Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Sunday, January 24, 2021

Mafarki na complete hausa novels

adsense here

Mafarki na complete hausa novels

 👰🏼 *MAFARKI NA* 👰🏼
*Written by*💅🏻💅🏻

*Salmah Ali Wada*

       *(Aunty)*

*PURE MOMENT OF LIFE    WRITERS (P•M•L•W)**Both on true life story*
Page 1🔚


Dai dai matan fada  road danja ta tsayar da mu,garin leke leke irin nawa Idona yakai kan wata fara mota wani had'ad'd'en guy ne a ciki wayyo Allah na! Looking him handsome guy,


Da Sauri na kuma gyara glass din dake idona, nan naga ya kira wani mai saida counter ya siya dai dai nan danja ya bamu hannu cikin nutsuwa yaja motar sa inda me adai-daita mun shima yaja, wayyo amma guy din nan ya tafi da tunanin Salmah wayyo!


Har muka fara tafiya idona be bar kallon sa ba,sai da muka hau play over sannan ya bacewa gani na,


Wata nannauyar ajiyar zuciya na saki,murya mai adai-daita ne ya katse mun tunanin da nake "wai bamu zo inda zaki sauka bane",

" yi haquri gaban kad'an zan sauka"


Haka na shiga gida jiki na ba k'wari,Umma na iske a falo tna waya sai da ta gama sannan nace mata "Umma na dawo" "to kin gama komai" 


"Gobe  zan koma" " to Allah ya bada sa'a" nace "Ameen"


Na tashi zan tafi naji Umma tace "ke" tsayawa nai "lafiya kuwa na ganki wata iri kuma sai wani murmushi kike kamar wadda tai gamo"?


Hmm Umma ke nan gamo nai amma na alkhaeri na fad'a a raina amma a fili murmushi kawai nai mata nace " lah Umma bakomai" kawai weather d'in garin ne  tai min dad'i "to maza kije ki d'ora girki ni meeting zan fita before 2:00pm" naga ma komai amma gaba d'aya yinin ranar da tunanin unknown guy na huni.............. 


  

            ❤❤

               ❤


" waya na ne yai ringin da sauri na d'auka ganin me kira na,king of my hrt sunan da nasa masa,


" haba Salmah Queen kin san kuwa ynda na matsu lokacin yazo amma ki zance a d'aga kuwa, tab Ae ko ma mene k'ya karasa a gida na kwana nawa ya rage"


Cikin muryan shagwab'a nake magana "kasan had'a aure da karatu kuwa da wuya" " bawani nan anjima,zan kawo miki invitation card d'in sannan zan ma driver magana sai ki fad'an tym d'in da zai dinga zuwa" 


"Tom shikke nan baby sai anjima"


Kashe wayar nai tare da rungume ta ina wani murmushi ni kad'ai nasan irin son da nake ma Prince d'ina


Haka aka fara shirin biki gyara ba Wanda ban sha ba har wani kyau na k'ara sai dai kash! Gaba d'aya Umma tace na cema prince ya daina zuwa .


Tun ranar laraba aka fara kamu wayyo kar kuso kuga irin kyaun da Salmah tayi masha Allah,


Daman ga Salmah slim beauty,with chocolate skin,hmm pinky lips, and sexy eyes, duk Wanda ya ganta sai ya kuma kallon ta gaba d'aya prince jiyake kmar ya d'auke sabida kyaunta


Haka akai ta party iri iri like fruity day,Fulani day,mother's night, sisters day da dai sauran su ranar lahadi da misalin karfe 11:00 dubban mutane suka shaida auren masoyan,


Tunda naji maroka suna fad'a na fara kuka,

Baby kwata ce take tsokana ta "amarya d'auko Riga kin zama d'aukko hula" Ae kuwa tuni kuka na ya kara girmama take suka daina suka dawo bani haquri a haka har yamma tayi,


Aunty zainab k'anwar ma ce ta shigo "wai ina Salmah ne har yanxu baki shirya ba" 


"Aunty kinga Tun d'azu take kuka tak'i tashi ko abinci tak'i ta ci mama" ta fad'a


Cikin sigar lallashi aunty Zainab tasa nai wanka ta shirya ni cki wata exclusive supper wax sky blue ta nad'e ni da blue din lafaya sannan ta feshe ni da Arabian perform, tuni nai kyau


 waya k'awaye na suka Ciro suka fara yimin photo duk da fuska ta a rufe take amma naji suna fad'an kyaun da nayiNan akai min fad'a sannan aka wuce dani gidana


Haka jama'a sukai ta santin gidan wata mata naji tana magana " kai amma gidan ya dace da ita gata mai kyau gidan ma haka" "Ae kuwa wata ta cafe da  mijin ma mai kyau fatan dai Allah ya bada zaman lafiya" suka amsa da Ameen.


Haka aka watse aka barni  ni ka dai tsoro duk ya cika ni ga ynwa da tun safe ban ci komai ba,


Motsin tafiya naji da sauri na kuma rufe fuska ta cikin  muryar sa me dad'i yai sallamah a hankali na amsa


Gefe na ya zauna ya salam k'amshi turaren sa naji Wanda nake mutukar so


Zame min lafayar Dana rufe fuska ta yayi "tsarki ya tabbata ga Wanda ya halicci wannan surar, amma baby love meyasa kikai wannan kuka haka kamar wadda za'a kai ki gidan mak'iyin ki"?


Cikin ragowar kuka na nace" ni Umma " too "lallai an fad'a miki cewar bazaki dinga zuwa bane"?


Nan yai ta lallashi na, da kansa yaje kitchen ya d'aukko plate da cups kajin da ya siyo ya zuba sannan ya zuba fresh milk yago kazar yayi " to Salmah queen bud'e bakin" kau da kai nayi " "kai me kike nufi ne?"


"Ni na koshi" "ban yarda ba, bari naji Ae zan gane in baki ci abincin ba" ciki na ya shafa yar naji jiki na yayi,


"Kin ji cikin kamar bakomai a ciki koma kice kin koshi mazabud'e bakin ki kan nai miki dura" 


A hankali na bud'e ya kai hannu zai sakan ke nan......


Umma ta girgiza ni da karfi "ke wannan wane irin bacci kike haka tuntuni anyi sallahr asuba 


 firgigit na zabura na tashi  daga nannauyyan bacci 


"Kalli karfe nawa ynx Tun d"azu nake kiran ki amma naji ki shiru" a hankali na kalli agogon dake dakin 6:45 


"Kiyi haquri umma" "ke tafi ni tun jiya na rasa meke damun ki, maza kitashi kiyi sallah ki gyara gidan ni,  zan huce su husna skul" 


K'arfe 7:30 Umma suka fito

" Umma Allah ya kiyaye Hanya" "ameen"


Nan na gyara gidan na shiga wanka cikin wata doguwar Riga ta material orange da green na shirya na yfa green din mayafi da takalmi sai na dauko orange din jaka na zuba credentials dina na fita skul


Haka ma shiga skul department din mu na tafi ba mutane a ciki office d'in sectere na shiga 


Yana miko min wani file naji wani k'amshi ya doki hanci na ban dago ba na cigaba da abin da nake,


"Sannu malam" naji anfada cikin wata murya mai dad'i "yawwa Ahmad kashigo ne" "eh wllh" juyowar da zanyi wazan gani ya salam guy d'in jiya da nagani ne,

Ina kallon sa naga yana kallo na "sannun ki" ya fad'a yana min murmushi " a hankali nace "yawwa"


Parlon office d'in na fito na zauna a d'aya daga cikin kujerun office d'in ina k'ok'arin had'a takardun nawa zama yai kusa dani da yake a 3seater na zauna "can I help u"? Murmushi  kawai nayi  " muga credentials d'in" k'arba yai yna had'a min ta gefen Ido nake satar kallon sa,


Yana yi yana min baya ni ina d'agowa karaf muka had'a ido dashi a kunyace na sunkuyar da kai na, "OK zaki iya submitting d'in sa koda yake bari naga" ya tashi yashiga ina beyi dashi nan yai submitting ni kuma nai signing sannan muka fita 


"Nagode da kulawan ka" "ah bakomai" ynx sai ina"? Ya tambay "gida zan tafi" Tun yanxu bazaki zauna muyi hira ba" uhmmmm nayi wani murmushi Wanda ni kaina nasan in nayi yana tafiya da hankalin Wanda naima, 


"Ai zan yi girki ne kar Umma tadawo ban gama ba" " OK "


Nan muka tawo " to zo nakai ki mana" da sauri na kalle shi wani killer smiling yayi min "irin wannan kallo haka sai kace wadda nace zan sace" a'a kayi haquri nagode"  nan muka fara tafiya zuwa bakin gate "sunana Ahmad" muka had'a ido hmmm "nace name" 


"What of you"? " Salmah "

*Salmah queen*" ba zato ba  naji ya fad'a wallhi gabana har faduwa yayi,tsinkar muryar sa nayi yace " amma kamar ke nagani jiya" anyya kuwa kawai nace" Dan har ynx ban gasgata abinda kunne na yaji ba wai *Salmah Queen*


Banga wannan tunanin ba naji "tom Salmah queen can I have your number"? 


Kallon sa nai " ko rowar za'ae min?" "A'a" lalubar aljihu yayi "af kinga wayar yana mota ban taki naga" ba musu na mika masa  number d'in sa yasa sannan yai dialling tana shiga ya miko min " to Salmah queen sai minyi waya" "to nagode fa" na shiga adai-adaita shi kuma ya koma cikin skul.Ina komawa gida nai Sauri na fad'a kitchen Dan 1:00yayi waya na na dauka na tura masa da message Dan nagane number d'in


_Aslm thank for your concerns Allah ya kara zumunci_ 


Ko wayar ban ajiye ba kiran sa ya shigo "Salmah queen kinje gida lafiya" muryar sa ta doki kunne na  "lafiya lau"

"Pls I will call u lttr zan yi sallah" " to Ae mana  addu'a"


"Kar ki damu za'ayi" ya kashe wayar 


Tundaga wannan lokacin muke wani lafiyayyen mutunci


As usual ya kira ni da Salmah queen "am not deserve it fa" nace

     "Why you say dat wllh kin cancanci fiye da haka,ni ba wannan ba zan zo gidan Ku sabida akwai maganar da nake so muhi mai muhimmanci" 

" tom shikke nan Allah ya kawo ka lfy"


Ran da yace zai zo ban sami cikkaken bacci ba sabida d'auki da farin ciki,


Ranar da zai zo rnar Friday haka nai k'walliya  kamar ba gobe cikin wata atamfa pink da purple masha Allah ni kai na san nayi kyau ina zaune ina jiran zuwan sa amma gabana har faduwa yake misalin 5:00pm ya kira ni yace ya iso....dammmm kirjina ya buga..........*I wish my dream are converting to reality* 
ya Allah ka taimaken haka na fita kirjina na bugawa kamar fado koda me yazo min ohooo cikin sallama na isa inda yake yayi kyau yana sanye da k'ananan kaya..........Nan na kawo k'arshen wannan takai taccen littafin nawa *Mafarki na* both on true life story 


Abinda nai dai dai Allah yabani lada Wanda nai ba daidai ba Allah ya yafe min,fatan sako na zai fadakar da ku,


Ki kasance mai aji a matsayin ki na 'ya mace ba daga kinga namiji in kinji kina son sa ki fada masa ba,bance hakan yna da illa ba amma kusan halin namu na yanxu,bakowa ne zaki ce kina son sa yai miki kyakkyawar fahimta,kiyi addu'a kinemi zabin Allah indai har alkhairi ne sai kiva yazo miki da kansa in km ba alkhairi bane Allah ya musanya miki da Wanda ya fishi

 Allha ya bamu abinda yafi alkhairi Ameen•


*Taku har kullum*

*Salmah Ali Wada*

     *(Aunty)*💅🏻💅🏻Love you all my heart!!!😍😍😍😍😍


adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *