannan ta fice bayan ta bawa Inna wayar ta kai ma Khaleefah ta wuce parlourn Daddy da yayi girman d'akuna uku. A gefen Daddy dake zaune akan kujera ta zauna a yayinda Nazeefah ke zaune a k'asa. Tunanin ya Nazeefah zata kar6i wannan bak'on al'amari kawai take, tasan akwai drama. 


  "Nazeefah jiya ina kika je da daddare?" Daddy ya soma da tambayarta. 


  "Daddy gidansu Eesha naje ba wani gun ba yayanta ne yamana tutorials na physics."


  "Nazeefah kin de san k'arya haramun ne kuma kikeyi ko? Nazeefah yaushe ne zaki daina sani acikin bakin jama'a? Ace 'ya ki gagareni ki gagari Mummynku tun bakije ko ina ba? How old are you? You're just 17. Mey kika nema kika rasa a duniyan nan da bazaki kare mutuncin ki da nawa ba Nazeefah? Kullum ace sekin saci ido na dana Mummynku da daddare kifita yawo? Tarbiyyan da muka baki kenan?" Shiru tayi ba amsa "Dake nake magana." Shirun da tayi ta cigaba dayi a yayinda take maganan zuci shikenan ita Daddy baida aikin dayafi yi mata wa'azi kullum ai ko shaid'an ma ana d'aga mishi k'afa.


  "Tunda wannan ne rayuwan da kika d'au wa kanki na rashin ji, kin nuna neither me nor your mother have a right on you, kin nuna mu ba kowa bane a idonki, kin nuna mu bamu isa muyi iko dake ba toh ni zan aurar dake kawai ki huta nima in huta, wata k'il idan akayi hakan you'll change for good." Aure fa Daddy yace? Wani irin wawan bugu zuciyarta tayi, kode wasa yake mata? 'Yar ita ne zai ce zeyi mata aure? Ma da wa tukuna? No this is a joke. 


  "Aure fa kace Daddy?" Ita da wasa ma ta d'au maganar "Haba Daddy!" Ta k'yalk'yale da dariya. 


  "Kin d'au wasa nake miki ne? Aure zanyi miki and I mean it ko zan huta ki huta kowa ma ya huta yaso kije chan ki k'arata da mijin naki."


   "Mummy kina jin Daddy? Wai aure zey min at this tender age? Daddy dan Allah idan wasa kakeyi stop it bana son irin wasan nan."


  "Wasa? Wasa fa kikace, yaushe na soma wasa dake Nazeefah? Ko kin ta6a jin inda akayi wasa da kalman aure?" Ya fad'a cikin tattausar muryan daya mugun razana Nazeefah, tabbas ba wasa acikin zancen da yakeyi amman mey ya buga kansa yace zai mata aure? A iya saninta iyayen da suke da k'arancin western education (ilimin boko) ne masu yima yaransu aure da wuri meyasa Daddy zai mata haka bayan shi be fad'a cikin jerin kalan iyayen chan ba. 


  "No Daddy don Allah kar ka min haka" ta fad'a a rude'e still finding it hard to believe "Daddy don Allah kayi hak'uri I'll change my ways I promise never to go out in the night again, Daddy I'll be a good girl dan Allah ka ja baya da zancen nan."


  "My decision is irrevocable Nazeefah, na baki enough time da ya kamata ace kinyi amfani da hankakinki kin sauya halayanki amman kink'i yin hakan, idan har ban d'au mataki akan ki ba yanzu to tabbas haka ina ji ina gani wataran zaki d'ibo min abin kunya ki kawo min gidan nan, so the earlier the better."


  "No Daddy please" ta rushe da kuka "Mummy please say something, stop him please! Wallahi na tuba na dena bin k'awayen banza, na daina bin maza from now henceforward I'll be a good girl Daddy don Allah karka min haka Daddy am too young."


  "Kinsan da hakan amman yau kene da wannan a gari gobe da wancan? Samarukan garin nan kaf ba wanda bey sanki ba, you've had your time and it's now over ko kin k'i ko kinso aurar dake zanyi idan kuma har kika ga auran nan be auku ba toh wallahi mutuwa kikayi ko kuwa guduwa wanda idan kikayi zan fidda ki daga sahun 'ya'yan dana haifa I mean it" ya fad'a cikin tattausar murya. 


  "Daddy please I'm sorry" kuka take sosai but neither Daddy nor Mummy suka tausaya mata saboda tsan-tsan rashin jin magananta kaman yadda Afzal ya mata shaida. 


   "Daddy karatu na fah? Yaushe na fara karatun da kake tunanin min aure? Daddy please don't do this wallahi bazan iya had'a aure da karatu ba."


   "Kije ki shirya Nazeefah" ya ce da ita tamkar beji duk abinda ta fad'a ba "An jima kad'an yaron dana samu ya taimaka ya amince ze aureki zaizo domin in mar godiya so idan yazo zan had'aku even though am sure kin waye shi saboda ba kowa bane banda Afzal yaron amini na Alhj Ahmad Amin."


   "What???" Tayi exclaiming unbelievably "Afzal fa kace Daddy? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" ji tayi kaman zata haukace. Afzal? Noo it's not possible tasani Afzal baze ta6a yarda ya amince ze aureta ba saboda irin tsanan daya mata kaman yadda itama bazata yarda ta aure sa ba cause kamar yadda ya tsaneta haka itama ta tsanesa. Mutumin da kullum idan ya ganta akan hanya yake watsa mata harara ne za'a ce ya amince ze aureta? Wanda idan ya ganta a gidansu yake ji tamkar ya bita da muciya? This is just some kind of game it can't be happening idan har ko ya amincen ma then there's not doubt akwai wata mumunar abinda ya shirya mata in store. 


   "Daddy don Allah karka kasheni kafin lokaci na, Daddy I beg you please wallahi bazan sake rashin ji ba, Daddy bana son Afzal bazan iya auran shi ba."


  "Shima ba sonki yake ba Nazeefah taimakawa zeyi ya aureki don ya rufa min asiri, ko a tunanin ki cikin 'yan iskan samarukan naki akwai wanda ze amince ya aureki ne? Abbanshi yace ya amince ne da auren ba don komi ba se don ya farinta masa rai. Rok'an Abbanshi nayi tayi daya taimaka yayi convincing d'an nasa ya aureki Nazeefah saboda bansan wazeyi hakan ba nan gaba. Da kalan gur6arcacciyar rayuwan nan da kika d'au wa kanki inada tabbacin cewa ba d'an na mijin da zaiji sha'awan auranki. So it's better tun ina raye in nemi wanda zai rik'e min ke amana ya kuma kula dake ya d'aura ki akan hanya madaidaiciya and I can't think of anyone else sama da Afzal. Afzal ya amsa sunan d'a a duk inda ake neman hakan, yaro mai hankali da ladabi dakuma sanin ya kamata I just wish you'll follow his steps and change for the good Nazeefah" ya fad'a cike ca takaici kamin ha mik'e "Kina iya tafiya" yana kaiwa nan ya wuce d'akinsa. 


   "Daddy please karka tafi" ganin Mummy ma ta miqe da niyyan bin bayansa yasa Nazeefah dawo da kallonta a gareta hawaye take sosai bazata iya tuna when last tayi kuka haka ba. "Mummy don girman Allah karki min haka, Mummy I beg of you please ki bawa Daddy hak'uri."

  Koda wasa Nazeefah bata ta6a kawowa a ranta Daddy ze iya mata abu irin haka ba, saboda coolness nasa da kuma shiru-shirunsa. Daman ance a guji 6acin ran miskilin mutum, duk kalan rashin ji da abubuwan da takeyi Daddy bai ta6a kiranta ya mata koda masifa ba iyaka ya tambayeta maisa tayi hakan ashe for all these while tara ta yake yau data kaisa maqora gashi har mak'ota ya shiga yana neman wanda zai taimaka ya aureta sekace wata bazawaran da tayi kwante, yau wannan wani irin abun kunya ne? Kuka ta cigaba dayi sosai a yayinda take rik'e da k'afan Mummy da jikinta yayi sanyi lis. Ita kanta Mummy bata ta6a  kawowa a ranta Daddy zey iya yima Nazeefah abu haka ba don ko ita be sanar da ita abinda yake ciki ba itama kamar yadda Nazeefah kejin news d'in haka yayi mata breaking d'azu. Sau dayawa takan zauna tayi tunanin mey tayi wa Allah ya bata 'yar da batajin magana ba kuma ta tsoron ido da bakin mutum kaman Nazeefah dukda tasan yin hakan kaman yima Allah shisshigi ne but she can't help it. Yarinya bata je ko ina ba amman ta gagari kowa? Shide Daddy yasan dalilin hakan, yasan the reason behind Nazeefah's naughtiness and everything tabbas past nasa ne yake hunting nashi, tabbas alhak'in baiwar Allahn daya ta6a ci in the past ne yake binsa...


  "Mummy am begging you please ki bawa Daddy hak'uri Mummy so kuke in kashe kaina? Auren dole fa Daddy yake shirin min and you're okay with it."


  "Am not okay with it Nazeefah" ta fad'a da k'yar tana danne hawayenta. "Banida wata option ne Sweetheart, Nazeefah ke kika janyo duk wani abinda yake samunki yau, kin nuna tsan-tsan rashin ji wa Daddy'nku tun yana hak'ura har hak'urin nasa ya k'are, Nazeefah your Dad is not proud of you, ze d'auki Khaleefah sau d'ari bey d'aukeki ba ki taimaka ki rufa mana duka asiri and obey him ayi wannan aure wata k'il ki shirya tsakaninku."


   "Mummy no please dan Allah kar kice haka wallahi zan canza give me one last chance wallahi I'll be the perfect daughter for you and Daddy amman karku min auren dole bana son Afzal, na tsane shi kaman yadda shima ya tsaneni Mummy please save me."


  "Ya zamo dole kenan ki yayyafa wa zuciyarki ruwan sanyi ki koyi sonshi saboda bakida wata option da tafi yin hakan, tashi kije d'akinki ki shirya ina zuwa" tana kaiwa nan ta janye k'afarta ta fice itama. Sabon kuka Nazeefah ta soma tsugune a wajen tamkar zata cire ranta. Seda tayi kaman ba gobe sannan a raunane ta mik'e tashiga takawa nan Khaleefah dake la6e yana sauraran komi a bakin staircase tun d'azu ya ruga sama a kuje to his room kafin ta kama sa. Shi kansa be tsamman Daddy ze iya yin abu haka ba, aiko tun wuri gomma ya shiga taitayinsa kamin ace za'a tura sa boarding kaman yadda Mummy ke fad'a masa kullum idan yayi wani rashin jin. 


  *         *            *             *             *         *

     BACK TO GIDAN ALHJ AHMAD AMIN. 


   "Oh! Esther seda nace miki kar kisa turaren wutan tukuna kibari se Prince ya fita amman kika k'i ji so kike ki kora min d'an nawa idan ya shigo?" Ummi ta tambayi Esther dake ta raba ido a k'asa. 


  "A'a Hajiya kiyi hak'uri hakan baze sake faruwa ba."


  "Kiyi sauri ki fita dashi toh."


  "Toh Hajiya" da haka Esther ta fice waje da turaren wutan ta k'ofan kitchen wato k'ofan baya. Window da labule Ummi ta shiga bud'ewa da d'agawa don hayak'in ya ragu kafin Afzal yazo ya mata tsaye bakin k'ofa yak'i shigowa. Bada dad'ewa ba ya fito daga site nasa yana sanye da farin Gezna d'inkin half jumper data mugun amsar komi nashi, ya kafa hulan nan ras wane a gudu dashi don had'ewa, idan me rubutu ta tsaya describing kalan kyan da yayi to da alama ba inda masu karatu zasu je don haka muje zuwa. 


  Duk angle daya bi se k'amshin designer turaren daya juye ajikinsa ya kama gun, cike da k'asaita kaman yadda ya saba tafiya yana juya key'n motarsa ya taka har ya k'ariso site na Ummi. Daga k'ofan ya tsaya don jin ko akwai hakay'i. 


  "Toh Malam kana iya shigowa don kai na sa aka fita da turaren" se anan ya shigo ya miyar da k'ofan. A gefenta akan two seater ya k'arisa ya zauna "Prince irin wannan shan kyau haka?" ta tsaya tana admiring nasa wato komi nashi yayi ne "Ai seka sa Nazeefah ta rikice."


   "Ummi please nifa gun Abbanta zanje ba gun ta ba" ya wani murtuk'e fuska, to the mention of Nazeefah's name yaji mood nasa ya 6aci ma gabad'aya. 


  "Toh du Allah wasa nike kana iya sake fuskan, so Abbanta yayi requesting ganinka wai ko?"


  "Yup haka Abba yace" ya amsa popping the P. 


  "Welldone my son ka sanya Abbanka farin ciki, farin ciki na sosai wanda ko ni matarsa ban tsammanin zan iya sashi ciki. Kaji yadda ya shigo yake ta yaba ka kuwa and tell you what?"


  "What?" Yayi saurin tambaya, bakin ta tayi saurin go6ewa "Subhanallahi wallahi sirri yace mun kayi hak'uri."


  "Shine kuma kika ja min rai?" Ya tambaya yana pouting bottom lip nasa. 


  "Kar ka damu bari in baka hint, yace yana son yayi surprising naka."


   "Awww" ya tsaya blushing tamkar a gudu dashi. 


  "Kalli kyakkyawan fuskanshi anan Allah yaso da me mahaifiyarka nike."


   "Uhm wai me yake niyyan bani?"


   "Prince sirri ne fah kaga tashi ka fita kafin kayi latti" ta canza topic d'in da wayo "Today is your first impression it can't be ruined."


  "Uhmm toh sena dawo" yayi maganan tare da miqewa. 


  "Maganan gaskia kayi kyau Prince yaci ace in d'auke ka hoto kafin ka fita."


   "God help me" ya fad'a murya ciki-ciki "Please Ummi sekace yau kika fara gani na?" 


   "Naji nide tsaya tukun" ba yadda ya iya hakan ya tsaya ta d'auke shi, don neman magana ko kallon cameran nata ma beyi ba saidai hakan be hanasa yin kyau ba, se hoton yayi kaman irin unlooking picture d'innan. "Toh a sake bani wani pose mana d'an bani swags naka man kad'an" ta fad'a cike ca wasa trying to stimulate him, murmusawa yayi sannan ya gyara tsayuwan nasa me kyau kaman wani model tare da rik'e hannun riganshi dai-dai gun cufflinks nasa. A dai-dai nan Ummi tayi snapping moment d'in. "Wow! Masha Allah, toh good luck seka dawo."


  "Ummi please ba fa jarabawa zani ba."


  "Uhn-uhn fa Prince" tace dashi wanda ya sanya sa murmusawa, "Kidding, kidding thank you sena dawo."


  "Yauwa ka gaishe min da maman nata idan kun had'u."


  "Alright" ya fad'a lastly before stepping out. Gun motarsa data sha wanki k'al yayi ya shiga ciki tare da kunna ignition d'in. Gidansu Nazeefah yayi direct inda yace abokinsa Sultan ya jirasa. 


*****

     Nazeefah na miqe akan gado a d'akinta tanata aikin kuka, damuwa da k'uncin rayuwa sun isheta Mummy tayi mata sallama akan cewa Afzal ya zo Daddy na kiranta. Ko ta kan Mummy batayi ba se kukan da take takanyin ta cigaba, nasiha sosai Mummy tayi mata akan idan har ba so take Daddy yayi mata baki ba toh ta rufa ma kanta asiri tabi umarnin sa ta amince ga auren nan. Ba don tana so ba ta sanya hijabi ta fice, fuskanta ya kumbura tim a yayinda idanunta suka kad'a sukayi jazir. La6ewa tayi daga jikin bango tana sauraran yadda Daddy ke tayima Afzal godiya sekace wanda ya basa gidan Aljannah kokuwa wanda za'a d'auki nakasasshiya a bashi, abin da yafi ci mata rai kenan. Itan da samari suke papa akanta suke binta amman wai ace Daddy har se ya had'a Afzal da Allah tukun ya amince ze aureta wani irin abin kunya da raini hakan ke nufi? Seda ta gama sauraron duk abinda suka ce tukuna tayi sallama ta zauna daga chan baya-baya. Sam batayi niyyan gaishe da Afzal ba amman tuna abinda Mummy tace mata yasa tayi unwillingly. Ko kallonta Afzal beyi ba hasali yima yayi at first kaman baze amsa ba sannan daga bisani ya amsan suka gaisa. 


   "Afzal ina sakeyi ma godiya daka rufa min asiri a garin nan ka amince da auren Nazeefah wallahi ga ka ga ita na baka dama aduk sanda tayi wani rashin hankalin ka hukunta min ita saboda ta zama taka yanzu, tarbiyyar ta da komai ya koma hannun ka, ina da tabbacin ba wanda ze kulamin da ita ya kuma d'aurata akan hanya madaidaiciya sama da kai."


  "Ba komai Daddy zamu cigaba dayi mata fatan shiryuwa kai kuma kadena min godiya haka na amince da wannan auren ne don Allah."


  "Allah yima albarka Afzal, Allah cigaba da kareka bazan manta da wannan abu ba nagode sosai bari in barku tare ko akwai abinda kake son sanar da ita zan shiga daga ciki."


  "Not really Daddy nima yanzu zan tafi, Nazeefah in bazaki damu ba ki biyoni waje akwai abinda nakeson nuna miki" daga fad'in haka ya mik'e. 


  "Bakiji mey yace bane kike zaune har yanzu?" Daddy ya tambayi Nazeefah dake ta faman kukan zuci tun d'azu hawaye nabin k'uncinta. 


  "Naji Daddy" ta amsa in a teary voice tare da miqewa tana bin bayan Afzal. Chan wajen gate inda yayi parking motarsa ya nufa, Sultan abokinsa dake gaban motan ne ya bud'e k'ofan ganin Afzal na isowa. A gefen k'ofan ya tsaya yana jiran Nazeefah ta k'ariso bayan tayi hakan yayi shiru ya tsaya yana kallonta. Kallon dayasa duk wani gashin jikinta tashi, kallo yake mata cike da rashin mutunci da k'yama kusan sau uku idansu ke had'uwa amman har yanzu baice da ita komi ba, ita kuma Allah bai bata ikon cewa wani abu ba. 


   Daga bisani yace, "Bazan aure ki ba Nazeefah, bazan ta6a auran k'azamar mace kamar ki ba wacce sama da maza goma sun ta6a kowani lungu na sashi a jikinta, bazan auri macen da take yawo akan hanya dressing almost half naked ba, bazan auri matar da batada kunya da kuma k'arancin ilimin addini ba kamar ki. You disgust me Nazeefah, idan har kinsan ciwon kanki kinsan ina ke maki ciwo baza kibari wannan aure ya auku tsakani na dake ba saboda I'll never learn to respect and regard you as a woman than a wife because kin riga kin zubar da darajar ki da k'ima da kuma mutunci a idanu na. Just to tell you how worthless you're, akuya ma tafiki daraja a idanu na" yana kaiwa nan ya tsaya don jin ko zata fad'i wani abu amman ko uffan ta kasa cewa. Hawaye ke bin k'uncinta kawai, tunda tasan kanta ba a ta6a humiliating nata haka ba, don ya fad'a mata wannan munanan kalamun ne dama ya ma Daddy k'arya yace yana son nuna mata wank abu? Ashe don yaci mata mutunci a gaban abokinsa ne? Don yasata ta tsani kanta? Bata san mey ya hanata miyar masa da magana ba a lokacin saboda sanin kowa ne Nazeefah nada baki ba'a ta6a ta tayi shiru se gashi a lokacin data fi buk'atan bakinta ya bud'u yak'i yin hakan. Toh mey zata ce masa bayan wannan munanan kalamun daya kwatanta ta dasu? Yes he might be right, there is amount of truth acikin duk abinda ya fad'a but just because Daddy yace ya basa ita doesn't mean he has the right to hurt her feelings like this. Ai ko macen da take sana'ar karuwanci ma bata so akira ta da mazinaciya. 


    Ganin bata da niyyan cewa komi banda hawayen da take tayi Afzal ya cigaba "They say a word is enough for the wise I hope this is message enough for you, you can go back in, greet your mother when you do sai anjima." Yana kaiwa nan ya zagaya to the driver's side ya tada motar tare da kad'a mata k'ura. Tsaye Nazeefah tayi wajen wane gunki se aikin kuka take, sauk'a har k'asa tayi a wajen tana kukan cire rai. 


   Wacce irin rayuwa ce wannan?


  



  RANA D'AYA

 #RD

 Love... King Miemiebee👄✨

[12/08, 22:25] ‪+234 907 483 8352‬: 🎀🎀🎀                 🎀🎀🎀

                🎀❣🎀

                   ❣❣


  💦💦                      🍃🍃🍃          

           *RANA D'AYA!*

  💦💦                      🍃🍃🍃

  April, 2018


     _Written by Miemiebee👄_



   *PAGE 0⃣6⃣*




    "Nifa ka sani acikin duhu, wai meke faruwa ne?" Sultan ya tambayi Afzal dake tuk'i cike da rashin hak'uri da neman k'arin bayani. Shiru Afzal ya masa yana me sa hankali sosai akan tuk'in da yakeyi. 


  "Triple A?" ya kuma kiransa kusan sau goma kenan tun zamar su cikin motar. 


  "Bansan yaushe ka kurmance ba wallahi, referring to abubuwan da kaji na fad'a mata ai yaci kasan auranta mahaifinta yakeson inyi."


   "Nazeefan fah?" Sultan ya tambaya cike da d'umbun mamaki. 


  "Ask me again" ya fad'a tare da basa d'aya daga cikin mugayen kallonsa sannan ya maida kallonsa kan hanya.


  "How?? Triple A kabani labari please."


  "Idiot ai labarin nakeson baka yasa nace ka taho."


   "Asshole" ya fad'a tare da kai masa punch a hannu "Am all ears" nan Afzal yashiga zazzage masa dukannim abubuwan da suka gabata tun daga yinin jiya, a haka har suka iso layin dake kusa da gidansu Amal. 


   "Tsaya maza mey kuma zamuyi anan? Mey ya kawomu unguwan nan? Kode kayi 6atan kai ne?" Sultan ya tambaya nan take. 


  "Nop" ya amsa tare da popping P d'in "Ina yarinyan dana fad'a maka na bugeta accidentally jiya?"


  "Yes" ya amsa tare da gyad'a kansa "Dr ya buk'aci a mayar da ita yau a sake treating k'afan so am here to fetch her" ya fayyace mar. 


  "Toh shine se kai ne zaka kaita? Ai tunda ka riga ka biya kud'in komai se ka bawa mamanta transport fee tana kaita."


   "No Sultan I cursed this upon them, ganganci na ya kaini kad'eta I have to take full responsibility."


  "Toh Mr good samaritan jeka ina jiranka" ya amsa shi cike da gatsine. K'aramin mirror dake gaban driver seat Afzal yaja yana duban fuskansa tare da sake daidaita hulansa sannan ya fice. Shi de Sultan baice komi ba illa binsa da kallo da yake. 


  Sallama yayi a hankali alokacin da yake sa kai cikin gidan. Amal ya tarar zaune akan benchin jiya da wani novel na English rik'e a hannunta ta zurfafa ciki tana karantawa. Sanye take da wata atamfa riga da skirt wanda ta mugun amshe kalan skin nata, kanta kuwa ba d'ankwali hakan ya bawa Afzal daman ganin silky gashinta dake nan kaman na bak'ak'en 'yan India. Kamashi tayi a tsakan kanta tare na nannad'e jelar wanda a sanadin haka Afzal be samu daman gano k'arshen ba. Kallonta ya tsaya yi musamman yadda ta miqar da k'afan nata me targad'e wane wacce ke jiran koda kuda ne ya ta6a ta hau bala'i da k'orafi. 


  "Uhm uhm" yayi gyaran murya wanda hakan yasa Amal tsaida duk wani abinda takeyi ta d'ago kanta domin ganin wanene. Wani irin d'an banzan tsinkewa zuciyarta tayi ganin Afzal tsaye akanta da ratan da befi meters biyu zuwa uku tsakaninsu ba. Da sauri ta dukar da kanta a lokacin da idanunsu suka had'e tana me neman mayafi don lullu6e jikinta sede ba halin yin hakan dan k'afarta. Yadda zama ke bata wuya haka zalika miqewa don haka kawai ta shiga kare k'irjinta dukda cewa bawai ya bayyano waje bane. Shiko Afzal ganin ta soma yin wasu abubuwan yayi saurin juya mata baya totally dan kuwa bega abun gani ba achan da take ta wani faman tarewa. 


  A hankali ta d'ago kanta taga gabad'aya ma baya ya juya mata aiko take ta murgud'a mai baki "Tafi nono fari" ta fad'i can k'asa-k'asa sannan ya k'wolla ma kira. 


   "Mamiiii!" Dan k'ara irin na muryarta seda Afzal ya toshe kunnensa. 


   "Ki fito kinyi bak'o and please ki taho min da hijabi na."


  "Toh" Mami ta amsa daga ciki, bada dad'ewa ba se gata nan ta fito, ganin mutum kaman Afzal ne yasata sakan murmushi. "A'ah Afzal ko?"


  Se anan ya kewayo nan ta tabbatar shi d'inne "Sannu da zuwa Baba na ina yini?" Ta gaishesa tana mik'a wa Amal hijabin data fito mata dashin. 


   "Yauwa Mami ina yini? Ya gajiya?" Ya amsa cike da girmamawa. 


  "Lafiya k'alau ya kayi tsaye haka? Ka k'ariso ciki mana. Ke Baby haka akeyi ne seki bar bak'o tsaye bazaki ce masa ya k'ariso ba?" Mami ta tambayi Amal data had'e gira gu d'aya. 


  "Yo ba nace ya shigo ba yayi tsaye wajen" ta fad'a cike da rashin kunya. Baki Afzal ya bud'e cike da mamaki yana kallonta wato acikin had'uwa biyu da sukayi ya karance Amal is such a big liar, gashi comfortably take yin k'arya kuma bata d'auki hakan a bakin komai ba. 


  "Toh gaisuwa fa? Kin gaishe shi?"


"Abinda na farayi kenan daya shigo" ta kuma amsawa. Shide Afzal bece komai ba. "Bari in d'auko ma taburma mana ka zauna Afzal ko ruwa ne kasha."


  "A'a Mami karki damu daga gida nake nazo d'aukan Amal ne ayi dressing k'afan nata kaman yadda Dr ya buk'ata" Kafin Mami tace za tayi magana Amal har ta tsoma baki ta soma k'orafi "Ni wallahi ban komawa asibitin chan in kanayi wa Allah ka koma inda ka fito nagode da kulawarka amman ban sake taka k'ofan asibitin chan." Har anan Afzal bece komi ba saboda yasan abinda ya tanadar mata. 


  "Yau ina ganin ikon Allah!" Mami ta tsaya kallonta tare da dafe k'irji "Ke da hankalinki? Yanzu ya dace ki fad'awa mutumin da ke nema maki lafiya wannan kalamu? Wallahi karki bari raina ya 6aci in basa hak'uri yayi tafiyansa yaso k'afan naki yayi tsami ya ru6e in kaiki nan gun wanzan a gintile kowa ya huta." Dariya sosai comment na Mami yabawa Afzal don haka ya shiga gyaran murya don had'iye dariyar sede still seda curves na murmishi suka nuna a fuskansa. Wani kallo Amal ta watsa masa tare da fad'in wasu kalamun chan k'asa-k'asan muryarta yadda ita kad'ai tasan abinda tace. 


  "Maza tashi karki 6ata min lokaci!" Seda ta gama tsiyarta sannan ta amince Mami ta taimaka mata ta miqar da ita. 


  "Toh Allah ya kare Afzal kaikuma Allah ya biya."


  "Ameen Mami" daga fad'in haka ya fice Amal na k'ingishi tana mara mai baya har suka isa gun da motarsa ke. Kasancewar motar tinted ce Amal bata samu daman gane cewa da akwai mutum acikin motar ba shi kuwa Afzal shiru yayi mata daya ga tana nufan k'ofan gaba. Tsaye yayi yana jiran na aukuwa ya faru. Tana bud'e k'ofan kawai setaga bak'on fuska na kallonta, kunya tajiyo sosai yanzu Afzal yasan da mutum cikin motan yamata shiru har ta bud'e? Yamar kyau. 


  "Ina yini?" Ta gaishe sa cike da kunya tana ja baya a hankali se kace ba ita ba. 


  "Lafiya 'yan mata kin 6ata ne?" Sultan ya tambaya danko besan itace yarinyan da Afzal ke nufi ba. 


   "Ban san da mutum aciki bane am sorry." K'ofan ta miyar mishi tare da d'ago kai tana kallon Afzal dake ta faman kallonta shima dariya ya ciko mar dam a baki amman ya dage ya danne. Ba tare da yace mata komai ba ya bud'e motan ya shiga wanda itama tayi hakan. Bayan ya kunna motan Sultan da kansa ya d'aure ya juya ya dubi Amal sannan ya kalli Afzal sam be kawo a ransa cewa budurwa ce Afzal ya buge ba cause yadda Afzal ya basa labarin k'iriniyar yarinyar seyayi picturing nata to be 13-14 years. 


  "Itace yarinyar?" Ya tambaya not believing it. 


  "Wai ba" Afzal ya amsa sa in an I don't care tone tare da yin reverse suka hau kan hanya. "Kana bani labari" cewar Sultan after a while "Amman Triple A bakada mutunci."


  "Da nayi meh?" Ya tambayesa yana me miyar da hankalinsa sosai game da tuk'in da yake a yayinda Amal dake baya ta ware kunnuwanta domin jin abinda wannan mara mutuncin yayi da har abokinsa ke mamaki haka. 

  

  "Kaji kalan kalamun daka fad'awa yarinyan chan mana Nazeefah" ta6e baki Amal tayi, dama tasan za'ayi haka a yayinda ta cigaba da kasa kunne. 


  "She needs to be told the truth" Afzal ya miyar masa ba tare da ya nuna damuwa ba. 


  "Toh kai kasan ka k'yamaceta haka meyasa ka amince da k'udurin auren nata?"

   Aure de? Amal ta nanata a ranta, lallai ta tausayawa 'yar da zata auri wannan mutumi me uban ji da kai haka, ai kuwa gashi tun ba'a je ko ina ba abokin shi yace baida mutunci be kyauta ba, ko mey ya gaya wa yarinyan se Allah. Shiru tayi tana me cigaba da sauraran hiran nasu. 


   "To make Abba happy" ya amsa sa simply. 


   "Hmm fire on the mountain sunan wani abu, Afzal da Nazeefah a k'ark'ashin rumfa d'aya ai akwai show" jin Afzal be amsa shi ba ya cigaba "Triple A tell me something mana kode dama kanada interest akan yarinyar ne?"


   "Interest?" Afzal ya nanata cike da mamaki yanzu upon all people Sultan ne ze fad'a masa wannan batu? Lallai amman be kyauta ba, ai wannan zagi ne. 


  "Dan Allah ka miyar da kallonka kan hanya kafin kaje ka zubda mu" yace da Afzal daya tsaya yana kallonsa da alama ya manta akan hanya yake domin ko niyyan kau da kansa ba beyi ba. 


   "This is an insult to my face Sultan, ai ko Nazeefah ce autan mata I'll never learn to love her, she simply disgusts me."


   "Hmmm nide nayi shiru amm-"


   "Shut up Sultan" yace dashi tare da katse sa. Shirun da Sultan beyi ba kenan ya cigaba da neman tsokan Afzal har sanda suka isa asibitin amman ko uffan Afzal be ce dashi ba, hasali manna mishi yayi. Dukansu uku suka kuguma suka fita inda suka nufi cikin asibitun tun daga harabar Amal ta soma kauce-kauce ita bata so Afzal yayi hak'uri ya maidata gida, ita kad'ai tasan azabar dataji jiya sede ko kallonta beyi ba bale yasan tanayi. Bayan sun gaisa da likitan ya kewayo da fatan ganin Amal se de ya ganta chan tsaye bakin k'ofa ta maraice fuska. Murmushin mugunta ya saki sannan ya dawo da kallonsa akan likitan tare da yin gyaran murya, "Dr ya naga kaman jiya baku ja k'afar yarinyan can kaman yadda ya kamata ba?"


   "Ba'a ja ba kuma Alanguburo? Meyasa kace haka?"


  "Toh gashi k'afan nata yayi tsami ya kumbura-"


  "Wallah bai kumbura ba" Amal da ta kasa kunne tana sauraronsu tayi saurin katsesa "Wallahi be yi tsami ba Dr don Allah karka sauraresa" ta fad'a cike da tashin hankali. Shareta Afzal yayi ya cigaba, "Gashi na kawota yau ina son ku jashi sosai please, a ja sosai saboda kar a samu complications nan gaba."


  "Toh Alanguburo in shaa Allah ina yarinyan ne? Ke shigo mana" yace da Amal yana maida kallonsa a gareta. Ja da baya ta farayi da niyyan ta gudu. 


   "Don't even think of running ga nurses da securities kota ina sasu zanyi su kama ki" Afzal ya fad'a cikin tattausar muryar data mugun razana Amal da tuni tasa kuka. Wai don meyasa yake mata haka? Kode don rashin kunyan da take mar ne yayi tunanin ramawa ta nan? Tayi tunanin haka a ranta. Ai kuwa ya zama dole ta basa hak'uri yanzu dukda cewa yin hakan bawai yana nufin bazata kuma mar rashin kunyan bane idan yayi mata abinda be gameta ba. 


  "Afzal- no" tayi saurin kad'a kanta "Ya Afzal dan Allah kayi hak'uri wallahi bazan sake ba."


  "Yaya?" Ya nanata a yayinda dariya me k'arfi ya ku6uce mar bashi kad'ai ba harta Sultan. "Ni ne Yaya? Guy kanajin yarinyan nan?" ya juya tare da tambayan Sultan nan suka kuma fashewa da wata dariyar barin ma Afzal da yake sark'ewa. Amal ji take kamar ta bisu da mari, ba abinda ta tsana kaman a tsaya ana yi mata dariya amman ya ta iya?


   "Wallahi a kullum kai Yaya na ne ai ko ido ma ma'auni ne" tayi saurin bashi amsa a rud'e. 


  "Kinga karki kaini inda Allah be kaini ba" ya fad'a yana composing kansa, "I don't have any sibling so am nobody's Yaya."


  "Wallahi a'a kai Yaya na ne kuma ai bazaka so a cutar maka da k'anwarka ba ko? Dan Allah ka fad'awa likitan nan karya ja min k'afa da zafi."


  "Nak'i" ya fad'a a takaice. 


  "Dan Allah Ya Afzal kayi hak'uri bazan sake maka rashin kunya."


  "Wancan kuma ke ya dama ki shigo suyi miki abinda ya kamata na maidaki gida I have things to attend to."


  "Dan Allah I'm sorry" ta fad'a tana kad'a kai. 


  "Doctor ka turo nurses su jawota jiki she's wasting my time."


  "A'a don Allah zan shigo da kaina."


  "Then make it quick" ya fad'a tare da galla mata wata mumunar kallo. "Kina fa 6ata min lokaci" ya kuma fad'i ganin bata motsa ba. 


  "Zan shigo zan shigo" ta fad'a a kid'ime sede fiye da minti biyu ta kasa takowa ciki. 


  "Ina nurses d'inne kam wai?" Afzal ya tambaya yana kewaya. 


  "A'a dan Allah zan shigo, wallahi zan shigo." Da hakan ta k'ariso ciki tana k'ingishi. "Please kace musu kar su ja min k'afan Ya Afzal."


  "Nak'i" ya sake nanata mata ko d'igon tausayi babu a tattare dashi. 


  "Bazan sake maka rashin kunya ba wallahi na tuba."


  "Guy pardon her please" fad'in Sultan dake tsaye daga gefe guda sede sanin taurin kai da zuciya irin na abokinsa yasan ba lallai bane ya jisa balle ya sassauta wa yarinyan. 


  "Make me" ya ce dashi tare da basa one of his nasty looks. "Ba ruwanka you better stay out of this, nurses take her in ku ja min k'afan nata sosai don idan yayi tsami ina tabbatar muku da cewa zanyi suing asibitin nan naku duk ku rasa aikinku kuma" ya razanasu. Haka nurses suka taho suka ja Amal se ihu take tana had'a Afzal da Allah amman yayi tamkar bada shi yake ba, idan ba hakan yayi mata ba bazata daina mai rashin kunyar ba. Bayan long draman da aka sha tsakanin Dr, nurses da Amal aka samu akayi retreating ciwon aka sa mata sabon bandage suka kuma jashi sosai kaman yadda Afzal ya buk'ata. Fuskan nan duk jirwayen majina da hawaye gabad'aya ta fita daga hayyacinta. 


  Dariya sosai Sultan ya saki lokacinda shi da Afzal suka shiga d'akin suka tarar da ita zaune bakin gado tana aikin share hawaye. Shima Afzal d'in dariyar ce ta k'eto mar amman kaman yadda ya saba bonewa hakan yayi. 


   "Lets go" yace da ita, da mamaki yaga ta mik'e ba gardama ba suratai. Lallai plan nasa yayi working. 


   "Triple A yaci ace an saya mata koda ice cream ne ta d'anji sanyi a ranta da wannan muguntar da kasa nurses sukayi mata" cewar Sultan lokacin da suka wuce ta downtown. D'ago ido Afzal yayi yana hangenta ta mirror yadda tayi tsit a motan kaman ba ita aciki. 


   "A saya miki kinaso?" Ya tambayeta da gan-gan yana wani murmusawa ta gefe. Idanunta takai inda nasa suke sannan ta kad'a kai a hankali "Karku damu nagode" ta fad'a a nitse ba Afzal kad'ai ba har Sultan yasha mamaki. Wani murmushin ya kuma sakewa sannan ya miyar da kallonsa kan hanyan. U turn yayi suka koma baya inda ya tsaya ya sai mata ice cream d'in. 


   Bayan ya kaita gida ya mik'a mata, jira yake ta amsa ta bud'e ta kwa6ar a k'asa tunda de wanka ta biya kud'in sabulu gashi ya kawota gida se kuwa yaga tana kad'a kai "Nagode ni zan wuce gida" ta sanar dashi kanta a sunkuye. 


    "Haba 'yan mata, yi hak'uri ki kar6a kinji?" Cewan Sultan cike da dabara. Ba ta kuma yin musu ba tasa hannu ta amsa tare da masu godiya sannan ta bud'e k'ofar. 


  "Sekuma gobe ko?" Cewar Afzal da gan-gan domin jin me zatace. 


  "Eh Allah kaimu" ta amsa calmly. Killer smile nasa ya saki ashede plan d'in yayi working, frankly ko shi be d'au ze iya yin abinda yasa akayi mata ba, but he had to it is the only way da zesa ta dena masa rashin kunya. 


   Tun daga ranan Afzal ya cigaba da d'awainiyar Amal kamar yadda yayi alk'awari. Mostly daga office bayan yaci lunch seya biyo ya d'auketa, wani sa'in sukan taho tare da Sultan mostly kuma shi kad'ai yake zuwa. Amal kuwa tun rana me kaman na ranan bata sake yiwa Afzal rashin kunya ba, cike da girmamawa da ladabi take gaishe sa duk sanda yazo, bata kuma fasa kiransa da Ya Afzal d'in ba, har abin ya zame mata jiki. Shima Afzal kullum daga clinic se sun tsaya a downtown sun sai mata ice cream. Ranan daya kaita dressing na k'arshe bayan ya kawota gida Amal tayita insisting cewa ya shigo ciki suyi final sallama da Mami tunda basu samu daman yin hakan ba d'azu kasancewar Mami bata gida daya taho. Sam baida niyyan shiga ciki again sede kuma yaga Amal nada point idan ba wani ikon Allahn ba kam ai ba abinda ze sake kawosa gidansu, yaci ace sunyi ban kwana da Mami. 


  "Kaji Ya Afzal kashigo ku gaisa da Mami please" ta kuma cewa ganin be ko motsa acikin motar ba. "Pleaseeee Ya Afzal." Juyowa yayi yana k'are mata kallo seji yake a jikinsa Amal is upto no good, dama chan bawai ya yarda da wannan d'abi'un da take portraying bane ace for the past 6 days ko rashin kunya bata mishi sema ladabi da biyayya. 


  "Amal?" Ya kira sunanta yana k'are mata kallo. 


  "Na'am" ta amsa tare da sunkuyar da kanta tana wasa da ledan ice cream daya siya mata. 


  "Wani abin kike shirin yi ko? Kinsan I don't trust you not even a single bit."


  "Haba Yaya har mey yayi zafi haka? Mey zanyi maka? Allah ba komai kawai inason kuyi bankwana ne da Mami kaga ai idan ba wani ikon Allahn ba bazaku k'ara had'uwa ba."


  Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauk'e "Let's go" nan ya kashe motan suka fice. Bayan sun k'arisa ciki Amal ta shimfid'a mai taburma tare da yima Mami da Papi sallama, bayan sun fito ta nuna musu ice cream da Afzal ya sai mata. Godiya sosai sukayi mishi sannan suka gaisa, da wayo ta saci jiki ta fice ba tare da sunyi realizing ba. 


  Pins da k'usosin da ta tanada ta ciro sannan ta k'arisa gun motan nasa, tayan baya ta sace dana gaba sannan ta gwada bud'e motar haushi taji datayi confirming a kulle ne if not da tayi niyyan kwa6ar mar da ice cream d'in acikin motar ne next time se taga idan ze sake sa mugayen likitocin asibiti su ja mata k'afa kai bama ita kad'ai ba koda wata ta daban. Seda ta ga tayoyin sun soma tsotsewa sannan ta kama hanyan gidansu Azee inda suka hau shan ice cream suna hira. Afzal kuwa bayan sun gama gaisawa dasu Mami sun d'an ta6a hira kad'an yace ze tafi, har wajen gida suka rakasa sannan suka koma ciki. Yana wasa da makullin motansa yana tafiya har ya isa inda yayi parking motan nashi, sam hankalinsa be kai ga patched tires guda biyun ba seda ya shiga yasa key ya shiga neman yin reverse yaji mota yak'i baya balle yayi gaba. Tirk'ashi, accelerator yata dannawa amman ina mota yak'i motsawa hakan yasa ya fito don duban inda matsalar take to his ultimate surprise yaga tire biyu duk a pache. Da farko yayi tunanin ko 'ya'yan unguwa ne suka mai d'anyen aikin nan amman tuna yadda Amal ta dage sam seya shiga sun gaisa da Mami yasa ya soma zarginta. 


   Tabbas yarinyan nan bata da kunya, upon duk d'awainiyyan dayayi ta mata da abinda zata saqa masa kenan? Lallai kuwa she's messing with fire. Ji yake kaman ya shiga gidansu ya nunawa Mami da Papinta abinda 'yarsu tayi mar amman tuna ba lallai ne su hukunta ta kaman yadda yakeso ba yasa ya fasa, yafison ya hukuntata da kansa, hukuncin da ko akan layi ta gansa seta canza hanya. Murmusawa yayi ya ciro wayansa daga aljihu tare da kiran mechanic nasa. Within 20 minutes ya iso sede ba pachi kad'ai Amal tayi ba, tiren gaban entirely yasamu matsala wanda idan ba ikon Allah ba se an canza shi gabad'aya. Anan de mechanic yamasa concluding cewa mota bazata gyaru a yau ba. Wayan Sultan ya kira don yazo ya d'aukeshi sede switched off yakeji. Be damu ba yashiga neman driver'n Daddy nan ma network yak'i barinsa. Abu fa kaman wasa se trying yake amman network yak'i bari call ya shiga chan kawai service ya d'auke gabad'aya.  Babban magana! Ji Afzal yake kaman ya k'urma ihu bayan nan yaje ya nemo duk inda Amal take a fad'in unguwansun nan ya nad'a mata na jaki. 


  Abu kaman wasa network yak'i dawowa gashi se ci yamma keyi, bayan d'an gyaran da mechanic yayi yakuma cire important parts na motan gudun kar 6arayi suyi gaba dasu dake motan ma se an barta ta kwana anan ya buk'aci Afzal daya bisa cikin keke napep daya taho sesu sauk'eshi a gida. Kallo Afzal ya tsaya yana mishi, wai da shi yake? Shi yake tsammanin ze shiga keke napep? Bawai yana nufin yafi k'arfin shiga bane sede bai ta6a shiga motan haya ba se gashi yau akan 'yar gudun hinirar can ze soma yin hakan? Lallai kuwa duk rananda Allah ya sake had'a path nasu seta gwammaci kid'a da karatu. 


  "Kayi shiru ranka ya dad'e yamma ne keyi fah" fad'in mechanic d'in. 


  "A'a kayi tafiyanka I'll wait a bit longer halan network ze dawo se in samu in kira gida suzo su d'aukeni."


  "Hmmm kana magana sekace ba a Maiduguri kake ba? Kade san idan network ta d'auke to se wani ikon Allah kesa ta dawo a lokacin da de hak'uran kayi muka kaika gida tunda ga keke free ne na yaron gidanmu."


  "Sekuma aka ce maka gudun kud'in nakeyi? Ni kawai kuje Allah kaimu goben."


  "Toh shikenan seda safe." Da haka suka fice a yayinda Afzal ya cigaba da tsayuwa wajen yana jiran dawowan network, can daya gaji ya bud'e motan nasa ya shiga se duban screen na wayansa yake ko network ze dawo amman ko alamun hakan babu. Around biyar da minti sha biyar na yamma 5:15pm Afzal ya soma losing hope, the earlier the better idan de ba so yake ya kwana cikin motan nan ba toh tun wuri ya kama hanya ya nemi a daidaita sahu ya shiga. Shi tunanin yadda ze fita cikin wannan kwamacalan unguwan ma yake, 'yan unguwa ba manya ba yara duk angle da mutum yabi se sun bisa da ido suna gulma k'asa-k'asa. Cike da takaici ya shiga takawa trying his best not to get distracted. Har bus stop yakai sannan ya soma ganin napep nan ma duk masu passengers aciki ne suke wucewa shi kuma ya rantse saidai dare yayi masa da yashiga me passenger. Yayi kusan minti sha biyar sannan ya samu empty ya shiga, kowani pothole (gargada) aka shiga har cikin k'wak'walwansa yake ji. Se yanzun ya ke sake yima Allah godiya da duk wani abinda ya mallaka masa badon wai yafi sonsa bane akan sauran bayinsa kokuwa don ya kai se don haka yaso abinsa. Isansu gida keda wuya Afzal gabaki d'aya ya galabaita d'ari biyar ya mik'a wa me mashin d'in inda yake tambayarsa ko yanada naira d'ari se ya bashi d'ari hud'u. 


  "Ka rik'e duka ko kayi sadaqa da abinda ya rage" ya sanar dashi rai a murtuk'e sannan ya k'arisa ciki aka bud'e mishi gate. Lokacin har an sauk'o daga sallan Maghrib, Abba ya tarar a waje shima yana shirin fita da driver a gaba yana sauri don bud'e mishi k'ofa. 


   "Ha'a wancan ba Prince bane?" Abba ya tambayi driver'n yana k'arewa figure'n Afzal kallo don tabbatar da zancen nasa. 


   "Shine Alhaji" driver'n ya masa confirming. 


  "Prince ya haka? Ina ka shige?" Abba ya tambaya alokacin da Afzal ya k'ariso inda suke. "Network ya d'auke muna ta neman ka amman bai shiga, ina ka shiga ne? Ina motanka kuma?"


   "Hmm Abba long story motana yayi pachi da keke napep ma na k'ariso gida" ya fad'a tamkar zeyi kuka. Dariya ce ta kauce wa Abba har yana neman sark'ewa, ina irin dariyan nan da alhazai keyi ana yi ana jan nishi? Irin shi Abba yay tayi da k'yar tukun ya samu ya tsagaitar. 


   Lallai ma kuwa Afzal ya furta a ransa yana me mamakin Abba yanzu dariya zeyi masa akan ya tausaya masa? Ai yasan Ummi bazata mishi haka ba. 


   "Ahhh it's good it's good" fad'in Abba yana neman kame dariyar da ke sake son kauce masa "Kaga ko a babu yau kayi sabon experience koba haka ba?" Saidai shiru Afzal yayi bece komi ba ga girar nan ya had'esu kum waje guda. "Toh ka kwantar da hankalinka wuyan daka sha yau d'innan tattare yake da alkhairi."

   Alkhairi de? Ya nanata a zuciyansa. Kallon Abba ya tsaya yi a yayinda ya zira hannu a aljihu tare da ciro wata k'aramar pack. 


   "Gashi open this" ba gardama ya amsa ya bud'e key'n mota ya tarar aciki. Toh fah! Ido ya d'ago yana kallon Abba cike da mamaki da neman k'arin bayani. 


   "Danna security ne kuma baka iya ba Prince?" Ya tambeysa jokingly. Nan ya danna inda d'aya daga cikin motocin da suke fake a parking lot tayi k'ara, da sauri ya maida kallonsa wajen tare da kuma dannawa don tabbatar da wace mota ce tayi k'aran. Sabuwar 2017 Mercedes Benz ce C43 AMG biturbo k'al acikin leda yaga tayi wuta, fara tas an k'ayata ta da black satin and ribbons. 


  "Abba!" Yayi exclaiming cike da mamaki bil adad alokaci guda ya nemi bak'in cikin da Amal ta tusa masa ya rasa. Shi abinda yafi basa mamaki ma  shine yadda Abba yasan wannan ne motan da yake tason ya siya tun watanni uku da suka shud'e wanda yake dai-dai da lokacin da motar ta fito. Kawai tuna lokacin da ya tura wa Sultan pic d'in yake, har yake cemar ga motan da yakeson ya siya toh har yaushe Abba ya shiga zuciyansa yasan sabon mota yake buk'ata when ko shekara biyu ma na wajensa beyi ba?


  "Abba! Mota ka siya min?" Ya sake tambaya full of wonder. 


   "Yes Prince ai na fad'a wa Umminka ta sanar da kai cewa na tanada maka tsaraba fatana de Allah sa tsaraban ya kar6u kuma ya burgek-" Afzal be basa daman k'arisa maganan daya soma ba ya rufe sa da runguma tsan-tsan murna da farin ciki. Da murmushi kwance fal a fuskan Abba ya zagaye hannayensa bayan d'an nasa shima, hugging him back. 


   "Abba thank you so much! I don't know how to express my gratitude walalhi you made my evening" ya sanar dashi ba tare da ya katse rungumar ba. 

  "Am glad you like it son" se anan Afzal ya sake shi sannan ya juya yana kallon motan. 


  "Nasan so kake kaje kaga cikin motar kaman yadda nima nake son fita yanzu inada conference da colleagues d'ina so ina fatan this year will be convenient for you ko?"


  "For what Abba?" Ya tambaya a takaice da farin ciki kwance a birnin zuciyansa. 


   "Hajj nakeson kaika inason ka zama Alhajin kanka kaima Prince" Dad'i ninkin ba ninkin na d'azu ne ya ziyarci zuciyan Afzal wai kam ya akayi duk abinda yake dashi in mind Abba ke shirin miyar masa dashi reality? Tabbas ranan sunyi hirar nan da Ummi na cewa yanason yayi aikin Hajji wannan shekaran saboda bai ta6ayi ba a kullum yaje Saudi Umarah kawai yakeyi. Ji yake as if duniyan ma tayi kad'an ta d'aukesa don murna. 


   "Abba bazan iya tuna when last nayi kuka ba but with what you're doing you're making me want to. Abba this is the perfect time da nakeson yin Hajji har nayi discussing da brand manager namu ma."


   "Toh Alhamdulillah seka shirya idan Allah ya kaimu lokacin seku tafi tare da Umminka."


   "Abba thank you so much, Allah miyar maka da gidan aljannah ya k'ara bud'i kuma."


   "Ameen Prince." 


  "Saide bansan me nayi dana cancanci kyautuka haka ba."


  "Prince farin cikin daka sanya ni da ka amince da k'udurin mahaifin y'ar nan kad'an ne daga cikin wanda kakeji yanzu. Nide ba abinda zance se Allah cigaba da yima albarka ya baka 'ya'yan da zasu kula da kai su kuma farinta maka kaman yadda kake min ko fiye da hakan ma."


  "Ameen Abba thank you so much."


  "You're welcome barin wuce kar na makara."


  "Toh Abba ka dawo lafiya" bayan motan Abba ya fice Afzal ya k'arisa gun sabuwar motarsa har ya shige ciki seya tuna be d'auke ta a hoto ba, nan ya fito ya d'ad'd'auka sannan ya koma ciki ya shiga dubanta. Ba don yana so ba se don beyi sallan Maghrib ba yasa ya sauk'o ya nufi site na Ummi, alokacin tana bayi tana wanka. Guest toilet ya fad'a yayi alwala sannan yayi sallah, bayan ya idar yayi azkhar nasa sannan ya wuce d'akin ta tare da knocking. Tana amsawa ya shiga inda ya tarar da ita zaune kan stool na dresser side tana kwalya. 


    "Oyoyo my Prince ina ka shige haka? Gabad'aya ka tada min hankali" ta fad'a tare da kewayowa tana kallonsa. 


  "Ummi you can't believe this!" Abinda ya soma ce mata kenan ko ta kan abinda tace beyi ba balle ya gaishe ta. 


  "An saya wa baby na mota!"


  "Yes!" Yayi exclaiming "So you knew?"


  "Eh mana ai surprise ne so did you like it?"


  "Yes!" Ya kuma exclaiming yana zama daga bakin kan gadon ta inda take zaune akan stool d'in. "Ni nama rasa ya Abba yayi yasan this car in particular nakeso wallahi kinsan tunda ya fito naketa budgeting yadda za'ayi in siya."


  "Thank your friend then."


  "Wa kenan Sultan?"


  "Shi de, shi Abba ya kira ya tambayeshi ko yanada masaniya akan abinda idan aka baka shi zakaji dad'i sosai ya bada amsa da wannan AMG."


  "Allah sarki Sultan, I feel like the happiest soul alive."


  "Ga kuma zamuje Hajj, it's a wrap!"


  "Ummi please thank Abba once more."


  "In shaa Allahu Prince."


  "Toh tashi muje kiga cikin motan kinga panaromic roof d'in kuwa? Da car radio d'in? My goodness! Wani abun ma sekinga gearbox d'in ga wani k'arar da take badawa kafin engine ya tashi" ya fad'a sounding happy.  


  "Tsaya to in gama jan girar nan se muje." Jirarta yayi bayan ta gama suka fice inda Ummi ta rik'a sawa motar albarka. 

  Suna cikin cin dinner ne ta tambayesa inda motarsa take kasancewar bata gani a inda ya soma parking ba. 


   "Kede kar ki tuno min da batun motan can kinsan kuwa acikin keke napep na dawo gida yau?" Dariyan da Abba yayi masa haka ma Ummi ta zauna tayi shide ya rasa abin dariya anan, "Wayaga Prince acikin a daidaita sahu" se ta kuma k'yalk'yalewa da wata dariyar. 


  "Seki tayi ai" ya fad'a a fusace tare da jan k'aramar tsuka. Bayan ta gama neman tsokanan nasa kwatsam sak'on da Abba ya bata ta isar masa ya fad'o mata. 

  "Yauwa Prince Abbanka yace in tambayeka."


  "Me fah?"


  "D'azu Abban Nazeefah na nan ai-"


  "Ni kinma 6ata min mood wallahi" ya katse ta yana mey had'e girarsa. 


  "Toh Prince ka manta ka riga ka amince da auren ne?" Ta fad'a a hankali gudun kar ransa ya kuma 6aci. 


  "Nikam ba yanzu ba" ya amsa a takaice. 


  "Toh se yaushe?" Shiru yayi be sake cewa komi ba se faman latsa wayansa yake yana going through memes da Sultan yayi mentioning nasa a twitter. Hannu tasa ta k'wace wayan "Ummi please give it back" ya fad'a da sauri. 


  "Ina maka magana kana latsa waya wallahi ko ka bani takamammen rana ko in bawa Abbanka duk wanda yayi min."


  "Toh kiyi mana ni ina ruwana ban damu da yarinyan ba balle aurenta ya zame min matsala ni bani wayana in wuce site d'ina."


  "Toh fah!" Ta fad'a tare da ta6e baki "Prince ka rufa mana asiri don Allah."


  "Da nayi mey?"   


  "Bade shirin wulak'anta yarinyan nan kake ba bayan anyi auren nan, don Allah kar kayi haka."


  "Kekam da assumption Ummi! Allah kyauta. Meyasa zan wulak'anta ta? Just pass me my phone" ba gardama ta miyar mishi "Toh yaushe kakeso ayi bikin? Kaga se su soma shiri suma, idan ranan is not convenient for them kuma se a zauna ayi adjusting koya kace?"


  "Toh why not su suyi fixing date d'in da kansu nifa adena tak'ura min."

  

  "Amman kai kam ba a iya maka ba wallahi sam bakada mutunci, naga ai girmama ka mahaifin nata yayi har yace kaine zaka za6i rana kasa amman kake wannan shagantakar."


  "Toh naji I'm sorry" ya fad'a tare da sauk'e nauyayyar ajiyar zuciya "Bari bayan mun dawo daga Hajj idan Allah ya kaimu rai da lafiya."


 "Toh ko kai fah? Kaga bayan babbar sallah se a d'aura ko?" Ta tambayesa cike da gastine. 


   "A'a k'ullewa ba d'aurawa ba" ya mayar mata da amsa. 


  "Me dafa maka abinci Prince ni zaka bawa amsa?" kafin tace zata mik'a hannu takai masa bugi har ya mik'e yana mata dariya


  "Shegen dogin k'afa a wajen" gwalo yayi mata sannan yace, "Ni zan wuce site d'ina it's been a hectic day zanyi Sallah in kwanta idan Abba ya dawo ki sake yi mashi godiya, goodnight I love you."


  "Sleep like a baby" da haka ya wuce site nasa. Bayan ya gama duk wani abinda zeyi ya d'ale gado ya kwanta dai-dai nan Sultan ya danna masa kira bayan sun gaisa yake tambayansa how went his day. Tsuka yaja sannan yace "Kaide ka barni da 'yar gudun hijirar can."


  Bayan dariyan da Sultan ya narka ya buk'aci Afzal da ya basa labarin meya faru. Nan ya labarta mai komi inda Sultan yata dariya kaman zararre yana mamakin guts na Amal, sam idan mutum ya ganta baze ce zata iya yin abubuwan da Afzal ke fad'i a kanta ba. 





  RANA D'AYA 

#RD

 Love... king miemiebee👄✨

[12/08, 22:25] ‪+234 907 483 8352‬: 🎀🎀🎀                 🎀🎀🎀

                🎀❣🎀

                   ❣❣


  💦💦                      🍃🍃🍃          

           *RANA D'AYA!*

  💦💦                      🍃🍃🍃

  April, 2018

 beeenovels.blogspot.com


     _Written by Miemiebee👄_




   *PAGE 0⃣7⃣*





     Rana bata k'arya saide uwar d'iya taji kunya. Yau ana sauran sati uku azumi kenan. Afzal ne da Sultan zaune bisa d'aya daga cikin teburan da suke baje acikin office nasu Afzal a ground floor suna hirar match da akayi jiya tsakanin Roma da Barcelona wanda aka sha Barcelona wane ayi musu kuka. Ana cikin haka ne Afzal da hankalinsa ya duk'ufa a waje yana kallon wasu 'yan mata biyun da suke tsaye da wani d'an saurayi a bakin gate d'in se rashin kunya suke zuba mishi barin ma me d'an haske me maroon hijabi wacce ke tsaye dab gabansa wane zata cukume masa collar. Dukda cewa besan meke faruwa ba alamu sun nuna me marron hijabin na tare wa k'awarta wacce ta kasance me talle fad'a ne. Abu kaman wasa fad'a yak'i ci yak'i k'arewa daga bisani kawai me maroon hijabin tasa hannu ta wafce wani abu kaman kud'i daga hannun saurayin wanda kafin tace zata sa gudu har ya cafko ta, ita ko a garin k'watan kanta ta ture wani glassy sign board me yin wuta-wuta dake gefen gate d'in wanda ke d'auke da sunan bankin aciki. Abu ne wanda ko ba a fad'a ba mutum yasan zeyi bala'in tsada saboda yadda yake a tsare da jan ido. Ba shiri securities sukayi wajen duk anan Afzal na kallonsu daga ciki. 


  "Dude wai meke faruwa ne kam achan?" Sultan da se yanzu hankalisa ya iske su ya tambaya. 


  "Let's go find out" ya amsa shi inda suka miqe suka nufi wajen. Juyowan da 'yan matan zasuyi kawai suka had'a ido hud'u da Amal. Ashe itace wacce ke sanye da maroon hijabin, wacce ke ta rashin kunya iya gadaman ranta, lallai kuwa ta shirya biya musu sign board. Idonsu na had'uwa Amal taji cikinta ya d'au ruwa a yayinda zuciyarta ta har6a, for a second ta nemi numfashinta ma ta rasa tuna abinda tayi masa last had'uwansu. Yau shikenan kashinta ya bushe ita a iya tsammaninta bazata sake had'uwa da shi ba se gashi Allah yayi proving nata wrong today.


   "Good day Sir" securities d'in duk suka gaishe shi. Wani har6awa bugun ziciyar Amal ya kuma yi jin securities sun kirasa da sir bade anan Afzal ke aiki ba yau nata ya k'are. 


  "What's going on in here?" Ya buk'ata cikin tattausar murya a yayinda yayi banza da Amal sam be nuna ya ta6a wayanta ba. 


  "Sir wannan yarinyar ce ta ture sign board d'innan ta biya kud'in kuma tak'i wai sam ba ita ta ture ba bayan kowa shaida ne anan itace ta ture so muna shirin yin police station ne da ita" d'ayan security'n yayi bayani. Take Amal taji cikinta ya sake to the mention of police station, yau ina zata sa kanta? Police station? Gidan yari fa kenan! Danqaree!


  "Wallahi bani na buge ba" ta kuma fad'a. 


  "Bake kika buge ba?" Tambayar securitin itade k'awar nata me tallen gyad'a ko uffan bata kuma cewa ba har yanzun gudun kar suce zasu had'a da ita akai police station d'in. Dama ita tun d'azu tace wa Amal su bar bawan Allan kawai da Allah tunda ya rantse yace shi baze basu kud'insu ba, Allah ze isar musu amman don rigima irin na Amal tak'i. 


  "Eh mana ina wannan ne ya jani baya a garin k'watan kaina se abin ya fad'i wallahi ni bani na fasa muku abunku ba don haka ba abinda zan biya" ta fad'a confidently dukda cewa chan ciki ta gama tsurewa. 


  "Se mu gani, se muga idan mukaje police station d'in sukace ki biya ko zaki fad'a musu hakan" Ganin fa dagaske police station d'in suke son yi da ita don kuwa gashi har sun kawo mota Amal ta soma jin fitsari nan take. Ubanwa zeyi bailing nata idan suka kaita chan d'in yanzu? Tasan ko had'a sama da k'asa zatayi Mami ko zuwa dubanta bazata yi ba Papi kuwa baida kud'in bailing nata. Yau kashin ta ya bushe, ashe da taji maganan Falmata sun ja mar Allah ya isan kawai. 


   

  "Kai meya faru ne?" Afzal da ya nisanta ya tambayi yaron. 


  "Kud'in gyad'an su nikeson basu suka k'i amsa wai sam suna bina bashin d'ari biyu nikuma banda masaniya akan hakan sharri kawai suke shirin min musamman wannan yarinyar" ya nuna Amal. 


  "Wallahi bawan Allah bazaka gama da duniya lafiya ba, kullum kata cin gyad'an nan a bashi kace bakasan da hakan ba?" Amal data katsesa ta tambaya. 


  "Yanzu akan N200 shine kuka rusar da wannan board d'in?" Afzal ya kuma tambayansa. 


  "Oga ni bani na rusa ba itace agarin wafce hannunta ta ture."


  "Yanzu ka basu kud'in gyad'an su" yace dashi. 


  "Wallahi ni basu bina kud'i ga kud'in gyad'ansu na yau N50."


  "Nace ka basu kud'in su" Afzal ya kuma nanatawa. 


  "Gaskiya ni bazan bada komi ba saboda basu bina komi."


  "Shikenan kayi tafiyanka" hannu ya sa a pants pocket nasa ya zaro wallet nasa tare da miqa wa Falmata d'ari biyar. 


  "A'a don Allah ka bari ni na barshi da Allah dama tun d'azu nike cewa Baby da ta barshi da Allah amman tak'i."


  "Karki damu amshi."


  "Toh ai banida canji."


  "Don't worry keep it." Hannu bibbiyu ta miqa ta amsa, "Nagode Allah saka da alheri Baby mu tafi."


 "Ku tafi? Ku tafi ina?" Afzal yayi saurin tambayarta tare da kewayo da kallonsa akan yaron "Kana iya tafiya kema me gyad'a kina iya barin nan."


   "Nagode k'awata fah?" Ta tambaya. 


  "Bakiji me securities d'in sukace bane? Police station zasuyi da ita in kuma kinason binta ne fine."


  "A'a a'a!" Tayi exclaiming da mamaki tana ja da baya, "Baby ki bisu zanyi sauri inje gida in sanar da Mami halin da ake ciki."  

   Lallai ma Amal ta furta a ranta yanzu tafiya Falmata zatayi ta barta bayan ta sanadinta komi ya faru? Hmm amman ba amana. 


  "Falmata don Allah karki tafi ki barni, Ya Afzal don Allah kayi hak'uri wallahi ba da gangan na buge ba" ta juyo tana kallon Afzal da maraicaccen fuska ko kunya bata ji ba. 


  "Securities ku tafi da ita make sure she pays for this or simply lock her up, Sultan lets get back in" ya yi declaring ba tare da ya kalli koda direction na Amal ba. 


  Da sauri ta shawo gabanshi "Don Allah karka min haka kayi hak'uri na tuba."


  "Get out of my sight!" ya sanar da ita a tsawace cikin tattausar muryan da yasa ta fashewa da kuka. "Ya Afzal don Allah kayi hak'uri na tuba, wallahi na tuba." Shiru yayi na 'yan lokuta sannan ya nisanta, "Na farko, I don't own this building kinyi 6arna dole ki biya there's nothing I can do."


  "Eh nasan ba naka bane amman alamu sun nuna kana da matsayi anan don Allah ka basu hak'uri su barni in tafi kafi kowa sanin cewa Mami da Papi basu da k'arfin bailing d'ina, ba don hali ba amman don Allah ka rufa min asiri Ya Afzal."


  "Sultan mu tafi mana me kake jira ne wai kam?" Yayi banza da ita. 


  "Ya Afzal don Allah karka min haka kayi hak'uri I'm so sorry" nan ta kuma fashe da wani kukan a yayinda hawaye ke ambaliya a fuskarta sede ko kallonta Afzal beyi ba balle tausayinta ya kamasa. 


  "Guy kayi mata hak'uri please I will settle the bill" fad'in Sultan da Amal ta basa tausayi dukda cewa beji dad'in abinda tayi ma abokinsa da mota ba. 


  "Wallahi tallahi kade ji rantsuwa ko guy? Idan har kayi bailing yarinyan nan ban yafe ba" Afzal ya sanar da Sultan in a serious tone, ai dama ya fad'a seya rama abinda ta yi masa. 

"Let's go" yace da shi, ba musu Sultan ya shiga binsa ganin yadda ran abokin nasa ya 6aci. 

  

  "Afzal please pity the girl" Sultan daya matso kusa da Afz ya sanar daahi yadda ba wanda ya jisu. Alokacin har securities sun soma kokuwa da Amal suna k'ok'arin sata cikin mota sede sun garara saboda k'in basu had'in kai da tayi. 


  "Pity her fa kace? Ko ka manta abinda tayi min da mota ne ranan?" 


  "We'll resolve everything yanzu dan Allah kayi mata hak'uri kar ka 6ata mata future kade san yanzu a cell zasuje su jefa ta har se idan ta biya kud'in abin nan kuma sanin kanka ne iyayenta basuda k'arfin nan" a hankali maganganun Sultan suke tasiri jikin Afzal se de still bai jin ze iya yafe mata. "Ince masu su dakata?" ya tambayesa a hankali, shirun da Afzal yayi ya bawa Sultan daman tsaida securities d'in, ba gardama sukayi hakan. 


    "Wai kam Sultan ka manta abinda tamin ranan ne?" Ya tambaya ransa na tafasa. 


  "Ni? yaushe kuma?" Amal da ta jiyo sa tayi saurin tambaya duk ta kid'ime. 


  "Oww k'arya kuma zaki sake yimin?" Nan ne ya juyo yana galla mata hararan daya sata had'iyan miyau ba shiri. "Guards what're you guys still waiting for? Kuzo ku jata mana ko sena kira branch manager'n tukuna yayi firing naku duka?" Ya tambaya yana galla musu harara. 


  "No Sir abokin ka ne yace a saketa."


  "Ni kuma nace take her away."


  "Dude please kayi mata hak'uri" cewar Sultan again. 


  "Ya Afzal don Allah have mercy on me, na tuba ka yafemin" ta fad'a tana kuka sosai a yayinda securities suka shiga janta. Ido ya musu suka saketa sannan ya kirata. Har tana neman cin tuntu6e ta k'ariso tana mey share hawayenta da k'asan hijabinta. 


  "Me kikayi min da mota ranan?" 


 "Kayi hak'uri don Allah na tuba" ta amsa cike da fargaba. 


  "That is not what I asked me kikayi min da mota ranan?"


  "Na maka pachin taya amman na tuba."


  "Meyasa? Ni sa'an kine?"


  "A'a don Allah kayi hak'uri na tuba."


  "Kinsan nawa ne wancan abinda kika rusan?" Ya tambayeta had'e da d'age gira d'aya, kai tayi saurin kad'awa. "It is nothing less than eighty five thousand (85k)" ya sanar da ita. Ido ta zaro waje wane 6eran da aka kama yana sata. 


  "Wallahi Papi baze iya biya ba don Allah ka basu hak'uri."


  "Hak'uri won't fix anything the only thing that could fix that mess is ayi replacing da sabo."


  "Ya Afzal wallahi ko nan da shekara ka bani bazan iya siyan sabo ba."


  "Then tun da wuri kisan yadda zakiyi hakan kokuma ki shirya zuwa gidan yari." 


   "Ya Afzal don darajan Allah ka taimaka min ka rufa min asiri ka basu hak'uri."


  "Kinsan wani abu? Inda wata ce chan ta rusa koda k'awar kice for example da tuni na bada kud'i an sai sabo, kinsan dalilin dayasa bazan taimake ki ba?"


 "Saboda na maka rashin kunya, na 6ata maka mota nayi maka abubuwa kala-kala amman don Allah kayi hak'uri wallahi ban k'arawa na tuba."


  "Jeki kira k'awarki dake la6e achan" ya buk'aceta. Falmata na ganin Amal na nufo inda take la6e ta shiga neman hanyan gudu da k'yar Amal tasamu ta amince ta biyota. 


  "Gata nan" cewar Amal. 


  "Dude kana cin abin nan ko?" Afzal ya tambayi Sultan yana nuni da soyayyen gyad'an dake kan Falmata wanda 'yan Maiduguri ke kira da mandawa. 


  "Yes?" Sultan ya amsa sa cike da neman k'arin bayani. 


  "Alright, k'irga gyad'an nawa ya rage duka" ya buk'aceta, nan ta sauk'e tray natan ta k'irga "Na d'ari biyar da hamsin ne N550."


  "Good amshi tray d'in Amal" ba musu tayi yadda ya buk'ata. 


  "Good inason ki zauna- no ki tsaya anan k'ark'ashin ranan nan ki shiga gyara gyad'an nan kina tarasu cikin leather daban, idan kin gama ki kawo min ciki and mind you ko alaman 6awo na gani aciki aikinki ia ruined zan saki a hannun securities d'innan suyi duk abinda sukayi niyya dake" ya fayyace mata muryansa ko alaman wasa babu bale Amal tace almarai yake bata. Ba ita kad'ai ba harta Sultan da Falmata seda suka sake baki ganin yawan mandawan da Afzal ke shirin sa Amal gyarawa. Mandawan da ko leda d'aya akace mutum ya gyara seya galabaita. 


  "Duka na kan tray d'in?" ta tambaya cike da rashin yarda. 


  "Yes you heard me right, haka ma zakiyi gobe da jibi in fact for a whole month or two only then zan amince in biya kud'in board d'incan da kika rusa. Kekuma Falmata ko?" Ya juyo kan k'awar nata "Daga yau kina ajiye min gyad'an nan naki na d'ari biyar and make sure kin taho tare da Amal, kina ji na?"


  "Eh, eh naji" ta amsa. 


  "Good oya kekuma me kike jira da baki fara gyarawa ba? ga chan tap (famfo) a chan go and wash your hand da akwai sanitizer a gefe kiyi sanitizing hannunki. Securities you can go back to your posts zanyi handling mess d'in."


  "Alright sir" suka amsa tare da ja da baya. 


  "Toh Ya Afzal amman naga kaman gyad'an d'ari biyar yayi wa Ya Sultan yawa ina laifin in 6are mishi na d'ari??" Amal ta tambayesa cikin best lady like manner nata. 


  "Sauran inga kina tayata kekuma" yace da Falmata totally ignoring Amal, "I'll be inside duk abinda kukeyi anan zan hangoku daga ciki don't think of messing with me, guy let's go."


  "Mu nemi inuwa toh mu zauna" cewar Amal tana mey neman inda akwai rumfa. 


  "Baki ji me nace bane? Nan k'ark'ashin ranan nakeso ki tsaya kiyi abinda na saki, ko jinguna naga kinyi jikin bango toh zan fasa biyan kud'in in kuma sasu su kaiki police station."


  Miyau ta had'iye "Allah sarki don Allah ka tausaya min." Be sake yi ta kanta ba shida Sultan suka wuce ciki. Tun Falmata na iya juran taya Amal tsayuwa k'ark'ashin ranan taga bazata iya ba ta nemi inuwa ta zauna, Amal baiwar Allah se gyaran gyad'a take ko 6awo bata bari kaman yadda Afzal ya buk'ata. Tayi leda shida (6) ta soma jin jiri saboda zafin ranan, ji take kaman ta tsala ihu amman ba daman yin hakan. Haka abin tausayi seda ta kwashi kusan  awa biyu k'ark'ashin rana me tafasar da k'wak'walwar mutum sannan ta samu ta gyara duka. Alokacin har ta gama kod'ewa idanunta sun kad'a sunyi ja, bayanta wane ze 6alle se gumi da zufa take had'awa. Security tasa yayi ma Afzal magana nan ma seda ya gama ja mata aji sannan ya fito da wani saucer a hannunsa kad'an daga cikin gyad'an ya d'iba ya kira Falmata ya mik'a mata ragowan "Ga wannan kici wanda zaki iya ci sauran ki kai wa k'annenki a gida kokuma kiyi sadaqa dashi a layi. hungo kud'in ki."


   Baki bud'e cike da mamaki Amal ta tsaya tana kallonsa. Yanzu duk uban wahalan nan d'an abinda ze d'iba kenan? Ina laifin ita data sha wuyan gyaran ne ma ze ce mata ta tafi da ragowan amman seya kama ya bawa Falmata??? Ji take kaman zuciyarta zata k'one don tafasar da takeyi. Na farko duk a sanadin Falmata ne wannan abu ya faru se gashi yanzu ta kwashi awa biyu tana aikin sarrafa gyad'a daga k'arshe kuma a bawa Falmata wai taci? Riba biyu fa kenan, ga kyautan sarrafaffen gyad'a ga kuma yanzu ba se tayita yawo a gari tana talle ba lokaci guda za'a siye mata fiye da rabin gyad'anta. Lallai kuwa daga yau tayi hankali wallahi duk wani abinda bai shafeta ba ba ruwanta dashi.


   ***

   Kaman yadda Afzal ya tsara haka Amal da Falmata suka zo ma yau, yadda akayi jiya haka a ka kuma yau, gyad'an d'ari biyar (500) tas ta sarrafa tsaye k'ark'ashin rana me uban tafasa k'wak'walwar mutum, sanin kowa ne yadda ranan Maiduguri yake daban da na kowani gari. Bayan ta k'are ya fito ya bawa Falmata duka mandawan yau kasancewar Sultan baya nan shi kuwa be iya ci ba, itade Amal k'una ne kawai zuciyarta batayi idan taga yabawa Falmata gyad'an dake d'aukanta awa biyu ko fiye tana gyarawa. 


    Anyi hakan na kwana hud'u Amal taga fa idan ta cigaba da haka toh wallahi setafi gawayi bak'i, ga shi tun ba'a je ko ina ba bayanta ya soma mata ciwo, kuma gashi tasan taurin kai da zuciya irin na Afzal ko mutuwa zatayi ta sake dawowa ba canza mind nasa zeyi ba tun akan abinda ya faru a asibiti ranan ta gano hakan, ta sani ras seta cika wata ko watanni biyu da ya yanke matan sede dukda hakan bazata kariya ba zata basa hak'uri. 


    Washegari bayan sun isa ita da Falmata sega Afzal na fitowa daga office da alama masallaci ze zarce yayi sallah, bayan ta jira ya idar ya fito ta taresa ta shiga basa hak'uri harda guntun hawayenta amman kaman yadda tayi tsammani haka ko kallonta beyi ba balle ya tausaya mata yaja baya da wannan punishment. Haka tana kuka ta koma k'ark'ashin ranan ta cigaba da gyaran daga inda ta tsaya. Bayan ta iso gida ta tsaya a shagon Usama ta sai 40 leaves. Bayan sallan Isha ta d'an huta sannan ta d'au littafin da biro ta shiga rubuta, "I'M SORRY YA AFZAL I WILL NEVER DISRESPECT YOU AGAIN" layi-layi tun daga fejin farko har seda ta kai na k'arshe, ko bacci bata samu tayi ba daren ranan se bayan sallan Asuba data gama. 


   Yau bayan ita da Falmata sun isa office nasu Afzal me gadi ya isar mata da saqon da Afzal ya bada a mik'a mata, na cewa baya nan ya fita meeting amman yasa asa mata ido kar ta kuskura ta ko tsuguna bale tayi tunanin shiga inuwa kokuma ta rok'i Falmata data tayata. Bayan kuma ta gama gyarawan ta d'iba rabi ta bawa Falmata rabi ta ajiye masa. Hakan tayi bayan tagama ta had'a masa rabin da littafin data siyan ta bawa me gadi sannan suka fice. 


  Se chan kusan yamma Afzal ya dawo office, bayan me gadi ya miqa masa saqon ya buk'acesa littafin kuma daga gun waye ne? A takaice ya amsa shi yace daga gun 'yan matan ne. Documents nasa ya tattara ya dawo gida inda ya kaiwa Ummi gyad'an. 


  "Prince mandawa dayawa haka kuma gashi har an 6are an gyara" fad'an Ummi tana k'ok'arin kai amount data d'iba baki. "Gaskia nagode."


  "You're welcome lemmi rush to my site."


  "Kaifa bazaka ci ba? Gashi ya soyu dai-dai be k'one ba."


  "Nahh ban iya ci ba."


 "Yo baka ta6a ci ba dama taya zaka iya? Kade gwada kaji Allah da dad'i."


  "No thanks" d'iba tayi a hannunta "Bud'e bakin in sa maka kaji" seda tayi dagaske ta samu ya bud'en tasa mishi se kuma ya mishi dad'i ashede for all these he's been missing alot. A saucer ta d'iba masa ya wuce site nasa dashi. Bayan ya watsa ruwa ya fito da alwala sannan ya shirya yaje masallacin unguwa yayi sallah. Wayansa ya had'a a charging ya shiga viewing Instagram feeds nasa yana jefa gyad'an time to time a baki. Chan ya mik'a hannu ya jawo littafin da me gadi ya basa na cewa Amal ce tace a bashi. First page d'in ya bud'e ya soma cin karo da kalmomin hak'urin data rubuta. Murmusawa yayi tare da flipping next page d'in nan ma haka, tsallakawa yayi ya kai tsakiya yaga har nan hak'urin take basa. Murmushin yake har yanzu ya shiga bi daga farko zuwa k'arshe sannan ya mik'a ya ajiye inda yake keeping important documents nasa. Ashe tasan yin rashin kunyar da take ba kyau amman takeyi, da kyau. 


  A tsammanin Amal washegari idan taje ze ce mata ya yafe sauran punishment d'in ta tafi sede ta tarar da opposite d'in hakan. Sam yi yayi wane saqon nata be iske sa ba, don dad'in da gyad'an ya masa jiya yau har cikin office nasa ya shigo dasu da ta gyara kad'an se ya kwashe yaci, kafin su hankara Afzal ya cinye gyad'an d'ari uku da ashirin (N320) shi kad'ai. Sai the following day ne bayan sunzo ya saye gyad'an har Amal ta fara gyarawa yace masu ta bari su tafi ya yafe mata. Dad'i sosai taji ashe de yana sauraron hak'uri lallai kuwa ta kama kanta kar ta sake yi masa abinda ze fusatar dashi if not itace zatayi bearing consequences. Don ta lura duk wani iskanci da rashin ji da take ji dashi Afzal yana gaba da ita. 


   Tun daga ranan kullum Falmata ke kawo wa Afzal gyad'a wani sa'in Amal kan biyota while most of the times ita kad'ai take zuwa. Anytime kuwa suka zo tare da Amal a bakin gate take la6ewa gudun kar ko kallonsa tayi yace ze bata wani punishment d'in, abu kaman wasa Afzal ya zama addict na gyad'an Falmata har idan gari ya waye beci ba baya jin dad'i. 


   Rana d'aya ko mey ya buga kan Amal kawai ta buk'aci Falmata da ta bata mandawan Afzal, zama tayi ta gyara masa su tsaf ko 6awo d'aya babu sannan ta baiwa Falmata da ta kai masa kaman kullum yau ma ta tsaya bakin gate tana jiran fitowarta. Sosai Afzal yasha mamaki bayan da Falmata ta mik'a mishi gyararren gyad'a cewa kuma daga Amal ne. Lallai yarinyan tayi hankali yayi tunanin haka a ransa kode she is upto something not good again ne? Waya sani ko ta barbad'a masa maganin da ze rud'a masa ciki yasa masa diarrhea (gudawa) amman kuwa idan har tayi kuskuren yin hakan se tayi nadaman shigowa duniya. 


  "Kikace Amal ce ta gyara duka wannan?" Ya sake tambayan Falmata yana mey bin mandawan da kallo. 


  "Eh" ta amsa tana kallonsa. 


  "Yau ma tana wajen ne?"


  "Eh."


  "Jeki kira min ita."


  "Toh" da haka ta sauk'a k'asa sede sam Amal tak'i biyota, da k'yar Falmata ta samu Amal ta amince bayan rantsuwan da tayi ta mata na cewa ba abinda Afzal zeyi mata. Ita Amal gabad'aya cikinta ya d'au ruwa gudunta wai kar yace tayi gwaninta yace ze sake bata wani punishmennt d'in. Bayan knocking da Falmata tayi Amal tayi sallama sannan suka shiga ciki. Yau kaman ba Amal ba harda durk'usawa da zata gaishe da Afzal, dama bahaushe yace fad'an da yafi k'arfinka dole ka mai dashi wasa. Yau duk taurin kai da rashin ji irin na Amal ta tarar da wanda yafita hakan. 


   "Ke kika gyara?" Ya tambaya yana tura mata ledan gyad'an gabanta. Kai ta gyad'a a hankali. 


  "Meyasa?"


  "Kawai."


  "Nace me yasa?" Ya kuma tambayarta. 


 "Allah babu."


  "Zo ki d'auka kici I don't trust you."


  "Wai tunani kake zan cutar dakai in sa maka wani abin a ciki?" Ta tambayesa da mamaki. 


  "Thank god you know."


  "Wallahi ba abinda nasa ciki."


 "Then zo kisa a bakinki kici in gani." Sanin ba abin cutarwan da tasa a ciki ta k'arisa ta d'iba kad'an ta kai baki ta tauna sannan ta had'iye, duk anan kallonta Afzal yake. "Kaga ba komai wallahi."


  "Thank you" yace da ita. 


  "You're welcome" ta amsa. 


  "Baki amsa min tambaya na ba har yanzu why did you do it?"


  "Ya Afzal bana son mu zame annabi da kafiri a matsayin mu na musulmai, nasan nayi maka laifi but like I said I'm sorry bamu san wa ze amfana da wani ba wataran kuma ni bana son in mutu sanin cewa wani ya rik'eni a zuciya, ko baka fad'a ba nasan ka tsaneni kana jin haushina but I'm sorry I promise never to disrespect you again."


  "Hah!" Dariya kad'an ya saki yana mey juya kansa akan office chair'n da yake zaune akai "So kinsan cewa disrespecting na gaba da kai ba kyau?" Ya tambaya had'e da d'age gira. 


  "Eh na sani kayi hak'uri" ta amsa a nitse tare da sunkuyar da kanta. 


   "Meyasa kikeyi then? Saboda mutane suyi miki baki? Kinsan sharrin bakin mutum kuwa?"


   "I'm sorry" ta furta tare da pouting bottom lip nata. 


  "We're good" ya fad'a bayan tsawon lokacin daya d'auka yana mey wasa da pen da yake rik'e dashi a hannunsa. 


  "Dagaske baka tsane niba yanzu?"


  "I never said I hate you."


  "Thank you Ya Afzal" ta fad'a wanda yasa sa murmusawa kad'an. Dubu ya zara ya mik'a wa Falmata "Ya Afzal ba canji" tayi saurin cewa. 


  "Ki bawa Amal change d'in ta rik'e in kin samu."


  "Name nikuma?" Tayi saurin tambaya. Wani banzan kallo ya watsa mata wanda yasa tuni ta shiga yi masa godiya ba tare da tasan tayi hakan ba. Aikin gabansa ya cigaba da yi yana cin gyad'an da Amal ta gyara masa time to time. 


   ****

    Haka nan tun daga ranan anytime Amal is less busy zata d'au lokaci na musamman ta gyara  gyad'a wa Afzal gyad'a rananda batada lokaci kuma haka Falmata ke kawo masa atimes ta gyara mishi most of the time kuma yace karta damu zeyi da kansa. 




  *** GIDAN ALHAJI ABDALLAH ***


  "Ina Nazeefan ne wai kam?" Cewar Mummy tana me lek'an k'ofa ko zata ganta. Bada dad'ewa ba sega Nazeefah tafe, ba shakka tunanin auren da ta sa a gaba ne ya zubar da ita haka dan kuwa har duhu ma tayi sekace ba ita ba. Ga kwana biyu ta rage jin kid'i da sauran rawan kan da ta saba, a takaice de ta sauya halayenta cikin samarukanta befi d'aya zuwa biyu suke huld'a ba yanzu, batun aure kuwa bata sanar da kowa ba banda Rumaysa k'awarta. 


  "Khaleefah be fad'a miki ina kiranki bane kam?" Abinda Mummy ta fara ce mata kenan. 


  "Ya fad'a gani" ta amsa tana neman zama gefen Mummy akan bed bench dake d'akin. 


  "Batun auren naki ne dama kun kusa gama semester'n nan ko?" Kai zalla ta gyad'a. 


  "Good tun last two to three weeks Daddy ya tura saqo wa Afzal amman se shekaran jiya ya bada amsa."


  "Amsan mey?" Tayi saurin tambaya.  


   "Game da ranan aurenku da Daddy ya buk'acesa yayi fixing, kaman yadda zaki Hajj this year shima Afzal hakan Abbansa ke shirin kaisa so yace bayan ya dawo ze bada specific date kinga by then kuna hutu kuma ko?"


  "Wannan cin fuska da mey yayi kama? Shin keda Daddy kuna son Afzal ya mutuntani ya ganni da k'ima kuwa? Yanzu Mummy ace ko ranar aure na Daddy baze bari inyi deciding da kaina ba komi se abinda Afzal yace, ba damuwa" ta k'are maganan hawaye na ciko mata a ido. 


  "Toh ya muka iya Nazeefah? Ko ni ban goyi bayan shawaran nan ba amman Daddy'nki koni ya dena jin maganata hak'uri ya zama dole, kede kawai ki cigaba da addu'a Allah yasa Afzal ya rik'e ki amana ya kula mana dake."


    "Da abinda Daddy keyi ko nine shi Afzal d'in bazan rik'e matar da iyayenta ke nunawa batada k'ima kona misqala zarratun da amana ba" ta fad'a chan ciki-ciki sanin sarai Mummy zata jita sannan a fili tace "Ni zan koma d'akina."


  "Tsaya tukuna kinsan gobe first of Ramadan ko? Daddy yace zan tayaki mu had'a kayan shan ruwa wa Afzal."


  "Wallahi ni bazanyi ba" nan take ta rushe da kuka. "Wallahi bazan yi ba."


   "Nazeefah da hankalinki?"


  "Mey hakan kuke shirin min keda Daddy please? Sekace wata bazawara second class slut wacce bata da k'ima da daraja a idanun jama'a. Haba Mummy koda Daddy ya amince be kamata ke ki biye masa ba, saboda farin cikinku na yarda na amince da auren dolen nan da kuke shirin min dukda cewa kun sani wallahi yau idan na kai k'arar ku gun ko wani malami ne a garin nan hana aukuwan auren nan za'ayi saboda ko musulunci ya hane yin auren dole amman duk baku ga k'ok'ari na ba? Haba mana! Yanzu kuma zaku sake tilasta ni in kai masa abinci? Shi waye? Mijina ne shi? Ko nid'in nace muku ina son shi ne da kuke ta nema min gindin zama gun shi haka?"


   "Allah baki hak'uri nide saqon da aka bada na isar miki idan kinga bazaki iya bi ba fine Nazeefah kece da rayuwarki kuma dama kin saba yin abinda kika ga dama ba abinda iyayenki sukeso ba, go ahead sue us to court if that will please you" Mummy ta sanar da ita rai a 6ace sam bata ji dad'in abinda Nazeefah tace mata ba, eh auren dole ba kyau amman ai kuma ita ta janyo komi wa kanta kuma tasani koda ba'a tone zuciyan Daddy ba, tasan bawai da son ransa yake yin abubuwan da yakeyi ba, he is only doing what he thinks is right as a father. 


   "Ki tashi kina iya tafiya" ta sanar da ita ba walwala a fuskanta sam. 


   "Kiyi hak'uri" daga fad'in haka ta mik'e da hawaye na bin k'uncinta ta fice. 


  Washegari Daddy da kansa ya tura Nazeefah kitchen ta samu masu aiki da Mummy suka had'a had'add'en kayan bud'an baki wa Afzal. Daddy ya bari masu aiki su kai mai ma yak'i wai sam se de Nazeefah in kuma bazata kai ba tabar masa gida. 


   Ita Nazeefah ko a mafarki bata ta6a kawowa a tunanin ta cewa Daddy ze juya mata baya haka ba. A da se abinda tace da kuma abinda takeso yakeyi amman yanzu ko damuwa da feelings nata baiyi, abinda ya mishi kawai yakeyi regardless of her feelings. Bayan kukan data dad'e tana yi a bayi ta wanko fuskanta sannan ta fito ta sanya hijabi ta d'au basket d'in ta fice. Wani sabon kukan ta soma yi a bakin gate d'in, seda ta gama shan kukanta sannan ta k'arisa. Site na Ummi ta nufa inda Afzal ke zaune kan two seater ya mik'ar da dogayen k'afafunsa kan centre table se faman latsa waya yakeyi. Sallama tayi ya amsa ba tare da sanin wacece ba, ganin itace yaja k'aramar tsuka tare da kawar da kansa idan da yasan ita tayi sallamar da be amsa ba. Wayansa ya cigaba da latsawa tamkar ba mutum bane ya shigo parlourn. Tafi minti biyu tsaye bakin k'ofan ta na neman koda inuwan mutum ne sede ba Ummi ba masu aiki da alama duk suna kitchen ne suna aiki, taso ta nufi kitchen d'in saidai kuma ba dad'i ka fad'a kan mutane suna ciki aiki. 


   Tsayuwan ta cigaba da yi tana jira 

Ko Afzal zey mata magana sede sam abun ba haka yake ta fannin sa ba. Chan da tsayuwan mutum ya ishesa a ka ya mik'e da niyan zarcewa site nasa. Yazo gab da wuceta ta danne zuciyarta tayi masa magana, "Ina Ummi please?"


  Bayan tsawon lokacin da ya d'auka yace, "In yau kika fara shigowa gidan let me know excuse me" ya sanar da ita cike da gadara ba tare da ya ko kalleta ba. 


  "Gashi inji Daddy a kawo maka" ta kuma danne zuciyarta da take yi mata k'ona. 


  "You can keep it on the table tell him nagode ya sha ruwa lafiya." Dab ya kaiga fita kenan sega Ummi ta shigo from nowhere. 


  "Ahh ahh Nazeefah kece a gidan namu yau" abinda ta soma cewa kenan a yayinda take sa kai cikin parlourn. 


  "Ina yini Ummi?" ta durk'usa har k'asa ta gaisheta. 


  "Lafiya k'alau Mama na ya kike ya azumi?" Nan de suka gaisa. "Prince shine baka sanar cewa Nazeefah ta shigo ba?" ta juyo tana kallonsa. 


  "Barin je in watsa ruwa it's getting to Maghrib" ya fad'a tamkar bey ji abinda Ummi ta fad'a ba. Kai kawai ta kad'a ta bisa da kallo yayinda ya fice. Pepper chicken da fruit salat ta d'iba wa Nazeefah kan ta kaiwa Mummy. 


  Bayan an sauk'o daga sallan Maghrib Afzal ya dawo site nasa da shirin cika cikinsa saboda ba k'arya azumin yau ya d'an garasa kasancewar ya kwana biyu beyi azumin Mondays and Thursdays da yake d'anyi ba. Har ya zauna kenan se ya lura da kulolin dake jera akan table d'in ba shakka sune wanda Nazeefah ta shigo dasu d'azu dan kuwa Ummi bata da kalan kulolin nan. 


   "Aikin Ummi" ya furta a fili. Yasan ba wanda zeyi masa kalan d'anyen aikin nan se ita. Sarai da gan-gan tayi hakan, rasa nayi yayi dan kuwa ko za'a had'a sama da k'asa baze ci girkin Nazeefah ba yasan wani concussion d'in tayi ciki? Fridge nasa ya nufa ya zaro wata silver flask daga gun freezer wanda Amal ta basa d'azu. Babban cup ya ciro daga cabinet ya juye kusan rabin zo6on aciki sannan ya shiga kwankwad'a be cire daga bakinsa ba sanda ya shanye nan ya sake cika rabin cup d'in ya kuma juyewa a cikinsa sannan ya d'an jisa da seti. Cookies ya d'aura a kai chan bayan Isha ya fita ya wuce restaurant inda yaci abinci, wanda Nazeefah ta kawo kuwa masu aiki ya kira yasa su suka zauna suka cinye tas sannan suka fita da kwanukan bayan warning daya kashe musu na cewa komin yaya kar Ummi tasan cewa bashi yaci abincin ba. 


   Washegari shi kad'ai ya yini a office kasancewar Sultan yana meeting. Amal kuwa ko mey ya hanata shigo masa yau se Allah if not yawancin kullum tana bin Falmata su taho tare, ko da Falmata ta koma makarantar kwana kuwa Amal bata fasa kawo masa ziyara bayan sati sati ba, se gashi yanzu kusan kullum seta shigo masa ta taya sa hira da wasu k'ananun aikin office wanda baza a rasa ba. Cikin d'an k'ank'anin lokaci suka saba suka soma sakewa da juna unlike Afzal, Amal nada saurin sakewa da sabo da mutum saboda iya zuba surutun ta. Wajajen hud'u Afzal na shirin barin office sega Amal ta shigo, ganinta kawai da yayi se yaji dad'i ya ziyarci zuciyansa atleast zata d'anyi masa lighting mood nasa. 


   Bayan sun gaisa ta zauna a kujeran data saba zama kullum, "Bade shirin tafiya kake ba Yaya?" Ta tambayesa. 


  "I thought you weren't coming today" ya amsa a takaice. 


  "Mami ne ta aikeni wallahi taji nace zan maka kunun aya shine itama wai senayi musu da Papi ta sake aika na kasuwa" tayi maganan tana ajiye masa wata medium sized silver flask a kan table. "Ka sa a fridge idan ka isa gida don yayi sanyi bamu yini da wuta ba yau."


  "Duka nawa?" Ya tambayeta. 


  "Nida nake cewa ma yayi kad'an kace bakason sugar so kad'an nasa."


  "Thank you Amal, ga flask naki na jiya."


  "You're welcome yau ina Ya Sultan?"


  "Yana office nasa suna da meeting so ko leqo nan ma beyi ba."


  "Ayyah, ka gaisheshi in kunyi waya."


  "Sure" ya fad'a yana k'arisa tattara documents nasa. 


  "Nima bari in tafi toh tunda kana sauri yau."


  "You want me to stay?" Ya tambayeta. 


  "Banson zuwa gida yanzu markad'e Mami zata tura ni" ta fad'a tana pouting bottom lip nata. Murmusawa yayi kad'an yana duban agogon hannunsa "Bakiya son aike ko?"


  "Wallahi a'a yaron meyin markad'en ne wai sona yake naje kullum ya ta cika min kunne da suratan banza."


  "Iyye ashe Baby'n tamu akwai farin jini haka" ya fad'a cike da neman tsokana. 


   "Kai ya Afzal" ta fad'a tana kare fuskanta cike da kunya. 


   "Alright let's spend some time together then."


  "Yeyy! Amm-" da sauri ya katseta "Yau ba suratan shirmen nan nakeso ba I want to ask you some reasonable questions."


  "Toh kuma-" ta fad'a tana turo bakinta a yayinda murnan daya ziyarci zuciyarta ya koma ciki. 


  "Ban ta6a jin kince zakije islamiyya ba Amal meyasa?"


  "Kwanan nan na fita."


   "Meyasa?" Yayi saurin tambayarta. K'eyarta ta shiga sosawa. "Kinyi girma wa islamiyya koh?"


   "A'a ni bance ba."


  "Toh meyasa kika fita?"


  "Yaya naga kaman na samu na sallah ne" ta fad'a a hankali chan ciki-ciki. 


  "Owww!" yaja numfashi yayinda idanunsa suke k'ok'rain kwararowa waje don mamaki "Dama haka abin yake? Da an samu na sallah se a yanke zuwa?" Ya tambayeta. Shiru tayi bata ce komai ba dan kuwa batada abin fad'i. "Izib naki nawa?"


   "Ashirin da bakwai (27)" ta amsa sa a takaice. 


   "Kuma hadda?"

  

   "Eh ba a tartil a islamiyyan se hadda zalla."


   "Masha Allah" ya fad'a sounding impressive. Sam be d'au tanada hadda haka akanta ba. 


   "Toh ina laifin ki koma ki had'a duka Amal? Ko bakiya son kiyi haddan Qur'ani duka? Bakiya son ranan qiyama ayi crowning Mami da Papinki a idanun duniya gabad'aya?"


  "Inaso sosai ma" ta amsa. 


   "Toh ki koma islamiyya."

  

  "Yaya..." 


  "I promise you idan har kikayi hadda kika sauk'e zan baki gaggarumin kyauta" ya sanar da ita tare da katse ta. 


   "Dagaske Yaya?" Ta tambaya cike da jin dad'i "Wani irin kyauta toh?"


   "Wanda bakiya tsammani." 


   "Kaman wani iri kenan?" 


  "Kede ki had'a ki gani mana."


  "Toh shikenan Yaya in shaa Allah zan koma."


   "That's my sis" yayi praising nata had'e da sakar mata murmushi wanda ta mayar masa itama cike da jin dad'i. 

   "Western education (karatun boko) fa?" Ya kuma tambayarta. "A ina kika tsaya? Ko akwai wanda kike zuwa?" 


    "Ko d'aya, tun da na gama secondary school ban sake komawa school ba." 


  "Meyasa?"


  "Papi baida kud'in sponsoring d'ina" ta fad'a misfortunately, yadda tayi maganan seta basa tausayi shi a cewarsa gabad'ai itace bata son bokon ashe ba haka abin yake ba. "Karki damu, university ko college kikeso?"


  "University idan so samu."


  "Masha Allah what's your ambition?"


  "To become a nurse." 


  "That's a very good ambition Amal."


   "Thank you" ta amsa shi ba walwala a fuskarta. 


   "Karki damu kinji? Zakiyi fulfilling dreams naki in shaa Allah cikin satin nan zan shigo muyi magana da Papi muddin ya amince nayi alk'awari zan d'au nauyin karatun ki."


  "Kai Yaya! Dagaske kake?" Ta tambaya cike da mamaki a yayinda ta kasa 6oye farin cikin data tsinci kanta aciki.  


  "Inade fatan bakiyi tsohuwa wa part one ba" ya tambayeta cike da neman tsokana wanda hakan yasata murtuk'e fuska. "Yanzu Yaya kallon tsohuwa kake min kenan?" Ta tambayesa tamkar zatayi kuka "Ayya I'm just 18 years old fah, 2016 nayi graduating ai kaga its not too late ko?"


  "Yanzu dama duk rashin kunyan nan you're just 18?" Ya tambaya da mamaki ai ya d'au tayi irin ashirin d'innan contrary to yadda bata jin tsoron idon mutum. Fuskanta ta shiga karewa da hijabin da take sanye dashi. 

  "Ai na tuba bazan sake yiwa Yaya rashin kunya ba."


  "Kikayi ma zana zaki sha yanzu kinde san yanda Yayu ke discipline k'annensu a gida ai ko? Haka zan miki."


  "A'a bazan ma yi ba bale ya kaiga zana, kasan wani abu?"


  "Tell me" ya buk'aceta. 


  "You're such a blessing."


  "Da nayi me fah?" Ya tambayeta had'e da tattaro hankalinsa akanta yana zuba mata ido. 


  "Da kace zakayi sponsoring karatu na, ba yadda ban yi ba don inga na shiga jami'a amman hakan ya gagara gashi mates d'ina yanzu suna part two yawancinsu."


   "It doesn't matter yaushe ka shiga university ko kuwa yaushe kayi graduating Amal, what matters the most is abinda kayi acheiving and albarkan dake cikinsa so ki cire ranki daga damuwa in shaa Allah your delay is for the good kinji?" Kai tayi saurin gyad'awa tana murmushi na sosai "Thank you Yaya."


   "You're welcome Lily."


   "Laa nice Lily?" Ta tambaya tana blushing. 


  "Eh mana you're my kid sis na chan baya-baya ma kuwa that makes you my lily ko bakiya son sunan?" Ya tambayeta cike da wasa. 


   "Ni wa ince banaso?" Murmushi kad'ai ya sake mata. "Kace ni kid sis taka ce ta chan baya-baya?"


   "Yup baki yarda ba?" Gira ta d'age masa "You're not looking that old you know."


  "See this girl o! Na fa girme ki sosai na sosai."


   "Kai Yaya kaman da shekaru nawa?"


  "Ni zaki ma wayo? You want me to tell you shekaru nawa na baki so that kiyi adding a kan naki ki gano asalin shekaru na ko?"


  "Kai Yaya bade wayo ba wallahi amman yi hak'uri ka fad'a min mana ni baka ga na sanar dakai nawa ba?"


  "Nak'i" yace zalla. 


  "Yi hak'uri."


  "Kiyi guessing."


  "Toh let me see..." nan ta tsaya nazari a yayinda ya zura mata ido. 


  "23??" Ta tambaya da gan-gan sanin yafi hakan. 


  "23?" Ya nanata cike da mamaki. "Seriously?"


   "Toh 24?"


  "C'mon I look older than that God this is a slap on my face I'll be turning 27 by December" ya sanar da ita ba tare da yasani ba. Oops!


   "Yeyyy na ji shekarun Yaya" ta fad'a tare da k'yalk'yalewa da dariya. Jinguna bayansa yayi ya kalmashe hannayensa across his chest yayinda ya k'ure mata ido se faman rawa take kan kujerarta tana masa gwalo. Don kanta tayi shiru "Kin gama?" Ya tambeyeta. 


   "I'm sorry" ta fad'a wani dariyan na neman kauce mata. "But seriously Yaya you look way younger than your age, sam mutum bazeyi tunanin har ka kusa cika 27 ba, wallahi na d'au duk tsanani 25 kake, wai tsaya muga shekaru nawa Yaya ya bani? 27-18. Borrow one from- Wow! shekara tara fah!" Tayi calculating nan take, "Uhm uhm uhm amman gaskiya wawiya nake inyi maka rashin kunya, kayi hak'uri kaji?"


   "Ya wuce Lily don't worry."


  "Yaya bakada k'anne ne wai kam? Ban ta6a jin kayi maganansu ba."


  "Babu sai ke kad'ai."


  "Iyye Yaya d'an autan daddy nikuma Lilly'n Yaya happy me." Murmushi kawai yake yana kallonta itade surutu da shirmeh bayi bata wuya "Yaya idan nayi maka wata tambaya ba zaka ji haushina ba?"


  "Go ahead."


  "Uhm uhmm" tayi gyaran murya "Karfa kace nid'in nan magulmaciya ce."


  "LOL I won't" ya amsa yana dariya. 


  "Toh some days back naji kai da Ya Sultan kuna hirar wata Nazeefah senaji kaman har yana ce maka ango, aure zakayi?" Shiru yayi na d'an lokaci "I'm sorry ba seka amsa ba idan kaga ba zaka iya ba, forget it please."


  "Eh aure zanyi."


  "Wow! Masha Allah, yanzu Yaya inada Aunty shine baka ta6a sanar dani ba bale ka had'amu a waya da ita kuma kake kirana Lilir ka?"


   "I'm sorry" kad'ai yace da ita don yadda bayison hirar da ta shafi Nazeefah. 


  "Amman ya akayi koda wasa ban ta6a jin kuna waya ba Yaya?"


   "Because she's not your Aunty with time zan nemo miki Aunt da take da hankali wacce zata sake d'aura ki akan hanya madaideciya ba wacce zata gur6antar min da tarbiyyar ki ba."


  "Wow! Nikam ka sani a cikin duhu Yaya kode baka sonta ne?"


  Seda ya nisanta sannan yace, "Yes bana son ta" cikin sauk'i. Baki Amal ta bud'e cike da neman k'arin bayani tana kallonsa. "Abbanta ne yakeson in aureta bawai don inaso ba" ya sanar da ita. 


"Allah sarki itace wacce naji kwanakin baya kana bawa Ya Sultan labarinta a mota kenan" tayi reasoning. 


  "Yupp" ya amsa popping the P. 


  "Ka kwantar da hankalinka Yaya in shaa Allah you're doing the right thing, Allah na tare da kai with time zaka koyi sonta."


    "Hmm!" yaja nishi "Only if it is that easy."


   "Why not?"


 "Bazaki gane ba Lily it's a long story but I promise duk rananda nake cike da labari I'll give you the whole story yau yunwa nakeji don't tell me bakiya jin azumin nan?" Da wayo ya samu ya canza topic of discussion d'in. 


    "Laa karde Yaya baya iya juran yunwa?" Ta tambaya da wasa. 


  "Eh mana" ya amsa yana duban lokaci "Wow kinga har quarter to six (shida saura minti sha biyar) tashi in kaiki gida muyi shirin bud'a baki." Ba musu ta taimaka suka tattara masa documents nasa sannan suka sauk'a k'asa ta lifter. 


    Chan gidan madara yabi da ita inda suka tsaya a Today's ya sai mata chocolates sannan ya kaita gida sukayi sallama bayan asha ruwa lafiyan da tayi wishing nasa. 




RANA D'AYA 

#RD

Love... King Miemiebee👄✨

[12/08, 22:26] ‪+234 907 483 8352‬: 🎀🎀🎀                 🎀🎀🎀

                🎀❣🎀

                   ❣❣


  💦💦                      🍃🍃🍃          

           *RANA D'AYA!*

  💦💦                      🍃🍃🍃

  April, 2018

 beeenovels.blogspot.com


     _Written by Miemiebee👄_



   *PAGE 0⃣8⃣*



   

   Haka kwanaki suka ta shud'ewa a yayyinda Afzal da Amal suke sake shak'uwa wane asalin 'yan uwan jini. Traditional smoothies d'innan ba wanda Amal bata yi mishi, yau ayi Aldeb, gobe Ginger, next day Zo6o. Shima sau dayawa yakan kaita gidan madara ko Sidis su sai mata chocolates, ice creams da makamancin hakan. 


  Ta fannin Nazeefah kuwa Daddy be fasa da abinda ya d'aura ta akai ba, kafin azumi ya fita seda ta kaiwa Afzal abinci kusan sau hud'u ko biyar don haka itama Ummi tayi tunanin ya kamata Afzal yayi wa Nazeefah kayan sallah shima as a token of appreciation saidai ta fanninsa bayida niyyan hakan ko kad'an, Amal tasa kad'ai zai saiwa kayan Sallah ba wata fand'ararriyar Nazeefah ba. Yana cikin shirin zuwa gidansu Amal don kai mata kayakin da yayi niyya ne sega kwatsam Ummi ta fad'a cikin d'akin ko sallama yau babu. 


  "Haba Ummi!" Yayi saurin fad'i "Taya zaki na shigo min d'aki ba sallama idan da kuma ban sanye da kaya fah?"


  "Seka godewa Allah uwarka ce ta shigo ba su Juliet ko Esther ba, speaking of ina shigo maka d'aki ba sallama wani abun kake 6oyewa?" Ta k'arisa tare da tsayawa ta gefen gadonsa. 


  "Me kuma zan 6oye?" Ya amsa yana bin jikinsa da body spray. 


  "Meye acikin leather'n chan?" Sauri yayi ze ja sede dake tafisa kusa da gadon ta rigasa d'agawa tare da zazzagewa akan gadon. Zani ta tarar wanda take da tabbacin super wax ne exclusive ma kuwa, da wata voil lace. 


  "Iyyeehh!" taja numfashi tana binsa da kallo cike da k'in yarda wanda Afzal ya manna mata hasali yima yayi wane be san dashi takeyi ba. 


  "Prince wannan kuma se ina?"


  "Wai kam Ummi ina ruwanki? Haa'a! Ni ki miyar min su cikin leather'n."


  "Lallai Prince ka girma tunda ka soma 6oye min al'amuranka wato kayi wata sabuwa awaje shine ko a sanar dani ita ko? Da kyau."


  "Kaman ya sabuwa a waje kuma?" Ya tambaya nan take. 


  "Ai sarai kasan mey nake nufi wannan d'in ina zaka kai?"


  "Gidansu k'anwata" ya bata takaicaccen amsa. 


  "K'anwa?" Ta nanata da mamaki "Kanwa fa kace Prince? Yaushe na haihu ban sani ba?"


  "God help me" ya furta can k'asa-k'asa. "Wai kam se wanda kuka fito ciki d'aya dashi ne ze zamo k'aninka?" Ya tambayeta. 


  "Ni ba abinda nake nufi ba kenan" ta amsa had'e da kare kanta. "Amm-" katseta yayi a hankali "Kinga na farko Amal ba budurwata bace, ina yarinyan nan da na ta6a bigewa days back?"


   "Wacce tayi targad'en nan?"


  "Eh ita she's the one am referring to my sister" ya fayyace mata. 


   "Ahhh ahhh!" Ta fad'a cike da neman tsokana "Kace tun daga nan ta sace maka zuciya!"


  "Ya Subhanallahi!" Yayi exclaiming a rud'e "When did I ever say that?"


    "Yo gashi alamu sun nuna da de 6oye-6oyen nan ka dena ka rok'eni in tayaka da addu'a." 

        

   "Ummi please! Ni ba abinda yake tsakani na da Amal banda dangartakan ya da k'anwa so please kar maganan nan ya isa kunnen Abba."


  "Hmm Allah sa gaskiya de kake fad'i."


  "Ya ma riga ya sa don am telling you nothing but the truth" ya amsa ta yana mey manne bakin cuff links na rigansa. 


  "Nide nace Allah ya sa don kuwa gashi har an sai mata kayan sallah ni uwar taka gabad'aya ko d'an kunne ba a sai mi ba."


  "Oh Ummin tawa akwai kishi, a tunanin ki har zan sai ma wata zani ban saya miki bane?" Wardrobe nasa ya bud'e ya ciro wata leather tare da miqa mata "Gashi open up" Da murmushi kwance fal a fuskanta cike da hanzari ta amsa tare da since bakin, super biyu ta tarar ciki wanda sukafi na Amal ma kyau seda wata had'ad'd'iyar purple lace me torches na white and black. 


   "Awwn Prince duka nawa?"


  "Eh mana you deserve even more."


  "Gasu duk da torches na purple a jiki my favorite color."


   "Ummi ai duk wanda yace besan purple ne best color naki ba toh besanki bane."


   "Thank you so very much Prince Allah yayi maka albarka ya k'ara bud'i ya kuma sa albarka acikin al'amuranka sakallahu bil jannah."


  "Ameen your prayers keep me moving."


   "Suna tare da kai a kullum Babana."


  "I'm grateful bari inyi sauri yamma nayi."


  "Uhmm Prince nace Nazeefah fah?" Ta tambaya cike da gudun 6ata masa rai. 


  "Ohhhh!" Yayi exclaiming tare da buga k'afansa a k'asa "Ummi please kibar zancen yarinyan chan she's not yet my responsibility kibari bayan na aureta ban yi mata kayan sallah ba seki min fad'a ki tilasta ni but not now please."


  "Ayyah Prince ai ko yanzun ma ba tilasta ka nake ba, har na kai insa Prince d'ina aikata abinda beyi niyyah bane? Naga kaman abune da ya kamata kuma ma ai yima kai ne, kana sane de da yadda take kawo maka abinci ba fashi ya kamata kai ma kayi mata wani abun in return kodan iyayenta ma" ta mai bayani a hankali yadda ransa baze 6aci ba.


   "Toh Ummi ni na aiketa? Ko ni nace lalle-lalle se ta kawo min abinci? Abincin da ba ci ma nake ba" ya fad'a ba tare da yasan yaushe ba. 


  "Ba ci kake ba?? Innalillahi Prince!"


  "Ni ba abinda nake nufi ba kenan I mean" nan ya shiga kame-kame. "I mean ni inba girkin kiba ban k'oshiwa ko naci natan sena k'ara da naki a kai."


   "Da Allah chan! Ni zaka ma zak'in baki? Wato zubar da abincin kakeyi kullum ko?"


  "Itama lace da atamfan kikeso a sai mata kokuwa?" Ya tambayeta deliberately da niyyan canza topic of discussion d'in.


   "Kasan mey za'ayi ne? Tunda zaka fita yanzu kuma gashi yamma tayi why not ka kai mata nawan yaso seka sake siyo min wani ko zuwa gobe? Bana son a samu akasi."


  "Like seriously?" Ya tambayeta cike da mamaki "Abinda na sai wa mahaifiyata kike son in kai wa wata?"


  "Ai ni nace kayi karka damu all shall be well."


  "A'a nikam tunda ba firewa zatayi ba gobe idan na fita sena saya mata in tura akai mata."


  "Prince wai yaushe muka fara jayayya da kai ne? Nifa ban san ka da halin nan ba."


  "I'm sorry" yayi saurin bata hak'uri. 


    "Ai Prince baya laifi nide alfarma nikeso kayi hak'uri ka kai wa yarinyan kayakin nan."


  "Duka ukun Ummi? Wallahi lace d'innan ba lalle ne asamu exact irinsa ba kuma ko da za'a samun ma ba exact color d'inba saboda wannan d'inma a online na gani na baiwa me kayan kud'i ya siyo min da ze tafi Dubai."


  "Ai ko daga ido ma ansan ba k'aramar lace bace wannan kuma nima banda niyyan baida wannan d'in dama atamfofin nike nufi."


  "Alright keep them aside bari in kira Juliet tazo ta kai mata."


  "Haba Juliet kuma Prince kai baka ga kullum ita da kanta take kawo maka kayan bud'a bakin ba?"


   "Ohhh! Ummi please."


  "Yi hak'uri d'an albarka d'an autan Abbansa kuma d'an gaban goshin Umminsa yi hak'uri" shiru yayi bece komi ba "Yau zan yi maka pepper soup na kifin nan da kakeso fah ko kar ayi?"


  "Ni bance ba" yayi saurin amsata "Naji zan kai mata."


  "Yauwa my charming Prince nagode ko? And please karka manta kace zaka tambaya min yarinyan nan da ta had'a maka aldeb na jiya."


  "Don't worry I'll ask her of it gidansu ma zani ai yanzu." 


  "Laaa! karde itace Amal d'in?"


  "Toh da waye? She's the only sister I have."


  "Iyyeh!" Nan ta shiga yi mai wani irin kallo cike da neman tsokana da magana, shide be ce mata ko k'ala ba hasali bema damu da abinda take tunani akanta tsakaninsa da Amal ba saboda yasan a matsayin k'anwarsa ya d'auketa kamar yadda itama ta d'aukesa a matsayin yayanta. Dressing mirror ya nufa inda ya daidaita hulansa tsab sannan ya shiga feshe varieties na designer turarukan dake jere gaban mirron. 


****


  Daga gefen gate na gidan Alhj Abdallah Afzal yayi parking motarsa inda yasa masu gadi suyi ma Nazeefah sallama, yana zaune cikin motarsa yana going through twitter feeds nasa yaji murya kaman na Daddy na kiransa. D'aga kan da zeyi suka yi ido hud'u. Fitowa yayi daga motar nasa take ya k'arisa inda na Daddy yake, nan Daddy ya bud'e k'ofa suka gaisa. Bayan gaisuwa yake tambayar Afzal dalilin dayasa be shiga ciki ba ya tsaya nan waje sekace wani bak'o. 


   "Wallahi sauri nake ne shiyasa I'm sorry."


  "Allah sarki ba komai, gun Nazeefah kazo ne?"


  "Eh Daddy saqo nakeson in bata." Wani dad'i ne ya ziyarci zuciyan Daddy a tunaninsa gabad'aya abubuwa sun soma daidaita ne tsakanin Nazeefah da Afzal not knowing the actual situation. 


  "Kuma shine take 6ata ma lokaci bayan gashi kace da akwai inda zaka zarce?"


  "Eh Daddy amman ba damuwa nima ban dad'e da zuwan ba."


  "Barin tura d'ayan me gadin ya kirat- yauwa gata nan ma." Ya sanar da Afzal sanda Nazeefah ke fitowa daga gate d'in tana sanye da bak'in hijab three quarter. "Ke haka akeyi ne Nazeefah seki ajiye bak'onki shiru haka?"


  "Daddy ina taya Mummy aiki ne a kitchen" tayi explaining cike da ladabi kaman ba ita ba. "Sannu da dawowa."


  "Yauwa sannu ki k'ariso Afzal yana son miki magana" ba musu ta nufi wajen motan Afzal daga baya-baya ta tsaya, ba don tanaso ba sedon idon Daddy data gani a kanta ta gaishe da Afzal harda d'an durk'usawa shima ganin idon Daddy yasanya sa amsa gaisuwan cike da walwala da murmushi seda yaga shigewan Daddy ciki sannan ya azo asalin fuskarsa. Motan nasa ya koma ciki ya fito da ledar "Gashi ki d'au d'aya ki bawa Mummy d'aya" ya sanar da ita ba tare da ya nuna damuwa ba. Mamaki ne ya mamaye zuciyan Nazeefah har ma ta mance yadda ake amsan abu gun mutum. Shiko ganin tana 6ata mar lokaci ya ajiye ledar kan bonnet na motan. 


   Wai Afzal ne ze siya mata kayan sallah? Ta tsaya tana tambayar kanta. Hannu ta mik'a ta janye ledan izuwa 6angarenta tana mey shawaran yi masa godiya kokuwa. 


  "Dont think twice about it" fad'in Afzal yana mey tsamota daga cikin duniyan tunanin data fad'a. "Ummi ne tace lalle-lalle sena kawo miki wani abun kodan bautan kawo min abincin da ban rok'a ba da kikeyi gudun kar ki tashi a tutan babu if not banida ra'ayin hakan sam."


  Hamdala ta saki na k'in masa godiyan da tayi, dan kuwa da tayi da taji kunya. Numfashi taja tace, "Kaman ka sani there is absolutely nothing in this world daze sani sanya wani abinda ka siyo da hannunka kokuwa kud'inka" ta fad'a cike da gadara da rashin kunya. 


  Murmusawa yayi ta gefe sannan lokaci guda ya tamk'e fuskan nan "Then that makes us even saboda ko wuta da aljannah aka bani bazan iya cin abinda kika girka ba, hannun da sama da maza goma sun rik'e sunyi gadamansu dashi. So idan ma shirin kawo wani tarkacen kike yau I'd better make your work easier for you tun a bakin gate ki tsaya ki rabawa securities because it'll be more of a westage idan suka shigo site d'ina cause tsab a toilet zan juye kamar yadda na saba inyi flushing." Duk yadda Nazeefah taso 6oye mamakinta ta kasa, lallai ya cika d'an halas. 


  "You can close back your mouth gudun kar flies su shiga my warmest regards to Khaleefah and Mummy" yana kaiwa nan ya bud'e motansa ya ja yabar gun da d'ankaren gudu har yana neman kad'a mata k'ura. 


  Gidansu Amal ya wuce inda ya tarar da ita da Papi dake shirin fita shima. Taburma Amal ta shimfid'a masa inda duk suka zauna suka gaisa, bayan gaisuwa Afzal ya mik'a wa Papi ledan dake hannunsa. Cike da jin dad'i Papi ya bud'e ledar se ganin kayaki yayi ba adadi, "Wai wai wai Baba na da wahala haka?" Ya tambayi Afzal cike da k'in yarda a yayinda yake fito da kayakin d'aya bayan d'aya. Ashe gogan naku zannuwa biyu ya sai wa Amal sannan da lace nata har ma da takalmi da jaka, d'ankunne dasu sark'a bugu da k'ari harma da d'inkekken hijabin da ze shiga da zannuwan nata. Se kuma atamfa super exclusive wa Mami da babban gezna wa Papi amman ya 6oye wa Ummi saboda yasani da tagani zata hau fassara masa niyya while actually shi bada wata manufar yayi ba illa don k'anwarsa ce. 


  "Kai Afzal mun gode mun gode k'warai wallahi bansan ta ina zamu fara ma godiya ba" Fad'in Papi da se d'aga zannuwan yake yana bi da kallo. Amal kam don yadda mamaki ya mamayeta tama kasa magana banda zuba ma kayakin ido da tayi tana mey mamakin anya kuwa ita zata sa kayakin nan? "Baby bakiga kayaki bane da baza ki bud'e baki ba kiyi godiya?" Papi ya tambayeta. 


   Kai ta kad'a tana mey dawo da kanta asalin rayuwa daga duniyar tunanin data fad'a. 

 "Yaya?! Duka wannan namu?" ta tambaya tana mey nuna kayakin. 


  "Ji Amal" ya fad'a had'e da murtuk'e gira "Kin ta6a jin inda babban yaya yasai wa kansa kayan sallah be yi wa k'anwarsa ba?"


  Cike da kunya ta kad'a kanta "Yaya mun gode sosai Allah k'ara bud'i ya kuma miyar maka da gidan aljannah."


  "Ameen" Papi ya amsa a fili a yayinda Afzal ya amsa a zuciya. 


   "Gaskiya Afzal ba muda bakin yima godiya sai dai muce Allah ya biya ya k'ara bud'i godiya ba adadi Allah ya sak'a ya shige maka gaba aduk abinda kake ciki kake kuma nema."


  "Ameen Papi please godiyan ya isa haka ana tare ai."


  "Toh masha Allah, Baby mai da kayakin ciki kinji kar k'ura ya 6ata" ya sanar da ita a yayinda yake k'ok'arin mik'ewa "Zan fita zani kasuwa sena dawo" ya sanar da Afzal. 


  "Papi idan ba sauri kake ba daman inaso muyi wata magana da kai ne" Afzal yayi saurin tanka shi. 


  "A'a ko kad'an Babana bismillah" nan ya koma ya zauna. 


  "Thank you, dama batun Amal ne munyi magana da ita kuma tace tana son ta koma makarantar boko idan har kaga hakan ba matsala I am willing to provide for her education se tayi sitting jamb muyi mata applying jami'a nan Unimaid."


  "Jami'ah! Allah sarki babana nauyin baze zo yayi maka yawa ba kuwa? Dan Allah karka damu nima ina kan tara mata kud'i ne ko nan Ramat ta shiga don Allah karka tada hankalinka."


  "Papi ni izinin ka kawai nake nema karka damu da komai."


 "Baby zaki deyi karatu baza kisa Yayan ki asaran kud'in makaranta bako?" Ya juyo yana kallon Amal data had'e gira. Lalle ma Papi sekace besan k'ok'arinta ba yake fad'a mata haka gaban Afzal, ai se Afzal ya d'au ita d'in doluwa ce. 


   Daga bisani tace, "Papi da gan-gan ka fad'i hakan donka kunyatani idon Yaya ko? Allah se in d'auko report sheets d'ina tun daga JSS1 in nuna mishi kaima kasan bana wasa da karatu."


  "Ah ah mamana na kaina yi hak'uri maida wuk'an wasa nike." Murmushi Afzal ya saki yana mey sha'awan relationship dake tsakanin Amal da Papinta. 


  "Toh Afzal nide ba abinda zance sede muyi ma addu'a Allah ya biyaka. Rashin shiganta babbar makaranta ba k'aramin damuna yake ba a matsayina na mey kula da ita barin ma yadda take da son karatu, tun tana damuna da cewa tanason ta shiga jami'a har tagaji ta dena saboda rashin samu, ba yabon kai ba amman uwata akwai ja inada tabbacin cewa bazata baka kunya ba, kuma nima zan sa ido sosai akanta inga ta cika maka burin ka nason ganin tayi karatun nan, Allah sak'a maka da alheri."


  "Ameen Papi nine da godiya daka amince da wannan k'udiri nawa zan d'anyi tambayoyi kad'an in shaa Allahu duk abinda akwai zan sanar dakai."


  "Toh toh Babana mungode mungode sosai Allah kad'ai ze biyaka shikenan ko akwai wata maganar kuma?"


  "A'a Papi kana iya tafiya nagode da ka bani lokacin ka."


  "Toh madallah madallah" ya fad'a yana mik'ewa. 


  "Toh a dawo lafiya" cewan Afzal. 


  "Allah tsare Papi" inji Amal. 


  "Ameen Afzal ameen uwata, mungode sosai sosai ka gaishe da gida idan ka koma."


  "In shaa Allah" Da haka ya fice ya rage Amal da Afzal kad'ai kasancewar Mami ta shiga mak'ota. 


  "Yaya wanne ne nawa?" Ta tambayesa cike da jin dad'i tana mey zazzago da kayakin. Murmusawa yayi ganin yadda ta kasa 6oye farin cikinta. Atamfan Mami yaja gefe da kuma shaddan Papi sannan yace, "Duka wannan naki ne."


  "Dagaske Yaya? Da wannan da wannan da wannan duka?" Ta tambaya cike da k'in yarda tana mey bin kayakin da yatsarta tana nunawa. 


  "Sosai ma."


  "Yaya you're truly an angel thank you so much."


  "You're welcome Lily" ya amsa yana mey miyar mata da murmushin da take masa. 


  "Toh ni da irin abubuwan nan da kake min dasu Papi me muke dashi da zamu iya baka in return?"


  "Addu'o'in ku kad'ai ya isheni Lily."


  "Are you sure Yaya?"


  "Absolutely sure Lily."


  "Toh shikenan Yaya ga addu'o'ina na yau da kullum a gareka; Allah sak'a maka da alheri, ya k'ara maka bud'i yasa ka cimma duk wani burinka a doron k'asa, Allah ya baka mace ta gari da 'ya'ya nagari ba masu rashin kunya da taurin kai kaman ni ba fa" Dariya sosai Afzal ya tsaya yi a yayinda ta cigaba "Allah sa ka gama da duniya lafiya, ya baka gidan aljannah kuma, kai Allah ya baka duk wani abinda kakeso tun a zuci ba seka furta shi waje ba." Shiru ta yi don jin yadda Afzal keta dariya tun zamansu dashi bata ta6a ganinsa yana dariya haka ba, ashe de haka dariya yake kar6ansa shine baya yi? Cankwad'i! aikuwa ta rik'a sashi dariya kenan kullum yanayi. 


  "Ka gama dariyar baka amsa da ameen ba."


  "LOL ameen Lily kema Allah ya miyar miki da duka addu'o'in da kikayi min."


  "Hmm ameen da babban murya kaga barin surfa waken nan kafin Mami ta shigo ta balbale ni tun d'azun tace inyi na tsaya ina shirme."


  "Kafin nan Ummi tace tanason ki koya mata yadda akeyin aldeb d'innan Lily na rage mata na jiya bakiga yadda tayita santinsa ba."


  "Kai Yaya dagaske?" Gira ya d'age mata "Wai yayi dad'i tace?" Ta tambaya zealously. 


  "Sosai ma."


  "Ai dama nasan na iya girki Mami ce kullum ke kusheni."


  "LOL that is because tanaso ki k'ara himma ne don't blame her it's what mothers do."


  "Hmm toh kasan me za'ayi? Barinje in kira Mami nan mak'ota tayi hak'uri tayi sirfen waken sena had'a wa Ummi da kai aldeb d'in ai idan nayi a gabanka zaka gane procedures d'in idan ka koma gida se kayi mata bayani ba?" Shiru Afzal yayi yana nazari shi banda dafa indomie, tafasa ruwa, farar shinkafa ko spaghetti da macroni anya akwai wani abinda ya iya?


  "Kode Yayana be iya girki bane sam?" Ta tambayesa cike da neman tsokana. 


  "Waya fad'a miki?" Ya wani 6ata rai yana cin fuska. 


  "Toh naji kayi shiru."


  "Of course, how do you expect me inje in fara yima Ummi bayanin yadda ake had'a aldeb mace ne ni? Kede yanzu ki bani number'n Mami in naje gida sena had'aku kiyi mata bayanin ta waya."


   "Haha nide na gane Yaya ajebo ne be iya komi a harkan kitchen ba."


  "Na yarda fad'i koma mey ba shi zey sa in amince da k'udirinki ba." 


  "Toh shikenan Yayana na kaina ai ni duk abinda ka fad'a ya zauna se ayi hakan." Bece da ita komi ba yayin da ta shiga ciro ingredients da zata buk'ata tsakar gidan, tana cikin taran ruwa daga famfo sega Mami ta shigo. Sosai tayi murnan ganin Afzal, bayan sun gaisa Amal ta fito mata da kayakin da Afzal ya kawo musu ta nuna mata, da godiya na kisa kam daya kashe Afzal a wajen saboda kalan godiyan da Mami tayita masa. 


   Bayan ta mai da kayakin ciki ta fito ta tarar da Amal na aiki daban maimakon sarrafa musu waken da zatayi. Ta soma k'orafi kenan Afzal ya shiga bata hak'uri had'e dayi mata bayanin lamarin cewa Ummi ce keson aldeb d'in. Ba tare da 6ata lokaci ba ta shiga surfen da kanta yayinda Amal ta cigaba da had'a aldeb d'in. Ido Afzal ya k'ura mata yana mey sa hankalinsa sosai game da duk wani abinda takeyi ko da ze iya fahimta yayi ma Ummi bayani ko dan kar Amal tayi underestimating nasa. 


   Abu d'aya daya karanchi tattare da Amal shine kominta tsaf-tsaf take yinsa ba dotti bale k'azanta hakan ba k'aramin burgesa yayi ba, a rayuwa ya washi mutum me shegen daud'a da k'azanta kasancewar acikin tsafta ya girma, mutane har suna cewa tsaftan Ummi yayi yawa, shara idan batayi atleast sau biyu ko uku a rana ba bata jin dad'i. 


   A haka har Amal ta samu ta gama ta d'ura masa cikin manya-manyan silver flasks guda biyu d'aya nasa wai d'aya na Ummi. 


   Kud'i ya k'irga yasa a hannun Mami cewa suyi d'inkin kayakin nasu dashi. Wayyo Mami ta ma rasa ina zata sa kanta, albarka tayita sa masa sannan suka rakasa har inda yayi parking motarsa, bayan ta mishi asha ruwa lafiya ta koma ciki ta barsa shi kad'ai da Amal. 


 "Here press Mami's number bayan ansha ruwa zan had'aku da Ummi se kiyi mata bayani" ya fad'a yana mey mik'a wa Amal wayansa da ta amsa da 'Toh.' Hannu na 6ari ta mik'a ta amsa tana mey fatan Allah ya kawo mata ranar da zatayi wayar kanta me k'aton screen kaman wannan ko shegiyar Bintun ajinsu na islamiyya zata shiga hankalinta ta daina yi musu yanga da wata k'aramar infinix nata da bai iya zama cikin jaka ba sede akan table don a nunawa 'yan aji ana da waya. Bayan ta zuba ta miyar masa da wayan inda yayi saving. 


  "Toh Lily ba-bye."


  "Mungode Yaya asha ruwa lafiya."


  Murmushi kad'ai ya saki mata yayinda ya bud'e murfin motan ya shiga, se da taga ficewansa sannan tabi lungun gidansu ta koma. 


****

BAYAN SHAN RUWA, GIDAN ALHJ AHMAD AMIN. 


   "Ni fa ban yarda ba kuma bazan yarda ba in zaka kira min yarinya kawai ka kira tayi min bayani da kanta dududu banda tafasa ruwa mey ka iya da zaka wani cemin ka iya had'a aldeb me dad'i irin na Amal in yarda" Fad'in Ummi dake zaune a gefen Afzal akan kujera a parlourn site nasa. 


  "Am serious Ummi a ido na ta had'a and I did observed her closely."


  "Oho nide kiramun ita se naji daga bakinta zan amince, ba ka amshi lambarta kona mahaifiyarta ba? Call her up for me."


  "Fine!" Ya fad'a aggressively tare da dannawa lamban Mami kira saida ya kusan tsinkewa aka d'aga. "Assalamu alaikum" yaji siririyar muryar data d'aga ta fad'a. For a moment ya shiga duhu yade san muryan Mami ba haka yake ba, na Amal shigen hakan ne seda kuma wannan d'in har yana son fin natan zak'i. 


  "Yaya?" Ta kirasa wanda hakan ya tabbatar masa da kokonton da yake.


  "Na'am Lily" ya amsa yayinda Ummi ta zura masa. 


  "Ina yini? An sha ruwa lafiya?"


  "Lafiya Alhamdulillah ya gida?"


  "Lafiya k'alau ya Ummi?"


  "She's okay ita ma ke son miki magana kafin nan Lily aldeb d'innan bada tsamiya, sugar, ruwa..." nan ya shiga irgo duka ingredients d'in sannan kuma da procedures d'in, sosai Amal ta sha mamakin yadda ya rik'e komi dai-dai dukda fad'in sau d'aya aka ta6a had'awa a gabansa. 


    "Wow! Impressive kai Yaya na akwai k'ok'ari ai kuwa ka bada procedures din dai-dai sede tsamiyan da ruwan zafi ake jik'a sa kuma sugar'n ma ba raw one ake sawa direct a ciki ba se an narkar dashi."


  "Ai na fad'a seda na fad'a maka narkar da sugar'n nan ake kak'i yarda Pff" nan Ummi ta shiga yi masa gwalo. 


  "Whatever ai nayi k'ok'ari for goodness sake yau fa na fara ganin yadda akeyi."


  "Eh sugar'n ma ana iya sa shi direct amman narkekken yafi fita ne" Amal dataji Ummi sama-sama ta waya ta amsa. Gwalo ya shiga yima Ummi shima "Pff to you! Kin deji da kunnen ki a hakan ma ana iya sawa."


  "Kai Yaya bade gwalo kake yima Ummin namu ba?" Ta tambayesa "D'an bata mu gaisa."


  "Barshi Amal 'yata gwalo yake min" Ummi ta amsa tana matsowa kusa da wayan. 


  "Toh bata mu gaisa."


  "Nak'i, ke bakiji sanda take min gwalon ba itama?"


  "Yi hak'uri toh ka bata" ba gardama ya mik'awa Ummi wayan inda suka gaisa take ta yaba aldeb na Amal wanda har ahakan yasata kunya sosai.


  "Ai da na bi procedures na Prince da nayi kwa6a" For a moment kan Amal ya d'aure karde sunan da ake kiran Yaya dashi kenan a gida Prince? Ta tambayi kanta, lallai kuwa d'an gata ne. "Kai Ummi ai yayi k'ok'ari" ta amsa cike da wasa. 


  "Bani waya na Ummi bani!" Ya fad'a trying to sound serious. Da sauri ta tare hannunsa "Kinsan kuwa banda tafasa ruwan zafi ba abinda ya iya? Taya mutumin da ko jollof be iya dafawa ba ze ce min ya iya had'a aldeb kuma in yarda, 'yata is it possible?" Dariya sosai Amal tasa har tana sark'ewa Afzal da ya kai har maqora se harara yake dannawa Ummi yayinda take tayi masa gwalo. Taya zata fad'awa Amal bai iya girki ba? So take ta raina sa? 


  "Ai fa ba laifinki bane nine nan na had'aku ai" yace da ita yana girgiza kai. 


  "Kinji Yayanki yamun fushi ko ki basa hak'uri" Ummi tace da Amal dake ta faman yi musu dariya tun d'azu. 


  "Laaa yayi mana hak'uri don Allah ai bamu iyawa da fushin Yaya, Yaya?"


  "Gashi amshi k'anwarka na son yi maka magana."


   "Nak'i" ya amsa ba walwala "Ni d'agani in mik'e idan kun gama wayan naku ki kawo min wayana ciki ko ki kirani inzo in kar6a." Kafin ya kaiga mik'ewa Ummi ta danneshi "Haba Prince yi hak'uri mana."


  "Toh Ummi seda safe, ki sake yiwa Yaya godiya sosai dan Allah munga kaya mun gode Mami tac-" wabce wayan yayi daga gun Ummi da sauri kafin Amal ta k'arisa zancenta had'e da katsewa yana mamakin dogon baki irin na Amal se kace bata san halin Ummi ba. 


  "Ya haka Prince?" 


 "Babu d'agani nikam."


 "Tsaya ma tukun wato ba wa ita kad'ai ka sai wa kayan sallan ba harda iyayenta ko?" Shiru yayi tamkar be jita ba, "Hmm su Prince an fad'a kogin soyayya."


   "God help me! Ni wallahi saboda irin suratan nan naki nak'i nuna miki kayakin duka baga irinta ba" ya fad'a a tak'ure. 


  "Aww ashe da gaske ne ka sai wa iyayenta kayan."


  "Eh na sai musu shikenan kin huta?"


  "Prince jokes aside kode son yarinyan nan kake ne amman ka kasa ganewa har yanzu?"


  "Haba Ummi! Taya zan so Amal please? Ai banyi adalci ba kenan."


   "Kamar ya bakayi adalci ba?"


  "For goodness sake a matsayin yayanta ta d'auke ni, ta na gani na da k'ima da daraja tana girmama ni kawai don ni na kawo rashin halacci da kunya duniya se in hau sonta? It's not possible."


  "Kana nufin in ba don wannan dalilin ba zaka iya sonta kenan?"


  "God help me!" Ya furta unbelievably "No that is not my point you know what? Let's just drop this topic" ya fad'a ransa na soma 6aci. 


  "Hmm tayi tsami maji."


  "Ummi please kidena blabbing d'innan haka Amal is just my sister there is no any other feeling attatched to it" ya fad'a cikin tattausar murya. Shiru Ummi tayi bata kuma cewa komi ba ganin yadda ransa ke 6aci. 



  ~•. .•~        ~•. .•~        ~•. .•~      ~•. .•~


     Bayan Sallah da k'imanin wata biyu dai-dai da lokacin watan Zul~Hijjah ta kama kenan Afzal da Ummi suka wuce Saudi wanda tafiyansu yazo dai-dai da na Nazeefah, Mummy da Khaleefah. A hotel d'aya duk suka sauk'a inda Khaleefah da Afzal suka had'a d'aki, Mummy, Ummi da Nazeefah ma haka. Kusan kullum tare suke fita suyi Ibadunsu har Allah ya kawo su k'arshen aikin Hajji. Ana jibi zasu juya ne Ummi tayita insisting cewa se Afzal ya kai Nazeefah shopping kar Mummy tayi zaton lallai-lallai tilasta masa akayi batun auren. Seda suka kusan haurawa sama Afzal ya amince. Bayan ya fito daga wanka, ya shafa lotions nasa sannan ya zira d'aya daga cikin expensive jallabiyan daya sissiya ya feffeshe jikinsa jak'ab da turare sannan ya tattara wayoyinsa. 


  "Khaleefah kace bazaka bimu ba? Da Nazeefah zamu fita fa" ya sanar da Khaleefah dake mik'e akan gado se faman buga game na world tip yake. 


  "Friend d'ina zezo za muje muyi playing video game kuje sekun dawo."


  "Alright make sure you lock the door idan zaka fita."


  "Toh Uncle Afzal Allah ya kare." Da haka ya fice ya sauk'a reception a k'asa. Numban Nazeefah da Ummi tayi masa saving about last two weeks yayi scrolling yakai kai amman bai jin ze iya kiranta. Bayan tsawon lokacin daya d'auka yana nazari k'arshe ya yanke hukuncin kiran Mummy. Bayan ta d'aga sun gaisa yake sanar da ita cewa yana reception yana jiran Nazeefah yana son su d'an fita yau, yayita trying layinta amman bai shiga. 


   "Allah sarki halan network ne don gata ma a gefe na bari yanzun nan zata sauk'o sannu ko Babana."


   "Yauwa Mummy thank you" da haka ya katse. 


  "Nazeefah maza tashi ki shirya Afzal na jiranki a reception."


  "Mey zey min?" Tayi saurin tambaya had'e da d'ago kanta. 


   "Jimin tambaya yace yana son ku fita go meet him downstairs."


  "Mummy ni wallahi da kince mishi na fita bana nan."


  "Dalili? Yanzu har yaro yayi creating time miki ki tsaya kina batun banza?" Itade Nazeefah bata kuma cewa komi ba amman tasan tabbas inma Ummi ce tasa sa na dole kokuwa yana shirin yi mata wani mumunan abun. "Ba zaki mik'e bane?"


  "Ba naji ba" ta amsa a tak'ure. Da haka ta kimtsa ta fice inda ta tarar da shi da wasu yaran larabawa se faman wasa sukeyi. Sallama tayi masa wanda se da ya gama 6ata mata lokacin duniya sannan ya amsa. Maimakon ya sallami yaran su tafi inda zasu, no wasan suka cigaba dayi yabar Nazeefah tsaye gun kaman ta6arya, seda ya tabbata ta gaji sannan ya sallami yaran ya mik'e. Don kanta ta shiga bin bayansa dan kuwa beyi niyyan yi mata magana ba. 


   A mall suka tsaya inda ya d'au trolley tare da ce mata "Pick whatever it is you want I'm doing this because of Ummi so karki kawo tunanin wani abun a ranki." Daga fad'in haka yaja nasa ya fice ya shiga shopping. Tafi minti biyu tsaye wajen sannan daga bisani taja trolley'n ta shiga kwasan duk abinda yazo hanyarta da abinda zatayi amfani da shi da wanda bata ma san meye shi ba komi kawai d'auka takeyi har Afzal ya gama kwasan abinda ze kwasa Nazeefah bata gama ba se chan ana cikin billing masa abubuwan da ya siya se gata nan cike da trolley tazo ta tsaya bayansa. Murmusawa yayi ba tare da yace da ita komi ba. 


  Kayakin nasa ta leqa ciki sede da mamaki taga yawancin kayan 'yan mata ya kwasa wanda ta nada tabbacin bana Ummi bane gashi bawai k'anwa ko ya yake dashi ba bale ace nasu ne, toh na waye ne? Kode budurwa yake dashi?? Toh ma ina ruwanta? Kanta ta kawar ta maido da kallonta akan wayarta har izuwa lokacin da billing ya iso kanta. Kud'in abubuwan data siya yayi ninkin na Afzal biyu, da gangan tayi hakan dama, fatanta kawai ace kud'insa ya kasa ta biya wa kanta tasasa jin kunya cikin mutane sede kash! Credit card nasa kawai taga ya zaro ya mik'a wa mutumin inda yayi debiting nasa suka miyar masa da abunsa, har maqora abin ya kai Nazeefah sam ba haka ta so ba. Acikin manya-manyan shopping bags aka sanya musu kayakin nasu suka fito. A bakin k'ofar Nazeefah ta tarar da beggers masu rok'o d'innan tsaye suna neman taimako, ledojin nata gabad'aya ta dank'a musu lokacinda taga Afzal ya kewayo yana kallonta. 


  Ya sha mamaki sosai amman yayi k'ok'arin 6oyewa, taxi d'in ya bud'e ya shiga tare da cewa driver'n su tafi, sa6anin tahowansu a rarrabe suka koma. Ko a babu itama tasan tayi mishi ba dad'i yau, a cigaba a hakan aga wa ze yi surrender. 


   ***

   Afzal ne mik'e kan gadon d'akinsu da Khaleefah se tunanin abinda Nazeefah tayi masa yake yana mey nazarin mey zeyi mata wanda zataji zafinsa haka itama a yayinda wata zuciyar ke cey masa kawai ya barta yaci girma sede yana ganin da k'yar idan ze iya. Ana cikin haka ne wayansa dake kife akan cikinsa ya shiga ruri, duban wa da zeyi ya tarar da Nigerian number, be kawo wani tunanin ba a ransa ya d'aga a tunaninsa gabad'aya ma Sultan ne sede ya tarar da muryar mace, macen ma Amal. 

  Yau akeyinta, bema san ta ina ze fara yi mata bayani ba saboda ko sanar da ita cewa zasa aikin Hajj beyi ba rabonsu tun kafin ya taho Saudi yau kusan sati uku kenan. Ma ya akayi ta samu numbansa? Katse wayar yayi gudun kar kud'inta ya k'are sannan ya kirata back. 


   "Lily?"


  "Na'am Yaya ka kyauta min kenan? Ai kam yanzu na tabbata ni ba Lilir ka bace kamar yadda kake fad'a tunda har zaka aikin Hajji amman baka sanar dani ba."


   "Lily ba haka bane."


  "Toh yaya ne Yaya? Kawai sena dena jinka ga layinka kullum switched off hankalina du yabi ya tashi haka su Papi ma gashi ban san gidanku ba, last week naje office naka nake tambayarka sukace kayi tafiya se yau kawai Allah ya had'a ni da Ya Sultan yake fad'a min wai Hajj ka tafi sannan ya bani numbanka truly am very disappointed."


  "Yi hak'uri kinji Lily? I know I've offended you ni kaina bansan meya hanani sanar dake ba but I'm sorry."


  "Saboda baka damu dani bane mana inda kayi ai da ka sanar dani."


  "Kema kinsan that's not true I do care about you Lily."


"Uhmm" tace kad'ai. 


   "Baki hak'ura ba?"


  "Ai Yaya baya laifi" ta fad'a tana murmushi. 


  "Masha Allah that's my Lily ya kike toh?"


  "Lafiya Alhamdulillah ya Ibada kun kammala ko? Allah yasa kar6e66iya ce."


  "Eh Lily ameen, jibi ma in shaa Allah zamu juyo, anyi sallah lafiya?"


  "Lafiya k'alau though I miss having you around." 


  "I miss you even more Lily yasu Mami da Papi?"


  "Duk lafiyansu suna gaisheka."


  "Ina amsawa my regards, ya karatu?"


  "Gashi muna ta fama da tilawa."


  "Allah ya taimaka guess what?"


  "Ameen, tell me Yaya I'm a bad guesser."


  "Alright digital Qur'an na sai miki na k'ira'a Al~Sudais complete."


   "Kai Yaya! Dagaske!" Tayi exclaiming yayinda ta tsinci kanta cikin farin ciki maras misaltuwa. "Kaman kuwa kasan k'ira'an Sudais nake bi nake kuma son koya."


   "Ai kin riga ma kin iya Lily sede kice kina son sake k'warewa."


  "Kai Yaya! Har yaushe ka sani?"


 "Am serious, there was a day naje gida na tarar dake kina karatu so I stayed back and listened to you as you recite."


  "Kai Yaya har kasa naji kunya."


  "Sosai fah Lily nan na gano k'ira'ar Sudais kike bi and masha Allah kin iya sosai."


  "Thank you Yaya."


  "You're welcome karatun boko fa kina d'an tab'awa ko?"


  "Eh wai February zamuyi Jamb ko?"


  "Eh in Allah ya yarda."


  "Ina d'an ta6awa amman akwai wasu abubuwan dana d'an manta a physics da chemistry kasan it's been long banbi ta kansu ba."


  "Don't worry idan na dawo I'll help you out."

  

  "Toh Allah ya dawo mana da ku lafiya."


  "Aameen." 

   

  "Amman Yaya dama ba commercial class kayi ba?"


  "Waya fad'a miki? I was once a science student."


  "Shine kuma kake aikin banki?"


  "Ai kowa ma zey iya aikin banki Lily ba se lalle wanda ya karanta accouting ko economics ba kuma kinga ni da bank of agriculture nake aiki."

  

  "Agric ka karanta kenan?"


  "Yes se nayi specializing a Horticulture and Agronomy."


  "Wow! I'm impressed" hira sosai suka tayi se kusan k'arfe goma wanda yake dai-dai da k'arfe sha biyu a k'asar Nigeria Afzal yayi tunanin suyi sallama kodan Amal ta samu tayi bacci, bayan seda safen da tayi masa ya jira tayi hanging sannan ya ajiye wayan a kan side drawer. Daidaita wa Khaleefah dake ta faman bacci blanket yayi sannan ya mik'e ya shiga bayi ya watsa ruwa had'e da d'auro alwalan bacci ya dawo ya kwanta a gefensa. 


 

 ~•. .•~       ~•. .•~       ~•. .•~      ~•. .•~


    Da dawowansu Afzal da sati biyu kayakin su na Cago suka iso nan yayi sorting out tsaraban da yayi ma mutanen hannun damansa ciki harda na Amal dasu Mami. Na Sultan ya soma kaiwa sannan na colleagues nasa a office. Daga can ya zarce gidansu Amal har ya soma sabawa da 'yan unguwa saboda yawan shiga da fitan da yakeyi. Parking yayi suka gaisa da 'yan bakin shago inda suke tambayarsa ko lafiya kwana biyu shiru yake sanar dasu cewa tafiya yayi. 


    Da kansa ya fito da ledojin har zuwa bakin k'ofar gidansu Amal inda ya shiga had'e da yin sallama saidai tun daga bakin k'ofar yake jin hayaniya, kasa kunnen da zeyi ya jiyo muryan Mami da ihun Amal da hanzari ya k'arisa ciki ya tarar dasu se kuje-kuje suke yayinda Mami ke rik'e da tsumagiya tana bin Amal da keta zagaya tsakar gidan. Mami ce ta soma yin tozali da idon Afzal don haka tayi saurin dakatar da abinda takeyi wanda hakan yasa Amal daina ihun da take ta faman yi. 


   "Afzal??" Mami ta kira sunansa cike da k'in yarda. 


  "Na'am Mami" ya amsa. Amal kam don mamaki da kunya tama kasa magana banda raba idon da takeyi. 


  "Wai! Wai! Lale lale mutanen Saudiya sannu da zuwa sannu da zuwa, Baby d'auko tabarma ki shimfid'a masa sannu da zuwa Baba na, sannu da zuwa" Tafiya take wane wanda k'wai ya fashe mata a ciki har ta isa bayan k'ofan d'akin Papi ta d'auko tabaramar. 


   "Zo ki shimfid'a a nan" cewar Mami tana mey mata nuni da inda take tsaye. K'arisawa tayi ta shimfid'a ta kai ga d'agowa kenan Mami dake fakonta ta sauk'e mata tsumagiyan zuwat a baya da iya k'arfin ta, wani irin rkicaccen ihu Amal ta saki yayinda ta shiga susa bayan nata take tana kuka. 


    "Subhanallahi!" Afzal daya zame shedan yadda tsumagiyar ta sauk'a da k'arfi akan bayan Amal yayi saurin furtawa "Dan Allah Mami kiyi hak'uri" be san lokacin da ya sake ledojin dake hannayensa ba a k'asa tare da shiga tsakanin Mami dake shirin sake kaiwa Amal wani zanan yayinda Amal ke ta faman kuka. 


   "Ba zaki rufa ma mutane k'aton bakin nan bako?" Mami ta tambayeta tana neman bin ta gefen Afzal don kuma sauk'e wa Amal wani zanan wanda da sauri Afzal yasa hannu ya k'wace bulalan yana mey bawa Mami hak'uri. 


  "Afzal don Allah ka barni da yarinyan nan yau seta fad'amun waya haifi wani tsakani na da ita a gidan nan."


  "Kiyi hak'uri Mami beyi zafi haka ba yi hak'uri."


  "Haba! Wace erin 'ya ce bata jin magana haka? Ba sa'anninki bane suke aure a k'auye amman don an barki anan kina girman jaki kina abinda kika ga dama zaki soma wuce gona da iri? Wancan ma a gefe amman ace kullum sekin k'ona min miya idan nace ki kula da shi? Kinada kud'in sake min wata cafanin ne?" Shiru Amal dake la6e bayan Afzal tayi se faman share hawayen dake ta faman zubo mata take da hannunta. 


   "Ba dake nake bane?" Nan Mami tayi kaman zata ture Afzal don ta jawo Amal daga bayansa ta gaggaura mata mari saidai Afzal be bar aukuwan hakan ba as da sauri ya janye Amal sukayi baya yana kareta. "Kice mata tayi hak'uri" ya juyo yana kallon Amal saidai ko d'ago kai ta kallesa batayi ba bale tayi yadda yace se faman kukan zucin da takeyi tana hawaye. "Lily ki bawa Mami hak'uri nace" ya sake fad'a mata. 


  "Kiyi hak'uri" ta furta a hankali. 


  "Ni da kene a gidan nan ai ba Papinki yayi tafiya ba? Zan koya miki hankali ma tukunna maza jeki ki tattaro duka novels d'innan ki kawo su nan in cinna musu wuta ba shakka suke d'auke miki hankali 'yar iska kawai."


  "Ya isa Mami please kiyi hak'uri bazata sake ba in shaa Allah kiyi hak'uri" Hak'uri Afzal ya cigaba da baiwa Mami yayinda take ta huci, kunde san yadda fad'an itayenmu mata yake idan suka kama basu san suyi shiru ba, da k'yar ya samu ta hak'ura tayi shiru ta janyo hijabi daga kan igiyan shanya tare da d'aukan purse nata akan benchi ta fice don zuwa bus stop ta sake yin wata cafanin. Tana fita Amal ta ruga cikin d'akinta a guje had'e da jan sakata inda ta fad'a kan katifarta tana kuka. Afzal dake tsaye totally out of what to do daga bisani yabi bayanta, k'ofan ya gwada bud'ewa yaji a rufe don haka ya kira sunanta a nitse. 


   "Lily?" Shiru tayi bata amsa ba se k'aran shesshek'an da takeyi yake ji. 


  "Yi hak'uri ki taso ki bud'e wa Yaya kinji?" Nan ma shiru. "Yaya na miki magana bazaki tashi ba Lily? Yi hak'uri kinji? Ina nan ba inda zani sekin bud'e k'ofar nan" Seda yayi dagaske sannan ya samu ta taso ta bud'e masa, ta kai ga juyawa ta koma ciki kenan ya rik'e k'asan rigarta stopping her. Idanunta da sunka kad'a sukayi ja ta d'ago tana kallonsa a maraice. 


 "Come with me" ba musu tabi bayansa inda suka zauna akan benchi. K'aramar gelen abayan daya tsinta a k'asa wanda yake da tabbacin a garin guje-gujen da suka ta6a da Mami ne ta yasar ya d'ago had'e da mik'a mata. "Gashi cover your hair" nan ma batayi musu ba ta amsa ta rufe bak'in gashinta me uban shek'i. 


   "What happened Lily? Kin manta alk'awarin da kika d'au mun na cewa bazaki sake sa Mami surutu ba? Mey kika mata yau kika fusatar da ita haka har ta ta6amin lafiyar jikinki?" Shiru tayi ta kasa cewa komi gudun kar da ta soma magana ta shiga yin kuka. 


  "Talk to me kinji?"


   "Yaya.." ta furta bayan tsawon lokacin data d'auka kafin ta iya furta wata kalman kuka yaci k'arfinta. Tausayi na hak'ik'a ta basa saboda be ta6a ganinta tana kuka me tsuma zuciya kaman na yau ba toh shin meya faru? A kan k'ona girki zalla de Amal baza tayi kuka haka ba kamar yadda itama Mami bazata tayin surutu yadda tayi ba, mey take nufi data kwatanta Amal da 'yar iska? shin meya faru? 


  Be sake cewa da ita komi ba saboda yasan how badly she needed to cry, ya sani kukan nan da takeyi ne kad'ai ze iya rage mata k'unar da zuciyarta keyi mata don haka ya zauna yana saurronta tanayi badon yanaso ba sedon ba shida wata mafitar. A hankali ta shiga yin shiru, handkerchief nasa ya ciro daga aljihun wandonsa ya shiga share mata hawayen nata a hankali har ya samu tayi shiru. 


   "Yaya-"


  "Shhh" ya katse ta a hankali "Don't speak."


  "Yaya but I need to let you know what's really happening ko Allah zeyi kai zaka yarda da ni kuma bazaka yimin kallon 'yar iskan da Mami keyi min ba."


  "Subhanallah Lily! Meya faru?"


  "Yaya Mami tak'i ta yarda dani dan Allah help me out" ta kuma fashewa da wata kukan. "Wallahi ni ba 'yar iska bace."


   "Shhh it's okay I'm here, yi shiru ki fad'a min meya faru."


  Hanci taja ta share hawayenta sannan ta fara kamar haka; "Ina yaron nan dana ta6a maka hirarsa ranan a office?" 


  "Wanne d'aya? Yaron me markad'en bakin hanyan nan?"


  "Shi" ta amsa tana gyad'a kai.


  "Meya faru?"


  Hawayenta ta share da hanky'n da Afzal ya bata ta cigaba "Yaya sharri yayi mun gun Mami wai kullum ba aikina idan ta tura ni markad'e saidai inyi ta mishi hirar banza ina tatta6ashi."


  "Subhanallah!" yayi exclaiming cike da k'in yarda. 


  "Yaya ko kai na ta6a shafa koda hannunka ne? Yaya ka yarda zan iya aikata abinda yake tuhumata da shi?" Ta tambayesa cikin kuka sosai. 


  "Ko kad'an Amal you'll never do such a thing kibar kukan haka kinji? Your Yaya is here."


  "Thank you Yaya but Mami tak'i yarda dani wai sam ni 'yar iska ce idona a bushe yake ni munafuka ce, bata sanar da Papi ba tukun amman ta rantse se tayi hakan, shekaran jiya data aikeni markad'e ashe yace mata tabi bayana yanada abinda ze nuna mata bayan ya k'arisa markad'en yace in k'arisa in d'auka, dai-dai na kai inda yake tsaye sauran in d'aga roban kenan na zame na fad'a jikinsa ba tare da na sani ba ashe 6awon ayaba yasa mun don in zame. A sanadiyyar ture ni da yayi naji wannan ciwo" nan ta d'aga bakin skirt nata zuwa idon sahu sega wani babban k'warzani, fatan gun gabad'aya ya d'aye don azaba.


  "Subhanallah" Afzal Yayi exclaiming cike da tausayin Lilirsa. "Me kikayi masa ya za6i yayi framing naki haka Amal?"


  "Wallahi Yaya ba abinda nayi masa."


  "Tell me the truth Amal bakiyi masa komi ba?"


  "Wallahi Yaya banda cewa da yayi yana sona na nuna masa ko wuta da aljannah ze bani bazanso mutum irinsa ba bakuma abinda ya sake had'amu shine yace min wai zan gani sena lahira ya fini sukuni." Shiru Afzal yayi ko nazarin me yake se Allah. "Yaya kaima baka yarda dani ba?" Ta tambayesa sabin hawaye na ambaliya a fuskarta "Wallahi ni ban aikata abinda yake tuhumata dashi ba, Yaya please believe me."


   "Shhh!" ya katse ta "I believe you Lily nasan bazaki ta6a aikata abu haka ba, I'm here bazan tsaya ba se inda k'arfi na ya k'are in shaa Allah yaron nan da kansa zaizo har nan gida ya baki hak'uri ya kuma yiwa Mami bayanin gaskiyan al'amarin da bakinsa."


  "Yaya how is that even possible?"


  "Trust me okay?" Kai tayi saurin gyad'awa had'e da yi masa godiya. "Girkin da take cewa kullum kina k'ona mata shi kuma fa, haka ne?"






 RANA D'AYA 

#RD

Love... king Miemiebee👄✨

[12/08, 22:36] ‪+234 907 483 8352‬: 🎀🎀🎀                 🎀🎀🎀

                🎀❣🎀

                   ❣❣


  💦💦                      🍃🍃🍃          

           *RANA D'AYA!*

  💦💦                      🍃🍃🍃

  April, 2018

 beeenovels.blogspot.com


     _Written by Miemiebee👄_



   *PAGE 0⃣9⃣*




    "Quite alright nasan ina k'ona mata miya but tun kan alk'awarin dana d'aukan maka wallahi ban sake ba se yau, kawai tana neman huce haushi na da takeji ne taketa nanatawa haka nan" ta fayyace mai hawaye na tsiyaya daga idanunta. 


  "Meyasa baki sa hankalinki ba kika bari har girkin ya k'one? Bance idan Mami ta saki aiki ki bar duk abinda kikeyi ba muddin ba sallah bane kisa hankalinki?"


  "Ka fad'a" ta amsa tare da dukar da kanta. 


  "Then what happened?"


 "Yaya duk hankalina baya jikina, na rasa ina zan sa kaina da abinda Abdul (yaron me markad'e) yayi min kuma wallahi ba wani novel d'in nake karantawa ba hasali ma ina zaune cikin kitchen d'in amman banma san miyan na k'onewa ba seda ta shigo ita kuma ta dage sam wai novel nike karantawa shi ya d'auke min hankali."


  "Shikenan ya isa, bar kukan haka kinji? Am here for you bari Mami ta dawo zan yi mata bayani."


  Bayan isowan Mami Afzal ya sa Amal ta amshi cafanin ta shiga sarrafawa acikin kitchen yayinda shida Mami suka zauna suna tattauna batun Amal da Abdul. Sam Mami tak'i yarda da abinda Afzal ya fad'a mata a cewarta wai kawai Amal ta tsara Afzal d'inne don ya tausaya mata, ita da ta ga abu da idonta Amal ta kwanta jikin Abdul ne kuma za'a tsaya ana mata wasa da hankali? Daga k'arshe ba don tana so ba se don tana jin nauyin Afzal ta nuna masa ta yarda komi ya wuce. Rok'anta sosai Afzal yayi cewa kar ta fad'awa Papi nan ma de tace taji baza ta fad'a mar ba amman dukda haka Afzal be yarda ba seda yasa ta d'au masa alk'awari. Nan ya zazzage tsaraban daya siyo musun, sosai tayi farin ciki da godiya da addu'a har ta buk'ace sa daya tsaya ya jira abinci amman ya nuna daga gida yake don haka a k'oshe yake. Amal ta kira ta nuna mata kayakin inda itama ta nuna farin cikinta sosai dukda cewa chan k'asa hankalinta a tashe yake. Godiya ba adadi tayi masa itama sannan suka rakosa waje, yau zuwa bakin k'ofa Mami ta rakasa tace su k'arisa da Amal kasancewar miyan dake kan wuta. Wajen motansa suka nufa suka shiga ciki suka k'arisa bakin layi gun markad'en su Abdul. 


   Plan daya shirya yayi ma Amal bayani sannan ya mik'a mata wayarsa bayan ya nuna mata inda zata danna da zaran sun fara magana da shi Abdul d'in. Daga cikin motansa ya zauna yana hangensu yayinda ta k'arasa ta sami Abdul.  


   "Abdul inason magana da kai" tace dashi ba gardama ya mik'e harda d'an guntun murmushinsa ya nufo inda take tsaye. A tunaninsa wai ko tazo ta fayyace mar soyayyan da take masa ne.  Nan Amal ta danna button na play had'e da b'oye wayar k'ark'ashin hijabinta gudun kar ya gani sannan ta fara kamar haka;


    "Yanzu Abdul abinda kayi min ka kyauta kenan?"


  "Mene? Ban fad'a miki cewa na lahira seya fiki jin dad'i ba muddin kika k'i bani had'in kai?"


  "Toh Abdul ana soyayyan dole ne? Ka gane mana bana sonka."


  "Ni kuwa sekin soni in ba haka ba ki shirya wa tashin hankalin dayafi wanda kika shiga a baya."


  "Mey kake nufi da hakan?"


  "Ina nufin a shirye nake da inyi komi domin inga na mallakeki."


   "Kana nufin zaka iya ta6a lafiyata idan banyi yadda kakeso ba?"


  "Sosai ma kuwa har kisan kai zan iyayi a kanki."


  "Lallai kuwa kasani Allah ya fika kuma ma ranan mey kasa min na zame?"


  "Aww ma tambaya kike? 6awon ayaba na ajiye miki bayan nasa Mami ta biyoki ranan don ta tabbatar da abinda na fad'a mata akanki."


  "Dukda cewa kasan k'arya ne ni ban ta6a koda rik'e hannunka ba?"


  "Tabbas sharri na miki mana amman ai na ja miki kunne ko ba haka ba? Kuma na baki nan da sati kije kiyi tunani idan har baki amince da soyayya ta ba ina tabbatar miki da cewa gaba abinda zan miki se 'yan unguwan nan sun k'yamace ki zaman unguwa ya kasa ki ba zaman gidanku kad'ai ba."


  "Nagode se muga yadda Allah ze baka nasara" daga fad'in haka ta juya ta fice. Tana shiga mota ta mik'a wa Afzal wayan inda yayi stopping ya kuma yi saving sannan yayi playing suka saurara. 


  "Good job Lily kinga da wannan muna iya kai k'arar sa kotu against the crime of misdemeanor but kafin nan I'll meet him personally to make him go and apologize for you idan har yak'i complying then I'll have to bring police for him."


    "Yaya you're going to do all these for me?" Ta tambayesa a hankali tana mamakin yadda Afzal ke nuna tsananin damuwa duk lokacinda ta shiga matsala. 


  "Wanda yafi haka ma zan miki Lily muddin ina raye kuma inada halin" ya jaddada mata. 


   "Thank you Yaya sakallahu bil jannah."


  "Ameen don't worry."


   "Toh barin koma gida ka gaishe da Ummi in ka isa."


  "Ki bari in mayar dake."


  "Haba Yaya nan da gidan ne kuma har seka mayar dani dan Allah ka bari."


  "Lily-"


  "Please Yaya karka damu" ta katse sa a nitse. 


  "Toh shikenan and please Lily karki sake yin abinda ze fusatar da Mami koda tana miki surutu kiyi mata shiru in har zakiyi magana toh ya zamanto hak'uri zaki bata kinji?"


  "In shaa Allah Yaya nagode."


  "Gobe ko jibi in shaa Allah zan shigo."


  "Toh Allah kaimu se anjima" da haka ta sauk'o daga motar tabi lungun da ze kaita gidansu. Isan Afzal gida keda wuya, bayan an sauk'o daga sallan Maghrib Abba yayi requesting presence nasa a site nasa. Wayansa kawai ya d'aga yabi bayan Micheal suka zarce site na Abba inda ya zauna kan kujera. Bayan d'an tambayoyin da Abba yamasa game da aiki da makamancin haka ya buk'aci Micheal daya mik'a masa bak'ar ledan dake ajiye akan dining table. 


  "Ga wannan wedding invitation cards naka ne Prince na d'ibi wanda zan rabar wa jama'a na haka Umminka ma wannan naka ne."


 "Duka wannan Abba?" Ya tambaya had'e da zaro idanu waje. Invitation cards sekace wanda za'a rabawa kaf 'yan Maiduguri!


  "Eh Prince nasan iya adadin mutanen da kake dasu fatana de baza su kasa ba ko?"


  "Baza su kasa ba Abba nagode."


  "Yauwa Allah yayi ma albarka."


  "Ameen Abba."


  "Yauwa nace iyayen yarinyan fa suna son fara yi mata jere tunda biki ya matso kusa ga gininka kuma kusan yanzu ma aka fara ina laifin ka yafe neman gidan hayan da kake seka za6i d'aya daga cikin gidaje na dake garin nan? Kowanne ya maka niko zan baka."


  "Ayyah Abba karka damu, I don't want to be a burden to you."


 "Nonsense ko ka manta d'a kake na cikina? Kai de karka damu ni da niyyan baka kyautan gidan ma nake as my own gift for you on your wedding."


  "Abba ba abinda zance sede Allah k'ara maka bud'i thank you so much in shaa Allah gobe nida PA'nka zamuje mu duba gidajen zan sanar da kai duk abinda akwai, nagode."


   "Toh hakan yayi sannu kana iya tafiya."


  "Toh Abba seda safe" da haka ya koma site nasa inda ya fad'a kan gadonsa had'e da zaro d'aya daga cikin invitation cards d'in yana galla mar harara. 25th December daya bada d'in shi ke rubuce jikin invitation card d'in ba abinda aka canza. Ji yake kaman ya tattara duka IV d'in gabad'aya ya k'ona don haushi, da k'yar ya samu yayi bacci ranan. 


   Washegari kamar yadda yayi promising Abba shida PA'n Abba suka dudduba gidajen Abba dake nan cikin Maiduguri wata bungalow ce a New GRA na layin NUJ yayi masa nan yayi deciding ze d'auka, 6angare biyu ne acikin gidan seda BQ. Na gaban wanda ya kasance master side na da two bedrooms, parlour, kitchen and toilet a ciki se main side d'in kuma wanda ya k'unshi four bedrooms da toilet each, two living rooms, kitchen, dining area da kuma store room. Tun a yinin ranan 'yan uwan Mummy da ita Mummy kanta suka shiga yiwa Nazeefah jere. 

   Afzal kuwa ranan be samu zuwa ganin Abdul ba se a washegari, shiga yayi cikin k'ananun kayan da suka mugun amsansa sannan yasa nerdy glasses (fararen tabarau) kafin wajen markad'en ya yi parking sannan ya fito ya tarar da Abdul wanda idan yayi shekaru dayawa a duniya shine ashirin. Ashe ma yaro ne, jiransa yayi bayan ya gama markad'en sannan ya k'arisa yayi masa sallama. 


   "Wa'alaikumus salam" Abdul ya amsa yana me zuba ma Afzal ido ko zey iya tuna ina ya wayi fuskan nasa sede ina ya kasa, ba tantama yau ne had'uwansu na farko kokuma halan yana ganin shiga da fitansa cikin unguwan nan. 


   "Abdul ko?" Afzal ya tambayesa wanda yasa sa gyad'a kai cike da neman k'arin bayani. 


  "Tambaya kake yi ne bawan Allah?" Ya tambayesa. 

  

  "A'a magana nakeso muyi."


  "Toh ina jinka."


  "Batun Amal ne" ya fad'a had'e da yin shiru. 


 "Amal wace Amal kenan?" Abdul ya tambaya yana mey nazari. 


  "Baby."


  "Oh! Wani abun ne?"


  "Game da abinda kayi mata ne nakeson jin gaskiyar batun daga bakinka." Dariya Abdul ya k'yalk'yale da ita "A dalilin mey kake tunanin har zaka ji wata abun daga bakina? Mey alak'arku? Ina da yak'inin cewa Baby batada Ya so meya kawo ka nan?"


 "To make you go and apologize to her and tell her mother the whole truth" Afzal ya sanar dashi cikin tattausar murya. 


  "Turanci kuma zakayi min? Toh dukda cewa ban fahimci duk abinda ka fad'a ba nadeji kanason in sami Mami in fad'a mata gaskiya, ko wani gaskiya kake nufi?"


  "Ka dena pretending kaman bakasan me nake nufi ba, ko ba kai kaje ka samu Mami ka irga mata k'arerayin banza ba akan Amal don ka 6ata mata suna? And also ka ajiye mata 6awon ayaba don ta taka ta zame koba haka ba? Ce maka akayi ana soyayyan dole?"


  "B'awon ayaba? Kai to na ajiye ayimin abinda Allah beyi min ba aikin banza har waye kai zaka tsaya kana gayamun magana iya son ranka wallahi idan ba aikin 'yan tasha kakeson gani ba anan zaka d'ibi k'afafunka ka koma inda ka fito yanzun nan."


  "Zaka je ka bata hak'urin ne kokuwa?"


  "Ba inda zanje ina nan" ya jaddada masa. 


  "Good" Afzal yace tare da ciro wayansa yayi playing mar audio da Amal ta d'auka shekaran jiya. Ido wuru-wuru Abdul ya zaro waje yayin da cikinsa ya d'au ruwa. "Taya ka samu wannan magana?"


   "Wancan be shafe ka ba abinda zan jaddada maka shine ka shirya dan kuwa hukuma zata shiga neman ka."


  "A dalilin meh?"


  "Because you've been found guilty of misdemeanor."


  "Ko mey hakan ke nufi?"


  "Laifi ne wanda kotu ke tuhumar duk wanda ta kama yana ma d'an uwansa barazanar yi masa illa kokuwa lahani na jiki ya kuma cimma hakan. Na farko na sanya wa Amal 6awon ayaba da kayi dagangan don ta taka is a battery crime, haka takawan da tayi kuma ta fad'i kakuma sake hankad'eta taji ciwo shima battery crime ne sannan barazanar illata ta da kayi na cewa idan batayi yadda kakeso ba rayuwarta zata iya shiga cikin matsala shi kuma assault crime ne don kuwa yanzu duk wani mumunin abin da ya sameta God forbid ala misali ma ace wani ne yayi mata kisan kai, kaine nan kotu zata tuhuma saboda nauyin kalamunka" Afzal yayi masa bayani. 


  "Toh naji nayi dukkanin abubuwan daka k'irga amman waya ganni ina cikin aikatawa?"


  "Smart guy kenan seems like ka mance muryanka ne acikin audio d'innan." 


  "Murya kace, murya kuwa sama da mutane goma suna iya yin murya iri d'aya kuma nan yanzu naga dama ina iya sauya murya na in k'aryata duk ewata hujjar da kake tak'ama da ita."


  "Zaka k'aryata fa kace?"


  "Sosai ma kuwa tunda ba fuskata bace murya ne."


  "LOL a gaskiya nayi mamakin yadda ka kasance baho a matsayinka na d'a na miji" Afzal yayi magann had'e da zaro glasses da yake sanye dasu. Wata k'aramar cable yaciro daga aljuhun wandonsa ya had'a da wayansa da glasses d'in sannan ya shiga yin 'yan wasu danne-danne. Shi de har anan Abdul kallonsa yake, zuciyarsa bata tashi tsinkewa ba seda yaga fuskansa live a cikin wayan Afzal tun daga lokacinda yake amsa sallaman da Afzal yayi masa har izuwa k'arshen maganan da yayi. Ashe de glasses me CCTV Afzal ke sanye da wanda ya aro daga gun wani abokinsa lawyer, glass ne me camera ta gefe biyu duka wanda yake baiwa wanda ke sanye da ita daman yin video record na duk abinda yake tsaye gabansa. 


  Nan take cikin Abdul ya d'au ruwa gyaran murya Afzal yayi had'e da kashe wayan nasa ya mayar aljihu "Se muga yadda zaka iya kare kanka yanzu a kotu idan na nuna musu wannan don kuwa akasin hakan na iya janyo maka one year inprisonment (shekara d'aya a gidan yari)."


   "Shekara de?" Abdul ya nanata cike da k'in yarda lallai kuwa ya yayyafa wa kansa ruwan sanyi. Ai kafin yasan Baby ma ya rayu se akayi yaya don tace bata son sa? Yaga de soyayya bata kisa. Yanzu bama wannan ba waze na taya mahaifiyarsa yin markad'ai da kula da kuma saiwa k'annensa 'yan biyu magani idan aka turasa gidan yari? Amman wannan mutumi baze gama da duniya lafiya ba yanzu akan d'an k'ank'anin abinda ya aikata wanda be d'aukesa a bakin komi ne ba har yake neman jefa masa rayuwa cikin had'ari haka? Hmm!


  "Ka shirya gobe polisawa zasu zo nemanka don kaika kotu muddin kayi tunanin guduwa kuma that will be a double offense and kasani cewa duk inda ka shiga a fad'in garin nan me sauk'i ne a kama ka, a word is enough for the wise" Afzal na kaiwa nan ya juya ya shiga tafiya. Daga bisani Abdul da yayi shiru tun d'azu ya rasa na cewa bLe nayi ya k'wala wa Afzal kira had'e da bin bayansa. 


  "Bawan Allan ka tsaya, don Allah ka tsaya kayi hak'uri" ko ta kansa Afzal beyi ba se faman tafiyansa yake. 


  "Dan Allah ka tsaya" Abdul ya fad'a a lokacin da ya iya yasha gaban Afzal causing him to stop. "Dan Allah karka kaini kotu kayi hak'uri, k'annena biyu suna iya rasa rayukansu idan kayi hakan please."


  "Ashe de bakada kunya? Kasan da hakan amma kai baka tsaya kayi tunanin cewa da abinda kayi wa Amal ka sa ta rasa martabarta da darajarta a idon iyayenta ba?"


  "Na tuba officer don Allah ka rufa min asiri."


   "Bana magana biyu bana kuma ja da baya, tun wuri ka nemo lawyer'n da ze iya tsaya maka a kotu dukda cewa nasan mey wuya ne yin hakan saboda evidences da nake dasu a kanka are strong."


  "Wallahi ko kud'in d'aukan lawyer ma banida kuma koda ina dashi ma ni bazanyi fad'a da kai a kotu ba amman kayi hak'uri don Allah."


  "Matsa min a gaba in wuce."


  "Naji na amince zan bawa Baby hak'uri in kuma fad'awa mahaifiyarta asalin gaskiyan al'amarin amman don Allah ka ja baya da kai k'arana kotun nan."


  "Come again kace zaka yi mey?" Sake nanata abinda ya fad'a yayi a rud'e "Wallahi idan kana so yanzun nan ma ina iya zuwa in bata hak'urin ni de kawai ka ja da baya da zancen nan."


  "Ni kakeson raina wa hankali? In ba wai ka kurmance bane I said to get out of my face ka kuma shirya gobe za'a zo a d'auke ka."


  "Officer dan Allah kayi min rai ka tausaya min." Bayan d'an tsawon lokacin da Afzal ya d'auka daga bisani yace, "Shige cikin motar nan."


  "Dan Allah kayi hak'uri."


  "Ba wani gun zan kaika ba a idanu na nakeson ka bawa Amal hak'uri saboda in zame sheda."


  "Ba kotun zaka kaini ba ko?"


 "Kaga alamun wasa a tattare da ni ne?" Da sauri Abdul daya gama rud'ewa ya kad'a kai tare da zagayawa ta passenger's side ya bud'e murfin motar ya shiga. Dai-dai inda Afzal ya saba parking yayi ma yau suka fito da Abdul dake biye dashi a baya suka k'arisa cikin gidansu Amal. Da mamaki Mami ta kar6esu ta shimfid'a musu tabarma sannan Afzal ya buk'aci ganin Amal. 


   "Tana Sallah" Mami ta amsa sa a takaice "Lafiya dai ko?" Ta tambaya duk ta kid'ime. 


  "Lafiya k'alau Mami ki kwantar da hankalinki" zaman jiran Amal suka shiga yi, bayan ta kammala azkhar nata ta fito sanye da d'aya daga cikin hijaban da Afzal ya d'inka mata chan daga gefen Mami ta zauna ta gaishesa bayan ya amsa ya ta6a Abdul da yayi tsit tun shigowansu ko gaishe da Mami ya kasa da nufin yayi magana. 


  "Bazaka yi maganan bane?" Afzal yace dashi cikin tattausar murya. 


  "Zanyi zanyi, Baby kiyi hak'uri" ya furta yana kallon k'asa. 


  "Ka d'ago kanka tana kallonka kana kallonta ka bata hak'uri don't make me change my mind." Kan nasa ya d'ago ya kuma bata hak'urin kamar yadda Afzal ya buk'ata, ita de Mami sosai ta tsinci kanta cikin duhu ko hak'urin mey?


  "Saura Mami."


  Gyaran murya Abdul yayi sannan ya nesanta yace, "Mami kema kiyi hak'uri ki yafe min wallahi sharri nayi wa Amal bata ta6a aikata koda rabin abinda na fad'a miki tanayi ba duk sanda kika turo ta markad'e, k'azafi nayi mata saboda tun ba yau ba nike cewa ina sonta amman tak'i bani had'in kai senayi tunanin hakan kadai ce mafitar da zeysa ta soni idan nasata na dole amman don Allah kiyi hak'uri."


  "Abdul? Da hankalinka kuwa? Kasan me kake fad'i?" Mami dake jin al'amarin kamar wata raha ta jero wa Abdul wannan tambayoyi cike da rashin yarda. 


  "Tabbas na sani Mami amman kiyi hak'uri."


  "Kai d'ago kai ka kalleni ka kuma sake nanata min abinda ka fad'a" ta buk'ata.  Ba gardama ya kuma yi, mamaki ne sosai ya rufe Mami akan kunyan da ta jiyo. Shin yanzu da wani idon zata sake kallon Amal? Amman kam Abdul be kyauta mata ba, take gun ta soma nadamar duk abunuwan da tayi ma Amal barin ma zaneta da tayi gaban Afzal da kuma kiranta 'yar iska da tayi shi yafi komi ci mata rai. Ita ta tarbiyyarta da Amal be kamata tayi kokonto akan hakan ba koda mey aka fad'a mata akanta face ta tara hujjoji da dama, amman kuma ai itama ba laifinta bane duk mahaifiyar data ga 'yarta na rungumar wani dole ranta ya 6aci but even still kamata yayi tayi bincike tabi diddigin komi ba wai tayi jumping into conclussion ba. 


   _Gareku iyaye bawai duk abinda aka zo aka fad'a akan 'ya'yanku zaku d'auka ku zauna akai ba saboda muna zamani ne yanzu wanda munafukai sukayi yawa wanda burinsu bai fi su 6ata wa yara suna a idanun iyayensu ba, mutum ya tabbata  yayi bincike sosai tukunnah saboda kamar yadda yara keda hak'k'i akan iyayensu to suma fa yaran nan haka suke da hak'ki akan iyayensu kuma duk wani iyayen da ya d'au hak'k'in d'ansa toh fa Allah ze tsayar dashi akan hakan, Allah is the best of all Allah kare mana zuri'ah, ameen._


   "Amman Abdul tsakani na da kai sede Allah ya isa wallahi."


  "A'a Mami dan Allah kar kice haka" fad'in Afzal. 


  "Toh mey zance Afzal? Ka dubi yadda na rik'a d'aukan alhak'in Baby mana Baby?" Ta kirata tare da kewayo da kallonta akan Amal datayi lamo jikin garu tana was da k'asan hijbinta. "Baby ki yafeni nasan nayi miki laifi Baby kiyi hak'uri."


   "Mami ya wuce Allah yafemu gabaki d'aya."


  "Baby nima ki yafeni don Allah" fad'in Abdul. 


  "Da Allah chan malam rufa man baki kuma maza ka tashi ka bar min gida kuma in shaa Allahu sena sanar da mahaifiyarka abinda kayi mana da 'yata tasan cewa bakada hankalin ko kobo."


  "Mami please calm down tunda har Allah yayi shi Abdul ya sauk'e girman kai ya gane kuransa ya kuma zo ya bada hak'uri kamata yayi ki yi hak'uri ki yafe masa mu kanmu munayi wa Allah laifi amman kuma yake yafe mana so please kiyi hak'uri" Afzal yayi bayani a hankali. 


  "Wallahi darajan Afzal kad'ai kaci in ba haka ba Allah ne kad'ai zai mana hisabi kuma dukda hakan ma se mahaifiyarka taji wannan zance." Hak'uri da wa'azi akan yafiya Afzal ya tayi wa Mami cewa duk wanda ya rufa wa d'an uwansa asiri toh shima Allah zeyi masa ranan gobe k'iyama, hakan ne kad'ai yasa Mami ta hak'ura daga k'arshe ta ja baya daga alwashin data d'aukan ta kuma jaddada masa cewa ya fita harkan Amal idan har ya sake yi mata wani abun ko ya tinkareta da kalman so toh se inda k'arfinta dana Papi ya k'are. 


   Da yazo tafiya ne ya mik'a wa Mami invitation card na d'aurin aurensa cewa a baiwa Papi. Sosai Mami ta tayasa da murna tare da yi mai fatan alkhairi. Ko bayan tafiyan Afzal kuwa hak'uri Mami tayita bawa Amal amman Amal ta nuna mata ba komai ya riga ya wuce. Alhamdulillah tunda Afzal ya cika mata burinta ya wanke ta daga cikin daud'an da Abdul ya aza mata. Bata san da wata bakin zatayi masa godiya ba. Da daren ranan ne bayan sallan Isha ta ari wayan Mami ta tura masa saqo tana mey masa godiya na sosai tare da yimasa addu'o'i da dama. 

  

~•. .•~                 ~•. .•~                 ~•. .•~


   Preparations na biki ne ya sha gaba sosai ta fannin Ango da Amarya gabad'aya as auren na faruwa ne acikin sati na uku me gabatowa. 

      Afzal yadda kuka san ba ango ba, ba abinda ya d'agashi bale ya nana shi a k'asa d'an shirye-shiryen angoncewan nan ba abinda ya ta6a. Muddin baya tare da Amal ko Sultan toh su uku suna tare ne, sosai yake taimaka mata da karatun jamb nata irin past questions d'innan duk ya sai mata tana bin exercises d'in on her own tana solving. Gashi Allah yayi kuwa Amal is a very fast learner, aya bata k'arya dama malamai sunce duk meh haddan Qur'ani a ka toh karatun boko baya basa wuya, Alhamdulillah Amal na ja sosai ta fannin boko. 


   Ta fannin Nazeefah kuwa dukda cewa ba son auren take ba amman don ta k'ure k'awayenta 'yan k'aryan nan ta bawa Mummy had'in kai sosai. Sam kuma bata nuna wa k'awayenta cewa auren had'i bane za ayi mata da Afzal, hasali ce musu take ita da Afzal sun jima suna soyayya kawai sun yi deciding to keep it private ne, gyaran jikin nan tun dawowansu daga Saudi wata mata daga Nijar keyi mata. Shirye-shirye de ba inda ba'a ta6o ba. 


   Ana saura sati biyu d'aurin aure Mummy da kanta ta kawo wa Ummi invitation na programmes of events da za'ayi wanda suke nan kusan guda biyar. Ita kanta Ummi shakkan sanar da Afzal take sanin halinsa, tasan sarai yau d'inma se sun haura sama kafin ya amince gashi ko Abba baze tilasta masa cewa lalle-lalle se yayi attending ba tunda ba abun addini bane saidai da mamaki data nuna mishi invitation d'in ko complaining beyi ba illa ma cewa da yayi Allah ya nuna mana. A satin gaba aka soma events wanda duk wanda ake buk'atan halattar Afzal ya samu yaje illa bridal shower da Walima wanda k'awayen amarya ne zallah da family. Bawanda ze ga Afzal da Nazeefah yayi tunanin wai auren dole aka sanya su saboda walwala da farin cikin da suke portraying. A haka ne har Allah ya kawo ranarda aka d'aura auren Afzal da Nazeefah akan sadaki dubu d'ari biyu da sisin gold guda hamsin wanda daren ranan Ummi tayi organizing gaggarumin dinner to welcome Nazeefah into the family. Budiri sosai aka sha gun dinner, ba yadda Afzal beyi ba da Amal cewa tayi attending event d'in amman tak'i a cewarta wai dinner ne bazeyi tasa hijabi ba se gyale ita kuma a rayuwa idan akwai abinda bata so shine ta fita da jikinta a bud'e. 


   Bayan abokan ango sun sallami k'awayen amarya suma bada dad'ewa ba suka tafi ya rage Afzal da amaryarsa kad'ai. Bayan rakiyan da yayi musu ya dawo ciki inda ya zarce kitchen ya d'au goran ruwa yana sha yana tafiya, har ya kaiga bud'e k'ofan d'akin seyaji Nazeefah na magana. Sa hankalin da zeyi ya gano a waya take maganar don haka ya kasa kunne yana mey saurararonta. 


   "Haba Bestie a dalilin mey zan had'a shimfid'a dashi? Ai da in bashi kyautan budurcina na gwammaci wasu 'yan iskan chan sunyi min fyad'e a kan layi... Hm ai kede bari tunda aka tauye min hak'k'i aka aura min shi I'll make sure shima na tattauye masa hak'k'i a gidan nan zamuga iya gudun ruwansa, sooner or later ze rubuta min takardan saki na se muga ko shima Daddy d'in ze sake bin gida by gida yana rok'on yaran mutane da su taimaka su aure masa yarinya."


  Murmushi Afzal ya saki tare da kad'a kai sannan daga bisani ya bud'e k'ofan yasa kai ciki. Nan take Nazeefah ta katse wayar tare da cusawa k'ark'ashin pillon dake gefen hannunta. Ko k'ala be ce mata ba ya nemi waje ya zauna ya kwankad'e ruwan daya d'auko daga kitchen, kazan amarcin da su Sultan suka sanya sa siyan na dole ne ya d'ago daga side drawer'n dake gefensa ledoji biyu ne ciki da alama kowanne da kaza d'ai aciki. D'aya ya d'auka ya tura mata d'ayan side nata. 


   Lek'a cikin tayi ta tabbatar kazan ne a ciki sannan tace, "Kana iya d'aga gabbage d'innan daga gaba na dan kuwa ba a yunwa ka d'auko ni daga gidan ubana ba" ta sanar dashi cike da rashin kunya bako tsoron ido, sede yadda kuka san bada Afzal take ba ko kallonta beyi ba bale yasan da shi take, ledan kazan ya gama bud'ewa ya shiga ci seda ya ci kusan rabi sannan ya kora da juice dake gefe se a nan ne ya dawo da kallonsa a gareta yaga de har yanzu bata ta6a kazan nata ba. 


  "Kina iya bar min d'aki I suppose this is my room and I want to sleep" yace da ita cikin deep voice nasa. Da mamaki ta tsaya tana kallonsa. "D'akinka fa kace? Wallahi idan har kaga nabar d'akin nan to gawa na akazo fita dashi idan kaga you can't cope with me the earlier the better tun wuri ka rubuta min takardan saki na ba d'akin kad'ai zan bar maka ba gidan in whole" Ba tare da yace komi ba ya zaro d'aya daga cikin ninkakkun kayakin baccinsa had'e da ragowan kazansa da drink nasa ya fice mata daga d'akin. Se yanzu Nazeefah ke bin d'akin da kallo tabbas tasan wannan gado baya d'aya daga cikin wanda ita da Mummy suka siyo daga Dubai bade Afzal bane ya taho da abinsa? Oho! Koma meye anan zata na kwana sede shi ya bar mata d'akin. Rage kayan jikinta tayi ta janyo kazan taci fiye da rabi, tun wayewan garin Allah yau banda tea da tasha seda maltina d'aya bata sake cin komi ba. Bayan tayi nak ta tsiyaye ruwa daga dispenser tasha sannan ta shiga bayi ta watsa ruwa tayi alwala tayi sallah daga k'arshe ta kwanta. Tun kwanciyanta ba abinda taji wane gawa se bayan dawowan Afzal daga massalaci ne yayi tunanin dubata don tabbatar da ko tayi sallah ko batayi ba. Knocking bisa k'ofar yayi sannan ya bud'e ya kunna wuta inda ya tarar da ita kwance se bacci take tayi. Wutan d'akin gabad'aya ya kunna wanda hakan ya sata bud'e idon dole. 


  "Kina iya tashi kiyi sallah" daga fad'in haka ya mai mata da k'ofan ya fita. Wayewan garin Allah keda wuya Afzal ya bud'e wayansa don going through feeds, mails da messages nasa gabad'aya ma ya mance yau birthday nasa ne seda ya soma cin karo da message na Amal wanda take wishing nasa happy birthday sena Ummi da Abba da sauran mutanensa. Kiransu yayi one by one yana musu godiya, kasancewar Amal ce ya kira k'arshe bayan sun k'are wayan take tambayarsa in ze iya shigowa yau she has a surprise for him. Bayan sun gama wayan ya katse ya fad'a bayi yayi brushing sannan ya zira d'aya daga cikin jallabiyansa ya fice siyo musu breakfast bayan yaci nasa ya zauna a parlour yana replying birthday wishes from followers and friends nasa na social media accounts nasa. 


   Yana cikin hakan ne chan sega Nazeefah ta fito daga d'akinta da alama banda brushing da tayi ko wanka bata d'aura akai ba dan kuwa da sleeping dress nata na jiya ta fito sanye da, kanta kuwa a bud'e yake ta kama sa sakwa-sakwa a tsakan kanta. Dining direct ta nufa tana hamma yayin da ta janye takeaway'n da Afzal ya ajiye mata ta soma ci ba gaisuwa bale godiya. A nitse ya mik'e ya bar mata dining d'in ya shiga d'akin data kwanan, kayanta na jiya, wayanta, charger, ragowar kazanta da wata k'aramar akwatin da yake da tabbacin ba nasa bane ya fito dasu bakin k'ofan ya ajiye sannan ya tattaro kayakinsa daga d'ayan d'akin daya kwanan ya maida su asalin d'akinsa had'e da locking k'ofar ya sa key d'in a aljihunsa dai-dai nan Nazeefah ke shigowa corridor d'in.


   "Ya haka Mallam?" Tayi saurin tambaya ita da take da aniyyar shiga d'akin ta koma bacci. Yi yayi tamkar be jita ba, ta gefenta yaso bi seta tare sa "Wannan wani irin childishness ne? Taya zaka watso min kayaki na waje? Wallahi tun wuri ka bud'e kokuma a kunnen Ummi."


  "Ummi kad'ai? I thought Abba zaki kira, I told you this is not your room why're you so dumb to realize that? Zan fita idan na dawo na tarar da kayakin nan anan don't be surprised idan na wulla su waje" Daga fad'in haka ya bud'e d'akin ya shiga tare da locking again. Bayi ya shiga yayi wanka tsaf ya shirya cikin k'ananun kayan da suke bala'in amsan figure'nsa ya fice gidansu Amal. Nazeefah dake tsaye har yanzu bakin k'ofan ta rasa nayi se binsa da kallo take a ranta tana tunanin abinda zatayi masa ta rama wannan rashin mutunci. Haka ba yadda ta iya ta tsuguna ta tattara kayakinta, sauran d'akunan ta dudduba sannan ta d'au d'aya aciki. Akwatunanta wanda muhimman kayakinta ke ciki ta jawo ta kaisu d'akin da ta tare sannan ta jejjerasu cikin wardrobe d'in. Bayan da ta gama ta fad'a bayi tayi wanka ta shiga bin gidan tana zagayawa har anan Afzal be dawo ba. Da azahar Nazeefah ta soma jin yunwa, tayi girki ne? Ta tambayi kanta. Amman ai amarya bata girki a ranar farkon kaita gidan miji kamata yayi har na wata Afzal yana siyo musu abinci ko ba haka ba? Zama tayi a parlour ta shiga duban channels na DSTV in search of abin kallo. 


   Afzal kuwa fitansa ya wuce gun Sultan daga chan ya zarce gidnsu Amal. Gani yayi an shimfid'a babbar dadduma a tsakar hidan gashi ko ina fefes kake gani fiye dana kullum. Kan daddumar ne aka jera kuloli na abinci daban-daban ga silver flasks kusan kala hud'u da yake da tabbacin Aldeb da su ginger ne aciki. Da murmushi kwance a fuskansa ya k'arisa ya zauna daga gefe chan sega Amal ta fito sanye da purple jallabiyar data sha stone work koba a tambaya ba ansan kaya ne me tsada kuma ba shakka yana d'aya ne daga cikin tsaraban da Afzal ya kawo mata. D'aurin kai me kyau tayi irin na zamanin nan da ake kira Zahra Buhari wanda k'awarta ta koya mata. 


   Cike da kunya da girmamawa ta k'ariso ta zauna daga d'ayan 6angaren da Afzal ke zauna had'e da gaishe sa. 


  "Yaya?" Ta kirasa for the second time jin be amsa gaisuwan ba da tayi mar banda kallonta da yake ko kyafta ido babu. "Yaya?" Ta kuma kiransa se anan ya kad'a kai yana me dawo da kansa asalin rayuwa daga duniyan tunanin daya fad'a. 


  "Lily?" Ya kirata yana me kasa d'auke idonsa a kanta har yanzun. Ba wai wani kwalyan azo a gani tayi ba kwalli zalla da powder ta shafa se lip gloss amman wani kyan da tayi sekace wacce a ka yima bridal makeover. 


  "Yaya lafiya?" Ta tambaya yayinda kallon da Afzal keyi mata ya soma sanya ta tsoro. 


  "I'm sorry" ya furta tare da kawar da kansa. 


  "Wani abu ne Yaya?"


  "Nothing Lily illa kyan da kikayi, kinyi kyau sosai" ya sanar da ita wani murmushi cike da jin kunya ta sakar masa. "Kai Yaya har kasa naji kunya" ta amsa tana kare fuskarta. 


   "Masha Allah ina Mami?"


  "Tana ciki tana fitowa."


  "Lily wannan kuma fah?" Ya tambayeta yana nuni da kulolin. 


  "Har ka mance yau birthday naka ne? This is my birthday treat for you."


  "Lily you didn't have to do all these for me, I'll appreciate even the little things from you."


  "Haba Yaya ai you deserve even more, nifa raine kawai zance baka d'auka ka bani ba so kabar damuwa don Allah, Happy birthday."


  "Thank you Lily, I do appreciate but next time please karki kashe kud'inki a kaina haka save it you'll need it more yanzu nawa kika kashe anan?"


   "Yaya ba wan-" katse ta yayi gano tana shirin yi mai k'arya "Remember kin d'au alk'awari cewa baza ki sake yimin k'arya ba."


  "Toh Yaya kabar tambaya na nasan zaka min fad'a."


  "I promise bazan yi ba."


  "Ba kud'i na ni kad'ai bane harda na Mami da Papi."


  "Lily!"


  "Yaya please stop complaining kai nawa ne baka kashe ba akan mu a gidan nan? Ina de fata Amarya bata cika maka ciki ba" da wayo ta canza topic d'in. 


  "Ai ko a k'oshe ma nake I must create room for Lily's cooking." Murmushi cike da jin dad'i ta sakar masa sannan ta shiga bud'e kulolin sede duka favorites na Afzal ne aciki, d'ayan flask d'in pepper soup na kifi ne aciki se kuma d'ayan garnished spaghetti wanda yasha sardines kaca-kaca aciki. A rayuwa ba abinda Afzal keso kaman kifi yafi sonsa fiye da kowani irin form of protein. Bayan n ga su spring rolls da samosa abinde ba'a cewa komi. 


  Amal na cikin serving nasa kenan sega Mami ta fito itama tayi wankanta fes cikin wata atamfa d'inkin riga da zani. 


   "Bak'on namu ya iso kenan" ta fad'i tana nufan inda suke tare da zama gefen Amal. "Ina yini Mami?" Afzal ya gaisheta cike da girmamawa, bayan nan tayi masa fatan alkhairi na shiga sabon shekara da addu'o'i da dama. 


  "Thank you Mami da wahala haka kuma."


  "Haba Afzal ai ka zamo na gida yanzu ina ce de abincin gishiri beyi yawa ba ka de san girkin Baby kullum da k'urak'uri."


   "Kai Mami! Lily fa ta iya girki ai daba don boko ba se a bud'e mata restaurant." Gwalo Amal ta juya tanayiwa Mami harda kama kunnenta. 


   "Kade hura mata kunne d'an girkin data iyan ma ta shiga kofsa sa."


   "Ai sede ta k'ara himma ko Lily?" 


   "Sosai ma Yaya kodan wasu suji kunya" Amal tayi maganan tana nufi da Mami. 


  "Aw taron dangi kuma za'ayi mun? Toh barin baku waje ina d'aki idan kuna buk'atan wani abun."


  "Toh Mami" Afzal ya amsa, da haka ta shige ciki yayainsa Amal ta rink'a jan Afzal da hira yana cin abincin har seda yayi nak sannan ya kora da zo6onsa me sanyi ta kawo masa ruwa da sabulu ya wanke hannunsa. 


  "Yaya are you free today?"


  "Sure Lily wani abu ne?"


  "Yaya saura sati biyu exams na mun gashi ban gama covering syllables d'in ba ko zaka taimaka min?"


  "Why not Lily? Jeki d'auko books nakin." Cike da jin d'adi ta shiga ta d'ibo books natan nan ya fara tutoring mata ababen da bata gane ba, mamaki ne sosai ya cika Amal sosai yadda Afzal ke solving questions d'in da ko ita da take fresh gradute ma baza ta iya ba. Sa hankali sosai tayi tana mey d'aukan duk abinda yake koyar mata ahaka har Papi ya dawo ya tarar dasu. Bayan sun gaisa yayi ma Afzal fatan alkhairi na shiga sabon shekaran da yayi shima sannan ya k'arisa ciki ya samu Mami. 


    Se La'asr Afzal ya musu sallama bayan tattara mishi ragowan birthday treats da Amal tayi cikin robobin takeaway daga k'arshe ta rakasa. Masallaci ya zarce yayi sallah inda ya wuce restaurant ya sai wa Nazeefah abinci shikam na Lilirsa zeci zuwa anjima. Isansa gida keda wuya ya tarar da Nazeefah da yunwa ya gama cin k'aniyanta se shar6an bacci take ta bar Tv na aiki da alama ko sallah ma batayi ba. Sauk'e ledojin dake hannunsan yayi akan centre table sannan ya d'au remote ya shiga bubbuga mata har se lokacinda ta tashi. 


   "Ke bakisan lokacin sallah yayi bane?"


  "Ka kama ka barni da yunwa laifin waye don banyi sallah akan lokaci ba?" Ta tambayesa cike da rashin kunya yayinda take adjusting position nata don zama. Ledojin ta shiga bi da kallo daga bisani kawai tasa hannu ta janye d'aya daga cikin ledojin da Amal ta had'awa Afzal wanda ke d'auke da Aldeb dasu samosa da wuri ya mik'a hannu ya wabce har yana neman ji mata ciwo. 


   "Ya haka Malam? Ko abincin ma hana ni ci zakayi?"


  "Yes tunda kika d'au wanda ba naki ba" ya amsa ta a takaice, takeaway'n daya tsaya ya sai mata a restor ya wurga mata "Ga naki."


  "Lallai ma! D'an wannan zaka bani? Sauran kuma fah? Ka kaisu ina? Ai wannan rashin adalci ne."


   "See banida lokacin exchanging words da ke in kinga ya kasa miki bazaki iya ci ba kinada mota kina iya fita ki sai abinda ya miki" yayi maganan had'e da zaro wallet nasa dubu uku ya k'irga ya ajiye mata "Here you go amman kam wannan ba naki bane don ko wacce tabani ma tasan da zamanki amman batace in ragar miki da komi ba" yana kaiwa nan ya tattara abunsa ya kai fridge ya sanya su ciki had'e da sa key ya zira a aljihunsa.  Binsa da mumunan kallo Nazeefah keyi yayinda ya zo wuceta ya shige d'akinsa. Mik'ewa tayi ta nufi fridge d'in ta gwada bud'ewa seji tayi ya kulle da key don takaici ji take kaman tasa hannu aka tayi ihu sa'ansa d'aya yasa key da kuwa sede ya tarar da empty goruna next idan ya fito. Kuma wai don rashin kunya har yake ce mata wai wacce ta basa bata ce da ita aciki ba? Hmm wato budurwa ma yake da? Ai kuwa bazata fasa kula samarukanta ba itama face ya dena kula 'yan matansa. Dry abincin nata ta zauna taci ta kora da ruwa sannan ta zarce d'akinta tayi sallah. 


***

     Wajajen 10:12pm Nazeefah ta ajiye wayarta da take ta faman chatting na asara tun d'azu. Sallan Isha ta idar sannan ta fito parlour don neman abinda zata sa a baki. Afzal ta tarar zaune a parlour da plate na samosa da su spring rolls kusan biyu a gabansa ga kuma flasks da take da tabbacin juice ne a ciki se faman cin abincinsa yake yana kallo. Murmushi ta sakar wa kanta don kuwa a nata tunanin kalan abincin dake gabansa itama ya sai mata. Cike da jin dad'i ta k'arisa dining da mamaki ta tarar da shi empty ko leda d'aya babu akai bale kula to ina abincin nata ita? Kitchen ta shiga ta leqa sede shar ba alaman komi, yau akeyinta. Parlon ta dawo taje tayi tsaye a kansa "Malam where is my dinner I'm hungry" ta sanar dashi cike da gadara kaman wanda bazeyi magana ba yace, "Seki shiga kitchen ki girka abinda ya miki."


   "Ban gane inyi girki ba ka ta6a jin inda Amarya tayi girki ne?"


   "Aww ashe amarya kike" ya amsa har anan be ko juyo ya kalleta ba balle ya san wani kalan kaya take sanye dashi. 


   "Wallahi Afzal bana cike da rashin mutunci wannan son kai da mey yayi kama? Kai ka sai wa kanka abinci ni kuma kace min inyi girki? Yanzu baka ji kunya ba."


   "I really don't know what you use your ears for I told you wannan duka da kike gani anan bani akayi bawai fita nayi na siya ban sai miki ba and don ke kuma bazan fita da daren nan ba da sunan sai miki abinci ko ki nemi abinda da zaki dafa kici or simply kisha ruwa ki kwanta bana son hayaniya kina iya barmin kai."


   "Kai wai rashin mutunci ka gada ko? Mu zuba ni da kai a gidan nan and see who will surrender first aikin banza kawai!" tana kaiwa nan ta nufi d'akinta Cookies ta k'wak'ulo cikin kayakinta ta zauna taci don kuwa ta gommaci ta kwana da yunwa data aikata abinda Afzal yace mata dan kuwa be isa yayi iko da ita ba. Juice nata tasha akai sannan ta cigaba da chatting nata har se lokacinda bacci ya d'auketa. Kamar jiya yau ma Afzal ne yazo ya tayar da ita sallan Asuba, yana mey mamakin sakaci irin nata ace da girmanta amman bazata iya sa alarm ta tashi tayi sallah ba yaso ta koma baccin. 


     Haka rayuwar nasu ta cigaba da kasancewa ba ci gaban ko k'ala, dai-dai da rana d'aya Nazeefah bata ta6a d'aukan tsinstiya ba da sunan shara iyaka idan d'akinta ya gama baza datti sannan zata d'an share sama-sama. Afzal da bai saba da zama cikin k'azanta da daud'a ba tuni yasa Micheal ya nemo masa me aiki na miji wanda bayan kwana bibbiyu yake zuwa ya share gidan tas ya kuma yi mopping harda goge amman banda d'akin Nazeefah kasancewar dokan da Afzal ya kafa masa. Bugu da k'ari Afzal be fasa siyo musu abinci ba kaman yadda ya d'au alk'awari wa kansa. Abinda ya kama daga kan breakfast, lunch and dinner duk ya d'auke wa Nazeefah ita de aikinta bai fin taci ta sha tayi wanka da bacci sede abinda yake damunta d'aya ne, yawan fitan da Afzal keyi. Ace mutum kullum bai yini a gida? Ya fita tun safe se yamma abinda ke kawosa kad'ai shine delivering abincinta. Bayan tana da tabbacin an basa leave a office balle yace aiki yake zuwa. Shin ina yake zuwa? Toh wallahi itama baza a barta a baya ba. Afzal na fita itama zata d'au wankanta tabi bayansa. Dai-dai da rana d'aya Afzal be ta6a tambayarta ina take zuwa ba koda kuwa ya dawo gida ne ya tarar bata nan harkan gabansa kawai yakeyi idan ta dawo kuwa ko kallonta baiyi bale ya tambayeta daga ina tafito. Tun abun bai damun oganniyan taku har ya soma ci mata rai yana tsaya mata a wuya shin shi Afzal d'innan wani irin miskilin mutum ne? So take yace ze mata magana kan yawon da take wataran amman ina. Rashin hankalin nata har ya kaiga wani sa'in ma mangariba ba a gida take ba amman haka ko d'aga ido ya kalleta bai yi idan ta dawo. Ita ba haka taso abin ba taso ace ya gwada tinkarar ta koda so d'aya saboda su yita ta k'are tayi masa rashin kunya iya son ranta in yaji zafi ya sake ta amman ko shiga harkanta baiyi a gidan. 


   Kasancewar k'arfe bakwai na safe Amal zatayi jamb nata yau tun shida Afzal ya gama shirinsa, yana cikin shan black tea sega Nazeefah da tun d'azu ya tada ita sallah amman tak'i tashi se yanzu ta fito, yanzun ma sabida ishin ruwan daya isheta ne. Da fari da ta gansa tayi tunanin ko office zasa amman seta gansa sanye da half jumper tabbatar mata da cewa ba chan d'in za sa ba. Lallai ma kuwa sabon iskancin daya koyo kenan, wato yanzu sammako ma ze fara yi toh Allah ya taimakesa ya kawo su ranan da zata tabbatar da zargin da take akansa in har ta tabbatar 'yan matan waje yake bi toh in shaa Allahu zamansu ya k'are don bazata hak'ura ba har seya sake ta, aikin banza kawai. K'arisawa gun fridge d'in tayi ta d'au ruwa ta koma d'akinta shiko yana kammala breakfast nasa ya fice. Already Amal na jiransa lokacinda ya isa, Allah bada sa'a su Mami suka mata sannan tabi bayan Afzal suka fito. Acikin Unimaid tayi jarabawartan, bayan addu'an da Afzal yayi mata ta k'arisa cikin exam hall d'in, Afzal be je ko ina ba zama yayi cikin motarsa kusan na awa biyu da k'ari yana jiran fitowar Amal. Sanin dole zata ji yunwa kaman yadda shima yakeji don kuwa gashi rana ta fito, bayan data gama exams d'in ya wuce dasu restaurant inda suka karya da chips sannan ya sai wa Nazeefah nata. Har gida ya mai da Amal ya komo nasa shima, akan dining ya ajiye wa Nazeefah abincin nata ya k'arisa d'akinsa ya kwanta don biyan baccin da yayi missing. 

   Bayan kwana uku results nasu Amal ya fito. Tunda Amal taji results ya fito hankalinta ya tashi jira kawai take Afzal ya kirata yace mata ta fad'i. Shiko Afzal a ranan da aka saki results d'in ya shiga website d'in ya duba mata inda ya tarar taci...




RANA D'AYA!

#RD

Love... King Miemiebee👄✨

[12/08, 22:40] ‪+234 907 483 8352‬: 🎀🎀🎀                 🎀🎀🎀

                🎀❣🎀

                   ❣❣


  💦💦                      🍃🍃🍃          

           *RANA D'AYA!*

  💦💦                      🍃🍃🍃

  May, 2018

 beeenovels.blogspot.com


     _Written by Miemiebee👄_



   *PAGE 1⃣0⃣*


  

     Points har 225, damn! Sosai yaji dad'i ya kuma yi alfahari da ita yana me kasa 6oye farin cikin da ya tsinci kansa a ciki. Layin Mami ya kira take, kasancewar itace ke kusa da wayan yasa ta d'aga, bayan sun gaisa ta kaiwa Amal wayar tun kan ya buk'aci hakan. 


  "Assalamu alaikum Yaya ina yini?" Ta fad'a lokacin da ta amshi wayan daga hannun Mami tana mey azawa a kunnenta. 


  "Wa'alaikumus salam Lily, ya kike?" Ya amsa. 


  "Alhamdulillah ya gida ya Nazeefah kuma?"


  "Lafiya Alhamdulillah."


   "Toh masha Allah."


   "Hmm" ya numfasa had'e da yin shiru, hakan yasa Amal tambayar ko lafiya. 


  "Results naku ne ya fito" ya sanar da ita cikin wani irin salon daya sa Amal yanke hukuncin ta ma riga ta fad'i exams d'inne. 

   "Innalillahi!" ta furta yayinda zuciyarta ta buga. 

  "Ban ci ba ko?" Ta tambayesa a hankali bayan d'an lokutan data d'auka. 


  "Toh gashi nan de-" ai bata basa daman k'arisa abinda yayi niyya ba ta katse wayar. Ba shiri ta fad'a bayi ta d'auro alwala, tana cikin shimfid'a sallaya wayan ya shiga ruri dubawan da zatayi taga Afzal ke kira wani tsinkewar zuciyarta ta kuma yi ba shakka ta fad'i d'inne in ba haka ba da tun da ya kira ze sanar da Mami. Nata ya k'are yau, shin ina zata sa kanta? Da wani idon zata sake kallon Afzal?? Hmm har ta hango tokari da habaicin da Mami zata yi mata idan ta gano ta fad'i jarabawar nan. Sanya wayan tayi a silent sannan ta shiga kawo nafilfilu. 


    Ta 6angaren Afzal daya san rud'ewa irin na Amal kuwa da gan-gan yayi hakan dama ba don komi ba se don yayi dariya kamar yadda yakeyi yanzu, har picturing fuskanta yadda ta rud'e yake a kansa. Two more missed calls ya k'ara mata har anan bata d'aga ba don haka ya tura mata sak'o;


   'Lily pick up that phone.' Dai-dai lokacin da take sallame sallan sak'on yake shigowa batayi ta kai ba seda ta gama tofe addu'o'inta sannan ta lek'a screen d'in. Bata kai ga bud'ewa ba se ga call nasa n shigowa ta sani muddin bata d'auka ba ransa ze 6aci, ba don tana so ba ta d'aga had'e da yin shiru. Shima shirun yayi don kanta ta soma magana. 


   "Yaya don Allah kayi hak'uri" jin yadda ta rud'e shiko ya canza ra'ayinsa na sanar da ita aslin batun ya soma da cewa, "Lily meya faru?"


  "Tell me Yaya na fad'i ko?" Ta tambayesa cike da tsoro. 


  "Your results..." se kuma yayi shiru. 


  "Yaya don Allah kayi hak'uri wallahi ni kaina ban san ya akayi na fad'i ba please don't tell Mami."


  "Am so disappointed in you Lily shin duk abubuwan dana koya miki daman ba ganesu kike ba kokuwa amfani da computer d'inne baki iya ba?"


   "Wallahi ni kaina ban sani ba amman kayi hak'uri don Allah."


  "Nide nayi asaran biyan kud'in jamb."


  "Please kayi hak'uri" ta furta a hankali yayin da takejin haushin kanta. 


  "Yanzu Lily ki rasa nawa zaki ci se 225?"


  "Na shiga uku 225!" ta nanata a rud'e tsabagen yadda ta rikice hankalinta be ma bata taci ba se chan abin ya buga mata kai "225 fa kace Yaya?"


  "Eh" ya amsa. 


  "Toh ai naci ko?"


  "Congratulations Lily" ya fad'i yana mata dariya. 


  "Omg! 225! Yaya I made it! Oh Alhamdulillah" take ta sauk'a k'asa tayo sujudush shukur tana meyiwa Allah godiya sannan ta cigaba da ihun, don kanta tayi shiru. 


  "Kin gama ihun? Afzal daya nisantar da wayan daga kunnesnsa ya tambaya. 


  "I'm sorry Yaya ban tsammanin zan iya 6oye farin cikina."


  "Sure you can't, ko ni nan na kasa 6oye nawa. Keep it up Lily I'mso proud of you."


  "Thank you Yaya but the accolades goes to you, kai ka koya min ababe da dama."


  "Duk da haka Lily kinyi k'ok'ari you know what? Kin cancanci kyauta." 


  "Kai Yaya dagaske?" Ta tambaya cike da kunya. 


  "Yup kina gida gobe?"


  "Eh" ta amsa. 


  "Good, zan shigo in shaa Allah."


  "Toh Yaya seka shigo amman fa ka tsinka min zuciya wallahi na d'au na fad'in ne dagaske har na soma tunanin da wani idon zan sake kallonka" ta fayyace mai. 


  "Matsoraciya kawai ashe baki yarda da kanki ba."


  "Not really kasan shi E exams sa'a ne ba a yi mishi baki."


  "Da wannan kuma but even still my Lily is such a clever girl."


  "Thank you Yaya" hira kad'an suka ta6a sannan suka yi sallama. Kan Mami da Papi ta fad'a bako sallama ta soma yi masu wak'an taci jarabawar ta inda suka mugun tayata da murna barin ma Papi. Alwala duk suka d'auro sukayi nafillah raka'a biyu don yima Allah godiya. 


   Washegari kaman yadda Afzal ya d'au alk'awari hakan ya cika yazo ya d'auki Amal ya kaita shopping amman kunya yak'i barinta ta d'au koda abu d'aya a ganinta wai hakan ya zamo rashin godiya taya akan duk d'awainiyyan da yake mata da kuma wanda zeyi mata a nan gaba ace ya kawota shopping ta baje tana kwasan kaya?


   "Lily kina son muyi fad'a ko?"


   "Yaya wallah nida nasan nan zaka kawo ni ma da ban biyoka ba tun farko don Allah karka damu am good."


  "Lily nifa na kawoki or isn't wrong for a brother to take his sister shopping?"


   "Not at all Yaya kawai ba abinda zan iya d'auka anan ne."


  "Dalili? Ba abinda ya miki anan? Kin fi son kiyi purchasing products naki online?"


   "Waye ubana?" Da sauri ta bige bakinta "Ni ba abinda nake nufi ba kenan kawai deh..." se kuma tayi shiru. 


  "Look kin de san rantsuwa ko?" Kai tayi saurin gyad'awa tana mey k'ure masa ido "Toh wallahi Lily muddin baki d'au ko da abu d'aya ba anan believe me anan d'in zamu yini inda hali har ma mu kwana."


  "Yaya please karka ce haka" tayi saurin fad'i. 


  "Am damn serious" ya sanar da ita cikin tattausar murya. Yana kaiwa nan ya juya ya je ya zauna gun cashier. Tsaye tayi gun jugum totally out of what to do, daga bisani ta juya ta shiga bin store d'in da kallo wanda ya k'unshi kayan kwalya zalla da turare da makamancin hakan. Yau ake yinta kwata-kwata idan za'a k'irga abubuwan data san amfaninsu a shagon basu fi biyar zuwa shida ba toh me zata d'auka don su rabu da Yayanta lafiya? Chan tunani ta fad'o mata gun turaruka ta nufa tuna turarenta ya kusa k'arewa. Bin su ta shiga yi da kallo tana me bud'e kan tana shinshinawa don samun wanda k'amshin zey mata, chan ta d'ago wani da aka rubuta 'adolfo-dominguez' a jiki. Ba k'aramin k'amshi turaren yayi mata ba gashi nan d'an tsut d'an k'arami hakan ya sata yanke hukuncin cewa bazeyi tsada ba. A nitse cike da jin dad'in ta k'ure Yayanta ta tako gun cashier'n inda Afzal ke zaune daga gefe hanklinsa ya duk'ufa akan wayansa se faman latsawa yake tayi gyaran mrya wanda hakan ya sanya sa d'ago kai.


  "Yes where is your basket?" Ya tambayeta, shiru tayi bata ce komi ba "kin d'ai san bana wasa dake ko Lily?"


  "Yaya gashi na d'au wannan" ta furta cike da tsoro tana mey fito da hannunta data 6oye a bayanta. 


  "Mey wannan d'in?" ya tambaya yana bin hannun nata da kollo. 


  "Turare" ta amsa a takaice. A tunaninta ze hau mata k'orafi setaga yana murmusawa ko dariyan mey yake? Ta tambayi kanta. "Kawo ayi miki billing" k'arisawa tayi ta bawa cashier'n inda ya d'au pointer don gano price d'in. 


   "N11,765 (dubu goma sha d'aya da naira d'ari bakwai da sittin da biyar)" ya sanar da su. Da idanu na zubewa a k'asa domin mamaki da na Amal sun jima dayin hakan. Dubu goma har da sha d'aya fa taji cashier'n ya ambata kode ya 6ata ne? D'an wannan turare dayake nan kaman a sa a hancin ne har dubu da k'ari lallae se yanzu ta fahimci ma'anar murmushin da Afzal keyi mata ashe de yasan tsadan turaren ne. Ita haushin kanta ma taji shin meya hanata duba price d'in bayan gashi an manna a jiki harda ticket nasa?


  "Akwai abinda zaki k'ara?" Afzal ya tambayeta cike da neman tsokana. 


  "Cashier d'an kawo wannan d'in Yaya zan canza turaren."


  "Ina wasa dake ne Lily?"


  "Yaya wallahi almubazaranci ne taya turare kad'ai har dubu goma? Don Allah kar ka biya kud'in ni da nasan ya kai haka tsada ma da ban d'auka ba tun farko" Shiru ya mata tare da zaro wallet nasa ya k'irga kud'in ya mik'a masa. Don takaici Amal ji take wane ta kashe kanta, da fesa turaren dubu goma ai gara a baiwa mutum kud'in ya biya buk'atunsa dashi. 


    Godiya sosai tayi masa sanda ya sauk'eta bakin lungun gidansu. Tazo dai-dai da shiga gida kenan sega Ameenatu na fitowa daga gidansu nan de suka gaisa inda Azee ke tayata murnan cin jarabawar da tayi yayinda Amal tayi mata godiya. 


  "Toh daga ina kuma kika fito haka?"


  "Wallahi babu nida Yaya ne muka d'an fita."


  "Oh Baby! Wannan Yayan naki fa ba k'aramin ji dake yake ba 'yan unguwa har sun soma cewa saurayinki ne."


  "Don girman Allah su rufa min asiri ina ni ina Yaya?" Ta tambaya had'e da kwararo idanunta waje. "Wallahi ba komi a tsakanin mu illa soyayyan dake tsakanin Ya da k'anwa."


  "Toh deh tayi tsami ma ji" ta amsata cike da gatsine. 


  "Wallahi Azee babu komai, haba mana kiyi tunani da kanki ina zan kai na miji kaman Yaya? Kema kinsan yafi k'arfina."


  "Haka de kikace amman wata soyayyar bata fi wata ba."


  "Na amince da hakan amman komin taurin kan zuciya still tasan da wa take yi, ba yadda za'ayi zuciyata ta soma son Yaya da wata manufa so tun wuri ku da 'yan unguwa ku sa hankalinku cikin ruwan sanyi."


  "Nifa ban ce komi ba, rana de bata k'arya, tukuna me wannan kika rik'e sekace k'wai a hannu?" Ta tambayeta had'e da zuba ido wa ledan da Amal ta damk'e a hannu. 


  "Wannan?" Amal ta d'aga tan nuna mat "Ai wannan yafi k'wai buk'atan adana."


  "Ko meya saki fad'in haka?"


  "Ke matsalarki bawai a baki labari bane kika tashi sekin k'ara gishirin ki a kai ki baza mutum a unguwa."


  "Haba k'awas wani asirin kika ta6a bani nayi miki haka?"


  "Kar deh?" Ta watsa mata harar. 


  "Ki yarda da ni wallahi ko Falmata bazata ji batun nan ba."


  "Hmm kawai Yaya ya kaini wata shago wai in d'auki duk abinda yamin..." nan de ta baiwa Azee labarin abinda ya faru baki wangalau cike da k'in yarda Azee  ta tsaya tana kallon Amal ita kan ma tak'i yarda seda Amal ta nuna mata receipt d'in. 


   "Wai wai wai gaskiya Yayan nan naki dagaske yake, kut!" Tayi exclaiming cike da k'in yarda. 


   "Ai kede ki bari hakan ma wai yana tambaya ta ko da akwai wani abinda nikeso again." 


  "Gaskiya Yayan nan naki na sonki Baby kuma kikace ba komi a tsakanin ku kai! Da akwai ayan tambaya."


  "Kinga irin halinki da baniso ko?"


  "Toh afuwan afuwan yanzu de d'an bani in fesa turaren a hammata na."


  "Shamawai! Ni me shi ban fesa ba se ke?"


  "Yi hak'uri mana ta Yaya Afzal ke inba ke bama har a kaiki siyayya ki tsaya kina plako ai idan baki buk'atan abubuwan kwalyan mu munayi kuma idan ba son kai bama da kikazo siyan turaren ai ko yan dubu ne seki d'aukan mana da Falmata."


  "Eh naji d'in matso kusa in miki feshi d'aya a hijabi amman ko ba a hammata ba Wallahi don koni ba kazai zanna shafa turaren nan ba se idan ta kama. Chan saman wardrobe m zan ajiye." Rok'arta Ameenatu ta rik'ayi har seda Amal ta amince ta bata turaren ta fesa a hammatarta, tamkar k'wai haka Amal ke tattalin wagga turare. 


****


   Da auren Afzal da Nazeefah wata d'aya da k'imanin sati biyu kenan Afzal yaga fa baze iya da siyan abinci ba kullum bayan gashi shi ba gauro ba. Wannan ma a gefe, hutun da Nazeefah ke samu ya soma yin yawa, na farko ko shara batayi bale mopping da goge-goge don haka ya yanke hukunci daga yau ze dena siyo abinci ita zata soma yi musu girki tunda Allah yayi ya biya sadaki. 


   Washegari, kamar yadda oganniyan taku ta saba se chan shad'aya saura ta tashi. Tayi brushing ta fito sanye da kayan baccinta gashin kan nan a hargitse wane gidan tsunstu. Dining ta nufa inda ta tarar da shi empty.  Dank'aree! Ta furta a zuciye bade abinci Afzal ya sai ba ita ba yau? Juyowan da zatayi se ga Afzal ya fito sanye da k'ananun riguna se buga k'amshi yake. Hannunsa rik'e yake da wata k'aramar saucer wanda ke nuni corn flakes yasha aciki. Gabansa tasha da wuri lokacinda ya zo shiga kitchen d'in tare da kama k'ugunta "Mallam ya ina breakfast d'ina?" Ta tambayesa cike da rashin kunya ko gaisuwa babu. Banza da ita yayi tare da niyyan bin gefenta ya wuce inda ta sake taresa. 


   "Ban gane ina maka magana ba kana miyar dani 'yar iska where is my breakfast?" Kaman wanda baze amsa ta ba yace "Tunda dumb head naki ya kasa figuring out miki abinda ya faru, abinci ne na daina siya, starting today ke zaki fara girki a gidan nan."


  Murmushi kad'ai ta iya ta saki yayinda mamaki ya mamaye mata zuciya. Ko k'ala ta kasa ce masa da kanta ta matsa mishi ya shiga kitchen ya ajiye saucer'n ya fice sannan ta shiga ta dafa indomie sharp sharp taci. Wajajen k'arfe uku Afzal ya dawo, ya d'ibo yunwan duniya ya taho dashi da niyyan cin abinci ya tarar da dining empty, banda plate na macronin da ya sha had'i da minced meat aciki dage gaban Nazeefah tana ci, bayan nan ba komai se cup na ruwanta da juice. 


   "Nawa kuma fah?" Ya tambayeta bayan jan ajin da ta gama yi masa daga bisani tace, "Ban girka ba" ba tare da ta kalli direction nasa ba.


  "Mey na ce miki kafin na fita?"


  "Ba zaka iya ba da barazanar siyo abinci? In ba shi ba toh na manta."


  "Young lady let me make this clear to you muddin kina zaune a cikin gidan nan a k'ark'ashina kike kina ganewa ko? I won't allow it you disrespect me in my own house."


   "Hilarious!" Tayi exclaiming tare da k'yalk'yalewa da dariyan daya mugun k'ular da Afzal "Sannu masu gida, nayi maka rashin kunyan me ka isa kayi? Iyaka kace zaka sakeni, please make it quick ko duka na zakayi? Yanzu kai bakaji kunya ba? Ka kalli tsabar cikin idanu na kace wai inyi maka girki? LOL ina gadara da ji da kai d'in ya tafi? Idan ban manta ba bakin da yace ayi mishi girki yau shi ya ta6a cewa baze iya cin abinda hannayena suka girka ba. Now I see you're not a man of your words" ta k'are tana zuba masa mumunan kallo da dara-daran idanunta. Da k'yar Afzal ya iya danne zuciyansa ya juya ya fice tare da bar mata gidan gabad'aya. Idan yace ze biyewa Nazeefah to k'arshenta zata sanya sa aikata abin kunya ne, amman ko ta guji randa zata turasa jikin bango. 


   Da harara ta bisa yayinda ya ficce tare da furta "Tafi nono fari" k'asa-k'asa. 


  A da yayi niyyan zuwa gida gun Ummi amman gudun abinda hakan ze iya haifarwa se kawai ya wuce gidansu Amal inda ya tarar da ita zaune kan tabarma tana bitan karatu. Sallama yayi a hankali sannan ya shiga. 


  "Wa'alaikumus Salam" ta amsa dai-dai lokacin data kai k'arshen aya jin murya kaman na yayanta . "Yaya!" Ta yi exclaiming cike da jin dad'i bayan ca ta tabbatar da cewa eh shi d'inne. Sede sam ba walwala a fuskarsa har izuwa lokacinda ya k'ariso ya zauna a kan benchin dake gefen taburman da take zaune. 


  "Yaya ina yini?" Ta gaishesa tana mey ajiye Qur'anin da take karantawa a kan mazauninsa. 


   "Yaya meya faru?" Ta kuma tambaya tana me k'are masa kallo. 


  "Lily I'm hungry" ya sanar da ita tamkar wani yaro k'arami. 


  "Yunwa kuma?" Ta nanata "Meya faru? Nazeefah bata gida ne?" Jin yayi shiru tayi saurin mik'ewa ta zarce kitchen Allah yaso yau shinkafa da wake da stew sukayi ba tuwo kaman na jiya ba. Da sauri-sauri tayi serving nasa ta d'auko masa d'aya daga cikin gorunan aldeb dake kula ta ajiye masa. 


  "Gashi Allah sa ka iya cin abincin gidan namu" a nitse ya shiga cin abincin yayinda ta d'ebo mishi ruwa a cikin wata plastic jug. Komawa tayi ta zauna akan taburman had'e da k'ura masa ido tana me mamakin yadda yake cin abincin a hankali dukda cewa yuwa ta addabesa, hakan ba k'aramin burgeta yayi ba. Seda ya cinye tas ya kora da ragowan ruwansa da aldeb d'in sannan ya maido da kallonsa akanta inda idonsu ya had'e, murmushi ta sakar masa "In k'ara maka?"


   "Me kika mayar dani, glutton?"


 Murmushi kad'an tasa had'e da kawar da kanta "Thank you Lily" ya furta wanda hakan yasata maido da kallonta a garesa "Don't mention Yaya you deserve morethan this" murmushin ya miyar mata "ina Mami?" Ya tambaya. 


  "Ta fita gidan biki."


  "Papi fah?"


  "Ya fita kasuwa."


  "Yau ma ked'ai ce a gida?"


  "Eh nima inason in gama bita na ne daman se in fita."


  "Se kuma nazo namiki ruining schedule ko?"


  "Haba Yaya ko kad'an wallahi karka damu amman meya faru?"


  "Game deh?" Ya tambayeta. 


  "Waya ta6a min kai? Waya hana min ka abinci?" Shirun da yayi tayi zaton ko Nazeefah ce, amman meye dalili?

  "Nazeefah ce?" Ta tambaya a hankali, kai zallah ya gyad'a mata. 


  "Toh meyasa?"


  "I don't wanna talk about it Lily I'm sorry."


  "It's okay na fahimce ka."


  "All I know is hak'uri na ya kusa k'arewa."


  "Ayya Yaya se kana had'awa da hak'uri kasan mu mata rauni ne."


   "Rainin hankalin Nazeefah ya soma yawa ne Lily, she is taking my patience for granted." 


  "Se hak'uri Yaya wataran se labari kuma ai kaga Nazeefah yarinya ce idan ban manta ba kai ka fad'a mun cewa she's just 17 years old wasu abubuwan se kana overlooking amman ka sake hak'uri."


  "Shikenan Lily ya wuce."


   

 **** Akan ana gaba zama ya daidaita, tsakanin Afzal da Nazeefah sede abinda ya k'aru. Tun kan rashin kunyan da tayi masa ya daina shiga harkarta kwata-kwata kowa zaman kansa yake a gidan, har rana me kaman ta yau kuwa kwana be ta6a had'asu ba, girki de Nazeefah nayi duk da cewa ba kullum ba amman tanayi na dai-dai bakinta kad'ai, shima Afzal ko da wasa be sakeyi takan kulolinta ba. Gado ba gwaninta ba, munde san hali irin na Afzal idan yayi fushi da abu to ciresa yake gabad'aya daga ransa. Abincinsa yawancin a restaurant yake ci kokuwa gida gun Ummi and atimes gun su Amal. 


   Ana cikin haka ne su Nazeefah suka bud'e makaranta zasu koma second semester kenan. Wayyo ita dad'i kasheta, aga wa Afzal zena fita yana bari a gida yanzu, itama idan ta fita tun safe se shida zata na dawowa abinta. Da safe tsab yau ta tashi ta shirya abinta, bayan ta karya ta leqa parlour taga Afzal bai nan d'akinsa ta nufa ta kwankwasa k'ofa, bayan d'an lokaci ya taso ya bud'e da alama bacci yake don wani kakkafewan da idanunsa sukeyi. Sanye yake da guntun wando zalla wanda hakan ya bawa Nazeefah daman k'are wa k'irar jikinsa kallo. Wai wai wai zalla take furtawa a zuciyanta yayinda ta kasa d'aga idanunta daga kan well visble abs nasa, packs guda shidan nan duk sun bayyano. Ouu la la!


   "Lafiya kinzo kinyi min tsaye bakin k'ofa?" Ya tambayeta yana me tsamo ta daga duniyar tunanin data wula. Da sauri ta kad'a kanta had'e da kawar da kai yayinda ta shiga jin haushin kanta yanzu shikenan Afzal ze soma jin kansa tunda ya kamata tana kallonsa ba ko kyaftawa haka shin meke damunta ne? Mstw! Mozewa tayi tace, "Zani school tunda kayi gwanintan d'aukoni daga gidan mahaifina ya zamo dole ka bani kud'in break bayan nan kuma inason yin full tank wa mota na."


  Se yanzu Afzal ya bud'e idanunsa da kyau yake kuma k'are mata kallo yanzu da irin wannan shirin ne matar aure zata fita? Lalle yau ya sake tabbatawa Nazeefah batada hankali. Kallonta yake daga sama zuwa k'asa. Na farko d'aurin kanta ma ba me mutunci bane ina d'aurin nan na ture kaga tsiya? Shi ta buga a kanta k'eyar nan gabad'ai gashinta ne a waje data nannad'e, ga kuma kayan da take sanye da, wata matsatssiyar straight gown me tsagu a baya wanda yabi surar jikinta tun daga sama har k'asa gaba kuma k'aramar mayafin data d'auka wanda ya kasance small size na gyalen R&S da ta nannad'e sa gefen kafad'arta d'aya. Be ce da ita komai ba ya juya cikin d'akin ya nufi gun safe nasa had'e da sa password d'in. Bayan ya bud'u ya k'irgo kud'i ya dawo ya mik'a mata amsa tayi cike da walak'anci da tak'ama sekace ba wacce tazo tana tambayar  abu ba. Da sauri ta shiga k'irgawa dubu shida ta tarar kafin ta kawo wata tunanin a ranta yace, "2k kud'in makarantar ki 4k kuma kiyi full tank da ita" yana kaiwa nan ya ja k'ofansa ya rufe ba tare da ya bata daman yin magana ba. 


   Mamaki ne ya mamaye Nazeefah don kuwa ko a mafarki bata ta6a kawowa a ranta cewa Afzal ze bata kud'in kashewa a rana har dubu biyu ba kode yana nufin har da na gobe ne? Amma ai da ya sanar da ita. 

   A gida ma gabad'aya dubu Mami ke bata dama-dama ma Daddy ne ke bata dubu biyu. Lallai kuwa auren nan ya d'an had'u ta wani fannin. 


  **** A makaranta...

   

   Nazeefah ne zaune da k'awayenta suna cin abinci a restaurant. Nana ce ta ta6e baki tace, "Amarya kenan kinga wani fresh da kika k'ara kuwa? Gaskia angon nan namu na kula dake."


   "Toh ba dolensa ba" ta amsa tana murmushi. 


  "Amman ya ganki yau da safe kuwa?"


  "Sosai ma ai da shi ze kawo nima nace ya bari kawai yayi baccinsa, wani abu ne?"


  "Babu ai naga wankan da kika d'aukan ne sekace ba matar aure ba."


  "So kike kice wai mijina baya kishina?"


  "Kusan hakan Babe kinga Hafiz (saurayinta da ake shirin yi masu aure) wallahi ko gyale ya haneni da sawa sena tabbata yayi tafiya nake sa abuna amman yana gari kam ban isa ba, d'an banzan kishi ne da shi." Sosai kalamun Nana suka tsaya wa Nazeefah a wuya, da biyu dama itama tayi wannan shed'anin shirin taji ko Afzal zeyi magana se gashi kamar yadda ya saba manna mata hakan yayi. Yo dama mutumin da ba sonka yake ba kam ai ba yadda za'ayi yayi kishin ka wai ma tukun meyasa ta damu? Da yayi kishinta da kar yayi duk uwa ubansu d'aya. 


   Dagewa tayi tace; "Ai da dad'ewa na fahimci Hafiz nakin nan d'an zamanin da ne yo me acikin sa gyale? Kuma kinga Baby na ya yarda dani yasan ko tsindir d'ina na fita bazan kula wani a waje ba kede ki binciki Hafiz naki gani nake kaman be yarda dake ba."


  "Haka dey kikace anyways ga ankon nan fa kunsan abun ya matso" Nana tayi maganan had'e da shiga photos a wayanta don nuna wa k'awayen nata sample. Nazeefah ce ta soma kar6a tana gani "Na farkon lace ce 15k ita zaku sa a pre wedding dinner se atamfar kuma a kamu ita 5k ce, next material d'in kuma na dinner'n ango ne wanda za'ayi a Abuja shi 10k ne altogether is 30k kenan. Kar ku damu da siyan head ango ya d'au nauyin duka biyun tare da makeup wa 3 best friends d'ina."


   "Awww kice mu soma booking makeup artist tun yanzu" cewar Nazeefah tana mik'a wa Adama wayar. 


  "Manyaaaa" Rumaysa tayi praising nata "Gaskiya na sha wutan lace d'innan bari zuwa anjima zan miki transferring kud'in."


  "Ni kuma ko zuwa gobe ko jibi haka kunsan Ummi sunyi tafiya banida enough kud'i" cewar Hadiza. 


  "Nazeefah kefa?" Tambayar Nana. 


  "Ai ko a yanzu ma ina iya k'irgawa in baki tunanin barin Baby na nike for this Abuja dinner anya kuwa zan iya?"


  "Su masu baby! Sha wannan iyayi sede kiyi ma su Rumaysa da basu da direction nikam kinga na kusa" take suka rushe da dariya. 


   "Alright zuwa anjima zan miki transferring."


  Chan da yamma Nazeefah ta dawo gida, ruwa ta watsa ta nemi vest da wata wandon data d'an sauk'o k'asan guiwa da kad'an tasa sannan ta shafa mai a kanta ta kama a tsakiya ta fito. A parlour ta tarar da Afzal yana d'an wasu aikin office d'in, kamar yadda ta saba ba sallama bale gaisuwa ta k'arisa kansa tayi tsaye "Malam ina buk'atan kud'i k'awata zatayi aure kud'in anko 30k, d'inki 15 se kuma na gudumawa 20k."


  Sai dai yadda kuka san kurma haka ya mata wajen ko d'aga kai ya kalleta ma beyi ba ran Nazeefah in yayi dubu be 6aci ba, a rayuwa ba abunda ta tsana kaman shariya. 


   "Mallam ya ina maka magana kana mai dani mahaukaciya?" Nan ma shirun yayi mata, gabansa ta shawo "Mallam magana fa nake" sede shiru by now zuciyan Nazeefah tafasa yake.  Paper'n data ga yana typing content nasa a computer tasa hannu ta waske se a nan ya d'ago lumsassun idanunsa yana kallonta. 


   "Ban gane ina maka magana ba kana mayar dani yar iska, da ba don kayi gwaninta ba ka aureni you think zan tsaya ina tambayarka kud'i ne har ma ka tsaya kana nuna min isa da tak'ama? Wallahi Afzal kake ko wa ka sani ba'a tsiya ka d'auko ni ba, a gida ban ta6a neman abu k'ark'ashin iyayena ba na rasa saboda haka I see no reaso why zanna maka magana kana manna min. Ka bani abinda nake buk'ata wallahi idan ka bari raina ya 6aci naje gida na tambaya kaine da jin kunya ace mutum ko rik'e mace tal ya kasa." Tun d'azun jira take yayi magana amman yak'iyi banda idon da ya kafa mata kaman hoto, bayan ya gama sauraronta daga bisani kawai ya wafce paper'n nasa data d'auke had'e da mik'ewa. Laptop nasa ya d'aga ya shiga nufan d'akinsa yayinda take binsa a baya tana k'orafi da surutu tana habaici tana zaginsa. 


   "Ai da fili ka fito kace baka da kud'in da yafi maka ba wai ka tsaya kana nuna isa da tak'ama ba andeji kunya wallahi ace common kud'in da be taka kara ya karya ba ya gagari mutum" har anan be tanka taba, yana kaiwa d'akinsa ya shiga had'e da sa makulli ya rufe. Ganin suratai da buga k'ofan nasa da take ba shi zaisa ya taso ya bata kud'in ba don kanta ta wuce d'akinta.


 Washegari tun 1 ta dawo gida ta dafa indomie taci sannan ta shirya tsaf ita gata me iyaye tunda miji ya hanata kud'i zata je ta amsa a gun su. Tana cikin shan ruwa sega Afzal ya dawo daga office ko meya faru kuma yau? Shi d'inda se yamma yake dawowa kode wata mantuwar yayi? Ta tambayi kanta. 


   "Yauwa Mallam ka dawo a dai-dai zani gidan mahaifina in tambayeshi kud'in daka hana mun, zan nuna maka rijiya ba gun wasan yaro bane keep your damn money" yana gama sauraronta ya shige d'akinsa file nasa daya mance ya d'auko sannan ya fito. Wato kuma yau don munafirci don zata gidansu shine har da sa babban mayafi ta lullu6e jikinta haka, lallai munafiki ya shiga uku a rayuwa Afzal yayi tunanin haka a ransa. Shi bema d'aurata a ka ba bale abubuwan da takeyi su damesa kamar yadda Amal ta fad'i yarinta ke damunta ga rashin wayo da tarbiyya. 


    Isarta gidansu keda wuya se lale masu gadi da masu aiki suke yi mata kasancewar ta d'au kusan sati biyu bata lek'o su ba. Ita da Khaleefah sekace ba karnukan da suka saba haushi ba harda hugging nasu ba k'arya sunyi kewar junansu. Parlour'n Daddy ta shiga inda ta tarar da shi da Mummy zaune. Waje ta nema a k'asa kaman mey hankalin k'arshe sannan ta gaishesu cike da girmamawa. Sosai suka ji dad'in ganinta cikin wannan kamilalliyar shirin, barin ma Daddy. Ina irin manyan gyalen nan na kashka shi ta lullu6e jikinta dashi tun daga kanta. 


    "Ina Afzal ko yau baku taho tare bane?" Ya tambayeta. 


  "Wallahi aiki yayi masa yawa in ba haka ba daman tare zamu taho amman ko yana gisheku barin ma Mummy wai yaushe zaki sake kawo mana kwad'on dambun nan naki mey dad'i."

Murmusawa Mummy tayi cike da jin dad'i ita kam Alhamdulillah Allah ya bata sirki d'an arziki imagine zuwansu sau biyu nan se yayi ma Khaleefah kyautan kud'i itako na zani. "Kice masa kwanan nan in shaa Allah."


  "Toh Mummy."


  "Toh bari in barku tare zan d'an fita" Daddy ya sanar dasu. 


  "Daddy idan ba damuwa ina d'an buk'atan wani abu."


  "Mene kenan Nazeefah akwai matsala ne?"


  "A'a" tayi saurin amsawa. 


  "Toh madallah ina jinki."


  "Daddy k'awata ce daman zatayi aure" ta fara a nitse. 


  "Toh masha-Allah Allah ya sanya alheri."


  "Ameen" both ita da Mummy suka amsa a tare. 


  "Toh Daddy kud'in anko nikeso dana gudumawa."


  "Toh nawa ne?"


  "Ankon 30k ne se kuma na d'inki 15k dana gudumawa dubu ashirin, Mummy ai zaki iya tuna k'awata data kawo min bedsheets na 40-40k d'innan guda biyu a bikina ko?"


  "Tabbas Allah ya basu zaman lafiya."


  "Yauwa toh daddy ita zata yi aure."


  "Toh kin tambayi Afzal kud'in ne kokuwa?" ya tambayeta. Gabanta ne taji yayi mumunan fad'i me hakan ke nufi? Kame-kame ta shiga yi chan de ta amsa da "A'a" k'sa-k'asa. 


    "Toh ai shi ya kamata ki soma tambaya Nazeefah bani ba."


  "Ban fahimce kaba Daddy" a bak'wance zancen ya isketa. 


  "Nauyin ki ya tashi daga kaina ya koma kan mijnki Afzal, duk abinda kike buk'ata shi zaki tambaya sai idan abin yafi k'arfinsa ne zan iya taimaka miki nan ma sena tambayi izininsa saboda kar a nuna masa rashin isa, ina fatan kin fahimce ni? So kije ki tambayesa tukuna se idan ya nuna baida hali dukda cewa ma nasan hakan baze faru ba amman idan abin ya juya hakan zan tambayesa izini ko nawa kikeso ni kuma na miki alk'awari zan baki."


  "Allah sarki Daddy se naga kaman hakan yayi sauri I mean da auren mu wata nawa ne da zan soma tambayansa kud'i masu yawa haka banda na makarantar da yake bani. Daddy please ko na yau kawai ka bani yaso zuwa nan gaba mun sake sakewa da juna sena soma tambayarsa banson yayi mun mumunar fassara yayi tunanin kud'insa nakeso cin ko makamancin haka."


  "Sam Afzal baze miki mumunar fahimta ba Nazeefah, Afzal yaro ne mey hankali da tunani."


  "Sosai ma kuwa" Mummy ta sanya baki tana mey gyad'a kai. Ji Nazeefah ke wane tasa hannu a kai ta k'urma ihu yanzu bayan gorin iyayen data gama yiwa Afzal ne Daddy keson ta koma ta sake tambayansa? Chab! Yau tana cikin wani yanayi tasani ko sama da k'asa zata had'a Afzal ba bata kud'in nan zeyi ba, menene mafita?


   "Daddy d-" ido Mummy tayi mata da wuri don haka tayi shiru "Toh ni bari in shirya zan d'an fita idan kin koma gida ki gaishe min da Afzal." Ba don tanaso ba ta amsa da "Toh Allah ya kare." Daddy na fita ta taso ta zauna kusa da Mummy. 


  "Mummy dan Allah ki taimaka min."


  "Dame?"


  "Mummy da kud'in please."


  "Wai baki ji abinda Daddy'nku ya fad'a miki bane? Bawai ana hanaki kud'in bane Nazeefah ki gane mana ba a son nunawa Afzal d'in rashin isa ne, baze ji dad'i ba amman yanzu ki gwada tambayansa muji me zece."


  "Ni banason in tambayesa."


  "Dalili?" Mummy ta tambaya da mamaki. 


  "Haba mana Mummy kinde san halin Afzal."


  "Kode naki ba? Tell me something kin tambayesa kud'in nan da rashin kunya da isa yak'i ya baki shine kikazo nan kina yi mana k'arya ko."


  "Ni bance ba."


  "Ja chan har ni zan haifeki ki tsaya kina min k'arya? Toh wallahi ki cigaba."


  "Toh Mummy laifi na ne? Na tambayesa ya hanani me kikeson inyi?"


  "K'arya kike wallahi, idan har a cikin girmamawa kika durk'usa kika tambayesa nasani tabbas ze baki kud'in nan tunda de Allah yayi yana da hali."


    "Wallahi yayi kad'an in durk'usa a gabansa" ta furta ba tare da tasan yaushe ba. 


  "Innalillahi! Kika ce mey?" Mummy ta tambaye ta cike da mamaki. "Wato rashin kunya kike yi masa a gidan ko? Toh wallahi ki cigaba ranan da ya illata ki kece da asara."


  "Mummy please ni in zaki bani kud'in toh in bazaki bani ba ni zan tafi."


  "Ki tafi kar kuma ki sake dawowa maras kunya kawai a da nayi niyyan baki kud'in nan amman tunda haka ne na fasa. Sani ya rage miki ko kiyi humbling kanki ki basa hak'uri ki tambayesa cike da girmamawa ko kuma kije bikin k'awarki ba anko ba gudumawa kece k'awaye zasuyi gulma a bayan ido bani ba kin ganni nan k'awata ta haihu zani suna in kin tashi tafiya ki gaishe min da Afzal."


  "Mummy dan Allah karki min haka Mummy kiyi hak'uri."


 "Afzal zaki baiwa hak'uri bani ba" tana kaiwa nan ta mik'e ko sake kallon Nazeefah dake ta kiran sunanta batayi ba ta wuce d'akinta. Haka idily Nazeefah ta cigaba da zama cikin parlourn totally out of what to do, gashi ba kud'in arziki bane acikin account nata sam be kai N50k ba.  Haka duk su Rumaysa suka sata gaba a bikinta seda kud'in nata ya k'are tas. Mstww! Dan kanta taja motarta ta fice ta koma gida tun isarta take tunanin yadda zata 6ullowa al'amarin nan don a gaskiya bata jin zata iya yin abinda Mummy tace tayi. Ai ma zubar da aji ne, idan ta durk'usa a gaban Afzal ai seya fara jin kanshi ya aza ya kai ne alhalin ba kowa yake ba a idanunta gaskiya no way! Toh kode ta fasa zuwa bikin ne? Gab da lokacin bikin ta soma yi musu k'aryan laulayi na damunta. Kai amman fa k'arya ba kyau don komin yaya ne a k'arshe za'a kamata, haka kawai mutuncinta ya kwa6e. Wayyo Allah menene mafita?


    Share maganar tayi har na tsawon kwana biyu, bayan sati d'aya Nana ta soma damunta da kira tana tambayarta ko lafiya ita da ta d'au Nazeefah ce zata soma siyan anko sekuma gashi. K'arya Nazeefah tayi mata cewa ta mance ne amman right away zatayi mata sending kud'in in shaa Allah da haka sukayi sallama. D'akin nata ta shiga zagayawa tana tunanin ya zata 6ullowa al'amarin sede ta kasa yanke hukuncin komi daga k'arshe de ta yanke hukuncin kirar aminiyarta ko zata iya ranta mata kud'i kafin nan. 


   "Babe wallahi banida kud'i nima da k'yar na samu na had'a kud'in ankon nan na bada d'inki haka ma yanzu bansan me zan kai mata as gudumawa ba wannan shegen saurayin nawa ne ya kod'a ni in gaya miki yace ze turo min kud'i shiru."


  "Toh bestie yanzu what is the way out?"


  "Hmm mafitar ki d'aya ce Bestie."


  "Mey fah?"


  "Humble yourself kawai ki tambayeshi da hankali banda rashin kunya."


  "Haba bestie yanzu wannan itace shawara?"


  "Idiot ai ba cewa nayi ki soma girmamasa ba amman yanzu ki gwada kigani maybe dalilin daya sa ya hanaki don kin tambayesa cike da rashin kunya ne kinde san maza da son a girmama su so ki gwada yin hakan muga ko ze baki."


  "Kai Bestie anya?"


  "Ki tsaya kina taurin kai karki sauk'e wannan girman kan muga inda ze kai ki wallahi kinsan aikinsu Adama k'iris suke jira suyi chaaa a kanki."


  "Toh naji zanyi tunani."


  "Yauwa se anjima Mama na kira na."


  "Aha bye." Da haka sukayi sallama. Zama gu d'aya Nazeefah tayi tana nazari ta bisa a hankalin ne ko kuwa? Timing nasa tayi bayan sallan isha dai-dai lokacinda yake kallon sports ta fito ta leqa sa sekuwa gashi kallon yakeyi. 

   It's now or never ta tunasar da kanta tare da numfasa sannan ta k'arisa parlourn, pack na takeaway'n daya gama ci tasa hannu ta d'aga "Kagama ci zan iya fita dashi?" Ta tambayesa cike da kissa. Kallonta ya tsaya yi na d'an lokaci da tunani kala-kala na tafiya a kansa kode aljanu sun shige ta ne? Kai ya gyad'a mata a hankali nan ta d'aga ta kai kitchen tayi disposing a dawowanta harda d'auko masa ruwa ta tsiyaye a cup ta ajiye masa tare da durk'usawa a gefe shide Afzal banda binta da kallo da yake ya kasa yin komi. 


   "Afzal nace dama kayi hak'uri game da rashin kunyan dana maka ka bani kud'in ankon please." Da mamaki ya zaro lumaassun idanunsa waje sekuma yayi sauri ya kawar da kansa ba tare da yace mata komi ba. 


   "Afzal?" Ta kuma kiransa. 


  "Nawa kike buk'ata?" Ya tambayeta bayan tsawon lokacin daya d'auka. 


  "30k ne ankon, sena d'inki 15k san-"


   "Nawa ne altogether?" Ya katse ta. 


  "65k" ta amsa k'asa-k'asa.


  "Naji" ya amsa sama-sama. Ganin be kuma yunk'urin cewa wani abu ba ta numfasa, "Afzal yau ne nike buk'atan kud'in."


   "Da daren nan kikeso inje ATM? Cash da yake wajena bekai sum da kike buk'ata ba."


   "Toh in baka account details d'ina mana seka min transferring" tayi tunani. Kaman wanda baze amsata ba yace, "Write it down for me" ba gardama ta d'ago wayanta dake kan cinyarta "Ko zaka bani number'nka se inyi maka sending?" Nan ma seda ya d'au tsawon lokaci sannan ya irga mata nan take gun ta yi mishi sending, shima ba tare da 6ata lokaci ba yayi mata transferring sum d'in. Baki bud'e cike da mamaki Nazeefah ta bud'e tana kallon cikin wayarta yayinda ta kasa amincewa da abinda idon ta ke gane mata. "Dubu saba'in?" ta furta a hankali. 


  Kai ta d'ago tana kallonsa yayinda ya mayar da hankalinsa kan Tv'n "Nagode" ta sanar dashi nan ma kaman wanda baze amsata ba yace da ita, "You're welcome" sama-sama. Mik'ewa tayi ta shiga d'akinta tare da fad'awa kan gado cike da jin dad'i. Aminiyarta ta kira dan breaking mata wagga news. "Babe you won't believe this!"


  "Ya meya faru?"


  "Dubu saba'in mutuminki yamin transferring."


  "Like forreal!"


  "I'm telling you wallahi ban d'au ze saurareni ba ma."


  "Hehe kode so yake kuyi sulhu ne?"


  "Lallai kuwa ze 6ata lokacinsa dan kuwa ni ba sa'ar yinsa bane."


  "Omo I dey feel my babe anyways congratulations sekiyi maza ki turawa Nana kud'in."


  "Ai right away, gobe zaki shigo school?"


  "Eh kefa?"


  "Also semun had'u."


  "Alright ba-bye" da haka sukayi sallama inda tayi wa Nana transferring kud'in.





RANA D'AYA

#RD


Love... King Miemiebee👄✨

[12/08, 22:45] ‪+234 907 483 8352‬: 🎀🎀🎀                 🎀🎀🎀

                🎀❣🎀

                   ❣❣


  💦💦                      🍃🍃🍃          

           *RANA D'AYA!*

  💦💦                      🍃🍃🍃

  June, 2018

 beeenovels.blogspot.com


     _Written by Miemiebee👄_



   *PAGE 1⃣1⃣*



  Haka nan de rayuwa ta cigaba da kasance ma wannan ma'aurata ba tare da cigaban komai ba. Nazeefah bata tashi kalmasa kalamunta ga Afzal se idan buk'atan ta ya tashi wanda shi kuma yake biyan mata badon komi ba se don yana ganin nauyinta ya koma kansa yanzu kuma tunda yana da hali. Bayan nan ba abinda yake sake had'asu, girki ma idan ta tashi yi ba dashi takeyi ba kaman yadda ko ta kan kulolinta bayyayi shima. Ana nan watan bikin Nana ya tashi, wanda akayi events duka a nan garin Maiduguri banda dinner wanda dangin ango sukayi organizing a Abuja. A daren tafiyan (bayan d'aurin aure) Nazeefah ta shirya akwatinta tsaf amman ko sanar da Afzal zatayi tafiya batayi ba shide kawai ganinta yayi washegari tana jan akwati amman ko k'ala be ce da ita ba. 


  Kamar yadda ango da abokansa zasu bi jirgi haka itama amarya da k'awayenta suka bi, cikin d'an k'ank'anin lokaci suka isa Abuja, da yammacin ranan suka shiga shirin dinner sede tun abun be damun Nazeefah har ya soma yi a hankali. Kusan kowacce daga cikin k'awayenta seda samarinsu suka kirasu suka yi masu sun sauk'a lafiya amman banda ita da take da miji, ko text message bata gani ba balle kira har d'aya daga cikin k'awartan ke tambayarta ko lafiya taji Afzal shiru itako tayi mata k'arya cewa shima Afzal d'in yayi tafiya bai ma k'asar kwata-kwata. 


  Haka nan suka je dinner suka dawo still Afzal be kirata ba yo taya za ayi ya kirata daman bayan bata sanar dashi inda zata ba. Ta fannin Afzal kuwa koda da yamma yayi har dare ya shiga amman Nazeefah bata dawo ba, be damu ya kirata ba kamar yadda be damu ya kira gidansu ba don jin ko lafiya. K'ofansa yayi locking yayi kwanciyansa. 


   **Washegari da kowa ke juyowa gida ita Nazeefah tak'i akan ita se washegari, haka seda ta k'ara kwana sannan ta juyo. Lafiya k'alau Allah ya dawo da ita gida, koda ta iso ciki a kulle ta tarar da k'ofa, da ta gwada tambayan me gadi key kuwa yake cemata Afzal be ajiye masa ba da ze fita haka nan ta zauna bakin k'ofa tana jiran zuwansa. Ba da dad'ewa ba ya iso inda ya tarar da ita zaune kan kujera a varenda, k'arisawa yayi ya bud'e k'ofar ya shiga ba tare da yace da ita komai ba, itama ko k'ala bata ce masa ba iyaka bin bayansa da tayi ta nufi d'akinta. 


   Gaba dai gaba dai, har Allah ya kawo su Nazeefah k'arshen semester Alhamdulillah ta samu tayi clearing duka courses nata. Tunda akayi hutu mutumiyar ku ta samu saran fita yawo tun safe se yamma take dawowa gida ba wai kuma tana tambayan izini bane fitanta kawai take tamkar zaman kanta take a gidan, ta d'ayan 6angaren kuwa Afzal ya riga ya rantse kan cewa duk uban rashin hankalin da zata tafka a gidan ba zeyi mata magana ba tunda Allah yayi tana da hankali bawai bata da shi ba, sarai tasan what's right and wrong. 


   Ana cikin tafiyan ne k'awar Nazeefah wato Nana wacce akayi auranta bada dad'ewa ba tayi mata waya take sanar da ita k'aruwan da suka samu ita da mijinta. Lis jikin Nazeefah ya mutu tuna yaushe ne akayi bikin nasu har gashi sun samu k'aruwa, ita da auranta ke neman wata shida ko bakwai amman shiru. Zama ita kad'ai tayi bayan wayan tana nazari, gashi de ta fad'i hali d'aya na Afzal da ke k'untata mata ta kasa har rana me kaman na yau bata ta6a jinsa yana waya da budurwa ba, kud'i idan ta tambaya yana bata, girki se ta ga dama takeyi kuma ko uffan bai ce mata, ta rasa dalilin daya sa basu jituwa. Samarukan nata ma da take ganin suna sonta tana da tabbas a kansu suma gashi yanzu da zama yayi zama suma sun soma watsewa suna ja da baya, shin me takeyi wa kanta? Tunani ta fara kode ta sauya halayenta ne ta bawa Afzal dama? Wala Allah zasu daidaita tsakaninsu suma su soma zaman lafiya kaman yadda kowani ma'aurata keyi saidai inaa jiji da kanta baze barta ba. Se ce mata wani ra'ayin yake ai ma idan neman sulhu ne na miji ne ya kamata ya fara ba mace ba don haka zata zuba wa Afzal ido taga iya gudun ruwansa bi izinillahi shi ze soma nemanta. Haka nan ta cigaba da tafka rashin hankalinta amman mey bata ga cigaban komi ba, sam ba canji ta fannin Afzal, tamkar bata gidan haka yake rayuwansa ko kallonta bayayi harkan gabansa kawai yake. Da kad'an-kad'an abun ya soma damun mutumiyarku har ya zammana ita kad'an ta seta had'a tagumi a d'aki tana tunani, ita bawai son sa take ba, ta rantse baza ta ta6a sonsa ba kawai de ita zama haka ba kulawa daga gun miji ne ya soma isanta, duk buro-uban da zata tada a gidan akan lallai-lallai se Afzal ya saketa shi ko be ta6a biye mata ba, hasali ma idan ta fara haukan nata d'akinsa yake shiga ya rufe k'ofa bai fitowa kuwa se ya tabbata tayi shiru kokuwa ya fita ya bar mata gidan ma gabad'aya. 

   

  Ganin ba mahalicci se Allah kawai ta d'au wayarta ta buga wa Aminiyarta Rumaysa kira don tuntu6arta shawara inda zancen nasu ya k'aye haka;

  "Hmm Babe kenan ai ni da jimawa nasan Afzal nakin nan na son ku daidaita tsakaninku kece de baki gane ba" cewar Rumaysa. 


  "Kaman ya kenan K'awa?" Nazeefah ta tambaya take.


  "Kiga mana bayi fa miki magana bale fad'a ko kin neme sa da magana ma baya biye miki gashi kud'i ko nawa kika tambaya ze baki, ai duk neman ki sauk'o ku shirya ne" tayi mata bayani. 


  "Toh meke hana sa sakewa dani? Kiji fa d'azu Nana ta kirani wai she's pregnant."


  "Kai don Allah!" Tayi exclaiming "Allah inganta."


  "Ameen fah wallahi jikina ya mutu haka ranan ma Mummy ta kirani tana min wani irin magana, bata de fito fili tace gashi ba amman na fahimci inda ta dosa."


   "Ke yanzu kina son Afzal d'inne?"


  "Allah wadai inso Afzal wallahi yayi kad'an."

  

  "Toh na me kike tada hankalinki akanshi?"


  "Rayuwa hakan ne ni ya isheni tunda baze iya bani kulawar da ya kamata ba a matsayin matarsa ya sakeni in je in auri wanda zamuyi zaman aure mana."


  "Kema kinsan Afzal kam baze sake ki ba."


  "Toh ya kikeson inyi?"


  "Ki sauya d'abi'un ki na banzan nan kawai, ku daidaita tsakaninku shikenan, shi Afzal bashi da matsala."


  "Babe wai nufi kike in soma yi masa ladabi da biyayya?"


 "Sosai ma kuwa" ta amsa ta take. 


  "Shamawai! Wallahi bazata saku ba wai bindiga a ruwa think of a better solution kawai."


  "That's the only option you have left Nazeefah ki duba kiga da auran ki beyi wata shida ko bakwai ba? Me kika tsinana wa kanki banda kondon-kondon zunubi?"


  "Yanzu K'awa nice kike gayawa magana haka? Ba laifinki bane ni na kiraki har nike tambayar ki shawara ai se anjima."


  "Nazeef-" bata bata daman k'arisa abinda tayi niyya ba ta katse wayar abinta tare da wulla sa kan gado yayinda ta shiga tunani. Tafi sati tana nazari akan abinda Rumaysa ta fad'a mata daga k'arshe de taga fa idan ba wai ta sauya halayan nan nata bane al'amura bazasu ta6a dai-daita tsakaninta da Afzal ba don haka tayi fad'a wa kanta ta d'an rage yawon banzan da take, da safe zata tashi tayi wanka tsaf tasha kwalya ta fito parlour ta zauna tana kallo sede ko Afzal ya fito bata iya gaishesa, dukda cewan tana son ta gaishesan amman ina tak'ama da jiji da kai irin nata baze barta ba. Shi de Afzal ko da yaga canji kwana biyu beyi magana ba, da farko kan ma yayi tunani ko motarta ce ta 6aci amman jin bata yi masa magana a kai ba se shima ya basar kawai ya zuba mata ido don ganin iya gudun ruwarta. Abinsa ze fita office daga chan idan ya tashi ya wuce gidansu Amal atimes kuma in batada abinyi a gida tazo ta tayasa da abokinsa Sultan hira a office nasa. Shak'uwa na hak'ik'a ne ya shiga tsakaninsu wanda a rana idan basu ga juna ba ko kuwa basu ji muryan juna ba se suji kaman zasu shiga cikin matsala. 


   A haka ne har new session ya gabato wato watan d'iban sabon admission wanda Afzal ya tsaya akai sosai don ganin Amal ta samu wannan course da take da buri akai, admission na fitowa bim sunan Amal na cikin first batch wayyo dad'i tunda Afzal ya fad'a mata ta samu admission take ta tsalle-tsalle a gidan ta hana kowa sakat. Chan anjima ta d'au wayan Mami ta kira shi ita yaushe ne zasu fara lectures ita bata ma tunanin registration da sauransu damuwarta kawai lectures ne. Ana fara registration Afzal ya sata a gaba haka ze karb'i excuse a office sujesu Unimaid su bi wa Amal layi inda sanin ido yayi magana ayi mata nata da wuri su gama su koma gida har Allah ya kawo su k'arshen registration d'in, kuma da ikon Allah basu ta6a had'uwa da Nazeefah ba se aranar k'arshe ne layin final clearance wata classmate na Nazeefah back then a secondary school wanda bata samu admission ba se this year ta ga Afzal da Amal. Binsu ta rink'ayi har seda taga sun shige mota sannan ta kira Nazeefah ta labarta mata komai wato Nazeefah bata ta6a sanin tana kishin Afzal ba se a wannan lokaci wani irin wawan kishi ne ya tokareta wanda alokacin takeji inda zata ga wannan yarinya seta soketa har lahira. A farko kan ma taso k'aryata batun k'awar nata har take cemata ai office Afzal d'in ya fita yau don tun 7am ya fita kaman yadda ya saba not knowing daga office d'in ya zarce gidansu Amal ne. Hankalinta de ya kasa kwanciya yayinda ta shiga sintiri a parlourn tana jiran isowan Afzal tayi confronting na shi. Ba shi ya tashi dawowa gida ba se chan yamma. Bata ce masa komi ba dukda cewan a tak'ure take ta mai magana sede wani abun nata rik'eta shin ma me zata ce masa bayan rabonsu da suyi magana wa juna kusan sati kenan yau tun ran da ta tambayesa kud'in wasu handouts da textbooks. Kuma ma ai idan ta mai maganan yanzu ze ga kaman ta fara sonsa ne har take kishi akansa kode ta share maganar ne? Kash sede tana ganin idan har batayi confronting nashi ba tana iya mutuwa don haka bayan sallan Isha ta tabbata ya dawo gida ta fito tayi kansa a lokacin yana zaune a parlour yana ta faman aiki akan laptop nasa. Kujeran dake kusa da nasa taje ta zauna akai, shi a tunaninsa ma gabad'aya kud'i take buk'ata dan kuwa bata tashi zama cikin kamala haka se idan damuwanta ya tashi, duk maganan da zata yi masa tana tsaye a kansa takeyi. Bata kaiga mar magana ba ya katseta "Nawa kike buk'ata?" Ya tambayeta ba tare da ya kalleta ba. 


   Har ga Allah ranta ya 6aci wato irin gata karuwan nan ba ta inda tafi kauri seta fannin kud'i but even still she has no one to blame but herself itace se idan tana neman abu take mar magana ko gaisuwa bai had'asu. Danne zuciyarta tayi tace, "Ni ba kud'i nake buk'ata ba." D'ago kai yayi yana kallonta da nufin idan ba shi ba toh me? Numfasa tayi sannan da k'yar ta furta kalaman "Ina kaje yau da ka fita?" Shi dariya ma ta basa, murmusawa ya shiga yi sosai ta gefe wanda hakan ya bawa one sided dimple nasa daman lotsewa ciki wanda hakan ya mugun fito da kyansa. Shi don dariyan data basa ma ko iya tanka ta ya kasa, don haka kawai ya miyar da kansa kan laptop nasa yana me cigaba da aikin gabansa. Nazeefah da ta ciko dam ji take kaman ta waske latptop d'in ta buga a k'asa wato ma mahaukaciya ya miyar da ita tana mishi magana sede ya kalleta yayi murmushi ya cigaba da harkan gabansa da kyau. 


   "Afzal magana nake maka" ta fad'a  cikin tattausar murya. 


  "Sorry regarding?" Ya tambayeta had'e da kafa mata lumsassun idanunsa. 


  "Where did you branch to after work today?"


  "I think that's none of your business" ya mayar mata tare da kawar da kansa. 


  "Ban gane it's none of my business ba, matarka ce ni and I demand to know your whereabouts."


  "Really?" Ya tambayeta yana me sauk'ar da laptop nasan zuwa kan center table had'e da kewayo da kallonsa gabad'aya a kanta. "Duk yawon da kikeyi a gidan nan did I ever questioned you ina kike zuwa? Tafiya kikayi gabad'aya kin sanar dani ne? And is like you seem to be forgetting wa ke zaman wani a gidan nan, remember that, kece kike k'ark'ashina and not the other way round."


  "Ai da sauk'i tunda ni yawo nakeyi ba'a ta6a buga maka waya ance an ganni ina yawo da wani k'ato akan layi ba kamar yadda kake yi da karuwanka-"


  "Kul!" Yayi saurin katseta "Ko da wasa kar ki sake kwatanta baiwar Allahn chan da karuwa."


  "Idan na sake fa?" Ta tare shi. "Ai ba k'arya nayi ba idan ba karuwa ba tasan kanada aure amman take janka kuna yawo a titi kowa na kallonku, wannan abun kunya dame yayi kama sede a kirani ace min ga miji na akan layi da wata?"


   "Tun yaushe kika fara regarding d'ina as mijinki? That aside koma wanene ya kawo miki wannan rahoto tell that person ba komai tsakani na da yarinyar nan da suka ganmu tare, ta samu admission ne na kuma taimaka mata ta kammala registration nata that's all."


  "That's all? Amman kana da mata a gida baka iya ka mata hakan ba? Kana ganin kayi adalci kenan?"


  "Lmao, har kina da bakin furta kalman adalci?? See I've had a very busy day and as you can see I'm still working idan ke baki da abinda yafi k'wak'wulo suratai please allow me work I'm not ready for this."


  "Toh wallahi ka cigaba muddin ni zan mutuntaka in dena biyewa samarukan da nikeso suke kuma sona don kare maka mutunci I see no reason why da bazaka min haka ba kaima ka dena biyewa karuwanka, ko ka dena ko in d'au mataki da kaina trust me you won't like the details nide na fad'a maka" tana kaiwa nan ta mik'e ta fice. Shi de Afzal bin ta kawai yayi da kallo sannan ya cigaba da harkan gabansa. 


   Washegari...

Gidan wata k'awar Ummi dake sayar da zannuwa, laces da ready made hijabs Afzal ya wuce inda ya d'iba wa Amal kaloli da dama, koda k'awar Ummi ke neman tsokanansa take tambayarsa duka wannan wa amaryar mu ne shiru yamata yana murmushi. Daga chan ya wuce 3G ya sai mata shoes and bags na dad'in fita lectures sannan ya biya gidansu. Kasancewar anyi musu kwalta yanzu har gaban gidansu mota na iya kaiwa, yayi parking dab gaban k'ofar nasun inda ya saba kullum sannan ya mata waya yace ta fito. Ba tare da 6ata lokaci ba ta fito sanye da hijabinta kamar kullum se fara'a takeyi ta k'arasa ta shige suka gaisa bayan nan take tambayarsa dalilin daya hanasa k'arisawa ciki yau. 


   "Haka kawai nace yau bazan shiga ba."


  "Kai Yaya kode wani laifin akayi maka ne inyi gaggawan bada hak'uri."


   "Ai Lily bata laifi."


  "Toh ya kake ya office?"


  "Alhamdulillah yau ba islamiyya ne?"


 "Akwai fa amman bazan samu daman zuwa ba Mami tace zan rakata suna."


  "Ohh! Ina fatan kin soma shirin school, kinsan in a week time zaku fara lectures."


  "Haka nagani a jikin time table d'in, Allah kai mu."


  "Ameen mu fita in sauk'e miki kayakin naki ina da meeting by 3" yayi maganan yana duban babban agogon dake d'aure a hannunsa. 


  "Wasu kayaki kuma Yaya?" Shiru yayi bece komi ba har seda ya bud'e booth d'in motan ya sauk'e kayakin tukuna. "Kinga jami'a zaki shiga yanzu dole kiyi sabin kayaki in bahaka ba wataran seki nemi na sawa ki fita lectures ma ki rasa."


  "Yaya kana nufin duka ledojin nan kayaki ne aciki?" Tayi maganan cike da k'in yarda yayin da take k'ok'arin lek'a cikin "Haba Yaya ina zan kai wannan kayaki haka? Gaskiya kayi hak'uri amman bazan iya amsa ba."


  "Kinde san bana wasa dake ko? Kai zo!" Ya kira wani almajirin dake wucewa, "Zo ka k'arisa da kayakin nan ciki" yana gama kaiwa ciki Afzal ya sallameshi. Ba yadda Amal batayi da Afzal ba yashiga ciki su Papi su mai godiya amman yak'i ya jirata ta shiga ciki ta musu magana ma yak'i haka nan ya tafi sannan ta shigo ciki tana kallon kayakin, ninke acikin d'aya daga cikin atamfofin ta tsinci kud'in d'inki. Ita kam sau dayawa takan zauna tayi tunanin mene tayi wa Allah daya shigo da Afzal cikin rayuwarta, damuwarta tun kan ta furta ze yaye mata shi, d'azun take tunanin yadda zata na fita lectures har ta fifftito da kayakinta tana ware sababbin wanda basu sha ruwa sosai ba. Koda ta kira sa anjima, chan bayan sallan Isha dan su Mami suyi masa godiya kashe wayan yayi wai shi baya so. Washegari ita da Mami suka kai mata d'inki.


    A satin daya zagayo ta amshi d'inkunan nata da tailor tasamu ta gama don fara fita lectures dasu, tomorrow being her first day at school, tun Asuba da Mami ta tada ta sallah bata sake komawa bacci ba ta fad'a bayi tayi wanka, tana cikin shafa mai sega wayan Mami na ruri kasancewar wayan a gunta ya kwana jiya. Ba tare da 6ata lokaci ba ta d'aga suka gaisa yake sanar da ita by 6:30am zezo ya d'auketa he'll be the one to drop her off today, duk yadda taso hanasa yak'i ya amince ita a ganinta d'awainiyan ze yi masa yawa. Shirin ta kammala nan da nan ta karya tashiga jiransa, ana cikin haka ne Papi ya fito ya tarar da ita, kud'in mota dana abinci ya bata inda take sanar dashi halin da ake ciki na cewa Afzal yace ze zo ya kaita. Fad'a sosai Papi yayi mata kan meyasa zata amince masa da hakan maza ta kirasa tace masa zata tafi da kanta. 


  Yana cikin karyawa wayan nasa na dake gefensa akan table ya shiga ruri dai-dai lokacin Nazeefah ke k'arisowa dining d'in zata d'au condensed milk daga cikin fridge da alama itama makarantar zata wuce kaman an aiketa ta lek'a screen na wayansa inda taga 'Lily' na flashing akai. Tunani ta soma don a iya saninta Afzal bai da k'anwa kowacece wannan d'in? Fridge d'in ta bud'e ta shiga neme-neme don ta samu daman sauraron wayan nasa. Goge bakinsa yayi da wata mini towel sannan yayi picking call d'in freely, "Halo Lily?"


  "Na'am Yaya nace ka bari kawai zan tafi da kai na."


  "Meyasa?" Ya tambayeta take. 


   "Kamar yadda na fad'a maka haka ma Papi yace babu amfani kawai zaka sa kanka wahala ne."


  "Ai ni nace zan kaiki ki jirani ina zuwa." Baki wangalau Nazeefah ta bud'e tana kallonsa daga baya kode wannan d'in itace wacce k'awarta Aisha ke fad'a mata ranan? Amman lallai Afzal ya cika wato ita be ta6a cewa ko hanya ze rage mata ba amman idan karuwarsa ce har nema-nema yake tana hanasa da kyau. Duk yadda taso sauraron abinda Amal ke fad'a ta wayan ta kasa. Daga k'arshe de taji Afzal ya kammala wayan da yana fitowa yanzu. Yana juyawa ya bud'e wallet ya ajiye wa Nazeefah kud'in makarantarta bekai da taka k'afa ba ta kira sunansa wanda hakan ya sanya sa tsayawa chak. "Yes?" Ya juya yana kallonta. 


  "Nace mota na ya lalace jiya shi kad'ansa yake hayak'i kuma gashi ina da lectures 7:30 you'll have to be the one to drop me off to school" ta shirya k'aryar nan take. Iska ya fisga yana me sosa kansa cike da rashin sanin abun yi "Why didn't you inform me tun jiya mey gyara yazo ya duba miki?"


  "Na mance se yanzu na tuna."


  "Inada muhimmin gun zuwa yanzu let me talk to Ummi's driver yazo ya kaiki" be bata daman magana ba ya fice. Tun kan ya fita ya kira driver'n Ummi ya sanar dashi buk'atan shi. Haushi ne ya cika Nazeefah dam daba don ta makara ba data bi sahunsa taga gidan wannan 'yar dake raba masa hankali. 


   Isan Afzal gidansu Amal keda wuya yayi parking ya shiga ciki, tana ganinsa ta mik'e tare da yi masa sannu da zuwa sannan ta shiga ta ma Papi magana. Bayan gaisuwa Papi ke masa fad'a kan mey nan da makaranta da baze bar Amal taje da kanta ba, se yake ce masa ai dan yau ranar zuwanta na farko ne shiyasa dukda kuwa shi bek'i kullum shi zena kaita ba muddin yana da hali. Da haka Papi ya musu Allah ya kare suka fito. 


  "Lily?" Ya kirata chak ta tsaya tare da juyawa tana kallonsa, camera kawai ya haskata dashi. "Bade hoto kamin ba Yaya?" Ta tambaya tana kare fuskarta. "Yaya dan Allah ka goge ai ba a yiwa mutum hoton bazata haka."


  "Village girl waya fad'a miki? Ke bakisan unexpected pictures sunfi kyau ba?"


  "Toh ai yau banyi kyau ba fuska na du yabi ya kumbura."


  "Inji waye? Ai dan kyan da kikayi yasa na d'aukeki hoton and today is your first day at school too."


  "Wai nayi kyau kaide kasan kan zagin mutum Yaya."


  "On a serious note kinyi kyau Lily, kyau sosai tabarakallahu feek."


  "Thank you Yaya" ta amsa cike da kunya, haka take duk lokacin da Afzal yace tayi kyau setaji kunya ya ziyarceta, ta kuma rasa dalili. K'arisawa cikin motan sukayi ya jasu, har gaban lecture room nasu ya sauk'eta sannan ya sallameta nan ma seda suka kusan fad'a sannan ta amince ta amshi kud'in, Allah bada sa'a ya mata ta fice seda yaga shigewanta ciki ya ja motansa ya wuce office. 


   Ta fannin Nazeefah kuwa koda driver'n Ummi yazo d'aukanta ko ta kansa batayi ba, motarta taja don bak'in ciki ta wuce school. Throughout the lectures kuwa hankalinta bai jikinta se tunani take haka har suka fita cin abinci ma daga k'arshe seda Rumaysa taja ta gefe take tambayarta ko lafiya, abinku da shagwa6a66iya ba seta 6arke da kuka ba kawai da k'yar Rumaysa tasamu ta sata tayi shiru, ta fad'i meke damunta kuma tak'i, k'arshe gida kawai ta dawo ta watsa ruwa ta kwanta ta hau tunani. 


   Bata son ta tabbatar da abinda zuciyar ta ke raya mata, taya ma zata fara son Afzal?? Is it even possible?? Taya zuciyarta zatayi mata haka bayan ta d'au alwashin bazata ta6a sonsa ba, a farko taso yaudarar kanta da cewa kishinsa kawai take ba sonsa ba amman kuma ai se idan kanason abu ne har zakayi kishi akansa yanzu shikenan ta fad'a kogin son Afzal kenan? Sai dai sam bata bawa kanta laifi ba dalili kuwa shine ta tabbata ko wace macece aka kawota gidan tabbas itama seta fad'a tarkon son Afzal batare da tasani ba, da irin abubuwan da yake yi komin taurin zuciyan mutum dole ne zuciyar tayi laushi ta soma sonsa. Na farko bai ta6a k'untata mata ba a gidan se har idan ita ta tsokolosa, na biyu se abinda takeso takeyi ko k'ala baya ce mata, ga kud'i ko nawa ta tambaya bata yake, wannan a gefe babban tashin hankalinta shine ta gansa zaune ba kaya gashi yadda kukasan al'ada haka ya camfa zama shirtless a gida. Muddin yana gida toh befi yasanya d'an three quarter wando ba idan yayi mutunci shine ya sanya singlet dake bayyana well defined chest nasa, taya idanunta bazasu kwad'aita wa zuciyarta wannan kyakkyawan halitta ba? Ita yanzu damuwanta d'aya ne yadda za'ayi ta cire soyayyan Afzal daga zuciyarta tun wuri kafin tayi mata illa, sede ya zatayi hakan? A tunaninta idan auran nasu ya mutu soyayyar ma zata mutu don haka yau tayi making up mind nata, Afzal na dawowa gida zata tisa sa a gaba yadda ko ya so ko ya k'i seya rubuta mata takardan sakinta tun wuri tasan inda gari ya waye mata.




RANA D'AYA

#RD


Love... King Miemiebee👄✨

[13/08, 00:29] ‪+234 907 483 8352‬: 🎀🎀🎀                 🎀🎀🎀

                🎀❣🎀

                   ❣❣


  💦💦                      🍃🍃🍃          

           *RANA D'AYA!*

  💦💦                      🍃🍃🍃

  June, 2018

 beeenovels.blogspot.com


     _Written by Miemiebee👄_



   *PAGE 1⃣2⃣*



   Tun dawowan Afzal gida ta soma yi masa k'orafi ita ya saketa zaman ya isheta, be kaiga sa key a k'ofan d'akinsa ba ta hankad'e k'ofan tana masa ihu haka yadda ya dawo a gajiye da ciwon kai ya sake ficewa abun tausayi yabar mata gidan gabad'aya ko tanka ta beyi ba. Gida kawai ya nufa ya wuce site nasa inda ya watsa ruwa ya mik'e kan gado se bacci chan kaman a mafarki yaji ana yi masa knocking tamkar wanda baze tashi ba ya lalla6a ya bud'e segani Ummi yayi tsaye bakin k'ofan. 


  "Ashe de dagaske ne ka shigo" ta soma da fad'i tana binsa da kallo na sosai, jin be amsa ba ta k'arisa ciki "Prince?"


  "Uhmm" ya amsa yana kakkafe lumsassun idanunsa wane wanda ya sha abu ya bugu. 


  "Lafiya dai ko? Mey haka sekace wanda yasha wani abu?"


  "Ummi please we'll talk later, a gaje nake yanzu, kaina ciwo allow me to rest."


"A gidanka ba wajen hutu ne da seka zo nan zaka kwanta? Ba za ayi wannan rashin hankalin dani ba. Meye dalilin ka? Chan d'in meya samesa?"


  "Ummi please kiyi hak'uri kaina ciwo yake I'll explain everything to you later."


  "Fad'a min meke faruwa tukun ko sena kira Abbanka?"


  "Gidana ba lafiya and I need to rest right now please kiyi hak'uri" ganin yadda idanunsa ke kakkafewa kawai yasa ta fice ta ja mar k'ofar. Komawa yayi ya kwanta bashi ya tashi ba se bayan Maghrib, ya na idar da sallah ya nufi site na Ummi inda ya zauna a gefenta suka gaisa take tambayarsa meke faruwa. 


   "Babu kawai mun samu misunerstanding ne da Nazeefah" yayi mata k'arya, har ga Allah beyi niyyan fasawa Nazeefah tyre ba saboda there's no point ma, k'arshenta kawai ze had'a kanta da iyayenta ne ya kuma zubar mata da mutunci da girma a idon Ummi. 


  "Prince kalleni" ta buk'acesa. "K'arya kakeyi."


  "Kamar ya kuma k'arya Ummi? Wallahi matsala muka samu amman na tabbata yanzu ta sauk'o zan koma gida muyi negotiating komi idan Abba ya dawo ki gaishe shi."


   "Toh shikenan ka gaishe da Nazeefan kuma ka k'ara hak'uri kaji? Ko zaka tsaya kaci abinci? An kusa sauk'ewa."


  "A'a bana jin yunwa tea kawai zansha idan na isa gida."


  "Toh Babana bari in raka ka se hak'uri zama da mace kaji?" har gun motansa ta rakasa tana yi masa nasiha sannan ta dawo ciki. Da ikon Allah har ya isa gida ya shige d'akinsa Nazeefah dake bayi tana wanka bataji dawowansa ba se chan kusan k'arfe goma da ya fito d'aukan soda daga fridge suka had'u, ba wanda yace ga d'an uwansa ko k'ala kowa harkan gabansa ya cigaba dayi. 


   Kusan sati Afzal ya jera yana kai Amal makaranta sannan ya samu wani me napep suka daidaita wanda ze na kai Amal makaranta yana d'aukota a k'arshen wata se a biya sa. Sosai Amal ta miyar da hankalinta ga karatu, daga bokon har islamiyyan bata bar ko d'aya ba. 


   Ta fannin Afzal kuwa ababen sun soma canzawa suna ca6e masa wanda kuma ya rasa dalilin hakan, haka kawai yake tsintar kansa cikin wani irin nishad'i duk lokacinda yake kallon hotunan Amal kokuwa yake sauraron muryarta baya manta sati d'ayan daya jera yana kaita makaranta, a kullum tana sanye da three quarter hijabanta da side bag nata a gefe kokuwa ta rataya backpack nata a baya. Komin bak'in cikin da Nazeefah ta cusa masa muddin ya shiga kallon hotunan Amal toh seya nemi wannan bak'in ciki ya rasa. Yau ma kaman kullum yana zaune a office nasa gabad'aya ya zurfafa yana kallon wani hoton Amal da take sanye da wani navy blue hijab me hannu, yatsunta ta k'ayatasu da jan lalle wanda ta rik'e fuskarta dasu ta gefe yayinda hankalinta ya duk'ufa kan wani abu, da alama bata ma san an d'auketa hoton ba. Har Sultan ya bud'e k'ofa ya k'ariso cikin office d'in ya zauna Afzal besan ya shigo ba se ji kawai yayi an fisge wayan daga hannunsa kafin yace ze amshe har Sultan ya k'are wa hoton kallo. 


   "Iyye! Ka fad'a kace" ya fad'a mishi cike da meman tsokana. "Kace ta sace maka zuciya."


  "Mtsw! bani waya na" Afzal daya had'e rai kaman hadari ya fad'a cike da tsiwa. Ba gardama Sultan ya mik'a masa wayan amsa yayi ya rufe had'e da cusawa cikin aljihunsa. 


   "Hope I'm not interrupting something?" Sultan ya sake tambayansa mockingly. 


  "Kaga bana son suratan banza, if you've nothing better to say just shut up."


  "Yau kuma? So tell me ka sanar da ita kokuwa kana jira muje ne tare?"


  "What're you even saying?" Ya tambayesa tamkar be fahimci inda ya doso ba. 


  "Don't pretend you don't know, maganan Amal nake."


  "What about her?"

  

  "C'mon maza yau kuma ni zaka 6oye ma abu? Kana son Amal ko ba haka ba?"


  "So fa kace? How is that even possible?"


  "I've been observing you lately, duk abinda ya shafi Amal baka wasa da lamarinsa, the way you smile anytime ta shigo office d'innan shima is not normal ba haka kake ba da gashi typical example yanzu har na bud'e k'ofan ka na shigo na zauna baka san da shigowa na ba gabad'aya hankalinka ya duk'ufa akan kallon hotonta."


   "Shikenan kuma se akace don ka k'irga wannan ababe ya zame ina sonta? Kokuma haramun ne in kalli hotunan dake cikin waya na?"


  "Ai ba kallon tsakani da Allah kake ba."


  "Lmao, da tsakani da tsuntsu ne?" ya tambayeshi sarcastically. 


   "Kallon soyayya kakeyi mata do you deny that?"


  "Shima son yana da kallo ashe ban sani ba."


  "Maza jokes apart daman ni nasan za'ayi haka jiran ranan kawai nake, so ka sanar da ita ne kokuwa kana jiran muje tare?"


  "Nifa suratan banza ne banaso shikenan ban isa in kalli hoto a waya na ba se kace ina son mutumin?"


  "Baka amsani ba zamu je tare ne kokuwa ni in je a madadin ka?"


  "Wallahi da kuwa me hanani yanka ka se Allah."


  "Lol ka yarda kana sonta kenan."


   "Dan Allah drop this topic ni ban ce maka ina son Amal ba, taya ma zan fara sonta bayan kasan yadda take mutuntani ta kuma d'aukeni a matsayin yayanta data amince da shi, that aside ko ka manta ma ni ina da mace a gida."


  "Toh kuna jituwa da matar naka ne kokuwa ance kai mijin mace d'aya ne?"


  "Ba a ce ba amman ni banida ra'ayin rik'e mata biyu."


   "Kana nufin da ba don igiyan auren Nazeefah dake a kanka ba kenan da zaka auri Amal?"


  "Eh I mean no! Subhanallah I mean please shut the fvck up!" Ya k'arisa a fusace. 


  "Woahhh! Lallai kayi nisa maza Amal ta gama da kai."


   "Tashi ka bar min office tashi ka fita."


   "Hab-"


  "Sultan am serious ka tashi ka fita min daga office idan har kasan suratan banza zaka cigaba dayi get out."


  "Lalle bature beyi k'arya ba daya ce love can make you do weird things yau amininka kake kora kaman kashi daga office akan mace?" Mik'ewa Afzal yayi a fusace "Tashi ka fita I'm damn serious." Ganin yadda Afzal ya fusata sosai Sultan yayi shiru ya shiga basa hak'uri yana mai da maganan wasa, "Yi hak'uri ni wasa nake da Allah."


  "Ka fita nace ko sena sa securities sunyi waje da kai?"


  "Idiot kai shikenan baka san wasa ba? I said I'm sorry."


  "Iskanci kawai mtsww" komawa yayi ya zauna "Ya office yau?"


  "Lafiya bazaka ci abinci bane yau?"


  "I'm not hungry yanzun nasha coffee I'm good."


  "Toh nikam bari in k'arisa I'm starving" fad'in Sultan sarai yasan inda Afzal ze nufa so yake ya biya ya d'auki Amal suje suci abincin su biyu. Yana ficewa ba da jimawa ba kuwa Afzal ya d'aga waya ya kira Amal ta wayan Mami da kusan kullum tana zuwa school da shi saboda security reasons. "Halo Lily?"


  "Na'am Yaya ina yini?"


  "Lafiya ya lectures?"


  "Alhamdulillah yanzu ma ya k'are sauran na 3 kuma."


  "Inzo muje muci abinci?"


  "Beyi maka nisa ba Yaya?"


  "Not at all inzo?"


  "Yaya har seka tambayeni izini ne? Se kazo ina jiranka" da haka sukayi sallama in less than 30 minutes Afzal ya iso ya d'auketa. A farko yaso su ci abincin ma a makaranta a cikin unimaid garden amman tuna achan Nazeefah ke cin abinci yasa suka fito suka nemi wani gun daban. Kaman kullum haka yata d'aukanta unexpected pictures tun tana hanasa har tagaji ta miyar da hankalinta ga abincinta kawai. Suna gama ci ya mai da ita school ya koma office. 


   A haka har su Amal suka samu wata d'aya a makaranta, sosai lectures yayi zafi har ya zammana bata samun time na karatun mahadiyya sosai amman dukda hakan ranan da bata gaji lis ba tana tashi cikin dare tayita bita ko hadda. Yau Asabar bayan sallan Azahar Amal ta shirya ta wuce cafe don yin assignment nata kasancewar bata da smartphone irin na zamani na Mami kuwa baida internet. Ana cikin mata assignment d'inne Afzal ya kirata dake ta fita da wayan Mami ta samu ta d'aga "Halo Yaya ina yini?"


  "Lafiya Lily ya kike?"


  "Lafiya k'alau ya weekends?"


  "Alhamdulillah ya lectures ko yau baki fita ba?"


  "Wallahi."


  "Why?" Yayi saurin tambaya a tunaninsa gabad'aya bata da lafiya ne. "Lafiya dai ko?"


  "Assignments aka bamu senazo cafe kuma zan samu inyi."


  "Geez Lily I'm sorry."


  "What for Yaya?"


  "Gabad'aya na manta bamu sai miki waya ba."


  "Kai Yaya kai kam kashe kud'i baya baka wuya, gashi Allah ya kawo sauk'i akwai cafe kota ina a unguwa mey amfanin wayan?"


  "Amman ai still stress ne, har yaushe zaki na fita cafe kullum kina yin assignments?"


  "It is worth the stress ai Yaya karka damu please."


  "Toh shikenan dama baki kira ba yau nace lemmi call up inji ko lafiya"


  "Wallahi lafiya kuma kana raina nima."


  "Alright toh a gama assignment lafiya I'm hanging up."

 

  "Alright take care" da haka sukayi sallama. Washegari da yamma ya shirya tsaf cikin wasu k'ananun kaya da suka mugun amsansa ya feffeshe da turare sannan ya fito parlour inda Nazeefah ke zaune tana yin assignment nata, a two seater ya ajiye wata ledar dake hannunsa sannan ya k'arisa dining space d'auko ruwa. Cikin wannan lokaci Nazeefah ta tashi ta bud'e ledar inda taga sabuwar iphone 6s dal cikin ledar. Mumunar fad'i gabanta yayi, take gun ta yanke hukuncin kaiwa budurwarsa zeyi, wani irin wawan kishi ne taji ya tokareta bata kaiga motsawa gun ba Afzal ya k'ariso ya k'wace ledan daga hannunta. 


  "Ina kuma zakaje?" ta tambayesa lokacinda yake duba cikin ledan don tabbatar da cewa bata ta6a abu aciki ba. Shiru ya mata ya kama hanyan tafiya yayinda tasha gabansa "Yanzu kana ganin abinda kakeyi ka kyauta kenan? Kana ganin kana min adalci kenan a gidan nan? Wallahi ka cigaba Allah na kallonka."


  "Kaman yadda yake kallonki ba, tell me mey kika ta6a nema a gidan nan kika rasa dukda rashin hankalin da kike min ban ta6a tauye miki hak'k'inki ba duk abinda kikeso shi kikeyi a gidan nan without getting questioned what else do you need?"


  "What else do I need?" Ta nanata da mmaki tana kallonsa "Your attention and for you stop flirting around taya da aurenka zaka tsaya kana bin 'yan mata a waje? Do you deny wannan wayar ba wa budurwarka zaka kaiwa ba?"


   "I don't have time for this, na sha fad'a miki ni banida budurwa a waje idan ma ina dashi ba abinda ya shafeki bane I'm a husband to four wives so learn to stay in your lane."


  "Abinda zaka fad'a min kenan Afzal? Dududu auren namu watanni nawa ne har zaka soma kula 'yan matan waje?"


  "Ko nayi ina da laifi ne? Never once did you ever regard me as your husband inba wai buk'atunki sun tashi ba, a tsammaninki kina da right na min magana ne?"


  "In girki ne kakeso naji na yarda zan fara yi maka girki." 


  "Ni bance ina son girkin ki ba, keep it to your self abu d'aya nakeso da ke learn to mind your business kaman yadda kike duk abinda ranki yaga dama a gidan nan ba wanda ke miki magana nima haka nake da 'yanci ko fiye da hakan ma because this is my house and I do only what pleases me."


    "Wallahi Allah ze sak'a min."


   "Tare ze mana sakyyan kuma kidena had'ani da Allah" yana kaiwa nan ya wuceta ya fice. Kuka kawai tasa a wajen da k'yar tayi shiru taja mayafinta se gida. Mummy na ganinta ta gaskata zancen akwai matsala a k'asa don haka ta jata d'aki ta shiga jero mata tambayoyi hajiyarku kam ba se kuka ba mutum na iya cewa wani gaggarumin laifi ne Afzal ya mata har Mummy ta soma tunanin ma ko dukanta Afzal d'in yayi. Da k'yar de ta samu Nazeefar tayi shiru sannan ta fad'a mata halin da ake ciki na cewa Afzal na shirin yi mata kishiya ne. Da Mummy ta tambayeta hujja kuwa bata da ko d'aya banda iphone 6 data ga cikin leda se kuma ce mata da yayi wai shi miji ga mata hud'u ne. 


  "Ke shikenan don kinga ya sai sabon waya seki ce wa budurwa ze kaiwa?"


  "Wallahi Mummy wa budurwa ne" ta fad'a tan share hawayenta sau dayawa ina jinsa yana waya da ita kuma ranan ma k'awata tace ta gansa da wata a school."


  "Toh ai koma meye Afzal d'in yayi banga laifinsa ba se naki inda kin bashi girmanshi kin rik'e shi da mutunci da amana kina kula dashi a matsayinsa na mijinki wallahi nasan Afzal baze fara gaggawan k'aro aure ba ko baki fad'a ba Nazeefah nasan baki kula da Afzal a gidan can da k'yar ma idan kina basa girmansa as mijinki wanda kike k'rk'ashinsa, kin musanta?" Shiru Nazeefah tayi tabbas ba k'arya cikin kalamun Mummy ko d'aya. "Dake fa nake? Nayi k'arya?" Shiru tayi chan ta kad'a kai. 


 "Tell me meyasa bazeyi tunanin sake yin aure ba tunda baki kula dashi baki basa muhimmanci?"


  "Toh Mummy shi yana nunawa ya damu dani ne? Tafiya nayi gabad'aya don ban sanar dashi ba ko kira na yayi min na isa lafiya beyi ba."


 "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un Nazeefah!" Mummy ta dafe k'irji "Yanzu har kiyi tafiya bazaki sanar da yaron nan ba? Yau kin fallasheni ni Fatsuma shin tarbiyyan dana baki kenan? Yanzu har kiyi tafiya bazaki sanar da mijinki ba? A tunaninki zaman kanki kike ne a gidan, Iyyeh? Kodan kinga bayi magana ne?" Shirun da Nazeefah tayi ya bata daman cigaba da magana "Da ke fa nike!"


   "Toh ai na tuba bazan sake ba ni kawai ki kirashi kice mishi ya dena neman wannan yarinyar da yake."


  "Saboda gani uwar banza ko? Lallai ya tabbata bakida hankali to ki bud'e wannan kunnuwan k'ashin naki wallahi  ki saurareni, in ke bakida hankali ni ina da shi kuma muddin baki zubda wannan banzayen halayen nan naki ba haka kinaji kina gani Afzal ze k'aro aure matar ta k'wace miki shi kina ji kina gani kuma ba abinda zaki iya k'arshe yaga dama ma ya sakoki."


  "Dan Allah Mummy ki kirashi ki bashi hak'uri wallahi zan dena rashin hankalin da nakeyi zan shiryu."


  "Kar ma kiyi mana karma is coming for you."


  "Mummy dan Allah kiyi hak'uri."


   "Sani fa ya rage wa me shiga rijiya ko ki canza ko ki sha mamaki."

  

  "Toh Mummy ya zanyi in karkato da hankalinsa a gareni? Wallahi bazan iya rayuwa da kishiya ba."


  "Kidena rashin ji, bari na bari- yi na yi, kina tsaftace kanki da muhallinki, girki kar ya ta6a wuceki, shin ina kika kai hud'uban dana miki kap kafin in kaiki gidanshi Nazeefah? A ina kika zubar dasu?"


  "I'm sorry" ta furta tana turo baki. 


  "Amman har me kike masa yasa sa wannan gaggawa? Dududu auren naku wata nawa ne?"


  "Ni ba abinda nake masa."


  "Oh bazaki bud'e baki kimin magana ba sena kira Daddy'nkunna k'irga mai komi tukun?"


  "Mummy dan Allah na tuba, wallahi komi ma na mishi Mummy ko girki ban ta6a mishi ba amman daga yau zan fara ni banason ya sake yin aure."


  "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un ai kuwa aure ki k'addara a ranki an riga an d'aura believe me idan da nine Afzal d'in wallahi tun auren naku na sati biyu zan kawo amaryata, wannan rashin hankalin da me yayi kama? Kina nufin for morethan five months yaron nan kullum siyan abinci yakeyi a waje? Where is my phone wallahi sena k'irga wa Daddy'nku." 


   "Dan Allah Mummy kiyi hak'uri" ta fad'a da sauri tare da janye wayan kafin Mummy ta d'aga.


  "Bani wayata sakariya kawai bani!" 


   "Mummy kiyi min rai wallahi Daddy yaji kasheni zeyi I'm sorry please don't call him." Fad'a sosai Mummy tayi mata Nazeefah se kuka, bayan nan tayi mata nasiha sannan ta tura ta gida. 


  Ta d'ayan 6angaren kuwa, Afzal tun fitansa ya zarce gidansu Amal acikin mota ta k'ariso ta samesa suka gaisa bayan d'an hiran da suka ta6a kad'an ya mik'a mata ledar. 


  "Toh kuma mey aciki Yaya?"


  "Amsa ki duba" ba gardama ta bud'e thunderstrucked taga sabuwar waya pil aciki wayan da ko a mafarki bata ta6a kawowa kusa da tunanin ta zata rik'e irinshi a kwanakin kusa ba. Dan mamaki da murna ta ma kasa magana se chan baya ta shiga tambayansa dagaske wayan nata ne kode wasa yake mata. Godiya sosai tayi masa, sam ta kasa 6oye farin cikinta a rayuwa batasan ya zatayi ba idan ba Afzal yanzu shikenan zata nayin assignments nata cikin sauk'i ba seta je cafe ba 'yan iskan samari nan suna bin mutum da kallo da kalamun soyayya. Sabon sim daya sai mata yasa mata a ciki ya nuna mata yadda zatayi charging wayar idan ta shiga ciki sannan ya mik'a mata ya kuma ce mata duk abinda bata gane ba she shoud feel free to call and ask him. Godiya mara adadi Amal ta tayi masa har zuwa lokacinda ya tafi. A hankali ya bud'e mata account a WhatsApp, Instagram da Snapchat dukda cewa ita bata wani damu da su bama, dama-dama WhatsApp d'inne take d'anyi dake anyi adding nata a group na 'yan class nasu ta na kuma samun informative messages ta wajen. 


   A hankali a hankali kan Amal ke wayewa har ta soma amfani dasu snapchat tazo ta bud'e Twitter account da kanta, yarinya tana wayewa tana k'ara kyau da k'warjini. Tuni samari suka fara yi mata chaa sede dake tasan daraja da k'imarta kota kansu batayi duk wanda ya tsareta ce masa take akwai tambayan wani a kanta. A haka har suka shak'u da wata coursemate nata Maamah, yarinyar nada hankali sosai kuma ba k'aramin son Amal take ba. Suna da kud'i amman hakan besa ta rasa tarbiyya ba yawancin kullum suna tare da Amal. Bayan lectures ya k'are yau Amal ta shiga sauri don kar ta rasa keke napep kasancewar mai napep nata bai ji dad'i ba ta sanar da Afzal yazo ya d'auketa kuma tana ganin duk sasa aiki ne gara kawai ta tafi da kanta. 


   "Ya naga kaman kina hanzari yau lafiya?" Maamah data karanchi saurin da Amal keyi ta tambaya. 


  "Wallahi me napep d'ina ba lafiya gashi kinga yamma yayi banason in rasa abu hawa."


  "Toh ki bari mana idan Yaya na yazo d'aukana se muyi dropping naki ba a Jiddari kike ba? Kinga mu muna Polo layin duk d'aya ne."


   "How kind of you, but na gode karki damu I can manage."


  "No please Amal I insist dan Allah kibari mu sauk'eki yau."


  "Maamah da kin bari kawai I don't want to he a burden."


  "C'mon karki damu kode tsoron Yayan nawa kike tun kafin ki gansa?"


  "Kusan hakan" ta amsata tana jin kunya. 

  

  "Karki damu Yaya baida matsala muje mu zauna akan slabs d'incan yanzu ze zo" ba gardama suka k'arisa suka zauna bada dad'ewa ba sega 406 na yayan Maamah ya iso, k'arisawa tayi ta mishi bayanin situation d'in gladly yace ta kira Amal d'in suyi dropping nata. Gidan baya Amal ta shiga ta zauna had'e da gaishesa kanta a sauk'e, shiko tun da ta taso yake kallonta haka kawai ta mishi kyau dukda cewar bawai wani makeup take sanye dashi ba. Throughout the drive yake satan kallon Amal ta mirror har Maamah ta gane, ba yadda Amal batayi dashi ba ya sauk'eta a bakin junction zata k'arisa ciki da kanta amman yak'i sam wai se ya kaita har k'ofar gidansu hakan kuwa akayi, godiya tayi musu sosai da suka sauk'eta. Bata kaiga shiga gida ba se ga call na Afzal, bayan ta d'aga yake tambayarta ko tana school ne har yanzu shi sam baida labarin rashin lafiyan driver'n nata se yanzu da ya kira mutumin don jin koya sauk'e Amal. 


   "A'a yanzun na iso gida ko shiga ciki ma banyi ba."


  "Mesa baki kirani nazo na d'auke kiba?"


  "Yaya I'm sorry amman naga kaman duk saka wahala ne tunda zan iya tahowa da kaina."


  "Ba fata ba amman idan aka sace min kefah?"


  Dariya kad'an ta saki "Haba Yaya sekace yarinya, bale ma brother'n friend d'ina ne ya kawo ni sun rage min hanya." Alokaci guda kawai yaji ransa ya 6aci yayinda wani irin zazzafan kishi ya mamaye masa zuciya. "Motan wani kika shiga?" Ya tambaya cike da 6acin rai da tsiwan daya mugun firgitar da Amal, sosai ta razana game da tsawan da ya daka mata. 


  "Yaya wan k'awata nefah" ta furta a hankali cike da tsoro. 


  "Meaning? Don wan k'awarki ne se akace ki shiga motanshi? Inda kuma bakinsu a had'e da k'awar naki suka yi miki wani abu fah? Ke bakisan ba a yarda da mutum so easily bane yanzu?" Ya k'ura ta. 


  "Yaya I'm sorr-" katse wayan ma yayi gabad'aya a kanta. Da mamaki ta sauk'e wayan daga kunnenta tana mamakin yadda ransa ya 6aci lokaci guda haka, tana iya rantsewa bata ta6- jin 6acin ransa ba se yau. Yau ta shiga uku ta 6ata wa Yayanta rai ita da tasan ransa ze 6aci haka dama bata sanar dashi gaskiyan lamarin ba kokuwa da bata amince ta shiga motan wan k'awar nata ba. Yanzu ta ina zata fara bashi hak'uri????




RANA D'AYA 

#RD


Love... King Miemiebee👄✨

[13/08, 00:34] ‪+234 907 483 8352‬: 🎀🎀🎀                 🎀🎀🎀

                🎀❣🎀

                   ❣❣


  💦💦                      🍃🍃🍃          

           *RANA D'AYA!*

  💦💦                      🍃🍃🍃

  June, 2018

 beeenovels.blogspot.com


     _Written by Miemiebee👄_



   *PAGE 1⃣3⃣*



  

   Da mamaki ta k'arasa ciki ta watsa ruwa taci abinci, dab bayan sallan Maghrib ta gwada kiran Afzal sede kamar yadda ta k'udurta a ranta haka mutuminku yak'i d'aukan wayan, sau biyu take kiransa ta regular line nasa amman yak'i d'agawa, private line nasa ta kira next. nan ma yak'i d'agawa dagangan dan kuwa wayan na a gefensa yana mik'e kan gado sede ya kalla ya cigaba da zura wa ceiling ido. Sak'o ta tura masa ta text message tana basa hak'uri nan ma yak'i reply bayan ya karanta. Duk da haka bata kariya ba, ta bisa whatsapp ta tura masa messages bil adad tana basa hak'uri tana kuka duk seya karanta ya kuma k'i reply abinda yafi ci mata rai kenan. Taya har ze karanta amman baze bata reply ba? Yau ina zata sa kanta? Assignments nata data d'ibo zatayi ma taji baza ta iya ba tsan-tsan tashin hankali. 


  Dab tazo kwanciya wajajen k'arfe goma na dare ta sake kiran lamban nasa sai da still Afzal yak'i d'agawa, ganin ba mahalicci se Allah kawai ta tofe addu'o'inta ta kwanta abinta duk da cewan ba baccin take ji ba, gabad'aya hankalinta yana kan halin da Afzal ke ciki. Ita da tasan hakan ze biyo baya wallahi da bata shiga motan Ya Abdul d'in bama tun farko. 


  Washegari lectures nata na safe na k'arewa tama driver'nta waya ya dawo da ita gida. Aldeb da zo6o me dad'in gaske ta d'au lokacinta ta had'a ta zuba masa a silver flasks nasa sannan ta tanadar wa Papi da Mami nasu a gefe. Wanka ta sakeyi ta canza kaya tasa matching color hijab ta feffeshe da turare sannan driver ya sauk'eta a office nasu Afzal. Tun da ta ga motansa a fake hankalinta ya d'an kwanta. Tana isa bakin office nasan a sama tayi knocking inda ya amsa da "Come in" a hankali ta bud'e ta shiga. Sosai mutuminku yayi murna da kuma mamakin ganinta amman ya dake a gun yana wani mozewa, kansa ya kawar tamkar ba mutum neba ya shigo office d'in had'e da cigaba da aikin dake gabansa. Ajiyar zuciya ta sauk'e ta k'arisa ciki ta zauna kan kujerar da ta saba zama a kai kullum tare da yin shiru. 


   Ganin be da niyyan yi mata magana na kusan tsawon minti biyu kawai se ta gaishesa "Yaya good afternoon" Yadda kuka san da kurma take magana haka yayi mata, ko kai be d'aga ba balle ya kalleta se rubuce-rubucen sa kawai yake. 


    "Yaya gaisuwan nawa ma bazaka amsa ba?" Ta tambayesa cikin kamala a hankali tamkar wacce take shirin yin kuka. "Yaya so kake ne ciwon zuciya ya kamani in mutu? Dan Allah kayi hak'uri" har anan be ce mata komi ba. 

  "Yaya I'm sorry, I'm so sorry" ta fad'a had'e da rik'e kunnuwanta yayinda idanunta suka soma cikowa da hawaye. 


    "Yaya yanzu se nayi kukan zaka mun magana?" Yanzu kam har hawayen sun soma d'iga sede har anan Afzal yak'i koda d'aga kai ne ya kalleta.


   "Toh shikenan" tayi maganan tana share hawayenta "Bari in koma inda na fito tunda ko d'aga kai bazaka iyayi ba ka kalleni" ta ja hanci "Ga Aldeb da zo6o nan na kawo maka, I'm still saying sorry" tana kaiwa nan ta mik'e, bata kai ga taka k'afarta ba Afzal ya mik'a hannu ya rik'e hijabinta,  chak ta tsaya gun ba tare da tace komi ba se faman kukanta take a hankali. 


  "Don't go" yace da ita a hankali dad'i sosai taji amman ta fake itama "Ni ka sake mun hijabi."


  "Nace ki tsaya" ya nanata cikin tattausar murya. Juyowa tayi tana kallonsa yayinda hawaye ke d'igowa sama-sama daga idanunta. "Bayan tun jiya ina baka hak'uri kak'i kulani bale ka hak'ura ni ka sakeni inyi tafiya ta dama tun ba yau ba na gano ba ka sona."


   "I'm sorry toh zauna kin ji?" Ya ce da ita a hankali. 


  "Nifa tafiya ta zanyi ka sakeni kurum."


  "Lily nace ki zauna."


  "Toh haka akeyi ne?" Ta tambayesa had'e da turo d'an bakinta. "Ko baccin kirki na kasa yi jiya, I called and texted you severally sarai kana gani kak'i responding d'ina, Wallahi if only ka san yadda hankali na ya..." ba se kawai ta rushe mishi da kuka ba. Yana tayi shiru tayi shiru kar ta tara masa jama'a amman inaa tak'i jinsa, se kukarta take harda me sauti. A haka ne har PA'n Afzal ta lek'o take tambayan ko lafiya. "Lafiya Blessing don't mind her kukan banza take" yace da PA'n sannan ya samu ta ja musu k'ofan ta fice. 


   "Yanzu Lily ni ke miki magana amman bakiya ji? In ce miki kiyi shiru kik'i yi? Se kin tara mun duka mutanen office d'in tukuna zaki ji dad'i?" Itama yadda kuka san bada ita yake ba, se aikin kukanta take harma tana k'ara sautin, gaban hijabinta ko lis ta jik'asa da hawaye. "Toh kiyi hak'uri, yi hak'uri kibar kukan haka" ya soma pampering nata yana bata hak'uri.


  "O'o ba tun jiya nake baka hak'uri ba kak'i ji na."


  "Toh ba ya wuce ba?"


  "Ni seka cemin ka hak'ura tukuna" ta fad'a tana zum6uro baki yayinda ta 6oye kusan rabin fuskarta k'ark'ashin hijabinta. 


  "I'll think about it keep quiet first."


 "O'o ni seka ce ka hak'ura" ta sake sa wani kukan sanin sarai ya tsani hayaniya. 


  "My Goodness!" Ya furta cike da tashin hankali yana susa temple nasa. "Da gan-gan kike ko?"


  "Ni se kace ka hak'ura" ta kuma sa wani kukan. 


  "Fine! Naji na hak'ura shikenan kiyi shiru."


  "Ka hak'ura dagaske? Bazaka sake ignoring calls d'ina ba?" Se anan ta ciro fuskan nata gabad'ai tana kallonsa. Ba k'aramin dariya ba reaction na fuskarta yasanya sa da k'yar ya had'iye dariyan ya gyad'a mata kai "Bazan sake ba" ya sanar da ita. 

  Se anan taji sanyi a ranta ta shiga share hawayenta, hannu ya cusa a  aljihunsa ya ciro hanky ya mik'a mata. Ba gardama ta amsa ta share hawayen nata dashi bayan da ta gama ta mayar mishi ya amsa ya mayar cikin aljihunsa. 


  "Wato taurin kan nan namu na nan har yanzu ko?"


  "Wani taurin kai kuma Yaya?" Ta tambayesa tamkar bata fahimci abinda yake nufi ba. 


  "Baki na nawa ina ce miki kiyi shiru amman ki k'i yi?"


  "Toh ba kaine ba, inata baka hak'uri amman kaki hak'ura."


  "Toh ai kece kika janyo."


  "Kawai don na shiga motan wan k'awata? Believe me da nasan hakan ze 6ata maka rai wallahi bazan soma ba."


   "Na ji and I'm sorry for making you worried and restless jiya but on a serious note bana son in sake jin kin shiga motan wani Lily, komin ya situation d'in yake kuwa, duk randa driver'n ki bashida lafiya call me up and let me know if I'm too busy to come pick you up zan tura driver'n office kona gida yaje ya d'auko ki banason in sake jin kin shiga motan wani, kinji?"


  "Na'am Yaya, in shaa Allah anyi na farko anyi na k'arshe."


  "Masha Allah that's my Lily."


 "Amma Yaya, Maamah is my very good friend bana tsammanin har zata iya cutar dani. I trust her."


  "Ni bance miki Maaman ne ban yarda da ita ba wan nata ne ban yarda dashi ba."


  "Toh amma-"


  "Lily enough, nide na fad'a miki in ba wai fad'a kikeso muyi ba toh karki sake shiga motanshi ko na wani banda nawa kinji?"


  "Naji Yaya" ta amsa tana mamakin iko irin na Afzal lallai wannan da ace yana da k'anne da sun taso da discipline don ba k'arya yayi kalan yayun dake jibgan k'annensu idan suka tafka rashin hankali. 


  "Ya lectures toh?" Yayi maganan yana janyo cup a saman fridge nasa don tsiyaye Aldeb d'in. "Kawo in tsiyaya maka" tayi maganan tana k'ok'arin amsan cup d'in "Lectures Alhamdulillah amma ba dad'i mutun kullum 7 ya fita sekace d'an secondary school."


  "Lol toh me maraban ki da 'yan secondary school d'in?"


 "Yaya wallahi akwai difference."


  "Toh big girl naji" yayi maganan yana amsan cup d'in "Thank you" yace da ita. 


  "You're welcome" chan tace, "Ba kace yayi dad'i ba" tare da had'e gira. 


  "Ina santi ze bar ni in fad'a? Rabonki da ki kawo mun Aldeb har na manta."


  "Forgive me Yaya daga yanzu kam zanyi k'ok'ari koda once in a week ne ina kawo maka."


  "Keda kike school yanzu? Don't bother."


  "When it comes to my Yaya komin yaya ne se an mishi abinda yakeso so kar ka damu."


  "Hakane?" Ya tambaya yana me jin dad'in amsan data basa. 


  "Sosai ma kuwa." 


  "Toh shikenan thank you."


  "You're welcome, I guess I can go now, kaima ka samu ka kammala aikin dake gabanka, zani gida inje inci abinci yunwa nakeji."


   "Let's eat out it's almost lunch time" yayi maganan yana duban agogonsa. Ba musu ta jirasa ya d'an k'imtsa kan table nasan sannan suka wuce restor suka ci abinci, bayan sun gama ci ya sauk'eta a gida sannan ya komo office. 


**** 

  A kwana a tashi be ragar da komi ba se gashi yau su Amal suna rubuta first semester exams nasu. A gida kuwa ta fannin Nazeefah da Afzal suna nan kaman kayan wanki ba cigaban komi, don koda tace wa Mummy kan zata fara yiwa Afzal girki koda wasa bata ta6ayi ba, ko tace zatayi se wata ra'ayin ta hanata ta hura mata kai kan cewa ai yanzu da zaran ta fara yi masa girki ze ga kaman sonsa take tana son su shirya kar tayi, itako seta biye wa ra'ayin. Amma se de bataji Afzal na waya da Amal ba, se zuciyarta tayi mata k'ona, zama take ta gabzi kukanta ta godewa Allah a hakan kuma ta tsaya tana cewa ita ba son Afzal take ba. 


   ****

  Amal da Maamah ne ke zaune akan slabs suna karatun paper'nsu na gobe Maamah ta fara janta da hira. 


   "Friendy?" Ta kirata. 


  "Na'am" Amal ta amsa cike da fara'a. 


  "Har yanzu fa baki bani amsa ba wallahi Ya Abdul ya tak'ura min."


  "Nikam kibar zancen can Maamah muyi karatu" Janye handout d'in Maamah tayi. "Ha'a! Ya da haka?" Amal ta tambaya tana k'ura mata ido. 


  "Wallahi yau kam sekin bani amsa haba mana friendy yanzu kodan k'awancan dake tsakaninmu ma baza ki bawa Ya Abdul dama ba? Wallahi he's a very cool and gentleman if you get to know him, baida matsala sam."


  "Na sani Maamah bazaki gane bane."


  "Mey ne bazan gane d'inba? Kede kawai kice kin k'i min Ya Abdul kuma shikenan na gode ni kika k'i ba shi ba wallahi."


  "Wallahi ba haka bane don Allah karkiyi magana haka."


  "Ya kikeson inyi toh? Yaya na fa kikayi rejecting tun yaushe nake k'ok'arin shawo kanki amman ko lambarki kin hana in basa wallahi ko baccin arziki Ya Abdul bai samu kwana biyun nan as kullum tunanin ki yake tun kan ranan daya rage miki hanya har izuwa shekaran jiya da ya kaimu Unimaid garden."


  "Ji k'arya wai ko bacci baya iyayi a d'akinsa kike kwana ne da zaki san hakan?"


  "Eh yimin wayo ki canza topic d'in" Maamah ta fad'a tana juya mata ido. 


  "Lol yi hak'uri toh."


  "Nide ba hak'urin da zanyi sekin amince in bawa Ya Abdul numbanki."


  "Ke dad'i na dake naci wallahi kibari mana mu gama karatun tukuna gobe ne fa exams d'in."


  "Friendy seconds nawa ne ze d'auke ki kice 'ki bashi' kawai? Wallahi rashin mutunci ba kyau."


  "Nikam kode biyanki Ya Abdul yayi ne? Dagewan naki fa yayi yawa."


  "Wallahi sam ba haka bane, you're just the perfect girl for him wallahi tun da nasan Ya Abdul 'yan mata biyu ya ta6a yi ta farkon har sun fara zancen aure Allah yayi mata rasuwa se kuma ta biyun sunyi nisa itama yazo ya gane tana son abokinsa se suka rabu daga baya tayi-tayi ta dawo mishi amman ina he's already heartbroken."


  "Allah sarki Allah ya jik'an ran musulmi."


  "Ameen" ta amsa, "Kuma kinga kusan wata shida kenan da faruwan hakan ban sake jin yana neman wata ba se daya kafa idanunsa akanki Wallahi he's intentions to you are clear."


  "Na ji kuma na gamsu Maamah kawai ina ganin this's not the right time for me to be in a relationship ne kiga part one fa kawai nake I have almost 5 years to go Ya Abdul baze iya jira na ba."


  "Wallahi ze iya, he is willing to wait till forever for you."


  "Hmm" ta numfasa. 


  "Kode kam Yayan nawa be miki bane? Yayi muni dayawa ko?"


  "Haba ai kema kinsan yana da kyau wallahi gashi chocolate skinned, ga saje ga ido kaman naki a nan."


  "Yana da kyau kenan?"


  "Eh mana" ta amsa without knowing when "I mean ni ba ruwana ki rufa min asiri kiban handout d'ina" ta shiga canza zancen. 


  "Amal pleasee ki amince pleasee wallahi ko na basa lamban naki baze kiraki ba se mun gama exams shi da bakinsa ya cemun haka."


  "Toh naji ba se kin cinye ni ba ki bashi shikenan?"


 "Yeyyyyy!!" tasa ihu had'e da hugging d'in Amal wane wacce ke neman suffocating nata. 


  "Toh nikam sakeni haka mu k'arisa karatun nan kinga har Azahar ya doso." Handout natan ta mayar mata suka cigaba da karatu suna iddawa sukaje sukayi sallah sannan kowacce tayi hanyan gida. Kamar yadda Ya Abdul ya d'au alk'awari, seda su Amal suka kammala exams bayan kwana biyu ya buga mata waya, lokacin tana zaune tsakar gida tana bita wayan ya shigo. Ganin new number yasa bata d'aga da wuri ba seda ya kusan tsinkewa. Shiru tayi da ta d'agan chan daga d'ayan 6angaren taji bak'on murya nayi mata sallama. Cikin sark'ak'k'iyar muryarta me sanyi ta amsa da "Wa'alaikumus salam wa rahmatullah."


   "Amal ya kike?" Sama-sama suka gaisa dake har yanzu bata fahimci wake magana ba. "Baki gane muryan bako har yanzu?"


  "Eh wallahi I'm sorry."


  "Abdul Rahman ne" ya sanar da ita. 


  "Abdul Rahman daga ina kenan?"


   Murmusawa yayi kad'an sannan yace, "Ya Abdul toh" se yanzu ta fahimta ashe de Abdul Rahman ne complete name nasa, wow. "Laa! Ya Abdul ina yini?"


  "Bayan wuyan da kika bani har kin manta dani ko?"


  "Haba Ya Abdul ina na isa."


  "Gashi kuwa."


  "A'a wallahi kullum da Ya Abdul Maamah ke addressing naka bata ta6a ambaton full name naka ba kaga ko bazeyi in gane wanene ba at first thought" ta mar bayani a hankali. 


  "You're right so ya hutu?"


  "Hutu Alhamdulillah ya aiki?"


  "Lafiya k'alau kun gama exams ko?"


  "Eh wallahi."


  "Toh Allah ya bada sa'a."


  "Ameen thank you."


  "I thought I should call and check up on you."


  "Ayyah to nagode sosai a gaishe da gida."


  "Zasuji take care" a haka sukayi sallama. "Phew!" Ta numfasa had'e da ajiye wayan a gefe sannan ta cigaba da karatunta. Tun daga ranan Ya Abdul ke kiran Amal suna gaisawa, kar kuma kuyi tsammanin irin kira barkatai ba fasali d'innan ne, no a sati befi suyi waya sau biyu ba idan yayi yawa shine sau uku ko hud'u. A hankali shak'uwa ya fara shiga tsakaninsu ba abinda ke burge Amal a gun Ya Abdul kaman yadda yake yawan sanyata dariya, sede basuyi waya ba koda ranta a 6ace ne seya faranta mata da kalamun sanya dariyansa, he's so jovial Maamah batayi k'arya ba da tace bashida matsala. A satin da zasu koma makaranta ne yayi insisting se ya zo sun had'u mutumiyarku da shegen tsoro kam ba se ta shiga yi masa corner-corner ba.  Yau tace zata islamiyya, gobe tace zata raka Mami gidan suna ko makamancin haka daga k'arshe de ya gane tsoro take ta ke6e dashi shi kad'ai kuma bega laifinta ba hasali ma yaba mata yayi sosai hakan na nufin tasan abinda takeyi ne. Don haka ya tambayeta idan ze taho da Maamah zata amince ta fito? Tuni ta amince. Hakan ko suka shirya ranar Laraba da yamma se gashi da Maamah sun k'ariso gidansu, har ciki Maamah ta shiga suka gaisa dasu Mami sannan suka fito da Amal inda Amal ta zauna a gidan gaba ita kuma ta koma baya. Bayan gaisuwa suka sha hira sosai dukansu ukun cikin motan, se dariya Ya Abdul yake sanya su barin ma Amal dake dariya harda k'walla, kusan k'arfe shida Ya Abdul yace ya kamata su tafi, don dad'in hira Amal ji take kaman kada su tafi. Dab tazo sauk'a daga motan kenan ya mik'a mata wata leda, ta kar6a ita kuwa tak'i ba yadda beyi ba amman tak'i, daga k'arshe seda ya baiwa Maamah ta shigar mata dashi ciki har cikin d'akinta. 


**** Bayan ta dawo ciki ta wuce d'akinta ta fito da ledar, zazzagewan da zatayi ta tarar da chocolates turum, ba wanda babu aciki da wanda Afzal ya koya mata ci da wanda se yau ma ta ta6a ganinsu, abu de yayi kyau. Haka nan ta 6oye abinta cikin akwati tana ci a hankali a hankali. Bayan sallan Isha ta kira Ya Abdul tayi masa godiya inda suka sake ta6a hira kad'an sannan sukayi sallama. Ganin goma be cika ba ta yi tunanin kiran Afzal da alama aiki yayi zafi ne ko nemanta bayya yi kwana biyu, daman yayi tafiya zuwa Lagos for a meeting, yau k'imanin kwana biyu zuwa uku kenan. Tana kiransa on the first ring ya d'aga, "Yaya kayi wuyan gani" ta soma cewa. 


  "Wallahi Lily, I've been so busy ko time na wayan ma bani dashi."


  "Allah sarki ya kake ya aikin?"


  "Alhamdulillah ya gida dasu Mami?"


  "Lafiyansu k'alau d'azu take cewa kwana biyu bata ji motsinka ba nace ai kayi tafiya, she's sending her warm greetings so as Papi."


  "Toh ayya ina amsawa."


  "Yaya I miss you yaushe zaka dawo?"


  "Saturday in shaa Allah."


  "Toh Allah kaimu barin barka haka nasan a gaje kake."


  "Alright Lily thank you have a peaceful night rest."


  "You too, seda safe" da haka sukayi sallama. 


**** 

  Nazeefah ce zaune gaban Tv ta sa channel na Zee world tana kallon wata indian series se faman buga tsaki take, ga takaicin rainin wayon da ake tayi a series d'in ga na rashin Afzal kwana biyun da tayi bata sanyasa a ido ba bata kuma ji muryansa ba, ba k'aramin tashin hankali ta shiga ba, se a yanzun take sake jaddada cewa lallai-lallai ta fad'a kogin sonsa. Seta d'au wayarta zata kirasa seta kashe ta fasa, tayi hakan sau fiye da a k'irga. Daga k'arshe de ta dage ta kira har ya shiga yana ringing, se cewa kanta take ai don ya sanar dani zeyi tafiya ne yasa zan kirasa, da ace tafiyansa kawai ya kama yayi wallahi ko ta kansa bazan yi ba bale har in kirasa. 


  Ya kusan tsinkewa ya d'aga kasancewar har ya fara bacci. Shiru tayi bayan da ya d'agan kaman yadda shima yayi shiru yana jiran ta soma magana dukda cewan yayi mamakin ganin kirarta amman dake yasan halin matar nasa, tunaninsa gabad'aya yayi kan ko so take ta sanar dashi kud'inta ya k'are ne ya hankad'o mata wasu. 


  Ganin ba mahalicci se Allah mutumiyarku tayi gyaran murya had'e da cewa "Halo?"


  "Yes?" Ya amsa cikin sleepy husky like voice nasa. Rasa na cewa ma tayi, tace ya isa lafiya ne? Toh ai tun shekaran jiya yayi tafiyar chan de ta gaishe sa kawai "Ina yini?"


   "Lafiya" ya amsa casually, "Ya kike?"


  "Lafiya k'alau ya aiki?"


  "Alhamdulillah."


  "Dama nace in ji ko kana lafiya."


  "Toh thank you I'm good ba wata matsala dai ko?"


  "Babu."


  "Toh yayi kyau."


  "Nace gobe zan fita gidan k'awata, ina neman uzuri."


  "Kikace?" Afzal da mamaki ya rufesa ya tambaya tun yana a mik'e akan gadon nasa har ya tashi ya zauna besani ba, kode gizo kunnensa ke masa ne? Har Nazeefah ce zata kira waya ta gaishesa musamman don ta tambayesa izini? Lallai yau za ayi ruwan mutane. 


  "Nace zani gidan k'awata gobe, am I permitted?"


  "Sure you're, kikaje ki gaisheta."


  "Toh seda safe."


  "Yauwa Allah tashe mu" da haka sukayi sallama. "Phewww!" Ta sauk'e ajiyar zuciya yayinda shima yayi haka ta d'ayan 6angaren. Afzal yana mey mamakin anya kuwa wannan Nazeefah ce yayin da ita kanta take tambayar kanta anya kuwa itace??


   Ranan da Afzal ze dawo ne Nazeefah ta fad'a cikin kan zata mai girki sede da zaran ta motsa d'auko tukunya se wata ra'ayin ta hanata kan cewa har na me zata masa girki? Ai seya d'au sonsa take, yayinda wata ra'ayin ke ce mata mey aciki don tayiwa mijijta girki, besides ma ai ya sanar da ita ranan da ze dawo. Haka dey tayi nan tayi chan daga k'arshe girkin da ba azo anyi ba kenan. Haka nan ya dawo gidan dry ta nad'e k'afa a kan kujera tana kallo. Sannu da zuwa kad'ai ta masa ya amsa ya wuce d'akinsa. Yana watsa ruwa ya canza kaya ya fito se buga k'amshi yake, ko bata tambaya ba tasan gidansu Amal ze wuce. Wani irin zazzafan kishi ne ya tokareta ji take kaman ta rik'o k'afarsa ta hanasa fitan. 


  Da ta zauna tayi nazari kuma se taga ai duk laifinta ne da ace ta dafa masa abinci da sede tace yaje dining yaci hakan baze ma samu daman fita ba. Holy sh*t. 


  Kaman Nazeefah ta sani gidansu Amal  direct Afzal ya wuce inda aka shirya masa abinci kala-kala ga smoothies d'innan ba wanda Amal bata had'a ba su Ginger ne, zo6o da kuma Aldeb nasa. Sosai ya ji dad'i, dalilin da ya hanasa cin abinci kenan through out yau saboda yasan Amal bazata taresa da dry hannu ba. Zama yayi ya gabza abincin sosai har ya buk'aci a sa masa ragowar a kula ya tafi dashi gida. Amal se dariya take tana neman tsokanansa tana kiransa glutton. Da yazo tafiya ne ya ciro masu tsarabar laces daya musu ita da Mami. 


****

   Haka nan tafiya ta cigaba har hutun su Amal ya k'are suka shiga second semester. Ita da Ya Abdul fa se abinda yayi gaba shi de har yanzu be furta mata kalamun so ba, but with the way he's being so extra ita kanta Amal tasan relationship nasu ya tashi daga friendship ya koma wani abun daban. A rana se suyi waya sau biyu zuwa uku, har Mami ta fara sa mata ido tana zata k'wace wayan idan batayi hankali ba. Ana nan ana nan kwatsam rana d'aya Ya Abdul ya fad'awa Amal abinda ya juma yake son sanar da ita kan yana sonta, so kuma na aure. A wannan lokaci itama Amal ba k'arya ta fad'a kogin sonsa, saboda ko be kirata a waya ba, ita zata d'au wayarta ta kirasa. Tunda ya furta mata wannan kalamu ta daina d'aga wayansa ko message ya mata bata responding, ba k'aramin tashin hankali ta sanya sa ciki ba gabad'aya ya rasa meke masa dad'i. Gun k'anwarsa Maamah ya nufa yayi mata bayanin abinda ke faruwa kan dan Allah ta taimaka masa. Kwantar mai da hankali tayi ta kuma tabbatar masa da cewa in shaa Allah Amal ta sa ce saboda ita ta riga ta gane Amal na sonsa. Washegari ko school Amal tak'i fita sanin the moment ta fita zasu had'u da Maamah itako zata kira Ya Abdul ta had'asu don haka ta fake a gida da cewan cikinta na ciwo. 


  Da misalin k'arfe goma Afzal ya kirata bayan sun gaisa yake tambayarta lectures take ce mai bata ji dad'i ba yau tana gida amman da sauk'i yanzu haka. "Se yau za'a same ki kenan Lily" yace da ita afterwards. 


  "Kamar ya Yaya?" Ta tambayesa cike da rashin fahimta. 


  "Throughout last week koda na kiraki kullum line busy nakeji wa muka samu haka?"


  "Kai Yaya ba kowa fa idan ka kira kaji line busy to da da Maamah nake waya."


  "Anya kuwa Lily?"


  "Dagaske Yaya."


  "Toh shikenan Allah k'ara sauk'i."


  "Ameen thank you." Da haka sukayi sallama bata kaiga ajiye wayan ba se ga call na Ya Abdul kaman wacce bazata d'aga ba seda call d'in ya kusa tsinkewa ta d'aga had'e da yin shiru. 


   "Alhamdulillah" ta ji ya furta "Amal?" Shiru tayi "Amal kuma bazaki amsa ba?"


  "Ina kwana?" Ta gaishesa a hankali. 


  LAmal mey nayi da zan fuskanci wannan hukunci daga gareki? Don't you think hukuncin nan naki yamin tsauri dayawa?"


  "I'm sorry."


  "Amal in sona ne bazaki iya yi ba you could have simply told me, I was worried sick about you gashi yau ko school kin k'i fita duk don gudun karki had'u da ni ne?"


   "Nifa ba haka bane, cikina ne yake ciwo."


  "Why do I feel like you're lying?"


  "I'm sorry" haka kawai ta tsinci kanta tana basa hak'uri ba gaira ba dalili ko de don ita kanta tasan abinda tayi masa bata kyauta masa bane?


  "Look I take back what I said to you kinji? Na gane you can't love me back but please karki 6ata friendship dake tsakanin mu I cherish our friendship alot Amal."


  "Ya Abdul ka dena magana haka."


  "Toh ya kikeson inyi Amal? Haka kawai kika dena recieving calls d'ina kina ignoring d'ina anyhow."


  "I'm sorry."


  "It's okay abu d'aya nakeson tambayanki Amal please give me a sincere answer."


  "What is it?"


  "Who's the lucky guy da ya rigani sace zuciyarki? I'm sure this's all about him."


  "Wallahi ba kowa Ya Abdul I just need some space."


  "You mean I still have hope?"


  "In zaka iya jira" ta amsa bayan tsawon lokacin da ta d'auka. 


  "Amal I'm ready to wait for eternity for you, Amal ba zaki gane irin soyayyan da nake miki ba, it's been long since I felt this. Amal out of the blue kika sace min zuciya, I love and adore everything about you and I'm willing to wait for you for as how long it takes until you're ready. Amal I love you."


  "Ya Abdul..." se kuma tayi shiru. 


  Yes Amal I love you and am not ashamed of it ko a gaban waye zan fad'a, I love you Amal."


  "Thank you Ya Abdul."


  "Gobe ki fita school kinji?"


  "Ni banida lafiya" ta fad'a stubbornly. 


  "Haba beautiful? Duk don gudun kar inzo d'aukan Maamah mu had'u ne? Ki kwantar da hankalinki ni gobe ma zanyi tafiya."


  "Tafiya kuma Ya Abdul?" Alokaci d'aya se taji kuma tana missing nasa. 


  "Ba abinda kikeso ba kenan."


   "A'a fa ni bance ba."


  "Toh zaki fita school gobe inzo in kun tashi?"


  "Eh kazo."


  Does this means you missed me too?"


  "Ya Abdul yes, I missed you" ta amsa cuke da kunya ita kad'ai ce a d'akin amman tana kare fuskarta da pillow. 


  "Wow!" Yayi exclaiming cike da murna da farin ciki "That's my girl, I miss you even more, so se na zo ko?"


  "Toh Allah kaimu" 


 "Ameen, you take care okay? I love you."


  You take care too" da haka ta karse wayar tare da rungume ta. Haka kawai ta tsinci kanta tana murmushi ita kad'anta there's no denying itama tana son Ya Abdul halan fiye da yadda yake jin yana sonta ma kawai de as a lady her ego comes before her feelings. 


*****

   Mu kwana mu tashi be ragar da komi ba, haka tun Amal tana 6oyewa Ya Abdul soyayyarta ta shiga nunawa, haka zata la6e a d'aki kaman tana bacci amman waya take. A school kuwa yawancin in sun fita break shima Ya Abdul seya kar6i excuse a office ya fito su had'u su sha firarsu. Afzal kuwa kasancewar ya samu cigaba a office, daga Assistant manager ya koma manager sam baya samun zama kullum cikin aiki yake da tafiye-tafiye hakan ya bawa Amal da Ya Abdul daman sake shak'uwa sosai. 


  Yau bayan juma'a Amal na karanta suratu Kahf wayarta ya shiga ruri dubawan da zatayi taga Afzal ke kira, wai wata sabon gani. D'agawa tayi take had'e da cewa, "Yau Yaya ya tuna dani kenan."


  "In ban tuna dake ba ai ke bakida niyyan kira na."


  "Inji wa Yaya? Wallahi kullum kana raina banason tak'ura maka da kira ne saboda naga kaman aiki na maka yawa yanzu."


  "Toh ya kike?"


  "I'm fine just that am missing you."


  "I miss you too Lily ya school?"


  "School lafiya k'alau."


  "Ki fito ina bakin k'ofa." Dum taji zuciyarta ta buga a tunaninta gabad'aya Afzal baya gari ne, dan kuwa yanzun sukayi waya da Ya Abdul yace mata yana tahowa ya zatayi idan yazo ya iskesu da Afzal? Yau nata ya k'are me hana afzal kurara ta se Allah motan wani kawai ta shiga seda ya kusan cinyeta bale ace har ta kawo saurayi gida? 

  "Halo Lily? Fitowan ne baza kiyi ba sena k'ariso ciki da kaina?"


  "A'a Yaya gani nan fitowa" daga nan ta ajiye wayan. Zagin kanta ta shiga yi, meyasa bata ce masa bata gida ba? Sede sarai tasan halinsa yana iya cewa bari ya k'ariso su gaisa da Mami, daga nan kuma Mami ta fallasheta. Numban Ya Abdul ta kira take don sanar dashi kar yazo yanzu ya bari se anjima zata fita sede kash two missed calls ta masa amman bai kusa. Yau akeyinta! Ta furta a ranta. 


  Qur'anin ta mayar mazauninsa ta d'an shafa powder da jan baki taja hijabinta ta sanya ta d'an feffeshe da turare sannan ta fice. Tun da ta fito Afzal dake zaune cikin motansa yake binta da kallo yayinda ya tsinci kansa cikin wani irin walwala da farin ciki maras misaltuwa. Se gani yake kaman yau ya fara sanya ta a idanunsa, tana k'arisawa cikin motan k'amshin turarenta ya mamaye ciki. "Kyau kenan Lily?" Ya ce da ita yana murmushi sosai. 


  "Kai Yaya" ta amsa tana kare fuskanta da hijabin nata "Dan Allah ka dena sani jin kunyanka."


   "Ai kuwa sede ki dunga cin kunyan nawa don bazan fasa fad'a miki kinyi kyau ba Lily."


  "Toh ai kaima kayi kyau in fact kullum ma cikin baza kyau kake."


  "Hakane?"


  "Sosai ma Yaya."


  "Toh tsaya in d'aukeki hoto."


  "Yaya wai kai se mutum yayi muni zaka ce zaka mai hoto?"


  "Kika sake cewa kinyi muni zamuyi fad'a."


 "Toh na dena amman d-" flash na cameran daya haskata ne y rufa mata baki. "Haba mana Yaya!" 


  "Tsaya mana kiga kinyi kyau" tsayawan tayi ya nuna mata se kuma taga batayi muni ba "See? I told you tsaya mu k'ara miki d'aya." Daidaita zamanta tayi daram tayi posing yayin da ya haska mata flash ras ta fito ta kuma yi bala'in kyau. 


  "Toh saura kai, kaima ka tsaya a d'aukeka."


  "Ce miki akayi maza suna hoto?"


  "Yimin yanga de Yaya" ta kai ga d'aukan wayanta a inda ta ajiye kenan sega Ya Abdul na kira kafin tace zata janye inaa har idon Afzal sun karance mishi sunan wanda ke kira as

  "LOML❤🔐" meaning 'Love Of My Life' danqaree! Ba zuciyan Amal kad'ai bane ya buga harta na Afzal, infact nasa ma yafi nata tsinkewa take wajen yaji jikinsa yayi sanyi lissss. A hankali ta janye wayan, yadda ta kasa d'agawa haka ta kasa katsewa ta bari se ringing yake, yana tsinkewa Ya Abdul ya shiga kira again se a karo na biyu ne ta katse. 


  "Mey na katsewa kuma?" Afzal ya tambayeta yana me k'ok'arin 6oye kishi, k'unci da bak'in cikin da ya fad'a aciki. 


  "Ba important call bane" ta fad'a a hankali, gabad'aya kunya yabi ya mamayeta ba haka taso sanar da Afzal batun Ya Abdul ba. 


  "Love of our live yana kira kice ba important call ba Lily?" 


  "Yaya please-" tana cikin maganan ne Ya Abdul ya shiga kira again bata kaiga katsewa ba Afzal yace, "You're excused, jeki amsa ina jiranki."


  "Yaya I can call him back later."


  "Ni nace ai kije Lily kar ki damu" kallonsa tayi one last time sannan ta sauk'a daga motan ta ke6e gefe guda. Afzal da yake ji tamkar na lahira ma yafisa jin dad'i besan lokacinda ya tada motan ba ya fice a guje ji kawai Amal tayi iska ya wuceta, juyawan da zatayi taga motan Afzal ne bata san lokacinda ta bawa Ya Abdul hak'uri akan anjima zasuyi magana ba ta katse wayar. 


   Yau kashinta ya bushe!



RANA D'AYA

#RD


Love... King Miemiebee👄✨


[13/08, 00:36] ‪+234 907 483 8352‬: 🎀🎀🎀                 🎀🎀🎀

                🎀❣🎀

                   ❣❣


  💦💦                      🍃🍃🍃          

           *RANA D'AYA!*

  💦💦                      🍃🍃🍃

  June, 2018

 beeenovels.blogspot.com


     _Written by Miemiebee👄_



   *PAGE 1⃣4⃣*




   Tuk'in ganganci Afzal ke wane wanda ke shirin afka hatsari da gan-gan, ikon Allah ne kawai ya kaisa gida nan ma da yayi parking ya fito ko ta kan motan beyi ba bale ya zara key har ya rufe k'ofar, a wangale ya barota ya k'ariso ciki. Yana bankad'e k'ofan ciki se ga Nazeefah a shirye tsaf da alama ma fita take shirin yi. 


  "Yauwa Afzal zani suna ina buk'atan 5k" ta tambayesa ba tare da ta karanci halin da yake ciki ba, don 6acin rai Afzal ko kallonta beyi ba bale ma ya amsata, yazo wuceta kenan ta kira sunansa "Afzal magana fa nake."


  "Nace bani da shi!" ya sanar da ita a tsawa ce. Ranta ne ya mugun 6aci dan rainin hankali banzan 5k ne ze tsaya yana mata walak'anci akai? Ai ba wai ta rasa 5k d'in bane itama kawai de don tana neman k'ari ne, ma ba laifinsa bane ita ta tambaya. "Wallahi kama kanka izinin ma na fasa tambaya" tace dashi yana cikin tafiyar. 


  "Karki tambayan kuma dan Allah in kin fitan karki sake tako k'afarki gidan nan aikin banza kawai" yana kaiwa nan ya wuce d'akinsa bang! Taji yayi banging k'ofar kad'an ya rage bata ci tuntu6e ba don yadda ta firgita. 


   Anya kuwa lafiya? ta tambayi kanta. K'arisawa waje tayi garin fito da motarta daga parking lot taga k'ofan motan Afzal a bud'e, lek'awan da zatayi taga motar ma a kunne ya barta nan ne ta tabbatar da cewa lallai-lallai something went wrong somewhere. Key'n ta zara ta kashe motan ta dawo ciki ta ajiye mai sannan tayi ficewarta. 


  Tun shigansa ciki ya fad'a kan gado ya kwanta can anjima ya mik'e ya shiga zagaya d'akin yayi nan yayi chan ba tunanin da be yi ba akan Amal da wannan mutumin da yaga tayi saving lambansa as 'LOML❤🔐', gabad'aya ya rasa meke masa dad'i. Hannunsa da ya d'aga kawai yakai jikin bango, blow ya rink'a kai wa bangon yadda kuka san baya jin zafin a jikinsa, kafin ace me hannun nasa duk ya faffashe yana yoyon jini, ana cikin haka ne wayansa dake aljihunsa ya soma ruri, be damu ya cie bale ma ya duba wa ke kira ba se a karo na biyu. Ganin Amal ke kira kawai yaji zuciyansa ya sake 6aci yayin da ya shiga tafasa yana masa wani irin k'ona wurgi yayi da wayar seda ta rugurguje a k'asa (Allah sarki iphone 7) sauk'a har k'asa yayi yana wani irin kakkarwa. Mutum na iya rantsewa aljanu ne suke aiki a kansa. Idonsa ya rufe gam bud'ewan da zeyi sega hawaye na tsiyaya. Yau ran maza ya 6aci! Yafi minti goma durk'ushe a wajen, jini se tsiyaya yake daga hannun nasa, a takaice de yayi staining kan tiles d'in gabad'aya. Daga bisani ya mik'e ya shiga bayi ya bud'e tap tare da sa hannunsa k'ark'ashin running water d'in. Kun de san yadda sabon ciwo ke rad'ad'i idan ruwa ya ta6a toh k'una da rad'ad'in da zuciyan Afzal keyi masa kwatankwacin hakan ne. Bayan da ya wanke ciwon ne ya rage kayan jikinsa ya watsa ruwa sannan ya fito yayi dressing hannun nasa ya mik'e a kan gado. 


  Ta fannin Amal kuwa hauka ne kawai batayi ba layin nasa ta cigaba da kira ammana inaa se switched off yake ta cemata, private number'nsa da take kira shima switched off ke cewa dake layin a kashe ne. Gabad'aya ta rasa me ke mata dad'i, ashe da tun farko ta sanar da Afzal d'in batun Ya Abdul, a ganinta da abubuwa bazasu cha6e haka ba dan kuwa ita ko da wasa bata kawo a ranta wai kishinta Afzal yake ba, a nata tunanin ta d'au kawai he's being over protective of her ne as her big bro. Ta d'au wai haushi Afzal yaji saboda bata sanar dashi kan cewa wani ya nemeta ba har sun daidaita, little did she know shi kansa Afzal d'in sonta yake. Har dare yayi har washegari bata fasa kiran layin nasa amman inaa se switched off yake ce mata, bayan data tashi daga school yau ta biya ta office nasa sede da mamaki securities suka ce mata ai be fito aiki ba yau kwata-kwata akan bey ji dad'in jikinsa ba. Wani sabon tashin hankalin ta fad'a, mey ke damun sa? Shin jikin yayi tsanani ne kokuwa? An rik'eshi a asibiti ne kokuwa yana jinya a gida? She needs to find out. Sede kamar yadda bata san gidansa ba haka kuma bata san gidansu ba balantana taje gun Ummi taji meke faruwa. Office nasu Sultan ta wuce chan ma ta tarar baya nan wai sun wuce meeting, zama tayi kusan na awa tana jiran dawowansa amman shiru dan haka kawai ta hak'ura ta komo gida. Tana isa gida ta watsa ruwa tad'an huta chan ta d'ago wayarta ta sake gwada numban Afzal luckily private line nasan ya shiga sede har ya tsinke be d'aga ba, a karo na biyu data gwada kuwa se yake ce mata number cannot be reached ko meye dalili? Ashe blocking contact natan Afzal yayi yasa a call divert yadda baza ta ta6a iya samunsa ba. 


  The following day still Afzal be fita office ba. Nazeefah kuwa ta rasa dalilin da ke sanya sa ababen da yakeyi kwana biyu, ko abincin da ya saba fita yana saya ma bata ga yayi ba yau, bayan nan ga bandejin data gani nannad'e a hannunsa. Ta duba dustbins na gidan kap bata ga fasassun glass ba bale ache ko yanka ya samu shin meke faruwa ne? Tun da ya kulle kansa a d'aki bey sake fita ba se zuwa masallaci kad'ai ke fitar dashi. Gwada tambayansa meya faru tayi inda sukayi baram-baram.  Akan me don ta damu dashi tana tambayansa meke damunsa ze tsaya yana mata masifa? Aikin banza. Bayan kwana biyu da faruwan abun ne Afzal ya soma fita office, hannun nasa da sauk'i kam amman still be since d'aurin ba saboda ba k'aramin ciwo ya jima kansa ba. 


   "Triple A ina ka 6oye ne wai kam kwana biyu?" Kafin Afzal ya amsa idon Sultan ya kai ga bandejin dake d'aure a hannun Afzal "Tsaya bandejin mey haka?" ya tambaya nan take. 


  "Babu banji dad'i bane kwana biyu."


  "Afzal I've known you for morethan 20 years kar kayi tsammanin zaka iya 6oye min abu. Amininka ne ni idan baka fad'a mun damuwanka ba mawa zaka fad'awa?"


  "Maza ba wani abu serious bane ciwon ciki ne ya rik'eni two days se kuma jiya na yanke da glass that's all."


  "Toh Allah sawwak'e ya cikin naka?"


  "Da sauk'i ya office?"


  "Alhamdulillah dama nace barin dubaka kwana biyu lines naka duka basu shiga."


  "An sace wayan ai sena sai sabo tukun."


  "Subhanallah private line naka fa? Har shima switched off yake cemun idan na kira."


   "Kasan ban cika kunnasa ba shi" Sarai Sultan yasan k'arya Afzal ke masa kawai baya son yayi pushing nasa ne saboda yasan halin abokin nasa abu kad'an kan 6ata masa rai kafin su hankara se suyi kaca-kaca anan. "Toh lemmi go back to work."


  "Alright take care" da haka sukayi sallama Sultan ya fice. Da yamma Sultan na zaune a office nasa PA'nsa tayi knocking ta shigo take ce mai yayi bak'uwa. 

  Bak'uwa de ya tambaya inda take jaddada masa eh. "Toh ki shigo da ita" yace mata. Ko da yaga Amal ce beyi mamaki ba saboda yasani dama komin rinsti da Amal Afzal ya samu matsala, yana da tabbacin ita kad'ai ce zata iya d'agawa Afzal hankali haka saboda tun ba yau ba ya karanci Afzal nason Amal. 


  "Amal?" Ya kirata. 


  "Na'am Ya Sultan" ta amsa tare da k'arisawa ciki ta tsaya. "Ina yini?" Ta gaishesa "K'ariso ki zauna kinji?" Ba gardama ta k'arisa ta zauna inda suka gaisa. "Yau kuma kin tuna dani kenan" yace da ita tamkar besan meke tafe da ita ba. 


  "Ai Ya Sultan kullum sede bamu had'u da Yaya ba se nace ya gaishe ka."


  "Toh nide sak'on ki be ta6a iske ni ba."


  "Afuwan toh."


"Ba komai, meke tafe dake ko de gaisuwa ce kawai?"


 "Eh toh duka biyu" ta fad'a tana nazari. 


  "Toh ina sauraronki."


  "Ya Sultan taimakonka nake nema don Allah."


 "Game da mey kenan?"


  "Yaya, Ya Afzal."


  "Meya faru?"


  "Yau kwana hud'u kenan ko biyar bana iya samunsa ta waya, koda naje office nasa kuma se acemun baya nan ya fita meeting dan Allah ka taimakeni."


  "Wait hold on, mey ya had'aku? Fad'a kukayi ne?"


  "Wallahi sam" se kuma tayi shiru bata san ta ina zata fara masa bayani ba tace mishi saurayinta ya kirata a gaban Afzal ne shikenan shi kuma ya hau zuciya yayi fushi da ita ko mey? Yau tana cikin wani yanayi. 


  "Feel free to talk to me kinji?"


  "Ya Sultan wallahi da nasan ransa ze 6aci da tun farko da Ya Abdul ya tinkareni da kalman so da bazan amince ba kokuwa da zan sanar da shi Yayan wallahi bansan ransa ze 6aci haka ba."


  "Hold on, waye kuma Ya Abdul?"


  "Wan k'awata ne..." nan de ta mar bayanin komi ba abinda ta ragar masa. 


  "Toh Amal naji bayanunki amman ke a tunaninki me zay sa Afzal miki fushi haka?"


  "Wallahi ban sani ba Ya Sultan na zauna nayi tunanin nayi tunanin amman ina na rasa k'wak'k'warar dalili sede tun lokacin da ya hanani shiga motan wani bayan nasa nasan ya damu da lafiyata ce sosai kuma baya son inayin abu ban sanar dashi ba" ta sanar da shi. 


  "Haka ne kam k'warai, so ke a ganinki yanzu da ace keda bakinki kika sanar dashi cewa gashi wani yace yana sonki shi Afzal d'in baze ji haushi ba?"


  "Eh Ya Sultan a gani na rashin sanar dashi da banyin bane ya haifar da komi, kuma wallahi ina da niyyan hakan kuma koda ace Yaya ya bud'i baki yace mun kar in amince da k'udurin shi Ya Abdul d'in in bari se karatu na yayi nisa tukun wallahi zan ji maganansa saboda tamkar wana na jini haka na d'auki Yaya nake kuma jinsa a jikina, duk abinda yace inyi muddin be sa6awa addini ba zan yisa, I respect him alot saboda son da yake nuna min bayan iyayena ban tsammanin akwai wanda ze nuna mun irinsa."


  "Toh Amal yanzu ya kenan? Bazan 6oye miki ba Afzal yana fushi dake sosai."


  "Wallahi nasani shiyasa nake neman taimakonka ka tayani basa hak'uri don Allah wallahi idan cewa yayi na dena kula Ya Abdul zan dena, zan iya yafe soyayyan kowa saboda farin cikin Yaya I care about him alot."


  "Toh shikenan Amal I'll do all I can in shaa Allah Afzal ze sauk'o zanyi masa magana."


  "Toh Ya Sultan thank you so much dan Allah duk abinda akwai ka taimaka ka kirani ka sanar dani."


  "Here write down your number for me" yayi maganan yana mik'a mata wata jotter nan da nan ta rubuta mai tana masa godiya. Ya rakata tace sam kar ya damu zata k'arasa da kanta. Bayan ta fice ya zaro wayansa daya 6oye k'ark'shin wani littafi had'e da stopping recorder d'in. Wow ashe tun d'azun recording hirarsu da Amal yakeyi. A tunaninsa idan har Afzal ya saurari hirar nasu, ya kuma gaskata kalamun nan daga bakin Amal hakan ze iya sanya sa sanar da ita Amal d'in abinda ke zuciyarsa don haka washegari ya kira Afzal akan suje suci abinci tare. Suna tsakan ci ne Sultan ya d'auko topic na Amal. 


  "Jiya Amal ta shigo min ai" dum Afzal yaji gabansa ya fad'i, sosai fuskansa ya bayyana mamakin da ya sha amman ya basar pretending like everything is cool. 


  "Oh haba? Ya take?"


  "Ba lafiya ba" ya amsa shi ba corner-corner. 


  "Why? Meya sameta?"


  "Haba Triple A drop the act already."


  "Sorry but I don't get you" yayi maganan had'e da d'age gira d'aya yana sipping drink nasa. 


  "Dan Allah ka dena wannan zurfin cikin wallahi ina gudun maka ranar da ciwon zuciya zata kama ka."


  "Why? Meya kawo wannan magana kuma?"


 "Mesa kake bawa 'yar yarinyan nan wahala haka? Shin baka tausaya mata ne? Wallahi ba haka so yake ba."


 "Excuse me?" Yayi maganan cike da rashin fahimta. 


  "Sarai kasan me nake nufi until when do you plan to stop torturing her life like this? Har yaushe Triple A? Kai fa na miji ne, idan kai a matsayinka na miji ka kasa tunkararta ka sanar da ita abinda ke zuciyarka taya ita a matsayinta na mace yarinya ma at that kake tunanin zata iya gano hakan da kanta, iyye?"


  "Ni ban fahimce ka ba."


  "Wow!" Sosai Sultan ya sha mamakin abokin nasa, be ta6a sanin zurfin cikin Afzal ya kai ga haka ba se yau. "You can deny me for as long as you want amman bazaka iya k'aryata cewa kana son Amal ba, bazaka iya k'aryata cewa akanta ne ka samu wannan munafikin ciwon dake hannunkan ba kuma akanta ne ka fasa wayanka har seda ka sake siyan sabo ba."


  "Look I'm not ready for this, idan kasan don haka ka kirani nan toh save it bana son sauraron ko kalma d'aya am leaving" wallet nasa ya ciro ya k'irga bill na abincin nasu ya ajiye akan table sannan ya mi'ke ya shiga tattara abubuwansa be kai ga takawa ba Sultan yayi playing audio'n da yayi recording jiya na hirarsa da Amal. Jin muryar Amal chak Afzal ya tsaya be sake motsi a wajen ba seda audio'n ta k'are. 


  Haushin kansa ya shiga ji na kasa sanar da Amal abinda ke cikin zuciyansa, na bawa zuciyarta daman son wani d'a na miji ba shi ba and k'arshe na sanya ta cikin damuwa haka. Ji yayi kaman ya wuce gidansu yanzun ya sanar da ita gaskiyan al'amarin ya tabbata kamar yadda ta fad'a idan da har ze bud'e baki yace yana sonta zata yafe soyayyar Abdul Rahman masa amman inaa baze iya ba, baze ta6a iyawa ba. Mutuncin da Amal ke basa baze ta6a basa daman ya furta mata kalamun so ba, baya son hakan ya zama sanadin da zesa Amal ta guje sa gara suta turawa a hakan. 


  "Ina had'a ka da Allah ka d'au mataki Triple A yarinyar nan bata ma san kana sonta ba nayi imani da Allah da ta sani wallahi bazata bawa shi Abdul d'in dama ba bale har su yi nisa haka."


 "Ni Afzal ban ta6a bud'e baki na ce maka ina son Amal ba kuma idan har baka son muyi kaca-kaca da kai bazaka je ka samu yarinyan nan ka fad'a mata cewan ina sonta ba tunda baka ji daga bakina ba. Idan kuwa har kayi hakan toh Allah ya isa ni ban yafe ba-"


  "Haba Afzal!" Sultan ya katse sa "Mey haka kakeyi? Mey yayi zafi haka har kake neman had'ani da Allah? Wallahi ko makaho ne yasan kana son Amal kuma muddin ka cigaba da wannan banzar d'abi'ar taka ba abin mamaki bane idan ciwon zuciya tazo ta kama ka, kamar kuma yadda kana ji kana gani Abdul d'innan ze auri 'yar nan a idonka ba yadda ka i-"


  "Enough Sultan!" Afzal da zuciyarsa ta fara tafarfasa ya katse sa cike da tsiwa "Ya isa haka don kana matsayin amini na doesn't mean you have the right to speak to me like this. Ban damu da wanda Amal take so ba, ban damu da wanda zata aura ba kamar yadda ta fad'a maka nima haka zan sake jaddada maka I'm just hurt saboda bata sanar dani wani yace yana sonta ba a matsayi na na wanda take kira yayanta, wanda ke d'aukan nauyin karatunta da sauran ababe. Bata yimin adalci ba ace har sun daidaita da wani bata sanar dani ba bayan nan I have nothing more against her so please bana son in sake jin kana cewa ina son yarinyar nan, nide na fad'a maka" Yana kaiwa nan ya fice ya nufi motansa, tunda ya soma tuk'i kalamun Amal suke masa raha a kunne duk yadda yaso kawar da hankalinsa daga hakan ya gagara k'arshe seda ya afka hatsari ya bige wani me sai da mangaro kafin ya ce ze taka burki inaa har ya buge mutumin sede Allah ya takaita abun mutumin fad'i kawai yayi be ji ciwo ba wheel barrown nashi ne ya fad'i komi na kai yayi k'asa. Da wuri ya sauk'a yayi kan mutumin kaman yadda mutanen kusa suka yi kansu suma, nan de ya basa hak'uri ya biyasa asaran da ya janyo masa. Office ya k'arasa ya kammala aikin da ya rage sannan yayi gida ya watsa ruwa ya kwanta. Sede abin ya gagara ya kasa daina tunanin Amal, kalamanta se yawo suke masa a kai lokaci d'aya tausayinta ya kama sa. 


   Wayansa ya janyo yayi searching contact nata tare da unblocking sannan ya kirata a karo na farko ta d'aga "Yaya?" Ta kirasa da mamaki ba tare da ta basa daman yin sallama ba. 


  "Na'am Lily" ya amsa pretending as if everything is cool. 


   "Yaya you called!" Tayi exclaiming cike da farin ciki da k'in yarda. 


  "Yes Lily ya kike?"


  "Yaya I'm sorry, I'm so sorry dan Allah kayi hak'uri."


  "Ya wuce kinji?"


  "No Yaya nasan abinda nayi maka ba dai-dai bane amman kayi hak'uri it shall never happen again please  forgive me."


  "It's okay, stop apologizing already ya wuce."


  "I missed you so much Yaya dan Allah karka sake hukuntani haka wallahi hukuncin yamin tsauri, Yaya duk abinda nayi ba dai-dai ba kana da ikon min fad'a har zana idan ta kama zakayi mun amman ignoring d'ina haka is not a solution please."

  

  "I'm sorry too Lily, I just didn't know how to react, my Lily is in love and I didn't know sede kawai ingani da ido na."


  "Wallahi ina da niyyan fad'a maka Yaya Allah ne kawai be bani iko ba amman kayi hak'uri."


   "So do you love him?" Ya tambayeta shiru tayi ta kasa amsawa "Lily?"


  "Na'am Yaya?"


  "Answer me."


  "Yaya..." se kuma tayi shiru "Yaya in ganin mu tare ne baka so ina iya sanar da shi in bashi hak'uri."


  "Not at all Lily ai farin cikink shine nawa besides ban ma san shi ba bale ince bana son shi so tell me about him."


  "Sunan shi Abdul Rahman he's 28 years old yana aiki a INEC office."


  "Masha Allah so do you love him?"


  "Yes Yaya I do" ta amsa chan k'asa-k'asa wani irin k'una zuciyan Afzal yayi da jin hakan daga bakinta danne zuciyansa kawai yayi yace, "Masha Allah ki ja mishi kunne fa kice mishi Yayanki yace kar ya kuskura yayi toying da feelings naki dan ko idan yayi na lahira ma seya fisa jin dad'i."


  Dariya tasa sosai "Kai Yaya nasan ai bazaka bari wani abun ya sameni ba besides Ya Abdul ma baze aikata abinda zesa a hukunta sa haka ba."


  "I like that spirit, so abu d'aya nakeso dake Lily ki mayar da hankalinki da karatunki kinji? Karki bari Abdul ya d'auke miki hankali kin ji?"


  "Na ji Yaya in shaa Allahu thank you."


  "Toh barin yi shirin sallah ko?"


  "Toh Yaya Allah ya kare goodnight." Sauk'e wayan yayi daga kunnensa a hankali yayin da zuciyar sa keyi masa wani irin rad'ad'i. Ta riga ta fad'a tana son Abdul in har Abdul ne farin cikinta toh shi kuma aikinsa ne a matsayinsa na yayanta yayi farin ciki da hakan. Meyasa yake jin haushi toh? Meyasa zuciyarsa take yi masa k'una haka? Yana son Amal, ya juma yana sonta, yana d'aya daga cikin burinsa na kullum ya mallaketa ya mai da ita nasa. Jira kawai idan lokacin yazo ya sanar da ita abinda ke cikin zuciyansa. 


  Da da jimawa yayi hakan amman baya son abinda ze raba mata hankali daga karatu se gashi nan wani daga chan yazo ya hargitsa masa plans nasa gabad'aya ya karya mishi zuciya, ya tarwatsar masa da mafarkin maida Amal amaryarsa, k'arshe kuma ya d'auke masa farin cikin rayuwarsa. Sosai idanunsa suka kad'a suka yi jaa zur idan ya tuna da dukka wannan ababe, k'iris ya rage beyi kuka ba.  Masallacin daya kasa zuwa kenan k'arshe a d'aki ya idar da sallan ya mik'e kan gado har bacci yayi awon gaba dashi. 


***

  Haka tafiya ta cigaba, gabad'aya Afzal ya rasa walwalar rayuwarsa kullum cikin k'unci da bak'in ciki yake. Amal ce me kirarsa kullum idan bata kira ba sede su zauna ahakan. Sau dayawa takan zuwa office nasa seya ce wa PA'nsa tace baya nan. Ita de Amal ta rasa dalilin duk wannan d'abi'u se Afzal ya d'au sati biyu be kawo mata ziyara kuma koda yazo d'inma baya iya sakewa da ita suyi hira kamar yadda suka saba, sau dayawa takan zauna tayi tunanin ko wani abun tayi masa amman ina ta duba ta duba ta rasa dalili. Ita da Ya Abdul nata kuwa se abinda ya k'au, tun bata barin ya d'auketa ita kad'ai a mota ta soma yarda da amincewa da shi. Zezo ya d'auketa su wuce gun shak'atawa idan ya tashi maido da ita gida kuwa ya cika mata leda da chocolates da ice creams. 


   Ta fannin Nazeefah ma sede abinda ya k'aru a kullum k'ara son Afzal take tun tana k'ok'arin 6oye masa abin ya gagara har ya kaiga shi Afzal d'in ya gane yanzu. Yau ma kaman jiya da ta tashi yin girki da shi tayi yana dawowa daga office tayi masa sannu da zuwa ya amsa sannan take ce masa food is ready. Banza yayi da ita seda ta bisa har d'aki "Afzal nace nayi girkin da kai fah."


   "Thank you a k'oshe nake."


  "Haka jiya ma kace, shikenan ni na rink'a girki kenan kullum kana cemin a k'oshe kake? Until when ne zaka dawo gidan nan da yunwa kaci abincin?"


 "Please! Save whatever this is kin dega daga office nake ko? I need to rest."


  "Toh wallahi ni kuma bazan yarda ba akan me zanna maka girki kak'i ciki?"


  "Ni na rok'eki kimin girki ne? Weren't you the one that said da kiyi min girki gara kinyi hauka?"


  "Toh kuma shikenan seka d'auka ka zauna akai? Ko kai zaman nan haka na maka dad'i I'm willing to change and start over this again why can't you?"


  "Because I don't love you Nazeefah kin gane ko? Ko mey kikayi you'll never impress me kin riga kin fita min a rai just let me be karki bari in sauk'e haushin da be shafe kiba akanki" yana kaiwa nan ya wuce bayi ya barta tsaye a gun. Hawaye kawai taji yana bin k'uncinta da k'yar ta iya tattara kanta tayi d'akinta ta shiga zuba kuka. Tun Mummy da Rumaysa suna ce mata tayi hankali tayi hankali kafin lokaci ya k'ureta tak'i ji gashi nan yau gar da gar Afzal ya bud'a baki ya ce mata ta fita masa a rai kuma ta tabbata ba komai bane ya janyo hakan illa rashin hankalin da tayita tafkawa, ina ma ace zata iya jan lokaci baya ta daidaita komi ba k'arya acikin zancen nan again tana son Afzal tana son shi kuma zatayi duk abinda ya kama don karkato da hankalinsa ya dawo a gareta. 


  Washegari da safe bim wajajen k'arfe sha d'aya ta shirya tsaf ta kira Afzal ta tambayesa izini sannan ta wuce gidansu Ummi dukda cewan bata sanar dashi inda zata. Maraba Ummi tayi mata suka zauna a parlour suka gaisa tasa su Esther suka kawo mata cookies da drinks. 


  "Kwana biyu kin k'i mu Nazeefah shima mijin naki ya kwan biyu be lek'o ba."


  "Allah sarki Ummi wallahi kinsan harkan makaranta yanzu ma dan mun samu hutu ne."


 "Wai bade har kun k'are part two din ba?"


  "Eh wallahi Ummi se three kuma yanzu."


  "Masha Allahu karatun naku na tafiya gaskiya Allah sanya albarka aciki."


  "Ameen ameen Ummi nagode dama alfarma nazo nema ne."


  "Toh 'yata ina jinki."


  "Game da Afzal ne."


  "Toh kuma bade wani abun bane ya faru ko? Ina sauraronki."


  "Ummi hak'uri nakeson ki basa."


  "Meya faru kunyi fad'a ne?"


  "Ki basa hak'uri ya soma cin girki na don Allah, Ummi bazan 6oye miki ba tun auran mu ba wata jituwa a tsakaninmu as dukan mu bawai muna so auran bane mun yisq ne don ladabi da biyayya ga iyayenmu."


   "Wannan haka take 'yata."


  "Toh Ummi bazan 6oye miki ba wallahi ko girki ban ta6a yiwa Afzal ba, rayuwansa yake daban a gidan nima haka, kullum daga office se parlour se d'akinsa yake zama nima daga school se parlour se d'akina amman abun ya isheni yanzu na zauna nayi wa kaina fad'a I want to give us a chance nace zan fara yi masa girki kuma na faran sede ko nayi baya ci Ummi wallahi ina son Afzal amman ko na second d'aya baya ma kallo na balle yasan ina cikin damuwa, be damu dani ba jiya har cemin yayi baze ta6a sona ba na riga na fita masa a rai and I don't blame him saboda ni ne na janyo komi da kaina amman na tuba yanzu Ummi I promise to be a good wife to him but ya k'i bani dama, bansan ya zanyi ba wallahi ina son sa."


  Iya mamaki Ummi ta sha bata tsamman gaban dake tsakaninsun ya kai har ga haka ba ita da take jiran jika amman ace haka ai wannan da alama ko had'a kwanciya basu ta6a yi ba, lallai kam akwai k'ura sede kuma ta gamsu da tuban Nazeefah. Idan ba so na hak'ik'a takeyi wa Afzal ba ba yadda za'ayi tana mace ace bata ji kunyan idon surkarta ba har tayi admitting kurakuren ta haka. 


  "Ummi dan Allah ki basa hak'uri ko ze soma cin abinci na ya dena had'a min rai haka kullum."


  "Naji matsalar ki Nazeefah sede abu d'aya nikeson tambaya."


  "Ina jinki Ummi."


  "Ina fatan a iya zamanku baki ta6a goranta mai da wani abun ba?" Shiru tayi tana nazari chan tace "Wallahi nayi na masa akan girki."


  "Ai kin 6ata komi kenan gorin da kikayi masan ne yasa har yau ya kasa cin girkin ki."


  "Ummi amman ai idan kika basa hak'uri zai sauk'o."


  "Zanyi iya k'ok'arina but I can't guarantee you hakan. Afzal halin mahaifin shi ya biyo se kuma har kaman nasa ma na son fin na mahaifin nasa. Kinga koni nan idan mukayi fad'a dashi se idan nazo na basa hak'uri yake sake amincewa yaci girkina kiyi imagining ke matarsa da har kikayi masa gori. Ina son ki sani cewa komin yaya fad'a ta 6arke muku da Afzal koda wasa karki kuskura ki goranta masa da wani abun dan shi idan yayi fushi da abu yayi ne har abada se wani ikon Allahn."


  "Innalillahi Ummi kina nufin yanzu Afzal baze ta6a cin girki na ba kenan?"


  "Bana fatan hakan, in shaa Allah zan kirasa muhi magana duk abinda akwai zan kiraki in sanar dake."


  "Amman Ummi nagode sosai please don't let Mummy know of this pleaase."


  "Karki damu 'yata in shaa Allah maganan nan a tsakanin mu ne."


  "Thank you so much I shall get going."


  "Bazaki bari kiyi Azahar ba tukun?" Tayi maganan tana duban lokaci. 


  "Zanje inyi girki kinsan yau juma'ah 2 Afzal ke dawowa gida."


  "Toh Mama na Allah miki albarka bari in raka ki." Tana raka Nazeefah ta dawo ta d'au wayarta ta kira Afzal a karo na farko ya d'auka. 


  "Halo Ummi?"


  "Na'am Prince d'ina."


  "My Ummi ya kike? Ya Abba?"


  "Lafiya k'alau ya aiki?"


  "Alhamdulillah nace zaka iya biyowa nan idan ka tashi daga office yau?"


  "Sure wani abu ne?"


  "Kai de seka zo kawai."


  "Toh shikenan ina idar da sallan Juma'ah zan zo."


  "Yauwa Baby na Allah kawo ka lafiya yayi maka albarka."


  "Ameen Ummi take care bye" da haka sukayi sallama. Kaman yadda ya fad'a mata hakan yayi yana tasowa daga Juma'ah ya d'au hanyan gida, a hanya Amal ta kirasa, connecting yayi da car Bluetooth nasa sannan ya amsa suka gaisa take yi masa barka da Juma'ah. Yana isa gida ya fara wucewa site na Abba suka gaisa sannan ya k'arisa na Ummi. 


  Bayan gaisuwa Ummi tayi gyaran murya, "Dama ba komai bane yasa nace kazo illa batun matarka Nazeefah."


  "Toh kuma meya faru Ummi?"


  "D'azu ai tana nan." Se anan ya gane ashe nan tazo da ta kira take tambayansa izini.  

  

  "Lafia dai ko?"


  "Ai ka fini sani, kai de bazaka ta6a barin wannan zurfin cikin naka ba ko?"


  "Mey tazo tace miki?"


  "Komi ma ta fad'a ba abinda ba ta sanar dani ba ai dama sau dayawa nayi suspecting zaman auren nan naku ashe haka kuka ta turawa har na tsawon shekara d'aya Prince? Wallahi I'm very disappointed in you idan ita Nazeefar yarinya ce bata da hankali ai kai seka nuna mata kana dashi amman ba wai ka tsaya kana biye mata ba kuna tafka wawanci ba, yanzu meye ribar ka? Yaci ace ka ajiye d'a a zaman ka yanzu haka wallahi."


  "Ummi don't just jump into conclusions wallahi Allah ma sheda ne nayi hak'uri da Nazeefah iyakan hak'uri, ba me iyayin hak'urin da nayi da ita ni kawai bana son 6ata ta a idonki ne kikaga ko kin tambayeni ya gida nake miki k'aryan cewa lafiya k'alau."


  "Kalleni Prince" ta buk'acesa, ba gardama ya dawo da kallonsa a gareta "Zanyi maka wata tambaya kuma I want only a sincere answer."


  "Ina jinki" ya amsa bayan tsawon lokacin daya d'auka. 


  "Yadda kasan zaka mutu tsakaninka da Allah ka ta6a bawa yarinyar nan hak'k'inta na aure a matsayinta na matar ka?" Shiru yayi yana mamakin bade abubuwan da Nazeefah tazo ta irga wa Ummi ba kenan cewa ko hak'k'inta be ta6a bata ba, lallai kuwa!

  

   "A dalilin mey zan had'a kwanciya da ita Ummi? Kinsan mey tace ne? Da kunne na najita tana cewa k'awarta da ta bani kanta gara 'yan iska akan layi sunyi mata fyad'e kina ganin ya dace in raya sunnan manzo da ita?"


  "Innalillahi! Nazeefar de?"


  "Ummi k'arya zan miki ne? Wallahi da kunne na naji kefa baki san rashin hakalin da yarinyan nan take ba kuma wallahi albarkacin Abba take ci dan yanzu da zaran na saketa ko nayi mata wani abun kaman wa Abba nayiwa hakan ze iya 6ata tsakaninsa da amininsa ko ba haka ba?"


  "Hakane Prince kuma na yabawa hak'urin ka amman seka duba kuma yanzu da ta gano kuranta take son ku fara sabon rayuwa, kamata yayi kayi hak'uri ka bata dama. Wallahi da bakinta anan take cemin tana sonka dan Allah in baka hak'uri."


  "Ni to bana sonta" ya fad'a mata gar. 


  "Wani irin magana ne haka Prince? Matarka ce fa! Haka kakeson ka cigaba da rayuwanka? Shin kai baka kwad'ayin ganin jininka ne?"


  "Inaso mana amman bada Nazeefah ba."


  "Prince dan Allah kar kayi magana haka kamar yadda ka tsani yarinyan nan fa itama haka ta tsaneka da fari amman mey? Data bud'e zuciyarta maka ba gashi soyayyarka ta shiga ba kaima fa zaka iya dan Allah kar kace a'a."


  "Ummi kin de sanni, kin fi kowa sani na idan abu yafita min a rai ya fita kenan har abada, a da kafin in auri Nazeefah ban tsane ta ba kaman yadda na tsaneta yanzu. Zaman da mukayi da ita ya sake sa na tsaneta yarinyan can bata da hankali, bata da tunani, ba ta da fasalin komi, ba yadda za'ayi ta zame uwa ga 'ya'yana no way!" Ya jaddada mata. 


  "Prince dan Allah ka dena magana haka, ka cigaba toh wallahi baza ka san lokacinda ze iske mahaifinka ba. Ka yayyafa wa zuciyanka ruwan sanyi kayi hak'uri ka bata dama ta sauk'e nauyinta a kanka a matsayinta na matarka."


  "Ni ta bari kawai na yafe mata haka zamu cigaba da zama har zuwa lokacin da Allah ze raba mu."


  "Wato kafi k'arfin in gaya maka magana kuma kaji ko Prince?"


  "Ummi please kar kiyi magana haka sanin kanki ne banida kaman ki ans I always heed to you."


  "Then listen to me ka bawa Nazeefah dama."


  "Ummi zuciyana na mace d'aya ne kuma wata chan ta riga ta sace ta tafi dashi ba komai anan" yayi nuni da inda zuciyarsa ke. "Kinga ko ba yadda za'ayi in fara son Nazeefah."


  "Babban magana! Bade shirin aure kake yi ba?"


  "Ko kad'an nide kawai na fad'a miki ne."


  "Akwai wacce kake so a waje kake nufi?"


  "Yes."


  "Wacece ita?"


 "I'm sorry Ummi but I can't tell."


 "Hmm yaron nan ina tausaya maka, ina rabaka da ciwon zuciya, ba shakka kana bin soyayyar yarinyar nan ne a zuciya har ka rame kayi bak'i haka kwana biyu. Afzal ka tausayawa kanka ka dena rik'e abu a zuciya haka uhn uhn fa!" Ta ja masa kunne. Shi de shiru yayi zaune a gun yana sauraronta dan kuwa bashida abin fad'a mata, soyayyar Amal ne de baze ta6a furtawa ba.





RANA D'AYA!💖

#RD


Love... Miemiebee👄✨

[13/08, 00:39] ‪+234 907 483 8352‬: 🎀🎀🎀                 🎀🎀🎀

                🎀❣🎀

                   ❣❣


  💦💦                      🍃🍃🍃          

           *RANA D'AYA!*

  💦💦                      🍃🍃🍃

  June, 2018

 beeenovels.blogspot.com


     _Written by Miemiebee👄_



   *PAGE 1⃣5⃣*



  

    Yana dawowa gida ya tarar da Nazeefah zaune a parlour ta sha wanka tayi kwalyanta ras tana kallo. Sannu da zuwa tayi masa tare da mik'ewa. Shiru yayi yana nazarin amsawa kokuwa chan de yace "Yauwa sannu."


  "Food is ready, zaka ci anan ko in kai maka d'aki?"


  "A k'oshe nake" yace da ita sama-sama yayin da ya shiga tafiya. 


  "Afzal shin baka jin hak'uri ne kam?" tayi sauri ta sha gabansa "Me kakeson inyi ka hak'ura?"


  "Nifa ki dena bani hak'uri don bance miki ina buk'ata ba."


  "Then me ke hana ka cin girki na?" 


  "A jinki zaki je ki samu Unmi a bayan idona ki had'a mata k'arya da gaskiya sannan kizo nan kina proving min innocence? LOL" ya sa dariyan rainin hankali. "Try harder."


  "Wallahi ni ban yi maka sharri gun Ummi ba."


  "Ohhh!" ya numfasa had'e da zaro lumsassun idanunsa waje "So kike kice Ummi na k'arya kenan?"


  "Ni ba haka nake nufi ba kawai ce mata nayi ta baka hak'uri nothing more."


  "Toh nak'i, nak'iyin hak'urin just let me."


  "Afzal please mey kakeson inyi maka ka hak'ura ka dena d'aura mun fuska haka? In hak'uri ne kakeso zan yita baka shi I'm sorry but please let's put a stop to this, shin zama hakan be isheka bane?"


   "Be isheni ba infact yanzu ma ya soma min dad'i, excuse me" yana kaiwa nan ya wuce d'akinsa. Sosai jikinta yayi sanyi amman dukda hakan bata kariya ba, dining ta nufa ta d'ibar mar abincin a plate ta d'au goran ruwa tayi d'akinsa luckily ta samu a bud'e. Shiga tayi taga ba kowa aciki da ta kasa kunne setaji alaman mutum a cikin bayin. Zama tayi daga gefen gadon nasa tana jiransa, be dad'e ba se gashi ya fito d'aure da towel a iya kunkuminsa yayinda droplets na ruwa ke d'iga daga kansa yana bin well defined abs nasa, omo Nazeefah ta kasa d'auke idonta daga kansa, ko kyaftawa ta kasa, yadda skin nasa ke wani glowing k'ark'ashin ranan da ya hasko d'akin kad'ai ya sata mance ina take, burinta a lokacin kawai ta aza hannunta akan jikinsa. 


  Ta fannin Afzal kuwa mamaki sosai ya sha da ya ganta a d'akinsa, a d'akin ma wai akan gadonsa. Gadonsa de! Shin waya bata izinin? Banda nan ga wani mayen kallon da takeyi masa wane zata cinyesa, ganin kallon nata ba na k'arewa bane yayi gyaran murya hakan ne ya dawo da ita daga duniyan tunanin data fad'a. Kanta tayi saurin sauk'arwa cike da kunya tare da mik'ewa "Dama abincin naka ne na shigo maka dashi" bata jira jin mey zey ce ba ta fice binta da kallo yayi sannan ya nufi kan abincin ya tsaya yana k'are mai kallo. 


  Toh kode wani abun cutarwan ta sanya masa aciki yadda ta k'osa seya ci? Yayi tunanin hakan a ransa. D'agawa yayi ya kai hancinsa dukda cewa yasan shunshuna abinci haramun ne. K'amshin spices zalla yaji ke tashi sede hakan be sanya sa cin abincin ba. Miyarwa yayi ya nufi wardrobe nasa ya ciro shorts da singlet, yana cikin sanya singlet nasan ne wayansa ya shiga ruri k'arisawa gefen gadon yayi ya d'aga ganin Amal ke kira se yaji gabad'aya jikinsa yayi sanyi ya mutu kaman wanda baze d'aga ba ya amsa. 


 "Halo Yaya?" Ta soma da cewa. 


  "Na'am Lily" ya amsa. 


  "Yaya are you free today?"


  "Wani abu ne?"


  "Na had'a maka Aldeb ne nake tunanin ko zaka zo ka d'auka."


  "Kash wallahi ban tsammanin zan iya zuwa aiki ya rik'eni yanzu haka ina shirin zuwa meeting ne" yayi mata k'arya. 


  "Toh Yaya ya zamuyi kenan?"

    

  "Se zuwa wani lokacin in shaa Allah Lily thank you."


  "Toh ba yadda za'ayi in kai maka ne ko a gida?"


  "Kibari zuwa wani lokacin kawai kinji?" Ba don tana so ba kawai tace masa "Toh shikenan Allah kaimu" da haka ta kashe wayan ta sauk'e. 


  "Ya wai?" Falmata da ke shirin rakata office na Afzal ta tambaya. 


  "Wai baze yuwu ba seko wani lokacin."


  "Baze yuwu ba kuma? Wani irin juyayyan magana ne haka?"


  "Wallahi ban sani ba Falmata, ban san meke damun Yaya ba ina fad'a miki tun kan lokacin da ya gane cewa Ya Abdul saurayina ne ban sake gane kan sa ba."

  

   "Hmmm Baby kenan ke yanzu har se an zauna an fad'a miki abinda ke faruwa?"


  "Abinda ke faruwa kaman ya kenan?" Ta tambaya cike da rashin fahimta. 


  "So kike kice wai baki san dalilin da yasa Ya Afzal ke nuna miki wannan halaye ba?"


  "Wallahi ban sani ba Falmata dan Allah ki fad'a min" ta amsa tana me tattaro hankalinta duka a gareta. 


  "Kin deji rantsuwa ba kaffara ko? Wallahi son ki Ya Afzal yake" dum Amal taji zuciyarta ta buga, yadda kuka san an sanar da ita mutuwan Mami haka jikinta ya mutu a wajen ko k'wak'k'warar motsi ta kasa tafi minti biyu zaune shiru a wajen sannan daga bisani ta shiga kad'a kanta tana k'aryata batun Falmata "K'arya ne hakan baze ta6a faruwa ba. Ba yadda za'ayi Yaya ya fara sona, Falmata it doesn't even make sense."


  "Ko meyasa? Meyasa Afzal baze fara sonki ba Amal bayan kullum kuna tare?"


  "A'a Falmata dan Allah kibar zancen nan ko matan duniya sun k'are Yaya baze ta6a cewa yana son k'waila kamata ba. Ke ni bama tsarirsa bace har mey Yaya zeyi da mace kamar ni? Kiyi tunani mana."


  "Shikenan Baby ki k'aryatani iya son ranki amman de gaskiya d'aya ce wallahi Ya Afzal sonki yake idan ba kishinki yake ba har mey yayi zafi don yaji kina da saurayi ransa ze 6aci yayi fushi dake? Bayan nan keda bakinki kikace tun lokacin chan har izuwa yanzu baki sake gane kansa ba kiyi tunani mana akwai 6oyayyen al'amari anan."


  "Tabbas akwai amman ba wai Yaya sona yake ba."


  "Toh shikenan amman de ki zauna kiyi tunani da a banza ne zeyi maki duka wannan d'awainiyyar da yake mikin Baby? Haba mana ai ko ba a fad'a miki ba yaci ace kin gano hakan da kanki ko shi d'in ki mayara dashi baho ne wanda be san meye zeyi da kud'insa ba? Kin deji rantsuwa ba wallahi ba mey maki wannan d'awainiyyar a banza in ba mahaifanki ba."


  "Ni nasan Yaya, nasan abinda ze aikata da abinda baze iya ba. Komi da kika ga Yaya namun tsakaninsa da Allah ne, idan da har so na yake kaman yadda kika fad'a da idan munyi waya baze na tambaya na ya Ya Abdul ba."


  "Aikin banza, wallahi 6ad'da k'afa yakeyi."


  "Falmata idan har da sona Yaya yake ina da tabbacin daya furta min idan ko beyi hakan ba ze samu Papi ya fad'a masa amman beyi ko d'aya ba taya kike tsammanin zan kawo tunanin hakan a raina? Kamar yadda nasan Yaya baze kalleni da idon so ba nima wallahi bazan iya kallonshi da hakan ba so please bana son sake jin maganan nan kafin har magana ya iskesa kisa ya fara min kallon wacce bata da godiya batin duk abinda yayi min in bud'i baki ince ina sonsa."


  Duk yadda Falmata taso fahimtar da Amal lamarin ina abun ya gagara ita k'wak'walwarta ma ta kasa d'aukan mata maganan, wai taya za'a ce Yaya yana sonta? Yaya deh? K'arya ne. 


   Chan dare wajajen k'arfe tara Amal na mik'e akan katifar ta tun tafiyan Falmata take ta tunanin abinda ta fad'a mata, ta kasa daina tunanin hakan. Wayanta dake gefenta ne ya shiga ruri yana me tsamurota daga duniyar tunanin data fad'a. Lek'awan da zatayi taga Ya Abdul ke kira ba tare da 6ata lokaci ba ta d'aga. 


  "Halo Baby?"


  "Na'am My heartthrob" ta amsa. "Ya kake?"


  "I miss you" yayi admitting. 


  LBaby I missed you too se yaushe ne zasu dawo min da kai?"


  "Se ko next week."


  "Har next week? Shi d'inma under question mark? Gaskia ni zan nemi wani saurayin shikenan kai kana cikin tafiye-tafiye kullum?"


  "Haba girlfriend yi hak'uri mana nima ba a son raina bane, guess what?"


  "Tell me."


  "Akwai tsarabar dana tanadar miki."


  "Kai Baby? Na meh fah?"


  "Toh kuma ana sanar da mutum tsaraba ne?" Ya had'e rai tamkar tana gabansa. 


  "Ai ni baby'nka ce zaka iya sanar dani ko ba haka ba?"


  "Kuma haka ne fah."


  "Yauwa dearest ome tell me toh."


  "Ina bracelet nan da Daddy ya saiwa Maamah kika ce kinason irinsa?"


  "Eh Baby bear" ta amsa anxiously. 


  "Toh wanda Baby'nki ya saya miki har ya fi nata kyau."


  "Kai Baby! Dagaske!" Tasa ihu. 


  "Yes Love."


  "Awwwnn I love you soo much nima ina kan tanadar maka da tsarabata." 


  "I trust my Baby."


  "Your baby is honored."


  "Toh ya kike yasu Mami?"


  "Lafiyansu k'alau ya chan d'in? Ina fatan ba wacce tasa maka ido kasan fa kullum se nayi maka add'ua."


  "Kai Baby karki damu I'm safe."


  "Ahtoh duk wacce tace maka tana sonka ma kace mata kai anyi maka mata a gida."


  "An gama Baby" yayi assuring nata. 


   "Yauwa Baby na" hira kad'an suka k'ara tayi masa seda safe. Tana ajiye wayar tunanin Afzal ya sake dawowa mata, daga k'arshe de ta d'au wayarta ta kirasa sede har ya tsinke be d'aga ba se a karo na biyu. 


   "Yaya?"


 "Na'am Lily" ya amsa yana mik'e akan gado daman tunaninta yake shima se gashi ta kira. 


  "Yaya muna fad'a ne?" Ta tambayesa. 


  "Kaman ya fad'a kuma Lily?"


 "Yaya ai ka fini sani."


  "Ban fahimce kiba Lily." 


  "Yaya idan wani laifin ne nayi maka ka sanar dani in baka hak'uri wallahi I miss you, Yaya ko kirana baka yi sede idan ni na kira ka, rabonka da ka kawo mana gaisuwa har na manta daga yau kace ba kada lafiya se gobe kace aiki ya rik'e ka, Yaya what is happening? Wani laifin ne nayi maka ya 6ata maka rai haka wanda ni ban sani ba?"


  "Lily-"


  "I'm sorry" ta katse sa "It's just that I miss you so much. I've had sleepless nights thinking about where and how I've wronged you amman nakasa figuring out komai" ta sanar da shi sincerely. Shiru Afzal yayi na d'an lokaci, gabad'aya se yaji ba dad'i tabbas yasan be kyauta mata ba kuma ko shi d'inma bawai yana jin dad'in zamansu hakan bane. He misses her dearly, he misses being with her, he misses her smiles and laughter, he misses picking up fights with her. A takaice yayi missing komai dangane da ita amman ba yadda ya iya ne. Ya zame masa dole ya nisantar da kansa daga gareta saboda gudun 6acin ransa da kuma jefa kansa acikin damuwanda yafi wannan da yake ciki yanzu. Baze iya jure ganin Amal da wani d'a na miji ba shi ba, baze iya jure ganin minti-minti wani na kiranta yana tambayan lafiyanta ba a takaice baze iya jure ganin wani d'a na miji da ba shiba yana sanya Lilirsa farin ciki, gara suyita tura tafiyan haka. 


  "Yaya baza kayi magana ba?" Tayi maganan yayinda idanunta ke cikowa da hawaye. 


  "I'm sorry kinji?" Ya tsinci kanta yana fad'a mata dan ko besan mey zey ce bayan hakan ba. 


  "Yaya ni ba hak'uri nakeso ba just tell me mey nayi maka in baka hak'uri wallahi bazan iya yafewa kaina ba idan har na 6ata maka rai ba tare da baka hak'uri ba" kawai seta sa kuka. "Yaya I'm sorry please forgive me."


  "Lily bade kuka kike ba?" Ya tambaya da mamaki. 


  "Yaya taya bazan yi kuka ba bayan kana fushi dani har nagaji da had'awa Papi k'arya kullum se yace mun kunyi waya kana lafiya amman ya rasa dalilin da ke hana ka zuwa, gani yake kaman ni nayi maka wani laifin, haka sede inyi masa k'arya ince aiki ne ya rik'e ka please forgive me."


   "Ya isa haka kinji? Ya isa bar kukan haka."


  "I can't bazan iya ba."


  "Are you free gobe?"


  "Eh" ta amsa tana share hawayenta.


  "Toh shikenan share hawayenki, se na shigo."


  "Dagaske Yaya zaka zo?" 


  "Everything for my Lily. Zanzo muje duk inda kikeso."


  "Toh Allah kaimu" ta amsa cike da jin dad'i. 


 "Ameen."


  "Amma bazaka sanar dani abinda nayi maka ba ko?"


  "Lily bakiyi mun laifi ba ai na sha fad'a miki Lily bata laifi."


  "Toh shikenan nagode sosai ka gaishe da Nazeefah."  Washegari kamar yadda yayi mata alk'awari bayan da ya dawo daga sallar jum'ah ya canza kaya ya sanya wata burgundy half jamfan daya mugun amshe skin colorsa da kuma figure. Wankan turare yayi ya sanya accessories nasa sannan ya d'au wayarsa ya fice. Yana cikin locking d'akinsa ne wayansa dake aljihu ya shiga ruri da sauri ya sa key'n ya zaro wayar se gani yayi Amal ke kira da alama don taji sa shiru ne takeson jin ko lafiya. Murmusawa kad'an yayi tare da sliding ya amsa sannan ya shiga tafiya. 


  "Halo Lily?"


  "Yaya naji shiru kode ka canza ra'ayinka ne?"


  "Na isa?"


  "Toh gashi har k'arfe hud'u baka zo ba" ta amsa had'e da zum6uro baki. 


  "Gani nan zuwa yanzun nan ki bani like 20 minutes okay?"


  "Alright toh seka iso" cike da farin ciki ta katse wayan. Nazeefah dake zaune kan kujera a parlour tuni ta cika dam da kishi, zuciyarta ta gama ta fasa sauran k'onuwa kawai. Wato duk uban wankan nan gun karuwarsa zasa ko? Da kyau ai bata basa izinin k'arisawa bakin k'ofa ba ta sha gabansa. 


  "Lafiya?" Ya tambayeta da mamaki had'e da d'age gira d'aya. 


  "Se ina kuma?" Ta tambayesa cike da kishi. 


  "Wai tsaya ni dake wake zaman wani ne kam a gidan nan?" Shi dariya ma ta basa. 


  "It doesn't matter, taya ina ji ina gani zaka gun wata daban?"


 "Aww ashe kinsan inda zani" yayi maganan cike da rainin wayo. 


  "Wallahi bazaka ba" tasa rantsuwa. 


  "Hana ni zakiyi?"


  "Wallahi idan ta kama zan hanaka ita karuwar taka bata san kana da aure bane?"


  "Nifa na gaya miki ki dena kwatanta yarinyar nan da karuwa."


  "Da malama kakeson in kwatanta da? Haba mana Afzal yanzu duk hak'urin da na baka da wanda Ummi ta baka be isheka ba, bazaka dena neme nemen matan nan ba?"


  "Kar ki sake kwatantani dame neme nemen mata kuma koda nayin ma you think kina da right na min magana ne? Look at you" ya tsaya yana k'are mata kallo "Tun yaushe kika fara regarding d'ina as your husband and incase you forget I'm a husband to four wives."


  "Wato ko kunyan ido na ma bakayi gar da gar kake fad'a min kana da budurwa ko?"


  "Lmao kunyan mara kunya asara ko inji bahaushe?"


  "Wallahi Afzal ka cigaba kuma kaji rantsuwa ba kaffara wallahi ko 'yar gidan ubanwa kake nema muddin na samu information akanta believe me sena rabaku ka nemi waje ka rubuta."


  "I would love to see you try" yayi maganan disgustedly yana mey watsa mata mumunan harara sannan ya fice. Rushewa tayi gun tana kuka na hak'ik'a bata san ya akayi soyayyar Afzal ya kamata haka ba, gani take kamar idan be zame nata ba tana iya rasa rayuwarta. Oh Allah ya kawo mata sauk'i. 


  **

  Yana isa gaban gidan nasu yayi ma Amal waya, nan da nan tayi touching over 'yar kwaliyarta ta sanya hijabinta sannan ta cire sim nata ta ajiye a gefe gudun kar Ya Abdul yazo ya kirata suna tare da Afzal hakan ya sake janyo mata wata matsalar. Da farin ciki kwance fal a ranta ta fice taje ta samesa, kamar yadda take masa fara'a shima hakan yake mata, ba k'arya sunyi kewar junansu. Hira sosai sukayi sannan ya tambayeta inda takeson suje ita dan murna ma kawai ce masa tayi suyita zagaya garin Maiduguri har se sun gaji. Haka suka d'au hanyan federal low cost chan farin Maiduguri suka kai suka sake d'auko hanyan University dake k'arshen Maiduguri daga chan suka bi ta gidan madara ya sai mata chocolates da dama. Bayan ya dawo da ita gida ta buk'aci ya jirata tana zuwa, fitowanta ta taho masa da aldeb da ginger. Sosai yaji dad'i danko yayi missing had'ad'd'en aldeb natan nan ba k'arya. Ba gardama ya amsa yayi mata godiya sannan ya tambayeta ko su Mami suna gida ya shiga su gaisa. Sosai su Papi suka ji dad'in ganinsa, sunyi hira kad'an Afzal yace ze tafi Maghrib ya gabato har waje duka suka raka sa sukayi sallama. 


   Haka Amal keyi duk sanda Afzal zezo mata seta cire sim nata ta ajiye, da ikon Allah kuma Afzal be sake d'auko mata maganan Ya Abdul ba, a hankali shak'uwa ya sake shiga tsakaninsu as duk abinda Amal tasan ze 6atawa Afzal rai gamw da Ya Abdul tana avoiding. Nazeefah bak'in ciki kaman ze kasheta ta rasa ya zatayi da ranta gashi har yau ta rasa information akan Amal ko idan Afzal ya fita tace zata bi bayansa kullum seya kamata seya canza gun zuwa kokuwa ya shiga nan ya shiga chan har se tayi losing track nasa. A haka ne har aka bud'e makaranta, su Amal 'yan part two. Wannan karan da kanta tayi registrations nata, koda Afzal yace ze taimaka mata ma k'i tayi tace zata iya da kanta. Bada dad'ewa ba suka fara lectures. 


  Yau bayan lectures ya k'are, Amal da Maamah suna zaune akan slab suna jiran Ya Abdul yazo suje su ci abinci sega Afzal na sauk'owa daga kan stairs tare da wani abokinsa wanda ya kasance assistant lecturer. Amal na ganinsa zuciyarta ta fad'i kafin tace zata tare fuskarta inaa Afzal har ya hangeta. Suna sallama da abokin nasa ya shiga dosan inda suke zaune da Maamah sede beyi nisa ba sega motan Ya Abdul yazo dai-dai gaban su Amal ya tsaya hakan yasa Afzal dakatawa shima se gani yayi mutumin ya fito cike da farin ciki ya tsaya akan su Amal. Wani irin k'ona zuciyansa ya shiga yi masa bade wannan bane saurayinta Abdul d'in ya tambayi kansa. Se chan yaga Amal ta mik'e sede har yanzun ta kasa juyawa ta kalli Afzal da k'afafunsa ke kakkarwa. Ba haka taso abun ba, bata som abinda ze 6ata wa Afzal rai. A hankali ta juyo tana kallonsa, excusing kanta tayi daga gun Ya Abdul akan tana zuwa, nan ta nufi gun Afzal yayinda shi da Maamah suka zuba mata ido. Tana k'arisawa ta la6e daga jikin wata bishiya. 


  "Yaya" ta kirasa cike da kunya ko kallon cikin idanunsa ta kasa. Danne zuciyarsa yayi da k'yar ya iya amsata "Na'am Lily."


  "Yaya good afternoon."


 "Afternoon ya lectures?"


  "Alhamdulillah Yaya shine zaka shigo school ba zaka sanar dani ba?"


  "Ba zama zanyi ba shiyasa lemmi get going" ya sanar da ita yana neman juyawa. 


  "Yaya bazaka tsaya ku gaisa da Ya Abdul ba? Tun ba yau ba yake son ku had'u."

  

  D'aga ido yai ya kalli Ya Abdul dake kallonsa shima, kau da kansa yayi take yace da ita, "Maybe next time Lily I'll be late for the meeting" be bata daman sake magana ba ya fice ya nufi motarsa tare da bata wuta. Kaman wanda k'wai ya fashewa a ciki Amal ta k'arisa gun su Maamah da suke kallonta har anan. 


  "Omg! Amal kinga ban yi mana submitting assignment namu ba, lemmi hurry" Maamah ta fad'a kafin Amal tace mata ai nayi d'azu har ta fice dama da gan-gan tace hakan don ta basu daman yin magana ne don tasan ko ba'a tambaya ba Ya Abdul na da abin cewa game da wannan abinda ya faru yanzu. 


  "Amal?" Ya kira sunanta a hankali bayan ficewan Maamah sede sam hankalinta yabar jikinta. "Amal?" Ya sake kirarta se a karo na uku ta amsa a firgice. "Amal meya faru?"


  "Babu I'm sorry mu tafi ko?"


  "Ba inda zamu sekin fad'amin abinda ke damunki."


  "Allah babu komai Ya Abdul lets go yunwa nakeji." Hijabinta ya ja seda ya zaunar da ita sannan ya zauna agefenta tare da barin rata a tsakaninsu. "Meya faru tell me kinji? Waye wancan da ya tafin?"


  "Ina Yaya na da nake fad'a maka? Shine ya tafi yanzun." A lokaci guda Ya Abdul yaji zuciyansa ya tsinke karde d'an wannan ne yayan da Amal ke damunsa da shi kullum? Lallai akwai k'ura shi a iya tunaninsa wani babba ne da ya girmesa ashe de yaro ne, ai ko be tambaya ba yasan ya girmesa. Inko wannan ne yayan nata shikenan ya tabbatar da zarginsa batun lokacin da Amal tace masa yayanta yayi fushi saboda yaji tana da saurayi. 


  "Baki fad'a masa ina son mu gaisa ba?"


  "I told him yace wai yana da meeting seko wataran" amsanta ne ya sake tabbatar masa da zarginsa ba shakka kaman yadda yake gudu wannan yayan nata sonta yake. Shin ita Amal bata sani bane? Kokuwa bata son shi ne? Amman kuma daga yadda take mganansa mutum ma ze san tana sonsa. Yau ya zeyi? Baya son ya rasa Amal baze iya jura rashinta ba. 

  Ka kwantar da zuciyanka wata ra'ayin tace dashi dan kawai be k'ariso kun gaisa ba doesn't mean yana gaba da kai ne ko wani abun ze iya yuwu wa meeting d'in zasa dagaske. Hakan ne ya d'an kwantar masa da hankali amma fa still hankalinsa be bar tashi. 


  "Tashi muje kici abinci toh, you're hungry aren't you?" Kai ta gyad'a masa "Maamah fah?"


  "She'll catch up with us mu tafi" ba gardama ta mik'e ta bisa a baya sede tun da ta shiga motar har suka isa restaurant d'in Amal shiru take a motar gabad'aya hankalinta ya duk'ufa akan Afzal. Duk yadda yaso 6oye haushi da kishin daya tokaresa yau da ya ga Ya Abdul abin ya gagara har seda Amal ta d'an gano wani abun don haka ta fara kawo tunanin abinda Falmata ta ta6a fad'a mata sede kuma gabad'aya abun be yi making sense mata ba. Taya wai Yaya ze fara sonta ne? Maybe kawai ya damu ne kar Ya Abdul ya d'aukar mata da hankali daga kan karatu. Amma kuma meyasa jikinsa yayi sanyi yau tun ganin Ya Abdul da yayi? 

   Haka har Ya Abdul yayi parking motar ya fito ya bud'e mata k'ofar Amal bata ma san yayi hakan ba. 


  "Baby?" Ya kirata a firgice ta d'ago kai "Sorry" wur-wur tayi ta fito suka k'arisa ciki. Bayan orders nasu sun iso Ya Abdul ya shiga ci Amal kam se ido. 


  "Tunaninshi kikeyi?" Ya tambayeta a hankali yana mey tsamota daga duniyan tunanin data fad'a. 


  "I'm sorry" ta furta tare da d'ago spoon nata. 


  "Fad'amun Amal mey tsakaninki da wannan Yayan naki?"


  "Wallahi Ya Abdul ba komai kar kayi tunanin wani abun" tayi saurin basa amsa. 


  "Taya bazanyi ba Amal bayan tun da ya ganmu tare kika rasa nutsuwar ki."


  "Ya Abdul wallahi ba haka bane kaima kasan kai kad'ai nakeso kai kuma zan aura kawai Yaya is a part of me ne, ya zama wani sashi a jikina wanda farin cikinsa matters to me alot bana son ganinsa a damuwa."


  "Kina ganin kuma kallon mu da yayi tare ya sanya sa a matsala?"


  "I fear so" ta amsa a hankali. 


  "Kina son shi kema?" Ido ta d'ago a razane tana kallonsa bata ta6a tsammanin irin wannan kalamu daga bakinsa ba. "Ya Abdul wani irin magana ne kuma haka?" Abinda bakinta ya iya ya furta kad'ai kenan yayinda mamaki ya gama mamaye mata zuciya. 


  "It's a question Amal answer me do you love him too?"


  "Ya Abdul gaskiya banji dad'in wannan kalamu daga bakinka ba, bayan kasan kai kad'ai nakeso kuma kace ko ina son Yaya? I told you ni ba komai tsakani na da Yaya ko shi Yayan ne ya sameka yace maka yana so na da har zaka tambayeni ko nima ina sonsa? I'm very upset with you right now."


  "I'm sorry I'm just curious, yadda yake kallona d'azu was more of na sace masa sanyin idanunsa da farin cikin rayuwansa, naga soyayyar ki a cikin idonsa Amal don't blame me." Ran Amal in yayi dubu be 6aci ba, abubuwanta ta shiga tattarawa taya akan kowa Ya Abdul ze ce mata ko tana son Yaya? Ai wannan ma iskanci ne. "Ina kuma zakije?" Yayi saurin tambayarta. 


  "Anywhere better than here" ta fad'a cike da 6acin rai. Hijabinta yayi saurin rik'ewa "I'm sorry I take whatever I've said back kiyi hak'uri kinji?"


  "Na rasa appetite d'ina ni zan tafi gida."


  "Shine nace kiyi hak'uri, yi hak'uri ki zauna kinji? I'm sorry" hak'uri yayi ta bata da k'yar ya samu ta koma ta zaunan chan bada dad'ewa ba sega Maamah ta shigo d'adi sosai Ya Abdul yaji inda yayi mata fillanci (yaransu) kan ta bawa Amal hak'uri ze koma office. Ko da yake yi mata sallama ma tak'i amsawa sam bata ji dad'in maganan da yayi mata ba. 


  "Meya faru ne Amal?" Maamah ta tambaya bayan ficewan Ya Abdul. "Ya na ganki haka?"


  "Meya ce miki da yaren naku? Gulma ta kukayi ko?"


  "Taya kuma gulmar ki? Wallahi hak'uri zalla yace in baki."


  "K'arya kike na sanki da Ya Abdul nakin ai."


  "Wallahi hak'uri ce zallah, tell me mey ya had'aku?"


  "Yayanki ne mana" se kuma tayi shiru. 


  "Yayi mey?" 


  "Taya ze kalleni yace mun wai ko ina son Yaya ne bayan yasan sarai shi nakeso."


  "Ayyah Amal kiyi hak'uri shi ba da wata manufa ya fad'a hakan ba gani yayi kaman shi Yayan naki na sonki ne."


  "Aww kema abinda zakice kenan? Wai yaushe ne dukanku zaku gane cewa Yaya ba so na yake ba he's just being overly protective of me a matsayina na k'anwarsa, yanzu ko ke Ya Abdul ya ganki da wani baze had'a mishi rai bane?" Cikin 6acin rai take maganan hakan yasa Maamah ta soma bata hak'uri. 


  "Tabbas ze ji haushi Amal amma kuma" se kuma tayi shiru sakamakon mumunar kallon da Amal ke watsa mata. 


  "Amma kuma mey?" Ta tambayeta a fusace. 


  "Amma bakiga kallon da Yayanki yayi wa Ya Abdul ba wallahi dole Ya Abdul yaji wani iri a matsayinsa na wanda yake sonki Amal."


  "Wani irin kallo yayi masa?"

  

  "Wannan ma a gefe a tunaninki haka ne kawai Yayan naki yak'i k'arisowa su gaisa da Ya Abdul? I'm sorry to say amma Amal komin ya kika musanta Yayan nan naki sonki yake ni yanzu ba abinda yafi damuna kaman Ya Abdul, wallahi shi nake tausayawa bana son ki tafi ki barsa Amal."


  "Shaidan da zaki yimun kenan Maamah a matsayinki na very close friend d'ina? So kike kice duk soyayyan da nake yi wa Yayanki na k'arya ne kenan? Wow!" Ta numfasa "I'm totally speechless dake da Yayan naki duk haushin ku nakeji yau" tana kaiwa nan ta fishe jakanta ta fice, da wuri Maamah tabi bayanta tana k'wala mata kira amma ina tak'i koda juyawa. Keke ta tsara ta wuce park daga chan ta tsari na gida. Akan gadon d'akinta ta fad'a yayinda ta shiga yin kuka. Haka kawai taji komi ya dak'ule mata kuma kuka ne kawai solution, wayanta dake ringing ta zaro daga jakarta dubawan da zatayi taga Ya Abdul ke kira dan haushi ma hanging tayi gabad'aya be dad'e ba se gashi yana sake kira nan ma kashewan ta kuma yi se a karo na biyar ta d'aga. Hak'uri ya shiga bata amman tak'i hak'uran seda yayi dagaske har kaman zeyi mata kuka a wayan sannan ya samu ya shawo kanta, yazo ma tace ita kar yazo she wants to be alone da haka sukayi sallama akan ze kirata anjima. 


***

   Ta fannin Afzal kuwa ikon Allah kad'ai ya kaisa gida sabida tuk'in gangancin da ya rink'ayi a hanya. Gabad'aya ji yayi rayuwarsa bata da wata ma'ana ashe haka kullum shi Abdul d'in yake kaiwa Amal ziyara makaranta? Time d'in da ya kamata shida Amal su sake shak'uwa da junansu Abdul ke amfani da ita yana matsowa kusa da zuciyar Amal? Oh Allah! D'akinsa ya zarce ko ta kan Nazeefah dake yi masa sannu da zuwa beyi ba yana isa ya fa'a kan gadonsa had'e da rik'e dai-dai saitin zuciyansa inda keyi masa k'una sosai. A d'akin ya yini ranan, k'arshe sallah ma a zaune yazo ya k'arisa saboda wani irin zazza6in daya rufesa lokaci guda. Wajajen goman dare Amal ta kira layinsa sede wayan yata ringing Afzal be d'aga ba, ko energy'n da ze mik'e ya d'au wayan daga wardrobe nasa ma bayi da shi kuma yana da tabbacin cewa Amal ce ke kira, ko mey zata fad'a masa? Haka tayita kiran nasa har ta gaji ta hak'ura. Washegari ko office Afzal ya kasa fita saboda tsananin da jikinsa yayi. 


   Chan Azahar Nazeefah taji shirun yayi yawa don haka tayi tunanin gwada lek'asa kode lafiya dan ko breakfast be fito yayi ba. K'ofan nasa ta gwada turewa taji a rufe da key, knocking tayita yi amman ba response. Bata 6ata lokaci ba ta zagaya ta window inda ta tarar da sumemmiyar jikin Afzal a kan sallaya. Wani irin d'ankaren ihu tasa tuni me gadi yayi kanta yana tambayarta ko lafiya. Tsabagen yadda ta tsure ta kuma rikice ko magana ta kasa banda nuni da takeyi masa da cikin d'akin da yatsa. A guje suka yo ciki ya shiga k'ok'arin 6alla k'ofar sede ina security door ce hakan seya gagara daga k'arshe welder aka kira yazo ya cire lock d'in gabad'aya, da haka ne aka samu akayi waje da Afzal. Nazeefah se kuka, ko kiran Ummi ta kasa. 


  Suna isa asibitin akayi emergency room da Afzal yayin da aka bawa Nazeefah wasu papers tayi signing da k'yar ta iya tayi signing d'in se anan ta shiga neman wayarta ashe ko fitowa da ita ma batayi ba. Takalman k'afaya ya duba taga ashe sawu d'aya ma na Afzal tasa. Wayan wata nurse ta ara agun ta zuba layin Mummy sannan ta kira. A karo na farko Mummy ta d'aga. 


  "Mummy" ta kirata cike da tashin hankali. 


  "Nazeefah?" Mummy ta tambaya. 


  "Mummy kizo kizo da sauri dan Allah" tayi maganan tana kuka. 


  "Meya faru? Kina ina?"


  "Afzal."


  "Meya samesa?" Ta tambaya take. 


  "Mummy kizo kawai muna TH shi kad'ansa ya sume wallahi bani bace ni ban yi mishi komi ba wallahi."


  "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" Mummy ta furta cike da tashin hankali "Shikenan ina zuwa" tana sauk'e wayan ta cigaba da salati yau Nazeefah ta gama da ita shikenan ta kashe wa mutane d'a yau ina zata sa kanta? Hasbunallahi wa ni'imal wakeel. Hannunta na kakkarwa  ta nemi lamban Ummi ta shiga kira bada dad'ewa ba sega Ummi ta d'auka. 


  "Halo In law?" Fad'in Ummi. 


  "Hajiya Mariam."


  "Na'am Hajiya Fatsuma ya kike?"


  "Hajiya Mariam ki shirya ki taho TH yanzun ba lafiya."


  "Subhanallahi waye ba lafiya? Bade autan mu ba?"


  "Afzal ne kiyi sauri."


  "Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un!" Ummi ta furta yayinda zuciyarta ta tsinke "Afzal?! Afzal d'ina?? Meya samesa?"


  "Wallahi nima ban sani ba yanzun Nazeefah ke sanar dani kiyi sauri kekam." Take Ummi ta ajiye wayan ta janyo hijabinta da hanzari tayi waje tana k'walla wa driver kira. Kusan a tare ita da Mummy suka isa asibitin suka nufi emergency ward inda suka tarar da Nazeefah zaune kan benci ta had'a tagumi se aikin kuka take. Da hanzari suka nufi kanta suna tambayarta ina Afzal d'in. Wani sabon kukan tasa musu a wajen tare da hugging Mummy, d'agata Mummy tayi take daga jikinta had'e da kifa mata wata zazzafan mari. Tunda Nazeefah tasan kanta ba a ta6a marinta a fuska ba se yau. Rikicaccen ihu tasa yayinda Ummi tayi sauri ta shiga tsakaninsu. 


  "Haba Hajiya Fatsuma! Meyayi zafi haka?"


  "Kin kyauta min kenan Nazeefah? Da abinda zaki sak'a min kenan? Ai kin huta yanzu da kika tura shi har gadon asibiti burin ki ya cika."


  "Mummy wallahi ni ban yi mishi komai ba Ummi wallahi bani ce sanadin halin da Afzal ke ciki ba, dan Allah ki yarda da ni wallahi a sume na tarar da shi a d'akinsa" ta jero amsa tana kuka sosai. 


  "K'arya kike! Nace k'arya kike" Mummy ta k'aryatata tana me sake k'ok'arin kai mata wani marin yayinda Ummi ta tareta. 


  "Ya isa haka please ya isa mu jira muji fitowan likitocin" da haka ne su uku suka koma suka zauna kan benchin d'azu. Nazeefah bata bar kuka ba har yanzu sede abinda ya k'aru ba wanda yayi ta kanta kuwa as duk tunanin wani hali Afzal ke ciki suke barin ma Ummi dake jin tana iya rasa ranta idan Afzal ya rasa nata. Chan red globe na d'akin ya mutu yayinda k'ofan ya bud'u revealing a doctor with two nurses behind him. A gigice su Ummi sukayi kansa suna masu jero masa tambayoyi, da k'yar ya samu sukayi shiru sannan yayi gyaran murya. 


  "Ko wacece mahaifiyarsa a cikinku?"


  "Dukan mune" Mummy ta amsa. Kallo yayi mata na d'an lokaci sannan ya gyad'a kai "Wannan kuma fa?" Yayi nuni da Nazeefah. 


  "Matarsa ce" Ummi ta amsa "Please Dr ka fad'a mun ya condition na d'an nawa yake."


  "Hajiya bazan 6oye miki ba amman condition na d'anki ba kyau, rayuwansa yana cikin matsala."


  "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" dukansu uku suka furta a tare yayinda Ummi ta shiga nanata hasbunallahu wa ni'imal wakil gabad'aya hanjalinta ya fita yabar jikinta. 


  "Dr meya samesa?" Mummy da tayi k'arfin hali ta tambaya. 


  "D'anki ya kamu da ciwon zuciya, base on gwajin da muka d'auka sakamako ya nuna cewa ya samu heart attack ne dalilin sumewanda yayi kenan."


  "Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un" suka kuma furtawa yayinda idanun Ummi suka kad'a sukayi ja nan take. "Heart attack? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" A raunane ta juyo tana kallon Nazeefah.  

   

  "Nazeefah mey kikayi wa Afzal? Me kikayi wa d'a na? Mey kika masa?" Take ta rushe da kuka. 




RANA D'AYA

#RD


Love... King Miemiebee👄✨

[13/08, 00:44] ‪+234 907 483 8352‬: 🎀🎀🎀                 🎀🎀🎀

                🎀❣🎀

                   ❣❣


  💦💦                      🍃🍃🍃          

           *RANA D'AYA!*

  💦💦                      🍃🍃🍃

  June, 2018

 beeenovels.blogspot.com


     _Written by Miemiebee👄_



   *PAGE 1⃣6⃣*




   Rawa bakinta yake tana kakkarwa tace, "Ummi wallahi ban yi mishi komai ba wallahi bani bace."


  "Da Allah rufa mana baki!" Mummy ta katse ta. "A jinki bama sane ne da kalan rashin hankalin da kikeyi masa a gidan? Tun yaushe yaron nan yake hak'uri dake? Gashi nan k'arshenta kin sanya masa ciwon zuciya amma karki damu komi yazo k'arshe Allah tada kafad'an shi ya rubata miki takardan sakinki ki huta shima ya huta kowa ma ya huta."


  "Mummy dan Allah kar kiyi mun haka wallahi inason Afzal kuma wallahi ni ba ni bace sanadin wannan rashin lafiyan nasa Ummi you've got to believe me" ta juyo tana kallon Ummi a raunane "Ku tambayi D'anladi me gadi wallahi ahaka muka tsince sa a d'akinsa dan Allah ku yarda dani" sede ba wanda yako kalleta a cikinsu ita kanta Ummi kuka takeyi. Mummy ko ta had'a tagumi tana tunanin yadda zata fara sanar da Daddy wannan labari me d'aci. 


  "Dr dan Allah kuyi duk abinda ya kamata ku tabbata d'ana ya rayu shi kad'ai gareni bazan iya rasa saba dan Allah kuyi mun rai."


  "Karki damu Hajiya we'll keep him under an intensive care da ikon Allah ze samu sauk'i sede ku sanya sa a addu'a abu da zuciya ba guarantee, Allah de ya bashi lafiya."


  "Ameen amma Dr dakata dan Allah, shin baku gano ko mey ya jawo masa wannan ciwo ba?"


  "Tukuna muna kan jiran sauran sakamakon su fito amma ina da tabbacin cewa tunani ne yayi masa yawa dake BP nasa ma ya hau, tabbas akwai abinda yake damunsa na tsawon lokaci wanda ya rik'e a ransa yake kuma bi da zuciya."


  "Ai na fad'a" Mummy tasa baki "Bin duk kalan halayya da rashin hankalin da fand'ararriyar 'yarnan keyi masa ya jawo mai wannan ciwon zuciyan. Kinyi asara wallahi Nazeefah kinyi asara." Banda kuka ba abinda Nazeefah ke iya yi, k'iri-k'iri tasan ba ita bace da laifi amma ake blaming nata ya zatayi idan wannan labari ya iske Daddy? Wayyo nata ya k'are. 


  "Nagode Dr zan iya shiga ganinsa?"


  "Sosai ma kuwa excuse me." Yana ficewa Ummi ta shige d'akin Afzal a karo na farko da idanunta suka sauk'a akansa ba se hawaye ba, kuka ta shiga yi na sosai da k'yar k'afafunta suka iya takata izuwa gefen gadon nasa. Hannu ta aza akan oxygen supply da aka sanya masa sannan ta koma gashin kansa tana shafawa a hankali yayinda take zubda hawaye sosai. 


  "Afzal Ummi ce" ta furta yayinda kuka yaci k'arfinta. "Afzal Baba na Allah tada kafad'anka in shaa Allahu zaka samu sauk'i sede na rasa dalilin da zaisa kana da uwa a raye amman ka gwammaci ka rik'e damuwanka wa kanka kai kad'ai. Meyasa Prince? Idan Nazeefar ce bakaso a yau ka sanar da Abbanka wallahi mey hana raba auren nan se Allah why do you have to do this to yourself?" Rungumosa tayi tana kuka na hak'ik'a se chan ta iya ta fito daga d'akin ta nufi inda Mummy ke zaune itama ta zauna. Nazeefah dake tsaye daga gefe ne ta k'araso ta durk'usa gabanta. 


  "Ummi dan Allah kiyi hak'uri kibar kukan nan haka."


  "Mey kika ma Afzal Nazeefah? Na d'au da kikazo kika sanar dani halin da kuke ciki zaki canza al'amuranki ne ku soma zaman lafiya a gidan meya faru?"


  "Ummi wallahi bani bace, duk abinda nasan ze 6ata wa Afzal rai ina k'ok'arin dainawa, wallahi ba nice sanadin rashin lafiyarsan nan ba. A sume haka muka samesa a d'akinsa da D'anladi daman tun jiya daya dawo gida ya rufe kansa a d'aki ban kuma jin motsinsa ba you have to believe me."


  "Hmmm I wish I could Nazeefah" amsan da Ummi kad'ai ta bata kenan sannan ta kau da kanta. Gun Mummy takeso ta nufa amman bata shirya shan wata marin ba dan haka ta tattara kanta taja gefe. Satan idonsu tayi sid'ak-sid'ak ta shige d'akin Afzal d'in. A hankali ta k'arisa gefen gadonsa ta tsuguna yayinda take zubda hawaye sosai. Hannunta dake kakkarwa ta d'aga ta sauk'e akan fuskarsa tana shafawa a hankali yayinda wani irin so da tausayinsa yake sake shiga zuciyarta. 


  "Afzal?" Ta kirasa a raunene tana shafa gashin kansa. 


  "Afzal wai nice sanadin rashin lafiyarka? Wai nice na janyo maka wannan ciwon? Dan Allah ka farfad'o ka fad'a musu ba ni bace. Afzal suna shirin rabani da kai, Afzal bazan iya rayuwa ba kai ba dan Allah ka tashi ka musu bayanin komai Afzal I love you, I love you so much and I'm not willing to let you go, I'm here, I'll always be by your side dan Allah kar ka bani kunya ka tashi." Kanta ta sauk'e akan k'irjinsa a hankali tana me cigaba da kukan tsuma zuciya. Ta dad'e a hakan badan tana so ba ta tashi ta fice se don kar azo a kamata. 

   

   Abba dake Morocco Ummi ta kira ta sanar dashi halin da ake ciki. A karo na farko kan ma yak'i amincewa don yadda kansa ya d'aure. Ciwon zuciya de? A dalilin mey? A iya zamansa da Afzal be ta6a sanin Afzal nada zurfin ciki ba toh meya faru? Kode zancen Ummi gaskiya ne, Nazeefah ce ke k'untata masa shiko yake bi a rai har abun ya kai ga haka? Aiko ya zama dole a d'au mataki dan akan zumunci baze rasa ran d'ansa guda ba. Ba shiri ya shiga booking flight of return. 


  Wajajen k'arfe takwas na dare likita ya dawo ya duba Afzal sede har yanzu ba cigaban da aka samu hak'uri ya basu kan su bari zuwa gobe. Ummi kam ba aikinta se kuka, har da Daddy yazo dubata ya tafi bata bar kukan ba. Ran Daddy ya matuk'ar 6aci, ya sani duk hakan na faruwa ne saboda laifin daya ta6a aikatawa, alhak'inta ne ke binsa shiyasa Allah ya basa 'ya gagararriya kamar Nazeefah. Oh Allah! Ko kallon Nazeefah da ke ta faman rantsuwa beyi ba ya fice. Sauk'a har k'asa tayi gun tana kuka me tsuma zuciya. 


  Wajajen k'arfe goma Mummy tace zata tafi, Ummi na jiran tafiyan Nazeefah amma shiru koda ta tambayeta se yaushe zata tafi kuwa tace mata ita anan zata kwana sede Ummi ta hanata bata son ko cikin dare idan Afzal d'in ya tashi ganin Nazeefah akansa kuma hakan ya sake haifar masa da wata rashin lafiyar dan su duk sun gama yarda cewa Nazeefah ce sanadin komai. Haka badon tana so ba aka sa driver ya dawo da ita gida, ko abinci ta kasa ci sallah kawai tayi ta kishingid'a jikin sallaya tana kuka har bacci yayi awon gaba da ita. 


  Washegari Mummy ta shirya breakfast ta kai wa Ummi haka Nazeefah ma, sede har izuwa wannan lokaci Afzal be farfad'o ba basu Ummi kad'ai ba harta shi kansa likitan ma jikinsa yayi sanyi har ya soma tunanin ko Afzal d'in ya shiga state of comma ne. Sultan da se a yau labari ke iskesa ne ya shirya ya taho. Ko daga jin batun yasan ba komai bane ze jawo wa abokin nasa ciwon zuciya banda tunanin Amal. Sosai ya tausayawa Afzal da yaga irin critical condition da yake ciki yayinda yake jin haushinsa kuma, ai dama seda ya fad'a masa ba inda zurfin ciki ze kaisa banda halak'a amman yak'i ji. Yana zaune a d'akin ne shida Ummi da Mummy Nazeefah tayi sallama zata shiga don ajiye masu basket na abincin ranan data dafa. 


  "Ban ce miki kar na sake ganin kin tako k'afar ki cikin d'akin nan ba? Duk abinda kikayi masa be isheki ba nan d'in ma sekin biyosa kin k'arasa sa?" Mummy ta kurarata. Magana ma ta kasa kawai maida k'ofan tayi ta fice ta nemi gu ta zauna ta shiga kuka, shin yaushe ne zasu amince akan cewa ba ita bace sanadin wannan rashin lafiya?


  Sultan da kansa ya d'aure ne ya juyo yana kallon Mummy da tayi maganan "Aunty me kuma had'in Nazeefah da condition na Afzal? Bade ita kuke zargi ba?"


  "Da wa kakeso a zarga idan ba ita ba Sultan? Abokin naka be ta6a baka labarin kalan zaman da sukayi da ita a gidan bane?" Ta tambayesa. 


  "Sure yana bani kawai de I don't think itace ta janyo masa wannan ciwo besides ai zatto ma zunubi ne kamata yayi ku jira ya farfad'o ya sanar daku da bakinsa kafin ku hau tsagwamanta haka."


  "Ko wa kakeso mu zarga? Idan ba Nazeefah ba to waye ne? Dan Allah ka sanar dani idan ma mutanen office ne I am ready to deal with them tell me Sultan" cewar Ummi. 


  "Ba mutanen office bane."


  "Then waye ne?"


  "Nima bansani ba amma kam ba Nazeefah bace."


  "Allah farfad'o da Afzal d'in koma wanene ze sanar dani" cewar Ummi had'e da cigaba da shafa gashin kansa. Sallama yayi musu akan yana zuwa ze dawo anjima. Yana fita ya kira numban Amal wanda ta d'auka bada dad'ewa ba. 


  "Assalamu alaikum."


"Wa'alaikumus salam" ya amsa. 


  "Ya sultan ina yini?"


  "Lafiya ya kike? Kina gida?"


  "Eh lafiya?"


 "Ki jirani ina zuwa" batayi musu ba tace "Allah kawo ka" ta sauk'e wayan. Anya kuwa lafiya? Yau Ya Sultan ne bashida fara'a haka ko kad'an?? Numban Afzal data gaji da kira ne ta sake gwadawa sede kaman yadda take tsammani haka ya gama ringing be d'aga ba toh meke faruwa ne? In minutes like 30 sega Sultan ya iso k'ofan gidansu. Fitowa yayi ya mata waya kan gashi bata 6ata lokaci ba ta sanya hijabinta ta fito. 


  "Ya Sultan yau kaine a gidan namu?"


 "Eh Amal dalili ya kawo ni" ya sanar da ita straight forward. 


  "Toh ina jinka."


  "Kin ko san Afzal ba shida lafiya yanzu haka as we speak? Yana kwance a gadon asibiti rai na a hannun Allah."


  "Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un" tasa salati yayinda ta nemi duk wani nutsuwarta ta rasa. "Ka ce mey????" Ta tambaya bayan tsawon lokacin data d'auka. 


  "Afzal na gadon asibiti haka as we speak fighting for his life" ya sake nanata mata. Take idanunta suka ciko da hawaye ashe dalilin daya sa ko ta kira baya d'agawa kenan toh meya samesa? Meya samu yayanta? Innalillahi!


  "Ya Sultan dan Allah ka fad'a min wasa kake hatsari yayi ne? Meya samesa?"


  "Wasa kuma Amal? Ana wasa da rashin lafiya ne? Ko baki gwada layinsa bane tun jiya?"


  "Wallahi kona gwada baya d'agawa se nayi tunanin ko yayi fushi dani ne."


  "Mey ya had'aku? Fad'a kukayi ne?"


  "Ya Sultan ni ba wannan ba meya samu Yaya? Hatsari yayi ne?"


  "Ko d'aya yasamu heart attack ne."


  "Ciwon zuciya??" Ta nanata had'e da zaro idanunta waje. "Me ya had'a Yaya da ciwon zuciya Ya Sultan dan Allah kace wasa kake."


  "Ba wannan a tsakanin mu Amal and bazan 6oye miki ba kece nan sanadin wannan rashin lafiya nasa."


  "Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un ni kuma Ya Sultan? Dan mey zaka ce nice sanadin rashin lafiyan Yaya bayan kasan nafi kowa damuwa da lafiyarsa da kuma farin cikinsa, dan Allah ka rufa mun asiri" kuka ta shiga yi sosai. 


  "Na k'aryata hakan Amal so kike kice har yanzu baki fahimce komai ba?"


  "Komai game da me fa?" 


  "Taya zakice har yanzun baki gane cewa Afzal na son ki ba? Tayaya Amal?" Wani irin sara kanta yayi mata yayinda jiri ya d'ibeta daba don Sultan da yayi saurin tareta ba da tuni ta sha k'asa, k'aryata zancensa ta shiga yi tana kad'a kai yayinda take kuka na hak'ik'a. 


  "Ya Sultan baka gane bane, baka gane ba Yaya ba sona yake ba. Yaya baze ta6a sona da wata manufan ba, dan Allah kabar fad'in haka."


  "Dalili? Kibani k'wak'k'warar dalilin da ze hana Afzal sonki Amal, kin d'au duk hidimar nan da yake miki a banza ce? Ko mey yakeyi muddin ke kika kira bari yake and be at your service you think it shall go in vein just like that?"


  "No amma kuma idan har dagaske ne Yaya yana sona da ya sanar dani idan beyi hakan ba kuwa ko Papi ne ze samu ya fad'a mishi baku gane bane Yaya ba sona yake ba."


  "Sosai yana da niyyan yin hakan sede baya son ya raba miki hankali ne daga karatu Amal, so yake se idan lokacin yayi ya sanar dake kwatsam se gashi kin samu wani har kun daidaita taya kike tsammanin zeji? Taya ciwon zuciya baze kama shi ba?"


  Salati kawai Amal ke ta nanatawa bayan nan ta kasa furta koda uffan. Meyasa bata gane cewa sonta Yaya yake ba?

  

  "Nide na fad'a miki kuma ina sa ran zaki d'au mataki ki ceto mana ran Afzal ke kad'ai keda ikon hakan."


   Taya ya Ya Sultan? Ta tambayesa cikin kuka sosai "Ya za'ayi nayi hakan? So kake in je in samesa a matsayina na mace in ce masa ina sonsa bayan banji daga bakinsa shi yana sona ba?"


    "I've said my own amman duk abinda ya samu abokina bazan yafe miki ba."


  "Ya Sultan ya kake magana haka? So kake in haukace in rasa raina? Kafi kowa sanin yadda farin cikin Yaya yake da matuk'ar muhimmancin a rayuwata. I'm willing to sacrifice everything for Yaya amma Ya Abdul fah? Meyasa Yaya be sanar dani tun wuri ba har ya bari soyayyan wani ya shiga zuciyana?"


  "Ban sani ba nima Amal, Afzal nada wani irin hali ko abu na damunsa bai son nunawa ko ni nan da nake miki wannan magana bawai shi Afzal d'in ya sameni ya fad'a min hakan bane, ni na karance sa har na gano hakan. Afzal na sonki Amal, idan har da zakiyi adalci kuma kema kin sani ba wanda ya kamanci soyayyar ki kaman shi. Rai ne kawai Afzal be d'auka ya baki ba, is about time kiyi repaying all the kind gestures da ya miki, nasan da ciwo amma ya zama dole ki rabu da Abdul naki kibawa Afzal soyayyar ki it is the only thing that can save his life." Shiru tayi tana share hawayenta, "Shin bazan iya zuwa in duba sa ba? I want to see him, I want to see him so badly."


  "Hakan zeyi wuya amma zanyi iya k'ok'ari na inga kin samu ganinsa."


  "Are you free yanzu? Zaka iya kaini?"


  "Sure let's go." Asibitin suka koma inda ya barota acikin mota ya fito ya samu Ummi yake ce mata taje gida ta huta ze cigaba da kula da Afzal zuwa lokacinda zata dawo bata masa musu ba ta kira driver ya kaita gida. Dama ba Nazeefah ba Mummy don haka ya shigo da Amal ya tsaya daga bakin k'ofa yana guarding nasu. Rawa jikinta yake sosai yayinda ta k'arasa cikin d'akin nasa ta zauna kan kujerar dake gefen gadon nasa. Wani irin mumunar tausayinsa ne ya kamata, ina ma ace zata iya kar6e rashin lafiyan nasa ita tasha wahala a maimakonsa. Sam wannan rashin lafiya be kamace sa ba, "Yaya?" Ta kira sunansa a hankali. 


  "Yaya dagaske ne? Dan Allah ka tashi kace musu k'arya ne. Yaya in har abinda suke fad'a gaskiya ne meyasa baka sanar dani ba? Yaya kafi sanin kowa yadda nake sonka, I'll sacrifice everything for your happiness mesa baka sanar dani da jimawa cewa wannan ne k'udurinka akaina ba har kabari na shigo da Ya Abdul cikin rayuwata? Kana tunanin da kaina zan gano hakan ne? Tabbas yaci ace na gane hakan amma banyi ba, I'm so sorry for every pain Yaya please forgive your Lily" tasa k'asan hijabinta tana share hawayenta. Tafi minti biyar zaune a gun tana aikin kuka akansa kawai taga alaman yayi blinking idonsa. 


  "Ya Sultan!" Ta k'wala masa kira ba shiri ya shigo ciki yana tambayarta ko lafiya. "Yaya ne yayi motsi get his doctor" a guje ya fice dan nemo likitan. "Yaya please open your eyes it's me your Lily, I'm right here kaji? You can do this" kalamun kwantar da hankali tayita furta masa a hanakli ya shiga bud'e idon nasa har ya bud'esu duka had'e da sauk'esu akanta. 


  "Yaya you're alive! You're alive" tasa ihu tana share hawayen farin cikin dake sauk'o mata. Kallonta kawai yake amman ya kasa cewa komi ahaka ne har Sultan ya dawo da Dr'n Afzal inda ya masa wasu gwajin ya tabbatar da cewa condition nasa is stable sannan ya fice. 


   "Yaya baka gane ni bane? It's me your Lily." Maida kallonsa akan Sultan yayi idonsa suna d'auke da d'imbun tambayoyi gano hakan Sultan yayi saurin cewa "bari in kira Ummi ina zuwa" nan ya fice ya barsu su biyu a d'akin. 


  "Yaya?" Ta kirasa sede ina yak'i koda juyawa ya kalleta. "Yaya I'm sorry, I'm so sorry dan Allah ka juyo ka kalleni" nan ma shiru. "Yaya I'm so sorry dan Allah ka dena fushi dani kayi hak'uri" sede fa duk had'asa da Allahn da tayita yi yak'i koda kallonta. Haka ba yadda ta iya ta mik'e tabar masa d'akin. 


  "Ya haka?" Sultan daya ga yadda take kuka yayi saurin tambaya. 


  "Yaya yak'i ya kalleni balle ma yamin magana, Ya Sultan ban san ya zanyi ba dan Allah ka basa hak'uri."


  "Yak'i ya miki magana kaman ya?"


  "I told you Yaya ba sona yake ba kune baku gane ba, I can't do this anymore ni zan tafi kawai."


  "Ah'ah ki tsaya tukuna" d'akin Afzal ya shiga ya zauna gefensa. 


  "Ya jikin naka?" Ya tambayesa. 


 "Meyasa ka kawo ta nan? Ina su Ummi?" Abinda ya soma cewa kenan. 


  "Abinda kad'ai zaka iya cewa kenan?Ka lek'a lahira ma bazaka zubar da wannan halin naka bako?"


  "Ba abinda na tambaya ba kenan ina Ummi? So kake su ganta? Mesa kake abu baka tunani ne kam Sultan? So kake se sun ganta sunyi zargin wani abun?"


  "Ai ko basuyi zargeta bama ni zan sanar dasu komai."


  "Komai kaman ya?"

  

 "A tunaninka baki na zeyi shiru ne? Na riga na sanar da Amal gaskiyan al'amarin cewa kana sonta sauran idan su Ummi sun iso suma in fad'a musu haka kawai ina ji ina gani bazaka cigaba da punishing Nazeefah ba bayan ita batayi komai ba."


  "Kayi meh kace?" Afzal ya tambayesa cike da tashin hankali yayinda zuciyansa ya tsinke da sauri ya rik'e wajen daya fara yi masa zafi. "Gara ka kwantar da hankalinka kabi komi a hankali dan idan wani attack d'in ya sake kamaka se lahira yanzu."


   "Amma me na fad'a maka? Ni na fad'a maka ba son Amal nake ba don mey zaka sameta kace mata ina sonta? What is the meaning of this Sultan?"


  "Aww har yanzu bazaka yi admitting son da kake yi wa yarinyar nan ba?"


  "Sultan just get out idan har kasan suratan banza zaka cigaba dayi ka tashi ka bar min d'aki."


  "Yanzu kai fisabilillahi baka tausayawa kanka da ita Nazeefah harda Amal d'inma? Wallahi girman kan nan ba inda ze kaika illa halaka Nazeefah bata san hawa ba bata san sauk'a ba aka d'aura mata laifin komai, Amal na da wanda takeso amman ya zama mata dole yanzu ta rabu dashi saboda kai duk hakan be isheka ba bazaka hak'ura ka amince da komai ba?"


  "Ni ban rok'eta tabar wanda take so ba Nazeefah kuwa ni bani na fad'awa su Ummi suyi blaming nata ba saboda haka nima kadena blaming d'ina."


  "Da kyau" yace dashi had'e da mik'ewa yabar masa d'akin kafin ya fita har Amal ta tafi nemanta ya shiga yi chan sega Nazeefah shigowa. 


  "Ina yini?" ta gaishesa. 


  "Lafiya Nazeefah ya hidima?"


  "Alhamdulillah wai Afzal ya farfad'o?"


  "Eh yana ciki kije ki samesa."


  "Toh ya naga kaman kana neman abu? Lafiya?"


  "Ko kinga wata yarinya da farin hijabi a hanya?"


  "Wata doguwa hakan nan?"


  "Eh ita."


  "Ina shigowa naga tana tsaran napep."


  "Toh shikenan thank you." Da haka ta wuce d'akin Afzal knocking tayi sannan ta shige. Basket na abincin ta ajiye akan table sannan ta k'arasa ta zauna a gefensa. 


  "Afzal ya jikin naka?"


  "Da sauk'i" ya amsa k'asa-k'asa. 


  "Thank you for staying alive, Allah k'ara maka lafiya."


  "Ameen thank you" ya amsa. 


  "In sa maka abinci?"


  "I'm not hungry."


  "Afzal kaman ya baka jin yunwa? Rabonka da abinci tun yaushe? Dan Allah kayi hak'uri in sa maka koda kad'an ne kaji?"


  "Nace bana jin yunwa" bata sauraresa ba ta d'iba ta d'au ruwa tazo ta zauna gefensa. "Tashi ka zauna kaji? Please don't say no."


  "Afzal magana fa nake maka dan Allah kayi hak'uri ka tashi" kaman wanda baze motsa ba ya shiga mik'ewa sede hakan ma ya gagara k'arshe seda ta taimaka masa. Abincin ta d'aga ta mik'a masa "Zaka iya ci ko in baka?" Beko kalleta ba ya amshe plate d'in bayan da ya k'are wa abincin kallo ya maido da kallonsa a gareta. 


  "Afzal lafiya?" Ta tambayesa saidai still kallonta yake. "Afzal tunanin ko wani abun na sa maka aciki kake? Dan mey zan cutar da kai? Wallahi ba komai aciki ina iya d'ibawa inci a gaban ka idan baka yarda dani ba" ganin ta mik'e yayi saurin cewa "Don't bother ki zauna" komowa tayi ta zauna yayin da ya shiga ci a hankali. 


  Murna kenan zan so kuga farin cikin daya bayyana a fuskan Nazeefah rabonta da tayi farin ciki irin na yau a rayuwarta har ta manta. Finally Afzal ya d'and'ana girkinta yau. Zama tayi tana kallonsa yayinda yake ci a hankali dududu beci ya kai rabi ba yace ya k'oshi. Ita a hakan ma ta gode. 


  "In had'a maka ruwa kayi alwala ko?" Nan ma kai zalla ya gyad'a mata bata kai da mik'ewa ba sega Ummi ta shigo. Da gudu tayi kansa had'e da rungumosa yayinda hawaye ya ciko mata a ido. 


  "Prince you're back! Alhamdulillah! Alhamdulillah!" A hankali ta sakesa ta shiga shafa fuskansa "Prince na d'au zaka tafi ka barni."


  "Come on Ummi, I'm here."


  "I missed you."


  "I missed you too bari inyi sallah."


  "Haka fa kafin nan kaci abinci? Barin aika driver yaje ya siya maka don miyan kuka akayi a gida."


  "Karki damu Nazeefah ta taho da abinci." Ita bata ma lura da presence na Nazeefah ba seda ya ambaci sunanta. 


  "Nazeefah?" Ta juyo da mamaki tana kallonta. 


  "Na'am Ummi?"


  "Prince?" Ta juya tana kallonsa shima. 


  "Yes?" Ya amsa. 


  "Kana lafiya? Ko a kira ma likitan ka?"


  "Why wani abu ne?"


  "Prince mun d'au ai idan kaga Nazeefah ciwon naka ze tashi ke Nazeefah ba ance ki kiyayi shigowa d'akin nasa ba kar wani abu ya samesa" Shiru Nazeefah tayi dan ko bata san me zata ce ba, tsana k'iri-k'iri both mahaifiyarta da surikarta suke nuna mata. Idanunta ta d'ago a raunane tana kallon Afzal tana jiran jin ko zeyi magana dan shi kad'ai yake da ikon wanketa daga wannan daud'a da su Ummi suke ganinta da. 


  "Meyasa?" Ya tambayi Ummi a k'arshe. 


  "Prince meye silar ciwon nan naka? Ba Nazeefah bace?"


  "Waya ce muku itace?"


  "Prince mey kake fad'i wai kam?" Ta tsaya kallonsa da mamaki. 


 "Nazeefah batayi komai ba I'll ask you to keep her away from this." Tirk'ashi wai meke faruwa ne? Ummi ta tambayi kanta "Kaje kayi alwalan zamuyi magana idan Abbanka ya iso munyi waya dashi d'azu jirginsu ya tashi." A nitse ya mik'e ya k'arisa bayin ya d'auro alwala kamin ya fito har Nazeefah ta shinfid'a masa sallaya. Sallolin daya rasa ya shiga ramawa. Ana cikin haka Mummy ta shigo itama suka gaisa bayan da ya idar d'in take sanar dashi abinda ke tafe da ita na cewa Daddy ya turota ne akan idan har ya ga baze iya ba da rashin hankalin Nazeefah ya sawwak'e mata kawai su koma gida yanzu tunda de tace ita bazatayi hankali ba. Kafin Afzal yayi magana Ummi ta rigasa. 


  "A'a shiko Alhaji ai ba haka akeyi ba, zama yakamata shi da Abban Afzal suyi da shi Afzal d'in kansa a dai-daita koma menene koba haka ba?"


  "Dan Allah kibar maganan nan Hajiya Mariam banason ganin ranan da za'ace ga 'yata nan ta kashe d'an wani kuma idan aka cigaba da tafiya haka tabbas wataran Nazeefah zata aikata hakan tunda gashi ta d'au hanya har ta sanya masa ciwon zuciya." Shiru Afzal da suke tsammanin zeyi magana yayi. "Afzal?" Ta kira sunansa yayinda da ya d'ago kai yana kallonta "Mey kace kai?"


   "Mummy ni Nazeefah bata yimun komai ba don haka bazan saketa ba kuma ina rok'anku da kudena blaming nata akan laifin da ba ita ta aikata ba" Wani irin sanyi Nazeefah ta jiyo a ranta bata tsamman Afzal ze kareta haka ba. 


  "Wani irin magana kake ne wai Prince? Idan ba Nazeefah ba toh waye?"


  "Ni ba wanda ya d'aura mun ciwo banda Allah, kuma na rungumi k'addara."


  "Ya kake neman raina mana hankali ne kam Prince? Dama ansan ai lafiya da rashinsa daga Allah ne ko ka ta6a jin jinin mutum ya hau ciwon zuciya ya kamasa ba tare da tashin hankali ba? Wallahi to kar kayi magana Abbanka na nan tafe idan yazo se muga ko wannan silly answers d'in zaka basa Hajiya Fatsuma tashi in raka ki Afzal is not willing to talk."


****

  Amal ce kwance akan katifarta se aikin kuka take, gabad'aya ta rasa meke mata dad'i tun dawowanta gida bata sake lek'a waje ba. Ba yadda Mami batayi da ita ba amman tak'i fad'a mata ainihin meke faruwa. Toh ma ta ina zata fara? Ta ina zata fara sanar da Ya Abdul wannan zance? Wayanta ta jawo ta shiga viewing pictures nasa da kuma nasu da suka d'auka tare, tana son shi tana son shi na sosai bata jin zata iya rabuwa dashi aman kuma ta d'ayan 6angaren bata son Sultan da shi kansa Afzal d'in da kuma duk wanda wannan labari ya iskesa suyi mata kallon butulu. Sedai har yanzu takasa amincewa da maganganun da Sultan ya sanar da ita, gashi abin haushi sun kasa dena yawo akanta. 



***

   Ba yadda Ummi batayi da Afzal ba akan cewa ya taho gida da ita amman yayi insisting yace shi fa Nazeefah ze bi. Haka nan suka komo gida tare ta tambayesa ko me yakeson ci. A karo na farko kam babu ya sanar da ita. Seda tayita had'a sa da Allah sannan yace indomie ma yayi. Ba tare da 6ata lokaci ba ta wuce kitchen ta shiga girka masa. Nan ya d'auko wayansa dake cikin wardrobe, gabad'aya gani yayi battery d'in yayi draining. Had'awa yayi bayan ya kawo wuta ya soma cin karo da sak'on Amal da sauri ya bud'e ya karanta kaman haka.  


  'Get well soon Yaya, my prayers are with you.'


  Duba lokacin da sak'on ya shigo yayi yaga wajajen k'arfe shida ta turo. Maida wayan yayi yayinda ya fad'a duniyan tunani. Yanzu da wannan shirmen da Sultan ya tafka masa da wani idon ze sake kallon Amal? 


  Washegari Abba ya turo driver akan ya taho da Afzal idan kuma jikin nasa baze iya barinsa ba shi da kansa yana iya tahowa su tattauna komai. Wanka yayi ya karya sannan suka fice. Suna is ya zarce parlourn Abba inda yaci karo da Sultan, take gabansa ya fad'i don mey za'a kira Sultan? Yana da tabbacin cewa aikin Ummi ne wannan. A nitse ya k'arisa d'akin ya zauna se kallon Sultan yake ko idonsu ze had'u yayi masa ido komin mey kar ya fad'i komai amman yadda kukasan gunki tun zaman Sultan ko kewaye-kewaye yak'i yi. Gaisawa sukayi da Abban yake tambayansa ya jiki sannan da Ummi bayan nan Abba yayi gyaran murya. 


  "Ina jinka Prince meya faru?"


  "Abba babu" ya amsa kansa a duke. 


  "Idan kun kasa jituwa da ita Nazeefan ne ai seka taho gida kamun bayani amfanin idan iyayenka suna raye kenan bawai ka tsaya kana bin abu a zuciya ba."


  "Abba ni Nazeefah bata yimun komai ba."


  "Sorry ban fahimce ka ba."


  "Nazeefah has nothing to do with this Abba" ya sake nanatawa Ummi dake gefensa ji tayi wane ta hankad'esa don haushi ita ta rasa dalilin da yasa yake rufa mata asiri. 


 "Toh wanene?"


  "Babu."


  "Nace wanene?" Abba ya sake tambayansa cikin tattausar murya. 


  "Abba matsala muka samu a office wanda nayita bi da zuciya shikenan."


  "Prince d'ago kai ka kalleni" ba gardama yayi hakan "Yanzu ni zaka kalli cikin idanu na kayi mun k'arya wallahi sam wannan ba d'abi'ar ka bace I'm very disappointed in you."


  "Abba kayi hak'uri."


  "Sultan?"


  "Na'am Abba" ya amsa. 


  "Tabbas nasan kana sane da duk wani abinda ke faruwa tunda Afzal ba shida amini sama da kai I'll ask you to tell me what is really going on idan ko kayi mun k'arya Allah na kallonka." Shiru Sultan yayi yana nazarin sanar da Abba gaskiyan batun ne koko a'a. Amma ai dan abokinsa besan ciwon kansa ba doesn't mean shima ya biye masa. 


  "Sultan magana nake maka."


  "Abba a gaskiya ni ban san mey zahirin maganan ba don ko ni nan Afzal be ajiye ni ya sanar dani abinda ke damunsa ba sede in baka amsa base on yadda na karanci yanayin sa."


  "Bismillah ina jinka."


  "Akwai wannan yarinyar da Afzal keyi ma hidima wanda da zama yayi zama na soma ganin alamun son yarinyar a tattare da shi koda na gwada masa magananta akan cewa is about time ya sanar da ita k'udirinsa kuwa se abin ya koma fad'a ransa ya 6aci. Toh kwatsam kawai se mukaji yarinyan ta samu wanin da har sun dai-daita dashi sunyi nisa. A tunani na wannan ne dalilin daya jefa Afzal cikin wannan hali dan tun daga lokacin ban sake gane kansa ba ko office nasu naje acikin tunani nake tsintansa kullum." Tunda Sultan ya soma bayanin Afzal ya dukar da kansa k'asa amman baze ta6a yafe masa wannan d'anyen aikin daya masa ba. 


  "Ko kasan yarinyar da kuma iyayenta?" Shiru Sultan yayi yana nazarin sanar dasu gaskiya koko a'a sarai ya sani idan yayi hakan Afzal na iya fushi dashi har abada don haka ya kad'a kai "Ban san komi akanta ba Abba banda hotunan ta da nake gani da a wayansa kafin ya goge."


  "Shikenan Sultan nagode Allah sak'a maka da alheri kana iya tafiya."


  "Ameen Abba, Ummi ni zan wuce."


  "Mungode sosai Sultan ka gaida gida" yana ficewa Ummi ta maido da kallonta akan Afzal "Ai dama na sani nasan za ayi haka kai baka san ciwon kanka bane kake neman kai kanka ga halaka akan mace iyye? Macen da kana da tabbacin zata amince da k'udirinka muddin idan ka sanar da ita amman kak'i har wani can ya sace maka ita? Meye amfanin mu Afzal da bazaka zo ka sanar damu damuwanka ba?" Shiru yayi bece komai ba. 


  "Afzal?" Abba ya kirasa. 


  "Na'am" ya amsa. 


  "Wacece wannan yarinya?"


  "Abba ni fa ba wata yarinya ni kaina ban san a ina Sultan ya had'o wannan labari ba ya baku kaman yadda na fad'a maka matsala muka samu a office na kusan rasa aiki na shine nabi a zuciya."


  "Nace wacece yarinyar?"


  "Abba I'm sorry amman kaman yadda na fad'a maka ba wata yarinya."


  "Afzal wai meke damunka ne? Kai bakasan zurfin ciki na kai mutum ga halaka ba?"


  "Ya isa Hajiya Mariam bar shi tashi ka tafi Allah k'ara ma lafiya."


  "Ameen nagode" yana kaiwa nan ya mik'e Ummi ce tabi bayansa tare da k'wala masa kira. 


  "Prince meke faruwa ne? Meya sameka? Prince idan baka sanar dani damuwanka ba mawa zakayi hakan? Wallahi koma wacece wannan yarinya da kakeso kasa zuciyanka a ruwan sanyi dan ka riga ka sameta just tell me wacece ka kuma bani address nata."


  "Ummi nagode amman ya kamata ki gane cewa ba wata yarinya."


"Da kyau Prince yau ka nuna min matsayina dake ba ni na tsuguna na haifeka ba dole ina tambayanka abu kana 6oye mun."


  "Ummi please wani irin magana kuma kike?"


  "No ka tafi nagode" nan ta juya ta shiga tafiya duk kiran da Afzal keyi mata tak'i juyawa har ta k'arasa site nata. 

  Tunanin had'uwansa da Sultan kawai yake a dalilin mey ze fad'awasu Abba gaskiyan al'amarin?




RANA D'AYA

#RD


 Love... King Miemiebee👄✨

[13/08, 00:40] ‪+234 907 483 8352‬: 🎀🎀🎀                 🎀🎀🎀

                🎀❣🎀

                   ❣❣


  💦💦                      🍃🍃🍃          

           *RANA D'AYA!*

  💦💦                      🍃🍃🍃

  June, 2018

 beeenovels.blogspot.com


     _Written by Miemiebee👄_



   *PAGE 1⃣7⃣*


  


     Yadda yak'i kiran Amal ita ma haka bata sake kiransa ba iyaka sak'on da ta sake masa sending take tambayarsa ya jiki Allah k'ara lafiya. Anan d'inma k'in replying yayi. Kan Ummi ya samu shawo bayan wuyan da ya sha dan sosai tayi fushi da shi amman dukda hakan yak'i sanar da ita batun Amal se musantawa yake sam fa shi ba wata yarinya. Bayan tafiyansa Ummi ta kira Sultan take rok'ansa cewa idan har ya san gidansu yarinyar nan karya 6ata lokaci ya fad'a mata kar ya biye wa abokin sa amman sanin abinda hakan ke iya haifar wa tsakaninsa da amininsa ya busar da ido yace wa Ummi shi sam be sani ba ai idan da ya sani ko basu tambaya ba ze sanar da su a haka ya samu sukayi sallama. 


  Abba kuwa be sake yi takan Afzal ba tunda kusan sau uku yana tambayansa abu d'aya amman yak'i sanar dashi idan tayi tsami shi da kansa ze bud'a bakinsa ba se an rok'esa ba. Sau dayawa Ummi na bawa Abba hak'uri akan ya sake kiran Afzal yayi masa magana k'ila ya amince ya fad'a musu damuwansa amman ina shifa Abba yace ba ruwansa again. 


    Kwana biyu Afzal ya d'auka sannan ya warware ya soma fita office, da safe Nazeefah ta tashi ta had'a mishi breakfast harda coffeen sa a flask da ze tafi da shi, yau kam har da godiya Afzal yayi mata sannan ya fice. Ba k'aramin dad'in hakan taji ba bayan tafiyansa itama ta shirya ta wuce school. A makaranta ne Ummi ta kirata bayan sun gaisa take bata hak'uri game da abinda tayi mata, sosai Nazeefah ta nuna mata komai ya riga ya wuce saboda ko itace a shoes na Ummi abinda zata aikata kenan kawai abinda bata ji dad'insa ba shine damar da ita da Mummy suka k'i bata tayi bayanin kanta. 


   Afzal ne zaune a office gabad'aya hankalinsa ya duk'ufa akan waya yana kallon hoton Amal Sultan yayi knocking bisa k'ofan, kafin yace ze kimtsa har shi Sultan d'in ya sa kai. Da wuri Afzal ya tura wayan nasa k'ark'ashin drawer sede Sultan ya riga ya gansa, kai kawai ya kad'a ya k'arisa ciki. Afzal kam ya sha mamakin ganin Sultan. Zama yayi akan kujera tare da mik'a wa Afzal hannu da ikon Allah Afzal ya kar6a suka gaisa. 


  "Ya jikin naka?" Ya tambayesa. 


  "Da sauk'i I'm fit."


  "Ma shaa Allah Amal ce ta turoni dama."


  "Da mey?" Yayi saurin tambaya. Ledan dake ajiye a gefen k'afansa ya d'ago tare da turawa Afzal ta 6angarensa "She's wishing you a speedy recovery." Amsa yayi ba musu ya sa a fridge bayan daya lek'a ciki yaga Aldeb ne kaca-kaca da zo60. "I'll call her up."


 "Alright ni zan wuce." Shiru Afzal yayi masa har ya kai ga bakin k'ofa sannan ya kira sunansa, hakan ya sanya sa tsayawa chak. 


  "Thank you" ya furta. 


  "You're welcome" ya amsa sannan ya fice had'e da ja masa k'ofar. Wayansa ya zaro yayi scrolling kan contact na Amal tare da dialing bada dad'ewa ba se gashi ta d'aga sede sa6anin yadda ta saba kiran sunansa anytime ya kirata yau d'in batayi ba ko sallama ma tak'iyi shi da kansa yayi gyaran murya yace, "Assalamu alaikum" da shirun yayi yawa. 


  "Wa'alaikumus salam Yaya ina kwana?"


  "Lafiya k'alau ya kike?"


  "I'm good ya jiki?"


  "Alhamdulillah yanzu Sultan ya iso min da sak'onki nagode ko?"


  "Ba komai Yaya Allah k'ara sauk'i." Sede daga yadda take mar magana sama-sama yasan tana fushi dashi kuma yes ya sani she has every single right to act this way. 


  "Ya school yau baki fita bane?"


  "Se anjima banida early morning lectures."


  "Alright toh."


  "Toh se anjima" wow ya numfasa a hankali yau har Amal ce ke neman kashe waya a kansa? "Wait" yayi saurin cewa. 


 "Yes wani abu ne?"


  "I'm sorry kinji?"


  "Ni baka mun komai ba Yaya."


 "Na sani Lily you don't deserve any of the attitude I've been giving you and I'm sorry."


  "Ba komai Yaya ya wuce."


  "Ki gaida su Mami toh."


  "Zasuji" da haka ta katse wayar. Tunani ya shiga yi shi kad'ansa. 


*****

  Haka nan tafiyar ta cigaba ba laifi Afzal ya soma sakewa da Nazeefah sukan zauna a parlour suyi kallon sports ko film tare har abinci ma sun soma ci tare akan dining table. Nazeefah can't ask for more a duk lokacin da suke tare da Afzal ji take like she's the most happiest girl on earth, tana son shi, tana sonshi sosai ba tantama akan hakan. Da kansa yau Asabar bayan sallan La'asr yayi tunanin zuwa gun Amal dan gabad'aya ta fita harkansa ko kiransa bata sake ba har yau, abinda ya mata a asibitin ba k'ramin 6ata mata rai yayi ba tace ta yafe amman bazata iya mancewa da shi ba. Shiri yayi tsaf ya wuce gidansu wanda baze iya tuna rabonsa da yin hakan ba, sosai yayi missing nata baze ma iya kwatantawa ba sede isansa ya tarar da exactly motan ranan wanda yake da tabbacin motan Ya Abdul ne. Daga bakin corner'n ya tsaya yayinda gabansa yayi wani irin mumunan fad'i lokacin da ya hango kan Amal cikin motan be 6ata lokaci ba ya juya. Tuk'i yake amman gabad'aya hankalinsa bai kan hanyan shi kansa besan inda ya dosa ba. Zuciyarsa ce ta soma yi masa k'ona yayinda idanunsa suka shiga kakkafewa dan azaba kafin ya hankara kawai ya jisa jikin pole. Da sauri mutanen kusa suka afka kansa akayi saurin kaisa asibiti sannan aka shiga neman 'yan uwansa. Abba aka samu aka kira ko daya ji beyi mamaki ba dama yasani nan kusa se abu makamancin hakan ya sake faruwa. Kafin ace mey labari ya iske 'yan uwa gabad'aya nan da nan shi da Ummi suka yo asibitin itama Nazeefah bata 6ata lokaci ba ta wuce a chan sukaje suka had'e. Bayan likita ya fito suka duk'ufa sukayi kansa suna tambayansa ya jikin Afzal d'in. 


  "Idan ban manta ba this was the patient I treated some weeks ago right?" Ya tambayesu. Ummi ce tayi saurin gyad'a kai "Yes Dr."


  "Haba Hajiya haba! Taya kuke neman halaka d'anku? Shin baku san idan ya cigaba da samun arrest d'innan wataran zuciyar tana iya mutuwa tak'i tashi gabad'aya ba? Yaci ace kun gano inda matsalar take kun magance ta tun wuri don bazan 6oye maku ba rayuwan d'anku na cikin hatsari" ya fayyace masu. Sosai Nazeefah ta shiga duhu toh meke jawo masa tsinkewan zuciyan ne? Gashi nan de a gida bazaka ta6a ganinsa cikin damuwa ba. Kode shida mutanen sa ne na office? Ta tambayi kanta sede bata da amsa.  


  "Yanzu ya jikin nasa?" Abba ya tambaya. 


  "Mude munyi abinda zamu iya sauran mun bar wa Allah."


  "Dr dan Allah do what you can to save him."


 "In shaa Allahu excuse me." Ummi da Nazeefah ne suka shiga ganinsa yayin da Abba ya ke6e a waje yana mamakin halin da Afzal ke neman jefa kansa. Wajajen k'arfe tara na dare Sultan yazo dubansa shi kad'ai ne a lokacin yana mik'e kan gadon nasa da hannunsa a d'aure inda ya samu targad'e sanadin accident da yayi encountering d'azu. 


  "Ya jikin?" Kai zallah ya gyad'a masa nufin da sauk'i. 


  "Afzal me kake shirin yima kanka? It has to stop idan kai baka valuing life naka mu munayi dan Allah ka yayyafa wa zuciyarka ruwan sanyi ka sauk'e girman kan nan ka sanar da Amal kana sonta. Don kayi hakan doesn't mean zaka mutu amman rik'ewan da kakeyin shine ze iya kashe ka."


  "So be it idan na mutu Sultan but gaskiya d'aya ce it's too late for everything."

  

  "It's not Afzal it's never too late." Kai ya kad'a da nufin a'a "Amal ta riga tayi mun nisa bazan iya samunta ba."


  "Ka bani go ahead kawai in sanar da Abba address nata ina da tabbacin su Abba bazasu hak'ura ba har se idan sun shawo kanta da iyayenta ta kasance taka."

  

   "Ban tsamman hakan is possible there's no point of telling Abba and Ummi about her, tana son Abdul bazata iya rabuwa dashi saboda ni ba."


  "Haka kake gani?"


  "Haka yake I went to visit her d'azu ne ko jiya ne bazan iya tunawa ba achan na gansu tare a motanshi, tana son shi Sultan, da k'yar zata iya yafe sonsa ma wani koda kuwa mutumin ya kasance ni ne."


  "Toh yanzu ya kenan? Kana nufin ba matakin da zaka iya d'auka?"


  "Babu tunda bata sona I can't force her into loving me."


  "Ya kake magana kaman ka sameta kace mata kana sonta tak'i ka ne? Fa Amal bata ma san kana sonta ba wallahi bata sani ba."


  "Toh what difference will it make koda ta sanin?"


 "What if I tell you itama Amal d'in tana sonka?"


  "Da kace ka sanar da ita ranan, dagaske kake?"


  "Yes Afzal bazan iya juran ganinka a haka ba so I told her you love her."


  "Mey tace?"

 

  "Ta kasa yarda amman bata bud'i baki kuma tace bazata iya sonka ba."


    "Just let her be there's nothing more I can do."

 

 "Kai ke da abunyi Afzal kuma har yanzu ina fad'a maka kana da daman mallakar Amal saboda ba wanda ya cancanci soyayyarta kaman ka."


 "How?? Dan ina mata hidima shikenan se ya zamanto dole ta soni?"


  "Ba haka nake nufi ba Triple A ina nufin a tsakaninka da Abdul yake kowaye, kai ka dubi k'aranchin shekarunta ne dakuma karatunta dalilin da yasa kaja baya kenan kak'i furta mata k'udirinka ko ba haka ba? Kafi son se karatun nata yayi nisa right?" Kai ya gyad'a a hankali yana mey sauraronsa. "Toh shikuma Abdul d'in be damu da ta cigaba da karatun nata ba koko a'a shi burinsa kawai ya mallaketa ne ko anan aka zauna aka duba ansan wa yafi wani kaifin tunani da kuma wanda ya cancani soyayyarta. Ka riga Abdul saninta, ka riga Abdul fata sonta saboda haka Amal taka ce ba tasa ba, ka sameta ka fad'a mata k'udrinka Afzal ina da tabbacin cewa Amal bazata yi turning naka down ba."


  "Ka mance da ita kawai Sultan."


  "Idan nayi kai bazaka iya ba Afzal, Amal ta riga ta zama jinin jikinka bazaka iya rayuwa ba ita ba."


  "Don't tell Abba anything about her please Sultan."


  "Afzal-"


  "Dan Allah nace maka komin yaya ne kar ka sanar da shi komai."


  "Haka kakeso ka cigaba da zama da wannan ciwo har seta kasheka tukun?"


  "Yafiye mun da inyi forcing Amal lallai-lallai seta soni."


  "Shikenan Allah k'ara ma lafiya."


  "Ameen thank you."


 "Toh ni zan wuce" yayi maganan had'e da mik'ewa. "Sena dawo gobe Ummah ma gobe zata shigo tace."

  

  "Allah ya kaimu kace ina gaisheta" da haka ya fice ya ja mishi k'ofan. Sallama yayi wasu Abba sannan yayi tafiyarsa.  


  Washegari shi da Ummansa suka dawo kaman yadda ya fad'a. Bayan sun duba Afzal sun fito Abba ya buk'aci Sultan da ya tsaya don haka Ummah ma ta tsaya jiransa. 


  "Hajiya Aisha?" Ya kirata. 


 "Na'am Alhj" ta amsa "Zamu wuce."


  "Mungode sosai Allah ya biya amman kafin nan I want to have a word with you."


  "Toh Alhj ina jinka."


  "Bismillah kizo ki zauna" ba gardama ta k'arisa gefen Ummi ta zauna. Gyaran murya Abba yayi sannan yace, "Ko ban tambaya ba Sultan nasan kasan gidansu yarinyar nan da take bawa Afzal wuya, ka dubi girman Allah da halin da yaron nan ke neman jefa kansa  ka kaini gidansu in samu iyayenta asan nayi. Idan shi baida wayo besan ciwon kansa ba ai kai a matsayinka na abokinsa kasan hakan ko ba haka ba?"


  "Wai Alhj kana nufin Sultan yana sane da komi yak'i yin magana?"


  "Haka nake zato Hajiya shiyasa nakeson a matsayinki na mahaifiyarsa ki rok'esa kisa baki ya bamu had'in kai mu ceto ran d'an nan baza mu biye masa ba."


  "Sultan?"


  "Na'am Ummah."


 "Yanzu kana sane da komai amman ka gwammace kayi shiru saboda rashin lafiyan abokin naka be dame ka ba?"


  "Wallahi Ummah ba haka bane Abba kayi hak'uri nake ganin nafi kowa damuwa da halin da Afzal ke ciki musamman ni dana san kalan hidiman da yake yima yarinyar nan, nauyin makarantarta gabad'aya ya d'auke wa iyayenta. Duk abinda ya dace ayi Afzal nayi mata amman ya furta mata k'udirinsa ya kasa wai sede ita ta gano hakan da kanta ita kuma ta kasa, nayi-nayi dashi abun ya gagara kuma ya had'ani da Allah kar in sanar daku komai akanta komin yaya ne."


  "Toh kuma seka biye masa ne Sultan? Bakaji me likitansa yace ba? The more yake samun attack d'in wataran zuciyan na bugawa gabad'aya ta daina aiki shikenan kuma k'arshensa kenan ai kamata yayi tun kan maganan yayi nisa haka kazo ka sameni ka fad'a mun abinde ake ciki wallahi banida labari se yau" cewar Ummi. "Meye sunan yarinyar?"


  "Amal" ya amsa. 


  "Amal?" Ta nanata, "Bade Amal da na ke ji a bakinsa ba? Yo Alhj ai nasan yarinyar mun sha gaisawa da ita ta wayan Prince."


  "Kinsanta fa kikace?" Abba ya tambaya da mamaki. 


  "Ban ta6a ganinta ba amman muna waya itace me kawo mana Aldeb me dad'in nan amman Afzal anyi bahon d'a wallahi yanzu yarinyar nan dake sonsa d'inne ya kasa tunkararta ya fad'a mata yana sonta har abun yayi nisa haka?"


  "Wallahi Ummi bakiga fad'an dana rink'a yi masa ba amman yak'i jina shine kawai na hak'ura na barsa in ga iya gudun ruwansa."


  "Ita yanzu yarinyar tasan yana sonta ne?" Abba ya tambaya. 


  "Bata sani ba Abba nine nayi gwanintan gaya mata."


  "Mey tace?"


  "Tak'i yarda sam har kuka tayi mun da hawaye wai sharri nakeyi wa shi Afzal d'in take cewa idan da har dagaske ne ai da ze sameta ya fad'a mata kokuwa iyayenta."


  "Tabbas tayi gaskiya" Ummah tace. 


  "Yanzu tashi ka kaini gidan nasu" cewar Ummi "Kai Alhj ba seka je ba tunda na riga nasan yarinyar zanyi mata magana in shaa Allahu za'a dace dan idan har itace Amal d'in kaman yadda Sultan ya fad'a toh yarinyar bata da matsala."


  "Toh Allah kare" basu kai ga mik'ewa ba sega Nazeefah ta shigo da basket na abinci rik'e a hannunta, binsu duka tayi da gaisuwa sannan take tambayarsu ina zasu bayan ga abinci nan ta kawo. 


  "Ermm.." Ummi ta shiga neman dalili "Zan rakasu ne nan in wuce gida in watsa ruwa kiyi sauri ki kai wa Afzal d'in kar yaji yunwa."


  "Toh Allah ya kare" nan ta zarce d'akin Afzal yayinda su kuma suka fice. Sauk'e Umma Sultan yayi sannan shida Ummi suka k'arisa gidansu Amal. Waya yayi mata akan cewa ta fito bayan ta fito ya sauk'o daga motan ya sameta inda suka gaisa. 


  "Ya Yaya yake? Ya jikin nasa?"


  "Jiki ya sake tashi ai yanzu haka ma yana asibiti."


  "Innalillahi wallahi banida labari, tun yaushe?"


  "Jiya bayan da yabar nan."  

  

  "Nan kuma?" Ta tambayesa cike da rashin fahimta "Yaya bezo nan bafa jiya."


  "Yazo kede baki gansa ba amman shi ya ganki."


  "Anya kuwa Ya Sultan? Da yaushe?"


  "Sosai kuwa lokacin da kuke tare da Abdul se be k'arisa ba ya juya. Bisa yadda ciwonsa ya tashi yayi hatsari a hanya amman da sauk'i targad'e kad'ai ya samu." Mutuwa sosai jikin Amal yayi gun ta ma kasa cewa komai se chan muryarta ta dawo mata. 


  "Ya Sultan-"


  "Ga Umminsa nan acikin mota tazo kuyi magana." Wani irin har6awa zuciyarta tayi, yanzu take gaskata zancen Falmata, Ya Abdul, Maamah da kuma shi kansa Ya Sultan d'in. Sede kanta ya d'aure, meyasa Yaya ya kasa sanar da ita k'udurinsa akanta? Meyasa yay ta wahalar da kansa akanta? Ko dan bata kai ya furta mata kalaman so bane? Well tasani Yaya ba tsarinta bane amman ai da ko Papi ne ya samu ya sanar da shi, da duk hakan be faru ba. Yanzu ba wannan ba, shin ina yake son tasa soyayyar Ya Abdul nata? 

    

  "Bismillah ki shiga motar" kai ta shiga kad'a masa da nufin a'a. 


  "Ya Sultan dan Allah ka rufa mun asiri wallahi ni ba nice sanadin halin da Yaya ke ciki, ban san Yaya so na yake ba wallahi da na gano hakan bazan ma fara kula Ya Abdul ba koda kuwa ace be furta yana so na ba please karka had'ani da Ummi."


  "Calm down Amal tazo ne ta nemi alfarma gunki ba da niyyan tashin hankali ba ki k'arisa ciki tana jirarki" sede ina Amal ta kasa gabad'aya ta rud'e k'arshe seda Ummin ce ta fito da kanta. Bakinta na rawa ta tsuguna ta gaishe da Ummi sannan ta d'agata ta share mata hawyenta ta jata izuwa wani benchi suka zauna. 


  "Baki gane ko ni wace ba ko 'yata?"

  

  "Ummin Afzal?" Kai Ummi ta gyad'a mata. "Ya jikin nasa?" Ta tambaya a hankali. 


  "Da sauk'i Alhamdulillah nasan kina mamakin gani na aban haka ba notice ko?" Nan ma kai ta gyad'a a nitse. "Taimako nake nema koma ince alfarma don shi yafi dacewa da k'udurin da nake tattare da shi. Zan iya samu?" Shirun da tayi ya bawa Ummi go ahead. 


  "Amal ran Afzal na cikin hatsari, likitansa yace idan ya cigaba da samun attack wataran yana iya rasa ransa gabad'aya kuma ke kad'ai keda ikon ceto mana ransa."


  "Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un" ta furta yayinda idanunta keta kan cikowa da hawaye. 


  "Kinji Mama na? Nasan da wuya da ciwo da kuma zafi amman dan Allah ki amince ki auri Afzal ki cetosa daga cikin wannan halin da ya fad'a" wani irin mumunan fad'i gaban Amal yayi. Aure gabad'aya? What if she's not ready? What of Ya Abdul? Shi anyi masa adalci kenan? 

  

  "Amal baki ce komai ba" Ummi tayi magana bayan shirun da Amal tayi. Baki na kakkarwa tace, "Ummi ban san me zance ba, ina son Yaya, banida kaman shi ban ta6a neman abu gunsa na rasa ba, komi nakeso yana mun, baya wasa da sha'ani na, na d'aukesa a matsayin wa na babba wanda nake da burin zama big aunty ga yaransa not that ni in kasance matarsa, bazan iya auran Yaya ba."


  "I know how it feels Amal ko ni nan da kike gani banso aure na da Abban Afzal ba, ba nice mahaifiyarsa ba. Ya ta ce mahaifiyarsa, ya ta na k'ut-k'ut mutuwa tayi mana k'atutuwa gashi lokacin Afzal na d'an jariri ko wata be kai ba. Dole aka sani rabuwa da masoyina aka aura min mijin ya ta imagine how difficult it must be for me amman hakan na hak'ura na rungumi k'addara look at where I am today, Abban Afzal shine sanyin idanu na bana jin zan iya rayuwa ba shi. Kema idan kika hak'ura komi me wucewa ne kinsan halin Afzal ba sena irga miki ba muddin yana son abu yana iya k'ok'arinsa yaga ya adana abun ya kuma kula dashi, Afzal will never disrespect or take you for granted dan Allah kiyi la'akari da halin nan da yake ciki ki amince Amal."


  "Ummi ni idan ta nine bani da matsala, I can sacrifice the entire world for Yaya, zan iya yafe farin cikina saboda na Yaya because he deserves it and kamar yadda kika fad'a nasan Yaya baze ta6a walak'anta ni ba matsalar ba daga ni bace."


  "Daga ina ne toh Mama na?"

  

  "Ya Abdul" ta numfasa. 


  "Waye shi?""


 "Shine wanda muke tare da shi, wanda yake da burin mallakata kaman yadda nima nake da burin kasancewa da shi. Ya zanyi? Ta ya kukeson in fara sanar da shi wannan labari? Bazan iya ba his last girlfriend cheated on him nima bazan iya masa hakan ba, Allah ma seya tambayeni" tasa kuka.

  

  "Shhh!" Ummi ta rungumota tana bata hak'uri "This is not called cheating my dear, ba da son ranki zaki rabu da shi ba and I know, na sani Afzal yayi kuskure amma bazamu iya maida hannun agogo baya ba all we can do now is to make things right. In har Abdul nakin na da tausayi ze fahimci halin da Afzal ke ciki ya yafe son da yake miki masa, Amal bana son in rasa d'ana."


   "In shaa Allah ba zaki rasa sa ba Ummi." 


  "Toh ki amince ki aure sa."

   

  "Ummi I'm not the one to decide like I told you zan iya yafe farin cikina saboda na Yaya idan Ya Abdul ze iya hak'ura nasan iyaye na ma basu da matsala dan Yaya kaman d'an gida yake  problem d'in kawai Ya Abdul ne."


  "A'ina ne gidansu ni da Abban Afzal muje muyi musu bayanin halin da ake ciki."


  "Yana nan Polo."


  "Zan iya samun layin wayanshi?" Kai ta gyad'a ta d'ago wayanta takai kan contact d'in sannan ta mik'a mata nan take ta kofe a wayarta. "Nagode sosai Amal, thank you so much." Nan ma kai zalla ta gyad'a "Zan iya komawa ciki?"


  "Sosai mamana ki gaishe Umminki idan kin shiga ina sauri ne da na tsaya mun gaisa."


  "Bakomai zataji" sallama tayi wa Sultan sannan ta wuce ciki direct se d'akinta. Kuka kawai ta shiga yi a tunaninta shi ze iya magance mata wannan musiba. Wannan wace irin k'addara ce da se an rabaka da masoyinka? Taya zata fara kallon idanun Yaya da wani manufa? Taya zata fara zaman aure da mutumin da ta d'aukesa a matsayin wanta na jini? This's so wrong bazata iya ba. Meyasa Yaya ya jata jiki haka bayan yasan da wannan manufan a zuciyansa? Oh Allah ga ni gareka. 



**** A gida Sultan ya sauk'e Ummi nan da nan ta samu Abba ta sanar da shi yadda sukayi da Amal. Amsan numban Abdul d'in yayi akan shi zeyi masa magana ko gobe se suje gidan nasu. Har a nan Afzal dake asibiti be san meke faruwa ba, shi de se duba wayansa yake ko zega sak'on Amal tunda daman ta daina kiransa yanzu amman sak'on ma yau babu. Amal nata kanta ko tunawa da shi batayi ba. Wajajen k'arfe goma Ya Abdul ya kirata. Share hawayenta tayi ta gyara muryarta gudun wai kar ya gane kuka take sannan ta d'aga. 


  "My Baby" ya soma da cewa. 


  "My Ya Abdul" ta amsa "Ina yini?"


  "Lafiya ya kike? Ya school?"


  "Alhamdulillah ya office? I missed you."


  "Alhamdulillah I missed you more my baby."


  "Shine baka zo ba?"


  "Aiki ne ya rik'eni Baby har ranan sunday ma ban tsira ba."


  "Ya suke wahalar min da Baby na hakane kam?"


  "Karki damu wahalan is worth it, atleast it comes with money kinga se nayita tarawa in auran mu yazo muyi gaggaruman celebration me hashtag irin na Instagram" dariya sosai ya sata dukda cewan bata mood d'in. 


  "Ko ba haka ba?" 


  "Hakane" ta ce dashi duk da cewan tasan idan ba wani ikon Allahn ba bazata iya kasancewa da Ya Abdul ba. 


  "Ya naji muryan ki k'asa-k'asa haka Baby lafiya?"


  "Lafiya Ya Abdul mura nakeyi."


  "Shine baki fad'amun ba ni da nace ko cizo sauro ya miki you should call and tell me." Nan ma bata da niyyan yin dariya amma seda ya sanya ta yi. "I'm sorry forgive your Baby."


  "Baby ta shirya shan pepper soup gobe se muran ya sauk'a gabad'aya."


  "There's no need for that ina shan magani."


  "Nifa na fad'a miki sauran inzo kik'i fitowa har cikin d'akinki zan shigo in fito dake."


  "D'ankaren nauyi ne da ni fa bazaka iya ba."


  "Niko d'ankaren k'arfi ne dani ba abinda bana iya d'agawa."


  "Toh shikenan da-" se kuma tayi shiru. Haka kawai taji kar tayi saurin sanar dashi abinda ke faruwa tana sa ran wani mu'ujizan ze faru ya zamanto Afzal ya warke ba se an raba ta da masoyinta ba. 


  "Ya kikayi shiru?" Yayi saurin tambaya. 


 "Babu."


  "A'a fad'i de."


  "Allah babu."

 

  "Baby so kike in taho da bulala gobe ko?"


  "Kuma seka zaneni?" Ta wani zum6uro baki. 


  "Toh tell me menene?"


  "Dagaske babu."


  "Kinga irin taurin kan naki da nakeso ba? Amal I can't wait to own you, ki bani go ahead amma kink'i kullum kice ke a'a it's almost getting to a year."


  "Kai Babe kai kuma harda zugau 5 months ne fa."


  "6 ne and it still makes no difference ni ko formal gaisuwa ne azo ayi su Mami de su san sunyi in law."


  "Ya Abdul I'm sorry" kawai seta rushe da kuka. 


 "Subhanallahi wani abun ne na fad'a? Dan Allah kibar kukan I take it back." Katse wayar tayi yayinda kukan yaci k'arfinta ta barsa yana ta faman 'hello? Hello?' Sosai kan sa ya d'aure ya rasa mene ya fad'a da ze sanya ta kuka haka kode batun turowan da yace zeyin ne? Shikam wasa yake mata he can wait for as long as it takes inde akan Amal ne har se idan ta amince ya turon. Take ya shiga kiran layin tan sede tana gani amman ta kasa d'agawa don kuka. Gajiya da trying layintan yayi kawai ya kira Maamah a waya da ta zo site nasa yanzun yana jiranta. Bata 6ata lokaci ba ta iso take tambayar sa ko lafiya. 


  "Ina wayanki?" Ba gardama ta mik'a masa. Numban Amal ya d'ura ya kira nan ma har ya tsinke bata d'aga ba se a karo na biyu. 


  "Amal I'm sorry" taji muryan Ya Abdul kafin tace zata kashe yayi saurin cewa "Please don't hang up" hak kawai kuma ta fasa. "Amal abinda na fad'a ne ya 6ata miki rai?" Kai ta kad'a wane yana gabanta "Amal I was only joking dan Allah kiyi hak'uri."


  "Ya Abdul ba kai bane" ta furta cikin tsananin kuka. 


  "Toh waye ne?"


  "Babu."


  "Kina kuka haka kice mun babu Amal? please tell me ko so kike in fito cikin daren nan in samu su Mami?"


  "Please don't."


  "Then tell me."


  "Ya Abdul I'm sorry I'm so sorry."


  "Amal please stop."


  "Ya Abdul no matter what happens ka sani ina sonka, you're my first love and I shall die with your love here in my heart. I've loved you since day one and I shall continue to love you forever, you'll always remain close here to my heart please don't forget this." Sosai ta sanyasa cikin rud'ani. 


  "I know Amal but why the sudden confessions? Meya faru? Please talk to me." Ya buk'ata cike da tashin hankali. 


  "Please forgive me seda safe."


  "Amal wait!" Saidai har ta kashe wayan. Hankalinsa ya matuk'ar tashi, ba shi kad'ai ba harta Maamah data kasa fahimtan meke faruwa. 


  "Ya Abdul meke faruwa?"


  "Maamah I don't know d'auko mun key'n mota na."


 "Kaje ina?" Ta tambaya da mamaki.  


  "Gidansu Amal."


  "Ya Abdul shin baka san k'arfe nawa bane yanzun? Dubi pass 10 fa."


  "I don't care Amal na cikin damuwa get my car key for me."


  "Toh iyayenta zaka je ka samu ko wa?"


  "I don't care I just want to see her and make her feel okay."


  "Ya Abdul dan Allah ka kwantar da hankalinka kayi hak'uri ka bari zuwa gobe ni ma zan raka ka muje muji meke faruwa amman fita cikin daren nan is not a good idea."


  "Maamah baki ji yadda take kuka bane?"


  "Naji gobe in shaa Allah zamuje mu dubata dan Allah ka kwantar da hankalinka" hak'uri tayita basa da k'yar hankalinsa ya d'an kwanta ya amince se goben zasu je su dubata. Sede kaman yadda Amal tayi kwana zaune tana kuka tana tuna rabuwanta da Ya Abdul, shima haka Ya Abdul d'in yayi kwana zaune yana tunanin halin da Amal tasa take ciki. Ji yake kaman gari baze waye ba.




RANA D'AYA!

#RD


Love... King Miemiebee👄✨

[13/08, 02:13] ‪+234 907 483 8352‬: 🎀🎀🎀                 🎀🎀🎀

                🎀❣🎀

                   ❣❣


  💦💦                      🍃🍃🍃          

           *RANA D'AYA!*

  💦💦                      🍃🍃🍃

  July, 2018

 beeenovels.blogspot.com


     _Written by Miemiebee👄_



   *PAGE 1⃣8⃣*



  ****

   "Alhj?" Ummi dake zaune a kan gado ta kirasa. 


  "Na'am" ya amsa yana me karkato da kallonsa a gareta. 

  

  "Nace ba ina laifin mu fara samun iyayen ita Amal d'in kafin mu nemi Abdul nake ga hakan ze fi fasali."


  "Ko meyasa kika ce haka?"


  "A tunani na hakan ze fi tunda de ita Amal da bakinta tace mun Prince kaman d'an gida yake a gurinsu and kaga ze fi sauk'i mana ma idan har iyayen nata ne zasu sanar da Abdul d'in halin da ake ciki zefi d'aukan maganan shima da muhimmanci."


   "You have a point."


  "Thank you so mey kace?"

  

  "We'll do it your way gobe in shaa Allahu se muje gidansu Amal d'in."


  "Yauwa toh Allah kaimu."


  "Ameen" kammala abinda yake yayi sannan ya k'ariso ya kwanta tare da kashe masu wutan d'akin. 


 Gari na wayewa wajajen k'arfe goma Abdul yasa Maamah a gaba suka wuce gidan su Amal. Kiranta ya tayi amman tak'i d'aga wayar, haka ma da ya gwada da lamban Maamah still tak'i picking don haka ya buk'aci Maamah da ta shiga ta tabbatar masu meke faruwa. Shigan Maamah taci karo da Mami se suratai take ita kad'ai da ta kasa kunne kuwa seta gano regarding Amal ne tana cewa "yarinya tun jiya ake tambayarki meke damunki amman kink'i kiyi magana se aukin kuka ki tayi" 

   "Assalamu Alaikum" tayi sallama hakan yasa Mami kewayowa had'e da amsawa. 

   "Wa'alaikumus salam, a'ah! Maamah?"


  "Na'am Mami ina kwana?" Ta tsuguna ta gaisheta "Lafiya k'alau ya kike ya makaranta?"


  "Alhamdulillah Amal na gida kuwa?"


  "Ga ta chan tana d'akinta tana kuka ki k'arisa ciki halan ke ta gaya miki meke damunta." Ba gardama ta k'arisa ta tsinci Amal nata kuka kaman yadda Mami ta fad'a gabad'aya ta fita daga kamanninta fuskan nan ya kumburo tum idanunta sunyi ja suma sun tara ruwa a k'asa. Hugging nata kawai tayi tsananin tausayin da ta bata, kukan ta cigaba dayi yayinda Maamah ke bata hak'uri da k'yar tasamu kukan nata yad'an lafa sannan ta shiga tambayarta meke faruwa sede Amal tak'i bata amsar komai. Ba yadda Maamah batayi da ita ba amman banda hawaye ba abinda Amal takeyi. Abdul da ya gaji da jiransu a waje ne ya kira Maamah don jin ko lafiya inda take irga mai ai Amal d'in tak'i sanar da ita komai. Abdul be san lokacinda zuciya ta d'aukesa ba ta diresa a cikin gidansu Amal ba shiri. Sallama yayi da wuri Mami taja hijabinta daga kan igiya ta sanya jin muryan na miji sannan ta amsa tana jiran ganin kowa. Bak'on fuskan data gani tsaye bakin k'ofan ne ya sanyata ja da baya kad'an. Se kuma taga tsananin kama tsakaninsa da Maamah to kode wanta ne? Ta tambayi kanta. Tun daga bakin k'ofan ya durk'usa har k'asa ya gaisheta. 


  "Tashi don Allah tashi kaji?" Amman yak'i seda ta amsa sannan ya mik'e. "K'ariso ciki, wan Maamah kake ko?" Mamakin daya bayyana a fuskansa ne ya sanyata murmushi "Bade mamakin ya na gano kake ba?" Dukda mugun halin da yake ciki hakan be hanasa mayar mata da murmushin ba "Sosai Mami" ya amsa. 


  "Yo ai kama kuke wane an tsaga kara marabanku de hasken data fika shikenan lale k'ariso ciki barin yi mata magana ta fito."


  "Toh nagode amma dama wajen ki nazo" ya sanar da ita. Da mamaki ta tsaya kallonsa "Gu na kuma?" Ta tambaya. 


  "Eh Mami I'm sorry please."


  "Ba komai bismillah k'ariso." Tabarma ta shinfid'a masa ya zauna sannan tayi hakan itama har anan Maamah da Amal dake cikin d'aki basu san meke faruwa ba. 


   "Toh gashi ban ma san sunan ka ba."


  "Abdurrahman" ya sanar da ita. 


  "Toh Abdurrahman meke tafe da kai?" Gyaran murya yayi tare da dukar da kansa "Mami a farko de ina son in fara da baki hak'uri, dan Allah kiyi hak'uri na shiga gonan ki da Papi da nayi na sace flawanku ba tare da sanar daku ba, I'm sorry." Sosai Mami ta shiga duhu "Baba na kayi hak'uri amman ban fahimce ka ba."

  Nauyayyan ajiyan zuciya ya sauk'e sannan yace, "Sama da wata shida kenan muna tare da Amal amman keda Papi ba kuda labari, what's worse is ko izinin nemanta banyi ba daga gareku which I know is very wrong of me amman ku gafarceni. Banida niyyan lalata Amal, ina sonta ne so na tsakani da Allah so na aure idan har zaku bani izini. Sau dayawa nakan gwada rok'an kanta da tabani dama in turo magabatana koda formal introduction ne ayi don asan juna amman hakan ya gagara kullum excuses da take bani daban amman ina da tabbacin tana da k'wak'waran dalilin dake sata hakan. Toh kuma se gashi tun jiya na kasa gane kanta, muna cikin waya kawai ta rushe da kuka tun wannan lokacin bata sake d'aukan kira na ko na Maamah ba. Yau na turo Maamah don ta tabbatar mana da me ke faruwa amman shiru Amal tak'i magana dalilin daya sa nayi wannan zuwan bazata kenan amman kiyi hak'uri sam ban so hakan ba nima da magabata na naso fara tako k'afa na cikin gidan nan, my sincere apologies please."

 

  Shiru Mami tayi tana assimilating kalamunsa wato har na kusan wata shida suna tare amman shine Amal bata ta6a bud'an baki koda wasa tace mata gashi ba? Sau dayawa takan jita a waya amman kota tambayeta da waye ne setace da Afzal ne ashe saurayi tayi a bayan idonsu. 


  "A gaskiya Abdurrahman bazan 6oye maka ba banji dad'in cewa se yau nakejin wannan batu ba ace na tsawon wata shida kana neman 'yata amman ba tare da ka nemi izini gun d'aya daga cikin iyayenta ba?"


  "Nasan ban kyauta maku ba Mami and I'm gravely sorry bana son hakan yasaki tunanin da wata manufan nake neman Amal wallahi my intentions are pure ina son Amal ne tsakani da Allah."


  "Kuma da ba don halin da ta fad'a d'inba bakada niyyan bayyana mana kanka yanzu ko ba haka ba?"


  "Mami bazan gaji da baki hak'uri ba saboda nasan ni me laifi ne amma kisani wallahi nima ba haka naso abunnan ya kasance ba. My apologies please, and ko a yau kukace in turo magabata na zanyi hakan saboda bana son abinda ze rabani da Amal, inason ta sosai." 


  "Naji bayanunka Aburrahman kuma na gamsu dasu idan Papinta ya dawo daga tafiya zan mai bayani duk abinda akwai zan sanar da kai."


  "Nagode sosai Mami kuma ina sake baki hak'uri."


  "Ba damuwa karka damu."


  "Se kuma batun Amal ko zan iya sanin meke damunta? Nayi nayi ta sanar dani amman tak'i bazan kuma 6oye miki ba hankali na ya matuk'an tashi banason ganin Amal cikin damuwa."


  "Wallahi bazan 6oye maka ba, yadda baka da masaniya akan halin nan da take ciki nima haka ne, tak'i sanar dani matsalarta se kuka kawai. Yanzu haka jiran Papinta kawai nake shi kad'ai take jin maganansa." Ya bud'e baki zeyi magana kenan sega k'ofan d'akin Amal ya bud'u Maamah na fitowa bayanta kuwa Amal ce ta rik'e k'ofan tana shirin rufewa. Idanunsu na had'ewa gabanta yayi mumunan tsinkewa barin ma ganinsa da tayi tare da Maami. Yau shikenan ya gama da ita, tasan she's in a big trouble idan Papi yazo. 


  "Amal!" Ya kira sunanta da sauri ta mayar da k'ofan kai zallah Mami ta kad'a wai kode aljanu ne suka shigeta? "Kafa kwantar da hankalinka yau Papin nata ze dawo koma mey ke damunta zata sanar dashi ko ta fad'a miki abu ne Maamah?" Ta juyo tana kallon Maamah. 


  "A'a wallahi tak'i sanar dani komai."


  "Toh Mami zamu koma nagode sosai da k'aramcin da kika nuna mun Allah sak'a da gidan aljannah."


  "Ameen Abdurrahman ba komai gashi har zaka tafi ko ruwa ban baka ba."


  "Haba daga gida nake karki damu mu tafi ko Maamah?" Yayi maganan had'e da mik'ewa har waje Mami ta rakasu sannan ta dawo ta nufi d'akin Amal tare da bankad'e k'ofar. "Ai Papinki ze dawo wai shin a ina kika koyo wannan d'abi'ar iyye? Har kiyi saurayi ba wanda ya sani a gidan nan? Abinda kikeyi a makarantar kenan ko?" Shiru Amal tayi mata don bata jin ma tana da energy'n yi mata bayanin komi. 


  "Sa'an ki d'aya wallahi yaron nada hankali wato har iyason turo magabatansa amman kike hanasa saboda ke bakison ku gina abinda kuke da shi akan addini ko? Kuma kiji ni kukan nan ya isa haka, ba dukanki akayi ba ba fad'a aka miki ba kawai kibi ki ta da wa mutane hankali haka a banza? Dubi yadda hankalin yaron nan ya tashi da safen nan kika d'agosa duk da hakan kin gansa kin kasa k'arisowa ki gaishesa toh ki cigaba Baby" tana kaiwa nan ta fice. Wani sabon kukan Amal ta rushe dashi a gun haka ta cigaba dayi har izuwa dawowan Papi. Bayan ya d'an huta Mami ta zaunar da shi ta labarta masa ababen da suka faru bayan tafiyansa ta ke kuma yabawa hankalin Abdul. Turata yayi da ta kira Amal bayan sun k'ariso Amal ta tsuguna daga waje-waje tana mey tare fuskarta da hijabinta. 


  "Mama na?" Ya kirata 


 "Na'am" ta amsa. 


 "Daina kukan haka kinji? Ya isa goge hawayenki." Ba musu ta shiga share hawayen nata "Gaya mun meke faruwa?"


  "Papi babu."


  "Nace ki gaya mun meke faruwa."


  "Babu komai."


  "Kode se kinji bugu ne?" Fad'in Mami. 


  "A'a beyi zafi haka ba zata fad'a da kanta gaya mun kinji keda waye ne?Keda Abdul d'inne?" Kai ta kad'a a hankali "Toh waye?"


  "Yaya" ta furta chan k'asa-k'asa. 


  "Afzal??" Papi ya tambaya da mamaki yayinda Mami ta bud'e baki tana kallonta itama cike da mamaki. 


  "Meya samesa? Wani abun ya miki?"


  "Ba shida lafiya, likita yace yana iya rasa ransa."


  "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" both shi da Mami suka sa salati. "A dalilin mey?!" Mami tayi exclaiming cike da tashin hankali Allah sarki ashe shiyasa kwana biyu baya zuwa kuma bayi ko kiranta ita ko Allah be bata ikon kiransa ba dukda cewan yana ranta ashe beji dad'i bane. 


  "Meya samesa?" Papi ya tambaya finally. 


  "Ya kamu da ciwon zuciya." Nan ma wani salatin suka kuma sawa. "Allah sarki d'an halak shine baki fad'a mana tun wuri ba Baby? Sede kiyita kuka amman baza kiyi magana muje mu dubasa ba? Haka akeyi ne aka ce miki?" Mami ta kurareta. 


  "Tun yaushe yake jinyan?"


  "Ya d'an kwana biyu Papi" ta amsa tana share hawayenta. 


  "Ya isa kukan haka in shaa Allah ze samu sauk'i ba wanda ze mutu kinji?" Kai ta gyad'a a hankali "Zamu shirya kuma duka muje mu dubasa kukan ya isa haka."


  "Nagode" bata kai ga mik'ewa ba ya dakatar da ita. 


  "Se kuma batun Abdurrahman ko?" Yayi maganan yana kallon Mami. 


  "Waye shi?"


  "Wan k'awata Maamah ne."


  "Mey a tsakaninku?" Shiru tayi ba amsa. "Meyasa baki ta6a sanar dani ko Maminki batu akansa ba? Haka aka ce miki akeyi?"


  "Papi I'm sorry kayi hak'uri."


  "Baki amsa tambaya na ba meyasa?"


"Papi kuskure ne amman kayi hak'uri."


  "Da yakeson turo magabatansa kuma meyasa kike hanasa?"


 "Papi ba hanasa nayi ba."


  "K'arya Mamin ki take kenan?" Kallon Mamin tayi sannan ta kad'a kai. "Toh meye dalili?"


  "Na d'au idan akayi hakan zaku hanasa kula ni ne."


  "A ganinki kula shi da kikeyi ba tare da izinin mu ba shine abinda ya kamata?"


  "A'a" ta amsa tana kad'a kai. 


  "Tun yaushe kuke tare?"


  "About 6 months now" ta amsa chan k'asa-k'asa. 


  "D'an gidan waye ne?"


  "A Zarma na bakin layin polo."


  "A Zarma me masallacin juma'ah?"


  "Eh shi."


  "Kina sonshi kuma?" Shiru tayi ta kasa amsawa. "Ke fa Baby kina son shi?"


  "Eh Papi" ta amsa murya a ciki kallonta Mami tayi had'e da turo baki. 


  "Idan nace ya turo magabatansa zaki amince ki auresa?"


  "Eh Papi."


  "Toh shikenan tashi ki fice amman nan gaba karki sake yin wannan rashin hankali duk wanda kuka had'u dashi ya nuna yana sonki kiyi masa kwatancen gidan nan kice yazo ya gana da Papinki kinji? Bawai kuje chan kuna sha'aninku ba bawanda yasani kin ji?"

  

  "Naji Papi nagode kuma ka sake yin hak'uri kema haka Mami."


  "Shikenan ta shi ki fice" da haka ta mik'e ta wuce d'akinta. 


  "Ban yarda wai saboda rashin lafiyan Afzal take wannan kuka ba" fad'in Mami. 


  "Ko?"


  "Sosai ma kuwa Baba kasan tun yaushe take wannan kuka? Da akwai 6oyayyan al'amari a tattare da yarinyar nan."


  "Nima nayi zaton hakan amman kinga koda k'arya take anjima idan mukaje asibitin zamu tabbatar da gaskiyar al'amarin."


  "Toh shikenan Allah kaimu."

  

****

   Nazeefah ce tayi knocking bisa k'ofan d'akin Afzal sannan ta bud'e ta shiga yana ganin itace ya kawar da kansa. K'arisowa tayi da basket na lunch nasa ta ajiye akan table "How're you feeling? Kana iya d'aga hannun?"


  "Tukunna amma da sauk'i" ya amsa. 


  "I cooked your favorite Rice and stew" ta sanar dashi tana me bud'e hulunan. Bayan tayi serving nasa ta taimaka masa ya zauna sannan ta zauna a gefensa itama da shirin basa abincin. 


  "Ahhh" ta buk'acesa. 


  "I can manage karki damu."


  "Come on Afzal open up."


  "Nace karki damu zan iya ci da kaina."


  "I know laifi ne don nayi feeding naka? Besides you're still not fit." Da k'yar ta samu ya amince ta shiga basa abincin har seda ya k'oshi. Godiya yayi mata sannan ta tsiyaye masa ruwa ya had'iye magunansa yake tambayanta Ina Ummi tun jiya be sake ganinta ba. 


  "Nima tun jiya da na ganta tsaye dasu Sultan da Ummah tace zata masu rakiya ban sake ganinta ba." Haka kawai seyaji gabansa ya tsinke bade wani d'anyen aikin suke shiryawa a bayan idonsa ba ya tambayi kansa. 


  "Wayyo!" Yasa ihun k'arya. 


  "Lafiya?" Tayi saurin tambaya. 


  "Get my Dr! Hurry! Washhh!"


  "Keep still ina zuwa" a guje ta fice neman likitansa inda ya ciro wayansa ya kira Sultan. A karo na farko ya d'auka. 

  "Sultan meke faruwa?"


  "Kaman ya? Lafiya?"


  "I don't want to believe ka sanar dasu Ummi batu akan Amal ka tuna ka d'au alk'awarin bazaka fad'a musu komi ba."


  "Sekuma akace maka na sanar dasu wani abun?" Ya mai k'arya. 


  "I just have a strange feeling."


  "Ka kwantar da hanaklinka ni ban sanar dasu komai ba."


  "Yauwa thank you."


  "Ya jikin naka?"


  "Alhamdulillah zuwa anjima ma zasu sallameni."


  "Toh madallah ko kun sake waya da Amal?"


  "Nah bata kirani ba nima ban kirata ba."


  "Alright sena shigo de."


  "Okay you take care." Da haka sukayi sallama. Dawowan Nazeefah da Dr seyace ai daya sha ruwan sanyi yaji sauk'i, dubasa sama-sama likitan yayi sannan ya fice. 


   Wajajen k'arfe biyu da rabi Ummi da Abba suka isa gidansu Amal. Sallama suka yi a bakin k'ofar seda aka amsa suka shiga, Ummi ce ta soma sa kai. 


  "Lale sannu da zuwa" cewan Mami lokacin da taga Abba a bayan Ummi ne tayi saurin mayar da hijabinta. "Sannunku da zuwa" dadduma ta shiga ciki ta dau ta shimfid'a musu sannan suka gaisa. "Baki gane ni bako?" Ummi ta tambayeta. 

  

  "Eh toh wallahi" ta amsa da fara'a. 


  "Ummi ce, mahaifiyar Afzal na gefena ko mijina na ne Abban shi."


"Wai wai wai ashe manyan bak'i mukayi lale lale sannunku da zuwa bari in kawo muku ruwa."


  "A'a karki damu daga gida muke" cewan Abba. 

  

  "Ya jikin Afzal d'in se yau Baby ke sanar damu wai beji dad'i ba."


  "Jiki Alhamdulillah da sauk'i" ya amsa. 

  

  "Toh Allah k'ara masa lafiya muma muna shirin zuwa dubasa dama da Kakan Baby."


  "Ayyah ba komai ko shi kakan nata na gida?" Abba ya tambaya. 


  "Eh barin yi mishi magana."


  "Yauwa toh" da haka ta shiga ciki ta kira shi yayin da ta lek'a d'akin Amal don tazo ta musu sannu da zuwa sede ta ga d'akin nata ba kowa ko yaushe ta fita ba tare da ta sanar da ita ba? Papi na fitowa suka gaisa da Abba sannan Ummi inda Papi keta sawa Afzal albarka yana fad'a masu irin hidiman da yakeyi wa Amal yake kuma godiya. Sosai shi Abba da Ummi suka ji dad'in halin taimako irin na Afzal. 


  "So Alhj Muh'd ba tare da 6ata lokaci ba bari in sanar da kai meke tafe damu" cewan Abba had'e da yin gyaran murya "Munzo ne batun Afzal."


  "Toh ina jinka Alhj."


  "Kaman yadda Amal ta fad'a muku be ji dad'i ba, hakan yake likita yayi gwaje-gwajensa an gano ya kamu ne da ciwon zuciya."


  "Tabbas haka Baby tace Allah k'ara mai lafiya ya kuma yaye mashi wannan ciwo."


  "Ameen ya Allah" duka suka amsa sannan Abba ya cigaba. "Sanadin wannan ciwo daya kama sa se kan kowa ya d'aure mun rasa sababin ciwon, ba irin tunanin da bamuyi ba amman ina mun kasa gano dalilin da ze sanya masa ciwon zuciya a k'arancin shekarun da yake da ita. A fari munyi tunanin ko rashin jituwar dake tsakaninsa da matarsa ne kasancewar auran biyayya duka sukayi amman da bincike yayi bincike se muka gano ba hakan bane ciwon son 'yarku Amal ne da ya kasa furtawa kowa."


  "Ciwon son Baby?" Shida Mami suka nanata cike da k'in yarda. 


  "Tabbas na tsawon lokaci Afzal na son Amal amman ya kasa samunta ko ku ya fad'a muku wanda har izuwa yanzu bamu san meyasa ba, kwatsam kuma kawai sega wannan shi Abdul ko?" Ya juya ya kalli Ummi inda ta gyad'a masa kai "Yauwa shi Abdul ya fito yace yana sonta har ya zamanna sunyi nisa da ita Amal d'in, toh wannan ne sababin rashin lafiyan nasa. Ganin su da yake kullum tare kuma ba yadda ya iya, gashi yana ganin lokaci ya riga ya k'ure masa se ya zammana ba aikinsa kullum se tunani, yana mey tak'ura wa kansa yana bin abun a zuciya har wannan ciwo yayi nasara akansa. Sau biyu kenan yake samun attack gashi likitansa yace muddin ba a magance masa wannan matsala ba yana iya rasa ransa idan ya cigaba da samun attack d'in."


  "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Mami ta sake sa wani salatin. 


  "Jiya ina nan ma ai na samu Amal nakeyi mata maganar inda ta tausaya wa halin da Afzal ke ciki ta kuma nuna min zata iya yafe komai saboda ceto ransa dukda cewan bata 6oye mun tsananin soyayyan dake tsakaninta da shi wannan saurayin nata ba amma tace muddin ku iyayenta kun amince ita me iya yafe farin cikinta saboda na Afzal ne. Tabbas mun san Afzal me laifi ne na hadissa duka wannan matsalar, da tun farko ya sanar daku komai da shi Abdul baze ma samu daman shigewa zuciyan Amal ba amma abinda ya faru ya riga ya faru sede ayi tunanin magance ta yanzu haka as we speak Afzal ma ba shida masaniya akan zuwan mu nan. Yanzu haka be ma san mun gano sababin rashin lafiyan nasa ba ma sabida wa amininsa Sultan kad'ai ya fad'awa damuwansa ba yadda bamuyi da shi ba ya fad'a mana meke damunsa amman yak'i da k'yar muka samu abokin nasa ya bamu had'in kai ya kawo mu gidan naku." Nauyayyar ajiyar zuciya both Papi da Mami suka sauk'e as suna mamakin wannan al'amari ashede kukan da Amal ta yini take tayi kenan tun jiya na zafin rabuwa da masoyinta ne, hak'ik'a tana son Abdul. Shi ko Afzal har yanzu sun rasa dalilin da ya hanasa sanar dasu cewan yana son Amal bayan yasan ba wanda ya cancanci soyayyarta sama da shi kodan hidimomin da yake mata. Sau dayawa Papi kan zauna yayi tunanin nan na cewa anya ba son Amal yake ba shiyasa yake mata wannan hidimomi sede tun yana sa ran wataran Afzal zeyi masa maganan Amal har ya dena saboda koda wasa Afzal be ta6a d'auko masa zancenta ba. Toh meyasa? Meya hanasa? Ko gani yake ko da ya furta masu kud'urina  zasu hanasa Amal d'inne? Ai shima yasan baza a ta6a yimasa haka ba toh meya hanasa sanar dasu?


  "Shine muke neman alfarma a gareku, ku kad'ai keda ikon ceto mana ran d'annan idan har Allah ze baku iko, shi kad'ai ne garemu bama son mu rasa sa kuma munsan yadda tambayan hakan agareku ya nuna tsan-tsan san kanmu amman ina da tabbacin duk iyayan da suka tsinci kansu acikin halin da muke ciki haka zasuyi suma" Ummi ta sake fad'a. 


  "Tabbas haka yake Ummin Afzal" Mami ta nunfasa "Nima koda nice na tsinci kaina acikin halin nan da kuke ciki bazan fasa ba har se inda k'arfi na ya k'are. Abu d'aya ne ya d'aure mun kai, dalilin da ze hana Afzal sanar damu k'udurinsa akan yarinyan nan bayan yasan baza a ta6a hanasa ita ba kuma a fari ita kanta Baby nasan bazata k'i sa ba, yanzu gashi tun tafiyanki jiya ta kulle kanta a d'aki tana ta aikin kuka ko ni tak'i sanar dani meke faruwa harta Papinta ma ce masa tayi babu da aka tak'ura mata ne se take ce mana wai Afzal ne bashida lafiya likita yace yana iya rasa ransa dalilin da ke sata kukan kenan amman dukkanmu ba wanda ya yarda da hakan saboda kukan yayi yawa. D'azu shi Abdul d'inma ya shigo kuma ya nuna a shirye yake da ya turo magabatansa anytime aka basa daman hakan, a gaskiya ban san ya zamu 6ullowa al'amarin nan ba. Yaran nan sunyi nisa ba adalci bane mu raba su, ta fannin Afzal kuwa ya cancanci komi a garemu ko saboda halaccin da yayi mana ko duniya yake buk'ata inde muna da ita ya zamo dole mu basa." Sosai Ummi suka ji dad'in maganan Mami suka shiga yi mata godiya. 


  "Toh yanke hukunci de ba namu bane" cewan Papi "Mude zamuyi k'ok'ari muga mun karkato da hankalin ita Baby da Abdurrahman d'in idan sun amince zasu iya yin shahada su ceto mana ran Afzal walillahil hamdu amman nikam bazan iya tilasta Baby auran wanda bata so ba, shi auren dole ba shida amfani kuma kun sani."


  "Wannan haka yake Alhj Muh'd" cewan Abba "Kuma a hakan ma muna godiya sosai and we pray for nothing but the best Allah sak'a muku da gidan aljannah."


   "Ameen wa iyya kum" ya amsa. 


  "So zamu wuce duk abinda akwai dan Allah ga number na" yayi maganan had'e da zaro card nasa daga aljihunsa ya ajiye a gaban Papi "Ka min waya."


  "Toh toh shikenan Allah sa mu dace."


  "Ameen ameen" da haka suka musu rakiya. 


   "Ai dama na fad'a miki iyayen Afzal ne" fad'in Amal dake la6e jikin k'ofansu Falmata tare da ita Falmatan. Tuntuni taso komawa gida amman cin karo da tayi da motar seta fasa gashi kuma kamar yadda ta fad'an ne su Ummi ne. 


  "Yanzu har sunzo sun sami su Papi kenan? Amal ki hak'ura da Ya Abdul kawai nasan da k'yar ki kasance tasa."


  "Falmata I love him I can't do without him."


  "Ya Afzal fa? Kina nufin duk halaccin da ya miki da butulcin nan zaki sak'a masa kenan?"


  "Falmata ban sani ba sun tafi barin k'arisa gida duk abinda akwai zan sanar da ke."


  "Toh se anjima." Tana isa gida Papi ya kirata ta k'arisa ta zauna a tsakankaninsa da Mami. "Uwata ina kika shige?"


  "Na jeni gidansu Falmata ne."


  "Toh tafiyanki iyayen Afzal suka zo suka kuma sanar damu dalilin kukan da kika kwana kinayi a gidan nan tambayata itace meyasa? Meyasa kika k'i sanar dani ko Maminki halin da kike ciki kika gwammace kisha wahala ke kad'anki?"


  "Papi I'm sorry ban san ya zan fara sanar daku bane shiyasa."


 "Ko tunani kike zamu bada ke ga Afzal d'in ko kink'i ko kin so?" A hankali ta gyad'a kanta. "Ko kad'an Baby se wanda kike so zaki aura kinji? Alk'awari na d'auka tunda Maminki ta haife ki na cewa zan kula dake tamkar nine mahaifinki kuma bazan bada ke ba se ga wanda kikeso."


   "Papi ina son Ya Abdul bana son rabuwa da shi" ta fad'a yayinda ta shiga kuka. 


   "Shi ko zaki aura in shaa Allah kinji? Se wanda kikeso zaki aura ki kwantar da hankalinki."


  "Toh Papi Yaya kuma fah? Ya zamuyi da shi? Kana ganin munyi mai adalci kenan bisa ga duk ababen alkhairin da yayi mana a gidan nan? Ace buk'atansa ya tashi amman mun kasa biya masa saboda son kai namu?"


  "Uwata meke tafe a k'wak'walwarki? Kina son Abdul?" Kai ta gyad'a take "Ba kiya kuma son Afzal ya rasa ransa?" Nanma kai tayi saurin gyad'awa "Amma kinsan bazaki iya auran maza biyu ba ko? Dole cikinsu d'aya ya hak'ura koba haka ba?"


  "Hakane Papi."


  "Toh wa zamu ba hak'uri? Dan ni se abinda kikeso zanyi miki."


  "Papi ban sani ba nima I don't want to lose them both."


  "Amman ya zama dole Baby, hungo Jamila ku shiga daga ciki duk hukuncin da kuka yanke shi zamuyi aiki akai." Yace da Mami ba gardama taja hannun Amal suka yi ciki kaman yadda Papi ya buk'ata sede banda kukan da Amal keyi ta k'i cewa komi. Daga k'arshe de Mami ta yanke hukuncin Amal zatayi istikharan kwana uku duk za6in da Allah yayi mata shi zata bi. Amal batayi musu ba ta amince da shawarar cikin dare yau ta fara. 



  2 days later...

    "Assalamu Alaikum" Mami ta fad'a tare da sa kai cikin d'akin Amal. Hawayenta ta shiga sharewa da wurwuri sede ina Mami ta riga ta ganta. K'arisowa tayi ta zauna a gefenta had'e da kiran sunanta. "Na'am" ta amsa sama-sama. 


  "Yau kika kammala istikharan ko?" Kai ta gyad'a a hankali. 


  "Wanne cikinsu yafi kwanciya miki a rai?"


  "Mami..." sekuma ta rushe da kuka, rungumota tayi tana shafa bayanta tana bata hak'uri har seda kukan nata ya lafa. "Waye ne ki gaya mun kinji?"


  "Mami it can't be Yaya it just can't! What of Ya Abdul? Bana son in rasa sa" ta kuma rushewa da wani kukan. 


  "Afzal?" Mami ta ambata da mamaki "Shi hankalinki yafi kwanciya da?"


  "Mami zan sake yin wani istikharan what of Ya Abdul? Me ze sameshi? Waze aure shi?"


  "Baby za6in Allah shine mafi alkhairi idan har hankalinki yafi kwanciya da Afzal toh shine za6in da Allah yayi miki ya zamo dole ki hak'ura da Abdul nakin."


  "But Mami I can't, I love Ya Abdul wallahi ina son sa kuma banjin zan iya rayuwa ba shi dan Allah karki fad'awa Papi wannan za6in zan sake yin wani istikharan."


  "Baby ai ba ayin istikhara sau biyu akan matsala d'ai kuma ina da tabbacin koda kin sake d'inma still Afzal Allah ze za6a miki."


  "Mami dan Allah ki bari in sakeyi please don't tell Papi."


  "Baby-"


  "Mami please" ta rushe jikinta tana kuka, sosai Mami ta tausaya mata daba don za6in Allah yafi ba da se suyi ma Papin k'aryan cewa Abdul ne yafi kwanciya mata a rai a shafe zancen Afzal. "Shikenan bar kukan haka zan sake baki kwana uku ki k'ara yin wani istikharan tunda abinda kikeso kenan."


  "Thank you Mami."


  "Shikenan toh kukan ya isa haka" tayi maganan tana share mata hawayenta. Bayan fitan Mami sega Ya Abdul na kiran Amal, hawayenta ta share ta gyara muryanta sannan ta d'aga. 


  "Halo my princess?"


  "Na'am my Baby good morning."


  "Morning ya kike?"


  "Lafiya k'alau ya office?"


  "Alhamdulillah baki fita school bane yau?"


  "Eh."

 

  "Baby why?"


  "Gobe zan fita in shaa Allah."


  "Toh Allah ya kaimu, Baby har yau bazaki bani date in turo su Baba ba? Ni ko formal introduction akayi I'm satisfied, bana son wani yazo yayi mun awuf dake."


  "Bayan kasan ni kai kad'ai nakeso?"


  "Even still my Princess, du da hakan inason iyayena suzo su sami su Papi."


   "Ya Abdul kad'an k'ara hak'uri kad'an kaji? In shaa Allah very soon zan kasance mallakar ka kaji?"


  "Promise?"


  "In shaa Allah Ya Abdul."


  "Thank you my Amal, I love you so much."


  "I love you even more you take care."


  "You too, bye" da haka sukayi sallama. Kwanciya tayi akan wayan yayinda wasu zafaffun hawayen suke shiga gangarowa akan kumatunta. Tasan 6ata lokacinta kawai take koda ta sake yin wani istikharan still Afzal Allah ze sake za6an mata but why not Ya Abdul? Ta fi son Ya Abdul akan Yaya a tunaninta kodan wannan Allah ze za6an mata shi akan Yaya but why?? Why Yaya? Kuka ta shiga yi a hankali. 


****

   Kwana biyar kenan yau su Abba suna sa ran kira daga gun Papi amman shiru, gabad'aya shida Ummi sun k'osa a fari ma shikam cewa yayi ko zasu sake komawa gidan nasu ne amman Ummi ta ce su k'ara hak'uri su bari zuwa gobe ko jibi idan har basu kirasu ba se su san nayi. Afzal kuwa har yau besan me ake ciki ba, lafiya k'alau suke zama da Nazeefah a gida. Kasancewar be fara fita office ba kafin ta fita school take shirya masa breakfast da lunch idan rana yayi se yayi heating a microwace yaci. 


Washegari...

    Tun shigowan Mami da tayi taga Amal ta baje kan sallaya tana kuka kawai ta yanke hukunci. K'arisawa tayi tare da hugging nata tana bata hak'uri "In shaa Allah Afzal shine za6i mafi alkhairi a gareki hak'uri ya zama dole kinji?"


  "Mami Ya Abdul fah?" Ta d'ago daga jikin Mami tana kuka sosai idanun nata sun kunburo sunyi ja wur. "Shikenan shi ko wacce budurwa yayi ta ringa tafiya tana barinsa kenan? What if shima ciwon zuciyan ya kama sa fa? I'm sure idan ya gano for all these while I've been deceiving him ze kamu da ciwon zuciya kokuwa yayi hauka."


  "Wa yace deceiving nasa kikayi Amal? K'addarace ta rabaku bawai ke kika yi niyyan barinsa ba saboda haka ki kwantar da hankalinki in shaa Allah shi Abdul d'in ze miki kyakkywar fahimta."


  "No Mami no matter what karku sanar da Ya Abdul zan auri Yaya banason ya rasa hankalinsa a sanadin hakan dan Allah kar ku fad'a mishi."


  "Toh ya kikeson ayi Baby? Ayita yaudararsa kenan? The earlier the better."


  "I know amman karku sanar da shi direct I don't care how you do it amman karku fad'a mishi cewan zan auri Yaya wallahi ina gudun abinda hakan ze iya haifarwa."


  "Shikenan zan yima Papinki bayani za'a san yadda za'a sanar da shi amma kibar kukan haka kinji?" Kai zalla ta gyad'a. Isan Mami d'akin Papi ta sanar da shi halin da ake ciki da kuma alfarman da Amal ke nema na cewa kar a sanar da Abdul direct bata son wani abun ya samesa. Dabara ce ta fad'o wa Papi bayan ya kira Abban Afzal ya sanar da shi outcome da suka samu bayan istikharan da Amal tayi Abba yayi ta godiya yace zuwa anjima ko gobe ma zasu shigo. D'akin Amal ya nufa ya buk'aceta numban Abdul inda take sake rok'ansu da komin yaya ne ita kar a sanar da Abdul direct cewa Yaya zata aura. Kwantar mata da hankali Papi yayi akan ta bar masa komi yasan yadda ze 6ullowa al'amarin. Bayan ya amshi lamban nasa ya kira sa tare da masa bayanin shi waye, bayan gaisuwa yake ce masa yana son ganin mahaifinsa idan da hali har ita mahaifiyarsan ma. 


   "In shaa Allah zanyi musu magana duk abinda akwai zan sanar da kai Papi nagode."


  "Nine da godiya Abdul Allah yima albarka."


  "Ameen" ya amsa "Toh se anjima." Isanaa gida can yamma ya watsa ruwa yad'an huta bayan sallan Isha ya samu mahaifinsa a site nasa yake sanar da shi halin da ake ciki. Sosai mahaifin nasa ya masa murna tun ba yau ba yake jiran wannan rana da Abdul ze ce masa gashi ya samu wata se gashi nan Allah ya k'addaro masa da ranan ashe da rabon zega auran d'ansa. In shaa Allahu gobe nida mahaifiyarka zamu je gidansu yarinyan kaji?"


  "Toh Baba nagode."


  "Yauwa d'an albarka ko 'yar wace gida ne?"


   Ba 'yar babban gida bane Baba amman she's from a well respected home."


   "Madallah, zamu je gobe in shaa Allah ko akwai wata matsalar?"


  "A'a shikenan." Da haka yayi masa seda safe ya wuce 6angarensa. Amal ya kira yake ta faman yi mata godiya a tunaninsa gabad'aya wai ita tabada daman ayi wannan formal introduction. Itako bata nuna masa komai ba, hira suka shafa kad'an tayi masa seda safe akan gobe tana da school. Washegari iyayen Abdul sukayo gaggarumin shopping na kayan abinci yadda al'ada ya kawo suka iso gidansu Amal har da shi Abdul d'in. Bayan gaisuwa da hiran da suka d'an ta6a Abdul yayi tunanin basu waje su tattauna dan haka ya fito waje ya shiga mota yana jiransu. Anan ne Papi ya samu daman yin magana.  





RANA D'AYA

#RD


Love... King Miemiebee👄✨

[13/08, 02:16] ‪+234 907 483 8352‬: 🎀🎀🎀                 🎀🎀🎀

                🎀❣🎀

                   ❣❣


  💦💦                      🍃🍃🍃          

           *RANA D'AYA!*

  💦💦                      🍃🍃🍃

  July, 2018

 beeenovels.blogspot.com


     _Written by Miemiebee👄_



   *PAGE 1⃣9⃣*




   Gyaran murya Papi yayi sannan ya numfasa "Iyayen Abdurrahman ku gafirceni, ba abinda kuke sa ran ji daga gareni nake da shirin sanar daku ba" ya ce dasu. Sosai suka shiga cikin rud'ani suka ma kasa cewa komi daga k'arshe de cikin tsan-tsan rashin fahimta Baba ya tambayesa "Ko game da mey Malam Muh'd? Ban fahimceka ba."


  "Zan fara de da neman gafararku nasan ni mey laifi ne amman ku sani banida wata mafitar ne shiyasa, har cikin raina banso hakan ya kasance ba sede k'addara ta riga faruwa."


   "Wannan haka yake" Baba ya amsa dukda cewan ba wai ya fahimci inda Papi ya dosa bane. 


  "Tabbas Abdurrahman yaro ne mai hankali da ladabi da biyayya da kuma sanin ya kamata, d'a ne da kowani mahaifi zeyi kwad'ayin samunsa a matsayin surki sede kana naka Allah na nasa. Da mahaifiyar Amal ta sanar dani batun za6in Amal akan cewa Abdurrahman ne wanda takeso take kuma son ta aura, wallahi nakega ba wanda ya kaini yin farin ciki. Sosai nayi murna saboda yadda ita Jamila ta yaba wa hankalinsa, sede wani hanzari ba gudu ba kwatsam sega wannan yaro Afzal wanda tun kamin had'uwan Amal da Abdul suke tare da Amal bawai as masoya ba a'a yadda dey kuka san shak'uwan dake tsakanin wa da k'anwa, tamkar d'an gida haka yake a gidan nan kusan kullum suna tare da Amal da Maminta. Sau dayawa nakan zauna inyi tunanin anya ko ba son 'yar nan yaron nan yake ba? Amman dai-dai da rana d'aya Afzal be ta6a nuna mana ko ita kanta Amal d'in alamomin da zema nuna cewa yana sonta ba banda hidimomin da yakeyi mata. Sati biyun da suka wuce muke samun labarin cewa ya kamu da ciwon zuciya a sanadin son Amal wanda be ta6a furtawa kowa ba. Na tsawon lokaci ya kasance masoyinta na 6oye amman ba wanda ya samu ya sanar da shi ko iyayensa ya 6oye musu zancen. Haka abun yayita cinsa barin ma idan yazo nan d'in ya tarar da ita Amal da Abdul, sau biyu yanzu kenan yake samun attack wanda shi likitansa ya nuna cewa idan har ba a magance masa wannan matsala ba to yana iya rasa ransa. Satin da ya wuce iyayensa sukazo sukayi mana bayanin halin da yake ciki suke kuma neman alfarma daga garemu na cewa a taimaka musu a had'a shi d'an nasu da Amal don ceto ransa, kar ku manta har anan shi Afzal d'in be san mey ake ciki ba. Da magana ya iske Amal kuwa ta nuna tsan-tsan rashin son rabuwanta da Abdurrahman. A matsayina na me kula da ita yazamo dole ne inyi mata abinda takeso don haka na baiwa iyayen shi yaron hak'uri akan cewa bazan iya tilasta mata auran wanda bata so ba tun farko Afzal d'in shi ya janyo komai da tuni ya d'au mataki akan soyayyar da yake yiwa yarinyar nan da anjima da wuce gurin don ba wanda ze hana sa ita kuma koni na tabbata a fari Amal bazata k'isa ba amman seda ya bari soyayyar wani ya shiga zuciyanta sannan kuma za'a zo a fara tunanin raba masoya biyu? Gaskiya na nuna musu hakan ba mey yuwu ba ne ni iyakan abinda zan iya yi shine in gwada karkato da hankalin Amal da na masoyin nata idan har sun amince zasu iya saudakar da son da suke yima junansu suyi shada su ceto masu ran d'a toh walillahil hamd amman de nikam bazan shiga tsakanin masoya biyu ba. Ita Amal da kanta tazo tayi tunani daga baya ta kuma yi la'akari da kalan hidimomi da d'awainiyyan da shi Afzal d'in yayi mata a baya taga kaman ba a kyuata masa ba idan har ba'a share mai da iyayen nasa hawaye ba. Gabad'aya de ta zamo confused ta rasa me take ciki, gashi bata son rasa Afzal alokaci d'aya kuma bata son rabuwa da masoyinta. Mahaifiyarta nan ce ta kawo shawarar cewa Amal tayi Istikhara duk za6in da Allah yayi mata se ayi amfani dashi. Idan har Abdul ne alkhairi a gareta walillahil hamd dama abinda akeso kenan se a baiwa iyayen Afzal hak'uri idan ko Afzal d'inne alkhairi a gareta se ta rungumi k'addara ta bawa Abdurrahman hak'uri. Yin hakan shine adalci saboda cikin duka 6angare biyu ba wanda zeyi jayayya da za6in Allah. Bayan da Amal ta k'are istikharan ta se za6in ya kasance Afzal amman haka nan yarinyar nan tak'i amincewa da sakamakon ba dan komi ba kuwa se don tsan-tsan son da takeyi wa Abdurrahman da kuma gudun rabuwa dashi. Kuka take tana rok'an mahaifiyarta da a sake bata wani daman ta kuma yin wani Istikharan. Yaushe akeyin istikhara sau biyu akan matsala d'aya inba abunku da yaron da soyayya ya rufe mai ido ba?" Ya tsaya tare da sakin murmushin takaici sannan ya cigaba "Haka nan aka zuba mata ido ta kuma wani istikharan sai dai still za6in d'aya ne Afzal. Gata chan har yau ta na rufe a d'akinta tana kukan rabuwa da Abdurrahman ko makaranta tak'i fita kwana biyu haka nan zata yini a d'aki tana kuka. Yanzu haka ita ta kawo shawaran kar mu sanar da Abdurrahman gaskiyan al'amarin gudun abinda hakan kan iya haifowa gwara idan ku iyayensa ku mai bayani, bata son sanadin hakan wani abu ya samesa. Dalilin da yasa na kira Abdurrahman na buk'aci idan da hali ina son ganinku kenan, nasan ba k'aramin karya muku zuciya wannan labari yayi ba amma dan Allah kuyi hak'uri ku sani bawai nuna banbanci muka soyi ba saboda munga Afzal d'an gida ne ko makamancin hakan kokuwa don kwad'ayin abin duniya muka raba Amal da Abdurrahman, kun deji rantsuwa ba kaffara wallahi da ba don wannan istikharan da 'yar nan tayi ba da ba abinda ze hanani had'ata da masoyinta don a fili ta nuna tafi son Abdul akan shi Afzal d'in dukda kalan hidima da d'awainiyan da yake yi mata hakan be rufe mata ido ba. Ina fatan zaku san yadda zaku sanar da Abdurrahman wannan labari ba tare da tsinka mai zuciya ba kamar yadda Amal ta buk'ata."


  Shiru kukeji a wajen Mama kanma ta kasa magana tsan-tsan tausayawa situation da d'anta ze shiga kawai da takeyi. Ta sani idan har ya gano gaskiyan al'amarin abun bazeyi kyau ba. Wannan karo na uku kenan da yake yin rashi, jikinsa har rawa yake idan yana bata labarin Amal tsabagen yadda yake sonta yake kuma sa ran finally ya samu sanyin idanunsa kwatsam kuma se gashi. Shi de tasa k'addarar kenan, akan 'yan mata to ita fatanta Allah yasa rabuwansa da Amal shine alkhairi a garesa. Baba da jikinsa ya mutu ne shima ya numfasa yace, "Mungode Malam Muh'd da har ka sanar damu gaskiyan al'amarin baka bari kwad'ayin abin duniya ya tsole maka ido ba kayita ja mana rai da d'an namu gabad'aya. Fatana Allah yasa rabuwnshi da Amal shine mafi alkhairi a garesa itako Amal da Afzal Allah basu zaman lafiya."


  "Nagode sosai da kyakkyawar fahimtar da kayi mun dukda cewan nasan hakan da ciwo nima sam ba haka naso abun nan ya kasance ba amman ku k'ara hak'uri abin ne nima yafi k'arfi na wallahi banso sake karyawa d'anku zuciya ba barin ma da Amal take cemun 'yan mata biyun da yayi a baya ma duka bezo ya k'are dasu ba d'aya mutuwa ya rabasu d'aya kuma abin bezo yayi ba, dan Allah kuyi hak'uri."


  "Ba komai Malam Muh'd k'addara ta riga faruwa kuma bazamu iya ja da za6in Allah ba in shaa Allahu zamu san yadda zamu sanar da shi. Abdul yaro ne mey tawakkali ina da tabbacin zeyi muku kyakkyawar fahimta ya mik'a komi wa Allah."


   "Godiya nake Alhj Zarma, Hajiya ina me sake baki hak'uri don Allah" yace da Mama da tayi lamo tun d'azun.


  "Hajiya kiyi hak'uri na gane yanayin da kike ciki amman kiyi hak'uri" Mami da tun da aka fara maganan batace komi ba ta fad'a. 


  "Ba komai Allah sa hakan ne mafi alkhairi ga kowa."


  "Ameen ya Allah" duk suka amsa.


  "Toh bari zamu wuce sede akwai kayakin da suke acikin mota idan da almajirai kusa sesu shigo muku dasu" Baba ya fad'a. 


  "Kayaki kuma? Wasu irin kayaki kenan?" Papi yayi saurin tambaya. 


  "Kayan abinci de da makamancinsu." 


   "Ko meyasa Alhj?"


  "Ji Malam Muh'd kuma da wata tambaya, yadda al'ada ya kawo de muka d'an yo cafani sede kuyi hak'uri ba yawa."


  "Haba! Haba Alhj! Ai idan har muka kar6i kayan nan kuma ya zamo bamuda kunya kenan, baza ayi haka ba yadda kuka taho dashi haka zaku koma dashi mungode sosai da fahimtar mu da kukayi."


  "Kaya an riga an siyo dan ku taya kuma kakeson mu koma da su? Dan Allah kar kace haka."


  "A'a Alhj wallahi bazamu kar6a ba ai be ma yi fasali ba, bayan aure baze auku ba kuma a kar6e kayan gaisuwa? A'a dan Allah."


  "Baka tunanin idan har aka koma da kayakin nan Abdul ze iya fahimtan akwai matsala? Ko ba don wannan bama kaya tunda aka siya da sunanku aka siya idan zakuyi mana adalci ya kamata ku kar6a koda baku so."


  "Hakane Alhj amma-"


  "Kar kaji komi Mallam Muh'd ai na fahimce ka abu ne Allah ya riga ya k'addara ba yadda muka iya so karka damu dan Allah." 


  "Toh Alhj amm-"


  "Dan Allah fa nace" ya katsesa. 


  "Toh shikenan Allah saka da alheri" nan suka rakosu waje inda aka nemi almajirai suka sauk'e kayakin daga mota suka jibge aciki. Kayan abinci ne ba abinda babu, shopping kaca-kaca su Baba sukayi. Godiya sosai su Mami sukayi musu har seda motansu ya fice sannan suka dawo ciki. 


  "Abba wallahi sam banji dad'in wannan abu ba" Mami ta fad'a bayan dawowansu ciki "Baka ga yadda jikin mahaifiyar nasa ya mutu ba wallahi sosai na ji musu ba dad'i barin ma shi Abdul d'in."


  "Tasa jarabawar kenan Jamila se muyi masa addu'a Allah ya basa ikon ci."


  "Ameen hakane kam itama Baby tana cikin tsaka me wuya rabuwa da masoyi babu dad'i."


  "Sosai shiyasa ya kamata mu jata jiki mu nuna mata so sosai don ba k'aramin buk'atanmu take ba yanzu."


  "Hakane bari in shiga daga ciki in sameta."


   "Toh nima barin d'an fita."

   

  "Toh Abba a dawo lafiya." Da haka ta k'arisa ciki ta samu Amal da keta faman kuka har yanzu hak'uri ta shiga bata tana fad'a mata kalamu masu dad'in da zasu kwantar mata da zuciya akan hakan na daga cikin jarabawanta ne itama idan tayi hak'uri ta kar6a hannu bibbiyu tayi tawakkali komi mey wucewa ne. Da k'yar ta samu kukan Amal d'in ya lafa take sanar da ita yanzun Abdul da iyayensa suka tafi bayan nan kuma sunyi gaggarumin siyayyan kayan abinci sun sauk'e musu dukda cewan Papi beso kar6a ba tunda aure ba yuwuwa zeyi ba amman Baban Abdul d'in ya nuna rashin damuwansa ga hakan ya dage lalle-lalle se sun kar6i kayakin. 


  "Toh yanzu ya kenan? Kun fad'a wa shi Abdul d'in kenan?" Ta tambayeta a nitse. 


  "A'a Papinki de ya buk'acesu da su san yadda zasu sanar da shi kaman yadda kika buk'ata so muna fatan zasu san yadda zasu fad'a mishi."


  "Mami bana son rabuwa da Ya Abdul."


  "Rabuwa ya zama dole Baby kede ki dage da addu'a Allah sa za6in nan shine mafi alkhairi a gareki nima zan tayaki da addu'a kinji?" Kai ta gyad'a a hankali had'e da kwantar da kanta akan cinyan Mami tana share hawayenta. 



*****

   Tun isansu Mama gida suke tunanin yadda zasu 6ulloma wannan al'amari tabbas Amal masoyiya ta hak'ik'a ce da har tayi tunanin cewa breaking wa Abdul news d'in haka kai tsaye na iya jefa rayuwarsa cikin matsala. Toh yanzu ya zasu 6ullowa al'amarin? Ya zasu fara sanar da shi Amal bazata iya auransa ba? 


   "Alhj bansan ya zanyi da Abdul ba wallahi ina mugun tausaya masa, bakaga yadda yakeson yarinyar nan ba ko hirarta yake mun jikinsa rawa yake don murna kawai."


  "Dama kina da labari?"


  "Ai har waya ya ta6a had'ani da yarinyar kuma itama tana sonsa wallahi wannan abu beyi ba."


  "Tasa k'addarar kenan akan 'yan matan da yakeso se muyi masa addu'a kaman yadda ya ci na baya ya sake cin wannan d'in."


  "Hakane Alhj amman gaskiya Amal nada kaifin tunani da tace kar ayi masa breaking news d'in kai tsaye wallahi nima tsoro nake idan kuma shima ciwon zuciyan ta kamasa fa? What of idan ya samu k'aramar hauka?"


  "Subhanallah ya kike magana haka Binta? In shaa Allahu ze fahimce mu."


  "Gaskiya a'a Alhj bana son abu ya samu Abdul kasan ya za'ayi kawai amman de kar a sanar dashi kai tsaye haka."


  "Ya kikeson ayi toh Binta? A cigaba da zolayarsa kenan? Har izuwa yaushe? I think the earlier the better."


  "Yes the earlier the better amman kuma sanar dashi kai tsaye Amal bazata aure shiba ba k'aramin hatsari bane wallahi ni nasan yadda yakeson yarinyan nan I'm very sure news d'innan zeyi devastating nasa ka yarda dani."


  "Toh Binta ya zamuyi?"


  "Ban sani ba amman we have to think of a way bana son abu ya samu Abdul."


  "Toh shikenan zamu tsaya muga me Allah ke ciki ko kafin nan da next week 6ullo mana da wata solution d'in."


  "Yauwa toh hakan yafi."


****. 

   GIDAN ALHJ AMIN (Abban Afzal)


  "Assalamu alaikum" Afzal yayi sallama had'e da sa kai cikin parlourn. 


  "Wa'alaikumus salam" Abba dake zaune a gefen Ummi ya amsa. "Bismillah k'ariso ciki." A nitse ya tako ciki ya nemi gu ya zauna had'e da gaishesu duka. 


  "Ya jikin naka?" Abba ya tambaya bayan nan. 


  "Alhamdulillah da sauk'i Monday zan fara fita office in shaa Allah."


  "Toh Allah k'ara sauk'i."


  "Ameen Abba nagode."


  "Dama magana nakeso muyi na turo akira ka."


  "Toh Abba ina ji."


 "Kafin nan d'ago kanka ka kalleni inason ina kallon cikin idanunka idan ina ma magana" beyi gardama ba ya d'ago kansa. 


  "Shin wani irin zama kakeyi da matarka Nazeefah a gida?"


  "Lafiya k'alau" ya amsa take. 


  "Kar kayi tunanin yimun k'arya Afzal" ya kirasa da asalin sunansa "Nace wani irin zama kakeyi da Nazeefah? Shin kana kula da ita a matsayinta na wacce take k'ark'ashinka? Shin kana bata hak'k'inta a matsayinta na matarka? Kana kula da tufafin da take sanyawa da kuma kalan mutanen da take mu'amala da su? Shin ka kafa mata dokokin da na miji ya kamata ya kafawa matarsa don kare ma kansa mutunci da ita kanta matar?"


  Shiru Afzal yayi don acikin ababen da Abba ya irgo idan akwai d'aya da yakeyi me kyau shine ciyar da Nazeefah da yakeyi se bata tufafi bayan nan ba komai again. 


  "Da kai nake magana Afzal."


  "Abba I'm trying, ina iya k'ok'arina don ganin nayi improving relationship namu I just need some space."


  "Lokaci? Lokaci fiye da shekara d'ai Afzal? Koma me de kasani duk abinda kakeyi a gidan Allah na kallonka muddin idan kai kake toye mata hak'k'i to fa Allah baze barka ba dan Allah baya barin a ci mai alhak'in bawa kaji ka sani idan ko ita ke tauye maka hak'k'i itama Allah baze barta ba."


  "Na sani Abba."


  "Bayan nan tun wuri ka zubar da wannan banzan d'abi'ar taka ta zurfin ciki wallahi banda halaka ba inda zata kai ka. Ace ina matsayin mahaifinka in tambayeka fiye da sau uku meke damunka amman ka bushe mun ido kace kai babu bayan soyayyar yarinya ke neman halaka ka? Toh koma me kake 6oyewa kasani munyo bincike kuma mun gano bakin zaren. Kuma wallahi sa'anka d'aya ne na cewa da likitanka yayi idan har ba a magance maka wannan matsala ba kana iya rasa rayuwanka idan ba don haka ba da na barka kasha d'an banzan wuya k'arshe shi Abdul ya aure Amal d'in a idonka muga ko zaka soma yawo tsirara akan hanya. Kana son mutum amman bazaka iya samunsa ka fad'a masa ba chan kuma ka bugi k'irji kace kai na miji ne? A ina aka ta6a yin hakan? Toh ka bud'e kunnuwan nan naka ka saurareni da kyau tun wuri idan kasan bazaka iya rik'e mata biyu ba ka fad'a min kar kazo kayi mun abin kunya."


  Gabad'aya kan Afzal ya d'aure ya rasa inda Abba ya dosa "Mata biyu kuma Abba?"


  "Eh matar mutum kabarinsa duk yadda Amal da iyayenta suka so kasancewarta da saurayinta Abdul Allah beso hakan ba ya za6ar mata kai a matsayin mijinta na aure bayan istikharan da takeyi har sau biyu just to tell you how much she loves that Abdul. Afzal ka bamu wuya kasa mun nuna son kai a fili na neman raba wannan masoya biyu. Shine tun wuri idan kasan bazaka iya yin adalci ba tsakanin yaran nan ka fad'a mun kar mu fara abinda baza mu iya k'arasawa ba."


  "Abba ban fahimce ka ba, kana nufin kai da Ummi kunje kun samu Amal da iyayenta akaina?"


  "Ban sani ba ko ka daina jin hausa da yamma."


  "Abba why? Abba ba lallai bane se Amal ta aureni tunda kaima da bakinka ka fad'a ba yadda ta iya ne, ina amfanin tilasta ta against her wish? A gani na hakan ba shida fa'ida. Nagode da d'awainiyan da kai da Ummi kukayi mun amman a gani na is better a bar Amal ta auri wanda takeso."


  "Kai kuma se kayi ya da ran naka da kuma son da kakeyi matan?"


  "Zan hak'ura Abba, haka Allah ya k'addara kenan amman banason in zame sanadin k'unci da bak'in ciki a rayuwan Amal."


  "Na yaushe kuma? Da tun farko da ka gano kana sonta ka tinkareta ka fad'a mata ai da du hakan be faru ba yanzu sede ayi maganan yadda za'ayi ka gyara kuskuren da kayi dan kuskure de kam ka riga kayita saboda haka nakeson gobe ka shirya kaje gidansu ka yima iyayenta da ita kanta godiya ka kuma basu hak'uri musamman ma ita Amal ba k'aramin jarumtaka tayi ba na saudakar da farin cikinta maka kaima ka sani ba sena fad'a maka ba."


  "Abba I'm sorry amman bana tunanin I can do this."


  Da mamaki both Ummi da Abba suka tsaya suna kallonsa. "Kana nufin duk hidiman da mukayi maka a banza ze tashi kenan?" Ummi ta tambayesa da mamaki shikam Abba yama kasa magana. 


  "Ummi kuyi hak'uri ba wai zuwa gidansu Amal in basu hak'urin bane bane bazan iya ba."


 "Mey toh?" Ta kuma tambayansa yayinda Abba ya kafa masa ido. 


  "Ummi bazan iya rik'e mata biyu ba Allah ma shaida ne bazan iya ba."


  "Kasan da hakan ka kwad'aita wa zuciyarka soyayyan Amal bayan kana da mata a gida?"


  "Ummi inda zan iya hana zuciya na son Amal da nayi hakan da jumawa amman ba daga ni bane, I really tried but abun ya gagara."


  "Ya zamo dole kenan kaman yadda kowa ma ya hak'ura kaima ka hak'ura ka san ya zaka koyi zama da mata biyu ko a jinka bamu da aikin yine feee se mu d'ibi k'afa mu sake komawa gidansu Amal muce musu gashi kai kace bazaka iya zama da mata biyu ba? Ka sani don lafiyarka muke yin komai Afzal idan ba don haka ba wallahi ko kallonka ma bazanyi ba nide na fad'a maka gobe kaje gidansu Amal ka bata hak'uri da iyayenta tun wuri kuma ka fara koyan zama da mata biyu kana iya tafiya." Abba yace da shi cike tsiwa. Daga yadda yake magana a san ransa ya 6aci. A raunane Afzal ya mik'e ya fice ko hak'uri ya kasa bawa mahaifin nasa. Ummi ce tabi bayansa tare da kiransa, site nata ta jasa suka wuce inda suka zauna akan kujera. 


  "Prince meyake damunka? Tun da kayi aure ban sake gane kanka ba, ko ka manta ni mahaifiyarka ce da kake gudun gaya mun damuwanka haka?"


  "Ummi ba haka bane."


  "Toh yaya ne? Kana son Amal ko baka sonta?"


  "Ummi it doesn't matter."


  "Yes it does kana sonta koko a'a?"


  "Ummi kema kin sani, I love her, I love Amal."

 

  "Meya hanaka sanar damu tun wuri toh da muke tambayanka?"


  "Saboda bansan ya zan fara zama da mata biyu ba I can't Ummi."


  "So kake ka saki Nazeefah kenan seka kawo Amal?"


  "Sam ba haka bane Ummi, Nazeefah bata min komai ba idan da adalci be kamata in saketa haka kawai ba don zan auro wata."


  "Toh seka had'asu su biyu ai dama tun kafin auran naku ma Abbanka yayi maka alk'awarin cewa kowa ka kawo daga baya kace kanaso za'a aura maka ita."


  "Ummi ina sane da hakan."


  "Amma abinda kayi ma Abbanka banji dad'insa ba ya kamata ka basa hak'uri."


  "Ummi I'm sorry amman bazan 6oye miki ba banji dad'in zuwa gidansu Amal da kukayi ba tare da kun sanar dani ba."


  "Ai ba wai haka kawai aka k'i sanar da kai ba Prince kai kanka kasani idan da mun sanar da kai bazaka yarda ba aje gidan nasu, kasani idan fa kai baka damu da halin da kake neman jefa rayuwarka aciki ba mu nan mun damu da kai. Ko ajinka idan ka cigaba da samun attack d'in zaka rayu ne? Wataran zuciyan na iya bugawa kuma tak'i tashi se lahira kenan. Mey kakeson ace damu? Iyayen da suka kasa magance wa d'ansu tilo damuwa? Abu d'aya nake so da kai Afzal ka rage zurfin cikin nan naka duk abinda yake damunka tell me I'm just a call away komin yaya ne zan san yadda zanyi in share maka hawayenka."


  "Ummi thank you and I'm sorry."


  "Ba komai ya wuce bayan nan kuma ina son ka daidaita tsakanin ka da Nazeefah ka sani idan kana tauye mata hak'k'i Allah baze barka ba, a matsayin matarka take dole ne kana biya mata buk'atunta ka kuma bata lokacinta only then Allah ze sa maka hannu acikin al'amuranka ya shige maka gaba."


  "In shaa Allah Ummi thank you."


  "Yanzu kaje ka bawa Abbanka hak'uri gobe in Allah ya kaimu seka jeka gidansu Amal d'in kaji?" Kai ya gyad'a a hankali "Very good." 

  Mik'ewa yayi tare da yimata se anjima ya fice, site na Abba ya nufa ya samesa zaune kaman yadda ya barosa. Durk'usawa yayi ya basa hak'uri se a karo na biyu Abba ya amsa tsabagen yadda ransa ya 6aci. Hak'urin yayita basa amman Abba ya nuna masa ba komai. 


   Isansa gida keda wuya ya shige d'akinsa had'e da mik'ewa akan gado se tunanin abinda Ummi ta fad'a masa yake. Ya sani sarai Sultan ne ya sanar dasu komai bama amfanin kiransa ya tambayesa. Bayan da ya dawo daga sallan isha ne ya tsinci Nazeefah zaune a parlour tana yin assignment nata. Sannu da zuwa tayi masa bayan ya amsa ya k'arisa inda take zaune akan rug yayi tsaye a kanta. Kai ta d'ago da mamaki tana kallonsa amman bata ce komai ba hannunsa biyu ya mik'a mata da nufin ta kama ya mik'ar da ita sede don mamaki tama kasa koda kyafta ido. "Come" ya buka'aceta biron nata ta ajiye sannan a hankali tasa hannayenta cikin nasa ya mik'ar da ita. Da hannunta cikin nasa yayi gyaran murya sannan ya kira sunanta. 


  "Na'am" ta amsa. Idanunsa ya d'ago yana kallon cikin nata idon sannan a hankali ya furta "I'm sorry."


  Mamaki ne ya rufeta kum tama kasa koda magana da fari ma tayi zaton kode aljanu ne suka shigesa yake bata hak'uri, toh ma hak'urin mey?

   "Afzal" ta kira sunansa a hankali. 


  "I'm sorry kinji? Starting today we'll be living a happily married life in shaa Allah." Dan murna tama kasa cewa komai kawai rungumesa tayi yayinda hawaye ya ciko mata a ido, "Afzal I'm sorry too, forgive me also."


  "Shhh!" ya buk'aceta had'e da hugging nata back sun kai kusan minti d'aya a haka sannan ya zame jikinsa had'e da share mata hawaye "Banda kuka kinji?" Kai ta gyad'a a hankali tana mai murmushi "I'm hungry akwai abinci?" Yayi maganan yana lek'an dining space. 


  "I'm sorry gabad'aya hankali na ya tafi akan assignment d'innan bari yanzu inje in dafa maka macaroni akwai stew na rana senayi heating."


  "Ki bari ki gama assignment d'in tukuna kinji?"


  "But kace kana jin yunwa."


  "I can wait finish up first."


  "Are you sure?"


  "Yes" ya amsa yana mata murmushi. 


  "Alright bari inyi sauri saura kad'an dama."

 

  "Okay barin watsa ruwa nima" mik'awa yayi had'e da placing mata light kiss a goshi sannan ya wuce. Mutuwan tsaye Nazeefah tayi gun yayinda farin ciki ya mamaye mata zuciya, ji take tamkar duk duniyan ba wanda ya kaita murna. Nan da nan ta k'arisa assignment natan ta wuce kitchen. 


   Washegari da yamma Afzal ya shirya tsaf cikin half jamfa maroon color ya feffeshe jikinsa da turare ya janyo k'ofar d'akinsa ya fito. 

  "Zan fita" yace da Nazeefah dai-dai lokacin da ya k'ariso parlourn. Sosai gabanta ya fad'i mostly idan yayi wanka haka da yamma gun zance yake wucewa ya zatayi yanzu? Gashi bata son da zaran tayi masa magana hakan ya haifar masu da wani fad'an dan haka kawai ta danne zuciyanta tace, "A dawo lafiya kayi kyau."


 "Thank you" ya amsa da murmushi sannan ya fice. Gidansu Amal ya wuce direct inda yayi parking ya shige. Mami da Papi ya tarar a tsakar gidan suna zaune. K'arisawa yayi ya tsuguna daga waje-waje had'e da gaishesu. 


  "Kuma ka tsuguna daga chan ka k'ariso ciki mana" Papi yace dashi ba musu ya k'ariso ya zauna daga bakin tabarman inda suka sake gaisawa da kyau. 


  "Ya jikin naka? Ka warware ko?"


  "Alhamdulillah" ya amsa. 


  "Shine ka k'i mu kwana biyu ko?" cewan Mami. 


  "Ba haka bane Mami kuyi hak'uri."


  "Gashi ka shigo Amal ta fita bata nan."


  "Ayya dama gunku nazo kafin nan."


  "Toh toh madallah" Papi ya amsa. 


  "Papi, Mami kuyi hak'uri nasan ni mey laifi ne amma d'an Adam ajizi ne ku gafirceni."


  "Ba komai Afzal komi ya riga ya wuce Allah sa hakan shi yafi alkhairi kawai."


  "Ameen nagode, Mami bakice komai ba ko senayi tsallen kwad'o tukuna?"


  "Ai ko abinda za'ayi kenan ace yadda muke da kai amman kana son Amal ka kasa furta mana Afzal? Har seda ciwo ya shige ka? Nakega tsallen kwad'on nan zan saka shine punishment naka."


  "Yi hak'uri Mami, Papi ka tayani bata hak'uri."


  "Wasa take maka ta hak'ura da jimawa itama yauwa nace ya batun matarka ta gida?"


  "Lafiyarta k'alau."


  "Shin tana sane da abinda ake ciki kuwa?"


  "A'a Papi amman idan lokacin yazo zan sanar da ita."


  "Kana ganin baza a samu matsala bako? Kasan shi rik'e mata biyu ba abu neba na wasa."


  "Tabbas Papi ina fatan Allah ze bani ikon yin adalci a tsakaninsu."


 "Toh Allah taimakeka Afzal kasan Amal yarinya ce se anayi ana hak'uri."


  "Karka damu Papi zan kula da Amal in rik'eta amana se inda k'arfi na ya k'are."


 "Na amince da kai Afzal dan Allah kar ka bani kunya ga Amal nan mun baka ita kaman yadda kake kula da ita da a baya ina fatan zaka k'ara himma yanzu da ta kasance mallakinka."


  "In shaa Allah bazan baku kunya ba Papi, you have my word."


  "Sekuma abu d'ayan da ya d'aure mun kai."


  "Ina jinka."


  "Inason jin dalilin daya hana ka sanar damu k'udurinka akan Amal." Shiru yayi be amsa ba "Afzal?"


  "Papi banason in zame mata distraction ne having that karatun nata beyi nisa ba, dalili na daman in bari idan tayi nisa da karatun se in fayyace mata koma mey ke tafeni kwatsam kuma sega Abdul abinda ya hanani sanar da ita kenan."


   "Kayi gaskiya amma da ko nine seka sameni ka fad'a mun ba lallai se ita Amal d'in ta sani ba."


  "Hakane Papi nayi kuskure amman ina sake baku hak'uri, kuyi hak'uri."


  "Allah sa mu dace."


 "Ameen bari in fita waje in jira Amal."


  "Shago ma fa taje bansan meya ajiyeta haka ba" cewan Mami yayinda Afzal ya mik'e. "Toh se anjima."


   "Ka gaishe da Abbanka."


  "Toh zeji in shaa Allah" da haka ya fice yaje ya tsaya gun motansa inda yake kallace-kallace chan ya hango Amal daga jikin wani shago. K'arisawa yayi ya tsaya daga bakin k'ofar yayinda take ce da me shagon ya bata pad, dai-dai ya mik'a mata ta juya tana shirin sanyawa acikin leda kenan se kawai sukayi ido hud'u da Afzal dake tsaye a bayanta wane wani aljani. Wani irin ruwa cikinta ya d'ura ga kuma kunyan da ya rufe ta duka atake, yasar da ledan kawai tayi abun nata ya fad'i a k'asa. Dukar da kanta tayi cike da kunya. Kafin yace zeyi mata magana har tabi gefensa da hanzari ta wuce murmusawa yayi gano kunyansa taji sannan ya tsuguna ya d'au abinda ta yasar d'in ya sanya cikin ledar ya shiga binta a baya yayinda take ta hanzari ta k'arisa gida. Taku guda biyar yayi masu kyau ya kamato, hijabinta ya rik'e hakan ya sa ta tsaya ba tare da ta juya ba. 


  "Lily?" Ya kira ta amma tak'i juyawa. Takowa yayi ya k'ariso gabanta tare da tare k'ofar gidan nasu don karta shige, kanta tayi saurin kawarwa. 


  "Lily taya kikeson in fara baki hak'uri tunda ko kallona bakiya son yi? I'm sorry kinji?" Se shiru tak'i koda kewayowa ta kallesa. "I should go down on my knees? I should?" Ya tambayeta nan ma shiru. "Okay" ya furta yayinda ya shiga sauk'a k'asa. 


  "Don't Yaya" tayi saurin katsesa kafin ya gama sauk'an. 


  "Then turn and look at me" sede har anan d'in ta kasa. Sarai kuma yasan kunya takeji har yanzu na ganinta da yayi tana sayan abin chan. Kawai ji tayi ya d'aga hannunta ta cikin hijabin ya sanya mata ledan aciki "Taho kinji?" Ya buk'aceta. 


  "Ina sauri zan shiga gida" ta furta a hankali. 


  "Lily nasan ni mey laifi ne amma idan kika cigaba da shareni haka ya kikeson in nemi tubarki? Please come down with me" bata sake yin musu ba tabarsa ya jata zuwa kan benchin dake wajen gidan nasu. Bayan data zauna shima ya zauna a gefenta. 


  "I'm sorry, I'm so sorry Lily ban san ta ina zan fara baki hak'uri ba I know I've wronged you in so many ways but I'm sorry, I'm sorry for making you pass through all those pains kiyi hak'uri."


  "Ba komai ya riga ya wuce" ta amsa ba tare da ta kallesa ba.


  "Lily mey zanyi kiyi hak'uri ki kalleni? Yaya is sorry."


  "It's really okay" ta amsa had'e da juyowa tana kallonsa. 


  "Thank you, Lily na san yadda kika tsaneni yanzu and I don't blame you ni na janyo komai, if only I could stop myself from loving you I would have ko dan kar in shiga tsakaninki da Abdul."


  "Ka dena kawo maganansa."


  "I'm sorry I really am."


  "Why didn't you tell me for all these time Yaya?" Ta tambayesa. 


  "Saboda nasan bazaki amince dani ba" ya amsa take. 


  "Meyasa kace haka?"


  "Saboda kina son Abdul."


   "Ina nufin kafin mu had'u da Ya Abdul."


  "Nima ban san mey ya hanani ba Lily but maybe kodan kunya nakeji."


  "Kunya?" Ta tambayesa da mamaki. 


  "Yes Lily I'm not your Yaya after all tunda har na bari zuciyata ta koyi sonki, ke kin iya kinyi respecting relationship namu ni kuma na kasa yin hakan har na bari soyayyarki tayi nisa a zuciyana, I felt disgusted at myself na rasa da wani idon zan sake kallonki and now I feel so sorry na shiga tsakaninki da Abdul da nayi, wallahi ban san su Abba sunzo nan ba se jiya yake sanar dani. Amal bana son in kasance sanadin k'unci da rashin walwala a rayuwarki if you know you can't find a place in your heart for me please tell me I can bring back Abdul for you, farin cikinki yafiye mun komai, we marry because of love not pity, ba sekin aure ni ba idan bakiya sona I will understand you."


 "Lafiyanka kuma fa Yaya? Ko ka manta mey likitanka yace? Bana son in rasaka Yaya, bana son a sanadi na ka rasa raywanka."


  "Karki damu dani Amal ai ciwo ba mutuwa bace."


  "In your own case mutuwa ce Yaya, bazan iya ba, bazan iya yafewa kaina ba idan har a sanandi na wani abun ya kuma samunka."


 "Abdul fa? Don't you love him?"


  "Yaya I'm sorry" kawai se ta rushe da kuka "But I do love Ya Abdul, I really love him so much" ta sanar dashi cikin tsananin kuka. Har cikin zuciyarsa yaji zafin kalamun nata yayinda sautin kukanta ke tada masa hankali. Mey matakin da ya kamata ya d'auka? Yana son Amal yana son kasancewa da ita amma meye amfanin ajiyeta a gurinsa idan har zuciyarta na tattare da wani daban? Sosai ya tausaya mata barin ma da yaga yadda take kukan cira rai. Ji yayi gabad'aya ya tsani kansa na jefata cikin wannan hali da yayi. Da ya sani da tun farko ya sanar da ita abinda yake zuciyansa kokuwa da ya gano tana da wanda takeso ya tattara ina inasa yabar musu garin inda hali k'asar ma gabad'aya. Sautin kukan ne ya ishesa ya shiga kiran sunanta a hankali. 


  "Yaya I'm sorry but I don't think I can do this" tana fad'in haka ta mik'e a guje ta wuce ciki ko ta kan su Mami batayi ba ta nufi d'akinta had'e da sa sakata ta kwanta kan katifarta ta shiga rera kuka. 




RANA D'AYA!

#RD


Love... King Miemiebee👄✨

[13/08, 02:18] ‪+234 907 483 8352‬: 🎀🎀🎀                 🎀🎀🎀

                🎀❣🎀

                   ❣❣


  💦💦                      🍃🍃🍃          

           *RANA D'AYA!*

  💦💦                      🍃🍃🍃

  July, 2018

 beeenovels.blogspot.com


     _Written by Miemiebee👄_



   *PAGE 2⃣0⃣*


   _My dearest Aunty Sis where're you? Here's a page I'm devoting in your honour, know that your daughter loves you hell much, Xx._ 😘



   

   Sosai kan Mami da Papi ya d'aure barin ma ganin yadda ta shigo a guje da sukayi ko amsa kira batayi, toh kode wani abun ne ya bita? Da wuri Mami tabi bayanta ta lek'a waje don tabbatar da me ke faruwa chan kawai ta hango Afzal zaune kan benchi ya had'a tagumi. K'arisawa tayi ta zauna a gefensa sede har anan be lura da cewa ma wani ya zauna kusa da shi ba. "Afzal?" Ta kira sunansa se a karo na biyu ya amsa a firgice. 


  "Lafiya?" Ta tambayesa. Sam be 6oye mata mumunan halin da yake ciki ba. "Ba lafiya ba Mami" ya amsa tamkar wanda zeyi kuka. 


  "Meya faru? Kai da Baby ne? Yanzu naga ta shiga ciki a guje wani abun ne?"


  "Mami Amal bata sona sam bata sona Abdul take so it breaks my heart watching her cry like this I can't take it anymore."


  "Laaa! Bade kukan kai ma zaka yimun ba?" Ta tambaya da mamaki. 

  

  "Mami no." 


  "Toh ya kakeson ayi kenan?"


  "Ni zan hak'ura yaso ta auri Abdul d'in kawai, farin cikinta ya fiye mun komai."


  "Kaman yadda kaima lafiyarka ya fiye mata komai ba."


  "Mami she's hurting alot please ku barta ta auri wanda zuciyanta keso."


  "Yaushe ne zaka gane kaine za6in da Allah yayi mata Afzal? Kuma yanzu da kake biye mata d'in kai kuma ya zakayi da naka ran? Idan ban manta bafa likitanka ne yace rashin magance maka wannan matsala yana iya saka rasa ranka koba haka ba?"


  "But Mami Amal's happiness comes before anything my life included."


  "Kar ka kariya Afzal kar ka bari tausayinta ya rufe maka ido tabbas Amal abar a tausaya mata ce amman kai be kamata ka kariya haka gabad'aya ba. Amal na buk'atanka yanzu. Idan har bata sonka ya zame dole kenan ka koya mata. Mu mata munada laushin zuciya garemu, abu kad'an yakan karakato mana da hankali hak'uri zakayi ka nuna mata tsan-tsan so hakan ne kawai zesa ta iya mancewa da Abdul ka kuma maye gur6insa a zuciyanta amma idan ka kariya haka ai kaman ka bata dama ne ta cigaba da kewan Abdul d'in koda yaushe, Amal taka ce Afzal."


  "Mami bana son ina ganinta cikin k'unci da hawaye haka duk laifi na ne gashi yanzu Amal ke shan wuya."


  "Ka dena cewa haka Afzal kuskure de an riga anyisa ba kuma amfanin nanatasa kaide yanzu ne ya kamata ka nuna jarumtakarka wajen tabbatar da cewa Baby ta mance da Abdul idan ko kayi sakaci..."


  "Thank you Mami."


  "Karka damu duk lokacinda kake buk'atan wani abu kar ka 6ata lokaci ka taho ka sanar dani damuwanka ina nan zan kuma yi iya k'ok'arina inga na magance ma wannan matsala kaji?" 


  "Thank you so much."


  "Ba komai zaka shiga ciki kokuwa?"


  "A'a zan wuce gida but please ki samu Amal ki bata hak'uri tabar kukan haka nan."


  "In shaa Allah" da haka ta rakasa gun motarsa bayan ya fice ta dawo ciki ta wuce d'akin Amal sede duk suratan da take tayi Amal tak'i tasowa ta koda bud'e mata k'ofar se kuka kawai take, k'arshe seda Papi yace ta hak'ura ta barta kawai. Tambayanta yayi ko meke faruwa inda ta zauna ta zazzage masa komai. Sosai ya tausayawa Afzal d'inma kansa tabbas ya cika masoyi na k'warai shima da har yake tunanin saudakar da rayuwansa gabad'aya saboda farin cikin Amal sede kaman yadda Mami ta fad'a kada ya kariya ya cigaba da nuna mata so a hankali zata koyi sonsa shima ta kuma manta da Abdurrahman. 


  Tun isan Afzal gida Nazeefah ta lura da yanayinsa gabad'aya ba walwala tattare da shi sa6anin yadda ya fita. Ko da tayi masa tayin dinner ma cewa yayi a k'oshe yake baze ci ba ya wuce d'akinsa amma bata sauraresa ba ta d'iban masa abincin ta d'au ruwa a fridge ta nufi d'akinsa. Knocking tayi bayan ya amsa ta shiga ciki. Tsince akan gadonsa ta samesa da wuri ya 6oye wayansa dayake ta faman kallon hotunan Amal k'ark'ashin pillow. Bayan ta k'ariso ta ajiye masa abincin akan side drawer tare da buk'atansa ya tashi ya ci. Beyi musu ba ya mik'e ya zauna. 


  "Wani abun ne yake damunka Afzal?" Ta tambayesa cikin siririn murya. "Feel free to talk to me kaji? I'm here."


  "Ba komai Nazeefah" ya amsa a sakalce. 


  "Taya zakace ba komai bayan gabad'aya ba haka ka fita kabar gidan nan ba."


  "Just pray for me kinji? Allah shige mun gaba."


  "In shaa Allah I'll ga abincinka kaci kar ka kwanta akan yunwa."


 "Thank you."


  "You're welcome akwai wani abinda kake buk'ata?"


  "Not at all."


"Alright ina parlour idan kana buk'atan wani abun." Kai zalla ya gyad'a mata yayinda ta mik'e ta fice. Abincin ya janyo ya shiga ci a hankali yayinda yake ta tunanin Amal. 


  Washegari...

   GIDAN ALHJ A. ZARMA. 


  "Assalamu alaikum" Abdul yayi sallama cikin parloun Baba inda shi da Mama suke zaune. 


  "Wa'alaikumus salam" duka shi da Mama suka amsa. K'arisowa cikin parlourn yayi sannan ya zauna a inda ya saba zama kullum "Sannu Mama"


  "Yauwa Abdul har kun taso?"


  "Eh, sannu Baba ka kirani."


  "Eh Abdul ya office?" 

 

  "Alhamdulillah."


  Gyaran murya Baba yayi ya cigaba "D'azu manager'nku yake mun wata magana akan yana son yi maka transfer zuwa Canada ko ya gaskiyan al'amarin yake?"


  "Tabbas yamun maganan amman ban kar6i transfer letter d'in bama bana so I'm not interested."


  "Dalili?" Ya tambaya da mamaki. 


  "Baba banason inyi nisa da gida most importantly bana son inyi nisa da Amal."


  "Ya kake magana haka Abdul sekace idan ka tafi ba za ka sake dawowa ba?"


  "Baba duk da hakan bana so I'm okay with my job in here."


  "Ka dubi kyan aikin fa Abdul ka kuma sani dama sau d'aya yake zuwa a rayuwa. Shi kansa manager'n naku cemun yayi dayawa sun samesa suna rok'ansa da ya basu aikin amman ya duba zumuncin dake tsakani na da kai ya d'auka ya baka amma kace kai baka so? Gaskiya be kamata kayi wasa da wannan damar ba, aikin tana da kyau albashi hud'u zuwa biyar fa shikenan ka zama DON (mey bala'in kud'i) na kanka ka sake tunani ai idan mu kake gudun yin kewar mu bature yayi video call idan ma Amal takan ce kuna iya yin video call da ita ko ba haka ba?"


  "Hakane Baba amma ai aikin nan nawa ma nada kyau."


  "Bance batada kyau ba amma sanin kanka ne ai bazaka had'a kyan albashinsa da shi na Canada d'in bako? A gaskiya tunaninkan nan beyi ba koba haka ba Hjy Binta?"


  "Hakane Alhj, Babana Abdul?" Ta kirasa. 


  "Na'am Mama."


  "Kabi shawaran Babanka kar ka bari wannan dama ta wuce ka this is your chance to build yourself into the millionaire you've always wanted zamu baka nan zuwa jibi ka zauna kayi tunani kaji?"


  "Toh Mama nagode Baba zanyi tunani in shaa Allah I'll get back at you."


  "Allah yima albarka Abdul."


  "Ameen Baba nagode zan wuce site d'ina."


  "Toh ka huta gajiya ko?" Yana ficewa Baba ya sauk'e nauyayyar ajiyar zuciya "A gaskiya keda Amal kunyi gaskiya Hjy Binta yanzu fa saboda yarinyar nan ne bayison tafiya bawai saboda mu ba."


  "Ai na fad'a maka he's so attached to her Allah kawo masa sauk'i."


 "Ameen."


  "Amma Alhj idan har yak'i amincewa fa? Ya zamuyi? Plan namu beyi ba fa kenan."


  "In shaa Allah zeyi ai aikin na da kyau."


  "Toh Allah yasa, kaga idan muka samu ya tafi yanzu se ita Amal d'in ta canza layinta gabad'aya yadda komin ya yakeson samunta baze iyaba ita kuwa Maamah komin ya zeyi da ita akan ta nemo masa new line na Amal zance kar ta basa, this's the only way nake ganin ze iya rabuwa da Amal cikin sauk'i."


  "In shaa Allahu wannan shawara taki tayi Hjy Binta Allah sak'a maki da mafificin alkhairi."


  "Ameen Alhj"****


  Bayan sallan Isha Abdul da gabad'aya kansa ya d'aure ya d'ago wayansa da aniyan kiran Amal. Shi kansa yana son aikin saboda kyansa amman kuma baya son yayi nisa da Amal baya son tafiyansa ya zame sanadin rabuwansu gashi idan ya tafi ze iya d'aukan kusan shekara ko biyu ma halan kafin ya dawo. Kai baze iya ba. A karo na biyu Amal ta d'aga wayan nasa. 


  "Halo Baby na?" Ta soma cewa. 


  "Na'am My Princess ya kike?"


  "Lafiya k'alau ya office I missed you two days."


 "I missed you even more office na shiga miki hak'k'i ko?"


  "Sosai ma."


 "Toh ya zamuyi? Gashi na samu promotion a office this time har Canada sukeson tura ni Baby."


  "Har Canada?" Jin hakan kawai ta gano iyayensa has something to do with this, Allah sarki ta inda suka 6ullo masa kenan so that idan ya tafi a hankali har ya soma mancewa da ita. 


  "Eh Baby kuma idan na tafi I might take a year or two kafin na dawo."


  "Babe congratulations nayi maka murna sosai this is such a massive promotion."


  "Yes it is amman ni nak'i amincewa nama k'i kar6an transfer letter'n."


  "Meyasa Baby?"


  "Toh kuma haka kawai se in tafi in barki har na tsawon shekara Baby? Kina tsammanin zan iya rayuwa ba ke ne?"


  "Baby yanzu danni kakeson barin wannan dama ta wuce ka?"


  "I can sacrifice the whole world for you darling."


  "Allah sarki Baby please don't do this, our love for one another is enough balle ma ai zamu na waya har har video call ma idan kana so amma please kar ka bari daman nan ya wuce ka saboda ni."


  "Baby bana son inyi kewarki."


  "I'm just a call away my Prince Charming kaji? You don't have to miss me."


  "Duk da hakan my Princess nifa bazan tafi ba."


  "Baby mana yanzu so kake kace zaka bar daman nan ta wuceka?"


  "Ni tama riga ta wuce dan bazan tafi Canada ba tare da ke ba."


  "Kana nufun idan zan bika zaka tafi?"


  "Mey ze hana ni?"


  "Toh Baby makaranta ta fa?"


  "Ai muna iya kar6a miki transfer letter se muyi aure mu wuce chan d'in tare." Ba k'aramin hawaye kalamun sa suka sanyata ba da wuri ta share kafin ya gane kuka takeyi. Ina ma ace hakan is possible, ina ma ace za ayi musu aure su tafi Canada and start a new life together, tana ganin da duk duniya ba wanda ze kaita jin dad'i amman Yaya fa? Shin ta kyauta masa kenan idan haka kawai ta tashi ta tafi ta barsa da ciwo? Upon all the hidimomin da yayi mata a baya? 


  "My Baby kinyi shiru."


  "Ya Abdul I want this morethan anything, ba abinda ze fiye mun kwanciyan hankali kamar rananda za'a d'aura mana aure in kasance mallakinka."


  "Then let's get married princess let's do and fly to Canada together zan d'au nauyin komai karki damu kawai ki amince don Allah."


  "But Ya Abdul su Mami bazasu amince ba."


  "Meyasa? Ina iya turo su Baba suyi masu magana ke kawai ki amince."


  "Ya Abdul kasan ina sonka ko?"


  "Yes Baby I do ai kema kin san ina sonki."


  "Sosai Sweetheart shiyasa nakeson ka kwantar da hankalinka, ina nan ba inda zani har kaje ka dawo ina jiranka, kaga idanma a shekara d'aya zaka dawo by then na kammala part 4 d'ina clinicals kawai ze rage mun idan kuma in two years ne kaga ma na kammala karatun kenan gabad'aya se muyi auren mu cikin kwanciyan hankali ba hanzari ba komai."


  "Princess why not now?"


  "Baby bana son had'a aure da karatu ne banason school yana shiga maka hak'k'i idan munyi aure."


   "Princess ni ban damu ba as long as zaki amince ki tafi dani Canada."


  "Baby please listen to what I told you, ina nan ba inda zani zan jiraka har kaje ka dawo, I'm yours alone."


  "Meyasa nake ji ajikina bayan tafiya na wani ze min gaba dake?"


  "Kuma har kake tsammanin zan amince in auri wani sama da kai? Baby shin baka yarda da soyayyan da nake yi maka bane?"


  "Of cours not Princess I trust in your love but-"


  "Them you don't have to worry Baby I will wait for you ko shekara nawa ne zan jira ka kaji? I love only you."


  "Promise?" Hawaye na d'iga daga idonta tace, "I promise."


  "Thank you Princess zan yima Baba magana suzo su samu Papi suyi masu bayani ko?"


   "Baby ba amfanin hakan."


  "Princess what if suka ji shirun nawa yayi yawa sukayi deciding su ba wani ke? I think is better su Baba su samesu suyi musu bayanin ina nan tafe kar su d'ay Princess d'ina suba wani chan."


  "Toh shikenan Baby tunda kayi insisting seka turo su Baban suzo."


  "That's my Princess."


  "Tafiyan yanzu ne?"


  "Eh baze fi nan da one month ba."


  "Ayyah I'll miss you so much."


  "I'll do that even the more Princess." Hira suka sha sosai sannan tayi masa seda safe. Washegari yaje ya samu su Baba ya musu bayanin shawaran da ya yanke, sosai suka ji dad'in amincewan da yayi amman ya nuna masu shi lalle fa se anje gidansu Amal an sanar dasu Papi batun tafiyan nasa kar bayan tafiyansa su aura mata wani. Basu masa musu ba suka amince duk dan son su 6atar da sahun abun. Koda labari ya iske Maamah, bata sha mamaki sosai ba saboda a karo na farko data fara ganin Afzal ta tabbatar da soyayyan da yakeyi wa Amal ita Ya Abdul kawai take tausayawa yanzu na k'arfi da yaji ana son turasa Canada. 


  Washegari kaman yadda Abdul yaso haka iyayensa suka shirya suka sake zuwa gidansu Amal duk se zolayansa suke.    

   A cikin wata d'aya da sati visan Abdul ya fito ya gama shiri tsaf sauran tafiya. Cikin wata d'ayan nan Amal bata ta6a d'aga waya ta kira Afzal ba saidai idan shi ya kirata shima befi sau biyu zuwa uku ya kirata ba don ya gane kaman tak'ura mata yake. Ko daga yadda take mai magana ma. Don haka se be sake kiranta ba haka kuma be sake taka k'ofar gidansu ba amma kullum da tunaninta yake kwana da kuma shi yake tashi. Sau dayawa suna fita tare da Nazeefah se yayi dropping nata a school sannan ya wuce office rananda yake da meeting d'in safe kuwa ita da kanta take tafiya. Lafiya k'alau suke zama a gidan rannam ma a d'akin Afzal ta kwana, suna cikin hira bacci yayi gaba da ita shiko be tada ita ba instead seya gyara mata kwanciyar suka yi kwanciyar su tare. Da Asuba da ya tada ita sallah kawai se ganin kanta tayi cikin d'akinsa, mamaki ne da farin ciki ya rufeta a lokaci d'aya bata d'au har Afzal ze barta ta kwana d'akinsa ba. Lallai idan mutum yayi hak'uri komai ma is possible, aiko hak'urin zata cigaba da yi har se ta gama karkato da hankalinsa akanta gabad'aya. Tana cikin sallan Asuba Afzal ya dawo daga masallaci bayan da ta idar suka gaisa sannan ta d'aga pillonta. "Ina kuma zakije?" Yayi saurin tambayarta. 


  "D'akina" ta sanar dashi tana kallon k'asa. 


  "A ina kika kwana?"


  "I'm sorry ai da ka tadani jiyan."


  "Ajiye pillonk kinji? You're sleeping in here." Dad'i kaman ze kashe Nazeefah mayar da pillon tayi ba musu ta kwanta chan shima yayi joining nata, bargon yaja ya rufesu suka koma bacci. 

  

   ***

   Ta fannin su Amal kuwa, ba k'aramin shareta Maamah ke ba, se wani kaffa-kaffa takeyi da ita sam bata sakewa da ita kaman da seda Amal ta zauna tayi mata bayanin komi dallah-dallah sannan ta kuma nuna mata how sorry she is Maamah ta amince suka sake dawo da k'awancensu na da. 

   

   Kasancewar tafiyan Abdul gobe ne yau tun da Azahar ya taho ya d'auki Amal suka wuce yawo ba shi ya dawo da ita ba se chan yamma bayan sun fito daga motan ya sa yara suka shiga mata da ledojin siyayyan da yayi mata sannan ya kira sunanta alokacin idon Amal ya cike dam da hawaye tasani daga yau kuma se idan Allah ya sake had'a su she's sure kafin ya dawo an yi mata aure da Afzal. 


  "Princess bade kuka kike ba?" Ya tambaya da mamaki. Kanta tayi saurin juyawa yayinda ta shiga share hawayenta. Zagayowa yayi ta gefenta "Princess so kike kisani kukan nima?" Kukan ne yaci k'arfinta sosai kawai ta fad'a jikinsa tana kukan tsuma zuciya. Tasan yin hakan haramun ne amman bazata iya jure rashinsa ba, mutuwan tsaye Abdul yayi wajen ko rik'eta ya kasa yi. Wai Amal da ko hannunta bata barin a ta6a ne ta fad'a jikinsa haka? Tunani ya fara yi anya ko lafiya? Ya yake ji kaman wannan ne had'uwansu na k'arshe? A hankali ya zagaye hannayensa a bayanta yayinda kukan nata ya tsananta, hak'uri ya shiga bata sannan ya d'agota a hankali ya shiga share mata hawayenta da handkerchief. 


   "Princess kukan ya isa haka kinji?"


  "Ya Abdul dan Allah kar ka tafi, I can't do without you I really can't" ta fad'a cikin tsakankanin kuka. 


  "Amal I'm sorry but I have to, we'll keep in touch kinji? Kukan ya isa haka, idan fa kika cigaba nima zanyi" Kalamai masu kwantar da hankali yayita fad'a mata har ya samu kukan nata ya lafa a hankali har ya d'auke gabad'aya. 


  "That's my Princess smile toh kinji?" Sede ta kad'a masa kai da nufin a'a. 


  "D'an murmushin ma yau bazaki yi mun ba? Sena kira Babana na fad'a mishi" Yayi maganan had'e da turo baki wane d'an yaro. Bata san lokacinda ta fashe da dariya ba, she'll surely miss him kodan sanyata dariyan da yake yi. Hira suka sake ta6awa kad'an gun sannan ya buk'acesu da suyi last selfie, suyi a wayanta suyi a wayanshi haka suka tayi har seda suka gaji. 


  "Toh Maghrib ya kusa muje muyi niyya ko Baby?" Yace da ita. "Ki gaishe mun da su Mami sosai sosai."


  "Toh my Baby semun sake waya ko?"


 "In shaa Allah I love you so very much" ya sanar da ita.


 "I love you too baby" ta amsa, a hankali ya mik'a yayi placing mata light kiss a goshi "Keep yourself safe for me okay?" Kai ta gyad'a cike da kunya ta juya ta k'arisa ciki. Washegari da safe kafin jirin su Abdul zuwa Abuja ya tashi ya kirata yayi mata sallama haka itama da suka isa ta kirasa tayi masa sannu. 


  The next day international flight nasu ya tashi tunda ya kira Amal don suyi sallama take faman yi masa kuka a wayan haka har ya ajiye bata fasa kukan ba. Tun Mami na bata hak'uri har tagaji ta barta. Haka nan tun tafiyan Abdul Amal ta koyi sabon sana'an kulle kanta a d'aki tayita kuka. Sau biyu Afzal na kiranta amman bata d'aga wayan nasa, yau bayan ya tashi daga office ya biya ta gidansu. Mami ya tarar a tsakar gida tana surfan wake. Bayan sun gaisa yake tambayarta ko Amal na gida. 


  "Gata chan a d'aki tun safe da ta fito ta karya ban sake jin motsinta ba."


  "Meya sameta? Bata da lafiya ne?"


  "A'a Abdul d'inne ya tafi."


  "Ina?"


  "Canada kode baka da labari ne?"


  "Sam" ya kad'a kai. Nan ta basa labarin duk yadda akayi, ashe de dalilin daya sa ko ya kirata kwana biyu bata d'auka kenan, Allah sarki. 


  "Toh ni zan kai markad'e nan mak'ota zaka jira in dawo?"


  "Eh Mami Allah kare."


 "Ameen" ta amsa tare da ficewa. Nauyayyan ajiyar zuciya ya sauk'e sannan ya mik'e ya nufi k'ofan d'akin Amal d'in tare da placing gentle knock sede shiru tak'i amsawa. Sallama yayi next se ji tayi kaman muryansa shiru tayi ko ze sake magana don ta tabbatar.


  "Lily?" Ya kirata anan ta tabbatar da cewan shi d'inne. "Lily fito kinji?" Manna masa tayi duk suratan da yata yi hakan besa ta fitowa ba daga d'akin, don kansa ya fito waje ya d'auko ledan da ya d'an yi mata sayayya tare da attaching note ajiki ya koma ya ajiye mata dab bakin k'ofan nata sannan ya fita waje ya jira dawowan Mami, tana k'arasowa yace ze wuce, se anjima tayi masa sannan ta k'arasa ciki. Chan da Amal ta tabbata Afzal d'in ya tafi wajajen Maghrib ta bud'o k'ofan d'akin nata inda ta tarar da farar leda tsugunawan da zatayi ta d'aga se note d'in ya fad'i d'agawa tayi ta karanta kaman haka;


   'Here're your favorites to light up your evening, I love you Xx.'


   Lek'a cikin ledar tayi taga favorite ice cream flavors nata ne da har sunyi melting da kuma chocolates, ciki ta koma ta ajiye ledan a d'akinta ta wuce bayi ta d'auro alwala sannan ta wuce kitchen dan ibo abinci. Achan suka had'u da Mami inda take ce da ita "Se yanzu kika ga daman fitowa?" Shiru ta mata bata amsa ba "Ga chan abincin alale na dafa."


  "Sannu da aiki."


  "D'azu Afzal yazo ai ko baki sani ba?"


  "Ban sani ba yaushe?"


  "D'azun."


  "Allah sarki" tayi maganan tana serving kanta. "Seki kirasa."


  "Toh" ta amsa tare da ficewa d'akinta. Instead ta kirasa kaman yadda Mami ta fad'a, bayan da ta idar da sallah taci abincin seta tura masa sak'o as 'Thank you.' 


    Suna zaune da Nazeefah sak'on ya shigo a farko yaso ya kirata amman sanin idan ya tashi a take Nazeefah na iya gano wani abun se kawai yayi replying nata as 'You're welcome.' Da daren ranan Abdul ya kirata suka sha hira kaman ba gobe tasan ya kamatabace ta canza layinta saboda kar Abdul d'in yana samunta kaman yadda iyayensa suka buk'aceta amman ina baza ta iya ba, son zuciya baze barta ba. Bata son rabuwa da shi, shi kad'ai ne idan tana tare dashi take jin dad'i yake kuma sanyata mancewa da dukkan matsalolinta


   Washegari Afzal yayi timing dai-dai break time nasu Amal ya jesa school nasu. A gaban lecture hall nasu yayi parking sannan ya kirata a lokacin wayan na a hannun Maamah tana kallon pictures. "Gashi Ya Afzal na kiranki" ko kallonta batayi ba tace "Bar shi kawai na koma gida zan kirashi."


  "Haba Amal rashin mutunci de ba kyau hungo ki amsa."


  "Nace zan kiranshi anjima" Maamah bata saurareta ba ta d'aga wayan tare da manna mata a kunne seda Amal ta watsa mata mumunan kallo sannan tayi sallama. 


  "Wa'alaikumus salam" ya amsa. 


  "Yaya ina yini?"


  "Lafiya Lily, ya kike? Kin fita school ko yau d'inma kina gida?"


  "Ina school."


  "Toh gani a gaban lecture hall naku.l


  "Yaya zan-"


  Gano neman excuse take yayi saurin katseta "Please come Lily." 


  "Wai yaya?"


  "Wai yana waje inje in sameshi kinga shiyasa nace ki bari se idan na koma gida in kirasa."


  "Amal running away from him won't solve anything, da hak'ura kikayi kika bud'e mishi zuciyarki."


  "Maamah it's not that easy, I love Yaya amma ba so na soyayya ba Maamah Ya Abdul kad'ai nakeso."


  "Na gane Amal but Ya Abdul ya miki nisa kema kin ba iya kasancewa tare zakuyi ba, beside time heals a hamkali zaki koyi sonsa, yanzu ki fita kije ki samesa kinji?"


  "Kefa? Mu je tare."

  

  "Ni meya kaini shiga tsakanin masoya? Barni kurum zan wuce hostel yaso semu had'u achan."


  "Maamah please kar kiyi mun haka mu tafi tare."


  "Ji min 'ya fa! Ya Afzal d'in bak'o ne? Abeg in zaki tashi ki wuce toh da ya fi miki." Haka tak'i raka Amal, books nata ta tattara ta d'an kimtsa fuskan ta sannan ta fice. "Shine se an shanya ni haka za a fito Lily?" Yayi maganan bayan da ta shiga motan. 


   "I'm sorry ina copying abu ne da ka kira."


  "Alright ya lectures toh?"


  "Alhamdulillah ya office?"


  "Very good only that I've been missing you haka jiya naje gida kika k'i fitowa."


  "Yaya ba haka bane."


  "Toh Yaya ne?" Yayi maganan lokacin da ya shiga tuk'i. "Are you still mad at me? Lily I'm sorry bazan gaji da baki hak'uri ba."


  "Yaya komai ya riga ya wuce ka dena damun kanka" be sake cewa da ita komai ba har suka isa restaurant da zasu ci abincin. Beso suci a restaurants na cikin school ba gudun kar suci karo da Nazeefah. Sede sa6anin yadda Amal ta saba sakewa da shi tayita masa hira yau jugum tayi ko uffan bata ce da shi ba. Afzal ya rasa meke masa dad'i besan mey zeyi ba Amal ta kuma sakewa da shi kaman da, gashi da zaran ya gwada d'auko mata maganan Abdul se ranta ya soma 6aci. Haka nan da suka gama ya mayar da ita school sam ba walwala tattare da ita. 


   Haka fa Afzal ya koma tamkar bak'o ga Amal. Sam bata sakewa da shi, kominbyadda yaso su koma yadda suke a da abun ya gagara. Sede kaman yadda Mami tace masa kada ya kariya haka yake danne zuciyansa yana hak'uri. Duk randa he is free yakan d'aukota daga school suje suci abinci a weekends ma idan bashida abunyi ko kuwa idan Nazeefah ta fita unguwa shima se ya shirya ya kawo mata ziyara even though bata ta6a kawo masa hira saidai shine yata zuba ita ko tayi ta basa short short answers. 


  Tun dawowansa gida yau ya karanchi yanayin Nazeefah ya soya tayi lagwai kaman wanda baida lafiya. "Sannu da zuwa" tace dashi lokacinda ya shiga parlourn. 


    "Yauwa sannu" ya amsa. 


  "Your lunch is ready" ta sanar da shi.


  "Thank you lafiya? Ya naga ganki haka?" Yayi maganan had'e da zama gefenta akan kujeran data jingina. 

  

   "Lafiya nakega stress ne kawai kar ka damu."


  "Are you sure?" Ya tambayeta yana ta6a jikinta don jin tempreture'nta. 


  "Yes karka damu" ta amsa had'e da yi masa murmushi. D'akinsa ya wuce ya watsa ruwa sannan ya fito yaci abinci sede be tarar da ita a parlourn ba, take ya yanke hukuncin ta shiga d'akinta ne. Shi kad'ansa ya zauna a parlour yana kallon sports har izuwa Maghrib. D'akinta yawuce inda ya tarar da ita tana kwance, k'arisawa ciki yayi tare da zama akan side drawer'n sannan ya shiga kiran sunanta. A hankali ta shiga amsawa "Tashi kiyi niyya lokacin sallah yayi."


  "Nagode" kad'ai ta iya cewa sannan ya fice. Be dawo gida ba se bayan Isha rashin ganinta da beyi a parlourn ba kawai ya yanke hukuncin jikin nata ne daman tunda ya dawo ya ganta wani iri d'akinta ya wuce ya sameta kwance lamo akan gado. K'arisawa yayi ya zauna gefenta tare da ta6a jikinta sosai tempreture'n nata ya hau. 


  "Nazeefah you're sick" ya yake hukunci. 


  "I fear I am" ta amsa murya ciki-ciki. 


  "Ya kikeji?"


  "Zazza6i" ta amsa a takaice. 


  "Bakiya fleeting d'akinki kwana biyu har sauro suka yita cizonki ko?" Kai ta gyad'a a hankali. 


  "Yanzu kin huta ai da malaria ya shigeki."


  "I'm sorry" ta furta a hankali. 


  "Ba magani a gida barin fita in siyo miki."


  "Ba seka fita cikin daren nan ba kabari ko zuwa gobe."


  "So kike in zuba miki ido haka? Ina zuwa kinji?" Kai kad'ai ta gyad'a yayinda ya ja bargo ya rufeta da shi sannan yayi adjusting AC'n d'akin. Dai-dai yazo fita ta kira sunansa "Na'am wani abu ne?"


  "Thank you Allah ya kare."


  "Ameen don't mention" ya amsa tare da sakar mata da murmushi nan da nan ya d'au key'n motarsa ya fice. A pharmacy'n dake unguwansu ya samu maganin ya sai mata nan da nan ya komo gida ya d'au ruwa ya wuce d'akinta da shi knocking yayi sannan ya shige. Lokacin har tayi bacci zama yayi gefenta ya tada ita had'e da taya ta zama "Sannu ko?"


  "Har ka dawo?" Ta tambayesa. 


  "Eh na samu anan bakin layi kinci abinci?" Kai ta kad'a "Bari in d'ibo miki toh seki sha maganin naki."


  "Bari zan sha maganin haka kawai bana son shinkafan."


  "Toh an ta6a shan magani akan yunwa ne Nazeefah?"


  "Afzal ko naci hararwa zanyi shiyasa."


  "Mey kikeso toh?"


  "Babu."


  "It can't be babu tell me , zaki ci indomie?l" Kai tayi saurin kad'awa "quarker oaths?" Nan ma kai ta kuma kad'awa "What of custards?"


  "Dama dama shi ma, bari zuwa anjima idan na d'an samu k'arfi zan had'a thank you so much Afzal."


  "Bari zan had'a miki."


  "Ka iya girki ne?" Ta tambayesa da mamaki murmusawa yayi "Halan ke kike mun da nake school."


  Dariya ta saki kad'an "I'm impressed."


  "Kwanta ki huta lemmi get it ready for you." Kwanciyan tayi ya ja mata bargo sannan ya wuce d'akinsa ya rage kayan jikinsa ya wuce kitchen d'in. Nan da nan ya tafasa ruwa a heater ya had'a mata custards d'in ya kai mata. A farko yayi tunanin barinta ta sha da kanta amman tuna yadda tayita masa d'awainiyya sanda yayi targad'e hannunsa yasa ya canza ra'ayinsa. Da kansa ya zauna ya bata custards d'in seda ta shanye tas sannan ya 6allo mata magunan ta ya bata ta had'iye. Bayi ya rakata tayi alwala sannan tayi sallah ta koma ta kwanta. D'akinsa ya koma ya kammala aikin dake gabansa, chan wajajen goma ya watsa ruwa ya sanya shorts nasa ya d'au pillonsa ya zarce d'akin Nazeefah. Ba k'aramin mamaki tasha ba ganinsa da tayi rik'e da pillow. Bade anan yake shirin kwana ba saboda bata da lafiya? Haka kawai ta tsinci kanta cikin farin ciki. Kallon ne yaga ya soma yin yawa yace, "Ko in koma ne?" Cike da wasa. 


  "Ni yaushe nace haka?" Taya saurin tambaya. 


  "Toh naga kin k'i matsa min ne ai" yayi maganan sanda yake tsaye akan gadon. 


  "Gadon ma gabad'aya idan kakeso zan bar maka." Murmushi ya sakar mata sannan ya ajiye pillonsa daga space da tayi masa providing. 


  "Do you need anything else?" Ya tambayeta kai ta kad'a da haka ya haura gadon ya sameta tare da kashe musu wuta. Jawota yayi a hankali izuwa jikinsa sannan ya furta "Goodnight Nazeefah."


  "Goodnight Afzal I love you." Peck yamata placing a hankali da haka har bacci yayi gaba da su duka. 




RANA D'AYA!

#RD


Love... King Miemiebee👄✨

[13/08, 02:20] ‪+234 907 483 8352‬: 🎀🎀🎀                 🎀🎀🎀

                🎀❣🎀

                   ❣❣


  💦💦                      🍃🍃🍃          

           *RANA D'AYA!*

  💦💦                      🍃🍃🍃

  July, 2018

 beeenovels.blogspot.com


     _Written by Miemiebee👄_



   *PAGE 2⃣1⃣*


  _Big sis🗣 (Maman Fadeel) where are you? I just want you to know that I'm devoting this entire page to you. Thank you for always trying to put a smile on my face, for treating me as if I'm one of your true little sis, know that your Lily loves you so much. XX 😘_




    Kasancewan jikin Nazeefah a gida Afzal yayi sallah ya jasu tare, bayan sun idar da sallan ne ya shiga shirin office inda tace zata had'a mishi breakfast. Take ya hanata akan ta kwanta ta huta tunda bata da lafiya, he can manage. Haka ya shirya ya had'a breakfast nasa ya ci sannan yayi mata sallama. Kaman yadda ya saba kiran Amal ko wani safiya haka nan ma yayi yau sede har yanzu Amal bata sakewa dashi sama-sama suka gaisa sannan ya katse.


   Da yamma bayan Amal ta dawo daga school ta la6e a d'akinta se hira suke a waya da Abdul not knowing Mami na la6e tana sauraronta tun d'azun. Ashe de har yau bata fasa waya da Abdul ba, shin wai meke damun Amal? Ta tambayi kanta, ace mutum an bada shi ma wani amma ya zauna yana hira da wani na daban? Bata yi mata magana ba ta koma ta cigaba da aikin dake gabanta. Bayan dawowan Papi ne ta zaunar dashi take fad'a masa abinda ke faruwa. Amal d'in ya kira bayan ta k'ariso take mai sannu da zuwa. 


  "Yauwa Mamana ya makaranta?"


  "Alhamdulillah."


  "Nace yaron nan Abdul ai baku waya yanzu ko? Kuma kin canza sim naki kaman yadda iyayensa suka buk'ata?" Shiru Amal tayi dan ko k'aryan da takeson yi d'inma ta gagara, kum taji bakinta ya kullu. 


  "Baby?" ya kirata. 


  "Na'am Papi" ta amsa. 


 "Baki jini bane? Kode har yanzu kuna waya ne dashi?" Nan ma shiru. "Ba magana ake miki bane Baby?" Mami tasa baki. 


  "Eh Papi" ta amsa murya chan ciki-ciki. 


  "Haka kukayi da iyayensa? Ke bakisan cin amana kike ba yanzu Baby? Taya bayan an bada ke ma wani amma ki tsaya kina hira da wani na daban? Kina ganin kin kyauta wa shi Afzal d'in kenan Baby?" Shiru tayi ta kasa cewa komai yayinda take nazarin rabuwa da Ya Abdul. 


  "Iyye? Kina ganin kin kyauta masa kenan?"


  "A'a" ta kad'a kai a hankali. 


  "Toh kije na baki nan da kwana biyu ki canza sim kuma kar in sakejin kina waya da Abdul d'in kinji?"


  "But Papi-"


  "Ko baki jini ba? Har yaushe kike son ki cigaba da yaudarar sa? Kefa kikace kin amince zaki auri Afzal kodan ki biyasa alkhairin da yayi miki a baya yanzu kuma kice ba haka ba Baby?"


  "Papi bawai dena waya da Ya Abdul d'inne bazan iya ba, naga tunda ba auran Yaya zanyi ba yanzu ai ba laifi idan muna gaisawa da Ya Abdul, Papi dan Allah karkace a'a."


  "Kaman ya Baby? Ni da na d'au da jimawa ma kin canza layin naki? Ke bakisan alkhairi ne miki ba idan kika rabu da Abdul d'in tun wuri, kema zaki fi samun kwanciyan haka shima a hankali Allah ze yaye masa son da yake miki kuma gaisuwa ne kad'ai kuke ko hirar masoya?"


  "But Papi-"


  "Ya isa haka Baby baki cika sa6awa dokokin da nake kafa miki ba, kar kiyi hakan yanzu nan da kwana biyu bana son in sake jin kina waya da Abdul idan kuma ba haka ba zan yima iyayen Afzal magana dama su basu k'i ko a satin nan a d'aura auren ba, se suzo ayi magana asa rana."


  "Papi dan Allah kar kayi mun haka."


  "Toh kiyi kaman yadda nace." Kai ta gyd'a a hankali tana share hawayenta "Tashi ki fice Allah yayi miki albarka" ko amsawa batayi ba ruga d'akinta a guje ta baje kan katifarta ta shiga aikin kuka. Wayanta ta jawo had'e da shiga photos tana kallon pictures nasu tare da Ya Abdul yayinda kukan yaso yaci k'arfinta. Chan dare kaman yadda ya saba kiranta haka nan ya danna mata kira bata 6ata lokaci ba ta d'aga suka sha firarsu sam bata nun masa wai da akwai matsala a k'asa ba sede ko da yakeson yi mata seda safe tak'i amincewa ya katse wayan ita wai suyita hira kawai. Haka ya biye mata dukda cewan bacci yakeji, wayan suka yita yi har zuwa lokacinda ta zarce bacci se anan yayi mata goodnight yayi hanging call d'in. Washegari bayan ta taso daga school ta wuce Post office ta sai sabon sim sannan ta dawo gida. Video call ta dannawa Ya Abdul shi kansa beyi expecting ba dan tun tafiyansa sau d'aya da sukayi video call basu kuma ba. Haka nan tayita masa hirar shirme har seda kud'inta ya k'are sannan ya kirata suka cigaba har anan bata nuna masa cewan akwai wani abu ba. Da daren ranan ne bayan sun k'are wayan ta karya sim d'in ta sa sabuwa tana kuka haka ta zuba pieces d'in a bola. Ranan ko bacci batayi ba, kuka ta kwana tana yi washegari idanun nan sun kumbura tim ko school ta k'i fita. Dama normally kowani safiya da good morning text messages na Ya Abdul take tashi se gashi yau wayam ba komai. Ba yadda Mami batai da ita ta fito ta karya ba amman tak'i. 


   Shiko Abdul chan da yamma bayan ya dawo daga office yayi tunanin kiran Amal tunda shiru yau bata kirasa ba sede fa switched off layin nata ke ce masa. Be kawo wani tunanin a ransa ba yace ze gwada anjima, sede har zuwa dare Amal bata kirasa ba gashi ko ya kira switched off da wasa da wasa hankalinsa ya soma tashi. Sak'onni da dama ya tura mata amma ba response yau akeyinta! Danne zuciyarsa yayi yace bari ya bari zuwa gobe. Safe bim ya sake trying layin nata amma still baya shiga, hankalinsa idan yayi dubu be tashi ba shin meke faruwa? Wutansu ne ya 6aci kokuwa wayarta ta aka sace? Tunani de ba wanda beyi ba k'arshe da shirun yayi yawa ya yanke hukuncin kiran Maamah. Tana ganin call nasan tasan Amal ta canza sim ne kenan. Allah sarki Ya Abdul. 


   Sam bata so d'aga wayan ba amman gudun kar ya fahimci wani abun seta d'auka bayan sun gaisa yake tambayarta ko ta fita school yau. K'arya ta mai tace bata fita ba. 


  "Toh Amal fa kunyi waya da ita?"


  "A'a wallahi tun shekaran jiya rabon mu da muyi waya."


  "Ikon Allah I've been trying to reach her but it ain't going through."


  "Toh kuma? Kasan wuta ya 6aci gabad'aya gari toh se a hankali nakega bata da chargi ne."


  "Nima nayi tunanin hakan gobe zaki fita school ai ko?"


  "Ka manta gobe Saturday ne? Besides bani da lecture ma."


  "Toh bazaki je gidansu ki duba mun ita ba?"


  "Ya Abdul ka kwantar da hankalinka mana ai Amal lafiyarta k'alau wuta ne ya lalace wayan nata ba chargi ka gane?"


  "Maamah are you sure?"


  "Dagaske amma sunce nan da sati ma zasu gyara."


  "Anya kuwa zan iya jure sati banji muryan Amal ba? Ni kawai gobe kije gidansu ki had'amu."


  "Allah sarki Ya Abdul zan raka Mama gidan biki fa kabari mana zuwa Monday."


  "Mey zakiyi jibi da bazaki je ba?"


  "Naji Allah kaimu."


  "Yauwa good girl nagode ko?"


  "Uhumm you're welcome" hira kad'an suka ta6a sannan sukayi sallama. Wayan ta ajiye had'e da sauk'e nauyayyar ajiyar zuciya gabad'aya ta rasa ya zata 6ullowa al'amarin. Mama taje ta samu ta irga mata halin da ake ciki inda take shawatarta da komin yaya karta kuskura ta basa sabon layin Amal. 

  

  Kamar yadda Abdul ya shiga tashin hankali haka Afzal ma, barin ma shi da bashida clue sam gameda rashin samunta a wayan ya rasa dalili, layin Mami ya kira itama unavailable yake cemata. Beso kiran na Papi ba akan zuwa gobe zeje ya duba ta yaji ko lafiya. Sosai Nazeefah ta warware, washegari bayan sallan La'asr Afzal ya zarce gidansu Amal. 


  Mami da Papi ya tarar a tsakar gidan bayan sun mishi sannu da zuwa ya k'arisa suka gaisa sannan yake tambayar ko lafiya jiya throughout yana neman Amal amma ya kasa samunta. 


  "Bade bata baka sabon lambar nata ba?" Papi ya furta a hankali sede Afzal ya jiyosa saboda nisan kunnensa. 


  "Na'am?" Ya tambaya. 


  "Bata kiraka da sabon layinta ba?"


  "A'a" ya kad'a kai cike da rashin fahimta. "Sabon layi kuma?"


  "Afzal nasan kana hak'uri amma ka k'ara, kasan Baby yarinya ce tunaninta kad'an ne, bayan nan kuma shi rabuwa da masoyi zafi gare shi, gabad'aya na kasa gane kan yarinyar nan gashi kuma idan akace ta rabu da kai ta koma ga Abdul d'in setace a'a ita bata son abinda ze sake samun lafiyanka ta fita harkan Abdul d'in kuma abun ya gagara. Afzal bazan 6oye maka ba amma idan kasa wasa kana sakaci toh wallahi da k'yar idan zaka iya maye gur6in Abdul a zuciyanta, ban san wani irin makahon so takeyi masa ba. Ka sani yanzu ne kake da daman shiga zuciyarta tunda Allah yayi ta canza layin nata zasu daina waya."


  Sosai Afzal yaji wa Amal, ba k'aramin tausayi take basa ba, yasan yadda takeji sarai saboda shima he went through such. Tunanin ya ze iya karkato da hankalinta akansa yake amma gabad'aya ya gagara. 


  "Papi Amal ta riga ta tsaneni, tsana har a fuska tana nuna mun, wallahi ina iya k'ok'arina don ganin nayi straightening relationship namu but she's not willing to give me a chance I don't know what to do again."


  "Abba a gani na idan ba aure akayi ma Baby da Afzal ba, yarinyan nan baza ta ta6a amincewa da cewa Abdul yayi mata nisa ba" Cewan Mami. 


  lBut Mami makarantar ta fa?l Afzal yayi saurin tambaya kafin Papi yayi magana "Bana son maganan aure ya raba mata hankali."


   "Hakane Afzal amma kuma akwai abin dubawa acikin abinda Mamin Baby ta fad'a, idan ba wai har rana taga an sa muku ba bazata ta6a fita daga harkan yaron nan ba tasan yanzu ba ita ba shi."


  "Tabbas hakane Papi toh zan gwada yimata maganan inji mey zatace duk abinda akwai zan sanar da ku."


  "Toh shikenan hakan ma yayi amma kam kayi sake haka kana ji kana gani 'yar nan zatayi maka nisa."


  "Toh zan wuce ko zan iya ganin Amal?"


  "Bari inyi mata magana" cewan Mami. 


 "Toh zan jirata a waje nagode sosai se anjima."


  "Ka gaida gida" Papi ya fad'a masa. Da haka ya mik'e ya fice. Koda Mami taje kiran Amal akan cewa Afzal yazo yana nemanta, shareta tayi k'arshe seda Papi ya sa baki. Fuskanta ta fito ta wanke sannan taje ta samesa lokacin har ya gaji da jirarta. 


  "Yaya ina yini?" Ta gaishesa daga chan nesa yayinda yake zaune kan benchin sa na kullum. 


  "Fa bazan amsa gaisuwan nan ba sekace wani bak'o Lily? K'ariso nan mu zauna kinji?" Bata mai gardama ba ta k'arisa ta zauna a gefensa. 


 "Meya faru fuskanki ya kumburo haka?"   


  "Babu" ta amsa tana tare fuskan nata. 


  "Dan ance se kin fito shine kike kukan nan Lily?"


   "Yaya ba haka bane."


  "Lily I'm sorry for making you hate me if you can't love me back please tell me."


  "Yaya wani irin magana kuma kake? Har na isa ince bana sonka ne?"


  "Gashi kuwa sede a bakin Papi zanji kin soya layinki you had zero intention of notifying me koba haka ba?"


 "Jiya fa na canza layin ko Maamah ma ban bata ita ba, ba wanda na kira da ita."


  "Toh shikenan dama magana nakeson miki."


  "Ina jinka."


  "Is it okay with you in turo su Abba for formal introduction?" Wani irin wawan fad'i gabanta yayi bade yanzu Afzal ke shirin auranta ba?  


  "Lily?"


  "Yaya..." se kuma tayi shiru. 

  

  "Talk to me kinji? Ki fad'a mun ra'ayinki I'll do only as you wish Lily."


  "Yaya Nazeefah fah? Yaya bana son shiga tsakaninka da matarka bana son tashin hankali."


  "And who said by agreeing to marrying me zaki shiga tsakani na da Nazeefah? Ke daban ita daban karki damu da ita zata fahimci al'amarin namu in shaa Allah."


  "Yaya what of my studies? Kaifa kace baka son abinda ze raba mun hankali dangane da karatu baka tunanin auran nan will be a great distraction to me? Yaya I'm sorry amma ban shirya da yin aure ba yanzu."


  "Is this just how much you don't want to be with me Lily? Yanzu inda Abdul ne yace ze turo ai bazaki ce masa haka ba ko? Shikenan ba matsala dama ra'ayinki kawai nakeson ji saboda in sanar dasu Papi. Kina iya komawa ciki" yayi maganan yana sa hannunsa cikin aljihu, wata envelope ya zaro ya sa mata a hannu. Kafin tace zatayi masa godiya har ya k'arisa cikin motansa yana k'ok'arin tada ita. Seda taga ficewansa sannan ta k'arisa ciki. Ko mutum be tambaya ha yasan ransa ya 6aci, daga yadda yayi magana ma. 


   Kud'in ta mik'awa Mami akan gashi Afzal ya bata. Zaunar da ita Mami tayi "Baby?"


  "Na'am?" Ta amsa. 


  "Yanzu kina ganin kina kyautawa Afzal kenan?"


  "Mami ni kuma mey nayi?"


  "Kisani wallahi koda ba don istikharan nan da kikayi ba, bawanda ya cancanci soyayyarki sama da Afzal ki tuna da kalan hidiman da yaron nan ya miki ba ke kad'ai ba harta ni da Papinki. Be sanmu ba, besan daga ina muke ba amma ya d'au nauyin karatunki, kud'in takardu da handouts tun kafin ki tambaya yana baki amma ace kike wulak'antasa haka Baby? Wallahi samun mutum kaman Afzal a zamanin yanzu se an tone. An sani rabuwa da masoyi da zafi amma yaci ace kin yayyafawa zuciyarki ruwan sanyi be kamata ace har ki bari Afzal ya fahimci cewa bakiya sonsa ba."


  "Mami ni yaushe nace bana son Yaya? Wallahi ban ta6a furta hakan wa kowa ba."

  

  "Amma haka halayyanki suke nunawa abinda nake fad'a kenan. Kuka ne kawai be min ba ranan gabad'aya kin tada masa hankali har yake cewa shi ze hak'ura kawai a dawo maki da Abdul d'in haba mana Baby ki sani fa ba duk abinda mutum keso yake samu ba a duniyan nan. Yanzu gashi duk da kalan rashin mutuncin da kike masa hakan be hanasa baki kud'in k'arshen watan ki ba harda k'arin dubu ashirin akai."


  "Zan kirasa inyi masa godiya."


  "Da kin kyauta dan babu dad'i hakan kiyi hak'uri ki sani Abdul ya riga ya miki nisa ki bud'ewa Afzal zuciyarki sanin kanki ne Afzal baze ta6a cutar dake ba."


  "Mami na sani."


  "Toh kina iya tafiya Allah yayi maki albarka."


  "Ameen" da haka ta wuce d'akinta. Wayarta ta d'auka ta kira Maamah se a karo na biyu ta d'aga kasancewar bata san layin ba. 


  "Halo Maamah? Amal ce."


  "Amal? Ya kike."


  "Lafiya k'alau ya kwana biyu?"


  "K'alau ai na d'au nima baza a nemeni da sabon layin bane."


  "Haba Maamah ya gida?"


  "Lafiya k'alau jiya Ya Abdul ya kirani wai baya samun line naki."


  "Allah sarki Ya Abdul I miss him already please komin ya za'ayi karki basa sabon layi na bana son in cigaba da zolayansa Maamah, ina tausayawa kaina but I pity Ya Abdul the most."


  "Haka ma Mama tace."


  "Maamah I'm so sorry for hurting your brother."


  "Ba komai Amal ai yin Allah ne ba naki ba."


  "Thank you so much for everything."


  "You're welcome."


  "Toh sekiyi saving numban nawa se mun had'u a school ran monday."


  "Alright I'll" da haka sukayi sallama bata kaiga ajiye wayan ba sega call na Ya Abdul. Ko gaisawa be bari sunyi ba ya hau kurareta akan tabar duk abinda takeyi taje gidansu Amal taji ko lafiya haka kawai yana ji a jikinsa ba k'alau ba. Corner-corner tayita masa akan yau bazeyi ta fita ba seko gobe haka nan ma washegarin daya kirata tace ai taje gidan su Amal d'in Mami tace bata gida amma lafiyarta k'alau. Matuk'a hankalinsa ya d'an kwanta na jin lafiyanta k'alau amma rashin jin muryarta hankalinsa ya kasa kwanciya gabad'aya. 


  Amal ko sosai take kewansa sede gabad'aya ta rasa me take ciki, sosai maganan da Mami tayi mata keta yawo mata a kai tun jiya se tunanin magann take gashi har yau bata kira Afzal d'in ba seta d'au wayan zata kirasa se ta fasa. Haka tayita yi har tazo ta kirasa k'arshe. A lokacin suna tare da Nazeefah suna kallo, ya tashi ya amsa yana gudun kar ta fahimci wani abun, yayi rejecting call d'in kuma baze iya ba haka kawai ya rufe ido ya d'auka. 


   "Assalamu Alaikum" ta soma da cewa. 


  "Wa'alaikumus salam" ya amsa sa6anin yadda ya saba kiranta da Lily yau sallamar kad'ai ya amsa ita ko se ta d'au kodan abin da tayi masa ne yake fushi. 


  "Yaya I'm sorry" ta furta chan ciki-ciki. 


  "Ba komai karki damu."


  "Dama na kira ne inyi maka godiya tun jiya ina trying numbanka baya shiga" tayi mai k'arya. 


  "Ayya bakomai."


  "Wannan ne new line nawan se kayi saving."


  "Alright I'll se anjima" nan ya katse, da mamaki Amal ta tsaya kallon wayanta yau har Yaya ne ya katse waya a kanta? Hmm


   Nazeefah kuwa kallon sa ta tsaya yi tana nazari kode da budurwansa yayi wayan ne? Kud'i ya bata ne take godiya har yake cewa ba komai? Amma kuma ai idan budurwarsa ce baze bari ma ya amsa wayan a gabanta ba, toh ko business colleague tasa ce?


   Kwana hud'u Maamah ta jera tana raina wa Ya Abdul wayo tun be d'auki abun da zafi ba har ya fara zaton wani abun daban. K'arshe da abun ya ishesa Mama ya kira yake ce mata gashi kwana biyu baya samun Amal yayi da Maamah da ta had'asu amma abun ya gagara inda hali please ko ma waye ne asamu a tura gidansu Amal d'in aji ko tana lafiya, Mama bata nuna masa komai ba tace washegari zata tura ayo bincike se anan hankalinsa ya d'an kwanta sede har gari ya waye rana ya sauk'a Mama bata kirasa ba duk yadda ya k'osa haka ya hak'ura ya bari se a jibi sannan ya sake kiranta itama wani hujjan ta nema ta sake basa. Haka suka yita waina sa, suna masa wasa da hankali ba wanda ya iya fitowa fili ya sanar dashi zahirin abinda ake ciki, ta fannin Amal kuwa duk yadda take missing d'insa hakan besa ta d'au waya ta kirasa ba dukda cewan bata k'i hakan ba. So dayawa takan zuba numbansa da niyyan zata kirasa amma idan ta tuna da fad'an Mami na ranan seta fasa. Sosai fad'an ya shigeta haka ko tana kewansa sede ta rufe kanta a d'aki ta sha kukanta amman bade ta kirasa ba. Hotunansu kuwa har yau ta kasa gogewa haka zata zauna tana kalla tana kuka. 


  Ta fannin Afzal kuma tun kan amsan da Amal ta basa ranan akan cewa ita bata shirya auransa ba gabad'aya ya rasa walwalansa ko kiranta be sakeyi ba, a gida kuwa ba yadda Nazeefah batayi da shi ba amman yak'i sanar da ita halin da yake ciki haka ya bari abin yayita chin sa har seda wani attack d'in yaso kamasa. Daga fitan Nazeefah d'auko masa ruwa dawowan da zatayi kawai ta tarar da shi zube a k'asa se birgima yake yayinda ya rik'e saitin zuciyansa inda yake masa k'una sosai, se wani sama-sama numfashinsa ke masa. Salati tasa yayin da yasar da goran ruwan a k'asa ta nufi kansa da gudu tana k'walla masa kira. 


  Kafin ta tashi tace zata nemi mai gadi dan yazo ya d'aukesa su kaisa asibiti ya rik'e hannunta. "Don't call Ummi.." ya furta da k'yar yayin da ya shiga yin tari. 


  "Afzal so kake ka mutu ne? Barin kira D'an ladi stay calm kaji?" Ta buk'acesa a rud'e "Don't call Abba too please" ya rok'eta kai tayi saurin gyad'a mai sannan ta kira D'anladi nan da nan ya cicci6esa suka yi mota. Akan cinyarta ta ajiye kansa yayinda take ta kuka ganin yadda yake wasu irin abubuwan wane wanda ake cire ma rai. 


   Sintiri ta rink'ayi bakin k'ofan nasa gabad'aya ta rasa me take ciki gashi yace mata karta kira su Ummi shin ta biye masa ne ko ta kira sun? Amma kuma tasan halinsa sarai ba k'aramin aikinsa bane idan ya farfad'o ya gansu akansa yayi mata fushi. Haka nan ta rasa me take ciki chan da likitan nasa ya fito ta nufi kansa tana tambayansa ya jikin nasa. 

   Ya buk'aceta ne da ta kwantar da hankalinta Allah yaso an samu an kawosa asibitin da wuri tun kafin heart d'in yayi failing, an kuma basa immediate treatment yanzu sauran a jira farfad'owansa nan da kaman minti ashirin haka. Hamdala ta saki yayin da ta shiga yi masa godiya. Bayan sa tabi ta shige d'akin Afzal inda ta tsince sa kwance kan gadon, wane wanda k'wai ya fashewa a ciki haka sid'ak-sid'ak ta k'arisa ta zauna kan kujerar dake gefen gadon nasa yayinda hawaye ya ciko mata dam a ido. Sunansa da tace zata kira kawai se hawaye. Kuka sosai ta sha wajen ta rasa me ke janyo masa bugawan zuciyan, komi da ta sani baya so tana iya k'ok'arin dainawa amma ace ciwo yak'i ci yak'i cijewa? Ita abu d'aya take gudu ranan da zuciyar nasa zata buga gabad'aya tak'i aiki tasan ko sama da k'asa zata had'a ba wanda ze ta6a amincewa akan ba ita ce sanadin ciwon nasa ba. Tana cikin kuka ba makawan ne Afzal ya shiga kyafta idanunsa har ya bud'e su gabad'aya. Da mamaki ya tsaya yana kallon yadda take kuka gabad'aya se ta basa tausayi.


   "Afzal" ta kira sunansa a hankali ko amsata ya kasa. "Dan Allah idan wani abun nake maka wanda ka kasa furta mun please tell me I'm tired of seeing you collapsing everyday like this idan wani abun nakeyi maka wanda baka jin dad'insa please tell me."


  "Nazeefah" ya kira sunanta cikin dashasshiyar murya. 


  "Please tell me Afzal I promise zan yi iya k'ok'ari na inga na kiyaye."


  "Bar kukan haka kinji?" Yayi maganan yn neman share mata hawayen nata. Fuskan nata taja baya "Not until you tell me mey ke jawo maka attck haka please tell me idan nice."


  "Bake bace bar kukan haka."


  "How can I? Bazan iya ba Afzal so kake se idan ka mutu kowa yace nice na kashe ka? Dan Allah ka tausaya mun ka fad'a mun matsalar."


  "Nazeefah nima han sani ba all I want is ki kwantar da hankalinki baki da alak'a da rashin lafiya na kuma ko a gaban waye me zanyi defending naki kinji? Stop bothering yourself like this."


  "Then mey ke jawo maka?"


  "Nazeefah I'm sorry but I can't tell you."


  "Afzal nasan ba wani jituwan kirki bane a tsakaninku nasan nayi maka laifuka da dama I know I'm not the perfect girl for you, amma matarka nake kodan wannan matsayin please tell me."


  "I can't Nazeefah" ya sanar da ita. 


 "Saboda ban kai inji damuwanka ba?"


  "Sam, saboda nima ban san meke damuna ba, I have no idea why."


  "Ban yarda da hakan ba Afzal tun ba yau ba nasan kana 6oye mun damuwanka zan cigaba da addu' har izuwa rananda zaka fara fad'amun damuwanka I believe mey hak'uri shi kan dafa dutse ya sha romo, I love you Afzal I'll do everything to stay by your side this's how much I love you."


  "Thank you Nazeefah, come here" hannunsa ya bud'e mata a kasalance, a hankali ta shige jikinta dai-dai saitin k'irjinsa ta aza kanta yayinda ya rufeta da hannayensa yana mey shafa bayanta a hankali. "Forgive me for hurting you this much? I'm so sorry." Kai ta gyad'a masa a hankali yayinda ta sake shigewa jikinsa tana mey cigaba da kukan da takeyi. A nitse ya d'agota had'e da share mata hawayen ta "Kin kira su Ummi?"


  Kai ta kad'a "Kace kar na kirasu."


  "Very good thank you so much Nazeefah Allah miki albarka."

 

  "Ameen" kafin tayi wani k'wak'k'waran motsi wayanta ya shiga ruri dubawan da azatayi taga Mummy ke kira. "Waye ne?" yayi saurin tambayarta. 


  "Mummy" ta amsa cike da fargaba. 


  "Ki d'auka."


  "What if tana gida taje duba mu ne fah?"


  "D'auka kice mata mun fita." Hakan ta d'aga Mummy take ce mata gata da Khhaleefah bakin gate sunata honk amma ba kowa. Kaman yadda Afzal ya buk'ata haka tayi tace mata sun fita ne D'anladi kuma yaje duban gida. 


   "Can I use your phone to call Sultan?" Ya tambayeta bayan da ta kammala wayan. 


  "Sure" tayi maganan tana mik'a masa "Amma banida numbansa."

 

  "Don't worry I have it off hand." Numban Sultan d'in ya zuba ya kirasa. 

  "Halo Sultan?"


  "Triple A?"


  "Yes Sultan kana ina?"


  "Office ina ka ajiye wayanka inata kiranka baka d'auka."


  "Kazo TH please."


  "Subhanallah bade jikin naka bane?"


  "Yes but da sauk'i and please don't tell Umma banason su Ummi suji ina asibiti nima yanzu zance suyi discharging d'ina come quickly."


  "Alright I'm on my way." 

  Be 6ata lokaci ba ya kar6i excuse a office ya kama hanyan TH saidai kafin nan ya kira Amal yasan sarai itace sanadin komai. Tana d'agawa yake sanar da ita ai Afzal ya sake samun wani attack d'in yanzu haka ma yana TH an rik'e shi. Sosai gabanta ya fad'i salati kawai ta shiga yi har Sultan ya ajiye wayan. Yanzu mey zatace wa su Ummi? A banza tana neman kashe musu d'a. Bata jira lectures d'in ya k'are ba ta tattara jakarta ta fice kasancewar university da TH ba nisa kusan a tare ita da Sultan suka isa tana sauk'a a napep se gashi yana k'ok'arin shiga shima. K'arisawa tayi cikin motan nasa suka shiga tare. A waiting room yace ta jirasa gudun kar kuma suna shiga suci karo da Nazeefah. Bayan ya k'arisa d'akin Afzal suka gaisa da Nazeefah sannan ta basu waje. 


   "Amal ce har yanzun?" Sultan ya soma da tambayansa. 


  "Sultan haka so yake?" Ya tambayesa a raunane. "Tunda nake ban ta6a son wani mahaluk'i sama da iyayena a duniyan nan ba, ban san haka so yake da sharri ba da nayi duk abinda zan iya na hana son Amal shigewa zuciyana."


   "Triple A..."


  "Sultan I'm tripping" ya katsesa, "Ban san ya zanyi da son Amal ba, ina sonta amma kona second d'aya bata sona, bata da niyyan bani daman in kasance masoyinta. she disperses me Sultan help me out please, ina jin idan ban samu Amal ba ina iya rasa rayuwana."


  "Calm down Afzal, meya faru?"


 "Komai ma ya faru ni yanzu nakega kawai zan hak'ura ne zan nemi transfer in d'au Nazeefah mu bar nan kawai maybe by doing so Allah ze rage mun sonta a zuciya, gar da gar ta nuna mun she can't marry me ya kake tsammanin zanji? I've tried my best to forget it but I can't, da kalamunta kullum nake tashi nake yini, I'm mad over her. And to be frank, I'm tired of seeing Nazeefah like this, gabad'aya ta d'au laifin komai ta d'aura wa kanta, na gaji I don't know what to do again."


  "Mun taho tare da Amal" ya sanar dashi.


  "You what?" Ya tambayesa cike da d'umbun mamaki. 


  "Yes tana waiting room, kana kirana itama na kirata se muka k'ariso tare."


  "Why? Meyasa ka kirata? So kake su had'u da Nazeefah? Maza why?"


  "Saboda tasani idan ta cigaba da abinda take yi maka tana iya jefa rayuwarka cikin matsala."


  "And? Ba wai kaman ta sona bane bale idan rayuwan nawa ya shiga matsala hakan ya dameta."


  "Taya zakace Amal bata sonka Triple A? Ai zuciya bata ta6a k'in me kyautata mata ya kamata ka gane cewa Amal na duk abinda takeyi ne saboda haushinka da takeji na shiga tsakaninta da Abdul amma bayan nan wallahi ko ita bata isa ta buga k'irji tace bata sonka ba."


  "Wai kam bakaji me ta fad'a mun bane? Amal bata sona."


  "Amal na sonka Afzal she's just too broken to realize that, gabad'aya soyayyar Abdul ne ya rufe mata ido aikinka ne ka maye gur6insa a zuciyarta idan ko kayi sakaci kana iya rasata har abada amma so kam akwai shi achan k'ark'ashin zuciyarta."


  "Ko meyasa kace haka?"

  

  "Da bata sonka da baza tabar duk abinda takeyi ta iso nan atake da na kirata ba, and you know the funniest part? Ta jirani a waiting room d'inma tak'i wai sam semun k'ariso tare, kallo d'aya mutum zeyi mata yasan tana cikin tashin hankali. Gabad'aya ta rasa natsuwarta a haka zaka ce bata sonka? Yanzu that aside, ya za'ayi in shigo da ita?"


  "I don't know nide bana son su had'u da Nazeefah ban shirya ma wani masifan ba."


  "Kasan ya za'ayi? I'll call Nazeefah se kace mata kana jin yunwa taje tayi maka girki kafin ta dawo de nasan Amal harta tafi."


  "Sultan nifa bana son su had'u."


  "Trust me" yana fad'in haka ya fice ya kira Nazeefah akan Afzal na nemanta. 


  K'arisowa tayi ta tsaya a kansa tana shafa kansa a hankali "Kana buk'atan wani abu ne?" Ta tambayeshi a maraice. 


  "I'm hungry" ya sanar da ita. 


  "Mey kakeson ci?" A farko yayi niyyan cewa stew tuna akwai stew a gida seyace spaghetti. 


  "Toh bari D'anladi ya zo ya kaini gida inyi sauri in had'a maka, shikenan ko kana buk'atan wani abu?"


  "Shikenan."


  "Alright I'll be right back."


 "Thank you."


  "Don't mention" murmushi kad'an ta sakar masa sannan tayi sallama da Sultan ta fice. Nan suka samu suka shigo da Amal. 


  Tana shiga ciki tayi kan gadon nasa a guje had'e da rushewa a gabansa tana kuka sosai sede ko kallonta Afzal beyi ba. Kukan tayita yi chan ta d'ago kanta ta shiga basa hak'uri. "Yaya I'm so sorry please kar ka mutu."


  "Bakiya son ya mutu kuma kike wulak'antasa haka Amal? Afzal d'in? Bari in kira su Mami in sanar dasu halin da kika jefasa daga nan se asan nayi idan ma rabaku za'ayi toh don da shi zefi alkhairi ma because bazan iya jure ganinki kina destroying min life na amini ba, Amal baki san idan kika cigaba da hakan ba kija iya zamewa sanadin mutuwansa ba?" 


  Kuka take sosai tace, "Ya Sultan please don't call Mami wallahi tana iya kasheni da duka kuma ya kake magana haka? Sanin kanka ne Yaya yafi k'arfin in wulak'antasa."


  "Kuma shine kike wulak'antasa hakan?"


  "Ni ban wulak'anta Yaya ba, sanin kanka ne ina son Yaya, Yaya please say something." Sede ko kallonta Afzal be juya yayi ba. 


  "Toh ai ba haka ake so ba Amal kowa ya sani rabuwa da masoyi da ciwo amma ya zamo dole ki hak'ura tunda an riga an bada ke wa Afzal ko ba haka ba?" Kai ta gyad'a a hankali. 


  "Yanzu haka iyayensa basu da labarin yana asibiti saboda baya son ya had'a kanku amma still kina wulak'antasa haka? Sanin kanki ne Afzal na sonki I don't have to tell you."


  "Ya Sultan I'm sorry dan Allah kayi hak'uri."


  "Ni baki yi mun komai ba Amal, Afzal zaki bawa hak'uri let me excuse you two" daga fad'in haka ya mik'e ya fice tare da ja musu k'ofan. Shiru ne ya rufesu a d'akin Afzal yak'i yayi magana itama Amal tayi shiru bata sake cewa komai ba. Chan ta numfasa had'e da kiran sunansa. 


  "Yaya please ka juya ka kalleni kaji? Yaya I'm sorry please look at me" ganin har yanzu be juya yako kalleta ba ai seta rushe da kuka wajen. Kuka sosai take tun Afzal na iya jure sautin kukan nata har abun ya gagara, be san a lokacinda ya juyo yana kallonta ba don kukan Amal ba k'aramin tada masa hankali yake ba. 


  "Yaya I'm so sorry dan Allah kayi hak'uri please don't go and leave me, I'm here please don't go."


 "You're not here Lily, you're never here. You don't love me, you don't even care about me baki damu dacna rayu ko na mutu ba. Lily nasan ni mey laifi ne but I'm sorry, bazan kuma gaji da baki hak'uri ba but please ki amince ki aureni, Lily bazan iya rayuwa ba ke ba you've become a part of who I am that I can't do without, you complete me, I feel so incomplete and lost without you. Lily idan baki kasance mallaki na ba ina iya rasa rayuwa na. I'm sorry but I love you, I love you morethan life itself, your love runs in my veins duk yadda naso 6oye soyayyarki hakan ya gagara, duk yadda na so cireki daga zuciyana nakasa, Lily I was created for you. Nazeefah might be my wife but you're my home, my soul, my happiness and life, please don't let me go astray."


  By now kuka Amal take sosai. A hankali kalamun Afzal suke shigewa jikinta suke kuma tasiri, tabbas ba k'arya ko d'aya acikin kalamunsa tasani batada masoyi sama da shi abu d'aya yake hanata sakewa da shi idan ta tuna yadda ya rabata da Abdul sede kuma da ta zauna tayi tunani, seta gano komi na faruwa ne saboda dalili. Allah nada dalilin daya ya turo Abdul rayuwarta ya kuma ciresa a lokaci guda, dalilin kuwa itace ta sani cewa ba duk abinda mutum yakeso yake samu ba a rayuwa. Hawayenta ta shiga sharewa a hankali ta soma da cewa;


   "Rana d'aya Allah ya kawo ka cikin rayuwana Yaya, acikin k'azanta da yarinta ka ganni ka kuma ce kana sona, baka sanni ba, baka san daga ina na fito ba, bakasan suwaye dangi na ba ka nuna min so da k'auna ka kuma ja ni jiki tamkar k'anwar ka ta jini ka k'ara bani daman kiranka Yayana. Rana d'aya bayan na cira ran zan sake komawa boko ka dawo mun da mafarki na ka nuna min everything is possible with you and God, ban ta6a neman abu na rasa a k'ark'ashinka ba Yaya. Damuwa na tun kafin in furta kake yaye minsu, baka wasa da sha'ani na komai nakeso shi kake mun taya bazan so ka ba Yaya? Idan nace bana sonka wallahi na zama mak'aryaciya but I love Ya Abdul too, ina sonshi amma bawai hakan na nufin ina shirin rasaka bane. Ina iya sadaukar da raina maka Yaya, batun maganan mu na ranan kuma ina sake neman gafararka kayi hak'uri na baka amsa bisa rashin tunani da shawara da nayi. Yaya idan har aurena ne ze farinta maka rai then I'm ready to be your wife, ko a yau kakeson in kasance matarka na amince zan aureka but please ka dena tada hankalinka a kaina haka bana son abinda ze ta6a lafiyanka bana son a sanadi na ka rasa rauwanka, dan Allah ka yayyafawa zuciyarka ruwan sanyi ka sani I'm only yours and no one else's."





RANA D'AYA

#RD


 Love... King Miemiebee👄✨

[13/08, 09:28] ‪+234 907 483 8352‬: 🎀🎀🎀                 🎀🎀🎀

                🎀❣🎀

                   ❣❣


  💦💦                      🍃🍃🍃          

           *RANA D'AYA!*

  💦💦                      🍃🍃🍃

  July, 2018

 beeenovels.blogspot.com


     _Written by Miemiebee👄_



   *PAGE 2⃣2⃣*


   

      Har cikin ransa yaji dad'in kalamunta dukda cewan ya san ta fad'i komai ne don kawai yaji dad'i bawai don har cikin zuciyanta tana nufin hakan ba, yasani tausayinsa kawai takeji bawai sonsa take ba. 

  "Yaya why are you not saying anything?" Ta tambayesa a sanadin shirun da yayi. "Dan Allah kayi hak'uri."


  "It's okay Lily you should get going thank you."


  "Yaya fushi kake dani har yanzu?"


  "Sanin kanki ne komin mey kikayi mun bazan ta6a iya yin fushi dake ba Lily."


  "Shine ko kallona bazaka juya kayi kace ka hak'ura ba?"


  "Will it change anything?" 


"Please Yaya kayi hak'uri Wallahi bazan iya jure fushinka ba." 


  "Toh na hak'ura" ya fad'a had'e da juyowa yana kallonta kaman yadda ta buk'ata. "Bar kukan haka toh" hannu tasa ta shiga share hawayenta. 


  "Thank you so very much, barin koma toh Allah k'ara sauk'i."


  "Ameen thanks too bari inyi ma Sultan magana ya kaiki gida."


  "A'a no need daga school nake zan koma I still have one lecture to attend" tayi maganan tana duban agogon hannunta. 


  "Are you sure?"


  "Yes Yaya" ta amsa had'e da sakar masa k'aramin murmushi. 

  

  "Alright you take care" a waje ta tarar da Sultan tayi masa sallama sannan ta fice. 

  Bada dad'ewa ba Nazeefah ta kawowa Afzal abincin, bayan ta basa ya ci ya buk'aci Dr'n da ya sallamesa. 


****

   Ta fannin Abdul kam k'aramin hauka ne kawai beyi ba, yau ko fita office ya kasa, banda tunanin Amal ba abinda yakeyi, gabad'aya ya rasa mey ke masa dad'i yau kwana nawa amma a rasa wanda zeje ya duba masa lafiyar Amal? itama Amal d'in kwana nawa yau amma bazata nemesa ba? Anya kuwa lafiya? Tunani de ba wanda beyi ba. Toh kode su Mami sunyi mata miji ne a gida suka hanata yin waya dashi suka amshe mata wayan ma gabad'aya? But ai bazasu ci amanar sa haka ba bayan seda ya tura su Baba da su sanar dasu shi yayi kamu then what could be the problem? Kwana yayi yana nazari, washegari da yamma ya kira Maamah. Har tsoron picking call d'in take amman haka ta d'aga don ba yadda ta iya. 

    

   "Maamah what is going on?"


  "Game da mey Ya Abdul?" Ta tambayesa tamkar bata fahimci inda ya dosa ba. 


  "Please tell me meke faruwa meyasa line na Amal baya shiga?"


  "Ya Abdul ban san-"


  "Maamah we both know you're lying sarai kinsan meyasa, dan Allah nace please tell me it's been over a week bana samunta har Mama nasa aje aji mun ya take amma shiru. I can smell it something is not alright."


  "Ya Abdul-"


  "Ki fad'a mun kinji?" Ya katse ta "Idan ma abu ne yasamu Amal d'in kuke 6oye mun just tell me I promise bazanyi reacting ba."


  "Ya Abdul ba abinda ya samu Amal, lafiyarta k'alau."


  "Then meya faru? Meyasa bata picking call d'ina?"


  "Ya Abdul I'm sorry."


  "Fad'a mun kinji? Kar kiji komai."


  "Kayi hak'uri amma bazan iya ba."


  "Meyasa?"


  "Na d'au alk'awarin komin yaya baza aji mutuwan sarki daga bakina ba, kayi hak'uri."


   "Aure Amal zatayi ko?" Ya tambayeta a hankali daga yadda yake magana mutum zesan zuciyarsa a karye take, sosai ta sha mamakin yadda ya gano hakan ba tare da wani ya sanar da shi ba. 


  "Ya Abd-"


  "Aure zatayi ko?" Yayi saurin katse ta "Just answer me."


 "Ya Abdul I'm sorry."


  "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" taji ya furta. "Meyasa baki fad'a mun ba Maamah?"


  "Nima labarin be dad'e da iske ni ba."


  "Ban yarda ba Maamah, dalilin da yasa Baba suka turoni nan dan Amal zatayi aure ne ko?"


  "Ya Abd-"


   "Just tell me yes or no kar kiyi mun k'arya" ya buk'aceta. 


  "Yes" ta furta a hankali "Amm-" be bata daman yin magana ba ya katse wayan. Nan take ta shiga kiransa sede tuni ya kashe wayan gabad'aya. Wajen Mama ta ruga aguje tana mata kuka "Mama Ya Abdul ya gano gaskiyan al'amarin he knows everything."


  "Kaman ya? Ban fahimceki ba." Nan ta kwashe duk yadda sukayi da Abdul ta zuba mata. "Jeki ki d'auko mun waya a d'aki yi sauri." Nan da nan taje ta d'auko ta kawo mata, layin Abdul ta shiga kira duka biyu amma switched off kukeji. Tirk'ashi idan hankalinta yayi dubu be tashi ba. Baba ta kira a office take sanar dashi halin da ake ciki, dama ya sani komin jimawa wataran Abdul ze gano gaskiya don haka ya buk'aceta da ta kwantar da hankalinta zeyi ma abokinsa dake chan wanda ya samowa Abdul aikin da yaje ya dubasa. Har anan hankalin Mama be kwanta ba, Maamah kam se kuka takeyi. 


  Tunda ya kashe wayan nasa ya shiga aikin kuka, kuka yake sosai kaman d'an yaro yayinda zuviyarsa keyi masa k'ona, ji yayi komi ya fita masa a rai, ina ma ba a k'addaro masa da wannan rana ba. Shikenan shi kuma tasa jarabawar kenan? Akan 'yan matan da yakeso? Until when ze samu sanyin idanunsa tunda gashi Amal da yake sa ran kasancewa da ita har k'arshen rayuwansa ma ta tafi ta barsa. Wai shin meyasa be gane gaskiyan al'amarin bama tun a farko? Ai da abun tambaya yadda duk cikin fad'in gun aikin nasu aka d'aukesa k'walli d'aya tal aka basa appointment letter'n. Da akwai abin tambaya game da yadda su Baba da ita kanta Amal d'in suka nace cewan lalle-lalle seya kar6i aikin. Meyasa be gane cewa aure Amal zatayi ba tun daga kan lokacin da ta soma yi masa kuka a waya haka kawai ba dalili har izuwa ranan daya tafi, kukan da ta keyi yafi k'arfin ace wai kawai na rabuwa da masoyi ne, ashe na zafin rabuwa dashi gabad'aya ne. Meyasa? Meyasa bata sanar da shi ba? Meyasa su Baba suka yita zolayarsa suka k'i sanar da shi gaskiyan al'amarin? Mey yayi zafi da har se sun turosa Canada? Gabad'aya he felt used and abandoned. Ganin kukan baze amfanar dashi da komai ba ya mik'e a raunane ya shige bayi inda ya bud'e shower akansa ruwan na zuba wala Allah hakan zey sanya sa mancewa da d'umbin matsalolinsa. 


   Ranan Abdul beyi bacci ba, se tunanin yadda Amal taci amanansa kawai yake. Saidai kuma da ya nutsu ya zauna yayi tunani yaga haka kawai fa Amal bazata rabu da shi ba, ba tare da wata k'wak'k'warar dalili ba, yana da tabbacin cewa ba a son ranta ta aikata koma mey tayi ba, ze iya rantsewa akan irin soyayyan da Amal takeyi masa, shi kansa yasan Amal na sonsa so kuma na tsakani da Allah ba yadda za'ayi ta amince zata auri wani ba don wani k'wak'k'waran dalili ba, what could be the reason? He need answers. 


*****

   Kaman yadda ta saba yi idan ta tashi kullum da safe hakan yau ma tayi, hotunan Abdul tasa a gaba tana kalla tana kuka, duk yadda takeson mancewa da shi abun ya gagara. Ba abinda takeso sama da ta saurari muryansa, she misses him so much, she wants to know how he's doing, what he's doing and all. Bata tsammanin zata iya cigaba da rayuwa ba shi badan tanaso ba ta share hawayenta ta mik'e. Kitchen ta zarce inda ta had'awa Afzal kunun aya da aldeb ta d'ura cikin silver flasks da ta saya da sunansa sannan ta wuce bayi tayi wanka ta shirya zuwa school. A office na Sultan ta tsaya ta mik'a masa sak'on Afzal sannan ta basa nasa shima take rok'ansa idan ya samu dama ya kaiwa Afzal kuma tana gaishe sa da jiki. 

   

  Bayan Sultan ya idar da sallan Azahar ya zarce gidan Afzal inda ya tarar da Afzal d'in kad'ai a gida kasancewar Nazeefah ta tafi school. Bayan sun gaisa ya mik'a masa sak'on Amal. Sosai Afzal yaji dad'i baze iya tuna when last yayi tasting hand made smoothies na ta ba, he really misses it alot. A fridge ya ajiye, se bayan La'asr Sultan ya tafi. Da Maghrib bayan Nazeefah ta idar da sallah ta wuce dining space dan d'auko ruwa kawai taci karo da flasks har biyu cikin fridge d'in wanda take da tabbacin ba nata bane. Sa idon da zatayi ta tabbatar da cewa ba yau ta soma sa flasks d'in a ido ba sanda take amarya sau dayawa Afzal yakan taho da flasks d'in har akwai lokacinda ta gwada d'aukan d'aya zata sha ya k'wace yake cewa ai wacce ta basa batace ta bata ba. Toh fa wata sabuwa! Shin flasks d'in waye ne wannan d'in? Kode na budurwarsan ce? Amma kuma ai kwana biyu bata jinsa yana waya har yaushe yayi wata sabuwa da zata fara kawo masa drinks? But she's sure wannan flasks d'in sune na budurwarsa ta da yau ya zatayi? Ina zata sa kanta? A rayuwa in akwai abinda ta tsana shine taga ko kuwa taji Afzal na kula wata. Zata iya jure komai amma banda kishiya, flasks d'in ta zaro ta ajiye akan table tana jiran dawowan Afzal. Be dad'e ba se gashi ya shigo, zuciyarta ta danne tayi mai sannu da zuwa sosai gabansa ya fad'i ganin flasks d'in da yayi a gabanta shin wai meya hanasa sanyasu cikin fridge na d'akinsa yasa key? Tashin hankali. Takawa yayi a nitse ya k'arisa dining table d'in "Zaki sha ne?" Ya tambayeta. Kai zalla ta kad'a. 


  "Then meyasa kika fito dasu? Naga acikin fridge d'in zasu fi yin sanyi."


  "Afzal?" Ta kirasa "Flasks na waye ne wannan d'in?"


  "Kaman ya na waye kuma?" Mik'ewa tayi ta tsaya "Ba wannan ne ba karo na farko da nake tarar da flasks d'innan a gidan nan am very sure na mutum d'aya ne tambayata itace ta wace ce?"


  "Nazeefah-"


  "Ta budurwarka ce ko?" Tayi saurin katse sa. 


  "Budurwa kuma Nazeefah?"


"Tun da nake amarya ina ganin flask d'innan tana kawo maka smoothies aciki yanzu ma taji batun rashin lafiyanka ne ta kawo maka kenan ko?"


  "Wani irin magana kike haka Nazeefah? Dan kinga flask shikenan seki ce na wata?"


  "Toh na waye ne?"


 "Na Umman Sultan ne" ya had'e mata k'arya nan take. 


  "Umman Sultan?"


  "Baki yarda bane? Ki tambayi Danladi d'azu Sultan ya kawo mun."


    "Taya tasan baka da lafiya bayan kace kar a sanar da kowa?"


  "Well Sultan told her before I could stop him."


  "Kana nufin tun fari itake kawo maka smoothies d'innan?" 


  "Nazeefah zan miki k'arya ne? Come here" hannunta ya kama ya jata jikinsa had'e da rik'e k'aramin k'wank'wasonta. 


  "Ba k'arya kake mun ba ko?"


  "Haba in miki k'arya." Kanta ta kwantar bisa k'irjinsa had'e da kewaye hannayenta a bayansa "I love you so much Afzal, ban tunanin zan iya sharing d'inka da wata, ina kishinka sosai please promise me bakada wata budurwar a waje." A hankali ya d'agota had'e da rik'o fuskanta cikin hannayensa "What does it matter koda ina da wata budurwar a waje Nazeefah? You'll always remain the Queen ke bakisan kece uwar gida ba?"


   "Yanzu kana nufin akwai wata a waje kenan?"


  "Ni bance ba" yayi saurin cewa. 


  "Afzal ba k'arya kake mun bako?" Matso da fuskansa yayi kusa da nata had'e da sauk'ar mata da gentle kiss a goshi "Stop bothering yourself okay? In kawo mana cup? Ko bakison ta6a aldeb na Umman Sultan?"


  "Bari in kawo mana" a nitse ya saketa ta zarce kitchen ta d'auko musu cups d'in. Har suka gama cin abincin Afzal se tunanin kalaman Nazeefah yake, ya santa ya san d'anyen aikinta ta ina ze soma sanar da ita batun Amal yanzu after making it clear ita akan kishiya zata iya aikata komai. Hmm!


***

   Kwana biyu iyayen Abdul suka jera suna nemansa amma wayoyinsa duk switched off kaman yasan Baba na iya turo abokinsa yazo ya dubasa ya tattara kayakinsa ya gudu hotel inda yake kwana. Ko fita office baya yi haka ze yini a d'aki yana tunanin Amal tamkar wani zararre ya koma. Se a daren na uku ne ya kunna wayansan, yana kunnawa kiran Mama na shiga kaman wanda baze d'auka ba yayi answering. 


   "Abdul! Alhj Abdul ya d'au wayan" ta sanar da Baba dake gefenta. "Abdul Baba na dan Allah kayi hak'uri."


  "Mik'o mun wayan" cewan Baba sede tak'i ita se taji muryan Abdul tukuna. 


  "Abdul yi hak'uri kayi mun magana, Mama is sorry."


  "Mama why?" Abinda ya fara tambayarta kenan. Matuk'a ya bata tausayi har takeji da ma tun farko ta sanar da shi gaskiyan kawai da war haka zuciyarsa ma ta warke. 


  "Abdul kayi hak'uri ka sani we only want the best for you."


  "Best for me Mama? A ganinku 6oyemun gaskiyan al'amari da turoni Canada shine abinda yadace?"


  "Abdul kayi hak'uri daga ni har mahaifinka ba wanda yake da zuciyan fad'a maka wannan abu, bamu san ta ina zamu fara sanar da kai ba amma kayi hak'uri."


   "Yaushe ne auran nata?"


  "Muma bamu sani ba Abdul but anytime soon."


  "Wa zata aura?"


  "Abdul ba amfani."


  "Just tell me."


  "Afzal."


  "Afzal??" Ya nanata da mamaki "Afzal??" Ya sake tambaya. 


  "Eh shi."


  "How???"


  "Abdul its a long story amma inason ka sani Amal masoyiyarka ce ta hak'ik'a, kuma ko da wasa kar kawo a ranka cewa taci amanar ka."


  "What happened Mama?" Gyaran murya tayi sannan ta kwashe labarin duk abinda ya faru ta basa bata bar komai ba. Gabad'aya se ya dena tausayawa kansa ya shiga tausayawa Amal. Tabbas Amal ta cika masoyiyarsa ta hak'ik'a kaman yadda Mama ta fad'a. Inde haka ne toh Allah sa hakan shi yafi alkhairi a garesu duka, ya kuma bawa Afzal ikon rik'e ta da amana sede bai tsammanin ze iya daina son Amal. Sam beso hakan ya faru ba, yaso ace shine mijin da ze kula da Amal, mijin da ze zauna da ita har ila k'arshen rayuwarta, yaso ace shine mijin da zata haifan masa yara rabi masu kama da shi rabi masu kama da ita sede kana naka Allah na nasa. 


  "Ga Babanka nason yi maka magana."


  "Toh ki bashi."


  "Baba na?" Baba ya kirasa. 


  "Na'am Baba ina yini?"


  "Ya kake?"


  "Lafiya" ya amsa sama-sama. 

   Hak'uri sosai Baba ya shiga basa amma ya nuna masa shi fa ba komai, abinda Allah ya riga ya k'addara bashida makawa and everything happens for a reason he's sure Allah nada dalilin shiga tsakaninsa da Amal da yayi, abu d'aya kawai yakeso a taya shi da addu'a Allah yasa rabuwa da Amal d'in shi yafi mashi alkhairi. Sosai Baba yaji dad'in kalamunsa daman yasan d'ansa da tawakkali, albarka yayita sa masa k'arshe yake tambayansa ko ze dawo gida ne? Yaso se a saya masa sabon aiki koma wani iri yakeso. 


  "A'a Baba nagode zan cigaba da zama nan d'in kawai."


  "Are you sure?"


  "Yes Baba ba amfanin dawowa na, gara inyi zama na anan ko wala Allah a hankali Allah ze yaye min son Amal."


  "Toh shikenan zamu tayaka da addu'a, so se yaushe zaka zo mana kenan?"


  "After a year or two in shaa Allah nan d'in yafi mun kwanciyan hankali."


  "Toh Allah yima albarka Baba na, Allah ya mayar maka da wacce tafi Amal kuma, addu'an mu na tare da kai a kullum."


  "Nagode Baba."


 "Toh ga Mamanka tana son yima magana." Itama Mama addu'a tayita masa tana sa masa albarka bayan nan sukayi sallama. Washegari Maamah da Amal suna zaune a makaranta tana bata labarin yadda suka k'aya da Ya Abdul jiya se kwatsam gashi yana kira bata 6ata lokaci ba ta d'aga bayan sun gaisa yake tambayarta ko tana gida ne. 


   "A'a ina school" ta amsa. 


  "Kuna tare da Amal kenan" kafin tayi tunanin yi masa k'arya yace, "Bata kinji? I just want a word with her" batayi gardama ba ta juyo gefen Amal. "Ya Abdul na son yi miki magana" ta sanar da ita. Kai Amal ta shiga kad'awa "I can't speak with him Maamah bazan iya ba ki basa hak'uri."


  "Sabida mey?"


  "Maamah naci amanan Ya Abdul , har abada bana tsammanin zan iya sake yi masa magana, kunya baze barni ba. "


  "Ya Abdul tak'i amsa" ta sanar da shi. 


  "Dalili?"


  "Wai she can't spek to you ever again kunyan abinda tayi maka take."


  "Sa a handsfree" ba musu ta sanya "Amal?" Ya kirata sede ta kasa amsawa. 


  "Amsa kinji? Kar ki damu" se kad'a kai take yayinda hawaye ya shiga ciko mata a ido amma ta kasa amsan wayan. "I'm not hanging up unless kinyi magana" hakan ko yak'i kashe wayan kud'insa se tafiya yake a iska ganin asaran ya soma yin yawa kawai ta amshe wayan daga hannun Maamah ba don taba so ba tare da miyarwa a headset "Ya Abdul" ta kirasa cikin sauti me rawa. 


  "Amal shikenan idan ban nemeki ba bazaki sake nema na ba? Haka akeyi?"


  "Ya Abdul ba haka bane amma dan Allah kayi hak'uri."


 "Bade kuka kike ba?"


  "I'm not cryi-" kukan ne yaci k'arfinta tama kasa k'arisa zance nata. Hak'uri yayi ta bata har seda ya samu kukan nata ya d'an lafa. 


  "Meyasa baki fad'a mun ba Amal?"


  "Ya Abdul ta ina kake tsammanin zan soma sanar da kai wannan labari mara dad'i mey uban d'aci? Dan Allah ka gafirceni nasan naci amanarka, naci amanar soyayyarka but I'm so sorry wallahi ba a son raina na rabu da kai ba. Yaya was dying and soyayyata kad'ai ce zata iya ceto da ransa, bazan iya barinsa ya mutu ba inspite of all the good fortunes da yayi mun dan Allah kayi mun kyakkyawan fahimta" ta k'are maganan cikin kuka. 

 

  "Amal I know ba'a son ranki kika rabu dani ba and I do understand everything, nasani Allah ne ya rabamu and am sure yana da dalilinsa na yin hakan I'm just hurt and broken saboda baki sanar dani ba kikayi ta zolayata for all these while."


  "Please forgive me amma zolayarkan ce kad'ai mafitar da nake da, banason a sanadin sanar dakai gaskiyan al'amarin wani abu ya samu kafiyarka Ya Abdul I value your life morethan I do value my own, idan har abu ya sameka ban tsammanin zan iya yafewa kaina shiyasa na buk'aci iyayenka da nawa kar su sanar da kai, I'm terribly sorry."


  "A tunaninki canza layi da kuma daina nema na shine baze cutar dani ba Amal? If only kin sanar dani ko kuwa kin bari an sanar dani da zuciya na baza ta min k'una da ciwon da takeyi mun yanzu ba, I felt used and abandoned."


  "I'm so sorry Ya Abdul bana son ka d'au naci amananka ne, please forgive me."


  "Na sani Amal bazaki ta6a cin amana na haka kazai ba. Kuma ba k'aramin lada kike dashi ba na yafe farin cikinki dan ceto ran Afzal ba, only God shall repay you."


  "But I never wished for it Ya Abdul, gabad'aya rayuwa na da kai nake planning. Na gama sa ran da kai zan raya sunnan manzo, I never wished to be separated from you, please believe me."


   "Shhh! Na yarda dake Amal kuma nasani Komai na faruwa ne bisa dalili Allah nada dalilin raba mu da yayi fatanmu kawai Allah sa hakan yafi alkhairi."


  "Please forgive me."


  "Baki yi mun komai ba Amal, ina iya rantsewa akan soyayyan da kika nuna min and har in mutu bazan ta6a mancewa da hakan ba, ina alfahari da ke Amal, tabbas kin cika masoyiyata na hak'ik'a and I shall never forget that just keep praying kinji?"


  "Ya Abdul I miss you, I terribly miss you" ta sanar dashi cikin tsananin kuka. 


 "I miss you even more my Princess, bazan iya kwatanta zafin rabuwa dake da nake ji ba but God's plan is the best, Allah tabbatar da alkhairi tsakaninki da Afzal ya sa ya kula mun dake kaman yadda ya saba da a baya."


  "Ameen" ta amsa a hankali. Kai kuma fa Ya Abdul? Wa ze kula mun da kai? Wa ze baka dukkan farin cikin da ka cancanta?" 


  "Allah, Allah ze ban dukkan ababen da kika k'irga Amal just pray for me."


  "Ya Abdul you're one of a kind, kafin a samu irinka se an tona. Allah ya baka mace wacce ta fini da komai wacce zata soka fiye da yadda na ta6a sonka, wacce zata sa kamance da ni a rayuwarka gabad'aya."


  "Ameen Amal amma bazan ta6a mancewa dake ba, bana tsammanin akwai macen da zata sanya ni in mance da kalan tsaftcacciyar soyayyar da kika nuna mun. Amal kin riga kin zamo 6angare a jikina, I'll forever cherish our relationship, I'll forever love you."


  "I'll forever love you too Ya Abdul or even more, thank you for understanding me."


  "My pleasure bar kukan haka kinji? Kinga nima kina sani" yayi maganan yana tare hawayen dake shirin zubo masa. 


  "Na daina please don't cry" ta amsa tana share hawayenta. 


  "Toh se wataran kuma Amal, take care of yourself-" Katse wayan kawai tayi, ta ma kasa barinsa ya k'arisa abinda yayi niyya yayinda ta rushe da wani irin masifaffen kuka. Shi kansa Abdul hawaye yake da ya sauk'e wayan he still can't believe sun rabu da Amal, matar da yake sanyata cikin duk wani plan na rayuwarsa aciki, matar da baya iya d'aukan minti biyu beyi tunaninta ba, "oh Allah you know what is best for me" ya furta a hankali yayinda yake share hawayensa. 


   Har zuwa Azahar Amal bata bar kukan da takeyi ba, Maamah se hak'uri take bata amma abun ya gagara. Suna zaune a masallci bayan sun idar da sallah sega wayanta yana ruri. Maamah ce ta ciro daga cikin jakar had'e da duban wake kira. 


  "Waye ne?" Amal ta tambayeta tana duban yadda fuskanta ya kumbura timm acikin madubi. 


   "Yaya ne" ta amsa. Kaman tace mata ta kashe saidai kuma ta d'au alk'awarin bazata kuma wulak'antansa ba, bata son abu ya sake samun lafiyansa. Haka ba don tana so ba ta d'aga. "Yaya" ta fara da cewa. 


  "Na'am Lily" ya amsa. 


  "Ina yini?" Ta gaishesa. 


  "Lafiya k'alau ya kike ya school?"


  "Alhamdulillah ya jikin naka?"


  "Na warware Alhamdulillah."


  "Toh Allah k'ara sauk'i."


  "Ameen inzo muje muci lunch?" Shiru tayi tana nazari har ga Allah bata da niyyan fita dashi yau ba don komai ba kuma se don kukan nan da tayita yi fuskanta ya kumbura, tabbas tasan yana ganin yadda fuskanta yayi timm d'innan ze hau tambayarta dalili. Tsoronta d'aya ne kar ya gane gaskiyan al'amarin k'rashe kuma ciwonsa ya sake tashi. "Lily?"


  "Na'am Yaya."


  "Inzo? Or are you busy? In baze yuwu ba just tell me kinji?"


  "A'a kazo Yaya I'm free." Sanyi yaji sosai "Alright I'm on my way."


   "Toh sekazo" nan ta katse. 


  "Maamah nakega kiyi joining su Aisha kawai Yaya yace zezo muje muci abinci."


  "Ayyah toh ba matsala adawo lafiya."


  "Thank you" nan ta mik'e ta bi su Aisha. Yayinda da Amal ta zaro kwalli daga jakarta taja a idonta sannan ta shafa powder duk wai don ta d'an 6oye kumburin fuskan nata amma ina da anganta ansan ta sha kuka, kukan ma mey wuya. Bada dad'ewa ba sega Afzal ya k'ariso kasancewar Nazeefah bata fita school ba yau se yayi tunanin suci abincin a cikin makaranta kawai. Unimaid garden suka k'arisa se anan yake tambayarta meya faru. 


  "Babu" ta amsa sama-sama tana kare fuskarta. Hijabin nata ya janye "Taya zakice babu bayan gashi fuskanki duk a kumbure Lily, meya faru?"


   "K'anwar coursemate d'ita ce ta rasu muka je ta'aziya" tayi mai k'arya saidai take waien ya gano k'arya take. Kukanta baya wuce akan Abdul, tunanin hakan ba k'aramin k'ona masa zuciya yayi ba. Danne zuciyan nasa yayi ya mata ta'aziyya, hira sama-sama sukayi bayan sun gama ci ya d'an zagaya da ita cikin school sannan ya mayar da ita lecture hall nasu ya koma office.


   Nazeefah na kitchen tana had'a girkin yamma taji ringing na wayanta akan dining table. Da wuri ta fito ta d'auka ganin k'awarta Khadijah ke kira. 


  "Halo Khadijah?"


  "Na'am Nazeefah ya kike?"


  "K'alau."


  Shiru yau baki fito school ba."


  "Wallahi cramps ne ya rik'e ni d'azu amma da sauk'i yanzun."


  "Ayyah Allah k'ara sauk'i toh."


  "Ameen yane toh?"


 "Nace ba wani mota ne kam mijinki yake hawa?"


   "AMG C43 lafiya?"


  "Chab! Wallahi shine! 'Yan mata shine!" Ta sanar da k'awayenta dake gefenta. 


  "Shine wa?" Nazeefah ta tambaya curiously. 

     

   "Babe mijinki muka ga tare da wata some minutes ago nan cikin unimaid garden." Wani irin mumunan fad'i gaban Nazeefah yayi. 


  "Afzal d'in?" Ta tambaya cike da k'in yarda. 


  "Wallahi shine shi da wata suka zo suka ci abinci suka fice duk a idonmu."


  "Kai k'arya ne ban yarda ba, bade Afzal ba sede ko me kama da shi."


  "Ki tsaya achan, ana fad'a miki abu kina musu wallahi shi muka ga ni bansan ma mey ya hanani d'aukansu a waya ba da na tura miki an kashe musun."


  "Khadeejah, Afzal fa kikace? Afzal kika gani da wata?"


  "Tabbas."


  "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Nashiga uku na lalace! Tun ba yau ba nake zarginsa ashe de gaskiya ne, amma ko! Yanzu rashin kunyansa har ya kai yana d'aukan 'yan mata yana kaisu cin abinci a idanun jama'ah?"


  "Hmm ai na miji ba d'an goyo bane Nazeefah komin dad'inki da shi seya cimiki amana."


  "Oh Allah nagode sena shigo gobe."


  "Allah kaimu." Tana ajiye wayan ta shiga sintiri a dining space d'in har miya ya soma k'onewa bata sani ba. A takaice girkin ranan sam ba hankali a jikinta tayi. Koda Afzal ya dawo bata mai maganan ba duda cewan ji take kaman ta rufesa da duka don zafin kishi. Lafiya k'alau tayi welcoming nasa bayan sallan Maghrib suna zaune a dining zasu fara cin abinci Afzal ya lura da kallon da Nazeefah ke tayi masa kusan tun dawowansa daga office. 


  "Nazeefah are you sure you're okay? " ya tambayeta. Kai tayi saurin gyad'a mai had'e da kawar da kanta. Nan da nan tayi serving nasu spoon d'aya Afzal ya kai baki ya harar da abincin waje. 


  "Subhanallahi!" Yayi exclaiming. 


  "Lafiya?" Tayi saurin tambaya. 


  "Ai na fad'a dama ba lafiya ba shin meke faruwa? Kinji uban gishirin dake cikin abincin nan kuwa? Bayan nan ga warin k'una what's really going on? Jikin naki ne har yanzu? Ai da kin bar girkin" Ji take tamkar ta d'aukesa da mari dan haushi. Bak'in cikin da yakeji yanzu kad'an ne dangane da wanda ya cusa mata. 


  "Mey kajeyi a makaranta yau?" Ta tambayesa. Sosai tambayan nata ya basa tsoro taya ma tasan ya shiga school yau bayan bata fita ba? Allah ya taimakesa bawai munafukan k'awayenta bane suka gansa tare da Amal suka kirata suka yi mata gulma. Shima tun farko mey ya kaisa cin abinci a cikin school? Ai don Nazeefah bata fita school ba that doesn't mean k'awayenta ma basu fita ba, yayi sakarci. Tabbas su suka had'a komai. 


  "Kayi shiru" ta sake da cewa. 


  "Naje ganin friend d'ina dake lecturing achan ne" ya shirya mata k'arya dukda cewa yasan ba zama zatayi akai ba. Kallon da takeyi masa zalla ma amsa ne game da tambayan da yake yi wa kansa. 


   "Wani abu ne?" Ya tambaya da kallon ya soma yi masa yawa. 


  "Babu kawai dama ance mun anganka a school ne yau."


  "Ohhh like I told you naje ganin friend d'ina ne" ya amsa saidai yasan k'arya take masa, kaman yadda shima yayi mata k'aryar. Tabbas an gansa da Amal ne aka kira aka gaya mata. 


  "Ya cikin naki ya daina ciwo?" Ya tambayeta yana neman canza topic d'in gudun kar fad'a ya 6arke musu. 


  "Da sauk'i" ta amsa sama-sama. 


  

  ***

   Tun kan wayan da Amal tayi da Abdul se gabad'aya halinta ya sake sauyawa ya koma na da, no matter how hard she tried ta kasa mancewa da shi, da tunaninsa take tashi da kuma shi take yini. Shima ta 6angarensa hakan ne. Kullum cikin tunaninta yake ba makawa. 


    Haka zata yini d'aki tana kuka. Kwana biyu kenan bata fita school ba ta fake da cewa wai period cramps ke damunta. Shiko Afzal da zaran yaji bataje school ba yasan batun Abdul ne. Hak'urinsa ya k'are, bai jin ze iya jure hakan again he wants Amal to be his alone gashi a gida be san ta ina ze fara sanar da Nazeefah cewan yana shirin k'ara aure ba tabbas yasan baza ta ta6a amincewa da hakan ba, a cikin d'an k'ank'anin lokaci ya gano irin zazzafan kishin da take da shi. Lallai se yayi taka tsan-tsan da d'aukan Amal a mota anyhow tunda yanzu har an soma kawo mata gulma gida. 


   Washegari ya shirya tsaf abinsa ya je gida gun Abba. Bayan sun gaisa yake ce mai shi yana son a tura gaisuwa gidansu Amal a shirye yake ya k'ara aure. Sosai Abba ya taya sa murna had'e da masa nasiha sosai akan yin adalci inda daga k'arshe kuma yake tambayansa ko ya sanar da Nazeefah batun auren ko kuwa tukuna. 


  "A'a tukuna amman ina da niyya nafison idan ku manya kun gama komai sena sameta in fad'a mata abinda ake ciki, kar taga kaman ba neman aure nake ba kawai ina flirting ne a waje."


  "Kana da point kam amma kana ganin k'in sanar da ita har se idan an sa rana ko makamancin hakan shine dai-dai?"


  "I suppose it is Abba" ya amsa sa. 


  "Toh shikenan Allah shige ma gaba zanyi magana da kawunanka cikin satin da za'a shiga se muje gidansu Amal d'in."


  "Toh Abba nagode sosai Allah saka da alkhairi."

 

  "Ba komai Allah yayi ma albarka."


  "Ameen bari in lek'a Ummi."


  "Ai bata gida baka sani bane?"


  "Wallahi no dake ina shigowa site naka na zarce."


  "Ayya ai ta fita suna wai."


  "Toh ba matsala ni zan wuce." Da haka sukayi sallama. Gidansu Amal direct ya wuce yayi mata waya kan ta fito gashi nan bakin k'ofa. Hijabinta ta ja ta sanya ta feshe jikinta da turare sannan ta fice taje ta samesa inda suka gaisa. Bayan nan ya kira sunanta a nitse. 


  "Na'am" ta amsa. 


  "Nace ba izun naki nawa ne yanzun? It's been long ban ji kina mun zancen islamiyya ba Lily."


  "I'm sorry kasan jami'a da islamiyyan ne se a hankali idan ba hutu akayi ba bana samun time na karatun kaman yadda nakeso."


  "Hakane kam, kina ma k'ok'ari ai am very proud of you tunda kika fara karatu baki samu carry over ba."


  "Thank you Yaya."


  "So izib nawa kika had'a so far?"


  "Saura goman k'asa in gama had'awa gabad'aya kuma dama chan tun da na ta6ayin biyar d'in k'asan a takaice de izu biyar ya rage mun idan na zauna nayi tilawa."


  "Masha Allah so ina da Hafizah as a wife to be kenan?" Kai ta gyad'a masa a hankali cike da kunya. "Zaki iya tuna alk'awarin dana d'aukan miki anytime kika gama haddanki?"


  "Eh toh not vividly amma de kace akwai special kyautan da zaka mun idan na had'a."


  "Very good Umarah nakeson mu tafi tare."


  "Saudi?" Ta tambayesa cike da k'in yarda. 


  "Eh Lily Saudi."


   "Yaya are you serious?" Ashe de Allah ze nuna mata ranan da zata kai wa d'akinsa ziyara. Oh Alhamdulillah!


  "I'm damn serious, I would want us two to go together."


   "Toh Allah nuna mana I really can't wait."


  "Ameen but kinsan bazeyi muyi tafiya mu biyu kad'ai ba ko? Tunda ni ba muharraminki bane."


  Dank'ari se yanzu hankalinta ya buga ta kuma fahimci inda ya dosa a takaice de so yake yace mata aurensu ya kusa. Oh Allah ita bawai auren neba matsalarta, tunanin yadda zata fara zaman aure da Afzal take wai ma zancen kishiya a gefe. Mutumin da duk rayuwarta ta d'aukesa a matsayin yayanta kuma rana d'aya seta fara kallonsa a matsayin mijinta? How is that even possible?





RANA D'AYA!

#RD


Love... king Miemiebee👄✨


[13/08, 09:31] ‪+234 907 483 8352‬: 🎀🎀🎀                 🎀🎀🎀

                🎀❣🎀

                   ❣❣


  💦💦                      🍃🍃🍃          

           *RANA D'AYA!*

  💦💦                      🍃🍃🍃

  July, 2018

 beeenovels.blogspot.com


     _Written by Miemiebee👄_



   *PAGE 2⃣3⃣*


         "Lily kinyi shiru" ya fad'a yana kallonta. 


  Kanta tayi saurin kawarwa tare da ambatan sunansa a hankali se kuma tayi shiru. 


  "Lily I'm sorry but I can't wait any longer, I've waited for so long to be with you and to make you mine and now is the perfect time, please kar kice a'a nasan kina iya had'a haddan naki acikin watanni biyu zuwa uku masu zuwa. Idan har kika samu kika had'a kinga se ayi bikin sauk'an naki dana auran mu at once bayan nan kuma se mu wuce Saudi for our honeymoon, don't say no please."


  Excuse ta shiga nema amma gabad'aya ta rasa ta mey zata ce masa. Bata san mey ba amma anytime Afzal yakeyi mata zancen aure gabanta yake tsinkewa yana fad'i, har wani tsoro-tsoronsa ma takeji. K'arshe de ta samu ta 6ullowa zancen ta hanyan sak'alo sunan Nazeefah. "Toh Yaya Nazeefah fah? Ita baza mu tafi da ita ba?"


  "Lily I want you to believe in me, ki sani cewa zanyi iya k'ok'arina don ganin nayi adalci tsakaninki da 'yar uwarki. Nasan auran mey mata a zamanin yanzu isn't something easy but I need you to believe in me, ni da Nazeefah cikin kwanakin nan zamu tafi in shaa Allah so that idan munzo tafiya dake bazata ga kaman anyi mata rashin adalci ba. But kafin mu tafi da ita I need your approval please ki amince zaki aureni, I've spoken with Abba already a shirye yake suzo su sami su Papi ayi maganan, amincewan ki kawai nake nema Lily."


   "Yaya I do believe in you, tsoro na d'aya ne" ta sanar da shi a nitse. 


  "What is it? Tell me" ya amsa take. 


  "Nazeefah, Yaya tsoron zama da kishiya nake bansan mey Nazeefah zata iya aikatawa ba, ban san irin kishin da take da shi ba, bansan ko zata amince dani kokuwa a'a ba, banason in zame d'aya daga cikin jeri matan da kishiyoyinsu suke yi musu illa kaman yadda banida niyyan cutar da ita bazan so nima ta cutar dani ba."


   "You're safe with me Lily, I'll do everything in my power to keep you save and kar kiyi tunanin Naeefah is that evil nasani kishi kam dole ne but she'll never hurt you, I'll make sure of that and besides banida niyyan had'aku gida d'aya, unguwa ma ba had'aku zanyi ba ni kawai ki amince."


  "Toh shikenan Yaya na amince da k'udurinka, kana iya turo su Abba but I have one favor to ask."


  "Ask me anything Lily."


  "Please kayi hak'uri semun kammala first semester d'in yaso se ayi auren cikin hutu, bana son hidiman bikin ya raba mun hankali."


  "I'll do only as you wish Lily se abari idan kin kammalan ba second semester kuke ba?"


  "Eh" ta amsa had'e da gyad'a kai. 


  "Allah taimaka toh."


  "Ameen."


  "So will you agree to marry me?"


  "Yaya ba nace eh ba."


  "I want to hear it again, Lily am head over hills for you, please tell me again will you marry me?"

  

  "Yes Yaya" ta amsa cike da kunya ko kallon gefensa ta kasa bale cikin idansa. 


  "Thank you Lily ji nake kaman duk duniya ba wanda ya kaini farin ciki, Lily a yau kin cika mun buri da kuma mafarki. I've been looking forward to this day and now I shall be looking forward to the day I'll make you mine, the day you'll start answering my name and the day I can call you my wife. Lily you don't have to worry because I've promised to take care of you, to love and protect you with my life, I've promised to never leave your side. In shaa Allah bazakiyi nadaman aurena ba."


  "I know Yaya Allah and I'm very grateful Allah ya baka ikon yin adalci tsakani na da Nazeefah."


  "Ameen Lily kinsan wani abu?"

  Kai tayi saurin kad'awa da nufin a'a . 


  "Guess!"


  "But I can't ka fad'a mun kawai."


  "I love you" ya sanar da ita. Har cikin ranta taji nauyin kalamun nasa yayinda kunya me tsanani ya rufeta fuskanta ta shiga karewa. "Kin san wani abu again?" Nan ma kai zalla ta iya kad'awa. 


  "I love you" ya kuma sanar da ita. By now kam Amal ji take kaman zata lume k'asa don kunya, bata san mey ba amma kunyansa takeji kunyan ma me tsananin tsiya bata tsammanin zata ta6a iya sakewa dashi. Wani sa'in tana missing relationship nasu na da dasuke a matsayin Yaya da Lily zallah ba wani abun ba. 


  "Can't I get an 'I love you' back?" Ya tanbayeta tare da had'e girarsa. 


  "Yaya..." se kuma tayi shiru. 


  "Lily I know you're not comfortable with me, nasan kina tsananin jin kunya na and I respect that alot but please give me the chance to love and make you happy."


  "Yaya I'm already yours ka daina damun kanka haka."


  "I feel honored then" ya amsa "Can I ask of a favor?"


  "Ina sauraronka."


  "Can you please tell me you love me too? I need to hear these words so badly."


  "Yaya-"

 

  "Lily I know it you don't love me-" ya katseta. 


   "Yaya ya kake magana haka?" Itama tayi saurin katse sa. 


  "Na sani Lily, nasani har yanzu Abdul ne a zuciyarki kuma shi kikeso and bawai ina kishi da hakan bane kokuwa ina jin haushi, nasan zafin rabuwa da masoyi nasan ze d'au lokaci kafin ki iya mancewa dashi ki bud'e mun zuciyarki. I just want you to know that no matter what I'll stand by your side. I'll provide support and love you regardless, I'll be here Lily even if you don't need me."


  "But Yaya I need you also-"


    "Shhh!" ya katse ta "And also bana son kiyi tunanin cewa banida godiya ne nake tinziraki haka ina gaggawa, ki sani it's just because I love you so damn much. Bayan nan I'm very grateful for all the sacrifices you've made to save my life, I'll forever remain grateful to you Lily I just need to hear these words koda kuwa you don't mean them just tell me."


  "Yaya I-" seta bud'e baki zata sanar da shi kalamun seta kasa ji tayi bakinta yayi nauyi, banda sunansa ba abinda take iya furtawa. 


  "Please try" ya rok'eta. Sede ina duk yadda taso sanar dashi hakan abun ya gagara se gani take kaman Ya Abdul na tsaye a gefen windon yana kallonta. 


  "I'm sorry then" yace k'arshe feeling so sad. 


  "Yaya ni ya kamata in baka hak'uri dan Allah kayi hak'uri Wallahi I'm trying, I really want to forget about Ya Abdul abun ne yafi k'arfina please forgive me" ta sanar da shi cikin sautin kuka. 


  "Its okay Lily ba se kinyi kuka ba, forgive me but ba laifi na bane don hak'uri na ya gaza, you're just like a drug, so addicting. Ji nake kaman in ban same ki ba ina iya rasa rayuwana."


   "Yaya dan Allah kabar magana haka I'll always and forever be yours, kasa a ranka na riga na zama taka bana son inji kana maganan rasa rayuwanka, ya kakeson in rayu in ba kai?" Tunda suka fara hirar se yanzu ne ta juyo tana kallonsa idonta cike da k'walla. 


"Forgive me, but bakiya sona ya kikeson inyi idan ba mutuwa ba?"


   "Yaya I care about you, I care about your existence morethan anything dan Allah kabar cewa haka." 

   

  "Anything for My Lily."


  "Thank you" ta amsa had'e da sakar masa k'aramin murmushi tana share hawayen nata. Murmushin shima ya miyar mata yayinda ta shiga duban lokaci a cikin wayanta. "Maghrib ya kusa ko?" Ya tambayeta. Kai ta gyad'a a hankali "Ya kamata mu soma yin niyyah."


  "Sure" ya amsa tare da mik'a hannunsa ta back seat ya janyo wata leda. "Here wannan naki ne."


  "Yaya baka gajiya da bani gifts ne kam kullum?"


  "Bazan ta6a gajiya da farinta miki ba Lily."


  "Amma Yaya-"


  "Not a word please" ya katseta. Bata k'ara musu ba ta mik'a hannu ta amsa  had'e da yimai godiya. Seda taga ficewansa ta k'arisa ciki. D'akinta ta nufa inda ta zazzage kayakin gabad'aya designer turaruka ne da man shafawa aciki seda su gel da sauran kayan shafe-shafe. Oh! Idan ta tuna da irin kashe kashen kud'in da Afzal yakeyi akanta setaji kaman ta samu Ummi tace ayi mishi fad'a ya daina. Bata son a sanadinta ya samu kariyar arziki ko makamancin hakan gashi ya dage kullum idan zezo se yayi mata gaggarumun shopping. 


  ***A nitse Afzal ya k'arisa gida sede tun da ya hau kan hanya yake tunanin kalamun Amal da kuma yadda ta kasa furta masa kalaman da kunnensa suke kwad'ayin ji. Be san kuma mey zey sakeyi Amal ta bud'e masa zuciyarta ba ta koyi sonsa, he misses her alot. He misses her smiles and laughter, everything about her he mise. Duk abinda yasan ya kamata yayi ya yi amma ina har yau ta kasa sakewa da shi. Yana isa gida Nazeefah ta taso tayi masa sannu da zuwa jawo hannunta kawai yayi ya rungumeta feeling so lonely. 


  Ta kai kusan minti d'aya tsaye ko motsi babu sannan a kid'ime ta zagaye hannayenta a bayansa hugging him back cike da rashin fahimta. "Afzal is everything okay with you?" Ta tambayesa a hankali har anan be saketa ba yayinda kuma ya kasa amsa ta. "Afzal?" Se anan ya raba jikin nasu. 


  "Nazeefah I feel so alone, shin bayan su Ummi akwai mey sona kuwa?"


  "Wani irin magana kuma kake haka? Meya faru?"


  "Just answer me, akwai?"


  "Akwai mana Afzal, and ina d'aya daga cikinsu. I love you Afzal no matter what, kar ka ta6a tsammanin bakada masoya bayan su Ummi. I'm here and I love you kaji?"

  Kai ya gyad'a a hankali "Thank you Nazeefah."


  "You shouldn't mention food is ready taho muje inyi serving naka ko seka dawo daga masallaci? Naga Maghrib ya kusa" Ta tambayesa. Bata kai da juyawa ba ya rik'o hannunta kafin ta fahimci abinda yake shirin yi kawai taji moist lips nasa akan nata, mutuwan tsaye tayi a wajen yayinda ta kasa koda kyafta ido.  A hankali taji large arms nasa yana rufe bayanta yayinda yake matso da ita kusa da shi, deepening the kiss in the process. Wani irin electrification taji yana bin jikinta yayinda taji numfashinta na neman d'auke mata, bata san a lokacin da ta shiga mayar masa da martani ba. A hankali a hankali suke tafiya manne da juna har seda Afzal ya turata jikin bango. Mutum na iya cewa sun mance da duniyan da suke ciki don zafin kiss kawai, gabad'aya sun fita daga hayyacinsu. Chan Afzal ya saketa a hankali yana k'ok'arin kama numfashinsa kaman yadda itama takeyi, goshinta ta sauk'e dai-dai saitin ha6arsa yayinda wani irin zazzafan sonsa yake shiga jikinta. Ji take gabad'aya duniya ba wanda ya kaita murna, ashe de Allah ze k'addaro mata da wannan rana? Oh she can't get over how sweet, soft and moist his lips were, bata k'i ya sake kissing nata over and over again ba. 


  "I'm sorry" taji ya furta a hankali yayin da minty breath nasa yake fifita hancinta. Shi kansa ya rasa gane meke faruwa. 


  "It's okay" ta mayar masa har anan ba wanda ya motsa acikinsu. 


  "I'm sorry" ya sake fad'a had'e da sauk'e hannayensa da suke rik'e da kunkuminta "I'm really sorry ban san meke shirin faruwa da ni ba please forgive me" kafin tace wani abun ya wuceta da hanzari inda ya zarce d'akinsa. Key ya sa had'e da manna bayansa jikin k'ofan. Idonsa ya rufe gam amma ya kasa daina tunanin kiss da sukayi sharing da Nazeefah shin meke faruwa? Gabad'aya ji yayi Amal yake kissing, mey soyayyar Amal ke shirin yi masa? Taya zeyi kissing Nazeefah ya d'au Amal yake kissing? Anya kuwa soyayarta ba shi ze halaka sa ba? Yanzu da wani ido ze sake kallon Nazeefah? Oh Allah! Yau yana cikin wani yanayi. Sallan Maghrib da be fita ba kenan ranan wane sabuwan amarya haka ya la6e a d'akin.  Tun Nazeefah na jiransa da ya fito suci abinci har bacci yayi gaba da ita zaune akan dining d'in. Chan wajajen goma ya lek'o waje a sanadin yunwan daya fafarosa. Sid'ak-sid'ak yake tafiya wai kar tajiyo motsinsa ta fito, ba k'aramin tsinkewa zuciyansa yayi ba ganinta da yayi zaune akan dining ta kafa kanta akan dining table d'in. A farko niyyan juyawa ya koma d'akinsa yayi tunda de bata gansa ba amma kuma ya fasa sanadin kukan da cikinsa yayi don yunwa. Matse idonsa yayi ya k'arisa wajen had'e da yin gyaran murya se kuma yaga bata motsa ba. 


  "Nazeefah?" Ya kira sunanta nan ma shiru lek'a fuskanta da zeyi kawai ya tarar bacci takeyi. Allah sarki bade bacci ne ya d'auketa anan ba tun tana jiransa ya fito suci abincin tare? Shin ta ma yi sallah kuwa? A hankali ya shiga tada ita har ta bud'e idonta. 


  "Kinyi sallah?" Ya soma da tambayarta. Kai zalla ta gyad'a masa yayinda idanunta suke neman kafewa. 


  "Abinci fa kinci?"


  "Ba tun d'azu ina jiranka ka fito muci ba kak'i."


  "Ba wai nak'i bane Nazeefah..." se kuma yayi shiru a bisa rashin sanin abinda ze sake cewa. 


  "Are you ashamed because you kissed me? Are you Afzal?" Ta tambayesa da mamaki. 


  "Ko kad'an ba haka bane."


  "Toh yaya ne? Afzal I know you don't love me but I'll never surrender, zan cigaba da hak'uri ina farinta maka har izuwa ranan da Allah ze sa a ranka kaji zaka iya yafe mun abubuwan da nayi maka da a baya, I really am sorry" ta k'are maganan idanunta na neman cikowa da hawaye. 


  Zama yayi a gefenta a hankali had'e da rik'o hannunta cikin nasa. "Kibar cewa haka please ni baki yimun komai ba."


  "Ban yi maka komai ba?" Ta tambayesa da d'umbun mamaki. 

  "Ban yi maka komai ba amma auran mu sama da shekara biyu kenan yau baka ta6a tunanin sauk'e mun hak'k'ina da Allah ya d'aura maka ba? Baka ta6a damuwa da wani halin nake ciki ba Afzal. Kana ganin ka kyauta mun kenan?"


  "Nazeefah-"


  "Amma kar ka damu har ga Allah ni na yafe ma komai saboda bana son Allah ya tsayar da kai ranan qiyama akai na" ta sanar da shi had'e da katse sa sannan ta cigaba. "Nasani ni na bud'e k'ofan duk wani tashin hankali da wulak'anci daga gareka, da tun farko na rik'e mutunci na nayi respecting naka da duk hakan be faru ba I just hope it's not too late to say sorry." Sosai kalamunta suka shigesa ya kuma tausaya mata. Ya sani tauye hak'k'in bawa ba abu bane me kyau musamman ma na tsakanin mata da miji but shima ai ba a son ransa yake hakan ba. 


  "A tunanin ki a son raina ne nake tauye miki hak'k'in ki? A tunanin ki nid'in zama haka dad'i yake mun ne? Kokuwa kina tunanin ni banida sha'awa ne? As much as you need me as your husband know that I need you as much amma-" se kuma yayi shiru. 


  "Amma mey? Please talk to me Afzal I can't do this anymore."


  "I can't Nazeefah, bazan ta6a iya had'a kwanciya dake ba.l Har cikin ranta taji zafin kalamun nasa ba shiri hawaye ya shiga tsiyaya daga idanunta. 


  "Afzal meyasa? Me nayi da zaka hukunta ni haka? Dan Allah kayi hak'uri, Afzal bazan iya rayuwa ba kai ba, wallahi da in rasa ka gara na rasa komai ciki harda rayuwa na. I love you Afzal I can't stop saying it no matter what."


    "Nazeefah I'm sorry."

    

  "Ni ba hak'urinka nakeso ba Afzal, ka gayamun dalilin da yasa bazaka iya had'a kwanciya dani ba idan wani laifin nayi in baka hak'uri."


  "Forget it, just forget it" kafin ya kai ga mik'ewa ta jawo hannunsa tana hawaye sosai "Please tell me Afzal a shirye nake da inyi ta baka hak'uri har se Allah ya huce ma zuciya dan Allah ka fad'a mun." A da ya d'au alk'awarin komin yaya baze ta6a sanar da ita laifin nan da tayi masa ba amma kukan da takeyi ba k'aramin karya masa zuciya yayi ba. 


  "Please tell me Afzal I can't do this anymore."


  "Remember the first day aka kawo ki gidan nan?" Kai tayi saurin gyad'a "Mey kikace wa k'awarki da ta kiraki?" Ya tambayeta, sede ta duba ta duba tayi tunanin gaba da baya amma ta kasa tuna komai. "Afzal wallahi bazan iya tunawa ba dan Allah ka fad'a mun."


  "I can't tell you, bazan iya ba Nazeefah saboda kalamun basuda dad'in sauraro zan baki nan da duk lokacin da kike buk'ata ki zauna kiyi tunani idan har kin tuna da kanki then I'm willing to forgive you."


  "Afzal please tell me I'm so sorry."


  "I'm sorry as well but I can't." Yana fad'in haka ya kuma mik'ewa da niyyan ficewa hannunsa ta sake rik'owa "Nasan kana jin yunwa please ka zauna kaci abinci."


  "Karki damu."


  "Please Afzal."


  "Kefa? Kinci?"


  "Ni idan har zaka ci ma hakan ya isa ya k'osar dani don't worry about me."


  "I'm not eating unless with you."


  "Toh ka zauna please kar ka tafi."


  "Toh kibar kukan haka" badan tana so ba ta shiga share hawayen nata seda ta bar kukan ya amince ya zauna nan tayi serving nasu suka ci bayan sun gama ta tattara plates d'in takai kitchen. D'akinta ta wuce dan watsa ruwa shima haka, chan yana shirin kwanciya se gata ta shigo daman ita yake jira. Bayan ta kwanta ya kashe musu wutan. Kan pillonta ta bari ta matso kusa da shi had'e da sauk'e kanta a birnin k'irjinsa tana mey zagaye hannunta akan cikinsa. A hankali taji hannayensa yana kewaye bayanta "Goodnight Nazeefah" ya sanar da ita had'e da sauk'e mata peck a kai. 


  "Goodnight Afzal I love you." Bada dad'ewa ba yayi bacci itako ta kasa, se tunanin maganansu na d'azu take. Shin mey ta fad'a da ya 6ata masa rai haka har ya gommaci ya tauye wa kansa hak'k'i ya sha wuya da ya kusance ta? Se kusan k'arfe biyu bacci ya d'auketa. Washegari wajajen k'arfe hud'u bayan Afzal ya dawo daga office tayi masa sannu da zuwa had'e da amshe jakansa. Har d'aki ta rakasa ta ajiye jakan nasa a mazauninsa sannan ta shiga bayi ta had'a masa ruwa ya shiga ya watsa bayan ya fito ya sanya shorts da singlet sannan suka fito dining inda suka ci abinci. Bayan sun gama ta tattare wajen tsaf. Har Afzal ya shiga takawa zuwa d'akinsa yaji muryan Nazeefah na kiransa, chak ya tsaya had'e da kewayowa. Mik'ewa tayi ta k'arisa ta samesa. 


   "Afzal I'm sorry I'm really sorry."


   "Why? What for?" Yyi saurin tambaya. 


  "Bayan tunanin da na yini inayi na tuna abinda na fad'a a daren auren mu dan Allah ka gafirceni, I was young and stupid then, yarinta na yawo a kaina bansan ciwon kai na but tuba nake please forgive me for hurting you like I did, wallahi I didn't mean a word."


  "It's okay Nazeefah ya wuce."


  "Dan Allah ka yafemun."


  "Na yafe miki komai Nazeefah forgive me also."


  "You have nothing to be sorry for."


  "Toh hawayen ya isa haka" ya fad'a had'e da sa hannunsa yana share mata hawayen nata. Hugging nasa kawai tayi yayinda kukan nata ya tsananta "Thank you for forgiving me Afzal, I love you so much." A hankali ya zagaye hannayensa a bayanta hugging her back. 


   "Its okay" ya sanar da ita yana shafa bayanta a hankali. Be barta ba seda kukan nata ya lafa hannunta ya ja izuwa parlourn inda suka zauna akan kujera. 


  "Yaushe zakuyi exams naku?"


  "Da d'an saura se nan da two months in shaa Allah."


  "Masha Allah shikenan an zama graduate kuma ko?"


  Ka manta ne? First semester muke ai? Se mun gama second tukuna."


   "Yesh haka My computer scientist" yayi complimenting nata. 


  "Thank you" ta amsa tana murmushin jin dad'i, har cikin ranta taji dad'in yadda ya kira ta 'his computer scientist.'


  "I'm so proud of you Nazeefah Allah sanya albarka acikin karatun."


  "Ameen Afzal thank you."


  "Ina son mu tafi Umarah tare."


  "Umarah?" Tayi exclaiming cike da mamaki. 


  "Yes just me and you."


  "OMG!" Tsalle tayi tare da hugging nasa. "Are you serious?" ta sake tambaya bayan da ta sake sa. "Yes Nazeefah" ya amsa. 


  "Yaushe toh?"


  "I guess se idan kun gama exams naku yanzu kinga ai kina school."


  "But ba wani serious lectures ma muke ba."


  "A'a Nazeefah bana son wasa da karatu ai 2 months d'in kaman gobe ne karki damu kinji?"


  "Toh shikenan Allah kaimu I just can't wait."


****

   Haka nan tun daga ranan Nazeefah da Afzal suka soma zaman lafiya a gidan. Kullum shi yake kaita school, idan lokacin lunch yayi kuma ya d'auketa suje su ci da ikon Allah basu ta6a had'uwa da Amal ba sannan duk sanda yake gida baya kiranta gudun kar Nazeefah ta gano wani abun. A satin da ya gabato ne su Abba suka turo gaisuwa gidansu Amal inda su Papi suka amince suka kuma bada Amal. Siyayya sosai su Abba suka yi fiye da wanda Baban Abdul sukayi, kayaki se de ace masha Allah. Kaman yadda Afzal ya buk'ata haka Abba ya sanar da iyayen Amal cewa baya son a d'au lokaci kafin ayi bikin so samu idan Amal ta kammala part three nata batun kayan d'aki da gara kuma yace ya d'auke masu nauyin su kawai su amince ayi bikin ba tare da an 6ata lokaci ba. Papi beyi jayayya da hakan ba shima dama bayi da ra'ayin jan bikin idan ma da akwai abinda ze sasu jan bikin shine shirin yima Amal kayan d'aki amma yanzu da Afzal ya nuna zeyi komai sede suyi musu fatan alkhairi. 


   Sati uku Papi ya basu a gaba da su dawo kafin nan Amal da mahaifiyarta sun gama yanke hukunci game da ranar da za'a sanya na auren. Sosai su Abba sukayi godiya inda suka sauk'e dubu ashirin da suka tashi tafiya. 


****

   Haka tafiyan ta cigaba duk da kalan halatayya irin na Amal, Afzal be kariya ba, be fasa kirarta da kuma zuwa gidansu dubanta ba. Gashi duk abinda ya gani me kyau se ya sai mata ita da Nazeefah sosai yake kwatanta yin adalci a tsakaninsu. Nazeefah kuwa har yau bata san meye ake ciki ba. 


  Ta fannin Abdul kuwa sosai yake kewar Amal, rana baya ta6a wucewa beyi tunaninta ba sede kuma bai fasa tashi cikin dare yana rok'an Allah ya kawo masa sauk'i ba. 


  ****

  Yau bayan sallan Isha Afzal da Nazeefah suka shirya tsaf inda suke je sukaci abinci bayan nan ya wuce da ita 3G gallery inda ta sassayi jakukkuna da dama. Bayan ya biya komai sun dawo mota ya sake fita da sunan yayi mantuwa inda ua sai wa Amal tasa itama jakukkunan ya bayar aka sa masa a booth suka k'arisa gida. Project nata ta d'auko suka cigaba da yi mata daga inda suka tsaya jiya, wajajen goma tace su bari haka su kwanta yaso su cigaba gobe. Yau wankan ma a bayin d'akinsa tayi, bayan ta fito shima ya shiga yayi zuwa k'arfe sha d'aya de suka samu suka kwanta. Kaman kullum ta gangara jikinsa sede yau Afzal ya d'au niyyan mayar da Nazeefarsa cikakkiyar mace. Yau fiye da sati biyu kenan tunda ta nemi tubansa amma ba abinda ya shiga tsakaninsu. Tun Nazeefah na sa ran ze nemeta har ta dena saidai ko da wasa bata sake yi masa maganar ba ita de bata fasa da yin addu'an Allah shirya tsakaninsu ba. Kaman acikin mafarki taji ana yi mata wani irin shafa, a firgice ta bud'e ido sede kafin tace zata mik'e zaune ya rik'ota gam a jikinsa. 


   "Shhh!" Ya buk'aceta se anan hankalinta ya d'an kwanta. A hankali cike da dabara ya shiga sarrafata yayin da take basa had'in kai har yaci nasaran raba ta da kayan jikinta. Wannan dare de da Nazeefah ta dad'e tana jira finally Allah ya kawo mata shi, anci kuka anji dad'i duk a lokaci d'aya. A hankali har bacci me nauyi yayi gaba dasu duka sede duk lokacin da Nazeefah ta tuna yadda Afzal ya riga tarerayarta se ta murmusa acikin baccin. Wani irin gobaran sonsa ne yake ruruwa a zuciyarta ji take idan ba shi bazata iya rayuwa ba. 


   Kiran sallan Asuban fari Afzal ya tashi, a hankali idanunsa suka sauk'a akan Nazeefah datake manne a jikinsa se bacci take bayan da ya kunna wutan d'akin. Murmusawa yayi a hankali yayinda events na last night suka soma dawo masa ashe de raguwa take se kurun bakin tsiya. Cike da dabara ya raba jikinsa daga nata had'e da lullu6e jikinta da bargo. Bayi ya fad'a yayi wanka sannan ya d'aura alwala ya had'a mata ruwan d'umi tukuna ya fito. Bayan ya sanya jallabiyansa ya nufi kan gadon inda take bacci har yanzun. 


  Sunanta ya shiga kira a hankali har seda ta bud'e idonta, da sauri ta sake kullesu bayan da suka had'a ido hakan ba k'aramin murmushi ya sanya sa ba, wai kam dama Nazeefah na da kunya? Wai toh idan tana irin wannan kunyan? Amal tasa fah? Amal da ko kalamun soyayya ya fad'a mata bata sake iya kallon cikin idansa. Lallai akwai k'ura a gaba. 


  Gyaran murya yayi yace, "Tashi haka toh kiyi wanka muyi sallah baccin ya isa."


   "Toh ka daina kallo na" tayi maganan idanta rufe gam. 


  "Yau kuma? Tashi kinga lokaci na k'urewa."


  "Toh Ya Afzal ka tashi ni idan da hali ma ka fita idan na kimtsa zanyi maka magana" ta sanar da shi. Murmusawa yayi sosai "Yau kuma nine Yaya saboda kinji wuya jiya?"


  "Ya Afzal mana" ta fad'a had'e da jawo pillow tana kare fuskanta. 


  "Toh naji naji, zan jiraki a parlour."


   "Toh ka tafi" mik'awa yayi ya janye pillon a hankali had'e da sanya mata light peck a goshi sannan ya mik'e ya fice. Seda taji k'aran kulluwan k'ofa sannan ta shiga bud'e idon nata a hankali. Haka kawai ta tsinci kanta cikin tsananin farin ciki, se murmushi wa kanta take barin ma idan ta tuna abubuwan da Afzal ya rink'a yi mata daren jiya, yadda ya rink'a binta a hankali yana kashe mata jiki. She felt like a princess, like a baby and all. Aww she's madly in love with him, a hankali ta mik'e ta nufi bayin. Shiganta ba da jimawa ba Afzal ya dawo d'akin, bedsheet d'in ya tattara yayi disposing. Kafin ta fito har ya shimfid'a sabo ya zauna bakin gadon yana jirarta. 


   "Ya Afzal" ta kirasa lokacinda ta fito tana tsaye bakin k'ofar d'aure da d'an guntun towel. Kafin yayi magana har idonta ya kai ga sabon bedsheet daya shimfid'a kan gadon. "Awwn Ya Afzal ai ko ni ma zan iya canzawa it doesn't have to be you."


  "Don't worry sanya kayanki muyi sallah" ya amsa. Nan da nan ta shirya ya jasu bayan sun kammala azkhar nasu suka shiga shirin office da school. Yau ma kaman kullum shi yayi dropping nata. Nazeefah fa ji take tamkar duniyan ma tayi kad'an ta d'auke ta dan murna da farin ciki kawai. Tuni ta sanya hoton Afzal a home and lock screen nata, idan ta isa gida ma zata canza na laptop nata ta sanya hoton nasa. 

   Da Azahar lectures nasu ya k'are saidai Afzal baze samu daman zuwa d'aukanta ba don haka ya tura driver'n Ummi da ya d'aukota kasancewar yana da meeting. Bayan da ya d'auketa se tayi tunanin ya wuce da ita gida gun Ummi ya kwana biyu basu lek'a juna ba. Sosai Ummi tayi murnan ganinta daman tana da anniyar kai masu visit this weekend saboda shirun yayi yawa. Hira suka sha sosai sekace ba surikai ba, suna cikin cin abinci ne Nazeefah tayi gyaran murya "Ummi?" Ta kirata. 


  "Na'am Nazeefar Mummy."


  "Kai Ummi wai yaushe zaki sauk'e sunan nan ne kam?"


  "Ko Nazeefar Afzal ce?"


  "Toh ko kefa? Ai hakan ma yafi dad'i" nan suka k'yalk'yale da dariya. 


  "Ahh lallai soyayya manya wannan kumatu da kika k'ara anya kuwa ba abu a k'asa?"

  

  "Laaa ji Ummi dan Allah ni kinga har zaki sa in mance abinda nakeson tambayarki ma wallahi."


   "A'a yi hak'uri tambayan ina jinki."


  "Shin mey yafi burge Ya Afzal game da mace?"


  "Addini" Ummi ta amsa nan take. "Yana bala'in son mace mey addini."


  "Allah Ummi?"


  "Sosai ma kuwa."


  "Ai kuwa ya zama dole in koma islamiyya kodan shi ma."


 "Toh fa mey Prince yayi har ake neman farinta masa rai haka."


 Hmm Ummi kenan ai komai ma Ya Afzal na mun jiyan nan ya kaini 3G gallery bakiga jakukkunan dana d'iba ba kuma duk ya biya makaranta yanzu kullum shi yake kaini sede idan banida lectures na safe please ki cigaba da sanyasa a addu'a keda kike mahaifiyarsa, nima inayi masa amman naki daban ne. Allah ya taimakesa ya k'ara masa bud'i."


  Masha Allahu sosai Ummi taji dad'in kalamun Nazeefah ashe in de haka ne Afzal yaji fad'an da ita da Abba su kayi masa kenan. Madallah gaskiya tayi wa Nazeefah murna sede kuma alokacin da ta fara jin dad'in aurenta a lokacin Afzal yake shirin k'aro mata kishiya. Oh kowa de da tasa k'addarar, Allah de ya sa ta d'au hakan a matsayin k'addararta ta kar6a hannu bibbiyu. 

   

   "A gaskiya naji dad'in kalamanki matuk'a Nazeefah, naji dad'i yanzu da ke da Afzal kuke zaman lafiya Allah yasa hakan ya d'aure ya kuma cigaba da had'a kawunanku."


  "Ameen Ummi so bayan addini sey kuma mey yakeso?"


  "Addini de itace babba, kika rik'e addini to kin kama k'afansa kenan, inda so samu wannan gyale ma ki daina sanyasu in ba a gida ba, yana son mace me sanya tufafin da ze rufe mata jiki bayan nan kuma mace mey tsafta, mey kunya. Ki zame mey kunya, mey kuma kamun kai ba kowani na miji zakina huld'a dashi a makaranta ba inba wanda ya zama dole ba." Se kai Nazeefah keta gyad'awa wane mey d'aukan lectures "Nake ga idan kika kiyaye wannan ababen da na k'irga miki toh fa kin riga kin mallake Prince kin zama uwar gidansa."


  "Thank you very much Ummi in shaa Allah zakiga canji wallahi ina son Ya Afzal and doing just what he likes makes me happy. A shirye nake da in sadaukar da farin cikina saboda nasa, please ki rink'a samin shi acikin addu'a Allah cigaba da karemun shi."





RANA D'AYA

#RD


Love... King Miemiebee👄✨

[13/08, 09:32] ‪+234 907 483 8352‬: 🎀🎀🎀                 🎀🎀🎀

                🎀❣🎀

                   ❣❣


  💦💦                      🍃🍃🍃          

           *RANA D'AYA!*

  💦💦                      🍃🍃🍃

  July, 2018

 beeenovels.blogspot.com


     _Written by Miemiebee👄_



   *PAGE 2⃣4⃣*



    

     "Allah cigaba da baku zaman lafiya Nazeefah ki dage da addu'a, itace komai."


  "In shaa Allahu Ummi zan wuce girki na jira na."


  "Toh bari ina zuwa." Kitchen ta nufa chan bada dad'ewa ba ta dawo rik'e da wasu robobi a hannunta. "Ga wannan spices ne k'awata take had'awa wannan a pepper soup zaki na sawa, wannan kuma ko a jollof ko fried rice yana gyara girki sosai nima ina amfani dasu."


  "Allah sarki Ummi baki gajiya da mun kyauta kullum idan na shigo?"


   "Jibeki ko kin manta a matsayin 'yata kike? Hungo kar6i ayi ma Prince girki mey dad'i yaci."


  "Toh shikenan Ummi" ta amsa tana murmushi "Nagode sosai akwai leda ne se in juye in baki robobin?"


  "Karki damu musamman na sai rabobin dan in zuba miki su aciki."


  "Kai Ummi da wahala haka? Nagode sosai zan ko nunawa Ya Afzal bari in wuce." Har wajen mota Ummi ta rakata sannan ta dawo ciki. Driver na sauk'e ta a gida ta rage kayan jikinta ta watsa ruwa sannan ta shiga kitchen bayan ta had'a kan girkin ta d'au wayanta ta kira k'awarta Aisha mey siyar da readymade hijabs akan ta kawo mata tana son siya. 


  Se wajajen k'arfe biyar Afzal ya dawo gida, lokacin Nazeefah na zaune da Aisha tana kan za6an hijaban. Mik'ewa tayi had'e da yi masa sannu da zuwa, bayan sun gaisa da Aisha, ya k'arisa ciki. Nan da nan Nazeefah ta gama za6e three quarter hijabai masu hannu kusan kala goma sha biyu. Duka-duka de ya tashi N21,600 kasancewar N1,800 ne kowani guda amma k'awar nata tayi mata ragi akan N20,000. 


  "Toh nagode zan miki transferring kud'in banida enough cash a wajena."


  "Ba komai toh zan wuce."


  "Yauwa nagode" bayan tayi mata rakiya ta tattara hijaban ta wuce d'akin Afzal dasu. A lokacin yana mik'e kan gado yana latsa wayansa. A kan gadon ta jibge kayakin yayin da ya kafa mata ido yana kallonta da mamaki. 


  "Wad'annan fah?" Ya tambaya. 


  "Na wa ne" ta amsa tana jin dad'i. 


 "Toh kuma" ya furta yana mamakin ina zata kai hijabai dayawa haka, inde don na sallah ne kam ai sunyi yawa. 


  "Starting today zan soma sanya hijabi ban sake fita da gyale" ta sanar da shi tana k'ok'arin sanya d'aya daga ciki. Da mamaki cike da jin dad'i ya tsaya yana kallonta ba k'arya kuma hijabin ya mugun amsanta. 


  "Ya mun kyau?"


 "Sosai ma kuwa RABB'ATUL BAIT (sarauniyar gida)" ya amsa yana bata full attention nasa. Sosai taji dad'in sunan dukda cewan bata san meye ma'anar ba amma ta de san abun arziki ne. "Duka wannan kika saya?" Ya tambayeta. 


  "Eh zan zo in k'ara ma daga baya."


  "Wow! I'm really impressed Nazeefah, Allah yayi miki albarka."


  "Ameen Ya Afzal."


  "So duka-duka nawa ne?"


  "N21,600 amma tabar mun akan N20k."


  "Alright zanyi miki transferring kud'in."


 "A'a kar ka damu inada enough kud'i a waje na."


  "You shouldn't bother as well kiyi amfani da kud'in ki sai wani abu daban zan biya na wannan d'in kinji?"


  "Toh shikenan thank you so much Allah k'ara bud'i."


  "Ameen my Rabba'atul bait." Dad'i sosai ta kuma ji sede ta kasa hak'ura taji ma'anan sunan dan haka ta tambayesa. "Ya Afzal meye ma'anar Rabba'atul bait d'in?"


   "Wai ashe matar tawa bata jin larabci" ya shiga neman tsokanarta. 


  "Kaga nifa shiyasa banason tambayar ka abu seka gama yi ma mutum dariyar mugunta tukuna amma karka damu kwanan nan zanyi joining islamiyya zaka sha mamaki."


   "Dagaske zakiyi joining Islamiyya?" Ya tambayeta cike da k'in yarda. 


  "In shaa Allah idan muka samu hutu, ko baka so?"


  "Taya bazan so matata ta shiga neman k'arin ilimin addini ba? I'm very happy in fact nima zan nemo miki islamiyyan da kaina."


   "Awwn Ya Azal da gaske?"


  "Sosai ma Rabba'atul bait."


  "Toh gayan mey ma'anan sa?"


  "It means The queen of my home (sarauniyar gida na)" bata san sanda ta shiga blushing ba. "Am I really?" Ta tambayesa cike da kunya da kuma jin dad'i. 


   "Yes Nazeefah you are."


  "Awwn Ya Afzal thank you so much I really am in love with the name."


  "You're welcome" ya amsa yana mayar mata da murmushin shima. 


  "I feel honored kaima ka jira nan da lokaci kad'an zan nemo maka romantic name in baka."


   "Toh shikenan ina jira."


  "Yau baka jin yunwa ne? Naga ko tambaya na abinci bakayi ba."


  "Ai nasan food will always be ready as long as kina gidan nan so yau mey aka girka mun?"


  "Fried rice ne da pepper chicken."


  "Wow! Har wani fitinannen yunwa ya kamani, let's go?"


  "Let's go" takawa yayi ya k'arisa inda take, da hannunta rik'e acikin nasa suka k'arisa dining d'in inda tayi serving nasa saidai spoon d'aya ya kai baki ya tsaya yana exaggerating girkin wai yayi dad'i murmusawa tayi sirrin Ummi ta fad'a a zuciyarta. Seda suka gama ci take fad'a mishi dalilin daya sa abincin yayi dad'i sosai yau, spices da Ummi ta bata ne. Sosai yaji dad'in zuwa duban Ummi da tayi ba tare da ya sanar da ita ba.



****                  ****


   "Abba ai wannan kaman tonawa Baby asiri ne" Mami tace da Papi yayinda suke zaune a d'akinsa. 


  "Kaman ya tona mata asiri Jameela?"


  "Abba banda ni da kai fa ba wanda yasan 6oyayyan al'amarin nan a tunani na ba amfanin sanar da iyayen Afzal wannan batu, mu rufa wa kanmu asiri kaman yadda Allah yake rufa mana banga amfanin tozarta kanmu wa mutane haka ba."


  "Ya kike magana haka Jameela? Shin bakisan duk auran da aka ginata akan k'arya bata d'aurewa ba?"


   "Na sani Abba amma gani nake kaman mutuncin mu ne ze zube barin ma naka dana Baby, wallahi da wuya mutanen nan su sake d'aukan Amal da k'ima da daraja ba." 


   "A'a Jameela, ba wani zancen abin kunya ko kuwa zancen zubewan mutunci anan, ba wanda yafi k'arfin jarabawa da k'addara. Gaskiya kuma ko bamu fad'eta ba wataran zata fito da kanta don haka gara mu fad'a musu komai da bakin mu akan suzo su gano gaskiya wataran, a gani na hakan ne zai zubar mana da mutunci da daraja a idonsu."


  "Amma Abba yau shekara nawa? Kusan ashirin amma banda mu ba wanda yasan wannan labari, tunda muka baro Askira ba tashin hankalin da ya sake binmu kana ganin ya dace mu sake jefa kanmu acikin wani rud'anin?"


  "Ki kwantar da hankalinki Jameela in shaa Allah ba rud'anin da ze biyo bayan yin abinda ya dace."


  "Toh shikenan tunda kace haka se a sanar dasu d'in dama ni kawai ina gudun tokarin da za'a zo ana yi wa Baby ne."


  "Har wa ya isa yayi mata tokarin? Ai ba lalle ne akace se sun aureta ba idan sunga bazasu iya auranta a haka ba walillahil hamd dama tun farko su sukace suna so ba tallar su akayi mata ba, amma kam ba dani za a a gina aure akan k'arya ba. Abinda ka raina kake ganin ba komai ba shi zezo ya zame maka babban matsala nan gaba. Ke zaki gani kaman ba komai bane yanzu koda ba'a sanar dasu ba amma rananda k'wai ya fashe se mutum ya raina ka yaga kaman ka ci mai amana ne ka zaluncesa saboda haka yanzu ne lokacin da ya dace da a sanar dasu gaskiyan al'amarin idan sunga su bazasu iya had'a zuri'a da ita ba shikenan Allah ze kawo mata wani, hannun mutum baya ru6ewa ya yasar."


  "Tsakani na da Khalifah sede Allah ya isa, Khalifah ya cuceni a rayuwa bansan da wani idon zan sake kallon Baby ba idan har ta jiyo gaskiyan labarinta, Khalifah ya cuceni ya cuceni!" Ta rushe da kuka. 


  "Yanzu kuka kike saboda Baby ta shigo ta tsince ki ahakan ko mey? Kisani Baby baza ta ta6a yi miki mumunan fahimta ba, sanin kowa ne Khalifah ne ya cuceki bawai ke kika cuci kanki ba. Ya auna tunaninki ne da k'arancin shekarunki yayi riba da hakan, shiyasa kika ga koda 'yan unguwa da dangi suke tsangwamar ki nayi tsaye na kareki, koda wasa ban ta6a baki laifin abinda ya faru ba kuma bazan ta6a ba Jameela ni nasan kalan tarbiyyan dana baki."


  "Abba banida kaman ka, bazan ta6a iya biyanka kalan halaccin da kayi mun ba a rayuwa fatana kawai Allah ya sak'a maka da gidan aljannah."


  "Ameen share hawayen naki haka ki shirya abinci wa bak'in namu munyi waya da Abban Afzal d'in yace suna tahowa."


  "Toh shikenan Abba" da haka ta fice instead ta wuce kitchen seta nufi d'akin Amal inda ta tarar da ita kwance kan katifarta. Tana jin k'aran k'ofa ta 6oye wayarta da take ta faman kallon hotunan Ya Abdul k'ark'ashin pillow. 


  "Bade bacci kike ba?" Ta soma da tambayarta. 


  "A'a nagama tilawa ne nace bari in d'an huta."


  "Oh dama nazo ne muyi wata magana" A nan Amal ta mik'e ta zauna tana mey baiwa Mami full concentration nata "Ina jinki."


  "Baby kiyi hak'uri ki yafe mun" ta sanar da ita. Cike da rud'ani Amal ta tsaya tana kallonta "Mami hak'urin mey kuma kike bani? Ai baki yi mun komai ba."


   "Ko da wasa kar kice haka 'yata, laifin da na miki har yau ba wanda yayi maki irinsa, Baby na cuceki a rayuwa, nayi miki k'arya gabad'aya rayuwarki, k'aryan da ban san ta ina zan soma wanke kaina ba amma dan Allah ki gafirceni kisani ba haka hali na yake ba, k'addara ce ta riga fata."

 

   "Mami ban fahimceki ba dan Allah meke faruwa?"


  "With time zaki fahimci komai Baby ni gafararki kawai nake nema."


  "Mami baki yi mun komai ba ni don haka nakeson ki daina tambaya na yafiya, you have nothing to be sorry for" k'arisawa tayi tare da hugging nata. "I love you so very mucu Mami no matter what." 


   "Allah yayi miki albarka Baby, ya cigaba da kare mun ke ya sanya miki albarka acikin dukkan al'amuranki."


  "Ameen Mami please don't cry" a hankali ta saketa ta shiga share mata hawayenta sannan suka wuce kitchen d'in tare suka shiga had'a kan girkin. 


   Bayan La'asr Afzal da Abbansa suka duro gidansu Amal. Bayan taransu da su Papi sukayi Mami ta sa Amal fito musu da drinks da aka tanadar musu don Abba ya ganta. Daga baya-baya ta tsuguna ta gaishe sa cike da ladabi da biyayya kanta sauk'e a k'asa bayan nan ta gaishe da Afzal sannan ta k'arisa ta ajiye tray d'in daga gabansu sannan ta tsiyaye musu juice d'in a cup each. 


   'A gaskiya Afzal ya iya za6i' abinda Abba keta furtawa a ransa kenan haka kawai Amal ta shige masa zuciya. Kaman yadda Afzal yake son mace kamila mey kunya shima mahaifin nasa haka ne, kamun kai, fasali da kunyan Amal ba k'aramun burgesa yayi ba, fatansa Allah basu zuri'a d'ayyiba. 


    Bayan Papi ya sanar da su Abba date da Amal ta za6a su Abba suka amince right away, bayanin komi dalla-dalla Papi yayi musu akan cewa ta za6i February d'inne saboda by then ta samu hutu a makaranta kuma da ikon Allah ta samu ta had'a haddan Al~Qur'anin da takeyi. Abba couldn't ask for more akan fasali da kamilancin nan kuma ga hafizancin Al~Qur'ani madallah nan take yafara shawaran kyautan da ze bata ranan sauk'an nata. Bayan Mami ta mik'e ta basu waje, Papi yayi gyaran murya ya fara kaman haka, "Godiya ya tabbata ga Allah yadda komi yake tafiya lami lafiya."


  "Tabbas, mune da godiya Mallam Muh'd Allah sak'a muku da alkhairi ya ji k'an mahaifa."


  "Ameen ameen saidai wani hanzari ba gudu ba."


  "Toh toh ina sauraranka."


  "Batun Amal ne, a gaskiya ni mutum ne mey fad'in gaskiya a ko da yaushe komin d'acinta komin kuma ya take."


  "Tabbas haka wannan yake ni kaina na fahimci hakan a d'an cikin kwanakin nan da muke tare."


  "Madallah, kasan shi gaskiya komin d'acinsa fad'inta yafi barinta da tayi tsami."


  "Tabbas Mallam Muh'd."


  "Ban san ya kai da Afzal zaku kar6i wannan labari ba amma ya zama dole a matsayina na wanda Amal take hannunsa in sanar daku duk wani abinda na sani game da ita baze yuwu don son abun duniya ko makamancin hakan inyi muku k'arya in tauye muku hak'k'i ba saboda son zuciya da gudun abin kunya."

  Na matuk'a both Afzal da Abbansa suka shiga cikin rud'ani amma ba wanda ya iya bud'a bakinsa ya tambayi meke faruwa, shiru sukayi suna jiran jin k'arshen labarin. 


  "Shi aure abu ne babba wanda ko addininmu ma ya nuna mana fa'idarsa shiyasa bana wasa da sha'aninsa, idan aure yayi kyau toh zuri'ah ma zatayi kyau idan ko ta 6aci zumunci da komai ya lalace kenan. D'aya daga cikin ababen da yake rusa d'aurewan aure kuwa shine ginata akan k'arya."


  "Wannan haka yake Mallam Muh'd" Afzal de ido ya zubawa Papi yayinda hak'urinsa ya gaza don jin k'arshen wannan labari. 


  "Shiyasa nace tun kafin magana yayi nisa gara in sanar daku wannan al'amarin dake 6oye a gareku. "


  "Ina jinka Mallam Muh'd."


  "Sanin kanku ne ba nine mahaifin Amal ba, Kakanta nake amma a hannu na ta girma."


  "Wannan haka yake Mallam Muh'd."


  "Afzal nasani ko ban tambaye ka ba ze iya yuwuwa Amal ta ta6a maka magana batun mahaifinta akan ya rasu, hakane?"


  "Hakane Papi da jimawa ma kuwa, a kullum addu'an mu na tattare da shi Allah ya jik'ansa ya sa mutuwa hutu ce a garesa."


  "Ameen" Abba ya amsa. 


 "Gaskiyan al'amarin shine banida yak'inin hakan. Kaman yadda bazan iya cewa eh gashi Abban Amal ya mutu ba haka zalika bazan iya cewa yana raye ba, masani se Allah."


  "Sorry?" Afzal da kansa ya d'aure yayi saurin tambaya. "Kana nufin baku san inda ya shiga ba kawai kukayi assuming ya rasu?"


  "Haka nake nufi Babana. Daga ni har Mamin nata bamu da masaniya akan inda bawan Allan nan yake."


  "Subhanallahi! Allah ya fito dashi a duk inda yake toh" Abba ya fad'a yayinda Afzal ya amsa da "ameen."


  "Ina son ku sani cewa ba a haifi Amal da uba ba, Amal bata da uba" kat kuma seya yi shiru. Yadda kuka san anyi mutuwa neither Afzal nor Abba spoke up. Shiru kukeji a wajen yayayinda fuskokinsu ke d'auke da d'imbun mamaki da neman k'arin bayani barin ma Afzal. 


  "No this can't be possible" Afzal ya shiga k'aryata zancen daga bisani "No I'm not believing this, taya zakace an haifi Amal ba uba bayan ita da bakinta tace mun ya rasu ne please Abba tell him this's not possible" yayi stating a kid'ime. A lokaci guda ya fita daga hayyacinsa. Taya batin kowa ace Amal tasa ce bata da uba? Wai mey ma hakan ke nufi? So ake ace mai Amal tasa shegiya ce? Bayan duk kamala, kamun kai, addini da hankalinta? No! Baze ta6a yarda da hakan ba. 


   "Afzal kayi hak'uri nasan ni mey laifi ne, yaci ace tun farko na sanar da kai da mahaifinka gaskiyan al'amarin ba se na bari har magana ta kai ga matakin aure ba amma kuma Allah be bani ikon yin hakan ba se yau, ka sani ko da wasa ban so zolayar ka ba. In da kuwa hakane da bazan ta6a sanar daku wannan al'amari ba dukda muhimmancinta se idan ranan da dubu ya cika saboda haka nake sake baku hak'uri idan har duk tsawon lokacin nan kunga kaman na 6ata muku lokaci ne ku gafirceni. Gaskiya de d'aya ce kuma na fad'eta ba a haifi Amal da uba ba tunda mahaifin nata ya samu abinda yake nema daga gun mahaifiyarta bamu sake ji daga garesa ba har yau. Yanzu haka Amal bata san da wannan magana ba saboda ba wanda ya ta6a sanar da ita gaskiyan labarin ta."


  Shiru ne ya d'au wajen, daga bisani Afzal ya shiga magana "Mey hakan ke nufi kenan Papi?" ya tambayesa cikin rud'ani "Kana nufin zaku rabani da Amal kenan?" Har anan Abba bece komai ba. 


  "Ba wai haka nake nufi ba Afzal shawara ya rage naka da na iyayenka kaman yadda bazan iya tilasta maku auren Amal ba haka bazan iya hana ku ba ni duk abinda kukace shi za'ayi kawai bana son agina aure ne akan k'arya."


  "Kaman ya Papi? Wani irin magana kake haka? Dan an haifi Amal ba uba shikenan se na k'ita? Laifin ta ne? Ya kake magana haka Papi?"


  "Ba wai abinda nake nufi ba kenan Afzal ka fahimceni, kade san irin zamanin da muke ciki a yanzu, yadda ake tsangwan yaran da suka tsinci kansu a cikin hali irin na Amal. Ni kuma muddin ina raye bazan bari aci zarafinta ba. Amsan ku nake jira idan kunga baza ku iya had'a zuri'a da ita a hakan ba toh kar kuji komai ku sanar dani haka Allah ya k'addara."


   "Tabbas kayi gaskiya Mallam Muh'd sam ba k'arya acikin abinda ka fad'a ko d'aya kuma ina gode maka na bud'e mana cikinka da kayi har ka sanar damu wannan sirri me uban nauyi. Ina son ka sani cewa sirrinka is safe with us, ba wanda ze kuma yaji wannan magana bale har hakan ya jawo wa Amal matsala a rayuwarta. Ya zama dole in yabawa halinka, a gaskiya samun irinku a zamanin yanzu se an tona. Sai dai ina son ka sani cewa this will not change a fact, kasani baza mu bari wannan labari ya dawo mana da hannun agogo baya ba kokuwa yasa a fasa abinda aka fara. Muddin Afzal yana son Amal kuma yana son ya aureta ko a hakan ni da mahaifiyarsa bamu da matsala saboda ba laifin Amal bane don an haifeta ba uba baza kuma a k'i ta don hakan ba so Afzal" nan ya juyo yana kallonsa "Mey zaka ce game da wannan al'amari? Kasani abinda kakeso shi zanyi maka."


  "Abba bansan na mey kake tambayan baki na ba, I love Amal and ko a yaya take zan aureta I don't care ko ta rasa ganinta kokuwa ji. Ko da gurguwa ta koma zan aureta a hakan saboda zuciyarta nakeso ba looks nata ko asalinta ba. I love her and I'll marry her regardless." Sosai Papi yaji dad'in kalamun Afzal da Abbansa tabbas sun cika mutanen k'warai sun kuma nuna wa Amal so tsakani da Allah. 


   "Toh Mallam Muh'd kade ji, saboda haka nake son ka kwantar da hankalinka ka sani wannan aure kaman an riga an d'aura ne da izinin Allah."


  "Toh madallah Allah sanya albarka aciki ya nuna mana ranan."


  "Ameen ya Allah" Abba ya amsa.


  "Papi ina da alfarma please" Afzal yace. 


  "Ina jinka Babana."


  "Kace Amal bata da masaniya game da al'amarin nan ko?"


  "Bayan ku da nake sanar ma wannan labari da mahaifiyarta ba wanda yake da masaniya ga al'amarin nan kuma nakega se 'yan unguwan da suke nan lokacin da abun ya faru a garin Askira."


  "Papi please kada a ta6a sanar da Amal wannan magana."


  "Ko meyasa kace haka Afzal?" Ya tambayesa cike da son k'arin bayani. 


"Bana son hakan yasa ta tsani kanta ta fara guje wa mutane ciki harda ni, please kar a fad'a mata komai this should remain as a secret between us kamin alk'awari kai da Mami baza ku ta6a fad'a mata komai game da maganan nan ba. I want her to remain the Amal that she is, with equal right like everyone possesses."


  "Afzal-"


  "Please Papi, Abba dan Allah ka rok'eshi da kar su sanar da Amal komai wallahi nasan halinta kad'an ne daga cikin aikinta bayan taji labarin nan tace ta fasa auren saboda tunaninta bata zeyi bata kai ta auri d'an halak ba, I love her this way and I wouldn't wanna be separated from her."

  

  "Toh Mallam Muh'd kade ji alfarman da Afzal yake nema inda hali kada a sanar da Amal d'in kaman yadda ya buk'ata dan Allah."


  "Alhj Amin nifa duk abinda kukace shi za'ayi saboda kun nuna mun halacci kun nuna wa Amal d'ina soyayyan da bayan nida mahaifiyarta bana tsammanin akwai wanda ze sake kwatanta mata irinsa idan har kuna ganin fad'a mata wannan magana ze iya jawo matsala se a fasa Allah tabbatar mana da alkhairi."


  "Ameen nagode" Afzal ya fad'a "Thank you so much Abba thank you Papi."


  "Ba komai d'an albarka Allah cigaba da yi ma albarka."


  "Ameen Papi thank you."


  "So zamu koma Afzal bismillah jeka fiddo da kayakin toshin."


  "Wasu kayakin toshi kuma Alhj Amin?"


  "Yadda de al'ada ta kawo d'an akwatuna uku ne da naka guda d'ai dana mahaifiyarta itama."


  "Shikenan mu kuma aikin mu komai aka kawo hab mun kar6a?"


  "D'aya daga cikin riban haifan 'ya mace kenan. 'Ya'ya mata arziki ne."


   "Hakane kam amma namun yayi yawa ne."

 

  "Toh wannan kuma sede kayi musu da al'ada dan ni shi nake bi tashi Prince ga makullin motar." Afzal da kansa ya shigo da akwatunan da suke guda biyar in number seda kit guda d'aya making it six. Godiya sosai Papi yayi sannan ya rakasu har bakin k'ofa. A hanyan su na komawa gida Afzal ya rok'a Abba da komin yaya karya sanar da Ummi wannan 6oyayyan al'amari ya buk'acesa da maganan da ya zauna a mtsayin sirri a tsakaninsu su biyu kad'ai. Abba beyi jayayya da hakan ba, shi de addu'ansa d'aya ne yadda Afzal ke son Amal da yadda itama ta sadaukar da soyayyarta masa Allah sa soyayyan nasu ya d'aure. 


  Bayan dawowan Papi ciki ya kira Mami inda yake nuna mata kayakin da su Afzal suka sauk'e yake kuma sanar da ita alfarman da Afzal ya rok'a. 


  "Toh Alhamdulillah sede nayi kaud'i na sanar da Baby nifa."


  "Kin sanar da ita mey? Yaushe?" Ya tambaya cike da k'in yarda. "Da izinin wa?"


  "Bawai na fad'a mata ainihin labarin ba neman tubanta kawai nayi da ta yafemun idan labari ya isketa."


  "Toh da sauk'i dan Afzal yace baya son a sanar da ita komai."


  "Allah sarki yaron nan ya cika d'an halas wallahi, tsakani da Allah yakeson Amal Allah yasa son ya d'aure har bayan auransu."


   "Ameen kira Baby'n ku shiga da kayakin ta duba barin shiga da nawa nima."


  "Sun amince da ranar da muka d'aukan ko sun buk'aci ayi canji beyi musu ba?"


  "A'a sun nuna komai ya musu yanzu de rana kawai ake jira."


  "Toh madallah Baby!" Ta k'olla mata kira. 


  "Na'am" ta amsa daga ciki. 


  "Fito mu shiga da kayakin gashi har akwatuna uku kika samu na toshi."



***** 8:12pm 

  Nazeefah ce a kitchen tana dafa musu  indomie ita da Afzal yayinda yake zaune a kan gado a d'aki yana had'a kan ragowan aikin da ya rage masa a office sega wayansa ya shiga ruri dubanwan da zeyi yaga Amal ke kira wai! Wata sabuwa, baze ma iya tuna rabon da ta kirasa ba. Be 6ata lokaci ba yayi picking, "Se yau aka tuna dani kenan."


   "Ai kullum kana cikin raina Yaya makaranta ne bayi bari na."


  "Toh ya kike?"


  "Lafiya k'alau ya aiki? Ya gida? Ya Nazeefah?"


  "Alhamdulillah komai k'alau ya school?"


  "School se godiya."


 "Madallah Allah taimaka toh."


  "Ameen Yaya da wahala haka kuma?"


  "Wani wahala ne kuma Lily nifa bana son godiyan nan naki."


  "Kayi hak'uri amma godiya ya zama dole Yaya, mungode sosai Allah saka da alkhairi ya k'ara bud'i please ka tayani yiwa Ummi godiya."


  "In shaa Allah Lily."


 "Toh goodnight kar in shiga hak'k'in Nazeefah."


   "Toh Lily goodight, I love you" daga nan ta katse. Mayar da wayan yayi ya ajiye yana me tunanin abinda Papi ya fad'a masa. Sede ya kasa yarda da hakan har yanzu gani yake kaman mafarki ne, shi Amal kawai yake tausayawa yasani komin jimawa wataran gaskiya ze fito he can't imagine the kind of pain Amal will go through idan ta gano gaskiyan labarin asalinta shide ya d'au alk'awari no matter what baze ta6a goranta mata da komai ba he'll love her until his last breath.


***

  A kwana a tashi kaman gobe ne ga mey rai a haka har su Amal suka kammala exams nasu na first semester daga nan ta mayar da hankalinta sosai ga karatun Qur'aninta dan son samu ta had'a kafin auran nasu, dududu saura watanni biyu ne bikin. 


   Ta fannin Afzal da Nazeefah kuwa sun gama shiri tsaf a yau jirginsu na zuwa Saudi ya tashi amma kafin nan seda suka bi gida sukayi sallama da kowa. Kaman yadda ya d'au wa Amal alk'awari, suna isa Jiddah yayi texting nata akan cewa sun isa lafiya. 


  Nazeefah dan farin ciki fa ji take kaman ma duniyan bazata iya d'aukanta ba. Lafiya k'alau suke zama ita da Afzal duk wani abinda tasan yana iya 6ata masa rai batayi, yi tayi bari ta bari. Ba k'aramin jin dad'in zama da ita Afzal yake ba, ba tashin hankali ba komai se zallan soyayya da kwanciyan hanakli. Haka nan tun sauk'ansu a Saudi kusan kullum se sun fita sunyi shopping sun fita yawo, sede wayon Afzal duk abinda ya sai wa Amal baya barin Nazeefah ta gani, ko da wasa be ta6a kawo abu d'aya daya saya wa Amal a hotel room nasu ba. Wani balarabe mey hankali ya samu wanda yake ajiye kayakin nasa a wajensa. Yau satinsu d'aya kenan amma tun kiran Afzal da Amal tayi don yi mai sannu da zuwa bata sake kiransa ba shima kuma da gan-gan be sake yi ta kanta ba, Allah ma yayi Nazeefah na d'auke masa kewa da idan yayi wasa se wani attack d'in ya sakd kamasa. Sosai yake missing nata amma yayi making mind nasa muddin ita bata kirasa ba toh shima baze sake kirarta ba har se idan sun dawo Nigeria lafiya. 

   

   Nazeefah na wanka a bayi kasancewan zasu fita unguwa kawai sega call na Amal dan mamaki yama kasa d'agawa seda call d'in ya kusa tsinkewa tukun. 


  "I'll call you back" ya sanar da ita had'e da katsewa. Mik'ewa yayi ya fice inda ya sauk'a k'asa sannan ya kirata. Bayan sun gaisa yake ce mata "Se yau aka tuno dani kenan ai na d'au bazaki kira ba."


  "Shine kak'i kira kaima wato ko?"


  "Gani nayi kaman ina damunki ne Lily not as before kwata-kwata yanzu baki kirana ko na kiraki ma Allah-Allah kike mu gama wayan ki huta ko ba haka ba?"


  "Se gashi na baka kunya na kiraka kuwa."


  "Waya sani ko Mami ce ta sanya ki na dole kaman ma ina jin muryarta k'asa-k'asa."


  "Kai Yaya banda sharri de ya Nazeefah?"


  "Lafiyarta k'alau tana wanka ma muna shiri zamu fita."


  "Toh yayi kyau a dawo lafiya se anjima."


  "Wait!" ya katse ta.  


  "Yes?"


  "Baki fad'a mun mey kikeso ba fa, ko bakiya son tsaraban Yaya?"


  "Ina so mana." 


  "Then tell me then mey kikeso, name anything."


  "Anything?" Ta tambayesa tana nazari. Sosai yake jin dad'in hiransu na yau. Watarana Amal ta sake tana hira dashi koda shike yasan ba har cikin ranta take hakan ba kawai de tanayi ne but even still he can't help but to feel happy. 


  "Anything Lily" ya jaddada mata. 


  "Ni tsarabar kanka kawai nakeso, ka taho mun da kanka cikin k'oshin lafiya."


 "Shikenan abinda kikeso?"


 "Yes Yaya" ta tabbatar masa. 


  "Toh karki damu dal acikin leda zan kawo miki kaina."


  "Wani dal acikin leda kuma? Zan de yi maneji da kai ko ka manta kai ba saurayi bane yanzu?"


  "Aww abun kuma gori ya koma?" Dariya tasa ta cikin wayan shima besan lokacinda ya jonata suka cigaba da dariyan ba. Ba k'arya acikin soyayyan da yake yi mata, ita ta daban ce, he'll choose spending time together with her than anything in this world. Shi kansa ya san son da yakeyi mata bayida k'arshe kaman yadda bayida farko. Da alama Allah ya soma amsa masa add'o'in da yata sauk'ewa akan Amal ne a gaban ka'aba shiyasa ta soma sakewa da shi haka. 


   "A hakan kuma zaki aureni ba."


  "Don't get too confident ina iya nemo d'an saurayi na in aura."


  "Nine nan de d'an saurayin naki karma ki 6ata lokacinki."


  "Toh Yaya kar na cinye wa uwar gidanmu lokaci je ka tayata shiri se anjima ko? Mami tace in gaishe ka."


  "Toh ina amsawa thanks for calling baby I love you." Wani irin bak'on yanayi ta tsinci kanta da yakirata da 'baby' dukda cewan sunanta ne na gida amma setaji wani iri kodan tana da tabbacin da wata manufar ya fad'a ne?


  "You take care" da haka sukayi sallama. Afzal ya kasa 6oye farin cikin da ya tsinci kansa aciki, se kallon ckin wayan nasa yake yana cize la66e. Da murmushi kwance fal a fuskansa ya haura sama d'akinsu inda ya tarar da Nazeefah zaune akan towel tana shafa mai. 


   "Ya rouhi (my soul, sunan da take kiransa da shi) ina kaje?" Ta soma da tambayarsa. 


  "Wani friend d'ina ne yazo na sauk'a muka gaisa" ya had'a mata k'aryar nan take. 


  "Ai na d'au tafiya kayi ka barni."


  "Har na isa in fita ba tare da Rabba'atul bait d'ina ba? Ko de so kike hukuma ta kamani?"


"Har kana tunanin zan bari hukuma ta kamaka?"


  "Toh gashi na d'au kafin in dawo har kin gama shiri sede gashi mai ma kike kan shafawa."


  "Toh Ya Rouhi ai bazaka had'a tsawon wanka na da naka ba kaifa cikin minti biyu shaa ka yi wanka ka fito."


  "Ke kuma har sama da minti talatin ba."


  "Eh mana" ta amsa tana murmusawa. 


  "Toh shirya dai ina jiranki." Zama yayi akan gado yana kallonta yayinda take ta shafa manta a hankali. A garin mik'ewa bayan da ta gama shafa man towel nata ya kusa sincewa da hanzari ta tattare sekace wacce aka ce mata idan ta bari towel d'in ya fad'i toh wuta za a kaita. Yadda ta kid'ime ne ya sanya Afzal dariya, ba shiri ya shiga dariya har yana neman k'warewa. Har akwai abinda be gani bane a jikin nata da take wannan rawar jikin? Shi bata ma ishesa da kallo ba. 


  "Ya rouhi wallahi mugunta ba kyau" ta sanar dashi tana turo baki. Dariyar yake har yanzu da k'yar ya iya ya tsagaitar sanan ya mik'e ya k'arisa inda take tsayen had'e ca janyota jikinsa yana mey zagaye hannayensa a 'yar k'ugunta yayinda da ta zagaye nata a wuyansa. 


  "Toh koda towel d'inma ya kunce mene ban gani ba anan d'in Rabba'atul bait?" Ya tambayeta yana yi mata nuni da ido. 


  "Kai Ya Rouhi dan Allah ka dena" ta fad'a cike da kunya, kafin tace zata sauk'e hannayen nata daga wuyan sa yayi sauri ya miyar dasu. A lokaci guda wani zuciyan ya raya masa da ya sanar da ita cewan ya kusa k'ara aure saboda this is the right time da zata yima kanta addu'a ko Allah ze sassauta mata zafin kishinta yayinda wani zuciyan kuma ya hanasa yin hakan yana rinjayansa cewan ai akwai sauran lokaci.


 "Tunanin mey kake haka Ya Rouhi?" Ta tambayesa a hankali bayan tsawon lokacin data d'auka tana kallonsa. 


  Kai yayi saurin kad'awa yana me sake matso da ita kusa da shi, har nishinsu na had'ewa sannan ya murmusa yana mey kallon cikin dara-daran idanunta. "Was I thinking of something?" Ya tambayeta. 


 "Gashi gabad'aya hankalinka baya jikin ka."


  "Well I'm just happy that you're happy being with me."


 "Awwn Ya Rouhi being with you is my absolute pleasure. I love you so much, so much that bazan ma iya kwatantawa ba."


  "Allah?"


  "Sosai fa wallahi k'awaye na har cemun suke wai nafi sonka fiye da yadda kakeso na kuma Allah na yarda da hakan."


  "Ko meyasa?"


  "Saboda baka ta6a cemun kana so na ba koda kuwa ni na fad'a maka" ta fad'a sincerely. Sosai ya tausaya mata saboda yasan how she must be feeling anytime yayi mata hakan, shima duk lokacin da yace wa Amal yana sonta amman tayi shiru tak'i mayar masa da amsa ba k'aramin damunsa hakan yake ba, wai a hakan ma shi na miji ina ga Nazeefah ita mace kuma? Murmusawa yayi "Then stop feeling sad about it."


  "But I can't."


  "You have to because I love you too my rabba'atul bait" ya sanar da ita. Har cikin ranta taji dad'in kalamun nasa yayinda suka kwanta a birnin k'irjinta . 

  "Ze iya yuwu wa ban ta6a furta miki ba amman ba wai hakan na nufin bana sonki bane I love you so much."


  "Dagaske Ya Rouhi? You really love me?" Ta tambayesa yayinda ta kasa 6oye farin cikin da ta tsinci kanta aciki. 

   

  "Wai tayaya ne ma bazan fara son wannan kyakkyawar yarinyar da bata da burin da ya fi taga ta farinta mun ba? Mace mey ladabi da biyayya, da iya soyayya da kuma sanin ya kamata, macen da ta gwammace ranta ya 6aci da nawa ya 6aci, wacce ta tsani ganin fushi na. Macen da kowani na miji zeyi alfaharin samunta a matsayin uwar gidansa taya ya kike tsammanin bazan so ki ba my rabba'atul bait? Amsa da kanki you think it's possible?" Kai ta kad'a a hankali cike da kunyan jin dad'i. "I love you kinji? I love you so much my rabba'atul bait."


  Bata san lokacinda ta soma zubar da hawayen jin dad'i ba "I love you much more Ya Rouhi, my husband, my heartbeat and everything, Allah ya bar min kai ya kare min kai wallahi banjin zan iya rayuwa idan ba soyayyarka."


  "Shhh!" Ya katse ta yana mey share mata hawayen nata "I'm never leaving your side till eternity bar kukan haka."


  "Thank you Ya Rouhi" a hankali ya mik'a had'e da sauk'e lips nasa akan nata yayin da ya shiga yi mata wani irin kiss yana kashe duk wani sassa a jikinta. Tuni yasa ta mance da inda take, basu hankara ba kawai suka jisu akan gado. Cike da daraba ya janye towel da take ta faman tare jikin nata da shi ya wullar a k'asa sannan ya shiga sarrafa ta yadda yakeso. Unguwan da basu zo suka fita ba kenan! 

  


  

RANA D'AYA!

#RD


 Love... King Miemiebee👄✨

[13/08, 09:33] ‪+234 907 483 8352‬: 🎀🎀🎀                 🎀🎀🎀

                🎀❣🎀

                   ❣❣


  💦💦                      🍃🍃🍃          

           *RANA D'AYA!*

  💦💦                      🍃🍃🍃

  July, 2018

 beeenovels.blogspot.com


     _Written by Miemiebee👄_



   *PAGE 2⃣5⃣*



   Shirye-shiryen biki kuma aka shiga yi na sosai, kaman yadda akayi bad'ad'in bad'a haka aka kuma. Kyautan gida Abba ya sake yiwa Afzal a matsayin gudumawan da ya bayar. Sosai Ummi take taimaka wa Afzal, kusan komi ita takeyi, duk wani abinda yake buk'ata fa toh tun kafin ya furta zata tambaya masa gun Abba. Akwatuna har guda ashirin da d'aya aka had'a wa Amal sannan na Nazeefah kuma set mey k'waya shida na fad'an kishiya. Kusan duk zannuwan da suke cikin na Amal akwai su a na Nazeefah babancin kawai na Amal sunfi yawa ne. Abinda ya kama daga kan kayan kitchen, gadaje, kujeru, show glasses, rugs, da komai Ummi ne suka siya, ba yadda Mami batayi da ita ba akan ta bari ko wani abu k'adan ne su kawo yaso se a had'a kud'in ayi siyayyan amman Ummi tak'i kasancewar Afzal ya rok'eta da komin yaya karta yadda ta amsa koda kobo ne daga gun su. Sude kawai suyi focusing akan abincin da za'a dafa.


     Mutum na iya rantsewa 'yar Ummi ce zatayi aure don kalan kayakin d'aki masu tsada da alfarman da ta sai wa Amal. Gida yayi kyau sosai se wanda ya gani. Yau ana saura sati uku d'aurin aure kenan. 


***

   "Halo Yaya?" Tace bayan ta d'aga wayan. 


  "Na'am Baby" ya amsa. 


   "Yaya wai yaushe ka fara kirana da Baby?" Yau kam ta kasa hak'ura seda ta tambayesa. Kusan sati kenan yana kiranta da hakan, kuma da gan-gan yake gano bata so. 


  "Jimin 'ya da ba sunanki bane?"


  "Ni Amal ne suna na."


  "Baby'n fah?"


  "Sunan gida ne." 


  "Ni d'in ba d'an gida bane?"


  "Ni ba haka nake nufi ba kawai na gwammaci kana kira na da Amal ne."


  "Toh nak'i ni Baby nafi so."


  "Toh Allah taimake ka, ina yini?" ta gaishesa. 


  "Lafiya d'an fito waje kinji?"


  "Yaya ka fa san an fara yimun gyaran jikin."


  "Se akace baki sake tako waje?" 


  "Toh ai Yaya idan na rink'a fita muna had'uwa bazaka ga effect na gyaran jikin ba."


  "Nide fito ina jiranki." Nan da nan ta janyo hijabinta tasa ta fita taje ta samesa. 


  "Tabarakallah gaskiya Allah yayi halitta anan" ya ce da ita lokacinda ta shiga motan "Masha Allah, Abba yayi gaskiya da yace na iya za6i kin ganki kuwa?"


  "Kai Yaya kadena zolayata mana."


 "I'm damn serious wai ma yaushe ne auren? I can't wait any longer."

 

   Wani irin ruwa cikinta ya d'auka, ba shiri ta had'iye miyau had'e da tambayansa,

  "Uhm so what brought you here?" Don canza topic d'in. 


  "Is it a crime idan ango ya zo ganin amaryarsa sati uku kafin aurensu?"


  "Ba wai haka nake nufi ba I mean akwai matsala ne?"


  "Ohh wato ma haka kika miyar dani se idan akwai matsala nake tahowa ko?"


  "Goodness! Nifa ba haka nake nufi ba."


  "Toh yaya ne?"


  "Babu nayi shiru."


 "Yauwa da yafi kam so jiya kika gama bada haddanki duka wai ko?"


  "Eh."


  "Congratulations then, Allah sanya albarka aciki yasa idan kika tashi haifo mun yara ki haifa mun hafizai kaman ki Lily I'm so proud of you."


  "Ameen Yaya thank you" ta amsa tana mey jin kunyansa. 


   "Yauwa wai inji Ummi tunda aka shiga yi maki jere baki je kinga gidan naki ba?"


  "Gida na kuma? Gidan mu de." Ba k'aramin dad'i lafazin nata yayi masa ba. 


 "Toh gidanmu" ya gyara kaman yadda ta buk'ata. 


 "Eh amma Mami tace cikin satin nan zamuje."


  "Toh ni nazo in kaiki ne yanzun."


  "Toh ai ya kamata in sanar da ita kafin nan."


  "I've already done that so don't worry."


 "Toh shikenan."


  "Kafin nan ina fatan kuna waya da tailor'n naki? Idan fa baki tak'ura mata da kira kad'an ne daga cikin aikinta tayi disappointing naki se ranar dinner'n yazo ki rasa kayan sawa."


  "Yaya ni dole ne se anyi wannan dinner?"


  "Wannan kuma seki tambayi Ummi tunda ita tace zatayi, da kud'in d'inkin ki dana komai ita tace zatayi handling ni karki sani cikin shirgin ku."


  "Toh ai laifinka ne da kace mata baka buk'ata tunda de Allah yayi wannan ba shine auren ka na farko ba ai zata ji."


 "Kefa kike gani kaman ba wannan ne aurena na farko ba tamkar sabon saurayin da ze angwance nake jin kaina so be calling the tailor on frequent basis kina mey tuna mata kayan naki, okay?"


  "Toh shikenan."


  "Sekuma batun wushe-wushe da kamu ko? Lokacin aurenmu da Nazeefah naga su Mummy sunyi mata and I can say I absolutely loved everything about the event inason a naki ma ayi."


  "Yaya dan Allah kayi hak'uri nifa ban ga amfanin tarukucen nan ba wallahi hanyan kashe kud'i ne kawai, kayan dinner kad'ai kusan dubu d'ari biyu wannan kuma nawa zasu ce? Ni gaskiya banason kashe kashen kud'in haka ya isa."


  "Toh banda ke da abunki wushe-wushe kam ba al'adanku bane ku shuwa? Ai ya zamo dole kiyi."


  "Bawani dole d'innan ni kashe kud'i ne bana so."


  "Laffaya nefa kawai zakisa."


  "Shi d'in bada kud'i za a siya bane?"


  "Lily wai ni ke miki magana kina jayayya dani?"


  "Ni ba jayayya da kai nake ba Yaya, a matsayina na wacce zaka aura ne nake yi maka gyara."


  "Toh banaso se anyi wushe-wushen da kamun ga wannan" yayi maganan yana d'auko wata bak'ar leda daga backseat. "Gashi" ya mik'a mata. Amsa tayi ba musu ta bud'e sabon laffaya ta gani me uban kyan k'arshe irin na 'yan Sudan masu d'ankaren tsadan nan. Yaya!" Tayi exclaiming. 


   "Yayi miki?"


  "Fisabillahi nawa ka kashe a nan?"


  "So kike in fad'a miki kud'in saboda kice baza ki sa ba? Ki kwantar da hankalinki ba tsada."


  "Mey k'arya..." se tayi shiru


  "Naji mey k'arya d'an wuta bade hakan ze sa in fad'a miki kud'in ba, so yanzu an gama da maganan wushe-wushe se kuma na Kamu."


  "Ni wallahi 6arna da kud'i ne banaso ga walima ga wushe-wushe ga dinner mey na wani kamu kuma? Kai baka tausaya wa kanka dasu Abba ne kam Yaya? Ni gaskiya ba wani kamun da za'ayi." 


 "Allah baki isa ba."


  "Har Allah fa kace Yaya?"


  "Eh baza kiyi auren nan dry ba mey sekace auren dole za ayi miki? Ai ko na Nazeefah da na dolen ne ma anyi celebrating se naki ne zaki wani ce a'a? Ko so kike ki nuna mun auren dole ake shirin miki Lily?"


  "Yaya ba haka bane kashe kud'in ne ya isheni dubi ko tsinke fa ka hana su Papi siya."


  "Ai ni na d'auke muku ba ku kukace nayi hakan ba kuma ko a addinance ma ya halatta idan miji nada k'arfi ya d'auke wa matar da ze aura da iyayenta nauyin komai so ki daina bothering kanki kinji? Ni naso in d'auke muku kuma ko a ina ma yin hakan ba laifi bane."


  "Thank you so much Yaya Allah k'ara bud'i, I really like this laffaya, wallahi yayi kyau sosai."


  "Ameen glad you like it, so kin amince ayi kamun? I'll just talk to our wedding planner."


  "Nikam a'a wushe-wushen ya wadatar."


  "Mey laifin in anyi duka toh Lily?" 


  "A'a gaskiya nikam guda d'aya za'ayi."


  "Toh wa ze hak'ura cikin mu?"


  "Yaya kai babba bazaka hak'ura ba?"


  "Nak'i hak'uran."


  "Toh shikenan ni k'arama zanci girma."


  "Nak'i yarda da hakan."


   "Toh kuma?"


  "Duka biyu za'ayi."


  "Wai kam cire kud'i ba amfanin nan baya damunka ne? Wallahi haramun ne ko sena ja maka aya tukun?"


  "Ko ki yarda ko in samu Papi ince mishi gashi tun kafin ayi aurem kina mun rashin kunya ina miki magana sam bakiya ji."


  "Ni yaushe na yi maka rashin kunya? Sharri zaka soma min tun kafin in shiga gidan naka?"


 "Toh ki amince kai karma ki amincen da kin k'i da kinso se anyi duka hungo wannan" yayi maganan yana d'auko wata bak'ar leda dake ajiye gun k'afansa. "Mey wannan d'in?" Ta tambaya tana warware ledar. Invitation card na programme of events na auren nasu ta tarar aciki, ashe duk surutun nan da yakeyi har ya riga ya sa an buga komai ciki harda kamu da wushe-wushen kawai neman sata surutu yake. 


  "Ashe har ka sa an buga."


  "Dama in fad'a miki ne kayan da zakisa a kamun already na gun tailorna bada measurement naki."


  "Ni wallahi har kunyarka nakeji Yaya komai kai kakeyi."


 "Ba wani abin kunya dama al'adan yarabawa ango shi keyin komai ko cokali mace bata kaiwa gidanta so stop bothering yourself."


   "I know thank you won't compensate but thank you so much Allah k'ara bud'i."


  "Ameen don't mention so mu tafi?"


  "Eh muje ba kace ka riga ka sanar da Mami ba?" Da haka ya jasu suka wuce gidan nasu wanda yake unguwan Old GRA. Amal seji take kaman komi a mafarki yake faruwa, koda wasa bata ta6awa kawowa a ranta cewan wataran zatayi aure acikin fankacecen gida irin wannan ba, itama 4 bedroom flat ne da parlour biyu se kitchen da store d'aya da kuma guest toilet d'aya. Ita ba abinda yafi burgeta ma kaman yadda aka k'aya kitchen natan, yadda komi yake in purple and white gaskiya ba k'aramin kud'i su Ummi suka kashe ba. Addu'a tayita yiwa Afzal da Ummi dan idan ba addu'ar ba bata tsammanin akwai abinda zata iya yi da ze iya biyansu kalan d'imbum alkhairin da sukayi mata. Gida sekace mutum na aljannar duniya. Bayan ya sauk'eta a gida sukayi sallama sannan ya biya gida gun Ummi. 


   "Kayakin Nazeefan kazo d'auka ko?"


  "Eh Ummi are they ready?"


  "In a moment, amma Prince kace akwati shida be isheta ba se har an yi mata goma? Sekace itace amaryar?"


  "Ummi kinsan halin Nazeefah yanzu haka idan taji na Amal 21 nata shida wallahi ba k'aramin tada mun hankali zata yi ba."


 "Lallai kam kai kaso amma ban ta6a jin inda akayi kayan fad'an kishiya set goma ba shidan nan da muka had'a mata a farko yayi."


  "Ayi mata goman kawai kowa ya huta."


  "Toh shikenan kayaki suna hanya sun kusa isowa."


  "Alright toh thank you so much Ummi Jazakillahu khair."


  "Ameen wa iyyaka, ya amaryar tamu? Munyi waya da Mami d'azu tace wai ka d'auki Amal ka kaita duban gidan nata."


  "Eh wallahi lafiyarta k'alau tana gashe  ki ma."


  "Ayya ina amsawa, yaya gidan tace wai? Komi yayi mata ko?"


  "Sosai ma, bakiga kalan godiya da addu'an da tayita yi maki ba wallahi."


  "Allah sarki 'yar albarka kace mata kar ta damu."


 "Ai ko na fad'a mata, wai ayi kamu da wushe-wushen da yake kaman al'adansu wai sam baza ayi ba walima ya wadatar ita bata son kashe kud'i dinner'n ma ta amince ne saboda tana jin kunyarki" ya sanar da ita. Dariya sosai Ummi tasa. "Ai ustazancin Amal takan nan kam se a hankali, kuma fa ba komai yake hanata amincewan ba tuna yadda zata fita ba mayafin kirki a idon jama'a ne yake damunta."


  "Ai kaman kin sani da fari ma cemun tayi wai abaya zata sa zuwa gun dinner'n" Nan ma wani dariyan Ummi ta kuma sawa "Kai!! Amal takan nan drama queen ce, ai nace da tailor'n nata tayi mata decent d'inki, kayan da baze bayyana jikinta ba."


  "Hakan yayi sosai."


 "Toh Allah bada zaman lafiya ya nuna mana ranar auren nan."


  "Ameen Ummi thank you for all that you've been through for me wallahi bansan ta ina zan fara biyanki ba."


  "Ba komai Prince karka damu bayan kai fa ba kowa idan ban yi maka abinda kakeso na lalata ka ba wa zan lalata toh?"


  "Your boy loves you so much."

   

  "I love him even more."


  "So mey Daddy'n Nazeefah yace bayan da Abba ya sanar dashi zan k'ara aure?"


  "Me kuwa zece? Ya taya ka murna mana ai har ya sanar da mahifiyar nata ma don jiya ta kirani take cewa in tayaka murna."


  "Ayyah Alhamdulillah toh."


  "Yanzu dey matsalar d'aya ce Nazeefah Allah sa tayi maka kyakkyawan fahimta duk da cewan ka makara, yaci ace ka sanar da ita da jimawa."


  "Ameen fah wallahi ni har tsoro ma nakeji kinsan kalan zafin kishinta kuwa? Akwai lokacin da Amal ta ta6a kawo mun aldeb sena zuba flasks d'in acikin fridge bakiga yadda hankalin yarinyan nan ya tashi ba da ta ci karo da flasks d'in."


  "Aikam daga yadda take magana ma mutum ze san tana da zazzafar kishi Allah de sa ta yayyafawa zuciyar tata ruwan sanyi tayi maka kyakkyawar fahimta."


 "Ameen Ummi" bada dad'ewa ba akwatunan da yasa a k'ara d'in suka iso nan ya had'a dana farkon ya cika goma cus aka sanya masa a booth. Sallama sukayi da Ummi sannan ya fice, se hasbunallai wa ni'imal wakeel yake ta nanata cikin motan yau yasan se gobara ya kusa tashi masa a gida.


   A cikin motan ya baro kayakin ya k'arisa ciki. Mik'ewa tayi tamai sannu da zuwa had'e ba sa light kiss on the lips. 

  "Ya Rouhi ina kaje haka tun d'azu ina jiranka?"


  "Akwai wasu ababen da na kula dasu ne I'm sorry for keeping you waiting."


  "Ayyah ba komai muje in had'a maka ruwa kayi wanka food is ready." D'akin nasa suka k'arisa nan da nan ta had'a masa warm water sannan ya shiga. Tana cikin ninke kayakin sa da ya cire dan kaisu laundry room wayan sa dake kan gado ya shiga ruri bata damu ta duba wa ke kira ba ta cigaba da harkar gabanta. Call d'in na tsinkewa meshi ya sake kira se anan ne tayi tunanin bari ta lek'a taga ko waye ne, idan Ummi ce tace mata yana wanka. 


  'Lily❤💕' taga yana flashing akan screen d'in bayan nan ga picture'n Amal da yayi saving contact d'in dashi. Wani irin mumunan fad'i gabanta yayi bata san lokacinda ta shiga yin kakkarwa ba. Tabbas ta wayi fuskan nan amma ta rasa a ina, kode a makaranta ne? Kai da wuya toh a ina ta waye ta? Da hanzari tayi picking kafin call d'in ya tsinke had'e da yin shiru. 


  "Halo Yaya?" Amal ta soma da cewa. 


   "Kina neman waye?" Nazeefah ta tambayeta, Amal na jin muryan tasan na Nazeefah ne bata sake cewa komai ba kawai ta katse wayar. Nazeefah bata kai ga ajiye wayan ba Afzal ya fito daga bayin d'aure da towel a iya kunkuminsa. Kallo d'aya yayi mata yasan ba lafiya ba, idanunsa na sauk'a akan hannunta da ke rik'e da wayan nasa kuwa ya gama tabbatar da abinda ke faruwa. Tabbas Amal ce ta kira Nazeefah kuma ta d'auka. Innalillahi! Meya hanasa shiga da wayan nasa bayi kaman yadda ya saba? Sam ba haka yaso ba, yafi son ya sanar da ita komai da bakinsa ba wai ta gano hakan da kanta ba. Nauyayyan numfashi ya sauk'e sannan ya k'arisa inda take tsayen har yanzu. 


   "Nazeefah-"

  

   "Da abinda zaka sak'a mun kenan Ya Rouhi?" Ta katse sa. 


  "Meya faru? Mey wayana keyi a hannunki kuma if I may ask?"


  "Kiranka akayi na d'aga" ta amsa. 


  "Kawo muga" ba gardama ta mik'a masa kaman yadda ya k'udura a ransa kuwa Amal d'in ce ta kira. 


  "Wacece ita? Meyasa take ce maka Yaya? Mey ma'anan wannan hearts da suke gaban sunanta?" Ta jero mai tambayiyo a lokaci guda. 


  "Nazeefah calm down."


  "I can't calm down Ya Rouhi I can't! You mean to tell me for all this while dama kana da wata a waje? Wow!" Ta numfasa cike da d'umbun mamaki se ganin al'amarin take kaman raha. 


   "Nazeefah I'm sorry but wallahi inada niyyan sanar dake komai."


  "Sanar dani mey? Akan kana da budurwa? Seriously Ya Rouhi? Meney bana yi maka a gidan nan da zaka za6i ka k'untata mun haka? Why do you have to flirt behind my back?" By now har idanunta sun soma cikowa da hawaye. 


  "Nazeefah please don't cry" ya fad'a a kid'ime. Hannun sa tayi saurin cirewa kafin ya samu ya rik'e ta. "I'm not flirting behind your back kema kinsan ba hali na bane hakan, I respect you a lot to hurt you like this."


  "Then explain mey contact na yarinyan nan keyi a cikin wayanka da kuma dalilin da zaisa tana kiranka Yayanta."


   "Sunanta Amal and am willing to marry her." Wani irin mumunan fad'i gabanta yayi aure de?

  "Aure?" Ta nanata cike da k'in yarda. "Aure Ya Rouhi? Aure kake shirin yi?"


  "Yes Nazeefah ina son in k'ara aure kuma Amal nike son in aura, kiyi hak'uri na rashin sanar dake da wuri da banyi ba but kar kiyi tunanin nayi hakan ne don inci zarafin ki. Not at all, I do have a reason for not informing you, nafi son se na gama had'a miki kayan fad'an kishiyanki ne, auran namu is in three weeks time in Allah ya yarda."


  "No!" kai ta shiga kad'awa yayinda take k'aryata duk wani abinda ya fad'a, take wan irin sharp headache ya kamata. "This can't be possible" ta shiga cewa "It can never be possible dan Allah kace wasa kake mun Ya Rouhi" ta rok'esa yayinda take hawaye sosai. 


   "Dan Allah kibar kukan haka Nazeefah."


  "Aure fa kace Ya Rouhi? Mey nayi maka da zaka auro mun kishiya? Idan wani laifin na maka wanda ban sani ba dan Allah ka sanar dani a shirye nake da in baka hak'uri amma please let this be a joke."


  "It is no joke Rabba'atul Bait and ni baki yi mun laifin komai ba, I love you, you know that right?"


  "No" ta katsesa "You don't love me Ya Rouhi, you've never loved me, inda kana so na da baza ka ta6a tunanin yi mun kishiya ba, why? Why?" Tuni ta rushe da wani irin masifaffen kuka. Rungumota yayi niyyan yi amman sam ta hanasa da k'yar ya samu ya rufe ta gam ajikinsa yayinda kukan nata ya tsananta. Sun dad'e a hakan yana ta bata hak'uri amma ina ta kasa hak'uran se kuka take. Chan ya d'agota daga jikinsa ya shiga share mata hawayen nata "Come with me" ya buk'aceta. Batayi gardama ba ta bisa a baya yayinda ya rik'e hannunta cikin nasa ya jata izuwa parlour inda D'anladi ya jera akwatunan nata. 


   "Do you believe it's not a joke now?" Ya tambayeta a nitse. 


  "Mey wannan d'in?" Ta tambayesa a hankali. 


  "Kayan fad'an kishiyanki Nazeefah." Bata iya k'ara yin magana ba yayinda ta rushewa da wani fitinannen kuka mey tsuma zuciya. Shikenan ya tabbata aure Afzal zeyi amma ko be kyauta mata ba, na mey zeyi mata kishiya bayan duk wani abinda yake so tana mishi, bayan nan ace seda aure ya rage sati uku ze sanar da ita? Me tayi da za ta fuskanci hukunci me tsauri haka daga garesa? Bazata iya zama da kishiya ba, da ta zauna da kishiya gomma ta rasa ranta. 


  "Ya Afzal you're such deceit, ka cuceni kaci amanata kuma ka sani I'll never forgive you, I'll never forgive you for tricking me that you did. For all these while you made me believed you loved me ashe ba haka bane wasa da hankalina kawai kake chan a waje kana da wacce kakeso kake kuma son ka aura ka kasance da ita, me na ta6a yi maka da zaka mun wasa da hankali haka? Ashe k'arya kake mun duk sanda ka ce ka yafemun."


   "Ko da wasa Nazeefah, ki yarda da ni idan nace miki na yafe miki na kuma mance da duk wani abinda kikayi mun da a baya, I'm terribly sorry Nazeefah bazan gaji da baki hak'uri ba ki sani ina sonki, I really do love you."


  "No you don't love stop lying to me" Hannayenta biyu ya had'a acikin nasa  "I'm not lying to you Nazeefah, I really do love you wallahi I do."


   "Wallahi k'arya kake you don't love me you've never once loved me" ta k'aryatasa cikin tsananin kuka. Tausayi sosai ta basa barin ma ganin yadda hawayen ke tsiyaya daga idanunta, na matuk'a ta basa tausayi. 


  "Nazeefah please stop crying" yayi maganan yana k'ok'arin rungumarta sede tak'i barinsa. "Don't you dare touch me!" Be saurareta ba haka na k'arfi yayi hugging nata ya shiga shafa bayanta a hankali yayinda yake showering kisses akanta. "Shhh! I've got you, I love you so much."


  "Idan da har kana so na da baza ka fara tunanin k'aro aure ba" tayi maganan had'e da raba jikinta da nasa tana share hawayenta "Mey yayi zafi da zaka yi mun kishiya Ya Rouhi? Mey ka ta6a nema a gidan nan ka rasa, girki ne inayi maka, ina respecting naka ina tsaftace maka muhalli baka ta6a neman hak'k'inka a guna ka rasa ba, duk abinda kace kana so shi nakeyi wanda baka so kuwa koda hobby na ne ina k'ok'arin dainawa, mey yayi zafi da har seka k'ara aure?"


  "Nazeefah kin manta ni miji ga mata hud'u ne? Bayan nan bakisan mata sun fi maza yawa a al'umma ba yanzun? Idan kowani na miji yace mace d'aya kacal ze aura sauran kuma waze auresu? Bakiya son 'yar uwarki ta raya sunna itama ta cika umarnin anmabin mu SAW?" Nasiha ya shiga yi mata sosai saidai ina kishi ya riga ya rufe mata ido bata jin kira. 


  "No Ya Afzal! Bazan bari ka auro wata muddin ina raye, bazan zauna da kishiya ba."


  "Wayace kishiya zan auro miki Nazeefah? Abokiyar zama zan kawo miki."


 "Bana sonta bana so."


  "Nazeefah please calm down kiga baki ma santa ba fa amma kike cewan baki sonta, Amal is a very nice girl ina da tabbacin you two will get along."


  "Bana son sanin ko ita wacece ina ji ina gani bazan bari wata ta sace mun kai ba Ya Afzal, I'll do whatever it takes in tabbata wannan aure be auku ba you'll see."


   "Nazeefah-"


  "Kuma ka tattara kayakin fad'an kishiyanka or whatever you call it bana buk'ata" tana kaiwa nan ta nufi d'akinta ko amsa kiran da yakeyi mata batayi ba. Hijabinta ta sanya ta d'au makullin motarta yana ganinta yasan fita zatayi be hanata ba saboda yasan ba amfani ko da yayi maganan ma ba sauraronsa zatayi ba. Kad'an ya rage bata take k'afan D'anladi ba da ta zo fita daga gate d'in, gida ta wuce direct se d'akin Mummy.


  Khalifah ta tarar mik'e kan gado se faman latsa wayansa yake. 


  "Ya Nazeefah" ya kirata had'e da mik'ewa zaune. 


  "Ina Mummy?"


  "Tana wanka" ya amsa take. 


  "Jeka d'auko mun ruwa" tayi maganan tana cire hijabinta. 


  "Ni shikenan kinzo ki fara aikan mutum ba" ya watsa mata harara. 


  "Nace kaje ka d'auko mun ruwa wallahi kar ka bari in sauk'e haushin da nakeji akanka."


  "Ki sauk'en mana a jinki zaki iya duka na ne?" yayi maganan had'e da mik'ewa, daga bakin k'ofa ya wulla mata gorar ruwan da ya d'auko matan sannan ya haura sama d'akinsa. Kad'an tasha ta rufe ta ajiye, bada dad'ewa ba sega Mummy ta fito. 


  "Ha'ah Nazeefah ce a gidan namu yau."


  "Mummy" ta kirata tana turo baki tamkar wacce zatayi kuka. 


  "Meya faru?"


  "Mummy kina jin Ya Afzal wai aure ze k'ara."


  "Dama bakida labari ne?" Mummy ta tambaya tana mey zama a gefenta. 


  "Aww kina sane dama?"


  "Eh though nima ban dad'e da sani ba be sanar dake bane ke?"


  "Wallahi se yau yake fad'amun."


  "Ai na d'au kina da labari auran sauran sati biyu ne ko uku nema."


  "Wallahi Mummy bazan yarda ba adalilin mey ze auro mun wata? Wai harda akwatin fad'an kishiyansa."


  "Guda nawa?"


  "Ni nama irga ne amma yafi shida de naga kaman."


  "Toh ai ki godewa Allah."


  "In godewa Allah fa kika ce Mummy? Uwar mey zanyi da kayan fad'an kishiyan nasa? Tsirara nake yawo ne?"


  "Kiga Nazeefah kowa yasan kishiya da zafi amma idan Allah ya k'addaro maka toh fa dole ne ka hak'ura banda ke da abin ki an riga an sa rana, rana ya gabato ajinki akwai borin da zakiyi ne da ze hanasa yin auren?"


  "Wallahi auren nan bazata saku ba komin yaya ne se nasan yadda zanyi in hana aukuwan hakan."


  "Uhn uhn fa Nazeefah kar ki bari kishi ya kaiki ga halaka ki kwantar da hankalinki don za ayi maka kishiya bawai hakan na nufin mijinka baya sonka bane, kefa da bakinki kikace yayi miki kayan fad'an kishiya ai yaci ace kin hak'ura Afzal na sonki ke kanki kin sani, a zamanin nan ba kowani na miji bane ze yiwa uwar gidansa akwati dan wai ze k'ara aure. Ga akwati ba d'ayaba ba biyu ba keda kanki kikace zasu fi shida."

   

   "Son banza so a baki, wallahi baya sona da yana sona da baze ma fara tunanin yin wani auren ba mene bani yi masa da zece seya sake aure. Ke yau shekara nawa kuke tare da Daddy meyasa bece ze sake yin wani auren ba? Idan ba fitina ba mata nawa yaga Abbansa ke da daze kama yace shi se yayi mata biyu."


  "Kowa da ra'ayinsa Nazeefah. Kisani Afzal daban yake da Abbansa ko ni dake nan ba d'aya muke dake ba. Shi kishiya kuma tana kan kowa wallahi ko ni nan ban isa in bugi k'irji ince Daddy'nku baze k'ara aure ba, a yau d'innan yaga dama ze k'ara auransa, hak'uri ya zama dole."


  "Ni wallahi bazan yarda ba auren namu dududu shekara nawa ne befa kai uku ba, ya bari ma idan na gama haihuwa na mana amma ko k'wark'wata ban ajiye ba har ya fara tunanin yin wani auren, Allah bazata saku ba." 


   "Ta ma riga ta saku ne fah Nazeefah don banga abinda ze hana aukuwan auran nan ba idan ba mutuwa ba. Dan Allah ki rufa min da Daddy'inku asiri ki d'au hakan a matsayin k'addarar ki, ni kaina zan saki a addu'a Allah ya sa hakan shi yafi alkhairi."


  "Amma Mummy kin ban dariya har akwai alkhairi ne acikin kishiya?"


  "Toh kije Nazeefah kiyi duk abinda kika ga ya dace amma idan kika zo kika rasa auren naki daga k'arshe kar kiyi blaming d'ina nide na fad'a miki" bata sake cewa komai ba ta ja hijabinta ta fice. Gidan k'awarta Suwaiba ta nufa da ikon Allah kuma mijinta baya gida. Zama tayi ta irga mata halin da ake ciki, sosai Suwaiba ta ji mata takaici amma ta nuna mata lokaci ya riga ya k'ure ba yadda za'ayi a hana aukuwan auren. 


  "Taya zakice haka Suwy? Nida nake cewa zaki share mun hawaye idan nazo."


  "Wallahi ba yadda za'ayi saidai idan malamai zaki fara bi."


   "Malamai? Wasu irin malamai kenan?"


  "Malaman tsibu nake nufi."


  "Subhanallahi Suwy! Kin san ko yin hakan shirka ne?"


  "Tabbas na sani amma kuma idan bada su ba mutum baze ta6a iya mallake mijinsa ba kinga Ibrahim (mijinta) idan nace masa zauna ya zauna se abinda nakeso yakeyi I can't bear the risk of sharing my husband da kowata shegiya idan a shirye kike gobe goben nan ina iya kaiki gidan malami na ya share miki hawaye."


  "A'a kam gaskiya zan zauna inyi tunani am sure akwai wata hanyan da zanbi in hana aukuwan auren nan ba tare da na fita daga musulinci ba."


  "Toh sani de ya rage wa me shiga rijiya kije kiyi shawaran anytime your mind is made up, gidan malam kullum a bud'e yake yana maraba wa bak'i."


  "Toh ni zan wuce."


  "Bari in raka ki."


  "A'a yi zamanki keda kikayi nauyi, Allah de raba lafiya."


  "Ameen toh se anjima." Maimakon ta zarce gida ta wuce gidan wata k'awarta Maimuna har bayan maghrib tak'i dawowa gida. Tun Afzal na trying numbanta har ya gaji ya dena don kashe wayan tayi gabad'aya don kar ya tak'ura mata. Se wajajen k'arfe tara ta dawo gida. Tana shiga sega Afzal zaune kan kujera kallonsa tayi sannan ta kawar da kai ji take kaman ta nad'a masa duka don takaici. Daga bisani ta shiga takawa bata kai ga shiga corridorn da ze kaita d'akinta ba ya kira sunanta. Banza da shi tayi se akaro na biyu sannan ta tsaya had'e da kewayowa. 


  "Ina kikaje?" Ya tambayeta. Shiru tamai ko ta kallesa ma bale wai tasan yanayi. 


  "Magana nake miki Nazeefah ina kikaje? I've been trying to reach you but am sure da gan-gan kika kashe wayan naki don kar in sameki, yeah?"


  "Gida naje, wayana kuma ya mutu ne ba charji" ta amsa sama-sama. 


  "Don't think of lying to me, na kira Mummy tace tun La'asr kika bar gida so where did you go?"


  "Gidan k'awata excuse me" bata kai ga juyawa ba ya dakatar da ita mik'ewa yayi ya tako zuwa inda take tsaye. "Da izinin wa kika fita sannan ya dace a matsayin ki na matar aure ki fita se cikin daren nan ki dawo?"


  "Kayi wa kanka fad'a kafin kayi mun Malam, ya dace a matsayin ka na magidanci amma kana neme neman mata? Bayan nan se three weeks to d'aurin aurenka zaka sanar da ni a matsayina na matarka?" Sosai ransa ke 6aci duk lokacinda ta kwatantasa da mey neme nemen mata sanin ba halinsa bane amma ya ya iya? Dan dole ya danne zuciyansa, yasani duk acikin zafin kishin ne don haka yayi mata uzuri. 


  "Look Nazeefah" yayi maganan had'e da aza hannunsa a kafad'unta "I know this's not going to be easy on you, I know how it must hurt, ina sane da komai shiyasa nake rok'anki da kiyi hak'uri dan zan k'ara aure bawai hakan na nufin mabud'in wahala maki bane kokuwa wai zan mance dake ko in walak'anta ki. Nazeefah I love you, I'm proud to have as my Rabba'atul bait, Amal might be my bride but kece uwar gida na, which applies being my soul. Please karki bari kishi ya rufe miki ido yayi destroying relationship namu, I love you Nazeefah and I don't wanna lose you."


   "Duk k'arya ne" ta fad'a had'e da sauk'e hannayensa daga jikinta "wallahi duk k'aryar banza ce inda kana so na da bazaka ta6a tunanin k'ara aure ba."


  "Nazeefah dan zan k'ara aure ba wai hakan na nufin na daina sonki bane, zan k'ara aure saboda sunna ne, ki d'au Amal a matsayin 'yar uwarki ba kishiya ba."


  "'Yar uwa fa kace? Kar ka sake kwatantata da 'yar uwata dan duk mutumin dake shirin sace maka miji ba d'an uwanka bane, Amal mak'iyata ce bana k'aunarta, bazan ta6a sonta ba kuma muddin ka auro ta a gidan nan toh wallahi kaida kwanciyan hankali kunyi sallama sena tabbata na tada maka hankali fiye da yadda ka tadamun nawa yanzu mu zuba da kai a gidan nan muga" tana kaiwa nan ta wucesa ta shige d'akinta had'e da sa key. Ruwa ta watsa ta sauk'e sallan Isha sannan ta fito in search of what to eat. Afzal ta tarar zaune kan dining yana shan corn flakes ko ta kansa batayi ba ta zarce kitchen ta shiga dafa indomie. Bayan da ya gama sha ya shiga yayi joining nata a kitchen d'in. 


  "Ni baza a dafa dani ba?" Ko juyawa ta kallesa batayi ba wai gani yake kaman wasa take ko? Ze gani. 


  "But I'm hungry."


  "Kula da yunwan ka ya tashi daga kaina ya koma kan na amaryar ka. Idan har bazaka iya jure yunwan ba your bride is just a call away kana iya fita kaje ka sameta daman ka saba" ta basa amsa ba tare da ta koda juya ta kallesa ba. Be sake cewa komai ba ya jira ta, bayan data gama girkin yabita har cikin d'akinta. Duk yadda takeson ce masa ya fita haka ta hak'ura, tasan da gan-gan yake hakan don ya sata yin surutu. Bayan da ta gama ci ta sinche bathrobe dake jikintan ta sanya kayan baccinta ta feffeshe jikinta da turare sannan ta kewayo garesa "Malam kana iya bar min d'akin zan kwanta."


  "Yau kuma nine Malam? Ba Ya Rouhi?" Shin wai ya d'au wasa take? Ze sha mamaki na lahira seya fisa jin dad'i. 


  "Ka de jini ka fice mun a d'aki."


  "Naji anan zamu kwana yau?"


  "Malam am damn serious ka fice mun daga d'aki zan kwanta."


  "In kinga nabar d'akin nan to dake ne in fact hak'k'i na ma nakeso, I need my wife."


  "Idan a garinku ana kusantar matar da take haila toh bismillah" ta sanar dashi cike da rashin kunya. Duk yadda yaso 6oye dariyansa ya kasa "Baby kin manta yanzu kika idar da sallah ne?" Yayi maganan yana nuni da sallayar da tayi sallan akai. K'aramar tsuka taja "seka cinye d'akin idan ya zama abinci" sannan ta janye pillonta ta fice. Bayanta yabi izuwa d'ayan d'akin data shiga, haka suka tayi k'arshe tazo ta kwanta a parlour akan d'aya daga cikin couches d'in. Sarai yasan kujeran ba iya d'aukansu zeyi duka ba amman ya bita har kai dan neman magana, kusan rabin jikinsa akan nata yake. 


  "Wai don Allah meye haka?" Bata kaiga mik'ewa ba ya jata nan ya samu ya baje akan kujerar had'e da aza ta akan k'irjinsa. Gagam ya matseta yadda ko k'wak'k'war motsi bazata iya ba. 


  "Malam ka sakeni!"


  "Shhh let's sleep baby."


  "Ka sakeni ko sena shak'e tukun?" Adjusting nata yayi yadda zata na iya nishi da kyau amman bawai ya saketa ba. Duk kalan suratan da tayi-tayi hakan besa ya saketa ba, dan kanta ta daina surutun sabida yadda ta galabaita. Acikin awa d'aya bacci mey nauyi yayi awon gaba da ita, seda Afzal ya tabbata baccin nata yayi nauyi sannan a hankali ya sauk'eta daga jikinsa. D'agata yayi cike da dabara ya kaita d'akinsa ya shinfid'a ta akan gadon had'e da gyara mata kwanciya. Bayi ya fad'a ya watsa ruwa sharp-sharp sannan ya fito ya kwanta a gefenta had'e da kashe musu wuta. Pillonsa ya kawo kusa da nata sannan ya zagaye hannunsa a jikinta wane wanda wani ke shirin k'wace masa ita, a hankali bacci ya d'aukesa. 





RANA D'AYA!

#RD


Love... King Miemiebee👄✨

[13/08, 09:33] ‪+234 907 483 8352‬: 🎀🎀🎀                 🎀🎀🎀

                🎀❣🎀

                   ❣❣


  💦💦                      🍃🍃🍃          

           *RANA D'AYA!*

  💦💦                      🍃🍃🍃

  July, 2018

 beeenovels.blogspot.com


     _Written by Miemiebee👄_



   *PAGE 2⃣6⃣*



    

    Asuban fari alarm na Afzal yayi ringing, bayan ya kashe ya kunna bedside lamp ya kewayo yana kallon Nazeefah dake ta bacci a hannunsa cikin kwanciyan hankali. Peck yayi placing mata a goshi had'e da furta "Allah sassauta miki wannan kishi Rabba'atul Bait, I love you" cike da dabara ya rabata daga jikinsa ya sauk'a daga kan gadon ya nufi bayi. Bayan ya fito yayi shirin zuwa masallaci sannan ya shiga tayar da ita. 


  "Ta shi kiyi sallah zan wuce masallaci" yana tabbatar da ta tashi ya fice.  

  Dawowansa ya tarar Nazeefah bata d'akin dama yasan za ayi hakan. Kwanciya yayi kan gadon ya koma bacci kasancewar yau Asabar ne ba aiki. Se wajajen goma sha d'aya ya tashi bayan yayi wanka ya d'au wayansa ya fice parlour inda ya tarar da Nazeefah zaune kan kujera tana faman latsa wayanta. K'amshin turarensa ne ya buga mata hanci, ba shiri ta d'ago kai tana kallonsa ba k'arya yayi kyau ina irin morning shower glow d'innan? Se wani k'yalli fatan jikinsa yake k'ark'ashin ranan dake haskowa ta window. Daga bisani ta kawar da kanta badan wai kallon sa ya isheta ba se don haushinsa da take ji. 


  "Rabba'atul bait yau ba gaisuwa?" Ya tambayeta yayin da yake takowa zuwa inda take. Shiru ta mai ko kallonsa bata sake d'aga kai tayi ba. "Good morning Babe" ya gaisheta had'e da sauk'e mata light kiss a gefen baki. Hannu tasa ta dirje cike da takaici wanda ya mugun basa dariya amma ya dake tare da yin tari dan korar da dariyan. 

  "Islamiyya fa yau bazaki je ba?" Shide a dole seya sata magana. 


  "Mallam kana damuna da surutu please."


  "Rabba'atul Bait please kiyi hak'uri haka nan" ya fad'a had'e da zama a gefenta "Nasan nayi miki ba dai-dai ba and I'm sorry bazan gaji da baki hak'uri ba but please kar ki 6ata tsakanin mu saboda Amal."


  "Seka fasa aurenta tunda baka son tsakanin mu ya 6aci as simple as that."


  "Tayaya kike tsammanin zan iya fasa aurenta bayan an riga an gama komai, mey kikeson incewa iyayenta bayan nan duk hidiman da Abba da Ummi suka yimin ya tafi a iska kenan?"


  "I don't care, kade sani zaman lafiyanka da na ita karuwar taka yayi depending akan hakan."


  "Subhanallahi! ki daina kwatanta Amal da karuwa Nazeefah tunda bata yi miki komai ba kuma baki ta6a ganinta tana wani alfashan ba." 


  "Bata yi mun komai ba?" Ta tambayesa yayinda take k'yalk'yalewa da dariya. "Bata yi mun komai ba fa kace? Tana shirin k'wace mun miji ka ce bata mun komai ba?"


  "Amal bata da shirin yin hakan Nazeefah, wannan abu da kikeyi shi ze sa in nisantar da kaina daga gareki please cut it out."


  "Oh really? So what do you expect me to do then? To fold my arms? K'ara aure fa kake shirin yi, kuma se three weeks to auren kake sanar dani how do you expect me to act? Ince Allah sanya alkhairi?"


  "Hak'urin nan dey shi zan cigaba da baki I know am at fault but abinda kike yin nan kuma ba shi ze hanani fasa auren nan ba kisani fa kaman yadda nake son kasancewa dake haka nakeson kasancewa da Amal, nasan da zafi amma idan kika hak'ura komi mey wucewa ne Nazeefah, I'm never leaving your side and as far as am concerned kece Rabba'atul Bait d'ina not Amal." 


  "K'aryar banza kawai" tayi maganan had'e da mik'ewa "Ni zan fita ina iya kai yamma kumma kafin in dawo kuma."


  "Breakfast d'ina fa?"


  "Ban girka ba kana iya samun karuwar taka aww sorry amaryar taka ta girka maka" bata kai da jin abinda zece ba ta wuce d'akinta. Nan da nan ta fito sanye da hijabi shide Afzal bece mata komai ba banda binta da ido da yayi. Gabad'aya ya rasa mey ke masa dad'i Nazeefah isn't at all ready to understand him, anya kuwa ze iya da wannan bala'in da yake neman afka masa? 


   Gidansu aminiyarta Rumaysa ta taje inda take bata labarin abinda ya faru. 


  "Kar ki gaya mun Babe!" Tayi exclaiming. 


  "Wallahil azeem aure Ya Afzal ze sake yi, ga chan akwatunan fad'an kishiyansa ko kallonsu ma banyi ba."


  "Chab! Amma shiko meyayi zafi da ze k'ara aure? Kode kun samu matsala ne?"


  "Wallahi lafiya k'alau Babe ni daya sanar dani ma na kasa yarda I can't believe for all these while he's been deceiving me."


  "Ai na miji bashida guarantee komin dad'in ki dashi idan be ci miki amana ba baya jin dad'i yanzu ya zakiyi?"


  "Wallahi ban sani ba jiya ina gidan Suwy nake tambayarta mafita tace wai mafitar d'ayace."


  "Wai meh?"


  "Malaman tsubu."


  "Boka de!" Rumaysa tayi exclaiming. 


  "Hmm ai nima nace ba dani ba a iya fahimtan addinin da nayi Allah na yafe ko wani irin zunubi amma banda shirka har mey yayi zafi akan wata shegiya in jefa kaina ga halaka."


  "Gaskiya kam wannan shawara batayi ba amma shin wacece yarinyar wai?"


  "Ina ko zan sani yanzu haka wata banza ce."


  "Kode ze iya yuwawa yarinyan nan da muka gansu tare ranan a Unimaid garden ne?"


  "Waya san masa ne da uban kwashe-kwashen nan nasa."


  "Tsaya ya yarinyar take? Kin ta6a ganinta ko a hoto?"


  "Eh kuma kinsan mey? Allah ba jiya na fara sata a ido ba tabbas nasan na wayi fuskan nata a wani wajen amma na kasa tunawa."


  "Ke ze iya yuwuwa a school ne tunda chan take itama."


  "I doubt a school ne, a de wani wajen muka had'u da ita omg! Wallahi na tuna tabbas itace wacce mukayi clashing da ita a asibiti lokacin da Ya Afzal ba shi da lafiya, Wallahi itace. Itace wacce Sultan yake tambaya ta ko naga ficewarta kutuma amma an jima ana raina mun wayo!" Tayi exclaiming. 


   "Lalle kam ashe har zuwa dubansa tana yi a asibiti."


  "Gashi kuwa am very sure flasks d'incan ma da Ya Afzal yace wai na Umman Sultan ne na yarinyar nan ne wallahi Ya Afzal babban mak'aryaci ne."


  "Ke ba Afzal naki kad'ai ba fa duk maza mak'aryatan kansu ne wallahi sede kawai k'aryan wani yafi na wani, mutanen nan basuda amana ko kad'an imagine yana gadon asibiti rai a hannun Allah amma still yana cin amanarki, tirrr wallahi."  


  "Ai shiyasa bazan bari auren nan ya yuwu ba, dole ne in hana aukuwan auren nan."


  "Aikam kada ki yarda wallahi ba da keba kishi da 'yar shuwa."


  "Aww shuwa ce?"


  "Sosai ma bakiga kalan halittarta bane? Shuwa ce kawai ba tayi hasken su sosai bane."


  "Shegiya sena tabbata na lahira ya fita jin dad'i ai."


  "Yanzu ya zakiyi? Lokaci ya riga ya k'ure miki."


  "A'a kam wallahi da saura."


  "Kefa kikace sati uku ya rage, how??" 


  "Wallahi ban sani ba one thing am sure of is aure de komin yaya ne baza a d'aura ba."


  "Tsaya tukuna ki kwantar da hankalinki ai ba haka akeyi ba, an dena tada hankali yanzu idan miji ze k'ara aure."


  "Ban fahince kiba so kike kice in nad'e hannu kaman sokuwa in zuba masa ido ya k'aro auren nan?"


  "Nahhh ba haka nake nufi ba yanzu ya tsakaninki da Afzal d'in?"


  "Oho mishi ni tun jiya ban sake yi ta kansa ba, yana ta lalashina yana bani hak'uri amma nak'i hakan. Yanzu haka sau biyu nake girki amma banyi da shi kwanciya ma ba a d'akinsa na kwana ba seda nayi bacci ya cicci6eni ya kaini d'akin nasa muka kwanta, da asuba da na tashi na sake komawa d'akina ba wai shi mata biyu yake so ba ze gani sena d'aga masa hankali ya rasa meke masa dad'i."


  "Lmao kai amma Nazeefah bakida dama" ta fad'a tana dariya. "Wanga gashi haka? Karfa ya k'one."


  "Ki barshi mana, a jiyan ma ai ya neme ni na hana sa kaina na fake da cewa ina haila."


  "Innalillahi! Wallah baki da dama" ta fad'a tana ta faman dariya. 


  "Allah bakisan yadda zuciyata ke tafasa bane Rumy, da Ya Afzal ya k'ara aure Allah gara na rasa kwalin degree d'ina."


  "Kai de don Allah!"


  "Wallahi am damn serious, ke bazaki gane irin son da nake yi mishi bane, akanshi fa ina iya yin komi shirka da kisa ne kawai bazan yi ba wallahi."


   "Calm down calm down duk beyi zafi haka ba kinsan mey nakeso da kene?"


 "Sekin fad'a."


  "Pretend like everything is cool kar ki nuna masa auran nan ya dameki in fact ina son idan kin koma gida yanzu kije ki basa hak'uri kiyi tuban muzuru kice kin amince ya k'ara auren."


   "A dalilin mey?!" Nazeefah ta katse ta cike da rashin hak'uri. 


 "Ke matsalata dake gajan hak'uri ki tsaya mana ki saurareni."


  "Ina jinki."


  "Yauwa kinga by doing so zey amince dake kuma ze yarda dake."


  "Kaman ya kenan?"


  "Ina nufin zakiyi earning trust nasa ko wani irin 6atancin aka zo aka fad'a akanki da wuya ya yarda koda kuwa maganan daga bakin mahaifiyarsa ce saboda ke kin riga kin nuna masa kin rungumi k'addarar ki a shirye kike da kuyi zaman lafiya da 'yar uwarki. Da fari yanzu zamu bayyana kan mu a dinan auran nasu ne kice masa zaki je don ki tayasu murna, kinga kowa ya ganki seya jinjina miki harta iyayen nata anan kuma se mu samu mu rugurguza musu komai. Babban aikin namu kuma seta shigo gidan, aya zamu gasa mata a hannu, mun ringa had'a kanta dana Afzal d'in kenan ta yadda koda ta fara kai k'aranki gunsa baze saurareta ba sabida ya riga ya amince dake, ya yarda dake, a hankali har k'orafin da take yi masa a kanki ze soma ishansa tunda de ke gashi baki ta6a furta kalman 6atanci akanta ba hasali ma idan kuka zauna da shi yabata kike kinga anan ze fara ganin kaman ita Amal d'in munafika ce tana son ta shiga tsakaninku ne ta fiddaki daga gidan ki. Toh fa anan hankalinsa ze soma karkatowa kanki ita ko idan tayi sake mutuwan auran nata kenan."


  "Wow wannan shawara tayi, amma ai ni auren ne gabad'aya bana son a d'aura Rumy, bani ma son ta shigo gidan bale ta samu d'uwawun zama."


  "Kema kinsan hakan ba me yuwu bane se de idan zaki d'au shawaran Suwy wanda bazan barki ki d'auka ba."


  "Yanzu haka ina ji ina gani kenan zan fara sharing Ya Afzal da wata shegiya ina raba kwanciya da ita?"


  "Karki damu zamu ci mata uwa idan ta shigo gidan, da k'afan da ta shigo dasu zata fita trust me."


  "Promise you'll not fail me babe."


  "Haba har yaushe na ta6a baki kunya I've got you."


  "I know I will always count on you thank you so much."


  "Karki damu kede kawai ki kwantar da hankalinki wallahi kishiya tayi kad'an ta d'agawa mutum hankali. Kuma kinga ke Allah ma ya taimakeki Afzal nada kirki wallahi wasu mazajen idan suka kusa yin aure wulak'anta uwar gidansu suke amma kiga ke fa har wani tattalinki yake kina mai iskaro."


  "Ai yasan abinda yayi be dace bane shiyasa."


  "Even still Babe ajinki maza suna da kunya ne? Wallahi dan wata shegiya achan karki 6ata tsakaninki da mijinki nifa idan nine ke wani irin mahaukacin soyayya ma zan fara nuna wa Afzal d'in yanzu, kin gane ai ki haukatar da shi da soyayyarki yadda ko 'yar shuwan chan bata isa ta d'auke mishi hankali ba."


  "Kai da wuya fah, kinsan shuwan nan da concussion nasu da iya asirce miji."


  "Yafi kayan mata ne, ai da kayan mata suka dogara su ma, dan haka kema zamu nemo miki akwai wata k'awar Mummy tana had'a kayan matan nan kuma bakiga yadda ake saya ba."


  "Kai Babe!"


  "Ina gaya miki, relax kar ki wani tada hankalinki mugun trap zamu shirya wa 'yar shuwan chan seta gwammace kid'a da karatu."


  "Shiyasa nake yinki sosai wallahi har naji hankalina ya d'an kwanta."


  "Ai ya kwanta ma gabad'aya, keda Afzal mutu ka raba wallahi takalmin kaza."


  ****

 Bayan sun idar da sallan Azahar Nazeefah ta d'au Rumaisa a mota sukayi gidan k'awar Mummy suka sai mata masu tsadan cikin kayakin, bayan matar tayi mata bayanin yadda za'ayi amfani da su suka sake komowa gidansu Rumaysan ba ita ta koma gidanta ba se wajajen biyar da rabi. Shiganta parlour taci karo da Afzal zaune kan kujera yana aiki akan laptop nasa. Jakan nata ta rik'e da kyau gudun kar ya zame asirinta ya tonu. Gyaran murya tayi had'e da yin sallama. A hankali ya d'ago kansa tare da amsawa sannan yayi mata sannu da zuwa. 


  A ranta sam bata da niyyar amsawa amma dan dole tayi in order to keep up with the act. 


  "Kin dawo?" Ya tambayeta yana neman ajiye laptop nasan. 


 "Eh" ta amsa. 


  "Your food is ready then" da mamaki ta tsaya kallonsa "Girki kayi?" Ta tambaya. 


  "Yes spaghetti."


 "Wow!" ta numfasa ai ita ta d'au idan ta dawo gida wani fad'an zasu 6arke da ita. Shin wai shi Afzal d'innan wani irin mutum ne? Ko yayi fushi ma ta fita tun safe amma se yanzu take dawowa? Fa duk yadda takeson ta tsanesa hakan ya gagara sema reasons da zesa ta k'ara sonsa yake bata. "Taho muje in had'a miki ruwa ki watsa se muci abinci ko?" Yayi maganan yana k'arisowa inda take. 


  "Ni a k'oshe nake."


  "Ba za kici girkin Ya Rouhin ki ba? Kar kiyi mun haka please" yayi maganan had'e rik'o hannunta cikin nasa. "Let's eat kinji?" Kai ta gyad'a a hankali sannan suka k'arisa d'akin. Bayan ya sirka mata ruwan ya d'auko mata towel ya barta ta cire kayan nata ma yak'i wai sam shi ze cire mata. Haka har bayin ya kaita sannan ya fito bayan ta watsa ruwa ta yi alwala ta fito, wani dogon rigan daya ware mata a gefe ta sanya ta feffeshe jikinta da turare sannan suka fito dining inda yayi serving nasu abincin sukaci. She can say he's very good at cooking saboda ba k'arya abincin yayi dad'i. Sosai take son ce masa girkin yayi dad'i amma tuna yana da niyyan kawo mata kishiya seta fasa. Shi da kansa ya tattare plates d'in bayan sun gama sannan ya ja kujera ya zauna agefenta tare da had'a hannunsu gu d'aya yana shafawa a hankali. 


  "Nazeefah I'm sorry kinji? Nasan na miki ba dai-dai ba kamata yayi tun kafin asa rana in sanar dake batun Amal amma son zuciya ya hanani I just want you to know that bawai nayi hakan dan inyi hurting naki bane I just couldn't muster the courage to tell you, I respect you alot Nazeefah gani nake idan na sanar dake ranki ze 6aci ni kuma gudun hakan nake, bana son abinda ze 6ata min ke but I'm sorry if my actions ended up hurting you, I'm so sorry kinji?"


  "It's okay Ya Rouhi ka dena bani hak'uri haka."


  "Eh??" Ya tambayeta cike da k'in gaskata abinda kunnensa suka jiye masa. 


  "I should be the one who's sorry, forgive me kaji?"


  "You have nothing to be sorry for Rabba'atul Bait, na fahimci halin da kike ciki and na sani kishi dole ne hak'uri kawai nake son ki k'ara akan wanda kikeyi."


  "Ba komai ya wuce."


  "Kin amince in k'ara auren?" Kai ta gyad'a masa a hankali, janyota yayi ya azata kan cinyarsa ba. "Like forreal? Kin amince?" Nan ma kan ta kuma gyad'awa. Besan lokacinda ya had'e lips nasu gu d'aya ya shiga kissing nata ba, bata 6ata lokaci ba ta shiga mayar masa da martani sun d'au lokaci suna abu d'aya sannan a hankali yayi breaking kiss d'in had'e da rik'o fuskanta "I love you Babe, Allah miki albarka."


  "Ameen Ya Rouhi I love you too." Wani kiss d'in ya sake sauk'e mata a goshi "Thank you so much da wannan had'in kan da kika bani, bazan ta6a mancewa da hakan ba Nazeefah and I want you to put you trust in me kisani zanyi iya k'ok'arina don ganin nayi adalci tsakaninki da Amal you have my words." Hannunta ta d'aga ta zagayesu a wuyansa had'e da sauk'e masa kiss a gefen lips nasa "I trust you Ya Rouhi, I believe in you ka dena damuwa kaji?" A hankali ya zagey nasa hannun a kunkuminta yana me sake matso da ita kusa da shi. 


  "Thanks Babe."


  "So tell me a ina kuka had'u da Amal d'in?"


  "Tun kafin muyi aure muke tare da ita."


 "So she was your first love."


  "I'm sorry but yes she is."


 "Wow toh meyasa baka aureta ba tun farkon?"


  "Relationship namu wasn't a love at first sight thing, daga baya ne nayi developing feelings mata and I had to marry you saboda inyi biyayya wa Abba kaman yadda kema kika aureni don yin biyayya wa Daddy ko ba haka ba?"


  "Hakane kam so tell me about her, inda hali inason jin komi akanta."


  "Ask me anything."


 "Like her age, school, family'nsu da komai."


  "Itama yarinya ce kaman ki sai dai zata girme ki da shekara d'aya zuwa biyu haka, sannan tana attending unimaid itama."


  "Haba wani department?"


  "Nursing tana part three."


 "Wow kace mun samu likita a gida kenan so waye mahaifinta?"


    "Ba wata 'yar babban gida bace, mahaifinta ma ya rasu agun kakanta take."


  "Allah sarki wace yare ce toh?"


  "Shuwa ce."


  "Shuwa?" Ta nanata sekace bata sani ba "Ya Rouhi yanzu da shuwa kakeson ka had'ani kishi? Ni na ma yi surrender, ai kaima kasan ban isa inyi kishi da 'yar shuwa ba."


  "Inji waye? Da mey ta fiki ai yadda kike da kyau itama hakan ne."


  "Ba wani ta fini kyau."


  "Amma ai kin fita hasken fata." 


  "Bawani ai naga hotonta a wayan ka itama fara ce."


  "Even still kin fita, kyau kuma dukan ku kyawawa ne."


  "Hmm Allah de baka ikon yin adalci a tsakaninmu Ya Rouhi." 


   "Se inda k'arfi na ya k'are in shaa Allah Nazeefah shiyasa nake son ki kwantar da hankalinki kisani kece babba a gidan nan, it doesn't matter Amal ta girmeki as far as we all are concerned kece Rabba'atul Bait ba kuma wanda ya isa ya k'wace martaban hakan daga gareki ba."


  "Bawani nasan tana shigowa ka d'anata zaka mance dani tunda gashi Allah yayi sabuwa dal take a leda."


  "Ai kema a sabuwanki na sameki Nazeefah I'll do my best to love you both equally."


  "Toh Allah ya baka iko."


 "Ameen abinda nake son ji kenan taho muje ki duba kayakin naki."


  "Ni bana so."


  "Why? Kayan basu miki ba a dad'o wasu?"


  "Sekuma in kaisu ina? Ai ahakan ma sunyi yawa kaya sekace nice amaryar."


 "Just to tell you how much I love you."


  "Thank you Ya Rouhi."


 "Always babe, taho muje ki duba toh kin ko san zannuwa iri d'aya Ummi ta sai miki keda 'yar uwarki?"


  "Allah sarki Ummi, Allah kad'ai ze iya biyanta." Da haka suka nufi d'akin nata inda ya jera mata akwatunan. Sosai tasha mamakin adadin kayakin da suke ciki tamkar itace amaryar. Bayan sun gama dubawa suka shiga shirin sallan maghrib. Haka nan tun daga ranan ba a sake jin kan Nazeefah da Afzal ba, shawarar k'awarta ta d'auka. Wani irin soyayya da kulawa na musamman ta fara nuna wa Afzal fiye da na da. Afzal couldn't ask for more rannan har buk'atansa tayi da ya had'ata waya da Amal su gaisa, ba Afzal kad'ai ba ita kanta Amal taji dad'in sauk'in kai irin na Nazeefah. Lafiya k'alau suka gaisa har ita Nazeefahn takeyi wa Amal fatan alkhairi. 

   

  Tsaf Afzal da Nazeefah suka shirya abinsu yau sukaje duban gidan Amal inda Nazeefah ke ta yabawa kayakin d'akin Amal akan sunyi kyau, hakan ba k'aramin burge Afzal yayi ba, yadda Nazeefah ke k'ok'arin 6oye kishinta don ta farinta masa. Be sanar da ita komai ba bayan kwana uku ta dawo daga unguwa kawai ta tarar an sake furnishing mata parlour da exact kalan kujeru da rug na Amal banbancin kawai color ne. Godiya tayita yi masa, ita kam dad'in har yayi mata yawa, tunda ta nunawa Afzal ta amince da auren nan tasamu wani girmamawa na daban daga garesa, kud'i yake bata anyhow ko bata tambaya ba, ga wani tarerayarta da yake yi. 


  A haka ne har Allah ya kawo satin bikin Afzal da Amal wanda aka fara da walima wanda aka had'a da na sauk'an Al~Qur'anin da tayi, ita tazo na biyu a gwajin da akayi musu. Sosai ta samu kyautuka da dama ciki harda kujeran hajji wanda ta bawa Papi, kaman yadda Abba yayi alk'awari shiko kyautan mota ya bata k'irar Matrix. Bayan walima akayi Kamu washegari wanda Amal ta bala'in yin kyau acikin pitch asoebin ta, ga lallen nan da makeup nata komi ya zauna. Afzal kansa ya kasa daina kallonta through out the event sece mata yake tayi kyau. Washegarin kamu akayi wushe-wushe wanda ta sanya laffayan da Afzal ya sai mata. Ranar Asabar aka d'aura aure akan sadaki dubu d'ari da sisin gold arba'in. Da yammacin ranan dangin ango sukazo suka d'aukan amaryarsu, kukan da Amal taci kam ba a cewa komai da k'yar aka samu aka fiddota daga gidan nasu aka kaita family house nasu Afzal inda aka shiga shiryata for dinner. Achan Nazeefah da k'awarta suka saci idan mutane suka d'auke head na Amal. Bayan an gama kwalliya za a shiga d'aurin kai, d'ankwali yace ku neme ni. Ba duban duniyan da ba'ayi ba amma babu hankalin kowa ya tashi gashi lokaci se k'urewa yake. Cikin masu neman head ana jan Allah ya isa aharda Nazeefah da k'awarta. 


   Da shirun yayi yawa ne Afzal ya kira Amal don jin ko lafiya. 


  "Yaya an d'auke mun head d'ina" ta sanar dashi tana kuka. 


  "Kaman ya an d'auke? Tayaya?"


  "I don't know" tana fad'in haka ta katse wayar don yadda kukan yaci k'arfinta. Hawayenta Maamah ta shiga share mata tana bata hak'uri akan in shaa Allah za'a samu. Ummi ya kira next ya tambayeta meke faruwa. 


  "Wallahi head na Amal aka d'auke."


  "Tayaya Ummi? Shin baku ajiye mutum ya kula da kayakin nata bane?"


  "An sa wallahi har mata biyu ni kaina ban san yadda hakan ya faru ba."


  "Toh yanzu ya za'ayi?"


  "Akwai wani bridal head wrap na 'yar k'awata Umaima yanzu haka ta fice taje d'auko mata nata da ta sa a bikinta tace color d'in exactly iri d'aya da na Amal ne."


  "Please make sure she looks perfect Ummi and ki bata hak'uri ta daina kukan I love her."


  "Karka damu ka kwantar da hankalinka zan kula da komai" da haka sukayi sallama. Bayan 20 minutes Umaima ta iso da bridal head wrap nata sosai kuma ya shiga da kalan kayan Amal kaman yadda ta fad'a. Nan da nan makeup artist ta d'aura mata da ikon Allah kuma d'aurin ya mugun amsan Amal har ma fiye da yadda asalin head natan ze kar6eta, Nazeefah da Rumaysa haushi kaman ya kashesu. Sosai maroon color d'in ya kar6i skin na Amal se hoto ake tayi mata ta ko ina. Nan da nan aka shiga tafiya, motan ango na isowa su Maamah suka k'arisa da Amal ciki. Afzal na iya rantsewa be ta6a ganin kyakkyawan halitta kaman ta ba. 


  "My bride you look so beautiful" ya sanar da ita. 


  "Thank you Yaya, you're not looking bad yourself."


  "Is everything okay?" Kai ta gyad'a a hankali "I'm just nervous."


  "I've got you okay?" Yayi maganan had'e da sauk'e mata light kiss akan hannunta. K'aramar murmushi ta sakar masa ahaka har suka k'arasa wajen da za'ayi event d'in. Nazeefah sarai tasan an hana zuwa da yara ta kikki6i wata cousin nata mey shekara shida taje da ita. Ana cikin presentations progammes of event kafin a k'ariso na cutting cake Nazeefah ta tura cousin natan da taje ta ture table na cake d'in. Ana shagali kawai aka ji k'aran rushewan abu a k'asa, da table da cake d'in duk sun tarwatse. Hankalin kowa ya tashi a wajen barin ma na Amal da Afzal wannan wani irin musiba ce? Nan aka shiga tambayan kowa yashigo da yaro sede ba wanda keda masaniya game da hakan, yarinyar ma k'aramar munafuka ana tambayanta wa ya shigo da ita ta bushe ido wai babu mota kawai ta gani ta shigo. Securities kuwa koda aka tambayesu dalilin da yasa suka bari ta shigo se sukace su basu ga shigewarta ba k'ila tabi cikin manya ta 6ace acikin su kasancewar Nazeefah ta biya su kud'i ta rufe masu baki. 


   Kuka kawai Amal ta farayi wajen farko head nata aka d'auke yanzu kuma aka tarwatsar mata da wedding cake. Haka aka lalla6a aka kammala event d'in ba walwala tattare da kowa barin ma Ummi data sha aiki don tabbatar da cewa komi ya tafi dai-dai. Se hak'uri Afzal keta bawa Amal cikin motan amma ina ta gagara yin shiru. Ajikinsa  ya kwantar da ita har suka isa gidan nasu wanda se wajajen sha d'aya da rabi k'awayen Amal suka watse ya rage Afzal kad'ai da amaryarsa. 


  Kazan amarcinsu ya shigo dashi d'akin inda take zaune a tsakar gadon kanta a sunkuye se kuka take tayi ta ciki-ciki. Ledan ya bud'e yayi serving nata se anan ya tuna be ibo cups ba, dawowan da zeyi kawai ya tarar da Amal tana kuka shark'af-shark'af. Da hanzari ya nufi kanta yana tambayarta ko lafiya amma ina ko amsasa ta kasa banda kukan nata ma daya tsananta. 


  "Lily what's wrong? Wani abu ne?" Kansa ne ya mugun d'aurewa kode missing k'awayenta take ya tambayi kansa "Lily please stop crying" hak'uri ya shiga bata saidai ta gagara yin shirun. Daga bisani kawai ta fad'a jikinsa yayin da kukan nata ya tsananta, rungumeta yayi gam a jikinsa yana shafa bayanta yana mey fad'a mata kalamai masu kwantar da hankali. Sun kai tsawon minti talatin a haka, "Lily?" Ya kira sunanta lokacinda yaji tayi lamo a jikinsa. "Lily?" Duba fuskan ta da zeyi ya tarar har bacci ya d'auketa. 


  A hankali ya d'agata daga jikinsa had'e da mik'ar da ita akan gadon. Wayanta da ya kusan fad'i a k'asa ne yayi sauri ya tare kafin yace ze ajiye idonsa yaci karo da sak'on da ya nuna last Amal ta karanta wanda ya kasance daga unknown number. Har ya ajiye wayan watak ra'ayin tace masa ya karanta, kasancewar wayan nata ba password haka ya basa daman bud'ewa ya shiga karantawa kaman haka


  _My dearest Princess, today two souls of yours have turned into one, I want you to know that you two are the most beautiful couple I’ve ever seen. May your love grow stronger and stronger during your married life. May you always be together as one and never split apart no matter the difficulties you may face in your future life._


  _Yours Abdul, Xx_ 😘 


  Har cikin ransa shima yaji ba dad'i tabbas ya shiga tsakanin wannan masoya guda biyu, Allah sarki ashe akan Abdul take wannan kuka. Mayar da wayan yayi ya ajiye sannan ya rage kayan jikinsa ya fad'a bayi ya watsa ruwa. Da towel d'aure a kunkuminsa ya shiga wardrobe na Amal inda ya ciro mata d'aya daga cikin sabin kayakin baccinta. K'arisawa kan gadon yayi ya shiga tada ita sede ina baccin nata yayi nauyi daga k'arshe ya yanke shawaran barinta ta kwana da kayan kawai sede kuma yayi tunanin kayan zeyi nauyi da wuya idan zata ji dad'in bacci aciki. Outerwear d'in ya cire a hankali ya rage fitted gown na cikin, a hankali ya zuge zip d'in har k'asa har anan bata tashi ba cewa da yayi bari ya ja kayan k'asa mutumiyar ku ta tashi a firgice had'e da k'urma wani d'ankaren ihun daya kusa tunzurar da Afzal daga kan gadon. 


  "Shh! It's me Afzal calm down calm down" ya shiga ce mata a hankali yayinda take ta hak'i tana ja da baya. 


  "Ba wani abun zan miki ba kayanki nakeson in canza miki gani nayi kaman ya miki nauyi bazaki iya kwanciya da shi ba." Kanta tayi saurin kawarwa ganinsa da tayi ba kaya ajikinsa banda towel dake d'aure a kunkuminsa. 


  "Lily?" Ya kirata amma shiru tayi gun se neman kare jikinta take tana tattara wuyan rigar nata sama kasancewar ya zuge zip d'in k'asa se k'ok'arin zamewa yake. "Lily?" ya sake kiranta sede tak'i juyowa ta kallesa murmushi ya sakar gano wai kunyan ganin sa ba kaya take mik'ewa yayi ya nufi side nasa acikin wardrobe d'in ya zaro jallabiya d'aya ya sanya "Juyo to nasa kaya" ya sanar da ita bayan ya dawo ya zauna. A hankali ta kewayo da kallonta a garesa "Taho in tayaki cire kayan kisa wannan ko zaki watsa ruwa tukuna?"


  Kai ta kad'a a hankali. 


  "Toh ai ya kamata ki watsa ruwa tunda kin tashi Lily kiyi refreshing kanki you'll feel much better." Nan ma kan ta sake kad'awa "Okay na gane kunya na kikeji ko? Zan fita in baki waje ki shiga kiyi wankan idan kin shirya sekiyi mun magana okay?" Ganin bata da niyyan amsa sa ya mik'e ya fice. A hankali ta janyo wayanta ta shiga sak'on da Abdul ya tura mata had'e da sake karantawa yayinda wani kukan ke neman kauce mata. Typing reply tayi as;


   _Thank you so much Ya Abdul, Allah yabar zumunci._ sannan ta ajiye wayan ta mik'e da shakka-shakka ta shiga rage kayan jikinta gudun kar Afzal ya bankad'e k'ofar ya tarar da ita ba riga. 

  

    Acikin minti ashirin ta gama duk wani shafe-shafen da zatayi, kayan da Afzal ya d'auko matan ta d'aga tana duba. Yanzu wannan d'an iskan kayan yake tsammanin zata sa? Ai ba maraban wannan da babu komi na jikin mutum gani za ayi. Wardrobe natan ta nufa ta shiga neman wani na daban sede inaa duk kayakin bana kamala a ciki. Yau akeyinta meyasa Ummi za tayi mata hakane? Ko d'an me riga da wando babu se masu net guntaye iya cinya ai kuwa bacci da towel ya kamata. Hijabi ta sanya akan towel d'in ta koma kan gadon ta zauna. Wani d'an banzan yunwa ne ya soma damunta bata san lokacinda ta hau kan kazar data gani k'ulle cikin ledan ba ta shiga ci ana cikin haka Afzal daya ji shiru yace bari ya lek'o, bud'e k'ofan da zeyi suka had'a ido hud'u da Amal. Kunya ta jiyo tamkar ta nitse k'asa, da sauri ta kawar da kanta ta shiga ture ledan gefe. Murmusawa yayi ya k'araso ya zauna kusa da ita. "Ci abinki kinji? Dama naki ne" Juice d'in yaja ya tsiyaye mata a cup tare da tura mata gabanta. A hankali ta shiga ci bayan dan ta gama ta kwankwad'e juice d'in akai. 


  "Kin k'oshi bazaki k'ara ba?" A hankali ta gyad'a kanta "Thank you" ta furta. 


  "Don't mention kina buk'atan wani abu?" Yadda kuka san kurma haka ta cigaba da amsa tambayoyinsa da jiki. 


  "Lets sleep then ko baki fad'a ba nasan a gaje kike." Yana tu6e jallayabiyan nasa Amal ta shiga kare fuskanta oh! Shi kam ya had'u da aiki. Daga chan k'arshen gadon ta ja pillonta ta kwanta, had'e da juya masa baya. Da mamaki ya tsaya kallonta bade da hijabin take shirin kwanciya ba? "Lily?" 


  "Uhmm?" Ta amsa ba tare da ta juya ta kallesa ba, shi kam wai baya jin kunya ne yake tsayuwa akan gajeren wando zalla a gabanta? Ta tambayi kanta, ita kam kunya ma baze barta ta kallesa ba. 


  "Da hijabin zaki kwanta?"


  "Uhmm" ta amsa. Takowa yayi izuwa gabanta ya zauna nan ta kulle idanta gam. Hannu yasa ya gwada d'aga hijabin nata da mamaki ya tarar da towel k'ark'ashi. Tirk'ashi! 


  "Lily!" Yayi exclaiming, bud'e idon da zatayi taga yana rik'e da k'asan hijabinta nata da hanzari ta k'wace ta shiga rufe jikinta. 


  "Wai mey haka? Da towel d'in zaki kwanta?"


  "Uhmm" ta amsa. 


  "Dalili?" Wai har ma dalili yake tambayarta? Shin bega kalan kayan bane ko a haka yake tsammanin zata sa? "Kefa Lily!"


  "Yaya baka ga kayan bane" se anan ta bud'e baki ta amsa idanta a rufe har yanzu. 


  "Meya samesa?" Ya buk'ata. 


  "Bazan iya sawa ba" ta amsa a takaice. Kayan ya d'ago daga kan side drawer yana kalla, besan lokacin da dariya ya kauce masa ba. "God help me" ya furta a hankali. Anya kuwa ze iya da kunyan nan nata? Yaga irin kayan da Nazeefah ke kwanciya da su kenan wasun ma wannan yafi su kamala. 

  Ido d'aya ta bud'e tana kallonsa. 


  "Mey anan d'in da bazaki iya sawa ba Lily? Hungo tashi kisa."


  "Ni gaskiya bazan saba kabarni haka kawai I'm good seda safe."


  "A ina aka ta6a kwanciya da towel ki tashi kisa mu kwanta bacci nakeji."


  "Toh Yaya na hanaka kwanciya ne?" 

  

  "So kike muyi fad'a ko?" Yayi maganan had'e da komawa gefenta ya zauna "Ko kisa kokuma in sa miki na k'arfi kinsan ba Mami bale kice zakiyi ihu ta taimakeki."


  "A'a Yaya dan Allah kayi hak'uri karka mun haka."


  "Toh amsa kisa."


  "Yaya bazan iya sawa ba dan Allah kayi hak'uri."


  "Fa bazan barki ki kwanta da towel ba."


  "Kayi hak'uri zuwa gobe zanje kasuwa in sai kayan baccin masu riga da wando se in fara sawa I promise bazan sake kwanciya da towel ba amma ka barni na yau d'in." Dariya sosai ta basa wai kam da abinda takeyi d'innan idan da kuma cewa yayi su raya first night kaman yadda kowasu ma'auratan keyi fa? Ashe seta tara masa jama'a. Ganin fa bata da shirin sanya kayan kawai ya damk'o hannunta. Wai d'an karen ihu tasa seda ya tsaya toshe kunnensa. Shin wani irin laushi hannun nata keda sekace auduga. 


  Kuka ta shiga yi yayinda yake k'ok'arin raba ta da hijabin nata. 


   "Zan sa wallahi zan sa da kaina dan Allah karka cire min hijabin Wallahi towel d'in ya warware kayi hak'uri" nan ma dariya ta basa sosai amma ya bone se kokowan cire hijabin yake. Kuka Amal ke tsakaninta da Allah tana rantsuwa akan ya saketa zata sa da kanta. Seda ya bata wuya sannan ya saketa "That's my Lily sanya toh da hannunki ina kallonki ko zaki shiga bathroom?"


  Kai ta gyad'a a kid'me. 


  "Je ki sanya toh ina jiranki." Batayi musu ba ta mik'e har tana neman cin tuntu6e ta nufi bayin. Hijabin nata ta kwaye ta ajiye a gefe sannan ta d'ago kayan ta shiga neman ta inda zata sa. Chan ta samo wuyar rigar ta sanya, gaban mirror ta tsaya tana kallon kanta surrata kap ba abinda be nuna ba, amma ko se Allah ya d'ibe ma baturen daya d'inka wannan kaya albarka. Yanzu a haka ne Afzal yake son taje ta samesa su kwanta sekace wata sabuwar karuwa? Uhn uhn kam gaskiya baza ayi haka da ita ba.  Ina ma ace da brazier a ciki da d'an sauk'i amma haka ba komai gaskiya da sake. Tunanin ya zata fita ta d'auko bra ta sanya ta soma ana cikin haka kawai taji Afzal ya wangale mata k'ofar ba notice. Ashe bata sa key ba, wani irin d'ankaran ihu ta k'urma had'e da juya mai bayanta yayinda ta shiga kare k'irjinta tana kakkarwa. 






RANA D'AYA!

#RD


Love... King Miemiebee👄✨

[13/08, 09:34] ‪+234 907 483 8352‬: 🎀🎀🎀                 🎀🎀🎀

                🎀❣🎀

                   ❣❣


  💦💦                      🍃🍃🍃          

           *RANA D'AYA!*

  💦💦                      🍃🍃🍃

  July, 2018

 beeenovels.blogspot.com


     _Written by Miemiebee👄_



   *PAGE 2⃣7⃣*



    

   Murmusawa ya tsaya yi yayinda yake k'are wa surar jikinta kallo, lallai Allah yayi halitta anan gata 'yar siririya amma fad'i gareta ta k'asa. Na d'an lokaci ya karanci tana da aniyar janye hijabin nata ne dake rataye jikin sink ta sanya, kafin ta aikace hakan yasa hannu ya janye. 


  Wai meyasa Yaya yake mata haka ne? A hankali take jin footsteps nasa suna dosoto, har6awa zuciyanta ya shiga yi yayinda k'afafunta suka shiga yin kakkarwa na sosai. A dai-dai saitin bayanta ya tsaya, hannu ya aza a kan bayanta a hankali yana tafiya sama, idanunta ta rufe gam yayinda wani irin sparks suka soma bin jikinta. Ji tayi ya tsaya chak se kuma taji yana shafa mata gashin kai, ribbon nata data nannad'e gashinta ajiki taji ya kama yana k'ok'arin sincewa. Kafin tayi wata k'wak'k'warar motsi taji ya since nan gashin nata data nannad'e jiki ya shiga warwaruwa. Da mamaki ya tsaya yana kallon irin tsawon gashin nata, har tsakiyan bayanta ya sauk'a yana lilo lub-lub yana shek'i. Har anan Amal bata juya ta kallesa ba se faman kakkarwa take, a hankali taji ya shiga takawa kuma, idanta ta rufe gam lokacinda ta gansa tsaye a gabanta, k'irjinta ta shiga karewa fiye dana d'azu yayinda takeji kaman tasa kuka dan kunya. Yafi minti d'aya tsaye a gabanta yana kallonta yana mey mamakin how fragile and delicate she is, hannu ya d'aga a hankali ya aza akan kafad'arta yana bin hannunta da wani irin shafa, se mamakin laushin jiki irin nata yake sekace auduga. Na sosai jikin Amal ya d'au wuta da irin abinda yakeyi mata. Ganin bata da niyyan bud'e ido ta kallesa ya kirata cikin sanyayyar murya. 


  "Lily?" Shiru tamai "Lily k-" katse sa tayi ta hanyan rungumarsa, hannayenta ta zagaye gagam ta rik'esa a jikinta yadda ko kykkyawan motsi baze iyayi ba yayinda ta datse idanunta. 


  "Goodness Lily" ya kira sunanta yana k'ok'arin raba jikin nasu sede ina ya kasa dan wani irin damk'an da tayi masa. 

   "Lily I can't even breathe let me go" yadda kuka san da iska yake magana haka ta mayar dashi ta kuma k'i sakin nasa ita a dole bata son ya kalle mata surar jiki kuma hakan ne kawai take ganin mafita. Ganin fa bata da niyyan sakesa ya shiga jasu waje a hankali, k'ank'amewa tayi a jikinsa har suka k'arasa izuwa bakin gadon nasu. 


  "Toh sakeni haka ki kwanta" nan ma kota motsa. "Lily da ke fa nake magana" ba suratan da beyi ba amma tak'i sakesa wane gum haka ta manne mai ajiki, haka ba yadda ya iya ya shiga sauk'a k'asa da ita har suka juye akan gadon sede tak'i sake sa har yanzun. "Lily yi hak'uri ki sakeni in kashe mana wutan kinji?" nan ma shiru duk kalan suratan da yatayi hakan besa ta sakesa ba haka a tak'ure manne da juna suka kwanta har bacci 6arawo ya d'auketa. Bayan da Afzal ya tabbata baccin nata yayi nauyi ya shiga raba ta daga jikinsa sede ina tak'i barin hakan se faman sake shigewa jikinsa take. Wai acikin baccin ma? Ya tambayi kansa. Haka sukayi baccin wahala ranan barin ma Afzal da ko nishi me kyau baya iya yi. 


  Asuban fari alarm nasa ya shiga ringing, da ya ce ze motsa dan kashewa se Amal ta sake kankamesa haka alarm d'in ya tayi har izuwa lokacinda ya tayar da ita daga baccin itama. 

  

  "Yi hak'uri ki sakeni muyi niyyan sallah kinji?" Dan albarkacin sallah kawai ta sakesa wanda da wuri ta juya mai baya ta shiga kare k'irjinta da pillow murmusawa yayi ya mik'e had'e da mik'ar da k'asusuwansa da suka murmurk'ushe, hijabin nata ya ja daga gefe ya wulla mata "Hungo sa abinki" ya sanar da ita chan ciki-ciki yace, "A hankali zaki sake da ni" bata 6ata lokaci ba ta amsa ta sanya murmushi kawai yayi ya k'arisa bayin bayan ya watsa ruwa yayi alwala ya buk'aceta da ta tashi tayi niyya itama. Yana kallonta ta shige cikin bayin da hijabin nata kafin ta fito har ya shimfid'a musu sallaya ya sanya jallabiyansa shima. Wardrobe nata ta k'arasa ta d'au zani d'aya ta d'aura sannan ya jasu sallan bayan sun idar sun kammala Azhkar nasu ta gaishesa a hankali cikin siririyar muryarta. 


  "Good morning Yaya."


  "Ba suna na ba kenan don haka bazan amsa ba" ya ce mata da mamaki ta d'ago kai tana kallonsa cike da neman k'arin bayani. 


  "Eh kin jini da kyau ni suna na ba Yaya ba."


  "Toh mey sunan naka?"


  "Afzal mana."


 "Amma ai kasan ba na kiranka da sunan ko?"


  "Yes KITTEN."


  "Toh ya kakeso inyi?"


  "Look for a name and start calling me with it, I'm your husband now not yaya anymore."


  "Amma ai duk d'aya ne Yaya."


  "Toh ni bana so."


  "Toh seka kawo sunan da kakeso."


  "Ni zan kawo ko ke zaki nema?"


   "A ina zan neman? Allah ban sani ba yi hak'uri ka amsa kaji?"


  "Nak'i se an min sabon suna."


 "Kayi hak'uri ka amsa na yau d'in zan nemo wani sunan in baka amma ba yanzu ba."


  "Se yaushe?"


  "Yaya ban sani ba nima."


 "Aww baki ma sani ba? Toh shikenan har se idan kin samo mun sabon suna bazan sake amsa gaisuwanki ba."


  "Yaya-"


  "Shhh na soke sunan chan so good morning my adorable kitten."


  "Kitten?" Ta tambayesa had'e da kafa masa fararen idanunta.


  "Yes Amal."


  "Why Kitten?"


  "You wanna know why?" Kai ta gyad'a a hankali. 


 "Come here sena fad'a miki."


  "A'a bar shi kawai."


  "Ba wani abin zan miki ba Kitten don't you trust me?"


  "I do Yaya."


  "Nifa na ce miki suna na ba Yaya ba."


  "Toh kayi hak'uri mana ka bari ko zuwa gobe idan nayi tunani ai kaima seda kayi tunani kafin ka samo Kitten d'in."


  "Ko kad'an Amal, kallonki zanyi sau d'aya sunaye sama da d'ari su taho min akai because you're just perfect in my every situation." Murmushi ta sakar masa "So matso kinji? Matso in fad'a miki sirrin dake bayan sunan naki."


  Kafad'a ta buga "Trust me ba abinda zan miki."


  "Dagaske?"


  "Wallahi" seda taji ya rantse ta amince, a hankali ta k'arasa kusa dashi hannunsa ya bud'e mata da nufin ta shiga ciki, seda ta kallesa sau d'aya again sannan ta mik'a ta kwantar da kanta a k'irjin nasa, hannayensa ya zagaye a bayanta yana mey sake matso da ita kusa dashi sannan yayi placing mata light kiss a kai yayinda yake perceiving k'amshin turaren dake tashi daga jikinta. 


  "So kina son kiji meyasa nake ce miki Kitten?" Kai ta gyad'a hankali. 


  "Kinsan mage (kulya) ba?"


  "Uhumm" ta gyad'a kai tana sauraronsa. 


  "Kina son halittar?"


  "Gaskiya ni tsoronsu nake."


  "K'ananan su fah?"

  

  "Awwn I love those ones."


  "How do they look?"


  "Cute and adorable, koda yaushe na ga d'aya sena ji kwad'ayin in d'auka."


  "That's exactly how you're to me Amal or even more, you're so cute and adorable, soft, delicate and fragile and anytime I see you kawai se inji ina son in rik'e ki a hannu without letting you go."


  "You too HABIB ALBY" ta amsa. 


  "Iyyehh say it again" kunya sosai taji ta sake lumewa jikinsa tana kare fuskarta. 


  "Kitten..." k'ok'arin d'agota ya shiga yi daga jikinsa amma ya kasa dan yadda ta k'ank'amesa ba k'aramin burgesa wannan kunyan nata yake ba. "I love you so much My Kitten and wannan kunyan naki, it is the most expensive jewelry you'll ever wear, never change who you're not even for me kinji? I want you to remain true to yourself, be the Amal I've fell in love you okay?"


  "Thank you Ya- Habib alby" tayi sauri ta gyara. Light kiss ya sauk'e mata a goshi. "Don't mention Kitten" Haka suka cigaba da zama wajen suna shak'ar k'amshin jikin juna yayinda zuciyoyinsu ke bugu wa juna har bacci yayi awon gaba da su. Wajajen takwas Afzal ya farka d'agata yayi a hankali ya mayar da ita kan gadon had'e da cire mata hijabin nata da kuma zanin da take d'aure dashi ya bar mata kayan baccin nata kad'ai. Haka kawai ya tsinci kansa cikin annashuwa da yake k'arewa surar jikinta kallo. Rungumarta yayi tsam a jikinsa wane mutum na shirin gudu masa da ita, ahaka ne har ya komma bacci. 


   Wajajen sha d'aya Amal ta tashi a hankali ta shiga bud'e idanunta har ta sauk'esu akan Afzal dake ta shar6an bacci a gefen ta. Mik'ewan da tace zatayi taji hannunsa rik'e da jikinta gam ta6a kanta da tayi kuwa taji ba hijabin ta ba kuma zani har yaushe ya tu6eta bata ji sa ba? Yanzu ya kalla mata jiki kenan? Kallon kanta tayi tana mey jin takaicin hakan. Duk yadda taso fita daga rik'on da yayi mata ta kasa dan haka kawai ta hak'ura. Kai ta d'ago ta shiga kallonsa tana mey k'arewa kyakkyawan halittarsa kalo. Tabbas Yaya kyakkyawa ne ta fad'a a ranta. Silky gashin girarsa dake nan a kwance luf ta tsaya tana kalla daga bisani ta d'aga hannunta a hankali ta aza akai tana shafawa, daga haka ta wuce izuwa dogayen eyelashes nasa da suke nan sekace na mace, daga nan ta koma kan hancinsa se kuma tabi sajen sa haka tayita shafa kowani inchi a fuskansa tana tafiya har ta sauk'o zuwa kan lips nasa da sauri ta cire hannunta gudun kar ta wuce gona da iri. Sekace wacce aljanu suka shigeta kawai taji tana son ta6a lips nasa, a hankali ta mayar da hannunta ta aza a kai, shafawa ta shigayi da zaran ya motsa seta cire hannun nata haka ta cigaba da yi har seda ta farkar da shi. Da sauri ta sauk'e hannunta gudun karya ganta saidai ina tuni ya ganta. Cusa kanta tayi a jikinsa tana neman gun la6ewa yayinda wani irin kunya ya kamata wane ta tone k'asa ta shiga. Shin meya kaita?


  Murmushi ya sauk'e ashe de ba mafarki yake ba dagaske ne tun d'azu anata shafa mishi baki. "Kitten good morning" ya fad'a yana sauk'e mata peck cikin gashinta me uban yawa yayinda k'amshin shamponsa ya buga mai ganci. Chan ciki-ciki yaji ta amsa "Good morning Yaya."


  "Nak'i in amsa."


  "Good morning Habib Alby."


  "Masha Allah toh ya kika daina? Actually I was enjoying your touch kitten." 


  "Nifa ban ta6a ka ba" ta k'aryatasa.


  "Nide nasan ba mafarki nake ba" shiru tayi ta bata sake cewa komai ba "Tashi toh let's freshen up and have breakfast." A hankali ta zame daga jikinsa sede yayi sauri ya tareta kafin ta gama fita "Baki fad'a mun mey ma'anan Habib Alby ba Kitten I wanna know."


  "Yaya so kake kace baka jin larabci?"


  "Eh bana ji tell me" yay mata k'arya so yake yaji fassaran daga bakinta.

  

  "Ban yarda ba."


  "Nide tell me."


  "It means the love of my heart (abun alfaharin zuciyata)"


  "Masha Allah I'm totally in love with the name zaki fara shiga ko sena fito?"


  "Kaje seka fito."


  "Alright" mik'ewa yayi ya nufi bayin in less than 10 minutes se gashi ya fito d'aure da towel a kunkuminsa kaman yadda ya saba. Idanunsu na had'ewa da Amal dake kallonsa ta shiga kare fuskarta cike da kunya, murmusawa yayi "You're next" ya sanar da ita. Tunanin ya zata fara tafiya acikin d'akin sanye da wannan kaya take, juyawa tayi in search of hijabi ko zaninta sede babu anan kusa Afzal daya gano hakan seya k'arasa ya d'auko mata  da kansa. Amsa tayi cike da kunya had'e da yi mai godiya. Hijabin ta sanya ta rik'e towel d'in a hannu sannan ta mik'e ta shiga bayin. Kafin ta fito har Afzal ya shirya tsaf d'akin se k'amshin turaren jikinsa yake, yellow T shirt yasa wanda ya bayyana well defined abs nasa da black three quarter wando sosai yayi kyau barin ma yadda skin nasa ke wani glowing. 


  "Kallon nan beyi yawa ba Kitten?" Kai tayi saurin kawarwa cike da kunya. "Kode nayi kyau ne?" Kai ta gyad'a masa a hankali "Thank you."


  "Youre welcome ta amsa ciki-ciki tana gyara fuskan hijabinta. 


  "Bara inyi excusing naki ki shirya in kin gama sekiyi mun magana kinji?" Kai ta gyad'a masa, nan ya mik'e ya fice ba k'aramin dad'i taji ba daman tunanin yadda zata fara sa kaya a gaban idonsa take se gashi yace ze bar mata d'akin ma gabad'aya. 


   Ta fannin Afzal kuwa gano irin tsananin kunyan da take dashi yasa yayi tunanin binta a hankali, baze yi rushing nata ba, a shirye yake da ya jirata har izuwa lokacinda zata fara sakewa dashi, so yake ta koyi sonsa da kanta bawai ya sata na dole ba inde akan Amal ne toh he is willing to wait for forever this's just how much he loves her. Nan da nan ta ciro kayan shafe-shafenta dana k'amshi ta shiga shafawa, light makeup tayi applying daga powder, se jan baki se kajal a ido amma wani irin d'ankaren kyau da tayi, barin ma yadda maroon jan bakin ya amshe shape na lips nata. Wardrobe nata ta nufa ta ciro d'aya daga cikin sabin d'inkunanta ta sanya. Sosai d'inkin ya zauna a jikinta daram, gaban mirron ta koma ta zauna ta shiga taje sumarta. Sauk'an knock taji a bakin k'ofa "Bismillah" tace da mey shi. Afzal taga ya lek'o. 


  "Zan iya shigowa ko in koma?"


  Dariya ya bata dan haka ta murmusa "Kai da gidanka kuma Yaya" gira ya had'e take nan take ta gyara kanta "I mean Habib Alby ka shigo." K'arisawa ciki yayi ya nufi gaban mirron inda take zaune, hannunta yayi saurin rik'owa ganin ta d'au ribbon tana shirin kama gashinta. 


  "Mey zakiyi?"


  "Zan kama kaina ne."


  "Meyasa?"


  "Haka nakeyi kullum."


  "Bana so."


  "Eh?" Ta kewayo cike da rashin fahimta tana kallonsa. 


  "Kibari haka kinfi kyau."


 "But Yay- Habib Alby" ta gyara da sauri. 


  "Trust me kinfi kyau haka" yayi maganan yana amshe ribbon d'in daga hannunta. Comb dake ajiye akan mirron ya d'aga ya shiga taje mata sumar nata ya kwantar mata a baya. "See kinfi kyau haka muddin kina gida bana son kina kama gashin ki barshi haka kinji Kitten?" Kai ta gyad'a masa a hankali. "Muje mu karya ko?" Nan ma kan ta kuma gyad'awa had'e da mik'ewa. "You look beautiful Kitten" ya sanar da ita bayan ta mik'en. 


 "Thank you Ya- Habib Alby" tayi sauri ta gyara, hannu yasa ya jawo ta jikinsa sannan ya d'ago fuskanta da yatsarsa ta yadda take kallon cikin idanunsa sede da sauri ta sake sauk'ar da idan nata. 


  "Hold on! Ina aka kaimun gashin girarki da nake mutuwan so d'innan?" Tun d'azun yake kallon fuskanta se gani yake wani iri ashe gashin girarta ne babu. 


  "Ba makeup artist da ka d'auko d'in bane bata sanar dani ba kawai ta kama ta aske mun gira" ta amsa tana turo bakinta. 


  "Subhanallah bata tambayeki ba?"


  "Bata tambaya ba nikuma ban san me take ba kawai duba mirron da zanyi naga duk ta kwashe."


  "Sorry Kitten."


  "Its not your fault Yaya."


  "Dena fushi you're still beautiful even like this."


  "Thank you, muje mu karya yunwa nakeji."


  "Alright amma kafin nan tsaya in d'aukeki hoto."


  "Ya- I mean Habib Alby bana so."


  "Kitten bade kunya na kike ba? Nine fa Yaya yau na fara d'aukanki hoto ne?"


  "Ba kace kai ba Yaya na bane yanzu ni kunyanka nakeji."


  "Naji nide ki tsaya."


  "Ni o'o" ta amsa tana buga kafad'arta. 


  "Sena miki kuka tukun?" 


  "Toh in ka d'auke ni nima zan d'aukeka ka yarda?"


  "Ni bana son hoto ai kema kin sani."


  "Toh ni d'in nace ma ina so ne."


  "Kitten ni kike ma rashin kunya ko? Ba damuwa dama na san bakiya sona" yana fad'in haka ya juya wai shi a dole yayi fushi. Hannunsa tayi saurin rik'owa chak ya tsaya had'e da kewayowa yana kallon hannun nata dake rik'e da nasa. Da sauri ta sake "I'm sorry" ta furta. 


  "Ni bana buk'atar hak'urinki let's go eat."


 "Toh ka tsaya ka d'aukenin."


  "Nayi fushi bana so ba rowan kanki kike mun ba."


  "Yaya mana."


  "Kuma ni suna na ba Yaya ba."


  "Toh yi hak'uri Habib Alby gashi na tsaya ka d'aukenin" ba k'aramin dad'i yaji ba amma ya moze "Ni bana so" gabansa ta shawo da sauri "I'm sorry kaji?" Wayansa ya zaro daga aljihunsa ya shiga d'aukanta ba shiri. 


  "Toh Yaya ka tsaya mana inyi posing tukuna" tana mai magana amma se d'aukanta yake kawai ta ko ina. 


  "Masha Allah am sure zan samu masu kyau sama da ashirin anan."


  "Toh saura kai."


  "Ni bana hoto."


  "Yaya mana!"


  "Nak'i."


  "Haba Habib Alby tsaya kaji?" Da wayo cike da dabara ta d'auko wayanta kan mirror ta shiga camera kaman yadda yayita d'aukanta papparazi ta ko ina ita ma hakan ta rama daga k'arshe seda ya k'wace wayar. "Se kin kashe mun ido tukuna." Tana dariya tace, "Yi hak'uri toh ka tsaya muyi selfie yanzu" beyi gardama ba suka sha hotuna acikin wayanta da nasa. Kawai seta tuna da Ya Abdul. Lokaci d'aya yanayinta ya canza, Afzal ya nemi walwalan ta ya rasa. 


  "Kitten?" Ya kirata a hankali. "Kitten are you crying?" Cewa da tayi bari ta amsa sa kawai kukan yaci k'arfinta, wani irin masifaffen kuka ta 6arke da, a kid'ime Afzal ya janyota jikinsa ya rungumeta yana shafa bayanta a hankali yana mey bata hak'uri. 


  "Kitten I'm so sorry idan wani abin na fad'a ya 6ata miki rai please kibar kukan haka."


  "Yaya ba kai bane" ta sanar dashi cikin tsananin kuka a hankali ya d'agota daga jikinsa. "Waye ne toh?" Ya tambaya yana share mata hawayen. 


  Kai zalla ta iya ta kad'a masa. 


  "Talk to me kitten I'm here please."


  "I'm sorry but I can't" ta sanar da shi. 


  "Abdul ne? Is this about him?" Ba k'aramin k'una zuciyarsa ta shiga yi masa ba na wannan tambaya da yayi mata. Har yaushe Amal tasa zata na kuka akan wani na miji haka? Yasan bayida right da ze hanata amma zuciyarsa bazata iya d'auka ba, yana tsananin kishinta. 


  "Yaya I'm sorry please forgive me I just can't help it, I miss Ya Abdul I terribly miss him I'm so sorry please ka yafemun." Na matuk'a ta basa tausayi rungumarta ya sakeyi a hankali. 


  "It's okay Kitten, na fahimci halin da kike ciki, ki dena bani hak'uri kinji?" A hankali yaji hannunta a bayansa tana hugging nasa back. 


  "I'm so sorry" sun d'au tsawon lokaci a haka sannan ya d'agota daga jikinsa tare da mik'awa yana kissing tears nata away. "Stop crying okay? I'm here and I love you."


  "Thank you Habib Alby."


  "Muje muci abinci I'm starving" da hannunta rik'e cikin nasa suka k'arisa dining d'in. 


  "Waya kawo kulolin nan?"  ta tambayesa "Na d'au fa zanyi mana girki ne."


  "Har kina tunanin zan bar ki kiyi girki Kitten? 'Yar uwarki ce ta kawo mana." 


  "Nazeefah?" Kai ya gyad'a mata da nufin eh "Allah sarki ita da kanta?"


  "A'a ta turo me gadinta ne."


  "Ayya zan kirata ko inyi mata godiya."


  "Let's eat first" ya bari tayi serving nasu ma k'i yayi shi da kansa ya zuba musu a plate d'ay bayan nan ya barta taci wai sam shi ze bata. Rigima suka 6arkr da, ita Amal tace sam ita zata ci da kanta shiko yace shi ze bata, da k'yar ya iya ya shawo kanta ta amince. Akan cinyarsa ya ajiye ta idan yaci ya bata haka har suka k'oshi sannan ta kira Nazeefah suka gaisa tayi mata godiya nan Afzal yace shima ta basa. 


  "Ya Rouhi" ta soma da cewa. 


  "Na'am Rabba'atul Bait ya kike?"


  "Lafiya k'alau kai fa?"

  

  "Alhamdulillah thank you for the breakfast."


  "Don't mention Ya Rouhi anything for you amaryar mu na kula mun da kai ko?"


  "Ai nace mata idan bata kula dani ba ma kince zaki kawo mata hukuma."


  "Ai kuwa I'm missing you alot ko bacci na kasa yi jiya, I miss your arms around me."


  Juyowa yayi ya kalli Amal yana me fatan Allah yasa bataji kalaman Nazeefah ba, se gani yayi tana harkan gabanta nema tana watsa da yatsunta. "I miss you too nida Amal zamu shigo miki karki damu."


 "Toh shikenan sekunzo."


  "Yauwa take care."


  "I love you."


  "I love you too" da haka sukayi sallama. 


  "Sharri zaka yi mun gun Rabba'atul Bait taka ko?"


  "Cewa tayi idan baki kula dani in fad'a mata ta turo miki hukuma."


  "Zaku taru kumin taron dangi ko? Ba matsala."


  "Ai amarya bata laifi Kitten" yayi maganan tare da had'a yatsotsinsu gu d'aya yana wasa da su. 


  "Kitten?"


  "Na'am Yay- Habib Alby" tayi sauri ta gyara kanta. 


  "Do you love me?"


  "Yaya..."


  "Just answer me Kitten, do you love me?" Shiru tayi ta kasa cewa komai "Feel free to tell me duk abinda ke cikin ranki kinji? You mustn't have to lie idan bakiya sona its simple just tell me."


   "Habib Albi ina son ka sani cewa ita fa zuciya tana son duk me kyautata mata ne ko kana tsammanin Allah kansa ze barni ne idan na bud'i baki nace bana sonka? Ni kaina bazan ta6a yafe wa kaina ba idan nayi hakan, abubuwan da kayi mun aduniya bayan Allah da mahaifana ba wanda ya kwatanta yimun irinsu. Banida kaman ka Habib Alby koda hankalina yana tare da Ya Abdul kasani zuciyata taka ce, sabida ba wanda ya cancanceta kaman ka bana son kana tada hankalinka a kaina bana son ciwon ka ta tashi bana son abinda ze ta6a mun lafiyarka Habib Albi."


  "Does this mean you love me?" Kai ta gyad'a masa a hankali. "Then say it to me Kitten you really don't know for how long I've been waiting for this day, I really need to hear these words please tell me" murmushi ta sakar masa sannan tace, "I love you Ya Afzal my Habib Albi, banida kaman ka." Afzal baze iya kwatanta irin dad'i da farin cikin daya ziyarci zuciyansa ba. Ba k'aramin nishad'i kalamun nata suka sanya sa ba all he knows is that he's never felt this happy. 


  "Please say it again Kitten tell me you love me again."


  "I love you again and again and again Habib Albi and I'll choose you over and over and over again even if I where to be given another life." Rungumarta yayi yana mey zagaye hannayensa a bayanta yayinda ta kwantar da kanta jikinsa tana hugging him back. 


  "Thank you so much Kitten yau kin cika mun burina, koda mutuwa naui yau zan mutu da murmushi kwance a fuskana saboda kin sanar dani mafi daddad'in kalamun da kunnuwana suka jima suna kwad'ayin son ji. I want you to know that I'll do everything in my power to make you smile and happy, I'll take care of you and adore you like the Queen that you're, thank you so much Allah yayi miki albarka."


  "Ameen Habib Albi don't mention" a hankali ya saketa tare da zaro wani k'aramar pack daga aljihunsa. Wata had'ad'd'iyar zobe ce aciki wanda ko ba a tambaya ba ansan me tsada ce don wani shek'in da takeyi. 6allo ta yayi a hankali daga cikin gidan nata tare da d'ago hannun Amal. 


  "I want you to have this Kitten."


  "Yaya isn't this expensive? Bana son kana kashe kud'i extravagantly akai na."


  "Kitten you're worth every diamond, you're worth morethan a gem so dan Allah ki dena damuwa idan ban 6ata kiba, matar wani zan 6ata?" Suul zoben ya wuce ring fingarta ba kuma k'aramin amsarta yayi ba. 


  "It's so beautiful Ya- Habib Albi" ta gyara kanta da wuri. 

 

  "Sede bekai rabin kyan da Allah yayi miki ba Kitten so do you love it?"


  "Absolutely" ta amsa tana mai murmushi yayinda ta kasa daina kallon zoben. 


  "Then do I get an appreciation kiss?(Sunbatan godiya)"


  "Yaya..." kunyansa ta shiga ji tana sauk'ar da idanunta a k'asa. 


  "I don't mean on the lips nasan ko sama da k'asa zan had'a ba iya kissing lips d'ina zakiyi ba, a kumatu ma ya isheni" shiru tayi ta kasa cewa komi wajen. "Please Kitten" nan ma shiru. "Kitten idan kina haka har zuwa tsawon yaushe zaki fara sakewa dani ko kin manta ni mijinki ne?" Kai ta kad'a masa a hankali. 


  "Then peck me I'm waiting."


  "Yaya zan d'auraye plate da muka ci abincin akai" ta sanar da shi wai a dole zatayi masa waya. Hannunta ya rik'o cikin nasa "Kiss me first ko kuwa bazan sake kiba."


  "Yaya..." 

 

  "Shhh! Anan kawai" yayi mata nuni da kumatun damansa sede ina bata jin zata iya. 

  "Alright let's do it this way, zan rufe ido na, I'm waiting" kai ta d'ago tana kallonsa "Allah baka rufe me kyau ba nasan kana gani na."


  "I'm serious I can't watch you." Hannu ta d'aga tana waving a fuskan nasa don tabbatar da ko ya rufe d'in dagaske.  A hankali ta shiga matso da fuskanta kusa da nasa dab zata sunbaci kumatun nasa kenan seya matsa kad'an da gan-gana, hakan yasa bakinta ya sauk'a akan nasa. Sandarewa tayi zaune a wajen, sun kai seconds goma a haka sannan daga bisani taja da baya. Mik'ewa tayi take ta ruga d'akinsu a guje, murmushi Afzal ya sa had'e da lasan lips nasan. Oh! Wannan kunya nata seya cire mata shi da ikon Allah.





RANA D'AYA!

#RD


Love... king Miemiebee👄✨

[13/08, 09:35] ‪+234 907 483 8352‬: 🎀🎀🎀                 🎀🎀🎀

                🎀❣🎀

                   ❣❣


  💦💦                      🍃🍃🍃          

           *RANA D'AYA!*

  💦💦                      🍃🍃🍃

  July, 2018

 beeenovels.blogspot.com


     _Written by Miemiebee👄_



   *PAGE 2⃣8⃣*



   

   Wayansa ya d'ago yayi texting nata  _I'll be going out, I won't take long_ bayan minti d'aya sega reply nata _Allah kare seka dawo._


 Wani sak'on ya sake tura mata,

  _Won't you miss me?_ murmusawa tayi ta sake tura masa reply _Ko kad'an ma._ 


  Dariya ya saki ya sake texting nata _😫😫😭._ da hanzari tayi replying nasa _I'm kidding kar kayi kuka, I'll miss you 😘_


  Yana murmushi ya tura mata _I'll miss you too take care Xx 😘_  seda ta tabbata ya fita sannan ta fito parlourn, d'akunan ta bi each tana kalla dama chan ranan da suka taho da Afzal bata samu dama tayi kallo kaman yadda takeso ba gudun karya cemata 'yar k'auye ta cika kalle-kalle. Bayan ta dawo ta zauna a parlour so take ta kunna TV'n amma kuma gudun karta rikitar da wani abun ta fasa dan haka ta zauna kawai. Wayan ta da take rik'e da shi ne ya shiga ruri dubawanda da zatayi taga Maamah ke kira da hanzari ta d'aga. 


  "Mata agidan Ya Afzal" ta soma da cewa. 


  "Uhmm ya kike?"


  "Ai baki amsa ba nace mata a gida Ya Afzal."


  "Kin fara ko?"


  "Ko yana kusa ne bakison ki d'aga murya ya jiki?"


  "Seki kwantar da bokatin hankalinki Yaya baima gida ya fita."


  "Ashe shiyasa aka d'au wayana nasan da yana nan da bazaki d'auka ba."


  "Haka dey kikace."


  "Toh ya kike?"


  "Lafiya k'alau."


  "K'alau k'alau de?"


  "K'alau mana" ta amsa a tak'ure. 


  "Ba wata jinya?"


 "Allah Maamah ke 'yar iska ce."


  "LOL" ta furta tana dariya "Ai gaskiya ce toh ya jiki?"


  "Ce miki akayi ina jinya?"


  "Ai ba se an fad'a ba da ganin Ya Afzal an san uhm uhm uhm ne."


  "Ni wallhi ba ruwa na."


"Ohh Amarsu ina yaje toh ya bar mana ke kad'ai a gida?"


  "Ni kawai cemin yayi ze fita and ban tambayesa ina zasa ba."


  "Kode gidan uwar gidansa zasa?"


 "Ban sani ba."


  "Kuma baki damu ba?"


  "Toh mutum da matarsa? Na isa in hanasa ne?"


  "Ahh ashe k'awar tawa bata da kishin hauka ai dama jin bakinki nake bale nasan ma ba gidan Nazeefah zasa ba."


  "Uhm so ya hutu?" hira suka ta6a sannan chan sukayi sallama. Tunanin me zatayi ta shiga yi zama hakan ne ya isheta gashi Afzal be dawo ba, chan dabara ta fad'o mata kitchen ta zarce ta shiga fito da groceries, had'ad'd'en jollof na spaghetti ta girka da minced meat ta ko ina a ciki, frozen chicken data ga a fridge ta ciro ta yanka ta gyara tayi pepper chicken da shi, bayan nan ta had'a zo6o me d'ankaren dad'i tayi slicing abarba aciki. Kan dining table d'in ta shirya gwanin sha'awa sannan ta kunna wuta ta turare gidan se k'amshi ke tashi. Nan ta kaiwa me gadi abincinsa sannan ta dawo ta fad'a bayi tayo sabon wanka tana fitowa ta idar da sallah ta ciro sabon d'inki ta sake sawa ta feffeshe jikinta da turare tayi kwalyanta ras. Har ta d'auko ribbon zata kama kanta seta tuna da kalamun Afzal na d'azu akan cewa tafi kyau idan ta sauk'e gashinta. Tajewa tayi ta sake a bayanta yana lilo, tana cikin d'aukan selfie taji k'aran bud'uwan gate nan fa gabanta ya fad'i seji tayi kaman ta goge kwalyar ma gabad'aya. 


   K'amshin turaren wuta ne ya bugi hancin Afzal yayin da ya sa kai cikin parlourn, ga k'amshi kota ina amma ba hayak'i unlike Ummi and Nazeefah da idan sukayi turare se hayak'i ya fitimi mutum na Amal k'amshi ne kawai ke tashi. Gaskiya he's really impressed. K'arisawa dining da yace zeyi don sauk'e ledan abincin daya siya musu ya tarar da kulolin abinci suna masa sallama. Da mamaki ya bi yana bud'ewa abinci ya tarar da dama aciki wow! Shin meyasa be sanar da ita cewa ze sai musu abinci ba? K'arisawa d'akin yayi tare da yin knocking, Amal naji ta gudu ta la6e bayan k'ofan sede Afzal ya ga shigewan ta kaman a kyaftawan ido murmushi ya sakar yayi kaman be ganta ba "Kitten?" Ya kirata yana lellek'a d'akin irin yana nemanta d'innan wajen bayin ya nufa yayi placing knock "Kitten are you in there? Bara in duba kitchen kota na chan" yace da kansa, ficewa yayi yaja k'ofan nan Amal ta sauk'e ajiyar zuciya cewan da tayi bari ta fito daga 6uyan Afzal ya wangale k'ofar "Got you!" Yayi shouting yana mata dariya, sosai ta firgita tare da dafe k'irjinta "Yaya you scared me!" Tayi complaining had'e da turo baki. 


   "I'm sorry Kitten come here" a hankali ta k'ariso, hannayensa ya zagaye a bayanta had'e da sake matso da ita kusa da shi. "You smell so good Kitten."


  "Thank you Habib Alby."


   "Wannan kwlaya fah? Duk ma ni neh?"


  "Toh kuma da wa me gadi zanyi wa ne?" Ta amsa tana turo mai baki. 


  "You look so beautiful Kitten." 

 

  "Thank you Habib Albi lets eat I cooked."


  "Haka na mance ban fad'a miki zan sai mana abinci ba."


  "Siyan abinci kuma Yaya?"


  "Yes Kitten ko kin manta amarya bata girki ne?"


  "But Yaya I want to cook for you."


  "I appreciate that Kitten amma kibari in kin gama amarcin ki tukuna kinji?"


  "Nide na gane kawai baka son cin girki na ne shikenan" ta fad'a tana 6ata rai. 


  "Not at all Kitten" yace yana mey shafa dogon sumarta "Bana son kina aikin wahala ne, na kawo ki gidan nan dan ki huta ne ba din kina aiki ba kinji?"


  "But ai hak'k'i na ne a matsayina na matarka in yi maka girki Yaya."


  "Kitten bana soke sunan nan ba?"


  "I'm sorry Habib Albi I just wanna cook for you dukda nasan girkin nawa ba dad'i I still want to cook for you."


  "Wayace baki k'ware a girki ba Kitten? Kin tuna rice and stew da kikayi mun lokacinda na dawo daga Hajj?" Kai ta gyad'a a hankali. "It's still my best Kitten, har yau banci Rice and Stew da yamin dad'i kaman shi ba."


  "Dagaske?" Ta tamabaya tana jin dad'i. 


  "Sosai Kitten I'm hoping you can cook it for me again."


  "Sure Habib Albi ko a gobe zan girka maka."


  "A'a mu bari se amarcin naki yak'are."


  "Har zuwa yaushe?"


  "2 months kacal."


  "Wata biyu kuma Habib Albi? Ina laifin sati d'aya?"


  "Are you kidding me?"


  "Toh sati biyu."


  "Why don't we do it this way tunda kina son yi min girki se muna yin na safe tare, kiyi na rana se na dare kuma muna ci a waje, okay


  "Habib-"


  "Please say yes Kitten" ya katseta cikin sauk'i. 


  "Sau d'aya zanna girki kenan?"


  "I'm sorry but yes."


  "Ina da alfarma toh."


  "Anything for my Kitten."


  "Amarcin ya zama na sati biyu."


  "Am not allowing that ko Nazeefah ma seda muka kusan two months sannan ta fara girki so kema haka."


  "Habib Albi toh wata d'aya please don't say no" ta rok'esa da fuskan tausayinta. 


  "Alright Kitten one month."


  "Yeyy! Thank you so muje inyi serving naka" har ta juya ya rik'o hannunta tare da kewayo da ita kafin ta gane abinda yake da anniyar yi kawai taji sauk'an lips nasa akan nata it was a very short kiss cikin seconds ya saketa. "I love you Kitten" kunya taji sosai kaman ta nitse k'asa. "I said I love you Kitten." Chan ciki-ciki tace "I love you too Habib Albi let's go." Dad'i yaji sosai suka k'arisa dining d'in abincin da ya siyan ya sa a microwave da niyyan anjima se suci. A plate d'aya ma suka ci abincin kaman d'azu, haka har suka k'oshi suka koma d'aki suka yini tare, sallah kad'ai ke fitar da Afzal, da dare yayi kuma da kansa yayi musu microwaving abincin daya siya d'azun suka ci. 



   **** 9:57pm

  Fitowan Afzal daga bayi kenan "You're next Kitten" mik'ewa tayi sanye da hijabi da towel ta ciki ta nufi bayin kaman jiya yau ma kafin ta fito har Afzal ya kimtsa gajeren wando zalla yasa d'akin se k'amshin turaren jikinsa yake. Gaban dressing mirror ta nufa ta shiga yin shafe-shafenta sannan ta k'arisa wardrobe ta shiga neman kayan baccin da zata sa sede duk ba marabansu da na jiya. Oh Rabbi ya zatayi? Tana cikin tunanin mafita kawai taji sauk'an hannun Afzal akan nata a kid'ime ta kewayo tana kallonsa. 


  "What's wrong Kitten?"


  "Ya- I mean Habib Albi I'm sorry ina neman kayan da zansa ne."


  "Baki samu ba har yanzu?" Ya tambayeta a hankali. Kai ta gyad'a "Ka bani minti biyu" kafin ta juya ya tsayar da ita "Wait" tsayawan tayi a hankali ya matsar da ita gefe bekai seconds talatin cikin wardrobe d'inba ya zaro d'aya daga cikin kayakin baccin nata shigen irin na jiya sede har gara na jiyan ma bak'i ne wannan milk color ne don haka yafi transparency. "Here wear this" amsa tayi ta d'aga tana kalla. 


  "Habib Albi I can't."


  "Why Kitten?"


  "Habib Albi..." se kuma tayi shiru. 


  "Look Kitten" yayi maganan tare da aza hannunsa akan kafad'unta yana murzawa a hankali "I'm not your Yaya anymore I'm your husband, kuma addini na ya halatta mun in kalleki acikin ko wani irin yanayi, ba haramun bane dan kinsa kayan nan na kalle ki Kitten."


  "Habib Albi I know kawai..." se kuma tayi shiru. 


  "Tell me kinji? Mene?"


  "Habib Albi kunyanka nakeji ina tsananin jin kunyanka and I don't know why." 


  "I guess I know why" ya sanar da ita. 


  "Really?" Ta tambayesa da mamaki. 


  "Yes Kitten saboda we started off as a brother and sister and not as lovers. It pains me that yadda kika d'aukeni da zuciya d'aya a matsayin wanki ni na kasa yin hakan. I know koda wasa baki ta6awa kawowa a ranki cewa aure ze shiga tsakanin mu ba one day se gashi zuciyata tayi karanbanin fad'awa tarkon sonki har ya zammana idan ban sameki ba rayuwata tana iya fad'awa cikin matsala. I'm very sorry Kitten amma ina son ki sani love is a feeling and not a decision one makes wallahi idan da zan iya bawa zuciyata hak'uri akan sonki da nayi kodan ki kasance tare da masoyinki Abdul amma ba daga ni bane, I can only control my mind and not my heart I'm really sorry" ya k'arisa tare da sauk'ar da kansa. Hannunta ta mik'a ta rik'o nasa wanda hakan ya sanya sa d'ago kansa. 


   "Habib Albi dan Allah ka daina magana haka kasani bazan ta6a k'inka don zuciyarka ta za6eni ba, abun alfahari ne ma ace Yaya na guda ya samu macen aure a tattare dani don d'abi'ata ko makamancin hakan."


  "Toh ki rage jin kunya na haka, gani nake kaman bakiya sona idan kina kunya na haka, is like kina adana jikin ki ma wani ne and not me:"


  "Yaya har kana tunanin zan ajiye kaina ma wani na miji sama da kai? I'm sorry if you felt that way."


  "Its okay Kitten just wear this." 


  "But-"


  "Please Kitten."


  "Habib-"


  "Please Kitten I want you to be free with me like old times, ki sanya kinji? Zan fita in kin gama shirin se in dawo" da fad'in haka ya mik'a tare da sauk'e mata light kiss a goshi sannan ya juya ya fice. Nauyayyan ajiyar zuciya ta sauk'e tana tunanin ta inda zata fara sa kayan, ta d'au tsawon minti biyu tsaye wajen sannan ta shiga kwaye hijabin nata, ba don tana so ba se don ya zama mata dole ta zira kayan ta k'arisa gaban mirror tana adjusting. "Huh!" Ta numfasa yayinda take kallon kanta acikin madubin kash sede bata tunanin zata iya yawo da kayan nan a gabansa da sauri ta sake mayar da hijabin ta sanya. Ita kanta haushin kunyan nan nata take, na sosai tana son ta sake da Afzal ko dan ta farinta masa rai amma kunyan nan ke hanata haka ta cigaba da tsaye a wajen har Afzal yayi knocking bisa k'ofan. Bayanta ta juya da wuri lokacin da ta ji ya bud'e k'ofar. A hankali take jin k'aran footsteps nasa suna iso ta chak ya tsaya a gabanta nan ta kafa idonta a k'asa. Hannunta taji ya kama acikin nasa yana murzawa a hankali yayinda ya shiga d'age mata hijabin da d'ayan hannun sa. Da sauri tasa hannu ta rik'e hijabin nata tana tsayar da shi. 


   "I've got you okay?" Da hankali ya sauk'e hannun nata ya shiga d'aga hijabin har ya kai ga kwayewa ta zare hannunta daga nasa ta shiga rik'e hijabin "Yaya I'm sorry but I don't think I can do this."


  "Shhh I've got you Kitten I've got you" cike da dabara ya sauk'e hannayen nata sannan a hankali ya kwaye hijabin ya cire daga jikinta kafin ta d'au hannu tace zata tare k'irjinta ya rik'o hannayen nata biyu cikin nasa. 


  "There" ya furta a hankali "Na fad'a miki ai zaki iya koba haka ba?" Hannun nata take kokawan k'wata daga nasa amma ta kasa har anan kuma ta kasa d'ago ido ta kallesa. "Kitten you're so beautiful" ya furta yayinda yake bin surar jikinta da kallo kunya tajiyo kaman ta nitse a k'asa a lokaci guda ta fisge hannayenta ta fad'a jikinsa tana kare fuskarta. Be hankara ba ya zageye hannayensa a bayanta yana shafata a hankali, wani irin wuta take ji yana bin jikinta. Bayan d'an lokaci ya d'agota daga jikinsa se sauk'ar da fuskanta take. Yatsa yasa ya d'ago fuskan nata "I love you Kitten" ya sanar da ita sede ta kasa cewa komai "Wani sa'in har tsoron irin soyayyar da nakeyi miki nake saboda ina ganin duk ranan da na rasaki toh tabbas nima za a rasani."


  "Yaya I'm here bazan ta6a barinka ba no matter what."


  "Thank you Kitten" a hankali ya shiga shafa fuskanta yana mey sa duk wani gashi a jikinta tashi, a nitse ya shiga matso da fuskansa kusa da nata har lips nasa suka sauk'a akan lallausar kumatunta, kisses ya shiga peppering mata tako ina har seda ya sauk'o k'asa zuwa wuyanta. Mutuwan tsaye Amal tayi wajen yayinda jikinta ya shiga rawa banda nishi masu nauyin da take sauk'ewa takasa yin komai. Kisses Afzal yata raining mata a fuska daga bisani kawai taji ya had'e lips nasu gu d'aya kafin ta iya turesa yayi sauri ya kama hannun ta cikin nasa yana mey cigaba da kissing nata, dukda cewan tak'i basa had'in kai hakan besa ya hak'ura ba. Wasu irin abubuwan ya shiga yi mata wanda tuni ya rikitar da Amal ya kuma mugun kashe mata jiki, a hankali yaji hannayenta cikin gashin kansa yayinda ta shiga kissing him back, sake matso da ita kusa da shi yayi tare da rik'o 'yar kunkuminta. Tafiya suka shiga yi a haka manne da juna har seda suka kai jikin bango. Na lokaci kad'an ya saketa kafin ta sauk'ar da kanta ya sake owning lips nata in a more demanding way, gabad'aya abinda yake mata ya gama tafiya mata da imani da k'yar ta iya pulling out tana maida numfashi, goshinta ta sauk'e saitin ha6arsa yayinda wani irin kunya ya rufeta. Bata tsammanin zata iya sake kallon cikin idanunsa. Oh Rabbi shin mey Afzal yakeyi mata haka? Meyasa ta kasa tsayar da kanta? Swollen lips nata ta shiga lasa a hankali yayinda ta rufe idonta gam. Hannunsa taji yana shafa fuskarta yana k'ok'arin sata ta kallesa sede tak'i, da k'yar ya samu ya ci nasaran hakan. Yatsansa ya kai akan lips nata da sukayi ja suka kumburo yana shafawa a hankali. Amal kad'ai tasan irin abinda take ji ajikinta. 

 

   "Kitten?" Ya kirata cikin hankali "Look at me" ya buk'aceta amman ta kasa kunya baze barta ba. "Don't feel shy Kitten, please look up."


  Duk yadda taso ta kallesa kaman yadda ya buk'ata hakan ya gagara da k'yar ya samu ta d'ago lumsassun idanunta ta sauk'e a kansa. 


  "There" ya furta yana mata murmushi yayinda yake tura gashin da suka rufe mata fuska baya. "Kin sani wani abu Kitten?" Ya yambayeta dan yadda suke kusa da juna har nishinsu had'ewa yake. Cike da kunya ta kad'a mai kanta. 


  "Your lips are probably the most sweetest thing I've ever tasted" ya sanar da ita yana shafe kan lips nata a hankali da yatsan sa. "May I get another taste?" Ya tambayeta amma kunya baze barta ta amsa ba duk da cewan she enjoyed kissing him also, itama tana iya rantsewa bata ta6a d'ana abu mafi dad'i kaman lips nasa ba, ga wani k'amshin mint da bakinsa yake. 


  "Kitten I badly want to kiss you again amma bazan yi hakan ba seda amincewar ki, may I?" Kai ta gyad'a masa a hankali idonta na kallon k'asa. 


  "No I want you to answer me with a yes or a no looking straight into my eyes."


  "Habib-"


  "Shhhh!" ya katseta yana mey cigaba da shafe kan lips natan. "May I kiss you again?"


  Seta bud'e baki zata amsa seta kasa  sau biyu yake sake tambayarta se ana uku tukuna ta amsa "Yes Yaya" wani mak'irin murmushi ya sakar sannan ya sake owning lips nata in a more possessive and demanding way, wasu irin abubuwa ya shiga yi wa Amal wanda tuni yasa ta fice daga hayyacinta, duk yadda taso keeping up da pace nasa ta kasa ba k'arya Afzal is a bad kisser, da k'yar ta iya tayi breaking kiss d'in tana maida numfashi yayinda jikinta ya d'au wuta gabad'aya. Bata hankara ba taji ya d'aga ta sama chak in a bride-like style. 


  "Hab-" toshe bakin nata yayi da wani kiss nasa se a kan gado ya direta inda ya cigaba da sarrafata iya san ransa banda maida numfashi ba abinda Amal ke iya yi gabad'aya ji tayi jikinta ya mutu. Yana ce bari ya gwada sauk'ar mata da hannun riga ta rik'e hannun nasa gam tana kad'a mai kai. Ba yadda beyi ba amma tak'i, gano dalilin hakan kawai seya mik'a hannu ya kashe wutan d'akin a hankali cike da k'issa irin nasa ya samu yaci nasara akanta har ya rabata da rigar nata...


  A daren ranan Afzal ya mai da Amal tasa cikakkiyar mace bayan gogormayan da ya sha. Daga kukan da takeyi har bacci ya d'auketa k'arshe. Yana cikin kallonta kwance a hannunsa shima har bacci me nauyi ya sacesa. 


   Da k'yar ya iya mik'a hannu ya kashe alarm d'in bayan da ya shiga ruri. Gani yayi yanzu ya kwanta amma wai har Asuba yayi. Wutan d'akin ya kunna sannan ya sauk'ar da kansa yana kallon Amal da tayi lamo tana bacci cikin hannunsa har yanzun, tabbas da ba don yana da hak'uri ba da sunyi bori da ita jiya saboda yadda ta gajar da shi ta yita basa wuya har ya samu ya biya buk'atansa. Haka kawai ya tsinci kansa cikin tsananin murmushi tuna sautin kukanta daga daren jiya, ai kam Nazeefah jaruma ce ganga da Amal. A hankali ya rabata daga jikinsa yaja towel ya nufi bayi bayan yayi wanka ya d'aura alawala akai sannan ya had'a mata warm water ya fito. D'aya daga cikin sabbin jallabiyansa ya zira sannan ya nufi kanta inda take ta faman bacci. Fuskanta ya shiga shafawa tun tana kawar da hannun nasa har ta tashi daga k'arshe. A hankali ta sauk'e idanunta da suka d'an kumburo akan fuskansa dake d'auke da murmushi, ba shiri ta sake kullesu. Dama yasan za'ayi haka.


   "Good morning my adorable Kitten" ya gaisheta sede kaman ce mata yayi tashi ki gudu. Bedsheet da take rufe da shi d'inne ta shiga tattarewa a jikinta yayinda take ja da baya. Dariya sosai hakan ya basa amma ya moze. 


  "Tashi kiyi wanka kiyi alwala muyi sallah ko? Na had'a miki warm water a tub" ya sanar da ita sede ko ta kyafta ido balle tasan yana yi. "Ko in miki da kaina ne?" Ya tambayeta ba shiri ta bud'e baki ta amsa sa "uhm uhm."


  "Tashi toh" sede ko ta sake motsawa. 


  "Kitten?" Nan ma shiru "Okay zan fita idan kin kimtsa seki mun magana okay? I love you" still shiru tayi masa seda taji k'aran ruhuwan k'ofa sannan a nitse ta bud'e idanun nata. Kallon gefe-gefe ta shiga yi dan janyo kayanta ta sanya amma ina kayan ya mata nesa dan haka ta mik'e da bedsheet d'in nannad'e a jikinta da zaran tace zata tsuguna kuwa se ta jiyo wani irin d'ankaren zafi a k'ark'ashinta bayan nan ga yadda cinyan nata yayi tsami. Haka a sannu a sannu ta k'arasa bayin hannu tasa cikin ruwan d'umin daya had'a mata har yaushe yake tsammanin zata iya shiga wanna ruwa mey uban zafi. Na sanyi ta bud'e ta tara seda yayi mata dai-dai sannan ta shiga ciki. Ta kai minti biyar ciki sannan ta fito ta bud'e shower tayi wanka ta d'aura alwala akai sannan ta fito se k'ingishi takeyi. Key tasa bakin k'ofan yadda Afzal ma baze iya sake shigowa d'akin ba. After everything bata tunanin zata sake iya kallon cikin idanunsa. Vest ta sanya ta d'aura zani tana cikin sanya hijabi tajiyo knock a bakin k'ofan tsabagen firgitan da tayi har chan k'asanta tajiyo zafin. 


  Da mamaki Afzal ya gwada bud'e k'ofan yaji bai bud'uwa. "Kitten?" Ya kirata, shiru tayi tsaye cikin d'akin. 


  "Kitten ba de kulle k'ofar nan kikayi ba" Nan ma shiru jijjigawa ya shiga yi sede ina bai bud'uwa gashi spare keys na k'ofofin gidan gabad'ai suna a cikin d'akin tirk'ashi! Rok'arta ya tayi da ta taso ta bud'e amma haka tana jinsa tak'i koda motsawa dan kansa ya bar wajen ya nufi d'ayan d'akin inda ya idar da sallansa ya kwanta. Bayan ta idar da nata itama ta tattara besheet d'in ta shiga bayi tasa a washing machine akan cewa da safe zata wanke. Sabon bedsheet ta shimfid'a sannan ta kashe wutan d'akin ta kwanta.


   Se chaan wajajen goma na safe ta tashi nan ma a sanadin ringing da wayanta yake ne da sauri ta d'aga ganin Mami ke kira. 


  "Halo Mami?"


  "Na'am Baby ya kike?"


  "Lafiya k'alau Mami ina kwana?"


  "Lafiya ya gida? Ya Afzal?"


  "Lafiya k'alau ya Papi?"


  "Yana nan k'alau shima ya fita d'azun."


  "Ayyah ba komai ko?"


  "Ba komai na ce bari in kira inji ko kina lafiya."


  "Thank you Mami."


  "Banda rashin kunya fa Baby, kiyi masa ladabi da biyayya duk abinda yace kiyi kiyi, wanda baya so kuma ki bari ba ruwanki da yima uwar gidansa rashin kunya kuma."


  "Mami na sani kin fad'a mun."


  "Toh Allah miki albarka bayan kwana biyu seki kira Ummi ki gaisheta kuma."


  "Toh Mami thank you."


  "Yauwa se mun sake waya." Sauk'e wayan tayi tana hamma duba agogon da zatayi taga goma da rabi tirk'ashi! Breakfast na Afzal fah? Mik'ewan da tace zatayi daga kan gadon tasa wani d'ankaren ihu bisa ga zogin da tajiyo a k'asarta a hankula ta mik'e ta shiga takawa sede kaman sake tsami cinyan  nata yayi yau ta shiga uku. Ji take kaman tayi kuka haka ta nufi bayin ta yi wanka ta fito ta shafa mai da turarukanta sannan ta sa wata doguwar rigar da ta mugun amsarta. Powder zalla ta shafa da farin lip gloss, tana cikin taje sumarta taji sauk'an knock bakin k'ofa, gabanta ne ya mugun fad'i amma bata ce komai ba. 


  "Kitten?" Ta jiyo muryan Afzal "Kitten I know you're awake ta shi ki bud'e mun kinji? Breakfast is ready" Kunya taji sosai taya yana mijinta zeyi girki ita ta kwanta kaman kayan wanki tana bacci. 


   "Kitten open up okay? Ko sena kira Papi tukuna ince gashi kin kulleni a waje?"

  Ce tayi wasa yake seda taji ya sa wayan a handsfree taji muryan Papi na sallama tukun. Ba shiri ta mik'e ta bud'e k'ofar murmushi ya sakar mata 


   "Dama nace in gaisheka ne Papi."


  "Toh Afzal nagode ko? Komai lafiya dai ko?"


  "Alhamdulillah."


  "Toh madallah."


  "Yauwa se mun sake waya."


  Toh ka gaishe mun da Baby."


  "Zata ji" nan ya kashe wayan. Baki ta turo sannan ta juya mai baya da k'ingishi ta shiga takawa har izuwa gaban mirron ta zauna. Kallonta ya tsaya yi yana mamakin ko meya sameta take tafiya haka. K'arisawa yayi ya sameta "Kitten?" Ya kirata.


  "Ina kwana?" ta gaishesa ba tare da ta kallesa ba. 


  "Taho kinji?" Hannunta yaja ya mik'ar da ita had'e da rungumarta. Lamo tayi ta kwanta a jikin sa "I'm sorry okay?" Ta ji ya fad'a. 


  Ko hak'urin mey yake bata? ta tambayi kanta. "Forgive me if I went rough on you last night Kitten" ya sanar da ita had'e da d'agota daga jikinsa. "I'm really sorry."


   "Ka dena bani hak'uri Habib Albi baka mun komai ba" ta fad'a ba tare da ta bari k'wayan idonsu ya had'u ba. 


  "Pain d'in sosai ne?" Ya tambayeta cike da tausayi, kai ta kad'a masa a hankali. 


  Fad'a mun gaskiya kinji? 


  Ba sosai bane don't worry" yatsa yasa ya d'ago fuskanta seda idanunsu ya had'e "I saw the way you were walking, mu kaiki clinic su duba ki?"


  "Ni banaso ze warke da kansa."


  "Toh let's go and have breakfast I cooked after then seki sha pain killer ze rage zafin okay?" Kai ta gyad'a mai a hankali. "Sannu ko Baby?"


  "Thank you Yaya" juyawanda zeyi yaga harta canza bedsheet na d'akin. 


  "Ina bedsheet d'in?" Ya tambaya. 


  "Na riga na wanke" ta sanar da shi. 


  "Kitten bana son kina sa kanki aiki."


  "Toh Yaya so kake in barka ka wanke da kanka ne?" Hannayensa ya zagaye a 'yar kunkuminta yana mey matso da ita kusa da shi. "Last night was amazing Kitten thank you."


  "Ni ka daina maganan bana so" ta fa'a cike da shagwa6a. 


  Dariya ya tsaya yana yi mata sannan ya shiga kwaikwayonta "Yaya ni bana so-"

 

  Rufe mai baki tayi take "Dan Allah ka daina" hannun nata ya sauk'e yana mey cigaba da neman tsokanarta sauran abubuwan da yake fad'an ma ko wuk'a aka sa mata a wuya baza ta iya tuna lokacin da ta fad'esu ba. Ganin tana shirin yi masa kuka ya daina "Na daina toh muje let's eat" a hankali suka shiga takawa ganin tafiyan na bata wuya kawai ya d'agata sama a hannunsa har dining space ya kaita sannan ya zaunar da ita akan cinyansa. Bayan sun gama karyawa ya 6allo mata maganin kashe zafin ya bata ta had'iye. 


  "Zaki iya fita yau kuwa?"


  "Ina?" ta tambayesa. 


  "Ina son muyi miki passport ne mu fara processing visan mu to Saudi."


  "Baza mu iya bari zuwa gobe ba Habib Albi?"


  "Ciwon sosai ne haka?"


  "Zuwa gobe ze daina in shaa Allah."


  "I'm sorry Kitten I didn't mean to bruise you."


  "It's okay Habib Albi."


  "Kikace baza mu kaiki Clinic ba?"


  "Ni gaskiya bana so."


  "Sannu ko Baby?" Kwantar da kanta tayi bisa k'irjinsa yayinda ya zagaye hannayensa a bayanta yana shafa gashinta a hankali. 


  Yini sukayi suna bacci ranan se wajajen k'arfe uku Afzal ya tashi a hankula ya sauk'e Amal daga jikinsa ya mik'e ya nufi bayi. Brushing yayi ya d'aura alwala sannan ya ajiye mata note gefen gado. Gentle kiss ya sauk'e mata a lips sannan ya sanya kayansa ya feffeshe jikinsa da turare ya fice.  


   Da la'asar Amal ta tashi mik'an da zatayi taji ba Afzal akan gadon. A hankali take bud'e idanunta inda suka sauk'a akan note da ya ajiye matan. Bata hankara ba ta d'aga ta karance kaman haka;


  _Will be back soon with our lunch don't mind cooking anything I love you, xx_ 😘 


  "Be back safely Yaya" ta furta tare da mik'ewa sede har yanzu da k'ingishin take tafiya bayi ta k'arisa tayi alwala tayi brushing sannan ta fito tayi sallah. Bayan ta kammala azkhar nata ta zarce gaban mirror tayi sabon kwalliya abinta kaman jiya yau ma tana cikin d'aukan selfies taji me gadi na bud'ewa Afzal k'ofa. Har ta bud'e k'ofa zata je ta taresa se taji muryan wani na tashi da hanzari ta koma ciki. Bada dad'ewa ba sega Afzal ya bud'e k'ofan ya shigo, ba k'aramin dad'i yaji ba ganinta da yayi da sabon kwalya. 


  "Kitten!" Yayi exclaiming cike da jin dad'i. 


  "Welcome back Habib Albi" hannunsa ya bud'e mata "Ni ka k'ariso" ta ce ganin takawan ze bata wahala, k'arisowan yayi sannan ta fad'a jikinsa. "Ya jikin naki toh?"


  "Da sauk'i" ta amsa.  


  "Sannu ko? Kinyi sallah?" Kai zalla ta gyad'a mar "Muje mun taho da Sultan yana son ku gaisa."


  "A'a nikam gaskiya bazan fita ba."


  "Kitten why?"


  "Kaman ya why Habib Albi? Da k'ingishin kakeso in fita ya ganni yasan..." sekuma tayi shiru. Dariya sosai ta basa amma ya moze "Kitten bazaki fita ku gaisa da aminin nawa ba kenan yanzu?"


  "Kace mishi ina bacci ni gaskiya bazan fita yamun dariya ba" yanzu kam dariya sosai Afzal yasa "Ya Sultan fa Kitten bazaki fita ku gaisa ba?"


  "Ba duk kai bane ka jimun ciwo" ta sanar dashi tamkar zatayi kuka "Kuma ka daina mun dariya" sake rungumarta yayi yana shafa gashin kanta a hankali "Yaya is sorry kinji? Baze k'ara ba." Kai ta gyad'a masa a hankali. 


  "Bari inje in same shi toh, in kawo miki abincin ki nan ko zaki jira in ya tafi muci tare?" Ya tambayeta bayan ya janyeta daga jikinsa. 


  "Zan jiraka jeka same shi" peck ya sauk'e mata a goshi sannan ya fice. 


  "Se yanzu amaryar ta barka ka fito kenan" Sultan da har d'uwawunsa yayi tsami dan zama yace. Da fari Afzal yayi niyyan masa k'arya yace Amal na bacci ne amma yanzu da Sultan ya kamasa haka ai ba halin yin k'arya kuma again. 


  "Actually..." ya furta yana sosa k'eyarsa yayinda yake tunanin wani k'aryan ze had'a. 


  "Na gane kar ka damu tace bazata fito ba tana jin kunya na."


  "Fvck! Keep your voice down Sultan kada ta jiyoka" ya sanar da shi cautiously. 


  "Hakan ne kuma ko?" Ya tambayesa yana dariya. 


  "Wallahi taji ka ba ruwa na nide ba ni na fad'a maka ba."


  "Triple A ansha k'amshi" yace da shi cike da neman tsokana. Punch Afzal ya kai masa a hannu yayin da ya zauna a gefensa "Ba kak'i kayi aure ba yau kaine a gidan nan gobe kaine a chan ka kasa settling da mace d'aya."


  "Ka bar matan nan kawai maza a jinka samun kaman Amal da sauk'i ne? Duk kud'in mutum kawai suke so ba komai ba."


  "Se muje k'auye mu auro maka d'aya ai kaga chan su kansu be waye ba basu san dad'in kud'i bama."


  "Amma Allah ya isa wallahi se gani na d'au 'yar k'auye na ajiye a gaban mota wai ita matata ko? Wallahi mugu kake Triple A."


  "LOL wai fa shawara ce."


  "Toh uwarka da shawaran ni da Allah kawo mun abinci inci."


  "Ai babu."


  "Kaman ya babu? Gidan amarya guda? Allah baza ta saku ba, in k'i cin abinci saboda zani gidan amarya kace mun ba abinci?"


  "Allah babu sede su chin-chin da dambu idan kana so."


  "Dalili?"


  "Amal d'ina bata girki" ya sanar da shi yana d'age mai gira. 


  "Jakar uba! Allah ban yarda ba."


  "Wallahi ba a idonka na shigo da ledan abinci ba kana gani?"


  "Waiiii morewa haka! gaskiya nima zanyi zuciya inyi auren nan."


  "Ahtoh ana fad'a maka kana wasa aure dad'i gareshi wallahi."


  "Kai maza!"


  "Niko nake fad'a maka."


  "Toh shikenan ha inyi nima in shiga daga ciki." Hira suka sake ta6awa kad'an Afzal harda korin Sultan wai ya tafi Amal tasa ta gaji da jiransa, iskanci ya ta yiwa Sultan yana neman tsokanansa k'arshe ya rakasa sannan ya je ya kira Amal dake d'auke da Qur'ani tana karatu. Seda ya jira takai k'arshen aya sannan ya gyara muryansa hakan yasa ta gano da mutum cikin d'akin.  


  "Masha Allah Kitten yaushe zaki fara bani karatun nima?"


  "Kai Habib Albi."


  "Taso to muje muci abinci" da kansa ya mik'ar da ita kaman d'azu ya d'auke ta har izuwa dining. 



  ****

   Da daddare bayan ya fito daga bayi yace da Amal "Tashi ki shiga na sirka miki warm water ki samu at least 7-10 minutes aciki ze miki healing ciwon kinji?"


  "Ni bana so."


  "Kaman ya bakiya so Kitten, meyasa? 


  "Zafi Habib Albi."


  "Bakiya son ki warke ne?"


  "Inaso."


 "Toh ai se kinyi hak'uri kin shiga gashi ma na saya miki man zafi, idan kika fito semu shafa miki, tashi ki shiga kinji?"


  "Ni bana so" lalashinta yatayi da k'yar ya samu ya jata cikin bayin "Ina tsaye a waje ina jiranki kinji?" Hannu tasa cikin ruwan "Wallahi yayi zafi."


  "Kitten in ba haka ba bazaki samu sauk'i da wuri ba fa."


  "Zan k'ara ruwan sanyi kad'an toh."


  "Kitten kar kisa fa in tu6eki anan in saki cikin ruwan nan da kaina."


  "A'a kayi hak'uri."


  "Toh ki shiga kuma karki k'ara ruwan sanyi akai, zan tsaya a waje kisani idan kika k'ara kuma zan sani."


  "Tayaya bayan kana waje?"


  "Are you daring me?" Ya fad'a cikin tattausar murya kai tayi saurin kad'awa "Good kar fa ki k'ara ruwan sanyin nan."


  Tana murmushi tace "Barin k'ara ba."


  "Kitten ba fa wasa nake ba."


   "Nace naji ka fita kar ya huce."


 "Ban yarda dake ba ki rantse bazaki k'ara ruwan sanyi akai ba."


  "Rantsuwa ba kyau ni gaskiya bazan rantse ba."


  "Kitten! So kike in miki wankan da kaina ko?"


  "A'a dan Allah zanyi da kaina."


  "Rantse bazaki k'ara ruwan sanyi akai ba toh idan na fita."


  "Allah bazan k'ara ba wallahi."


  "That's my kitten ki samu at least 7 minutes aciki it'll help in shaa Allah." Kai ta gyad'a mar sannan ya fice. Kayan jikinta ta tu6e sannan a hankali ta shiga tub d'in da k'yar ta iya ta zauna a ciki seda ta kusan minti takwas a ciki ta tashi lokacin har ruwan ya huce, watsa ruwa tayi, tayi brushing ta d'aura alwalan bacci ta fito.


  Bayan ta gama shiri ta sanya kayan baccin ta da kanta yau amma bata tu6e hijabin ba seda ta iso gadon ta zauna. (Su Amal an fara sakewa da Afzal.)


  "Zamu shafa miki man zafin ko?"


  "Habib Albi is it necessary?"


  "Yes it is Kitten bakiya son ki warke da wuri ne?" Shiru tayi bata kuma cewa komai ba har ya d'auko maganin ya dawo ya zauna k'afafun nata ya mik'ar akan cinyansa sannan ya d'an tattare rigan nata sama sede yana tattarewa tana sauk'arwa.


  "Wai mey haka Kitten?"


  "Toh kamun a haka mana seka d'age mun kayan ne" ta amsa tana turo mai baki. 


  "Nasan maganin fitsararren bakin nan ai" shiru tayi bata sake cewa komai ba har ya kuma tattare kayan sama "ina ne?" Ya tambayeta nuni da wajen tai masa sannan ya shafa maganin a wajen cewa da yayi bari ya murza ta sa wani d'ankren ihu. 


  "Wayyo Mami naaaaa!!!" Tare da cire hannunsa. 





RANA D'AYA!

#RD


Love... King Miemiebee👄✨

[13/08, 09:36] ‪+234 907 483 8352‬: 🎀🎀🎀                 🎀🎀🎀

                🎀❣🎀

                   ❣❣


  💦💦                      🍃🍃🍃          

           *RANA D'AYA!*

  💦💦                      🍃🍃🍃

  July, 2018

 beeenovels.blogspot.com


     _Written by Miemiebee👄_



   *PAGE 2⃣9⃣*



    

   A rayuwa ba abinda yake rikita wa Afzal lisafi kaman sautin ihun Amal, kad'an ya rage be fad'i a k'asa ba. "Haba Kitten!" Yayi exclaiming yana murza kunnensa "So kike ki kurmantar da ni ne?"


  "Toh Yaya haka ake shafawa mutum man zafi ne? Ba a hankali ake yi ba kasan mey? Bar shi ma kawai in shaa Allah ze warke da kansa."


  "Raguwa kawai."


  "Ayya Habib Albi amma ai kasan k'arfin mu ba d'aya ba ko?"


  "Toh Baby tsaya in miki a hankali" da zaran yace ze murza seta sa ihu dan ba wasa ba cinyoyin nata sun mugun yin tsami, ganin fa ba bari zatayi ya shafa mata ba ga shi lokaci se tafiya yake kawai ya had'e hannayen nata gu d'aya ya danneta sannan ya shiga murzawa maganin, duk kalan ihun da takeyi hakan besa ya saketa ba seda ya murza ya kuma tabbata maganin ya shiga ciki tukuna. 


   Kuka take sosai harda majina yayinda cinyoyin nata suke yi mata zogi, ba k'aramin dariya ta basa ba amma ya moze, gaban mirror ya nufa ya kawo mata tissue "Hungo share hawayenki Kitten kukan ya isa haka" ko ta kansa batayi ba se lek'a k'afan nata take yayinda take jin yadda maganin ke shiga jikinta.


  "Haba Baby naa yi hak'uri kinji? Yaya is sorry" Yayi maganan had'e da zama a gefenta yana k'ok'arin fara share mata hawayen, cike da takaici ta k'wace tissuen nan ta shiga sharewa da kanta bayan ta gama ya amsa yayi disposing "Let's sleep okay?" Ko kallonsa batayi ba taja pilonta izuwa k'arshen gadon ta kwanta, murmushi yayi sannan ya kashe musu wutan ya haura gadon ya kwanta. Pillonsa ya matsar kusa da nata had'e da ya6a hannunsa akan cikinta wanda ta cire da sauri. Mayarwa ya sakeyi itako ta sake cirewa. 


   "Haba my Baby yi hak'uri bazan sake ba" shiru ta mai bata amsa saba. 


  "I'm sorry bazan sake ba, yi hak'uri ki juyo mu kwanta my arms feels so empty without you."


  "Haka kawai don kaga kafini k'arfi kayita mun mugunta ba, ni gobe zan koma gida gun Mami na."


  "Laaa yi hak'uri beyi zafi haka ba Kitten" cike da dabara ya juyo da ita had'e da aza kanta akan k'irjinsa yana mey shafa bayanta a hankali. "Sannu kinji? Yi hak'uri, kika tafi ai bazan iya rayuwa ba" da haka har bacci mey nauyi ya d'aukesu duka. 


  Ko a washegari Afzal be bari suka fita d'in ba saboda gani da yake kar cinyan nata suji tafiya su k'ara yin tsami. Sosai ya tausaya mata barin ma idan yaga yadda take k'ingishi, banda wanka be sake bari ta koda d'aga tsinke ba. 

   Da k'yar Amal ta barsa ya fita siya musu abinci ita sam wai ita zatayi girki shi kuma ya rantse seta samu sauk'i tukun. Gidan Nazeefah ya fara nufa dan duba lafiyarta, shi kansa kunya yakeji ace tun da ya k'ara aure be lek'o uwar gidansa ya duba lafiyarta ba sede suyi magana a waya, yau yini na uku kenan. 


   Sallama yayi yayinda ya shiga parlourn kasancewar bata nan se ba wanda ya amsa. K'arisawa yayi ciki ya lek'a kitchen ganinta da beyi ba seya zarce d'akinta knocking yayi sannan ya bud'e zaune kan gado tana waya ya tarar da ita. 


  "Ya Rouhi!" Tayi exclaiming had'e da katse wayan, a guje ta mik'e taje tayi hugging nasa, "My Rabba'atul Bait I miss you" ya furta yana mey matse ta gam a jikinsa. Sun d'au tsawon lokaci a haka sannan ya sakota a hankali. 


   "Ashe zaka kewayo nan."


  "Kuma wani irin magana kike haka Rabba'atul Bait?"


  "Eh mana Ya Rouhi gashi tun da kayi amarya ka mance ni."


  "Ba haka bane Rabba'atul Bait-"


  "Toh yaya ne?" ta katse sa "Nayi maka uzuri a ranan farko amma ai yaci ace ka lek'o ni jiya koba haka ba?"


  "I'm really sorry Nazeefah nasan nayi miki laifi but forgive me okay?" 


  "Ba komai dama nasan baka damu da ni ba."


  "Inji waye?" Yayi maganan had'e da zaro wata k'aramar pack daga aljihunsa cike da rashin hak'uri ta tsaya tana kallonsa yayinda yake bud'ewa "Here I want you to have this" ya sanar da ita lokacin da ya bud'e pack d'in. Zobe ne me kyau aciki shigen irin na Amal sede akwai banbanci kad'an.  


   "Wow Ya Rouhi" ta numfasa hannunta ya d'ago a hankali ya sanya mata zoben sirr aciki. "Its so lovely Ya Rouhi thank you!" Ta sanar dashi had'e da brushing masa light kiss a baki yayinda ta kasa daina kallon yadda zoben ke yalk'iya, ko ba a tambaya ba ansan me tsada ne. "It's so beautiful."


  "Don't mention Rabba'atul Bait so kin yafe mun?"


  "Ai Ya Rouhi baya laifi."


   "That's my girl, so ya kike?"


  "Lafiya ya Amal?"


  "Lafiyarta k'alau na barota tana bacci if not da mun taho tare."


  "Ayyah I miss you Ya Rouhi."


  "I miss you too Rabba'atul Bait I miss you even more."

   

  "Anya kuwa? Kaida Amal ke d'ebe maka kewa."


  "Ke daban ita daban Nazeefah ki daina had'a kanku kinji?" Kai ta gyad'a mar zalla "I hope you're okay ba wata matsala ko?"

  

  "Babu just that I miss you."


  "Na kusa dawowa ai."


  "4 more days fa ya rage Ya Rouhi anya kuwa zan iya?"


  "Zaki iya mana Rabba'atul Bait I trust you" ya fad'a yana placing mata kiss a kumatu. "Uhm kin tuna sanda muka tafi Umarah tare?" Kai tayi saurin gyad'awa "Good ina son mu tafi da 'yar uwarki itama."


   "Ni kuma fa?" Wani irin kishi maras misaltuwa ne taji ya rufeta. 


  "Nazeefah ba mun tafi dake ba why not with Amal yanzu?"


  "No Ya Rouhi bazan yarda ba, bayan ka gama yi mata sati kuma ka sake d'iban k'afa ku tafi Umara har zuwa yaushe? Ni shikenan ni kad'ai na zan na cigaba da zama a gidan nan? Kana ganin ka mun adalci kenan?"


  "Nazeefah calm down please ya kike magana haka? Please calm down. It's not as if ban ta6a tafiya dake ba, in fact dake ma na fara tafiya to avoid circumstances like this ko kin manta kece Rabba'atul Bait d'ina and komi zanyi daga kanki zan fara? Please calm down ba komai aciki fa dan na tafi da Amal yanzu please understand."


  Da fari tayi niyyan tada mai bori amma tuna kalamun Rumaysa na cewa "_Kar ki ta6a nuna masa kishinki duk abinda ya shafi Amal ki nuna mai baki da damuwa da hakan_" seta canza ra'ayinta na dole ta shiga yayyafa wa zuciyarta ruwan sanyi. 


  "Nazeefah nasan kishi da zafi but Allah ya riga ya k'addaro miki sede ki k'ara hak'uri akan wanda kikeyi wallahi I appreciate and respect you alot and I love you so much, kin cika uwar gida a duk inda ake neman hakan please don't change, it gives me pleasure when you and Amal are getting along. In shaa Allah idan Allah ya dawo damu lafiya daga baya zamu shirya dukan mu uku mutafi I promise you." Murmushi yaga ta sakar tana zagaye hannayenta a wuyansa "It's okay Ya Rouhi kayi hak'uri na amsan dana baka bisa ga rashin yin tunani, na amince kai da Amal ku tafi Umran tare after all ai nima ka kaini kuma addini yace kaso wa d'an uwanka abinda kaso wa kanka so kaman yadda naji dad'i da ka kaini Umaran itama Amal zanso taji dad'in nan." Da mamaki ya tsaya yana kallonta tunda ta fara maganan wai shin wannan Nazeefar da ya sani ne?


  "Rabba'atul Bait" ya kirata se kuma ya kasa cewa komai. "Are you sure?" Shi kansa ya kasa amincewa da ita. 


   "Yes Ya Rouhi I'm totally cool with it, yaushe ne tafiyan naku?"


  "Da saura dan bamu fara processing visan bama tukun I wanted to let you know on time." 


  "Thank you Ya Rouhi I love you so much."


  "I love you even more Rabba'atul Bait" ya amsa had'e da kai mata light kiss.

  "Toh bari zan koma."


  "Bazaka tsaya kaci abinci ba?"


  "Don't worry bana jin yunwa" har gun mota ta rakasa inda ya irga dubu goma ya mik'a mata. "Na mey kuma wannan Ya Rouhi?"


  "Ki k'ara akan wanda na baki and keep it kinji?"


  "Ya Rouhi kud'in beyi yawa ba? I barely even touched that one."


   "Kin manta Ke Rabba'atul Bait ce?" Dad'i sosai taji tayi hugging nasa "Thank you so much."


  "Don't mention" ya amsa had'e da d'agota "Ka gaishe da Amal idan ka isa."


   "In shaa Allah you take care okay?" Kai ta gyad'a mar a nitse, seda taga ficewarsa sannan ta koma ciki wayarta ta d'aga ta dannawa Rumy kira. 


   "Babe yane?"


  "Ba k'alau ba wallahi."


  "Meya faru?"


  "Ni dama tun farko na fad'a miki plan d'innan be min ba da bari kikayi naci uwarta tun kamin ta shigo."


  "Keko meya faru haka?"


  "Gashi ta samu d'uwawun zama wai har Saudi ze kaita."


  "Kai dan Allah!"


  "Wallahi yanzu dan Allah ya zanyi?"


  "A ina kika jiyo labarin?"


  "Yanzun Ya Afzal yazo ya sanar dani."


  "Ina de baki nuna masa hankalinki ya tashi ba?"


  "Kad'an ya rage amma sena sake calming kaina."


  "Good this is to our benefit Babe."


  "Ban gane ba kina jin zasuyi tafiya kina zancen benefit?"


  "Ke dad'i na dake gajan hak'uri wallahi ki barsu suyi tafiyan, kinga idan suka dawo se mu nemo mata 'yar aiki muce kar aikin gida yayi mata yawa."


  "Mey riban hakan? A dalilin uwar mey zan nemo mata 'yar aiki?"


  "Ke kuwa calm down mana ai ba wai don tsakani da Allah bane, akwai yaran mey mana aiki guda biyu a k'auye zan yi ma uwar nasu magana ta kawo mun su kinga seki d'au d'aya mu bawa Amal d'aya itama, we will make her part of our plan duk wani mak'ircin da mukeso da ita zamuna amfani da infact kinga komi ma zefi zuwa mana da sauk'i tunda ita tana cikin gidan instructions kawai zamu na bata in shaa Allahu se mun fidda Amal kowa take daga gidan."


   "Kai Babe ban san ya zanyi ba ke ba wallahi, Allah tsunduma mun ke cikin aljannah."


  "Ai muddin ina raye baza kisha wuya ba barsu suje Saudi su dawo tashin hankali na nan yana jiransu."


 "Toh kiyi ma matar magana tun yanzu da Allah ba se idan lokaci ya k'ure ba."


  "Karki damu kede kawai ki kwantar da hankalinki kuma komin yaya kar ki nuna masa kishinki balle ki bud'e k'ofan da ze zarge ki."


  "Toh shikenan Babe thank you."


****

  Washegari su Afzal suka fita inda akayi wa Amal passort aka shiga yi mata processing, yini sukayi a wajen se wajajen biyar suka dawo gida. Washegari da safe still suka sake fita se wajajen uku suka bar wajen nan ma ba don an gama ba se don suna son su d'anyi ziyara. Gida gun Ummi suka fara zuwa, sosai Ummi taji dad'in ganinsu, hira suka ta6a kad'an sannan Afzal yace zasu tafi yana son su duba Nazeefah. Spices da dama ta d'ibo ta bawa Amal inda tayi godiya sosai. Daga nan suka wuce gidan Nazeefah. Dan munafirci harda hugging Amal, da fara'a sosai ta kar6esu tayi serving nasu drinks da snacks ba wanda zece wai duk fara'an nan na munafirci ne se hira suke su uku suna dariya. Da suka zo tafiya kuma Nazeefah harda cewa wai Afzal ya bar Amal yaso se dare yazo ya d'auketa. 


   A kwana na uku suka gama processing International passport na Amal sannan suka shiga yin na visansu, shi wannan d'in be basu wuya ba kasancewar akwai abokin Afzal da ke aiki a wajan, yanzu jira kawai suke idan visan ya fito su fara shirin tafiya. 


    Afzal na iya rantsewa wannan sati d'aya da yayi tare da Amal shine one of the best weeks of his life, ba fad'a ba tashin hankali ba fargaba ba komai se zallan soyayya kawai. Tabbas son Amal daga sama aka turo masa shi, komin yaya yayi baze ta6a iya had'a soyayyarta da na wani ba bayan iyayensa, soyayyarta a jininsa yake idan ba ita baya jin ze iya rayuwa. A gobe  Allah ze kai su k'arshen sati inda kwanan Afzal ze k'are. Tunda Amal taga ya shiga tattara kayakinsa jikinta yayi sanyi se taji gabad'aya bata so ya tafin dan yadda suka saba na sati gudan nan. Sosai Afzal ya saba mata da zama ajikinsa muddin yana gida toh fa se ajikinshi take zaune take kwanciya, ya zata yi yanzu idan ya tafi? Gaskiya Nazeefah tayi na mijin k'ok'ari da har ta bar mata Afzal na sati guda ita kwana biyu kacal zeyi ya sake dawo mata amma seji take kaman ta bisa. 


  "Kitten bazaki tayani shirya kayakin nawa ba?" Ya tambayeta yayinda yake nannad'e boxers nasa yana sasu cikin wata k'aramar akwati. Bata 6oye mai ba tace "Bana son ka tafi Habib Albi."


  "Are you gonna miss me?" Ya kewayo yana tambayarta. Kai ta gyad'a masa a hankali cike da shagwa6a. 


  "Toh ai tafiya ya zama dole Kitten kwananki na sun k'are anan ko bakiya son inje in samu 'yar uwarki?"


   "Ina so mana kawai zanyi missing naka ne" ta sanar da shi. 


  "I can't even tell how am gonna miss you Kitten but two days kawai zanyi in sake dawowa."

  

  "Mesa baza ka na mana kwana d'ai-d'ai ba toh?"


  "A'a bibbiyun de zefi Kitten d'ai-d'ai akwai gajiya."


  "Toh shikenan" ta furta ba walwala tattare da ita. 


  "Come here" ya kirata batayi gardama ba ta mik'e taje ta samesa akan cinyarsa ya zaunar da ita. "Bar had'e ran haka kinji?" yayi maganan yana shafa fuskanta "Two days kacal zanyi in dawo in shaa Allah" Kai ta gyad'a mar a hankali sannan yayi crashing lips nasa akan nata kissing her slowly with tender touches. Na d'an lokaci ya saketa, nan ta fad'a jikinsa, hannayensa ya zagaye a bayanta yana shafata a hankali. 


  "Kin san wani abu?" Kai tayi saurin kad'awa tare da d'ago kanta daga jikinsa. Jan bakinta daya kama bakinsa ta shiga goge mai a hankali. 


  "Muyi wanka tare yau."


  "Wanka tare kuma Habib Albi?" Ta tambayesa had'e da zaro ido. 


  "Yes Kitten aren't you gonna miss me?"


  "Of course I'll amma wanka tare kuma..."


 "Toh ba Annabi ma nayi da matansa ba" shiru tayi bata ce komai ba "Ko baki sani ba?"


  "Na sani" ta furta ciki-ciki. 

 

  "Good I want us to bathe together too just me and you Kitten" Kanta ta sauk'ar akan k'irjinsa had'e da zagaye hannayenta a bayansa "Ni kunyanka nakeji" ta sanar da shi murmushi ya sakar had'e da zagaye hannayensa a bayanta shima. 


  "Zaki daina in shaa Allah" taya shi tayi  ya gama shirya kayakin nasa, bayan nan suka tu6e suka d'aura towel sannan suka shiga bayin a tare. Shi da kansa ya sirka musu ruwan d'umin dam yacika bathtub d'in sannan ya zuba shower gel aciki ya kad'a seda yayi bubbles (kumfa.)


  "Toh ki fara shiga."


  "Habib Albi..." ta furta cike da shagwa6a tana turo mai baki. "Ni ka fara shiga."


  "No Kitten after you."


  "Toh ka juya bayanka."


  "Kitten wai mey haka?"


  "Ni de ka juya bayanka kawai" murmushi ya sakar sannan ya juya d'in "Ni ban yarda ba, nasan sena tu6e zaka juyo ka kalleni ni bazan yarda ba."


  "Kitten don't you trust me?"


  "I do."


  "Toh ki shiga." 


  "ka rantse bazaka juyo ba."


 Dariya yake sosai yace "Na rantse toh shikenan? Yi ki shiga" seda ta k'are masa kallo sannan a hankali ta sauk'e towel d'in da sauri ta k'arisa ta shiga cikin tub d'in, yana jin k'aran splash na ruwa ya juyo se ganinta yayi ciki se faman tattara kumfan take a jikinta yadda baze samu ya gane mata jiki ba." 


  "There" ya furta yana admiring nata. "Saura ni ko?" Kai ta gyad'a masa a hankali acewanta ze bari seta juya kanta ta kafin ya shiga kawai taga ya tu6e a gabanta kai tayi saurin kawarwa shi yake amma ita ke ji mai kunya. A hankali taji ya shiga ya sanyata a tsakankanin k'afafunsa. Kanta ya kwantar a jikinsa, da zaran ya ta6ata se tayi wincing haka suka tayi har seda ta saba da hannunsa na yawo a jikinta. Hira da wasa suka tayi cikin tub d'in kaman ba gobe, chan Amal tace tana jin bacci don haka suka wanke jikinsu suka fito kayan baccinta ta sanya shima yasa gajeren wandonsa sannan suka haye gado suka kwanta. Tun ranan da abu ya shiga tsakaninsu Afzal be sake nemanta ba se yau, dalilinsa kuwa befi baya son ya sake fama mata ciwon ta ba. A hankali a hankali yana tarerayarta da kalaman soyayyarsa har ya rabata da kayan jikinta, sosai suka gamsar da junansu ranan daga k'arshe suka fad'a bacci.  


  Tunda suka koma baccin Asuba basu tashi ba se wajajen sha d'aya nan ma tare suka sakeyin wankan sannan suka fito suka shirya suka nufi kitchen suka had'a breakfast. 

   Rice and stew had'ad'd'iya ta girka musu for lunch bayan sun k'are ci ya tattare wajen sannan yajata sukaje parlour inda ya zaunar da ita akan cinyarsa kaman kullum. 


  "Kitten ban ta6a ganin kin kunna TV a gidan nan ba shin bakiya kallo ne?"


  "Inayi" ta amsa. 


  "Meyasa bakiya yi toh?"


  Bata mai k'arya ba tace "Ni gudu nake kar na rikitar da wani abun ban ma iya kunna TV'n ba."


  "Toh ai sekice in koya miki Kitten."


   "Toh ka koya mun" dad'i sosai Afzal yakeji yadda Amal ta sakewa da shi yanzu. 

 

  "Mik'o remote d'in toh" bayan ta mik'o masa ya sake zaunar da ita kan cinyansa sannan ya shiga nuna mata. 


  "Akwai tashan Sunna TV ko Manara?Ina son ina jin wa'azi."


  "Masha Allah that's very thoughtful of you Kitten" scrolling yayi ya kai mata kai "Shikenan?"


  "Thank you Habib Albi."


  "Don't mention Kitten" mik'awa yayi tare da pecking nata a gefen bakinta. 


  "Se microwave d'innan shima ka koya mun amfani dashi incase zanyi heating abinci baka nan." Kitchen d'in suka nufa ya nunnuna mata yadda akeyi sosai kuwa ta fahimta. Wajajen shida na yamma Afzal yace ze tafi Amal gabad'aya bata son ya tafi se gani take kaman idan ya tafi baze sake dawowa ba. "Bazaki rakani ba Kitten?" Hannunsa ya mik'a mata tana sanya nata a ciki ya mik'ar da ita har waje suka kai bayan yasa akwatin nasa acikin motar ya kewayo kawai me ze gani Amal harda 'yar k'wallanta. 


  "Ohh Kitten" janyota yayi had'e da kwantar da kanta a k'irjinsa yana shafa kanta "Shhhh! Please don't cry, zan dawo ai kukan ya isa haka kinji? Bar kukan haka."


  "I'll miss you Habib Albi."


  "I'll miss you even more Baby" ya fad'a had'e da d'agota. K'aramin fuskanta ya rik'o cikin hannayensa sannan ya shiga kissing tears nata yana share mata su "Ya isa kinji?" Kai ta gyad'a masa a hankali had'e da aza hannunta kan nasa dake rik'e fa fuskan nata. A hankali ya mik'a yayi capturing lips nata, wani irin mugun kiss mey ratsa jiki ya bata, be sake ta ba seda ya tabbata ya gushar da duk wani tsoron dake tattare da ita. 


  "I love you Hun" ya sanar da ita lumsassun idanunta ta d'ago a hankali ta aza kan kyakkyawar fuskansa "I love you too Habib Albi" hannunta ta sauk'e kan lips nasa tana goge masa jan bakinta daya kama. 


  "Wani abu ne?" Ya tambayeta. 


  "Lipstick d'ina ne ya kama ka tsaya in goge kar Rabba'atul Bait ta gani ka had'a kanmu." Murmushi ya sakar mata "Toh goge ina jiranki."


  "There ya fita" ta sanar da shi had'e da sauk'e hannunta. 


  "Ina zuwa" yace da ita cikin motansa ya shiga ya fito da wata envelope "Ga wannan ki rik'e incase wani need yayi arising" yace yana sa mata envelope d'in cikin hannu. 


  "Habib Albi na mey kuma? Please ka rik'e" ta fad'a tana k'ok'arin miyar mai. Hannun nata ya rik'e "Shhh naki ne kinji? And don't hesitate to call me if you need more I'm just a call away."


  "Habib-"


  "Please Kitten spend it, it's all yours."


  "Thank you Habib Albi Allah k'ara bud'i."


  "Ameen koma ciki toh."


  "Ni senaga ficewanka tukun" be sake yin musu ba ya shige motan waving suka ma juna yana kallonta ta mirror har seda mai gadi ya kulle gate sannan ta dawo ciki. Tuk'i yake amma hankalinsa gabad'aya na akan Amal. 



  ****

  "Oyoyo Ya Rouhi" Nazeefah ta ruga aguje had'e da rungumesa tana yi masa sannu da zuwa lokacinda ya shigo parlourn. Da k'yar ya iya ya ajiye akwatin nasa sannan ya d'agata chak a sama. 


  "Rabba'atul Bait you look so beautiful" ya sanar da ita tare da sauk'e ta, ba k'arya kuwa tayi kyau, tasha makeup sosai ga kitso da lallenta duk masha Allah. 


  "Duk kwaliyan nan ma ni ne?"


  "Eh mana Ya Rouhi."


  "Gaskiya dole na biya kud'in kwalyan nan kin ganki kuwa?"


  "Kai Ya Rouhi banda zolaya."


  "Allah fa dagaske kinyi kyau sosai."


  "Thank you sweetheart" jakan nasa ta tsuguna ta d'aga suka k'arisa d'aki "In had'a maka ruwa ka watsa?"


  "Yes please" nan da nan ta sirka mai ruwa ya shiga ya watsa sannan ya fito da alwala. A gida suka idar da sallah bayan nan ta jasa dining inda tayi serving nasa fried rice and chicken da coleslaw da ta had'a sosai abun yayi armashi se praising girkin nata yake kaman ba gobe. Chan dare bayan duk sun watsa ruwa Nazeefah ta kwantar da shi tana mai massage (tausa) daga nan suka wula duniyar ma'aurata. 


   Ita da kanta ta shirya Afzal office washegari kasancewar hutun sati d'aya da aka basa ya k'are se wani tarerayarsa take abinda bata ta6a yi masa ba ma ta fara yi yanzu duk don ta burgesa, sosai yake jin dad'in kulawanda yake samu daga gareta har gun parking lot ta rakasa ta basa good luck kiss sannan ta dawo ta koma bacci abinta. 


  Afzal na isa office bayan ya kammala necessary abinda ya kamata ya kira Kitten nasa ba k'arya yayi missing nata. Tana cikin bacci taji rurin wayanta cike da gyangyad'i ta mik'a hannu ta d'aga ko duban waye batayi ba. 


  "Halo?" Ta furta cikin sleepy voice nata. 


  "Good morning my adorable Kitten" taji muryan Afzal. 


  "Habib Albi" ta fad'a cike da mamaki batayi tsammanin ze kirata early this morning ba. 


  "Na'am Kitten ya kike?"


  "Lafiya" ta amsa tana hamma, yana jin muryanta ya gano bacci take shi ya d'agata. 


  "Na tada ke daga bacci ko?"


  "A'a kar ka damu ina kwana?"


  "Lafiya kwanta kiyi baccinki kinji? I'll call you back later."


  "Okay Habib Albi."


  "I love you."


  "I love you too" da haka ta katse ta koma bacci. Wajajen goma ta tashi wanka ta farayi sannan ta had'a breakfast nata da na mai gadi. Bayan ta gama ci tayi sharanta da wanke-wanke ta koma d'aki ta tsara kwalyanta ta baza gashinta a baya sannan ta yima Afzal video call. Yana cikin aiki a office ya ga shigowan call d'in da mamaki ya tsaya yana kallon screen d'in wai Amal da ya sani ne take yi masa video call? Lallai! be 6ata lokaci ba ya d'aga da kyakkyawan fuskanta ya soma cin karo. 


   "Wow!" kawai ya ke iya furtawa. 


  "Good morning Habib Albi" ta gaishesa. 

  

  "Good morning my adorable Kitten."


  "Ya kake? Ya office?"


  "Alhamdulillah you look amazing Kitten" ko kyafta ido ya kasa se kallonta yake kaman ze zak'ulota ta wayan. 


  "You're not looking bad yourself Habib Albi yaya Nazeefah?"


  "Lafiyarta k'alau tana gida ba wani matsala ko?"


  "Ko kad'an."


  "Kinyi breakfast?" Kai ta gyad'a masa "Mey kika ci?"


   "Toasted bread da tea."


  "Hmm interesting baki tambayeni mey naci ba ni."


  "Bana son inyi shisshigi ne Habib Albi."


  "Toh ask me" ya buk'aceta yana had'e rai. Murmushi tasa wanda ya mugun k'ayata ta. 

  "Toh Habib Albi mey Rabba'atul Bait namu ta girka maka?"


  "Fries and omalet."


  "Kaifa d'an gata ne Habib Albi."


  "Really? Ai kema 'YAR GATA CE Kitten."


  "Gata na be kai naka ba ai."


  "Allah ko meyasa kikace haka?"


  "Because ka na da mata biyun da zasu iya kwantar da ransu dan soyayyar da suke maka."


  "Really? Kina so na har haka Kitten?"


  "Of course Habib Albi kaman yadda Rabba'atul Bait taka keson ka ko fiye da haka ma."


  "I'm impressed yau Kitten ce take admitting feelings nata haka kode dan missing d'ina da takeyi ne?"


  "Ko ba don hakan bama Yaya cikin d'an satin nan da mukayi tare na gano you're so special to me."


  "So you are to me, you're my long lost medallion Baby I love you so much."


  "I love you too Habib Albi I'm sorry if it took me long to admit."


  "I was ready to wait until eternity for you Darling so ki daina bani hak'uri kinji?"


  "Toh Habib Albi bari in barka haka kayi aiki take care okay?"


  "I'll and you too" kiss yayi mata blowing ta screen d'in ita kuma tayi pretending kaman ta kama tayi placing a kumatunta da haka tayi stopping call d'in. Murmushi Afzal yatayi shi kad'ai a office d'in wajajen sha biyu sega call d'in Nazeefah be hankara ba ya d'aga. 


  "Halo my Rabba'atul Bait."


  "Na'am Ya Rouhi ya kake?"


  "I'm good you?"


  "Lafiya ya office?"


  "Very boring I'm missing you."


  "Same here Baby mey kakeso kaci for lunch?"


  "Yau kuma Rabba'atul Bait? Ba ke kike yin komai ba?"


  "A'a kai nakeso kayi deciding yau so what do you want to eat for lunch Baby?"


  "Anything will be fine."


 "No specify."


  "Let's see..." ya fad'a yana nazari "cous-cous da miyan yakuwa."


  "Oh! Ya Rouhi kowa na bin dama kai kana hagu yaushe aka fara cin cous-cous da yakuwa?"


  "Ni haka nake so bana son tuwo."


  "Toh Baby consider it done."


  "Thanks babe."


  "Don't mention seka dawo I love you."


  "I love you too take care" nan ta kashe. Maida wayan yayi ya cigaba da aikin gabansa yayinda kalamun Amal suka shiga dawo masa _Because ka na da mata biyun da zasu iya kwantar da ransu dan soyayar da suke maka._ 

   Tabbas tayi gaskiya sabida ze iya rantsewa akan kalan soyayyar da Nazeefah takeyi masa fatansa kawai Allah ya basa ikon kwatanta adalci ne a tsakaninsu. 


  Be zarce ko ina ba se gida daya taso daga office inda Nazeefah ta kar6esa, sosai yaji dad'in kwana biyun da yayi mata, ba fad'a bale tashin hankali. Duk abinda yakeso shi Nazeegah ke masa, ana gobe ze tafi bayan ya dawo daga sallan Isha suka shirya tsaf suka ci abinci a waje daga chan suka wuce 3G gallery yasan Nazeefah da son jaka duk sanda yake son farinta mata nan d'in kawai yake kaita tayita kwasan jakukkuna. Yau k'waya uku ta kwasa designers masu kyau. 


  "Yau uku ya isheki kenan?"


  "Uhm" ta gyad'a masa kai tana murmushi "Bari in d'auka wa Amal itama toh." Wani irin kishi taji ya tokareta a rayuwa ba abinda ta tsana kaman taji yana maganan Amal kokuwa yana cewa zeyi mata wani abun. Halan ya karanci yanayinta se ji tayi yana tambayarta "Ko kar a saya mata ita?"


  "A'a Ya Rouhi ka d'auka mata please" murmushi ya mata sannan ya mik'e wata purple jakar channel mey chain ya d'auka mata da ja saboda Amal na son wannan colors d'in se da wani bak'in  valentino. Nazeefah tsabaragen kishi ita fa ta za6i nata da kanta amma ganin wanda ya za6a wa Amal se taga gabad'aya natan ma ya bar mata kyau, taji na Amal d'in kawai takeso amma ya ta iya? Idan har tana son cimma burinta dole tayi hak'uri, bayan ya biya kud'in aka sanya musu a seperate leda sannan suka taho gida. 


    Washegari da yazo tafiya Nazeefah harda munafurcin basa wani turaren wuta wai ya kaiwa Amal Mummy ce ta siyo mata shine tayi tunanin ta raba musu. Sosai Afzal yaji dad'i had'e da yi mata godiya itama har gun motarsa ta rakasa sannan ta dawo ciki bayan daya sallameta. Da goshin Maghrib ya iso gidan Amal, itakam don yadda tayi missing nasa ta kasa jira ya shigo ciki tun daga waje taje taransa, yana fitowa daga motan ta fad'a jikinsa, hannayensa ya zagaye a bayanta yana mey maste ta ajikinsa yayin da yake shak'an daddad'an k'amshin turaren jikinta. 


  "I miss you Habib Albi" ta sanar da shi. 


  "I miss you even more My adorable Kitten" yace had'e da d'agota daga jikinsa. "Masha Allah, gaskiya Allah ya miki baiwan kyau Kitten you look... you look" yama kasa k'arisawa se kallonta kawai yake. 


  "Beautiful? Is that the word you're looking for?"


  "Yes Kitten you're looking spectacularly beautiful."


  "Thank you Habib Albi welcome home."


  "Thanks Baby" ya amsa had'e da juyawa cikin motan wata leda ya ciro nan ta mik'a hannu zata kar6a. 


  "A'a Kitten ze miki nauyi."


  "Haba Habib Albi."


  "Bari zan rik'e kinji?"


  "Toh shikenan tunda kace haka" nan suka k'arisa ciki, se faman k'amshi gidan yake, ya fad'a turaren wutan Amal daban yake dana kowa ya rasa ya take cire hayak'in tabar k'amshi kad'ai wataran seya gwada tambayarta shima ya koya wa Nazeefar sa. Ruwa ta had'a masa amma ya rantse shi idan ba da ita ba bazeyi wankan ba itako bata dad'e da yin wanka ba bayan nan so yake ta goge wannan kwalyar da tayi duka? Yau fa harda foundation ta shafa kaman yadda Maamah ta koya mata gaskiya baze saku ba. 


  "Habib Albi please mana Maghriba fa tayi."


  "Toh ki taho muyi wankan tare semuyi sallan."


  "Ba lokaci."


  "Toh shikenan na fasa."


  "Toh yanzu so kake in goge kwaliyan nan gabad'aya?"


  "Ba lalle ba."


  "Toh an ta6a yin wanka kwalya be gogu bane?"


  "Matso kiga" matsowan tayi ba gardama kafin ta gane meyake shirin yi kawai taji sauk'an lips nasa akan nata, be saketa ba seda ya tand'e jan bakin tas ga wani k'amshin berries da jan bakin keyi, ko ragowa be bari ba. "There kinga yanzu babu so let's bathe."

  Wajen mirror ta nufa da mamaki kuwa taga ya tand'e jan bakin tas. 


 "Haba Habib Albi! Haba!"


  "Kefa kikace bakiya son kiyi asaran kwaliyar ki."


   "Toh yanzun ba asaran jan baki kayi mun ba?"


  "Ba asara bane tunda Habibin ki ne ya tand'e koba haka ba? Taho to muyi wankan."


  "Kaga yanzu Maghrib yayi kabari idan mukayi sallah kaci abinci ka huta semuyi wankan k'arshe?"


 "Ni yanzu nakeso."


  "Habib Albi bakaji kiran Sallah ba? Kuma kaga wankan mu tare ai yana d'aukan lokaci koba haka ba? Let's pray first okay?"


  "Okay darling duk abinda kikace taho muyi alwalan toh" ba musu ta k'arisa suka shiga bayin suka d'aura alwala suka fito sukayi sallah, bayan nan taja hannunsa izuwa dining inda ta cike kan table d'in dam da abinci kala-kala ga smoothies har kala biyu aldeb da zo6o wow! His Amal is so extra. Kaman yadda suka saba cin abinci a plate d'aya hakan ma sukayi yau sede yau Amal tace ita zata basa beyi musu ba ya barta, haka ta basa ta bawa kanta har suka k'oshi. D'aki suka koma inda ya d'auko ledan daya shigo da shi d'azun ya ciro jakukkunan "Gashi wannan naki" ya fad'a yana tura mata su gabanta. 


  "Duka Habib Albi?" Ta tambaya da mamaki. 


  "Yes Kitten."


  "Wow!" Ta numfasa had'e da d'ago jan duk shi yafi yi mata kyau kodan tafi son abu ja ne. "Habib Albi basuyi yawa ba?"


  "Not when they're to be presented to a damsel like you Kitten."


  "Thank you so much Habib Albi kai da kanka ka za6a kuma?"


  "Mey kika ga?"


  "Ai naga ba na aibantawa ne aciki, ace guda d'aya zan d'auka ciki toh sede ruwan ido ya kasheni don duka sunyi kyau wallahi."


  "Ni na za6a mana."


  "Kai Habib Albi anya kuwa ba wata mata kasamu acikin shagon kace ta za6a maka ba?"


  "Kina iya kiran Nazeefah ki tambayeta a gaban ta na d'iba miki."


  "Ahh na yarda gaskiya mijin nawa ya iya za6i."


  "Abba ma seda yace haka ranan farko da ya fara sanya ki a ido."


 "Kai Habib Albi."


  "I'm telling you."


  "Wai meyace?" Ta tambayesa cike da jin dad'i. 


  "Mey kuwa? Ai kaman yadda nake fad'a miki cewa yayi you're very beautiful."


  "Allah sarki Abba kasan ko jiya ma seda ya kirani wallahi naji kunya sosai tunda akayi auren ban nemesa ba se gashi kwatsam ya kirani."


  "Ayyah wai mey gaisuwa?"


  "Eh bayan nan kuma yace duk sanda ka mun abinda be gameni ba kar inji tsoro in kirasa in sanar da shi yace ze zane ka."


  "Abban dey?!" Yayi exclaiming. 


  "Sosai ma kuwa" ta d'age mai gira tana faman dariya. 


  "Toh bani jakana na fasa bakin bani kayana" tattarewa tayi da wuri ta matsesu a jikinta. Hannu yasa zey k'wace ta hanasa cakulkuli ya shiga yi mata nan ta fad'a kan gadon da baya yayinda ya d'ale kanta se faman yi mata cakulkulin yake tana dariya. 


  "Ha- Habib Alb- Habib Albi ya isa please wallahi cakulkuli k'anin mutuwa ne" ta samu ta fad'a da k'yar dan dariya har hawaye take se anan ya ga daman sake ta. Fuskansa ya matso gab kusa da nata sannan ya share mata hawayen "Yanzu in Abba yace ze zaneni seki barsa Kitten?" Kai ta gyad'a mar tana dariya. 


  "Ha in tattara kayakina in koma gun Rabba'atul Bait d'ina dama chan nasan ba sona kike ba" kafin ya sauk'a daga kanta tayi sauri ta janyo hannunsa had'e da zagaye hannayenta a wuyansa. 


  "Kai baka san wasa bane Habib Albi? Ai wasa nake maka, shi kansa Abba acikin raha ya fad'a kuma idan ma ta kama ze zane ka d'in ai sede in shiga a zaneni a madadinka I wouldn't want anything to harm you Habib Albi" a hankali kalaman nata suke kwanciya a kan zuciyansa. 


  "How much do you love me Kitten?" Ya tambayeta cike da jin dad'in kalamunta yayinda yake shafe kan lips nata da yatsansa. 


 "10 on the scale of 10 Habib Albi, a shirye nake da in rasa farincikina saboda naka, rayuwata gabad'aya zan iya sadaukarwa dan inceto naka I love you so much." Yanzu kam ya kasa 6oye farin cikinsa "I'm ready to sacrifice the last kobo I have to make you happy Kitten, I will travel a thousand miles without food or water just to be with you, this's just a little out of how much you mean the world to me."


  "Thanks Habib Albi" matso da fuskansa ya sake yi ta hanyan rufe duk wani gab dake tsakaninsu kissing k'asan hancinta yayi sannan a hankali ya gangaro kan lips nata da suka fi masa dad'i fiye da komai a duniyan nan ya shiga yin gadamansa dasu. 





RANA D'AYA. 

#RD


Love... King Miemiebee👄✨

[13/08, 09:36] ‪+234 907 483 8352‬: 🎀🎀🎀                 🎀🎀🎀

                🎀❣🎀

                   ❣❣


  💦💦                      🍃🍃🍃          

           *RANA D'AYA!*

  💦💦                      🍃🍃🍃

  August, 2018

 beeenovels.blogspot.com


     _Written by Miemiebee👄_



   *PAGE 3⃣0⃣*



    

   Getting enough of her strawberry lips, a hankali yayi breaking kiss d'in had'e da mik'ar da ita suka zauna "Ya kamata kayi wanka Habib Albi akwai office gobe."


  "Kin manta tare zamuyi wankan ne?"


  "Toh tashi muyi ka samu ka huta ka kwanta."


 "Ni massage (tausa) nakeso."


  "Komey kakeso zanyi maka Habib Albi yanzu de ka mik'e tukun."


  "Kafin nan" yayi maganan had'e da zaro roban da Nazeefah ta basa akan ya bawa Amal "Ga wannan daga gun 'yar uwarki" amsa tayi tare da kaiwa hancinta don shinshinawa "Wow turaren wuta!" Ta fad'a cike ca jin dad'i. "Allah sarki Nazeefah yanzun zan kirata inyi mata godiya kafin in manta."


  "Yakamata kam."


   "D'an mik'o mun wayana" nan da nan ta kira Nazeefah tayi mata godiya inda ita kuma ta nuna mata ba komai. 


  "Yauwa Kitten may I ask you something?" Ya tamabyeta bayan ta ajiye wayan. 


  "Anything Habib Albi."


  "Shin ya kikesa turaren wutan kine?"


  "Mey kaga?"


  "Unlike na Ummi da Nazeefah naki hayak'in baya yin yawa se k'amshi zalla."


  "LOL Habib Albi kai baka san shuwa da turaren wuta bane? I think tun ina shekara goma na fara kunna turaren wuta."


  "Nasani I'm just curious so tell me."


  "LOL okay ni ba se dab zaka dawo nake sawa ba, timing lokacin da zaka shigo nakeyi se in kunna 20-25 minutes before haka."


  "Window a kulle ko a bud'e kike sawa?"


   "Ina kulle windows in sauk'ar da curtains, idan nabi gidan da turaren gabad'aya se in bashi kaman 10-12 minutes ya kama haka sannan in bud'e windon kad'an in kunna fan hayak'in ya fita, yana d'an fita se in sake kullewa kar k'amshin yabi iska shima a hankali har hayak'in ze watse gabad'aya yabar k'amshi."


  "No wonder mana kullum inyita mamaki."


  "Yanzu ka gane?"


  "Yes Kitten" ya amsa nan da nan suka d'aura towel suka nufi bayi inda sukayi wanka, sun dad'e aciki sannan suka fito d'aure da alwala. Sallan isha suka idar suka kammala Azkhar nasu sannan suka sanya kayakin baccinsu. A hankali ta kwantar da Afzal akan k'afarta sannan ta shiga yi masa tausar, kasancewar hannayen nata sirara suke kuma k'anana se ji yake kaman cakulkuli takeyi masa. Duk lokacin da ta ta6asa seya sa dariya haushi ya bata k'arshe ta turesa daga jikinta. 


   "Ni na fasa yi" ta fad'a a fusace had'e da gangarawa wajenta. Bin ta yayi ya haye kanta ya shiga showering mata kisses tun daga wuya har izuwa fuska yana teasing nata sannan ya mik'a hannu ya kashe musu wutan d'akin. Xxx


  Washegari bayan sun idar da sallan Asuba ta taya Afzal shiri dukda cewa da yayi karta damu ta koma bacci ze iya shirya kansa, seda ta rakasa har waje sannan ta dawo ciki ta koma bacci. Kaman yadda yake kiran Amal kowace safiya da yake gun Nazeefah haka ma ya kira Nazeefar yau suka gaisa seda ya tabbata bata da wata matsala sannan sukayi sallama. 


   Wajajen k'arfe biyu Amal ta d'au waya ta kira Afzal bayan ta tamabayesa ya aiki tayi gyaran murya "Habib Albi se nawa kake tashi daga office yanzu?"


  "Wani abu ne Kitten?"


  "I miss Mami and Papi" ta sanar dashi. 


  "Kina son kije ki dubasu?"


  "Eh."


  "Toh ba ga motarki ba?"


  "Toh Habib Albi na iya tuk'i ne?"


  "Haka kuma fa semun koya miki a hankali."


  "Nifa tsoron tuk'i nake."


  "Toh haka zaki ta kallon motan naki Kitten?"


  "A'a in zaka iya seka nemo min driver yana kaini duk inda nakeso amma nikam bazan iya tuk'i ba."


  "Me zai hana ki Kitten? We'll discuss that later so kikace kinason ki duba su Mami?" Kai ta gyad'a wane yana gabanta. 


  "Alright bari inyi clearing schedule d'ina se in taho muje."


  "Dagaske Habib Albi? Ban shiga ma hak'k'in office ba ko?"


  "Ai aikin office na zuwa ne a bayan farin cikin Kitten d'ina so I'll be home in a jiffy kinji?"


  "Toh Habib Albi seka zo I love you."


  "I love you most Kitten" da haka ta katse wayan. Girkin nata tayi sauri ta kammala ta zubawa mai gadi nasa sannan ta shirya kan dining. Bayan nan ta tsaya yin shawara ta kunna turaren wuta ne kota fara shiga wanka daga k'arshe de ta fara da shiga wankan. Bayan ta fito ta shafa mai ta tsara kwalyarta sannan ta sa wata bak'ar lace da touches and stone works na golden sannan ta fice parlour. Show glass nata ta bud'e ta ciro kwalban data juye turaren wutan da Nazeefah ta bata, haka kawai taji bari ta gwada kunnasa taji k'amshinsa yau. Gawayinta na kamawa ta zuba cikin kasko sannan ta barbad'a turaren akai se sauri take kar Afzal ya taho yanzu ya tarar da hayak'i. Tana zuba turaren akan gawayin kawai wani irin hayak'i ya shiga tashi tunda take bata ta6a ganin abu haka ba hurawa ta shiga yi a hankali amma ina se k'aruwa hayak'in yake har yana sanyata tari, shin wani irin turaren wuta ne wannan Nazeefah ta bata? Gashi nan da nan ya k'one ya fara bada warin k'onuwa da hanzari ta fita waje dashi ta k'ofan kitchen ta zubar.  

   Sabon gawayi ta d'ibo zata had'a kwatsam taji k'aran motan Afzal sosai gabanta ya fad'i parlourn ta dawo da wuri amma ta rasa ta ina zata fara fidda wannan uban hayak'i. Inda ma ace hayak'i ne zalla da da sauk'i amma ga warin k'onuwa gabad'aya ya d'umama gidan yau ta shiga uku. Afzal na bud'e k'ofan parlourn yayi sauri ya koma baya dan wani irin hayak'in dayaci karo da. 


  "Subhanallahi!" Yayi exclaiming da sauri had'e da zaro hanky yana toshe hancinsa. "Kitten ki fito kafin hayak'in ya miki illa" yace da ita yana mamakin ya akayi take tsaye har yanzu cikin tsabar hayak'in nan. "Kitten hurry!" kamar wacce k'wai ya fashe ma aciki ta fito ta samesa a waje. 


  "Ya haka meya faru?" Yayi saurin tambayanta. 


  "Yaya-" se kuma tayi shiru, gabad'aya ta kid'ime.


  "Abu ne ya k'one miki?" Kai zalla take iya kad'a mai "Ya gidan da hayak'i haka toh? Ga kuma warin k'onuwa." Har ta bud'e baki zata sanar da shi turaren wutan da Nazeefah ta bata ne ba kyau se kuma ta tuna nasihan da Mami tayi mata na cewa;

   _Ko da wasa karki fara ki had'a kansa da na matarsa, komin mey ta miki kar kice zaki kai k'ararta gunsa idan har kece da gaskiya toh Allah da kansa ze wanke ki dan shi ba azzalimin bawa bane_ wannan lafazi yasa ta canza ra'ayinta tayi shiru. 


   "Yes??" Ya sake tambayarta jin tayi shiru. 


  "Ermm... Naje ina kula da girki ne se har turaren ya k'one akan gawayin I'm sorry."


  "Shikenan ba komai ina de baki k'one ba?"


  "A'a."


  "Shikenan don't worry mu zauna anan se hayak'in ya ragu kafin mu shiga."


  "Barin shiga in bubbud'e windows d'in in d'aga labule zefi fita da wuri."


  "So kike ki shak'i wannan uban hayak'i har seya miki illa Kitten?"


  "Toh Yaya in ba haka ba baze fita da wuri ba har ka samu kaci abinci mu fita."


  "Toh muje in tayaki se muyi da sauri."


  "A'a ka jirani anan."


  "No Kitten I insist" haka suka k'arisa ciki suka shiga bubbud'e windows d'in, da hanky mak'ale a hancin Afzal amma dukda haka wari da hayak'in be barsa ba, gabad'aya jikin Amal yayi sanyi sam ba haka taso abinta ba. A waje suka zauna seda hayak'in ya ragu sannan suka koma ciki bin parlourn tayi da turaren Khumra don kashe warin. Bayan ta sirka masa ruwa yayi wanka suka fito dining don cin abinci sede tun d'azun yake kallonta gabad'aya tayi shiru ba walwala tattare da ita. 


  "Kitten?"


  "Na'am?" Ta amsa tana d'ago kai. 


  "Yau achan zaki zauna?" Kai ta gyad'a zalla "Why?"


  "Yaya I'm sorry."


  "Why? What for?"


  "For the inconvenience wallahi ban san ya akayi turaren ya k'one haka ba please forgive me."


  "Ohh Kitten!" Ya numfasa "Come here" ba gardama ta mik'e daga kujeran nata ta samesa, a cinyarsa ya zaunar da ita "It's really okay dear, kullum kinayi me kyau dan an samu akasai yau kuma seya zama abun magana? Kidena damun kanki kinji? Ni baki mun komai ba."


  "Thank you" tace dashi cikin sanyi, shi da kansa yayi serving nasu sannan ya shiga feeding nata seda suka k'oshi tukun suka jira La'asr yayi suka yi sallah suka shiga shiri, se wajajen biyar da rabi suka dawo gida se hira Mami take jansu da. 


   Bayan sallan Maghrib Amal da Afzal suna zaune a parlour Afzal ya mik'ar da k'afafunta akan cinyansa tana tayasa kallon sports se wayanta ya shiga ruri dubawan da zatayi taga Nazeefah ke kira bata hankara ba ta d'aga. 


  "Assalamu Alaikum."


  "Wa'alaikumus salam Nazeefah" ta amsa '"Yar uwa ya kike?"


  "Lafiya k'alau ya gida da wahala kuma?"


  "Wani wahala ne kuma, gida k'alau ya Ya Afzal?"


  "Lafiyanshi k'alau."


  "Nace kinyi amfani da turaren wutan nan kuwa?"


  "Eh."


  "Gosh! Dama kira nayi ince karkiyi amfani dashi bashida kyau yanzu Mummy ta kirani take sanar dani matar da ta sayar matan ta cuce tane" ta shirya mata k'arya don dama da gan-gan ta bata turaren wutan sanin bashida kyau. 


  "Ayyah wallahi har na kunna d'azu."


 "Ba dad'i ko?"


 "Unfortunately gashi yata hayak'i kuma yana k'onewa gabad'aya ya d'umamamun gidan."


  "Subhanallahi Ya Afzal na gida kuma? Kinsan bayi son hayak'i."


  "Wallahi abun beyi ba sam, ina cikin sawa ya dawo."


  "Allah sarki kiyi hak'uri dan Allah ban san bashida kyau ba da ban baki ba."


  "Ba komai Nazeefah ai bazaki cutar dani da gan-gan ba."


  "Toh bari in barki haka kar in shiga hak'k'in Ya Afzal."


  "A'a fa karki damu."


  "Toh ki gaishesa seda safe."


  "Allah bamu alkhairi" da haka sukayi sallama. "Huuh!" Tayi exhaling had'e da ajiye wayan "Waye ne? Nazeefah ce?" Ya tambayeta. 


  "Eh tana gaisheka."


  "Ina amsawa maganan mey naji kuke haka?"


  "Batun turaren wutan ne kasan wanda ta ba nin na kunna ashe wai bashida kyau matar data had'an bata k'ware ba seta damfari Mummy dama kira tayi tace kar in kunna nace ai tun d'azu na kunna."


  "Ayyah kinga bama laifinki bane kike ta tada hankalinki daga turaren wutan ne."


  "Ai toh naga baka son hayak'i ne shine hankalina ya tashi."


  "Next time ki kwantar da hankalinki kinji?" Kai ta gyad'a mar a hankali sannan ya shiga tickling toes nata ya na mata cakulkuli, dariya ta tsaya yi na sosai chan wajajen tara da rabi suka kashe TV'n suka yi wanka suka kwanta. 


   Washegari da yamma Afzal ya koma gun Nazeefah, tsaf ta gyara gidan ta itama ta kunna turare sede hayak'in ne yayi yawa. Bayan sun yi Sallah sun ci abinci suna zaune a parlour Afzal yayi gyaran murya ya kira ta "Rabba'atul Bait?"


  "Na'am Ya Rouhi" ta amsa. 


  "Shin ya kike sa turaren wutan ki ne kam?"


  "Mey kaga?"


  "I'm just curious ya kike sawa?"


  "Dab zaka zo nake sawa."


  "Shiyasa hayak'in yake yin yawa."


  "Yana damunka ko?"


  "I'm sorry but yes kinsan bana son hayak'i."


  "I'm sorry a haka fa na bubbud'e window ma dan ya d'an ragu."


  "Kinsan ya Ummi takeyin nata?" Beso ya ambaci sunan Amal ba gudun kar hakan ya sanyata kishi. Kai ta kad'a a nitse. 


  "Kunnawa take 20-25 minutes idan tana expecting bak'o saboda hayak'in ya tafi."


  "Toh Ya Rouhi k'amshin ai se k'are kafin nan."


  "Nop kinga zaki kulle windows ki sauk'ar da curtains seki sa ki basa like 10-12 minutes haka ya kama, then ki d'an bud'e window ki kunna fan ya tafi da hayak'in yana d'an fita sekiyi shutting back windows d'in kinga haka k'amshin ki yana nan hayak'i kuma ya tafi." 


  "Kai amma Ummi akwai fasali na gane Ya Rouhi nima haka zan fara sawa in shaa Allah."


  "Yauwa Rabba'atul Bait shiyasa nake sonki."


  "Uhm Ya Rouhi?"


  "Yes Babe?"


  "Wallahi wata tambaya nake son inyi maka amma bana son kamin mumunar fahimta."


  "What is it? Feel free to ask me."


  "Bazaka mun mumunar fahimta ba?"


  "Just ask me Nazeefah."


  "I've been curious for a while tun da aka kusan auranka ciwon zuciyanka be sake tashi ba shin dama mey dalilin? Meyake jawo maka attack d'in?"


 "Naze-"


  "Please tell me Ya Rouhi the last time I asked you banji dad'in yadda ka nuna mun a fili bazaka iya sanar dani ba I felt like you didn't trust me as your wife."


  "Ba haka bane Nazeefah of course I do trust you."


  "Toh yaya ne Ya Rouhi ai idan da ka yarda dani komi naka zaka iya sanar dani nasan da Amal ce ta tambaya da tuni ka sanar da ita."


  "No please don't ever say that again kaman yadda Amal take matata kema haka ne so ki daina tada hankalinki kina ganin kaman nafi sonta fiye da ke, I love you both okay?"


  "Okay Ya Rouhi kayi hak'uri idan magana na ya 6ata maka rai."


  "Ba komai ya wuce."


  "So zaka iya fad'a mun?" Nauyayyan ajiyan zuciya ya sauk'e "I'm very sorry Nazeefah amma Amal ce sababin ciwon nawa, rashinta a kusani dani shi yake haddisa mun ciwon nawa."

  

  "Amal?" Ta tambaya cike da mamaki bil adad "Rashin Amal Ya Rouhi?"


  "Yes Nazeefah, Amal."


  "Wow!" Ta numfasa yanzu akan Amal Mummy ta mareta ranan a fuska? Yanzu akan Amal tsakaninsu da Ummi ya kusan 6aci? Wow! Ai dama seda jikinta ya bata haka amma tak'i amincewa ashe gaskiya ne in bahaka ba kanta ya mugun d'aurewa yadda ciwon nasa be sake tashi ba tun da ya kusan aure. 

 

   "Amma ban fahimce ka ba Ya Rouhi shin ba auran soyayya kukayi da ita Amal d'in bane dama har kake tsoron rasata haka?"


  "It's a long story Nazeefah."


  "Will it be okay if you tell me?" Numfasa yayi sannan ya fara kaman haka;

  "I've known Amal for three years now tun kafin muyi aure muke tare da ita amma ba a matsayin saurayi da budurwa ba don daga baya ne nayi developing feelings mata lokacin kuma ita har sunyi nisa da wani saurayinta Abdul kin gane sababin ciwon nawa?"


  "Anytime ka gansu tare se ciwon naka ya tashi kai kuma ka kasa sanar da ita kana sonta?" Kai ya gyad'a zalla. 


  "Toh ina shi saurayin nata yanzu?"


  "Yana Canada."


  "Ya sadaukar maka da soyayyanta kenan?"


  "Yes Nazeefah."


  "Allah sarki gaskiya na ji ma wannan masoya guda biyu Allah sa hakan shi yafi alkhairi a gareku duka."


   "Ameen Rabba'atul Bait I hope I've answered your question."


  "Yes you did Ya Rouhi muje ka watsa ruwa mu kwanta gobe office ko?"


*****

   Haka kwanaki suka ta shud'ewa yayinda shak'uwa da soyayya keta dad'uwa tsakanin Afzal da Amal, a yau jirginsu na zuwa Saudi ya tashi kad'an ya rage Amal batayi kuka ba sanda jirginsu yazo tashi tsabaragen tsoro. 

   

   Da zuwansu yau sun samu sati kenan lafiya k'alau suke zaune, kullum suna cikin fita shopping da wajajen shak'atawa, tsaraba da dama Afzal ya sai wa Nazeefah wasu ababen ma Amal ce ke cewa ya saya mata, sosai yake jin dad'in yadda Amal ta d'au Nazeefah da zuciya d'aya. 

  Yau a d'aki sukayi deciding su yini Amal na mik'e akan gado tana latsa wayarta yayinda Afzal ke tsaye gaban mirror ko mey yakeyi oho. 

   "Arghh!" ya saki k'ara bisa yankewan da yayi da reza. 


  "Subhanallahi lafiya?" Amal ta tambaya. Ba shiri ta mik'e lokacin da taga jini na bulbula daga yatsn nasa. 


   "Innalillahi! Habib Albi!" Tissue taja da wuri gaban mirron ta shiga tare mai jinin "Omg I'm so sorry sannu" tace dashi a rikice tamkar zatayi kuka da mamaki Afzal ya tsaya yana kallonta shi da ya yanken ma hankalinsa be tashi ba kaman yadda nata ya tashi. Iska take hura masa tana ce mai sannu ba makawa.  


  "Kitten calm down yanka nefa kawai."


  "But yankam ai deep ne Habib Albi sannu" iska ta cigaba da hura masa sannan tajasa izuwa bayi, spirit ta bud'e "Ka rufe idonka zeyi zafi" dariya sosai ta basa "Ce miki akayi rago ne ni?" A hankali ta shiga bulbula masa akan ciwon, wincing kad'an yayi Amal kam sekace ita aka sawa akan ciwo se tashi tsikan jikinta yake. Cike da lalashi tana hura mai iska tana ce mishi sannu ta mishi dressing ciwon ta tasa bandage. Se kallonta yake yayinda wani irin wutan sonsa yake ruruwa a zuciyansa. 


  "Kitten it's okay."


  "It's not Habib Albi baka ga yadda yata jini bane?" hannun nasa ya zame daga nata had'e da rik'o k'aramar kunkuminta seda ya matso da ita kusa da shi "Bade kuka kike shirin yi ba Kitten?"


  "No" ta amsa ciki-ciki mik'awa yayi had'e da kissing soft lips nata, sun d'au tsawon lokaci suna abu d'aya sannan a hankali tayi pulling out. "Thank you Kitten" ya furta yana maida gashin ta baya.


  "What for Habib Albi?" Ta amsa tana zagaye hannayenta a wuyansa. 


  "For everything sweetheart, I can't imagine life without you, Allah yayi miki albarka I love you so much."


  "Ameen Habib Albi I love you most" peck ta masa placing a kumatu "Muje ka huta" d'akin suka koma ta mik'e akan gado tana duba messages nata yayinda ya canza kayan jikinsa da jini yad'an 6ata. Hankalinta gabad'aya ya duk'ufa akan chatting da takeyi da Maamah kawai taji Afzal ya k'wace wayan kafin tace ya bata ya mik'e a jikinta had'e da kwantar da kansa a saitin k'irjinta wane d'an wani yaro. 


  "Habib Albi-"


  "Lets sleep Kitten bacci nakeji."


  "Toh ka tsaya in gyara kaji?"


  "Ni haka nakeso" murmusawa tayi sannan tayi placing mai light kiss acikin gashin kansa yayinda take shafashi a hankali. A haka har bacci ya d'aukesu duka. 


   Sati biyu sukayi sannan suka dawo Nigeria, a ranan da suka dawo Nazeefah ta shirya musu abinci da dama ta kai musu haka Ummi da ma Mami, washegari sukayi sorting out tsaraban kowa suka kai musu, da yammacib ranan ya wuce gidan Nazeefah. Bayan sun k'are dinner sun dawo d'aki ta zaune gefensa akan gado inda take sanar da shi batun makaranta akan cewa in a week time zasu bud'e. 


  "Yes haka Amal tace kekam final semester d'inki kenan ai ko?"


  "Yes Ya Rouhi."


  "Toh Allah nuna mana graduation nakun."


  "Ameen thank you nace ba.." se kuma tayi shiru. 


  "Yes what is it?"


  "Ya Rouhi are you okay with it in d'auko mey aiki? Kaga semester'n nan na neman concentration sosai bazan zo in iya da aiki da shara d'innan ba shine nace idan ka amince na riga nayi magana da wata mata yaranta are ready to work for me and Amal."


  "Itama Amal tace tana buk'atan mey aikin ne?"


  "Bata fad'a ba amma nasan zata buk'ata ai Ya Rouhi ita da course nata yafi nawa wuya ma ai kaga zata fini buk'ata ma."


  "Hakane kam so masu aikin kwana ne ko na jeka ka dawo?"


  "Na kwana ne saboda daga k'auye za'a kawo su bawai anan suke da zama ba."


  "Masu aikin kwana kuma Rabba'atul Bait?"


  "Ya Rouhi nasan me kake gudu karka damu yara ne fah Khaleefah ma ya girmesu d'ayar 16 d'ayar kuma 14 kaga ai baza a samu wata matsala ba in shaa Allahu."


  "Toh zanyi ma Amal magana."


  "Yauwa duk abinda akwai seka sanar da ni muyi making arrangements ya zammana de sun fara aikin tun yanzu ba se an bud'e makaranta ba."


  "Jazakillahu khair Rabba'atul Bait yadda kikeso wa Amal abinda kikeso wa kanki."


  "Ameen Ya Rouhi an zamo d'aya ai yanzu zamu kwanta ko?"


  "Wallahi kaman kin sani a gaje nake."


 "Akwai gajiya ai ko nayi maka tausa tukun?"


  "Baki gaji ba?"


  "Ai bana gajiya when it comes to you" mik'ewa yayi kan gadon ta shiga yimai tausan a hankali tana relieving mai tension.


  *****

   Kwana biyu yayi mata sannan ya dawo gun Amal. 

  Amal fa ba wasa kitso taje aka rangad'a mata k'anana sannan ta sha lalle ja a tafin hannu ta baya kuma akayi mata bak'i irin na zamanin nan mey kyau. Kafin Afzal yazo ta gama girkinta ta bi gidan da turare se k'amshi zallah ke tashi. 


  "Oyoyo Habib Albi" taje tayi hugging nasa da gudu. 


  "Oyoyo my Kitten" sun d'au kusan minti d'aya manne a jikin juna sannan ya d'agota a hankali "Masha Allah kin ganki kuwa?"


  "Nayi kyau?" Ta tambayesa tana wasa da yatsun hannunsa. 


  "Yes Kitten yakamata in biya kud'in wankan nan."


  "Awwn thank you Habib Albi" ciki suka k'arisa suka nufi d'akinsu inda ya rage kayan jikinsa suka haye kan gado "Yau mey aka girka mun Baby?"


  "Your favorite!" Ta sanar da shi. 


  "Spaghetti?


  "Uhumm."


  "Wow! Ya kike toh?"


 "Lafiya k'alau ka baro Nazeefah lafiya?"


  "Lafiya k'alau tace in gaisheki."


  "Ayya ina amsawa jiya ma Mami tana nan ai tazo muka yini mun."


  "Allah sarki ya take?"


  "She's fine" ta amsa se kuma taga yadda Afzal keta kallonta tun d'azu da fari ma tsarguwa tayi kode jan bakinta ya hau kan fuskanta ne?


  "Habib Albi lafiya?"


  "Matso kiji" matsowa tayi kusa da shi hakan be masa ba seda ya aza ta kan cinyansa "Kitten?"


  "Yes?"


  "Anya kuwa?"


  "Anya kuwa mey Habib Albib? Wani abun ne?"


  "Anya babu ajiya na anan?" Ya tambayeta had'e da aza hannunsa kan cikinta wani kunya maras misaltuwa taji ya rufeta "Kai Yaya" nan ta shiga kare fuskanta. 


  "Seriously naga kin k'ara freshness ne ai skin naki se wani glowing yake."


  "Toh Yaya naje k'asa me tsarki ba dole ba ko ka manta kwanana na hud'u kacal daga dawowa daga Saudiyya?"


  "Ina sane kawai de ina tambaya ne."


  "Toh ka kwantar da hankalinka ba komi anan" ta fad'a tare da aza hannunta akan nasa dake manne da cikinta. 


  "Kai Kitten kode 6oye mun kike ne?"


  "A dalilin mey zan 6oye maka Habib Albi?"


  "Toh yaushe rabon ki da kiga period naki."


  "Ni bana son tambaya" ta fad'a tana neman mik'ewa hannunta yayi saurin ja "Ai sai kin amsani."


  "Yaya mana hannu na" saketa yayi a hankali "So answer me."

  

   "Yaya jiya fa nayi wankan sallah."


  "Kitten k'arya kike mun ko?"


  "Yaya na ta6a maka k'arya ne?" Ta maraice fuska. 


  "Toh shikenan very soon nasan seed d'ina zeyi germinating."


  "Muje kaci abinci toh."


  "Yauwa Nazeefah tace in fad'a miki ta sama muku masu aiki tunda kun kusa komawa school kar aikin gida yayi interfering muku da school."


  "Mey aiki kuma Habib Albi?"


  "Yes haka tace."


  "Na mey? Ni bana buk'atan mey aiki da safe kafin in fita school zan iya kammala aiki na, ranan da nake da lectures 7 kuma idan na dawo gida se inyi abu na."


  "Gajiyan baze zo ya miki yawa ba Kitten I think shawaran Nazeefah fa yayi mey aikin zata taimaka miki kinga kafin ki dawo daga school ta gama miki komai kika dawo girki kawai zakiyi ki huta."


  "Habib Albi ni gaskiya bana so."


  "Toh yanzu ya kenan? Ince wa Nazeefah bakiya so? Ai bazata ji dad'i ba tunda har tayi wa mutanen magana kuma tun daga k'auye tace za'a kawo su."


  "Kyansa dama ta tambayeni ko kai kafin tayi musu maganan."


  "Hakane amma ai ita bata d'au zaki k'i taimako ba."


  "Ba wani nak'i bane Yaya kawai ina ganin bana buk'ata ne."


  "Zaki buk'ata fa Kitten keda kike yin tough course aikin gidan zezo yayi miki yawa."


  "Toh shikenan tunda kaima ka goyi bayan hakan."


  "I'm sorry if I'm forcing you into this kinsan halin Nazeefah ba sena fad'a miki ba kina k'i yanzu zata ce bakiya appreciating effort nata ne ta fara k'ananun suratai kawai kiyi hak'uri ki amince shine kwanciyan hankalinmu duka. Bazan 6oye miki ba ko ni banji dad'in yadda seda ta gama komai sannan ta sanar dani ba amma haka nima nayi hak'uri."


  "Hakane kam ba komai zan kirata inyi mata godiya."


  "That's by Babeh let's go eat toh I'm craving for your delicious already." Hannunta acikin nasa suka nufi dining suka ci abinci ba da dad'ewa ba Maghrib ya shiga ita kad'ai tayi nata kasancewar Afzal ya soma fita Masallaci yanzu. 


  Washegari***

   "Ya Babe shiru har yanzu? Cewan Rumaysa daga d'ayan 6angaren. 


  "Wallahi layin Ya Afzal nake ta gwadawa amma bai d'auka nakega suna meeting ne so nike in tambayesa izini kamin in fito."


  "Toh ina jiranki." Kashe wayan tayi 10 minutes later ta sake trying numban Afzal amma still baya d'agawa. Se chan k'arfe uku taga call nasa na shigowa da hanzari ta d'aga. 


  "Babe ina ka ajiye wayanka?"


  "I'm sorry meeting muke se yanzu muka fito ya akayi?"


  "Izini nake son nema zani gidan k'awata."


  "Toh bismillah go ahead you're permitted."


  "Thank you Ya Rouhi."


  "Aha bye." Dama ashirye take key'n motarta ta d'auka kawai ta fice chan gidansu Rumaysa ta wuce inda ta nuna mata 'yan matan. Bayan sun gaisa Rumy ke tambayarta "So wacce zaki d'auka?"


  "K'aramar kai ai babban zata fi mana harka da kyau senu kaiwa Amal babban."


  "Toh Hindu ga Aunty'nki Nazeefah ita zata d'aukeki aiki ke kuma Safiyya zamu kaiki wa amaryarta" kai duka suka gyad'a "kina iya tafiya ko Hindu na?" Cewar Nazeefah "Bari muyi magana da yarki" ba musu ta mik'e ta fice. 


  "Yauwa kaman yadda na fad'a miki wannan itace Aunty Nazeefar itace wacce mukeso ki bamu had'in kai dan fitar da shegiyar da ta aure mata miji."


  "Duk abinda kukace shi za ayi Aunty."


  "Yauwa Sofin gaye ga waya nan Aunty Nazeefah ce tace a sai miki za kuna waya da ita ta ciki koda wasa kuma kar kiyi saving lambarta saboda ba'a san yadda abu ze zo ya kasance ba da kinga lamba me 08102 toh nata ne kin gane?" 


  "Na gane."


  "Good kuma kina yi mata ladabi da biyayya kinji?" Nazeefah ta kar6e Rumaysa "Sunanta Amal amma Aunty zaki na ce mata duk aikin da takeso a gidan kinayi mata shi ba ruwanki da yi mata sata, duk abinda kikeso ki kirani zan baki kina ji na ai?"


  "Eh Aunty."


  "Yauwa zuwa gobe zan zo in d'aukeki da 'yar uwarki in kaiki gidan nata."


  "Toh Aunty."


   "Rumy ta fad'a muku albashinku ko?"


  "Eh dubu goma."


  "Yes sannan naki zanna k'ara miki extra dubu goma akai ko wani k'arshen wata idan har zakiyi mun aiki me kyau zuwa lokacin da zan samu in cimma burina."


  "Toh Aunty godiya nake."


  "Yauwa bayan nan kuma ko k'anwarki ce karki sanar da ita, wannan magana ya rage sirri a tsakanin mu kin gane?"


  "Na gane Aunty."


  "Toh Babe barin koma." Har waje Rumy ta rakata sannan ta dawo ciki.


   Washegari kaman yadda suka tsara Nazeefah tazo ta d'aukesu gidan Amal suka fara wucewa lokacin Afzal ma bai gida ya fita office. Sannu da zuwa Amal tayi musu ta shigo dasu "Bari in d'auko muku ruwa."


  "A'a 'yar uwa (yadda take kiran Amal) karki damu ai daga gida nake wannan ne masu aikin zan d'au k'aramar in baki babban tunda daman ke yayata ce."


  "Kai Nazeefah ai kece babba a gidan nan."


  "Toh nide zan d'au k'aramar Hindu ke kuma babban Safiyya."


  "Toh Safiyya sannu da zuwa:"


  "Yauwa Aunty nagode."


  "Safiyya ban da rashin kunya kinji ko? Yi kinyi bari kin bari."


  "In shaa Allah Aunty."


  "Toh bari zamu wuce gida muma."


  "Toh kin shigo da kayakin ki duka ko?" Amal ta tambayi Safiyya.


  "Eh Aunty" ta amsa. 


  "Toh bari mu raka ku" nan suka rakasu har gun mota bayan sun dawo ciki Amal ta kai Safiyya d'akin data bata wanda zata na kwana aciki. D'aki ne harda bayi aciki ga gado da drawer harda dressing mirror. Yadda ake kunna shower da kuma yadda ake flushing ta nuna mata sannan ta bata waje ta watsa ruwa. 


  Bayan Afzal ya dawo daga aiki ya watsa ruwa ya d'an huta take sanar da shi akan cewa Nazeefah ta kawo mata mey aiki d'azu "Bari inyi mata magana ku gaisa."


   "Ko gobe ma baza mu gaisa bane Kitten?"


  "Toh ai kana fita office da wuri bari de ku gaisa yanzun lemmi speak with her" Nan ta mik'e, tare suka taho da Safiyya tana binta a baya daga baki bakin parlourn ta tsuguna ta gaishe da Afzal cike da ladabi da biyayya, shima ba yabo ba fallasa ya amsa. 


   Washegari bayan Amal ta shirya Afzal office ta dawo ciki ta koma bacci se wajajen goma ta tashi, wanka tayi tasa kaya sannan ta fito da mamaki ta tsaya tana bin parlourn nata da kallo yadda Safiyya ta share tayi mopping, dining ta zarce nan ma ko ina sparkling yake. "Wow!" Ta furta wai ita da take shirin koya mata yadda zata na yin aikin? 


  "Safiyya!" Ta k'wala mata kira. 

  "Safiyya!"


   "Na'am Aunty" ta amsa tana shigowa ta k'ofar kitchen. "Ina kwana?" ta tsuguna ta gaisheta. 


  "Lafiya kin tashi lafiya?"


  "Lafiya k'alau Aunty."


  "Sannu da aiki ga ko ina yayi kyau."


  "Nagode Aunty Tv'n ne banso in goge ba kar in ta6a wani abun."


  "That's so thoughtful of you, zan gwada miki da kaina amma kafin nan kin karya?"


  "A'a tukuna."


  "Toh bari in shirya mana breakfast" nan da nan suka shiga kitchen d'in Safiyya tana tayata, bayan sun gama tayi wanke-wanke sannan Amal ta nuna mata yadda zata na goge TV da stand d'insa. Bayan sun gama Amal ta sallameta ta wuce d'akinta. Tana cikin buga game a wayarta Nazeefah ta sa mata kira nan ta d'aga tare da kashe muryarta yadda ba waje baze jita ba. 


   "Assalamu Alaikum Aunty."


  "Wa'alaikumus salam Safiyya ya kike?"


  "Lafiya Aunty ina kwana?"


  "Lafiya k'alau ya wajen aikin naki? Ba wata matsala ko?"


  "Babu komai."


  "Ta baki abun karin kumallo?"


  "Eh flask d'in ma ta ajiye mun a gaba na wai in d'iba da kaina."


  "Mak'ira kawai, ke kika shirya wa Ya Afzal breakfast ko ita da kanta?"


  "Ita da kanta nace zan tayata tace zatayi da kanta inje in kwanta."


 "Mak'ira mey ta girka masa?"


  "Dafaffen dankali ne da sauc da wani abu kaman nama nama aciki."


  "Lallai aikin ki na kyau kwanan nan zamu fara aikinmu akanta kede ki tabbata kina mata duk wani ladabin da ya kamata."


  "Toh Aunty."


  "Yauwa karki manta kina goge lamba na daga call logs naki duk sanda muka gama waya."


  "Toh Aunty ki gaishe mun da Hindu."


  "Tana bacci idan ta tashi zan sanar da ita sai anjima."


  "Yauwa nagode" da haka sukayi sallama. 






RANA D'AYA!

#RD


Love... King Miemiebee👄✨

[13/08, 09:37] ‪+234 907 483 8352‬: 🎀🎀🎀                 🎀🎀🎀

                🎀❣🎀

                   ❣❣


  💦💦                      🍃🍃🍃          

           *RANA D'AYA!*

  💦💦                      🍃🍃🍃

  August, 2018

 beeenovels.blogspot.com


     _Written by Miemiebee👄_



   *PAGE 3⃣1⃣*



       

    Nazeefah de bata da aikin da yafi kiran Safiyya kullum tana tambayarta mey Amal ta girka wa Afzal, shin idan ya dawo daga aiki mey sukeyi, suna yawan fita ne ko kuwa zama suke a gida suna wasa? Komai so take tana ji haka kawai tayita tada wa kanta hankali. 

  Kwana bibbiyu Afzal ya cigaba da yima kowaccensu, bada dad'ewa ba aka bud'e makaranta. Ranan da kwanan Amal ne kuma tana da early morning lectures tare suke shiri su fita se yayi dropping nata kafin ya wuce office haka ma idan kwanan Nazeefah. 


   Yau Amal da Afzal suka cika wata d'aya da aure se kuma Allah yayi ranan ya fad'o a kwananta se rawa jikinsa yake he can't wait to go back home. Itama Amal bata mance da wannan muhimmiyar rana ba, morning lectures nata na k'arewa wajajen sha d'aya driver'n da Afzal ya mata hiring ya dawo gida ta shiga kitchen yayinda Safiyya ke tayata aiki. Abinci kala-kala suka had'a da juices abin se wanda ya gani ga fruit salad ba abinda babu dam suka cika kan dining table d'in da kayan abinci. Dab ta fito daga wanka around three kenan Afzal ya buga mata waya. 


  "Halo my adorable Kitten?" Ya fad'a bayan da ta d'aga. 


  "Yes Habib Albi ya kake ya office?" Ta amsa. 


  "I'm soo missing you Baby" ya sanar da ita. 


  "I miss you too Habib Albi ai ka kusa dawowa."


  "Wani kusa? Kina ji wai muna da meeting."


   "Meeting kuma? Se goma zaka dawo kenan?" Ta tambayesa tamkar zatayi kuka. 


  "Ai nima ba iya jira zan ba I miss you so much Babe."  

  

   "I miss you even more darling amma ya zamuyi?"


  "K'arya nayi nace musu bakida lafiya zan kaiki asibiti so I'll be back in a jiffy."


  "Awwwn Habib Albi se kazo toh Allah ya kare."


  "Ameen Kitten I love you."


  "I love you too darling" ta fad'a had'e da katse wayar. Nan da nan ta ciro wata had'ad'd'iyar purple blouse ta sanya da wani bak'in straight skirt ba k'aramin amsan ta skirt d'in yayi ba yadda yabi perfect curves nata. Zama tayi gaban mirror ta rangad'a kwalya yau harda yin lining saman idonta tasa mascara ta taje dogayen eye lashes nata sannan tasa maroon janbaki ba k'aramin kyau tayi ba gashinta da tayi stretching jiya a salon ta jik'a da mai sannan ta taje ta kwantar a jikinta ta feffeshe da turare tana cikin sanya d'ankunne se taji k'aran motan Afzal da hanzari ta k'arasa tasa bracelets nata ta d'aura agogo ta fita taransa. Dai-dai bakin k'ofan ta tsaya yadda yana bud'e k'ofan ze fara cin karo da ita. 


  Hannunsa a cike ya fito daga motan d'aya rik'e bouquet na flower d'aya kuma da ledan da ya yo mata shopping aciki. Yana bud'e k'ofan sega Damsel tasa tsaye tana mar murmushi. 


  "Dayyummm!" Ya furta yayin da yakasa koda kyafta ido se kallonta yake kaman ze hambuleta tsabagen kyan da tayi. 


    "Happy one month anniversary Habib Albi" ta sanar da shi ledan ya ajiye a kan wani stool dake kusa da bakin k'ofan sannan ya mik'a mata flower'n "Happy anniversary to you too Baby I love you" amsa tayi sannan yayi hugging nata yana mey shak'an daddad'an k'amshin turaran jikinta, sun dad'e a haka sannan ta raba hug d'in a hankali. 


  "You're looking.. you're looking fabulous Kitten, gosh you're so beautiful" ya sanar da ita tun daga k'ark'ashin zuciyansa wani sa'in har mamakin kalan kyawawan yaran da Amal zata haifa masa yake tabbas idan zasu bi ta ba k'aramin kyau zasuyi ba. 


  "Thank you Habib Albi thank you for the roses too."


  "Don't mention Darling" jakarsa ta amsa ya d'aga ledan suka k'arasa d'aki inda ya rage kayan jikinsa yabar nickers zalla. 


  "Baka ci abinci ai bako?" Ta tanbayesa tana zaune a gefensa. 


  "Bayan kince kar naci se kuma in ci Kitten? Yunwa nakeji kaman zan mutu."


  "Kar ka mutu kaji? Taho muje kaci abinci."


  "Wow" kawai yake furtawa lokacin da suka isa kan dining d'in kuloli sekace fiest za'ayi se sallama suke masa ga wani chocolate cake babba da aka rubuta caption na "Happy Anniversary Habib Albi" akai ajiye a gaban sa. 


  "Duka wannan kika girka Kitten?"


  "Yes Habib Albi nida Safiyya."


  "Wow I'm impressed the cake is so beautiful."


  "Thank you Habib Albi shi catering nayi" ta fad'a had'e da yankan kad'an tayi feeding nasa da shi. "Mmnm" ya furta yana santi "Chocolate cake."


  "Your favorite right?" Kai ya gyad'a eagerly "Shin mey da mey da mey Kitten d'ina ta tanada mun haka?" Ya tambaya se tsinkewa miyaun sa yake. 


  "Kai de bud'e kaga" flasks d'in ya shiga bubbud'ewa daga na pepper soup na kifi sena ganda se fried rice da coleslaw ga su samosa dasu spring rolls da ta sa akayi mata bayan nan ga apple juice da su aldeb da zo6o abun de se wanda ya gani. 


  "Kitten isn't this too much?"


  "Ka manta kai d'an gata na ne?" bi tayi one-by-one tana d'iba mai a plate sannan tayi serving nasa. Yaci wai sam shi seda ita haka tayi joining nasa. A kan cinyarsa ya zaunar da ita haka ya bata yaci har suka cinye inda ta kira Safiyya da ta tattare wajen seta d'iba duk abinda ya mata itama taci idan ta gama se tayi wanke-wanke. Safiyya se washe baki take taga pepper soup har kala biyu ga cake. 


   D'aki su Afzal suka dawo inda da k'yar Amal ta sanya sa ya watsa ruwa wai sam shi seda ita zeyi, ita kuwa tace bazata goge wannan kwalyan nan duka ba. Bayan ya fito ya sanya nickers nasa sannan ya iso ya zauna a gefenta "Here this is for you Wifey" ya fad'a yana mik'a mata ledan d'azu cike da jin dad'i ta amsa ta shiga fiddo da kayakin da suke ciki. Waya taga sabuwa pil k'irar Iphone X aciki, seda wasu shoes and bags kala biyu da wani purple doguwar riga voile me combination na colors a jiki wanda ko ba a tambaya ba ansan mey d'ankaren tsada ne k'arshe kuma seda wani photo album wanda ciki hotunansu ne da dama wanda suka d'ad'd'auka a waya yakai aka wanke masa. 


  "Omg Habib Albi this's too much" ta d'ago kai tana kallonsa yayinda idanunta suka ciko da hawaye tsan-tsan farin ciki. 


  "Oh Kitten not again" yayi maganan yana matse ta a jikinsa, kukan farin ciki ta shiga yi yayinda ta kasa 6oye farin cikinta. "Please don't ruin this beautiful moment Love" ya buk'aceta yana shafa gashin kanta sannan a hankali ya d'ago ta daga jikinsa yana share mata hawayen nata da babban yatsansa. 


  "I'm sorry I just don't know how to react Habib Albi banida bakin yi maka godiya, wallahi ban san ta ina zan fara ba, I know thank you won't compensate for this but thank you so much Habib Albi, Allah saka da alkhairi ya k'ara maka bud'i I love you soo much."


  "Masha Allah Kitten ameen kuma nagode, I love you even more. I don't think I can survive without you, in fact my life has no subtle in the absence of your love Amal, duk yadda nakeso in nuna miki how deeply in love I am with you bazan iya ba because no words can describe the love I have for you, not even feelings could show Kitten, one thing I'm sure is that there's no ME without a YOU" ya k'arisa yana mey rik'o k'ananun hannayenta cikin nasa tare da placing gentle kiss akai. 

   Hawaye sosai Amal take dan farin ciki sau dayawa takan zauna ta tambayi kanta shin mey ta ta6ayi wa Allah da ya bata miji mey kyautatawa kaman Afzal, mijin da burinsa bai fi yaga ya sanya ta farin ciki, mijin da be ta6a k'untata mata ba a iya zaman da sukayi, mijin da se abinda take so yakeyi mata. Gani take kaman bata cancanci mutum kamansa ba, shin anya zata iya rayuwa idan ba shi?


  "I can't leave without you Habib Albi wallahi I can't" ta rushe da kuka rungumarta yayi yana shafa gashinta a hankali sun d'au tsawon lokaci a haka sannan a hankali ya d'agota bayan da kukan nata ya lafa "Cry nomore okay? I love you so much" Kai ta gyad'a tare da kwantar da kanta a k'irjinsa "I love you more Habib Albi."


  ****

  Bayan sallan Isha suka shirya tsaf suka fice wajen shan ice cream se hoto Afzal yake tayi mata tun tana ce mai ya bari bata so chan itama da abin ya isheta ta d'au sabuwar wayarta ta shiga d'aukansa tana mai video, shak'atawa suka tayi abinsu suka bar Safiyya kad'ai a gida. Ita kam ta samu TV se fata take kada su dawo ita bata k'i ma su kwana a waje ba saboda tayita kallon series abinta. Haka har wayanta ya gama ringing bata ji ba se a karo na biyu tsabagen yadda hankalinta ya duk'ufa kan kallon.


  "Assalamu Alaikum Aunty ina yini?"


  "Ina kika ajiye wayanki ina kiranki Safiyya?" Nazeefah ta kurareta. 


  "Kiyi hak'uri kallo nakeyi."


  "Ya uwar d'akin naki? Meya faru yau?"


  "Hmm Aunty baki san meya faru ba."


  "Gayan mey?" Ta tambaya cike da rashin hak'uri. 


  "Kinga abincin da Aunty ta girka wa Uncle kuwa? Wallahi sunyi kala ashirin pepper soup babu irin wanda batayi ba ga juice d'innan da su meat pie."


  "Kai! Wai meke faruwa?"


  "Wallahi wai ani.. ani-- ani wallahi na mance sunan abun amma tace wai yau ani wani abinsu ne shiyasa ta mai wannan girke-girken kuma baki ji yadda komi yayi dad'i ba."


  '"Yar k'auye anniversary? Yau anniversary'nsu?"


  "Yauwa wallahi shi! Anibasari haka tace."


  "Innalillahi!" Ta furta cike da tashin hankali yayinda wani irin kishi da haushin Amal taji ya rufeta kup, shekaranta uku a gidan Afzal amma bata ta6a celebrating anniversarin su ba sega Amal da ta shigo na wata d'aya tayi hakan taya Amal zata fita kaifin tunani? Inaaaa baze yuwu baa! "Yanzu ina suke?"


   "Sun fita tun d'azu tun bayan sallan Isha."


  "Basu dawo ba har yanzun?" Ta tambaya had'e da zaro ido tana duban agogon bangon d'akinta. 


  "Eh."


  "K'arfe goma fa! Ina sukaje ta fad'a miki?"


  "Cemun kawai tayi zasu fita."


  "Innalillahi wallahi hawan jini ya kusan kamani 'yar nan zata sace mun miji, na shiga uku ke wawiya meyasa baki k'ok'k'ona mata girkin nata ba?"


  "Bata bari na ko kusa da cookan nata iyaka in yanka mata su albasa ko in daka mata maggi."


  "Wawiya ki bud'e kunnenki ki saurareni kina jina?"


  "Eh Aunty."


  "Anytime ta sake saki yi mata jajjage ko kuwa daka maggi kiyi excess ki k'ara naki akai yadda abincin zeyi rad'au yayi yaji ya rud'awa Ya Afzal ciki ya kasa ci kinji? Haka ne kawai zesa abincinta ya fita masa a rai."


   "Aunty toh ai zata gane."


  "Banza ce mata zakiyi bakiji adadin da tace ki d'iba ba."


  "Amma fa ita take d'iba ni kawai bani take in daka ko in yanka."


  "Ki jini, nan gaba idan kuka shiga kitchen tun kafin ta d'iba mikin kice zaki d'iba da kanki seki tambayeta nawa, anan seki k'ara da naki akai idan ta tambayeki kice baki ji da kyau bane kinji?"


  "Toh Aunty an gama."


  "Yauwa bayan nan se meya sake faruwa kingan shi ya saya mata wani abun?"


  "Toh wallahi ban san wannan ba dake ina cikin d'aki ya taho."


  "Bance kullum kina jin k'aran motansa ki fito ba kiga meya shigo da shi?"


   "Aunty na shiga ba ne."


  Aikin kenan kullum mstww wallahi ina da tabbacin ya mata sayayya shima soko d'aya ya cigaba se 'yar shuwan nan ta tsiyatar da shi tukuna yanzu kinsan mey nakeso dake?"


  "Sekin fad'a."


  "D'akinsu zaki shiga ki duba mun kiga koya sai mata wani abun."


  "Aunty-"


  "Bade tsoro kikeji ba?"


  "Aunty idan suka dawo ina cikin d'akin fah?"


  "Wawiya idan baki cire tsoron nan ba  ya zaki yi mun aiki toh? Ko bakison extra dubu goma akan albashinki k'arshen watan nan?"


  "Ina so."


  "Good jeki lek'a mun d'akin nasu."


  Mik'ewa tayi ta nufi d'akinsu Amal cike da fargaba ta gwada bud'e k'ofar sede a kulle ta tarar. Koda wasa Amal bata ta6a fita bata kulle musu d'aki ba not that tana zargin Safiyya na sata se don gudun abinda shaitan ze iya raya wa mutum wataran. "Aunty a rufe" ta sanar da ita. 


  "A rufe de!"


  "Eh wallahi."


   "Amma 'yar nan shegiya ce wallahi barta watan cin ubanta ya kusa kamawa wallahi da ikon Allah sena koreta daga gidan nan Ya Afzal is mine alone." Nan ta kashe wayan cike da takaici, safa da marwa ta shiga yi a d'akin nata yayinda hankalinta ya mugun tashi ji take kaman zatayi hauka. Wai taya ma shawaran celebrating anniversary be ta6a bugo mata akai ba? Shin hakan na nufin Amal ta fita iya tarerayan miji? Mstw! Wayanta ta bud'e ta shiga date tana neman yaushe 25th zeyi itama anniversary'n ta ya kewayo, dubawa tayi taga next week ne, nan ta shiga irgawa tana fatan Allah yasa ranan ya fad'o a kwanan ta, da ikon Allah kuwa se ya fad'a a kwanan nata. Toh ma auren nasu shekara uku da wata nawa ne? Ana March yanzu sun yi auren a December that is 3 years three months, perfect! 


   Jira tayi har ranan da anniversay'n nasu ya kewayo itama ta shirya gaggarumin girki, ba abinda bata had'a ba sauran abubuwan ma catering tayi dam ta cika kan dining itama. Tasha lalle da kitso ba dama ta sanya sabon d'inki. K'arfe biyar da rabi Afzal ya baro gidan Amal zuwa na Nazeefah, tun daga bakin gate k'amshin turare ya ke tashi gashi tunda ya gwada mata yadda ake sa turaren wutan ta koya takeyi itama. Tun daga gun parking lot taje ta taresa. 


   "Welcome home Ya Rouhi" tace da shi had'e da pecking nasa a kumatu. 

   "Wannan kwalya fa Rabba'atul Bait?" ya tambaya yana kallonta admiringly ba k'arya tayi kyau gashi unlike Amal da bata yin heavy makeup Nazeefah idan ta tashi yin kwalya yi take wane makeup artist ce ta zana mata fuska. 

  

   "Naka mana Ya Rouhi" ta amsa tana amshe mai jakansa. 


  "You look awesome Babe."


  "Thanks Baby" nan suka k'arisa ciki "Wai wai wai kulolin nan fah daga ina?" Ya tambaya yana bin dining table d'in da kallo. 


  "Happy anniversary Babe."


  "Wow!" Kawai ya iya furtawa yayinda kansa ya rud'e "Happy anniversary Dear" ya miyar mata had'e da brushing light kiss a lips nata "But wait I thought a December mukayi aure yau kuma March ko ba haka ba?"


   "Yes Ya Rouhi yau 25th march which marks 3 years 3 months of our marriage ko ka manta?"


   "Yeahh right" yayi reasoning da ita "Thank you Babes."


  "Muje ka watsa ruwa se mu ci abinci ko? Ina ba a k'oshe kake ba?"


  "Ai ko a k'oshe nake ya zama dole inyi creating space wa delicious d'in Rabba'atul Bait d'ina" sosai taji dad'in amsansa. A tare suka k'arisa d'akin nan da nan ta had'a mishi ruwa ya shiga ya watsa fitowansa ya nufi wardrobe dan ciro wandon da ze sanya se cin karo yayi da wani k'aramin pack da akayi wrapping da wrapping sheet cike da mamaki ya d'aga ya bud'e wani had'ad'd'en designer agogo ya tarar mey d'ankaren tsada aciki, gefensa kuwa wani happy anniversary card ne daya sha k'amshin turare. Da murmushi kwance a fuskansa ya karance, a ko da yaushe godiya yake yi wa Allah da ya shiryar mar da Nazeefar sa har sukayi sorting out differences nasu suke zaman lafiya yanzu. Baya jin ze iya rayuwa ba ita, a hankali soyayyarta ya ginu a zuciyansa.  A da be ta6a kawowa koda kusa da mafarki cewa wataran ze auri mata biyu ya zauna da su kuma ya sosu duka ba se yanzu da hakan yake faruwa. Ya sani son Amal daban yake a zuciyansa amma kuma Nazeefah na da wani gur6in da ta mamaye a zuciyansa, gur6in da ba me iya mamayewa se ita. 


  "Rabba'atul Bait?" Ya kewayo yana kallonta cike da soyayya. 


  "Yes Ya Rouhi" ta amsa had'e da takowa zuwa inda yake. 


  "Is this for me?" 


  "Yes Ya Rouhi Happy 3 years anniversary I love you so much" 'yar kunkuminta ya kama had'e da matso da ita kusa dashi sannan yayi owning lips nata kissing her so gently with thousands of emotions and gratefulness. A hankali yayi pulling out "Thank you Nazeefah, this means alot to me Allah miki albarka."

 

  "Ameen Ya Rouhi you deserve alot morethan this."


   "Kin san ina sonki ko?" Kai ta gyad'a masa a hankali tana mai murmushi "Ko zaka sake sanar dani?"


   Murmushin ya miyar mata sannan yace, "I love you Nazeefah ni kaina mamakin kalan soyayyan da nake miki nake ban ta6a kawowa kusa da raina that I'll one day love you like I'm doing, Allah ne kad'ai sheda akan kalan soyayyan da nake miki, I just pray it continues to grow and never fades away, Allah bar min ke Rabba'atul Bait ya miki albarka kuma."


   "Ameen Ya Rouhi I love you even more gani nake kaman idan ba kai bazan iya rayuwa ba. Ka sani ka riga ka zama 6angare daga jikina wanda idan aka cire bazan iya rayuwa ba, please never leave my side."


   "We'll forever remain together Nazeefah in shaa Allah har mu mutu sannan kuma mu cigaba da soyyayar namu achan Jannah where we'll reunite." 


  "In shaa Allah Ya Rouhi. I'll choose you a million times if I were given the chance to, muje kaci abinci ko?" Kai ya gyad'a mata sannan ya zaro wandonsa ya sanya dining d'in suka k'arisa inda tayi serving nasa sannan ta zauna gefensa tana masa hirar soyayya har ya gama ci. Sosai ya yabawa girkin nata ranan. Washegari tun k'arfe sha biyu ya dawo daga office ya watsa ruwa se wajajen uku Nazeefah ta dawo daga school sannu da zuwa yayi mata ya sirka mata ruwa ta watsa sannan yajata dining da taci abinci. Bud'e flask da zatayi kawai ta tarar da kwalin waya ciki k'irar Iphone X sak irin na Amal fari itama. 


  "Omg! Ya Rouhi!" Tayi exclaiming had'e da d'agowa "Ya Rouhi an iX!"


  "Yes Rabba'atul Bait this's my anniversary gift to you I hope it's not too late?"


  "It's never too late Ya Rouhi thank you soo much Allah k'ara bud'i I love you endlessly."


  "I love you too darling so ki shirya muje muci abinci nima yunwa nakeji." Nan da nan suka shirya suka fice Nazeefah dad'i kaman ze kasheta sede jikinta se bata yake Afzal ya sai wa Amal itama iphone X d'in, da ta tuna da hakan se ranta ya 6aci she can't wait ta fitar da ita daga gidan. Washegari bayan Afzal ya dawo daga office ya shiga tattara wasu documents nasa da ze buk'ata idan ya tafi gun Amal kasancewar yau kwanan Nazeefah ya k'are. Tunda Nazeefah ta shigo d'akin ya karanci mood nata sam ba walwala a tattare da ita. 


  "Rabba'atul Bait?" Ya kirata. 


  "Uhmm?" Ta amsa had'e da d'ago kai tana kallonsa a maraice. 


  "Lafiya?" Ya tambeyeta kai zalla ta gyad'a mar sede be yarda ba yana gama tattara documents nasan ya sanyasu cikin briefcase nasa ya k'arisa gefenta ya zauna. "What's going Dear?"


  "Ya Rouhi..." kawai seta rushe da kuka cike da tashin hankali ya rungumeta a jikinsa yana shafa bayanta a hankali yana bata hak'uri kukan ta cigaba da yi chan da kukan nata ya lafa ya d'agota yana share mata hawayen nata. "Ya isa kinji?" Kai ta gyad'a masa a hankali sannan ya tambayeta meya faru a cewan shi gabad'aya mutuwa akayi mata. 


  "Ya Rouhi I can't do this anymore."


  "Talk to me Nazeefah I'm here."


  "Ya Rouhi muje asibiti."


   "Why? Meya faru? Bakida lafiya ne?" Yayi saurin jero mata tambayoyi. 


  "Ya Rouhi shin baka tunanin ko ina da wata matsala?"


  "Matsala kaman ya kenan Nazeefah?"


  "I don't think I can conceive (bana jin zan iya haihuwa.)"


  "Subhanallahi meyasa kika ce haka?"


   "Ya Rouhi it's been three years."


   "Se mey? Meya kawo maganan nan?"


  "Ya Rouhi k'awayena da akayi auransu bayan namu duk sun haihu wasu kuma suna hanya amma ni shiru ko miscarriage ban ta6a yi ba, yanzu Asma'u ta kirani wai she's pregnant Asma'u da last two months mukayi bikinta" se ta fashe da wani kukan. Hugging nata yayi a hankali yana mey cigaba da bata hak'uri, sosai ta basa tausayi be saketa ba seda ya tabbata kukan nata ya lafa. 

  

  Fuskanta ya rik'o cikin hannayensa a hankali ya fara ce mata, "It doesn't matter Rabba'atul Bait it doesn't matter saboda wanda kika rigasu yin aure sun riga haihuwa ko makamancin hakan remember kowa da lokacinsa a duniyan nan, we weren't born together, we shall die alone and so shall live our lives differently. Kisa a ranki kema naki lokacin na nan zuwa kuma koda ma baki haihu mun bama ni banida matsala da hakan, dai-dai da RANA D'AYA Ummi bata ta6a cemun meyasa taji shiru ba har yanzu saboda tasan shi haihuwa yin Allah ne yau shekaranta nawa ita da Abba amma ta ta6a haihuwa ne?" Kai ta kad'a a hankali "Good kuma Abba yak'i ta don hakan ne? Har yanzu suna tare and deeply in love so ki kwantar da hankalinki bazan ta6a k'in ki ba wai don baki haihu mun ba a gidan nan kuma duk wanda ya goranta miki da hakan zan tabbata na mishi ba dad'i ke bakisan matsalar ma ze iya yuwuwa daga ni bane?"


  "Ai kaima kasan ba daga kai bane Ya Rouhi ba haka ranan wata tace mun  wai dan bana haihuwa ne ka k'ara aure ba, I'm very sure kwanan nan zamuji Amal tana d'auke da cikinka."


  "Subhanallahi! Don't you ever say that Rabba'atul Bait kin de ji rantsuwa ko? Wallahil azeem ban auri Amal wai saboda ke bakiya haihuwa ba, Nazeefah ban ta6a d'aukan rashin haihuwan mu a matsayin damuwa ko matsala a zamantakewan auren mu ba kuma bazan ta6a ba saboda nasani haihuwa yin Allah ne. Kuma da kike maganan kwanan nan za aji Amal na d'auke da juna biyu se mey? Ai d'an Amal kaman d'anki ne kaman yadda kema d'anki yake matsayin nata. Ke baki san duk mun zama abu d'aya ba yanzu? Kuma ki sani dan Amal ta haihu kafin ke doesn't mean anything, it won't change the fact that kece Rabba'atul Bait d'ina and that I love you so much. Saboda haka nakeson ki kwantar da hankalinki mu cigaba da addu'a Allah kawo mana nagari masu albarka ko bakisan sometimes Allah yana hana bawa haihuwa bane saboda ya ga yaron ze zo ya zame mai matsala?"


  "Na sani Ya Rouhi."


  "Toh sekiyi aiki da hakan kisa a ranki koda baki haihu ba bawai Allah ya k'i ki bane inda haihuwa wani abu ne da duk duniya ba wanda ze kai Aisha R.A yawan yara amma kuma mey? Ko miscarriage bamu ta6a jin tayi ba haka kad'ai ya isa ya kwantar miki da hankali Rabba'atul Bait."


 "Thank you so much Ya Rouhi I'm so lost without you, wallahi bansan ya rayuwata zata kasance idan ba kai ba, ban ta6a neman abu na rasa a k'ark'ashinka ba please forgive me if I've every wronged you." Ta fad'a jikinsa tana kuka, rungumarta yayi yana shafa bayanta a hankali. 


  "It's okay Darling kibar kukan haka kinji? Ita kuma Asma'au Allah ya inganta ya raba lafiya."


  "Ameen Ya Rouhi."


  "Smile toh in san ranki ba a 6ace yake ba." Ya fad'a had'e da d'ago ta. Murmushin ta sakar masa kad'an "That's my girl bari in gama shiri toh."


  "Zaka koma gun Amal ko?"


  "Eh."

  

  "Akwai abinda kake so in tayaka da shi?"


  "Kawai ki daina damun kanki bana son in sake jin kina maganan rashin haihuwar ki a gidan nan kinji?"


  "In shaa Allah Ya Rouhi yauwa se kud'in fees na Islamiyya na kasan mun shiga sabon term dukda yanzu ba kullum zanna samu ina zuwa ba saboda boko."


  "Alright zan miki transferring shikenan ko akwai wata matsalar?"


  "Babu bayan nan thank you."


  "Don't mention" tayasa gama shiri tayi sannan ta rakasa har waje ta dawo ciki bayan ya sallameta. 


   ***

  Kasancewar Nazeefah ta cika masa ciki da abinci koda ya isa gidan Amal be buk'aci abinci ba se chan wajajen tara, serving nasa tayi ta zauna a gefe kasancewar macaronin be gameta ba yau. Cokali d'aya ya kai baki ya harar take. 


  "Subhanallah Habib Albi!" Tayi exclaiming a rud'e. Goran ruwan dake gefensa kawai ya bud'e ya shiga kwankwad'a seda ya kusan shanye duka ya cire. "Habib Albi lafiya?"


  "Kitten mey kikasa a abincin nan haka?"


  "Kaman ya mey nasa kuma Habib Albi? Wani abu ne?"


  "Kinji gishiri da barkonon da yake ciki? Baki san bana son yaji bane?"


  "Barkono da gishiri kuma Habib Albi?" Ta tambayesa da mamaki a iya saninta attarugu biyu tasa gishiri kuwa kad'an maggi ma tafi bawa k'arfi a girkin, mey Afzal yake cewa toh?


  "Yes" ya jaddada mata tare da k'arar da ruwan goran plate d'in taja don d'anawa sede be barta ba yayi sauri yaja "Don't mind bazaki iya tasting ba."


  "Wallahi attarugu biyu kacal nasa."


    "Maybe yana da zafi ne."


  "Toh gishirin fah? Har dana kusan sauk'ewa ma fa na d'ana kuma banji yayi rad'au ba please ka bani in ta6a inji." Plate d'in ya tura mata spoon d'aya takai itama ta harar gora ya mik'a mata da wuri nan ta kur6e itama. "Kinji?"


   Mamaki ne ya cikata shin ya akayi haka? Abincin se kace an d'ibo ledan gishiri ne aka juye a ciki ga wani d'an banzan borkono "Habib Albi I'm so sorry wallahi ban san ya hakan ya faru ba believe me har dana kusan sauk'ewa ma na d'ana and everything was okay ka kira Safiyya ka tambayeta kaji."

  

  "Haba Kitten me yayi zafi harda tambayan Safiyya? It's okay kinji? Karki damu ina Safiyya kirata tazo ta zubar da abincin don ko almajirai ban jin ya dace a basu abincan."


  "Habib Albi dan Allah kayi hak'uri I'm very sorry."


  "Ohh Kitten" yayi maganan had'e da dafe hannunta dake ajiye kan table d'in "It's really okay just be careful next time okay?" Kai ta gyad'a hankali har cikin ranta bata ji dad'in hakan ba, sam ta rasa ya akayi hakan ya faru koda wasa kuma bata kawo a ranta wai Safiya zata iya zuba mata borkono da gishiri cikin girki ba. 


   "In dafa maka indomie toh?"


  "Karki damu."


   "Habib Albi kayi fushi dani ne?" Ta tambayesa tamkar zatayi kuka. 


  "Meyasa zanyi fushi dake Kitten kinsan mey?" Kai zalla ta kad'a mar. "Sanya hijabinki muje muci abinci a waje."


  "Hab-"


  "Shhh not a word" da kansa ya kira Safiyya ta zubar da abincin sannan ya sanar da ita zasu fita. Suna fita ta d'au wayanta ta kira Nazeefah a karo na farko ta d'aga. "Aunty ina yini?"


  "Lafiya ya kike?"


  "Lafiya k'alau Aunty yau baki san meya faru ba."


  "Meneh?"


  "Hmmm abinci Aunty ta ke girkawa da ta shiga d'aki na saci idonta na shiga kitchen d'in na barbad'a borkono da gishiri akai gashi yanzu Uncle ya dawo ya kasa cin abincin k'arshe ma cemin yayi in zubar."


  "Kai Safiyya!" Tayi exclaiming cike da jin dad'i. 


  "Wallahi Aunty."


  "Wow kinci kyauta, aikinki yayi kyau yanzu ina suke?"


  "Naga sun fita amma de kam beji dad'i ba da be tarar da girki mey kyau ba har a fuskansa naga hakan."


   "Haka nakeso ki cigaba da gashi Sofin gaye niko na miki alk'awain sabon atamfa harda d'inki."


  "Godiya nake Aunty."


  "Yauwa se anjima aikinki na kyau" da haka sukayi sallama. 


  *****

    Haka tun daga ranan sede Amal batayi girki ba se Safiyya ta zagaya ta zabga mata gishiri ko yaji aciki gashi koda wasa Amal bata ta6a zarginta ba saboda yadda ta amince da Safiyya ta rik'eta da zuciya d'aya bayan nan ga yadda it Safiyyan da kanta take nuna mata girmamawa da k'auna. Gashi kaman dagaske duk sanda girkin ya 6aci ta rink'a nuna damuwa. Abun daya sake d'aurewa Amal kai shine se idan Afzal ze zo mata ne girkin yake tashi 6aci idan ba haka ba girkinta me kyau takeyi idan baya nan amma da zaran ya dawo se gishiri da borkono su fara zarcewa. Abu kaman wasa seda Afzal ya ya tattare borkono da gishirin ya kulle a storeroom, attarugu kuwa ya kyautar don kar girkin nata yana 6aci sede aikin banza yayi. Muddin Amal tayi mai girki toh se gishiri da borkono yayi yawa. Sosai abun ya d'aure masa kai. Amal kam har kaman ta fara samun ta6in hankali ne tsan-tsan tashin hankali. Ba aikinta se kuka a gidan, ace wai yanzu Afzal nata baze iya cin girkinta ba? Hakan ba k'aramin k'ona mata rai yake ba. Gabad'aya ta fita daga hayyacinta barin ma yanzu da Afzal ya fara zancen hanata yin girki kwata-kwata don tun baya nuna damuwa abun ya fara damunsa. Ya rasa gane meke faruwa. Tunani ya fara kode iskokai ne suke mata wasa da hankali? Sede be san ta ina ze fara sanar da ita hakan ba, shi kansa ba wai ya amince da hakan bane, be ta6a ganin mace mey son addini kaman Amal tasa ba har taya iskokai zasu ci nasara akanta? Kullum suka fita seta tuna masa yayi addu'an barin gida haka idan suka dawo, na shiga bayin nan bata wasa da shi ko ruwan d'umi zata zubar setayi istihaza toh tayaya aljanu zasuyi nasara akanta? Sede kuma ba wanda yafi k'arfin jarawaba. 


   Kuka take sosai tana rantse mishi akan cewa lallai-lallai bata sa gishiri da attarugu ko d'igo ba cikin girkin amma ga abincin nan rad'au da uban borkono. Yau kusan sati biyu kenan suna abu d'aya. 


   "Kitten it's okay kibar kukan haka."


   "Habib Albi please believe me."


  "I do believe you Kitten I do" ya amsa yana share mata hawayenta amma ina se zuba sabi suke. 


  "Wallahi ban bud'e storeroom d'in na ciro gishirin ba kana iya zuwa muje ka gani ko kuwa ka tambayi Safiyya, a kulle d'akin yake wallahi ban bud'e ba" hannunsa ta kama da niyyan jansa storeroom d'in akan yaje ya gani sede yayi saurin tsayar da ita ta hanyan rik'e ta. 


   "Shhhh it's okay it's okay" ya fad'a yana k'ok'arin calming nata. "Calm down okay? I believe you, I do believe you Kitten nasan baki bud'e d'akin ba amma ai kinji amount na gishirin da yake cikin abincin ko?"


  "Wallahi ban sa gishiri ba Yaya."


  "I know Kitten and I do believe you, kinsan mey nake so da ke? Ki huta na kwana biyun nan kar ki sakeyin girki duk abinda kikeso zan siya miki ko kuwa Safiyya ta girka miki amma ke karki sake aza tukunya a gidan nan hala stress na school ne yake damunki you need to rest."


   "Har zuwa yaushe Habib Albi? I don't need to rest ba hauka nake da shi ba wallahi ban sa gishiri cikin girkin nan ba you have to believe me tunda ka tattare gishirin ka rufe a store ban sake yin girki da shi ba, taya zakace kar in sake aza tukunya a gidan nan Habib Albi?"


  "It's just for some time Kitten please stop crying" Ya amsa yana share mata rushing tears nata had'e da rungumarta "Kiyi hak'uri kibar girkin na kwana biyu until everything is okay kinji?" Jikinta ta janye daga nasa "Kai kuma fa Yaya? Wa ze na maka girki? Wa ze na dafa maka abinci? Shikenan bazaka sake cin girki na ba?"


  "Wayace bazan sake cin girkin ki ba Kitten? It's just for the mean time okay? Zan na ci a restaurant kafin nan kin huta kema I'm sure stress ne ya miki yawa."


  "Yaya wani irin stress? Wallahi ba wani stress dan Allah kar ka hanani yi maka girki I beg you please Yaya" kuka take sosai tana rok'ansa. Hannayensa ya kama acikin nata. 


  "Kitten dan Allah kibar kukan nan haka bawai hanaki yi mun girki nake shirin yi ba its just for the meantime."


   "Yaya please I beg you, I promise daga yanzu zanna sa hankali maggi baze sake zarce mun ba please kar ka hanani yi maka girki."

  Kuka take sosai shi kansa ya rasa mey yake ciki shin ya kira malami a yi mata ruk'iya ne? Kokuwa likitan mahaukata ze nema? Shin meyake damun Kitten tasa? He don't want to believe ta6in hankali ne ke shirin kamata, he can't afford to lose her. Taya zata na rantsuwa bata sa gishiri da barkono a girki ba amma kuma ga abinci rad'au? Meke faruwa? Hugging nata yayi gam a jikinsa yana shafa bayanta har suka sauk'a k'asa akan gado. Be saketa ba seda ya tabbata bacci ya d'auketa. A hankali ya shimfid'ar da ita akan gadon ya rufeta da bargo sannan ya fito. D'akin Safiyya ya nufa yayi knocking bisa k'ofan take ta amsa ta fito. 


  "Sannu Uncle."


  "Safiyya?" Ya kirata "Na'am?" ta amsa tana kallon k'asa. "Meyake faruwa idan na tafi office?"


  "Kaman ya Uncle?"


  "Meyake samun Auntin ki? Meyasa girkinta kullum gishiri yake zarcewa bayan na tattare gishirin na kullesu a d'aki ke kike d'auko mata?"


 "Wallahi ba ni bace Uncle kuma kaman yadda baka sani ba wallahi nima banida masaniya game da abinda yake faruwa ni kaina mamaki abun yake bani a ido na tayi girkin d'azun nan maggi da tattasai zalla tasa kuma har da ta kusan sauk'ewa seda muka d'ana mata amma da zaran ansa a flask se abincin ya 6aci."


  "Are you sure?"


  "Na'am?"


  "Nace kin tabbata?"


  "Eh Uncle."


  "Bake kike yin gwaninta ki k'ara mata a bayan idonta ba?"


  "Meyasa zanyi hakan Uncle? Allah ma shaidana ne."


  "Huhhh" nauyayyan ajiyan zuciya ya sauk'e. 


  "Ban so inyi maganan ba d'azu a gabanta sede ranan naga Aunty tana wani abin al'ajabi."


  "Abin al'ajabi?" Ya tambayeta cike da rashin fahimta. 


  "Eh uncle a kitchen ranan naganta  tana magana da kanta haka jiya ma."


  "Tana magana da kanta kuma?"


 "Eh Uncle ita kad'ai sekaga tana suratai dama Aunty tana da aljanu ne?"


  "Aljanu kuma? Kina ganin aljanu ne suke mata wasa da hankali?"


  "Toh ban sani ba amma da abun tambaya dan akwai wata k'anwar mamar mu a k'auye da aljanu suka tak'ura mata. Itama amarya take kaman Aunty amma sai dai bata d'aura girki ba baya nuna. Ko kwana kwanon zeyi akan murhu baze ta6a nuna ba daga k'arshe seda aka kaita gun Malami akayi mata ruk'iya sannan ta samu sauk'i."


   "Subhanallah" ya furta yana shafa sajensa "I'll figure out what to do dan ko ni na fara zaton aljanun ne nima gashi de kema kince bata sa gishiri toh taya abincin yakeyin rad'au haka?"


  "A gwada nemo malami yayi mata ruk'iyan ni kaina tausayi Aunty take bani wallahi se kaga kukan da takeyi d'azu."


  "Kiga koda wasa kar ki nuna mata munyi maganan nan kinji ai ko? Bana son kowa yaji maganan daga ni sai ke, kin gane?"


  "In shaa Allah Uncle Allah ya bata lafiya."


  "Ameen" da haka ya koma d'akin nasu ya zauna a gefenta hannunta ya rik'o cikin nasa a hankali yana murzawa "Kitten what's really going on? Meyake faruwa? Why is this happening to you?" Sosai ya tausaya mata he can't believe aljanu na son haukatar masa da ita. 


  Kuka sosai Amal ta sha washegari da Afzal ya hanata yi masa breakfast yasa Safiyya. Ko makaranta tak'i fita ranan tun fitan Afzal ta rufe kanta a d'aki tana kuka, se hak'uri Safiyya ke bata kaman dagaske chan tace zata shiga bayi tana ficewa taje ta kulle kanta a d'aki ta d'au paper'n da Nazeefah ta rubuta mata lambarta ta zuba tare da danna mata kira. 





RANA D'AYA!

#RD


 Love... King Miemiebee👄✨

[13/08, 09:37] ‪+234 907 483 8352‬: 🎀🎀🎀                 🎀🎀🎀

                🎀❣🎀

                   ❣❣


  💦💦                      🍃🍃🍃          

           *RANA D'AYA!*

  💦💦                      🍃🍃🍃

  August, 2018

 beeenovels.blogspot.com


     _Written by Miemiebee👄_



   *PAGE 3⃣2⃣*



        "Assalamu Alaikum Aunty ina kwana?"


  "Sofin gaye ya kike?"


  "Lafiya k'alau Aunty ya Hindu?"


  "Hindu tana gida ni na fita school ya uwar d'akinki?"


  "Hmmm Aunty ina da labari mey dad'i miki."


  "Kai Sofin gaye har ta gama haukacewan ne?"


  "Gashi Uncle jiya yazo d'akina yana tambayata ko meke faruwa na tsara mishi labari kaman yadda kikace inyi yanzu haka yace ze nemo malami ayi mata ruk'iya don shima ya fara zargin ko aljanun ne."


  "Kin min dau-dai shin ta sake yi masa girki?"


  "Ai hanata yayi yau gata chan a d'akinta se kuka take."


  "Bravo alaiki Sofin gaye tsaraban ki na nan na tanadar miki."


  "Toh amma Aunty yanzu idan aka kira Malamin ya duba ta yace lafiya fah? Za a iya gano ni ke k'ara mata gishirin fah."


  "Inji wa? Taya za a gane ki bayan duk malaman ruk'iyan nan kud'i kawai suke so? Da mutum nada ciwo da bashida shi muddin an kaisa gun su se sun bada magani dan abasu kud'i in return saboda haka ki kwantar da hankalinki in shaa Allah baza a kama ki ba kede ki cigaba da gashi."


  "Toh Aunty."


  "Mission number one complete muddin akayi mata maganin kar ki sake 6ata mata girki mu barta nan haka se idan an kwana biyu se mu fara mission number two."

   

  "Ohh kar in sake sa mata gishirin?"

  

  "Eh mana baya riga ya hanata yi mai girki ba yanzu?"


  "Eh."


  "Toh kinga idan akayi mata maganin seya zammana kaman dama akwai matsalar amma an samu an magance yanzu."


  "Nagane."


  "Yauwa jeki sameta kiyita bata hak'uri idan Ya Afzal ya dawo kice d'azu ma kin ganta ita kad'ai tana suratai."


  "Toh Aunty" da haka sukayi sallama. Wani irin dad'i maras misaltuwa Nazeefah taji burinta ya cika ta haukatar da Amal ta sa Afzal ya daina cin girkinta, ita taso ace ta6in hankali ma Afzal ya soma zarginta da shi bama aljanu ba yadda za a d'auketa akaita chaan asibitin mahaukata ta fara rayuwarta ta bar mata Afzal nata amma hakan ma be 6aci ba. 


  ****

   Da Azahar Afzal ya wuce restaurant yaci abinci daga chan ya biya gida gun Ummi kallo d'aya tayi masa ta gano akwai matsala. 


  "Prince?"


  "Ummi" ya amsa a ksalance. 


  "Meke faruwa?" ta tambayesa. 


  "Ummi it's Amal."


  "Subhanallah lafiya dai ko?"


 "Ummi I don't know na rasa gane ta6in hankali ne yake neman kamata ko kuwa aljanu ne suke mata wasa da hankali."


  "Subhanallahi meya faru? Wani abun tayi ne?" Labarin komi ya kwashe ya bata batare da ya skipping komai ba. 


  "Shine baka ta6a bud'an baki ka fad'a mun ba Prince? Allah sarki Amal gata mahadacciyar Qur'ani oh! kowa da tasa jarabawan amma anya kuwa aljanu ne? Ba ta6in hankali ba?"


  "Ummi I don't know I'm totally clueless kuka take yau seta yimun breakfast amma na hanata saboda ko tayi ba iya chi zan ba banda gishiri da borkono ba abinda yake cikin girkinta yanzu."


  "Kuma ba ita take sawa ba?"


  "Gashi na tambayi Safiyya tace a gabanta Amal tayi girkin bata sa gishiri ba shiyasa nake zaton ko aljanu ne."


  "Kuma gashi yarinyan tace tana ganinta tana magana ita d'ai?"


  "Har sau biyu ma tace."


  "Ikon Allah kode aljanun ne toh?"


  "Shine nima ban sani ba mu fara kaita psychiatric hospital (asibitin mahaukata) ne su duba ta ko mu fara dana gargajiyan?"


  "Toh nide gani nake kaman aljanu ne amma a fara kaita asibitin idan sun kasa gane kan abun se mu dawo na gargajiyan, akwai sanannen malamin dana sani yana ruk'iya sosai zan nemesa."


  "Toh yanzu ya zan fara sanar da ita zan kaita asibitin mahaukata Ummi? Wallahi bazata amince ba bayan nan kuma gani zatayi kaman naci amanarta ne ina danganta mata ciwon hauka kuma bana son su Mami suji maganan nan se idan abu ya gagara tukun zamu sanar dasu ko ba haka ba?"


  "Tabbas kayi tunani Prince tunda de yanzu Amal responsibility'n muce."


  "Toh kinga..."

  

  "Ka san yadda zaka sanar da ita Prince ai matarka ce zata fahimce ka in shaa Allahu."


  "Toh Ummi I'll try, please karki manta kiyi wa Malamin magana."


  "In shaa Allah Prince kuma duk abinda akwai ka kira ka sanar dani Allah ya bata lafiya."

  

  "Ameen bari zan koma" rakiya tayi masa sannan ta dawo ciki. Yana isa gida Safiyya tayi mishi sannu da zuwa sannan ya k'arisa d'aki inda Amal ke mik'e akan gado amma ba bacci take ba ko da taji shigowansa bata juya ta kallesa ba Sallama yayi ta amsa ciki-ciki ba tare da ta kewayo ba. Kayan jikinsa ya rage sannan ya k'arisa gefen gadon ya zauna a gefenta. 


  "Kitten?" Ya kirata sede bata amsa ba. "I called you twice baki d'aga ba why?"


   "Ban san inda na jefar da wayan ba" ta amsa ba tare da ta kallesa ba. Hannu ya mik'a ya mik'ar da ita zaune "How're you feeling?" Ya tambayeta. 


  "Kaci abinci?" Ta mayar masa tunanin da take tayi tun d'azu kenan, shin yaci abinci, mey yaci? Ya k'oshi? It pains her alot idan ta tuna Afzal baze sake cin girkinta ba yanzu, sosai zuciyarta keyi mata k'ona. 

  Allah sarki sosai ta basa tausayi, bata ma damu da lafiyarta ba, ita burinta kawai taji yaci abinci ne, "Kefa kin ci?" Ya tambayeta. 


  "Yaya I really want to cook for you koda sau d'aya ne ka barni in sake yi maka girki please Yaya I miss feeding you" ta rok'esa yayin da idanunta suka shiga cikowa da hawaye. 


  "Kitten please cut it out, kibar kukan haka."


  "Then allow me cook for you and feed you one last time."


  "Baby" ya ambaci sunanta had'e da rik'o hannunta cikin nasa yana murzawa a hankali "Ba kida lafiya ki bari se in kin samu sauk'i kinji? I myself miss your cooking kinsan kece best cook d'ina ko?"


  "Yaya can't you see? I'm perfectly okay wallahi lafiyata k'alau ba abinda yake damu na" kwantar da ita yayi a jikinsa yana shafa bayanta a hankali "Zamu kaiki asibiti gobe su duba ki in shaa Allah idan kika samu sauk'i se kiyi resuming normal duties naki ki cigaba da yimun girki kinji?" cike da rashin fahimta ta d'ago kanta tana kallonsa "Asibiti Habib Albi?"


  "Kitten I'm so sorry-"


  "No" ta furta cike da tashin hankali tare da janye jikinta daga nasa. 


  "Kitten please understand me-"


  "No Yaya" da sauri ta janye hannunta da yake k'ok'arin rik'ewa "Mey kake nufi da hakan? Ina da hauka?" Ta tambayesa cike da d'umbun mamaki. 


  "No Kitten ba haka nake nufi ba" ya amsa a rud'e shima, a rayuwa ba abinda yafi tayar masa da hankali kaman yaga Amal tana kuka, da zaran yace ze rik'e hannunta se ta ja da baya. 

  

   "Ni Mahaukaciya?" Ta ambata da mamaki yayinda hawaye ke bin k'uncinta. 

  "Kallon mahaukaciya kake mun Yaya?"


  "Kitten please-"


  "Yaya.." kasa cewa komi tayi kawai ta rushe da wani irin masifaffen kuka yayinda ta mik'e da hanzari dan bar mai d'akin. Hannunta ya cafko ya kwantar da ita a jikinsa had'e da matse ta gagam wane wani na shirin k'watar masa ita. Kokowa take sosai ya saketa amma yak'i hak'uri ya ta bata yana shafa bayanta a hankali har seda ya sauk'ar da temper'nta. A hankali ya d'agota yana share mata hawayen nata "Kitten please understand me bawai cewa nayi kina da hauka ba, bazan ta6a kwatanta ki da mahaukaciya ba but contrary to abubuwan da suke faruwa bakiya tunanin ko akwai wata matsala?"


  "Yaya ashe Allah ze kawo ranan da zaka yi mun kallon mahaukaciya?" Ta tambayesa hawaye na bin k'uncinta. 


  "Kitten I will never refer to you as that kema kin sani I love you and I only want the best for you, dan za ki ga psychiatrist doctor (likitan mahaukata) bawai hakan na nufin kinada hauka bane, ze iya yuwuwa wani matsalan ne daban yake damun ki psychologically ko stress ko makamancin hakan."


  "There is no stress Yaya and I'm not losing my mind ni ba mahaukaciya bace kana tsammanin zansa gishiri acikin girki ba tare da na san nayi hakan bane? I told you ni bani kesa gishiri da attarugu ba, ba ni bace!" Sosai ranta ya 6aci taya upon all people Afzal baze yarda da ita ba? Taya za'a ce mijinta tilo yana yi mata kallon mak'aryaciya kuma mahaukaciya? Cikin tsananin kuka tace, "I thought you love me Yaya, I thought you trust and believe in me."


  "Of course I do Darling, I love you with every burning fiber in my soul and I do trust and believe in you than I do myself."


  "No Yaya inda har kana nufin abinda ka fad'a da baza ka fara tunanin kaini gun likitan mahaukata ba, da zaka yarda dani idan nace maka bani kesa gishiri da borkono cikin girkin ka ba."


  "I know Kitten nasan ba ke kike sawa ba shiyasa na fara zargin ko aljanu ne suke miki wasa da hankali."


  "Aljanu? Yanzu kuma mey kallon iskokai kake mun Yaya? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" juyawa tayi da niyyan bar mai d'akin bata ma jin zata iya yi masa magana. Da sauri ya sha gabanta "Kitten please ki fahimceni ki sani lafiya nake nema miki wallahi na gaji da ganinki haka cikin k'unci da kuka kullum, kiyi hak'uri ki bari a magance miki wannan matsala please."

 

   "Ni bana tattare da aljanu I know how I feel saboda haka ba wanda zeyi mun ruk'iya, nasan kaina kuma na dogara da addu'o'in da nakeyi."


  "Kitten bawai ina jayayya da hakan bane ni kaina sheda ne game da yadda bakiya wasa da addu'o'in kariyan nan I'm aware of everything." 


  "Toh mey kake nufi Yaya? Kallon mey iskokai da ta6in hankali fa kake mun how do you expect me to feel and react?"


   "Darling I'm sorry but I'm just worried, ke da bakinki kika ce bake ke sa gishiri da borkonon nan ba kuma na amince da hakan I trust you Kitten amma toh wa yake sawa? Bakiya tunanin akwai wata 6oyayyan al'amari? Kuma baza mu ta6a iya gano inda matsalar take ba bale a magance miki se har idan kin amince kin bada had'in kai Kitten. I promise no harm will come to you, I've got you Baby, ba wanda yace kina da ta6in hankali I just need to find out what's really going on. Please calm down everything is going to be alright in shaa Allah okay?" Ya k'are yana matso da ita kusa da shi. Cike da dabara ya kwantar da kanta a k'irjinsa yana shafa kanta "I love you so much" ya furta mata, a hankali yaji hannayenta a bayansa tana hugging nasa back "I love you too" ta furta. Washegari Afzal be fita office ba, wanka sukayi tsaf tare suka shirya, da kansa ya had'a musu breakfast sannan suka wuce psychiatric hospital inda aka duba Amal akayi mata gwaji da dama akan washegari su dawo su kar6i sakamako. 

   

   Washegari Afzal ya koma ya amshi results d'in shi kad'ai kasancewar daga office ya biya wajen sede da mamaki sakamakon ya nuna ba abinda yake damun Amal, hankalinta dai-dai yake dana mutane ba wata matsala. Hakan ba k'aramin d'aure wa Afzal kai yayi ba don haka kawai ya yanke hukuncin aljanu ne toh sukeyi mata wasa da hankali nan take ya kira Ummi yayi mata bayani dama ta riga tayi magana da Malamin yace koda yaushe suka shirya suje yana jiransu. Address kawai ta tura masa. 


   Gida gun Amal ya koma yaci ace ya koma gun Nazeefah dake kwanan Amal ya k'are amma baze iya barin Amal cikin wannan yanayi da iska suke wasa da hankalinta haka ba har se idan ya samo mata lafiya. Nazeefar yayi niyyan kira ya sanar da ita halin da ake ciki se ya sha'afa. Itako chan a gidanta ta gama girki ta gama komi jiran zuwansa kawai take amma shiru gashi har shida da rabi yayi. Jin shirun yayi yawa gashi be kirata ya sanar da ita dalilin hakan ba ta d'au waya kawai ta kirasa a karo na farko ya d'aga suka gaisa. 

  "Kin jini shiru ko?" 


  "Eh Ya Rouhi lafiya?"


  "Amal ce bataji dad'i ba I'm afraid I can't make it today ina fatan hakan ba matsala."


  "Allah sarki meke damunta?"


  "Ermm... ermmm zazza6i ce" yayi mata k'arya haka kawai yaji baya son ya fayyace mata gaskiyan al'amarin. Amal na kwance kan cinyansa tana sauraransu. 


  "Ayyah ka gaisheta da jiki da Allah, Allah k'ara mata lafiya zan kirata in gaisheta."


  "Ameen in shaa Allah ba wata matsala ko?"


  "Ba komai."


  "Toh seda safe I'll call you tomorrow."


  "Alright take care" wata mak'irar murmushi ta sakar yayin da ta katse wayar. "Ai kad'an ka ga se zaman gidan chan ya gagareka you'll see."


  "Nazeefah na gaisheki" ya sanar da Amal had'e da sanya hannunsa cikin gashin kanta yana massaging mata cikin kai a hankali, kai zalla ta gyad'a masa. "Kina jin yunwa?" Nan ma kai ta kad'a a hankali. 


  "I called Ummi earlier batun Malamin tace ta riga tayi mai magana so she sent me his address gobe zamu kaiki baki da wani test a school ai ko?"


  "Babu" ta amsa ciki-ciki. Wace irin msuiba ce wannan? Tana ji tana gani ana dangata mata ciwon aljanu ciwon da tasan ba ta da shi. Kan nata ya cigaba da massaging mata chan ya dafa musu indomie bayan sun gama ci sukayi wanka sukayi sallah suka tofe addu'an bacci sannan suka kwanta. Washegari da yamma bayan sallan La'asar suka wuce gidan Malamin. A mota ya barota ya k'arisa ciki bayan sun gaisa yayi wa Malamin bayanin abinda yake damunta ciki harda ce masa da Safiyya tayi akan Amal ita kad'ai tana magana ya kuma buk'acesa da koda ya shigo da Amal d'in kar yayi maganan komai a gabanta. Bayan Malamin ya fahimce shi ya koma ya shigo da Amal karatu Malamin ya shiga yi mata amma ba alamun komai a tattare da ita, bayan ya k'are karatun yayi mata hayak'i nan ma ko alaman aljanu babu. 


  "Gaskiya bata tattare da iska sede ze iya yuwuwa shafanta sukeyi su barta amma bawai sun shiga jikinta ba."


  "Toh yanzu ya kenan Malam?" Afzal ya tambaya. 


  "Sede ince ta dage da addu'a ta kuma rage kalle-kalle da fita da kai a bud'e. Zan baku turaren almisky tana amfani da shi tana kuma shan man hul6a ta na karatun Al~Qur'ani sosai in shaa Allahu iskokan zasuyi nesa da ita."


   "Tana yi sosai wallahi Malam mun gode in shaa Allah zata kiyaye duka ababen da ka irgon."

  Almiskin ya d'iba musu da man hul6an Afzal ya biya kud'in. Tun shigansu mota har suka dawo gida Amal bata mai magana ba. Waje ya fita ya kira Ummi ya sanar da ita abinda Malamin yace. 


  "Ai Malamin ya iya aiki da ikon Allah zata samu sauk'i kuma shi ba ta kud'i yake ba kaga idan wani ne yanzu ya rink'a raina mana wayo kenan yana mana k'arya akan lallai akwai aljanun a jikinta ayita ruk'iya ana kashe kud'i ana bata wuya."


  "Hakane kam wallahi thank you so much Ummi."


   "Ya Amal d'in toh?"


  "Lafiyarta."


  "Tana kusa ne ka had'amu?"


  "Eh toh" nan ya bud'e k'ofan ya dawo ciki ya k'arisa ciki. "Kitten?" Ya kirata. 


  "Uhmm?" Ta kewayo tana kallonsa 


  "Ga Ummi tana son ku gaisa" ba gardama ta amsa suka gaisa sannan ta miyar masa. Ya so ya sake kwana mata amma baya son ya shiga hak'k'in Nazeefah dayawa dan haka ya shiga tattare abubuwan da ze buk'ata. Yana gamawa ya kewayo kan Amal dake mik'e kan gado "Kitten zan koma wajen Nazeefah" ya sanar da ita yana takowa inda take hannunsa ya mik'a mata kamar wacce bazata kama ba tasa nata ciki a nitse ya mik'ar da ita yana shafa fuskanta a hankali. 


   "Kina amfani da turaren kinji? Man hul6an kuma kina sha safe da yamma kaman yadda Malamin ya fad'a nasan kina karatun Al~Qur'ani sosai ba sena ce kiyi ba Allah baki lafiya Sweetheart I love you so much." Kai ta gyad'a masa a hankali "Muje in raka ka" da sauri ya rik'o ta kafin ta ku6uta daga hannunsa yana mey zagaye hannayensa a 'yar kunkuminta. 


   "Where's my cheerful and loving Kitten please tell her I miss her so much and that I want her back"  yayi maganan yana shafa kan lips nata a hankali da babban yatsansa. "Allah baki lafiya Kitten I can't wait for you to get better, I love you so much."


  "I love you too Habib Albi" ta sanar da shi a hankali ya mik'a yayi owning lips nata kissing her gently and taking her fears away seda nishinta ya kusan d'aukewa ya saketa ya shiga shafa fuskanta a hankali "Take care of yourself okay? Duk abinda kike buk'ata ki fad'awa drivernki yaje ya siya miki idan kuma Safiyya zata iya seta girka miki amma kar ki sakeyin girki se kin samu sauk'i kinji?" kai zalla ta gyad'a masa. "Na ajiye miki kud'inki a gaban mirror ki kwanta ki d'an huta kafin Maghrib Sena dawo."


  "Thank you bara in raka ka."


  "A'a kiyi zaman ki I can manage" peck ya sauk'e mata akan goshi sannan ya fice. Koda ya koma gun Nazeefah hankalinsa gabad'aya na akan Amal ne minti minti yake d'aukan waya yana kirarta yana tambayarta ko lafiya se yanzu yake regretting meya hanasa amsan lamban Safiyya da ita zena kira yana tambaya ko lafiya baya son abin da tak'urawa Amal tasa, sosai yake missing nata ji yake shima kaman ba shida lafiya. He can't explain how much he's missing her giggles, laughs and smiles. Suna zaune a d'aki Nazeefah na masa tausa tayi gyaran murya "Ya Rouni?" ta kirasa cikin wani irin salo. 


  "Yes Rabba'atul Bait?"


  "What's wrong tun shigowanka jiya na ganka wani iri meke damunka?"


  Be 6oye mata ba ya sanar da ita gaskiyan al'amarin "It's Amal Rabba'atul Bait I'm worried about her."


  "Allah sarki zata samu sauk'i in shaa Allah muna kan mata addu'a."


  "Thank you Rabba'atul Bait."


  "Don't mention love amma ciwon nata zazza6i ne kawai?"


  "Wani abu ne?"


  "A'a d'azu dana kirata ne take cemun wai abun nata harda iska-iska haka."


  "Ita da bakinta?"


  "Eh" ta jaddada masa dukda kuwa tasan k'arya takeyi basu ma yi waya da Amal ba yau bale har wai Amal ya sanar da ita akan iskokai ne suke damunta. 


  "Malamin yace basu shige ta ba kawai sun shafeta ne amma ya bamu magani in shaa Allah zata samu sauk'i."


  "Allah sarki Amal, shin bata karatun Al~Qur'ani ne? Kasan ance aljanu basa kama me yawaita karatun Al~Qur'ani."


  "Tana yi kinsan shi jarabawa kowa da irin nasa, Amal mahaddaciyar Al~Qur'ani ce kullum seta d'au Qur'ani tayi karatu I guess wannan itace jarabawarta." Haushi taji sosai Amal na da haddan izu sittin akanta ita tana nan tana fama da izu goman k'asa. Taya bazata tsani Amal ba bayan ta ko ina seta nuna tana son ta k'ureta. 


  "Allah sarki Allah bata lafiya toh" ta fad'a ba don tana so ba tana k'wak'ulo murmushin dole. 

  

  "Ameen" ya amsa. 


****

  Duk da kwanan Nazeefah ne hakan bai hana Afzal zuwa duban Amal da safe kullum kafin ya wuce office, da kwanan ta ya zagayo kuwa komi shi yake k'ok'arin yi mata, ba k'aramin kula da ita yake ba. Da yamma idan ya dawo daga office zasu d'au Qur'ani suyita karatu har zuwa Magriba. Tun ranan da suka dawo daga gun Malamin Afzal be sake gane kan Amal ba. Gabad'aya yanayinta ya canza a gidan sa6anin yadda suke zama suyi hira suyi dariya yanzu kam jugum sede shine ma yayita zuba ita befi tana amsa sa da eh ko a'a ba. Hakan ba k'aramin damun Afzal yake ba he can't explain how much he's missing her. 


   Yau sati biyu kenan tun dawowansu daga gun Malamin, cikin ikon Allah ta shiga sake sakewa da Afzal ta fara yi mai hira har suka koma zama yadda suke da. A hankali a hankali suka fara shiga kitchen tare suna yin girki har yazo ya fara barinta tanayi ita kad'ai. Afzal baze iya kwatanta irin murna da farin cikin da ya tsinta kansa aciki ba da Amal ta soma yin girki ba matsala yanzu, Ummi ya soma kira ya sanar da ita. A kullum son Amal dad'a k'aruwa yake a birnin zuciyansa, tabbas baze iya rayuwa ba ita ba. 


   Yau ya na tashi daga office ya wuce gida straight he can't wait ya iso gida ya samu Kitten tasa. Fresh flowers ya tsaya ya saya mata a florist shop sannan ya k'arisa gida. Sede sa6anin kullum yau Kitten tasa bata fito ta tare sa ba k'arisawa ciki yayi amma Safiyya kad'ai ya tarar bayan ta mai sannu da zuwa ya tambayeta ko ina Amal take ta ce mai tana d'aki. D'akin nasu ya k'arisa sede be ganta ciki ba, kasa kunnen da zeyi yaji splashes na ruwa a bayan gidan don haka yayi knocking bisa k'ofan "Kitten I'm home."


  "Welcome home Habib Albi."


  "Mey kikeyi wanka?"


  "Eh" ta amsa. 


  "In shigo?"


  "Ka shigo Habib Albi" ta amsa tana murmushi, kayan jikinsa ya rage ya d'aura towel sannan ya d'au flower'n ya shiga bayin. "Here this's for my adorable Kitten."


   "Awwn thank you Habib Albi" tace tare da amsa "I love orchids" ta sanar da shi "Don't mention Love, matsa min toh in shiga" batayi gardama ba ta gyara masa ya shiga ya zauna had'e da riginginar da ita a jikinsa. Wasa suka tayi cikin tub d'in k'arshe suka wanke jikinsu suka d'aura alwala sannan suka fito. Sosai yaji dad'in kwana biyun da sukayi tare ba k'arya yayi missing delicious nata baze fasa yima Allah godiya ba da ya bawa Kitten nasa lafiya. Musamman ya koma gun Malamin da yayi musu maganin ya mishi kyautan kud'i. Kaman kar ya tafi yau da kwanansa ya k'are, yadda ta saba raka sa haka tayi ta kaisa har gun mota inda ya shiga kissing nata awajen be saketa ba seda ya tand'e jan bakin data shafan tas sannan ya sallameta ta dawo ciki. Yana isa gidan Nazeefah ta taresa da wani hot kiss nata itama bayan sun k'arisa d'aki seya karanci yanayinta ya sauya a lokaci guda. 


  "Rabba'atul Bait lafiya?"


  "Ai kai zan tambaya Ya Rouhi" ta amsa tana turo baki 


  "Da nayi me Sweetheart?"


  "Ba wani Sweetheart d'innan ai nasan inda ka ajiye ni."


  "Haba Darling meya faru haka?" tasowa yayi daga gaban mirron ya k'arisa inda take had'e da zauna a gefenta. 


   "Gaya mun waya ta6a mun Rabba'atul Bait d'ina."


  "Ba amaryarka bace."


  "Amal?" Kai ta gyad'a cike da shagwa6a. 


  "Me kuma tayi?"


  "Cemin tayi kullm ka fita seka taho mata da flower ni dai-dai da RANA D'AYA ko yashi baka ta6a ibowa kace gashi Rabba'atul Bait wannan naki ne shin kana ma sona kuwa Ya Rouhi?" Mamaki da kunya yaji duka a lokaci d'aya. Be ta6a tsammanin hakan daga gun Amal ba. Wani irin abin kunya take shirin yi masa haka? Taya zata na fad'awa Nazeefah abinda yake mata? Meye riban hakan?


  "Bayan nan kuma tace sede baka je gida mata ba baka bari ta zauna a ko ina se a kan cinyanka, ko abinci akan plate d'aya kuke ci ni duk baka mun ko d'aya Ya Rouhi" ta sanar da shi kar kusha mamaki komi nan Safiyya ne ke fad'a mata. Afzal baze iya kwatanta irin tsananin kunyan da yaji ba yayinda ya kasa daina mamakin dalilin da zai sa Amal tayi masa haka, shin mey ya buga mata kai? So take ta 6ata tsakaninsa da Nazeefah?


  "Rabba'atul Bait I'm really sorry" ya furta cike da disappointment, a hankali ya d'agata ya zaunar da ita kan cinyoyinsa. 


  "Ba komai dama nasan kafi son Amal akaina ai."


  "Please don't you ever say that nasan nayi kuskure amma kiyi hak'uri I'll make it up to you in shaa Allah I promise." Hannayenta ta zagaye a wuyansa "Can I count on you?"


  "In shaa Allah Rabba'atul Bait, I love you so very much."


  "I love you more Baby" ta amsa fuskanta ya shiga bi yana kissing har seda ya kai kan lips nata. 


***

  Bayan sallan isha ya d'auketa a mota suka je suka ci abinci a waje daga chan suka wuce 3G inda ta kwashi jakukkuna guda uku masu kyau, tana jiran taji yace bari ya d'auka wa Amal kaman yadda ya saba fad'a ta ji yayi shiru yau kud'in kawai ya biya suka fito. Ai kuwa idan haka ne plan nata ya fara aiki kenan, da alama bai ji dad'in abinda tace masa Amal tayi bane shiyasa ko jakar ma yak'i sai mata, ai ko idan haka ne ta ringa 6ata Amal a gabansa kenan se tasa ta fita masa a rai gabad'aya. Zata sa Safiyya ta musu ido sosai tana d'auko mata rahoto. 


***

   Kamar yadda ta d'au alk'awari hakan ta cigaba da 6ata Amal gaban Afzal, duk abinda yayi ma Amal se Safiyya ta kwashe ta fad'a mata itako idan kwanan ta ya zagayo seta maraice fuska tace ai gashi-gashi abinda Amal ta kirata ta fad'a mata. Sosai abun yake k'ona ma Afzal rai be ta6a sanin Amal da halin nan ba se yanzu shin meye ribanta na fad'awa Nazeefah abubuwn da yakeyi mata? Sabida ta 6ata tsakaninsu ne take hakan kokuwa dan ta nuna wa Nazeefah a fili baya adalci a tsakaninsu? A kullum 6aci ransa yake idan Nazeefah ta irga masa abubuwan da yayi ma Amal wanda beyi mata ba amma dai-dai da RANA D'AYA be ta6a tunkarar Amal da maganan ba. A tunaninsa da kanta zata gano abinda takeyi ba dai-dai bane ta daina amma ina abun se worse yakeyi ko bathroom slippers ya sai mata be sai wa Nazeefah ba seya ji a bakin Nazeefah sosai abin ya isheshi har ya zamma ko tsinke ya daina saiwa Amal yana kai mata idan har ya sai mata abu to ya sai wa Nazeefah ne amma special treatment kam ya daina bata. 


     ****

     Yau ranan ya kewayo kwanan Amal wanka tayi tasha kwalya tasa sabon d'inki ba k'aramin kyau tayi ba sannan tayi zaman jiransa se after six ya iso shida kullum 5:30 ya shigo. Tun daga bakin parking lot taje ta taresa sede kaman zuwansa na biyu da suka wuce yau d'inma haka ya shigo fuskansa a d'aure, d'aure fuskan yau d'inma yafi na kowanne, ko attempting kissing nasa da ta gwada yi se taga yayi dodging abinda be ta6ayi ba shin meke faruwa? Jakansa ta gwada amsa nan ma ya hanata ya wuce gaba, cike da mamaki ta bi bayansa suka k'arisa ciki. 


   "Ya office?" ta tambayesa bayan sun shigo d'akinsu. 


  "Lafiya" ya amsa sama-sama ko kallonta beyi ba. Toh me tayi yake shasshareta haka?


    "In sirka maka ruwa ko?" Ta tambayesa.


  "Yanzun na yi a chan gida karki damu."


   "Toh muyi tare" ta sake fad'a duk don ya amince. "Maybe next time" ya amsa nan ma ko kallonta beyi ba. Wow! Shin meke faruwa? Ta tambayi kanta. 


  "Toh abinci fah?" Ta sake tambayansa a hankali, sosai jikinta ya mutu da irin short-short answers da yake bata. 


  "Nazeefah ta bani" ya amsata, amsan da a iya zamansu be ta6a bata ba. 


  "Habib Albi amma kullum fa kana ci idan ka dawo."


  "Bana jin yunwa Amal" taji ya kirata gatsau da sunanta. Tirk'ashi! Bata sake yi masa magana ba se chan wajajen k'arfe tara. A tunaninta wai ko stress ne daga office yake sanya sa yin abinda yake yi bari ta barsa ya huta. Bayan ta k'are karatun Al~Qur'ani ta d'an ta6a na bokon ta fito ta sami Afzal dake zaune a parlour yana kan tattara documents nasa yana sanya su cikin briefcase. K'arisawa tayi ta zauna akan cinyansa. 


   "Sekin yi hak'uri kin tashi na buge k'afa na d'azu zafi yake mun" yayi mata k'arya. 


  "Subhanallahi! Sannu shine baka sanar dani ba? Mu shafa maka man zafi ne?"


  "Karki damu I'll be fine" da haka ya sauk'eta.


  "Baka ci abinci ba Habib Albi."

 

  "Bana jin yunwa."


  "Kana nufin yau abinci na zeyi kwante kenan?"


  "I'm sorry but I guess yes excuse me" yana kaiwa nan ya d'aga briefcase nasa ya koma d'aki. Mamaki ne sosai ya cika Amal shin mey tayi wa Afzal yake shareta haka? A iya saninta de bata mai komai ba meyasa yake shareta haka toh? Safiyya ta kira ta tayata suka juye abincin suka sa a fridge sannan ta bi Afzal ta koma d'akin inda ta tarar da shi yana tu6e kaya da alama wanka zeyi. "Habib Albi wanka zakayi?" Ta tambayesa inda ya gyad'a mata kai zalla. 


  "Muyi tare?" 


  "Bacci nakeji Amal ki bari ko gobe" har cikin ranta taji zafin yadda yayi rejecting nata, ta rasa mey tayi yake yi mata haka amma tabbas tasan da akwai abu a k'asa amma bazata masa magana nan take ba zata yi masa uzuri halan wani abun ne yake damunsa. Haka tana ganinsa ya wuce bayin ya watsa ruwan ya fito ya sanya boxers nasa, bata ce da shi komai ba ta mik'e ta shiga itama fitowan da zatayi ta gansa da coke da cookies yana ci so ashe yana jin yunwa amma yayi mata k'arya wai baya ji don kar ya ci girkin ta. Mey tayi masa yanzu da baze ci girkinta ba? Hmm duk yadda ranta ya 6aci da kuma yadda taso tambayan sa dalilin da yasa yakeyi mata haka kwana biyu ta danne zuciyarta ta fasa. Wani shara-sharan rigan baccinta ta sanya tana ta zirga-zirga a d'akin duk don ta karkatar mai da hankali amma ko d'aga ido ya kalleta beyi ba bale yasan tana yi. Yana gama cinye cookies nasa yayi disposing goran da ledan ya haye gado ya kwanta had'e da juya mata baya. Addu'o'in baccinta ta tofe sannan ta samesa akan gadon ta gangaro da pillonta kusa da nasa inda yayi shiru kaman be jita ba. 


   "Habib Albi?" Ta kirasa shiru yayi kaman baya jinta. "Habib Albi I miss you" ta sanar da shi. "Please turn around" ta buk'acesa amma ko ya motsa bale tasan yanayi. A rayuwa baya son munafikin mutum mey yayi zafi da zata na kiran Nazeefah tana yi mata gulman abubuwan da yakeyi mata se yazo nan kuma ta tsaya tana maraice fuska tana acting kaman wata salihar k'warai. 


   Amal ta kasa bacci ranan se tunanin dalilin da zaisa Afzal yana shareta haka ta kwana tana yi, be ta6a dawowa be nemeta ba se wannan karan gashi ko da ta gwada nemansan ma yak'i ya kulata kuma sarai tasan ba bacci yakeyi ba lokacin. 


    Washegari ko da ta gaishesa sama-sama ya amsa, yana shiga bayi don yin wanka ta wuce kitchen ta shiga had'a masa breakfast sede da ya fito ko kallon kulolin nata beyi ba bale yayi tunanin ci. Yana cikin had'a black tea se gata ta fito don serving nasa. 


  "Karki damu bazan ci ba."


  "Bazaka ci ba kuma Habib Albi?"


  "Eh" ya jaddada mata. 


  "Toh mey kakeso in girka maka?"


  "Karki damu ina Safiyya? Safiyya!" Ya k'wala mata kira nan da nan ta fito daga d'akinta ta gaishesa sannan Amal. 

   

   "Zo ki soya mun k'wai biyu kiyi sauri I'm already late" Sandarewa Amal tayi wajen ko k'ala ta kasa cewa yayinda zuciyanta yakeyi mata k'ona sosai wato ya gwammace Safiyya ta soya masa k'wai da yaci girkinta? Hmm. Haka ba yadda iya ta koma d'aki ji take kaman tayi kuka. 

   Gashi tun da ya fita office ranan be dawo gida ba har wajajen tara na dare. Ba irin kiran duniyan da Amal batayi masa ba amma yana ganin calls d'in yak'i d'agawa a rayuwa baya son munafikin mutum taya zata na d'iban duk abinda sukayi tana kai wa Nazeefah kuma ya tabbata ba k'arya Nazeefah takeyi ba idan ba a bakinta ba a ina Nazeefah zata na jin dukkan abubuwan da suke faruwa idan yaje mata kwana? Ace wai har kayan abincin da ya siya ya kaiwa su Papi seda ta kira Nazeefah ta fad'a mata, dan kawai yana kyautata mata da iyayenta shikenan seta shiga neman 6ata tsakaninsa da uwar gidansa tana sanya sa looking maras adalci a fili, yanzu mey ze faru idan Nazeefah taje ta fad'awa iyayenta har magana ya kai kunnen Abba? Sam be santa da wannan munafikin hali ba kode k'awaye ne suke zigata? Toh ta cigaba shi de baze yi mata magana ba. 


    Amal na zaune a parlour tana jiran dawowan Afzal se taji k'aran gate. Agogo ta duba taga ana neman goma ko meya rik'esa se war haka yake zuwa gida? Yet she's still grateful Allah ya dawo mata da shi gida lafiya. Da hanzari ta mik'e Afzal na bud'e k'ofar ta ruga taje tayi hugging nasa. 


   "Habib Albi where've you been? I've been trying your number but you weren't picking up wallahi hankalina ya matuk'ar tashi." Cike da tak'ura ya janyeta daga jikinsa "Meeting muka yi se yanzu muka tashi ni kuma ban sake duba waya na ba" yayi mata k'arya bayan gidansu Sultan yaje ya yini throughout. 


  "Bakada lafiya ne?" Ta tambaya tana shafa fuskansa. 


  "I'm just stressed out lemmi take a shower" yayi maganan yana sauk'e hannunta daga fuskansa. 


  "Kawo jakan naka in rik'e maka."


  "Bari karki damu" nan ya wuce ta ya k'arasa d'akin ji tayi tamkar tayi kuka bata ma iya ta bisa d'akin ba a parlourn ta cigaba da zama yayinda tunani ya mamaye mata k'wak'walwa ji take kaman tayi kuka ta rasa mey tayi masa yake bata wannan attitude. Se chan ta iya ta mik'e ta bisa d'akin. A kwance ta tarar da shi yana jin motsinta ya 6oye wayansa da yake ta faman chatting da Nazeefah k'ark'ashin pillow yana pretending kaman yana bacci. "Habib Albi?" Ta kirasa shiru yayi yak'i amsawa a hankali yakejin takunta har lokacin da ta k'ariso kan gadon ta zaune gefensa. 


  "Habib Albi bazaka ci abinci ba?" Nan ma shiru yayi mata sarai kuma tasan ba bacci yake ba. Hijabinta ta cire ta kwanta a d'an space dake gabansa had'e da kwantar da kanta a k'irjinsa tana mey zagaye hannunta kan cikinsa sannan ta ja musu bargo ta rufesu. "Goodnight Habib Albi I love you" ta furta a hankali bacci me wuya ya d'auketa chan tukuna shima Afzal baccin ya d'aukesa. 

  Kasancewar tana da morning lectures washegari se suka gama shiri kusan a tare, dukda cewan se shareta Afzal yake. Yau kwata-kwata ma k'in karyawa yayi wai ze fita da azumi. Gano itama school zata se yayi mata k'arya wai bazeyi ya kaita ba yana da meeting driver ya kaita kawai. Kud'in makarantar ta ya ajye mata ya fice ko kiss daya saba yi mata beyi ba yau haka ma jiya. Na matuk'a hankalin Amal ya tashi ta rasa mey tayi Afzal yake yi mata haka, Maamah ce ta karanci yanayinta a makaranta ta tambayeta ko lafiya. 


  "Babu" ta amsa. 


  "Taya zakice babu Amal? Tun d'azu fa na lura banda tunani ba a inda kike tayi mey ne?"


  "Maamah it's Yaya."


  "What about him."


  "Wallahi ni kaina ban sani ba, na rasa gane meke damunsa kusan sati kenan yau idan yazo baya sakewa dani seda yata d'aura mun fuska ko girki na baya son chi d'an tsaraban daya saba siyo mun idan ze dawo gida ma ya daina I don't know why."


  "Subhanallahi Ya Afzal d'in?"


  "Wallahi aka ce mun Yaya zemin haka wataran bazan yarda ba kinga tun da ya fita office jiya be dawo ba se kusan goman dare nasan sarai ba wani meeting da sukayi k'arya yake mun gashi ba kiran duniyan da ban masa ba haka yata ignoring calls d'ina maganan da nake miki haka yanzu ko nema na bayayi."


  "Ikon Allah this's serious toh ke mey kikayi masa? Am very sure Ya Afzal baze fara shareki haka kawai ba dole da akwai sila."


  "Wallahi ban yi masa komai ba Maamah I can't take this anymore bana jin dad'in yadda Yaya yake fushi da ni haka wallahi ko karatu na kasa yi jiya gashi muna da test gobe I can't stop thinking about him, I miss him so much bazan iya rayuwa ba shi ba" ta k'are maganan idanunta na cikowa da hawaye. 


  "Ke kuwa kar kiyi kuka mana" Maamah tayi maganan tana kwantar da ita a jikinta "Yi hak'uri don't cry komi mey wuce wa ne."


  "Har zuwa yaushe toh Maamah?"


  "Kiga toh kiyi confronting nasa mana ki tambayesa mey kikayi yake shareki haka talk to him Amal silence is never a solution."


   "Maamah bana son hakan ya 6ata masa rai."


  "Toh haka zaku cigaba da zama ne? Har zuwa yaushe? Kiyi masa magana dole da akwai abu a k'asa tunda shi yak'i yayi confronting naki ai ke se kiyi hala wani laifin kikayi masa baki sani ba."


  "Bazan iya ba mey zan fara ce masa? Bana son yaga kaman rashin kunya nake shirin yi masa I respect him alot."


  "Ai ba rashin kunya aka ce kiyi masa ba Amal cike da kissa zaki tambayesa idan laifi kikayi masa ya yafe miki da haka har ze sanar dake abinda kikayi masa seku daidaita tsakaninku."


  "Okay I'll try."


  "Yauwa yanzu tashi muje muyi karatu nasan idan kika je gida ba iyawa zakiyi ba in shaa Allah everything will be fine."





RANA D'AYA!

#RD


Love... King Miemiebee👄✨

[13/08, 09:38] ‪+234 907 483 8352‬: 🎀🎀🎀                 🎀🎀🎀

                🎀❣🎀

                   ❣❣


  💦💦                      🍃🍃🍃          

           *RANA D'AYA!*

  💦💦                      🍃🍃🍃

  August, 2018

 beeenovels.blogspot.com


     _Written by Miemiebee👄_



   *PAGE 3⃣3⃣*



    

   Se yamma Amal ta dawo gida bayan sun k'are karatu da Maamah. Driver na sauk'eta ta zarce d'akinsu inda ta tarar da Afzal yana shirin komawa gun Nazeefah ko sannu da zuwa beyi mata ba hasali yi ma yayi tamkar be ganta ba. Itace tayi gyaran murya ta gaishesa tukun ya amsa sama-sama. 

  "Zan koma gida gun Nazeefah ga kud'inki ajiye a gaban mirror" ya sanar da ita. 


  "Habib Albi tun yanzu zaka tafi?" Ta tambayesa tana mey duban agogo dududu 5:17 ne amma yake zancen nan bayan se pass 6 yake tafiya kullum. 


  "Eh wani abu ne?"


  "Habib Albi ko ka mance da alk'awarin da kayi mun?"


  "Na mey fa?"


  "Kace kafin ka tafi zamuyi wanka tare I miss bathing with you Habib Albi, I really do" tayi admitting abun tausayi. Kau da kansa yayi gudun kar tausayinta ya kama sa. 


  "Nata jiranki baki dawo ba Amal ni kuma sauri nake maybe next time."


  "Abinci fa kaci? Nasa Safiyya ta maka microwaving sauce d'in ta dafa maka white rice tayi?"


  "A k'oshe nake karki damu na wuce."


  "Yaya" ta kira sunansa da sauri lokacinda ya shiga takawa chak ya tsaya had'e da kewayowa. 


  "Wani abu ne?" So take tayi masa magana kaman yadda Maamah tace da ita amma inaa bata jin zata iya, mugun nauyinsa takeji bata son a sanadin hakan yaga kaman rashin kunya take son yi masa don haka kawai tayi shiru. "Sauri nake" ya sanar da ita. 


  "Ermm nace Allah dawo da kai lafiya ka gaishe da Nazeefah idan ka isa."


  "Kaman dagaske" ya furta chan ciki-ciki. 


  "Na'am?" Ta tambaya kasancewar bata jisa da kyau ba. 


   "Nace naji" da haka ya fice Allah kare Safiyya dake sharan parlour tayi mishi sannan ya k'arisa. 


   Safiyya na ganin fitansa tayi hanzari ta kammala sharan nata da wuri ta wuce d'akinta inda tasa key ta danna wa Nazeefah kira bayan sun gaisa take ce mata, "Aunty bazaki amince da abinda nake shirin fad'a miki ba."


  "Mene meya faru?"


  "Hmm yanzun Uncle ya bar gida toh kafin ya fito ina cikin share corridon d'akinsu naji su suna magana da Aunty."


  "Wai mey suke cewa?"


  "Nide ban gane kan zancen nasu ba amma naji tana ce masa wai yayi mata alk'awarin zasuyi wanka tare se gashi kafin ta dawo daga makaranta har yayi wankansa ya gama shiri."


  "Wanka tare?!" Nazeefah ta tambaya da d'umbun mamaki "Wanka tare de?" Ta sake nanatawa yayinda ta kasa amincewa da hakan. 


  "Wallahi Aunty."


  "Kaiiii inaaaa! Baki ji su da kyau ba, wannan k'arya ne."


  "Wallahi na jisu da kyau Aunty kuma daman tun ba yau ba ina zaton hakan dan akwai ranan da abokin Uncle yazo Uncle Sultan se yace inje inyi ma Uncle magana toh dana k'arisa d'akin nasu sena tarar da k'ofan a bud'e nayita sallama amman shiru chan dana kasa kunne najiyo hayaniyansu acikin bayin."


  "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un wallahi Amal mak'ira ce, shegiya 'yar asiri toh dan ubanta bazeyi wankan ba kiji mun karuwanci fah! Wato har wanka ma sukeyi tare? Chab!"


  "Hmm wallahi ko amma kuma kinsan tun dawowan Uncle wannan karan ko fita sau d'aya basuyi ba? Jiya kanma da tayi masa breakfast k'in ci yayi yace wai nice zan yi masa baya son nata. Bayan nan zama da sukeyi a parlour suyi kallo ma basuyi yanzu gashi banda d'ad'd'aure mata fuska ba abinda yakeyi yau tana da makaranta da safe amma yak'i kaita sa6anin kullum yace se de driver ya kaita shi yana da gun da zasa. Maganan da nake miki yanzu ko tsinke ban ga ya siyo mata ba tun zuwan sannan."


   "Ai kibari kad'an ta gani da izinin Allah se Ya Afzal ya tsani taka k'afa acikin gidanta kede kiyi k'ok'ari ki sato min littafin makarantar ta guda d'aya mu samu copy na handwriting nata, zata gani ba har wanka sukeyi ba? Allah kawo shi gida."


  "Zanyi k'ok'ari in samo miki bari in gudu ina kan aiki."


  "Jeki Safiyya aikin ki na kyau se anjima."


  "Toh se anjima" da haka sukayi sallama. 


   Fresh flowers Afzal ya tsaya ya amsa mata a florist shop sannan ya k'arisa sede har ya shigo parlourn bata mik'e tayi masa sannu da zuwa ba ko sallamansa ma k'in amsawa tayi. Da mamaki kwance a fuskansa ya k'arisa kan kujerar da take zaune ya zauna daga gefe. 


  "Rabba'atul Bait I'm home" ya sanar da ita. 


  "Sannu da zuwa" tace da shi zalla ba walwala tattare da ita. 


  "Rabba'atul Bait what's wrong?" Hannunta ya gwada rik'ewa wanda tayi saurin wabcewa "Sweetheart please talk to me keda nake marmarin in dawo wajenki saboda ki cire min bak'in cikin da 'yar uwarki ta cusa mun kuma kike haka? What have I done this time?"


  "Ai mey hali bai ta6a fasawa amma nagode." Cike da rashin fahimta ya tambayeta "Mey kike nufi Rabba'atul Bait please talk to me."


  "Ni de wallahi na gaji bazan iya ba da rashin mutuncin nan da tokari tunda baka sona kawai ka sallameni in tafi gida gun Mummy yaso ka cigaba da sha'aninka da amaryarka."


   "Wani irin magana kuma kike haka Rabba'atul Bait sanin kanki ne ina sonki kuma bazan iya rayuwa ba ke ba."


  "Wallahi baka sona Ya Rouhi" ta fad'a tana cika idonta da hawayen munafirci. 


  "Please don't cry darling."


  "Ka daina kira na darling tunda ba sona har zuciya kake ba, idan da har ka d'auke ni da muhimmanci kaman yadda na d'auke ka da Amal baza tana kirana tana mun gori ba."


  "Amal?"


  "Eh ita."


  "Oh Dear! Mey wancan ta kira kuma ta sake ce miki? Wallahi we're not on good terms with her girkinta haka ban d'ana ba tun zuwa na, mey tace miki?" Ya tambayeta ransa na 6aci. 


  "Ni baza ka ji komai daga bakina ba har ga Allah bazan so in had'a kanku ba amma de ka cigaba wallahi ranan da komi ya isheni tattara kayakina zanyi in koma gida inyi ma Daddy magana asan ya za'ayi tunda gashi a fili ka nuna baka sona kuma baza ka iya yin adalci a tsakanin mu ba. Ka nunawa Amal ni ba kowa bace banida daraja a idonka idan ba haka ba taya zata na kira na tana gaya mun magana iya son ranta?"


  "Nazeefah please calm down ke kanki kinsan I'll never do this to you, I love and respect you alot, dan Allah ki daina magana haka kiyi hak'uri mey yayi zafi da zakice zaki koma gida? Believe me duk abinda Amal ta kira tace miki nayi mata wallahi k'arya take don ko tsinke ban sai na bata ma tun komawa na." 


   "Ai idan da har ba kayi mata abubuwan dagaske da koda wasa bazata kira tace mun gashi ba nasan ba k'arya take mun ba." 


  "Ni ke miki miki k'aryan kenan Rabba'atul Bait? Please tell me what is it that Amal told you."


  "Ka kirata ka tambayeta da kanka ni bazan had'a kanku ba."


  "Ita d'in ba so take ta had'a kanmu ba take kiran ki take miki k'arerayi a waya? Please tell me."


  "Dan tamun haka nima senayi mata? Ai ko addini cewa yayi karka sak'a wa mutumin da yayi maka sharri da sharri Allah ma shaida ne ni da zuciya d'aya na d'auki Amal amma ita kam ba haka bane."


   "Rabba'atul Bait wallahi ba k'arya nake miki ba I and Amal aren't even speaking to each other ko tamun magana shareta nake saboda na gaji da kalan abubuwan da take yi miki, I'm tired." 


   "I'm not buying any of your lies again Ya Rouhi zaka ce mun bakuwa magana da Amal bayan d'azun nan na kirata dan mu gaisa take ce min kana jiranta a tub zakuyi wanka tare."


  "Amal d'in?"


  "K'arya zanyi maka ne?" wayanta ta janyo ta shiga call logs ta nuna mai wayan da sukayi da Amal d'in. Kuma tabbas ta kirata d'azu sun gaisa amma bawai Amal tayi mata magana makamancin haka ba. 


  "Innalillahi!" Ya furta cike da tashin hankali "Wallahi tallahi k'arya take yi miki Nazeefah-"


  "A'a Ya Afzal" tayi saurin katsesa "Karka 6ata lokacinka, ba seka mun bayanin komai ba na riga na fahimceka na sani kafi son Amal akai na dama idan ba ni da shashanci bama taya zan had'a soyayyan da kake mun da wacce kake yima Amal ita da take matar so a gareka bayan ni auran had'i akayi mana? Ni abu d'aya nake buk'ata kawai ka sawwak'e mun in koma gida bazan iya ba da wannan walak'anci da cin fuska" ta k'are tare da rushewa da kuka. Sosai ransa ya mugun 6aci yayinda wutan tsanan Amal ke sake ruruwa a zuciyarsa. Gabad'aya ji yayi ta fita masa a rai, amma ko tana tattare da babban asara. 

   "Rabba'atul Bait" ya kira sunanta cike da tausayi yana mey k'ok'arin rungumarta sede tayi saurin janye jikinta yayinda ta cigaba da kuka. 


  "Nazeefah dan Allah kiyi hak'uri kibar kukan haka I'm dearly sorry."


  "Ka rik'e hak'urinka Ya Afzal ba laifinka bane don zuciyarka ta fi kwanciya da Amal akai na, ni kawai ka sawwak'e mun zey fiye mun kwanciyan hankali idan ina gida gun iyayena."


  "Please don't talk like this wallahi k'arya Amal take yi miki you have to believe me" a hankali ya janyota jikinsa yana hugging nata "Idan kika tafi wa ze zame Rabba'atul Bait d'ina? Please stop crying I love you and you know it isn't that all that matters Sweetheart? By Allah duk abinda Amal ta ce miki nayi mata k'arya ne ki yarda da ni" be d'agota ba seda tabar kukan munafircin nata. Hak'uri yayi ta bata ranan throughout chan dare da yazo yin wanka yace suyi tare Nazeefah tana so tana kaiwa kasuwa wai ita baza tayi ba. Lalashinta yata yi har seda ta amince suka shiga bayin wasa suka yita yi sannan sukayi wanka a k'arshe ya sanyata sukayi alwalan bacci kaman yadda Amal ke tunasar masa kullum. Da kansa ya sanya mata kayan baccinta sannan suka kwanta inda yata tattalinta yana mata wasu irin abubuwan da tuni yasa ta fita daga hayyacinta. Wani irin so na musamman Afzal ya shiga nunawa Nazeefah na d'an kwana biyun da sukayi, ji yayi kaman kada ya tafi da kwanansa ya k'are sam baya sha'awan komawa gun Amal gabad'aya ta fita akansa da abubuwan da takeyi. 


  "Ya Rouhi har six baka fara shirin tafiya ba ka manta yau kwanan ka ya k'are anan?"


  "Ba se gobe ba?"


  "Gobe kuma? Da Allah ka tashi ka shirya kar mu shiga hak'k'in Amal."


  "She can wait se bayan Maghrib zan tafi."


  "Ni baza ayi rashin adalcin nan da ni ba gaskiya."


  "Tashi ka shirya Ya Rouhi."


  "Zo ki d'agani toh."


  "Ni da kai wa ze d'aga wani?"


  "We wouldn't know until you give it a try so zo ki d'agani" bata sake musu ba ta k'arisa kan gadon. Hannun sa ta kama ta shiga ja sede ko motsawa baiyi a lokaci d'aya ya jata bata sauk'a ako ina ba se akan jikinsa inda sukayi gware. 


  "Awch!" Ta furta tana murza goshin nata "Ya Rouhi!" Tayi exclaiming. 


  "Toh ai na fiki jin zafi."


  "Tayaya?"


  "Ba goshinki yafi nawa tudu ba."


  "Wallahi k'arya ne banida goshi" ta fad'a had'e da kai masa bugin wasa a k'irji. 


  "Mu gwada ne?" Yace yana mata dariya. 


  "Ban sanin ba ni ka sakeni" ta fad'a tana k'ok'arin mik'ewa, kankameta ya sakeyi a jikinsa tare da placing mata kiss a gefen baki hannu tasa ta dirje ita a dole tayi zuciya yace mata mey goshi at once yayi flipping position nasu ya zammana shi a sama ita a k'asa. 


  "Babe you're the most beautiful girl I've ever seen."

 

  "Ba wanin nan nice mey goshi ba? Tashi ka barmun gida jeka samu amaryarka."


  "Haba Rabba'atul Bait idan kika koreni gun wa zanje?"


  "Amal mana of course."


  "Nifa nace ki daina kawo mun magananta."


  "Nide d'agani." 


   "Haba my beautiful Rabba'atul Bait" yayi maganan had'e da matso da fuskansa gab da nata yayinda ta zagaye hannayenta a wuyansa "I love you Babe" ya sanar da ita. 


  "I love you too Darling" a hankali ya sauk'e lips nasa akan nata ya shiga kissing nata yayinda take miyar masa da martani kaman wasa suka fara wuce gona da iri kafin su hankara har sun wula wani duniyan daban. Bayan sun gamsar da juna suka yi wanka tare Nazeefah na mik'e akan gado tana kallon Afzal cike da adoration da soyayya yayinda yake faman neman kayan da ze sa a wardrobe. Wayansa dake kan gado ne ya shiga ruri ko motsawa Nazeefah dake kan gadon batayi ba ina irin ita ba ruwanta da yi mai shisshigi d'innan shi da kansa yace "Who's calling?"


  "I don't know" ta mayar masa tana gyara d'aurin towel nata. 


  "Duba" ya umarceta. Lek'awa tayi taga Kitten❤💍🔐 na flashing akai ga picture'nsu da yayi saving contact natan dashi wani selfie'nsu ba hassada sunyi kyau. 


   "Amal ce" ta amsa tana k'ok'arin 6oye kishin daya rufeta lokaci guda "Ayya taji shiru."


  "D'aga kice mata idan nayi sallah zan shigo."


  "Ya Rouhi kana ganin yin hakan ya dace?"


  "Toh ki bari seta ga shigowa na kawai" ya amsa tare da juyawa yana mey cigaba da neman abinda ze sa. Bada dad'ewa ba sega Amal na sake kira wayan ta d'aga tayi answering had'e da yin shiru. 


  "Halo Habib Albi?"


  '"Yar uwa Nazeefah ce" ta sanar da ita. 


  "Oh Nazeefah, ina yini?"


  "Lafiya k'alau, kinji Ya Afzal shiru ko? Yana hanya abu ne ya rik'esa."


  "Ayya ba komai seya shigo toh."


  "Aha seda safe" da haka sukayi sallama sauk'e wayan tayi tana ma Afzal murmushi yayinda shima ya miyar mata yana mey mamakin hali irin na Amal ace duk yadda Nazeefah ke sonta har take kirarta da 'yar uwa amma se tana kiranta tana irga mata ababen da tasan zasu 6ata mata rai. Seda sukayi sallan Maghrib sannan Afzal ya tafi yau har doubling kud'in daya saba ajiye musu yayi wa Nazeefah ita kam dad'i kasheta she can't wait ta gama aikin ta akan Amal ta fiddata daga gidan finally. 


  Yana isa gida Amal ta bud'e k'ofa tayi masa sannu da zuwa tana cewa bari tayi hugging nasa yaja da baya. Dama a cike take dam tunda ta kirasa taji Nazeefah ta d'aga wayansa gashi yau se bayan maghrib ya shigo abinda be ta6a yi ba. Kuka kawai ta rushe da sede da mamaki taga ko d'aga kai Afzal beyi ba bale yasan tanayi. "Excuse me" yace da ita yana neman wuceta hannu tasa ta dakatar da shi. 


  "Yaya mey nayi maka haka ka za6i kana shareni kana wulak'anta ni a gidan nan? Idan wani laifin nayi maka dan Allah ka fad'a mun a shirye nake da in baka hak'uri" ta sanar da shi cikin tsan-tsan kuka. Shi dariya ma ta basa bayan duk rashin hankalin da take tafkawa still tana da bakin da zata tambayesa mey tayi? Lallai she thinks she's smart. Kallonta kawai ya tsaya yi ko uffan bece mata ba. 


  "Yaya please talk to me I can't do this anymore yau kwana nawa idan ka shigo mun sede kayita d'aura mun fuska, ka daina cin girki na, d'an gifts da ka saba siyo mun ka daina, ka daina kwanciya da ni yanzu ko jikinka kana neman hanani ta6awa baka tunanin hukuncin nan da ka yanka yayi tsauri dayawa?"


  "Yayi tsauri fa kikace Amal? I'm truly disgusted at you I never expected this from you how could you stoop this low? Tell me mey kikayi benefiting da wannan abun kunyan da kikayi mun kika kuma yi wa kanki?" Ya tambayeta cike da tsiwa. Hawaye take sosai yayinda kanta ya d'aure shin mey yake fad'i? Wani abun kunyan tayi masa?


  "Yaya wani irin magana kakeyi? Wani abun kunya nayi maka please talk to me ban fahimce ka ba."


  "Ai dama baza ki ta6a fahimta ta ba Amal you know what? I don't have time for this idan kinsan k'arya zaki tsaya kina mun just forget it."


  "Yaya dan Allah kar kayi mun haka I beg of you wallahi ba k'arya nake maka ba" ta rok'esa cikin tsananin kuka. 


   "Ohhh itace take k'arya kenan?"


   "Ita wa?"


  "Seriously Amal? Har tambayana kike ita wa? Kin d'au magana baze zagayo kunne na bane? Kede ki cigaba."


  "Wallahi ban fahimceka ba Yaya bansan akan mey kake magana ba kuma a iya sani na ban yi maka wani abun ba sede ban sani ba ko a bisa rashin sani yet still zan baka hak'uri dan Allah kayi hak'uri ka rage wannan hukunci wallahi yayi mun tsauri dayawa Yaya can't you see? I'm slowly losing my mind and going crazy fushinka a gareni ba k'aramin tashin hankali bane please kayi hak'uri ka gafirceni I'm dearly sorry."


  "Idan ba kiya son ina fushi dake se ki iya bakinki ki koyi rik'e sirrin gidanki ki dena buga waya tako ina kina irga wa mutane abinda mijinki yake miki, how could you Amal? I thought kina da hankali kuma kinsan abinda ya kamata ashe ba haka bane, wallahi ba halin ki bane ban san ki da halin nan ba."


  "Ni Yaya? Wa na kira na sanar dashi sirrin gidan nan? Wallahi ban buga wa kowa waya ba ko Mami."


  "Kiji I don't have time to listen to your lies because a sane nake da komai don haka ba abinda zakice da zaisa in amince dake I've heard enough and I'm very disappointed with you ban ta6a sanin kina da wannan mumunan hali ba amma ki cigaba ni bazan miki baki ba sede inyi miki fatan shiryuwa idan ma k'awaye kike bi suke rud'anki suke d'aura ki akan gur6arcacciyar hanyan nan gara tun wuri kin rabu da su ina Safiyya!" Nan Safiyya dake lek'ansu ta koma cikin d'akinta a 360 seda ya sake kiranta a karo na biyu sannan ta fito tana wani hamma irin bacci takeyi ya kirata d'innan. 


  "Ina yini Uncle?" ta gaishesa. 


  "Lafiya ki dafa mun indomie biyu da k'wai biyu kiyi sauri I'm hungry."


  "Akwai abinci fah Rice and Stew Aunty ta girka."


  "Ina sane ai nace ki dafa mun indomin."


  "Toh" da haka ta wuce kitchen d'in wani pathetic look ya bawa Amal ya wuceta ya shige d'akinsu. Har k'asa ta sauk'a tana kuka wajen gabad'aya ta rasa mey ke mata dad'i sam bata da masaniya ga abinda Afzal yake cewa mey yake nufi da ta daina kiran mutane tana yad'a musu sirrin aurenta a ina tayi hakan? Ita da ko da iskokai suka shafeta ma bata kira Mami ta sanar da ita ba wani sirri yake nufin tana yad'awa idan akwai mutumi d'ayan da ta mar maganan aurenta itace Maamah kuma ta yarda da Maamah tasan Maamah baza ta ta6a ci mata amana ba. Kuka tayita sha wajen har zuwa lokacinda Safiyya ta gama abincin Afzal ta ajiye masa kan dining gun Amal ta k'arisa ta durk'usa. 


  "Aunty kiyi hak'uri dan Allah ga abincin Uncle yayi."


  "Kije kice mishi ya fito."


  "Da kaina?" Kai zalla ta gyad'a mata nan ta wuce bayan tayi mar sallama ta sanar dashi ta gama godiya yayi mata sannan ta dawo kan Amal tana cigaba da bata hak'uri kaman dagaske. 


  "Kije d'akinki Safiyya ba komai" haka Afzal yazo ya tarar da ita zaune a wajen, ko kallonta beyi ba ya k'arisa dining. Da k'yar ta tattara kanta ta koma d'aki Qur'ani kawai ta d'auka ta shiga karancewa shi kad'ai take jin ze iya rage mata wannan k'unci da bak'in cikin da takeji. Bayan Afzal ya gama cin abinci yazo shiga d'akin yaji sautin karatunta na tashi, na d'an lokaci ya tsaya ya saurareta sannan ya koma parlourn ya cigaba da zama be sake kewayowa d'akin ba se da ya tabbata tayi bacci wajajen sha d'aya kenan. Tsince akan gado tana bacci ya tarar da ita da alama karatu take bacci ne ya d'auketa don ga handouts nata baje a gabanta, Jallabiyan jikinsa ya tu6e sannan ya tattare handouts d'in ya ajiye a gefe ya gyara mata kwanciyan nata ya haura ya kwanta daga chan gefe shima had'e da kashe musu wuta. 


   Haka ya cigaba da d'aga mata kai yana shareta, washegari Amal tayi kuka har ta godewa Allah test da ta rubutan ma dukda cewan tayi karatu batazo ta gane mey ta rubuta ba saboda gabad'aya ba hankalinta a jikinta. 


   "Amal kiyi hak'uri haka kukan nan ba shida amfani" fuskanta daya kumbura tim ta d'ago daga kan benchi tana share hawayenta "Maamah a rayuwa ba abinda na tsana kuma yafi k'ona mun rai kaman banyi abu ba ace nayi fisabilillahi ko ke na ta6a sanar dake sirrin gida na ne in ba wannan karan da matsaloli suka yi mun yawa ba?" Kai Maamah ta kad'a mata a hankali cike da tausayi "Amma cemin yayi wai ba aiki na se buga waya wa mutane ina sanar dasu sirrin gida na harda wai ya d'au ina da hankali ashe babu duk na munafirci ne Yaya fa Maamah, Yaya yake kwatantani da wannan munanan kalamu" ta sake rushewa da wani kukan. 


  "Amal ki kira Mami ki sanar da ita kawai taya Ya Afzal ze miki haka ina laifin ma ya sanar dake laifin da kika yin amma haka kawai ya barki acikin duhu ai ba yi bane hakan."


   "So kike ya gama tsanata idan na sanar da su Mami? Ban kira kowa bana yace ina kiran waya ina yad'a sirrin gida na bale har in kira Mami? Hmm ashe ina tona kabari na da kaina kenan."


  "Toh ya zakiyi Amal? Ni anya kuwa ba kishiyarki bace take neman had'a kanki da Ya Afzal?"


  "Nazeefah wai?"


  "Sosai ma kiyi tunani mana mey yake nufi da yace miki ita take k'aryar? Nazeefah yake nufi."


  "Da wuya idan itace I trust Nazeefah bata da wani mugun hali kuma kinga ita bama zuwa gida na take ba bale ace taga wani abun taje tayi mai gulma."


  "Don't get too confident trusting her Amal wallahi halin mutum se Allah idan ba haka ba waze shiga tsakaninki da Ya Afzal haka?"


  "Maamah ban sani ba amma zan cigaba da addu'a har se idan Allah ya amsa kuka na."


  "Toh Allah taimakeki ya shige miki gaba Amal shi kuma Ya Afzal Allah sa ya gano gaskiya ya sani cewa idan mutum yayi laifi confronting nasa ake bawai a rik'e shi a zuci ana k'untata mai ba."


**

  Washegari kasancewar Amal tana iya kai har yanma a school ta yi girkin rananta tun da safe kafin ta fita. Abinda Safiyya zatayi kawai tayi wa Afzal microwaving ne idan ya dawo daga office that is idan ze ci ma kenan tunda yanzu ya k'aura daga cin girkinta. Tun k'arfe sha biyu ya dawo gida yana shiga ciki yaga cup da snacks haka akan table sekace anyi bak'o sallama yayi Safiyya ta fito tayi mai sannu da zuwa. 


   "Auntinki na gida ne?"


  "A'a ta fita school."


  "Wannan fah?" Ya nuna cup d'in "Kinyi bak'uwa ne?"


  "A'a Aunty ne ta shigo bada dad'ewa ba ita da wani."


  "Excuse me?!" Yayi exclaiming had'e da zaro idanunsa waje. 


  "Yanzu suka bar nan."


  "Ita da wa?"


  "Ita da wani na miji suka shigo ta d'au wasu takardu suka d'an zauna se suka sake fita tace tayi mantuwa ne."


  "Amal ta kawo na miji gidan nan?" Sam ya kasa amincewa da hakan. 


  "Ni na d'au ma ko d'an uwanta ne yadda suka zauna a kujera d'aya."


  "A kujera d'aya!?" Ya sake tambaya idanun nan kaman zasu fad'o a k'asa dan mamaki. Dan yadda zuciyarsa ta shiga k'ona ko k'ala be sake cewa da Safiyyan ba take idanunsa suka kad'a sukayi ja. Cikin wani irin taku ya k'arisa d'akin nasu kawai ji Safiyya tayi ya buga k'ofan wane yana neman 6allesa, d'aki ta koma jiki na rawa ta kira Nazeefah. 


  "Aunty na aikata, kuma wallahi ya amince."


  "Kai haba!"


  "Bakiga yadda yake ta nishi ba kaman zaki."


  "Kinyi dai-dai ai in shaa Allahu kwanan Amal a gidan nan ya kusa k'arewa aikinki na kyau."


  Amal baiwar Allah da tun fitanta k'arfe sha d'aya se biyar ta dawo bata san meyake jirarta ba a gida. A galabaice driver ya dawo da ita tana shiga parlour ta tarar da Afzal zaune kan kujera ko d'aga ido beyi ba bale yasan mutum ya shigo gidan se harkan gabansa kawai yake itama bata yi mai magana ba sanin ko tayi ba amsata zeyi ba. Da mamaki ya bita da kallo wato ma ko magana baza tayi masa ba lallai rainin har ya kai haka? Bayan ta kawo masa k'ato gida ta dawo kuma bazata iya ce mai sannu ba, wuyanta ya kai yanka. Da abinda zata sak'a masa kenan duk kalan halaccin da yayi mata a rayuwa? Wajajen goma ya koma d'akin kwance akan gado ya tarar da ita a galabaice. 


   "Kibar min d'akin nan kije ki kwana wani wajen" yace da ita zallah.


  Da mamaki ta tsaya kallonsa ashe Allah ze kawo ranan da zeyi mata gori akan abubuwan da yayi mata a rayuwa? Ko k'ala bata ce da shi ba ta d'au pillonta da waya ta bar masa d'akin bayanta yabi yayi locking k'ofar sannan ya dawo ya kwanta yana mamakin wannan sabon d'abi'artan wato ma tsabagen tasan halinta ta kuma san mey takeyi shiyasa ko a bakin zaninta bale ta tambayesa dalilin da ze hanata kwana masa a d'aki ba. Toh ta cigaba. 


  Ta d'ayan fannin kuka Amal ta kwana tana yi bata jin zata iya da wannan walak'anci mey yayi zafi da ze koreta daga d'aki? Saboda bata kawo ko tsinke gidan ba? Da k'yar bacci yazo ya d'auketa. Kasancewar tana da morning lectures washegari bayan Asuba tayi wanka sannan ta wuce d'akin nasu dan d'auko kayan da zata sa sallama tayi jin shiru seta bud'e k'ofan amma bata gansa a ciki ba don haka kawai ta yanke hukuncin yana bayi ne. Wajen wardrobe ta nufa ta shiga fiddo da kayan da zata sa tana cikin hakan Afzal ya fito daga bayi ko juyawa ta kallesa batayi ba harkan gabanta ta cigaba da yi daga wajen wardrobe ta k'arisa gun mirror ta tattara man shafawanta da turare da sauran abubuwan da zata buk'ata ta fice. Binta da kallo yayi shima bece da ita ko k'ala ba. Tana gama shirinta tayi ma driver magana ko tambayan Afzal kud'in makaranta batayi ba sallama kawai tayiwa Safiyya ta fice. Yau ma kaman jiya Afzal ya riga Amal dawowa and thesame thing cup ya tarar a kan centre table da plate na abinci daya tambayi Safiyya still ta basa amsa irin na jiya akan Amal ce ta shigo da wani basu jima da tafiya ba. Na matuk'a ransa ya 6aci yau kam baya jin ze iya d'aukan rashin hankalin nata abun ya ishesa zama yayi a parlourn yana jiran dawowanta chan bada dad'ewa ba ta iso yau ma a galabaice. Kanta ta sunkuyar lokacinda ta shiga parlourn har ta kai ga wucesa ya kira sunanta chak ta tsaya had'e da kewayowa. 


   "Wa kika kawo mun gidan d'azu?"


   "Mey kake fad'i Yaya? 


  "I'm not repeating myself Amal wa kika kawo mun gida d'azu?"


   "Wa zan shigo maka dashi gida Yaya? A iya zama na da kai na ta6a shigo maka da na miji gidan nan ne? Why don't you believe me Yaya? Na d'au ko da an fad'a maka hakan bazaka amince ba saboda a tunani na kafi kowa sanin hali na, a tunani na kafi kowa sanin abinda zan iya aikatawa da abinda bazan iya ba I'm so disappointed with you Yaya" ta tsaya ta numfasa yayinda hawaye yake ciko mata a ido "Ina soyayyar da kake ikirarin kana mun? Ashe za a iya fad'a maka magana akaina ka hau ka zauna akai ba tare da kayi bincike akai ba?"


   "Stop acting like you're the Amal I used to know saboda gabad'aya kin canza, I can't trust you anymore Amal yau komin ya girman laifi yake aka ce mun kin aikata zan amince saboda I've lost my trust in you since the day kika fara d'iban sirrin gidan ki kina yad'a wa jama'a."


  "Allah ma shaida ne ban ta6a kwasan abinda kake mun a gidan nan na fad'awa kowa ba not even Mami" ta amsa tana share hawayenta. 


  "Ki bud'e kunnenki ki saurareni da kyau ban yafe ba idan kika sake kawo mun wani k'ato cikin gidan nan."


  "Yaya please idan wani abun nayi maka ka fito fili ka fad'a mun amma ka daina cemun nayi abinda ban aikata ba, yaushe na shigo gidan nan tun fita na bale har in shigo da wani?"


  "Da ace ban shigo na tarar da ragowan snacks da drink da kikayi serving nasa bane se ki gaya mun maganan banza."


  "Drink? Wallahi ni ban kawo wani gidan nan ba ka kira driver ka tambayeshi ko ya dawo dani gida tun fita na da safe in ba yanzu ba."


  "You're not as smart as you think you're Amal and ki cigaba."


  "See Yaya idan gajiya dani ne kayi kawai ka fad'a mun I'll understand you it's too early for this, taya banyi abu ba ina ji ina gani zaka na mun sharri da fari kace ina kire-kiren waya ina baza sirrin gida na a waje yanzu kuma zargi na ka fara? Har kana tunanin kai na ya waye da zan fara kawo maka maza a gida? Wallahi a da koda wasa aka cemun zaka yi mun abinda kakeyi mun yanzu bazan amince ba amma ka cigaba dama nasani dole wataran zaka goranta mun tun da har ka iya ka koreni daga d'akinka jiya." Bata jira jin mey zece ba ta wuce d'akin data koma a guje. Kuka ta shigayi daga haka har ta fara yin amai, bata tsaya ba seda ta harar da abincin cikinta tas har jiri na neman d'ibanta. Da rarrafe ta k'arisa d'akin ta kwanta ahaka har wahalallen bacci ya d'auketa. Next da ta tashi Safiyya ke ce mata Afzal ya riga ya tafi kai kawai ta gyad'a mata har ta tashi zata tafi seta kira ta. 


  "Na'am Aunty?"


  "Mey kika cewa Ya Afzal jiya da bana gida?"


 "Game da mey Aunty?"


  "Kinsan mey nake nufi ai."


  "Wallahi ban fahimce ki ba dan ni magana ma be had'ani da Uncle ba."


  "Waya ce mishi na shigo da na miji gidan nan?"


  "Na miji? Wallahi bani bace Aunty dan meyasa zan miki sharri? Wallahi bani bace."


  "Shikenan tashi ki tafi." Chan bayan sallan Isha ta fito kitchen dan had'a custards ta sha sanadin wani irin yunwan da ya dameta. Tana tsaye a kitchen tana jiran ruwan ya tafasa Safiyya ta shigo zata dafa indomie. 


  "Ki d'au k'wai biyu ki soya" tace da ita. 


  "Toh Aunty nagode" jiki na rawa ta bud'e fride d'in ko ya akayi kawai d'aya ya ku6uce daga hannunta ya fad'i ya fashe. 


  "Subhanallahi! Ya akayi haka Safiyya?" Amal tayi saurin tambaya tana neman toshe hancinta. 


  "Aunty dan Allah kiyi hak'uri wallahi ban sa ya akayi ba bari in goge da wuri ina tissue" kafin ace mey k'arnin ya mamaye kitchen d'in gabad'aya gas d'in Amal ta kashe da wuri sannan ta juya sink ta shiga kwararo amai, amai tayita yi wane zata harar da hanjinta yayinda Safiyya ke bata hak'uri. Bakinta ta wanke Safiyya ta taimaka ta jata izuwa d'aki.  


  "Sannu Aunty kina buk'atan wani abun?" Kakkarwa take sosai ta kad'a mata kai "Ki had'a mun black tea kawai."

  

  "Toh ina zuwa" nan da nan ta had'o ta kawo mata. 


  "Shikenan kina iya tafiya."


  "Ba wani abinda kike buk'ata?"


  "Babu kar ki damu."


  "Allah sawwak'e." 

Da k'yar Amal ta samu ta sha rabin tea d'in taji ta k'oshi zazza6i ne ya rufeta a lokaci guda ko makaranta ta kasa fita washegari ga shi jikin nata ya d'au zafi. Maamah ce da ta jita shiru ta kira dan tambayan ko lafiya. 


  "Wallahi zazza6i Maamah kaman zan mutu."


  "Allah sarki shafakillahu habibty Allah baki lafiya."


  "Ameen nagode."


  "Na yi miki assignment d'in na mana submitting."


  "Allah sarki Maamah kaman kinsan ina ta bi a raina wallahi nagode sosai Allah ya bar zumunci."


  "Ameen munyi waya da Ya Abdul ma yace in gaisheki."


  "Allah sarki ina amsawa."


  "Ya Afzal fah? Be kaiki asibiti bane?"


  "Ya koma gun Nazeefah tun jiya ai."


  "Baki kira kin sanar da shi bakida lafiya bane?"


  "Ko nayi mey zai mun? Kin manta ba wanda ya tsana kaman ni ne a duniyan nan yanzu?"


  "Allah sarki Amal do you need anything? Wallahi Ya Afzal bai kyautawa." 


  "Ba komai Nazeefah wataran se labari nagode" ta amsa hawaye na tsiyaya mata daga ido. 


  "Gobe zan shigo in duba ki in shaa Allah ki huta kinji? I love you."


  "I love you too sekinzo."


****

  Se wajajen sha biyu Amal ta samu k'arfin jiki a gida ta yini ranan ba inda taje, chan Maghrib nayi kuma zazza6in ya sake tashi ga amai idan ta fara kaman zata harar da kayan cikinta sosai Safiyya ta tausaya mata take kuma k'ok'arin kula da ita. Har anan Afzal be san mey ake ciki ba kaman yadda be kira Amal ba haka itama bata kirasa ta sanar da shi batun rashin lafiyarta ba ko Mami bata kira ba. 


  Bayan Safiyya ta tattare plate d'in ta fita dashi Amal ta janyo wayanta ta shiga calender tana counting yau kwana uku kenan da missing period nata anya kuwa lafiya? Kode? Subhanallahi it can't be possible Allah yasa ba abinda take zargi bane inde haka ne ya zamo dole gobe taje asibiti ta tabbatar da koma mey amma fatanta Allah yasa ba abinda take zargi bane. Se sha d'aya ta fita washegari bayan da zazza6in nata yad'an sauk'a. A wani private clinic Driver ya sauk'eta inda ta k'arasa ta bud'e file tukun ta shiga ganin doctor tayi mata bayanin yadda takeji. Murmushi likitan tayi mata tace "Amma Amarya ce ke ko?" Kai Amal ta gyad'a mata cike da rashin fahimta. 


  "Shiyasa ai."


  "Ban fahimce ki ba Dr Sadiya."


  "Congratulations you're pregnant Mrs Abdallah."


  "Pregnant?" Amal ta nanata cike da k'in yarda "Taya bakiyi mun gwaji ba bakiyi komi ba kice ina da ciki?" Murmushi ta saki kad'an "ni da aiki na kuma Mrs Abdallah ai ko ban miki gwaji ba idanunki kad'ai ma shaida ce kina d'auke da juna biyu."


  "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" taji Amal ta furta. 


  "Lafiya?" Tayi saurin tambaya. 


  "Dan Allah kiyi mun tests d'in tukuna I can't be pregnant at least not when babu jituwa tsakani na da mijina, I can't be pregnant Dr please do something" ta fad'a cike da tashin hankali. 


  "Subhanallahi please calm down, taya zaki k'i kyauta daga Allah haka Mrs Abdallah?"


  "Ba haka bane Dr matsaloli sunyi mun yawa and cikin nan will only add to it please help me."


   "That's where you're wrong wannan ciki sede ya warware miki duk wani matsalan da keda mijinki kuke fuskanta, ki yarda dani mijinki na jin wannan news ze sauk'o daga kowani irin temper yake kai, kede ki godewa Allah kawai" ta sanar da ita ta na wani rubutu jikin wani paper "Ga wannan kije next room zasu yi miki scanning mu gano sati nawa ne duk abinda akwai zasu sanar dake kafin ki fara zuwa pre natals naki, congratulations once more." Jiki na k'yarma Amal ta amshi paper'n "Don't be afraid Mrs Abdallah in shaa Allahu juna biyun nan shi ze zame sanadin shirya tsakaninki da mijinki."


  "Toh nagode Dr."


  "Sey kuma ga wannan magunan basuda k'arfi in shaa Allah baza suyi komi wa cikin ba, zasu rage yawan jin jiri da kuma yawan yin amai da zazza6in duka, Allah inganta."


  "Ameen Dr nagode se anjima." Next room ta shiga inda akayi mata scanning cikin. Kwata-kwata ma cikin sati uku ne sede maimakon Amal tayi murna tun dawowanta gida take aikin kuka gabad'aya ta rasa meke mata dad'i bata ma san wa zata fara kira ta sanar da shi wannan labari ba abu d'aya da ta sani shine Afzal ne mutumi na k'arshe da zata kira ta sanar da shi. Tunda ya fara zarginta yanzu ai da k'yar ma idan ze amince cikinsa ne a jikinta, ya zatayi? Wannan musiba da mey yayi kama??






RANA D'AYA!

#RD


Love... King Miemiebee👄✨

[13/08, 09:39] ‪+234 907 483 8352‬: 🎀🎀🎀                 🎀🎀🎀

                🎀❣🎀

                   ❣❣


  💦💦                      🍃🍃🍃          

           *RANA D'AYA!*

  💦💦                      🍃🍃🍃

  August, 2018

 beeenovels.blogspot.com


     _Written by Miemiebee👄_



   *PAGE 3⃣4⃣* 



      


    Ko makaranta Amal ta kasa fita washegari saboda yadda jikin nata ya tsananta, gashi de ta fara shan maganin amma ba sauk'i. Kaman yadda Maamah ta d'au alk'awari haka tazo ta duba Amal da soft drinks nata, Safiyya ce ta amsa ta sa a fridge sannan ta kai ta d'aki inda Amal ke kwance akan gado ta duk'unk'une kanta acikin bargo se kakkarawa take. K'arya ne mutum ya ganta be tausaya mata ba. 


   "Subhanallahi Amal!" Maamah tayi exclaiming cike da tashin hankali. "Amal dan Allah karki mutu" take idanunta suka ciko da hawaye tsan-tsan tausayi. 

   

  "Amal mey kike yima kanki haka? Meyasa baki kira Mami ba? Meke damunki dan Allah?"


  "Maamah calm down ki kwantar da hankalinki."


  "Ya jikin naki? How are you feeling?"


  "Da sauk'i zuwa anjima zazza6in ze sauk'a morning fever ne."


  "Subhanallahi sannu ai baki fad'a mun zazza6in yayi tsanani haka ba what's wrong?"


  "Maamah I'm pregnant" ta sanar da ita. 


  "You're what?!" Tayi exclaiming had'e da zaro ido waje. 


  "Maamah ina d'auke da cikin Yaya" ta jaddada mata yayinda ta rushe da kuka. Hugging nata Maamah tayi tana kukan tare da ita sun dad'e a haka sannan ta janye Amal a hankali tana mey share mata hawayenta. 


  "Amal I'm so happy for you, Allah ya inganta idan lokacin yayi ya raba lafiya."


  "Ameen" ta amsa chan ciki-ciki. 


  "Ya Afzal ya sani?"


  "Ke na fara fad'awa ko Mami ban kira na sanar da ita ba."


  "Amal why? Ai Ya Afzal ya kamata ya fara sani ke bakisan wannan news shi ze zame sanadin shirya tsakaninku ba?"


  "Shirya tsakanin mu?" Ta tambayeta had'e da sakar da murmushin takaici "Maamah things just got worst kin san mey Yaya yamun?" Kai Maamah tayi saurin kad'awa. 


  "Korana yayi daga d'akinsa shiyasa kika ganni anan bayan nan jiya yake ja mun Allah ya isa idan har na sake shigo masa da na miji gida Maamah zargi na Yaya yake, gani yake kaman duk zaman mu cin amanan sa nake."


  "Innalillahi wa inna ilai raji'un the fuck is wrong with Ya Afzal? Ya yake abu kaman wanda baida ilimi? Ai yaci ace yasan abinda zaki iya aikatawa da abinda bazaki iya ba daga gun wani d'an jakar uban yaji wannan batu? Waya gaya mishi kina shigo da maza gidan nan?"


  "Wallahi ban sani ba Maamah kinsan zurfin cikin Yaya bayi ta6a fitowa fili ya fad'awa mutum abu."


  "Amal dan Allah ki tattara kayakinki kibar mai gidan nan haka wannan walak'anci dame yayi kama? Se kikace mishi mey dayace kibar masa d'akin nasa?"


  "Mey kuwa zance masa? Pillow na kawai na ja na fice mey zance masa?"


 "Hmm wallahi munafukar mey aikin ki d'innan nake zargi da ganin yadda fuskanta yake bak'i k'irin d'innan haka zuciyarta take in ba haka ba ina Ya Afzal zeji batun nan? Bawai zama yake a gida koda yaushe ba dole gaya mishi akeyi."


 "Na gwada mata magana tace ba ita bace banida lafiya ban so jan maganan ba nace kawai shikenan."


  "Wallahi itace kinji rantsuwa ba kaffara ina gaya miki Nazeefah ba kishiryar arziki bace wallahi aiki suke tare da 'yar nan dalilin daya sa tun farko ta kawo miki ita kenan. Wallahi aiki suke tare."


   "Nazeefah kuma?"


  "Don't be fooled by her kind gestures makashinka na nan tare da kai duk inda kake, kiyi tunani ita munafukar Safiyyan ce take kai wa Nazeefah rahoton komi a gidan nan ita kuma mak'irar seta ce ke ce kika kira kika sanar da ita."


  "Maamah ni bana son abu da tashin hankali da tada magana idan ma aiki suke tare wataran dubunsu ze cika dukda cewan ban yarda da hakan ba I know Nazeefah baza ta ta6a yimun haka ba."


  "Hmm Amal kenan ki bud'e idonki kisani yadda ka d'auki mutum ba haka yake d'aukanka ba ko a jinki kowa ne keda zuciya d'aya kamanki? Wallahi ba haka bane, balle wai har kice kin aminta da kishiyarki? Kishiyan da ba wacce take gaba dashi a fad'in duniya kaman ka? Ki bani izini inyi questioning mey aikin kin nan kawai."


  "Maamah please ki barta bana son k'ananun magana" Maamah bata saurareta ba ta mik'e "Maamah dan Allah ki dawo" ficewa tayi ta dawo da Safiyya biye a bayanta "Bani wayanki" ta buk'aceta. 


  "Waya na kuma?"


  "Eh wayanki."


  "Lafiya?"


  "Wani abun kike 6oyewa ne?"


  "Wani irin magana kuma kike Aunty? Mey zan 6oye?"


  "Good then pass me your phone" hannu ta mik'a mata tana jiran ta sanya mata shi aciki bayan Saffiya ta d'au lokaci ta sanya wayan cikin hannun Maamah cike da fargaba. 


  "Amal ya numban Nazeefan yake?"


 "Maamah dan Allah ki bata wayanta ni bana son matsala."


  "Mstw" wayan Amal taja ta bud'e ta latsa numban Nazeefah had'e da zubawa cikin wayan Safiyya sede da mamaki taga babu numban a wayan Safiyya how can it be possible? Ta tambayi kanta. 


  "Babu ba?" Amal ta tambayeta kai zalla ta gyad'a "Ai na fad'a miki ba su bane dan Allah ki bata wayarta amshi Safiyya kiyi hak'uri."


  Amsa tayi tace "Ba komai Aunty Allah k'ara miki lafiya" da haka ta fice.


  "This can't be possible wallahi ina ji a jikina 'yar nan munafuka ce."


  "Maamah please enough gashi de kin gani ko lamban Nazeefah bata dashi kuma bataje boko ba bale kice ta haddace lamban ne akanta ranan lamban ta na tambayeta amma bata sani ba, babu yadda za'ayi kuma ace ta haddace na Nazeefah, na gaya miki ba had'in Safiyya da Nazeefah."


  "Hmm toh mey gadin kine? Wallahi dole akwai wanda yake fad'awa Ya Afzal abubuwan nan ko kina tsammanin shi yake zama yake shirya zancen?"


  "I will not be surprised idan shi yake shirya komi Maamah saboda a fili yake nuna mun na fita a kansa baya sona ban ta6a tsammanin Yaya zemin haka ba watarana wallahi yanzu nake nadaman auransa da nayi nasan ko da wasa Ya Abdul baze ta6a yimun haka ba."


   "Kar ki ce haka Amal Ya Afzal mijinki ne har yanzu."


  "Maamah I miss Ya Abdul I miss him so much" hugging nata Maamah tayi yayinda ta cigaba da bata hak'uri. 


   "Amal be kamata mu nad'e hannu mu zubawa koma wa yake miki wannan aika-aika ido ba we have to do something."


   "Mey zamuyi toh Maamah? Ba muda hujja bamuda komai."


   "Ido ya kamata ki sawa mey aikin kin nan wallahi ina ji ajikina itace munafukar lamarin nan." 


  "Nace miki ki cire Safiyya daga lamarin nan."


  "Hmm toh ke yanzu haka zaki cigaba da zama a gidan nan Ya Afzal na cusa miki bak'in ciki yana miki walak'anci har seya kasheki tukuna? Da wanne zakiji? Da laulayi ko kuwa da masifan miji?" 


  "Maamah tunda nasan ni banyi masa komai ba ya cigaba da koma mey yakeyi tabbas wataran Allah ze wanke ni kuma shi zeji kunya, zan cigaba da kai kuka na wa Allah ai shi ba azzalimin bawa bane."


  "Haka wannan yake amma ki kira Mami ki sanar da ita wannan k'aruwan da kika samu."


  "I'll amma ba yanzu ba saboda nasan one way or the other magana ze kai kunnen Yaya idan har na sanar da Mami abinda bana so kuma kenan bana son Yaya yasan ina da ciki."


  "Amma ai ya kamata ya riga kowa sani tunda shine mahaifin abinda ke cikin naki, Amal you can't do this on your own."


  "Ki yarda dani idan nace miki Yaya yana iya denying baby'n nan yace ba nashi bane tunda har ya iya bud'an baki yace mun ina kawo masa maza gida."


  "Wallahi Ya Afzal na tattare da babban asara tunda de kome aka gaya mishi hawa yake ya zauna akai ba tare da yayi bincike ba, sannu kinji?"


****

  Yini ranan Maamah tayi mata se wajajen biyar da rabi ta tafi. Seda Safiyya ta tabbata Amal tayi bacci ta dannawa Nazeefah kira lokacinda tasan Afzal bai gida ya fita masallaci. 


  "Hello Aunty?"


  "Ya zaki kirani warhaka idan da Ya Afzal na gida fa?"


  "Aunty naga kaman lokacin isha yayi ya fita sallah ne."


  "Idan da kuma bai fita ba fah? Ba nace se ya fita office zaki na kirana ba?"


  "Aunty kiran gaggawa ne."


  "Meya faru?"


  "Wallahi Aunty ciki take dashi."


  "Ci mey!" Nazeefah tasa wani d'ankaren ihu. 


  "Wallahi ciki take dashi."


  "Innalila..inna..innalila" dan rikicewa tama kasa k'arisa salatin yayinda cikinta ya d'au ruwa. Yau ga ranan da ta jima tana gudu. "Amal nada ciki kikace?"


  "Eh Aunty."


  "Wayyo na shiga uku na lalace ya kika gane? Kinsan ba a wasa da zancen ciki ko?"


  "Wallahi ba wasa ba Aunty, tun rananda Uncle ya tafi ta ke zazza6i da amai d'azu wata k'awarta tazo sena ji suna tattauna wallahi ciki ne da ita."


  "Yau na mutu na lalace taya Amal zatayi ciki gabani na? Wallahi baze yuwu ba koda sama da k'asa ne zasu had'u se na san yadda zanyi na zubar da cikin nan wallahi bazata haifesa ba."


  "Aunty gashin be isa haka ba? Wallahi Aunty ta fara zargi na kokuma ince k'awarta, k'awarta ta fara zargi na d'azu harda amsan wayana ta zuba lamban ki aciki da ace nayi saving da shikenan sun kama mu."


  "Wata mak'irar k'awarce take neman rusa mun plan bayan na kusan cimma burina?"


  "Wata wai Maamah."


  "Safiyya aikin mu ya koma baya be kamata ace Amal nada ciki ba nashiga uku amma Ya Afzal be sani bako?"


  "Gaskiya da wuya kinsan basu magana."


  "This's the only opportunity I have ya zama mun dole in zubar da cikin nan kafin su shirya dan muddin suka shirya shikenan nawa ya k'are ya zamuyi? Be kamata mu bari Ya Afzal ya gano Amal na d'auke da cikinsa ba."


  "Toh ya zamuyi Aunty ni Wallahi tsoro nakeji kar a kama ni, ko a haka muka bar Aunty ta sha wuya, ya isa haka please."


  "Wawiya ki saurareni gobe Afzal ze dawo mata inason ki taho mu had'u dake inda muka saba an gama rubutun zan baki seki je ki sa mun cikin wardrobe nasa ta k'ark'ashin kayakinsa kina jina?"


  "Eh Aunty."


  "In shaa Allahu daga gobe zaman Amal a gidan ya k'are na tabbata idan Ya Afzal ya karance rubutun nan se ciwon zuciyansa ya kusan tashi daga nan seya buga mata saki ta tattara tabar gidan mu samu mu zubar da cikin kowa ya huta."


  ***

  Ba k'aramin rama Amal tayi ba acikin wannan kwana biyu sosai cikin yake bata wuya d'an kumatun da take da shi ma tuni suka zube ta kuma yi duhu. Yau da yamma ana neman shida Afzal ya dawo gida sannu da zuwa Safiyya tayi masa sannan ya wuce d'aki ya rage kayan jikinsa ya bud'e wardrobe nasa ya sanya wasu files aciki ya sake kullewa sannan ya fito parlour. 


  "Amal na gida ne?" Ya tambayi Safiyya. 


  "Eh tana d'akinta."


  "Batun maganan da kikayi mun ranan shin dagaske ne Amal ta shigo da wani gidan nan?" Har yau zuciyarsa ta kasa aminta masa da hakan. 


  "Uncle meyasa zan fad'a maka abinda idanu na basu gane mun ba? Ni tasa na kawo masa drink da snacks wallahi ka yarda dani."


  "In tambayi mey gadi? Kisani idan har sharri kikayi mata ina iya 6a6alla ki a gidan nan." Sosai cikin Safiyya ya d'au ruwa yadda Afzal yake maganan sam ba wasa tattare da shi. 

 

  "Kasan Malam Ahmad da zama a majalisa kuna fita shima yake fita se lokacin dawowanku ya ke shigowa da k'yar idan yana nan Aunty ta shigo in kuma baka yarda dani ba muje a gabanta ka tambayeni a idonta in shaa Allahu amsan dana baka zan sake nanatawa saboda ba k'arya nake yi maka ba."


  Sajen fuskansa ya shafe cike da mamaki da kuma rashin sanin abunyi gabad'aya kansa ya d'aure. "Shikenan mey kuka girka?"


  "Babu Aunty bata ji dad'i ba kwana biyu so bata girka komi ba nima batace in girka komi ba kuma."


  "Bata da lafiya?"


  "Eh."


  "Meyake damunta?"


  "Toh nima ban sani ba gaskiya."


  "Ina take?"


  "Tana kwance a d'akinta tana bacci nakega."


  "Jeki ce mata ta shirya driver ya kaita asibiti."


  "Toh" ta amsa ta fice sallama tayi bakin k'ofan Amal sannan ta shiga ta k'arisa ciki had'e da durk'usawa daga gefen gadon. 


  "Wani abu ne?" Amal ta tambaya. 


  "Uncle ne ya dawo."


  "In yunwa yake ji seki dafa masa abinci kinsan banida lafiya ban iya nayi girki ba."


  "Eh na sanar dashi."


  "Rashin lafiyan nawa?"


  "Eh."


  "Meya kaiki? Ni na aike ki?"


  "Kiyi hak'uri Aunty yanzu de yace ince miki ki shirya wai driver ya kaiki asibiti."


  "Kice mishi nagode bana buk'ata."

 Sak abinda Amal ta fad'a mata taje ta fad'awa Afzal a fusace yace, "Ki ce mata ta shirya ba wasa nake ba." Haka ta dawo ta fad'awa Amal inda Amal ta sake turata kice mishi "Nace bazan je ba."


  "Uncle wai bazata je ba" a fusace ya k'arisa d'akin had'e da bankad'e k'ofan na sosai Amal ta tsorata. 


  "Ki tashi a kaiki asibiti nace."


  "Nace bazan je ba nagode."


  "In ta halin ki za a bi a jinki ko kallon ki zanyi ne a gidan nan? Karki 6ata mun rai Amal ki tashi driver ya kaiki asibiti."


  "Nace bazan jeba Yaya ana dole ne?"


  "Rashin kunya kuma zakiyi mun? Ki cigaba Amal zamuga inda wannan banzan d'abi'ar zata kaiki" bata sake ce masa komai ba har yaja k'ofan ya fice. Wani irin masifaffen kuka ta rushe da, maghrib nayi ta mik'e tayi niyya bayan sallan Isha ta sanya hijabi ta fito waje takawa take wane wacce k'wai ya fashewa aciki har ta wuce Afzal dake zaune a parlour yana aiki akan laptop nasa, be ce mata komi ba itama bata ce da shi ko k'ala ba. Chan bada dad'ewa ba yana zaune kawai ya fara jin sautin amai daga kitchen besan lokacinda yayi wulli da laptop nasa ba ya nufi kitchen d'in inda ya tarar da Amal tsugune jikin sink tana ta kwararo amai. Na matuk'a ta basa tausayi kad'an ya rage beje ya rungumeta ba amma ya dakatar da kansa. Kallonta ya cigaba dayi har tagama ta d'auraye bakinta zamewa k'asa tayi don yadda bata da k'arfin ko sisi sosai Afzal yake ji ajikinsa duk yadda yaso shareta hakan ya gagara besan a lokacinda ya k'arisa ciki ya shiga d'agata ba. 


  "Ka sauke'eni bana so I can take care of myself" ta fad'a a galabaice sede be saurareta ba ya d'agata sama chak be sauk'eta a ko ina ba se akan kujera a parlour "Safiyya!"


  "Na'am Uncle" ta amsa had'e da fitowa daga d'akinta. 


  "Wuce ki d'auko mun key'n mota na."


  "Ki dawo Safiyya nace maka bazan je asibiti ba" Amal ta fad'a a kasalance "Zo ki tayani in mik'e Safiyya" ta buka'ceta har Safiyya ta shiga takowa gun Amal Afzal ya dakatar da ita "Nace kije ki d'auko mun key'n mota na ko?"


  "Uncl-"


  "Bakiya ji ne?" Har ta shiga takawa zuwa d'akin nasu Amal ta tsayar da ita "Nace kizo ki tayani in mik'e baki jini bane?"


  "Uncle dan Allah ka bari in taimaka mata kayi hak'uri" ta fad'a tana kakkarwa. 


  "Kije idan kika kashe kanki seki huta kowa ma ya huta" yace da Amal ko kallonsa batayi ba ta jira Safiyya ta taho ta taimaka mata ta kaita d'aki. 


  "Sannu ko Aunty?"


  "Ki had'a mun black tea please."


  "Toh Aunty" da haka ta fice nan da nan ta had'o mata tean tazo wucewa d'akinta Afzal ya kirata chak ta tsaya had'e da tsugunawa. 


  "Na'am Uncle?"


  "Meyake damun Amal? Karki yi mun k'arya."


  "Uncle wallahi ban sani ba zazza6i tace mun."


  "Kin ganta taje asibiti?"


  "Gaskiya a'a tunda ka tafi ko makaranta bata sake fita ba" ta mai k'arya gudun kar ya gano gaskiyan al'amarin. 


  "Ya jikin nata?"


  "Tace in had'a mata tea."


  "Shikenan kina iya tafiya." Yana kammala abinda yakeyi ya rufe laptop d'in ya koma d'akinsa towel yaja ya shiga bayi ya watsa ruwa fitowansa ya nufi wardrobe nasa yana neman shorts da ze sa k'ark'ashin wani wandon da yakeda niyyan sanyawa da fari Safiyya ta ajiye takardan da Nazeefah ta bata har ze janye wandon seya fasa ya hango wani a sama, zara yayi ya sanya sannan ya kwanta sede ya kasa yin bacci se tunanin Amal kawai yake tuna yadda take amai d'azu kaman wacce ke neman harar da hanjin cikinta. Shin meyake damunta? Ko da wasa k'wak'walwarsa be kawo masa ciki ne da ita ba. 


   Washegari Amal ta d'an samu sauk'i don haka ta shiga shirin makaranta koda ta fito ta tarar da Afzal zaune kan dining yana karyawa bata yimai magana ba harkan gabanta kawai ta cigaba da yi. Sosai ya sha mamakin yadda ya ganta back on her feet contrary to yadda take jiya kaman wacce zata mutu. Sosai yake son tambayarta ya jiki amma ya kasa har yanzun haushinta yake ji na abubuwan data ringa yi masa tana gama abinda zatayi tayi ma Safiyya sallama yana jiran ko zata tambayesa kud'in makarantar ta yaga kawai ta fice.


   K'arfe biyu Afzal ya dawo daga office lokacin Amal ma har ta dawo tana zaune a d'akinta tana karatu, d'akinsa ya wuce bayan Safiyya tayi masa sannu da zuwa. Kayan jikinsa ya rage ya fad'a bayi ya watsa ruwa fitowansa ya nufi wardrobe nasa dan neman kayan da zaisa a garin haka takardan da Safiyya ta sanya a tsakankanin wandunansa ya fad'i hannu yasa ya d'aga tare da bud'ewa in da ya soma karancewa kaman haka;


  _To my most beloved soul on earth (Ya Abdul) I write this with a very heavy heart. Darling words cannot describe how much I miss you, I miss you terribly I wish I hadn't sacrificed your love for Ya Afzal cause it's true he doesn't deserve my love, I regret the day I chose him over you, Ya Abdul I wish you were here to cry along with me and take my sorrows away, I wish you were here to fight for me and set me free from this miserable torture. If I were to be given another chance, I would choose you a thousand times over Ya Afzal. Ya Afzal is such a heartless demon now that I've thought of it I just realized it was never love he really felt for me but rather lust. All these while he's been after my body and now that he's gotten what he's wanted he treats me more like a maid than his wife, Ya Abdul you're the one I truly love and not Ya Afzal I'll never love a heartless demon like him, I so hate him and I hate destiny even the more for separating me from you. My love for you will never die Habibi it's still fresh like an open wound and I shall continue to hold onto it, I believe that one day you'll come back to me, I will forever love you Ya Abdul. Life without you is so dull and colourless I need you to brighten up my world and wake me up from this horrible nightmare-_


   Afzal be k'arisa karancewa ba ya fad'i a k'asa bisa ga wani irin k'una da ciwon da zuciyansa ya shiga yi masa birgima ya shiga yi wajen yana rik'e dai-dai saitin zuciyansa yayinda idanunsa suka kad'a sukayi ja zir cike da wahala ya d'age carpet ya 6oye takardan aciki. Wayansa ya shiga lalima amman yayi masa nisa haka ya cigaba da birgima a wajen har seda ya sume chan Safiyya da ta gama had'a masa abincinsa tayi sallama bakin k'ofan. 


  "Uncle na gama" takai minti biyu tana magana bakin k'ofar amma shiru dan haka taje ta samu Amal. 


  "Lafiya?"


  "Aunty uncle ne yace in dafa masa farar spaghetti ya taho da sauce gashi na gama naje kiransa ina ta sallama bakin k'ofar d'akinsa amman shiru."


  "Hala wanka yake ki jira idan ya fito."


  "Toh" da haka ta fice bayan minti kusan biyar amma bata ji hayaniyan Afzal ba ta koma bakin k'ofan inda ta cigaba da yin sallama amma ba response d'akin Amal ta koma ta sanar da ita shiru fa har yanzu. 


  "Safiyya kina damuna kije mana ki lek'a d'akin halan bacci yake." Da haka ta koma d'akin ta bud'e k'ofan wani irin rikicaccen ihu ta k'urma bisa ga sumammiyar jikin Afzal da ta tarar a k'asa. 


   "Auntyy!!!" ta k'urma wa Amal kira ba shiri Amal dake kwance ta zabura tana tambayan ko lafiya har ta iso bakin k'ofan inda Safiyya keyi mata nuni da cikin d'akin a rikice. Lek'a d'akin da Amal tace zatayi itama ta k'urma wani d'ankaren ihu had'e da k'arisasa da salati a guje tayi kan Afzal had'e da aza kansa akan cinyarta tana bubbuga fuskansa "Yaya? Yaya? Yaya please wake up" ba shiri ta shiga yin kuka "Yaya I'm terribly sorry dan Allah kayi hak'uri ka tashi na shiga uku Safiyya kije ki kirawo driver" a guje Safiyya ta fice Amal se kuka take a wajen yayinda take kakkarwa "Yaya dan Allah karka tafi ka barni I'm so sorry please don't go." Mik'ewa tayi ta janyo kayansa ta sanya masa sannan driver ya k'arisa ya cicci6esa sukayi mota duka har da Safiyya. Tunda aka shige da Afzal emergency room Amal keta safa da marwah bakin corridon gabad'aya ta rasa nutsuwarta tsabaragen yadda ta tsule ko Mami ta kasa kira bale su Ummi. Safiyya ce ta kira Nazefah ta sanar da ita, ita kanta Nazeefah bata d'au hakan ze tayar wa Afzal ciwonsa ba sosai ta rikice yanzu idan hakan kuma ya zame sanadiyan mutuwansa? Da ko itace da babban asara. Sarai tasan Afzal bayi so idan ciwonsa ya tashi iyayensa su sani amma da gan-gan dan aga laifin Amal ta kira Ummi ta sanar da ita akan Afzal ya samu attack ba shiri Ummi ta kira Abba ta sanar da shi. 


   Kaman daga sama kawai Amal taga Nazeefah na shigowa bada dad'ewa ba sega Ummi har ma da Abba. Yau nata ya k'are 'hasbunallahu wa ni'imal wakeel' kawai take ta nanatawa. Kanta suka yo duka suna tambayarta meya faru Amal ta kasa magana se hawaye kawai daga k'arshe suka koma kan Safiyya. 


  "Wallahi ban sani ba ya shigo gida yace in dafa masa spaghetti bayan da na gama naje nayi mai sallama amman shiru se nida Aunty mukayi zaton ko wanka yakeyi chan da shirun yayi yawa na sake duba shi bud'e k'ofan da zanyi kawai na tarar da sumemmiyar jikinsa a k'asa."


  "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" Ummi ta furta cike da tashin hankali. 


  "Dole akwai abinda akayi masa" cewan Nazeefah dake ta faman kukan munafirci "Sanin mune nan duka ciwon Ya Afzal bai ta6a tashi kazai haka dole saida sanadi" Nan ta kewayo kan Amal da gaban hijabinta ya jik'e jak'ab da hawaye. "Amal mey kikayi wa Ya Afzal? Sanin kowa ne kece sanadin ciwon sannan mey kikayi masa?"


  "Nazeefah wani irin magana kike haka? Har kina tunanin zanyi wa Yaya abinda ze tayar masa da ciwonsa da gan-gan? Wallahi banyi wa Yaya komai ba wallahi ban mishi komai ba Ummi" ta sanar dasu cikin tsan-tsan kuka. 


  "Taya zakice baki yi masa komai ba Amal bayan kinsan kece sanadin ciwon nasa? Bayan sarai kinsan da zaran kinyi masa abinda zuciyar bata so ciwon na iya tashi yet you still went ahead kika k'untata masa. Idan ban manta ba jiya kafin Ya Afzal yabar gidana seda yace kina yi masa abubuwan da baya jin dad'insu amma baze yi miki magana ba saboda yana gudun 6acin ranki meyasa ke bazaki mishi haka ba ki nisanci duk abinda ze 6ata masa rai?"


  "Nazeefah ki yarda da ni Ummi, Abba wallahi ban yi wa Yaya komai ba."


  "Ummi wallahi ita ce ita ta janyo komi koda rasa ransa Ya Afzal yayi kisani kece sanadi Amal kuma bazan ta6a yafe miki ba idan wani abun ya samesa" nan ta fad'a jikin Ummi tana kuka. 


  "Amal me kikayi wa d'ana? Mey kikayi wa Prince? A tunani na kece mace ta k'arshe da zata guji yi masa abinda zuciyarsa bata so meya faru Amal?"


   "Hajiya Mariam ya isa haka please mu jira likitan su fito tukuna" da haka Abba ya samu ya toshe wa Nazeefah da Ummi baki koda kowa ya nemi waje ya zauna Amal ta kasa zama se safa da marwah take a wajen chan globe na bakin k'ofan da akeyi wa Afzal aiki aciki ya mutu nan suka duk'ufa suna jiran fitowan Dr. Kusan a tare duk suka jefa masa tambaya. 


  "Humm!" Dr'n ya sauk'e nauyayyan numfashi "Bazan 6oye muku ba ku sani by each attack da yake samu hakan na weakening rate and efficiency na heartbeat nasa ku magance masa matsala tun ba yau ba kun kasa kun zuba masa ido ranan da zuciyan ta buga gabad'aya shikenan se ku huta muma mu huta."


  "Yanzu ya jikin nasa?" Abba ya tambaya. 


  "Munyi masa abinda zamu iya sauran ku jira ya farfad'o d'ayan ku ya biyoni ya amshi list na drugs da za'a sai mishi." Abba ne yabi bayansa ya rage su Ummi. 


  "Ummi dan Allah kibar kukan haka" cewan Nazeefah tana share mata hawaye. "Amal kin de ji abinda Dr'n Ya Afzal yace ko? Rayuwan Afzal yayi depending akan ki ne dan Allah ki kiyaye k'untata masa idan baki damu da shi ba mu nan we love and care about him."


  "Nazeefah-"


  Katse ta tayi da wuri "Ummi wallahi tun ba yau ba Ya Afzal yake mun complaining akanta gashi yanzu seda ta kwantar mana da shi."


  "Nazeefah wallahi bani bace dan Allah ki yarda dani."


  "Toh wa kikeso a zarga idan ba ke ba Amal? Ummi dan Allah ki sa baki."


  "Amal dan Allah ba dan ni ba dan Allah nace kiyi hak'uri ki rufa mun asiri ki na yima Afzal abinda yakeso kin fi kowa sanin halin da yake ciki" Ummi ta rok'eta cikin kuka. "Na sani ba koda yaushe Afzal yake da dad'i ba amma dan Allah kina hak'uri da shi kina yi mishi abinda yakeso please Amal I can't afford to lose him shi kad'ai Allah ya bani."


  "Ummi dan Allah kiyi hak'uri I'm so sorry, please forgive me."


  "Shikenan bari in shiga in duba sa" ta kai kusan minti goma aciki sannan ta fito har anan Afzal be tashi ba tana fitowa sega Abba nan shima ya dawo da magunan Afzal wanda ya mik'a wa Ummi. Bayanta ya bi ya shiga ya duba Afzal shima bayan ya fito ya buk'aci Nazeefah next da ta shiga, k'arshe Amal  ta shiga. A hankali ta k'arisa cikin d'akin ta zauna daga gefensa tare da sa hannunta cikin gashin kansa tana shafawa a hankali. 


  "Yaya I'm so sorry dan Allah ka tashi ka fad'a musu bani bace" kuka ta shiga yi sosai a wajen a hankaki ta kwantar da kanta a k'irjinsa yayinda kukan nata ya tsananta "Yaya please wake up wallahi ban aikata ko abu d'aya daga cikin ababen da kake tokari na dasu ba wallahi wasu ne suke neman shiga tsakanin mu Yaya bazan ta6a aikata abinda nasan ze 6ata maka rai ko zubar maka da mutunci ba you have to believe me and stop bothering yourself I beg of you please" a hankali ta d'ago da kanta tare da had'a hannunsu gu d'aya "I love you so much and no matter what I'll never leave your side" a hankali ta sauk'e light kiss akai. Har ta kai ga mik'ewa taga ya motsa yatsansa zamanta ta gyara ta shiga kiran sunansa har seda ya bud'e idonsa. 


  "Yaya you're back!" Tayi exclaiming ba shiri tayi hugging nasa sede ko ta6a jikinta beyi ba gabad'aya ji yayi ta haramta masa tunda har yanzu Abdul ne a zuciyarta. A hankali ta d'ago daga jikinsa "Yaya what happened?" ta tambayesa had'e da zira hannunta cikin gashin kansa. Kan nasa ya shiga girgizawa da nufin baya so a hankali ta maida hannun nata "I'm sorry" tayi apologizing. 


  "Su Ummi suna waje bari inyi musu magana su shigo" kansa taga ya kawar gabad'aya dan ko kallon ta baya sha'awan yi ko a mafarki akace masa Amal zatayi masa haka baze yarda ba kuma ba abinda yafi tsana kaman wannan munafikin halin hawainiyan nata, zatayi abu kuma ta zagayo kaman batayi komi ba tana proving innocence. Ko a ina yaci karo da rubutun chan yasan nata ne. 


  "Yaya har yanzu fushi kake dani? Yaya wallahi ban aikata ko d'aya daga cikin abubuwan da kake tokarina dasu ba Yaya sanin kanka ne ina sonka kuma bazan ta6a yin abinda ze 6ata maka rai ko zubar maka da mutunci ba you have to believe me."


  "Ki kira mun Ummi da Nazeefah" yace da ita zalla ba tare da ya kalleta ba hawayenta ta share sannan ta mik'e "Allah baka lafiya" ko ta kanta beyi ba har ta fice


  "Ya Afzal ya farfad'o Ummi."


  "Ya farfad'o?" Ummi ta tambaya had'e da mik'ewa. Haushi Nazeefah taji wato seda Amal ta shiga ne ya ga daman tashi akan duk uban kalaman soyayyan da tayita fad'a masa? Duk su kwantar da hankalinsu soon enough ze saki Amal d'in. 


  "Yana buk'atan ganinki da Nazeefah."


  "Alhamdulillah! Alhamdulillah" ta mik'a godiyar wa Allah. 


  "Abba fah?" Amal ta tambaya. 


  "Ya koma" Nazeefah ta amsa. Tana ganin shigewansu ta kira Safiyya suka koma gida tunda baya buk'atan ta na mey zata cigaba da zama? 


  "Prince!" Ummi ta kira sunansa had'e da hugging nasa "Prince dan Allah kayi a hankali wallahi likitanka na jiye maka."


  "Ummi please it's okay I'll be fine."


  "Welcome back Ya Afzal" Nazeefah dake tsaye akansa ta fad'a mai. 


  "Thank you Rabba'atul Bait" ya amsa yana mata murmushi. 


  "Prince meya faru? Mey Amal tayi maka?"


  "Amal kuma?"


  "Ka fara da zurfin cikin nan naka ko? Nazeefah ba ke kikace Amal ce bata kyautata masa ba?" Ido ya d'ago yana kallon Nazeefah da cikinta ya d'au ruwa tuni ta shiga rarraba ido. 


  "Haka nace miki?"


  "Ya Afzal naga.. ermm... Toh ai sanin kanmu ne duka nan Amal ce sanadin ciwon naka Ya Afzal ko ba kai ka fad'a mun ba?"


  "Se kuma nace miki Amal ce bata kyautata mun?"


  "Toh waye ne?" Ummi ta tambayesa "Wayene idan ba Amal d'in ba?" Shiru yayi bece komai ba dan haka Ummi tayi tunanin ko bayi son yayi maganan a gaban Nazeefah ne. "Ermm nace mey kakeso kaci Prince Nazeefah ta girka ta kawo maka? Girkin waye ne acikinku?" Ta tambayi Nazeefah. 


  "Girkin Amal ne amma ba damuwa zan girka in kawo masa mey kakeso Ya Afzal?"


  "Boiled potatoes da egg sauce" ya sanar da ita.


  "Toh bari inje zan dawo yanzu in shaa Allah." Tana ficewa Ummi ta dawo da kallonta akan Afzal "Toh Nazeefar ta tafi gaya mun meke faruwa?"


  "Ummi babu" mari me zafi ta kai masa akan cinya. "Ummi please! Kin fa san hannunki da zafi."


  "Ina tambayanka abu kana kallon cikin idona kana mun k'arya? Nace meya faru? Wallahi ka kuskura kayi mun k'arya toh ni da kai."


  "Ummi misunderstanding muka samu."


  "Fad'a kukayi?" Kai ya gyad'a mata "Amma mun shirya shigowantan nan."


  "Ka tabbata?"


  "Eh Ummi."


  "Ba senayi mata magana ba?"


  "Babu amfani komi ya wuce."


  "Toh koma meye ne de ka daina bin komi da zuciya haka kasan yadda zuciyar taka take da rauni please Prince Abbanka ma na nan ai d'azun ya tafi."


  "Allah sarki ku daina tada hankalinku please I'll be fine."


  "Zaka kwana ko zaka koma gida a yau?"


  "Kwana kuma? Na samu sauk'i se in kwana a asibiti? Nazeefah na kawo mun abinci naci zan koma gida."


  "Kana buk'atan wani abu toh?"


  "A'a zaki iya tafiya Ummi thank you so much."


  "Don't mention my boy Allah baka lafiya ko?" Kai ya gyad'a tare da amsawa yanayi mata murmushi. "Bari inyi ma Amal magana tazo ta tayaka zama kafin nan." Da mamaki ta nemi Amal bayan fitanta ta rasa ta dawowa ciki tayi tace, "Ban ganta ba fa, kode ta tafi ne?"


  "Ohh ban fad'a miki ba ko? Na ce ta koma kinsan itama kwana biyu bata ji dad'i ba zazza6i ya sata a gaba."


  "Haba! Shiyasa na ga ta rame Allah sarki Allah shi bata lafiya."


  "Ameen Ummi." Zama ya cigaba dayi cikin d'akin har zuwa lokacinda Nazeefah ta kawo masa abincin ita da kanta ta basa bayan da ya gama tayi ma likitin nasa magana akayi discharging nasu. Kasancewar kwanan Amal ne har cikin gida Nazeefah ta kaisa sannan ta juya ta wuce nata gidan. Sannu da zuwa Safiyya tayi masa lokacinda ya shigo ciki. 


  "Ina Amal?" Ya tambayeta. 


  "Tana d'akinta" k'arisawa d'akinsa yayi ya zaro takardan d'azun had'e da ninkewa ya adana. Wayansa ya d'aga dan kiran Sultan inda ya tarar da missed call na Abba nan take ya kirasa back suka gaisa Abba yake mishi jaje. Suna k'are wayan ya kira Sultan. 


   "Maza yane?"


  "Ba lafiya ba yanzu haka daga asibiti nake."


  "Subhanallahi meya faru ciwon naka ne?"


  "Yes and alot has happened Sultan ka shigo gobe kaji?"


  "Toh sannu ya Amal ko gun Nazeefah kake?"


  "Ni seka shigo kawai" tun daga amsan sa Sultan ya gane akwai matsala "Allah kaimu goben toh."


  "Ameen" Afzal ya amsa had'e da katse wayan. Zama ya cigaba dayi a d'akin chan bayan sallan Maghrib Amal tayi sallama cikin d'akin nasa shiru yayi yak'i amsawa dan haka ta bud'e k'ofan ta shiga kansa yayi saurin kawarwa. 


  "Yaya-"


  "Get out Amal bana k'aunan sake ganinki a cikin d'akin nan in shaa Allahu burin ki ya kusan cika kiban lokaci kad'an."


  "Yaya mey kake nufi? Wani buri?"


  "Just get out Amal in kuma fitan ne bazaki iya ba ina iya bar miki gidan gabad'aya."


  "Allah huci zuciyanka" tace mishi zalla ta juya ta fice d'akinta ta koma inda ta kwanta kan gado ta shiga kuka sosai. 


  Washegari kaman yadda Sultan ya mar alk'awari haka yazarce gidan nasu daga office da Amal suka fara had'uwa lokacin tana zaune a dining tana cin abinci sannu da zuwa tayi masa tasa Safiyya ta kawo masa drink da snacks. 


  "Kinyi wuyan gani amarya."


  "Ji Ya Sultan nice amaryar?"


  "Amaryar amini na ma kuwa ke baki san yadda nake ji dake ba ko?"


  "Uhm haka de kace amma ka barni da makaranta yana ta bani wuya."


  "Karde shiya ramar dake haka? Har kun fara tests ne?"


  "Ai mu kullum cikin tests muke Ya Sultan se a hankali."


  "Allah sarki ba three kike ba yanzu? Kinyi mey wuyan ai Allah sa albarka."


  "Ameen Ya Sultan yasu Umma?"


  "Lafiyansu k'alau Afzal fa yana gida?"


  "Eh ba motansa na waje ba?"


  "Na sani koya fita strolling ya jikin nasa?"


  "Toh Alhamdulillah de bari inyi mishi magana" nan ta mik'e ta nufi d'akin nasa sallama tayi amma be amsa ba dan haka ta bud'e ta shiga akan gado ta tsincesa yana bacci k'arisawa tayi had'e da tapping nasa a k'afa a hankali. 


  "Yaya? Yaya ka tashi Ya Sultan yazo" a hankali ya shiga bud'e idonsa har ya bud'e su duka ganin ita ne yayi saurin kawar da kansa "Bance kar in sake ganin ki acikin d'akin nan ba?"


  "I'm sorry Ya Sultan ne yazo ya turo in kira ka" da haka ta juya ta fice. Brushing yayi ya wanke fuskansa sannan ya sanya shiry akan gajeren wandonsa ya fito ya sami Sultan. Bayan sun gaisa ya ce mishi su k'arisa ciki. 


  "Meya samu nan d'in? Ko so kake mu koro Amal waje ita da gidanta?"


  "Bata d'akin come in" be sake musu ba ya mik'e suka k'arisa d'akin. Note na Amal ya d'au ya wulla wa Sultan akan cinya "Wannan fah?" Sultan yayi saurin tambaya. 


  "Ka bud'e kayi observing handwriting dake ciki" yadda aka ce da shi haka yayi bayan ya karance rubutun ya d'ago kai "Ehen?"


  "Here take a look at this handwriting" yayi maganan yana zaro takardan d'azun daga inda ya 6oye "Handwriting na mutum d'aya ne ko kuwa?"


  "Of course na mutum d'aya ne mana" Sultan ya amsa bayan yayi comparing handwriting d'in. 


  "Thank you ka zauna da kyau ka karanta content d'in." Hankali ya miyar kai ya shiga karancewa yayinda mamaki ya mamaye mai fuska da zuciya. 


  "Waya rubuta wannan maza?"


  "Ka duba sunan dake jikin littafin" Afzal ya umarcesa. 


  "You don't mean this!" ya furta bayan daya duba yaga sunan Amal rubuce a bangon littafin. 


  "Yanzu zaka ga laifina idan na yanka mata ko wani irin hukunci?"


  "Ban fahimce ka ba Triple A kana nufin Amal ce ta rubuta wannan?" Ya tambaya da d'umbun mamaki. 


   "Baka iya karatu bane?"


  "I'm just confused Triple A, Amal de? Har Amal ce zata rubuta wannan abu? Kode kafin kuyi aure ne?"


  "Kana ganin sabon paper sabon rubutu kana zancen kafin muyi aure?" 


   "Amma meya faru? Meyayi zafi da har Amal zata rubuta wannan abu a matsayinta na matarka?"


  "Gata chan a chan d'akin kana iya zuwa ka tambayeta."


   "Wow!" Ya numfasa totally speechless. 


  "Maza ban san meyake damun Amal ba yarinyar nan ta sauya gabad'aya ta koma wani abun daban banda munafurci da had'a kaina da Nazeefah ba abinda takeyi ko tsinke na sai mata seta buga waya wa Nazeefah ta fad'a mata knowing right ba duka abinda nakeyi mata nakeyi wa Nazeefah ba sedan kawai ta 6ata ni idon Nazeefah tasa Nazeefah tayi mun kallon maras adalci hakan be isheta ba har course mates nata maza ta fara kawo mun cikin gidan nan suna zama a kujera d'aya."


  "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un wacce Amal tukuna? Amal Amal naka da na sani?"


  "Ita de Amal ta cikin gidan nan."


  "Maza are you sure of what you're saying? Amal ce har zata shigo maka da gardawa cikin gidan nan?"


  "In kira maka mey aikinta ne ka tambayeta?"


  "Subhanallahi meya sameta?"


   "Waya san mata ne?"


  "Mey kake nufi kenan yanzu kana nufin kana zargin Amal kenan? Kana zargin tana ci maka amana?"


  "Nooo not at all nasan Amal baza ta ta6a cin amanan aurena ba, ko tunanin yin hakan ma baza tayi ba I know that."


  "Toh mey kake nufi da tana shigo maka da maza gida?"


  "Yes ta daina shigo mun da coursemates nata saboda ba'a san abinda shaid'an ze iya raya musu ba wataran koba d'abi'arta bane wataran shi gardin ze iya kwad'aitar mata da hakan ko ba ka gane abinda nake nufi ba?"


  "Sosai na fahimce ka amma Afzal I'm still shocked Amal da muka sani ce ta sauya haka take yin ababen nan da ka irgo? Innocent Amal taka?? Na tabbata haka kawai Amal bazata sauya halayanta ba sede idan kai kayi pushing nata don't you forget that for every reaction there's an action."


  "Mey zanyi mata maza? Kafi kowa sanin irin son da nake yiwa yarinyar nan, Wallahi Amal bata ta6a neman abu a guna ta rasa ba komi ina yi mata da iyayenta amma ka kalli da abinda zata sak'a mun kuma abinda yafi bani haushi shine k'aryata komi da takeyi har yanzu ita bata amince da laifukanta ba bale ta nemi tuba mu sasanta tsakanin mu ni bazan iya ba, I can't do this anymore I'm tired of her sick behavior."


  "Mey kake shirin yi?"


  "Ba Abdul kowa take so ba? Seta je ta samesa."


  "Wani irin magana kake haka Afzal? Da igiyan auranka akanta kake son taje ta auri wani?"


  "Sawwak'e mata zanyi."


  "Mey?? Kana da hankali kuwa Afzal? Wani irin zafin kishi ne da kai haka?"


  "Toh mey kakeso inyi? Ba gara na sawwak'e mata ba taje ta samu shi wanda take son? Bazan iya zama da ita ba knowing zuciyarta na tare da wani gara na rasata gabad'aya dan idan har na cigaba da zama da ita toh zan cigaba da kallonta da abin ne wanda zuciya ta baza ta iya d'auka ba wataran sede ta har6a tabar aiki."


   "Idan ka sawwak'e mata ta koma gun Abdul kai kuma fah?"


  "Na sani sena fita shan wuya bayan rabuwan nan amma ka gaya mun mey riban ajiyeta a wajena idan zuciyarta na tare da wani daban Sultan? I love Amal kuma har duniya ta nad'e bazan fasa sonta ba but this is not reason enough to keep her with me tunda gashi da hannunta ta rubuta bata sona tayi nadaman aurena. Kaji fa har cewa take wai dama tun fari tasan jikinta kawai nake so yanzu da na samu abinda nake nema gashi ina walak'anta ta. Ni fa Maza? Ni d'in da ko hannunta ban ta6a sha'awan rik'ewa ba... excuse me" tari ya shiga yi yayinda zuciyansa ya fara tashi yana yi masa k'una tsan-tsan takaici da bak'in ciki da 6acin rai. 


  "Dan Allah kayi a hankali ba senun sake kaika asibiti ba it's okay ya isa."


   Gyaran murya yayi ya cigaba "So I think it'll be better idan na barta taje ta samu shi wanda take so d'in ta huta kowa ma ya huta."


  "Kai kuma fa Triple A? Ya zakayi da rayuwanka idan kuka rabu? Shin ka manta rayuwanka gabad'aya yana revolving ne a jikin na Amal? Shin ka manta idan ba soyayyarta zuciyarka bazata iya aiki ba? Shin ka manta idan ba ita a kusa da kai rayuwarka tana cikin gwagwarmaya? Ina ka mance da dukkan hakan Afzal har kake tunanin sawwak'ewa Amal? Besides ni ban yarda ma innocent Amal d'in da na sani zata iya aikata wannan munanan abubuwan da kake tokarinta da su ba. She's too innocent to do all these I know Amal kuma na yarda da ita."






RANA D'AYA!

#RD


Love... King Miemiebee👄✨


adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *